Toggle menu
24K
666
183
158.3K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/3/Rijayar Lemo Tafsir2: Difference between revisions

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
No edit summary
 
(12 intermediate revisions by the same user not shown)
Line 586: Line 586:
# Rowa tana daga cikin manyan laifukan da Allah zai yi wa bawa ukuba a kanta.
# Rowa tana daga cikin manyan laifukan da Allah zai yi wa bawa ukuba a kanta.


== 181-184 ==
== Tarjama Da Tafsirin ayoyin 181-184 ==


# Tabbas hakika Allah ya ji maganar wadannan da suka ce: "Lalle Allah [[matalauci|mataulaci]] ne, mu ne mawadata." Da sannu za Mu rubuta abin da suka fada, da kuma kisan da suka dinga yi wa [[annabawa]] ba tare da wani hakki ba, kuma za Mu ce: "Ku [[dandani]] azaba mai [[ƙuna]]." --[[Quran/3/181]]
# Tabbas hakika Allah ya ji maganar wadannan da suka ce: "Lalle Allah [[matalauci|mataulaci]] ne, mu ne mawadata." Da sannu za Mu rubuta abin da suka fada, da kuma kisan da suka dinga yi wa [[annabawa]] ba tare da wani hakki ba, kuma za Mu ce: "Ku [[dandani]] azaba mai [[ƙuna]]." --[[Quran/3/181]]
Line 604: Line 604:
181- Indeed, Allâh has heard the statement of those (Jews) who say: "Truly, Allâh is poor and we are rich!" We shall record what they have said and their killing of the Prophets with no just cause, and We shall say: "Taste you the torment of the burning (Fire)." It is narrated on the authority of Ibn 'Abbâs [Allâh be pleased with them] that he said: Abu Bakr [Allâh Be Pleased with him] entered Bayt Al-Midrâs (the place where the Jews study the Torah) and found many of them gathering around someone called Finhâs, who was one of their scholars and rabbis with someone called Ashya'. Abu Bakr [Allâh Be Pleased with him] said to Finhâs: "Woe to you, fear Allâh. By Allâh, you know that Muhammad [peace be upon him] is the Messenger of Allâh who came with the truth from Allâh and you can find that in your Torah and Gospel". Finhâs said to Abu Bakr [Allâh Be Pleased with him]: "By Allâh, O Abu Bakr, we are not in need of Allâh; it is He Who Is in need of us. We do not [[invoke]] Him as He Invokes us. We are rich and He Is not, for had He Been rich, He Would not Have Borrowed our property as your Prophet claims. He Forbids you from usury and Permits us to deal in it. If He Had Been rich, He Would not Have Permitted us to deal in usury". Abu Bakr [Allâh Be Pleased with him] became angry and slapped the face of Finhâs and said: "By The One in Whose Hand my soul is, had it not been for the covenant between us and you, I would have smashed your head, O enemy of Allâh”. Finhâs, accordingly, went to the Messenger of Allâh [peace be upon him] and said: "O Muhammad, look at what your Companion (Abu Bakr) has done to me". The Messenger of Allâh [peace be upon him] said: "What drove you to do so, O Abu Bakr?" Abu Bakr [Allâh Be Pleased with him] replied: “This enemy of Allâh said a grave saying: he claimed that Allâh Almighty Is in need for them and that they are rich. When he said so, I became angry for the Sake of Allâh Almighty and slapped his face". Therefore, Finhâs denied this and said: "I did not say so". On that occasion, Allâh Almighty Revealed this Qur'anic Verse. [Ibn Ishâq and Ibn Abu Hâtim] .
181- Indeed, Allâh has heard the statement of those (Jews) who say: "Truly, Allâh is poor and we are rich!" We shall record what they have said and their killing of the Prophets with no just cause, and We shall say: "Taste you the torment of the burning (Fire)." It is narrated on the authority of Ibn 'Abbâs [Allâh be pleased with them] that he said: Abu Bakr [Allâh Be Pleased with him] entered Bayt Al-Midrâs (the place where the Jews study the Torah) and found many of them gathering around someone called Finhâs, who was one of their scholars and rabbis with someone called Ashya'. Abu Bakr [Allâh Be Pleased with him] said to Finhâs: "Woe to you, fear Allâh. By Allâh, you know that Muhammad [peace be upon him] is the Messenger of Allâh who came with the truth from Allâh and you can find that in your Torah and Gospel". Finhâs said to Abu Bakr [Allâh Be Pleased with him]: "By Allâh, O Abu Bakr, we are not in need of Allâh; it is He Who Is in need of us. We do not [[invoke]] Him as He Invokes us. We are rich and He Is not, for had He Been rich, He Would not Have Borrowed our property as your Prophet claims. He Forbids you from usury and Permits us to deal in it. If He Had Been rich, He Would not Have Permitted us to deal in usury". Abu Bakr [Allâh Be Pleased with him] became angry and slapped the face of Finhâs and said: "By The One in Whose Hand my soul is, had it not been for the covenant between us and you, I would have smashed your head, O enemy of Allâh”. Finhâs, accordingly, went to the Messenger of Allâh [peace be upon him] and said: "O Muhammad, look at what your Companion (Abu Bakr) has done to me". The Messenger of Allâh [peace be upon him] said: "What drove you to do so, O Abu Bakr?" Abu Bakr [Allâh Be Pleased with him] replied: “This enemy of Allâh said a grave saying: he claimed that Allâh Almighty Is in need for them and that they are rich. When he said so, I became angry for the Sake of Allâh Almighty and slapped his face". Therefore, Finhâs denied this and said: "I did not say so". On that occasion, Allâh Almighty Revealed this Qur'anic Verse. [Ibn Ishâq and Ibn Abu Hâtim] .


Sannan kuma Allah ya fallasa wata karyar ta Yahudawa, wadda suka yi da'awar cewa, Allah ya yi musu wasiyya da kada su yi imani da wani Manzo har sai ya zo musu da wata sadaka wadda wuta za ta zo ta cinye ta a gabansu suna gani, sannan ne za su yarda shi Manzon Allah ne, su yi imani da shi.
Sannan kuma Allah ya fallasa wata karyar ta Yahudawa, wadda suka yi da'awar cewa, Allah ya yi musu wasiyya da kada su yi imani da wani Manzo har sai ya zo musu da wata sadaka wadda wuta za ta zo ta cinye ta a gabansu suna gani, sannan ne za su yarda shi Manzon Allah ne, su yi imani da shi. Sai Allah ya umarci Annabinsa ya mayar musu martani da cewa, ai akwai manzanni da yawa a gabaninsu, wadanda suka zaaike wa jama'arsu suna dauke da mu'ujizoji da dama, wadanda suka hada har da irin wannan mu'ujizar da suka nema, to amma sai ba su yi imani ba. Hasali ma kashe wasu annabawan suka yi. To don me suka kashe su, in har da gaske suke cewa, Allah ya umarce su da kada su yi imani sai da wanda ya zo musu da irin wannan mu'ujizar?


pg479
Sai Allah ya lallashi Annabinsa da kada ya damu don karyatawar da wadannan Yahudawan suke yi masa, domin ba shi ne farau ba; manzanni da dama da suka gabace shi, sun zo da mu'ujizoji da littattafai da aka saukar musu, wadanda ke dauke da wa'azuzzuka da nasihu masu ratsa zukata.
 
'''Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:'''
# Duk abin da bayi suke yi na alheri ko na sharri ana rubutawa.
# Duk wanda ya yarda da laifin mai laifi, to shi ma ya zama mai laifi. Shi ya sa Allah yake jingina wa Yahudawan zamanin Annabi SAW laifin iyayensu, domin sun yarda da wannan laifin.
# Karyata gaskiya da yi wa Allah karya wata siffa ce ta Yahudawa.
 
== Tarjama Da Tafsirin ayoyin 185-186 ==
 
# Kowane rai zai dandani mutuwa. Kuma a ranar alqiyama ne za a cika muku ladan ayyukanku; to duk wanda aka nisanta shi daga wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to hakika ya rabauta. Kuma rayuwar duniya ba komai ba ce face cin daɗi mai ruɗarwa. --[[Quran/3/185]]
# Lalle za a jarrabe ku a cikin dukiyoyinku da rayukanku, kuma lalle za ku rika jin cutarwa mai yawa daga wadanda aka bai wa Littafi kafinku, haka kuma daga wadanda suke mushrikai. Amma idan har kuka yi hakuri, kuma kuka tsare dokar Allah, to lalle wannan yana daga cikin manyan al'amura. --[[Quran/3/186]]
 
Tafsiri:
 
A wadannan ayoyi, yana bayyana cewa, kowane rai dole ne sai ya mutu, kuma Allah ne ke yi wa kowa cikakken sakamako na aikinsa ranar gobe qiyama. To duk wanda aka tserar da shi daga shiga wuta, sannan aka shigar da shi Aljanna, to hakika wannan mutum ya rabauta, kuma rayuwar duniya wani ɗan jin daɗi ne ƙanƙani, mai gushewa da gaggawa bayan ya ruɗi ma'abocinsa.
 
An karbo daga Abu Huraira rA ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Lalle gurbin [[bulala]] a Aljanna ya fi duniya da abin da yake cikinta. Ku karanta wannan ayar in kun ga dama: "To duk wanda aka nisanta shi daga wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to hakika ya rabauta, kuma rayuwar duniya ba komai ba ce, face ɗan jin daɗi mai ruɗarwa." [Tirmizi #3013 da Nasa'i, As-Sunan Alkubra #11085]
 
Narrated Abu Hurairah: that the Messenger of Allah (ﷺ) said: "Indeed the space in Paradise taken up by a whip, is better than the world and what is in it. Recite if you wish: 'And whoever is moved away from the Fire and admitted to Paradise, he indeed is successful. The life of this world is only the enjoyment of deception (3:185).'" [https://sunnah.com/tirmidhi:3013<nowiki>] </nowiki>
 
Sannan Allah swt ya faɗa wa muminai cewa za a jarrabe su da aukawar masifu a dukiyoyinsu, ta hanyar lalacewarsu ko hasarar kasuwanci, kuma za a jarabce su a rayukansu, ta hanyar mutuwa ko kisa ko samun raunuka ko rashin lafiya. Sannan kuma za su dinga jin maganganu na cutarwa da gallazawa daga makiyansu wadanda aka ba wa Littafi gabaninsu, wato Yahudawa da Nasara, da kuma mushirkai, saboda za su rika zagin su, suna sukar addininsu, suna jifar su da tuhumce-tuhumce iri-iri da yin izgili ga shari'arsu. To amma idan sun yi hakuri a kan hakan, kuma suka kiyaye dokokin Allah, to yin hakan yana daga cikin manyan al'amura da suke bukatar juriya da himma.
 
'''Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:'''
# Kwadaitarwa a kan yawaita aikata ayyukan alheri kafin zuwan ajali, saboda babu wanda ya san lokacin mutuwarsa.
#Nuna kaskancin duniya da rashin tabbas dinta, domin duk wani abin jin dadi da yake cikinta mai gushewa ne. Don haka bai kamata ta rudi mai hankali ba.
#Ya kamata mumini ya sani cewa, duk irin yanayin da yake ciki, mai dadi ko marar dadi, wata jarrabawa ce daga Allah, domin ya ga godiyarsa ko hakurinsa, ko kuma rashinsu.
#Allah ya ba muminai labarin abin da za su rika gani daga magabtansu, Ma'abota Littafi da mushirikai, na cutarwa mai yawa, domin wasu hikimomi kamar haka:
##Don a tantance Musulmi na kwarai da lalatacce.
##Don Allah ya daukaka darajar muminai da wannan ya kuma kankare musu laifuffukansu.
##Don imaninsu ya ƙaru yayin da suka ga aukuwar abin da Allah ya ba su labarinsa.
##Don su shirya wa faruwar hakan.
##Don idan ya faru su yi hakuri, su jure.
 
== 187-188 ==
 
# Kuma ka tuna lokacin da Allah Ya dauki alkawari daga wadanda aka bai wa Littafi cewa: "Lalle ku bayyana shi ga mutane, kuma kada ku boye shi." Sai suka jefar da shi can bayansu, kuma suka musanya shi da wani dan farashi kankani. To tir da abin da suke yin musanye da shi. --[[Quran/3/187]]
# Kada ka yi tsammanin wadanda suke yin farin ciki da irin abin da suka aikata, kuma suna son a rika yabon su da abin da ba su aikata ba, to kada ka yi tsammanin za su tsira daga azaba, kuma suna da azaba mai raɗaɗi. --[[Quran/3/188]]
 
Tafsiri:
 
A wadannan ayoyi, Allah swt yana tuna wa Annabinsa SAW wani mummunan aiki na Yahudawa da Nasara, lokacin da Allah ya yi ƙaƙƙarfan alkawari da su na cewa, za su fito su bayyana wa mutane abin da yake cikin littattafan da aka saukar wa annabawansu, kuma ba za su boye komai daga ciki ba. Daga ciki kuwa har da siffofin Annabi SAW da suka zo a Attaura da Linjila; to amma sai suka saɓa wannan alƙawari, suka ɓoye waɗannan siffofin Annabi SAW, ba don komai ba, sai don ɗan abin da za su samu na duniya. Sai Allah ya yi tir da irin wannan aiki nasu.
 
An karbo daga Abu Huraira rA ya ce: Annabi SAW ya ce: "Duk wanda aka yi masa tambaya ta ilimi, sannan ya boye, to za a sa masa linzamin wuta ranar gobe qiyama." [Abu Dawud #3658 da Tirmizi #2649 da ibnu Majah #266].
 
Narrated Abu Hurairah: that the Messenger of Allah (ﷺ) said: "Whoever is asked about some knowledge that he knows, then he [[conceals]] it, he will be bridled with bridle of fire." [https://sunnah.com/tirmidhi:2649<nowiki>]</nowiki>
 
Sai kuma Allah swt ya fada wa Annabinsa cewa, kada ya yi zaton mutanen da suke farin ciki da miyagun ayyukan da suka yin a boye ilimin da Allah ya ba su, kuma suke son a rika yaba musu akan aikin da ba su yi ba, kada ya yi zaton wadannan mutane za su tsira daga azabar Allah ranar alqiyama; tabbas suna da wata azaba mai radadi.
{| class="wikitable"
|+
!1
!Narrated Abu Sa`id Al-Khudri:
!An karbo daga Abu Sa'id Alkhudri rA ya ce:
|-
|2
|During the lifetime of Allah's Messenger (ﷺ), some men among the hypocrites used to remain behind him (i.e. did not accompany him) when he went out for a Ghazwa and they would be pleased to stay at home behind Allah's Messenger (ﷺ)
|Wasu munafukai duk sanda Annabi SAW ya fita yaqi, sai su noqe su qi fita tare da shi, kuma su riqa farin ciki da hakan.
|-
|3
|When Allah's Messenger (ﷺ) returned (from the battle) they would put forward (false) excuses and take oaths, wishing to be praised for what they had not done.
|Idan Annabi SAW ya [[dawo]] daga yaqi, sai su je suna rantsuwa, suna fadar hanzari na qarya, sannan uma su riqa son ya yabe su da aikin da ba su yi ba.
|-
|4
|So there was revealed:-- "Think not that those who rejoice in what they have done, and love to be praised for what they have not done.." (3.188)
|Sai wannan ayar ta sauka: "Kada ku yi tsammanin wadanda suke farin ciki da abin da suka yi, kuma suna son a riqa yabon su da abin da ba su aikata ba..."
|}
Bukhari #4567 da Muslim #2777 https://sunnah.com/bukhari:4567
 
'''Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:'''
# Wajabcin bayyana ilimi a kan masu ilimi ta duk hanyar da ta dace.
# Sukan masu son a yaba musu a kan aikin da ba nasu ba.
# Babu laifi a yaba wa mutum a kan aikin da ya yi na alheri, don qarfafa masa gwiwa, idan kuma babu jin tsoron girman kai ya shige shi.
# Babu laifi mutum ya yi farin ciki a kan yabonsa da aka yi bisa wani aikin alheri, matuqar ba ya yi ne domin riya ba, kuma bai yarda jiji da kai ya kama shi ba.
 
== 189-195 ==
# Kuma ga Allah ne mulkin sammai da qasa yake. Kuma Allah Mai iko ne a kan komai. --[[Quran/3/189]]<br> And to Allah belongs the dominion of the heavens and the earth, and Allah is over all things competent. (189)
# Lalle a cikin halittar sammai da qasa da sassab'awar dare da rana, tabbas akwai ayoyi ga ma'abota lafiyayyun hankula. --[[Quran/3/190]]<br> Indeed, in the creation of the heavens and the earth and the [[alternation]] of the night and the day are signs for those of understanding. (190)
# Su ne wadanda suke ambaton Allah a tsaye da kuma [[zaune]] da kuma [[kishingid'e]], suna kuma tunani a kan halittar sammai da qasa, (suna cewa): "Ya Ubangijinmu, ba Ka halicci wannan a banza ba, tsarki ya tabbata gare Ka, Ka tserar da mu daga azabar wuta. --[[Quran/3/191]]<br> Who remember Allah while [[standing]] or [[sitting]] or [lying] on their sides and give thought to the creation of the heavens and the earth, [saying], "Our Lord, You did not create this [[aimlessly]]; exalted are You [above such a thing]; then protect us from the punishment of the Fire. (191)
# "Ya Ubangijinmu, lalle duk wanda Ka [[shigar]] da shi wuta, to haqiqa Ka [[kunyata]] shi; kuma [[azzalumai]] ba su da mai taimakon su. --[[Quran/3/192]] Our Lord, indeed whoever You [[admit]] to the Fire - You have [[disgraced]] him, and for the [[wrongdoers]] there are no helpers. (192)
# "Ya Ubangijinmu, lalle mu mun ji wani mai kira yana yin kira zuwa imani cewa: "Ku yi imani da Ubangijinku;" sai muka yi imani. Ya Ubangijinmu, Ka gafarta mana zunubanmu, kuma Ka kankare mana [[kurakurai|kurakuranmu]], kuma Ka karb'i rayukanmu tare da mutane masu [[ɗa'a]]. --[[Quran/3/193]]<br> Our Lord, indeed we have heard a caller calling to faith, [saying], 'Believe in your Lord,' and we have believed. Our Lord, so forgive us our sins and remove from us our [[misdeeds]] and cause us to die with the righteous. (193)
#"Ya Ubangijinmu, kuma Ka ba mu abin da Ka yi mana alqawari da shi ta harshen manzanninka, kuma kada Ka [[kunyatar]] da mu ranar alqiyama. Lalle Kai ba Ka sab'a alqawari." --[[Quran/3/194]] Our Lord, and grant us what You promised us through Your messengers and do not [[disgrace]] us on the Day of Resurrection. Indeed, You do not fail in [Your] promise." (194)
#Sai Ubangijinsu Ya amsa musu (cewa): "Lalle Ni ba zan tozarta aikin wani mai aiki daga cikinku ba, namiji ne ko mace; sashinku yana tare da sashe. To wadanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidajensu kuma aka cutar da su wajen bin tafarkina kuma suka yi yaqi kuma aka kashe su, lalle zan kankare musu krakuransu, kuma lalle zan shigar da su gidajen Aljanna wadanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu. Wannan lada ne daga wajen Allah, kuma a wurin Allah ne mafi kyawun lada yake." --[[Quran/3/195]]
 
=== Tafsiri: ===
A cikin wadannan ayoyi Allah swt yana bayyana cewa, shi kadai ne mai mulkin sammai da qasa da abin da yake cikinsu, kuma shi ne mai cikakken iko a kan komai. Sannan ya sanar da cewa, a cikin halittar sammai da qasa da abubuwan da suka qunsa da cancanzawar dare da rana, wannan ya zo, wannan ya tafi, lalle akwai manya-manyan ayoyi da dalilai ga masu lafiyayyen hankali, da suke tabbatar da samuwar Mahalicci da siffofinsa. Wadannan kuwa su ne masu ambaton Allah koyaushe, a cikin kowane yanayi, a tsaye suke ko a zaune ko a kwance. Suna tunani game da halittar sammai da qasa, suna cewa: "Ya Ubangijinmu, mun yi imani ba ka yi wannan halittar a banza ba; ka tsarkaka daga yin wannan, don haka ka tsare mu daga da shi, kuma azzalumai ba su da masu taimaka musu." Suka ci gaba da cewa: "Ya Ubangijinmu, mun ji Annabinka yana kira zuwa ga yin imani da kai, kuma mun amsa kiransa, mun yi imani, don haka ka gafarta mana laifukanmu, kuma ka kankare mana munanan ayyukanmu, kuma ka karb'i rayukanmu tare da mutanen kirki. Ya kyakkyawan sakamako ka zartar da shi, kada kuma ka kunyata mu a ranar alqiyama a gaban halittunka; lalle mun tabbatar ba ka sab'a alqawari."
 
Sai ko Allah swt ya bayyana cewa, ya karb'i wannan roqo nasu, kuma ya yi alqawarin ba zai tab'a tozarta aikin mai aiki ba, namiji ne shi ko mace ce. Don haka wadanda suka baro garuruwansu na kafirci ko kuma kafirai suka koro su, aka cutar da su saboda sun riqe gaskiya, sun yi imani da Allah da Manzonsa, suka kuma yi yaqi don Allah, kuma aka kashe su, to wadannan Allah zai kankare musu laifukansu, kuma zai saka su gidajen Aljanna, wadanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu; wannan babban sakamako ne a gare su, saboda qoqarin da suka yi na aikin alheri a duniya. Allah shi ne mai kyakkyawan sakamako ga duk wanda ya yi aikin qwarai; zai saka masa da abin da ido bai tab'a gani ba, kunne bai tab'a ji ba, zuciyar wani d'an Adam ba ta tab'a tunaninsa ba.
 
