Toggle menu
24.1K
670
183
158.6K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/all

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Revision as of 23:40, 6 May 2017 by Admin (talk | contribs)

Example Sentence

  1. In the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful. <> Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. = --Qur'an 1:1
    [All] praise is [due] to Allah, Lord of the worlds - <> Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu; = --Qur'an 1:2
    The Entirely Merciful, the Especially Merciful, <> Mai rahama, Mai jin ƙai; = --Qur'an 1:3
    Sovereign of the Day of Recompense. <> Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako. = --Qur'an 1:4
    It is You we worship and You we ask for help. <> Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa. = --Qur'an 1:5
    Guide us to the straight path - <> Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya. = --Qur'an 1:6
    The path of those upon whom You have bestowed favor, not of those who have evoked [Your] anger or of those who are astray. <> Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba. = --Qur'an 1:7
    Alif, Lam, Meem. <> A. L̃. M̃. = --Qur'an 2:1
    This is the Book about which there is no doubt, a guidance for those conscious of Allah - <> Wãncan ne Littãfi, bãbu shakka a cikinsa, shiriya ne ga mãsu taƙawa. = --Qur'an 2:2
    Who believe in the unseen, establish prayer, and spend out of what We have provided for them, <> Waɗanda suke yin ĩmãni game da gaibi, kuma suna tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azurta su suna ciyarwa. = --Qur'an 2:3
    And who believe in what has been revealed to you, [O Muhammad], and what was revealed before you, and of the Hereafter they are certain [in faith]. <> Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabãninka, kuma game da Lãhira suna yin yaƙĩni. = --Qur'an 2:4
    Those are upon [right] guidance from their Lord, and it is those who are the successful. <> Waɗannan suna kan shiriya, daga Ubangjinsu, kuma waɗannan su ne mãsu cin nasara. = --Qur'an 2:5
    Indeed, those who disbelieve - it is all the same for them whether you warn them or do not warn them - they will not believe. <> Lalle ne waɗanda suka kãfirta daidai ne a kansu, shin kã yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, ba zã su yi ĩmãni ba. = --Qur'an 2:6
    Allah has set a seal upon their hearts and upon their hearing, and over their vision is a veil. And for them is a great punishment. <> Allah Ya sa hãtimi a kan zukãtansu, da a kan jinsu, kuma a Kan ganin su akwai wata yãna; kuma suna da wata azãba mai girma. = --Qur'an 2:7
    And of the people are some who say, "We believe in Allah and the Last Day," but they are not believers. <> Kuma akwai daga mutãne wanda yake cewa: "Mun yi imani da Allah kuma da Yinin Lãhira." Alhãli kuwa su ba muminai ba ne. = --Qur'an 2:8
    They [think to] deceive Allah and those who believe, but they deceive not except themselves and perceive [it] not. <> Suna yaudarayya da Allah da waɗanda suka yi ĩmãni, alhãli bã su yaudarar kõwa fãce kansu, kuma bã su sakankancẽwa! = --Qur'an 2:9
    In their hearts is disease, so Allah has increased their disease; and for them is a painful punishment because they [habitually] used to lie. <> A cikin zukãtansu akwai wata cũta. Sai Allah Ya ƙãramusu wata cũta, kuma suna da azãba mai raɗaɗi sabõda ãbin da suka kasance suna yi na ƙarya. = --Qur'an 2:10
    And when it is said to them, "Do not cause corruption on the earth," they say, "We are but reformers." <> Kuma idan aka ce musu: "Kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa," sukan ce: "Mũ mãsu kyautatawa kawai ne!" = --Qur'an 2:11
    Unquestionably, it is they who are the corrupters, but they perceive [it] not. <> To, lalle ne su, sũne mãsu ɓarna, kuma amma bã su sansancewa. = --Qur'an 2:12
    And when it is said to them, "Believe as the people have believed," they say, "Should we believe as the foolish have believed?" Unquestionably, it is they who are the foolish, but they know [it] not. <> Kuma idan aka ce musu: "ku yi ĩmãni kamar yadda mutãne suka yi ĩmãni," sukan ce: "Zã mu yi ĩmãni ne kamar yadda wãwãye suka yi ĩmãni?" To, lalle ne su, sũ ne wãwãye, kuma amma bã su sani. = --Qur'an 2:13
    And when they meet those who believe, they say, "We believe"; but when they are alone with their evil ones, they say, "Indeed, we are with you; we were only mockers." <> Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni, sukan ce: "Mun yi ĩmãni. "Kuma idan sun wõfinta zuwa ga shaiɗãnunsu, sukan ce: "Lalle ne muna tãre da ku: Mu mãsu izgili, kawai ne." = --Qur'an 2:14
    [But] Allah mocks them and prolongs them in their transgression [while] they wander blindly. <> Allah Yana yin izgili gare su kuma Yana taimakon su a cikin ɓatarsu, suna ɗimuwa. = --Qur'an 2:15
    Those are the ones who have purchased error [in exchange] for guidance, so their transaction has brought no profit, nor were they guided. <> Waɗannan su ne waɗanda suka sayi ɓata da shiriya, sai fataucinsu bai yi rĩba ba, kuma ba su kasance masu shiryuwa ba. = --Qur'an 2:16
    Their example is that of one who kindled a fire, but when it illuminated what was around him, Allah took away their light and left them in darkness [so] they could not see. <> Misãlinsu shĩ ne kamar misãlin wanda ya hũra wuta, to, a lõkacin da ta haskake abin da yake gẽfensa (na abin tsõro), Allah Ya tafi da haskensu, kuma Ya bar su a cikin duffai, bã su gani. = --Qur'an 2:17
    Deaf, dumb and blind - so they will not return [to the right path]. <> Kurãme, bẽbãye, makãfi, sabõda haka bã su kõmõwa. = --Qur'an 2:18
    Or [it is] like a rainstorm from the sky within which is darkness, thunder and lightning. They put their fingers in their ears against the thunderclaps in dread of death. But Allah is encompassing of the disbelievers. <> Ko kuwa kamar girgije mai zuba daga sama, a cikinsa akwai duffai da tsãwa da walƙiya: suna sanyãwar yãtsunsu a cikin kunnuwansu dãga tsãwarwakin, dõmin tsõron mutuwa. Kuma Allah Mai kẽwayewane gã kãfirai! = --Qur'an 2:19
    The lightning almost snatches away their sight. Every time it lights [the way] for them, they walk therein; but when darkness comes over them, they stand [still]. And if Allah had willed, He could have taken away their hearing and their sight. Indeed, Allah is over all things competent. <> Walƙiyar tana yin kusa ta fizge gannansu, ko da yaushe ta haskakã musu, sai su yi tafiya a cikinta, kuma idan ta yi duhu a kansu, sai su yi tsaye. Kuma dã Allah Yã so, sai Ya tafi da jinsu da gannansu. Lalle ne Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne. = --Qur'an 2:20
    O mankind, worship your Lord, who created you and those before you, that you may become righteous - <> Yã ku mutãne! Ku bauta wa Ubangjinku, Wanda Ya halicce ku, kũ da waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku ku kãre kanku! = --Qur'an 2:21
    [He] who made for you the earth a bed [spread out] and the sky a ceiling and sent down from the sky, rain and brought forth thereby fruits as provision for you. So do not attribute to Allah equals while you know [that there is nothing similar to Him]. <> Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma sama gini, kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya fitar da abinci daga 'ya'yan itãce game da shi, sabõda ku. Sabõda haka kada ku sanya wa Allah wasu kĩshiyõyi, alhãli kuwa kuna sane. = --Qur'an 2:22
    And if you are in doubt about what We have sent down upon Our Servant [Muhammad], then produce a surah the like thereof and call upon your witnesses other than Allah, if you should be truthful. <> Kuma idan kun kasance a cikin shakka daga abin da Muka sassaukar ga Bãwanmu, to, ku zõ da sũra guda daga misalinsa (Alƙur'ãni). Kuma ku kirãwo shaidunku baicin Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya. = --Qur'an 2:23
    But if you do not - and you will never be able to - then fear the Fire, whose fuel is men and stones, prepared for the disbelievers. <> To, idan ba ku aikata (kãwo sura) ba, to, bã zã ku aikataba, sabõda haka, ku ji tsoron wuta, wadda makãmashinta mutãne da duwãtsu ne, an yi tattalinta dõmin kãfurai. = --Qur'an 2:24
    And give good tidings to those who believe and do righteous deeds that they will have gardens [in Paradise] beneath which rivers flow. Whenever they are provided with a provision of fruit therefrom, they will say, "This is what we were provided with before." And it is given to them in likeness. And they will have therein purified spouses, and they will abide therein eternally. <> Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka yi ĩmãni. kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, cẽwa lallene, suna da gidãjen Aljanna, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Ko da yaushe aka azurta su da abinci daga wasu 'ya'yan itãce daga gare su, sai su ce: "Wannan shi ne aka azurta mu da shi daga gabãnin haka," Kuma a je musu da shi yana mai kama da juna, Kuma sunã da, a cikin su, mãtan aure mãsu tsarki, kuma su, cikin su madawwama ne. = --Qur'an 2:25
    Indeed, Allah is not timid to present an example - that of a mosquito or what is smaller than it. And those who have believed know that it is the truth from their Lord. But as for those who disbelieve, they say, "What did Allah intend by this as an example?" He misleads many thereby and guides many thereby. And He misleads not except the defiantly disobedient, <> Lalle ne, Allah bã Ya jin kunyar Ya bayyana wani misãli, kõwane iri ne, sauro da abin da yake bisa gare shi. To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, sai su san cewa lalle shi ne gaskiya daga Ubangijin su, kuma amma waɗanda suka kãfirta, sai su ce: "Mẽne ne Allah Ya yi nufi da wannan ya zama misãli?" na ɓatar da wasu mãsu yawa da shi, kuma Yana shiryar da wasu mãsu yawada shi, kuma bã Ya ɓatarwa da shi fãce fasiƙai. = --Qur'an 2:26
    Who break the covenant of Allah after contracting it and sever that which Allah has ordered to be joined and cause corruption on earth. It is those who are the losers. <> Waɗanda suke warware alƙawarin Allah daga bãyan ƙulla shi, kuma su yanke abin da Allah Ya yi umurni da shi a sãdar, kuma suna ɓarna a cikin ƙasa, waɗannan sũ ne mãsu hasãra. = --Qur'an 2:27
    How can you disbelieve in Allah when you were lifeless and He brought you to life; then He will cause you to die, then He will bring you [back] to life, and then to Him you will be returned. <> Yaya kuke kãfirta da Allah, alhãli kuwa kun kasance matattu sa'an nan Ya rãyar da ku, sa'nnan kuma Ya matar da ku, sa'an nan kuma Ya rãya ku, sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku? = --Qur'an 2:28
    It is He who created for you all of that which is on the earth. Then He directed Himself to the heaven, [His being above all creation], and made them seven heavens, and He is Knowing of all things. <> Shi ne Wanda Ya halitta muku abin da ke a cikin ƙasa gaba ɗaya, sa'an nan kuma Ya daidaita zuwa sama, sa'an nan Y a aikata su sammai bakwai. Kuma Shi ga dukan kõmai Masani ne. = --Qur'an 2:29
    And [mention, O Muhammad], when your Lord said to the angels, "Indeed, I will make upon the earth a successive authority." They said, "Will You place upon it one who causes corruption therein and sheds blood, while we declare Your praise and sanctify You?" Allah said, "Indeed, I know that which you do not know." <> Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya ce ga malã'iku: "Lalle ne, Ni Mai sanya wani halĩfa ne a cikin ƙasa," suka ce: "Ashe, zã Ka sanya a cikinta, wanda zai yi ɓarna a cikinta, kuma mu, muna yi maka tasbihi tare da gõde maka, kuma muna tsarkakewa gareka" Ya ce: "Lalle ne, Ni Na san abin da ba ku sani ba." = --Qur'an 2:30
    And He taught Adam the names - all of them. Then He showed them to the angels and said, "Inform Me of the names of these, if you are truthful." <> Kuma Ya sanar da Ãdam sũnãye dukansu, sa'an nan kuma ya gitta su a kan malã'iku, sa'n nan Ya ce: "Ku gaya mini sũnayen waɗannan, idan kun nasance mãsu gaskiya." = --Qur'an 2:31
    They said, "Exalted are You; we have no knowledge except what You have taught us. Indeed, it is You who is the Knowing, the Wise." <> Suka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka! Bãbu sani a gare mu, lalle ne Kai, Kai ne Masani, Mai hikima." = --Qur'an 2:32
    He said, "O Adam, inform them of their names." And when he had informed them of their names, He said, "Did I not tell you that I know the unseen [aspects] of the heavens and the earth? And I know what you reveal and what you have concealed." <> Ya ce: "Yã Ãdam! Ka gaya musu sũnãyensu." To, a lokacin da ya gaya musu sũnãyensu, (Allah) Ya ce: "Ashe, ban ce muku ba, lalle Ni, Inã sane da gaibin sammai da ƙasa, kuma (Inã sane da) abin da kuke bayyanawa da abin da kuka kasance kuna ɓõyewa?" = --Qur'an 2:33
    And [mention] when We said to the angels, "Prostrate before Adam"; so they prostrated, except for Iblees. He refused and was arrogant and became of the disbelievers. <> Kuma a lõkacin da Muka ce ga malã'iku: "Ku yi sujada ga Ãdam," Sai suka yi sujada, fãce Ibilĩsa ya ƙi, kuma ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai. = --Qur'an 2:34
    And We said, "O Adam, dwell, you and your wife, in Paradise and eat therefrom in [ease and] abundance from wherever you will. But do not approach this tree, lest you be among the wrongdoers." <> Kuma muka ce: "Ya Ãdam! Ka zauna kai da matarka a gidan Aljanna, kuma ku ci daga gare ta, bisa wadãta, inda kuke so, kuma kada ku kusanci wannan itãciyar, har ku kasance daga azzãlumai." = --Qur'an 2:35
    But Satan caused them to slip out of it and removed them from that [condition] in which they had been. And We said, "Go down, [all of you], as enemies to one another, and you will have upon the earth a place of settlement and provision for a time." <> Sai Shaiɗan ya talãlãɓantar da su ga barinta, sai ya fitar da su daga abin da suka kasance a cikinsa. Kuma muka ce: "Sãshenku nã maƙiyi ga sãshe, kuma kuna da a cikin ƙasa matabbata da jin dãɗi zuwa ga wani lõkaci." = --Qur'an 2:36
    Then Adam received from his Lord [some] words, and He accepted his repentance. Indeed, it is He who is the Accepting of repentance, the Merciful. <> Sai Ãdam ya karɓi wasu kalmõmi daga Ubangjjinsa, sabõda haka ya karɓi tũba a kansa. Lalle ne Shi, Shĩ ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai. = --Qur'an 2:37
    We said, "Go down from it, all of you. And when guidance comes to you from Me, whoever follows My guidance - there will be no fear concerning them, nor will they grieve. <> Muka ce: "Ku ku sauka daga gare ta gabã ɗaya. To, imma lalle shiriya ta je muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiriya ta to, bãbu tsõro a kansu, kuma bã su yin baƙin ciki." = --Qur'an 2:38
    And those who disbelieve and deny Our signs - those will be companions of the Fire; they will abide therein eternally." <> "Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu, waɗannan sũ ne abõkan Wuta; sũ a cikinta madawwama ne." = --Qur'an 2:39
    O Children of Israel, remember My favor which I have bestowed upon you and fulfill My covenant [upon you] that I will fulfill your covenant [from Me], and be afraid of [only] Me. <> Yã Banĩ Isrã'Ĩla! Ku tuna ni'imãTa a kanku, kuma ku cika alƙawariNa, In cika muku da alƙawarinku. kuma Ni, ku ji tsõro Na. = --Qur'an 2:40
    And believe in what I have sent down confirming that which is [already] with you, and be not the first to disbelieve in it. And do not exchange My signs for a small price, and fear [only] Me. <> Kuma, ku yi ĩmãni da abin da na saukar, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku, kuma kada ku kasance farkon kãfiri game da shi, Kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ãyõyiNa. Kuma ku ji tsõrõNa, Nĩ kaɗai. = --Qur'an 2:41
    And do not mix the truth with falsehood or conceal the truth while you know [it]. <> Kuma kada ku lulluɓe gaskiya da ƙarya, kuma ku ɓõye gaskiya, alhãli kuwa kuna sane. = --Qur'an 2:42
    And establish prayer and give zakah and bow with those who bow [in worship and obedience]. <> Kuma ku tsayar da salla; kuma ku bãyar da zakka; kuma ku yi rukũ'i tãre da mãsu yin rukũ'i. = --Qur'an 2:43
    Do you order righteousness of the people and forget yourselves while you recite the Scripture? Then will you not reason? <> Shin, kuna umurnin mutãne da alhẽri, kuma ku manta da kanku alhãli kuwa kuna karatun littãfi? Shin, bãzã ku hankalta ba? = --Qur'an 2:44
    And seek help through patience and prayer, and indeed, it is difficult except for the humbly submissive [to Allah] <> Kuma ku nẽmi taimako da yin haƙuri, da salla. Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa, mai girma ce fãce fa a kan mãsu tsõron Allah. = --Qur'an 2:45
    Who are certain that they will meet their Lord and that they will return to Him. <> Waɗanda suka tabbata cẽwa lalle ne su mãsu haɗuwa da Ubangijinsu, kuma lalle ne sũ a gareshi mãsu kõmãwa ne. = --Qur'an 2:46
    O Children of Israel, remember My favor that I have bestowed upon you and that I preferred you over the worlds. <> Yã banĩ Isrã'ĩla! Ku tuna ni'imaTa, wadda Na ni'imta a kanku, kuma lalle ne Ni, na fĩfĩta ku a kan tãlikai. = --Qur'an 2:47
    And fear a Day when no soul will suffice for another soul at all, nor will intercession be accepted from it, nor will compensation be taken from it, nor will they be aided. <> Kuma ku ji tsron wani yini, (a cikinsa) rai bã ya Wadãtar da wani rai da kõme, kuma bã a karɓar cetõ daga gareshi, kuma ba a karɓar fansa daga gare shi, kuma bã su zama ana taimakon su ba. = --Qur'an 2:48
    And [recall] when We saved your forefathers from the people of Pharaoh, who afflicted you with the worst torment, slaughtering your [newborn] sons and keeping your females alive. And in that was a great trial from your Lord. <> Kuma a lõkacin da muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, su na taya muku muguntar azãba, su na yayyanke ɗiyanku maza su na rãyar da mãtanku. Kuma a cikin wancan akwai jarabawa mai girma daga Ubangijinku. = --Qur'an 2:49
    And [recall] when We parted the sea for you and saved you and drowned the people of Pharaoh while you were looking on. <> Kuma a lõkacin da Muka raba tẽku sabõda ku, sai Muka tsĩrar da ku kuma Muka nutsar da mutãnen Fir'auna, alhãli kuwa kũ kuna kallo. = --Qur'an 2:50
    And [recall] when We made an appointment with Moses for forty nights. Then you took [for worship] the calf after him, while you were wrongdoers. <> Kuma a lõkacin da muka yi wa'adi ga Mũsa, dare arba'in, sa'an nan kuma kuka riƙi maraƙi daga bãyansa, alhãli kũ, kuna mãsu zãlunci (da bauta masa). = --Qur'an 2:51
    Then We forgave you after that so perhaps you would be grateful. <> Sa'an nan kuma muka yãfe muku daga bãyan wancan, tsammãninku, kuna gõdẽwa. = --Qur'an 2:52
    And [recall] when We gave Moses the Scripture and criterion that perhaps you would be guided. <> Kuma a lõkacin da Muka baiwa Mũsa Littãfi da rarrabẽwa, tsammãninku, kuna shiryuwa. = --Qur'an 2:53
    And [recall] when Moses said to his people, "O my people, indeed you have wronged yourselves by your taking of the calf [for worship]. So repent to your Creator and kill yourselves. That is best for [all of] you in the sight of your Creator." Then He accepted your repentance; indeed, He is the Accepting of repentance, the Merciful. <> Kuma a lõkacin da Mũsa ya ce ga mutãnensa: "Ya mutãnena! Lalle ne ku, kun zãlunci kanku game da riƙonku maraƙin, sai ku tũba zuwa ga Mahaliccinku, sai ku kashe kãwunanku. Wancan ne mafii alheri a wajen mahaliccinku. Sa'an nan Ya karɓi tuba a kanku. lalle ne Shi, Shi ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai. = --Qur'an 2:54
    And [recall] when you said, "O Moses, we will never believe you until we see Allah outright"; so the thunderbolt took you while you were looking on. <> Kuma a lõkacin da kuka ce: "Ya Musa! Bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka, sai munga Allah bayyane," sabada haka tsãwar nan ta kamaku, alhãli kuwa kuna kallo. = --Qur'an 2:55
    Then We revived you after your death that perhaps you would be grateful. <> Sa'an nan kuma Muka tãyar da ku daga bãyan mutuwarku, tsammãninku, kuna gõdẽwa. = --Qur'an 2:56
    And We shaded you with clouds and sent down to you manna and quails, [saying], "Eat from the good things with which We have provided you." And they wronged Us not - but they were [only] wronging themselves. <> Kuma Muka sanya girgije ya yi inuwa a kanku, kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kanku; "Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku." kuma ba su zãlunce Mu ba, kuma amma kansu suka kasance suna zãlunta. = --Qur'an 2:57
    And [recall] when We said, "Enter this city and eat from it wherever you will in [ease and] abundance, and enter the gate bowing humbly and say, 'Relieve us of our burdens.' We will [then] forgive your sins for you, and We will increase the doers of good [in goodness and reward]." <> Kuma a lokacin da Muka ce: "Ku shiga wannan alƙarya. San nan ku ci daga gareta, idan kuka so, bisa wadata, kuma ku shiga ƙofa kuna masu tawalu'i, kuma ku ce; "kãyar da zunubai" Mu gãfarta muku laifukanku, kuma zã mu ƙãra wa mãsu kyautatawa." = --Qur'an 2:58
    But those who wronged changed [those words] to a statement other than that which had been said to them, so We sent down upon those who wronged a punishment from the sky because they were defiantly disobeying. <> Sai waɗanda suka yi zalunci suka sake magana watar wannan da aka ce musu, saboda haka muka saukar a kan waɗanda suka yi zãlunci da azãba daga sama sabõda abin da suka kasance suna yi na fãsiƙanci. = --Qur'an 2:59
    And [recall] when Moses prayed for water for his people, so We said, "Strike with your staff the stone." And there gushed forth from it twelve springs, and every people knew its watering place. "Eat and drink from the provision of Allah, and do not commit abuse on the earth, spreading corruption." <> Kuma a lokacin da Mũsa ya nemi shãyarwa domin mutãnensa, Muka ce; "Ka dõki dũtsen da sandarka." Sai marmaro gõma sha biyu suka ɓuɓɓugo, haƙĩƙa, kõwaɗanne mutãne sun san wurin shansu. "Ku ci kuma ku sha daga arziƙin Ubangijinku, kuma kada ku yi fasadi, a cikin ƙasa, kuna mãsu ɓarna." = --Qur'an 2:60
    And [recall] when you said, "O Moses, we can never endure one [kind of] food. So call upon your Lord to bring forth for us from the earth its green herbs and its cucumbers and its garlic and its lentils and its onions." [Moses] said, "Would you exchange what is better for what is less? Go into [any] settlement and indeed, you will have what you have asked." And they were covered with humiliation and poverty and returned with anger from Allah [upon them]. That was because they [repeatedly] disbelieved in the signs of Allah and killed the prophets without right. That was because they disobeyed and were [habitually] transgressing. <> Kuma a lõkacin da kuka ce: "Yã Mũsã! Bã zã mu yi haƙuri ba a kan abinci guda. Sai ka rõƙa mana Ubangijinka Ya fitar mana daga abin da ƙasa take tsirarwa daga ganyenta, dumanta, da alkamarta da albasarta. Ya ce: "Kuna nẽman musanya abin da yake mafi ƙasƙanci da wanda yake mafi alhẽri? Ku sauka wani birni (daga cikin birane), lalle ne, kuna da abin da kuka rõƙa. "Kuma Muka dõka musu walãƙanci da talauci. Kuma suka kõma da wani fushi daga Allah. Wancan sabõda lalle su, sun kasance suna kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe Aannabãwa, bãda hakki ba. Wancan, sabõda sãɓawarsu ne, kuma sun kasance suna ƙẽtarewar haddi. = --Qur'an 2:61
    Indeed, those who believed and those who were Jews or Christians or Sabeans [before Prophet Muhammad] - those [among them] who believed in Allah and the Last Day and did righteousness - will have their reward with their Lord, and no fear will there be concerning them, nor will they grieve. <> Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, da waɗanda suka tũba, da Nasãra da Makarkata, wana ya yi ĩmani da Allah da Yinin Lãhira, kuma ya aikata aikin ƙwarai, to, suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba. = --Qur'an 2:62
    And [recall] when We took your covenant, [O Children of Israel, to abide by the Torah] and We raised over you the mount, [saying], "Take what We have given you with determination and remember what is in it that perhaps you may become righteous." <> Kuma a lõkacin da Muka riƙi alƙawarinku, kuma Muka ɗaukaka dũtse a bisa gareku: "Ku kãma abin da Muka baku da ƙarfi. Kuma ku ambaci abin da yake a cikin sa, tsammãninku ku kãrekanku. = --Qur'an 2:63
    Then you turned away after that. And if not for the favor of Allah upon you and His mercy, you would have been among the losers. <> Sa'an nan kuma kuka jũya daga bayan wancan, to, bã dõmin falalar Allah ba da rahamarSa a kanku, haƙĩƙa, dã kun kasance daga mãsu hasãra." = --Qur'an 2:64
    And you had already known about those who transgressed among you concerning the sabbath, and We said to them, "Be apes, despised." <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, kun san waɗanda suka ƙẽtare haddi daga gare ku a cikin Asabar, sai muka ce musu: "ku kasance birai ƙasƙantattu." = --Qur'an 2:65
    And We made it a deterrent punishment for those who were present and those who succeeded [them] and a lesson for those who fear Allah. <> Muka sanya ta (mas'alar) azãba, dõmin abin da yake gaba gareta, da yake a bãyanta, kuma wa'azi ga mãsu taƙawa. = --Qur'an 2:66
    And [recall] when Moses said to his people, "Indeed, Allah commands you to slaughter a cow." They said, "Do you take us in ridicule?" He said, "I seek refuge in Allah from being among the ignorant." <> Kuma a lõkacin da Musa yace ga mutanensa: "Lalle ne, Allah Yana umurtar ku da ku yanka wata sãniya." Suka ce: "Shin kana riƙon mu ne da izgili?" Ya ce: "Ina nẽman tsari daga Allah da in kasance daga jãhilai." = --Qur'an 2:67
    They said, "Call upon your Lord to make clear to us what it is." [Moses] said, "[Allah] says, 'It is a cow which is neither old nor virgin, but median between that,' so do what you are commanded." <> Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana, mecẽ ce ita?" Ya ce: "Lalle ne, Shi, Yana cewa: "Lalle ne ita sãniya ce; bã tsõfuwa ba, bã kuma budurwa ba, tsakãtsaki ce a tsakãnin wancan,' sai ku aikata abin da ake umurninku." = --Qur'an 2:68
    They said, "Call upon your Lord to show us what is her color." He said, "He says, 'It is a yellow cow, bright in color - pleasing to the observers.' " <> Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka Ya bayyana mana abin da yake launinta." Ya ce: "Lalle ne, Shi Yana cewa: "Ita wata saniya ce fatsa-fatsa, mai tsan-tsan launi, tana faranta ran mausu kallonta." = --Qur'an 2:69
    They said, "Call upon your Lord to make clear to us what it is. Indeed, [all] cows look alike to us. And indeed we, if Allah wills, will be guided." <> Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana abin da yake ita, lalle ne shãnu suna yi mana kamã da jũna, kuma mu, idan Allah Yã so, haƙĩƙa, shiryuwa ne." = --Qur'an 2:70
    He said, "He says, 'It is a cow neither trained to plow the earth nor to irrigate the field, one free from fault with no spot upon her.' " They said, "Now you have come with the truth." So they slaughtered her, but they could hardly do it. <> Ya ce: "Lalle ne Shi, Yana cẽwa: "Ita wata sãniya ce; ba horarra bã tana noman ƙasa, kuma ba ta shayar da shuka, lãfiyayya ce: bãbu wani sõfane a cikinta." Suka ce: "Yanzu kã zo da gaskiya. Sai suka yanka ta, kamar ba zã su aikata ba. = --Qur'an 2:71
    And [recall] when you slew a man and disputed over it, but Allah was to bring out that which you were concealing. <> Kuma a lõkacin da kuka yi kisan kai, kuka dinga tunkuɗa wa jũna laifĩ a cikinsa, kuma Allah Mai fitar da abin da kuka kasance kuna ɓõyẽwa ne. = --Qur'an 2:72
    So, We said, "Strike the slain man with part of it." Thus does Allah bring the dead to life, and He shows you His signs that you might reason. <> Sai Muka ce: "Ku dõke shi da wani sãshenta." Kamar wancan ne Allah Yake rãyar da matattu, kuma Ya nũna muku ayõyinSa, tsammãninku kuna hankalta. = --Qur'an 2:73
    Then your hearts became hardened after that, being like stones or even harder. For indeed, there are stones from which rivers burst forth, and there are some of them that split open and water comes out, and there are some of them that fall down for fear of Allah. And Allah is not unaware of what you do. <> San'nan kuma zukãtanku, suka ƙẽƙashe daga bãyan wancan. Sabõda haka suka zamanto kamar duwatsu. Ko mafi tsananin ƙeƙashewa. kuma lalle ne daga duwãtsu, haƙĩka, akwai abin da maremari suke ɓuɓɓuga daga gare shi, kuma lalle ne daga gare su, haƙĩƙa, akwai abin da yake tsatstsagewa har ruwa ya fita daga gare shi, kuma lalle ne, haƙĩƙa, daga gare su, haƙĩƙa, akwai da yake fãɗõwa dõmin tsõron Allah, kuma Allah bai zama gãfili ba daga barin abin da kuke aikatãwa. = --Qur'an 2:74
    Do you covet [the hope, O believers], that they would believe for you while a party of them used to hear the words of Allah and then distort the Torah after they had understood it while they were knowing? <> Shin fa kuna tsammãnin zã su yi imãni sabõda ku, alhãli kuwa, haƙĩƙa, wata ƙungiya daga gare su sun kasance suna jin maganar Allah, sa'an nan kuma su karkatar da ita daga bãyan sun gãne ta, alhãli sũ, suna sane? = --Qur'an 2:75
    And when they meet those who believe, they say, "We have believed"; but when they are alone with one another, they say, "Do you talk to them about what Allah has revealed to you so they can argue with you about it before your Lord?" Then will you not reason? <> Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni sukan ce: "Mun yi ĩmãni," kuma idan sãshensu ya wõfinta zuwa ga sãshe, sukan ce: "Shin, kuna yi musu magana da abin da Allah Ya buɗa muku ne dõmin su yi muku hujja da shi a wurin Ubangijinku?" Shin fa, bã ku hankalta? = --Qur'an 2:76
    But do they not know that Allah knows what they conceal and what they declare? <> Shin, kuma bã su sanin cẽwa lalle ne Allah Yana sanin abin da suke ɓõyẽwa da abin da suke bayyanãwa? = --Qur'an 2:77
    And among them are unlettered ones who do not know the Scripture except in wishful thinking, but they are only assuming. <> Kuma daga cikinsu akwai ummiyyai, bã su da sanin Littãfi, fãce tãtsuniyoyi, kuma sũ bã kõme suke yi ba fãce suna yin zato. = --Qur'an 2:78
    So woe to those who write the "scripture" with their own hands, then say, "This is from Allah," in order to exchange it for a small price. Woe to them for what their hands have written and woe to them for what they earn. <> To, bone ya tabbata ga waɗanda suke rubũta littãfi da hannuwansu sa'an nan kuma su ce wannan daga wurin Allah yake, dõmin su sayi kuɗi kaɗan da shi, san nan bone ya tabbata a gare su daga abin da hannayensu ke rubũtãwa, kuma bone ya tabbata a gare su daga abin da suke sanã'antãwa. = --Qur'an 2:79
    And they say, "Never will the Fire touch us, except for a few days." Say, "Have you taken a covenant with Allah? For Allah will never break His covenant. Or do you say about Allah that which you do not know?" <> Kuma suka ce: "Wuta bã zã ta shãfe mu ba, fãce, 'yan kwãnuka ƙidãyayyu."Ka ce: "Ashe kun riƙi wani alkawari a wurin Allah, sa'an nan Allah ba zai sãɓa wa alkawarinSa ba ko kuwa kuna faɗin abin da ba ku sani ba bisa ga Allah?" = --Qur'an 2:80
    Yes, whoever earns evil and his sin has encompassed him - those are the companions of the Fire; they will abide therein eternally. <> Na'am! Wanda ya yi tsiwur-wurin mũgun abu, kuma laifinsa ya kẽwaye shi, to, waɗannan su ne 'yan Wuta, sũ a cikinta madawwama ne. = --Qur'an 2:81
    But they who believe and do righteous deeds - those are the companions of Paradise; they will abide therein eternally. <> Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, waɗannan, 'yan Aljanna ne, sũ a cikinta madawwama ne. = --Qur'an 2:82
    And [recall] when We took the covenant from the Children of Israel, [enjoining upon them], "Do not worship except Allah; and to parents do good and to relatives, orphans, and the needy. And speak to people good [words] and establish prayer and give zakah." Then you turned away, except a few of you, and you were refusing. <> Kuma a lõkacin da Muka karɓi alkawarin Bani-Isrã'ĩla: "Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah, kuma ga mahaifa ku kyautata, da mai zumunta da marãyu da matalauta, kuma ku faɗi magana mai kyau zuwa ga mutãne, kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka, sa'an nan kuka jũya bãya, fãce kaɗan daga gare ku, alhãli kuwa kuna mãsu bijirẽwa. = --Qur'an 2:83
    And [recall] when We took your covenant, [saying], "Do not shed each other's blood or evict one another from your homes." Then you acknowledged [this] while you were witnessing. <> Lõkacin da Muka riƙi alkawarinku; bã zã ku zubar da jininku ba, kuma bã zã ku fitar da kanku daga gidãjenku ba; sa'an nan kuka tabbatar alhãli kuwa kuna bãyar da shaida (a kanku). = --Qur'an 2:84
    Then, you are those [same ones who are] killing one another and evicting a party of your people from their homes, cooperating against them in sin and aggression. And if they come to you as captives, you ransom them, although their eviction was forbidden to you. So do you believe in part of the Scripture and disbelieve in part? Then what is the recompense for those who do that among you except disgrace in worldly life; and on the Day of Resurrection they will be sent back to the severest of punishment. And Allah is not unaware of what you do. <> Sa'an nan kuma, gã ku, yã waɗannan! Kuna kashe kanku, kuma kuna fitar da wani ɓangare daga gare ku daga gidãjensu, kuna taimakon jũna a kansu da zunubi da zãlunci kuma idan kãmammu suka je muku kuna fansarsu alhãli kuwa shĩ fitar da su abin da aka haramta muku ne. Shin fa, kuna ĩmãni da sãshen Littãfin ne, kuma ku kãfirta da sãshe? To, mẽne ne sakamakon wanda ke aikata wancan daga gare ku fãce wulãkanci a cikin rãyuwar dũniya? Kuma a Rãnar ¡iyãma ana mayar da su zuwa ga mafi tsananin azãba. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga barin abin da kuke aikatãwa. = --Qur'an 2:85
    Those are the ones who have bought the life of this world [in exchange] for the Hereafter, so the punishment will not be lightened for them, nor will they be aided. <> Waɗannan su ne waɗanda suka sayi rãyuwar dũniya da Lãhira, dõmin haka bã zã a sauƙaƙa azãba ba daga kansu, kuma sũ, bã ataimakonsu. = --Qur'an 2:86
    And We did certainly give Moses the Torah and followed up after him with messengers. And We gave Jesus, the son of Mary, clear proofs and supported him with the Pure Spirit. But is it [not] that every time a messenger came to you, [O Children of Israel], with what your souls did not desire, you were arrogant? And a party [of messengers] you denied and another party you killed. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Munbai wa Mũsã Littãfi, kuma Mun biyar daga bãyansa da wasu Manzanni, kuma Muka bai wa Ĩsã ɗan Maryama hujjõji bayyanannu, kuma Muka ƙarfafa shi da Rũhi mai tsarki. Shinfa, kõ da yaushe wani manzo ya je muku tãre da abin da rãyukanku bã su so, sai ku kangara, wani ɓangare kun ƙaryata, kuma wani ɓangare kuna kashẽwa? = --Qur'an 2:87
    And they said, "Our hearts are wrapped." But, [in fact], Allah has cursed them for their disbelief, so little is it that they believe. <> Kuma suka ce: "Zukatanmu suna cikin rufi." A'a, Allah Yã la'ane su, dõmin kafircinsu kadan kwarai suke yin ĩmãni! = --Qur'an 2:88
    And when there came to them a Book from Allah confirming that which was with them - although before they used to pray for victory against those who disbelieved - but [then] when there came to them that which they recognized, they disbelieved in it; so the curse of Allah will be upon the disbelievers. <> Kuma a lõkacin da wani Littãfi daga wurin Allah ya je musu, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da su, alhãli kuwa sun kasance daga gabãnin haka suna fãtar taimako da shi a kan waɗanda suka kãfirta. To, a lõkacin da abin da suka sani ya je musu, sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka la'anar Allah ta tabbata a kan kãfirai. = --Qur'an 2:89
    How wretched is that for which they sold themselves - that they would disbelieve in what Allah has revealed through [their] outrage that Allah would send down His favor upon whom He wills from among His servants. So they returned having [earned] wrath upon wrath. And for the disbelievers is a humiliating punishment. <> Tir, da abin da suka sayi rãyukansu da shi; watau su kãfirta da abin da Allah Ya saukar sabõda zãlunci; kada Allah Ya saukar da falalarsa a kan wanda Yake so daga bãyinsa. Sai suka kõmo da fushi game da wani fushi. Kuma ga kãfirai akwai azãba mai wulãƙantarwa. = --Qur'an 2:90
    And when it is said to them, "Believe in what Allah has revealed," they say, "We believe [only] in what was revealed to us." And they disbelieve in what came after it, while it is the truth confirming that which is with them. Say, "Then why did you kill the prophets of Allah before, if you are [indeed] believers?" <> Kuma idan aka ce musu: "Ku yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar." Sai su ce: "Muna ĩmãni da abin da aka saukar a gare mu," kuma suna kãfircẽwa da abin da ke bãyansa, alhãli kuwa, shi ne gaskiyar (da suka sani) mai gaskatawa ga abin da yake tãre da su (na Attaura) Ka ce: "To, don me kuke kashe annabãwan Allah gabãnin wannan, idan kun kasance mãsu bãyar da gaskiya?" = --Qur'an 2:91
    And Moses had certainly brought you clear proofs. Then you took the calf [in worship] after that, while you were wrongdoers. <> Kuma lalle ne haƙĩƙa Mũsã ya zo muku da hujjõji bayyanannu, sa'an nan kuka riƙi maraƙi (daga bãyansa, alhãli kuwa kuna mãsu zãlunci. = --Qur'an 2:92
    And [recall] when We took your covenant and raised over you the mount, [saying], "Take what We have given you with determination and listen." They said [instead], "We hear and disobey." And their hearts absorbed [the worship of] the calf because of their disbelief. Say, "How wretched is that which your faith enjoins upon you, if you should be believers." <> Kuma a lõkacin da Muka riƙi alkawarinku kuma Muka ɗaukaka dutse a bisa gare ku, (Muka ce:) "Ku riƙi abin da Muka kãwo muku da ƙarfi kuma ku ji" Suka ce: "Mun ji kuma mun ƙi." Kuma aka zuba son maraƙin a cikin zukatansu sabõda kãfircinsu. Ka ce: "Tir da abin da ĩmãninku yake umurnin ku da shi, har idan kun kasance mãsu ĩmãni!" = --Qur'an 2:93
    Say, [O Muhammad], "If the home of the Hereafter with Allah is for you alone and not the [other] people, then wish for death, if you should be truthful. <> Ka ce: "Idan Gidan Lãhira ya kasance sabõda ku, a wurin Allah keɓe bã da sauran mutãne ba, to, ku yi gũrin mutuwa, idan kun kasance mãsu gaskiya." = --Qur'an 2:94
    But they will never wish for it, ever, because of what their hands have put forth. And Allah is Knowing of the wrongdoers. <> Kuma bã zã su yi gũrinta bahar abada sabõda abin da hannayensu, suka gabãtar. Kuma Allah Masani ne ga azzãlumai. = --Qur'an 2:95
    And you will surely find them the most greedy of people for life - [even] more than those who associate others with Allah. One of them wishes that he could be granted life a thousand years, but it would not remove him in the least from the [coming] punishment that he should be granted life. And Allah is Seeing of what they do. <> Kuma lalle ne, zã ka sãme su mafiya kwaɗayin mutãne a kan rãyuwa, kuma sũ ne mafiya kwaɗayin rãyuwa daga waɗanda suka yi shirka. ¦ayansu yana son dã zã a rãyar da shi shekara dubu, kuma bã ya zama mai nĩsantar da shi daga azãba dõmin an rãyar da shi. Kuma Allah, Mai gani ne ga abin da suke aikatãwa. = --Qur'an 2:96
    Say, "Whoever is an enemy to Gabriel - it is [none but] he who has brought the Qur'an down upon your heart, [O Muhammad], by permission of Allah, confirming that which was before it and as guidance and good tidings for the believers." <> Ka ce: Wanda ya kasance maƙiyi ga Jibirilu, to, lalle ne shi ya saukar da shi a kan zũciyarka da izinin Allah, yana mai gaskatãwa ga abin da yake gaba gare shi, kuma da shiriya da bishãra ga mũminai. = --Qur'an 2:97
    Whoever is an enemy to Allah and His angels and His messengers and Gabriel and Michael - then indeed, Allah is an enemy to the disbelievers. <> Wanda ya kasance maƙiyi ga Allah da malã'ikunSa da manzanninSa da Jibirĩla da Mĩkã'ĩla to, lalle ne, Allah Maƙiyi ne ga kãfirai. = --Qur'an 2:98
    And We have certainly revealed to you verses [which are] clear proofs, and no one would deny them except the defiantly disobedient. <> Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun saukar, zuwa gare ka, ãyõyi bayyanannu, kuma ba wanda yake kãfirta da su fãce fãsikai. = --Qur'an 2:99
    Is it not [true] that every time they took a covenant a party of them threw it away? But, [in fact], most of them do not believe. <> Shin, kuma a kõ da yaushe suka ƙulla wani alkawari sai wani ɓangare daga gare su ya, yi jĩfa da shi? Ã'a, mafi yawansu bã su yin ĩmãni. = --Qur'an 2:100
    And when a messenger from Allah came to them confirming that which was with them, a party of those who had been given the Scripture threw the Scripture of Allah behind their backs as if they did not know [what it contained]. <> Kuma a lõkacin da wani manzo (Muhammadu) daga wurin Allah ya je musu, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da su, sai wani ɓangare daga waɗanda aka bai wa Littãfi, suka yar da Littãfin (Alƙur'ãnin) Allah a bãyan bãyansu, kamar dai sũ ba su sani ba. = --Qur'an 2:101
    And they followed [instead] what the devils had recited during the reign of Solomon. It was not Solomon who disbelieved, but the devils disbelieved, teaching people magic and that which was revealed to the two angels at Babylon, Harut and Marut. But the two angels do not teach anyone unless they say, "We are a trial, so do not disbelieve [by practicing magic]." And [yet] they learn from them that by which they cause separation between a man and his wife. But they do not harm anyone through it except by permission of Allah. And the people learn what harms them and does not benefit them. But the Children of Israel certainly knew that whoever purchased the magic would not have in the Hereafter any share. And wretched is that for which they sold themselves, if they only knew. <> Kuma suka bi abin da shaiɗãnu ke karantawa a kan mulkin Sulaimãnu, kuma Sulaimãnu bai yi kãfirci ba, kuma Shaidãnun, sũ ne suka yi kãfirci, suna karantar da mutãne sihiri. Kuma ba a saukar da shi ba a kan malã'iku biyu a Bãbila, Harũta da Mãrũta. Kuma ba su sanar da kõwa ba balle su ce: "Mũ fitina kawai ne, sabõda haka kada ka kãfirta," balle har su yi ta nẽman ilmin abin da suke rarrabẽwa tsakãnin mutum da mãtarsa da shi daga gare su. Kuma su (mãsu yin sihirin) ba su zama mãsu cũtar da kõwa da shi ba, fãce da iznin Allah. Kuma suna nẽman ilmin abin da yake cũtar da su, kuma bã ya amfaninsu. Kuma lalle ne, haƙiƙa, sun sani, tabbas, wanda ya saye shi, bã ya da wani rabo a cikin Lãhira. Kuma tir da abin da suka sayar da rãyukansu da shi, dã sun kasance suna sani. = --Qur'an 2:102
    And if they had believed and feared Allah, then the reward from Allah would have been [far] better, if they only knew. <> Kuma dã lalle ne sũ, sun yi ĩmani, kuma sun yi taƙawa, haƙiƙa, da sakamako daga wurin Allah shi ne mafi alhẽri, dã sun kasance suna sani. = --Qur'an 2:103
    O you who have believed, say not [to Allah 's Messenger], "Ra'ina" but say, "Unthurna" and listen. And for the disbelievers is a painful punishment. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku ce: 'Rã'inã' kuma ku ce: 'Jinkirtã manã', kuma ku saurara. Kuma kãfirai suna da azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 2:104
    Neither those who disbelieve from the People of the Scripture nor the polytheists wish that any good should be sent down to you from your Lord. But Allah selects for His mercy whom He wills, and Allah is the possessor of great bounty. <> Waɗanda suka kãfirta daga Ma'abuta Littãfi, bã su son a saukar da wani alhẽri a kanku daga Ubangijinku, kuma mushirikai mã bã su so. Kuma Allah Yana keɓance da wanda Yake so da rahamarSa. Kuma Allah Ma'abũcin falala mai girma ne. = --Qur'an 2:105
