Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

GLOSS/410 Taraba Supply

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
(Redirected from GLOSS/410)

https://gloss.dliflc.edu/products/gloss/hua_soc410/hua_soc410_source.html

Taraba Supply Taraba Supply
Namiji: To ga wata sanarwa. Man: Okay, here is an announcement.
Mace: Taraba Supply ya samu cin-gaba. Mun yi sabon gini a hanyar Munkaila a bakin kasuwa. Mun ƙara wuri. Mun ƙara kaya. Duk abinda kuke bukata, za ku samu a wurinmu. Zo ku gani da idanunku. Kuma daga ranar litinin har zuwa alhmis muna yin bikin buɗewar sabon shagonmu. Zo ku sha shayi da kaffe kyauta domin taya mu murna. Haka kuma mun rage farasoshimu don nuna godiyarmu ga duk wanda ya zo shan biki da mu. Woman: Taraba Supply is moving forward. We've built a new building on Munkaila Road next to the market. We've added room. We've added products. You can find everything you need here. Come see with your own eyes. Also, from Monday to Thursday, we are celebrating the opening of our new store. Come and have tea and coffee on us and help us celebrate. We've also reduced our prices in order to thank everyone who comes to celebrate with us.
Idan kuna bukata sabon waya ta salula, ku zo. Muna da wayoyi kowane iri masu kyau. Ga kuma arha. If you need a new cell phone, come on down. We have great phones of all types and for great prices.
Idan tufafi ne ake bukata, ya ku. Muna da tufafi na mata da na maza daga ko’ina a duniya. Muna da wanduna da riguna da huluna da takalma na kowane iri. Ga kuma kayan ado da kwalliya daga Turai da Amirka. If you need clothing, get down here. We have men's and women's clothing from all over the world. We have pants, shirts, hats, and shoes of every kind. There are also cosmetics and jewelry from America and Europe.
Idan cefane kuke yi,ku zo yanzu ku ga ire-iren kayan abinci masu kyau daga kowane nahiya ta duniya. Akwai taliya da filawa da kaffe da shayi da madara da lemu iri-iri. If you are shopping for groceries, come now to see various types of great food from every continent. We have pasta, flour, coffee, tea, milk, and soft drinks of every kind.
Idan kuna bukata kaya a gidanku kamar kujera ko teburi ko kayan dafa abinci har ma da telebijin da rediyo, nan za a samu. Muna da kaya kowane iri, na zamani. If you need household supplies like chairs, a table, kitchen supplies, or even a television or a radio, you will find it here. We have all sorts of modern products.
Idan kayan aiki ne kuke bukata, kar ku je wani wuri! Muna da litattafai da alkalamai da takarda da duk abinda za ka bukata a ofishinku. Har ma na’urori na lissafi da kuma kwamfutoci, muna da akwai. If you need office supplies, don't go anywhere else! We have books, pens, paper, and everything that you need for your office. Even calculators and computers, we have those too.
Mun ƙara yawan kayan da muke saida, amma mun rage farasoshinmu. Ku zo ku sha biki! Ku taya mu murna! We have added to the number of products that we carry, but we have reduced the prices. Come to our party! Help us celebrate!
Duk abinda kuke bukata a wuri ɗaya! Taraba Supply kenan. Kar ku makara! Ku zo Taraba Supply yanzu. Everything you need in one place! That's Taraba Supply. Don't be late! Come to Taraba Supply now.
Muna nan a sabon gininmu a bakin kasuwa a hanyar Munkaila. Muna jiranku. We are in our new building next to the market on Munkaila Road. We're waiting for you.
Sai kun zo! See you here!