An karbo daga Abdullahi d'an Abbas rA ya ce: Wani dare na kwana a d'akin Maimuna uwar muminai. kuma a ranar Annabi SAW yana d'akinta, domin in ga yadda yake sallarsa ta dare. Annabi SAW ya yi hira da iyalinsa na wani d'an lokaci, sannan ya kwanta ya yi barci. A sulusin qarshe na dare, sai ya tashi zaune, ya d'aga kai sama, sai ya karanta wannan aya (ta Quran/3/190), sannan ya tashi ya yi alwala, ya yi asiwaki, sannan ya yi salla raka'a goma sha d'aya, sannan Bilal ya kira sallar Asuba. Sai Annabi SAW ya sallaci raka'a biyu, sannan ya fita ya jagoranci sallar Asuba. [Bukhari #7452].
 
Narrated Ibn `Abbas: Once I stayed overnight at the house of (my aunt ) Maimuna while the Prophet (ﷺ) was with her, to see how was the night prayer of Allah's Apostle Allah's Messenger (ﷺ) talked to his wife for a while and then slept. When it was the last third of the night (or part of it), the Prophet (ﷺ) got up and looked towards the sky and recited the Verse:-- 'Verily! In the creation of the Heavens and the Earth....there are indeed signs for the men of understanding.' (3.190) Then He got up and performed the ablution, brushed his teeth and offered eleven rak`at. Then Bilal pronounced the Adhan whereupon the Prophet (ﷺ) offered a two-rak`at (Sunna) prayer and went out to lead the people in Fajr (morning compulsory congregational prayer. https://sunnah.com/bukhari:7452
 
'''Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:'''
# Kira zuwa ga yin tunani game da halittar sammai da qasa, saboda abubuwan da suka qunsa na manyan dalilai masu tabbatar da Ɗayantakar Allah da cancantar a bauta masa shi kad'ai.
#Tunani da duba cikin halittar sammai da qasa yana qara wa bawa imani da yaqini.
#Duk sa'adda mutum ya zama mai zurfin hankali, to saninsa ga Allah da ayoyinsa za su qara hab'aka.
#Halaccin yin tawassuli da siffofin Allah da ayyuka na qwarai, kamar imani da Allah da Manzonsa SAW.
#Yana daga cikin ladubban addu'a, mutum ya yawaita yabo da kirari ga Allah Ta'ala.
#Babu wani bambanci tsakanin namiji da mace wajen sakamakin ayyukan ibada da kusanci zuwa ga Allah. Duk wanda ya yi aiki na gari, Allah zai yi masa sakayya da kyakkyawan sakamako, ba tare da la'akari da bambancin jinsi ba.
 
== 196-200 ==
 
# Kada zirga-zirgar kafirai a cikin qasa ta rud'e ka. --[[Quran/3/196]]<br> Be not deceived by the [uninhibited] movement of the disbelievers throughout the land. (196)
# Wani d'an [[jin dad'i]] ne ƙanƙani, sannan makomarsu Jahannama. Kuma tir da wannan shifid'ar. --[[Quran/3/197]]<br> [It is but] a small [[enjoyment]]; then their [final] refuge is Hell, and wretched is the resting place. (197)
# Amma wadanda suka bi dokokin Ubangijinsu suna da gidajen Aljanna wadanda  qoramu suke gudana ta qarqashinsu, za su dawwama a cikinsu, wannan gara ce ta musamman daga wajen Allah. Kuma abin da yake wajen Allah shi ne mfai alheri ga masu biyayya. --[[Quran/3/198]]
# Kuma lalle a cikin Ma'abota Littafi, tabbas akwai wadanda suke yin imani da Allah da kuma abin da aka saukar musu, suna masu jin tsoron Allah, ba sa musanya ayoyin Allah da wani d'an farashi qanqani. Wadannan suna da lada a wajen Ubangijinsu. Lalle Allah Mai gaggawar hisabi ne. --[[Quran/3/199]]
# Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi hakuri, kuma ku jure matuqa ga yin hakuri, kuma ku tsare iyakokin qasa, kuma ku tsoraci Allah ko kwa sami [[rabauta]]. --[[Quran/3/200]]
Tafsiri:
 
A wadannan ayoyi Allah swt yana yi wa Annabinsa SAW kashedi da rudawa da kai-komon kafirai a duniya da tinqahon da suke yi da bunqasar harkar kasuwanci da qarfin tattalin arziki da qarfin sojoji. Duk wadannan wani dan taqaitaccen jin dadi ne; nan da nan zai qare, sannan daga qarshe wutar jahannama ce makomarsu tir kuwa da irin wannan makoma.
 
To amma masu bin dokokin Ubangijinsu ta hanyar aikata abin da ya wajabta musu da barin abin da ya haramta musu; to an tanadar musu gidajen Aljanna wadanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, kuma su zauna cikinsu har abada. Wannan wata liyafa ce Allah ya shirya musu. Don haka abin da yake wurin Allah na kyakkyawan sakamako ga wadanda suka bi shi, ya fi alheri fiye da wani d'an gajeren jin dad'i na duniya.
 
Sannan Allah swt ya bayyana cewa, a cikin Ma'abota Littafi akwai wadanda sun yi imani da Allah, suna kad'aita shi da bauta, kuma sun yi imani da Manzonsa da Alqur'anin da aka saukar masa da kuma littattafan da aka saukar musu, suna masu qasqantar da kansu ga Allah, ba sa canza abin da yake cikin littattafansu, ba sa kuma b'oye gaskiyar da take ciki, domin samun d'an wani taqaitaccen jin dad'i na duniya; to wadannan suna da babban sakamako a wurin Allah swt. Lalle kuma Allah mai gaggawar sakamako ne.
 
An karb'o daga Anas d'an Malik rA ya ce: Lokacin da labarin rasuwar Najjashiy ta zo mana, Annabi SAW ya ce mana: "Ku yi masa salla." Sai Allah ya saukar da fad'arsa: "Kuma lalle cikin ma'abota Littafi, tabbas akwai wadanda suka yi imani da Allah da kuma abin da aka saukar muku da kuma abin da aka saukar musu, suna masu qasqantar da kansu ga Allah."
 
It was narrated from Anas bin Malik (may Allah be pleased with him) that: When the news of the death of Najjashi reached us, the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him) said to us: "Pray for him." Then Allah revealed: "And among the People of the Book are those who believe in Allah and what has been revealed to you and what has been revealed to them, and they humble themselves before Allah."  [https://sunnah.com/bukhari:1327 See also: https://sunnah.com/bukhari:1327]
 
Sai kuma Allah swt ya umarci bayinsa muminai da yin haquri da kuma dauriya a kan rinjayar maqiya addinin Allah, su jajirce har su ma su sami nasara a kan maqiyansu kuma su tsare kan iyakokin da ake tsoron shigowar maqiya daga gare su, sannan su kiyaye dokokin Allah, ta hanyar aikata umarninsa da barin haninsa; da wannan ne za su sami rabauta duniya da lahira.
 
'''Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:'''
# Hani ga Musulmi da kar ya rud'u da irin ni'ima da jin dad'i da kafirai suke mora; wannan d'an wani abu ne qanqani, kuma mai gushewa da gaggawa.
# Samun arziki da jin dad'in duniya ba shi yake nuna yardar Allah da soyayyarsa ga wanda ya wwa baiwar ba. Ma'aunin yarda da soyayyar Allah ita ce yi wa Allah da Manzonsa SAW d'a'a.
# Babu wata hanyar samun rabo daga Allah, sai ta yin haquri da juriya da jajircewa da kuma biyayya ga Allah da taimakon addininsa.
# Addinin Musulunci ya tattara ne a kan abubuwa guda uku:
## Aikata abin da aka yi umarni da shi
## da barin abin da aka hana
## da kuma haquri a kan abin da Allah ya qaddara faruwarsa.
 
 
pg491
[[Category:Quran/3]]
[[Category:Quran/3]]

Latest revision as of 01:39, 16 January 2025

Quran/3 > Quran/3/Rijayar_Lemo_Tafsir > Quran/3/Rijayar_Lemo_Tafsir2

Tarjama Da Tafsirin ayoyin 100-101 na Surar Ali Imran

  1. Ya ku wadanda suka yi imani, idan kuka bi wani bangare na wadanda aka ba wa Littafi, to za su mayar da ku kafirai bayan imaninku. --Quran/3/100
  2. Ta yaya kuma za ku kafirce, ga shi kuwa ana karanta muku ayoyin Allah, kuma Manzonsa yana tare da ku? Duk kuwa wanda ya riki Allah, to hakika an shiryar da shi tafarki madaidaici. --Quran/3/101

A wadannan ayoyi Allah yana gargadin muminai da cewa, idan suka kuskura suka nuna biyayyarsu ga Yahudawa da Nasara, wadanda suke yi musu hassadar Alqur'ani da Allah ya ba su da falalar Musulunci; to tabbas za su raba su da imaninsu, su mayar da su kafirai suna ji suna gani. Amma Allah ya nuna cewa, da wahala kwarai muminai su yarda su koma kafirci bayan ga Alkur'ani nan kullum suna ji ana karanta musu ayoyinsa, sannan ga Manzon Allah nan a tsakaninsu, yana isar musu duk wani saƙo da aka saukar dominsu. Shi imani idan har ya ratsa ƙoƙon zuciya; to abu ne mai wuyar gaske a iya cire shi, sai dai wani iko na Allah.

Sannan Allah ya bayyana musu wata hanya wadda idan suka bi ta, za su tsare kawunansu daga fadawa ramin kafirci. Wannan hanya ita ce, rike Allah da dogaro da shi, domin shi ne madogara ta samun shiriya. Duk wanda ya koma ga Allah a cikin kowanne hali nasa, ya nemi mafaka a wurinsa, ya dogara da shi dogaro na gaskiya, ya rike addininsa; to hakika wannan an shiryar da shi ga hanya mikakkiya dodar, wadda babu karkata ko kadan a cikinta, ita ce za ta yi masa jagoranci har ta kai shi gidan Aljanna.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Gargadin Musulmi a kan su yi hattara wajen yarda da maganganun Yahudawa da Nasara da aiki da su, ko kwaikwayon wani tsari nasu na rayuwa, domin zukatansu cike suke da hassada da kullata ga Musulmi, a kullum suna tunanin hanyar da za su bi su raba Musulmi suka yi sakaci suka karbi tsare-tsarensu na rayuwa; to za su iya kai su ga halaka.
  2. Sanin falalar sahabban Manzon Allah SAW, ta kasancewarsa ya rayu dauke da shi, kuma ya zame musu ƙaƙƙarfar katanga mai kare su daga faɗawa kafirci ko karkace hanyar gaskiya. Wannan ba karamar falala ba ce ga sahabbai; babu wanda ya sami irinta cikin wannan al'umma sai su.
  3. Riƙo da littafin Allah da sunnar Annabi SAW shi ne babban abin da zai tsare mumini daga kauce wa hanyar Allah, ko fadawa cikin kafirci.
  4. Idan zaman Annabi SAW a cikin wannan al'umma ya ƙare lokacin rayuwarsa, to ai ayoyin Allah da sunnonin Annabinsa suna nan a tsakanin al'umma, kuma Musulmi a yau ana neman su da aiki da Alƙur'ani da sunna, kamar irin yadda aka nemi musulmin farko da hakan; don haka har yanzu hanyar samun kariya da tsari a fili take.

Tarjama Da Tafsirin ayoyin 102-109

  1. Ya ku waɗanda suka yi imani, ku yi taƙawa ga Allah haƙiƙanin taƙawa, kuma lalle kada ku mutu face kuna Musulmi. --Quran/3/102
  2. Kuma ku yi riƙo da igiyar Allah gaba ɗaya, kada kuma ku rarraba. Kuma ku tuna ni'imar Allah da Ya yi muku yayin da kuka zamo abokan gaban juna sai Ya hada tsakanin zukatanku, sai kuka zamo 'yan'uwan juna a sakamakon ni'imarsa, a da kuma kun kasance a kan gabar ramin wuta sai Ya tserar da ku daga gare ta. Kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ayoyinsa don ko kwa shiriya. --Quran/3/103
  3. A cikinku lalle a sami wata al'umma wadanda suke kira zuwa ga alheri, kuma suke umarni da kyakkyawa, kuma suke yin hani daga mummuna. Wadannan su ne masu rabauta. --Quran/3/104
  4. Kuma kada ku kasance kamar wadanda suka rarrabu, kuma suka sassaba bayan hujjoji sun zo musu. Wadannan kuwa suna da azaba mai girma. --Quran/3/105
  5. Ranar da wadansu fuskoki za su yi fari, wadansu fuskokin kuma za su yi baki. Amma wadanda fuskokinsu suka yi baki, (ca a ce da su): "Shin ku ne kuka kafirce bayan imaninku? To ku dandani azaba, saboda kafircin da kuka kasance kuna yi." --Quran/3/106
  6. Amma wadanda fuskokinsu suka yi fari kuwa, to suna cikin rahamar Allah, suna masu dawwama a cikinta. --Quran/3/107
  7. Wadannan ayoyin Allah ne muke karanta maka su da gaskiya. Kuma Allah ba Ya nufin zalunci ga talikai. --Quran/3/108
  8. Kuma duk abin da yake cikin sammai da kasa na Allah ne. Kuma zuwa ga Allah ne ake mayar da duk al'amura. --Quran/3/109

A wadannan ayoyi, Allah SWT yana umartar bayinsa muminai da su ji tsoronsa gwargwadon ikonsu, sannan su ci gaba da rike wannan addini ƙam-ƙam har mutuwa ta zo musu. Kuma lalle su haɗa kansu, su zama abu guda a kan gaskiya, su taru su riƙe igiyar Allah, wadda ita ce Alƙur'anin da Manzo ya zo musu da shi da sunnarsa; kada su yarda su rarrabu.

An karbo daga Abu Huraira ya ce: Annabi ya ce:

"Lalle Allah ya yarje muku abubuwa uku (3), kuma ya ƙi muku abubuwa uku. Ya yarje muku da ku bauta masa, kuma kada ku haɗa komai da shi, kuma duk ilahirinku ku yi riƙo da igiyar Allah, kada ku rarrabu, kuma ya ƙi muku bin jita-jita da yawan tambaya da ɓarnata dukiya." [Muslim #1715]

Abu Huraira reported Allah's Messenger (ﷺ) as saying:

Verily Allah likes three things for you and He disapproves three things for you. He is pleased with you that you worship Him and associate nor anything with Him, that you hold fast the rope of Allah, and be not scattered; and He disapproves for you irrelevant talk, persistent questioning and the wasting of wealth. https://sunnah.com/muslim:1715a

Sannan Allah ya umarce su da su tuna ni'imarsa da ya yi musu lokacin da suka hadu a kan Musulunci, suka zama 'yan'uwan juna, bayan a da kafin zuwan Musulunci a rarrabe suke, suna gaba da fada da junansu a kan abin da bai taka kara ya karya ba, sai ga shi Allah ya haɗa zukatansu gaba ɗaya sun zama 'yan'uwa masu ƙaunar junansu, kamar yadda ya bayyana hakan a Suratul Anfali, aya ta 62-63.

Kuma Allah ya tunatar da su cewa, suna dab da fadawa ramin wuta, sai Allah ya ceto su, domin babu abin da ya rage musu su fada cikinta sai mutuwa idan har suna cikin wannan hali na kafirci. To kamar irin wannan bayani da ya yi musu filla-filla har suka fahimta; to haka yake fayyace musu sauran ayoyin nasa, don su zame musu fitilar gane hanyar shiriya da gaskiya.

Sannan Allah ya umarci bayinsa da cewa, lalle a sami wata kungiya daga cikinsu, wadanda za su dauki nauyin yin umarni da kyakkyawan aiki da hana mummuna a cikin al'umma; wannan shi ne maganin rabuwar kai a tsakaninsu. Domin duk al'ummar da take rayuwa kara-zube, kowa yana yin abin da ya ga dama, babu mai tsawata masa yayin da ya yi ba daidai ba, to wannan al'umma za ta rasa haduwar kai a tsakanin 'ya'yanta, domin soye-soyen zukatan mutane mabambanta ne. Allah ya bayyana cewa, wadanda suka siffantu da sifar nan ta umarni da kyakkyawan abu, da hana mummuna, su ne masu samun babban rabo a duniya da lahira.

An karbo daga Huzaifa dan Alyaman ya ce, Annabi SAW ya ce: "Na rantse da wanda rai na yake hannunsa, Wallahi, ko dai ku yi umarni da kyakkyawan aiki, ku hana mummuna, ko kuma ba da dadewa ba Allah ya aiko muku da wata ukuba daga gare shi, ku yi ta addu'a ya ki amsa muku!" [Ahmad #23349 da Tirmizi #2169].

Hudhaifah bin Al-Yaman narrated that the Prophet (s.a.w) said: "By the One in Whose Hand is my soul! Either you command good and forbid evil, or Allah will soon send upon you a punishment from Him, then you will call upon Him, but He will not respond to you." https://sunnah.com/tirmidhi:2169

Sai kuma Allah ya hana muminai rarrabuwa, kamar yadda Yahudu da Nasara a gabaninsu suka rarraba a addininsu, bayan hujjoji daga Allah, a ranar da fuskokin 'yan Aljanna za su yi fari, fuskokin 'yan wuta kuma su yi baki. Sai cikin zargi a ce wa masu bakaken fuskoki: "Shin ku ne kuka kafirce bayan imaninku? To ku dandani azaba saboda kafircinku." Amma masu fararen fuskoki, za su kasance ne a cikin rahamar Allah, tare da jin dadin da Allah ya tanadar musu a Aljanna na ni'imomi masu yawa, za su ci gaba da rayuwa a cikinsu har abada.

Sannan Allah ya tabbatar wa Annabinsa cewa; wadancan ayoyi da ya karanta masa su ne gaskiya, kuma tabbas Allah ba wanda yake zalunta cikin halittunsa. Duk abubuwan da suke cikin sammai, da wadanda suke kasa na Allah ne shi kadai, kuma duk al'amura gaba daya gare shi za a mayar da su ranar alkiyama, domin ya saka wa kowa aikin da ya yi; idan ya aikata alheri, ya ga alheri, idan kuwa sharri ya aikata, to ya ga sharri.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Wajibi a kan Musulmi su ƙanƙame ma addinin Musulunci, kar su rabu da shi har zuwa mutuwarsu.
  2. Wajibi ne Musulmi su hada kai su zama al'umma daya. Hanyar hada kan kuma ita ce rike shari'ar Allah, wadda take kunshe cikin Alkur'ani da sunnar Annabi. Sabananin haka kuma shi ne rarrabuwa, wadda take nufin rike bidi'o'i da son zuciya.
  3. Tunowa da ni'imomin Allah ga bayinsa, wadanda suka shafi addininsu ko rayuwarsu ta duniya, da gode wa Allah a kansu a zukata da harshe, wannan zai kara musu son Allah, sai shi kuma ya kara musu falalarsa da kyautarsa.
  4. Kira zuwa ga addinin Allah wani ginshiki ne na tabbatar da tsarin Allah a bayan kasa da kuma murkushe karya da barna da kawar da mummunan aiki da tabbatar da kyakkyawa. To masu irin wannan aiki su ne masu rabauta duniya da lahira.

Tarjama Da Tafsirin ayoyin 110-112

  1. Ku ne mafi alherin al'umma wadanda aka fitar ga mutane, kuna umarni da kyakkyawan aiki, kuma kuna hana mummuna, kuma kuna yin imani da Allah. Da a ce kuwa Ma'abota Littafi za su yi imani da ya fi alheri a gare su. A cikinsu akwai muminai, amma mafiya yawansu fasikai ne. --Quran/3/110
  2. Ba za su taba iya cutar da ku ba sai dai cutarwa kadan; kuma in da za su yake ku, sai sun juya muku baya, sannan ba za a taimake su ba. --Quran/3/111
  3. An hada su da kaskanci a duk inda aka same su, sai dai wadanda suke rike da wani alkawari daga Allah ko wani alkawari daga mutane, kuma sun dawo da wani fushi daga Allah, kuma an hada su da talauci. Hakan kuwa saboda sun kasance suna kafirce wa ayoyiin Allah, kuma suna kashe annabawa ba tare da wani hakki ba, hakan yana faruwa ne saboda sabo da suka yi, kuma sun kasance suna ketare iyaka.

A wadannan ayoyi, Allah yana magana da wadannan al'umma. Farkon wadanda suka shiga cikin wannan kiran, su ne sahabban Annabi, domin su ne farkon wadanda ayar ta yi magana da su. Wannan matsayi mai girma sun cancance shi ne saboda sun siffantu da yin umarni da kyakkyawan aiki da hani da mummuna da kuma imani da Allah. Wannan ne ya sanya suka tsere wa al'ummomin da suka gabace su.

