Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

GLOSS/406 Shan Nonon Uwa (Nursing)

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
(Redirected from GLOSS/406)
Shan Nonon Uwa <> Nursing
Yaku uwaye ku ji wata sanarwa game da muhimmancin nonon uwa ga jarirai. <> Parents of infants, listen to this message about the importance of breastfeeding infants.
Wannan makon da aka shiga shi ne mako na ƙarfafa shayar da nonon uwa a duniya. Saboda haka ga wani saƙo daga Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, watau WHO, a kan muhimmancin nonon uwa ga jarirai. Ya kamata uwayen jarirai su saurara su ji. <> This week is World Breastfeeding Week. This is a message from the World Health Organization, or WHO, about the importance of breastfeeding. Parents of infants should listen.
Shayar da nonon uwa tana da muhimmanci sosai ga ceto rayukan yara. Rashin abinci mai gina jiki shi ne ke haddasa mutuwar yara kusan miliyan 3 'yan ƙasa da shekara 5 kowace shekara. Wannan matsala ta fi muni a ƙasashenmu na Afirka. Amma nonon uwa yana da sinadaran da za su iya kare lafiyar jarirai da yara ƙanana fiye da kowane abinci. Saboda haka ya kamata kowane jariri ya sha nonon uwa kaɗai har ya kai a ƙalla wata shidda da haifuwa. <> Breast milk is vital in saving the lives of children. The lack of nutritious food causes nearly three million deaths per year in children under five years of age. This problem is the worst in Africa. However, breast milk has more nutrients for protecting infants than any other food. That is why every infant should solely nurse until at least six months of age.
A tuna fa, ya kamata kowane jariri ya fara shan nonon uwa cikin minti 30 da haifuwa. Haka kuma, ya kamata a riƙe shayar da nonon uwa har zuwa a ƙalla wata shidda da haifuwa. <> Remember, every infant should start nursing within thirty minutes of birth. Furthermore, they should continue nursing until at least six months of age.
Nonon uwa yana ƙara wa jariri garkuwar jiki. Yana kuma ƙara ƙarfinsa. Haka kuma jararan da ke shan nonon uwa sun fi ƙiba sosai. <> Breast milk fortifies the infant’s immune system. It also gives them strength. Furthermore, breastfed infants have more body fat.
Amma a tuna da cewa ya kamata uwar da ke shayar da jariri ta samu abinci mai gina jiki sosai. Ya kamata ta riƙa cin nama da sauran abubuwa masu gina jiki. <> But, remember that the mother of a nursing child should eat nutritious foods. She should always eat meat and other foods high in nutrients.
Daga yau kowane asibiti a kasarmu zai maida hankali kan ilimintar da uwaye a kan muhimancin shayar da nonon uwa. A je asibiti don samun ƙarin bayani a kan amfanin nonon uwa ga jarirai. <> Beginning today, every hospital in the country will be increasing their efforts to educate parents on the importance of breastfeeding. Go to the clinic to receive additional information on the benefits of breastfeeding.