    We do not abrogate a verse or cause it to be forgotten except that We bring forth [one] better than it or similar to it. Do you not know that Allah is over all things competent? <> Abin da Muka shãfe daga ãya, ko kuwa Muka jinkirtar da ita, zã Mu zo da mafi alhẽri daga gare ta ko kuwa misãlinta. Ashe, ba ka sani ba, cẽwa lalle ne, Allah a kan dukkan kõme Mai ĩkon yi ne? = --Qur'an 2:106
    Do you not know that to Allah belongs the dominion of the heavens and the earth and [that] you have not besides Allah any protector or any helper? <> Shin ba ka sani ba, cẽwa lalle ne Allah, Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa kuma bã ku da, baicin Allah, wani majiɓinci, kuma bã ku da wani mataimaki? = --Qur'an 2:107
    Or do you intend to ask your Messenger as Moses was asked before? And whoever exchanges faith for disbelief has certainly strayed from the soundness of the way. <> Kõ kuna nufin ku tambayi Manzonku, kamar yadda aka tambayi Mũsã a gabãnin haka? Kuma wanda ya musanya kãfirci da ĩmãni, to, lalle ne yã ɓace tsakar hanya. = --Qur'an 2:108
    Many of the People of the Scripture wish they could turn you back to disbelief after you have believed, out of envy from themselves [even] after the truth has become clear to them. So pardon and overlook until Allah delivers His command. Indeed, Allah is over all things competent. <> Mãsu yawa daga Ma'abuta Littãfi sunã gũrin dã sun mayar da ku, daga bãyan ĩmãninku, kãfirai, sabõda hãsada daga wurin rãyukansu, daga bayãn gaskiya tã bayyana a gare su. To, ku yãfe, kuma ku kau da kai, sai Allah Yã zo da umurninSa. Lalle ne Allah a kan dukkan kõme Mai ĩkon yi ne. = --Qur'an 2:109
    And establish prayer and give zakah, and whatever good you put forward for yourselves - you will find it with Allah. Indeed, Allah of what you do, is Seeing. <> Kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka. Kuma abin da kuka gabãtar dõmin kanku daga alhẽri, zã ku sãme shi a wurin Allah. Lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatãwa Mai gani ne. = --Qur'an 2:110
    And they say, "None will enter Paradise except one who is a Jew or a Christian." That is [merely] their wishful thinking, Say, "Produce your proof, if you should be truthful." <> Kuma suka ce: "Bãbu mai shiga Aljanna fãce waɗanda suka zama Yahũdu ko Nasãra." Waɗancan tãtsũniyõyinsu ne. Ka ce: "Ku kãwo dalilinku idan kun kasance mãsu gaskiya." = --Qur'an 2:111
    Yes [on the contrary], whoever submits his face in Islam to Allah while being a doer of good will have his reward with his Lord. And no fear will there be concerning them, nor will they grieve. <> Na'am! Wanda ya sallama fuskarsa ga Allah, alhãli kuwa yana mai kyautatãwa, to, yana da ijãrarsa, a wurin Ubangijinsa, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba. = --Qur'an 2:112
    The Jews say "The Christians have nothing [true] to stand on," and the Christians say, "The Jews have nothing to stand on," although they [both] recite the Scripture. Thus the polytheists speak the same as their words. But Allah will judge between them on the Day of Resurrection concerning that over which they used to differ. <> Kuma Yahũdãwa suka ce: "Nasãra ba su zamana a kan kõme ba," kuma Nasãra suka ce: "Yahũdãwa ba su zamana a kan kõmeba," alhãli kuwa su, suna karãtun Littãfi. Kamar wancan ne waɗanda ba su sani ba suka faɗa, kamar maganarsu sabõda haka Allah ne ke yin hukunci a tsakãninsu a Rãnar ¡iyãma, a cikin abin da suka kasance suna sãɓawa jũna a cikinsa. = --Qur'an 2:113
    And who are more unjust than those who prevent the name of Allah from being mentioned in His mosques and strive toward their destruction. It is not for them to enter them except in fear. For them in this world is disgrace, and they will have in the Hereafter a great punishment. <> Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya hana masallãtan Allah, dõmin kada a ambaci sunanSa a cikinsu, sai kuma ya yi aiki ga rushe su? Waɗannan bã ya kasancẽwa a gare su su shigẽ su fãce suna mãsu tsõro. Suna da, a cikin duniya wani wulãkanci, kuma suna da, a cikin Lãhira, azãba mai girma. = --Qur'an 2:114
    And to Allah belongs the east and the west. So wherever you [might] turn, there is the Face of Allah. Indeed, Allah is all-Encompassing and Knowing. <> Kuma Allah ɗai yake da gabas da yamma sabõda haka, inda duk aka jũyar da ku, to, a can fuskar Allah take. Lalle ne, Allah Mawadãci ne, Mai ilmi. = --Qur'an 2:115
    They say, "Allah has taken a son." Exalted is He! Rather, to Him belongs whatever is in the heavens and the earth. All are devoutly obedient to Him, <> Kuma suka ce: "Allah Yã riƙi ɗã." Tsarki yã tabbata a gare Shi! A'a, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da ƙasa, dukansu, a gare Shi, mãsu ƙanƙan da kai ne. = --Qur'an 2:116
    Originator of the heavens and the earth. When He decrees a matter, He only says to it, "Be," and it is. <> Mai kyautata halittar sammai da ƙasa, kuma idan Ya hukunta wani al'amari, sai kawai Ya ce masa: "Kasance." Sai ya yi ta kasancewa. = --Qur'an 2:117
    Those who do not know say, "Why does Allah not speak to us or there come to us a sign?" Thus spoke those before them like their words. Their hearts resemble each other. We have shown clearly the signs to a people who are certain [in faith]. <> Kuma waɗanda bã su da sani suka ce: "Don me Allah bã Ya yi mana magana, ko wata ãyã ta zo mana?" Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu suka faɗa, kamar maganarsu. zukãtansu sun yi kamã da jũna. Lalle ne, Mun bayyana ãyõyi ga mutãne masu sakankancewa. = --Qur'an 2:118
    Indeed, We have sent you, [O Muhammad], with the truth as a bringer of good tidings and a warner, and you will not be asked about the companions of Hellfire. <> Lalle ne Mun aike ka da gaskiya, kana mai bãyar da bishãra, kuma mai gargaɗi, kuma bã zã a tambaye ka ba, game da abõkan Wuta. = --Qur'an 2:119
    And never will the Jews or the Christians approve of you until you follow their religion. Say, "Indeed, the guidance of Allah is the [only] guidance." If you were to follow their desires after what has come to you of knowledge, you would have against Allah no protector or helper. <> Kuma Yahũdu bã zã su yarda da kõme daga gare ka ba, kuma Nasãra bã zã su yarda ba, sai kã bi irin aƙidarsu. Ka ce: "Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya." Kuma lalle ne idan ka bi son zũciyõyinsu a bãyan abin da ya zo maka na ilmi, bã ka da, daga Allah, wani majiɓinci, kuma bãbu wani mataimaki. = --Qur'an 2:120
    Those to whom We have given the Book recite it with its true recital. They [are the ones who] believe in it. And whoever disbelieves in it - it is they who are the losers. <> Waɗanda Muka bai wa Littãfi suna karãtunsa a kan haƙƙin karãtunsa, waɗannan suna ĩmani da shi (Alƙur'ãni). Kuma wanda ya kãfirta da shi, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra. = --Qur'an 2:121
    O Children of Israel, remember My favor which I have bestowed upon you and that I preferred you over the worlds. <> Yã Banĩ Isrã'ĩla! Ku tuna ni'imaTa wadda Na ni'imtar da ita a kanku, kuma lalle ne Nĩ, Nã fĩfĩtã ku a kan tãlikai. = --Qur'an 2:122
    And fear a Day when no soul will suffice for another soul at all, and no compensation will be accepted from it, nor will any intercession benefit it, nor will they be aided. <> Ku ji tsõron wani yini, (a cikinsa) wani rai bã ya tunkuɗe wa wani rai kõme kuma bã a karɓar fansa daga gare shi, kuma wani cẽto bã ya amfanin sa, kuma ba su zama ana taimakon su ba. = --Qur'an 2:123
    And [mention, O Muhammad], when Abraham was tried by his Lord with commands and he fulfilled them. [Allah] said, "Indeed, I will make you a leader for the people." [Abraham] said, "And of my descendants?" [Allah] said, "My covenant does not include the wrongdoers." <> Kuma a lõkacin da Ubangijin Ibrãhim Ya jarrabẽ shi da wasu kalmõmi, sai ya cika su. Ya ce: "Lalle ne Nĩ, Mai sanya ka shugaba dõmin mutãne ne." Ya ce: "Kuma daga zũriyata." Ya ce: "AlkawarĩNa bã zai sãmu azzãlumai ba." = --Qur'an 2:124
    And [mention] when We made the House a place of return for the people and [a place of] security. And take, [O believers], from the standing place of Abraham a place of prayer. And We charged Abraham and Ishmael, [saying], "Purify My House for those who perform Tawaf and those who are staying [there] for worship and those who bow and prostrate [in prayer]." <> Kuma a lõkacin da Muka sanya ¦ãkin ya zama makõma ga mutãne, da aminci, kuma ku riƙi wurin salla daga Maƙãmi Ibrãhĩm, kuma Muka yi alƙawari zuwa ga Ibrãhĩm, da Ismã'ila da cẽwa: "Ku tsarkake ¦ãkiNa dõmin mãsu ɗawãfi da mãsu lizimta da mãsu rukũ'i, mãsu sujada." = --Qur'an 2:125
    And [mention] when Abraham said, "My Lord, make this a secure city and provide its people with fruits - whoever of them believes in Allah and the Last Day." [Allah] said. "And whoever disbelieves - I will grant him enjoyment for a little; then I will force him to the punishment of the Fire, and wretched is the destination." <> Kuma a lõkacin da lbrãhĩm ya ce: "Yã Ubangijĩna! Ka sanya wannan gari amintacce, Ka azurta mutãnensa, daga 'ya'yan itãcen, wanda ya yi ĩmãni, daga gare su, da Allah da Ranar Lãhira." Allah Ya ce: "Wanda ya kãfirta ma Ina jiyar da shi dãɗi kaɗan, sa'an nan kuma Ina tĩlastã shi zuwa ga azãbar Wuta. Kuma makõmar, ta munana." = --Qur'an 2:126
    And [mention] when Abraham was raising the foundations of the House and [with him] Ishmael, [saying], "Our Lord, accept [this] from us. Indeed You are the Hearing, the Knowing. <> Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm yake ɗaukaka harsãshin gini ga ¦ãkin, da Ismã'ĩla (suna cẽwa:) "Yã Ubangijnmu! Ka karɓa daga gare mu, lalle ne Kai, Kai ne Mai ji, Mai sani. = --Qur'an 2:127
    Our Lord, and make us Muslims [in submission] to You and from our descendants a Muslim nation [in submission] to You. And show us our rites and accept our repentance. Indeed, You are the Accepting of repentance, the Merciful. <> "Ya Ubangijnmu! Ka sanyã mu, mu biyu, waɗanda suka sallama (al'amari) gare Ka, kuma daga zuriyarmu (Ka sanya) al'umma mai sallamãwa zuwa gare Ka, Kuma Ka nũna mana wurãren ibãdar hajjinmu, kuma Ka karɓi tũba a kanmu. Lalle ne Kai, Kai ne Mai karɓar tũba, Mai rahama. = --Qur'an 2:128
    Our Lord, and send among them a messenger from themselves who will recite to them Your verses and teach them the Book and wisdom and purify them. Indeed, You are the Exalted in Might, the Wise." <> "Ya Ubangijinmu! Ka aiko, a cikinsu, wani manzo daga gare su, yana karanta musu ãyõyinKa, kuma yana karantar da su Littãfin da hikimar, kuma yana tsarkake su. Lalle ne Kai, Kai ne Mabuwãyi Mai hikima." = --Qur'an 2:129
    And who would be averse to the religion of Abraham except one who makes a fool of himself. And We had chosen him in this world, and indeed he, in the Hereafter, will be among the righteous. <> Kuma wãne ne yake gudu daga aƙĩdar Ibrãhĩm, fãce wanda ya jãhilta ga ransa? Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe shi, a cikin dũniya, kuma lalle ne shi, a cikin Lãhira, haƙĩƙa, yana daga sãlihai. = --Qur'an 2:130
    When his Lord said to him, "Submit", he said "I have submitted [in Islam] to the Lord of the worlds." <> A lõkacin da Ubangijinsa Ya ce masa: "Ka miƙa wuya," ya ce: "Nã miƙa wuya ga Ubangijin tãlikai." = --Qur'an 2:131
    And Abraham instructed his sons [to do the same] and [so did] Jacob, [saying], "O my sons, indeed Allah has chosen for you this religion, so do not die except while you are Muslims." <> Kuma lbrãhĩm ya yi wasiyya da ita ga ɗiyansa, kuma Ya'aƙũbu (ya yi wasiyya, suka ce:) "Yã ɗiyãna! Lalle ne, Allah Ya zãɓã muku addini don haka kada ku mutu, lalle, fãce kuna Musulmi." = --Qur'an 2:132
    Or were you witnesses when death approached Jacob, when he said to his sons, "What will you worship after me?" They said, "We will worship your God and the God of your fathers, Abraham and Ishmael and Isaac - one God. And we are Muslims [in submission] to Him." <> Ko kun kasance halarce a lõkacin da mutuwa ta halarci Ya'aƙũbu, a lõkacin da ya ce wa ɗiyansa: "Mẽne ne zã ku bauta wa daga bãyãna?" Suka ce: "Muna bauta wa Abin bautawarka kuma Abin bautawar ubanninka lbrãhĩm da lsmã'ĩla da Is'hãƙa, Ubangiji Guda, kuma mu a gare Shi mãsu miƙa wuya ne." = --Qur'an 2:133
    That was a nation which has passed on. It will have [the consequence of] what it earned, and you will have what you have earned. And you will not be asked about what they used to do. <> Waccan, wata al'umma ce, ta riga ta shige, tana da abin da ta sanã'anta kuma kuna da abin da kuka sanã'anta, Kuma bã zã a tambaye ku ba daga abin da suka kasance suna aikatãwa. = --Qur'an 2:134
    They say, "Be Jews or Christians [so] you will be guided." Say, "Rather, [we follow] the religion of Abraham, inclining toward truth, and he was not of the polytheists." <> Kuma suka ce: "Ku kasance Yahũdãwa ko Nasãra, kwã shiryu."Ka ce: "A'a aƙidar Ibrãhĩm dai, maikarkata, zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba." = --Qur'an 2:135
    Say, [O believers], "We have believed in Allah and what has been revealed to us and what has been revealed to Abraham and Ishmael and Isaac and Jacob and the Descendants and what was given to Moses and Jesus and what was given to the prophets from their Lord. We make no distinction between any of them, and we are Muslims [in submission] to Him." <> Ku ce: "Mun yi ĩmãni da Allah, da abin da aka saukar zuwa gare mu, da abin da aka saukar zuwa ga Ibrãhĩm da Ismã'ĩla da Is'hãka da Ya'aƙũbu da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da Ĩsã, da abin da aka bai wa annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu rarrabẽwa a tsakãnin kõwa daga gare su, kuma mu, a gare Shi, mãsu miƙa wuya ne." = --Qur'an 2:136
    So if they believe in the same as you believe in, then they have been [rightly] guided; but if they turn away, they are only in dissension, and Allah will be sufficient for you against them. And He is the Hearing, the Knowing. <> To, idan sun yi ĩmãni da misãlin abin da kuka yi ĩmãni da shi, to, lalle ne sun shiryu, kuma idan sun jũya bãya, to, suna a cikin sãɓãni kawai sabõda haka Allah zai isar maka a gare su, kuma Shi ne Mai ji, Masani. = --Qur'an 2:137
    [And say, "Ours is] the religion of Allah. And who is better than Allah in [ordaining] religion? And we are worshippers of Him." <> Rinin Allah! Kuma wãne ne mafi kyau ga rini daga Allah? Kuma mu, a gare Shi, mãsu bautãwa ne. = --Qur'an 2:138
    Say, [O Muhammad], "Do you argue with us about Allah while He is our Lord and your Lord? For us are our deeds, and for you are your deeds. And we are sincere [in deed and intention] to Him." <> Ka ce: Shin kuna jãyayyar hujia ne da mu a cikin al'amarin Allah, alhãli kuwa Shi ne Ubangijinmu kuma Ubangijinku, kuma muna da ayyukanmu, kuma kuna da ayyukanku, kuma mũ, a gare Shi, mãsu tsarkakẽwane? = --Qur'an 2:139
    Or do you say that Abraham and Ishmael and Isaac and Jacob and the Descendants were Jews or Christians? Say, "Are you more knowing or is Allah?" And who is more unjust than one who conceals a testimony he has from Allah? And Allah is not unaware of what you do. <> Ko kuna cẽwa: Lalle ne, Ibrãhĩm da Ismã'ĩla da Is'hãƙa da Ya'aƙũbu da Jĩkõki, sun kasance Yahũdãwa kõ kuwa Nasãra? Ka ce: Shin kũ ne kuke mafi sani kõAllah? Kuma wãne ne ya zama mafi zãlunci daga wanda ya bõye shaida a wurinsa daga Allah? Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da kuke aikatãwa! = --Qur'an 2:140
    That is a nation which has passed on. It will have [the consequence of] what it earned, and you will have what you have earned. And you will not be asked about what they used to do. <> Waccan, wata al'umma ce, tã riga ta shige, suna da abin da suka sana'anta kuma kuna da abin da kuka sana'anta kuma bã a tambayar ku daga abin da suka kasance suna aikatãwa. = --Qur'an 2:141
    The foolish among the people will say, "What has turned them away from their qiblah, which they used to face?" Say, "To Allah belongs the east and the west. He guides whom He wills to a straight path." <> Wãwãye daga mutãne zã su ce: Mẽne ne ya jũyar da su daga alƙiblarsu wadda suka kasance a kanta? Ka ce: "Allah ¦ai ne Yake da gabas da yamma, Yana shiryar da wanda Yake so zuwa ga hanya madaidaiciya." = --Qur'an 2:142
    And thus we have made you a just community that you will be witnesses over the people and the Messenger will be a witness over you. And We did not make the qiblah which you used to face except that We might make evident who would follow the Messenger from who would turn back on his heels. And indeed, it is difficult except for those whom Allah has guided. And never would Allah have caused you to lose your faith. Indeed Allah is, to the people, Kind and Merciful. <> Kuma kamar wancan, Muka sanya ku al'umma matsakaiciya dõmin ku kasance mãsu bãyar da shaida a kan mutãne. Kuma Manzo ya kasance mai shaida a kanku. Kuma ba Mu sanya Alƙibla wadda ka kasance a kanta ba, fãce dõmin Mu san wanda yake biyar Manzo daga wanda yake jũyãwa a kan duga-dugansa. Kuma lalle ne, tã kasance haƙĩƙa, mai girma, sai a kan waɗanda Allah Ya shiryar. Kuma ba ya yiwuwa ga Allah Ya tõzartar da ĩmãninku. Lalle ne, Allah, ga mutãne, haƙĩƙa, Mai tausayi ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 2:143
    We have certainly seen the turning of your face, [O Muhammad], toward the heaven, and We will surely turn you to a qiblah with which you will be pleased. So turn your face toward al-Masjid al-Haram. And wherever you [believers] are, turn your faces toward it [in prayer]. Indeed, those who have been given the Scripture well know that it is the truth from their Lord. And Allah is not unaware of what they do. <> Lalle ne, Muna ganin jujjũyãwar fuskarka a cikin sama. To, lalle ne, Mu jũyar da kai ga Alƙibla wadda kake yardã da ita. Sai ka jũyar da fuskarka wajen Masallãci Tsararre, kuma inda duk kuka kasance, to, ku jũyar da fuskõkinku jiharsa. Kuma lalle ne waɗanda aka bai wa Littãfi, haƙĩƙa su, sunã sanin lalle ne, shĩ ne gaskiya, daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da suke aikatãwa. = --Qur'an 2:144
    And if you brought to those who were given the Scripture every sign, they would not follow your qiblah. Nor will you be a follower of their qiblah. Nor would they be followers of one another's qiblah. So if you were to follow their desires after what has come to you of knowledge, indeed, you would then be among the wrongdoers. <> Kuma hakĩka, idan ka je wawaɗanda aka bai wa Littafi da dukan ãyã, bã zã su bi Alƙiblarka ba, kuma kai ba ka zama mai bin Alƙiblarsu ba, kuma sãshensu bã mai bin Alƙiblar sãshe ba ne. Kuma haƙĩƙa, idan ka bi son zũciyõyinsu daga bãyan abin da ya zo maka daga ilmi, lalle ne kai, sa'an nan, haƙiƙa, azzãlumi kake. = --Qur'an 2:145
    Those to whom We gave the Scripture know him as they know their own sons. But indeed, a party of them conceal the truth while they know [it]. <> Waɗanda Muka bã su Littãfi, suna saninsa kamar yadda suke sanin ɗiyansu. Kuma lalle ne wani ɓangare daga gare su, haƙiƙa, suna ɓõyewar gaskiya alhãli kuwa sũ, suna sane. = --Qur'an 2:146
    The truth is from your Lord, so never be among the doubters. <> Gaskiya daga Ubangijinka take sabõda haka, lalle kada ka kasance daga mãsu shakka. = --Qur'an 2:147
    For each [religious following] is a direction toward which it faces. So race to [all that is] good. Wherever you may be, Allah will bring you forth [for judgement] all together. Indeed, Allah is over all things competent. <> Kuma kõwane ɓangare yana da alƙibla wadda yake shi mai fuskantar ta ne. Sai ku yi tsẽre zuwa ga ayyukan alhẽri, inda kuka kasance duka Allah zai zo da ku gabã ɗaya. Lalle ne Allah, a kan kõme, Mai ĩkon yi ne. = --Qur'an 2:148
    So from wherever you go out [for prayer, O Muhammad] turn your face toward al- Masjid al-Haram, and indeed, it is the truth from your Lord. And Allah is not unaware of what you do. <> Kuma daga inda ka fita, to, sai ka jũyar da fuskarka a wajen Masallãci Tsararre kuma lalle tabbas, shi ne gaskiya daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da kuke aikatãwa ba. = --Qur'an 2:149
    And from wherever you go out [for prayer], turn your face toward al-Masjid al-Haram. And wherever you [believers] may be, turn your faces toward it in order that the people will not have any argument against you, except for those of them who commit wrong; so fear them not but fear Me. And [it is] so I may complete My favor upon you and that you may be guided. <> Kuma daga inda ka fita, to, ka jũyar da fuskarka a wajen Masallãci Tsararre kuma inda kuke duka, to, ku jũyar da fuskõkinku a wajensa, dõmin kada wata hujja ta kasance ga mutãne a kanku, fãce waɗanda suka yi zãlunci daga gare su. Sabõda haka kada ku ji tsõronsu kuma ku ji tsõrõNa kuma dõmin In cika ni'imaTa a kanku, kuma tsammãninku zã ku shiryu. = --Qur'an 2:150
    Just as We have sent among you a messenger from yourselves reciting to you Our verses and purifying you and teaching you the Book and wisdom and teaching you that which you did not know. <> Kamar yadda Muka aika Manzo a cikinku, daga gare ku, yana karanta ãyõyinMu a gare ku kuma yana tsarkake ku, kuma yana sanar da ku Littãfi da hikima, kuma yana sanar da ku abin da ba ku kasance kuna sani ba. = --Qur'an 2:151
    So remember Me; I will remember you. And be grateful to Me and do not deny Me. <> Sabõda haka, ku tuna Ni, In tunã ku, kuma ku yi gõdiya gare Ni, kuma kada ku butulce Mini. = --Qur'an 2:152
    O you who have believed, seek help through patience and prayer. Indeed, Allah is with the patient. <> Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku nẽmi taimako da haƙuri game da salla. Lalle ne, Allah na tãre da mãsu haƙuri. = --Qur'an 2:153
    And do not say about those who are killed in the way of Allah, "They are dead." Rather, they are alive, but you perceive [it] not. <> Kada ku ce ga waɗanda ake kashẽwa a cikin hanyar Allah: "Matattu ne." Ã'a, rãyayyu ne, kuma amma bã ku sansancẽwa. = --Qur'an 2:154
    And We will surely test you with something of fear and hunger and a loss of wealth and lives and fruits, but give good tidings to the patient, <> Kuma lalle ne, Muna jarrabar ku da wani abu daga tsõro da yunwa da naƙasa daga dũkiya da rãyuka da 'ya'yan itãce. Kuma ka yi bishãra ga mãsu haƙuri. = --Qur'an 2:155
    Who, when disaster strikes them, say, "Indeed we belong to Allah, and indeed to Him we will return." <> Waɗanda suke idan wata masĩfa ta sãme su, sai su ce: "Lalle ne mũ ga Allah muke, kuma lalle ne mũ, zuwa gare Shi, muke kõmãwa." = --Qur'an 2:156
    Those are the ones upon whom are blessings from their Lord and mercy. And it is those who are the [rightly] guided. <> Waɗannan akwai albarku a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama. Kuma waɗannan sũ ne shiryayyu. = --Qur'an 2:157
    Indeed, as-Safa and al-Marwah are among the symbols of Allah. So whoever makes Hajj to the House or performs 'umrah - there is no blame upon him for walking between them. And whoever volunteers good - then indeed, Allah is appreciative and Knowing. <> Lalle ne Safã da Marwa suna daga wurãren ibãdar Allah, to, wanda ya yi hajin ¦ãki kõ kuwa ya yi Umra, to, bãbu laifi a kansa ga ya yi ɗawãfi gare su, su biyu. Kuma wanda ya ƙãra yin wani aikin alhẽri to, lalle ne Allah Mai gõdiya ne, Masani. = --Qur'an 2:158
    Indeed, those who conceal what We sent down of clear proofs and guidance after We made it clear for the people in the Scripture - those are cursed by Allah and cursed by those who curse, <> Lalle ne waɗanda suke ɓõyẽwar abin da Allah Ya saukar da ga hujjõji bayyanannu, da shiriya, daga bãyan Mun bayyana shi ga mutãne, a cikin Littãfi (Alƙur'ãni), waɗannan Allah Yana la'anar su, kuma mãsu la'ana suna la'anar su. = --Qur'an 2:159
    Except for those who repent and correct themselves and make evident [what they concealed]. Those - I will accept their repentance, and I am the Accepting of repentance, the Merciful. <> Sai waɗanda suka tũba, kuma suka gyãra, kuma suka bayyana, to waɗannan Ina karɓar tũba a kansu kuma Nĩ ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai. = --Qur'an 2:160
    Indeed, those who disbelieve and die while they are disbelievers - upon them will be the curse of Allah and of the angels and the people, all together, <> Lalle ne, waɗanda suka kãfirta kuma suka mutu alhãli kuwa suna kãfirai, waɗannan akwai, a kansu, la'anar Allah da Malã'iku da mutãne gabã ɗaya. = --Qur'an 2:161
    Abiding eternally therein. The punishment will not be lightened for them, nor will they be reprieved. <> Suna madawwama a cikinta, bã a sauƙaƙa azãba daga barinsu, kuma ba su zama ana jinkirta musu ba. = --Qur'an 2:162
    And your god is one God. There is no deity [worthy of worship] except Him, the Entirely Merciful, the Especially Merciful. <> Kuma Ubangijinku Ubangiji Guda ne. Bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Mai rahama, Mai jin ƙai. = --Qur'an 2:163
    Indeed, in the creation of the heavens and earth, and the alternation of the night and the day, and the [great] ships which sail through the sea with that which benefits people, and what Allah has sent down from the heavens of rain, giving life thereby to the earth after its lifelessness and dispersing therein every [kind of] moving creature, and [His] directing of the winds and the clouds controlled between the heaven and the earth are signs for a people who use reason. <> Lalle ne, a cikin halittar sammai da ƙasa, da sãɓãwar dare da yini, da jirãge wadaɗnda suke gudana a cikin tẽku (ɗauke) da abin da yake amfãnin mutãne, da abin da Allah Ya saukar daga sama daga ruwa, sai Ya rãyar da ƙasa da shi a bãyan mutuwarta, kuma Ya wãtsa, a cikinta, daga dukan dabba, kuma da jũyãwar iskõki da girgije hõrarre a tsakãnin sama da ƙasa; haƙĩƙa, akwaiãyõyi ga mutãne mãsu yin hankali. = --Qur'an 2:164
    And [yet], among the people are those who take other than Allah as equals [to Him]. They love them as they [should] love Allah. But those who believe are stronger in love for Allah. And if only they who have wronged would consider [that] when they see the punishment, [they will be certain] that all power belongs to Allah and that Allah is severe in punishment. <> Kuma akwai daga mutãne wanda yake riƙon kinãye, baicin Allah, suna son su, kamar son Allah, kuma waɗanda suka yi ĩmãni ne mafiya tsananin so ga Allah. Kuma dã waɗanda suka yi zãlunci, suna ganin lõkacin da zã su ga azãba, da cewa lalle ne ƙarfi ga Allah yake duka, da cẽwa lalle neAllah Mai tsananin azãba ne. = --Qur'an 2:165
    [And they should consider that] when those who have been followed disassociate themselves from those who followed [them], and they [all] see the punishment, and cut off from them are the ties [of relationship], <> A lõkacin da waɗanda aka bi suka barranta daga waɗanda suka bi, kuma suka ga azãba, kuma sabubba suka yanke da su. = --Qur'an 2:166
    Those who followed will say, "If only we had another turn [at worldly life] so we could disassociate ourselves from them as they have disassociated themselves from us." Thus will Allah show them their deeds as regrets upon them. And they are never to emerge from the Fire. <> Kuma waɗanda suka bi, suka ce: "Dã lalle ne muna da wata kõmãwa (dũniya) sai mu barranta dagagare su kamar yadda suka barranta daga gare mu (dã ba su riƙi kinãyen ba)." Kamar wancan ne Allah ke nũna musu ayyukansu, suna da nadãmõmi a kansu, kuma ba su zama mãsu fita daga wutar ba. = --Qur'an 2:167
    O mankind, eat from whatever is on earth [that is] lawful and good and do not follow the footsteps of Satan. Indeed, he is to you a clear enemy. <> Yã ku mutãne! Ku ci daga abin da yake a cikin ƙasa, wanda yake halal, mai dãɗi. Kuma kada ku bi zambiyõyin Shaiɗan. Lalle ne shi, gare ku, maƙiyi ne bayyananne. = --Qur'an 2:168
    He only orders you to evil and immorality and to say about Allah what you do not know. <> Yana umurnin ku ne kawai da mugun aiki da alfãsha, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba ga Allah. = --Qur'an 2:169
    And when it is said to them, "Follow what Allah has revealed," they say, "Rather, we will follow that which we found our fathers doing." Even though their fathers understood nothing, nor were they guided? <> Kuma idan aka ce musu: "Ku bi abin da Allah Ya saukar," sai su ce: Ã'a, muna bin abin da muka iske ubanninmu a kansa." Shin, kuma kõ dã ubanninsu bã su hankaltar kõme, kuma bã su shiryuwa? = --Qur'an 2:170
    The example of those who disbelieve is like that of one who shouts at what hears nothing but calls and cries cattle or sheep - deaf, dumb and blind, so they do not understand. <> Kuma misãlin (mai kiran) waɗanda suka kãfirta kamar misãlin wanda ke yin me! me! ga abin da ba ya ji ne, fãce kira da ƙãra, kurãme, bẽbãye, makafi, sabõda haka bã su hankalta. = --Qur'an 2:171
    O you who have believed, eat from the good things which We have provided for you and be grateful to Allah if it is [indeed] Him that you worship. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ci ku sha daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku. Kuma ku gõde wa Allah, idan kun kasance Shi kuke bauta wa. = --Qur'an 2:172
    He has only forbidden to you dead animals, blood, the flesh of swine, and that which has been dedicated to other than Allah. But whoever is forced [by necessity], neither desiring [it] nor transgressing [its limit], there is no sin upon him. Indeed, Allah is Forgiving and Merciful. <> Kawai abin da Ya haramta a kanku, mũshe da Jini da nãman alade da abin da aka kurũrũta game da shi ga wanin Allah. To, wanda aka matsã, wanin ɗan tãwãye, kuma banda mai zãlunci, to bãbu laifi a kansa. Lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 2:173
    Indeed, they who conceal what Allah has sent down of the Book and exchange it for a small price - those consume not into their bellies except the Fire. And Allah will not speak to them on the Day of Resurrection, nor will He purify them. And they will have a painful punishment. <> Lalle ne waɗannan da suke ɓõye abin da Allah Ya saukar daga Littãfi, kuma suna sayen kuɗi kaɗan da shi; waɗannan bã su cin kome a cikin cikkunansu fãce wuta, kuma Allah bã zai yi musu magana ba a Rãnar ¡iyãma, kuma bã zai tsarkake su ba, kuma suna da azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 2:174
    Those are the ones who have exchanged guidance for error and forgiveness for punishment. How patient they are in pursuit of the Fire! <> Waɗannan su ne waɗanda suka sayi ɓata da shiriya, kuma azãba da gãfara. To, me ya yi haƙurinsu a kan Wuta! = --Qur'an 2:175
    That is [deserved by them] because Allah has sent down the Book in truth. And indeed, those who differ over the Book are in extreme dissension. <> Wancan dõmin lalle ne Allah Ya saukar da Littafi da gaskiya, kuma lalle ne waɗanda suka sãɓã a cikin Littãfin, haƙĩƙa, suna a cikin sãɓãni mai nĩsa. = --Qur'an 2:176
    Righteousness is not that you turn your faces toward the east or the west, but [true] righteousness is [in] one who believes in Allah, the Last Day, the angels, the Book, and the prophets and gives wealth, in spite of love for it, to relatives, orphans, the needy, the traveler, those who ask [for help], and for freeing slaves; [and who] establishes prayer and gives zakah; [those who] fulfill their promise when they promise; and [those who] are patient in poverty and hardship and during battle. Those are the ones who have been true, and it is those who are the righteous. <> Bai zama addini ba dõmin kun jũyar da fuskõkinku wajen gabas da yamma, kuma amma addini shi ne ga wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira da malã'iku da Littattafan sama da Annabãwa, kuma ya bãyar da dũkiya, akan yana son ta, ga mai zumunta da marãyu da matalauta da ɗan hanya da mãsu rõƙo, kuma a cikin fansar wuya, kuma ya tsayar da salla, kuma ya bãyar da zakka, da mãsu cika alkawari idan sun ƙulla alkawarin da mãsu haƙuri a cikin tsanani da cũta da lõkacin yãƙi. Waɗannan su ne suka yi gaskiya. Kuma waɗannan su ne mãsu taƙawa. = --Qur'an 2:177
    O you who have believed, prescribed for you is legal retribution for those murdered - the free for the free, the slave for the slave, and the female for the female. But whoever overlooks from his brother anything, then there should be a suitable follow-up and payment to him with good conduct. This is an alleviation from your Lord and a mercy. But whoever transgresses after that will have a painful punishment. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta, a kanku, yin ƙisãsi a cikin kasassu. ɗa da ɗa kuma bãwa da bãwa, kuma mace da mace, to, wanda aka yi rangwamen wani abu gare shi daga ɗan'uwansa to a bi da alhẽri da biya zuwa gare, shi da kyautatãwa. Wancan sauƙaƙewa ne daga Ubangijinku, kuma rahama ce. To, wanda ya yi zãlunci a bãyan wancan, to, yana da azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 2:178
    And there is for you in legal retribution [saving of] life, O you [people] of understanding, that you may become righteous. <> Kuma kuna da rãyuwa a cikin ƙisãsi, yã ma'abuta hankula; tsammãninku, zã ku yi taƙawa. = --Qur'an 2:179
    Prescribed for you when death approaches [any] one of you if he leaves wealth [is that he should make] a bequest for the parents and near relatives according to what is acceptable - a duty upon the righteous. <> Kuma an wajabta, a kanku idan mutuwa ta halarci ɗayanku, idan ya bar wata dũkiya, wasiyya dõmin mahaifa da dangi bisa ga abin da aka sani; wajabce a kan mãsu taƙawa. = --Qur'an 2:180
    Then whoever alters the bequest after he has heard it - the sin is only upon those who have altered it. Indeed, Allah is Hearing and Knowing. <> To, wanda ya musanya masa a bãyan ya ji shi, to, kawai laifinsa yana a kan waɗanda suke musanya shi. Lalle ne, Allah Mai ji ne, Masani. = --Qur'an 2:181
    But if one fears from the bequeather [some] error or sin and corrects that which is between them, there is no sin upon him. Indeed, Allah is Forgiving and Merciful. <> To, wanda ya ji tsõron karkata ko kuwa wani zunubi daga mai wasiyyar, sai ya yi sulhi a tsakãninsu to bãbu laifi a kansa. Lalle ne Allah, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 2:182
    O you who have believed, decreed upon you is fasting as it was decreed upon those before you that you may become righteous - <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku, zã ku yi taƙawa, = --Qur'an 2:183
    [Fasting for] a limited number of days. So whoever among you is ill or on a journey [during them] - then an equal number of days [are to be made up]. And upon those who are able [to fast, but with hardship] - a ransom [as substitute] of feeding a poor person [each day]. And whoever volunteers excess - it is better for him. But to fast is best for you, if you only knew. <> Kwanuka ƙidãyayyu. To, wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuwa yana a kan tafiya, sai (ya biya) adadi daga wasu kwanuka na dabam. Kuma a kan waɗanda suke yin sa da wahala akwai fansa; ciyar da matalauci, sai dai wanda ya ƙãra alhẽri to, shi ne mafi alhẽri a gare shi. Kuma ku yi azumi (da wahalar) ne mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance kuna sani. = --Qur'an 2:184
    The month of Ramadhan [is that] in which was revealed the Qur'an, a guidance for the people and clear proofs of guidance and criterion. So whoever sights [the new moon of] the month, let him fast it; and whoever is ill or on a journey - then an equal number of other days. Allah intends for you ease and does not intend for you hardship and [wants] for you to complete the period and to glorify Allah for that [to] which He has guided you; and perhaps you will be grateful. <> Watan Ramalãna ne wanda aka saukar da Alƙur'ãni a cikinsa yana shiriya ga mutãne da hujjõji bayyanannu daga shiriya da rarrabẽwa. To, wanda ya halarta daga gare ku a watan, sai ya azumce shi, kuma wanda ya kasance majinyaci ko kuwa a kan tafiya, sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na dabam. Allah Yana nufin sauƙi gare ku, kuma ba Ya nufin tsanani gare ku, kuma dõmin ku cika adadin, kuma dõmin ku girmama Allah a kan Yã shiryar da ku, kuma tsammãninku, zã ku gõde. = --Qur'an 2:185
    And when My servants ask you, [O Muhammad], concerning Me - indeed I am near. I respond to the invocation of the supplicant when he calls upon Me. So let them respond to Me [by obedience] and believe in Me that they may be [rightly] guided. <> Kuma idan bãyiNa suka tambaye ka daga gare Ni, to, lalle Ni Makusanci ne. Ina karɓa kiran mai kira idan ya kirã Ni. Sabõda haka su nẽmi karɓawaTa, kuma su yi ĩmãni da Ni: tsammãninsu, su shiryu. = --Qur'an 2:186
    It has been made permissible for you the night preceding fasting to go to your wives [for sexual relations]. They are clothing for you and you are clothing for them. Allah knows that you used to deceive yourselves, so He accepted your repentance and forgave you. So now, have relations with them and seek that which Allah has decreed for you. And eat and drink until the white thread of dawn becomes distinct to you from the black thread [of night]. Then complete the fast until the sunset. And do not have relations with them as long as you are staying for worship in the mosques. These are the limits [set by] Allah, so do not approach them. Thus does Allah make clear His ordinances to the people that they may become righteous. <> An halatta a gare ku, a daren azumi, yin jima'i zuwa ga matanku sũ tufa ne a gare ku, kuma kũ tufa ne a gare su, Allah Yã sani lalle ne ku kun kasance kuna yaudarar kanku. Sabõda haka Yã karɓi tũbarku, kuma Yã yãfe muku. To, yanzu ku rungume su kuma ku nẽmi abin da Allah yã rubũta muku. Kuma ku ci kuma ku sha har sĩlĩli fari ya bayyana a gare ku daga sĩlĩli baƙi daga alfijiri, sa'an nan kuma ku cika azumi zuwa ga dare. Kuma kada ku rungume su alhãli kuna mãsu itikãfi a cikin masallãtai. Waɗancan iyãkokin Allah ne: don haka kada ku kusancesu kamar haka ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa ga mutãne: tsammãninsu, zã su yi taƙawa. = --Qur'an 2:187
    And do not consume one another's wealth unjustly or send it [in bribery] to the rulers in order that [they might aid] you [to] consume a portion of the wealth of the people in sin, while you know [it is unlawful]. <> Kada ku ci dukiyõyinku a tsakãninku da ƙarya, kuma ku sãdu da ita zuwa ga mahukunta dõmin ku ci wani yanki daga dũkiyõyin mutãne da zunubi alhãli kuwa kũ, kuna sane. = --Qur'an 2:188
    They ask you, [O Muhammad], about the new moons. Say, "They are measurements of time for the people and for Hajj." And it is not righteousness to enter houses from the back, but righteousness is [in] one who fears Allah. And enter houses from their doors. And fear Allah that you may succeed. <> Kuma suna tambayar ka daga jirajiran wata. Ka ce: "Su lõkatai ne dõmin mutãne da haji, kuma bã addini ba ne ku je wa gidãje daga bãyansu: kuma amma abin da yake addini shi ne wanda ya yi taƙawa. Kuma ku je wa gidãje daga ƙõfõfinsu, kuma ku bi Allah da taƙawa: tsammãninku, ku ci nasara. = --Qur'an 2:189
    Fight in the way of Allah those who fight you but do not transgress. Indeed. Allah does not like transgressors. <> Kuma ku yãƙi waɗanda suke yãƙinku, a cikin hanyar Allah, kuma kada ku yi tsõkana, lalle ne Allah bã Ya son mãsu tsõkana. = --Qur'an 2:190
    And kill them wherever you overtake them and expel them from wherever they have expelled you, and fitnah is worse than killing. And do not fight them at al-Masjid al- Haram until they fight you there. But if they fight you, then kill them. Such is the recompense of the disbelievers. <> Kuma ku yãƙe su inda kuka sãme su, kuma ku fitar da su daga inda suka fitar da ku. Kuma fitina ita ce mafi tsanani daga kisa. Kuma kada ku yãƙe su a wurin Masallãci Tsararre (Hurumin Makka) fãce fa idan sun yãƙe ku a cikinsa. To, idan sun yãƙe ku, sai ku yãƙe su. Kamar wancan ne sakamakon kãfirai yake. = --Qur'an 2:191
    And if they cease, then indeed, Allah is Forgiving and Merciful. <> Sa'an nan idan sun hanu, to, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 2:192
    Fight them until there is no [more] fitnah and [until] worship is [acknowledged to be] for Allah. But if they cease, then there is to be no aggression except against the oppressors. <> Kuma ku yãƙe su har ya zama wata fitina bã zã ta kasance ba, kuma addini ya zama na Allah. Sa'an nan idan sun hanu to bãbu tsõkana fãce a kan azzãlumai. = --Qur'an 2:193
    [Fighting in] the sacred month is for [aggression committed in] the sacred month, and for [all] violations is legal retribution. So whoever has assaulted you, then assault him in the same way that he has assaulted you. And fear Allah and know that Allah is with those who fear Him. <> Watan alfarma da wani watan alfarma alfarmõmi mãsu dũkar jũna ne. Sabõda haka wanda ya yi tsõkana a kanku, sai ku yi tsokana a kansa da misãlin abin da ya yi tsõkana a kanku. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Yana tãre da mãsu taƙawa. = --Qur'an 2:194
    And spend in the way of Allah and do not throw [yourselves] with your [own] hands into destruction [by refraining]. And do good; indeed, Allah loves the doers of good. <> Kuma ku ciyar a cikin hanyar Allah. Kuma kada ku jefa kanku da hannayenku, zuwa ga halaka. Kuma ku kyautata; lalle ne, Allah Yana son mãsu kyautatãwa. = --Qur'an 2:195
    And complete the Hajj and 'umrah for Allah. But if you are prevented, then [offer] what can be obtained with ease of sacrificial animals. And do not shave your heads until the sacrificial animal has reached its place of slaughter. And whoever among you is ill or has an ailment of the head [making shaving necessary must offer] a ransom of fasting [three days] or charity or sacrifice. And when you are secure, then whoever performs 'umrah [during the Hajj months] followed by Hajj [offers] what can be obtained with ease of sacrificial animals. And whoever cannot find [or afford such an animal] - then a fast of three days during Hajj and of seven when you have returned [home]. Those are ten complete [days]. This is for those whose family is not in the area of al-Masjid al-Haram. And fear Allah and know that Allah is severe in penalty. <> Kuma ku cika hajji da umra dõmin Allah. To idan an kange ku, to, ku bãyar da abin da ya sauƙaƙa na hadaya. Kuma kada ku aske kãnunku, sai hadaya ta kai wurinta. To, wanda ya kasance majinyaci daga cikinku, kõ kuwa akwai wata cũta daga kansa (ya yi aski) sai fansa (fidiya) daga azumi ko kuwa sadaka ko kuwa yanka. To, idan kuna cikin aminci to, wanda ya ji dãdi da umra zuwa haji, sai ya biya abin da ya sauƙaƙa daga hadaya, sa'an nan wanda bai sãmu ba, sai azumin yini uku a cikin haji da bakwai idan kun kõma, waɗancan gõma ne cikakku. Wancan yana ga wanda iyãlinsa ba su kasance mazaunan Masallãci Tsararre ba. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cewa Allah Mai tsananin uƙũba ne. = --Qur'an 2:196
    Hajj is [during] well-known months, so whoever has made Hajj obligatory upon himself therein [by entering the state of ihram], there is [to be for him] no sexual relations and no disobedience and no disputing during Hajj. And whatever good you do - Allah knows it. And take provisions, but indeed, the best provision is fear of Allah. And fear Me, O you of understanding. <> Hajji watanni ne sanannu. To, wanda ya yi niyyar hajji a cikinsu to bãbu jimã'i kuma bãbu fãsiƙanci, kuma bãbu jãyayya a cikin hajji. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, Allah Ya san shi. Kuma ku yi guzuri. To, mafi alhẽrin guzuri yin taƙawa. Kuma ku bi Ni da taƙawa, ya ma'abuta hankula. = --Qur'an 2:197
    There is no blame upon you for seeking bounty from your Lord [during Hajj]. But when you depart from 'Arafat, remember Allah at al- Mash'ar al-Haram. And remember Him, as He has guided you, for indeed, you were before that among those astray. <> Bãbu laifi a kanku ga ku nẽmi falala daga Ubangijinku. Sa'an nan idan kun malãlo daga Arafãt, sai ku yi ta ambatar Allah a wurin Mash'aril Harãmi kuma ku tuna Shi kamar shiriyar da Ya yi muku kuma lalle ne kun kasance a gabãninsa, haƙĩƙa, daga ɓatattu. = --Qur'an 2:198
