(Redirected from GLOSS/407)
A Wurin Aikina | <> | In My Workplace |
To, ni ma’aikaciyar jinya ce, watau nas. Bayan na fito daga sakandare, na shiga kwalejin inda ake koyar da aikin jinya, na samu digiri. To bayan na samu digiri, sai na koma nan Matameye don in yi aikin jinya a asibiti. A nan nike aiki a ɗakin agajin gaggawa, da ɗakunan tiyata, da kuma sauran yankunan asibiti. Wannan aiki ya haɗa da ayyuka daban-daban. | <> | So, I am a nursing worker, that is, a nurse. After I finished secondary school, I entered the college where they teach nursing, and got my degree. After I got my degree, I returned here to Matameye to do nursing at that hospital. Here, I work in the emergency room, the surgery rooms, and other parts of the hospital. This work includes various tasks. |
Ina zagaya asibti don duba halin da marasa lafiya ke ciki. Ina auna bugun zuciyarsu da na’urar auna bugun zuciya. Haka kuma ina auna lafiyar huhu. Ina kawo musu ƙwayoyin magani da suke sha. Ina kuma kawo wa kowane majinyata abinci, da ruwan sha. Haka kuma wani lokaci ina yi musu allura. Ina bai wa yara maganin rigakafi don hana cutar shan inna da kyanda da dai sauransu haka. Ina wanke raunuka, kuma ina canza wa masu rauni bandeji. Ina kula da halin da raunukansu ke ciki don tabbatar da cewa suna warkewa. | <> | I circulate around the hospital to check on the state that the ill people are in. I measure their heart rate with a stethoscope. I also check their lung health. I bring them medicine [pills] to take. I also bring each patient food and water. Additionally, I sometimes give them shots. I give children immunizations to prevent polio and measles and other such illnesses. I clean their wounds, and I change their bandages. I monitor the state of their wounds in order to ensure that they are healing. |
Ina ɗaukan jinni domin aunar jinni. Idan na ɗauki jinni da allura, sai na kai shi ɗakin gwaje-gwaje. A nan ana gwada jinnin. Idan an samu sakamakon gwaji, ina kawo sakamakon ɗin zuwa likita. Idan za a yi tiyata, ina bada taimako iri-iri. Ina wanke kayan aikin tiyata, kuma ina bai wa likita kayan aikin da yake bukata. Bayan an gama aikin fiɗa, ina tsabtace ɗakin tiyata. | <> | I draw blood for blood tests. After I draw blood with a needle, I take it to the lab. There, they test the blood. When they get results from the test, I bring the results to the doctor. When surgery is performed, I give various types of help. I wash the surgical tools, and I give the doctor the tools that he needs. After surgery is complete, I clean the surgery room. |
A asibiti akwai marasa lafiya da ke ɗauke da cututtuka masu yaɗuwa irinsu kanjamau da tarin fuka. Saboda haka, tsabta da muhimmanci ƙwarai da gaske a asibiti. Gaskiya, aikin jinya na da wuya! Amma aiki ne mai muhimmanci. | <> | At the hospital, there are sick people who have transmissible diseases like AIDS and tuberculosis. Because of this, cleanliness is very important in the hospital. Truly, nursing is difficult! But it is important. |