Da a ce Yahudawa da Nasara sun yi imani da Annabi da abin da ya zo da shi daga Ubangijinsa, to da ya fi musu alheri. Sai dai wadanda suka yi imani a cikinsu 'yan kadan ne, da dama daga cikinsu sun ci gaba ne da zama a kan kangare wa Allah da Manzonsa SAW. Wannan shi zai hana su kaunaci muminai sai dai su yi ta gaba da su da kokarin cutar da su duk sanda suka sami dama. Amma dai duk yadda suka kai ga nuna musu kiyayya da kokarin cin zarafinsu, ba za su iya ba in banda cutarwa da fatar baki ba. Idan ma da fada zai hada su da muminai; to ba za su iya taɓuka komai ba sai dai su gudu, kuma ba za a taimaka musu ba, domin kuwa Allah ya hada su da kaskanci da wulakanci a duk inda suke a bayan kasa, ba sa samun nutsuwa da kwanciyar hankali, sai da wani alkawari daga Allah ko daga mutane. Sannan kuma sun cancanci fushin Allah, kuma ga alamun talauci sun bayyana a tare da su. Irin wannan sakamakon ya faru da su ne saboda kafirce wa ayoyin Allah da suke yi, da kuma kashe annabawa ba tare da wani laifi ba, sai don zalunci kawai. Kuma abin da ya kai su ga wannan hali na kafirci da kisa, shi ne sabon Allah da suke yi da ketare iyakokinsa da shari'arsa.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Ayar farko tana nuna falalar sahabban Annabi da fifikonsu a cikin wannan al'umma. Duk da cewa ayar ta hada har da sauran muminai wadanda suka zo bayan sahabbai, sai dai sahabban ne aka fara fuskanta da ita, shi ya sa suka fi cancanta da ita. Sannan siffar umarni da kyakkyawan aiki, da hana mummunan aiki da siffar umarni da kyakkyawan aiki, da hana mummunan aiki da siffar imani da Allah, duk sun fi bayyana tare da sahabbai fiye da sauran muminai da za su zo bayansu.
    An karbo daga Abdullahi dan Abbas ya ce,
    Manzon Allah ya ce: "Mafi alherin mutane su ne na ƙarnina, sannan wadanda suke bi musu, sannan wadanda suke bi musu..." [Bukhari #3651]
    The Prophet (ﷺ) said, "The best people are those living in my generation, and then those who will follow them, and then those who will follow the latter. Then there will come some people who will bear witness before taking oaths, and take oaths before bearing witness." (Ibrahim, a sub-narrator said, "They used to beat us for witnesses and covenants when we were still children.") https://sunnah.com/bukhari:3651
  2. Ya kamata al'ummar Musulmi su fahimci cewa, su ne fiyayyu a cikin duk wata al'umma da aka taba yi a bayan kasa, don su fahimci kimarsu da darajarsu, kuma su gane cewa, sun fito ne don su ja ragamar tafiyar wannan al'umma. Kuma nufin Allah shi ne alheri ya yi jagoranci a bayan kasa ba sharri ba, a bayan kasa, don haka ya kamata su zama koyaushe su ne masu bayarwa, ba masu karba ba. Kuma abin da za su bayar na akida da ilimi da halayya da tsarin rayuwa ya zama mai inganci ne.
  3. Fahimtar cewa umarni da kyakkyawan aiki da hana mummunan aiki abu ne mai girman matsayi a addinin Musulunci, domin shi ne tubalin ginin fifikon wannan al'umma a kan sauran al'ummomi.
  4. Himmatuwa da samar da ingantaccen imani da Allah a zuciya, domin sai da shi ne za a yi umarni da kyakkyawa, a hana mummuna, saboda shi ne sahihin ma'auni na tantance abu mai kyau da mummuna.
  5. Fifita wannan al'umma da Allah ya yi a kan sauran al'ummomi, saboda siffantuwarsu ne da umarni da kyakkyawa da hani da mummuna. Hakan yana nuna wannan siffar ba za ta yanke ba a cikin al'ummar.
  6. Allah ya gabatar da ambaton umarni da kyakkyawan aiki da hana mummunan aiki, saboda dalilai kamar haka:
  • Domin nuna falalar umarni da kyakkyawan aiki da hani da mummunan aiki.
  • Kasancewar ana magana ne a kan fifita wannan al'umma a kan dukkan al'ummomi, muminansu da kafiransu, shi ya sa aka ambaci sifar da kowa ya yarda mai kyau ce.
  • Kuma domin kasancewar umarni da kyakkyawan aiki da hani da mummuna yana matsayin garkuwa mai kare imani, sai aka fara faɗar sa da farko, domin makarin kowane abu ana gabatar da shi ne.
  • Hakanan akwai shaguɓe ga Ma'abota Littafi waɗanda suke da'awar sun yi imani, amma sun kasa tsayawa su yi umarni da kyakkyawan aiki su yi hani da mummuna.
  • Kuma don a nuna cewa wannan al'umma sun tsaya a kan wannan aiki ne saboda sun yi imani da Allah da bayyana addininsa a fili.

Tarjama Da Tafsirin ayoyin 113-115

  1. Ba dukansu ne suka zama daya ba. Cikin Ma'abota Littafi akwai al'umma tsayayya, suna karanta Littafin Allah a cikin dare alhalin suna sujada. --Quran/3/113
  2. Suna yin imani da Allah da ranar karshe, kuma suna umarni da kyakkyawan aiki, kuma suna hana mummuna, kuma suna hanzari wajen ayyukan alheri, wadannan kuwa suna cikin salihan bayi.
  3. Kuma duk abin da suka aikata na alheri, to ba za a hana musu ladansa ba. Kuma Allah Yana sane da masu taqawa.

Bayan Allah ya ambaci kungiyar fasikai daga Ma'abota Littafi, sai kuma a wadannan ayoyi ya bayyana cewa, ba dukkansu suka taru suka zama daya ba; a cikinsu akwai mutanen kirki, wadanda Allah ya shirye su suka musulunta, suka rike gaskiya, suna kuma karanta littafin Allah a cikin sallolinsu na dare, kuma suna yin imani da Allah da ranar lahira. Kuma ba su tsaya ga gyara zukatansu su kadai ba; suna yin nasu kokarin su gyara wasu ta hanyar umartar su da kyawawan ayyuka da hana su aikata munana suna kuma gaggawa wajen aikata ayyukan alheri. Irin wadannan mutane su ne mutanen kirki salihai, kuma duk wani aikin alheri da za su yi ba za a haramta musu ladansa ba a wajen Allah. Allah kuma ya san masu taqawa, yana ganin ayyukansu, kuma zai yi musu kyakkyawan sakamako a lahira.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Adalcin Allah. Bayan ya soki kungiyar Ma'abota Littafi masu kafirce wa Allah, da kashe annabawa ba da wani hakki ba. To don kada wani ya zaci duka haka halayensu suke, sai Allah ya bayyana cewa, a cikinsu akwai na kirki, masu halaye da yake so. To haka ya wajaba a rika yin adalci, ko da kuwa da wanda ake sabani da shi ne.
  2. Muhimmancin yawan karatun Alkur'ani cikin dare. Kuma sallar nafila ta dare ta fi ta rana saboda mai salla a lokacin ya fi tara hankalinsa wuri guda, domin babu wani abu da zai dauki hankalinsa kamar da rana, kuma akwai kauce wa riya a cikinta, da sauran wasu abubuwa masu rushe ayyuka, ko su nakasa su.
  3. Muhimmancin umarni da kyakkyawan aiki, da hani da mummuna. Saboda muminai bayan sun inganta kansu da imani, kuma suna kokarin inganta wasu ta hanyar umartar su da kyawawan ayyuka, da kuma hana su munana, wannan kuwa shi ne matukar kamala.
  4. An gabatar da ambaton karatun Alkur'ani a kan imani da Allah da ranar lahira, domin bai yiwuwa mutum ya yi imani da abu, sai bayan ya san shi, don haka idan sun karanta ayoyin Allah, sai su san mene ne ranar lahira, sannan su yi imani da ita.

Tarjama Da Tafsirin ayoyin 116-117

  1. Lalle wadanda suka kafirta, dukiyoyinsu da 'ya'yansu ba za su wadatar da su komai ba a wurin Allah; kuma wadannan su ne ma'abota wuta; suna masu dawwama a cikinta. --Quran/3/116
  2. Misalin abin da suke ciyarwa a wannan rayuwa ta duniya kamar misalin iska ce mai tsananin sanyi, sai ta auka kan shukar wadansu mutanen da suka zalunci kawunansu, sai ta lalata ta. Kuma Allah bai zalunce su ba, sai dai kawunansu suke zalunta. --Quran/3/117

Bayan da Allah ya ambaci siffofin wadanda suka yi imani daga cikin kafirai, sai kuma a wadancan ayoyi Allah ya bayyana siffofin kafirai da azabar da ya tanada musu a ranar Alkiyama, domin a gane bambancin da ke tsakanin mumini da kafiri. Allah ya bayyana cewa yawan dukiya da 'ya'ya da kafirai suke takama da shi a duniya, a wurin Allah ba zai wadatar da su komai ba, domin ba zai kare su daga azabar Allah ba; za a jefa su wutar Jahannama ne, su dawwama a cikinta har abada.

Kuma dukiyar da kafirai suke ta batarwa a nan duniya, da nufin yakar gaskiya da masu kira zuwa gareta, za su kashe ta ne a banza, domin ba za su taba cin nasara ba. Domin misalin wannan ta'asar da suke yi ta yi kama ne da wanda ya yi shuka, yana fatan samun amfaninta, sai wata guguwa mai karfi da sanyi ta taso ta halaka shukar gaba daya, bai tsira da komai ba daga amfaninta, kamar yadda Allah ya bayyana a Suratu Anfali, aya ta 36. Kuma wannan sakamako da Allah ya yi wa kafirai bai zalunce su da komai ba, suka zalunci kawunansu ta hanyar kafirci da fafutukar sai sun bice hasken Allah.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Sanin cikar ikon Allah, ta yadda babu wata hanya da kafirai za su iya bi su kare kansu daga azabarsa, komai yawan dukiyarsu da 'ya'yansu, domin ba za su tsinana musu komai ba a wajen Allah.
  2. Gargadi a kan guje wa ruduwa da yawan dukiya ko 'ya'ya. Domin wanda duk ya rudu da su; to ba zai saurari mai fada masa gaskiya ba, domin shi a ganinsa yawan dukiyar da aka ba shi ya ishe shi komai, don haka da wuya ya saurari gaskiya, ko ya nemi saninta.
  3. Ran mutum a wajensa amana ce Allah ya danka a hannunsa, don haka tilas ne ya kula da wannan amanar, kada ya aikata wani abu da zai cutar da ran nasa' idan har ya yi haka; to ya zama azzalumi.
  4. Allah Ta'ala ya kebance dukiya da 'ya'ya da ambato, domin su ne suka fi amfani ga mutum fiye da komai. Da dukiyarsa zai iya fansar kansa, ko ya kare kansa daga tafka asara; 'ya'ya kuma za su taimaka wa mahaifinsu, su ba shi kariya. To idan ya zamanto dan da mutum ya haifa ba zai iya tsinana masa komai ba, kuma dukiyar da yake da iko a kanta ba za ta yi masa wani amfani ba; to mene ne bayan su zai amfane shi, ya tsare shi daga kamun Ubangijinsa?

Tarjama Da Tafsirin ayoyin 118-120

  1. Ya ku wadanda suka yi imani, kada ku riki abokanan shawara wadanda ba a cikinku suke ba, ba za su sassauta muku mugunta ba, sun yi burin duk abin da zai kuntata muku, hakika kiyayya ta bayyana daga bakunansu; amma abin da zukatansu suke boyewa ya fi girma. Hakika Mun bayyana muku ayoyi; in kun kasance kuna hankalta. --Quran/3/118
  2. Sai ga shi ku dinnan kuna son su, su kuwa ba sa son ku, kuma ku kuna yin imani da Littattafai gaba dayansu, kuma idan sun gamu da ku, sai su ce: "Mun yi imani." Idan kuma sun kebanta, sai su rika cizon 'yan yatsu a kanku saboda bakin ciki. Ka ce: "Sai dai ku mutu da bakin cikinku." Lalle Allah Masanin abin da yake cikin kiraza ne. --Quran/3/119
  3. Idan wani kyakkyawan abu ya same ku sai ya bakanta musu rai, amma idan wani mummunan a ya same ku, sai su rika farin ciki da shi; amma idan kuka yi hakuri, kuma kuka yi takawa, makircinsu ba zai cutar da ku komai ba. Lalle Allah Yana kewaye da sanin abin da kuke aikatawa. --Quran/3/120 When you ˹believers˺ are touched with good, they grieve; but when you are afflicted with evil, they rejoice. ˹Yet,˺ if you are patient and mindful ˹of Allah˺, their schemes will not harm you in the least. Surely Allah is Fully Aware of what they do.

Tafsiri:

Bayan Allah SWT ya gama bayani a kan halayen muminai da na kafirai, sai kuma a wadannan ayoyi yake gargadin muminai da kada suna nuna musu asirinsu, su bar 'yan'uwansu muminai domin wadannan kadiran bai kamata a amince musu ba; duk sa'adda suka sami wata dama ta cutar da muminai; to sai sun yi amfani da ita. Kullum kuma suna jiran su ga muminai sun fada cikin wata wahala su kuma su samu abin yi musu dariya. Saboda tsananin kiyayyarsu ga muminai, har ta kai ba za su iya boye kiyayyar a zuciyarsu ba, sai su rika subutar baki suna fito da ita a fili, duk da haka kuma kiyayyar da ke cikin zukatansu ta fi girma fiye da wadda bakunansu suka furta har muminai suka ji. Allah ya bayyana ayoyinsa ga muminai a fili, kuma bayanin zai amfane su har idan sun saurare shi, sun kuma fahimce shi.

An karbo daga Abu Sa'id Alkhudiri (rA) ya ce,

Annabi SAW ya ce: "Babu wani annabi da Allah ya taba aiko shi, ko wani halifa da Allah ya ba shi halifanci, face yana da kashi biyu na masu ba shi shawara; kashin farko suna umartar sa da kyakkyawan aiki, suna kwadaitar da shi a kai; kashi na biyu kuwa suna umatarsa da sharri, kuma suna kwadaitar da shi a kan aikata shi. To tsararre shi ne wanda Allah ya tsare. [Bukhari #7198]

Narrated Abu Sa`id Al-Khudri:

The Prophet (ﷺ) said, "Allah never sends a prophet or gives the Caliphate to a Caliph but that he (the prophet or the Caliph) has two groups of advisors: A group advising him to do good and exhorts him to do it, and the other group advising him to do evil and exhorts him to do it. But the protected person (against such evil advisors) is the one protected by Allah.' " https://sunnah.com/bukhari:7198

Sannan Allah ya bayyana wani abu da ya wajaba muminai su yi hattara da shi dangane da sha'anin kafirai da munafukai; wannan abu kuwa shi ne saboda tsananin kiyayya da hassadar da ke cikin zukatansu ga muminai, ba za su taba jin suna son su a zukatansu ba. Su muminai kam suna nuna suna kaunar su su kuma kafitai ba sa son su, ba sa kuma kaunar su; tsakaninsu da su kiyayya ce kawai. Kamar yadda muminai suka yi imani da duk littattafan da Allah ya saukar wa annabawa, amma su kafirai na Yahudu da Nasara sun ki yin imani da abin da aka saukar ga Annabi SAW, bayan kuma sun jirkita nasu littattafan. To duk wanda irin wannan ne halinsa; to kamata ya yi a ki miyagun halayensu na munafirci, duk sa'adda za su hadu da muminai sai su rika nuna musu sun yi imani, amma kuma da zarar sun ware, sun kadaita da junansu, sai su rika cizon 'yan yatsunansu, saboda tsananin bakin ciki da haushin muminai, domin suna ganin irin hadin kan muminai da kaunar da ke tsakaninsu. Sai Allah ya umarci Annabinsa ya gaya musu: "Sai dai ku mutu da bakin cikinku" domin Allah ya yi alkawarin sai ya cika wannan ni'imar tasa, ya daukaka addininsa ko ba sa so, sai dai bakin ciki ya kashe su. Allah kuma yana sane da bin da yake boye a cikin kirazan bayinsa, don haka zai yi wa kowa sakayya a kan abin da ya aikata.

Sannan Allah ya bayyana abin da yake kara tsananin gabar kafiran ga muminai, watau duk lokacin da wani abin farin ciki ya sami muminai, sai su rika jin haushi, suna damuwa; yayin da kuma wani abin bakin ciki ya same su, sai su rika murna, suna jin dadi. Sai Allah ya koyar da muminai abin da zai taimaka musu wajen jure irin wannan hali na kafirai, watau su zama masu hakuri, kuma masu taqwa, domin idan har sun rungumi wadannan siffofi guda biyu, to babu wani makirci da zai cutar da su. Allah yana kewaye da saninsa game da abin da wadannan kafiran da munafukan suke yi, kuma zai saka musu a kan hakan.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Nisantar miyagun abokan shawara yana daga cikin imani, shi ya sa aka fuskantar da wannan maganar ga muminai.
  2. A nan an nuna ba kowa ne ya kamata ya zama abokin shawara ba. Idan an jarrabi mutum da mu'amala da makiya; to ya kamata mu'amalarsa ta kasance sama-sama, kada ya saki jiki ya rika buda masa sirrinsa, ko da kuwa zai rantse masa cewa yana son sa.
  3. Fadar Allah Ta'ala: "Sun so duk wani abu da zai kuntata muku..." yana nuna cewa, makiyammu suna son ganin duk abin da zai jefa mu cikin wahala, ya same mu; suna son ganin sun rushe mana tattalin arzikinmu da tsarin siyasarmu da zamantakewarmu, su kuma rusa mana addininmu, wanda samun haka shi ya fi komai muhimmanci a wurinsu.
  4. Aiki da luwa da amfani da hankali wajen la'akari da ayoyin Allah, shi ne hanyar samun ilimi da waywa.
  5. Duk sa'adda mutum ya zama mai zurfin hankali ne; to ya fi fahimtar ayoyin Allah.
  6. Gargadi ga muminai a kan haɗarin shugabantar da Yahudawa da Nasara a kan wani al'amarinsu na jagoranci. Domin su mutane ne da ba za su taƙaita ba wajen aikata wa Musulmi mugunta duk sanda suka samu dama. Kuma duk wani abin baƙin ciki da zai sami muminai to su za su yi farin ciki da shi ne; duk kuma wani abu na farin ciki da zai sami muminai to su baƙin ciki za su yi da shi. To irin waɗannan ta yaya muminai za su danƙa ragamar shugabancinsu a hannunsu?
  7. Maƙiyanmu ba za su gaji da shirya mana makirci da sharri ba; to maganin wannan kawai shi ne haƙuri da taƙawa. Mu yi haƙuri wajen aikata duk wani umarni da aka ba mu, da guje wa duk wani abu da aka hana mu. Duk wanda ya yi haƙuri ya ji tsoron Allah; to yana ƙarƙashin kulawar Ubangijinsa, babu makircin da zai cutar da shi.
  8. A ƙarƙashin aya ta 3:120, malamai suka fitar da ƙa'ida game da maƙiyi, suka ce shi ne wanda yake farin ciki da abin da ya baƙanta maka, yake baƙin ciki da abin da ya faranta maka. When you ˹believers˺ are touched with good, they grieve; but when you are afflicted with evil, they rejoice. ˹Yet,˺ if you are patient and mindful ˹of Allah˺, their schemes will not harm you in the least. Surely Allah is Fully Aware of what they do.

Tarjama Da Tafsirin ayoyin 121-129

  1. Kuma ka tuna lokacin da ka yi sammako daga wajen iyalinka, ka je kana shirya wa muminai wuraren tsayuwarsu don yaƙi. Allah kuwa Mai ji ne, Masani. --Quran/3/121
  2. Tuna lokacin da wadansu kungiyoyi guda biyu daga cikinku suka yi niyyar su ja da baya, amma Allah ne Majibincin lamarinsu. Sai muminai su dogara ga Allah kadai. --Quran/3/122
  3. Kuma tabbas hakika Allah Ya taimake ku a (yakin) Badar, alhalin kuna raunana, to ku ji tsoron Allah don ku zamanto masu godiya a gare Shi. --Quran/3/123
  4. Ka tuna lokacin da kake ce wa muminai: "Shin bai ishe ku ba idan Ubangijinku Ya kawo muku agajin mala'iku dubu uku wadanda za a saukar da su (daga sama). --Quran/3/124
  5. Haka ne, idan har za ku yi hakuri, kuma ku yi taqawa, kuma (kafirai) suka auko muku cikin gaggawa a wannan lokacin, to Ubangijinku zai ƙaro muku agaji da mala'iku dubu biyar masu alamomi. --Quran/3/125
  6. Kuma Allah bai sanya wannan ba sai don albishir a gare ku, kuma domin zukatanku su nutsu da shi. Kuma nasara ba ta zuwa daga kowa sai daga Allah Mabuwayi, Mai hikima. --Quran/3/126
  7. Domin Ya karya lagon wani bangare na kafirai ko Ya ƙasƙantar da su, sai su juya da baya suna taɓaɓɓu. --Quran/3/127
  8. Ba ka da komai cikin lamarin, ko dai (Allah) Ya karɓi tubansu, ko Ya yi musu azaba, lalle su dai azzalumai ne. --Quran/3/128
  9. Kuma abin da yake cikin sammai da kuma abin da yake cikin ƙasa na Allah ne. Yana yin gafara ga wanda Ya ga dama, Yana kuma yin azaba ga wanda Ya ga dama. Kuma Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai. --Quran/3/129

Tafsiri:

Bayan Allah SWT ya bayyana cewa hakuri da taqawa su ne makamin da mumini zai tsare kansa da shi daga cutarwar maƙiyansa,sai kuma a wadannan ayoyi Allah ya fito da bayanin abubuwan da kan sabbaba rashin samun nasara a kan maƙiya.