    Then depart from the place from where [all] the people depart and ask forgiveness of Allah. Indeed, Allah is Forgiving and Merciful. <> Sa'an nan kuma ku malãlo daga inda mutãne suke malalowa. Kuma ku nemi gafara ga Allah. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 2:199
    And when you have completed your rites, remember Allah like your [previous] remembrance of your fathers or with [much] greater remembrance. And among the people is he who says, "Our Lord, give us in this world," and he will have in the Hereafter no share. <> To, idan kun ƙãre ayyukan hajji, sai ku ambaci Allah kamar ambatarku ga ubanninku, kõ kuwa mafi tsanani ga ambato. To, daga cikin mutãne akwai wanda yake cẽwa: "Ya Ubangjinmu! Ka bã mu a cikin dũniya! Kuma bã ya da wanirabo a cikin Lãhira. = --Qur'an 2:200
    But among them is he who says, "Our Lord, give us in this world [that which is] good and in the Hereafter [that which is] good and protect us from the punishment of the Fire." <> Kuma daga gare su akwai wanda yake cẽwa: "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu mai kyau a cikin dũniya da mai kyau a cikin Lãhira, kuma Ka tsare mana azãbar Wuta!" = --Qur'an 2:201
    Those will have a share of what they have earned, and Allah is swift in account. <> Waɗannan suna da rabo daga abin da suka sanã'anta; kuma Allah Mai gaggãwar sakamako da yawa ne. = --Qur'an 2:202
    And remember Allah during [specific] numbered days. Then whoever hastens [his departure] in two days - there is no sin upon him; and whoever delays [until the third] - there is no sin upon him - for him who fears Allah. And fear Allah and know that unto Him you will be gathered. <> Kuma ku ambaci Allah a cikin kwanuka ƙidayayyu. To, wanda ya yi gaggawa a cikin kwana biyu, to, bãbu laifi a kansa, kuma wanda ya jinkirta, to, bãbu laifi a kansa, ga wanda ya yi taƙawa. Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma ku sani cewa lalle ne kũ, zuwa gare Shi ake tãrã ku. = --Qur'an 2:203
    And of the people is he whose speech pleases you in worldly life, and he calls Allah to witness as to what is in his heart, yet he is the fiercest of opponents. <> Kuma akwai daga mutãne wanda maganarsa tana bã ka sha'awa a cikin rãyuwar dũniya, alhãli yanã shaidar da Allah a kan abin da yake cikin zuciyarsa, kuma shi mai tsananin husũma ne. = --Qur'an 2:204
    And when he goes away, he strives throughout the land to cause corruption therein and destroy crops and animals. And Allah does not like corruption. <> Kuma idan ya jũya sai ya yi gaggawa a cikin ƙasa dõmin ya yi ɓarna a cikinta, kuma ya halaka shũka da 'ya'yan dabbõbi. Kuma Allah bã Ya son ɓarna. = --Qur'an 2:205
    And when it is said to him, "Fear Allah," pride in the sin takes hold of him. Sufficient for him is Hellfire, and how wretched is the resting place. <> Kuma idan an ce masa: "Ka ji tsõron Allah," sai girman kai da yin zunubi ya ɗauke shi To abin da yake mai isarsa Jahannama ce. Kuma haƙĩƙa, shimfiɗa tã munana. = --Qur'an 2:206
    And of the people is he who sells himself, seeking means to the approval of Allah. And Allah is kind to [His] servants. <> Kuma akwai daga mutãne wanda yake sayar da ransa, dõmin nẽman yardar Allah: KumaAllah Mai tausayi ga bãyi ne. = --Qur'an 2:207
    O you who have believed, enter into Islam completely [and perfectly] and do not follow the footsteps of Satan. Indeed, he is to you a clear enemy. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Ku shiga cikin Musulunci gabã ɗaya; kuma kada ku bi zambiyõyin Shaiɗan; lalle ne shĩ a gare ku maƙiyine, bayyananne. = --Qur'an 2:208
    But if you deviate after clear proofs have come to you, then know that Allah is Exalted in Might and Wise. <> To, idan kun karkace daga bayan hujjõji bayyanannu sun zo muku to ku sani cẽwa lalle ne Allah, Mabuwãyi ne, Mai hikima. = --Qur'an 2:209
    Do they await but that Allah should come to them in covers of clouds and the angels [as well] and the matter is [then] decided? And to Allah [all] matters are returned. <> Shin suna jira, fãce dai Allah Ya je musu a cikin wasu inuwõyi na girgije, da malã'iku, kuma an hukunta al'amarin? Kuma zuwa ga Allah al'amurra ake mayar da su. = --Qur'an 2:210
    Ask the Children of Israel how many a sign of evidence We have given them. And whoever exchanges the favor of Allah [for disbelief] after it has come to him - then indeed, Allah is severe in penalty. <> Ka tambayi Banĩ Isrã'ila, da yawa Muka bã su daga ãyõyi bayyanannu. Kuma wanda ya musanya ni'imar Allah daga bãyan tã je masa, to, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne. = --Qur'an 2:211
    Beautified for those who disbelieve is the life of this world, and they ridicule those who believe. But those who fear Allah are above them on the Day of Resurrection. And Allah gives provision to whom He wills without account. <> An ƙawata rãyuwar dũniya ga waɗanda suka kãfirta, kuma suna izgili daga waɗanda suka yi ĩmãni, alhãli waɗanda suka yi taƙawa suna bisa gare su, a Rãnar ¡iyãma. Kuma Allah Yana azurta wanda Yake so, bã da lissãfi ba. = --Qur'an 2:212
    Mankind was [of] one religion [before their deviation]; then Allah sent the prophets as bringers of good tidings and warners and sent down with them the Scripture in truth to judge between the people concerning that in which they differed. And none differed over the Scripture except those who were given it - after the clear proofs came to them - out of jealous animosity among themselves. And Allah guided those who believed to the truth concerning that over which they had differed, by His permission. And Allah guides whom He wills to a straight path. <> Mutãne sun kasance al'umma guda. Sai Allah Ya aiki annabãwa suna mãsu bãyar da bishãra kuma mãsu gargaɗi; kuma Ya saukar da Littãfi da gaskiya tãre da su dõmin (Littãfin) ya yi hukunci a tsakãnin mutãnen a cikin abin da suka sãɓã wa jũna a cikinsa. kuma bãbu wanda ya sãɓã, a cikinsa, fãce waɗanda aka bai wa shi daga bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu dõmin zãlunci a tsakãninsu. Sai Allah Ya shiryar da waɗanda suka yi ĩmani ga abin da suka sãɓã a cikinsa daga gaskiya da izninSa. Kuma Allah Yana shiryar da wanda Yake so, zuwa ga hanya madaidaiciya. = --Qur'an 2:213
    Or do you think that you will enter Paradise while such [trial] has not yet come to you as came to those who passed on before you? They were touched by poverty and hardship and were shaken until [even their] messenger and those who believed with him said, "When is the help of Allah?" Unquestionably, the help of Allah is near. <> Ko kuna zaton ku shiga Aljanna kuma tun misãlin waɗanda suka shige daga gabãninku bai zo muku ba? Wahalõli da cũta sun shãfe su, kuma aka tsõratar da su har manzonsu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi su ce: "Yaushe taimakon Allah zai zo?" To! Lalle ne, taimakon Allah yana kusa! = --Qur'an 2:214
    They ask you, [O Muhammad], what they should spend. Say, "Whatever you spend of good is [to be] for parents and relatives and orphans and the needy and the traveler. And whatever you do of good - indeed, Allah is Knowing of it." <> Suna tambayar ka mẽne nezã su ciyar. Ka ce: Abin da kuka ciyar daga alhẽri sai ga mahaifa da mafi kusantar dangantaka da marãyu da matalauta da ɗan hanya. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, to, lalle ne, Allah gare shi Masani ne. = --Qur'an 2:215
    Fighting has been enjoined upon you while it is hateful to you. But perhaps you hate a thing and it is good for you; and perhaps you love a thing and it is bad for you. And Allah Knows, while you know not. <> An wajabta yãƙi a kanku, alhãli kuwa shi abin ƙi ne a gare ku, akwai fãtar cẽwa ku ƙi wani abu, alhãli shi ne mafi alhẽri a gare ku, kumaakwai fãtar cẽwa kuna son wani abu alhãli kuwa shi ne mafi sharri a gare ku. Kuma Allah ne Yake sani, kuma kũ ba ku sani ba. = --Qur'an 2:216
    They ask you about the sacred month - about fighting therein. Say, "Fighting therein is great [sin], but averting [people] from the way of Allah and disbelief in Him and [preventing access to] al-Masjid al-Haram and the expulsion of its people therefrom are greater [evil] in the sight of Allah. And fitnah is greater than killing." And they will continue to fight you until they turn you back from your religion if they are able. And whoever of you reverts from his religion [to disbelief] and dies while he is a disbeliever - for those, their deeds have become worthless in this world and the Hereafter, and those are the companions of the Fire, they will abide therein eternally. <> Suna tambayar ka game da Watan Alfarma: yin yãki a cikinsa. Ka ce: "Yin yãƙi a cikinsa babban zunubi ne, kuma hani daga hanyar Allah, da kuma kãfirci da Shi, da kuma da Masallaci Tsararre, da Kuma fitar da mutãnensa daga gare shi, shi ne mafi girman zunubi a wurin Allah." Kuma fitina ita ce mafi girma daga kisa. Kuma bã su gushẽwa suna yãƙinku har su mayar da ku daga barin addininku idan za su iya. Kuma wanda ya yi ridda daga gare ku ga barin addininsa har ya mutu alhãli kuwa yana kãfiri, to, waɗannan ayyukansu sun ɓãci a cikin dũniya da Lãhira. Kuma waɗannan abõkan Wuta ne, sũ a cikinta madawwama ne. = --Qur'an 2:217
    Indeed, those who have believed and those who have emigrated and fought in the cause of Allah - those expect the mercy of Allah. And Allah is Forgiving and Merciful. <> Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, da waɗanda suka yi hijira kuma suka yi jihãdi a cikin hanyar Allah waɗannan suna fãtar (sãmun) rahamar Allah kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 2:218
    They ask you about wine and gambling. Say, "In them is great sin and [yet, some] benefit for people. But their sin is greater than their benefit." And they ask you what they should spend. Say, "The excess [beyond needs]." Thus Allah makes clear to you the verses [of revelation] that you might give thought. <> Suna tambayar ka game da giya da cãcã. Ka ce: "A cikinsu akwai zunubi mai girma da wasu amfãnõni ga mutãne, kuma zunubinsu ne mafi girma daga amfaninsu." Kuma suna tambayar ka mẽne ne zã su ciyar; ka ce: "Abin da ya rage." Kamar wancan ne Allah Yake bayyanawar ãyõyi a gare ku; tsammãninku, kuna tunãni. = --Qur'an 2:219
    To this world and the Hereafter. And they ask you about orphans. Say, "Improvement for them is best. And if you mix your affairs with theirs - they are your brothers. And Allah knows the corrupter from the amender. And if Allah had willed, He could have put you in difficulty. Indeed, Allah is Exalted in Might and Wise. <> A cikin dũniya da Lãhira. Kuma suna tambayar ka game da marãyu. Ka ce: "Kyautatãwa gare su ne mafi alhẽri, kuma idan kun haɗa da su (wajen abinci), to, 'yan'uwanku ne; kuma Allah Yana sanin mai ɓãtãwa daga mai kyautatãwa. Kuma dã Allah Yã so, dã Ya tsananta muku. Lalle ne Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima. = --Qur'an 2:220
    And do not marry polytheistic women until they believe. And a believing slave woman is better than a polytheist, even though she might please you. And do not marry polytheistic men [to your women] until they believe. And a believing slave is better than a polytheist, even though he might please you. Those invite [you] to the Fire, but Allah invites to Paradise and to forgiveness, by His permission. And He makes clear His verses to the people that perhaps they may remember. <> Kuma kada ku auri mãtã mushirikai sai sun yi ĩmãni: Kuma lalle ne baiwa mũminaita ce mafi alhẽri daga ɗiya kãfira, kuma kõ da tã bã ku sha'awa. Kuma kada ku aurar wa maza mushirikai sai sun yi ĩmãni, kuma lalle ne bãwa mũmini shi ne mafi alhẽri daga da mushiriki, kuma kõ da yã bã ku sha'awa, waɗannan suna kira ne zuwa ga wuta kuma Allah Yana kira zuwa ga Aljanna da gãfara da izninsa. Kuma Yana bayyana ãyõyinsa ga mutãne; tsammãninsu suna tunãwa. = --Qur'an 2:221
    And they ask you about menstruation. Say, "It is harm, so keep away from wives during menstruation. And do not approach them until they are pure. And when they have purified themselves, then come to them from where Allah has ordained for you. Indeed, Allah loves those who are constantly repentant and loves those who purify themselves." <> Kuma suna tambayar ka game da haila Ka ce: Shi cũta ne. Sabõda haka ku nĩsanci mãta a cikin wurin haila kuma kada ku kusance su sai sun yi tsarki. To, idan sun yi wanka sai ku je musu daga inda Allah Ya umurce ku. Lalle ne Allah Yana son mãsu tũba kuma Yana son mãsu tsarkakẽwa. = --Qur'an 2:222
    Your wives are a place of sowing of seed for you, so come to your place of cultivation however you wish and put forth [righteousness] for yourselves. And fear Allah and know that you will meet Him. And give good tidings to the believers. <> Mãtanku gõnaki ne a gare ku, sabõda haka ku je wa gõnakinku yadda kuka so. Kuma ku gabãtar (da alheri) sabõda kanku, ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle nekũ mãsu haɗuwa da Shi ne. Kuma ka bãyar da bishãra ga mũminai. = --Qur'an 2:223
    And do not make [your oath by] Allah an excuse against being righteous and fearing Allah and making peace among people. And Allah is Hearing and Knowing. <> Kuma kada ku sanya Allah kambu ga rantsuwõyinku dõmin kada ku yi wani alhẽri, kuma ku yi taƙawa, kuma ku yi wani gyara tsakãnin mutãne, kuma Allah Mai jĩ ne, Masani. = --Qur'an 2:224
    Allah does not impose blame upon you for what is unintentional in your oaths, but He imposes blame upon you for what your hearts have earned. And Allah is Forgiving and Forbearing. <> Allah ba Ya kãmã ku da laifi sabõda yãsasshiya a cikin rantsuwõyinku. Kuma amma Yana kama ku sabõda abin da zukãtanku suka sanã'anta. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri. = --Qur'an 2:225
    For those who swear not to have sexual relations with their wives is a waiting time of four months, but if they return [to normal relations] - then indeed, Allah is Forgiving and Merciful. <> Ga waɗanda suke yin rantsuwa daga matansu akwai jinkirin watã huɗu. To, idan sun kõma, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 2:226
    And if they decide on divorce - then indeed, Allah is Hearing and Knowing. <> Kuma idan sun yi niyyar saki, to, lalle ne, Allah Mai ji ne, Masani. = --Qur'an 2:227
    Divorced women remain in waiting for three periods, and it is not lawful for them to conceal what Allah has created in their wombs if they believe in Allah and the Last Day. And their husbands have more right to take them back in this [period] if they want reconciliation. And due to the wives is similar to what is expected of them, according to what is reasonable. But the men have a degree over them [in responsibility and authority]. And Allah is Exalted in Might and Wise. <> Kuma mãtã waɗanda aka saki aurensu, suna jinkiri da kansu tsarki uku. Kuma bã ya halatta a gare su, su ɓõye abin da Allah Ya halitta a cikin mahaifunsu, idan sun kasance suna yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma mazan aurensu su ne mafiya haƙƙi ga mayar da su a cikin wancan, idan sun yi nufin gyãrawa. Kuma sũ mãtan suna da kamar abin da yake a kansu, yadda aka sani. Kuma maza suna da wata daraja a kansu (su mãtan). Kuma Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima. = --Qur'an 2:228
    Divorce is twice. Then, either keep [her] in an acceptable manner or release [her] with good treatment. And it is not lawful for you to take anything of what you have given them unless both fear that they will not be able to keep [within] the limits of Allah. But if you fear that they will not keep [within] the limits of Allah, then there is no blame upon either of them concerning that by which she ransoms herself. These are the limits of Allah, so do not transgress them. And whoever transgresses the limits of Allah - it is those who are the wrongdoers. <> Saki sau biyu yake, sai a riƙa da alh ẽri, ko kuwa a sallama bisa kyautatãwa. Kuma ba ya halatta a gare ku (maza) ku karɓe wani abu daga abin da kuka bã su, fãce fa idan su (ma'auran) na tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, Idan kun (danginsu) ji tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, to, bãbu laifi a kansu a cikin abin da ta yi fansa da shi. Waɗancan iyãkõkin Allah ne sabõda haka kada ku kẽtare su. Kuma wanda ya ƙẽtare iyãkõkin Allah, to waɗannan su ne azzãlumai. = --Qur'an 2:229
    And if he has divorced her [for the third time], then she is not lawful to him afterward until [after] she marries a husband other than him. And if the latter husband divorces her [or dies], there is no blame upon the woman and her former husband for returning to each other if they think that they can keep [within] the limits of Allah. These are the limits of Allah, which He makes clear to a people who know. <> Sa'an nan idan ya sake ta (na uku), to, bã ta halatta a gare shi, daga bãya, sai tã yi jima'i da wani miji waninsa. Sa'an nan idan (sãbon mijin, watau na biyu) ya sake ta, to, bãbu laifi a kansu ga su kõma wa (auren) jũna, idan sun (mijin farko da matar) yi zaton cẽwa zã su tsayar da iyãkõkin Allah, kuma waɗancan dõkõkin Allah ne Yana bayyana su ga mutãne waɗanda suke sani. = --Qur'an 2:230
    And when you divorce women and they have [nearly] fulfilled their term, either retain them according to acceptable terms or release them according to acceptable terms, and do not keep them, intending harm, to transgress [against them]. And whoever does that has certainly wronged himself. And do not take the verses of Allah in jest. And remember the favor of Allah upon you and what has been revealed to you of the Book and wisdom by which He instructs you. And fear Allah and know that Allah is Knowing of all things. <> Kuma idan kun saki mãta, sa'an nan suka isa ga ajalinsu (iddarsu), sai ku riƙe su da alhẽri ko ku sallame su da alhẽri, kuma kada ku riƙe su a kan cũtarwa dõmin ta tsawaita idda. Kuma wanda ya aikata wancan, to, haƙĩƙa, yã zãlunci kansa. Kuma kada ku riƙi ãyõyin Allah da izgili. Kuma ku tuna ni'imar Allah da abin da Ya saukar a kanku na Littãfi da hikima. Yana yi muku wa'azi da shi. Kuma ku bi Allah da takawa kuma ku sani cewa lalle ne Allah ga dukan kõme Masani ne. = --Qur'an 2:231
    And when you divorce women and they have fulfilled their term, do not prevent them from remarrying their [former] husbands if they agree among themselves on an acceptable basis. That is instructed to whoever of you believes in Allah and the Last Day. That is better for you and purer, and Allah knows and you know not. <> Kuma idan kuka saki mãta, har suka isa ga ajalinsu (iddarsu), to, kada ku (waliyyansu) hana su, su auri mazansu (da suka sake su) idan sun yarda da jũna a tsakãninsu (tsõhon miji da tsõhuwar mãta) da alhẽri. Wancan ana yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance daga gare ku yana ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Wancan ne mafi mutunci a gare ku, kuma mafi tsarki. Kuma Allah Yana sani, kuma kũ ba ku sani ba. = --Qur'an 2:232
    Mothers may breastfeed their children two complete years for whoever wishes to complete the nursing [period]. Upon the father is the mothers' provision and their clothing according to what is acceptable. No person is charged with more than his capacity. No mother should be harmed through her child, and no father through his child. And upon the [father's] heir is [a duty] like that [of the father]. And if they both desire weaning through mutual consent from both of them and consultation, there is no blame upon either of them. And if you wish to have your children nursed by a substitute, there is no blame upon you as long as you give payment according to what is acceptable. And fear Allah and know that Allah is Seeing of what you do. <> Kuma mãsu haifuwa (sakakku) suna shãyar da abin haifuwarsu shẽkara biyu cikakku ga wanda ya yi nufin ya cika shãyarwa. Kuma ciyar da su da tufãtar da su yana a kan wanda aka haifar masa da alhẽri. Bã a kallafa wa rai fãce iyãwarsa. Bã a cũtar da uwa game da ɗanta, kuma bã a cũtar da uba game da ɗansa, kuma a kan magãji akwai misãlin wancan. To, idan suka yi nufin yãye, a kan yardatayya daga gare su, da shãwartar jũna, to bãbu laifi a kansu. Kuma idan, kun yi nufin ku bãyar da ɗiyanku shãyarwa, to, bãbu laifi a kanku idan kun mĩƙa abin da kukazo da shi bisa al'ãda. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatawa, Mai gani ne. = --Qur'an 2:233
    And those who are taken in death among you and leave wives behind - they, [the wives, shall] wait four months and ten [days]. And when they have fulfilled their term, then there is no blame upon you for what they do with themselves in an acceptable manner. And Allah is [fully] Acquainted with what you do. <> Kuma waɗanda suke mutuwa daga gare ku suna barin mãtan aure, mãtan suna jinkiri da kansu wata huɗu da kwãna goma. To, idan sun isa ga ajalinsu, to, bãbu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu ga al'ãda. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne. = --Qur'an 2:234
    There is no blame upon you for that to which you [indirectly] allude concerning a proposal to women or for what you conceal within yourselves. Allah knows that you will have them in mind. But do not promise them secretly except for saying a proper saying. And do not determine to undertake a marriage contract until the decreed period reaches its end. And know that Allah knows what is within yourselves, so beware of Him. And know that Allah is Forgiving and Forbearing. <> Kuma bãbu laifi a kanku a cikin abin da kuka gitta da shi daga nẽman auren mãtãko kuwa kuka ɓõye a cikin zukatanku. Allah Ya san cẽwa lalle ne ku za ku ambata musu (shi). Kuma amma kada ku yi wa jũna alkawari da shia ɓõye, fãce dai ku faɗi magana sananniya. Kuma kada ku ƙulla niyyar daurin auren sai littãfin (idda) ya kai ga ajalinsa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne Allah Yana sanin abin da yake cikin zukatanku, sabõda haka ku ji tsõronsa. Kuma ku sani cewa Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri. = --Qur'an 2:235
    There is no blame upon you if you divorce women you have not touched nor specified for them an obligation. But give them [a gift of] compensation - the wealthy according to his capability and the poor according to his capability - a provision according to what is acceptable, a duty upon the doers of good. <> Kuma bãbu laifi a kanku idan kun saki mãtã matuƙar ba ku shãfe su ba, kuma ba ku yanka musu sadãki ba. Kuma ku bã su kyautar dãɗaɗãwa, a kan mawadãci gwargwadonsa, kuma a kan maƙuntaci gwargwadonsa; dõmin dãɗaɗrwa, da alhẽri, wãjibi ne a kan mãsu kyautatãwa. = --Qur'an 2:236
    And if you divorce them before you have touched them and you have already specified for them an obligation, then [give] half of what you specified - unless they forego the right or the one in whose hand is the marriage contract foregoes it. And to forego it is nearer to righteousness. And do not forget graciousness between you. Indeed Allah, of whatever you do, is Seeing. <> Kuma idan kuka sake su daga gabãnin ku shãfe su, alhãli kuwa kun yanka musu sadãki, to, rabin abin da kuka yanka fãce idan sun yãfe, kõ wanda ɗaurin auren yake ga hannunsa ya yãfe. Kuma ku yãfe ɗin ne mafi kusa da taƙawa. Kuma kada ku manta da falala a tsakãninku. Lalle ne Allah ga abin da kuke aikatãwa Mai gani ne. = --Qur'an 2:237
    Maintain with care the [obligatory] prayers and [in particular] the middle prayer and stand before Allah, devoutly obedient. <> Ku tsare lõkatai a kan sallõli da salla mafificiya. Kuma ku tsayu kuna mãsu ƙanƙan da kai ga Allah. = --Qur'an 2:238
    And if you fear [an enemy, then pray] on foot or riding. But when you are secure, then remember Allah [in prayer], as He has taught you that which you did not [previously] know. <> To, idan kun ji tsõro, to (ku dai yi salla gwargwadon hali) da tafiya ƙasa kõ kuwa a kan dabbobi. Sa'an nan idan kun amince sai ku ambaci Allah, kamar yadda Ya nũna muku abin da ba ku kasance kuna sani ba. = --Qur'an 2:239
    And those who are taken in death among you and leave wives behind - for their wives is a bequest: maintenance for one year without turning [them] out. But if they leave [of their own accord], then there is no blame upon you for what they do with themselves in an acceptable way. And Allah is Exalted in Might and Wise. <> Kuma waɗanda suke mutuwa daga gare ku, alhãli suna barin mãtan aure, wasiyya ga mãtan aurensu da dãɗaɗãwa zuwa ga shekara guda bãbu fitarwa, to, idan sun fita to bãbu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu daga abin da aka sani, kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima. = --Qur'an 2:240
    And for divorced women is a provision according to what is acceptable - a duty upon the righteous. <> Kuma waɗanda aka saki suna da dãɗaɗãwa gwargwadon hãli, wajabce a kan mãsu taƙawa. = --Qur'an 2:241
    Thus does Allah make clear to you His verses that you might use reason. <> Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ãyõyinSa; tsammãninku, kuna hankalta. = --Qur'an 2:242
    Have you not considered those who left their homes in many thousands, fearing death? Allah said to them, "Die"; then He restored them to life. And Allah is full of bounty to the people, but most of the people do not show gratitude. <> Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suka fita daga gidãjensu, alhãli kuwa sũ dubbai ne, dõmin tsõron mutuwa? Sai Allah Ya ce musu: "Ku mutu." Sa'an nan kuma Ya rãyar da su, lalle ne Allah, haƙĩƙa Ma'abũcin falala a kan mutãne ne, kuma amma mafi yawan mutãne bã su gõdẽwa. = --Qur'an 2:243
    And fight in the cause of Allah and know that Allah is Hearing and Knowing. <> Kuma ku yi yãƙi a cikin hanyar Allah, kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Mai jĩ ne, Masani. = --Qur'an 2:244
    Who is it that would loan Allah a goodly loan so He may multiply it for him many times over? And it is Allah who withholds and grants abundance, and to Him you will be returned. <> Wãne ne wanda zai bai wa Allah rance, rance mai kyau, dõmin Ya riɓanya masa, riɓanyãwa mai yawa? Kuma Allah Shi ne ke damƙewa, kuma yana shimfiɗawa, kuma zuwa a gare Shi ake mayar da ku. = --Qur'an 2:245
    Have you not considered the assembly of the Children of Israel after [the time of] Moses when they said to a prophet of theirs, "Send to us a king, and we will fight in the way of Allah "? He said, "Would you perhaps refrain from fighting if fighting was prescribed for you?" They said, "And why should we not fight in the cause of Allah when we have been driven out from our homes and from our children?" But when fighting was prescribed for them, they turned away, except for a few of them. And Allah is Knowing of the wrongdoers. <> Shin, ba ka gani ba zuwa ga wasu mashãwarta daga Bani Isrã'ĩla daga bãyan Mũsã, a lõkacinda suka ce ga wani annabi nãsu: "Naɗã mana sarki, mu yi yãƙi a cikin hanyar Allah." Ya ce: "Ashe, akwai tsammãninku idan an wajabta yãƙi a kanku cẽwa bã zã ku yi yãƙin ba?" Suka ce: "Kuma mẽne ne a gare mu, ba zã mu yi yãƙi ba, a cikin hanyar Allah, alhãli kuwa, haƙiƙa, an fitar da mu daga gidãjenmu da ɗiyanmu?" To, a lõkacin da aka wajabta yãƙin a kansu, suka jũya, sai kaɗan daga gare su. Kuma Allah Masani ne ga azzãlumai. = --Qur'an 2:246
    And their prophet said to them, "Indeed, Allah has sent to you Saul as a king." They said, "How can he have kingship over us while we are more worthy of kingship than him and he has not been given any measure of wealth?" He said, "Indeed, Allah has chosen him over you and has increased him abundantly in knowledge and stature. And Allah gives His sovereignty to whom He wills. And Allah is all-Encompassing [in favor] and Knowing." <> Kuma annabinsu ya ce musu: "Lalle ne, Allah ya naɗa muku ¦ãlũta ya zama sarki." Suka ce: "Yãya ne sarauta zã ta kasance a gare shi, a kanmu, alhãli kuwa mũ ne mafi cancanta da sarauta daga gare shi, kuma ba a bã shi wata wadata ba daga dũkiya?" Ya ce: "Lalle ne, Allah Yã zãɓe shi a kanku, kuma Ya ƙãra masa yalwa a cikin ilmi da jiki. Kuma Allah Yana bãyar da mulkinSa ga wanda Yake so, kuma Allah Mawadaci ne, Masani. = --Qur'an 2:247
    And their prophet said to them, "Indeed, a sign of his kingship is that the chest will come to you in which is assurance from your Lord and a remnant of what the family of Moses and the family of Aaron had left, carried by the angels. Indeed in that is a sign for you, if you are believers." <> Kuma annabinsu ya ce musu: "Lalle ne alãmar mulkinSa ita ce akwatin nan ya zo muku, a cikinsa akwai natsuwa daga Ubangijinku da sauran kaya daga abin da Gidan Mũsã da Gidan Hãrũna suka bari malã'iku suna ɗaukarsa. Lalle ne a cikin wancan akwai alãma a gare ku (ta naɗin ¦ãlũta daga Allah ne) idan kun kasance mãsu ĩmãni." = --Qur'an 2:248
    And when Saul went forth with the soldiers, he said, "Indeed, Allah will be testing you with a river. So whoever drinks from it is not of me, and whoever does not taste it is indeed of me, excepting one who takes [from it] in the hollow of his hand." But they drank from it, except a [very] few of them. Then when he had crossed it along with those who believed with him, they said, "There is no power for us today against Goliath and his soldiers." But those who were certain that they would meet Allah said, "How many a small company has overcome a large company by permission of Allah. And Allah is with the patient." <> A lõkacin da ¦ãlũta ya fita da rundunõnin, ya ce: "Lalle ne Allah Mai jarrabarku ne da wani kõgi. To, wanda ya sha daga gare shi, to, ba shi daga gare ni, kuma wanda bai ɗanɗane shi ba to lalle ne shi, yana daga gare ni, fãce, wanda ya kamfata, kamfata guda da hannunsa." Sai suka sha daga gare shi, fãce kaɗan daga gare su. To, a lõkacin da (¦ãlũta) ya ƙẽtare shi, shi da waɗanda suka yi ĩmani tãre da shi, (sai waɗanda suka sha) suka ce: "Babu ĩko a gare mu yau game da Jãlũta da rundunõninsa."Waɗanda suka tabbata cẽwa lalle sũ mãsu gamuwa ne da Allah, suka ce: "Da yawa ƙungiya kaɗan ta rinjayi wata ƙungiya mai yawa da iznin Allah, kuma Allah Yana tãre da mãsu haƙuri." = --Qur'an 2:249
    And when they went forth to [face] Goliath and his soldiers, they said, "Our Lord, pour upon us patience and plant firmly our feet and give us victory over the disbelieving people." <> Kuma a lõkacin da suka bayyana ga Jãlũta da rundunoninsa, suka ce: "Yã Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu kuma Ka tabbatar da sãwayenmu, kuma Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai." = --Qur'an 2:250
    So they defeated them by permission of Allah, and David killed Goliath, and Allah gave him the kingship and prophethood and taught him from that which He willed. And if it were not for Allah checking [some] people by means of others, the earth would have been corrupted, but Allah is full of bounty to the worlds. <> Sai suka karya su da iznin Allah. Kuma Dãwudu ya kashe Jãlũta, kuma Allah Ya bã shi mulki da hikima kuma Ya sanar da shi daga abin da Yake so. Kuma bã dõmin tunkuɗẽwar Allah ga mutãne sãshensu da sãshe ba lalle ne dã ƙasa tã ɓãci; kuma amma Allah Ma'abũcin falala ne a kan tãlikai. = --Qur'an 2:251
    These are the verses of Allah which We recite to you, [O Muhammad], in truth. And indeed, you are from among the messengers. <> Waɗancan ayõyin Allah ne: Muna karanta su a kanka da gaskiya: Kuma lalle ne kai, hakĩka, kana daga manzanni. = --Qur'an 2:252
    Those messengers - some of them We caused to exceed others. Among them were those to whom Allah spoke, and He raised some of them in degree. And We gave Jesus, the Son of Mary, clear proofs, and We supported him with the Pure Spirit. If Allah had willed, those [generations] succeeding them would not have fought each other after the clear proofs had come to them. But they differed, and some of them believed and some of them disbelieved. And if Allah had willed, they would not have fought each other, but Allah does what He intends. <> Waɗancan manzannin Mun fĩfĩta sãshensu a kan sãshe: Daga cikinsu akwai wanda Allah Ya yi masa magana; kuma Ya ɗaukaka sãshensu da darajõji; kuma Muka bai wa Ĩsã dan Maryama hujjõji bayyanannu, kuma Muka ƙarfafã shi da Rũhi mai tsarki. Kuma dã Allah Yã so dã waɗanda suke daga bãyansu, bã zã su yi yãƙi ba, daga bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu. Kuma amma sun sãɓa wa jũna, sabõda haka daga cikinsu akwai wanda ya yi ĩmãni, kuma daga cikin su akwai wanda ya kãfirta. Kuma dã Allah Yã so dã bã zã su yãƙi jũna ba, kuma amma Allah Yana aikata abin da Yake nufi. = --Qur'an 2:253
    O you who have believed, spend from that which We have provided for you before there comes a Day in which there is no exchange and no friendship and no intercession. And the disbelievers - they are the wrongdoers. <> Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ciyar daga abin da Muka azurta ku daga gabãnin wani yini ya zo bãbu ciniki a cikinsa kuma bãbu abũta, kuma bãbu cẽto, kuma kãfirai sũ ne azzãlumai. = --Qur'an 2:254
    Allah - there is no deity except Him, the Ever-Living, the Sustainer of [all] existence. Neither drowsiness overtakes Him nor sleep. To Him belongs whatever is in the heavens and whatever is on the earth. Who is it that can intercede with Him except by His permission? He knows what is [presently] before them and what will be after them, and they encompass not a thing of His knowledge except for what He wills. His Kursi extends over the heavens and the earth, and their preservation tires Him not. And He is the Most High, the Most Great. <> Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Mai tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wane ne wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma. = --Qur'an 2:255
    There shall be no compulsion in [acceptance of] the religion. The right course has become clear from the wrong. So whoever disbelieves in Taghut and believes in Allah has grasped the most trustworthy handhold with no break in it. And Allah is Hearing and Knowing. <> Bãbu tĩlastãwa a cikin addini, haƙĩƙa shiriya tã bayyana daga ɓata; Sabõda haka wanda ya kãfirta da ¦ãgũta kuma ya yi ĩmãni da Allah, to, haƙĩƙa, yã yi riƙo ga igiya amintacciya, bãbu yankẽwa agare ta. Kuma Allah Mai ji ne, Masani. = --Qur'an 2:256
    Allah is the ally of those who believe. He brings them out from darknesses into the light. And those who disbelieve - their allies are Taghut. They take them out of the light into darknesses. Those are the companions of the Fire; they will abide eternally therein. <> Allah Shi ne Masõyin waɗanda suka yi ĩmãni; Yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske, kuma waɗanda suka kãfirta, masõyansu ¦ãgũtu ne; suna fitar da su daga haske zuwa ga duffai. Waɗannan abokan Wuta ne, sũ a cikinta madawwama ne. = --Qur'an 2:257
    Have you not considered the one who argued with Abraham about his Lord [merely] because Allah had given him kingship? When Abraham said, "My Lord is the one who gives life and causes death," he said, "I give life and cause death." Abraham said, "Indeed, Allah brings up the sun from the east, so bring it up from the west." So the disbeliever was overwhelmed [by astonishment], and Allah does not guide the wrongdoing people. <> Shin, ba ka gani ba zuwa ga wanda ya yi hujjatayya da Ibrãhĩm a cikin (al'amarin) Ubangijinsa dõmin Allah Yã bã shi mulki, a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ubangijina Shi ne Wanda Yake rãyawa kuma Yana matarwa." Ya ce: "Nĩ ina rãyarwa kuma ina matarwa." Ibrãhĩm ya ce: "To, lalle ne Allah Yana zuwa da rana daga gabas: To, ka zo da ita daga yamma." Sai aka ɗimautar da wanda yakãfirta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne azzãlumai. = --Qur'an 2:258
    Or [consider such an example] as the one who passed by a township which had fallen into ruin. He said, "How will Allah bring this to life after its death?" So Allah caused him to die for a hundred years; then He revived him. He said, "How long have you remained?" The man said, "I have remained a day or part of a day." He said, "Rather, you have remained one hundred years. Look at your food and your drink; it has not changed with time. And look at your donkey; and We will make you a sign for the people. And look at the bones [of this donkey] - how We raise them and then We cover them with flesh." And when it became clear to him, he said, "I know that Allah is over all things competent." <> Kõ kuwa wanda ya shũɗe a kan wata alƙarya, alhãli kuwa tana wõfintacciya a kan gadãjen rẽsunanta. Ya ce: "Yaya Allah zai rãyar da wannan a bãyan mutuwarta." Sai Allah Ya matar da shi, shẽkara ɗari; sa'an nankuma ya tãyar da shi. Ya ce: "Nawa ka zauna?" Ya ce: "Na zauna yini ɗaya ko kuwa rabin yini." Ya ce: "A'a kã zauna shẽkara ɗari." To, ka dũba zuwa ga abincinka, da abin shanka, (kõwanensu) bai sãke ba, kuma ka dũba zuwa ga jãkinka, kuma dõmin Mu sanya ka wata ãyã ga mutãne. Kuma ka duba zuwa ga ƙasũsuwa yadda Muke mõtsarda su sa'an nan kuma Mu tufãtar da su, da nãma", To, a lõkacin da (abin) ya bayyana a gare shi, ya ce: "Ina sanin cẽwa lalle Allah a kan dukan kõme Mai ĩkõn yi ne." = --Qur'an 2:259
    And [mention] when Abraham said, "My Lord, show me how You give life to the dead." [Allah] said, "Have you not believed?" He said, "Yes, but [I ask] only that my heart may be satisfied." [Allah] said, "Take four birds and commit them to yourself. Then [after slaughtering them] put on each hill a portion of them; then call them - they will come [flying] to you in haste. And know that Allah is Exalted in Might and Wise." <> Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ya Ubangijina! Ka nũna mini yadda Kake rãyar da matattu." Ya ce: "Shin, kuma ba ka yi ĩmãni ba?" Ya ce: "Na'am! Kuma amma dõmin zũciyãta, ta natsu." Ya ce: "To ka riƙi huɗu daga tsuntsãye, ka karkatar da su zuwa gare ka, ka yanka su, sa'an nan kuma ka sanya juzu'i daga gare su a kan kõwane dũtse, sa'an nan kuma ka kira su zã su zo maka gudãne. Kuma ka sani cẽwa lalle Allah Mabuwãyi ne, Masani." = --Qur'an 2:260
    The example of those who spend their wealth in the way of Allah is like a seed [of grain] which grows seven spikes; in each spike is a hundred grains. And Allah multiplies [His reward] for whom He wills. And Allah is all-Encompassing and Knowing. <> Sifar waɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu a cikin hanyar Allah, kamar sifar ƙwãyã ce wadda ta tsirar da zangarniya bakwai, a cikin kõwace zangarniya akwai ƙwãya ɗari. Kuma Allah Yana riɓinyawa ga wanda Ya so. Kuma Allah Mawadãci ne, Masani. = --Qur'an 2:261
    Those who spend their wealth in the way of Allah and then do not follow up what they have spent with reminders [of it] or [other] injury will have their reward with their Lord, and there will be no fear concerning them, nor will they grieve. <> Waɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu a cikin hanyar Allah, sa'an nan kuma bã su biyar wa abin da suka ciyar ɗin da gõri, ko cũta, suna da sakamakonsu a wurin ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba. = --Qur'an 2:262
    Kind speech and forgiveness are better than charity followed by injury. And Allah is Free of need and Forbearing. <> Magana mai kyau da gãfartawa su ne mafi alhẽri daga sadaka wadda wata cũtarwa take biyar ta. Kuma Allah Wadatacce ne, Mai haƙuri. = --Qur'an 2:263
    O you who have believed, do not invalidate your charities with reminders or injury as does one who spends his wealth [only] to be seen by the people and does not believe in Allah and the Last Day. His example is like that of a [large] smooth stone upon which is dust and is hit by a downpour that leaves it bare. They are unable [to keep] anything of what they have earned. And Allah does not guide the disbelieving people. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ɓãta sadakõkinku da gõri da cũtarwa, kamar wanda yake ciyar da dũkiyarsa dõmin nũna wa mutãne, kuma bã ya yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. To, abin da yake misãlinsa, kamar falalen dũtse ne, a kansa akwai turɓãya, sai wãbilin hadari ya sãme shi, sai ya bar shi ƙanƙara. Bã su iya amfani da kõme daga abin da suka sanã'anta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne kãfirai. = --Qur'an 2:264
    And the example of those who spend their wealth seeking means to the approval of Allah and assuring [reward for] themselves is like a garden on high ground which is hit by a downpour - so it yields its fruits in double. And [even] if it is not hit by a downpour, then a drizzle [is sufficient]. And Allah, of what you do, is Seeing. <> Kuma sifar waɗanda suke ciyar da dũkiyarsu dõmin nẽman yardõjin Allah, kuma da tabbatarwa daga kansu, kamar misãlin lambu ne a jigãwa wadda wãbilin hadari ya sãmu, sai ta bãyar da amfãninta ninki biyu To, idan wãbili bai sãme ta ba, sai yayyafi (ya ishe ta). Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Mai gani ne. = --Qur'an 2:265
    Would one of you like to have a garden of palm trees and grapevines underneath which rivers flow in which he has from every fruit? But he is afflicted with old age and has weak offspring, and it is hit by a whirlwind containing fire and is burned. Thus does Allah make clear to you [His] verses that you might give thought. <> Shin ɗayanku nã son cẽwa wani lambu ya kasance a gare shi daga dabĩnai da inabõbi' marẽmari suna gudãna daga ƙarƙashinsa, yana da, a cikinsa daga kõwane 'ya'yan itãce, kuma tsũfa ya sãme shi, alhãli kuwa yana da zũriyya masu rauni sai gũguwa wadda take a cikinta akwai wuta, ta sãme shi, har ta ƙõne? Kamar wancan ne Allah Yana bayyanãwar ãyõyi a gare ku, tsammãninku kuna tunãni. = --Qur'an 2:266
    O you who have believed, spend from the good things which you have earned and from that which We have produced for you from the earth. And do not aim toward the defective therefrom, spending [from that] while you would not take it [yourself] except with closed eyes. And know that Allah is Free of need and Praiseworthy. <> Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ciyar daga mai kyaun abin da kuka sanã'anta, kuma daga abin da Muka fitar sabõda ku daga ƙasa, kuma kada ku yi nufin mummuna ya zama daga gare shi ne kuke ciyarwa, alhãli kuwa ba ku zama mãsu karɓarsa ba fãce kun runtse ido a cikinsa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Mawadãci ne, Gõdadde. = --Qur'an 2:267
    Satan threatens you with poverty and orders you to immorality, while Allah promises you forgiveness from Him and bounty. And Allah is all-Encompassing and Knowing. <> Shaiɗan yana yi muku alƙawarin talauci, kuma yana umurnin ku da alfasha, kuma Allah Yana yi muku alƙawarin gãfara daga gare shi da ƙãri, kuma Allah Mawadãci ne, Masani. = --Qur'an 2:268
    He gives wisdom to whom He wills, and whoever has been given wisdom has certainly been given much good. And none will remember except those of understanding. <> Yana bãyar da hikima (ga fahimtar gaskiyar abubuwa) ga wanda Yake so. Kuma wanda aka bai wa hikima to lalle ne an bã shi alhẽri mai yawa. Kuma bãbu mai tunãni fãce ma'abuta hankula. = --Qur'an 2:269
    And whatever you spend of expenditures or make of vows - indeed, Allah knows of it. And for the wrongdoers there are no helpers. <> Kuma abin da kuka ciyar daga ciyarwa, kõ kuka cika alwãshi daga wani bãkance, to, lalle ne, Allah Yana sanin sa. Kuma azzãlumai bã su da wasu mataimaka. = --Qur'an 2:270
    If you disclose your charitable expenditures, they are good; but if you conceal them and give them to the poor, it is better for you, and He will remove from you some of your misdeeds [thereby]. And Allah, with what you do, is [fully] Acquainted. <> Idan kun nũna sadakõki to, yana da kyau ƙwarai kuma idan kuka ɓõye su kuma kuka je da su ga matalauta, to shi ne mafi alhẽri a gareku, kuma Yana kankarẽwa, daga barinku, daga miyãgun ayyukanku. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne. = --Qur'an 2:271
    Not upon you, [O Muhammad], is [responsibility for] their guidance, but Allah guides whom He wills. And whatever good you [believers] spend is for yourselves, and you do not spend except seeking the countenance of Allah. And whatever you spend of good - it will be fully repaid to you, and you will not be wronged. <> Shiryar da su bã ya a kanka, kuma amma Allah Shi ne Yake shiryar da wanda Yake so, kuma abin da kuka ciyar daga alhẽri, to, dõmin kanku ne, kuma bã ku ciyarwa, fãce dõmin nẽman yardar Allah, kuma abin da kuke ciyarwa daga alhẽri zã a cika lãdarsa zuwa gare ku, alhãli kuwa kũ bã a zãluntarku. = --Qur'an 2:272
