Suna (Noun)
Jam'i |
m mutumin da ba Balarabe ba ne, ko ƙabila da ba ta Larabawa ba. Misali a ma'ana da tauhidi ana cewa
- Muhammadu ja'a bil ƙur'ani al'azim ɗariƙul huda ila kafatil Muslimina wa ila kafatil Arabi wal ajami
watau Muhammadu (S. A. W.) ya zo da Alƙur'ani mai girma, tafarkin shiriya ga dukkan Musulmi, da Larabawa da mu bebayi (watau. marasa bakin Larabci).
Siffa (Adjective)
- Siffa tare da "rubutu", rubutun ajami. Rubutu da baƙaƙen Larabci amma ba harshen Larabci aka rubuta ba. Bambance rubutu tsakanin na allo da na boko. Rubutun Hausa da haruffan Larabci. <> Hausa or another language other than Arabic written in Arabic script.
Tarihin Kalmar daga VOA Hausa na 15 Oktoba 2016