Allah yana tunatar da Annabinsa Muhammadu SAW lokacin da ya fito daga gidansa domin haduwa da kafiran Makka a ranar yakin Uhudu, lokacin da yake shirya rundunar muminai domin fita yaki, yana sanya kowa a muhallin da ya dace da shi. Domin Allah yana jin komai, yana jin shawarar da Annabi SAW ya yi da sahabbansa a kan wurin da ya kamata a yi wannan yaki. Kuma Allah shi ne masani dangane da ra'ayin da ya fi dacewa daga cikin ra'ayoyin da aka kawo a lokacin. Kuma yana sane da irin mugun nufin da kafirai da munafukai suka boye a zukatansu, har ma da abin da daukacin halittunsa suka boye a zukatansu.

Allah yana tunatar da Annabi SAW lokacin da wasu kungiyoyi biyu daga cikin muminai, suka yi nufin su janye daga wannan yaki, su ne kabilun Banu Salima da na Banu Harisa, sai dai kuma Allah ya kafe dugadugansu. Allah ya sanar wa Annabi SAW cewa, gare shi shi kadai ya wajaba muminai su dogara.

An karbo daga Jabir dan Abdullahi (rA) ya ce: A kanmu wannan ayar ta sauka:

"Ka tuna lokacin da wasu kungiyoyi biyu daga cikinku suka yi nufin su ja da baya, amma Allah ne majibincin lamarinsu..." Jabir ya ce: Mu ne kungiyoyin biyu, watau (i.e.) kabilar Banu Harisa da kabilar Banu Salima, kuma saukar da wannan ayar ya faranta mini rai, saboda fadarsa: "...amma Allah ne majibincin lamarinsu..." [Bukhari #4558]

Narrated Jabir bin `Abdullah:

The Verse:--

"When two parties from among you were about to lose heart, but Allah was their Protector," (3.122) was revealed concerning us, and we were the two parties, i.e. Banu Haritha and Banu Salama, and we do not wish (that it had not been revealed) or I would not have been pleased (if it had not been revealed), for Allah says:--"...Allah was their Protector."


Allah yana goranta wa muminai nasarar da ya ba su a ranar yakin Badar ne a yayin da suke 'yan kadan, masu rauni. Don haka ya dace su ji tsoron sa, su kiyaye dokokinsa, wala-alla su gode masa da baiwar da ya yi musu.

Sannan ya sake tunatar da Annabinsa Muhammad SAW, lokacin da yake yi wa sahabbansa albishir, yana cewa: "Shin ba zai ishe ku ba, Alla ya kawo muku dauki na mala'iku dubu uku (3,000), wadanda zai sauko da su daga sama su taya ku yaki?" To hakanan zai kawo muku tallafi idan har kun yi hakuri, kuma kun yi taqawa, kuma mushirkai sun bullo muku ta inda suka bullo cikin gaggawa.

Page 432

Sai Allah ya bayyana musu cewa, sanar da su da ya yi cewa, zai kawo musu agaji na mala'iku, wani albishir ne yake yi musu, domin su sami nutsuwar zukata. Daga karshe, nasara daga Allah take shi kadai, shi ne Mabuwayi, wanda ya fi karfin kowa, kuma mai hikima, zai ba su nasara ya kuma halakar da wasu kafiran, ko ya tozartar da wasu daga cikinsu, ya wulakanta su, daga karshe su koma garuruwansu a wulakance, ba tare da sun cim ma wata nasara ba. Ko kuma idan Allah SWT ya ga dama ya shiryar da su su musulunta, ko kuma ya yi musu azaba saboda zaluncinsu. Duk dai al'amauransu gaba daya suna komawa ne ga Allah, babu komai na al'amarinsu da yake a hannun wannan Annabi.

An karbo daga Anas dan Malik ya ce: An karya wa Annabi hakoransa na gaba ranar yakin Uhudu, aka kuma fasa masa kai, sai ya rika share jini daga jikinsa yana cewa: "Ta yaya mutanen da suka fasa kan Annabinsu, suka karya masa hakorinsa na gaba za su rabauta, alhalin yana kiran su zuwa ga Allah?" Sai Allah Ta'ala ya saukar da fadarsa: "Babu wani al'amari da yake hannunka..." [Muslim #1791]

It has been narrated on the authority of Anas that the Messenger of Allah (ﷺ) had his front teeth damaged on the day of the Battle of Uhud, and got a wound on his head. He was wiping the blood (from his face) and was saying:

How will these people attain salvation who have wounded their Prophet and broken his tooth while he called them towards God? At this time, God, the Exalted and Glorious, revealed the Verse:" Thou hast no authority" (iii. 127).

Sai kuma Allah ya tabbatar da cewa, shi kadai ne mai mulkin duk wani abu da yake sama, da wanda yake kasa, yana kuma yafe wa wanda ya ga damar yafe masa daga cikin bayinsa, ya kuma yi ukuba ga wanda ya ga damar yi masa ukuba, amma duk da haka shi mai yawan gafara ne, mai yawan rahama.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Kwarewar Annabi SAW wajen tsara sojojinsa a wurin yaki.
  2. Abu ne mai matukar muhimmanci ga jagoran mayaka, ya shirya mayakansa, kowanne ya nuna masa wurin tsayuwarsa da ya dace da shi, domin yin hakan yana daya daga cikin sabubban samun nasara a yaki.
  3. Kariya daga Allah take. Ba don wannan kariyar ba, da babu wanda zai kubuta daga aukawa cikin ramukan sabon Allah da zunubbai.
  4. Allah mai rufa asirin bayinsa ne masu laifi. Don haka a nan sai Allah bai fadi sunan kabilun da suka yi nufin janyewa daga fagen yaki tare da Annabi ba, kawai sai ya ce 'wadansu kungiyoyi biyu'. God conceals the faults of His slaves... hence why He didn't specify which exact groups.
  5. Allah mai tausaya wa bawansa ne, sai ya nefe shi da tsayawa da jajircewa a kan gaskiya.
  6. Wajabcin dogara ga Allah; yin haka yana daga cikin imani da Allah.
  7. Ya wajaba ga Musulmi ya sama wa kansa kariya daga duk wani abin ki, ta hanyar dogoro ga Allah, ka da ya zama mai raki.
  8. Taqawa tana daga cikin hanyoyin gode wa Allah; ita ce Musulmi zai sanya ta zama katanga tsakaninsa da azabar Allah, watau dai ya aikata abin da aka wajabta masa, ya kuma bar abin da aka haramta masa. Wannan kuwa shi ne hakikanin godiya ga Allah.
  9. Duk sa'adda bawa ya fi nuna kaskancinsa ga Allah, to ya fi kusa da samun nasararsa. A duk kuma lokacin da bawa yake nuna tsarsa, to lokacin ne yake rasa samun taimakon Allah a gare shi.
  10. Bayanin irin kyakkyawar mu'amalar Manzon Allah SAW ga sahabbansa lokacin da suke fuskantar wata fargaba da tashin hankali. Annabi SAW yakan shigar musu da kyakkyawan fata a zukatansu, wanda hakan shi ne yakan dawo musu da kuzarinsu, ya tafiyar musu da bakin cikinsu da damuwarsu, ya sa su tashi tsaye domin aiki ba ja da baya.
  11. Sama ita ce mazaunin mala'iku, sai dai sau tari sukan sauko kasa da umarni Allah.
  12. Allah yakan ba wa muminai nasara a kan kafirai, domin ya rage mugun iri, ba don ya halaka duk ilahirin kafirai ba. Saboda yana daga cikin hikimar Allah, ya bar imani da kfafirci su ci gaba da wanzuwa, suna ta qaruwa, domin tantance mumini na gaskiya da wanda ba na gaskiya ba.
  13. Cewar da Allah ya yi, al'amari ba a hannun Annabi yake ba, don haka ba ya halattun Ubangiji ba mallakinsa ne ba, don haka ba ya halatta mumini ya roke shi, ko ya nemi agajinsa da taimakonsa a kan abin da ba mai yin sa sai Allah, ballantana kuma wani waliyyi.
  14. Annabi SAW shi ma bawa ne na Allah, kuma har ya bar duniya yana karbar umarni da hani ne daga Allah. Da wannan ne za mu fahinci batan masu da'awar cewa, akwai wasu waliyyai da suke kaiwa matakin da sun fi karfin su karbi umarni ko hani daga Allah, ko kuma bawa ya kai wani matakin da shari'a take sauka daga kansa. Wannan kafirci ne, ba Musulunci ba.
  15. Allah yakan yi wa kafirai azabar da babu hannun wani Musulmi a ciki.

Tarjama Da Tafsirin Aya Ta (130-132)

  1. Ya ku wadanda suka yi imani, kada ku ci riba ninki-ba-ninkin, kuma ku ji tsoron Allah don ku rabauta. --Quran/3/130
  2. Kuma ku tsoraci wuta wadda aka riga aka yi tanadinta domin kafirai.
  3. Kuma ku bi Allah da Manzo don a ji qan ku (a ranar tashin alqiyama).

Tafsiri:

Bayan Allah ya bayyana cewa, ya taimaka wa muminai yayin da suke raunana, kuma ya taimake su ne saboda taqawarsu da bin umarninsa. Haka kuma lokacin da suka sami matsala a yakin Uhudu saboda saba wa umarnin Manzon Allah da suka yi, sai kuma a nan Allah ya tsawace su da su guji tsananin kwadayin tara dukiya, musamman ta hanyar cin dukiyar riba ninkin-ba-ninkin, wanda yana daga manyan laifukan da suka yadu a wannan lokacin.

Sannan kuma ya nuna musu hanyar samun taqawa, wadda ita ce tafarkin samun duk wata nasara. Taqawa da ma ita ce aikata umarnin Allah da guje wa haninsa. Don haka a karshen wadannan ayoyi, Allah ya ja hankalin muminai da su ji tsoron Allah, don su sami rabauta duniya da lahira, kuma su tsoraci wuta, ta hanyar sanya shamaki tsakaninsu da ita, wadda an shirya ta ne musamman domin kafirai, wadanda suka bijire wa imani da Allah da abin da ya saukar wa Annabinsa. Ya umarci muminai da su yi wa Allah da'a da Manzonsa, domin da haka ne za su sami rahama duniya da lahira.

Daga wadannan...

  1. Kaurace wa cin riba yana daga cikin imani.
  2. Taqawa ita take sa bawa ya guje wa aikata abin da ya saba aikatawa wanda Allah ba ya so.
  3. Bawa yana sa ran samun rahamar Allah ne yayin da ya yi biyayya ga Allah da Manzonsa.
  4. Dalilin ambaton 'ninkin-ba-ninkin' a lamarin riba, saboda abin da yake faruwa ke nan a lokacin da ayar take sauka. Domin mutum a lokacin yakan ba wa wani bashi amma da kari, shi kuma sai ya biya shi a lokacin da suka kayyade a tsakaninsu. Idan lokacin biya ya yi ba shi da abin da zai biya, sai mai kudin ya kara masa lokaci, tare da kara masa wani kudin na riba a kan na da, da haka, da haka har ribar ta ninnika uwar kudin. Shi ne ya sa Allah ya yi bayanin abin da yake faruwa, ba wai ana nufin riba ba za ta zama haramun ba sai ta zama ninkin-ba-ninkin, kamar yadda wasu suke da'awa. Riba haramun ce komai karancinta, kamar yadda Allah ya bayyana a Suratul Baqara, aya ta 287 Quran/2/287.
  5. Bayanin an riga an halicci wutar Jahannama, tana nan an tanade ta domin kafirai masu dawwama a cikinta har abada. Amma Musulmai masu sabon Allah, su za su shige ta ne a yi musu azaba gwargwadon laifuffukansu, sannan a fitar da su daga cikinta.

Tarjama Da Tafsirin Aya Ta (133-136)

  1. Kuma ku yi gaggawa zuwa ga neman gafara ta musamman kuma Aljanna wadda fadinta yake daidai da sammai da kasa, an yi tanadinta domin masu taqawa. --Quran/3/133
  2. Su ne wadanda suke ciyarwa a cikin halin yalwa da halin kunci, kuma masu boye fushi kuma masu yin afuwa ga mutane. Allah kuwa Yana son masu kyautatawa. --Quran/3/134
  3. Su ne kuma wadanda idan sun aikata mummunan aiki, ko suka zalunci kansu, nan take sai suka tuna da Allah, sai su nemi gafarar zunubansu. Wane ne kuwa mai gafarar zunubbai in ba Allah ba? Kuma ba sa zarcewa a kan abin da suka yi, alhali suna sane. --Quran/3/135
  4. Wadannan sakamakonsu shi ne gafara ta musamman daga wajen Ubangijinsu, da gidajen Aljanna wadanda koramu suke gudana ta karkashinsu, suna masu dawwama a cikinsu. Kuma madalla da sakamakon masu aiki. --Quran/3/136

Tafsiri (page 438):

A wadannan ayoyi, Allah yana umartar muminai da yin gaggawa wajen samun gafarar Allah, da samun shiga Aljanna, wadda fadinta ya kai girman sammai da kassai. An tanade ta domin masu taqawa, su ne masu ba da dukiyarsu taimako a halin suna cikin yalwa ko halin kunci, ba sa rowar abin da suka mallaka. Kuma suna iya mallakar zukatansu lokacin fushi, suna danne bacin ransu, kuma masu afuwa ga wadanda suka munana musu. Wadannan siffofi ne na masu kyautatawa, Allah kuwa yana son masu kyautatawa.

Tarjama Da Tafsirin ayoyin 137-141

  1. Haƙiƙa sunnoni (na Allah) sun riga sun shuɗe gabaninku, to sai ku yi tafiya cikin ƙasa, sai ku duba ku ga yaya ƙarshen masu ƙaryatawa ya zama? --Quran/3/137
  2. Wannan bayani ne don mutane, kuma shiriya ce da kuma wa'azi ga masu taqwa. --Quran/3/138
  3. Kuma kada ku yi rauni, kuma kada ku yi bakin ciki, kuma ku ne mafiya daukaka in dai har kun kasance muminai. --Quran/3/139
  4. Idan ma wani miki ne ya same ku a jiki, to hakika miki irinsa ya sami mutanen (Makka). Kuma wadannan kwanaki ne da muke jujjuya su tsakanin mutane domin Allah Ya bayyanar da wadanda suka yi imani (a gane su), kuma Ya riƙi shahidai a cikinku. Allah kuwa ba Ya son azzalumai. --Quran/3/140
  5. Kuma don Allah Ya tace wadanda suka yi imani, kuma don Ya halakar da kafirai. --Quran/3/141

Tafsiri: (shafin/pg 441)

A wadannan ayoyi Allah yana lallashin zukatan Musulmi ne bayan abin da ya faru gare su a yakin Uhudu, na kashe da dama daga cikinsu da kafirai suka yi. Allah yana bayyana masu cewa, su zagaya a bayan kasa don su ga yadda sunnonin Allah suka faru ga al'ummomin da suka gabace su, su ga yadda Allah ya yi wa kafiran ga daukacin mutane, yana fayyace musu gaskiya, yana kuma nuna musu hanyar barna don su guje ta, sannan yana shiryar da masu taqwa zuwa mikakkiyar hanya, yana gargadin su da nisantar hanyoyin bata.

Allah kuma ya umarci Musulmi da kada su yi rauni domin abin da ya same su a yakin Uhudu; su ne ko yaushe suke a sama, kuma masu rinjaye matukar suna rike da imaninsu. Idan suna ganin an kashe musu 'yan'uwa a yakin Uhudu ko an yi wa wasu raununnika, to su tuna su ma kafiran irin haka ya faru gare su, an kashe wasu da dama daga cikinsu, an raunana wasu a yakin Uhudu da yakin Badar. Don haka kada su ci gaba da wannan damuwar da suke ciki, su sani wannan sunna ce ta Allah, haka yake jujjuya kwanaki a tsakanin mutane, yau ku yi nasara, gobe kuma makiyanku su yi nasara a kanku. To amma hikimar Allah a irin wannan aiki nasa ita ce don ya rarrabe tsakanin muminai na gaskiya da wadanda suke na jabu, kuma Allah ya nufi wasu muminai da yin shahada, watau wadanda za a kashe don daukaka addininsa. Allah ba ya son azzalumai, wadanda su ne kafirai da munafukai faɗararru wadanda suka zalunci kawunansu. Kuma yana daga hikimar Allah a wannan aiki nasa, ya tsarkake muminai daga zunubbansu a dalilin abin da ya same su na kisa da raunatarwa, domin idan ya zamanto koyaushe su suke ta samun nasara, to sai ji-ji-da-kai ya shiga zukatansu, sai kuma su sami raunin imani, wanda kuma shi ne zai jawo musu fushin Allah da azabarsa. Sannan kuma Allah ya yi alkawarin sai ya halakar da kafirai saboda dagawarsu da zurfafawa cikin zalunci da kafirci, wanda shi zai sa Allah ya kawar da su daga bayan ƙasa gaba dayansu.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Kwadaitarwa a kan yin izinai da wa'azi daga abubuwan da suka faru ga al'ummomin da suka gabata.
  2. Nuni a kan cewa abin da ya faru ga masu ƙaryatawa na farko, irinsa zai iya faruwa ga masu karyatawa na yau da na gobe. Don haka al'umma su kwantar da hankulansu a kan duk wani zalunci da yake faruwa gare su, kuma su yi taka-tsan-tsan kada su shigar da kansu cikin masu karyatawa, sai uƙubar da ta same su su ma ta haɗa da su. Don haka a nan akwai lallashi, da kuma jan kunne.
  3. Allah yana kwantar da hankalin Musulmi cewa, gwagwarmaya tsakanin gaskiya da karya wani dadadden abu ne a tarihin kafuwar duniya, kuma koyaushe masu gaskiya ne suke samun galaba a kan makaryata ta hanyar taqwa da hakuri.
  4. Ana yin tafiya ne a bayan kasa don wata kyakkyawar manufa a shari'ance. Amma idan tafiye-tafien mutum ba da wata kyakkyawar manufa ba ne, to wannan wahalar da kai ne kawai da barnar dukiya wadda shari'a ta hana.
  5. Alkur'ani littafi ne da ya zo da shiriya ga mumini da kafiri.
  6. Alkur'ani ya tattara bayanai a kan kowane abu kuma ga kowa da kowa, babu abin da Allah bai aje tushen bayaninsa a Alkur'ani ba, hakanan babu wanda bayanin Alkur'ani bai shafe shi ba.
  7. Babu masu amfanuwa da Alkur'ani sai masu taqwa. Don haka taqwa ita ce musabbabin samun shiriyar Allah, da kuma wa'azantuwa da Alkur'ani.
  8. Wanda duk bai wa'azantu da Alkur'ani ba, to ya tuhumi kansa.
  9. Duk sa'adda taqwar mutum ta kara, to shiriyarsa da wa'azantuwarsa da Alkur'ani ma za su karu.
  10. Imani yana kara sanya wa zuciya karfi da karin dogaro ga Allah a cikinta.
  11. Ya kamata mumini a kullum ya kasance mai karfin hali da rashin karayar zuci, domin duk sa'adda mutum ya karaya, ya yi rauni, to zai yi asarar alheri mai yawa. Da zarar ya tashi tsaye da karfinsa, to zai cim ma samun duk alhairin da yake nema da izinin Allah, domin ba wanda ya san gobe sai Allah.
  12. Duk sa'adda imanin al'umma ya karu, to daukakarta ma za ta karu, don haka bawa yana samun daukaka ne a wurin Allah, gwargwadon imaninsa.
  13. Allah swt yakan hada bawansa da nau'in jarraba iri-iri don ya gwada imaninsa.
  14. Allah swt ya sanya rayuwar duniya ta zama mai jujjuyawa ga dan'adam daga dadi zuwa wuya, daga wuya zuwa dadi ko daga sharri zuwa alheri ko daga alheri zuwa sharri, domin kada mutum ya nutsu a kan cewa kullum zai yi ta zama ne a yanayin jin dadi, wanda hakan yana iya mantar da shi ranar lahira. Kuma da a ce Allah ya aje duniya a yanayin azaba koyaushe, to da dan'adam ya jikkata.
  15. A cikin wadannan ayoyi, Allah ya lallashi zukatan muminai a kan matsalar da ta same su a yakin Uhudu sai ya bayyana musu wasu hikimomin da suka sa ya yi hakan, kamar haka:
    1. 1) Ita duniya Allah yana bayar da ita ga mumini da kafiri, saboda da man ita gida ne mai karewa, sabanin lahira, ita Allah ba ya bayar da ita sai ga mumini kadai.
    2. 2) Allah yana jarrabar bayinsa ya sa kafirai su yi galaba a kansu don tantance tsakanin mumini na gaskiya da wanda ba na gaskiya ba.
    3. 3) Da a ce koyaushe Musulmi su ne masu cin nasara a kan kafirai, to da sai mutane su rika shiga Musulunci ba don suna so ba, sai don suna tsoro.
    4. 4) Allah yakan dora kafirai a kan Musulmi, a wasu lokuta su kashe su, domin ya zabi shahidai a cikinsu.
    5. 5) Don Allah ya tsarkake muminai daga zunubbansu.
    6. 6) Don Allah ya halaka kafirai da azabarsa yayin da kafircinsu da zaluncinsu suka tsananta.
  16. Fadar Allah swt cewa: "Allah ba ya son azzalumai." yana nuna cewa, shahidai ba sa yin zalunci ta hanyar saba wa Allah da Manzonsa cikin ayyukansu. Don haka wanda ya mutu ta hanyar zaluntar wasu ba zai taba zama shahidi ba a wurin Allah, don Allah ba ya son azzalumai.
  17. Duk sa'adda aka siffanta wata daula da siffar zalunci, to ba za ta yi karbo ba, Allah zai kawar da ita komai dadewa.