    [Charity is] for the poor who have been restricted for the cause of Allah, unable to move about in the land. An ignorant [person] would think them self-sufficient because of their restraint, but you will know them by their [characteristic] sign. They do not ask people persistently [or at all]. And whatever you spend of good - indeed, Allah is Knowing of it. <> (Ciyarwar a yĩ ta) ga matalautan nan waɗanda aka tsare a cikin hanyar Allah, ba su iya tafiyar fatauci a cikin ƙasa, jãhilin hãlinsu yana zaton su wadãtattu sabõda kãmun kai kana sanin su da alãmarsu, ba su rõƙon mutãne da nãcẽwa. Kuma abin da kuka ciyar daga alhẽri, to, lalle Allah gare shi Masani ne. = --Qur'an 2:273
    Those who spend their wealth [in Allah 's way] by night and by day, secretly and publicly - they will have their reward with their Lord. And no fear will there be concerning them, nor will they grieve. <> Waɗanda suke ciyar da dukiyõyinsu, a dare da yini, ɓõye da bayyane, to suna da sakamakonsu a wurin Ubangijinsu. Kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba. = --Qur'an 2:274
    Those who consume interest cannot stand [on the Day of Resurrection] except as one stands who is being beaten by Satan into insanity. That is because they say, "Trade is [just] like interest." But Allah has permitted trade and has forbidden interest. So whoever has received an admonition from his Lord and desists may have what is past, and his affair rests with Allah. But whoever returns to [dealing in interest or usury] - those are the companions of the Fire; they will abide eternally therein. <> Wadanda suke cin ribã ba su tashi, fãce kamar yadda wanda da Shaiɗan yake ɗimautarwa daga shafa yake tashi. Wancan, dõmin lalle ne sun ce: "Ciniki kamar riba yake."Kuma Allah Ya halatta ciniki kuma Ya haramta riba. To, wanda wa'azi daga Ubangijinsa, ya je masa, sa'an nan ya hanu, to yana da abin da ya shige, kuma al'amarinsa (ana wakkala shi) zuwa ga Allah. Kuma wanda ya kõma, to, waɗannan sũ ne abõkan Wuta, sũ a cikinta madawwama ne. = --Qur'an 2:275
    Allah destroys interest and gives increase for charities. And Allah does not like every sinning disbeliever. <> Allah Yana shãfe albarkar riba, kuma Yana ƙãra sadakõki. Kuma Allah bã Ya son dukan mai yawan kãfirci, mai zunubi. = --Qur'an 2:276
    Indeed, those who believe and do righteous deeds and establish prayer and give zakah will have their reward with their Lord, and there will be no fear concerning them, nor will they grieve. <> Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka, suna da sakamakonsu a wurin Ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba. = --Qur'an 2:277
    O you who have believed, fear Allah and give up what remains [due to you] of interest, if you should be believers. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma ku bar abin da ya rage daga riba, idan kun kasance mãsu ĩmãni. = --Qur'an 2:278
    And if you do not, then be informed of a war [against you] from Allah and His Messenger. But if you repent, you may have your principal - [thus] you do no wrong, nor are you wronged. <> To, idan ba ku aikata ba to, ku sani fa da akwai yãƙi daga Allah da ManzonSa. Kuma idan kun tũba to kuna da asalin dũkiyõyinku, bã ku zãlunta, kuma bã a zãluntar ku. = --Qur'an 2:279
    And if someone is in hardship, then [let there be] postponement until [a time of] ease. But if you give [from your right as] charity, then it is better for you, if you only knew. <> Kuma idan ma'abucin wahala ya kasance (mawahalci) to, jinkirtãwa ake yi zuwa ga sauƙin al'amarinsa, kuma dã kun yi sadaka, shi ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kuna sani. = --Qur'an 2:280
    And fear a Day when you will be returned to Allah. Then every soul will be compensated for what it earned, and they will not be treated unjustly. <> Kuma ku ji tsõron wani yini wanda ake mayar da ku a cikinsa zuwa ga Allah, sa'an nan kuma a cika wa kõwane rai abin da ya sanã'anta, kuma sũ bã a zãluntar su. = --Qur'an 2:281
    O you who have believed, when you contract a debt for a specified term, write it down. And let a scribe write [it] between you in justice. Let no scribe refuse to write as Allah has taught him. So let him write and let the one who has the obligation dictate. And let him fear Allah, his Lord, and not leave anything out of it. But if the one who has the obligation is of limited understanding or weak or unable to dictate himself, then let his guardian dictate in justice. And bring to witness two witnesses from among your men. And if there are not two men [available], then a man and two women from those whom you accept as witnesses - so that if one of the women errs, then the other can remind her. And let not the witnesses refuse when they are called upon. And do not be [too] weary to write it, whether it is small or large, for its [specified] term. That is more just in the sight of Allah and stronger as evidence and more likely to prevent doubt between you, except when it is an immediate transaction which you conduct among yourselves. For [then] there is no blame upon you if you do not write it. And take witnesses when you conclude a contract. Let no scribe be harmed or any witness. For if you do so, indeed, it is [grave] disobedience in you. And fear Allah. And Allah teaches you. And Allah is Knowing of all things. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi mu'ãmalar bãyar da bãshi zuwa ga wani ajali ambatacce, sai ku rubũta shi. Kuma wani marubuci ya yi rubũtu a tsakaninku da ãdalci. Kuma kada marubũci ya ki rubũtãwa, kamar yadda Allah Ya sanar da shi, sai ya rubũta. Kuma wanda bãshin yake a kansa sai ya yi shibta, kuma ya ji tsõron Allah, Ubangijinsa, da taƙawa, kuma kada ya rage wani abu daga gare shi. To, idan wanda bãshin yake a kansa yã kasance wãwã ne kõ kuwa rarrauna, kõ kuwa shi bã ya iya shibta, to, sai waliyyinsa ya yi shibtar da ãdalci. Kuma ku shaidar da shaidu biyu daga mazanku, to, idan ba su zama maza biyu ba, to, namiji guda da mãtã biyu, daga waɗanda kuke yarda da su daga shaidun dõmin mantuwar ɗayansu, sai gudarsu ta mazãkũtar da ɗayar. Kuma kada shaidun su ƙi, idan an kira su. Kuma kada ku ƙõsa ga rubũta shi, ƙarami ya kasance kõ babba, zuwa ajalinsa. Wancan ne mafi ãdalci a wurin Allah kuma mafi tsayuwa ga shaida, kuma mafi kusa ga rashin shakkarku. Sai idan ya kasance fatauci ne halartacce wanda kuke gẽwayarwa da shi hannu da hannu a tsakãninku to bãbu laifi a kanku, ya zama ba ku rubũta shi ba. Kuma ku shaidar idan kun yi sayayya. Kuma kada a wahalarda marubuci, kuma kada a wahalar da shaidu kuma idan kun aikata to, lalle ne, shi fãsiƙanci ne game da ku. Kumaku bi Allah da takƙawa, kuma Allah Ya sanar da ku. Kuma Allah ga dukan kõme Masani ne. = --Qur'an 2:282
    And if you are on a journey and cannot find a scribe, then a security deposit [should be] taken. And if one of you entrusts another, then let him who is entrusted discharge his trust [faithfully] and let him fear Allah, his Lord. And do not conceal testimony, for whoever conceals it - his heart is indeed sinful, and Allah is Knowing of what you do. <> Kuma idan kun kasance a kan tafiya, kuma ba ku sami marubũci ba, to, a bãyar da jingina karɓaɓɓiya (ga hannu). To, idan sãshenku ya amince wa sãshe, to, wanda aka amincẽ wannan sai ya bãyar da amãnarsa, kuma ya bi Allah, Ubangijinsa, da taƙawa. Kuma kada ku ɓõye shaida, kuma wanda ya ɓõye ta, to, shi mai zunubin zũciyarsa ne. KumaAllah ga abin da kuke aikatãwa Masani ne. = --Qur'an 2:283
    To Allah belongs whatever is in the heavens and whatever is in the earth. Whether you show what is within yourselves or conceal it, Allah will bring you to account for it. Then He will forgive whom He wills and punish whom He wills, and Allah is over all things competent. <> Allah ne, da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, kuma idan kun bayyana abin da yake a cikin zukatanku (na shaida), ko kuka ɓõye shi, Allah zai bincike ku da shi, sa'an nan Ya yi gãfara ga wanda Yake so, kuma Ya azabta wanda Yake so. Kuma Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne. = --Qur'an 2:284
    The Messenger has believed in what was revealed to him from his Lord, and [so have] the believers. All of them have believed in Allah and His angels and His books and His messengers, [saying], "We make no distinction between any of His messengers." And they say, "We hear and we obey. [We seek] Your forgiveness, our Lord, and to You is the [final] destination." <> Manzon Allah yã yi ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare shi daga Ubangijinsa, da mũminai. Kõwanensu yã yi ĩmãni da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da manzanninSa. Bã mu rarrabẽwa a tsakãnin daya daga manzanninSa. Kuma (mũminai) suka ce: "Mun ji kuma mun yi dã'a; (Muna nẽman) gãfararKa, yã Ubangijinmu, kuma zuwa a gare Ka makõma take " = --Qur'an 2:285
    Allah does not charge a soul except [with that within] its capacity. It will have [the consequence of] what [good] it has gained, and it will bear [the consequence of] what [evil] it has earned. "Our Lord, do not impose blame upon us if we have forgotten or erred. Our Lord, and lay not upon us a burden like that which You laid upon those before us. Our Lord, and burden us not with that which we have no ability to bear. And pardon us; and forgive us; and have mercy upon us. You are our protector, so give us victory over the disbelieving people." <> Allah ba Ya kallafa wa rai fãce ikon yinsa, yana da lãdar abin da ya tsirfanta, kuma a kansa akwai zunubin abin da ya yi ta aikatãwa: "Yã Ubangijinmu! Kada Ka kãmã mu, idan mun yi mantuwa, ko kuma mun yi kuskure. Yã Ubangijinmu! Kuma kada Ka aza nauyi a kanmu, kamar yadda Ka aza shi a kan waɗanda suke a gabãninmu. Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanya mu ɗaukar abin da bãbu ĩko gare mu da shi. Kuma Ka yãfe daga gare mu, kuma Ka gãfarta mana, kuma Ka yi jin ƙai gare mu. Kai ne Majibincinmu, sabõda haka Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai." = --Qur'an 2:286
    Alif, Lam, Meem. <> A. L̃. M̃. = --Qur'an 3:1
    Allah - there is no deity except Him, the Ever-Living, the Sustainer of existence. <> Allah, bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Rãyayye Mai tsayuwa da kõme. = --Qur'an 3:2
    He has sent down upon you, [O Muhammad], the Book in truth, confirming what was before it. And He revealed the Torah and the Gospel. <> Yã sassaukar da Littãfi a gare ka da gaskiya, yana mai gaskatãwa ga abin da ke gaba gare shi, kuma Allah Yã saukar da Attaura da Linjĩlã. = --Qur'an 3:3
    Before, as guidance for the people. And He revealed the Qur'an. Indeed, those who disbelieve in the verses of Allah will have a severe punishment, and Allah is exalted in Might, the Owner of Retribution. <> A gabãni, suna shiryar da mutãne, kuma Ya saukar da littattafai mãsu rarrabẽwa. Lalle ne waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah, suna da azãba mai tsanani. Kuma Allah Mabuwayi ne, Ma'abucin azãbar rãmuwa. = --Qur'an 3:4
    Indeed, from Allah nothing is hidden in the earth nor in the heaven. <> Lalle ne, Allah bãbu wani abin da ke ɓõyuwa gare Shi a cikin ƙasa, kuma bãbu a cikin sama. = --Qur'an 3:5
    It is He who forms you in the wombs however He wills. There is no deity except Him, the Exalted in Might, the Wise. <> Shi ne wanda Yake suranta ku a cikin mahaifu yadda Yake so. Bãbu abin bautãwa fãce Shi Mabuwãyi, Mai hikima. = --Qur'an 3:6
    It is He who has sent down to you, [O Muhammad], the Book; in it are verses [that are] precise - they are the foundation of the Book - and others unspecific. As for those in whose hearts is deviation [from truth], they will follow that of it which is unspecific, seeking discord and seeking an interpretation [suitable to them]. And no one knows its [true] interpretation except Allah. But those firm in knowledge say, "We believe in it. All [of it] is from our Lord." And no one will be reminded except those of understanding. <> Shi ne wanda ya saukar da Littãfi a gare ka, daga cikinsa akwai ãyõyi bayyanannu, su ne mafi yawan Littãfin, da wasu mãsu kamã da jũna. To, amma waɗanda yake a cikin zukãtansu akwai karkata sai suna bin abin da yake da kamã da jũna daga gare shi, dõmin nẽman yin fitina da tãwĩlinsa. Kuma bãbu wanda ya san tãwĩlinsafãce Allah. Kuma matabbata a cikin ilmi sunã cẽwa: "Mun yi ĩmãni da Shi; dukkansa daga wurin Ubangijinmu yake." Kuma bãbu mai tunãni fãce ma'abũta hankula. = --Qur'an 3:7
    [Who say], "Our Lord, let not our hearts deviate after You have guided us and grant us from Yourself mercy. Indeed, You are the Bestower. <> Yã Ubangijinmu! Kada Ka karkatar da zukãtanmu bãyan har Kã shiryar da mu, kuma Ka bã mu rahama daga gunKa. Lalle ne, Kai, Kai ne Mai yawan kyauta. = --Qur'an 3:8
    Our Lord, surely You will gather the people for a Day about which there is no doubt. Indeed, Allah does not fail in His promise." <> "Yã Ubangijimu! Lalle ne Kai, Mai tãra mutãne ne dõmin wani yini wanda bãbu shakka a gare shi, Lalle ne Allah bã Ya sãɓãwar lõkacin alkawari." = --Qur'an 3:9
    Indeed, those who disbelieve - never will their wealth or their children avail them against Allah at all. And it is they who are fuel for the Fire. <> Lalle ne waɗanda suka kãfirta, dũkiyõyinsu bã su tunkuɗe musu kõme daga Allah, kuma 'ya'yansu bã su tunkuɗẽwa, kuma waɗannan, sũ ne makãmashin wuta. = --Qur'an 3:10
    [Theirs is] like the custom of the people of Pharaoh and those before them. They denied Our signs, so Allah seized them for their sins. And Allah is severe in penalty. <> Kamar ɗabi'ar mutãnen Fir'auna da waɗanda ke a gabãninsu, sun ƙaryata ãyõyinMu, sai Allah Ya kãmã su sabõda zunubansu, kuma Allah Mai tsananin uƙũba ne. = --Qur'an 3:11
    Say to those who disbelieve, "You will be overcome and gathered together to Hell, and wretched is the resting place." <> Ka ce wa waɗanda suka kãfirta: "Za a rinjãye ku, kuma a tãraku zuwa Jahannama, kuma shimfiɗar tã mũnana! = --Qur'an 3:12
    Already there has been for you a sign in the two armies which met - one fighting in the cause of Allah and another of disbelievers. They saw them [to be] twice their [own] number by [their] eyesight. But Allah supports with His victory whom He wills. Indeed in that is a lesson for those of vision. <> "Lalle ne wata ãyã tã kasance a gare ku a cikin ƙungiyõyi biyu da suka haɗu; ƙungiya guda tana yãƙi a cikin hanyar Allah, da wata kãfira, suna ganin su ninki biyu nãsu, a ganin ido. Kuma Allah Yana ƙarfafa wanda Yake so da taimakonSa. Lalle ne a cikin wannan, hakĩƙa, akwai abin kula ga maabũta basĩra. = --Qur'an 3:13
    Beautified for people is the love of that which they desire - of women and sons, heaped-up sums of gold and silver, fine branded horses, and cattle and tilled land. That is the enjoyment of worldly life, but Allah has with Him the best return. <> An ƙawata wa mutãne son sha'awõyi daga mãtã da ɗiya da dũkiyõyi abũbuwan tãrãwa daga zinariya da azurfa, da dawãki kiwãtattu da dabbõbin ci da hatsi. Wannan shi ne dãɗin rãyuwar dũniya. Kuma Allah a wurinsa kyakkyãwar makõma take. = --Qur'an 3:14
    Say, "Shall I inform you of [something] better than that? For those who fear Allah will be gardens in the presence of their Lord beneath which rivers flow, wherein they abide eternally, and purified spouses and approval from Allah. And Allah is Seeing of [His] servants - <> Ka ce: Shin kuma, in gaya muku mafi alhẽri daga wannan? Akwai gidãjen Aljanna a wurin Ubangiji sabõda waɗanda suka bi Shi da taƙawa, kõguna suna gudãna daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu, da mãtan aure tsarkakakku, da yarda daga Allah. Kuma Allah Mai gani ne ga bãyinSa. = --Qur'an 3:15
    Those who say, "Our Lord, indeed we have believed, so forgive us our sins and protect us from the punishment of the Fire," <> Waɗanda suke cẽwa: "Ya Ubangijinmu! Lalle ne mu, mun yi ĩmãni, sai Ka gãfarta mana zunubanmu kuma Ka tsare mu daga azãbar wuta." = --Qur'an 3:16
    The patient, the true, the obedient, those who spend [in the way of Allah], and those who seek forgiveness before dawn. <> Mãsu haƙuri, da mãsu gaskiya, da mãsu ƙanƙan da kai, da mãsu ciyarwa da mãsu istingifari a lõkutan asuba. = --Qur'an 3:17
    Allah witnesses that there is no deity except Him, and [so do] the angels and those of knowledge - [that He is] maintaining [creation] in justice. There is no deity except Him, the Exalted in Might, the Wise. <> Allah Ya shaida cẽwa: Lalle ne bãbu abin bautãwa fãce Shi kuma malãiku da ma'abũta ilmi sun shaida, yana tsaye da ãdalci, bãbu abin bautãwa face Shi, Mabuwãyi, Mai hikima. = --Qur'an 3:18
    Indeed, the religion in the sight of Allah is Islam. And those who were given the Scripture did not differ except after knowledge had come to them - out of jealous animosity between themselves. And whoever disbelieves in the verses of Allah, then indeed, Allah is swift in [taking] account. <> Lalle ne, addini a wurin Allah, Shi ne Musulunci. Kuma waɗanda aka bai wa Littafi ba su sãɓã ba, fãce a bãyan ilmi ya je musu, bisa zãlunci a tsakãninsu. Kuma wanda ya kãfirta da ãyõyin Allah, to, lalle ne Allah Mai gaugãwar sakamako ne. = --Qur'an 3:19
    So if they argue with you, say, "I have submitted myself to Allah [in Islam], and [so have] those who follow me." And say to those who were given the Scripture and [to] the unlearned, "Have you submitted yourselves?" And if they submit [in Islam], they are rightly guided; but if they turn away - then upon you is only the [duty of] notification. And Allah is Seeing of [His] servants. <> To, idan sun yi musu da kai, sai ka ce: "Nã sallama fuskata ga Allah, kuma wanda ya bi ni (haka)." Kuma ka ce wa waɗanda aka bai wa littãfi da Ummiyyai: "Shin kun sallama?" To, idan sun sallama, haƙĩƙa, sun shiryu kuma idan sun jũya, to, kawai abinda ke kanka, shi ne iyarwa. Kuma Allah Mai gani ne ga bãyinSa. = --Qur'an 3:20
    Those who disbelieve in the signs of Allah and kill the prophets without right and kill those who order justice from among the people - give them tidings of a painful punishment. <> Lalle ne waɗanda suke kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe Annabãwa bã da wani hakki ba, kuma suna kashe waɗanda ke umurni da yin ãdalci daga mutãne, to, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 3:21
    They are the ones whose deeds have become worthless in this world and the Hereafter, and for them there will be no helpers. <> Waɗannan ne waɗanda ayyukansu suka ɓãci a cikin dũniya da Lãhira, kuma bã su da wasu mataimaka. = --Qur'an 3:22
    Do you not consider, [O Muhammad], those who were given a portion of the Scripture? They are invited to the Scripture of Allah that it should arbitrate between them; then a party of them turns away, and they are refusing. <> Shin, ba ka ga waɗanda aka bai wa rabo daga littãfi ba ana kiran su zuwa ga Littãfin Allah dõmin ya yi hukunci a tsakãninsu sa'an nan wata ƙungiya daga cikinsu ta jũya bãya, kuma sunã mãsu bijirẽwa? = --Qur'an 3:23
    That is because they say, "Never will the Fire touch us except for [a few] numbered days," and [because] they were deluded in their religion by what they were inventing. <> Wannan kuwa, dõmin lalle ne su sun ce: "Wutã bã zã ta shãfe mu ba, fãce a 'yan kwãnaki ƙidãyayyu." Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya ya rũɗẽ su a cikin addininsu. = --Qur'an 3:24
    So how will it be when We assemble them for a Day about which there is no doubt? And each soul will be compensated [in full for] what it earned, and they will not be wronged. <> To, yãya idan Mun tãra su a yini wanda bãbu shakka a cikinsa, kuma aka cikã wa kõwane rai sakamakon abin da ya tsirfanta, alhãli kuwa, sũ bã zã a zãlunce su ba? = --Qur'an 3:25
    Say, "O Allah, Owner of Sovereignty, You give sovereignty to whom You will and You take sovereignty away from whom You will. You honor whom You will and You humble whom You will. In Your hand is [all] good. Indeed, You are over all things competent. <> Ka ce: "Yã Allah Mamallakin mulki, Kanã bayar da mulki ga wanda Kake so, Kanã zãre mulki daga wanda Kake so, kuma Kanã buwãyar da wanda Kake so, kuma Kanã ƙasƙantar da wanda Kake so, ga hannunKa alhẽri yake. Lalle ne Kai, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi ne." = --Qur'an 3:26
    You cause the night to enter the day, and You cause the day to enter the night; and You bring the living out of the dead, and You bring the dead out of the living. And You give provision to whom You will without account." <> "Kanã shigar da dare a cikin yini, kuma Kanã shigar da yini a cikin dare, kuma Kana fitar da mai rai daga mamaci, kuma Kanã fitar da mamaci daga mai rai, kuma Kanã azurta wanda Kake so bã da lissafi ba." = --Qur'an 3:27
    Let not believers take disbelievers as allies rather than believers. And whoever [of you] does that has nothing with Allah, except when taking precaution against them in prudence. And Allah warns you of Himself, and to Allah is the [final] destination. <> Kada mũminai su riƙi kãfirai masõya, baicin mũminai. Kuma wanda ya yi wannan, to, bai zama a cikin kõme ba daga Allah, fãce fa dõmin ku yi tsaro daga gare su da 'yar kãriya. Kuma Allah yana tsõratar da ku kanSa. Kuma zuwa ga Allah makõma take. = --Qur'an 3:28
    Say, "Whether you conceal what is in your breasts or reveal it, Allah knows it. And He knows that which is in the heavens and that which is on the earth. And Allah is over all things competent. <> Ka ce: "Idan kun ɓõye abin da ke a cikin ƙirãzanku, kõ kuwa kun bayyana shi, Allah Yana sanin sa. Kuma Yana sanin abin da ke a cikin sammai da ƙasa. Kuma Allah a kan kõwane abu Mai ĩkon yi ne." = --Qur'an 3:29
    The Day every soul will find what it has done of good present [before it] and what it has done of evil, it will wish that between itself and that [evil] was a great distance. And Allah warns you of Himself, and Allah is Kind to [His] servants." <> A Rãnar da kõwane rai yake sãmun abin da ya aikata daga alhẽri, a halarce, da kuma abin da ya aikata daga sharri, alhãli yana gũrin, dã dai lalle a ce akwai fage mai nĩsa a tsakãninsa da abin daya aikata na sharrin! Kuma Allah Yanã tsõratar da kũ kanSa. Kuma Allah Mai tausayi ne ga bãyinSa. = --Qur'an 3:30
    Say, [O Muhammad], "If you should love Allah, then follow me, [so] Allah will love you and forgive you your sins. And Allah is Forgiving and Merciful." <> Ka ce: "Idan kun kasance kunã son Allah to, ku bĩ ni, Allah Ya sõ ku, kuma Ya gãfarta muku zunubanku. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai." = --Qur'an 3:31
    Say, "Obey Allah and the Messenger." But if they turn away - then indeed, Allah does not like the disbelievers. <> Ka ce: "Ku yi ɗã'a ga Allah da Manzo." To, amma idan sun jũya bãya, to, lalle ne Allah bã Ya son kãfirai. = --Qur'an 3:32
    Indeed, Allah chose Adam and Noah and the family of Abraham and the family of 'Imran over the worlds - <> Lalle ne Allah Yã zãɓi Ãdama da Nũhu da Gidan Ibrãhĩma da Gidan Imrãna a kan tãlikai. = --Qur'an 3:33
    Descendants, some of them from others. And Allah is Hearing and Knowing. <> Zuriyya ce sãshensu daga sãshe, kuma Allah Mai ji ne, Masani. = --Qur'an 3:34
    [Mention, O Muhammad], when the wife of 'Imran said, "My Lord, indeed I have pledged to You what is in my womb, consecrated [for Your service], so accept this from me. Indeed, You are the Hearing, the Knowing." <> A lõkacin da mãtar Imrãna ta ce: "Ya Ubangijina! Lalle ni, nã yi bãkancen abin da ke cikin cikĩna gare Ka; ya zama 'yantacce, sai Ka karɓa daga gare ni. Lalle ne Kai, Kai ne Mai ji, Masani." = --Qur'an 3:35
    But when she delivered her, she said, "My Lord, I have delivered a female." And Allah was most knowing of what she delivered, "And the male is not like the female. And I have named her Mary, and I seek refuge for her in You and [for] her descendants from Satan, the expelled [from the mercy of Allah]." <> To, a lõkacin da ta haife ta sai ta ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne nĩ, nã haife ta mace!"KumaAllah ne Mafi sanin abin da ta haifa." Kuma namiji bai zama kamar mace ba. Kuma nĩ nã yi mata suna Maryamu kuma lalle ne ni, ina nẽma mata tsari gare Ka, ita da zũriyarta daga Shaiɗan jẽfaffe." = --Qur'an 3:36
    So her Lord accepted her with good acceptance and caused her to grow in a good manner and put her in the care of Zechariah. Every time Zechariah entered upon her in the prayer chamber, he found with her provision. He said, "O Mary, from where is this [coming] to you?" She said, "It is from Allah. Indeed, Allah provides for whom He wills without account." <> Sai Ubangijinta Ya karɓe ta karɓa mai kyau. Kuma Ya yabanyartar da ita yabanyartarwa mai kyau, kuma Ya sanya rẽnonta ga Zakariyya. Ko da yaushe Zakariyya ya shiga masallãci, a gare ta, sai ya sãmi abinci a wurinta. (Sai kuwa) ya ce: "Yã Maryamu! Daga ina wannan yake gare ki?" (Sai) ta ce: "Daga wurin Allah yake. Lalle ne Allah yana azurta wanda Ya so ba da lissafi ba." = --Qur'an 3:37
    At that, Zechariah called upon his Lord, saying, "My Lord, grant me from Yourself a good offspring. Indeed, You are the Hearer of supplication." <> A can ne Zakariyya ya rõki Ubangijinsa, ya ce: "Ya Ubangijina! Ka bã ni zuriyya mai kyau daga gunKa. Lalle ne Kai Mai jin addu'a Kake." = --Qur'an 3:38
    So the angels called him while he was standing in prayer in the chamber, "Indeed, Allah gives you good tidings of John, confirming a word from Allah and [who will be] honorable, abstaining [from women], and a prophet from among the righteous." <> Sai malã'iku suka kirãye shi, alhãli kuwa shĩ yanã tsaye yana salla a cikin masallãci. (Suka ce), "Lalle ne Allah yana bã ka bushãra da Yahaya, alhãli yana mai gaskatãwar wata kalma daga Allah, kuma shugaba, kuma tsarkakke kuma annabi daga sãlihai." = --Qur'an 3:39
    He said, "My Lord, how will I have a boy when I have reached old age and my wife is barren?" The angel said, "Such is Allah; He does what He wills." <> Ya ce: "Yã Ubangijina! Yãya yãro zai sãmu a gare ni, alhãli kuwa, lalle tsũfa ya sãme ni, kuma mãtãta bakarãriya ce?" Allah ya ce, "Kamar hakan ne, Allah yana aikata abin da Yake so." = --Qur'an 3:40
    He said, "My Lord, make for me a sign." He Said, "Your sign is that you will not [be able to] speak to the people for three days except by gesture. And remember your Lord much and exalt [Him with praise] in the evening and the morning." <> Ya ce: "Yã Ubangijinã! Ka sanya mini wata alãma!" (Allah) Ya ce "Alãmarka ita ce ba zã ka iya yi wa mutãne magana ba har yini uku face da ishãra. Sai ka ambaci Ubangijinka da yawa. Kuma ka yi tasbĩhi da marece da sãfe." = --Qur'an 3:41
    And [mention] when the angels said, "O Mary, indeed Allah has chosen you and purified you and chosen you above the women of the worlds. <> Kuma a lõkacin da malã'iku suka ce: "Ya Maryamu! Lalle ne, Allah Ya zãɓe ki, kuma Ya tsarkake ki, kuma Ya zaɓe ki a kan mãtan tãlikai." = --Qur'an 3:42
    O Mary, be devoutly obedient to your Lord and prostrate and bow with those who bow [in prayer]." <> "Yã Maryamu! Ki yi ƙanƙan da kai ga Ubangijinki, kuma ki yi sujada, kuma ki yi rukũ'i tãre da mãsu rukũ'i." = --Qur'an 3:43
    That is from the news of the unseen which We reveal to you, [O Muhammad]. And you were not with them when they cast their pens as to which of them should be responsible for Mary. Nor were you with them when they disputed. <> Wannan yana daga lãbarun gaibi, Munã yin wahayinsa zuwa gare ka (Muhammadu). Ba ka kasance ba a wurinsu a lõkacin da suke jẽfa alƙalumansu (domin ƙuri'a) wãne ne zai yi rẽnon Maryam. Kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lõkacin da suke ta yin husũma. = --Qur'an 3:44
    [And mention] when the angels said, "O Mary, indeed Allah gives you good tidings of a word from Him, whose name will be the Messiah, Jesus, the son of Mary - distinguished in this world and the Hereafter and among those brought near [to Allah]. <> A lõkacin da malã'iku suka ce "Yã Maryamu! Lalle ne Allah Yana bã ki bushãra da wata kalma daga gare Shi; sũnansa Masĩhu ĩsa ɗan Maryama, yana mai daraja a dũniya da Lãhira kuma daga Makusanta. = --Qur'an 3:45
    He will speak to the people in the cradle and in maturity and will be of the righteous." <> "Kuma yana yi wa mutãne magana a cikin shimfiɗar jariri, da kuma lõkacin da yana dattijo, kuma yana daga sãlihai." = --Qur'an 3:46
    She said, "My Lord, how will I have a child when no man has touched me?" [The angel] said, "Such is Allah; He creates what He wills. When He decrees a matter, He only says to it, 'Be,' and it is. <> Ta ce: "Yã Ubangijina! Yãya yãro zai kasance a gare ni, alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba?" (Allah) Ya ce: "Kamar wannan ne, Allah yana halittar abin da Yake so. Idan Ya hukunta wani al'amari, sai ya ce masa, "Ka kasance!, Sai yana kasancẽwa." = --Qur'an 3:47
    And He will teach him writing and wisdom and the Torah and the Gospel <> Kuma Ya sanar da shi rubũtu da hikima da Taurata da injĩla. = --Qur'an 3:48
    And [make him] a messenger to the Children of Israel, [who will say], 'Indeed I have come to you with a sign from your Lord in that I design for you from clay [that which is] like the form of a bird, then I breathe into it and it becomes a bird by permission of Allah. And I cure the blind and the leper, and I give life to the dead - by permission of Allah. And I inform you of what you eat and what you store in your houses. Indeed in that is a sign for you, if you are believers. <> Kuma (Ya sanya shi) manzo zuwa ga Bani Isrãila'ĩla (da sãko, cẽwa), Lalle ne, ni haƙĩƙa nã zõ muku, da wata ãyã daga Ubangijinku. Lalle ne ni ina halitta muku daga lãka, kamar siffar tsuntsu sa'an nan in hũra a cikinsa, sai ya kasance tsuntsu, da izinin Allah. Kuma ina warkar da wanda aka haifa makãho da kuturu, kuma ina rãyar da matottu, da izibin Allah. Kuma ina gayã muku abin da kuke ci da abin da kuke ajiyẽwa acikin gidãjenku. Lalle ne, a cikin wannan akwai ãyã a gare ku, idan kun kasance mãsu yin ĩmãni. = --Qur'an 3:49
    And [I have come] confirming what was before me of the Torah and to make lawful for you some of what was forbidden to you. And I have come to you with a sign from your Lord, so fear Allah and obey me. <> "Kuma inã mai gaskatãwa ga abin da yake a gabãnina daga Taurata. Kuma (nãzo) dõmin in halatta muku sãshen abin da aka haramta muku. Kuma nã tafo muku da wata ãyã daga Ubangijinku. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã. = --Qur'an 3:50
    Indeed, Allah is my Lord and your Lord, so worship Him. That is the straight path." <> "Lalle Allah shi ne Ubangijina, kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan ce hanya madaidaiciya." = --Qur'an 3:51
    But when Jesus felt [persistence in] disbelief from them, he said, "Who are my supporters for [the cause of] Allah?" The disciples said, "We are supporters for Allah. We have believed in Allah and testify that we are Muslims [submitting to Him]. <> To, a lõkacin da Ĩsa ya gane kãfirci daga gare su, sai ya ce: "Su wãne ne mataimakãna zuwa ga Allah?" Hawãriyãwa suka ce: "Mu ne mataimakan Allah. Mun yi ĩmani da Allah. Kuma ka shaida cẽwa lalle ne mu, mãsu sallamãwa ne. = --Qur'an 3:52
    Our Lord, we have believed in what You revealed and have followed the messenger Jesus, so register us among the witnesses [to truth]." <> "Yã Ubangijinmu! Mun yi imãni da abin da Ka saukar, kuma mun bi ManzonKa, sai Ka rubũta mu tãre da mãsu shaida.. = --Qur'an 3:53
    And the disbelievers planned, but Allah planned. And Allah is the best of planners. <> Kuma (Kãfirai) suka yi mãkirci, Allah kuma Ya yi musu (sakamakon) makircin, kuma Allah ne Mafi alhẽrin mãsu sãka wamãkirci. = --Qur'an 3:54
    [Mention] when Allah said, "O Jesus, indeed I will take you and raise you to Myself and purify you from those who disbelieve and make those who follow you [in submission to Allah alone] superior to those who disbelieve until the Day of Resurrection. Then to Me is your return, and I will judge between you concerning that in which you used to differ. <> A lõkacin da Ubangiji Ya ce: "Ya Ĩsa! Lalle NĨ Mai karɓar ranka ne, kuma Mai ɗauke ka ne zuwa gare Ni, kuma Mai tsarkake ka daga waɗanda suka kãfirta, kuma Mai sanya waɗanda suka bĩ ka a bisa waɗanda suka kãfirta har Rãnar ¡iyãma. Sa'an nan kuma zuwa gare Ni makõmarku take, sa'an nan in yi hukunci a tsakãninku, a cikin abin da kuka kasance kuna sãɓã wa jũna. = --Qur'an 3:55
    And as for those who disbelieved, I will punish them with a severe punishment in this world and the Hereafter, and they will have no helpers." <> "To, amma waɗanda suka kãfirta sai In azabta su da azãba mai tsanani, a cikin dũniya da Lãhira, kuma bã su da wasu mãsu taimako. = --Qur'an 3:56
    But as for those who believed and did righteous deeds, He will give them in full their rewards, and Allah does not like the wrongdoers. <> Kuma amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sai (Allah) Ya cikã musu ijãrõrinsu. Kuma Allah bã Ya son azzãlumai. = --Qur'an 3:57
    This is what We recite to you, [O Muhammad], of [Our] verses and the precise [and wise] message. <> "Wannan Muna karanta shi a gare ka (Muhammad) daga ãyõyi, da Tunatarwa mai hikima (Alƙur'ãni)." = --Qur'an 3:58
    Indeed, the example of Jesus to Allah is like that of Adam. He created Him from dust; then He said to him, "Be," and he was. <> Lalle ne misãlin Ĩsã a wurin Allah kamar misãlin Ãdama ne, (Allah) Yã halitta shi daga turɓãya, sa'an nan kuma Ya ce masa: "Ka kasance: "Sai yana kasancewa. = --Qur'an 3:59
    The truth is from your Lord, so do not be among the doubters. <> Gaskiya daga Ubangijinka take sabõda haka kada ka kasance daga mãsu shakka. = --Qur'an 3:60
    Then whoever argues with you about it after [this] knowledge has come to you - say, "Come, let us call our sons and your sons, our women and your women, ourselves and yourselves, then supplicate earnestly [together] and invoke the curse of Allah upon the liars [among us]." <> To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bãyan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: "Ku zo mu kirãyi, 'yã'yanmu da 'yã'yanku da mãtanmu da mãtanku da kanmu da kanku sa'an nan kuma mu ƙanƙantar da kai sa'an nan kuma mu sanya la'anar, Allah a kan maƙaryata." = --Qur'an 3:61
    Indeed, this is the true narration. And there is no deity except Allah. And indeed, Allah is the Exalted in Might, the Wise. <> Lalle ne wannan, haƙĩƙa, shi ne lãbãri tabbatacce, kuma bãbu wani abin bautawa fãce Allah, kuma lalle ne, Allah, haƙĩƙa, Shi ne Mabuwãyi Mai hikima. = --Qur'an 3:62
    But if they turn away, then indeed - Allah is Knowing of the corrupters. <> To, idan sun jũya bãya, to, lalle Allah Masani ne ga maɓannata. = --Qur'an 3:63
    Say, "O People of the Scripture, come to a word that is equitable between us and you - that we will not worship except Allah and not associate anything with Him and not take one another as lords instead of Allah." But if they turn away, then say, "Bear witness that we are Muslims [submitting to Him]." <> Ka ce: "Yã ku Mutãnen Littãfi! Ku tafo zuwa ga kalma mai daidaitãwa a tsakã ninmu da ku; kada mu bauta wa kõwa fã ce Allah. Kuma kada mu haɗa kõme da Shi, kuma kada sãshenmu ya riƙi sãshe Ubangiji, baicin Allah." To, idan sun jũya bã ya sai ku ce: "ku yi shaida cẽwa, lalle ne mu masu sallamã wa ne." = --Qur'an 3:64
    O People of the Scripture, why do you argue about Abraham while the Torah and the Gospel were not revealed until after him? Then will you not reason? <> Yã Mutãnen Littãfi! Don me kuke hujjacẽwa a cikin sha'anin lbrãhĩma, alhãli kuwa ba a saukar da Attaura da injĩla ba fãce daga bãyansa? Shin bã ku hankalta? = --Qur'an 3:65
    Here you are - those who have argued about that of which you have [some] knowledge, but why do you argue about that of which you have no knowledge? And Allah knows, while you know not. <> Gã ku yã waɗannan! Kun yi hujjacẽwa a cikin abin da yake kunã da wani ilmi game da shi, to, don me kuma kuke yin hujjacẽwa a cikin abin da bã ku da wani ilmi game da shi? Allah yana sani, kuma kũ, ba ku sani ba! = --Qur'an 3:66
    Abraham was neither a Jew nor a Christian, but he was one inclining toward truth, a Muslim [submitting to Allah]. And he was not of the polytheists. <> Ibrãhĩma bai kasance Bayahũde ba, kuma bai kasance Banasãre ba, amma yã kasance mai karkata zuwa ga gaskiya, mai sallamãwa, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba. = --Qur'an 3:67
    Indeed, the most worthy of Abraham among the people are those who followed him [in submission to Allah] and this prophet, and those who believe [in his message]. And Allah is the ally of the believers. <> Lalle ne mafi hakkin mutãne da Ibrãhĩma haƙĩƙa, sũ ne waɗanda suka bi shi a (zamaninsa) da wannan Annabi (Muhammadu) da waɗanda suka yi ĩmãni. Kuma Allah ne Majiɓincin mũminai. = --Qur'an 3:68
    A faction of the people of the Scripture wish they could mislead you. But they do not mislead except themselves, and they perceive [it] not. <> Wata ƙungiya daga Mutãnen Littãfi sun yi gũrin su ɓatar da ku, to, ba su ɓatar da kõwa ba fãce kansu, kuma bã su sansancewa! = --Qur'an 3:69
    O People of the Scripture, why do you disbelieve in the verses of Allah while you witness [to their truth]? <> Yã Mutãnen Littãfi! Don me kuka kãfirta da ãyõyin Allah, alhãli kuwa kũ, kuna shaida (cẽwa sũ gaskiya ne)? = --Qur'an 3:70
    O People of the Scripture, why do you confuse the truth with falsehood and conceal the truth while you know [it]? <> Yã Mutãnen Littãfi! Don me kuke lulluɓe gaskiya da ƙarya, kuma kuke ɓõye gaskiya, alhãli kuwa kuna sane? = --Qur'an 3:71
    And a faction of the People of the Scripture say [to each other], "Believe in that which was revealed to the believers at the beginning of the day and reject it at its end that perhaps they will abandon their religion, <> Kuma wata ƙungiya daga Mutãnen Littãfi ta ce: "Ku yi ĩmãni da abin da aka saukar a kan waɗanda suka yi ĩmãni (da Muhammadu) a farkon yini, kuma ku kãfirta a ƙarshensa; tsammãninsu, zã su kõmõ." = --Qur'an 3:72
    And do not trust except those who follow your religion." Say, "Indeed, the [true] guidance is the guidance of Allah. [Do you fear] lest someone be given [knowledge] like you were given or that they would [thereby] argue with you before your Lord?" Say, "Indeed, [all] bounty is in the hand of Allah - He grants it to whom He wills. And Allah is all-Encompassing and Wise." <> "Kada ku yi ĩmãni fãce da wanda ya bi addininku." Ka ce: "Lalle ne, shiriya ita ce shiriyar Allah. (Kuma kada ku yi ĩmãni) cẽwa an bai wa wani irin abin da aka bã ku, kõ kuwa su yi musu da ku a wurin Ubangijinku." Ka ce: "Lalle ne falala ga hannun Allah take, yana bãyar da ita ga wanda Yake so, kuma Allah Mawadãci ne, Masani." = --Qur'an 3:73
    He selects for His mercy whom He wills. And Allah is the possessor of great bounty. <> Yanã keɓance wanda Ya so da rahamarSa, kuma Allah Ma'abucin falala ne, Mai girma. = --Qur'an 3:74
    And among the People of the Scripture is he who, if you entrust him with a great amount [of wealth], he will return it to you. And among them is he who, if you entrust him with a [single] silver coin, he will not return it to you unless you are constantly standing over him [demanding it]. That is because they say, "There is no blame upon us concerning the unlearned." And they speak untruth about Allah while they know [it]. <> Kuma daga Mutãnen Littãfi akwai wanda yake idan ka bã shi amãnar kinɗãri, zai bãyar da shi gare ka, kuma daga gare su akwai wanda idan ka bã shi amãnar dĩnari, bã zai bãyar da shi gare ka ba, fãce idan kã dawwama a kansa kanã tsaye. Wannan kuwa, dõmin lalle ne sũ sun ce, "Bãbu laifi a kanmu a cikin Ummiyyai." Suna faɗar ƙarya ga Allah, alhãli kuwa suna sane. = --Qur'an 3:75
    But yes, whoever fulfills his commitment and fears Allah - then indeed, Allah loves those who fear Him. <> Na'am! Wanda ya cika alkawarinsa, kuma ya yi taƙawa, to, lalle ne Allah yana son mãsu taƙawa. = --Qur'an 3:76
    Indeed, those who exchange the covenant of Allah and their [own] oaths for a small price will have no share in the Hereafter, and Allah will not speak to them or look at them on the Day of Resurrection, nor will He purify them; and they will have a painful punishment. <> Lalle ne waɗanda suke sayen 'yan tamani kaɗan da alkawarin Allah da rantsuwõyinsu, waɗannan bãbu wani rabo a gare su a Lãhira, Kuma Allah bã Ya yin magana da su, kuma bã Ya dũbi zuwa gare su, a Rãnar ¡iyãma, kuma bã Ya tsarkake su, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 3:77
    And indeed, there is among them a party who alter the Scripture with their tongues so you may think it is from the Scripture, but it is not from the Scripture. And they say, "This is from Allah," but it is not from Allah. And they speak untruth about Allah while they know. <> Kuma lalle ne, daga gare su akwai wata ƙungiya suna karkatar da harsunansu da Littãfi dõmin ku yi zaton sa daga Littãfin, alhãli kuwa bã shi daga Littãfin. Kuma suna cẽwa: "Shi daga wurinAllah yake." Alhãli kuwa shi, bã daga wurin Allah yake ba. Sunã faɗar ƙarya ga Allah, alhãli kuwa sunã sane. = --Qur'an 3:78
    It is not for a human [prophet] that Allah should give him the Scripture and authority and prophethood and then he would say to the people, "Be servants to me rather than Allah," but [instead, he would say], "Be pious scholars of the Lord because of what you have taught of the Scripture and because of what you have studied." <> Ba ya yiwuwa ga wani mutum, Allah Ya bã shi Littãfi da hukunci da Annabci, sa'an nan kuma ya ce wa mutãne: "Ku kasance bãyi gare ni, baicin Allah." Amma (zai ce): "Ku kasance mãsu aikin ibãda da abin da kuka kasance kuna karantar da Littãfin, kuma da abin da kuka kasance kuna karantãwa." = --Qur'an 3:79
    Nor could he order you to take the angels and prophets as lords. Would he order you to disbelief after you had been Muslims? <> Kuma ba ya umurnin ku da ku riƙi malã'iku da annabãwa lyãyengiji. Shin, zai umurce ku da kãfirci ne a bãyan kun riga kun zama mãsu sallamãwa (Musulmi)? = --Qur'an 3:80
    And [recall, O People of the Scripture], when Allah took the covenant of the prophets, [saying], "Whatever I give you of the Scripture and wisdom and then there comes to you a messenger confirming what is with you, you [must] believe in him and support him." [Allah] said, "Have you acknowledged and taken upon that My commitment?" They said, "We have acknowledged it." He said, "Then bear witness, and I am with you among the witnesses." <> Kuma a lõkacin da Allah Ya riƙi alkawarin Annabãwa: "Lalle ne ban bã ku wani abu ba daga Littãfi da hikima, sa'an nan kuma wani manzo ya je muku, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku; lalle ne zã ku gaskata Shi, kuma lalle ne zã ku taimake shi." Ya ce: "Shin, kun tabbatar kuma kun riƙi alkawarĩNa a kan wannan a gare ku?" suka ce: "Mun tabbatar." Ya ce: "To, ku yi shaida, kuma Nĩ a tãre da ku Inã daga mãsu shaida." = --Qur'an 3:81
    And whoever turned away after that - they were the defiantly disobedient. <> To, waɗanda kuma suka jũya bãya a bãyan wannan, to, waɗannan sũ ne fãsiƙai. = --Qur'an 3:82
    So is it other than the religion of Allah they desire, while to Him have submitted [all] those within the heavens and earth, willingly or by compulsion, and to Him they will be returned? <> Shin wanin Addinin Allah suke nẽma, alhãli kuwa a gare Shi ne waɗanda ke cikin sama da ƙasa suka sallama wa, a kan sõ da ƙĩ, kuma zuwa gare Shi ake mayar da su? = --Qur'an 3:83
    Say, "We have believed in Allah and in what was revealed to us and what was revealed to Abraham, Ishmael, Isaac, Jacob, and the Descendants, and in what was given to Moses and Jesus and to the prophets from their Lord. We make no distinction between any of them, and we are Muslims [submitting] to Him." <> Ka ce: "Mun yi ĩmãni da Allah kuma da abin da aka saukar mana da abin da aka saukar wa Ibrãhĩma da Isma'ĩla da Is'hãƙa da Yãƙũba da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da ĩsã da annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu bambantãwa a tsakãnin kõwa daga gare su. Kuma mũ, zuwa gare Shi mãsu sallamãwa ne." = --Qur'an 3:84
