Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

GLOSS/404 Zazzaɓin Cizon Sauro (Malaria)

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
(Redirected from GLOSS/404)
Zazzaɓin Cizon Sauro <> Malaria
Jama’a, sallama alaikum. <> Hello everybody.
Kamar yadda kowa ya sani, cutar zazzaɓin cizon sauro annoba ce a ƙasarmu. Mun jima muna yaƙi da wannan cuta, amma har yanzu tana kashe mutane da yawa duk shekara. <> As everyone knows, malaria is an epidemic in our country. We have been fighting this disease for a long time, but it continues to kill many people each year.
Ko ka sani, a kowace shekara maleriya tana kashe mutane fiye da miliyan a duniya. A Nijeriya kaɗai kuma, tana kashe mutum dubu ɗari uku a kowace shekara. <> Did you know that malaria kills over a million people worldwide every year? In Nigeria alone, it kills 300,000 people each year.
Masu bincike suna ta neman wani maganin rigakafi na cutar maleriya. Amma dai, har yanzu ba a samu ba. <> Researchers are looking for a vaccination for malaria. But, as of yet, there is still no vaccination for malaria.
Amma jama’a, akwai abubuwa da dama da za ku iya yi domin kare kanku daga wannan cuta. <> But, people, there are many things that you can do to protect yourselves from this disease.
Da farko, ya kamata kowa ya yi amfani da gidan sauro. Ana iya samun gidan sauro a kowane asibiti. Kuma ba su da tsada. <> First of all, everyone should use a mosquito net. You can get a mosquito net at any hospital, and they are not expensive.
Na biyu kuma, kar ku bar ruwa ya yi zama a gidanku idan ba a rufe shi ba. Haka kuma, kar ku bar ciyawa ta tashi a cikin gida. Dalili shi ne: sauro yana haifuwa inda akwai ruwa da ba ta gudana. <> Secondly, do not leave water uncovered in your home. Also, do not allow grass and weeds to grow in your home. The reason is this: mosquitoes hatch where there is standing water.
Ya kamata kowa ya san alamun cutar maleriya. Ga wasu alamun cutar: <> Everyone should know the symptoms of malaria. Here are some of the symptoms:
Akwai zazzaɓi mai zafi da rawar dare. Za a ji ciwo da tsami a jiki. Za a kuma ji gajiya sosai. Haka kuma wane lokaci za a yi amai. <> A person will have a high fever and chills. They will feel aches and pains. They will also be very tired, and sometimes there will be vomiting.
Idan an fara ganin iri wannan alamu, ya kamata a je wurin likita domin a tabbata maleriya ce ko a’a. Idan yaro yana da irin wannan alamu mai muhimmanci sosai a je wurin likita. <> If a person starts to notice these symptoms, they should go to the doctor in order to verify if they have malaria. If a child shows these symptoms, it is very important to go to the doctor.
A tuna fa, ba mu da maganin rigakafi na cutar maleriya, amma akwai maganin da zai taimaka waje warkewa daga cutar. Yawancin lokaci, idan mutum ya samu magani daga likita zai warke daga cutar. <> Remember, there is not a vaccination for malaria, but there is medicine that will help a person to recover from the disease. Usually a person who is treated by a doctor will recover from the disease.
Kar mu mance yara ne suka fi fuskantar kasada ta mutuwa daga cutar maleriya. Cutar maleriya ita ce ta fi kashe yara a nahiyar Afirka. Domin haka kar ku makara wajen kai yara wurin likita. <> Do not forget that children are at the greatest risk of death from malaria. Malaria is the biggest killer of children in Africa. Because of that, do not delay in taking your children to the doctor.
Mu haɗa kanmu mu hana wannan muguwar cuta a gidajemu, da kuma a duk faɗin ƙasarmu. <> Let’s work together to prevent this horrible disease in our homes and in our country.
Allah ya bada alheri, Amin. <> May God bless you.