Tarjama Da Tafsirin ayoyin 142-145 na Surar Ali Imran

  1. 142) Yanzu kuma tsammanin za ku shiga Aljanna ne alhalin Allah bai bayyanar da masu yin jihadi daga cikinku ba, kuma bai bayyanar da masu hakuri ba. --Quran/3/142
  2. Kuma hakika kun kasance a da can kuna ta burin mutuwa tun kafin ku gamu da ita, to hakika a yau ga ta kun gan ta alhali kuna kallo da ido. --Quran/3/143
  3. Kuma Muhammadu ba wani ne ba face Manzo kawai wanda hakika manzanni sun shude gabaninsa. Shin yanzu idan ya mutu ko aka kashe shi, sai ku juya baya a kan dugaduganku? Duk kuwa wanda ya juya baya a kan dugadugansa to ba zai cuci Allah da komai ba. Kuma da sannu Allah zai saka wa masu godiya. --Quran/3/144
  4. Kuma babu wani rai da zai mutu sai da izinin Allah, rubutaccen abu ne qayyadajje. Kuma duk wanda yake nufin sakamakon duniya, za mu ba shi ita, wanda kuma yake nufin sakamakon lahira, to za mu ba shi ita. Kuma da sannu za mu saka ma masu godiya.

Tafsiri:

A nan Allah yana nuna kuskuren muminai masu zaton cewa za su shiga Aljanna don kawai sun yi imani, ba tare da Allah ya jarrabe su ya tantance masu jihadi dominsa da kuma masu hakuri.

Allah kuma ya tuna musu cewa, sun kasance a baya suna fatan haduwarsu da abokan gabarsu, suna mararin su yi mutuwar shahada; to ga shi a ranar Uhudu sun ga mutuwar da idanunsu, kuma sun kasa jurewa su yi hakuri, har su kai ga samun abin da suke fatan su samu.

Sannan Allah ya ci gaba da bayanin cewa, Annabi SAW ba mai dawwama ne a duniya ba; shi ma kamar sauran annabawa yake; wasu daga cikinsu mutuwa suka yi, wasu kuma kashe su aka yi. To yanzu idan shi ma ajalinsa ya qare ta hanyar mutuwa ko kisa, shi ke nan sai su yi ridda su bar addininsu? To wanda duk ya yi ridda ya bar addinin Allah, to ba zai cutar da Allah da komai ba, kuma Allah zai saka wa masu godiya daga cikin bayinsa.

Allah kuma ya bayyana cewa, babu wani rai a duniya da zai mutu sai da izinin Allah, wato idan ajalinsa ya yi. Sannan Allah ya bayyana cewa, yana ba wa kowa sakamakon aikinsa daidai da niyyarsa; wanda ya yi aikinsa don neman duniya, to sai Allah ya ba shi wani abu daga cikinta; wanda kuma ya yi aikinsa don neman ladan lahira, shi ma sai Allah ya ba shi wani abu daga cikinta kuma zai saka wa masu godiya.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Son Allah da son gidan lahira ba kawai da fatar baki yake ba; abu ne da yake tare da aiki da jarrabawa ta Ubangiji. Yayin da Allah zai jarraba bayinsa da wata masifa to a nan ne zai tantance mumini na gaskiya da bara-gurbi.
  2. Ba a shiga Aljanna ta hanyar buri kadai; ana samun Aljanna ne ta hanyar aiki na gari da juriya a kan barin saba wa Allah.
  3. Bai dace ga mumini ya rika yi wa kansa fatan gamuwa da mummunan abu ko mai wahala ba. Don haka aka hana muminai fatan faruwar yaki, sai fa idan Allah ne ya qaddara faruwarsa, to sai su yi hakuri su jajirce.
  4. Babban abin da yake yin tasiri wajen samun kyakkyawa ko mummunan sakamako daga Allah, shi ne niyyar bawa, ba kawai abin da yake na zahirin aikinsa ba.
  5. Tabbatar da cewa, Annabi mutum ne kamar sauran annabawa da Allah ya aiko. Ya rayu har ya isar da saqon da aka aiko shi da shi, kuma ya rasu ya koma ga Ubangijinsa; don haka ba ya nan a duniya kamar yadda wasu suke riyawa.

Tarjama Da Tafsirin ayoyin 146-148 na Surar Ali Imran

  1. 146) Kuma sau da yawa an sami wani annabi (daga cikin annabawa), mabiya masu yawa sun yi yaki tare da shi, amma ba su taba yin rauni ba saboda abin da ya same su a tafarkin Allah, kuma ba su taba yin ragwanci ba, kuma ba su taba mika wuya ba. Kuma Allah Yana son masu hakuri. --Quran/3/146
  2. Kuma ba su da wata magana sai fadar: "Ya Ubangiji, Ka gafarta mana zunubanmu da ketare iyakar da muka yi cikin lamurranmu, kuma Ka tabbatar da dugaduganmu, kuma Ka taimake mu a kan mutanen da suke kafirai. --Quran/3/147
  3. Sai Allah Ya ba su ladan duniya da kyakkyawan lada na lahira. Kuma Allah Yana son masu kyautawa. --Quran/3/148

Tafsiri:

Bayan Allah ya ba da labarin abin da ya faru ga muminai a ranar yakin Uhudu, sanda aka samu cikas a yakin, har wasu daga cikinsu suka gudu daga fagen daga, sai kuma Allah ya nuna musu cewa, hanyar mabiya annabawa iri daya ce, watau hakuri da juriya a wurin jihadi, saboda haka su ma bai dace da su gudu ba.

A kan wannan ne Allah yake ba da labarin cewa, sau da yawa wani annabi daga cikin annabawa yakan yi yaki tare da mabiyansa masu yawa, kuma wani rauni ya same su a yakin, amma hakan bai sa sun karaya sun rabu da addininsu ko sun watsar da jihadin daukaka kalmar Allah ba; jikinsu bai yi sanyi ba, zukatansu ba su yi rauni ba, himmarsu ba ta dakushe ba, ba su ba makiyansu kai bori ya hau ba. Don haka Allah yake son masu hakuri irin wadannan.

Bugu da kari, duk irin abin da ya sami wadannan jarumai a yake-yakensu, ba abin da suke furtawa da bakunansu sai kawai neman gafarar Allah a kan zunubbansu ko abin da suka ketare iyakar Ubangijinsu a cikin lamuransu. Suna kuma rokon sa ya ba su ikon jajircewa, ya kuma ba su nasara a kan makiyansu kafirai. A sakamakon haka, sai Allah ya yi musu kyakkyawar sakayya ta duniya, ya ba su nasara da ganima da daukaka, kuma ga kyakkyawan sakamako na lahira, suka cim ma yardar Allah da dawwama a gidan Aljanna. Allah kuwa yana son masu kyautatawa, don haka ne ya yi musu kyautayinsa a duniya da lahira.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Yin koyi da magabata na gari daga cikin al'ummomin da suka gabace mu.
  2. Wanda duk ya yi hakuri a wajen biyayya ga Allah Ta'ala, bai nuna gazawa ba ko raki, to wannan Allah zai so shi.
  3. Wanda duk zai dogara da dabararsa da karfinsa wajen neman biyan bukatarsa, to zai gamu da cikas da kaskanci, amma wanda zai rika addu'a da komawa ga Allah, yana neman taimakonsa, to wannan shi ne mai samun biyan bukatarsa.
  4. Gabatar da tuba da neman gafara a lokacin addu'a yayin da wani bala'i ya sauka. Domin duk wani bala'i da zai auku a duniya, to yana aukuwa ne saboda zunubban dan'adam, don haka ba abin da zai yaye shi, sai tuba da neman gafara.

Tarjama Da Tafsirin ayoyin 149-155 na Surar Ali Imran

  1. 149) Ya ku wadanda suka yi imani, idan har kuka yi biyayya ga wadanda suka kafirta, to za su mayar da ku baya a kan dugaduganku, sai ku juya kuna hasararru. --Quran/3/149
  2. A'a, Allah Shi ne Majibincin lamarinku; kuma Shi ne Fiyayyen masu taimako. --Quran/3/150
  3. Da sannu za Mu jefa tsoro a cikin zukatan wadanda suka kafirta saboda abin da suka yi an sanya wa Allah kishiya, abin da bai saukar da hujja a kai ba; kuma makomarsu ita ce wuta. Kuma tir da makomar azzalumai (idan ta zama wuta). --Quran/3/151
  4. Kuma tabbas hakika Allah Ya cika muku alkawarinsa yayin da izininsa; har zuwa lokacin da kuka yi rauni, kuma kuka yi jayayya a cikin umarnin (Manzo), kuma daga karshe kuka saba bayan (Allah) Ya nuna muku irin abin da kuke so. Cikinku akwai wadanda suke nufin duniya, kuma cikinku akwai wadanda suke nufin lahira. Sannan sai Ya kautar da ku kuka bar su don ya jarrabe ku; kuma tabbas hakika Allah Ya yi muku afuwa. Kuma Allah Ma'abocin falala ne ga muminai. --Quran/3/152
  5. Ka tuna lokacin da kuke gudowa ba kwa waiwaye ma ku ga wanda yake baya da ku, kuma Manzo yana can bayanku yana ta kiran ku, sai (Allah) Ya saka muku da damuwa bisa damuwa domin kar ku yi bakin ciki bisa abin da ya kubuce muku, da abin da ya same ku. Allah kuma Mai cikakken sanin abin da kuke aikatawa ne. --Quran/3/153
  6. Sannan bayan damuwa sai (Allah) Ya saukar muku da kwanciyar hankali har gyangyadi yana daukar wasu daga cikinku; amma wani sashin kuma tasu ta ishe su, suna yi wa Allah zato wanda ba na gaskiya ba, zato irin na jahiliyya; suna cewa: "Anya kuwa muna da ta cewa cikin wannan lamari?" Ka ce: "Lalle al'amari gaba daya na Allah ne." Suna boyewa a cikin rayukansu abin da ba sa bayyana maka shi; suna cewa: "In da al'amarin a hannunmu yake ai da ba a kashe mu a nan ba." Ka ce: "Ko da kun kasance kuna cikin gidajenku, tabbas da wadanda aka rubuta za su mutu sun fito da kansu, sun zo inda nan ne za su kwanta (dama)." Kuma Allah (Ya kaddara haka) don Ya jarraba abin da yake cikin qirazanku, kuma don Ya tace abin da yake cikin zukatanku. Kuma Allah Masanin abin da yake cikin zukata ne. --Quran/3/154
  7. Lalle wadanda suka gudu daga cikinku yayin da runduna biyu suka hadu, Shaidan ne ya so ya zamar da su saboda wani laifi da suka yi; kuma tabbas hakika Allah Ya yi musu afuwa. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai hakuri. --Quran/3/155

Tafsiri:

A wadannan ayoyi Allah yana gargadin muminai ne da kada su buye ma ta kafirai, domin yi musu biyayya zai iya jefa su cikin kafirci, su halaka duniya da lahira. Allah shi ne mai jibintar lamarin bayinsa, kuma shi ne mai ba da nasara; su kuma kafirai ba wata nasara ko taimako da za su iya ba muminai.

Sannan Allah ya yi wa muminai albishir cewa, zai jefa tsoro a cikin zukatan kafirai, saboda shirkar da suke yi wa Allah ba tare da wata hujja ko wani dalili ba, a lahira kuma wutar Jahannama ce makomarsu, tir kuwa da wannan irin makoma ta azzalumai.

Sai Allah ya cigaba da tunatar da sahabban Annabi SAW matsalar da aka samu a yakin Uhudu ta bangaren wasu daga cikinsu saboda saba wa umarnin Annabi SAW da suka yi, bayan da Allah SWT ya cika musu alkawarin da ya yi musu na ba su nasara a kan abokan gabarsu. Da farko Allah ya dora muminai a kan kafirai, har sun fara kashe su, sai kuma Musulmi suka fara ja da baya a sakamakon sabanin da ya barke tsakanin maharba hamsin da Annabi ya ajiye su a kan wani bangare na dutsen Uhudu, ya umarce su da kada su bar wannan wurin ko da kuwa sun ga alamun cin nasara tare da Musulmi. To amma sai suka saba wannan umarni yayin da suka ga Musulmi sun fara cin nasara a kan kafirai, suna bin su da sara da suka, sai kuma wasu suka tafi suna kwasar ganima, suka bar wurin tsayuwarsu, amma wasu sun ci gaba da tsayuwa inda aka tsayar da su. Daga nan sai Allah ya juyar da lamarin muminai, galaba ta tabbata ga kafirai, suka juyo kan Musulmi da sara da suka ta gaba ta baya.

Jabir dan Abdullahi rA ya ba mu labarin abin da ya faru a ranar Uhudu ya ce: "Mun hadu a filin yaki tare da mushrikai, Annabi SAW ya ajiye wasu maharba a kan wani dutse, ya shugabantar musu da wani sahabi ana kiran sa Abdullahi dan Jubai rA, ya kuma fada musu cewa: "Kada ku bar wurarenku ko da kuwa kun ga mu ne muka yi galaba a kansu ko kuma kun ga sun yi galaba a kanmu, to kada ku taho taimaka mana." Jabir ya ce: "Yayin da muka fara fafatawa da su, sai suka ranta a na kare, muka ga mata suna ta gudu suna hawan duwatsu, sun bude qwaurinsu ana ganin mundayensu. Da maharban nan na kan dutse suka ga haka, sai suka rika cewa: "Ganima! Ganima!!" Sai shugabansu Abdullahi ya ce musu: "Annabi SAW fa ya umarce mu da kada mu bar wurarenmu." Sai suka qi jin maganarsa, suka shiga kwasar ganima. Haka na faruwa, sai reshe ya juye da mujiya, mushirikai suka yiwo kansu, har suka kashe sahabbai saba'in. Daga nan Abu Sufyan ya leko yana cewa: "Muhammadu na cikinku? Dan Abu Quhafata yana cikinku? Dan Khaddab yana cikinku?" Duk Annabi SAW yana ce wa sahabbai: "Kada ku amsa masa." Sai Abu Sufyan ya ce: "Duk an kashe wadannan. Da a ce suna da rai, da sun amsa." Sai Umar ya kasa hakuri, ya ce: "Karya kake maqiyin Allah! Allah ya bar maka abin da zai ci gaba da tozarta ka." Sai Abu Sufyan ya ce: "Sama dai, sama dai gunkin Hubal." Sai Annabi SAW ya ce: "Ku ba shi amsa." Sai suka ce: "Me za mu ce masa?" Sai ya ce: "Ku ce: Allah ne mafi daukaka, kuma mafi girma." Sai Abu Sufyan ya ce: "Muna da Uzza, amma ku ba ku da Uzza." Sai Annabi SAW ya ce: Ku ba shi amsa." Sai suka ce: "Me za mu ce?" Sai Annabi SAW ya ce: "Ku ce Allah ne mai jibintar mu, ku ba ku da mai jibintar ku." Sai Abu Sufyan ya ce: "Wannan rana ta zama a madadin ranar Badar. Yaki yau nasara gare ka ne, gobe ga makiyanka. Za ku ga wanda aka daddatsa shi bayan an kashe shi cikin mutanenku, ba ni ne na yi umarni da hakan ba, amma kuma bai baqanta mini rai ba." [Bukhari #4043]

1 We faced the pagans on that day (of the battle of Uhud) and Mun hadu a filin yaki tare da mushrikai,
2 the Prophet (ﷺ) placed a batch of archers (at a special place) and appointed `Abdullah (bin Jubair) as their commander and said, Annabi SAW ya ajiye wasu maharba a kan wani dutse, ya shugabantar musu da wani sahabi ana kiran sa Abdullahi dan Jubai rA, ya kuma fada musu cewa:
3 "Do not leave this place; if you should see us conquering the enemy, do not leave this place, and if you should see them conquering us, do not (come to) help us," "Kada ku bar wurarenku ko da kuwa kun ga mu ne muka yi galaba a kansu ko kuma kun ga sun yi galaba a kanmu, to kada ku taho taimaka mana."
4

Wannan jarraba ce da Allah swt ya yi wa muminai don ya bambance mai biyayya daga cikinsu da wanda ya fanɗare. To amma kuma Allah ya ce ya yafe musu, domin haka yake yin falalarsa ga muminai.

Sannan Allah ya ci gaba da tunatar da su lokacin da suka fita a guje ba mai waiwayen wani, lokacin kuma Annabi SAW yana ta kiran su, yana neman su da su tsaya su daina gudu; to amma ina, sun bar shi a bayansu, ba sa amsa kiransa, sai a sakamakon haka Allah ya jefa musu wani bakin ciki a zukatansu, inda aka baza jita-jitar cewa an kashe Annabi SAW. Wannan ya zarce sauran ababen bakin cikin da ya same su a wannan ranar, na rashin samun nasara ko ganima, da kashe wasu daga cikinsu, da yi wa wasu rauni.

Bayan wannan bakin ciki ne sai kuma Allah swt ya saukar wa muminai nutsuwa, har wasu daga cikinsu suka rika gyangyadi. An karbo daga Anas dan Malik rA ya ce: Abu Dalhata rA ya ce:

"Na daga kai na ranar yakin Uhudu na duba, kowa na gani a ranar gyangyadi yake ta bayan garkuwarsa, shi ya sa Allah swt ya saukar da fadarsa: "Sannan ya saukar muku da aminci bayan damuwar da kuka sami kanku a ciki, har gyangyadi ya rika lullube wasu daga cikinku." [Tirmizi #3007].

Narrated Anas: that Abu Talhah said: "I raised my head to look around[1] on the Day of Uhud, and there was not one of them that day except that he was swaying under his shield due to drowsiness. Allah said about that: Then He sent down upon you - after the distress - a slumber of security (3:154).

Wasu kuwa suka kasa samun nutsuwa suna tunanin kada a kashe su, wadannan su ne munafukai, wadanda suka rika yi wa Allah mummunan zato suna cewa, ba zai taimaka wa muminai da nasara ba. Wannan kuwa zato ne irin na jahilai wadanda ba su san Allah ba. Har ma ta kai suna cewa, su tilas ce ta sa suka fito wannan yakin, don maganar ba a hannunsu take ba, da a hannunsu take da ba a fito ba. Sai Allah swt ya umarci Annabinsa ya mayar musu da martini da cewa, ai duk al'amura suna hannun Allah swt ne shi kadai.

Sannan Allah swt ya ci gaba da bayyana siffofin munafukai da cewa, suna boye wani abu a ransu wanda ba sa bayyana shi ga Annabi SAW, watau maganar da suke yi a tsakaninsu cewa, da a ce suna da zabi a kan fitowa wannan yaki, da ba su zabi fitowa daga Madina ba, kuma da yanzu ba a kashe kowa ba. Sai Allah swt ya umarci Annabinsa ya fada musu cewa, ai ko da suna gidajensu ba su fito wurin yaki ba, da sai wadanda Allah ya rubuta mutuwarsu sun fito zuwa inda za su mutu, don haka ya kamata su san da cewa, daga Allah ne qaddara fitowarsu take, ba daga gare su ba, kuma Allah swt ya yi haka ne don ya jarraba abin da yake cikin zukatansu, ya fito da mai kyau da marasa kyau. Kuma Allah ya san abin da bayinsa suke boyewa a zukatansu, zai yi wa kowa hisabi gwargwadon aikinsa.

Sai kuma Allah swt ya bayyana cewa, gudun da wasu sahabbai suka yi daga fagen yaki a wannan rana, ai Shaidan ne ya ingiza su ciki, kuma ya sami wannan damar ne a kansu saboda wasu laifuffukansu, amma duk da haka Allah swt ya ce ya yafe musu. Allah kuma mai yawan gafara ne, mai yawan hakuri.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Gargadi ga muminai da kada su sake su biye ma ta makiyansu kafirai; wannan zai sa su yi ta jan su a hankali har su kai su ga yin ridda su bar Musulunci.
  2. Gargadi game da yin shirka, wadda ita ce ke janyo bala'i a duniya da lahira. Kuma masu yin shirka koyaushe a tsorace suke, kuma za su gamu da azabar lahira ne.
  3. Jayayya da sabon Allah swt suna daga cikin abubuwan da ke jawo rashin cin nasara.
  4. Kwadaitarwa a kan hadin kai tsakanin Musulmi.
  5. Wajibi jagoran mayaqa ya zama jarumi, marasa tsoro, wanda zai yi kokarin tattaro mayaqansa idan an sami matsalar da ta sa wasu daga cikinsu suka gudu daga fagen yaki.
  6. Bayyana jarumtar Annabi SAW a fagen yaki da rashin tsoronsa ga abokan gaba.
  7. Mutum ya saba wa Allah bayan wata ni'ima da ya yi masa, ya fi girma da tsanani fiye da wanda ya yi sabo ba cikin ni'ima ba, shi ya sa Allah SWT ya ce: "Kuma daga karshe kuka saɓa bayan ya nuna muku abin da kuke so."
  8. Sahabbai ba ma'asumai ne ba; sukan yi laifi, sai dai sukan gaggauta tuba, Allah swt kuma yana yafe musu.
  9. Tarbiyantar da muminai a kan cewa, kada su rika nuna damuwa a kan wata jarrabawa da ta same su. Domin abin da Allah swt ya qaddara faruwarsa shi ne yake faruwa, kuma bakin ciki ba ya dawo da abin da aka rasa, sai dai ya qara wa bawa wani sabon bala'in, domin zai hana shi aikata komai na maslahar rayuwarsa.
  10. Allah yana duba zukatan bayinsa ne. Duk sa'adda zuciya ta gyaru; to aiki ma zai gyaru, amma idan ta bace, to aikin ma sai ya bace.
  11. Babu wanda zai iya kauce wa qaddara, kowane irin mataki kuwa zai dauka.
  12. Aikata zunubi yakan jawo wani zunubin, kamar yadda aikata alheri yakan haifar da wani alheri a bayansa.