    And whoever desires other than Islam as religion - never will it be accepted from him, and he, in the Hereafter, will be among the losers. <> Kuma wanda ya nẽmi wanin Musulunci ya zama addini, to, bã zã a karɓa daga gare shi ba. Kuma shi a Lãhira yana daga cikin mãsu hasãra. = --Qur'an 3:85
    How shall Allah guide a people who disbelieved after their belief and had witnessed that the Messenger is true and clear signs had come to them? And Allah does not guide the wrongdoing people. <> Yãya Allah zai shiryar da mutãne waɗanda suka kãfirta a bãyan ĩmãninsu, kuma sun yi shaidar cẽwa, lalle Manzo gaskiya ne, kuma hujjõji bayyanannu sun je musu? Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai. = --Qur'an 3:86
    Those - their recompense will be that upon them is the curse of Allah and the angels and the people, all together, <> Waɗannan, sakamakonsu shi ne, lalle a kansu akwai la'anar Allah da mãla'iku da mutãne gabã ɗaya. = --Qur'an 3:87
    Abiding eternally therein. The punishment will not be lightened for them, nor will they be reprieved. <> Sunã mãsu dawwama a cikinta, bã a sauƙaƙa azãbar gare su, kuma ba su zama ana yi musu jinkiri ba. = --Qur'an 3:88
    Except for those who repent after that and correct themselves. For indeed, Allah is Forgiving and Merciful. <> Fãce waɗanda suka tũba daga bãyan wannan, kuma suka yi gyãra, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne Mai jin ƙai. = --Qur'an 3:89
    Indeed, those who reject the message after their belief and then increase in disbelief - never will their [claimed] repentance be accepted, and they are the ones astray. <> Lalle ne waɗanda suka kãfirta a bãyan ĩmãninsu, sa'an nan kuma suka ƙãra kãfirci bã zã a karɓi tũbarsu ba. Kuma waɗannan sũ ne ɓatattu. = --Qur'an 3:90
    Indeed, those who disbelieve and die while they are disbelievers - never would the [whole] capacity of the earth in gold be accepted from one of them if he would [seek to] ransom himself with it. For those there will be a painful punishment, and they will have no helpers. <> Lalle ne wanɗanda suka kãfirta, kuma suka mutu alhãli kuwa suna kãfirai to bã zã a karɓi cike da ƙasa na zinãri daga ɗayansu ba, kõ dã ya yi fansa da shi, waɗannan sunã da azãba mai raɗaɗi, kuma bã su da wasu mataimaka. = --Qur'an 3:91
    Never will you attain the good [reward] until you spend [in the way of Allah] from that which you love. And whatever you spend - indeed, Allah is Knowing of it. <> Bã zã ku sãmi kyautatãwa ba, sai kun ciyar daga abin da kuke so. Kuma abin da kuka ciyar, kõ mẽne ne, to, lalle ne Allah, gare shi, Masani ne. = --Qur'an 3:92
    All food was lawful to the Children of Israel except what Israel had made unlawful to himself before the Torah was revealed. Say, [O Muhammad], "So bring the Torah and recite it, if you should be truthful." <> Dukan abinci yã kasance halal ne ga Bani lsrã'ĩla, fãce abinda Isrã'ĩla ya haramta wa kansadaga gabãnin saukar da Attaura. Ka ce: "To, ku zo da Attaura sa'an nan ku karantã ta, idan kun kasance mãsu gaskiya ne. = --Qur'an 3:93
    And whoever invents about Allah untruth after that - then those are [truly] the wrongdoers. <> "To, wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah daga bãyan wannan, to, waɗannan sũ ne azzãlumai." = --Qur'an 3:94
    Say, "Allah has told the truth. So follow the religion of Abraham, inclining toward truth; and he was not of the polytheists." <> Ka ce: "Allah Ya yi gaskiya, sabõda haka ku bi aƙĩdar Ibrãhĩma mai karkata zuwa ga gaskiya; kuma bai kasance daga mãsu shirki ba." = --Qur'an 3:95
    Indeed, the first House [of worship] established for mankind was that at Makkah - blessed and a guidance for the worlds. <> Kuma lalle ne, ¦aki na farko da aka aza dõmin mutãne, haƙĩƙa, shi ne wanda ke Bakka mai albarka kuma shiriya ga tãlikai. = --Qur'an 3:96
    In it are clear signs [such as] the standing place of Abraham. And whoever enters it shall be safe. And [due] to Allah from the people is a pilgrimage to the House - for whoever is able to find thereto a way. But whoever disbelieves - then indeed, Allah is free from need of the worlds. <> A cikinsa akwai ãyõyi bayyanannu; (ga misãli) matsayin Ibrãhĩma. Kuma wanda ya shige shi yã kasance amintacce. Kuma akwai hajjin ¦ãkin dõmin Allah a kan mutãne, ga wanda ya sãmi ĩkon zuwa gare shi, kuma wanda ya kafirta to lalle Allah Mawadãci ne daga barin tãlikai. = --Qur'an 3:97
    Say, "O People of the Scripture, why do you disbelieve in the verses of Allah while Allah is Witness over what you do?" <> Ka ce: "Ya kũ Mutãnen Littãfi! Don me kuke kãfirta da ãyõyin Allah, alhãli kuwa Allah Mai shaida ne a kan abin da kuke aikatãwa?" = --Qur'an 3:98
    Say, "O People of the Scripture, why do you avert from the way of Allah those who believe, seeking to make it [seem] deviant, while you are witnesses [to the truth]? And Allah is not unaware of what you do." <> Ka ce: "Ya ku Mutãnen Littãfi! Don me kuke taushe wanda ya yi ĩmani, daga hanyar Allah, kuma kunã nẽman ta zama karkatacciya, alhãli kuwa kunã mãsu shaida? Kuma Allah bai gushe daga abin da kuke aikatãwa ba yana Masani." = --Qur'an 3:99
    O you who have believed, if you obey a party of those who were given the Scripture, they would turn you back, after your belief, [to being] unbelievers. <> Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi ɗã'aga wani ɓangare daga waɗanda aka bai wa Littãfi, zã su mayar da ku kãfirai a bãyan ĩmãninku! = --Qur'an 3:100
    And how could you disbelieve while to you are being recited the verses of Allah and among you is His Messenger? And whoever holds firmly to Allah has [indeed] been guided to a straight path. <> Kuma yãyã kuke kãfircẽwa alhãli kuwa anã karanta ãyõyin Allah a gare ku, kuma a cikinku akwai manzonSa? Kuma wanda ya nẽmi tsari da Allah, to, an shiryar da shi zuwa ga hanya miƙaƙƙiya. = --Qur'an 3:101
    O you who have believed, fear Allah as He should be feared and do not die except as Muslims [in submission to Him]. <> Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, a kan hakkin binsa da taƙawa, kuma kada ku mutu fãce kuna mãsu sallamawa (Musulmi). = --Qur'an 3:102
    And hold firmly to the rope of Allah all together and do not become divided. And remember the favor of Allah upon you - when you were enemies and He brought your hearts together and you became, by His favor, brothers. And you were on the edge of a pit of the Fire, and He saved you from it. Thus does Allah make clear to you His verses that you may be guided. <> Kuma ku yi daidami da igiyar Allah gabã ɗaya, kuma kada ku rarraba. Kuma ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da kuka kasance maƙiya sai Ya sanya sõyayya a tsakãnin zukãtanku sabõda haka kuka wãyi gari, da ni'imarSa, 'yan'uwa. Kuma kun kasance a kan gãɓar rãmi na wutã sai Ya tsãmar da ku daga gare ta, Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ayõyinSa, tsammãninku, zã ku shiryu. = --Qur'an 3:103
    And let there be [arising] from you a nation inviting to [all that is] good, enjoining what is right and forbidding what is wrong, and those will be the successful. <> Kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alhẽri, kuma suna umurnida alhẽri, kuma suna hani dagaabin da ake ƙi. Kuma waɗannan, sũ ne mãsu cin nasara. = --Qur'an 3:104
    And do not be like the ones who became divided and differed after the clear proofs had come to them. And those will have a great punishment. <> Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka rarrabu kuma suka sãɓã wa jũna, bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu kuma waɗannan sunã da azãba mai girma. = --Qur'an 3:105
    On the Day [some] faces will turn white and [some] faces will turn black. As for those whose faces turn black, [to them it will be said], "Did you disbelieve after your belief? Then taste the punishment for what you used to reject." <> A rãnar da wasu fuskõki suke yin fari kuma wasu fuskõki suke yin baƙi (zã a ce wa waɗanda fuskokinsu suke yin baƙin): "Shin kun kãfirta a bayan ĩmãninku? Don haka sai ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kasance kuna yi na kãfirci." = --Qur'an 3:106
    But as for those whose faces will turn white, [they will be] within the mercy of Allah. They will abide therein eternally. <> Kuma amma waɗanda fuskõkinsu suka yi fari, to sũ suna cikin rahamar Allah kuma, su a cikinta, madawwama, ne. = --Qur'an 3:107
    These are the verses of Allah. We recite them to you, [O Muhammad], in truth; and Allah wants no injustice to the worlds. <> Waɗannan ãyõyin Allah ne, muna karanta su a gare ka da gaskiya, kuma Allah bã Ya nufin wani zãlunci ga tãlikai. = --Qur'an 3:108
    To Allah belongs whatever is in the heavens and whatever is on the earth. And to Allah will [all] matters be returned. <> Kuma abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa na Allah ne, kuma zuwa gare Shi ake mayar da al'amurra. = --Qur'an 3:109
    You are the best nation produced [as an example] for mankind. You enjoin what is right and forbid what is wrong and believe in Allah. If only the People of the Scripture had believed, it would have been better for them. Among them are believers, but most of them are defiantly disobedient. <> Kun kasance mafi alhẽrin al'umma wadda aka fitar ga mutãne kuna umurni da alhẽri kuma kunã hani daga abin da ake ƙi, kuma kunã ĩmãni da Allah. Kuma dã Mutãnen Littãfi sun yi ĩmãni, lalle ne, dã (haka) yã kasance mafi alhẽri a gare su. Daga cikinsu akwai mũminai, kuma mafi yawansufãsiƙai ne. = --Qur'an 3:110
    They will not harm you except for [some] annoyance. And if they fight you, they will show you their backs; then they will not be aided. <> Bã zã su cũce ku ba, fãce dai tsangwama. Kuma idan sun yãƙe ku zã su jũya muku bãya, sa'an nan kuma bã zã a taimake su ba. = --Qur'an 3:111
    They have been put under humiliation [by Allah] wherever they are overtaken, except for a covenant from Allah and a rope from the Muslims. And they have drawn upon themselves anger from Allah and have been put under destitution. That is because they disbelieved in the verses of Allah and killed the prophets without right. That is because they disobeyed and [habitually] transgressed. <> An dõka ƙasƙanci a kansu a inda duk aka sãme su fãce da wani alkawari daga Allah, da alkawari daga mutãne. Kuma sun kõma da fushi daga Allah, kuma aka dõka talauci a kansu. Wannan kuwa dõmin sũ, lalle sun kasance suna kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe annabãwa, bã da wani haƙƙi ba. Wannan kuwa dõmin sãɓãwar da suka yi ne, kuma sun kasance suna yin ta'adi. = --Qur'an 3:112
    They are not [all] the same; among the People of the Scripture is a community standing [in obedience], reciting the verses of Allah during periods of the night and prostrating [in prayer]. <> Ba su zama daidai ba; daga Mutãnen Littafi akwai wata al'umma wadda take tsaye, suna karãtun ayõyin Allah a cikin sã'õ'in dare, alhãli kuwa sunã yin sujada. = --Qur'an 3:113
    They believe in Allah and the Last Day, and they enjoin what is right and forbid what is wrong and hasten to good deeds. And those are among the righteous. <> Suna ĩmãni da Allah da Yinin Lãhira, kuma suna umurui da abin da aka sani kuma suna hani daga abin da ba a sani ba, kuma sunã gaugãwa a cikin alhẽrai. Kuma waɗannan suna cikin sãlihai. = --Qur'an 3:114
    And whatever good they do - never will it be removed from them. And Allah is Knowing of the righteous. <> Kuma abin da suka aikata daga alhẽri, to, bã zã a yi musu musunsa ba. Kuma Allah Masani ne ga mãsu taƙawa. = --Qur'an 3:115
    Indeed, those who disbelieve - never will their wealth or their children avail them against Allah at all, and those are the companions of the Fire; they will abide therein eternally. <> Lalle ne waɗanda suka kãfirta, dũkiyõyinsu kõ ɗiyansu bã zã su wadatar musu da kõme ba daga Allah kuma waɗannan abõkan wuta ne, sũ, acikinta, madawwama ne. = --Qur'an 3:116
    The example of what they spend in this worldly life is like that of a wind containing frost which strikes the harvest of a people who have wronged themselves and destroys it. And Allah has not wronged them, but they wrong themselves. <> Misãlin abin da suke ciyarwa, a cikin wannan rãyuwar dũniya, kamar misãlin iska ce (wadda) a cikinta akwai tsananin sanyi, ta sãmi shukar wasu mutãne waɗanda suka zãlunci kansu, sai ta halakar da ita. Allah bai zãlunce su ba, amma kansu suka kasance sunã zãlunta. = --Qur'an 3:117
    O you who have believed, do not take as intimates those other than yourselves, for they will not spare you [any] ruin. They wish you would have hardship. Hatred has already appeared from their mouths, and what their breasts conceal is greater. We have certainly made clear to you the signs, if you will use reason. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi abõkan asĩri daga waninku, ba su taƙaita muku ɓarna. Kuma sun yi gũrin abin da zã ku cũtu da shi. Haƙĩka, ƙiyayya tã bayyana daga bãkunansu, kuma abin da zukãtansu ke ɓõyẽwane mafi girma. Kuma lalle ne, Mun bayyana muku ãyõyi, idan kun kasance kunã hankalta. = --Qur'an 3:118
    Here you are loving them but they are not loving you, while you believe in the Scripture - all of it. And when they meet you, they say, "We believe." But when they are alone, they bite their fingertips at you in rage. Say, "Die in your rage. Indeed, Allah is Knowing of that within the breasts." <> Gã ku yã waɗannan! Kunã son su bã su son ku, kuma kuna ĩmãni da Littãfi dukansa. Kuma idan sun haɗu da ku sukan ce "Mun yi ĩmani". Kuma idan sun kaɗaita sai su ciji yãtsu a kanku don takaici. Ka ce "Ku mutu da takaicinku. Lalle ne, Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza." = --Qur'an 3:119
    If good touches you, it distresses them; but if harm strikes you, they rejoice at it. And if you are patient and fear Allah, their plot will not harm you at all. Indeed, Allah is encompassing of what they do. <> Idan wani alhẽri ya shãfe ku sai ya baƙanta musu rai, kuma idan wata cũtar ta shãfe ku sai su yi farin ciki da ita. Kuma idan kun yi haƙuri kuma kuka yi taƙawa, ƙullinsu bã ya cũtar ku da kõme. Lalle ne, Allah ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa ne. = --Qur'an 3:120
    And [remember] when you, [O Muhammad], left your family in the morning to post the believers at their stations for the battle [of Uhud] - and Allah is Hearing and Knowing - <> Kuma a lõkacin da ka yi sauko daga iyãlanka kana zaunar da mũminai a wurãren zamadõmin yãƙi, kuma Allah Mai ji ne, Masani. = --Qur'an 3:121
    When two parties among you were about to lose courage, but Allah was their ally; and upon Allah the believers should rely. <> A lõkacin da ƙungiyõyi biyu daga gare ku suka yi niyyar su karye, kuma Allah ne Majiɓincinsu, don haka, ga Allah mũminai sai su dogara. = --Qur'an 3:122
    And already had Allah given you victory at [the battle of] Badr while you were few in number. Then fear Allah; perhaps you will be grateful. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Allah Yã taimake ku a Badar, alhãli kuwa kunã mafiya rauni, sabõda haka ku bi Allah da taƙawa tsammãninku, kuna gõdẽwa. = --Qur'an 3:123
    [Remember] when you said to the believers, "Is it not sufficient for you that your Lord should reinforce you with three thousand angels sent down? <> A lõkacin da kake cẽwa ga mũminai, "Shin bai ishe ku ba, Ubangijinku Ya taimake ku da dubu uku daga malã'iku saukakku?" = --Qur'an 3:124
    Yes, if you remain patient and conscious of Allah and the enemy come upon you [attacking] in rage, your Lord will reinforce you with five thousand angels having marks [of distinction] <> "Na'am! Idan kuka yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, kuma suka zo muku da gaugawarsu, irin wannan, Ubangijinku zai ƙãre ku da dubu biyar daga malãiku mãsu alãma." = --Qur'an 3:125
    And Allah made it not except as [a sign of] good tidings for you and to reassure your hearts thereby. And victory is not except from Allah, the Exalted in Might, the Wise - <> Kuma Allah bai sanya shi ba, fãce dõmin bushãra a gare ku, kuma dõmin zukãtanku su natsu da shi. Taimako bai kasance ba fãce daga wurin Allah, Mabuwãyi, Mai hikima. = --Qur'an 3:126
    That He might cut down a section of the disbelievers or suppress them so that they turn back disappointed. <> Dõmin Ya katse wani gẽfe daga waɗanda suka kãfirta ko kuma Ya ƙasƙantã su, har su jũya, suna mãsu ruɓushi. = --Qur'an 3:127
    Not for you, [O Muhammad, but for Allah], is the decision whether He should [cut them down] or forgive them or punish them, for indeed, they are wrongdoers. <> Bãbu kõme a gare ka game da al'amarin (shiryar da su banda iyar da manzanci). Ko Allah Ya karɓi tũbarsu, kõ kuwa Ya yimusu azãba, to lalle ne sũ, mãsu zãlunci ne. = --Qur'an 3:128
    And to Allah belongs whatever is in the heavens and whatever is on the earth. He forgives whom He wills and punishes whom He wills. And Allah is Forgiving and Merciful. <> Allah ne da mulkin abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, yana gãfarta wa wanda Yake so, kuma yana azabta wanda Yake so, kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 3:129
    O you who have believed, do not consume usury, doubled and multiplied, but fear Allah that you may be successful. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ci riba ninkininki, riɓanye, kuma ku bi Allah da taƙawa, tsammãninku zã ku ci nasara. = --Qur'an 3:130
    And fear the Fire, which has been prepared for the disbelievers. <> Kuma ku ji tsõron wutã wadda aka yi tattali dõmin kãfirai. = --Qur'an 3:131
    And obey Allah and the Messenger that you may obtain mercy. <> Kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, tsammaninku a yi muku rahama. = --Qur'an 3:132
    And hasten to forgiveness from your Lord and a garden as wide as the heavens and earth, prepared for the righteous <> Kuma ku yi gaugawa zuwa ga nẽman gãfara daga Ubangijinku da wata Aljanna wadda fãɗinta (dai dai da) sammai da ƙasa ne, an yi tattalinta dõmin mãsu taƙawa. = --Qur'an 3:133
    Who spend [in the cause of Allah] during ease and hardship and who restrain anger and who pardon the people - and Allah loves the doers of good; <> Waɗanda suke ciyarwa a cikin sauƙi da tsanani kuma suke mãsu haɗiyẽwar fushi, kuma mãsu yãfe wa mutãne laifi. Kuma Allah Yana son mãsu kyautatãwa. = --Qur'an 3:134
    And those who, when they commit an immorality or wrong themselves [by transgression], remember Allah and seek forgiveness for their sins - and who can forgive sins except Allah? - and [who] do not persist in what they have done while they know. <> Kuma waɗanda suke idan suka aikata wata alfãsha ko suka zãlunci kansu sai su tunã da Allah, sabõda su nẽmi gãfarar zunubansu ga Allah. Kuma wãne ne ke gãfara ga zunubai, fãce Allah? Kuma ba su dõge a kan abin da suka aikata ba, alhãli kuwa suna sane. = --Qur'an 3:135
    Those - their reward is forgiveness from their Lord and gardens beneath which rivers flow [in Paradise], wherein they will abide eternally; and excellent is the reward of the [righteous] workers. <> Waɗannan sakamakonsu gãfara ce daga Ubangijinsu, daga Gidajen Aljanna (waɗanda) ƙõramu na gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu. Kuma mãdalla da ijãrar mãsu aiki. = --Qur'an 3:136
    Similar situations [as yours] have passed on before you, so proceed throughout the earth and observe how was the end of those who denied. <> Lalle ne misãlai sun shũɗe a gabãninku, sai ku yi tafiya a cikin ƙasa sa'an nan ku dũba, yãyã ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance. = --Qur'an 3:137
    This [Qur'an] is a clear statement to [all] the people and a guidance and instruction for those conscious of Allah. <> Wannan bayãni ne ga mutãne, kuma shiryuwa ce da wa'azi ga mãsu taƙawa. = --Qur'an 3:138
    So do not weaken and do not grieve, and you will be superior if you are [true] believers. <> Kuma kada ku yi rauni, kuma kada ku yi baƙin ciki, alhãli kuwa kũ ne mafiya ɗaukaka, idan kun kasance mãsu ĩmãni. = --Qur'an 3:139
    If a wound should touch you - there has already touched the [opposing] people a wound similar to it. And these days [of varying conditions] We alternate among the people so that Allah may make evident those who believe and [may] take to Himself from among you martyrs - and Allah does not like the wrongdoers - <> Idan wani mĩki ya shãfe ku, to, lalle ne, wani mĩki kamarsa ya shãfi mutãnen, kuma waɗancan kwãnaki Muna sarrafa su a tsakãnin mutãne dõmin Allah Ya san waɗanda suka yi ĩmãni kuma Ya sãmi mãsu shahãda daga gare ku. Kuma Allah ba Ya son azzãlumai. = --Qur'an 3:140
    And that Allah may purify the believers [through trials] and destroy the disbelievers. <> Kuma dõmin Allah Ya ɗauraye waɗanda suka yi ĩmãni, kuma Ya ƙõƙe kãfirai. = --Qur'an 3:141
    Or do you think that you will enter Paradise while Allah has not yet made evident those of you who fight in His cause and made evident those who are steadfast? <> Ko kun yi zaton ku shiga Aljanna alhãli kuwa Allah bai bãda sanin waɗanda suka yĩ jihãdi daga gare ku ba, kuma Ya san mãsu haƙuri? = --Qur'an 3:142
    And you had certainly wished for martyrdom before you encountered it, and you have [now] seen it [before you] while you were looking on. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa kun kasance kuna gũrin mutuwa tun a gabãnin ku haɗu da ita, to lalle ne kun gan ta, alhãli kuwa kuna kallo. = --Qur'an 3:143
    Muhammad is not but a messenger. [Other] messengers have passed on before him. So if he was to die or be killed, would you turn back on your heels [to unbelief]? And he who turns back on his heels will never harm Allah at all; but Allah will reward the grateful. <> Kuma Muhammadu bai zama ba face manzo lalle ne manzanni sun shũɗe a gabãninsa. Ashe idan ya mutu ko kuwa aka kashe shi, zã kujũya a kan dugaduganku? To, wanda ya jũya a kan dugadugansa, bã zai cũci Allah da kõme ba. Kuma Allah zai sãka wa mãsu gõdiya. = --Qur'an 3:144
    And it is not [possible] for one to die except by permission of Allah at a decree determined. And whoever desires the reward of this world - We will give him thereof; and whoever desires the reward of the Hereafter - We will give him thereof. And we will reward the grateful. <> Kuma bã ya yiwuwa ga wani rai ya mutu fãce da iznin Allah, wa'adi ne mai ƙayyadadden ajali. Kuma wanda yake nufin sakamakon dũniya Muna bã shi daga gare ta. Kuma wanda ke nufin samakon Lãhira Muna bã shi daga gare ta. Kuma zã Mu sãka wa mãsu godiya. = --Qur'an 3:145
    And how many a prophet [fought and] with him fought many religious scholars. But they never lost assurance due to what afflicted them in the cause of Allah, nor did they weaken or submit. And Allah loves the steadfast. <> Kuma da yawa wani Annabi wanda ya yi yãƙi, akwai jama'a mãsu yawa tãre da shi, sa'an nan ba su yi laushi ba ga abin da ya same su a cikin hanyar Allah, kuma ba su yi rauni ba kuma ba su sad da kai ba. Kuma Allah yana son mãsu haƙuri. = --Qur'an 3:146
    And their words were not but that they said, "Our Lord, forgive us our sins and the excess [committed] in our affairs and plant firmly our feet and give us victory over the disbelieving people." <> Kuma bãbu abin da ya kasance maganarsu fãce faɗarsu cẽwa: "Ya Ubangijinmu! Ka gãfarta mana zunubanmu da ɓarnarmu a cikin al'amarinmu, kuma Ka tabbatar da dugaduganmu, kuma Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai." = --Qur'an 3:147
    So Allah gave them the reward of this world and the good reward of the Hereafter. And Allah loves the doers of good. <> Allah Yã sãka musu da sakamakon dũniya da kuma kyakkyawan sakamakon Lãhira. Kuma Allah yana son mãsu kyautatãwa. = --Qur'an 3:148
    O you who have believed, if you obey those who disbelieve, they will turn you back on your heels, and you will [then] become losers. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi ɗa'aga waɗanda suka kãfirta zã su mayar da ku a kan dugãduganku, har ku jũya kunã mãsu hasãra. = --Qur'an 3:149
    But Allah is your protector, and He is the best of helpers. <> Ã'a, Allah ne Majiɓincinku kuma ShĨ ne Mafi alhẽrin matai maka. = --Qur'an 3:150
    We will cast terror into the hearts of those who disbelieve for what they have associated with Allah of which He had not sent down [any] authority. And their refuge will be the Fire, and wretched is the residence of the wrongdoers. <> Zã Mu jẽfa tsõro a cikin zukãtan waɗanda suka kãfirta sabõda shirkin da suka yi da Allah gãme da abin da bai saukar da wani dalili ba game da shi. Kuma makõmarsu wuta ce, kuma tir da mazaunin azzãlumai! = --Qur'an 3:151
    And Allah had certainly fulfilled His promise to you when you were killing the enemy by His permission until [the time] when you lost courage and fell to disputing about the order [given by the Prophet] and disobeyed after He had shown you that which you love. Among you are some who desire this world, and among you are some who desire the Hereafter. Then he turned you back from them [defeated] that He might test you. And He has already forgiven you, and Allah is the possessor of bounty for the believers. <> Kuma lalle ne haƙĩƙa Allah Yã yi muku gaskiya ga wa'adinSa, a lokacin da kuke kashe su da izninSa har zuwa lõkacin da kuka kãsa, kuma kuka yi jãyayya a cikin al'amarin, kuma kuka sãɓã a bãyan (Allah) Ya nũna muku abin da kuke so. Daga cikinku akwai wanda yake nufin duniya kuma daga cikinku akwai wanda ke nufin Lãhĩra. Sa'an nan kuma Ya jũyar da ku daga gare su, dõmin Ya jarrabe ku. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Ya yãfe muku laifinku. Kuma Allah Ma'abucin falala ne ga mũminai. = --Qur'an 3:152
    [Remember] when you [fled and] climbed [the mountain] without looking aside at anyone while the Messenger was calling you from behind. So Allah repaid you with distress upon distress so you would not grieve for that which had escaped you [of victory and spoils of war] or [for] that which had befallen you [of injury and death]. And Allah is [fully] Acquainted with what you do. <> A lõkacin da kuke hawan dũtse, gudãne. Kuma ba ku karkata a kan kõwa ba, alhãli kuwa Manzon Allah nã kiran ku a cikin na ƙarshenku. Sa'an nan (Allah) Ya sãkã muku da baƙin ciki a tãre da wani baƙin ciki. Domin kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, kuma kada ku yi baƙin cikin a kan abin da ya sãme ku. Kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa. = --Qur'an 3:153
    Then after distress, He sent down upon you security [in the form of] drowsiness, overcoming a faction of you, while another faction worried about themselves, thinking of Allah other than the truth - the thought of ignorance, saying, "Is there anything for us [to have done] in this matter?" Say, "Indeed, the matter belongs completely to Allah." They conceal within themselves what they will not reveal to you. They say, "If there was anything we could have done in the matter, some of us would not have been killed right here." Say, "Even if you had been inside your houses, those decreed to be killed would have come out to their death beds." [It was] so that Allah might test what is in your breasts and purify what is in your hearts. And Allah is Knowing of that within the breasts. <> Sa'an nan kuma (Allah) Ya saukar da wani aminci a gare ku daga bãyan baƙin cikin; gyangyaɗi yanã rufe wata ƙungiya daga gare ku, kuma wata ƙungiya, lalle ne, rãyukansu sun shagaltar da su, suna zaton abin da bã shi ne gaskiya ba, a game da Allah, irin zaton jahiliyya, suna cẽwa: "Ko akwai waniabu a gare mu dai daga al'amarin?" Ka ce, "Lalle ne al'amari dukansa na Allah ne." Suna ɓõyẽwa a cikin zukatansu, abin da bã su bayyana shi a gare ka. Suna cẽwa: "Da munã da wani abu daga al'amarin dã ba a kashe mu ba a nan."Ka ce: "Kõ dã kun kasance a cikin gidãjenku, dã waɗanda aka rubũta musu kisa sun fita zuwa ga wurãren kwanciyarsu;" kuma (wannan abu yã auku ne) dõmin Allah Ya jarrabi abin da ke cikin ƙirãzanku. Kuma dõmin Ya tsarkake abin da ke cikin zukãtanku. Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza. = --Qur'an 3:154
    Indeed, those of you who turned back on the day the two armies met, it was Satan who caused them to slip because of some [blame] they had earned. But Allah has already forgiven them. Indeed, Allah is Forgiving and Forbearing. <> Lalle ne waɗanda suka jũya daga gare ku a ranar haɗuwar jama'a biyu, shaiɗan kawai ne ya talãlãɓantar da su, sabõda sãshen abin da suka tsirfanta. Kuma lalle ne haƙĩƙa, Allah Ya yãfe laifidaga gare su. Lalle Allah ne Mai gãfara Mai haƙuri. = --Qur'an 3:155
    O you who have believed, do not be like those who disbelieved and said about their brothers when they traveled through the land or went out to fight, "If they had been with us, they would not have died or have been killed," so Allah makes that [misconception] a regret within their hearts. And it is Allah who gives life and causes death, and Allah is Seeing of what you do. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku kasance kamar waɗanda suka kãfirta kuma suka ce wa'yan'uwansu idan, sun yi tafiya a cikin ƙasa kõ kuwa suka kasance a wurin yãƙi: "Dã sun kasance a wurinmu dã ba su mutun ba, kuma dã ba a, kashe su ba." (Wannan kuwa) Dõmin Allah Ya sanya waccan magana ta zama nadãma a cikin zukãtansu. Kuma Allah ne Yake rãyarwa kuma Yake matarwa. Kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Mai gani ne. = --Qur'an 3:156
    And if you are killed in the cause of Allah or die - then forgiveness from Allah and mercy are better than whatever they accumulate [in this world]. <> Kuma lalle ne idan aka kashe, ku a cikin hanyar Allah, ko kuwa kuka mutu, haƙĩƙa, gãfara daga Allah da rahama ne mafi alhẽri daga abin da suke tãrãwa. = --Qur'an 3:157
    And whether you die or are killed, unto Allah you will be gathered. <> Kuma lalle ne idan kun mutu ko kuwa aka kashe ku, haƙĩƙa, zuwa ga Allah ake tãra ku. = --Qur'an 3:158
    So by mercy from Allah, [O Muhammad], you were lenient with them. And if you had been rude [in speech] and harsh in heart, they would have disbanded from about you. So pardon them and ask forgiveness for them and consult them in the matter. And when you have decided, then rely upon Allah. Indeed, Allah loves those who rely [upon Him]. <> Sabõda wata rahama ce daga Allah ka yi sanyin hali a gare su. Kuma dã kã kasance mai hushi mai kaurin zuciya, dã sun wãtse daga gẽfenka. Sai ka yãfe musu laifinsu, kuma ka nẽma musu gãfara, kuma ka yi shãwara da su a cikin al'amarin. Sa'an nan kuma idan ka yi niyyar zartarwa, to, ka dõgara ga Allah, lalle ne, Allah Yana son mãsu tawakkali. = --Qur'an 3:159
    If Allah should aid you, no one can overcome you; but if He should forsake you, who is there that can aid you after Him? And upon Allah let the believers rely. <> Idan Allah Ya taimake ku, to, bãbu marinjayi a gare ku. Kuma idan Ya yarɓe ku, to, wãnẽ ne wanda yake taimakon ku bãyanSa? Kuma ga Allah sai mũminai su dõgara. = --Qur'an 3:160
    It is not [attributable] to any prophet that he would act unfaithfully [in regard to war booty]. And whoever betrays, [taking unlawfully], will come with what he took on the Day of Resurrection. Then will every soul be [fully] compensated for what it earned, and they will not be wronged. <> Kuma bã ya yiwuwa ga wani annabi ya ci gulũlu. Wanda ya ci gulũlu zai je da abin da ya ci na gulũlun, a Rãnar ¡iyama. Sa'an nan a cika wa kõwane rai sakamakon abin da ya tsirfanta. Kuma sũ, bã zã a zãlunce su ba. = --Qur'an 3:161
    So is one who pursues the pleasure of Allah like one who brings upon himself the anger of Allah and whose refuge is Hell? And wretched is the destination. <> Shin fa, wanda ya bĩbiyi yardar Allah, yana zama kamar wanda ya kõma da fushi daga Allah kuma makomarsa Jahannama ce? Kuma tir da makõma ita! = --Qur'an 3:162
    They are [varying] degrees in the sight of Allah, and Allah is Seeing of whatever they do. <> Sũ, darajõji ne a wurin Allah, kuma Allah Mai gani ne ga abin da suke aikatawa. = --Qur'an 3:163
    Certainly did Allah confer [great] favor upon the believers when He sent among them a Messenger from themselves, reciting to them His verses and purifying them and teaching them the Book and wisdom, although they had been before in manifest error. <> Lalle ne haƙĩƙa Allah Yã yi babbar falala a kan mũminai, dõmin Yã aika a cikinsu, Manzo daga ainihinsu yana karanta ãyõyinSa a gare su, kuma yana tsar kake su, kuma yana karantar da su Littãfi da hikima kuma lalle, sun kasance daga gabãni, haƙĩƙa suna cikin ɓata bayyananniya. = --Qur'an 3:164
    Why [is it that] when a [single] disaster struck you [on the day of Uhud], although you had struck [the enemy in the battle of Badr] with one twice as great, you said, "From where is this?" Say, "It is from yourselves." Indeed, Allah is over all things competent. <> Shin kuma a lõkacin da wata masĩfa, haƙĩƙa, ta sãme ku alhãli kuwa kun sãmar da biyunta, kun ce: "Daga ina wannan yake?" Ka ce: "Daga wurin rãyukanku yake." Lalle ne, Allah, a kan dukan kõme, Mai ĩkon yi ne. = --Qur'an 3:165
    And what struck you on the day the two armies met was by permission of Allah that He might make evident the [true] believers. <> Kuma abin da ya sãme ku a rãnar haɗuwar jama'a biyu, to, da izinin Allah ne, kuma dõmin (Allah) Ya san mũminai (na gaskiya). = --Qur'an 3:166
    And that He might make evident those who are hypocrites. For it was said to them, "Come, fight in the way of Allah or [at least] defend." They said, "If we had known [there would be] fighting, we would have followed you." They were nearer to disbelief that day than to faith, saying with their mouths what was not in their hearts. And Allah is most Knowing of what they conceal - <> Kuma dõmin Ya san waɗanda suka yi munãfunci, kuma an ce musu: "Ku zo ku yi yãƙi a cikin hanyar Allah, kõ kuwa ku tunkuɗe." Suka ce: "Dã mun san (yadda ake) yãƙi dã mun bĩ ku." Sũ zuwa ga kãfirci a rãnar nan, sun fi kusa daga gare su zuwa ga ĩmãni. Sunã cẽwa da bãkunansu abin da bã shi ne a cikin zukãtansu ba. Allah ne Mafi sani ga abin da suke ɓõyewa. = --Qur'an 3:167
    Those who said about their brothers while sitting [at home], "If they had obeyed us, they would not have been killed." Say, "Then prevent death from yourselves, if you should be truthful." <> Waɗanda suka ce wa 'yan'uwansu kuma suka zauna abinsu: "Dã sun yi mana ɗã'a, dã ba a kashe su ba." Ka ce: "To, ku tunkuɗe mutuwa daga rãyukanku, idan kun kasance mãsu gaskiya." = --Qur'an 3:168
    And never think of those who have been killed in the cause of Allah as dead. Rather, they are alive with their Lord, receiving provision, <> Kada ka yi zaton waɗanda aka kashe a cikin hanyar Allah matattu ne. A'a, rãyayyu ne su, a wurin bangijinsu. Ana ciyar da su. = --Qur'an 3:169
    Rejoicing in what Allah has bestowed upon them of His bounty, and they receive good tidings about those [to be martyred] after them who have not yet joined them - that there will be no fear concerning them, nor will they grieve. <> Suna mãsu farin ciki sabõda abin da Allah Ya bã su daga falalarSa, kuma suna yin bushãra ga waɗanda ba su risku da su ba, daga bayansu; "Bãbu tsõro a kansu kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba." = --Qur'an 3:170
    They receive good tidings of favor from Allah and bounty and [of the fact] that Allah does not allow the reward of believers to be lost - <> Suna yin bushãra sabõda wata ni'ima daga Allah da wata falala. Kuma lalle ne, Allah bã Ya tozartar da ijãrar mũminai. = --Qur'an 3:171
    Those [believers] who responded to Allah and the Messenger after injury had struck them. For those who did good among them and feared Allah is a great reward - <> Waɗanda suka karɓa kira zuwa ga Allah da ManzonSa, daga bãyan mĩki ya sãme su. Akwai wata lãda mai girma ga waɗanda suka kyautata yi daga gare su, kuma suka yi taƙawa. = --Qur'an 3:172
    Those to whom hypocrites said, "Indeed, the people have gathered against you, so fear them." But it [merely] increased them in faith, and they said, "Sufficient for us is Allah, and [He is] the best Disposer of affairs." <> Waɗanda mutãne suka ce musu: "Lalle ne, mutãne sun tãra (rundunõni) sabõda ku, don haka ku ji tsõrnsu. Sai (wannan magana) ta ƙara musu ĩmãni, kuma suka ce: "Mai isarmu Allah ne kuma mãdalla da wakili Shĩ." = --Qur'an 3:173
    So they returned with favor from Allah and bounty, no harm having touched them. And they pursued the pleasure of Allah, and Allah is the possessor of great bounty. <> Sa'an nan sukajũya da wata ni'ima daga Allah da wata falala, wata cũta ba ta shãfe su ba, kuma suka bi yardar Allah. Kuma Allah ne Ma'abucin falala Mai girma. = --Qur'an 3:174
    That is only Satan who frightens [you] of his supporters. So fear them not, but fear Me, if you are [indeed] believers. <> Wancan, Shaiɗan ne kawai yake tsõratar da, ku masõyansa. To, kada ku ji tsõronsu ku ji tsõro Na idãn kun kasance mãsu ĩmãni. = --Qur'an 3:175
    And do not be grieved, [O Muhammad], by those who hasten into disbelief. Indeed, they will never harm Allah at all. Allah intends that He should give them no share in the Hereafter, and for them is a great punishment. <> Kuma waɗannan da suke gaugãwa a cikin kãfirci kada su ɓãta maka rai. Lalle ne su, bã zã su cũci Allah da kõme ba. Allah yanã nufin cẽwa, bã zai sanya musu wani rabo ba a cikin Lãhira kuma suna da wata azãba mai girma. = --Qur'an 3:176
    Indeed, those who purchase disbelief [in exchange] for faith - never will they harm Allah at all, and for them is a painful punishment. <> Lalle ne, waɗanda suka sayi kãfirci da ĩmani, ba zã su cũci Allah da kõme ba. Koma sunã da azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 3:177
    And let not those who disbelieve ever think that [because] We extend their time [of enjoyment] it is better for them. We only extend it for them so that they may increase in sin, and for them is a humiliating punishment. <> Kuma kada waɗanda suka kãfirta su yi zaton cẽwa, lalle ne jinkirin da Muke yi musu alhẽri ne ga rãyukansu. Munã yi musu jinkirin ne dõmin su ƙãra laifi kawai kuma suna da azãba mai wulãƙantarwa. = --Qur'an 3:178
    Allah would not leave the believers in that [state] you are in [presently] until He separates the evil from the good. Nor would Allah reveal to you the unseen. But [instead], Allah chooses of His messengers whom He wills, so believe in Allah and His messengers. And if you believe and fear Him, then for you is a great reward. <> Allah bai kasance yana barin mũminai a kan abin da kuke kansa ba, sai Ya rarrabe mummũna daga mai kyau. Kuma Al lah bai kasance Yanã sanar da ku gaibi ba. Kuma amma Allah Yana zãɓen wanda Ya so daga manzanninSa. Sabõda haka ku yi ĩmãni da Allah da manzanninSa Kuma idan kun yi ĩmãni kuma kuka yi taƙawa, to, kunã da lãdã mai girma. = --Qur'an 3:179
    And let not those who [greedily] withhold what Allah has given them of His bounty ever think that it is better for them. Rather, it is worse for them. Their necks will be encircled by what they withheld on the Day of Resurrection. And to Allah belongs the heritage of the heavens and the earth. And Allah, with what you do, is [fully] Acquainted. <> Kuma kada waɗannan da suke yin rõwa da abin da Allah Ya bã su daga falalarSa su yi zaton shĩ ne mafi alhẽri a gare su A'a, shĩ mafi sharri ne a gare su. Zã a yi musu saƙandami da abin da suka yi rõwa da Shi a Rãnar ¡iyãma Kuma ga Allah gãdon sammai da ƙasa yake, kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Masani ne. = --Qur'an 3:180
    Allah has certainly heard the statement of those [Jews] who said, "Indeed, Allah is poor, while we are rich." We will record what they said and their killing of the prophets without right and will say, "Taste the punishment of the Burning Fire. <> Lalle ne, haƙĩƙa Allah Yã ji maganar waɗanda suka ce: "Lalle ne, Allah faƙĩri ne, mũ ne wadãtattu." za mu rubũta abin da suka faɗa, da kisan da suka yi wa Annabãwa bã da wani haƙƙi ba kuma Mu ce: "Ku ɗanɗani azãbar gõbara! = --Qur'an 3:181
    That is for what your hands have put forth and because Allah is not ever unjust to [His] servants." <> "Wannan (azãbar) kuwa sabõda abin da hannuwanku suka gabãtar ne. Kuma lalle ne Allah bai zama mai zãlunci ga bãyinsa ba." = --Qur'an 3:182
    [They are] those who said, "Indeed, Allah has taken our promise not to believe any messenger until he brings us an offering which fire [from heaven] will consume." Say, "There have already come to you messengers before me with clear proofs and [even] that of which you speak. So why did you kill them, if you should be truthful?" <> Waɗanda suka ce: "Lalle ne Allah Yã yi alkawari zuwa gare mu, kada mu yi ĩmãni sabõda wani Manzo sai yã zo mana da Baiko wadda wuta za ta ci." Ka ce: "Lalle ne wasu manzanni sun je muku, a gabãnĩna, da hujjõji bayyanannu, kuma da abin da kuka faɗa, to, don me kuka kashe su, idan kun kasance mãsu gaskiya?" = --Qur'an 3:183
    Then if they deny you, [O Muhammad] - so were messengers denied before you, who brought clear proofs and written ordinances and the enlightening Scripture. <> To, idan sun ƙaryata ka, to lalle ne, an ƙaryata wasu manzanni a gabãninka, sun je musu da hujjõji bayyanannu da littattafai, da kuma Littafi mai haske. = --Qur'an 3:184
    Every soul will taste death, and you will only be given your [full] compensation on the Day of Resurrection. So he who is drawn away from the Fire and admitted to Paradise has attained [his desire]. And what is the life of this world except the enjoyment of delusion. <> Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma ana cika muku ijãrõrinku kawai ne a Rãnar ¡iyãma. To, wanda aka nĩsantar daga barin wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to, lalle ne yã tsĩra. Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba fãce jin dãɗin rũɗi. = --Qur'an 3:185
    You will surely be tested in your possessions and in yourselves. And you will surely hear from those who were given the Scripture before you and from those who associate others with Allah much abuse. But if you are patient and fear Allah - indeed, that is of the matters [worthy] of determination. <> Lalle ne zã a jarraba ku a cikin dũkiyarku da rãyukanku, kuma lalle ne kuna jin cũtarwa mai yawa daga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku da kuma waɗanda suka yi shirki. Kuma idan kun yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, to lalle ne, wannan yana daga manyan al'amurra. = --Qur'an 3:186
    And [mention, O Muhammad], when Allah took a covenant from those who were given the Scripture, [saying], "You must make it clear to the people and not conceal it." But they threw it away behind their backs and exchanged it for a small price. And wretched is that which they purchased. <> Kuma a lõkacin da Allah Ya riƙi alkawarin waɗanda aka bai wa Littãfi, "Lalle ne kuna bayyana shi ga mutãne, kuma bã zã ku ɓõye shi ba." Sai suka jẽfarda shi a bãyan bãyansu, kuma suka sayi 'yan kuɗi kaɗan da shi. To, tir da abin da suke saye! = --Qur'an 3:187
    And never think that those who rejoice in what they have perpetrated and like to be praised for what they did not do - never think them [to be] in safety from the punishment, and for them is a painful punishment. <> Kada lalle ka yi zaton waɗanda suke yin farin ciki da abin da suka bãyar, kuma suna son a yabe su da abin da ba su aikatã ba. To, kada lalle ka yi zaton su da tsĩra daga azãba. Kuma suna da azãba mai raɗadi. = --Qur'an 3:188
    And to Allah belongs the dominion of the heavens and the earth, and Allah is over all things competent. <> Kuma ga Allah mulkin sammai da ƙasa yake. Kuma Allah, a kan kõme, Mai ĩkon yi ne. = --Qur'an 3:189
    Indeed, in the creation of the heavens and the earth and the alternation of the night and the day are signs for those of understanding. <> Lalle ne, a cikin halittar sammai da ƙasa da sãɓãwar dare da yini akwai ãyõyi ga ma'abũta hankali. = --Qur'an 3:190
    Who remember Allah while standing or sitting or [lying] on their sides and give thought to the creation of the heavens and the earth, [saying], "Our Lord, You did not create this aimlessly; exalted are You [above such a thing]; then protect us from the punishment of the Fire. <> Waɗanda suke ambatar Allah a tsaye da zaune da a kan sãsanninsu, kuma suna tunãni a kan halittar sammai da ƙasa: "Yã Ubangijinmu! Ba Ka halitta wannan a kan banza ba. TsarkinKa! Sabõda haka Ka tsare mu daga azãbar wuta. = --Qur'an 3:191
