Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

GLOSS/406soc Sanarwa (An Announcement)

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
(Redirected from GLOSS/406soc)
Sanarwa <> An Announcement
Ga wannan sanarwa. <> Now, an announcement.
Ina masu sauraron sashen Hausa na Muryar Amurka a jihohin Bauci, Gombe, Taraba, Yobe, Jigawa, Plateau, da makwabtansu? <> Calling all listeners of the Hausa Section of Voice of America in Bauchi, Gombe, Taraba, Yobe, Jigawa, Plateau State, and their neighbors.
Albishirinku. <> Here is some good news for you!
Sashen Hausa na Muryar Amurka ya shirya wani gaggarumin taro na yaƙi da cututukan mata da yara ƙanana da kuma kawar da cutar zazzaɓin cizon sauro a Bauci, a birnin Yakubu. <> The Hausa Section of the VOA has organized an important event for the fight against diseases that affect women and children, as well as the fight to eradicate malaria, which is to be held in the city of Yakubu, in Bauchi.
Za a gudanar da wannan babban taro ranar Alhamis tara ga wata nan na Oktoba a babban ɗakin taro na Malam Isa Yaguda, a otel ɗin Zaranda da ke Bauci daga ƙarfe tara na safe. <> The event will be held on Thursday, October 9, in the Isa Yaguda conference room of the Zaranda Hotel in Bauchi beginning at 9 a.m.
Babban baƙo na musamman shi ne mai girma gwaman jihar Bauci Malam Isa Yaguda. Babbar baƙuwa ita ce mai girma first lady ta jihar Bauci Hajiya Aisha Yaguda. <> The guest of honor will be his honor the governor of Bauchi State, Mr. Isa Yaguda. The other guest of honor will be the first lady of Bauchi State, Hajiya Aisha Yaguda.
Sauran baƙi a zauren taron sun haɗa da Shugaban sashen Hausa na Muryar Amurka Sunday Dare, da wasu manyan baƙi daga Amurka. <> Other guests will include the director of the VOA Hausa section, Sunday Dare, as well as other important guests from America.
A bayan tattanawa da tambayoyin da jama’a za su iya yi, za a rarraba kyaututuka masu yawa cike da akwatunan rediyo na mussaman guda goma ga waɗanda suka ci sa’a a zauren wannan taro. <> After the speeches are given and the guests have an opportunity to ask questions, a huge number of gifts, including 10 special radios, will be handed out to some lucky winners at the event.
Akwai kuma mawaƙan Hausa na zamani na musamman da za su zo domin tabbatar da cewa ba a bar ku a zaune ba haka kawai cikin zauren taron. <> There will be modern Hausa musicians who will come especially to make sure you will not spend the whole time sitting.
Kada a mance, za a yi wannan taro na Bauci ranar Alhamis a otel din Zaranda daga ƙarfe tara na safe, kuma za a yi ta rarraba kyautar akwatunan rediyo a duk tsawon rana. <> Do not forget this event in Bauchi, which will be held on Thursday at the Zaranda Hotel, starting at 9 a.m. Radios will be given out throughout the day.
Sai kun zo! <> We’ll see you there!