Tarjama Da Tafsirin ayoyin 156-158 na Surar Ali Imran

  1. 156) Ya ku wadanda suka yi imani, kada ku kasance kamar wadanda suka kafirta, kuma suka rika fada wa 'yan'uwansu yayin da suka yi tafiya a bayan qasa, ko kuma suka kasance mayaqa: "In da sun kasance tare da mu, ai da ba su mutu ba, kuma da ba a kashe su ba," don Allah Ya sanya waccan (maganar) ta zamo nadama a cikin zukatansu. Kuma Allah Shi ne Mai rayawa, kuma Shi ne Mai kashewa. Kuma Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne. --Quran/3/156
  2. Kuma lalle idan ma har an kashe ku a wajen yada kalmar Allah ko kuma kuka mutu, to kuna da gafara ta musamman a wajen Allah da kuma rahama, wanda shi ne mafi alheri fiye da abin da suke tarawa. --Quran/3/157
  3. Kuma lalle in kuka mutu ko aka kashe ku, lalle zuwa ga Allah dai za a mayar da ku. --Quran/3/158

Tafsiri

A wadannan ayoyi Allah yana yi wa muminai kashedi daga yin munanan maganganu irin na kafirai masu nuna rashin imani da qaddarar Allah swt. Watau sun saba duk lokacin da 'yan'uwansu kafirai suka yi tafiya ta kasuwanci ko yaqi, sai Allah ya qaddari mutuwarsu a can, sai 'yan'uwan nasu kafirai su rika cewa, da ba su fita ko'ina ba sun yi zamansu a garuruwansu da hakan bai faru gare su ba. Wannan irin muguwar akida ita ta sa Allah ya sanya musu nadama a zukatansu, masifarsu kuma ta yi qaruwa. Sun manta da cewa Allah shi kdai yake da ikon rayawa da kashewa; babu wani rai da zai mutu har sai ajalinsa ya cika, Allah kuma yana ganin duk abin da bayinsa suke aikatawa.

Sannan Allah ya tabbatar wa muminai cewa, duk wanda aka kashe shi ko ya mutu wajen daukaka Kalmar Allah, to abin da zai samu na gafarar Allah da rahamarsa, ya fi masa alheri fiye da zamansa a duniya da abin da masu tara dukiya a duniya suke tarawa. Allah kuma ya sake tuna musa cewa, ko mutuwa suka yi ko kuma kashe su aka yi, to makoma dai zuwa ga Allah take.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Ilimin Allah da qaddararsa babu wanda ya isa ya canza su. Wanda Allah ya qaddara wa rayuwa, don ya fita jihadi wannan ba zai sa shi ya mutu ba, hakanan wanda ya qaddara mutuwarsa, rashin fitarsa jihadi ba zai hana masa mutuwa ba. To gara ma ya yi mutuwar da take mafificiya a wurin Allah Ta'ala, ita ce mutuwar shahada, domin duka dai qarshe makomar daya ce, to amma sakamakon ya sha bamban.
  2. Allah ya hada tsakanin gafara da rahama, domin farin cikin dan'adam ya cika. Gafara tana nufin kawar masa da abin qi, rahama kuma tana nufin samun abin da yake qauna.

Tarjama Da Tafsirin ayoyin 159-161 na Surar Ali Imran

  1. 159) To saboda rahama ta musamman daga Allah, sai ka zamo mai tausasawa gare su; in da kuwa ka kasance mai kaushin mu'amala, mai qeqasasshiyar zuciya ne, to da sun watse sun bar ka. To ka yi musu afuwa, kuma ka nema musu gafara, kuma ka nemi shawararsu cikin duk lamura; amma idan ka riga ka qulla niyya, to ka dogara ga Allah. Lalle Allah Yana son masu dogara a gare Shi. --Quran/3/159
  2. Idan Allah Ya ba ku nasara, to ba wanda ya isa ya rinjaye ku, amma idan Ya taɓar da ku, to wane ne ya isa ya taimake ku in ba shi ba? Kuma muminai wajibi ne su dogara ga Allah Shi kadai. --Quran/3/160
  3. Kuma bai dace ba ga wani annabi ya yi ha'inci. Duk wanda ya yi ha'inci kuwa zai zo da abin da ya ha'inta ranar tashin alqiyama. Sannan kowane rai a cika masa (sakamakon) abin da ya aikata, kuma su (halitta) ba za a zalunce su ba. --Quran/3/161

Tafsiri:

A wadannan ayoyi Allah swt yana fada wa Annabinsa cewa, saboda rahamar da Allah ya yi masa ne, ya sa ya zama mai saukin kai ga sahabbansa, mai tausasa musu mu'amala, don haka duk suka tattaru a wurinsa, suna bin umarninsa. Da abin a ce shi mai mummunan hali ne, mai kakkausar zuciya, to da duk sun watse sun bar shi.

An karbo daga Aɗa'u dan Yasar ya ce: "Na gamu da Abdullahi da Amru dan Asi, sai na ce masa: "Fada mini siffar Annabi SAW da take cikin littafin Attaura." Sai ya ce: "Kwarai an siffanta shi a Littafin Attaura da wasu siffofinsa da suke cikin Alqur'ani, inda Allah yake cewa: "Ya kai wannan Annabi, lalle mun aiko ka a matsayin mai shaida, kuma mai albishir mai gargadi, kuma mai tsaron Ummiyyai, watau Larabawan da ba sa rubutu da karatu. Kai bawana ne, kuma Manzona, na sa maka suna 'Mai dogaro', ba mai mugun hali ba ko mai kaushin zuciya ko mai yawan hayaniya a kasuwanni ba, ba ya rama mummuna da mummuna, sai dai ya yi afuwa ya yi gafara. Kuma Allah ba zai karbi rayuwarsa ba, har sai bayan ya tsaida addini da shi, har mutane su furta Kalmar Shahada, wadda ita za ta bude idanun da suka makance da kunnuwan da suka kurumce da zukatan da suka toshe." [Bukhari #2124].

‘Ata’ ibn Yasar reported: I met Abdullah ibn Amr, may Allah be pleased with him, and I said, “Tell me about the description of the Messenger of Allah, peace and blessings be upon him, in the Torah.” Abdullah said, “By Allah, he is described in the Torah with some of what is mentioned in the Quran: O Prophet, We have sent you as a witness, a bringer of glad tidings, and to give warning, (33:45) and to guard over the illiterate, for you are My servant and My messenger. I have called you a trustworthy man, who is neither rude nor loud in the markets, nor does he return evil with evil, rather he pardons and forgives. Allah Almighty will not take him back until he has made straight the religion which was crooked, that they will say there is no God but Allah, through which eyes are made to see, ears are made to hear, and neglectful hearts are awakened.” [Source: Ṣaḥīḥ al-Bukhārī 2125].

1 ‘Ata’ ibn Yasar reported: I met Abdullah ibn Amr, may Allah be pleased with him, and I said, An karbo daga Aɗa'u dan Yasar ya ce: "Na gamu da Abdullahi da Amru dan Asi, sai na ce masa:
2 “Tell me about the description of the Messenger of Allah, peace and blessings be upon him, in the Torah.” "Fada mini siffar Annabi SAW da take cikin littafin Attaura."
3 Abdullah said, “By Allah, he is described in the Torah with some of what is mentioned in the Quran: Sai ya ce: "Kwarai an siffanta shi a Littafin Attaura da wasu siffofinsa da suke cikin Alqur'ani, inda Allah yake cewa:
4 O Prophet, We have sent you as a witness, a bringer of glad tidings, and to give warning, (33:45) "Ya kai wannan Annabi, lalle mun aiko ka a matsayin mai shaida, kuma mai albishir mai gargadi,
5 and to guard over the illiterate, for you are My servant and My messenger. kuma mai tsaron Ummiyyai, watau Larabawan da ba sa rubutu da karatu. Kai bawana ne, kuma Manzona,
6 I have called you a trustworthy man, who is neither rude nor loud in the markets, nor does he return evil with evil, rather he pardons and forgives. na sa maka suna 'Mai dogaro', ba mai mugun hali ba ko mai kaushin zuciya ko mai yawan hayaniya a kasuwanni ba, ba ya rama mummuna da mummuna, sai dai ya yi afuwa ya yi gafara.
7 Allah Almighty will not take him back until he has made straight the religion which was crooked, that they will say there is no God but Allah, through which eyes are made to see, ears are made to hear, and neglectful hearts are awakened.” Kuma Allah ba zai karbi rayuwarsa ba, har sai bayan ya tsaida addini da shi, har mutane su furta Kalmar Shahada, wadda ita za ta bude idanun da suka makance da kunnuwan da suka kurumce da zukatan da suka toshe."

Sannan Allah swt ya umarce shi da ya yi afuwa a kan kurakuransu da gajiyawarsu, kuma ya nema musu gafarar Allah, ya kuma nemi shawararsu cikin abubuwan da kan taso masu bukatar sai an yi shawara. Bayan shawara kuma, duk abin da ya ga shi ne ya fi maslaha, to ya ci gaba da zartar da shi, ya dogara ga Allah, Allah yana son masu dogara da shi.

Sai kuma Allah swt ya bayyana wa muminai cewa, idan har ya qaddara musu samun wata nasara, to babu wanda ya isa ya karya su ko ya ci galaba a kansu; idan kuwa ya yi watsi da su, ya kyale su, to har abada babu mai iya taimakon su, don haka lalle muminai su dogara da Allah shi kadai.

Sannan Allah ya fadakar da cewa, ba ya daga cikin halayen annabawa su saci dukiyar ganima, domin Allah ya tsare su daga cin amana ko wani mugun hali, don haka bai dace a tuhume su da wani abu irin wannan ba.

Yawancin makaranta sun karanta ayar kamar haka: An yugal - watau suka yi rufu'a a kan (yu), suka kuma yi fataha a kan ayn. Ma'ana "Bai kamata ba a ha'inci wani annabi...".

Sai kuma ya ambaci sakamakon wanda ya saci dukiyar ganima da cewa, zai zo dauke da kayanta a ranar gobe qiyama a gadon bayansa, sannan kowane rai za a yi masa sakayya a kan aikinsa, kuma babu wanda za a zalunta komai.

An karbo daga Mu'azu dan Jabal rA ya ce: "Manzon Allah SAW ya aike ni, bayan na kama hanya na tafi, sai kuma ya aika a kirawo ni. Da na dawo sai ya ce: "Ko ka san don me na aika a kirawo ka? Kada ka kuskura ka dauki wani abu na ganima ba tare da izini na ba, domin yin haka satar dukiyar ganima ce wanda duk ya saci dukiyar ganima, to zai zo da abin da ya sata ranar alqiyama. Don haka ne na kirawo ka, sai ka tafi wurin aikinka." [Bukhari #200].

From Mu’az bin Jabal, he said: “The Messenger of Allah (saw) sent me to Yemen. As I traveled he sent someone after me to call me back so I returned. He said: ‘Do you know why I sent for you? Don’t acquire anything without my permission as it is illicit (Ghulul), and whoever acquired illicitly will bear what he acquired on the Day of Judgement. For this I called you. So proceed with your work’” (source: narrated by Tirmidhi).

An karbo daga Umar dan Khattab rA ya ce: "Ranar yakin Khaibara, wasu sahabbai sun zo suna lissafa wa Manzon Allah SAW cewa, wane ya yi shahada, wane ma ya yi shahada, har suka zo kan wani mutum, sai suka ce, wane ma ya yi shahada." Sai Manzon Allah SAW ya ce: "A'a, ba haka ba ne, ni na gan shi a wutar Jahannama saboda wani mayafi da ya sata daga dukiyar ganima." Sannan Manzon Allah ya ce: "Ya kai dan Khattab, tafi ka yi shela a cikin mutane cewa, babu mai shiga Aljanna sai muminai kadai." Ya ce: "Sai na fita na shelanta wa mutane cewa, babu mai shiga Aljanna sai mumini kadai." [Muslim #114]

It is narrated on the authority of 'Umar b. Khattab that when it was the day of Khaibar a party of Companions of the Apostle (ﷺ) came there and said:

So and so is a martyr, till they happened to pass by a man and said: So and so is a martyr. Upon this the Messenger of Allah remarked: Nay, not so verily I have seen him in the Fire for the garment or cloak that he had stolen from the booty, Then the Messenger of Allah (ﷺ) said: Umar son of Khattab, go and announce to the people that none but the believers shall enter Paradise. He ('Umar b. Khattab) narrated: I went out and proclaimed: Verily none but the believers would enter Paradise. [Source: Sahih Muslim 114]

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Kwadaitarwa a kan kyawawan halaye da tausasawa wajen mu'amala, domin yin haka ne yake kawo hadin kai na al'umma, ya haifar da soyayyar juna; rashinsa kuma shi ne yake haifar da rarrabuwar kai da qiyayyar juna.
  2. Kyawawan halayen shugaba na addini sukan sa mutane su gane addinin, su karbe shi, yayin da miyagun halayensa kan iya sa mutane su nisanci addinin, su tsane shi.
  3. Neman shawara ibada ce da mai yin ta zai sami kusanci ga Allah.
  4. A cikin neman shawara, akwai hikimomi da yawa, daga cikinsu akwai:
    1. Hana shugaba yin mulkin kama-karya.
    2. Koya wa mutane yadda za su gudanar da al'amuransu, su sami gogewa a kai.
    3. Koyar da tawali'u wajen neman shawara. Domin duk shugaban da yake neman shawara a kan lamuransa, wannan yana nuna shi mai tawali'u ne.
    4. Motsa kuzarin al'umma. Yayin da za su ga ana neman shawararsu wannan zai kara musu kuzari a kan ayyukan alheri.
    5. Idan ra'ayoyi daban-daban suka hadu tare da kyakkyawar niyya, sau tari akan dace da daidai. Domin mutum shi kadai zai iya hango maslahar wani al'amari, amma ya kasa gano barnar da ke cikinsa, musamman ma idan idonsa ya rufe wajen son wannan abu; to amma bayan an yi shawara sai a gane duk abin da ke ciki na maslaha da na barna.
    6. Idan an gudanar da kowane abu ta hanyar shawara, to ba za a sami rarrabuwar jama'a ba, domin karbabbun mutane masu gaskiya da gogewa a cikin al'amura, su ne ake neman shawararsu.
  5. Haramun ne wani ya ci amanar wani, ko ya saci dukiyarsa. Kebance Annabi SAW da ambato a qira'ar da aka ce: "Bai kamata ba a ci amanar wani annabi...", yana nuna duk sanda wanda aka yi wa laifin ya zamanto babban mutum ne mai daraja, to laifin ya fi girma da tsanani. Manzon Allah SAW shi ne mafificin halitta, don haka yi masa laifi ya fi tsanani da muni. Sannan kuma shi Annabi SAW ana yi masa wahayi lokaci bayan lokaci, don haka duk wanda ya ha'ince shi, to wahayi na iya sauka nan take ya tona asirin mai ha'incin tun a duniya, baya ga azabar lahira idan ya mutu bai tuba ba. Sannan kuma Musulmi a lokacin suna cikin matsanancin talauci, don haka ha'inci a sannan yake da matukar muni.
  6. Dogaro ga Allah yana nufin mutum ya rike sabubba tare da mayar da al'amarinsa ga Allah.
  7. Idan mutum ya bi dukkan hanyoyi da suka cancanta wajen neman wani abu ko aikata wani abu, sannan ya nemi taimakon Allah ta hanyar dogaro gare shi, to kada ya tsaya kai-komo wajen zartar da abin da ya yi kuduri, ta yadda al'amarinsa zai zamar masa damuwa da rashin kwanciyar hankali.

Tarjama Da Tafsirin ayoyin 162-168 na Surar Ali Imran

  1. 162) Shin yanzu wanda ya bi yardar Allah, zai yi kamar wanda ya dawo da fushin Allah? Kuma, makomarsa ta zamo Jahannama? Kuma tir da wannan makoma. --Quran/3/162
  2. Su darajoji ne a wajen Allah. Allah kuma Mai ganin abin da suke aikatawa ne. --Quran/3/163
  3. Lalle hakika Allah Ya yi ni'ima ga muminai yayin da Ya aiko musu Manzo daga cikinsu, wanda yake karanta musu ayoyinsa, kuma yake tsarkake su, kuma yake koyar da su Littafi da Hikima, ko da yake kuma sun kasance kafin (zuwansa) tabbas suna cikin ɓata mabayyani. --Quran/3/164
  4. Shin yayin da wata musifa ta same ku, wadda kuma hakika kun yi wa (kafirai) irinta ninki biyu, sai ku rika cewa: "Yaya haka ta faru?" Ka ce: "Ai wannan daga kanku ne." Lalle Allah Mai iko ne a kan komai. --Quran/3/165
  5. Kuma abin da ya same ku ranar da kungiyoyin nan biyu suka hadu, to da izinin Allah ne, kuma don Ya bayyana muminai. --Quran/3/166
  6. Kuma don Ya bayyana wadanda suka yi munafunci; kuma aka rika cewa da su: "Ku zo ku yi yaki don Allah ko don kariya." Sai suka ce: "Da mun san za a yi yaki ai da lalle mun biyo ku." Su a wannan lokacin sun fi kusanci ga kafirci fiye da imani, suna fadi da bakunansu abin da ba ya cikin zukatansu. Kuma Allah Ya san abin da suke boyewa. --Quran/3/167
  7. Su ne wadanda suke fada wa 'yan'uwansu, alhalin suna zaune a gida cewa: "In da sun bi (shawarar) mu da ba a kashe su ba." Ka ce: "To ku kare kanku daga mutuwa in har kun kasance masu gaskiya." --Quran/3/168

Tafsiri:

A wadannan ayoyi, Allah swt yana bayyana cewa, wanda ya kasance yardar Allah ce abin nemansa da wanda ya riga ya dulmiya cikin sabon Allah, ya dawo da fushinsa ba za su taba zama daya ba, wadannan kuma wutar Jahannama ita ce makomarsa. Tir kuma da wannan makoma. Allah kuma ya kara jaddada cewa, wadanda suka nemi yardar Allah suna da matakai daban-daban na daukaka; wadanda kuma Allah ya yi fushi da su su ma suna da matakai daban-daban na kaskanci. Kuma Allah yana ganin duk abin da bayinsa suke aikatawa, kuma zai yi musu sakayya a kansa.

Sai kuma Allah swt ya bayyana irin ni'imar da ya yi wa muminai, ta hanyar aiko musu da Manzo daga cikin jinsinsu na mutane, yana karanta musu Alkur'ani, yana tsarkake su daga shirka da sabon Allah da miyagun halayya, kuma yana koya musu ma'anonin Alkur'ani da sunnarsa, duk da cewa kafin zuwan wannan Manzo, suna cikin bata mabayyani.

Sannan Allah swt ya kalubalanci muminai, lokacin da musiba ta same su a ranar yakin Uhudu, ta yi musabbabin kashe mutum saba'in, alhali su kuma sun yi sanadiyyar jawo musu musifa ribi biyu, ta hanyar kashe musu mutum saba'in da kama mutum saba'in, amma kuma sai suka rika tambayar yaya aka yi wannan musibar ta same su? Sai Allah ya umarci Annabinsa SAW ya fada musu cewa, abin da ya same su fa su ne suka jawo shi da kansu, lokacin da suka rika jayayya a kan umarnin Annabi SAW, kuma suka saba wa umarninsa. Don haka Allah mai iko ne a kan yi musu uquba irin ta ranar yakin Uhudu, kuma yana da ikon ba su nasara, don haka kada su yi wa Allah swt zaton da ba na gaskiya ba.

Sannan Allah swt ya gaya wa muminai cewa, abin da ya same su a yakin Uhudu, lokacin haduwarsu da rundunar mushrikai, ya faru ne da nufin Allah da hukuncinsa, don ya tantance tsakanin muminai na gaskiya da munafukan da suke boye cikin sahun Musulmi. Kuma ai asirinsu ya tonu lokacin da aka kirawo su su fito yaki na daukaka addinin Allah, ko kuma don kare kasa da mutanen cikinta, sai kawai suka rika ba da wani hanzari na banza suna cewa, da sun san idan an fita za a fafata tsakanin musulmai da kafirai, da sai su fita, to amma suna ganin hakan ba zai faru ba. Allah ya bayyana cewa, munafukai a wannan lokacin sun fi kusa da kafirci fiye da imani. Suna boyewa a ransu, sabanin abin da suke bayyanawa, kuma Allah yana ganin duk abin da suke boyewa.

Munafukan da suka qi fita yaki dai sun rika ce wa danginsu da suka fita, aka kashe su, cewa: "Da sun karbi shawararmu sun qi fita, ai da ba a kashe su ba." Sai Allah swt ya umarci Annabinsa ya fada musu cewa, su masu ba da shawara ai sai su kare kawunansu daga mutuwa, idan har su masu gaskiya ne, cewar da sun yi musu biyayya da ba a kashe su ba.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Bawan da yake neman yardar Allah, yake aiki da umarninsa, ba zai taba zama daya da wanda ya dukufa a kan sabon Allah ba.
  2. Musiba da tabewa tana samun bawa ne a dalilin sabon Allah da yake yi. Don haka tuba ga Allah shi ne maganin duk wata musifa, kamar yadda Allah ya bayyana a Suratu Hud, aya ta 3 da 52.
  3. Halayyar mutum takan caccanza, wani lokaci ya zamanto ya fi kusa da kafirci, wani lokaci kuma ya dawo ya fi kusa da imani.