    Our Lord, indeed whoever You admit to the Fire - You have disgraced him, and for the wrongdoers there are no helpers. <> "Ya Ubangijinmu! Lalle ne Kai, wanda Ka shigar a cikin wuta to, haƙĩƙa, Ka tozarta shi kuma bãbu wasu mataimaka ga azzãlumai. = --Qur'an 3:192
    Our Lord, indeed we have heard a caller calling to faith, [saying], 'Believe in your Lord,' and we have believed. Our Lord, so forgive us our sins and remove from us our misdeeds and cause us to die with the righteous. <> "Yã Ubangijinmu! Lalle ne mũ mun ji Mai kira yanã kira zuwa ga ĩmãni cẽwa, 'Ku yi ĩmãni da Ubangijinku.' Sai muka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu! Sabõda haka Ka gãfarta mana zunubanmu, kuma Ka kankare miyãgun ayyukanmu daga gare mu. Kuma Ka karɓi rãyukanmu tãre da mutãnen kirki. = --Qur'an 3:193
    Our Lord, and grant us what You promised us through Your messengers and do not disgrace us on the Day of Resurrection. Indeed, You do not fail in [Your] promise." <> "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu abin da Ka yi mana wa'adi (alkawari) a kan manzanninKa, kuma kada Ka tozarta mu a Rãnar ¡iyãma. Lalle ne Kai, bã Ka sãɓãwar alkawari." = --Qur'an 3:194
    And their Lord responded to them, "Never will I allow to be lost the work of [any] worker among you, whether male or female; you are of one another. So those who emigrated or were evicted from their homes or were harmed in My cause or fought or were killed - I will surely remove from them their misdeeds, and I will surely admit them to gardens beneath which rivers flow as reward from Allah, and Allah has with Him the best reward." <> Sabõda haka Ubangijinsu Ya karɓa musu cẽwa, "Lallene Nĩ bã zan tozartar da aikin wani mai aiki ba daga gare ku, namiji ne ko kuwa mace, sãshenku daga sãshe. To, waɗanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidãjensu, kuma aka cũtar da su a cikin hanyaTa, kuma suka yi yãƙi, kuma aka kashe su, lalle ne zan kankare musumiyagun ayyukansu, kuma lalle ne zan shigar da su gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙoramu ke gudãna daga ƙarƙashinsu, a kan sakamako daga wurin Allah. Kuma a wurinSa akwai kyakkyawan sakamako. = --Qur'an 3:195
    Be not deceived by the [uninhibited] movement of the disbelievers throughout the land. <> Kada jujjuyawar waɗanda suka kãfirta a cikin garũruwa ta rũɗe ka. = --Qur'an 3:196
    [It is but] a small enjoyment; then their [final] refuge is Hell, and wretched is the resting place. <> Jin dãɗi ne kaɗan sa'an nan makõmarsu Jahannama ce, kuma tir da shimfiɗa ita! = --Qur'an 3:197
    But those who feared their Lord will have gardens beneath which rivers flow, abiding eternally therein, as accommodation from Allah. And that which is with Allah is best for the righteous. <> Amma waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa sunã da Gidãjen Aljanna (waɗabda) ƙoramu ke gudãna a ƙarƙashinsu suna madawwama a cikinsu, a kan, liyãfa daga wurin Allah, kuma abin da ke wurin Allah ne mafi alhẽri ga barrantattu. = --Qur'an 3:198
    And indeed, among the People of the Scripture are those who believe in Allah and what was revealed to you and what was revealed to them, [being] humbly submissive to Allah. They do not exchange the verses of Allah for a small price. Those will have their reward with their Lord. Indeed, Allah is swift in account. <> Kuma lalle ne daga Mutãnen Littãfi haƙĩƙa akwai wanda yake yin ĩmãnĩ da Allah da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar zuwa gare su, sunã mãsu tawãlu'i ga Allah, bã su sayen tamani kaɗan da ãyõyin Allah. Waɗannan suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu. Lalle ne Allah Mai gaugãwar sakamako da yawa ne. = --Qur'an 3:199
    O you who have believed, persevere and endure and remain stationed and fear Allah that you may be successful. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Ku yi haƙuri kuma ku yi dauriya, kuma ku yi zaman dãko, kuma ku yi taƙawa, tsammãninku zã ku ci nasara. = --Qur'an 3:200
    O mankind, fear your Lord, who created you from one soul and created from it its mate and dispersed from both of them many men and women. And fear Allah, through whom you ask one another, and the wombs. Indeed Allah is ever, over you, an Observer. <> Ya ku mutãne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya halitta, daga gare shi, ma'auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza mãsu yawa da mãtã. Kuma ku bi Allah da taƙawa Wanda kuke rõƙon jũna da (sũnan), shi, da kuma zumunta. Lalle ne Allah Ya kasance, a kanku, Mai tsaro ne. = --Qur'an 4:1
    And give to the orphans their properties and do not substitute the defective [of your own] for the good [of theirs]. And do not consume their properties into your own. Indeed, that is ever a great sin. <> Kuma ku bai wa marãyu dũkiyõyinsu, kuma kada ku musanya mummuna da mai kyau. Kuma kada ku ci dũkiyõyinsu zuwa ga dũkiyõyinku. Lalle shi, yã kasance zunubi ne mai girma. = --Qur'an 4:2
    And if you fear that you will not deal justly with the orphan girls, then marry those that please you of [other] women, two or three or four. But if you fear that you will not be just, then [marry only] one or those your right hand possesses. That is more suitable that you may not incline [to injustice]. <> Kuma idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba a cikin marãyu, to, (akwai yadda zã a yi) ku auri abin da ya yi muku dãɗi daga mãtã; biyu-biyu, da uku-uku, da huɗu-huɗu. Sa'an nan idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba, to, (ku auri) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba. = --Qur'an 4:3
    And give the women [upon marriage] their [bridal] gifts graciously. But if they give up willingly to you anything of it, then take it in satisfaction and ease. <> Kuma ku bai wa mãtã sadãkõkĩnsu da sauƙin bãyarwa. Sa'an nan idan suka yãfe muku wani abu daga gare shi, da dãɗin rai, to, ku ci shi da jin dãɗi da sauƙin haɗiya. = --Qur'an 4:4
    And do not give the weak-minded your property, which Allah has made a means of sustenance for you, but provide for them with it and clothe them and speak to them words of appropriate kindness. <> Kada ku bai wa wãwãye dũkiyarku, wadda Allah Ya sanya ta a gare ku, kunã mãsu tsayuwa (ga gyãranta). Kuma ku ciyar da su a cikinta, kuma ku tufãtar da su, kuma ku gaya musu magana sananniya ta alhẽri. = --Qur'an 4:5
    And test the orphans [in their abilities] until they reach marriageable age. Then if you perceive in them sound judgement, release their property to them. And do not consume it excessively and quickly, [anticipating] that they will grow up. And whoever, [when acting as guardian], is self-sufficient should refrain [from taking a fee]; and whoever is poor - let him take according to what is acceptable. Then when you release their property to them, bring witnesses upon them. And sufficient is Allah as Accountant. <> Kuma ku jarraba marãyu, har a lõkacin da suka isa aure. To, idan kun lura da shiriya daga gare su, to, ku mĩƙa musu dũkiyõyinsu. Kada ku cĩ ta da ɓarna, kuma da gaggawa kãfin su girma. Kuma wanda yake wadãtacce, to, ya kãma kãnsa, kuma wanda yake faƙĩri, to, ya ci, gwargwadon yadda ya kamata. To, idan kun mĩƙa musu dũkiyõyinsu, sai ku shaidar a kansu. Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai bincike. = --Qur'an 4:6
    For men is a share of what the parents and close relatives leave, and for women is a share of what the parents and close relatives leave, be it little or much - an obligatory share. <> Maza suna da rabo daga abin da iyãye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, kuma mãtã suna da rabo daga abin da iyãye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, daga abin da ya ƙaranta daga gare shi kõ kuwa ya yi yawa, rabo yankakke. = --Qur'an 4:7
    And when [other] relatives and orphans and the needy are present at the [time of] division, then provide for them [something] out of the estate and speak to them words of appropriate kindness. <> Kuma idan ma'abũta zumunta da marãyu da matalauta suka halarci rabon, to, ku azurta su daga gare shi, kuma ku faɗa musu magana sananniya ta alhẽri. = --Qur'an 4:8
    And let those [executors and guardians] fear [injustice] as if they [themselves] had left weak offspring behind and feared for them. So let them fear Allah and speak words of appropriate justice. <> Kuma waɗanda suke dã sun bar zuriyya mãsu rauni a bãyansu, zã su ji tsõro a kansu, su yi sauna, sa'an nan su bi Allah da taƙawa, kuma su faɗi magana madaidaiciya. = --Qur'an 4:9
    Indeed, those who devour the property of orphans unjustly are only consuming into their bellies fire. And they will be burned in a Blaze. <> Lalle ne, waɗanda suke cĩn dũkiyar marãyu da zãlunci, to, wuta kawai suke ci a cikin cikkunansu, kuma za su shiga cikin wata wuta mai tsanani. = --Qur'an 4:10
    Allah instructs you concerning your children: for the male, what is equal to the share of two females. But if there are [only] daughters, two or more, for them is two thirds of one's estate. And if there is only one, for her is half. And for one's parents, to each one of them is a sixth of his estate if he left children. But if he had no children and the parents [alone] inherit from him, then for his mother is one third. And if he had brothers [or sisters], for his mother is a sixth, after any bequest he [may have] made or debt. Your parents or your children - you know not which of them are nearest to you in benefit. [These shares are] an obligation [imposed] by Allah. Indeed, Allah is ever Knowing and Wise. <> Allah Yanã yi muku wasiyya a cikin 'ya'yanku; namiji yanã da rabon mãtã biyu. Idan sun kasance mãtã ne fiye da biyu kuwa, to, suna da biyu daga kashi uku ɗin abin da ya bari, kuma idan ta zama guda ce (kawai) to, tana da rabi. Kuma iyãyensa biyu kõwane ɗaya daga cikinsu yanã da ɗaya daga kashi shida ɗin abin da ya bari idan wani rẽshe ya kasance gare shi, to, idan rẽshe bai kasance gare shi ba, kuma iyãyensa ne (kawai) suka gãje shi, to, uwa tanã da sulusi (ɗaya daga cikin kashi uku). Sa'an nan idan 'yan'uwa sun kasance gare shi, to, uwarsa tana da sudusi (ɗaya daga cikin kashi shida) daga bayan wasiyya wadda ya yi kõ kuwa bãshi. Ubanninku da 'yã'yan ku, ba ku sani ba, wannensu ne mafi kusantar amfani, a gare ku. Yankawa daga Allah. Lalle ne, Allah Yã kasance Masani Mai hikima. = --Qur'an 4:11
    And for you is half of what your wives leave if they have no child. But if they have a child, for you is one fourth of what they leave, after any bequest they [may have] made or debt. And for the wives is one fourth if you leave no child. But if you leave a child, then for them is an eighth of what you leave, after any bequest you [may have] made or debt. And if a man or woman leaves neither ascendants nor descendants but has a brother or a sister, then for each one of them is a sixth. But if they are more than two, they share a third, after any bequest which was made or debt, as long as there is no detriment [caused]. [This is] an ordinance from Allah, and Allah is Knowing and Forbearing. <> Kuma kunã da rabin abin da mãtanku na aure suka bari idan rẽshe bai kasance gare su ba. Sa'an nan idan rẽshe ya kasance gare su, to, kunã da rubu'i (ɗaya daga cikin kashi huɗu) daga abin da suka barin, daga bãyan wasiyya wadda suka yi kõ kuma bãshi. (Sũ) kuma suna da rubu'i daga abin da kuka bari idan rẽshe bai kasance ba gare ku, idan kuwa rẽshe ya kasance gare ku, to, sunã da sumuni (ɗaya daga cikin kashi takwas) daga abin da kuka bari, daga bãyan wasiyya wadda kuka yi kõ kuwa bãshi. Idan wani namiji ya kasance ana gãdon sa bisa kalãla, ko kuwa wata mace alhãli kuwa yana da ɗan'uwa kõ 'yar'uwa to, kõwane ɗaya daga cikinsu yana da sudusi (ɗaya daga cikin kashi shida), sai idan sun kasance mafi yawa daga wannan, to, sũ abõkan tãrayya ne a cikinsulusi (ɗaya bisa uku), daga bãyan wasiyya wadda aka yi kõ kuma bãshi. Bã da yana mai cũtarwa ba, ga wasiyya, daga Allah. Kuma Allah Masani ne Mai haƙuri. = --Qur'an 4:12
    These are the limits [set by] Allah, and whoever obeys Allah and His Messenger will be admitted by Him to gardens [in Paradise] under which rivers flow, abiding eternally therein; and that is the great attainment. <> Waɗancan iyãkõkin Allah ne. Wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, (Allah) zai shigar da shi gidãjen Aljanna (waɗanda) ɗõramu suna gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu, kuma wannan shi ne rabo babba. = --Qur'an 4:13
    And whoever disobeys Allah and His Messenger and transgresses His limits - He will put him into the Fire to abide eternally therein, and he will have a humiliating punishment. <> Kuma wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa, kuma ya ƙẽtare iyãkõkinSa, zai shigarda shi wuta, yana madawwami a cikinta, kuma yana da wata azãba mai walãkantarwa. = --Qur'an 4:14
    Those who commit unlawful sexual intercourse of your women - bring against them four [witnesses] from among you. And if they testify, confine the guilty women to houses until death takes them or Allah ordains for them [another] way. <> Kuma waɗanda suka je wa alfãsha daga mãtanku, to, ku nẽmi Shaidar mutãne huɗu daga gare ku a kansu. To, idan sun yi shaida, sai ku tsare su a cikin gidãje har mutuwa ta karɓi rãyukansu, ko kuwa Allah Ya sanya wata hanya a gare su. = --Qur'an 4:15
    And the two who commit it among you, dishonor them both. But if they repent and correct themselves, leave them alone. Indeed, Allah is ever Accepting of repentance and Merciful. <> Kuma waɗanda (mazã biyu) suka je mata daga ku, to, ku cũtar da su, sa'an nan idan sun tũba kuma suka kyautata hãlãyensu, sai ku kau da kai da ga barinsu. Lalle ne Allah Yã kasance Mai kaɓar tũba ne, Mai jin ƙai = --Qur'an 4:16
    The repentance accepted by Allah is only for those who do wrong in ignorance [or carelessness] and then repent soon after. It is those to whom Allah will turn in forgiveness, and Allah is ever Knowing and Wise. <> Abar da take tũba kawai ga Allah, ita ce ga waɗanda suke aikatãwar mugun aiki da jãhilci sa'an nan su tũba nan kusa to, waɗannan Allah Yanã karɓar tũ barsu kuma Allah Yã kasance Masani ne, Mai hikima. = --Qur'an 4:17
    But repentance is not [accepted] of those who [continue to] do evil deeds up until, when death comes to one of them, he says, "Indeed, I have repented now," or of those who die while they are disbelievers. For them We have prepared a painful punishment. <> Bã tũba ba ce ga waɗanda suke aikatãwar mũnanan ayyuka har idan mutuwa ta halarci ɗayansu ya ce: "Lalle ne ni, na tũba yanzu," kuma bã tũba ba ce ga waɗanda suke mutuwa alhãli kuwa sunã kãfi rai Waɗannan mun yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi = --Qur'an 4:18
    O you who have believed, it is not lawful for you to inherit women by compulsion. And do not make difficulties for them in order to take [back] part of what you gave them unless they commit a clear immorality. And live with them in kindness. For if you dislike them - perhaps you dislike a thing and Allah makes therein much good. <> Ku waɗanda suka yi ĩmãni! Bã ya halatta a gare ku, ku gãji mãtã a kan tĩlas kuma kadaku hana su aure dõmin ku tafi da sãshen abin da kuka ba su, fãce idan suka zo da wata alfãsha bayya nanniya kuma ku yi zamantakẽwa da su da alhẽri sa'an nan idan kun ƙĩ su, to akwai tsammãnin ku ƙi wani abu alhãli kuwa Allah Ya sanya wani alhẽri mai yawaa cikinsa. = --Qur'an 4:19
    But if you want to replace one wife with another and you have given one of them a great amount [in gifts], do not take [back] from it anything. Would you take it in injustice and manifest sin? <> Kuma idan kun yi nufin musanya mãta a matsayin wata mãta, alhãli kuwa kun bai wa ɗayarsu ƙinɗari to kada ku karɓi kõme daga gare, shi, shin, zã ku karɓe shi da ƙarya da zunubi bãyyananne? = --Qur'an 4:20
    And how could you take it while you have gone in unto each other and they have taken from you a solemn covenant? <> Kuma yãyã zã ku karɓe shi alhãli kuwa, haƙĩƙa, sãshenkuyã sãdu zuwa ga sãshe, kuma sun riƙi alkawari mai kauri daga gare ku? = --Qur'an 4:21
    And do not marry those [women] whom your fathers married, except what has already occurred. Indeed, it was an immorality and hateful [to Allah] and was evil as a way. <> Kuma kada ku auri abin da ubanninku suka aura daga mãtã, fãce abin da ya shige. Lalle ne shi, ya kasance alfãsha da abin ƙyãma. Kuma ya mũnana ya zama hanya. = --Qur'an 4:22
    Prohibited to you [for marriage] are your mothers, your daughters, your sisters, your father's sisters, your mother's sisters, your brother's daughters, your sister's daughters, your [milk] mothers who nursed you, your sisters through nursing, your wives' mothers, and your step-daughters under your guardianship [born] of your wives unto whom you have gone in. But if you have not gone in unto them, there is no sin upon you. And [also prohibited are] the wives of your sons who are from your [own] loins, and that you take [in marriage] two sisters simultaneously, except for what has already occurred. Indeed, Allah is ever Forgiving and Merciful. <> An haramta muku uwãyenku, da 'yã'yanku, da 'yan'uwanku mãtã, da goggonninku, da innoninku, da 'yã'yan ɗan'uwa, da 'ya'yan 'yar'uwa, da uwãyenku waɗanan da suka shãyar da ku mãma, da 'yan'uwanku mãtã na shan mãma, da uwãyen mãtanku, da agõlolinku waɗanda suke cikin ɗãkunanku daga mãtanku, waɗanda kuka yi duhũli da su, kuma idan ba ku yi duhũli da sũ ba, to, bãbu laifi a kanku, da mãtan 'yã'yanku waɗanda, suke daga tsatsonku, kuma kada ku haɗa tsakanin 'yan'uwa biyu mãtã, fãce abin da ya shige. Lalle ne, Allah Yã kasance Mai gãfara ne Mai jin ƙai. = --Qur'an 4:23
    And [also prohibited to you are all] married women except those your right hands possess. [This is] the decree of Allah upon you. And lawful to you are [all others] beyond these, [provided] that you seek them [in marriage] with [gifts from] your property, desiring chastity, not unlawful sexual intercourse. So for whatever you enjoy [of marriage] from them, give them their due compensation as an obligation. And there is no blame upon you for what you mutually agree to beyond the obligation. Indeed, Allah is ever Knowing and Wise. <> Da tsararrun auren wasu maza, fãce dai abin da hannuwanku suka mallaka. (Ku tsare) Littãfin Allah a kanku. Kuma an halatta muku abin da yake bayan wancan. Ku nẽma da dukiyõyinku, kunã mãsu yin aure, bã mãsu yin zina ba. sa'an nan abin da kuka ji daɗi da shi daga gare su, to, ku bã su ijãrõrinsu bisa farillar sadãki. Bãbu laifia gare ku ga abin da kuka yi yardatayya da shi a bãyan farillar sadãki. Lalle ne Allah Yã kasance Masani ne, Mai hikima. = --Qur'an 4:24
    And whoever among you cannot [find] the means to marry free, believing women, then [he may marry] from those whom your right hands possess of believing slave girls. And Allah is most knowing about your faith. You [believers] are of one another. So marry them with the permission of their people and give them their due compensation according to what is acceptable. [They should be] chaste, neither [of] those who commit unlawful intercourse randomly nor those who take [secret] lovers. But once they are sheltered in marriage, if they should commit adultery, then for them is half the punishment for free [unmarried] women. This [allowance] is for him among you who fears sin, but to be patient is better for you. And Allah is Forgiving and Merciful. <> Kuma wanda bai sãmi wadãta ba daga cikinku bisa ga ya auri 'ya'ya mũminai, to, (ya aura) daga abin da hannuwanku na dãma suka mallaka, daga kuyanginku mũminai. Kuma Allah ne Mafi sani ga ĩmãninku, sãshenku daga sãshe. Sai ku aurẽ su da izinin mutãnensu. Kuma ku bã su ijãrõrinsu bisa ga abin da aka sani, suna mãsu kamun kai bã mãsu zina ba, kuma bã mãsu riƙon abõkai ba. To, idan aka aure su, sai kuma suka zo da wata alfãsha, to, akwai a kansu rabin abin da ko a kan, 'ya'ya daga azãba. wancan (auren kuyanga) ga wanda ya ji tsõron wahala ne daga gare ku. Kuma ku yi haƙuri shi ne mafi alhẽri a gare ku. Kuma Allah Mai gãfara ne Mai jin ƙai. = --Qur'an 4:25
    Allah wants to make clear to you [the lawful from the unlawful] and guide you to the [good] practices of those before you and to accept your repentance. And Allah is Knowing and Wise. <> Allah Yanã nufin Ya bayyana muku, kuma Ya shiryar da ku hanyõyin waɗanda suke a gabãninku kuma Ya karɓi tũbarku. Kuma Allah Masani ne Mai hikima. = --Qur'an 4:26
    Allah wants to accept your repentance, but those who follow [their] passions want you to digress [into] a great deviation. <> Kuma Allah Yanã nufin Ya karɓi tũbarku. Kuma waɗanda suke bin sha'awõyi suna nufin ku karkata, karkata mai girma. = --Qur'an 4:27
    And Allah wants to lighten for you [your difficulties]; and mankind was created weak. <> Allah Yana nufin Ya yi muku sauƙi, kuma an halitta mutum yana mai rauni. = --Qur'an 4:28
    O you who have believed, do not consume one another's wealth unjustly but only [in lawful] business by mutual consent. And do not kill yourselves [or one another]. Indeed, Allah is to you ever Merciful. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ci dũkiyõyinku a tsakãninku da yaudara, fãce idan ya kasance, daga fatauci ne, bisa yardatayya daga gare ku. Kuma kada ku kashe kãnku. Lalle ne Allah Yã kasance, game da ku, Mai jin ƙai ne. = --Qur'an 4:29
    And whoever does that in aggression and injustice - then We will drive him into a Fire. And that, for Allah, is [always] easy. <> Wanda ya aikata wancan bisa ta'adi da zãlunci, to, zã Mu ƙõne shi da Wuta. Kuma wannan yã kasance ga Allah (abu ne) mai sauƙi. = --Qur'an 4:30
    If you avoid the major sins which you are forbidden, We will remove from you your lesser sins and admit you to a noble entrance [into Paradise]. <> Idan kuka nĩsanci manyan abubuwan da ake hana ku aikatãwa, to, zã Mu kankare mũnanan ayyukanku daga gare ku, kuma Mu shigar da ku mashiga ta karimci. = --Qur'an 4:31
    And do not wish for that by which Allah has made some of you exceed others. For men is a share of what they have earned, and for women is a share of what they have earned. And ask Allah of his bounty. Indeed Allah is ever, of all things, Knowing. <> Kuma kada ku yi gurin abin da Allah Ya fifita sãshenku da shi a kan sãshe; maza suna da rabo daga abin da suka tsirfanta, kuma mãtã suna da rabo daga abin da suka tsirfanta. Ku rõƙi Allah daga falalarSa. Lalle ne Allah Yã kasance ga dukkan kõme, Masani. = --Qur'an 4:32
    And for all, We have made heirs to what is left by parents and relatives. And to those whom your oaths have bound [to you] - give them their share. Indeed Allah is ever, over all things, a Witness. <> Kuma ga kõwa, Mun sanya magada daga abin da mahaifa da mafiya kusancin zumunta suka bari. Kuma waɗanda rantsuwõyinku suka ƙulla ku bã su rabonsu. Lalle ne, Allah Yã kasance, a kan dukkan kõme, Mahalarci. = --Qur'an 4:33
    Men are in charge of women by [right of] what Allah has given one over the other and what they spend [for maintenance] from their wealth. So righteous women are devoutly obedient, guarding in [the husband's] absence what Allah would have them guard. But those [wives] from whom you fear arrogance - [first] advise them; [then if they persist], forsake them in bed; and [finally], strike them. But if they obey you [once more], seek no means against them. Indeed, Allah is ever Exalted and Grand. <> Maza mãsu tsayuwa ne a kan mãtã, sabõda abin da Allah Ya fifita sãshensu da shi a kan sãshe kuma sabõda abin da suka ciyar daga dũkiyõyinsu. To, sãlihanmãtã mãsu ɗã'a ne, mãsu tsarẽwa ga gaibi sabõda abin da Allah Ya tsare. Kuma waɗanda kuke tsõron bijirewarsu, to, ku yi musu gargaɗi, kuma ku ƙaurace musu a cikin wurãren kwanciya, kuma ku dõke su. Sa'an nan kuma, idan sun yi muku ɗa'a, to, kada ku nẽmiwata hanya a kansu. Lalle ne Allah Yã kasance Maɗaukaki, Mai girma. = --Qur'an 4:34
    And if you fear dissension between the two, send an arbitrator from his people and an arbitrator from her people. If they both desire reconciliation, Allah will cause it between them. Indeed, Allah is ever Knowing and Acquainted [with all things]. <> Kuma idan kun ji tsõron sãɓãwar tsakãninsu to ku aika da wani mai sulhu daga mutãnensa da wani mai sulhu daga mutãnenta. Idan sun yi nufin gyãrãwa, Allah zai daidaita tsakãninsu (ma'auran). Lalle ne Allah Yã kasance Masani Mai jarrabãwa. = --Qur'an 4:35
    Worship Allah and associate nothing with Him, and to parents do good, and to relatives, orphans, the needy, the near neighbor, the neighbor farther away, the companion at your side, the traveler, and those whom your right hands possess. Indeed, Allah does not like those who are self-deluding and boastful. <> Kuma ku bauta wa Allah kuma kada ku haɗa wani da Shi, kuma ga mahaifa ku yi kyautatãwa, kuma ga ma'abũcin zumunta da marãyu da matalauta, da maƙwabci ma'abũcin kusanta, da maƙwabci manĩsanci, da abõki a gẽfe da ɗan hanya, da abin da hannuwanku na dãma suka mallaka. Lalle ne Allah bã Ya son wanda ya kasance mai tãƙama, mai yawan alfahari. = --Qur'an 4:36
    Who are stingy and enjoin upon [other] people stinginess and conceal what Allah has given them of His bounty - and We have prepared for the disbelievers a humiliating punishment - <> Waɗanda suke yin rõwa, kuma sunã umurnin mutãne da yin rõwa, kuma suna ɓõyewar abin da Allah Ya bã su na falalarSa. Kuma Mun yi tattali, sabõda kãfirai, azãba mai walãkantarwa. = --Qur'an 4:37
    And [also] those who spend of their wealth to be seen by the people and believe not in Allah nor in the Last Day. And he to whom Satan is a companion - then evil is he as a companion. <> Kuma waɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu dõmin nũna wa mutãne, kuma bã su yin ĩmãni da Allah, kuma bã su yin ĩmãnida Rãnar Lãhira kuma wanda Shaiɗan ya kasance abõkin haɗi a gare shi, to, yã mũnana ga abõkinhaɗi. = --Qur'an 4:38
    And what [harm would come] upon them if they believed in Allah and the Last Day and spent out of what Allah provided for them? And Allah is ever, about them, Knowing. <> Kuma mẽne ne a kansu, idan sun yi ĩmãni da Allah, kumada Rãnar Lãhira, kuma sun ciyar da abin da Allah Yã azurtã su, kuma Allah Ya kasance, gare su, Masani? = --Qur'an 4:39
    Indeed, Allah does not do injustice, [even] as much as an atom's weight; while if there is a good deed, He multiplies it and gives from Himself a great reward. <> Lalle ne, Allah bã Ya zãluncin gwargwadon nauyin zarra, idan ta kasance alhẽri ce, zai riɓanya ta, kuma Ya kãwo daga gunsa ijãra mai girma. = --Qur'an 4:40
    So how [will it be] when We bring from every nation a witness and we bring you, [O Muhammad] against these [people] as a witness? <> To, yãyã, idan Mun zo da shaidu daga dukkan al'umma, kuma Muka zo da kai a kan waɗannan, kana mai shaida! = --Qur'an 4:41
    That Day, those who disbelieved and disobeyed the Messenger will wish they could be covered by the earth. And they will not conceal from Allah a [single] statement. <> A rãnar nan, waɗanda suka kãfirta kuma suka sãɓã wa Manzo, sunã gũrin dã an baje ƙasa dasu, kuma bã su ɓõye wa Allah wani labãri. = --Qur'an 4:42
    O you who have believed, do not approach prayer while you are intoxicated until you know what you are saying or in a state of janabah, except those passing through [a place of prayer], until you have washed [your whole body]. And if you are ill or on a journey or one of you comes from the place of relieving himself or you have contacted women and find no water, then seek clean earth and wipe over your faces and your hands [with it]. Indeed, Allah is ever Pardoning and Forgiving. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kusanci salla alhãli kuwa kuna mãsu mãye, sai kun san abin da kuke faɗa kuma haka idan kuna mãsu janaba, fãce mai ƙẽtare hanya, har ku yi wanka. Kuma idan kun kasance majinyata, ko kuwa a kan tafiya ko kuwa wani daga cikinku, idan ya zo daga kãshi, kõ kuwa kun shãfi mãtã ba ku sãmi ruwa ba, to ku nufi, fuskar ƙasa mai kyau, ku yi shãfa ga fuskokinku da hannuwanku. Lalle ne Allah Yã kasance Mai yãfẽwa Mai gãfara. = --Qur'an 4:43
    Have you not seen those who were given a portion of the Scripture, purchasing error [in exchange for it] and wishing you would lose the way? <> Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda aka bai wa rabo daga Littafi, suna sayen ɓata, kuma suna nẽman ku ɓace daga hanya? = --Qur'an 4:44
    And Allah is most knowing of your enemies; and sufficient is Allah as an ally, and sufficient is Allah as a helper. <> Kuma Allah ne Mafi sani ga maƙiyanku, kuma Allah Yã isa Ya zama Majibinci, kuma Yã isa Ya zama Mataimaki. = --Qur'an 4:45
    Among the Jews are those who distort words from their [proper] usages and say, "We hear and disobey" and "Hear but be not heard" and "Ra'ina," twisting their tongues and defaming the religion. And if they had said [instead], "We hear and obey" and "Wait for us [to understand]," it would have been better for them and more suitable. But Allah has cursed them for their disbelief, so they believe not, except for a few. <> Daga waɗanda suka tũba (Yahũdu), akwai wasu sunã karkatar da magana daga wurãrenta suna cẽwa: "Munjiya kuma mun ƙiya, kuma ka jiya a wani wurin jiyãwa, kuma rã'ina (da ma'anar 'ruɓaɓɓe'), ka tsare mu," dõmin karkatarwa da harsunansu, kuma dõmin sũkã a cikin addini. Kuma dã lalle sũ, sun ce: "Mun jiya kuma mun yi ɗa'a, kuma ka saurãra kuma ka dãkata mana," haƙĩƙa, dã ya kasance mafi alhẽri a gare su, kuma mafi daidaita; amma Allah Yã la'anẽ su, sabõda kãfircinsu don haka bã zã su yi ĩmãni ba, sai kaɗan. = --Qur'an 4:46
    O you who were given the Scripture, believe in what We have sent down [to Muhammad], confirming that which is with you, before We obliterate faces and turn them toward their backs or curse them as We cursed the sabbath-breakers. And ever is the decree of Allah accomplished. <> Yã kũ waɗanda aka bai wa Littãfi! Ku yi ĩmãni da abinda Muka saukar, yana mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku, tun gabanin Mu shãfe wasu fuskõki, sa'an nan Mu mayar da su a kan bãyayyakinsu, ko Mu la'ane su kamar yadda Muka la'ani masu Asabar. Kuma umurnin Allah ya kasance abin aikatãwa. = --Qur'an 4:47
    Indeed, Allah does not forgive association with Him, but He forgives what is less than that for whom He wills. And he who associates others with Allah has certainly fabricated a tremendous sin. <> Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki game da Shi, kuma Yana gãfarta abin da yake bãyan wannan ga wanda Yake so, kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne ya ƙirƙiri zunubi mai girma. = --Qur'an 4:48
    Have you not seen those who claim themselves to be pure? Rather, Allah purifies whom He wills, and injustice is not done to them, [even] as much as a thread [inside a date seed]. <> Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke tsarkake kansu? Ã'a, Allah ne Yake tsarkake wanda Yake so. Kuma ba za a zalunce su da zaren gurtsun dabĩno ba. = --Qur'an 4:49
    Look how they invent about Allah untruth, and sufficient is that as a manifest sin. <> Ka dũba yadda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah! Kuma shi ya isa ga zama zunubi bayyananne. = --Qur'an 4:50
    Have you not seen those who were given a portion of the Scripture, who believe in superstition and false objects of worship and say about the disbelievers, "These are better guided than the believers as to the way"? <> Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka bai wa rabõ da ga Littafi suna ĩmãni da gunki da Shaiɗan kuma suna cẽwa ga waɗanda suka kãfirta: "Waɗannan ne mafiya shiriya daga waɗanda suka yi ĩmãni ga hanya"? = --Qur'an 4:51
    Those are the ones whom Allah has cursed; and he whom Allah curses - never will you find for him a helper. <> Waɗannan ne waɗanda Allah Ya la'ane su, kuma wanda Allah Ya la'ana to bã zã ka sãmi mataimaki a gare shi ba. = --Qur'an 4:52
    Or have they a share of dominion? Then [if that were so], they would not give the people [even as much as] the speck on a date seed. <> Ko suna da rabõ ne daga mulki? To, a sa'an nan bã zã su iya bai wa mutãne hancin gurtsun dabino ba. = --Qur'an 4:53
    Or do they envy people for what Allah has given them of His bounty? But we had already given the family of Abraham the Scripture and wisdom and conferred upon them a great kingdom. <> Ko suna hãsadar mutãne ne a kan abin da Allah Ya bã su daga falalarSa? To, lalle ne, Mun bai wa gidan Ibrãhĩm Littãfida hikima kuma Mun bã su mulki mai girma. = --Qur'an 4:54
    And some among them believed in it, and some among them were averse to it. And sufficient is Hell as a blaze. <> To, daga cikinsu akwai wanda ya yi ĩmãni da shi, kuma daga cikinsu akwai wanda ya kange daga gare shi. Kuma yã isa Jahannama ta hũru da shi. = --Qur'an 4:55
    Indeed, those who disbelieve in Our verses - We will drive them into a Fire. Every time their skins are roasted through We will replace them with other skins so they may taste the punishment. Indeed, Allah is ever Exalted in Might and Wise. <> Lalle ne waɗanda suka kãfirta da ayõyinMu za Mu ƙõne su da wuta, kõ da yaushe fãtunsu suka nuna, sai Mu musanya musu wasu fãtun, dõmin su ɗanɗani azãba. Lalle ne Allah Yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima. = --Qur'an 4:56
    But those who believe and do righteous deeds - We will admit them to gardens beneath which rivers flow, wherein they abide forever. For them therein are purified spouses, and We will admit them to deepening shade. <> Kuma waɗanda suka yiĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, zã Mu shigar da su gidãjen Aljanna, (waɗanda) ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã dawwamammu a cikinsu har abada suna da, a cikinsu, mãtan aure mãsu tsarki, Kuma Munã shigar da su a wata inuwa matabbaciyar lumshi. = --Qur'an 4:57
    Indeed, Allah commands you to render trusts to whom they are due and when you judge between people to judge with justice. Excellent is that which Allah instructs you. Indeed, Allah is ever Hearing and Seeing. <> Lalle ne Allah Yanã umurnin ku ku bãyar da amãnõni zuwa ga mãsu sũ. Kuma idan kun yi hukunci a tsakãnin mutãne, ku yi hukunci da ãdalci. Lalle ne Allah mãdalla da abin da Yake yi muku wa'azi da shi. Lalle ne Allah Yã kasance Mai ji ne, Mai gani. = --Qur'an 4:58
    O you who have believed, obey Allah and obey the Messenger and those in authority among you. And if you disagree over anything, refer it to Allah and the Messenger, if you should believe in Allah and the Last Day. That is the best [way] and best in result. <> Yã kũ waɗanda suka yiĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga ManzonSa, da ma'abũta al'amari daga cikinku. Idan kun yi jãyayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kunã ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. wannan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara. = --Qur'an 4:59
    Have you not seen those who claim to have believed in what was revealed to you, [O Muhammad], and what was revealed before you? They wish to refer legislation to Taghut, while they were commanded to reject it; and Satan wishes to lead them far astray. <> Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke riyãwar cẽwa sunã ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka da abin da aka saukar daga gabãninka, sunã nufin su kai ƙãra zuwa ga ¦ãgũtu alhãli kuwa, lalle ne, an umurce su da su kãfirta da shi, kuma Shaiɗan yanã nẽman ya ɓatar da su, ɓatarwa mai nĩsa. = --Qur'an 4:60
    And when it is said to them, "Come to what Allah has revealed and to the Messenger," you see the hypocrites turning away from you in aversion. <> Kuma idan aka ce musu: "Ku zo zuwa ga abin da Allah Ya saukar, kuma zuwa ga Manzo" zã ka ga munãfukai sunã kange mutãne daga gare ka, kangẽwa. = --Qur'an 4:61
    So how [will it be] when disaster strikes them because of what their hands have put forth and then they come to you swearing by Allah, "We intended nothing but good conduct and accommodation." <> To, yaya, idan wata masĩfa ta sãme su, sabõda abin da hannuwansu suka gabãtar sa'an nan kuma su je maka sunã rantsuwa da Allah cẽwa, "Ba mu yi nufin kõme ba sai kyautatawa da daidaitãwa."? = --Qur'an 4:62
    Those are the ones of whom Allah knows what is in their hearts, so turn away from them but admonish them and speak to them a far-reaching word. <> Waɗannan ne waɗanda Allah Ya san abin da ke cikin zukãtansu. Sabõda haka ka kau da kai daga gare su, kuma ka yi musu gargaɗi, kuma ka gaya musu, a cikin sha'anin kansu, magana mai nauyi da fasãha. = --Qur'an 4:63
    And We did not send any messenger except to be obeyed by permission of Allah. And if, when they wronged themselves, they had come to you, [O Muhammad], and asked forgiveness of Allah and the Messenger had asked forgiveness for them, they would have found Allah Accepting of repentance and Merciful. <> Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba fãce dõmin a yi masa ɗã'a da izinin Allah. Kuma dã dai lalle sũ a lõkacin da suka zãlunci kansu, sun zo maka sa'an nan suka nẽmi gãfarar Allah kuma Manzo ya nẽma musu gãfara, haƙĩƙa, dã sun sãmi Allah Mai karɓar tũba Mai jin ƙai. = --Qur'an 4:64
    But no, by your Lord, they will not [truly] believe until they make you, [O Muhammad], judge concerning that over which they dispute among themselves and then find within themselves no discomfort from what you have judged and submit in [full, willing] submission. <> To, a'aha! Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi ĩmãni ba, sai sun yarda da hukuncinka ga abin da ya sãɓa a tsakãninsu, sa'an nan kuma ba su sãmi wani ƙunci a cikin zukãtansu ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama sallamãwa. = --Qur'an 4:65
    And if We had decreed upon them, "Kill yourselves" or "Leave your homes," they would not have done it, except for a few of them. But if they had done what they were instructed, it would have been better for them and a firmer position [for them in faith]. <> Kuma dã dai lalle Mũ, Mun wajabta musu cẽwa, "Ku kashe kanku, ko kuwa ku, fita daga gidãjenku," dã ba su aikata shi ba, fãce kaɗan daga gare su. Kuma dã dai lalle sũ sun aikata abin da ake yi musu gargaɗi da shi, haƙĩƙa, dã yã kasance mafi alhẽri dagagare su, kuma mafi tsanani ga tabbatarwa. = --Qur'an 4:66
    And then We would have given them from Us a great reward. <> Kuma a sa'an nan, haƙĩƙa, dã Mun bã su, lãda mai girma, daga gunMu. = --Qur'an 4:67
    And We would have guided them to a straight path. <> Kuma lalle ne, dã Mun shiryar da su hanya madaidaiciya. = --Qur'an 4:68
    And whoever obeys Allah and the Messenger - those will be with the ones upon whom Allah has bestowed favor of the prophets, the steadfast affirmers of truth, the martyrs and the righteous. And excellent are those as companions. <> Kuma waɗannan da suka yi ɗã'a ga Allah da Mazonsa, to, waɗannan sunã tãre da waɗanda Allah Ya yi ni'ima a kansu, daga annabãwa da mãsu yawan gaskatãwa, da masu shahãda da sãlihai. kuma waɗannan sun kyautatu ga zama abõkan tafiya. = --Qur'an 4:69
    That is the bounty from Allah, and sufficient is Allah as Knower. <> Waccan falalar daga Allah take, kuma Allah Yã isa zama Masani. = --Qur'an 4:70
    O you who have believed, take your precaution and [either] go forth in companies or go forth all together. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku riƙi shirinku sa'an nan ku fitar da hari jama'a, jama'a ko ku fitar da yaƙi gaba ɗaya. = --Qur'an 4:71
    And indeed, there is among you he who lingers behind; and if disaster strikes you, he says, "Allah has favored me in that I was not present with them." <> Kuma lalle ne daga cikinku akwai mai fãsarwa. To idan wata masĩfa ta sãme ku, sai ya ce: "Lalle ne, Allah Ya yi mini ni'ima dõmin ban kasance mahalarci tãre da su ba." = --Qur'an 4:72
    But if bounty comes to you from Allah, he will surely say, as if there had never been between you and him any affection. "Oh, I wish I had been with them so I could have attained a great attainment." <> Kuma lalle ne idan wata falala daga Allah ta sãme ku haƙĩƙa, tabbas, yanã cẽwa, kamar wata sõyayya ba ta kasance a tsakãninku da shi ba: "Yã kaitona! Dã na zama tãre da su dai, dõmin in rabonta da rabõ mai girma!" = --Qur'an 4:73
    So let those fight in the cause of Allah who sell the life of this world for the Hereafter. And he who fights in the cause of Allah and is killed or achieves victory - We will bestow upon him a great reward. <> Sai waɗanda suke sayar da rayuwar dũniya su karɓi ta Lãhira su yi yãƙi, a cikin hanyar Allah. Kuma wanda ya yi yãki a cikin hanyar Allah to a kashe shi ko kuwa ya rinjãya, sa'an nan zã Mu ba shi ijãra mai girma. = --Qur'an 4:74
    And what is [the matter] with you that you fight not in the cause of Allah and [for] the oppressed among men, women, and children who say, "Our Lord, take us out of this city of oppressive people and appoint for us from Yourself a protector and appoint for us from Yourself a helper?" <> Kuma mẽne ne ya sãme ku, bã ku yin yãƙi a cikin hanyar Allah, da waɗanda aka raunanar daga maza da mata da yãra sunã cewa: "Yã Ubangijinmu! Ka fitar da mu daga wannan alƙarya wadda mutãnenta suke da zãlunci, kuma Ka sanya mana majiɓinci daga gunKa, kuma Ka sanya mana mataimaki daga gunKa."? = --Qur'an 4:75
    Those who believe fight in the cause of Allah, and those who disbelieve fight in the cause of Taghut. So fight against the allies of Satan. Indeed, the plot of Satan has ever been weak. <> Waɗanda suka yi ĩmãni, sunã yãki a cikin hanyar Allah, kuma waɗanda suka kãfirta sunã yãƙi a cikin hanyar ¦ãgũtu (Shaiɗan). To, ku yãƙi majiɓintan Shaiɗan. Lalle ne kaidin Shaiɗan yã kasance mai rauni. = --Qur'an 4:76
    Have you not seen those who were told, "Restrain your hands [from fighting] and establish prayer and give zakah"? But then when fighting was ordained for them, at once a party of them feared men as they fear Allah or with [even] greater fear. They said, "Our Lord, why have You decreed upon us fighting? If only You had postponed [it for] us for a short time." Say, The enjoyment of this world is little, and the Hereafter is better for he who fears Allah. And injustice will not be done to you, [even] as much as a thread [inside a date seed]." <> Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka ce musu: "Ku kange hannuwanku, kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka."? To a lõkacin da aka wajabta musu yãƙi sai ga wani ɓangare daga cikinsu sunã tsõron mutãne kamar tsõron Allah kõ kuwa mafi tsanani ga tsõron, kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Don me Ka wajabta yãƙi a kanmu? Me ya hana Ka jinkirta mana zuwa ga wani ajali na kusa?"Ka ce: "Jin dãɗin dũniya kaɗan ne, kuma Lãhira ce mafi alhẽri ga wanda ya yi taƙawa. Kuma bã a zãluntar ku da sĩlĩlin hancin gurtsun dabĩno! = --Qur'an 4:77
    Wherever you may be, death will overtake you, even if you should be within towers of lofty construction. But if good comes to them, they say, "This is from Allah "; and if evil befalls them, they say, "This is from you." Say, "All [things] are from Allah." So what is [the matter] with those people that they can hardly understand any statement? <> "Inda duk kuka kasance, mutuwa zã ta riske ku, kuma kõ da kun kasance ne a cikin gãnuwõyi ingãtattu!"Kuma idan wani alhẽri ya sãme su sai su ce: "Wannan daga wurin Allah ne," kuma idan wata cũta ta sãme su, sai su ce: "Wannan daga gare ka ne."Ka ce: "Dukkansu daga Allah ne." To, me ya sãmi waɗannan mutãne, bã su kusantar fahimtar magana? = --Qur'an 4:78
    What comes to you of good is from Allah, but what comes to you of evil, [O man], is from yourself. And We have sent you, [O Muhammad], to the people as a messenger, and sufficient is Allah as Witness. <> Abin da ya sãme ka daga alhẽri, to, daga Allah yake, kuma abin da ya sãme ka daga sharri, to, daga kanka yake, kuma Mun aike ka zuwa ga mutãne, (kana) Manzo, kuma Allah Yã isa ga zama shaida. = --Qur'an 4:79
    He who obeys the Messenger has obeyed Allah; but those who turn away - We have not sent you over them as a guardian. <> Wanda ya yi ɗã'a ga Manzo, to, haƙĩƙa, yã yi ɗã'a ga Allah. Kuma wanda ya jũya bãya, to, ba Mu aike ka ba don ka zama mai tsaro a kansu. = --Qur'an 4:80
