Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

GLOSS/405 Ku Bar Shan Taba (Quit Smoking)

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
(Redirected from GLOSS/405)
Ku Bar Shan Taba! <> Quit Smoking!
Jama’a salama alaikum. Ya kamata kowane mai shan taba sigari ya zo kusa ya saurara. <> Greetings everyone. Every smoker should listen carefully.
Muna da sabon shirin da muka kafa a asibitin Murtala. Wannan shiri zai taimaki duk wanda yake so ya bar shan taba. Ya kamata masu shan taba su zo su samu taimako. <> We have created a new program at the Murtala Hospital. This is a program that will help anyone who wants to quit smoking. Smokers should come and get help.
Ku tuna fa: <> Remember:
  • Shan taba yana rage wa mutum ƙarfe. Yana kuma haifar da cuttutuka. Haka kuma yana da tsada.
  • Idan kana shan taba yana ƙara yiwuwar samun sankara da cutar zuciya sosai.
  • Haka kuma waɗanda ke kusa da mai shan taba, su ma suna fuskancin kasada.
<>
  • Smoking reduces a person’s energy. It causes diseases. It is also expensive.
  • If you smoke cigarettes, you have an increased likelihood of cancer or heart disease.
  • Also, people who are close to smokers face their own risk.
Amma mun san da cewa barin shan taba na da wuya. Saboda haka za mu bada taimako ga duk wanda yake so ya bar shan taba. Ku zo asibitin Murtala. Ku nemi dokta Ali Laminu. Shi ne ke jagorancin wannan shiri. <> However, we also understand that quitting is difficult. That is why we are offering help to anyone who smokes. Come to the Murtala Hospital. Ask for Doctor Ali Laminu. He is the director of this program.
Ga wasu bayanai game da shan taba sigari: <> Here are some facts about smoking:
  • A kowane minti ɗaya, mutum takwas suna mutuwa saboda shan taba a duniya.
  • Daga cikin dukkan mutanen da ke a duniya yau, shan taba zai kashe miliayan ɗari biyar.
  • Shan taba shi ne sanadin kashi 87 daga cikin 100 na waɗanda ke mutuwa saboda cutar sankara ta huhu.
  • Kwana ɗaya bayan an daina shan taba, kasadar mutuwa za ta fara ragewa.
  • Shekara ɗaya bayan an bar shan taba kasadar mutawa har ya rage da rabi.
<>
  • Every minute, eight people die because of smoking worldwide.
  • Of the people who are alive today, 500 million will die from smoking.
  • Smoking is the cause of 87 percent of the lung cancer deaths in the world.
  • One day after quitting smoking, the risk of death begins to reduce.
  • One year after quitting smoking, the risk of death is reduced by half.
A tuna, shan taba na kawo illoli daban daban. Haka kuma shan taba yana zama wa mutum jaraba. Watau, yana kama mutum. Saboda haka ku zo ku samu taimako. Za ku iya daina shan taba. <> Remember, smoking has numerous ill effects. Also, smoking is addictive. It catches hold of a person. So come and get help. You can quit smoking.
Ku zo asibitin Murtala. Ku tuntuɓi dokta Ali Laminu. Za ku samu taimako. <> Come to the Murtala Hospital. Talk to doctor Ali Laminu; you will get help.
Allah ya bada lafiya. <> May God give you health.