Tarjama Da Tafsirin ayoyin 169-171 na Surar Ali Imran

  1. 169) Kuma kada ka yi tsammanin wadanda aka kashe su a wajen yada kalmar Allah matattu ne. A'a, rayayyu ne a wajen Ubangijinsu, ana arzurta su. --Quran/3/169
  2. Suna cike da farin cikin abin da Allah Ya ba su na falalarsa, kuma suna masu yin albishir ga wadanda ba su riga sun riske su ba daga bayansu cewa, babu jin tsoro a gare su, sannan kuma babu bakin ciki tattare da su. --Quran/3/170
  3. Suna ta farin ciki da ni'ima daga Allah da falala, kuma Allah ba Ya tozarta ladan masu imani.

Tafsiri:

A wadannan ayoyi, Allah swt yana umartar Annabinsa da kada ya yi zaton cewa, sahabbansa da aka kashe a ranar Uhudu matattu ne; a'a su rayayyu ne wata rayuwa ta musamman a wurin Ubangijinsu, suna nan kusa da shi, suna jin dadi da ni'imar da ya tanadar musu a gidan Aljanna, suna cike da farin ciki da irin manya-manyan ni'imomi da ya ba su. Hakanan suna yin albishir ga 'yan'uwansu wadanda suka baro a duniya suna fafata yakin daukaka kalmar Allah, suna cewa, su ma da zarar an kashe su a wannan yanayi, to za su sami saduwa da su, ba tare da sun ji tsoron abin da za su iske ba, ko bakin cikin abin da suka bari a duniya. Za su yi farin ciki da albishir da karramawa da falalar da Allah ya yi musu. Kuma Allah ba ya tozarta ladan muminai.

An karbo daga Abdullahi dan Abbas rA ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Lokacin da aka kashe 'yan'uwanku a yakin Uhudu, sai Allah ya sanya rayukansu a cikin cikkunan wasu korayen tsuntsaye, suna zuwa koramun Aljanna suna sha, kuma suna cin kayan marmarinta, sannan su koma ga wasu fitilu na zinariya da ke rataye a inuwar Al-Arshi. Lokacin da suka sami abinci mai dadi da abin sha mai dadi da makwanci na alfarma, sai suka ce: 'Wane ne zai kai labarinmu ga 'yan'uwanmu cewa muna nan a Aljanna ana ciyar da mu, domin kada su guji jihadi su bar yaki?' Sai Allah ya ce: 'Ni ne zan kai musu labarinku.' Sai ya saukar da fadarsa: 'Kuma kada ku yi tsammanin wadanda aka kashe a wajen daukaka kalmar Allah matattu ne, a'a, rayayyu ne a wajen Ubangijinsu ana arzuta su.' [Ahmad #2388 da Abu Dawud #2520]

The Prophet ﷺ said: When your brethren were smitten at the battle of Uhud, Allah put their spirits in the crops of green birds which go down to the rivers of Paradise, eat its fruit and nestle in lamps of gold in the shade of the Throne. Then when they experienced the sweetness of their food, drink and rest, they asked: Who will tell our brethren about us that we are alive in Paradise provided with provision, in order that they might not be disinterested in jihad and recoil in war? Allah Most High said: I shall tell them about you; so Allah sent down; "And do not consider those who have been killed in Allah's path." till the end of the verse. (Using translation from Abū Dāʾūd 2520)  [https://hadithunlocked.com/ahmad:2388]

1 When your brethren were smitten at the battle of Uhud Lokacin da aka kashe 'yan'uwanku a yakin Uhudu
2 Allah put their spirits in the crops of green birds which go down to the rivers of Paradise sai Allah ya sanya rayukansu a cikin cikkunan wasu korayen tsuntsaye, suna zuwa koramun Aljanna
3 eat its fruit and nestle in lamps of gold in the shade of the Throne. suna sha, kuma suna cin kayan marmarinta, sannan su koma ga wasu fitilu na zinariya da ke rataye a inuwar Al-Arshi.
4 Then when they experienced the sweetness of their food, drink and rest, they asked: Lokacin da suka sami abinci mai dadi da abin sha mai dadi da makwanci na alfarma, sai suka ce:
5 Who will tell our brethren about us that we are alive in Paradise provided with provision, Wane ne zai kai labarinmu ga 'yan'uwanmu cewa muna nan a Aljanna ana ciyar da mu,
6 in order that they might not be disinterested in jihad and recoil in war? domin kada su guji jihadi su bar yaki?
7 Allah Most High said: I shall tell them about you; so Allah sent down; "And do not consider those who have been killed in Allah's path." till the end of the verse. Sai Allah ya ce: 'Ni ne zan kai musu labarinku.' Sai ya saukar da fadarsa: 'Kuma kada ku yi tsammanin wadanda aka kashe a wajen daukaka kalmar Allah matattu ne, a'a, rayayyu ne a wajen Ubangijinsu ana arzuta su.'

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Falalar wadanda aka kashe su wajen yada addinin Allah, kuma suna da wata rayuwa a kabarinsu wadda ta zarce rayuwarsu ta duniya a kamala da jin dadi.
  2. Tabbatar da samun ni'imar kabari ga bayin Allah na kwarai.
  3. Muminai suna shiga Aljanna ne da falalar Ubangijinsu, ba don yawan aikinsu ba.
  4. Abu ne mai kyau mumini ya taya dan'uwansa mumini farin ciki idan ya gan shi a cikin aikin biyayya ga Allah.
  5. Tabbatar da adalcin Ubangiji da cewa ba ya tozarta ladan muminai.

Tarjama Da Tafsirin ayoyin 172-176 na Surar Ali Imran

  1. 172) Su ne wadanda suka amsa kiran Allah da Manzo bayan miki (injury) ya same su a jikinsu. Lalle wadanda suka kyautata a cikinsu, kuma suka yi taqwa, suna da lada mai girma. --Quran/3/172
  2. Su ne wadanda mutane suka ce da su: "Lalle mutanen (Makka) fa sun tara muku runduna, to sai ku tsorace su." Amma sai hakan ya kara musu imani, sai suka rika cewa: "Allah Ya wadace mu, kuma madalla da abin dogara (idan har shi ne Allah)." --Quran/3/173
  3. (A sakamakon haka) sai suka dawo da ni'ima ta musamman daga Allah da falala, wani abin qi bai shafe su ba, kuma (suka dace da cewa) sun bi yardar Allah. Allah kuma Ma'abocin falala ne wadda take mai girma. --Quran/3/174
  4. Wannan (labarin), Shaidan ne kawai yake tsoratar da ku masoyansa, don haka kar ku ji tsoron su, amma ku ji tsoro Na in dai har ku muminai ne. --Quran/3/175
  5. Kuma kada wadanda suke gaggawar shiga cikin (ayyukan) kafirci, su fusata ka. Hakika su ba za su cutar da Allah komai ba. Allah Ya yi nufin ba zai sanya musu wani rabo a lahira ba; kuma suna da azaba mai girma. --Quran/3/176

Tafsiri:

Yayin da Annabi SAW ya dawo Madina daga yakin Uhudu, sai ya sami labarin cewa, Abu Sufyan da mutanensa suna kokarin dawowa Madina, sai Annabi SAW ya nemi sahabbansa kowa ya fito har da masu raunuka, don su amsa kiran Allah da Manzonsa, suka nufi wani wuri da ake kira Hamra'ul Asad. Da suka isa wurin, sai wani ya zo yana ce musu: "Mutane fa sun yi muku taron dangi da nufin sai sun ga bayanku gaba daya." Ya kuwa fada musu haka ne don ya tsorata su; to amma a maimakon su tsorata, sai wannan ya kara musu imani da dogaro ga Allah, suka ce: "Mu dai Allah ya ishe mu, kuma madalla da abin dogaro Allah." Sai ga shi sun dawo daga wannan wurin da wata ni'ima daga Allah da falala, ba abin da ya same su na cutarwa daga bangaren makiyansu, kuma sun bi yardar Allah lokacin da suka karba kiran Allah da Manzonsa, suka sake fitowa. Allah ma'abocin falala ne wadda take mai girma.

Sannan Allah swt ya bayyana cewa, wannan da yake tsoratar da su ba wani ne ba illa Shaidan, kuma yana so ne ya shuka tsoron jama'arsa mushirikai a zukatan muminai. Sannan Allah ya ce, kar wanda ya ji tsoron mushirikai; Allah kadai za su ji tsoro idan har su muminai ne.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Idan bawa bai amsa kiran Manzon Allah swt ba, to bai amsa na Allah ba ke nan.
  2. Falalar sahabban Annabi SAW, yayin da raunin da ke jikinsu bai hana musu amsa kiran Allah da na Manzonsa ba.
  3. Wajibi ne a kan muminai duk sa'adda suka samu kansu cikin wata matsala, to su nemi mafaka a wurin Allah da taimakonsa, babu mai kare muminai daga kowane sharri sai Allah shi kadai.
  4. Imani yana karuwa ta hanyar yi wa Allah biyayya, yana kuma raguwa ta hanyar saba masa.
  5. Masu dogaro ga Allah su suke da kyakkyawan karshe.

Tarjama Da Tafsirin ayoyin 177-180 na Surar Ali Imran

  1. 177) Lalle wadanda suka musanya imani da kafirci ba su cutar da Allah da komai ba, kuma suna da azaba mai radadi. --Quran/3/177
  2. Kuma wadanda suka kafirta kar su yi tsammanin cewa, jinkiri da Muke yi musu wani alheri ne ga kawunansu. Ai Muna saurara musu ne kawai don su kara laifi (a kan laifinsu). Kuma suna da azaba mai wulakantarwa. --Quran/3/178
  3. Da dai Allah ba zai kyale muminai a yadda kuke din nan ba har sai Ya rarrabe tsakanin lalatacce da kyakkyawa. Kuma Allah ba zai sanar da ku gaibu ba, sai dai Allah Yana zabar wanda Ya so cikin manzanninsa ne; don haka ku kara yin imani da Allah da manzanninsa. Idan kun yi imani, kun yi taqwa kuwa, to kuna da lada mai girma. --Quran/3/179
  4. Kuma wadanda suke yin rowar abin da Allah Ya ba su na falalarsa kar su yi tsammanin hakan alheri ne a gare su; a'a, hakan sharri ne a gare su; da sannu za a yi musu saqandami da abin da suka yi rowa da shi a ranar Alqiyama. Kuma Allah Shi ne Mai gadon sammai da kasa. Kuma Allah Mai cikakken sanin abin da kuke aikatawa ne. --Quran/3/180

Tafsiri:

A wadannan ayoyi, Allah swt yana ba da labarin wadanda suka musanya imani da kafirci cewa, ba za su cuci Allah da komai ba; kawunansu kadai za su cuta, domin za su cancanci uqubar Allah ne mai tsanani.

Sannan Allah ya bayyana wa Annabinsa cewa, kada ya yi zato, su ma kafirai kar su yi zaton rashin gaggauto musu da azabar Allah da kyale su suna more rayuwarsu yadda suke so, su dauka wannan falala ko alheri Ubangiji yake yi musu; Allah ya yi musu haka ne don su kara daukar wa kawunansu wasu tarin laifuka, sannan za su fuskanci azaba mai wulakantarwa.

Allah kuma ya bayyana cewa, ba ya daga cikin hikimarsa ya kyale muminai da munafukai su ci gaba da zama a gauraye, ba tare da ya ware kowanne daga cikinsu ba. Dole ne a sami jarrabawa iri-iri wadda ta hanyarta ne za a gane mumini na gaskiya, kuma a gane munafuki.

Hakanan ba ya daga cikin hikimar Allah, ya bayyana wa wani abin da yake cikin zukatan bayinsa, har ya iya gane muminai da munafukai; sai dai Allah ya kawo wata jarrabawa wadda ta hanyarta ne zai bambance tsakanin mumini da munafuki. Amma duk da haka Allah yakan zabi wasu manzanni nasa ya sanar da su wani gaibu da izininsa da yardarsa.

Sannan Allah ya umarci muminai da su kara tabbata a kan imani da Allah da manzanninsa, ya kuma yi musu alkawarin idan har sun yi hakan, to suna da wani lada mai girma.

Sai kuma Allah ya tunatar da Annabinsa SAW, da cewa, wadanda suke rowa da dukiyar da Allah ya ba su daga falalarsa, kada su yi tsammani wannan rowar alheri ne gare su; a'a, sharri ne gare su, domin Allah ya yi musu tanadin azaba mai tsanani, wadda a lahira zai mayar musu da wannan dukiyar wani saqandami, watau abin wuya na wutar Jahannama da zai rataya musu a wuyoyinsu, a yi ta yi musu azaba da shi ba qaqqautawa. Allah kuma ya bayyana cewa, sammai da kasa duk nasa ne, don haka duk abin da halittunsa suka mallaka zai koma gare shi ne bayan sun halaka, shi zai gaje shi, kuma Allah yana da cikakken sanin bayinsa, kuma zai saka wa kowa.

An karbo daga Abu Huraira rA ya ce: Annabi SAW ya ce: "Duk wanda Allah ya ba shi dukiya bai fitar da zakka ba, to ranar alqiyama za a mayar da wannan dukiya bai fitar da zakka ba, to ranar alqiyama za a mayar da wannan dukiyar wani tsohon kumurci mai kodadden kai da digon baqi a idanunsa, a rataya masa shi a ranar alqiyama, ya rika fincikar hab'arsa yana cewa: "Ni ne dukiyarka, ni ne ajiyayyar taskarka." Sannan Annabi SAW ya karanta fad'ar Allah: "Kuma wadanda suke yin rowa da abin da Allah ya ba su na falalarsa, kar su yi tsammanin hakan alheri ne a gare su..." [Bukhari #4565]

Narrated Abu Huraira: Allah's Messenger (ﷺ) said, "Anyone whom Allah has given wealth but he does not pay its Zakat, then, on the Day of Resurrection, his wealth will be presented to him in the shape of a bald-headed poisonous male snake with two poisonous glands in its mouth and it will encircle itself round his neck and bite him over his cheeks and say, "I am your wealth; I am your treasure." Then the Prophet (ﷺ) recited this Divine Verse:-- "And let not those who covetously withhold of that which Allah has bestowed upon them of His Bounty." (3.180) [https://sunnah.com/bukhari:4565]

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Samun ni'imar duniya ba dalili ne da yake nuna Allah ya yarda da wanda ya ba shi ni'imar ba, wannan ni'imar tana iya zama sanadiyyar azabtar da shi a lahira.
  2. Ya wajaba mumini a kullum ya rika duba rayuwarsa a kan me yake tafiyar da ita, yana tafiyar da ita ne a kan ɗa'a ga Allah ko a kan saɓon Allah? Domin yawan rai yana amfanar mutum ne idan ya tafiyar da shi a cikin da'ar Allah.
  3. Ba a tantance mumini na gaskiya da munafuki a lokacin da ake cikin yalwa da ni'ima; ana tantancewa da su ne a lokacin da aka shiga wani tsanani ko bala'i.
  4. Rowa tana daga cikin manyan laifukan da Allah zai yi wa bawa ukuba a kanta.

Tarjama Da Tafsirin ayoyin 181-184

  1. Tabbas hakika Allah ya ji maganar wadannan da suka ce: "Lalle Allah mataulaci ne, mu ne mawadata." Da sannu za Mu rubuta abin da suka fada, da kuma kisan da suka dinga yi wa annabawa ba tare da wani hakki ba, kuma za Mu ce: "Ku dandani azaba mai ƙuna." --Quran/3/181
  2. "Wannan kuwa, saboda abin da hannayenku suka gabatar ne, kuma lalle Allah ba Ya zaluntar bayinsa." --Quran/3/182
  3. Su ne wadanda suka ce: "Lalle Allah Ya yi alqawari da mu kar mu yarda da kowane manzo har sai ya zo mana da wata sadaka wadda wuta za ta cinye ta." Ka ce: "Hakika manzanni sun zo muku tun kafin ni, da hujjohi da kuma abin da kuka ce din, to don me kuka rika kashe su in kun kasance masu gaskiya?" --Quran/3/183
  4. To idan sun karyata ka, to hakika an karyata manzanni kafinka, wadanda suka zo da hujjoji da littattafai da Littafi mai haskakawa. --Quran/3/184

Tafsiri:

A nan Allah yana ba da labarin cewa, ya ji irin rashin kunyar da Yahudawa suka yi wa Allah suna cewa, wai Allah shi ne matalauci, su kuma mawadata ne. Allah ya tabbatar musu cewa, zai rubuta wadannan miyagun maganganu nasu, har ma da ta'asar da suka yi ta kashe annabawa ba da wani hakki ba, sannan ranar alqiyama zai ce musu: Ku dandani azabar wuta mai quna, saboda laifukan da kuka aikata a duniya, kuma Allah ba mai zaluntar bayinsa ne ba.

Dalilin saukar wannan ayar shi ne, kamar yadda Ibn Abbas ra ya ruwaito cewa: Wata rana Abubakar rA ya ce wa wani babban malamin Yahudawa, mai suna Finhasu, cewa: "Ka ji tsoron Allah ka musulunta. Wallahi ka san cewa, Annabi SAW Manzo ne daga Allah, ya zo muku da gaskiya daga gare shi, kuma kun karanta siffofinsa a cikin Littafin Attaura da Linjila." Sai Finhasu ya ce: "Ya Ababakar, mu fa ba mu da wata bukata a wurin Allah, shi ne ma yake da bukata a wurinmu, kuma mu ba ma marairaice masa, kamar yadda shi yake marairaice mana. Mu mun wadatu, ba mu da wata bukata a wurinsa, kuma shi ma da ya wadatu, ba shi da wata bukata a wurinmu, to da bai karbi rance a wurinmu ba, kamar yadda mutumin naku yake riyawa. Shi ya hana ku ci riba, shi kuma yana ba mu, da ba shi da bukatarmu, da bai ba mu riba ba." Sai Sayyidina Abubakar ya fusata, har ya mari Finhasu, sai Finhasu ya je ya fada wa Manzon Allah cewa, Abubakar ya mare shi. Sai Annabi ya tambayi Abubakar, me ya sa ya yi haka? Sai Abubakar ya fada masa duk abin da ya faru. Sai Finhasu ya musanta, ya ce shi bai fadi haka ba. Sai Allah ya saukar da wannan ayar: "Tabbas hakika, Allah ya ji maganar wadanda suka ce lalle Allah matalauci ne, mu ne mawadata..." [At-Tabari 7:441]

The time when Abu Bakr r.a slapped a jew and Allah ﷻ revealed a verse in the Qur'an regarding it

https://www.reddit.com/r/islam/comments/1bei4sn/the_time_when_abu_bakr_ra_slapped_a_jew_and_allah/

181- Indeed, Allâh has heard the statement of those (Jews) who say: "Truly, Allâh is poor and we are rich!" We shall record what they have said and their killing of the Prophets with no just cause, and We shall say: "Taste you the torment of the burning (Fire)." It is narrated on the authority of Ibn 'Abbâs [Allâh be pleased with them] that he said: Abu Bakr [Allâh Be Pleased with him] entered Bayt Al-Midrâs (the place where the Jews study the Torah) and found many of them gathering around someone called Finhâs, who was one of their scholars and rabbis with someone called Ashya'. Abu Bakr [Allâh Be Pleased with him] said to Finhâs: "Woe to you, fear Allâh. By Allâh, you know that Muhammad [peace be upon him] is the Messenger of Allâh who came with the truth from Allâh and you can find that in your Torah and Gospel". Finhâs said to Abu Bakr [Allâh Be Pleased with him]: "By Allâh, O Abu Bakr, we are not in need of Allâh; it is He Who Is in need of us. We do not invoke Him as He Invokes us. We are rich and He Is not, for had He Been rich, He Would not Have Borrowed our property as your Prophet claims. He Forbids you from usury and Permits us to deal in it. If He Had Been rich, He Would not Have Permitted us to deal in usury". Abu Bakr [Allâh Be Pleased with him] became angry and slapped the face of Finhâs and said: "By The One in Whose Hand my soul is, had it not been for the covenant between us and you, I would have smashed your head, O enemy of Allâh”. Finhâs, accordingly, went to the Messenger of Allâh [peace be upon him] and said: "O Muhammad, look at what your Companion (Abu Bakr) has done to me". The Messenger of Allâh [peace be upon him] said: "What drove you to do so, O Abu Bakr?" Abu Bakr [Allâh Be Pleased with him] replied: “This enemy of Allâh said a grave saying: he claimed that Allâh Almighty Is in need for them and that they are rich. When he said so, I became angry for the Sake of Allâh Almighty and slapped his face". Therefore, Finhâs denied this and said: "I did not say so". On that occasion, Allâh Almighty Revealed this Qur'anic Verse. [Ibn Ishâq and Ibn Abu Hâtim] .

Sannan kuma Allah ya fallasa wata karyar ta Yahudawa, wadda suka yi da'awar cewa, Allah ya yi musu wasiyya da kada su yi imani da wani Manzo har sai ya zo musu da wata sadaka wadda wuta za ta zo ta cinye ta a gabansu suna gani, sannan ne za su yarda shi Manzon Allah ne, su yi imani da shi. Sai Allah ya umarci Annabinsa ya mayar musu martani da cewa, ai akwai manzanni da yawa a gabaninsu, wadanda suka zaaike wa jama'arsu suna dauke da mu'ujizoji da dama, wadanda suka hada har da irin wannan mu'ujizar da suka nema, to amma sai ba su yi imani ba. Hasali ma kashe wasu annabawan suka yi. To don me suka kashe su, in har da gaske suke cewa, Allah ya umarce su da kada su yi imani sai da wanda ya zo musu da irin wannan mu'ujizar?