    And they say, "[We pledge] obedience." But when they leave you, a group of them spend the night determining to do other than what you say. But Allah records what they plan by night. So leave them alone and rely upon Allah. And sufficient is Allah as Disposer of affairs. <> Kuma sunã cẽwa, "Dã'a" sa'an nan idan sun fita daga wurinka, sai wata ƙungiya daga cikinsu ta kwãna da niyyar wanin abin da take faɗa, alhãli kuwa Allah na rubũta abin da suke kwãna da niyyarsa. Sabõda haka ka kau da kai daga gare su, kuma ka dõgara ga Allah, kuma Allah Yã isa ya zama wakĩli. = --Qur'an 4:81
    Then do they not reflect upon the Qur'an? If it had been from [any] other than Allah, they would have found within it much contradiction. <> Shin, bã su kula da Alƙur'ãni, kuma dã yã kasance daga wurin wanin Allah haƙĩƙa, dã sun sãmu, a cikinsa, sãɓã wa jũnamai yawa? = --Qur'an 4:82
    And when there comes to them information about [public] security or fear, they spread it around. But if they had referred it back to the Messenger or to those of authority among them, then the ones who [can] draw correct conclusions from it would have known about it. And if not for the favor of Allah upon you and His mercy, you would have followed Satan, except for a few. <> Kuma idan wani al'amari daga aminci ko tsõro ya je musu, sai su wãtsa shi. Dã sun mayar da shi zuwa ga Manzo da ma'abũta al'amari daga gare su, lalle ne, waɗanda suke yin bincikensa, daga gare su, zã su san shi. Kuma bã dõmin falalar Allah bã a kanku da rahamarSa, haƙĩƙa, dã kun bi Shaiɗan fãce kaɗan. = --Qur'an 4:83
    So fight, [O Muhammad], in the cause of Allah; you are not held responsible except for yourself. And encourage the believers [to join you] that perhaps Allah will restrain the [military] might of those who disbelieve. And Allah is greater in might and stronger in [exemplary] punishment. <> Sabõda haka, ka yi yãƙi a cikin hanyar Allah, ba a kallafa maka ba, face a kanka, kuma ka kwaɗaitar da mũminai. Akwai tsammãnin Allah Ya kange gãfin waɗanda suka kãfirta, kuma Allah ne Mafi tsananin gãfi, kuma Mafi tsananin azabtãwa. = --Qur'an 4:84
    Whoever intercedes for a good cause will have a reward therefrom; and whoever intercedes for an evil cause will have a burden therefrom. And ever is Allah, over all things, a Keeper. <> Wanda ya yi cẽto, cẽto mai kyau, zai sãmi rabo daga gare shi, kuma wanda ya yi cẽto, cẽto mummũna, zai sãmi ma'aunidaga gare shi, Kuma Allah Yã kasance, a kan dukkan kõme, Mai ƙayyade lõkaci. = --Qur'an 4:85
    And when you are greeted with a greeting, greet [in return] with one better than it or [at least] return it [in a like manner]. Indeed, Allah is ever, over all things, an Accountant. <> Kuma idan an gaishe ku da wata gaisuwa, to, ku yi gaisuwa da abin da yake mafi kyau daga gare ta, kõ kuwa ku mayar da ita. Kuma Allah Yã kasance a kan dukkan kõme Mai lissãfi. = --Qur'an 4:86
    Allah - there is no deity except Him. He will surely assemble you for [account on] the Day of Resurrection, about which there is no doubt. And who is more truthful than Allah in statement. <> Allah bãbu abin bautawa face Shi. Lalle ne haƙĩƙa Yana tãra ku har zuwa ga Yinin ¡iyãma bãbu shakka a cikinsa. Kuma wãne ne mafi gaskiya daga Allah ga 1ãbãri. = --Qur'an 4:87
    What is [the matter] with you [that you are] two groups concerning the hypocrites, while Allah has made them fall back [into error and disbelief] for what they earned. Do you wish to guide those whom Allah has sent astray? And he whom Allah sends astray - never will you find for him a way [of guidance]. <> To, mẽne ne ya sãme ku a cikin munãfukai kun zama ƙungiya biyu, alhãli kuwa Allah ne Ya mayar da su sabõda abin da suka tsirfanta? Shin, kunã nufin ku shiryar da wanda Allah Ya ɓatar ne? Kuma wanda Allah Ya ɓatar to bã zã ka sãmi wata hanya ba zuwa gare shi. = --Qur'an 4:88
    They wish you would disbelieve as they disbelieved so you would be alike. So do not take from among them allies until they emigrate for the cause of Allah. But if they turn away, then seize them and kill them wherever you find them and take not from among them any ally or helper. <> Suna gũrin ku kãfirta kamar yadda suka kãfirta, dõmin ku kasance daidai. Sabõda haka kada ku riƙi wasu masõya daga cikinsu, sai sun yõ hijira a cikin hanyar Allah. Sa'an nan idan sun jũya, to, ku kãmã su kuma ku kashe su inda duk kuka sãme su. Kuma kada ku riƙi wani masõyi daga gare su ko wani mataimaki. = --Qur'an 4:89
    Except for those who take refuge with a people between yourselves and whom is a treaty or those who come to you, their hearts strained at [the prospect of] fighting you or fighting their own people. And if Allah had willed, He could have given them power over you, and they would have fought you. So if they remove themselves from you and do not fight you and offer you peace, then Allah has not made for you a cause [for fighting] against them. <> Fãce dai waɗanda suke sãduwa zuwa ga wasu mutãne waɗanda a tsakãninku da su akwai alkawari, kõ kuwa waɗanda suke sun je muku (domin) ƙirãzansu sun yi ƙunci ga su yãke ku, kõ su yãƙi mutãnensu. Kuma dã Allah Yã so lalle ne, dã Yã bã su ĩko a kanku, sa'an nan, haƙĩka, su yãke ku. To, idan sun nĩsance ku sa'an nan ba su yãƙe ku ba, kuma suka jẽfa sulhu zuwa gare ku, to, Allah bai sanya wata hanya ba, a gare ku, a kansu. = --Qur'an 4:90
    You will find others who wish to obtain security from you and [to] obtain security from their people. Every time they are returned to [the influence of] disbelief, they fall back into it. So if they do not withdraw from you or offer you peace or restrain their hands, then seize them and kill them wherever you overtake them. And those - We have made for you against them a clear authorization. <> Za ku sãmi wasu sunã nufin su amintar da ku kuma su amintar da mutãnensu, kõ da yaushe aka mayar da su ga fitina, sai a dulmuyã su a cikinta. To, idan ba su nĩsance ku ba, kuma sun jẽfa sulhu zuwa gare ku, kuma sun kange hannuwansu, to, ku kãmã su, kuma ku kashe su inda duk kuka kãmã su, kuma waɗannan, Mun sanya muku dalĩli bayyanannea kansu. = --Qur'an 4:91
    And never is it for a believer to kill a believer except by mistake. And whoever kills a believer by mistake - then the freeing of a believing slave and a compensation payment presented to the deceased's family [is required] unless they give [up their right as] charity. But if the deceased was from a people at war with you and he was a believer - then [only] the freeing of a believing slave; and if he was from a people with whom you have a treaty - then a compensation payment presented to his family and the freeing of a believing slave. And whoever does not find [one or cannot afford to buy one] - then [instead], a fast for two months consecutively, [seeking] acceptance of repentance from Allah. And Allah is ever Knowing and Wise. <> Kuma bã ya kasancẽwa ga mũmini ya kashe wani mũmini, fãce bisa ga kuskure. Kuma wanda ya kashe mũmini bisa ga kuskure, sai ya 'yanta wuya mũmina tare da mĩƙa diyya ga mutãnensa, ãce idan sun bari sadaka. Sa'an nan idan (wanda aka kashe) ya kasance daga wasu mutãne maƙiya a gare ku, kuma shi mũminine, sai ya 'yanta wuya mũmina. Kuma idan ya kasance daga wasu mutãne ne (waɗanda) a tsakãninku da tsakãninsu akwai alkawari, sai ya bãyar da diyya ga mutãnensa, tare da 'yanta wuya mũmina. To, wanda bai sãmi (wuyan ba) sai azumin watanni biyu jẽre, dõmin tũba daga Allah. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima. = --Qur'an 4:92
    But whoever kills a believer intentionally - his recompense is Hell, wherein he will abide eternally, and Allah has become angry with him and has cursed him and has prepared for him a great punishment. <> Kuma wanda ya kashe wani mũmini da ganganci, to, sakamakonsa Jahannama, yana madawwami a cikinta kuma Allah Yã yi fushi a kansa, kuma Ya la'ane shi, kuma Ya yi masa tattalin azãba mai girma. = --Qur'an 4:93
    O you who have believed, when you go forth [to fight] in the cause of Allah, investigate; and do not say to one who gives you [a greeting of] peace "You are not a believer," aspiring for the goods of worldly life; for with Allah are many acquisitions. You [yourselves] were like that before; then Allah conferred His favor upon you, so investigate. Indeed Allah is ever, with what you do, Acquainted. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi tafiya (a cikin ƙasa), dõmin jihãdi, to, ku nẽmi bãyani. Kuma kada ku ce wa wanda ya jĩfa sallama zuwa gare ku: "Bã Musulmi kake ba." Kunã nẽman hãjar rãyuwar dũniya, to, a wurin Allah akwai ganimõmi mãsu yawa. Kamar wannan ne kuka kasance a gabãnin ku musulunta, sa'an nan Allah Ya yi muku falala. Sabõda haka ku zan nẽman bayãni. Lalle ne Allah Yã kasance, ga abin da kuke aikatãwa, Masani. = --Qur'an 4:94
    Not equal are those believers remaining [at home] - other than the disabled - and the mujahideen, [who strive and fight] in the cause of Allah with their wealth and their lives. Allah has preferred the mujahideen through their wealth and their lives over those who remain [behind], by degrees. And to both Allah has promised the best [reward]. But Allah has preferred the mujahideen over those who remain [behind] with a great reward - <> Mãsu zama daga barin yãƙi daga mũminai, wasun ma'abũta larũra da mãsu jihãdi a cikin hanyar Allah da dũkiyõyinsu da rãyukansu, bã su zama daidai. Allah Yã fĩfĩta mãsu jihãdi da dũkiyoyinsu da rãyukansu a kan mãsu zama, ga daraja. Kuma dukansu Allah Yã yi musu alkawari da abu mai kyau. Kuma Allah yã fĩfĩta mãsu jihãdi a kan mãsu zama da lãda mai girma. = --Qur'an 4:95
    Degrees [of high position] from Him and forgiveness and mercy. And Allah is ever Forgiving and Merciful. <> Darajõji daga gare Shi da gãfara da rahama. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 4:96
    Indeed, those whom the angels take [in death] while wronging themselves - [the angels] will say, "In what [condition] were you?" They will say, "We were oppressed in the land." The angels will say, "Was not the earth of Allah spacious [enough] for you to emigrate therein?" For those, their refuge is Hell - and evil it is as a destination. <> Lalle ne, waɗanda malã'ĩku suka karɓi rãyukansu, (alhãli) sunã mãsu zãluntar kansu, sun ce (musu): "A cikin me kuka kasance?" (Su kuma) suka ce: "Mun kasance waɗanda aka raunana a cikin ƙasa." Suka ce: "Ashe ƙasar Allah ba ta kasance mayalwaciya ba, dõmin ku yi hijira a cikinta?" To, waɗannan makõmarsu Jahannama ce. Kuma tã mũnana ta zama makõma. = --Qur'an 4:97
    Except for the oppressed among men, women and children who cannot devise a plan nor are they directed to a way - <> Fãce waɗanda aka raunana daga maza da mãtã da yãra waɗanda bã su iya yin wata dabãra, kuma bã su shiryuwa ga hanya. = --Qur'an 4:98
    For those it is expected that Allah will pardon them, and Allah is ever Pardoning and Forgiving. <> To, waɗannan akwai tsammãnin Allah Ya yãfe laifi daga gare su, kuma Allah Yã kasance Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara. = --Qur'an 4:99
    And whoever emigrates for the cause of Allah will find on the earth many [alternative] locations and abundance. And whoever leaves his home as an emigrant to Allah and His Messenger and then death overtakes him - his reward has already become incumbent upon Allah. And Allah is ever Forgiving and Merciful. <> Kuma wanda ya yi hijira a cikin hanyar Allah, zai sãmu, a cikin ƙasa, wurãren jũyãwa mãsu yawa da yalwa. Kuma wanda ya fita daga gidansa yana mai hijira zuwa ga Allah da ManzonSa, sa'an nan kuma mutuwa ta riske shi, to, lalle ne, lãdarsa tã auku ga Allah, Kuma Allah Yã kasance, a gare ku, Mai gãfara, Mai jin ƙai. = --Qur'an 4:100
    And when you travel throughout the land, there is no blame upon you for shortening the prayer, [especially] if you fear that those who disbelieve may disrupt [or attack] you. Indeed, the disbelievers are ever to you a clear enemy. <> Kuma idan kun yi tafiya a cikin ƙasa to, bãbu laifi a kanku ku rage daga salla idan kun ji tsõron waɗanda suka kãfirta su fitine ku. Lalle ne kãfirai sun kasance, a gare ku, maƙiyi bayyananne. = --Qur'an 4:101
    And when you are among them and lead them in prayer, let a group of them stand [in prayer] with you and let them carry their arms. And when they have prostrated, let them be [in position] behind you and have the other group come forward which has not [yet] prayed and let them pray with you, taking precaution and carrying their arms. Those who disbelieve wish that you would neglect your weapons and your baggage so they could come down upon you in one [single] attack. But there is no blame upon you, if you are troubled by rain or are ill, for putting down your arms, but take precaution. Indeed, Allah has prepared for the disbelievers a humiliating punishment. <> Kuma idan kã kasance a cikinsu, sai ka tsayar musu da salla, to, wata ƙungiya daga gare su ta tsaya tãre da kai, kuma sai su riƙe makãmansu. Sa'an nan idan sun yi salla, to, sai su kasance daga bãyanku. Kuma wata ƙungiya ta dabam (ta) waɗanda ba su yi sallar ba, ta zo, sa'an nan su yi sallar tãre da kai. Kuma su riƙi shirinsu da makãmansu. Waɗanda suka kãfirta sun yi gũrin dã dai kuna shagala daga makamanku da kãyanku dõmin su karkata a kanku, karkata guda. Kuma bãbu laifi, a kanku idan wata cũta daga ruwan sama ta kasance a gare ku, kõ kuwa kun kasance mãsu jinya ga ku ajiye makãmanku kuma dai ku riƙi shirinku. Lalle ne, Allah Yã yi tattali, ga kãfirai, azãba mai walakantarwa. = --Qur'an 4:102
    And when you have completed the prayer, remember Allah standing, sitting, or [lying] on your sides. But when you become secure, re-establish [regular] prayer. Indeed, prayer has been decreed upon the believers a decree of specified times. <> Sa'an nan idan kun ƙãre salla, to ku ambaci Allah tsaye da zaune da a kan sãsanninku. Sa'an nan idan kun natsu, to, ku tsayar da Salla. Lalle ne salla tã kasance a kan mũminai, farilla mai ƙayyadaddun lõkuta. = --Qur'an 4:103
    And do not weaken in pursuit of the enemy. If you should be suffering - so are they suffering as you are suffering, but you expect from Allah that which they expect not. And Allah is ever Knowing and Wise. <> Kuma kada ku sassauta a cikin nẽman mutãnen idankun kasance kuna jin zõgi, to, lalle sũ ma, suna jin zõgi kamar yadda kuke jin zõgi. Kuma kuna tsammãni, daga Allah, abin da bã su tsammãni. Kuma Allah Yã kasance Masani Mai hikima. = --Qur'an 4:104
    Indeed, We have revealed to you, [O Muhammad], the Book in truth so you may judge between the people by that which Allah has shown you. And do not be for the deceitful an advocate. <> Lalle ne, Mũ, Mun saukar, zuwa gare ka, Littãfi da gaskiya, dõmin ka yi hukunci a tsakãnin mutãne da abin da Allah Ya nũna maka, kuma kada ka kasance mai husũma dõmin mãsu yaudara. = --Qur'an 4:105
    And seek forgiveness of Allah. Indeed, Allah is ever Forgiving and Merciful. <> Kuma ka nẽmi Allah gãfara. Lalle ne Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai. = --Qur'an 4:106
    And do not argue on behalf of those who deceive themselves. Indeed, Allah loves not one who is a habitually sinful deceiver. <> Kuma kada ka yi jãyayya dõmin tunkuɗe wa waɗanda suka yaudari kansu. Lalle ne Allah ba Ya son wanda ya kasance mai yawan hã'inci mai yawan zunubi. = --Qur'an 4:107
    They conceal [their evil intentions and deeds] from the people, but they cannot conceal [them] from Allah, and He is with them [in His knowledge] when they spend the night in such as He does not accept of speech. And ever is Allah, of what they do, encompassing. <> Suna nẽman ɓõyewa daga mutãne kuma bã su nẽmanɓõyewa daga Allah, alhãli kuwa Shi Yana tãre da su a lõkacin da suke kwãna da niyyar yin abin da bã Ya yarda da shi daga maganar. Kuma Allah Yã kasance ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa. = --Qur'an 4:108
    Here you are - those who argue on their behalf in [this] worldly life - but who will argue with Allah for them on the Day of Resurrection, or who will [then] be their representative? <> Gã ku, yã waɗannan! Kun yi jidãli, dõmin tunkuɗe musu (kunya) a cikin rãyuwar dũniya, to, wane ne zai yi jidali domin tunkuɗe musu a Rãnar ¡iyãma? Ko kuwa wãne ne zai kasance wakĩli a kansu? = --Qur'an 4:109
    And whoever does a wrong or wrongs himself but then seeks forgiveness of Allah will find Allah Forgiving and Merciful. <> Kuma wanda ya aikata cũta kõ kuwa ya zãlunci kansa, sa'an nan kuma ya nẽmi Allah gãfara, zai sãmi Allah Mai gãfara, Mai jin ƙai. = --Qur'an 4:110
    And whoever commits a sin only earns it against himself. And Allah is ever Knowing and Wise. <> Kuma wanda ya yi tsirfanci zunubi, to yanã tsirfarsa ne a kan kansa kawai. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima. = --Qur'an 4:111
    But whoever earns an offense or a sin and then blames it on an innocent [person] has taken upon himself a slander and manifest sin. <> Kuma wanda ya yi tsiwirwirin kuskure ko kuwa zunubi sa'an nan kuma ya jẽfi wani barrantacce da shi, to, lalle ne yã tattali ƙirƙiren ƙarya da zunubi bayyananne. = --Qur'an 4:112
    And if it was not for the favor of Allah upon you, [O Muhammad], and His mercy, a group of them would have determined to mislead you. But they do not mislead except themselves, and they will not harm you at all. And Allah has revealed to you the Book and wisdom and has taught you that which you did not know. And ever has the favor of Allah upon you been great. <> Kuma bã dõmin falalar Allah ba, a kanka, da rahamarSa, haƙĩƙa, dã wata ƙungiya daga gare su ta himmatu ga su ɓatar da kai. Kuma bã su ɓatarwa fãce kansu, kuma bã su cũtar ka daga kõme, Kuma Allah Yã saukar da Littãfi da hikima gare ka, kuma Ya sanar da kai abin da ba ka kasance kã sani ba. Kuma falalar Allah tã kasance mai girma a gare ka. = --Qur'an 4:113
    No good is there in much of their private conversation, except for those who enjoin charity or that which is right or conciliation between people. And whoever does that seeking means to the approval of Allah - then We are going to give him a great reward. <> Bãbu wani alhẽri a cikin mãsu yawa daga gãnawarsu fãce wanda ya yi umurni da wata sadaka kõ kuwa wani alhẽri kõ kuwa gyãra a tsakãnin mutãne. Wanda ya aikata haka dõmin nẽman yardõdin Allah to zã Mu bã shi lãda mai girma. = --Qur'an 4:114
    And whoever opposes the Messenger after guidance has become clear to him and follows other than the way of the believers - We will give him what he has taken and drive him into Hell, and evil it is as a destination. <> Kuma wanda ya sãɓã wa Manzo daga bãyan shiriya tã bayyana a gare shi, kuma ya bi wanin hanyar mũminai, zã Mu jiɓintar masa abin da ya jiɓinta, kuma Mu ƙõne shi da Jahannama. Kuma tã mũnana ta zama makõma. = --Qur'an 4:115
    Indeed, Allah does not forgive association with Him, but He forgives what is less than that for whom He wills. And he who associates others with Allah has certainly gone far astray. <> Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki da Shi, kuma Yana gãfarta abin da yake bãyan wannan, ga wanda Yake so. Kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne ya ɓace ɓata mai nĩsa. = --Qur'an 4:116
    They call upon instead of Him none but female [deities], and they [actually] call upon none but a rebellious Satan. <> Bã su kiran kõwa, baicin Shi, fãce mãtã kuma bã su kiran kõwa fãce Shaiɗan, mai tsaurin kai. = --Qur'an 4:117
    Whom Allah has cursed. For he had said, "I will surely take from among Your servants a specific portion. <> Allah Yã la'ane shi. Kuma ya ce: "Lalle ne, zã ni riƙi rabõ yankakke, daga bãyinKa. = --Qur'an 4:118
    And I will mislead them, and I will arouse in them [sinful] desires, and I will command them so they will slit the ears of cattle, and I will command them so they will change the creation of Allah." And whoever takes Satan as an ally instead of Allah has certainly sustained a clear loss. <> "Kuma lalle ne, inã ɓatar da su, kuma lalle ne inã sanya musu gũri, kuma lalle ne ina umurnin su dõmin su kãtse kunnuwan dabbõbi, kuma lalle ne inã umurnin su dõmin su canza halittar Allah." Kuma wanda ya riƙi Shaiɗan majiɓinci, baicin Allah, to, haƙĩƙa yã yi hasara, hasara bayyananniya. = --Qur'an 4:119
    Satan promises them and arouses desire in them. But Satan does not promise them except delusion. <> Yanã yi musu alkawari, kuma yanã sanya musu gũri, alhãli Shaiɗan bã ya yi musu wani wa'adĩn kõme face ruɗi. = --Qur'an 4:120
    The refuge of those will be Hell, and they will not find from it an escape. <> Waɗannan matattararsu Jahannama ce, kuma bã sãmun makarkata daga gare ta. = --Qur'an 4:121
    But the ones who believe and do righteous deeds - We will admit them to gardens beneath which rivers flow, wherein they will abide forever. [It is] the promise of Allah, [which is] truth, and who is more truthful than Allah in statement. <> Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, zã mu shigar da su gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙõramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, sunã mãsu dawwama a cikinsu har abada bisa ga wa'adin Allah tabbatacce. Wãne ne mafi gaskiya daga Allah ga magana? = --Qur'an 4:122
    Paradise is not [obtained] by your wishful thinking nor by that of the People of the Scripture. Whoever does a wrong will be recompensed for it, and he will not find besides Allah a protector or a helper. <> (Al'amari) bai zama gũrace- gũracenku ba, kuma ba gũrace- gũracen Mutãnen Littãfi ba ne. Wanda ya aikata mummunan aiki zã a sãka masa da shi kuma bã zai sãmi wani masõyi ba, baicin Allah, kuma bã zai sãmi mataimaki ba. = --Qur'an 4:123
    And whoever does righteous deeds, whether male or female, while being a believer - those will enter Paradise and will not be wronged, [even as much as] the speck on a date seed. <> Kuma wanda ya yi aiki daga ayyukan ƙwarai, namiji ne ko kuwa mace, alhãli kuwa Yanã mũmini, to, waɗannan sunã shiga Aljanna kuma bã zã a zãlunce su da gwargwadon hancin gurtsun dabĩ no ba. = --Qur'an 4:124
    And who is better in religion than one who submits himself to Allah while being a doer of good and follows the religion of Abraham, inclining toward truth? And Allah took Abraham as an intimate friend. <> Kuma wãne ne ya fi kyau ga addini daga wanda ya sallama fuskarsa ga Allah, alhãli kuwa yanã mai kyautatawa kuma ya bi aƙidar Ibrãhĩm, Yanã mai karkata zuwa ga gaskiya? Allah Yã riƙi Ibrãhĩm badãɗayi. = --Qur'an 4:125
    And to Allah belongs whatever is in the heavens and whatever is on the earth. And ever is Allah, of all things, encompassing. <> Kuma Allah ke da (mallakar) abin da ke cikin sammai da kuma abin da ke cikin ƙasa kuma Allah Yã kasance, a dukkan, kõme, Mai kẽwayewa. = --Qur'an 4:126
    And they request from you, [O Muhammad], a [legal] ruling concerning women. Say, "Allah gives you a ruling about them and [about] what has been recited to you in the Book concerning the orphan girls to whom you do not give what is decreed for them - and [yet] you desire to marry them - and concerning the oppressed among children and that you maintain for orphans [their rights] in justice." And whatever you do of good - indeed, Allah is ever Knowing of it. <> Sunã yi maka fatawa a cikin sha'anin mãtã. Ka ce: "Allah Yanã bayyana fatawarku a cikin sha'aninsu, da abin da ake karantãwa a kanku a cikin Littãfi, a cikin sha'anin marãyun mãtã waɗanda ba ku bã su abin da aka rubũta musu (na gãdo) ba, kuma kunã kwaɗayin ku aurẽ su, da sha'anin waɗanda aka raunana daga yãra, da sha'anin tsayuwarku ga marãyu da ãdalci. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, to, lalle ne, Allah Yã kasance Masani a gare shi." = --Qur'an 4:127
    And if a woman fears from her husband contempt or evasion, there is no sin upon them if they make terms of settlement between them - and settlement is best. And present in [human] souls is stinginess. But if you do good and fear Allah - then indeed Allah is ever, with what you do, Acquainted. <> Kuma idan wata mace ta ji tsõron ƙiyo daga mijinta kõ kuwa bijirẽwa to, bãbu laifi a kansu su yi sulhu a tsakãninsu, sulhu (mai kyau) Kuma yin sulhu ne mafi alhẽri. Kuma an halartar wa rayũka yin rõwa. Kuma idan kun kyautata, kuma kuka yi taƙawa, to, lalle ne, Allah Yã kasance, ga abin da kuke aikatãwa, Masani. = --Qur'an 4:128
    And you will never be able to be equal [in feeling] between wives, even if you should strive [to do so]. So do not incline completely [toward one] and leave another hanging. And if you amend [your affairs] and fear Allah - then indeed, Allah is ever Forgiving and Merciful. <> Kuma bã zã ku iya yin ãdalci ba a tsakanin mãtã kõ dã kun yi kwaɗayin yi. Sabõda haka kada ku karkata, dukan karkata, har ku bar ta kamar wadda aka rãtaye. Kuma idan kun yi sulhu, kuma kuka yi taƙawa, to, lalle ne Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai. = --Qur'an 4:129
    But if they separate [by divorce], Allah will enrich each [of them] from His abundance. And ever is Allah Encompassing and Wise. <> Kuma idan sun rabu, Allah zai wadãtar da kõwanne daga yalwarSa. Kuma Allah Yã kasance Mayalwaci, Mai hikima. = --Qur'an 4:130
    And to Allah belongs whatever is in the heavens and whatever is on the earth. And We have instructed those who were given the Scripture before you and yourselves to fear Allah. But if you disbelieve - then to Allah belongs whatever is in the heavens and whatever is on the earth. And ever is Allah Free of need and Praiseworthy. <> Kuma Allah ne da mulkin abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun yi wasiyya ga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku, da kũ, cẽwa ku bi Allah da taƙawa, kuma idan kun kãfirta, to, lalle ne, Allah Yanã da abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa. Kuma Allah Yã kasance wadãtacce, Gõdadde. = --Qur'an 4:131
    And to Allah belongs whatever is in the heavens and whatever is on the earth. And sufficient is Allah as Disposer of affairs. <> Kuma Allah ne da mulkin abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa, kuma Allah Yã isa Ya zama wakĩli. = --Qur'an 4:132
    If He wills, He can do away with you, O people, and bring others [in your place]. And ever is Allah competent to do that. <> Idan Yã so, zã Ya tafi da ku, yã kũ mutãne! kuma Ya zo da wasu. Allah Yã kasance a kan haka, Mai ĩkon yi ne. = --Qur'an 4:133
    Whoever desires the reward of this world - then with Allah is the reward of this world and the Hereafter. And ever is Allah Hearing and Seeing. <> Wanda ya kasance Yanã nufin sakamakon dũniya, to, a wurin Allah sakamakon dũniya da Lãhira yake. Kuma Allah Yã kasance Mai ji, Mai gani. = --Qur'an 4:134
    O you who have believed, be persistently standing firm in justice, witnesses for Allah, even if it be against yourselves or parents and relatives. Whether one is rich or poor, Allah is more worthy of both. So follow not [personal] inclination, lest you not be just. And if you distort [your testimony] or refuse [to give it], then indeed Allah is ever, with what you do, Acquainted. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayuwa da ãdalci, mãsu shaida sabõda Allah, kuma kõ dã a kanku ne kõ kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida kõ a kansa) ya kasance mawadãci kõ matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al'amarinsu. Sabõda haka, kada ku bĩbiyi son zũciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, kõ kuwa kuka kau da kai, to lalle ne Allah Yã kasance Masani ga abin da kuke aikatãwa. = --Qur'an 4:135
    O you who have believed, believe in Allah and His Messenger and the Book that He sent down upon His Messenger and the Scripture which He sent down before. And whoever disbelieves in Allah, His angels, His books, His messengers, and the Last Day has certainly gone far astray. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ĩmãni da Allah da Manzonsa, da Littãfin da Ya sassaukar ga ManzonSa da Littãfin nan wanda Ya saukar daga gabãni. To, wanda ya kãfirta da Allah da malã'ikunSa, da LittattafanSa, da ManzanninSa, da Rãnar Lãhira, to, lalle ne yã ɓace, ɓata mai nĩsa. = --Qur'an 4:136
    Indeed, those who have believed then disbelieved, then believed, then disbelieved, and then increased in disbelief - never will Allah forgive them, nor will He guide them to a way. <> Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, sa'an nan kuma suka kãfirta, sa'an nan kuma suka yi ĩmani, sa'an nan kuma suka kãfirta sa'an nan kuma suka ƙãra kãfirci, Allah bai kasance Yanã gãfarta musu ba, kuma bã zai shiryar da su ga hanya ba. = --Qur'an 4:137
    Give tidings to the hypocrites that there is for them a painful punishment - <> Ka yi wa munãfukai bushãra da cẽwa lalle ne sunã da azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 4:138
    Those who take disbelievers as allies instead of the believers. Do they seek with them honor [through power]? But indeed, honor belongs to Allah entirely. <> Waɗanda suke riƙon kãfirai masõya, baicin mũminai. Shin sunã nẽman izza ne a wurinsu? To, lalle ne izza ga Allah take gabã ɗaya. = --Qur'an 4:139
    And it has already come down to you in the Book that when you hear the verses of Allah [recited], they are denied [by them] and ridiculed; so do not sit with them until they enter into another conversation. Indeed, you would then be like them. Indeed Allah will gather the hypocrites and disbelievers in Hell all together - <> Kuma lalle ne Yã sassaukar muku a cikin Littãfi cẽwa idan kun ji ãyõyin Allah, anã kãfirta da su, kuma anã izgili da su, to, kada ku zauna tãre da sũ, sai sun shiga cikin wani lãbãri. Lalle ne kũ, a lõkacin nan misãlinsu kuke. Lalle ne, Allah Mai tãra munãfukai da kãfirai ne a cikin Jahannama gabã ɗaya. = --Qur'an 4:140
    Those who wait [and watch] you. Then if you gain a victory from Allah, they say, "Were we not with you?" But if the disbelievers have a success, they say [to them], "Did we not gain the advantage over you, but we protected you from the believers?" Allah will judge between [all of] you on the Day of Resurrection, and never will Allah give the disbelievers over the believers a way [to overcome them]. <> Waɗanda suke jiran dãko game da ku; har idan wata nasara daga Allah ta kasance a gare ku, sai su ce: "Ashe, ba mu kasance tãre da kũ ba?" Kuma idan wani rabo ya sãmu ga kãfirai sai su ce: "Ashe ba mu rinjãye ku ba, kuma muka tsare ku daga mũminai?" To, Allah ne Yake yin hukunci tsakãninku a Rãnar ¡iyãma, kuma Allah bã zai sanya hanya ba ga kãfirai a kan mũminai. = --Qur'an 4:141
    Indeed, the hypocrites [think to] deceive Allah, but He is deceiving them. And when they stand for prayer, they stand lazily, showing [themselves to] the people and not remembering Allah except a little, <> Lalle ne munãfukai sunã yaudarẽwa da Allah, alhãli kuwa Shi ne mai yaudarasu; kuma idan sun tãshi zuwa ga salla, sai su tãshi sunã mãsu kasãla. Suna nũnawa mutãne, kuma ba su ambatar Allah sai kaɗan. = --Qur'an 4:142
    Wavering between them, [belonging] neither to the believers nor to the disbelievers. And whoever Allah leaves astray - never will you find for him a way. <> Mãsu kai-kawo ne a tsakãnin wancan; bã zuwa ga waɗannan ba, kuma bã zuwa ga waɗannan ba. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã za ka sãmar masa wata hanya ba. = --Qur'an 4:143
    O you who have believed, do not take the disbelievers as allies instead of the believers. Do you wish to give Allah against yourselves a clear case? <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi kãfirai masõya, baicin mũminai. Shin, kanã nufin ku sanyã wa Allah dalĩli bayyananne a kanku? = --Qur'an 4:144
    Indeed, the hypocrites will be in the lowest depths of the Fire - and never will you find for them a helper - <> Lalle ne, manãfukai sunã a magangara mafi ƙasƙanci daga wuta. Kuma bã zã ka sãma musu mataimaki ba. = --Qur'an 4:145
    Except for those who repent, correct themselves, hold fast to Allah, and are sincere in their religion for Allah, for those will be with the believers. And Allah is going to give the believers a great reward. <> Sai waɗanda suka tũba, kuma suka gyãra, kuma suka nẽmi fakuwa ga Allah, kuma suka tsarkake addininsu dõmin Allah, to, waɗannan sunã tãre da mũminai, kuma Allah zai bai wa mũminai lãda mai girma. = --Qur'an 4:146
    What would Allah do with your punishment if you are grateful and believe? And ever is Allah Appreciative and Knowing. <> Mẽne ne Allah zai amfãna da yi maku azãba idan kun gõde, kuma kun yi ĩmãni? Allah Yã ksance Mai gõdiya Masani. = --Qur'an 4:147
    Allah does not like the public mention of evil except by one who has been wronged. And ever is Allah Hearing and Knowing. <> Allah bã Ya son bayyanãwa da mũnãna daga magana fãce ga wanda aka zãlunta. Kuma Allah Yã kasance Mai ji, Masani. = --Qur'an 4:148
    If [instead] you show [some] good or conceal it or pardon an offense - indeed, Allah is ever Pardoning and Competent. <> Idan kun bayyana alhẽri, kõ kuwa kuka ɓõye shi, kõ kuwa kuka yãfe laifi daga cũta, to, lalle ne Allah Yã kasance Mai yãfewa, Mai ikon yi. = --Qur'an 4:149
    Indeed, those who disbelieve in Allah and His messengers and wish to discriminate between Allah and His messengers and say, "We believe in some and disbelieve in others," and wish to adopt a way in between - <> Lalle ne, waɗanda uke kãfirta da Allah da ManzonSa kuma sunã nufin su rarrabe a tsakãnin Allah da manzanninSa, kuma sunã cẽwa: "Munã ĩmãni da sãshe, kuma munã kãfirta da sãshe." Kuma sunã nufin su riƙi hanya a tsakãnin wannan. = --Qur'an 4:150
    Those are the disbelievers, truly. And We have prepared for the disbelievers a humiliating punishment. <> Waɗannan sũ ne kãfirai sõsai, kuma Mun yi tattali, dõmin kãfirai, azãba mai walãkantarwa. = --Qur'an 4:151
    But they who believe in Allah and His messengers and do not discriminate between any of them - to those He is going to give their rewards. And ever is Allah Forgiving and Merciful. <> Kuma waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da manzanninSa, kuma ba su rarrabe a tsakãnin kõwa ba daga gare su, waɗannan zã Mu bã su ijãrõrinsu, kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai. = --Qur'an 4:152
    The People of the Scripture ask you to bring down to them a book from the heaven. But they had asked of Moses [even] greater than that and said, "Show us Allah outright," so the thunderbolt struck them for their wrongdoing. Then they took the calf [for worship] after clear evidences had come to them, and We pardoned that. And We gave Moses a clear authority. <> Mutãnen Littãfi sunã tambayar ka ka saukar da wani littãfi daga sama, a kansu, to, lalle ne sun tambayi Mũsã mũfã girma daga wannan, suka ce: "Ka nũna mana Allah bayyane." Sai tsãwa ta kãmã su sabõda zãluncinsu, sa'an nan kuma suka riƙi maraƙi (abin bautãwa) bãyan hujjoji bayyanannu sun je musu. Sa'an nan Muka yãfe laifi daga wancan. Kuma Mun bai wa Mũsã dalĩli bayyananne. = --Qur'an 4:153
    And We raised over them the mount for [refusal of] their covenant; and We said to them, "Enter the gate bowing humbly", and We said to them, "Do not transgress on the sabbath", and We took from them a solemn covenant. <> Kuma Muka ɗaukaka dũtse sãma da su, sabõda alkawarinsu, kuma Muka ce musu: "Ku shiga ƙõfar kunã mãsu tawãli'u," Kuma Muka ce musu: "Kada ku ƙẽtare haddi a cikin Asabat," kuma Muka riƙi alkawari mai kauri daga gare su." = --Qur'an 4:154
    And [We cursed them] for their breaking of the covenant and their disbelief in the signs of Allah and their killing of the prophets without right and their saying, "Our hearts are wrapped". Rather, Allah has sealed them because of their disbelief, so they believe not, except for a few. <> To, sabõda warwarẽwarsu ga alkawarinsu, da kãfirtarsu da ãyõyin Allah, da kisansu ga Annabãwa, bã da hakki ba, da maganarsu: "Zukãtanmu sunã cikin rufi." Ã'a, Allah ne Ya yunƙe a kansu sabõda kãfircinsu, sabõda haka bã zã su yi ĩmãni ba fãce kaɗan. = --Qur'an 4:155
    And [We cursed them] for their disbelief and their saying against Mary a great slander, <> Kuma sabõda kãfircinsu da faɗarsu, a kan Maryama, ƙiren ƙarya mai girma. = --Qur'an 4:156
    And [for] their saying, "Indeed, we have killed the Messiah, Jesus, the son of Mary, the messenger of Allah." And they did not kill him, nor did they crucify him; but [another] was made to resemble him to them. And indeed, those who differ over it are in doubt about it. They have no knowledge of it except the following of assumption. And they did not kill him, for certain. <> Da faɗarsu: "Lalle ne mu, mun kashe Masĩhu ĩsã ɗan Maryama Manzon Allah," alhãli kuwa ba su kashe shi ba, kuma ba su kẽre shi ba, kuma ammaan kamanta shi ne a garẽ su. Lalle ne waɗanda sauka sãɓã wa jũna a cikin sha'aninsa lalle ne, sunã shakka daga gare, shi, bã da wani ilmi fãce bin zato kuma ba su kashe shi ba bisa ga yaƙĩni. = --Qur'an 4:157
    Rather, Allah raised him to Himself. And ever is Allah Exalted in Might and Wise. <> Ã'a, Allah Ya ɗauke shi zuwa garẽ Shi, kuma Allah Yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima. = --Qur'an 4:158
    And there is none from the People of the Scripture but that he will surely believe in Jesus before his death. And on the Day of Resurrection he will be against them a witness. <> Kuma bãbu kõwa daga Mutãnen Littafi, fãce lalle yanã ĩmãni da shi a gabãnin mutuwarsa, kuma a Rãnar ¡iyãma yana kasancẽwa mai shaida, a kansu. = --Qur'an 4:159
    For wrongdoing on the part of the Jews, We made unlawful for them [certain] good foods which had been lawful to them, and for their averting from the way of Allah many [people], <> To, sabõda zãlunci daga waɗanda suka tũba (Yahũdu) Muka haramta musu abũbuwa masu dãɗi waɗanda aka halatta su a gare su, kuma sabõda taushẽwarsu daga hanyar Allah da yawa. = --Qur'an 4:160
    And [for] their taking of usury while they had been forbidden from it, and their consuming of the people's wealth unjustly. And we have prepared for the disbelievers among them a painful punishment. <> Da karɓarsu ga riba, alhãli kuwa an hana su daga gare ta, da cin su ga dũkiyar mutãne daƙarya. Kuma Muka yi tattali, dõmin kãfirai, azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 4:161
    But those firm in knowledge among them and the believers believe in what has been revealed to you, [O Muhammad], and what was revealed before you. And the establishers of prayer [especially] and the givers of zakah and the believers in Allah and the Last Day - those We will give a great reward. <> Amma tabbatattu a cikin ilmi daga gare su, da mũminai, suna ĩmani da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabãninka, madalla da masu tsai da salla, da mãsu bãyar da zakka, da mãsu ĩmãni daAllah da Rãnar Lãhira. Waɗannan zã Mu bã su lãda mai girma. = --Qur'an 4:162
    Indeed, We have revealed to you, [O Muhammad], as We revealed to Noah and the prophets after him. And we revealed to Abraham, Ishmael, Isaac, Jacob, the Descendants, Jesus, Job, Jonah, Aaron, and Solomon, and to David We gave the book [of Psalms]. <> Lalle ne Mu, Mun yi wahayi zuwa gare ka, kamar yadda Muka yi wahayi zuwa ga Nũhu da annabãwa daga bãyansa. Kuma Mun yi wahayi zuwa ga Ibrãhĩma da Ismã'ĩla da Is'hãƙa da Yaƙũbu da jĩkõki da ĩsa da Ayũba da Yũnusa da Hãruna da Sulaimãn. Kuma Mun bai wa Dãwũda zabũra. = --Qur'an 4:163
    And [We sent] messengers about whom We have related [their stories] to you before and messengers about whom We have not related to you. And Allah spoke to Moses with [direct] speech. <> Da wasu Manzanni, haƙĩ ƙa, Mun bã da lãbarinsu a gare ka daga gabãni, da wasu manzanni waɗanda ba Mu bã da lãbãrinsu ba a gare ka, kuma Allah Yã yi magana da Mũsã, magana sõsai. = --Qur'an 4:164
    [We sent] messengers as bringers of good tidings and warners so that mankind will have no argument against Allah after the messengers. And ever is Allah Exalted in Might and Wise. <> Manzanni mãsu bãyar da bushãra kuma mãsu gargaɗi dõmin kada wata hujja ta kasance ga mutãne a kan Allah bãyan Manzannin. Kuma Allah yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima. = --Qur'an 4:165
    But Allah bears witness to that which He has revealed to you. He has sent it down with His knowledge, and the angels bear witness [as well]. And sufficient is Allah as Witness. <> Amma Allah Yanã shaida da abin da Ya saukar zuwa gare ka. Yã saukar da shi da saninSa. Kuma malã'iku sunã shaida. Kuma Allah Yã isa Ya zama shaida. = --Qur'an 4:166
    Indeed, those who disbelieve and avert [people] from the way of Allah have certainly gone far astray. <> Lalle ne, waɗanda suka kãfirta kuma suka kange (wasu mutãne) daga hanyar Allah, haƙĩƙa, sun ɓace, ɓata mai nĩsa. = --Qur'an 4:167
    Indeed, those who disbelieve and commit wrong [or injustice] - never will Allah forgive them, nor will He guide them to a path. <> Lalle ne waɗanda suka kãfirta, kuma suka yi zãlunci, Allah bai kasance Yana yi musu gãfara ba, kuma bã Ya shiryar da su ga hanya. = --Qur'an 4:168
    Except the path of Hell; they will abide therein forever. And that, for Allah, is [always] easy. <> Fãce hanyar Jahannama, sunã mãsu dawwama a cikinta har abada, kuma wannan yã kasance, ga Allah, mai sauƙi. = --Qur'an 4:169
    O Mankind, the Messenger has come to you with the truth from your Lord, so believe; it is better for you. But if you disbelieve - then indeed, to Allah belongs whatever is in the heavens and earth. And ever is Allah Knowing and Wise. <> Yã kũ mutãne! Haƙĩƙa, Manzo yã je muku da gaskiya daga Ubangijinku. Sabõda haka ku yi ĩmãni yã fi zama alhẽri a gare ku. Kuma idan kun kãfirta, to, Allah Yanã da abin da ke cikin sammai da ƙasa. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima. = --Qur'an 4:170
    O People of the Scripture, do not commit excess in your religion or say about Allah except the truth. The Messiah, Jesus, the son of Mary, was but a messenger of Allah and His word which He directed to Mary and a soul [created at a command] from Him. So believe in Allah and His messengers. And do not say, "Three"; desist - it is better for you. Indeed, Allah is but one God. Exalted is He above having a son. To Him belongs whatever is in the heavens and whatever is on the earth. And sufficient is Allah as Disposer of affairs. <> Yã Mutãnen Littãfi! Kada ku zurfafã a cikin addininku. Kuma kada ku faɗa, ga Allah, fãce gaskiya. Abin da aka sani kawai, Masĩ hu ĩsa ɗan Maryama Manzon Allah ne, kuma kalmarSa, yã jẽfa ta zuwa ga Maryama, kuma rũhi ne daga gare Shi. Sabõda haka, ku yi ĩmãni da Allah da manzanninSa, kuma kada ku ce, "Uku". Ku hanu (daga faɗin haka) yã fi zama alhẽri a gare ku. Abin da aka sani kawai, Allah Ubangiji ne Guda. TsarkinSa yã tabbata daga wani abin haifuwa ya kasance a gare Shi! Shĩ ne da abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa kuma Allah Yã isa Ya zama wakĩli. = --Qur'an 4:171
    Never would the Messiah disdain to be a servant of Allah, nor would the angels near [to Him]. And whoever disdains His worship and is arrogant - He will gather them to Himself all together. <> Masĩhu bã ya ƙyãmar ya kasance bãwa ga Allah, kuma haka malã'ikun nan makusanta. Kuma wanda ya yi ƙyãmar bautarSa kuma yi yi girman kai, to, zai tãra su zuwa gare shi gabã ɗaya. = --Qur'an 4:172
    And as for those who believed and did righteous deeds, He will give them in full their rewards and grant them extra from His bounty. But as for those who disdained and were arrogant, He will punish them with a painful punishment, and they will not find for themselves besides Allah any protector or helper. <> To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwaiai, to zã Ya cika musu ijãrõrinsu, kuma Yanã ƙãra musu daga falalarSa. Kuma amma waɗanda suka yi ƙyãma, kuma suka yi girman kai, to, zã Ya yi musu azãba, azãba mai raɗɗi kuma bã su samun wani masõyi dõmin kansu, baicin Allah, kuma bã su samun mataimaki. = --Qur'an 4:173
    O mankind, there has come to you a conclusive proof from your Lord, and We have sent down to you a clear light. <> Yã kũ mutãne! Haƙĩƙa wani dalĩli daga Ubangijinku yã je muku kuma Mun saukar da wani haske, bayyananne zuwa gare ku. = --Qur'an 4:174
    So those who believe in Allah and hold fast to Him - He will admit them to mercy from Himself and bounty and guide them to Himself on a straight path. <> To, amma waɗanda suka yi ĩmãni da Allah kuma suka faku a gare Shi, to, zai shigar da su cikin wata rahama daga gare Shi da wata falala, kuma Ya shiryar da su zuwa gare Shi ga tafarki madaidaici. = --Qur'an 4:175