Sai Allah ya lallashi Annabinsa da kada ya damu don karyatawar da wadannan Yahudawan suke yi masa, domin ba shi ne farau ba; manzanni da dama da suka gabace shi, sun zo da mu'ujizoji da littattafai da aka saukar musu, wadanda ke dauke da wa'azuzzuka da nasihu masu ratsa zukata.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Duk abin da bayi suke yi na alheri ko na sharri ana rubutawa.
  2. Duk wanda ya yarda da laifin mai laifi, to shi ma ya zama mai laifi. Shi ya sa Allah yake jingina wa Yahudawan zamanin Annabi SAW laifin iyayensu, domin sun yarda da wannan laifin.
  3. Karyata gaskiya da yi wa Allah karya wata siffa ce ta Yahudawa.

Tarjama Da Tafsirin ayoyin 185-186

  1. Kowane rai zai dandani mutuwa. Kuma a ranar alqiyama ne za a cika muku ladan ayyukanku; to duk wanda aka nisanta shi daga wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to hakika ya rabauta. Kuma rayuwar duniya ba komai ba ce face cin daɗi mai ruɗarwa. --Quran/3/185
  2. Lalle za a jarrabe ku a cikin dukiyoyinku da rayukanku, kuma lalle za ku rika jin cutarwa mai yawa daga wadanda aka bai wa Littafi kafinku, haka kuma daga wadanda suke mushrikai. Amma idan har kuka yi hakuri, kuma kuka tsare dokar Allah, to lalle wannan yana daga cikin manyan al'amura. --Quran/3/186

Tafsiri:

A wadannan ayoyi, yana bayyana cewa, kowane rai dole ne sai ya mutu, kuma Allah ne ke yi wa kowa cikakken sakamako na aikinsa ranar gobe qiyama. To duk wanda aka tserar da shi daga shiga wuta, sannan aka shigar da shi Aljanna, to hakika wannan mutum ya rabauta, kuma rayuwar duniya wani ɗan jin daɗi ne ƙanƙani, mai gushewa da gaggawa bayan ya ruɗi ma'abocinsa.

An karbo daga Abu Huraira rA ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Lalle gurbin bulala a Aljanna ya fi duniya da abin da yake cikinta. Ku karanta wannan ayar in kun ga dama: "To duk wanda aka nisanta shi daga wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to hakika ya rabauta, kuma rayuwar duniya ba komai ba ce, face ɗan jin daɗi mai ruɗarwa." [Tirmizi #3013 da Nasa'i, As-Sunan Alkubra #11085]

Narrated Abu Hurairah: that the Messenger of Allah (ﷺ) said: "Indeed the space in Paradise taken up by a whip, is better than the world and what is in it. Recite if you wish: 'And whoever is moved away from the Fire and admitted to Paradise, he indeed is successful. The life of this world is only the enjoyment of deception (3:185).'" [https://sunnah.com/tirmidhi:3013]

Sannan Allah swt ya faɗa wa muminai cewa za a jarrabe su da aukawar masifu a dukiyoyinsu, ta hanyar lalacewarsu ko hasarar kasuwanci, kuma za a jarabce su a rayukansu, ta hanyar mutuwa ko kisa ko samun raunuka ko rashin lafiya. Sannan kuma za su dinga jin maganganu na cutarwa da gallazawa daga makiyansu wadanda aka ba wa Littafi gabaninsu, wato Yahudawa da Nasara, da kuma mushirkai, saboda za su rika zagin su, suna sukar addininsu, suna jifar su da tuhumce-tuhumce iri-iri da yin izgili ga shari'arsu. To amma idan sun yi hakuri a kan hakan, kuma suka kiyaye dokokin Allah, to yin hakan yana daga cikin manyan al'amura da suke bukatar juriya da himma.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Kwadaitarwa a kan yawaita aikata ayyukan alheri kafin zuwan ajali, saboda babu wanda ya san lokacin mutuwarsa.
  2. Nuna kaskancin duniya da rashin tabbas dinta, domin duk wani abin jin dadi da yake cikinta mai gushewa ne. Don haka bai kamata ta rudi mai hankali ba.
  3. Ya kamata mumini ya sani cewa, duk irin yanayin da yake ciki, mai dadi ko marar dadi, wata jarrabawa ce daga Allah, domin ya ga godiyarsa ko hakurinsa, ko kuma rashinsu.
  4. Allah ya ba muminai labarin abin da za su rika gani daga magabtansu, Ma'abota Littafi da mushirikai, na cutarwa mai yawa, domin wasu hikimomi kamar haka:
    1. Don a tantance Musulmi na kwarai da lalatacce.
    2. Don Allah ya daukaka darajar muminai da wannan ya kuma kankare musu laifuffukansu.
    3. Don imaninsu ya ƙaru yayin da suka ga aukuwar abin da Allah ya ba su labarinsa.
    4. Don su shirya wa faruwar hakan.
    5. Don idan ya faru su yi hakuri, su jure.

187-188

  1. Kuma ka tuna lokacin da Allah Ya dauki alkawari daga wadanda aka bai wa Littafi cewa: "Lalle ku bayyana shi ga mutane, kuma kada ku boye shi." Sai suka jefar da shi can bayansu, kuma suka musanya shi da wani dan farashi kankani. To tir da abin da suke yin musanye da shi. --Quran/3/187
  2. Kada ka yi tsammanin wadanda suke yin farin ciki da irin abin da suka aikata, kuma suna son a rika yabon su da abin da ba su aikata ba, to kada ka yi tsammanin za su tsira daga azaba, kuma suna da azaba mai raɗaɗi. --Quran/3/188

Tafsiri:

A wadannan ayoyi, Allah swt yana tuna wa Annabinsa SAW wani mummunan aiki na Yahudawa da Nasara, lokacin da Allah ya yi ƙaƙƙarfan alkawari da su na cewa, za su fito su bayyana wa mutane abin da yake cikin littattafan da aka saukar wa annabawansu, kuma ba za su boye komai daga ciki ba. Daga ciki kuwa har da siffofin Annabi SAW da suka zo a Attaura da Linjila; to amma sai suka saɓa wannan alƙawari, suka ɓoye waɗannan siffofin Annabi SAW, ba don komai ba, sai don ɗan abin da za su samu na duniya. Sai Allah ya yi tir da irin wannan aiki nasu.

An karbo daga Abu Huraira rA ya ce: Annabi SAW ya ce: "Duk wanda aka yi masa tambaya ta ilimi, sannan ya boye, to za a sa masa linzamin wuta ranar gobe qiyama." [Abu Dawud #3658 da Tirmizi #2649 da ibnu Majah #266].

Narrated Abu Hurairah: that the Messenger of Allah (ﷺ) said: "Whoever is asked about some knowledge that he knows, then he conceals it, he will be bridled with bridle of fire." [https://sunnah.com/tirmidhi:2649]

Sai kuma Allah swt ya fada wa Annabinsa cewa, kada ya yi zaton mutanen da suke farin ciki da miyagun ayyukan da suka yin a boye ilimin da Allah ya ba su, kuma suke son a rika yaba musu akan aikin da ba su yi ba, kada ya yi zaton wadannan mutane za su tsira daga azabar Allah ranar alqiyama; tabbas suna da wata azaba mai radadi.

1 Narrated Abu Sa`id Al-Khudri: An karbo daga Abu Sa'id Alkhudri rA ya ce:
2 During the lifetime of Allah's Messenger (ﷺ), some men among the hypocrites used to remain behind him (i.e. did not accompany him) when he went out for a Ghazwa and they would be pleased to stay at home behind Allah's Messenger (ﷺ) Wasu munafukai duk sanda Annabi SAW ya fita yaqi, sai su noqe su qi fita tare da shi, kuma su riqa farin ciki da hakan.
3 When Allah's Messenger (ﷺ) returned (from the battle) they would put forward (false) excuses and take oaths, wishing to be praised for what they had not done. Idan Annabi SAW ya dawo daga yaqi, sai su je suna rantsuwa, suna fadar hanzari na qarya, sannan uma su riqa son ya yabe su da aikin da ba su yi ba.
4 So there was revealed:-- "Think not that those who rejoice in what they have done, and love to be praised for what they have not done.." (3.188) Sai wannan ayar ta sauka: "Kada ku yi tsammanin wadanda suke farin ciki da abin da suka yi, kuma suna son a riqa yabon su da abin da ba su aikata ba..."

Bukhari #4567 da Muslim #2777 https://sunnah.com/bukhari:4567

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Wajabcin bayyana ilimi a kan masu ilimi ta duk hanyar da ta dace.
  2. Sukan masu son a yaba musu a kan aikin da ba nasu ba.
  3. Babu laifi a yaba wa mutum a kan aikin da ya yi na alheri, don qarfafa masa gwiwa, idan kuma babu jin tsoron girman kai ya shige shi.
  4. Babu laifi mutum ya yi farin ciki a kan yabonsa da aka yi bisa wani aikin alheri, matuqar ba ya yi ne domin riya ba, kuma bai yarda jiji da kai ya kama shi ba.

189-195

  1. Kuma ga Allah ne mulkin sammai da qasa yake. Kuma Allah Mai iko ne a kan komai. --Quran/3/189
    And to Allah belongs the dominion of the heavens and the earth, and Allah is over all things competent. (189)
  2. Lalle a cikin halittar sammai da qasa da sassab'awar dare da rana, tabbas akwai ayoyi ga ma'abota lafiyayyun hankula. --Quran/3/190
    Indeed, in the creation of the heavens and the earth and the alternation of the night and the day are signs for those of understanding. (190)
  3. Su ne wadanda suke ambaton Allah a tsaye da kuma zaune da kuma kishingid'e, suna kuma tunani a kan halittar sammai da qasa, (suna cewa): "Ya Ubangijinmu, ba Ka halicci wannan a banza ba, tsarki ya tabbata gare Ka, Ka tserar da mu daga azabar wuta. --Quran/3/191
    Who remember Allah while standing or sitting or [lying] on their sides and give thought to the creation of the heavens and the earth, [saying], "Our Lord, You did not create this aimlessly; exalted are You [above such a thing]; then protect us from the punishment of the Fire. (191)
  4. "Ya Ubangijinmu, lalle duk wanda Ka shigar da shi wuta, to haqiqa Ka kunyata shi; kuma azzalumai ba su da mai taimakon su. --Quran/3/192 Our Lord, indeed whoever You admit to the Fire - You have disgraced him, and for the wrongdoers there are no helpers. (192)
  5. "Ya Ubangijinmu, lalle mu mun ji wani mai kira yana yin kira zuwa imani cewa: "Ku yi imani da Ubangijinku;" sai muka yi imani. Ya Ubangijinmu, Ka gafarta mana zunubanmu, kuma Ka kankare mana kurakuranmu, kuma Ka karb'i rayukanmu tare da mutane masu ɗa'a. --Quran/3/193
    Our Lord, indeed we have heard a caller calling to faith, [saying], 'Believe in your Lord,' and we have believed. Our Lord, so forgive us our sins and remove from us our misdeeds and cause us to die with the righteous. (193)
  6. "Ya Ubangijinmu, kuma Ka ba mu abin da Ka yi mana alqawari da shi ta harshen manzanninka, kuma kada Ka kunyatar da mu ranar alqiyama. Lalle Kai ba Ka sab'a alqawari." --Quran/3/194 Our Lord, and grant us what You promised us through Your messengers and do not disgrace us on the Day of Resurrection. Indeed, You do not fail in [Your] promise." (194)
  7. Sai Ubangijinsu Ya amsa musu (cewa): "Lalle Ni ba zan tozarta aikin wani mai aiki daga cikinku ba, namiji ne ko mace; sashinku yana tare da sashe. To wadanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidajensu kuma aka cutar da su wajen bin tafarkina kuma suka yi yaqi kuma aka kashe su, lalle zan kankare musu krakuransu, kuma lalle zan shigar da su gidajen Aljanna wadanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu. Wannan lada ne daga wajen Allah, kuma a wurin Allah ne mafi kyawun lada yake." --Quran/3/195

Tafsiri:

A cikin wadannan ayoyi Allah swt yana bayyana cewa, shi kadai ne mai mulkin sammai da qasa da abin da yake cikinsu, kuma shi ne mai cikakken iko a kan komai. Sannan ya sanar da cewa, a cikin halittar sammai da qasa da abubuwan da suka qunsa da cancanzawar dare da rana, wannan ya zo, wannan ya tafi, lalle akwai manya-manyan ayoyi da dalilai ga masu lafiyayyen hankali, da suke tabbatar da samuwar Mahalicci da siffofinsa. Wadannan kuwa su ne masu ambaton Allah koyaushe, a cikin kowane yanayi, a tsaye suke ko a zaune ko a kwance. Suna tunani game da halittar sammai da qasa, suna cewa: "Ya Ubangijinmu, mun yi imani ba ka yi wannan halittar a banza ba; ka tsarkaka daga yin wannan, don haka ka tsare mu daga da shi, kuma azzalumai ba su da masu taimaka musu." Suka ci gaba da cewa: "Ya Ubangijinmu, mun ji Annabinka yana kira zuwa ga yin imani da kai, kuma mun amsa kiransa, mun yi imani, don haka ka gafarta mana laifukanmu, kuma ka kankare mana munanan ayyukanmu, kuma ka karb'i rayukanmu tare da mutanen kirki. Ya kyakkyawan sakamako ka zartar da shi, kada kuma ka kunyata mu a ranar alqiyama a gaban halittunka; lalle mun tabbatar ba ka sab'a alqawari."

Sai ko Allah swt ya bayyana cewa, ya karb'i wannan roqo nasu, kuma ya yi alqawarin ba zai tab'a tozarta aikin mai aiki ba, namiji ne shi ko mace ce. Don haka wadanda suka baro garuruwansu na kafirci ko kuma kafirai suka koro su, aka cutar da su saboda sun riqe gaskiya, sun yi imani da Allah da Manzonsa, suka kuma yi yaqi don Allah, kuma aka kashe su, to wadannan Allah zai kankare musu laifukansu, kuma zai saka su gidajen Aljanna, wadanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu; wannan babban sakamako ne a gare su, saboda qoqarin da suka yi na aikin alheri a duniya. Allah shi ne mai kyakkyawan sakamako ga duk wanda ya yi aikin qwarai; zai saka masa da abin da ido bai tab'a gani ba, kunne bai tab'a ji ba, zuciyar wani d'an Adam ba ta tab'a tunaninsa ba.

An karbo daga Abdullahi d'an Abbas rA ya ce: Wani dare na kwana a d'akin Maimuna uwar muminai. kuma a ranar Annabi SAW yana d'akinta, domin in ga yadda yake sallarsa ta dare. Annabi SAW ya yi hira da iyalinsa na wani d'an lokaci, sannan ya kwanta ya yi barci. A sulusin qarshe na dare, sai ya tashi zaune, ya d'aga kai sama, sai ya karanta wannan aya (ta Quran/3/190), sannan ya tashi ya yi alwala, ya yi asiwaki, sannan ya yi salla raka'a goma sha d'aya, sannan Bilal ya kira sallar Asuba. Sai Annabi SAW ya sallaci raka'a biyu, sannan ya fita ya jagoranci sallar Asuba. [Bukhari #7452].

Narrated Ibn `Abbas: Once I stayed overnight at the house of (my aunt ) Maimuna while the Prophet (ﷺ) was with her, to see how was the night prayer of Allah's Apostle Allah's Messenger (ﷺ) talked to his wife for a while and then slept. When it was the last third of the night (or part of it), the Prophet (ﷺ) got up and looked towards the sky and recited the Verse:-- 'Verily! In the creation of the Heavens and the Earth....there are indeed signs for the men of understanding.' (3.190) Then He got up and performed the ablution, brushed his teeth and offered eleven rak`at. Then Bilal pronounced the Adhan whereupon the Prophet (ﷺ) offered a two-rak`at (Sunna) prayer and went out to lead the people in Fajr (morning compulsory congregational prayer. https://sunnah.com/bukhari:7452

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Kira zuwa ga yin tunani game da halittar sammai da qasa, saboda abubuwan da suka qunsa na manyan dalilai masu tabbatar da Ɗayantakar Allah da cancantar a bauta masa shi kad'ai.
  2. Tunani da duba cikin halittar sammai da qasa yana qara wa bawa imani da yaqini.
  3. Duk sa'adda mutum ya zama mai zurfin hankali, to saninsa ga Allah da ayoyinsa za su qara hab'aka.
  4. Halaccin yin tawassuli da siffofin Allah da ayyuka na qwarai, kamar imani da Allah da Manzonsa SAW.
  5. Yana daga cikin ladubban addu'a, mutum ya yawaita yabo da kirari ga Allah Ta'ala.
  6. Babu wani bambanci tsakanin namiji da mace wajen sakamakin ayyukan ibada da kusanci zuwa ga Allah. Duk wanda ya yi aiki na gari, Allah zai yi masa sakayya da kyakkyawan sakamako, ba tare da la'akari da bambancin jinsi ba.

196-200

  1. Kada zirga-zirgar kafirai a cikin qasa ta rud'e ka. --Quran/3/196
    Be not deceived by the [uninhibited] movement of the disbelievers throughout the land. (196)
  2. Wani d'an jin dad'i ne ƙanƙani, sannan makomarsu Jahannama. Kuma tir da wannan shifid'ar. --Quran/3/197
    [It is but] a small enjoyment; then their [final] refuge is Hell, and wretched is the resting place. (197)
  3. Amma wadanda suka bi dokokin Ubangijinsu suna da gidajen Aljanna wadanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, za su dawwama a cikinsu, wannan gara ce ta musamman daga wajen Allah. Kuma abin da yake wajen Allah shi ne mfai alheri ga masu biyayya. --Quran/3/198
  4. Kuma lalle a cikin Ma'abota Littafi, tabbas akwai wadanda suke yin imani da Allah da kuma abin da aka saukar musu, suna masu jin tsoron Allah, ba sa musanya ayoyin Allah da wani d'an farashi qanqani. Wadannan suna da lada a wajen Ubangijinsu. Lalle Allah Mai gaggawar hisabi ne. --Quran/3/199
  5. Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi hakuri, kuma ku jure matuqa ga yin hakuri, kuma ku tsare iyakokin qasa, kuma ku tsoraci Allah ko kwa sami rabauta. --Quran/3/200

Tafsiri:

A wadannan ayoyi Allah swt yana yi wa Annabinsa SAW kashedi da rudawa da kai-komon kafirai a duniya da tinqahon da suke yi da bunqasar harkar kasuwanci da qarfin tattalin arziki da qarfin sojoji. Duk wadannan wani dan taqaitaccen jin dadi ne; nan da nan zai qare, sannan daga qarshe wutar jahannama ce makomarsu tir kuwa da irin wannan makoma.

To amma masu bin dokokin Ubangijinsu ta hanyar aikata abin da ya wajabta musu da barin abin da ya haramta musu; to an tanadar musu gidajen Aljanna wadanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, kuma su zauna cikinsu har abada. Wannan wata liyafa ce Allah ya shirya musu. Don haka abin da yake wurin Allah na kyakkyawan sakamako ga wadanda suka bi shi, ya fi alheri fiye da wani d'an gajeren jin dad'i na duniya.

Sannan Allah swt ya bayyana cewa, a cikin Ma'abota Littafi akwai wadanda sun yi imani da Allah, suna kad'aita shi da bauta, kuma sun yi imani da Manzonsa da Alqur'anin da aka saukar masa da kuma littattafan da aka saukar musu, suna masu qasqantar da kansu ga Allah, ba sa canza abin da yake cikin littattafansu, ba sa kuma b'oye gaskiyar da take ciki, domin samun d'an wani taqaitaccen jin dad'i na duniya; to wadannan suna da babban sakamako a wurin Allah swt. Lalle kuma Allah mai gaggawar sakamako ne.

An karb'o daga Anas d'an Malik rA ya ce: Lokacin da labarin rasuwar Najjashiy ta zo mana, Annabi SAW ya ce mana: "Ku yi masa salla." Sai Allah ya saukar da fad'arsa: "Kuma lalle cikin ma'abota Littafi, tabbas akwai wadanda suka yi imani da Allah da kuma abin da aka saukar muku da kuma abin da aka saukar musu, suna masu qasqantar da kansu ga Allah."

It was narrated from Anas bin Malik (may Allah be pleased with him) that: When the news of the death of Najjashi reached us, the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him) said to us: "Pray for him." Then Allah revealed: "And among the People of the Book are those who believe in Allah and what has been revealed to you and what has been revealed to them, and they humble themselves before Allah." See also: https://sunnah.com/bukhari:1327

Sai kuma Allah swt ya umarci bayinsa muminai da yin haquri da kuma dauriya a kan rinjayar maqiya addinin Allah, su jajirce har su ma su sami nasara a kan maqiyansu kuma su tsare kan iyakokin da ake tsoron shigowar maqiya daga gare su, sannan su kiyaye dokokin Allah, ta hanyar aikata umarninsa da barin haninsa; da wannan ne za su sami rabauta duniya da lahira.

Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:

  1. Hani ga Musulmi da kar ya rud'u da irin ni'ima da jin dad'i da kafirai suke mora; wannan d'an wani abu ne qanqani, kuma mai gushewa da gaggawa.
  2. Samun arziki da jin dad'in duniya ba shi yake nuna yardar Allah da soyayyarsa ga wanda ya wwa baiwar ba. Ma'aunin yarda da soyayyar Allah ita ce yi wa Allah da Manzonsa SAW d'a'a.
  3. Babu wata hanyar samun rabo daga Allah, sai ta yin haquri da juriya da jajircewa da kuma biyayya ga Allah da taimakon addininsa.
  4. Addinin Musulunci ya tattara ne a kan abubuwa guda uku:
    1. Aikata abin da aka yi umarni da shi
    2. da barin abin da aka hana
    3. da kuma haquri a kan abin da Allah ya qaddara faruwarsa.


pg491