    They request from you a [legal] ruling. Say, "Allah gives you a ruling concerning one having neither descendants nor ascendants [as heirs]." If a man dies, leaving no child but [only] a sister, she will have half of what he left. And he inherits from her if she [dies and] has no child. But if there are two sisters [or more], they will have two-thirds of what he left. If there are both brothers and sisters, the male will have the share of two females. Allah makes clear to you [His law], lest you go astray. And Allah is Knowing of all things. <> Sunã yi maka fatawa. Ka ce: "Allah Yanã bayyana muku fatawa a cikin 'Kalãla."' Idan mutum ya halaka, ba shi da, rẽshe kuma yana da 'yar'uwa, to, tana da rabin abin da ya bari, kuma shi yana gãdon ta, idan wani rẽshe bai kasance ba a gare ta. Sa'an nan idan ('yan'uwa mãtã) suka kasance biyu, to suna da kashi biyu daga kashi uku ɗin abin da ya bari. Kuma idan sun kasance, 'yan'uwa, maza da mãtã to namiji yana da misãlin rabon mãtã biyu. Allah Yana bayyanawa a gare ku, dõmin kada ku ɓace. Kuma Allah ne, Masani ga dukan kõme. = --Qur'an 4:176
    O you who have believed, fulfill [all] contracts. Lawful for you are the animals of grazing livestock except for that which is recited to you [in this Qur'an] - hunting not being permitted while you are in the state of ihram. Indeed, Allah ordains what He intends. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! ku cika alkawurra. An halatta muku dabbobin jin dãɗi fãce abin da ake karantãwa a kanku, bã kunã mãsu halattar da farauta ba alhãli kuwa kunã mãsu harama. Lalle ne, Allah Yanã hukunta abin da yake nufi. = --Qur'an 5:1
    O you who have believed, do not violate the rites of Allah or [the sanctity of] the sacred month or [neglect the marking of] the sacrificial animals and garlanding [them] or [violate the safety of] those coming to the Sacred House seeking bounty from their Lord and [His] approval. But when you come out of ihram, then [you may] hunt. And do not let the hatred of a people for having obstructed you from al-Masjid al-Haram lead you to transgress. And cooperate in righteousness and piety, but do not cooperate in sin and aggression. And fear Allah; indeed, Allah is severe in penalty. <> Ya kũ waɗanda suka yi ĩmãni! kada ku halattar da ayyukan ibãdar Allah game da hajji, kuma da watã mai alfarma, kuma da hadaya, kuma da rãtayar raƙuman hadaya, kuma da mãsu nufin ¦ãki mai alfarma, sunã neman falala daga Ubangijinsu da yarda. Kuma idan kun kwance harama, to, ku yi farauta. Kuma kada ƙiyayya da wasu mutãne ta ɗauke ku, dõmin sun kange ku daga Masallãci Mai alfarma, ga ku yi zãlunci. Kuma ku taimaki junã a kan aikin ƙwarai da taƙawa. Kuma kada ku taimaki juna a kan zunubi da zãlunci, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne. = --Qur'an 5:2
    Prohibited to you are dead animals, blood, the flesh of swine, and that which has been dedicated to other than Allah, and [those animals] killed by strangling or by a violent blow or by a head-long fall or by the goring of horns, and those from which a wild animal has eaten, except what you [are able to] slaughter [before its death], and those which are sacrificed on stone altars, and [prohibited is] that you seek decision through divining arrows. That is grave disobedience. This day those who disbelieve have despaired of [defeating] your religion; so fear them not, but fear Me. This day I have perfected for you your religion and completed My favor upon you and have approved for you Islam as religion. But whoever is forced by severe hunger with no inclination to sin - then indeed, Allah is Forgiving and Merciful. <> An haramta muku mũshe da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah a gare shi, da mãƙararriya da jefaffiya da mai gangarõwa da sõkakkiya, da abin da mãsu dãgi suka ci, fãce abin da kuka yanka, da abin da aka yanka a kan gunki (shĩ ma an haramta). Kuma kada ku yi rabo da kibiyoyi na cãca wannan fãsiƙanci ne, A yau waɗanda suka kãfirta sun yanke ƙauna daga addininku. Sabõda haka kada ku ji tsõronsu kuma ku ji tsõroNa. A yau Nã kammalã muku addininku, Kuma Nã cika ni'imaTa a kanku, Kuma Nã yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku. To, wanda aka sanya wa lalũra a cikin yunwa mai tsanani, bã yana mai karkata zuwa ga wani zunubi ba, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 5:3
    They ask you, [O Muhammad], what has been made lawful for them. Say, "Lawful for you are [all] good foods and [game caught by] what you have trained of hunting animals which you train as Allah has taught you. So eat of what they catch for you, and mention the name of Allah upon it, and fear Allah." Indeed, Allah is swift in account. <> Suna tambayar ka cewa mene ne aka halatta musu? Ka ce: "An halatta muku abũbuwa mãsu dãɗi da abin da kuka sanar (farauta) daga mãsu yin mĩki, kunã mãsu sakinsu daga hannuwanku, kunã sanar da su daga abin da Allah Ya sanar da ku. To, ku ci daga abin da suka kama sabõda ku, kuma ku ambaci sunan Allah a kansa, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai gaugawar sakamako da yawã ne. = --Qur'an 5:4
    This day [all] good foods have been made lawful, and the food of those who were given the Scripture is lawful for you and your food is lawful for them. And [lawful in marriage are] chaste women from among the believers and chaste women from among those who were given the Scripture before you, when you have given them their due compensation, desiring chastity, not unlawful sexual intercourse or taking [secret] lovers. And whoever denies the faith - his work has become worthless, and he, in the Hereafter, will be among the losers. <> A yau an halatta muku abũbuwa mãsu dãɗi kuma abincin waɗanda aka bai wa Littãfi halal ne a gare ku, kuma abincinku halal ne a gare su, da mãtã mãsu kãmun kai daga muminai da mãtã 'yã'ya daga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku idan kun je musu da sadãkõkinsu, kuna mãsu yin aure, ba masu yin zina ba, kuma bã mãsu riƙon abõkai ba. Kuma wanda ya kãfirta da ĩmãni to, lalle ne aikinsa yã ɓãci, kuma shĩ, a cikin Lãhira, yanã daga mãsu hasãra. = --Qur'an 5:5
    O you who have believed, when you rise to [perform] prayer, wash your faces and your forearms to the elbows and wipe over your heads and wash your feet to the ankles. And if you are in a state of janabah, then purify yourselves. But if you are ill or on a journey or one of you comes from the place of relieving himself or you have contacted women and do not find water, then seek clean earth and wipe over your faces and hands with it. Allah does not intend to make difficulty for you, but He intends to purify you and complete His favor upon you that you may be grateful. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! idan kun tãshi zuwa ga salla, to, ku wanke fuskõkinku da hannuwanku zuwa ga magincirõri, kuma ku yi shãfa ga kãnunku, kuma ku (wanke) ƙafãfunku zuwa idãnun sãwu biyu. Kuma idan kun kasance mãsu janaba, to, ku yi tsarki, kuma idan kun kasance majinyata, kõ kuwa a kan tafiya, kõ kuwa ɗaya daga gare ku ya zo daga kãshi, kõ kuka yi shãfayyar junã da mãtã, sa'an nan ba ku sãmi ruwa ba to ku yi nufin wuri mai kyau, sa'an nan ku yi shãfa ga fuskõkinku da hannuwanku daga gare shi. Allah bã Ya nufi dõmin Ya sanya wani ƙunci a kanku, kuma amma Yanã nufi dõmin Ya cika ni'imarSa a kanku, tsammãninku kunã gõdewa. = --Qur'an 5:6
    And remember the favor of Allah upon you and His covenant with which He bound you when you said, "We hear and we obey"; and fear Allah. Indeed, Allah is Knowing of that within the breasts. <> Kuma ku tuna ni'imar Allah akanku da alkawarinku wanda Ya ɗaure ku da shi, a lõkacin da kuka ce: "Mun ji kuma mun yi ɗã'a Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Masani ne ga abin da ke a cikin zukata." = --Qur'an 5:7
    O you who have believed, be persistently standing firm for Allah, witnesses in justice, and do not let the hatred of a people prevent you from being just. Be just; that is nearer to righteousness. And fear Allah; indeed, Allah is Acquainted with what you do. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayin daka dõmin Allah mãsu shaida da ãdalci. Kuma kada ƙiyayya da wasu mutane ta ɗauke ku a kan bã zã ku yi ãdalci ba. Ku yi ãdalci Shĩ ne mafi kusa ga taƙawa. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa. = --Qur'an 5:8
    Allah has promised those who believe and do righteous deeds [that] for them there is forgiveness and great reward. <> Allah Yã yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Sunã da wata gãfara da lãda mai girma. = --Qur'an 5:9
    But those who disbelieve and deny Our signs - those are the companions of Hellfire. <> Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryatã, game da ãyõyinMu, waɗannan su ne abõkan wuta. = --Qur'an 5:10
    O you who have believed, remember the favor of Allah upon you when a people determined to extend their hands [in aggression] against you, but He withheld their hands from you; and fear Allah. And upon Allah let the believers rely. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da wasu mutãne suka yi niyyar su shimfiɗa hannuwansu zuwa gare ku sai Ya kange hannuwansu daga gare ku, kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma sai muminai su dogara ga Allah kawai. = --Qur'an 5:11
    And Allah had already taken a covenant from the Children of Israel, and We delegated from among them twelve leaders. And Allah said, "I am with you. If you establish prayer and give zakah and believe in My messengers and support them and loan Allah a goodly loan, I will surely remove from you your misdeeds and admit you to gardens beneath which rivers flow. But whoever of you disbelieves after that has certainly strayed from the soundness of the way." <> Kuma lalle Allah Yã riƙi alkawarin Banĩ lsrã' ĩla kuma Muka ayyana wakilai gõma shã biyu daga gare su kuma Allah Ya ce: "Lalle ne Nĩ, Inã tãre da ku, haƙĩƙa, idan kun tsayar da salla, kuma kun bãyar da zakka, kuma kun yi ĩmani da manzannĩNa, kuma kuka taimake su, kuma kuka bai wa Allah rance mai kyau, haƙĩƙa, Inã kankare laifukanku daga gare ku, kuma haƙĩƙa, Inã shigar da ku gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙõramu sanã gudãna a ƙarƙashinsu, sa'an nan wanda ya kãfirta a bãyan wannan daga gare ku, to, lalle ne, yã ɓace daga tsakar hanya." = --Qur'an 5:12
    So for their breaking of the covenant We cursed them and made their hearts hard. They distort words from their [proper] usages and have forgotten a portion of that of which they were reminded. And you will still observe deceit among them, except a few of them. But pardon them and overlook [their misdeeds]. Indeed, Allah loves the doers of good. <> To, sabõda warwarewarsu ga alkawarinsu Muka la'ane su, kuma Muka sanya zukãtansu ƙeƙasassu, sunã karkatar da magana daga wurãrenta, kuma suka manta da wani yanki daga abin da aka tunãtar da su da shi, kuma bã zã ka gushe ba kana tsinkãyar yaudara daga gare su fãce kaɗan daga gare su. To, ka yãfe laifi daga gare su, kuma ka kau da kai. Lalle ne, Allah Yanã son mãsu kyautatãwa. = --Qur'an 5:13
    And from those who say, "We are Christians" We took their covenant; but they forgot a portion of that of which they were reminded. So We caused among them animosity and hatred until the Day of Resurrection. And Allah is going to inform them about what they used to do. <> Kuma daga waɗanda suka ce: "Lalle ne mu Nasãra ne" Mun riƙi alkawarinsu, sai suka manta da wani yanki daga abin da aka tunãtar da su da shi, sai Muka shushuta adãwa da ƙeta a tsakãninsu har ya zuwa ga Rãnar ¡iyãma. Kuma Allah zai bã su lãbari da abin da suka kasance sunã sanã'antawa. = --Qur'an 5:14
    O People of the Scripture, there has come to you Our Messenger making clear to you much of what you used to conceal of the Scripture and overlooking much. There has come to you from Allah a light and a clear Book. <> Yã Mutãnen littãfi! Lalle ne, ManzonMu yã je muku, yanã bayyana muku abu mai yawa daga abin da kuka kasance kunã ɓõyewa daga Littãfi, kuma yanã rangwame daga abu mai yawa. Haƙĩƙa, wani haske da wani Littafi mai bayyanãwa yã je muku daga Allah. = --Qur'an 5:15
    By which Allah guides those who pursue His pleasure to the ways of peace and brings them out from darknesses into the light, by His permission, and guides them to a straight path. <> Dashĩ, Allah Yanã shiryar da wanda ya bi yardarsa zuwa ga hanyõyin aminci, kuma Yanã fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izninsa, kuma Yanã shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya. = --Qur'an 5:16
    They have certainly disbelieved who say that Allah is Christ, the son of Mary. Say, "Then who could prevent Allah at all if He had intended to destroy Christ, the son of Mary, or his mother or everyone on the earth?" And to Allah belongs the dominion of the heavens and the earth and whatever is between them. He creates what He wills, and Allah is over all things competent. <> Lalle haƙĩƙa waɗanda suka ce: "Lalle Allah Shĩ ne Masĩhu ɗan Maryama," sun kãfirta. Ka ce: "To, wane ne ke iya mallakar wani abu daga Allah, idan Yã nufi Ya halakar da Masĩhu ɗanMaryama da uwarsa da wanda yake a cikin ƙasa gabã ɗaya?" Kuma Allah ne da mallakar sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, Yanã halitta abin da Yake so. Kuma Allah a kan dukkan kõme, Mai ĩkon yi ne. = --Qur'an 5:17
    But the Jews and the Christians say, "We are the children of Allah and His beloved." Say, "Then why does He punish you for your sins?" Rather, you are human beings from among those He has created. He forgives whom He wills, and He punishes whom He wills. And to Allah belongs the dominion of the heavens and the earth and whatever is between them, and to Him is the [final] destination. <> Kuma Yahudu da Nasãra sun ce: "Mu ne ɗiyan Allah, kuma masõyansa." Ka ce: "To, don me Yake yi muku azãba da zunubanku? Ã'a ku mutãne ne daga waɗanda Ya halitta, Yanã gãfartãwa ga wanda Yake so, kuma Yanã azabta wanda Yake so. Kuma Allah ne da mulkin sammai da ƙasa da abin da ke tsakãninsu kuma zuwa gare shi makomã take." = --Qur'an 5:18
    O People of the Scripture, there has come to you Our Messenger to make clear to you [the religion] after a period [of suspension] of messengers, lest you say, "There came not to us any bringer of good tidings or a warner." But there has come to you a bringer of good tidings and a warner. And Allah is over all things competent. <> Yã Mutãnen Littãfi! Lalle ManzonMu yã je muku yanã bayyana muku, a kan lõkacin fatara daga manzanni, dõmin kada ku ce: "wani mai bayar da bushãra bai zo mana ba, kuma haka wani mai gargaɗi bai zo ba." To, haƙĩƙa, mai bãyar da bushãra da mai gargaɗi sunje muku. Kuma Allah ne, a kan dukkan kõme, Mai ĩkon yi. = --Qur'an 5:19
    And [mention, O Muhammad], when Moses said to his people, "O my people, remember the favor of Allah upon you when He appointed among you prophets and made you possessors and gave you that which He had not given anyone among the worlds. <> Kuma a lõkacin da Musa ya ce wa mutãnensa: "Yã ku mutãnena! Ku tuna ni'imar Allah a kanku; dõmin Yã sanya annabãwa a cikinku, kuma Yã sanya ku sarãkuna, kuma Yã bã ku abin da bai bai wa kõwa ba daga tãlikai." = --Qur'an 5:20
    O my people, enter the Holy Land which Allah has assigned to you and do not turn back [from fighting in Allah 's cause] and [thus] become losers." <> "Yã mutãnena! Ku shiga ƙasar nan, abar tsarkakewa, wadda Allah Ya rubuta sabõda ku, kuma kada ku kõma da bãya, har ku juya kunã mãsu hasara." = --Qur'an 5:21
    They said, "O Moses, indeed within it is a people of tyrannical strength, and indeed, we will never enter it until they leave it; but if they leave it, then we will enter." <> Suka ce: "Ya Musã! Lalle ne, a cikinta akwai wasu mutãne mãsu ƙarfi kuma lalle ne bã zã mu shige ta ba sai sun fice daga gare ta, to, idan sun fice daga gare ta, to, lalle ne mu, masu shiga ne." = --Qur'an 5:22
    Said two men from those who feared [to disobey] upon whom Allah had bestowed favor, "Enter upon them through the gate, for when you have entered it, you will be predominant. And upon Allah rely, if you should be believers." <> Wasu maza biyu daga waɗanda suke tsõron Allah, Allah Yã yi ni'ima a kansu, suka ce: "Ku shiga gare su, daga ƙõfar, dõmin idan kuka shige shi, to, lalle ne ku, mãsu rinjãya ne, kuma ga Allah sai ku dogara idan kun kasance muminai." = --Qur'an 5:23
    They said, "O Moses, indeed we will not enter it, ever, as long as they are within it; so go, you and your Lord, and fight. Indeed, we are remaining right here." <> Suka ce: "Ya Musa! Lalle ne mu, bã za mu shige ta ba har abada matuƙar sun dawwama a cikinta sai ka tafi kai da Ubangijinka dõmin ku yi yãƙi. Lalle ne mu, munã a nan zaune." = --Qur'an 5:24
    [Moses] said, "My Lord, indeed I do not possess except myself and my brother, so part us from the defiantly disobedient people." <> Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, bã ni mallakar kõwa fãce kaina da ɗan'uwãna, sai Ka rarrabe a tsakãninmu da tsakãnin mutãne fãsiƙai." = --Qur'an 5:25
    [Allah] said, "Then indeed, it is forbidden to them for forty years [in which] they will wander throughout the land. So do not grieve over the defiantly disobedient people." <> (Allah) Ya ce: "To, lalle ne ita abar haramtãwa ce a gare su, shekara arba'in, sunã yin ɗimuwa a cikin ƙasa. Sabõda haka kada ka yi baƙin ciki a kan mutãne fãsiƙai." = --Qur'an 5:26
    And recite to them the story of Adam's two sons, in truth, when they both offered a sacrifice [to Allah], and it was accepted from one of them but was not accepted from the other. Said [the latter], "I will surely kill you." Said [the former], "Indeed, Allah only accepts from the righteous [who fear Him]. <> Kuma karantã musu lãbãrin ɗiya biyu na Ãdamu, da gaskiya, a lõkacin da suka bãyar da baiko, sai aka karɓa daga ɗayansu kuma ba a karɓa daga ɗayan ba, ya ce: "Lalle ne zan kashe ka." (¦ayan kuma) ya ce: "Abin sani dai, Allah Yana karɓã daga mãsu taƙawa ne." = --Qur'an 5:27
    If you should raise your hand against me to kill me - I shall not raise my hand against you to kill you. Indeed, I fear Allah, Lord of the worlds. <> "Lalle ne idan ka shimfiɗa hannunka zuwa gare ni dõmin ka kashe ni, ban zama mai shimfiɗa hannuna zuwa gare ka ba dõmin in kashe ka. Lalle ne nĩ inã tsõron Allah Ubangijin tãlikai. = --Qur'an 5:28
    Indeed I want you to obtain [thereby] my sin and your sin so you will be among the companions of the Fire. And that is the recompense of wrongdoers." <> "Lalle ne nĩ inã nufin ka kõma da zunubina game da zunubinka, har ka kasance daga abõkan wuta. Kuma wannan shĩ ne sakamakon azzãlumai." = --Qur'an 5:29
    And his soul permitted to him the murder of his brother, so he killed him and became among the losers. <> Sai ransa ya ƙawãtar masa kashewar ɗan'uwansa, sai kuwa ya kashe shi, sa'an nan ya wayi gari daga mãsu hasãra. = --Qur'an 5:30
    Then Allah sent a crow searching in the ground to show him how to hide the disgrace of his brother. He said, "O woe to me! Have I failed to be like this crow and hide the body of my brother?" And he became of the regretful. <> Sai Allah Ya aiki wani hankãka, yanã tõno a cikin ƙasa dõmin ya nuna masa yadda zai turbuɗe gãwar ɗan'uwansa. Ya ce: "Kaitõna! Nã kãsa in kasance kamar wannan hankãka dõmin in turbuɗe gãwar ɗan'uwana?" Sai ya wãyi gari daga mãsu nadãmã. = --Qur'an 5:31
    Because of that, We decreed upon the Children of Israel that whoever kills a soul unless for a soul or for corruption [done] in the land - it is as if he had slain mankind entirely. And whoever saves one - it is as if he had saved mankind entirely. And our messengers had certainly come to them with clear proofs. Then indeed many of them, [even] after that, throughout the land, were transgressors. <> Daga sababin wannan, Muka rubuta a kan Banĩ lsrã'ĩla cewa, lalle ne wanda ya kashe rai bã da wani rai ba, ko ɓarna a cikin ƙasa, to kamar yã kashe mutãne duka ne, kuma wanda ya rãya rai, to, kamar yã rãyar da mutãne ne gabã ɗaya. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, ManzanninMu sun je musu da hujjõji bayyanannu, sa'an nan kuma lalle ne, mãsu yawa daga gare su, a bãyan wannan, haƙĩƙa, mãsuɓarna ne a cikin ƙasa. = --Qur'an 5:32
    Indeed, the penalty for those who wage war against Allah and His Messenger and strive upon earth [to cause] corruption is none but that they be killed or crucified or that their hands and feet be cut off from opposite sides or that they be exiled from the land. That is for them a disgrace in this world; and for them in the Hereafter is a great punishment, <> Abin sani kawai sakamakon waɗanda suke Yãƙin Allah da Manzonsa, kuma sunã aiki a cikin ƙasa dõmin ɓarna a kashe su ko kuwa a ƙere su, kõ kuwa a kakkãtse hannuwansu da ƙafãfunsu daga sãɓãni, ko kuwa a kõre su daga ƙasa. Sannan gare su wulakanci ne a cikin rãyuwar duniya, kuma a Lãhira sunã da wata azãba mai girma. = --Qur'an 5:33
    Except for those who return [repenting] before you apprehend them. And know that Allah is Forgiving and Merciful. <> Fãce fa waɗanda suka tuba tun a gabãnin ku sãmi ĩko akansu, to, ku sani cewa lalle ne, Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 5:34
    O you who have believed, fear Allah and seek the means [of nearness] to Him and strive in His cause that you may succeed. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, kuma ku nemi tsari zuwa gare shi, kuma ku yi jihãdi a cikin hanyarsa, tsammãninku, za ku ci nasara. = --Qur'an 5:35
    Indeed, those who disbelieve - if they should have all that is in the earth and the like of it with it by which to ransom themselves from the punishment of the Day of Resurrection, it will not be accepted from them, and for them is a painful punishment <> Lalle ne waɗanda suka kãfirta, lalle dã sunã da abin da ke a cikin ƙasa gabã ɗaya da misãlinsa tãre da shi, dõmin su yi fansa da shi daga azãbar Rãnar ¡iyãma, bã a karɓarsa daga gare su, kuma sunã da azãba mai raɗadi. = --Qur'an 5:36
    They will wish to get out of the Fire, but never are they to emerge therefrom, and for them is an enduring punishment. <> Sunã nufin su fita ne daga wuta, kuma ba su zama mãsu fita daga gare ta ba, kuma sunã da azãba zaunanniya. = --Qur'an 5:37
    [As for] the thief, the male and the female, amputate their hands in recompense for what they committed as a deterrent [punishment] from Allah. And Allah is Exalted in Might and Wise. <> Kuma ɓarãwo da ɓarauniya sai ku yanke hannuwansu, bisa sakamako ga abin da suka tsirfanta, a kan azãba daga Allah. Kuma Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima. = --Qur'an 5:38
    But whoever repents after his wrongdoing and reforms, indeed, Allah will turn to him in forgiveness. Indeed, Allah is Forgiving and Merciful. <> To, wanda ya tuba a bãyan zãluncinsa, kuma ya gyãra (halinsa), to, lalle ne Allah Yanã karɓar tubarsa. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 5:39
    Do you not know that to Allah belongs the dominion of the heavens and the earth? He punishes whom He wills and forgives whom He wills, and Allah is over all things competent. <> Shin, ba ka sani ba cewa lalle ne, Allah Shi ne da mulkin sammai da ƙasa, Yanã azãbtar da wanda Yake so, kuma Yanã yin gãfara ga wanda yake so, kuma Allah a dukkan kõme, Mai ĩkon yi ne? = --Qur'an 5:40
    O Messenger, let them not grieve you who hasten into disbelief of those who say, "We believe" with their mouths, but their hearts believe not, and from among the Jews. [They are] avid listeners to falsehood, listening to another people who have not come to you. They distort words beyond their [proper] usages, saying "If you are given this, take it; but if you are not given it, then beware." But he for whom Allah intends fitnah - never will you possess [power to do] for him a thing against Allah. Those are the ones for whom Allah does not intend to purify their hearts. For them in this world is disgrace, and for them in the Hereafter is a great punishment. <> Yã kai Manzo! Kada waɗanda suke tseren gaugawa a cikin kãfirci su ɓãta maka rai, daga waɗanda suka ce: "Mun yi ĩmãni" da bãkunansu, alhãli zukatansu ba su yi ĩmãnin ba, kuma daga waɗanda suka tuba (watau Yahudu) mãsu yawan saurare ga wasu mutane na dabam waɗanda ba su je maka ba, sunã karkatar da zance daga bãyan wurarensa, sunã cewa: "Idan an bã ku wannan, to, ku karɓa, kuma idan ba a bã ku shĩ ba, to, ku yi sauna."Kuma wanda Allah Ya yi nufin fitinarsa, to bã zã ka mallaka masa kõme ba, daga Allah. Waɗannan ne waɗanda Allah bai yi nufin Ya tsarkake zukãtansu ba. Sunã da kunya a cikin duniya, kuma sunã da wata azãba mai girma a cikin 1ãhira. = --Qur'an 5:41
    [They are] avid listeners to falsehood, devourers of [what is] unlawful. So if they come to you, [O Muhammad], judge between them or turn away from them. And if you turn away from them - never will they harm you at all. And if you judge, judge between them with justice. Indeed, Allah loves those who act justly. <> Mãsu yawan saurãre ga ƙarya ne, mãsu yawan ci ga haram, to, idan sun zo maka, sai ka yi hukunci a tsakãninsu kõ ka bijira daga gare su. Kuma idan ka bijira daga gare su, to, bã zã su cuce ka da kõme ba, kuma idan ka yi hukunci, to, sai ka hukunta a tsakãninsu da ãdalci. Lalle ne, Allah Yanã son mãsu ãdalci. = --Qur'an 5:42
    But how is it that they come to you for judgement while they have the Torah, in which is the judgement of Allah? Then they turn away, [even] after that; but those are not [in fact] believers. <> Kuma yãya suke gabãtar da kai ga hukunci, alhãli a wurinsu akwai Attaura, a cikinta akwai hukuncin Allah, sa'an nan kuma sunã karkacewa a bãyan wannan? waɗannan bã muminai ba ne! = --Qur'an 5:43
    Indeed, We sent down the Torah, in which was guidance and light. The prophets who submitted [to Allah] judged by it for the Jews, as did the rabbis and scholars by that with which they were entrusted of the Scripture of Allah, and they were witnesses thereto. So do not fear the people but fear Me, and do not exchange My verses for a small price. And whoever does not judge by what Allah has revealed - then it is those who are the disbelievers. <> Lalle ne Mu, Mun saukar da Attaura, a cikinta akwai shiriya da haske Annabãwa waɗanda suke sun sallamã, sunã yin hukunci da ita ga waɗanda suka tuba (Yahudu), da mãlaman tarbiyya, da manyan malamai ga abin da aka neme su da su tsare daga Littãfin Allah, kuma sun kasance, a kansa, mãsu bã da shaida. To, kada ku ji tsõron mutãne kuma ku ji tsõroNa kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ãyoyiNa. wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne kafirai. = --Qur'an 5:44
    And We ordained for them therein a life for a life, an eye for an eye, a nose for a nose, an ear for an ear, a tooth for a tooth, and for wounds is legal retribution. But whoever gives [up his right as] charity, it is an expiation for him. And whoever does not judge by what Allah has revealed - then it is those who are the wrongdoers. <> Kuma Mun rubuta a kansu, a cikinta cewa, lalle (anã kashe) rai sabõda rai, kuma (anã ɗebe) idõ sabõda idõ, kuma (ana katse) hanci sabõda hanci, kuma kunne sabõda kunne kuma haƙori sabõda haƙõri kuma a raunuka a yi sakayya. To, wanda ya yi sadaka da shi, to, shi kaffãra ce a gare shi. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne azzãlumai. = --Qur'an 5:45
    And We sent, following in their footsteps, Jesus, the son of Mary, confirming that which came before him in the Torah; and We gave him the Gospel, in which was guidance and light and confirming that which preceded it of the Torah as guidance and instruction for the righteous. <> Kuma Muka biyar a kan gurãbansu da Ĩsa ɗan Maryama, yãnã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Attaura, kuma Muka bã shi Injĩla a cikinsa akwai shiriya da haske, yanã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Attaura, kuma shi shiriya ne da wa'azi ga mãsu taƙawa. = --Qur'an 5:46
    And let the People of the Gospel judge by what Allah has revealed therein. And whoever does not judge by what Allah has revealed - then it is those who are the defiantly disobedient. <> Kuma sai mutãnen injĩla su yi hukunci da abin da Allah ya saukar a cikinta. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah ya saukar, to, waɗannan su ne fãsiƙai. = --Qur'an 5:47
    And We have revealed to you, [O Muhammad], the Book in truth, confirming that which preceded it of the Scripture and as a criterion over it. So judge between them by what Allah has revealed and do not follow their inclinations away from what has come to you of the truth. To each of you We prescribed a law and a method. Had Allah willed, He would have made you one nation [united in religion], but [He intended] to test you in what He has given you; so race to [all that is] good. To Allah is your return all together, and He will [then] inform you concerning that over which you used to differ. <> Kuma Mun saukar da Littãfi zuwa gare ka da gaskiya, yanã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Littãfi (Attaura da Injĩla), kuma mai halartãwa a kansa. sai ka yi hukunci a tsakãninsu da abin da Allah Ya saukar kuma kada ka bĩbiyi son zũciyõyiniu daga abin da ya zo maka daga gaskiya. Ga kõwanne daga gare ku Mun sanya sharĩa da hanya (ta bin ta). Kuma dã Allah Yã so, dã Yã sanya ku al'umma guda, kuma amma dõmin Ya jarraba ku a cikin abin da Ya bã ku. Sai ku yi tsere ga ayyukan alheri. Zuwa ga Allah makõmarku take gabã ɗaya. Sa'an nan Ya bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance kunã sãɓãwa a cikinsa. = --Qur'an 5:48
    And judge, [O Muhammad], between them by what Allah has revealed and do not follow their inclinations and beware of them, lest they tempt you away from some of what Allah has revealed to you. And if they turn away - then know that Allah only intends to afflict them with some of their [own] sins. And indeed, many among the people are defiantly disobedient. <> Kuma ka yi hukunci a tsakãninsu da abin da Allah Ya saukar kuma kada ka bĩbiyi son zũciyõyinsu, kuma ka yi saunar su fitine ka daga sãshen abin da Allah Ya saukar zuwa gare ka. To, idan sun juya bãya, to, ka sani cewa, kawai Allah yana nufin Ya sãme su da masĩfa ne sabõda sãshen zunubansu. Kuma lalle ne, mãsu yawa daga mutãne, haƙĩƙa, fãsiƙai ne. = --Qur'an 5:49
    Then is it the judgement of [the time of] ignorance they desire? But who is better than Allah in judgement for a people who are certain [in faith]. <> Shin, hukuncin Jãhiliyya suke nema? Kuma wane ne mafi kyau ga hukunci daga Allah sabõda mutãne waɗanda suke yin yaƙĩni (tabbataccen ĩmãni)? = --Qur'an 5:50
    O you who have believed, do not take the Jews and the Christians as allies. They are [in fact] allies of one another. And whoever is an ally to them among you - then indeed, he is [one] of them. Indeed, Allah guides not the wrongdoing people. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi Yahudu da Nasãra majiɓinta. Sãshensu majiɓinci ne ga sãshe. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, lalle ne shĩ, yanã daga gare su. Lalle Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai. = --Qur'an 5:51
    So you see those in whose hearts is disease hastening into [association with] them, saying, "We are afraid a misfortune may strike us." But perhaps Allah will bring conquest or a decision from Him, and they will become, over what they have been concealing within themselves, regretful. <> Sai ka ga waɗanda a cikin zukatansu akwai cuta, sunã tseren gaugawa a cikinsu, sunã cewa: "Munã tsõron kada wata masĩfa ta sãme mu." To, akwai tsammãnin Allah Ya zo da buɗi, kõ kuwa wani umurni daga wurinSa, har su wãyi gari a kan abin da suka ɓõye a cikin zukatansu, sunã mãsu nadãmã. = --Qur'an 5:52
    And those who believe will say, "Are these the ones who swore by Allah their strongest oaths that indeed they were with you?" Their deeds have become worthless, and they have become losers. <> Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sunã cewa: "Shin, waɗannan ne waɗanda suka yi rantsuwa da Allah iyãkar rantsuwõyinsu, cewa su, lalle sunã tãre da ku?" Ayyukansu sun ɓãci, sabõda haka suka wãyi gari sunã mãsu hasãra. = --Qur'an 5:53
    O you who have believed, whoever of you should revert from his religion - Allah will bring forth [in place of them] a people He will love and who will love Him [who are] humble toward the believers, powerful against the disbelievers; they strive in the cause of Allah and do not fear the blame of a critic. That is the favor of Allah; He bestows it upon whom He wills. And Allah is all-Encompassing and Knowing. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! wanda ya yi ridda daga gare ku daga addininSa, to, Allah zai zo da wasu mutãne, Yanã son su kuma sunã son Sa, mãsu tawãlu'i a kan muminai mãsu izza a kan kãfurai. Sunã yin, jihãdi a cikin hanyar Allah, kuma bã su tsõron zargin wani mai zargi. Waccan falalar Allah ce, Yanã bãyar da ita ga wanda Yake so. Kuma Allah Mayalwaci ne, Mai ilmi. = --Qur'an 5:54
    Your ally is none but Allah and [therefore] His Messenger and those who have believed - those who establish prayer and give zakah, and they bow [in worship]. <> Abin sani kawai, majiɓincinku Allah ne da ManzonSa da waɗanda suka yi ĩmãni, waɗanda suke sunã tsayar da salla kuma sunã bãyar da zakka kuma sunã ruku'i, = --Qur'an 5:55
    And whoever is an ally of Allah and His Messenger and those who have believed - indeed, the party of Allah - they will be the predominant. <> Kuma wanda ya jiɓinci Allah da ManzonSa da waɗanda suka yi ĩmãni, to, ƙungiyar Allah sune mãsu rinjãya. = --Qur'an 5:56
    O you who have believed, take not those who have taken your religion in ridicule and amusement among the ones who were given the Scripture before you nor the disbelievers as allies. And fear Allah, if you should [truly] be believers. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi waɗanda suka riƙi addininku bisa izgili da wãsa, daga waɗanda aka bai wa Littãfi daga gabãninku da kãfirai, masõya, Kuma ku bi Allah da taƙawa idan kun kasance muminai. = --Qur'an 5:57
    And when you call to prayer, they take it in ridicule and amusement. That is because they are a people who do not use reason. <> Kuma idan kuka yi kira zuwa ga salla, sai su riƙe ta bisa izgili da wãsa. Wannan dõmin lalle ne su, mutãne ne (waɗanda) bã su hankalta. = --Qur'an 5:58
    Say, "O People of the Scripture, do you resent us except [for the fact] that we have believed in Allah and what was revealed to us and what was revealed before and because most of you are defiantly disobedient?" <> Ka ce: "Ya Mutãnen Littãfi! Shin, kunã ganin wani laifi daga gare mu? Fãce dai dõmin mun yi ĩmãni da Allah da abin da aka Saukar zuwa gare mu da abin da aka saukar daga gabãni, kuma dõmin mafi yawanku fãsiƙai ne." = --Qur'an 5:59
    Say, "Shall I inform you of [what is] worse than that as penalty from Allah? [It is that of] those whom Allah has cursed and with whom He became angry and made of them apes and pigs and slaves of Taghut. Those are worse in position and further astray from the sound way." <> Ka ce: "Shin, in gaya muku mafi sharri daga wannan, dõmin sakamako daga wurin Allah? wanda Allah Ya la'ane shi kuma Ya yi fushi da shi, kuma Ya sanya daga gare su birai da aladai, kuma ya bauta wa ¦ãguta. Waɗannan ne mafiya sharrin wuri, kuma mafiya ɓata daga tsakar hanya." = --Qur'an 5:60
    And when they come to you, they say, "We believe." But they have entered with disbelief [in their hearts], and they have certainly left with it. And Allah is most knowing of what they were concealing. <> Kuma idan sun zo muku sai su ce: "Mun yi ĩmãni." Alhãli kuwa haƙĩƙa, sun shigo da kãfirci, kuma su lalle ne, sun fita da shi, kuma Allah ne Mafi sani ga abin da suka kasance sunã ɓõyewa. = --Qur'an 5:61
    And you see many of them hastening into sin and aggression and the devouring of [what is] unlawful. How wretched is what they have been doing. <> Kuma kana ganin mãsu yawa daga gare su, sunã tseren gaugawa a cikin zunubi da zãlunci da cinsu ga haram. Haƙĩƙa, tir da abin da suka kasance suna aikatãwa. = --Qur'an 5:62
    Why do the rabbis and religious scholars not forbid them from saying what is sinful and devouring what is unlawful? How wretched is what they have been practicing. <> Don me Malaman Tarbiyya da manyan malamai (na Yahudu) ba su hanã su daga faɗarsu ga zunubi da cinsu ga haram ba? Haƙiƙa, tir daga abin da suka kasance sunã sanã'antãwa. = --Qur'an 5:63
    And the Jews say, "The hand of Allah is chained." Chained are their hands, and cursed are they for what they say. Rather, both His hands are extended; He spends however He wills. And that which has been revealed to you from your Lord will surely increase many of them in transgression and disbelief. And We have cast among them animosity and hatred until the Day of Resurrection. Every time they kindled the fire of war [against you], Allah extinguished it. And they strive throughout the land [causing] corruption, and Allah does not like corrupters. <> Kuma Yahudu suka ce: "Hannun Allah abin yi wa ƙuƙumi ne. " An sanya hannuwansu a cikin ƙuƙumi! Kuma an la'ane su sabõda abin da suka faɗa. Ã'a, hannuwanSa biyu shimfiɗaɗɗu ne, Yanã ciyarwa yadda Yake so. Kuma lalle ne abin da aka saukar zuwa gare ka yanã ƙãra wa mãsu yawa daga gare su, girman kai da kãfirci. Kuma Mun jefa a tsakãninsu, ƙiyayya da ƙeta, zuwa Rãnar ¡iyãma, kõ da yaushe suka hura wata wuta dõmin yãƙi, sai Allah Ya bice ta. Sunã aiki a cikin ƙasa dõmin ɓarna, alhãli kuwa Allah bã Ya son mãsu fasãdi. = --Qur'an 5:64
    And if only the People of the Scripture had believed and feared Allah, We would have removed from them their misdeeds and admitted them to Gardens of Pleasure. <> Kuma dã dai lalle Mutãnen Littãfi sun yi ĩmãni, kuma sun yi taƙawa, haƙĩƙa, dã Mun kankare miyãgun ayyukansu daga gare su, kuma dã Mun shigar da su gidãjen Aljannar Ni'ima. = --Qur'an 5:65
    And if only they upheld [the law of] the Torah, the Gospel, and what has been revealed to them from their Lord, they would have consumed [provision] from above them and from beneath their feet. Among them are a moderate community, but many of them - evil is that which they do. <> Kuma dã dai lalle su, sun tsayar da Attaura da Injĩla da abin da aka saukar zuwa gare su daga Ubangijinsu, haƙĩƙa, dã sun ci daga bisansu da kuma daga ƙarƙashin ƙafãfunsu. Daga gare su akwai wata al'umma mai tsakaitãwa kuma mãsu yawa daga gare su, abin da suke aikatawa yã munana. = --Qur'an 5:66
    O Messenger, announce that which has been revealed to you from your Lord, and if you do not, then you have not conveyed His message. And Allah will protect you from the people. Indeed, Allah does not guide the disbelieving people. <> Yã kai Manzo! Ka iyar da abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka. Kuma idan ba ka aikata ba, to, ba ka iyar da manzancinSa ba ke nan. Kuma Allah Yanã tsare ka daga mutãne. Lalle ne, Allah bã Ya shiryar da mutãne kãfirai. = --Qur'an 5:67
    Say, "O People of the Scripture, you are [standing] on nothing until you uphold [the law of] the Torah, the Gospel, and what has been revealed to you from your Lord." And that which has been revealed to you from your Lord will surely increase many of them in transgression and disbelief. So do not grieve over the disbelieving people. <> Ka ce: "Yã ku Mutãnen Littãfi! Ba ku zama a kan kõme ba, sai kun tsayar da Attaura da Injĩla da abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku."Kuma lalle ne, abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, yanã ƙara wa mãsu yawa daga gare su girman kai da kãfirci. To, kada ka yi baƙin ciki a kan mutãne kãfirai. = --Qur'an 5:68
    Indeed, those who have believed [in Prophet Muhammad] and those [before Him] who were Jews or Sabeans or Christians - those [among them] who believed in Allah and the Last Day and did righteousness - no fear will there be concerning them, nor will they grieve. <> Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmãni da waɗanda sukatuba (Yahũdu) da Karkatattu da Nasãra, wanda ya yi ĩmãni da Allahda Rãnar Lãhira, kuma ya aikata aiki na ƙwarai, to, bãbu tsõro a kansu, kuma bã su zamo sunã baƙin ciki ba. = --Qur'an 5:69
    We had already taken the covenant of the Children of Israel and had sent to them messengers. Whenever there came to them a messenger with what their souls did not desire, a party [of messengers] they denied, and another party they killed. <> Lalle ne haƙĩƙa Mun riƙi alkawarin Bani Isrã'ĩla, kumaMun aiki manzanni zuwa gare su, ko da yaushe wani manzo ya je musu da abin da rãyukansu bã su so, wani ɓangare sun ƙaryata, kuma wani ɓangare sunã kashewa, = --Qur'an 5:70
    And they thought there would be no [resulting] punishment, so they became blind and deaf. Then Allah turned to them in forgiveness; then [again] many of them became blind and deaf. And Allah is Seeing of what they do. <> Kuma suka yi zaton cewa wata fitina bã zã ta kasance ba sai Suka makanta, kuma suka kurubta, sa'an nan Allah Ya karɓi tuba a gare su, sa'an nan suka makanta kuma suka kurunta mãsu yawa daga gare su, alhãli Allah Mai gani ne ga abin da suke aikatãwa. = --Qur'an 5:71
    They have certainly disbelieved who say, "Allah is the Messiah, the son of Mary" while the Messiah has said, "O Children of Israel, worship Allah, my Lord and your Lord." Indeed, he who associates others with Allah - Allah has forbidden him Paradise, and his refuge is the Fire. And there are not for the wrongdoers any helpers. <> Lalle ne haƙĩƙa waɗanda suka ce: "Lalle ne Allah, shĩne Masĩhu, ɗan Maryama," sun kãfirta. Alhãli kuwa Masĩhu yã ce: "Yã Banĩ Isrã'ĩla! Ku bauta wa Allah Ubangijina, kuma Ubangijinku." Lalle ne shĩ, wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne, Allah Yã haramta masa Aljanna. Kuma bãbu wasu mataimaka ga azzãlumai. = --Qur'an 5:72
    They have certainly disbelieved who say, "Allah is the third of three." And there is no god except one God. And if they do not desist from what they are saying, there will surely afflict the disbelievers among them a painful punishment. <> Lalle ne, haƙĩƙa, waɗanda suka ce: "Allah na ukun uku ne," sun kãfirta, kuma babu wani abin bautãwa fãce Ubangji Guda. Kuma idan ba su hanu daga abin da suke faɗa ba, haƙĩƙa, wata azãba mai raɗaɗi tãnã shãfar waɗanda suka kãfirta daga gare su. = --Qur'an 5:73
    So will they not repent to Allah and seek His forgiveness? And Allah is Forgiving and Merciful. <> shin fã, bã su tuba zuwa ga Allah, kuma su neme Shi gãfara, alhãli kuwa Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai? = --Qur'an 5:74
    The Messiah, son of Mary, was not but a messenger; [other] messengers have passed on before him. And his mother was a supporter of truth. They both used to eat food. Look how We make clear to them the signs; then look how they are deluded. <> Masĩhu ɗan Maryama bai zama ba fãce Manzo ne kawai, haƙĩƙa, manzanni sun shige dage gabãninsa, kuma uwarsa siddika ce. Sun kasance sunã cin abinci. Ka duba yadda Muke bayyana musu ãyõyi. Sa'an nan kuma ka duba yadda ake karkatar da su. = --Qur'an 5:75
    Say, "Do you worship besides Allah that which holds for you no [power of] harm or benefit while it is Allah who is the Hearing, the Knowing?" <> Ka ce: "Ashe kunã bauta wa, baicin Allah, abin da ba ya mallakar wata cuta sabõda ku kuma haka wani amfani alhãli kuwa Allah Shi ne Mai ji, Masani?" = --Qur'an 5:76
    Say, "O People of the Scripture, do not exceed limits in your religion beyond the truth and do not follow the inclinations of a people who had gone astray before and misled many and have strayed from the soundness of the way." <> Ka ce: "Yã ku Mutanen Littãfi! Kada ku zurfafa a cikin addininku, abin da bã gaskiya ba, kuma kada ku bĩbiyi son zuciyõyin waɗansu mutãne waɗanda suka riga suka ɓace a gabãni, kuma suka ɓatar da wasu mãsu yawa, kuma suka ɓace daga tsakar hanya." = --Qur'an 5:77
    Cursed were those who disbelieved among the Children of Israel by the tongue of David and of Jesus, the son of Mary. That was because they disobeyed and [habitually] transgressed. <> An la'ani waɗanda suka kãfirta daga Banĩ Isrã'ĩla a kan harshen Dãwuda da Ĩsa ɗan Maryama. wannan kuwa sabõda sãɓãwar da suka yi ne, kuma sun kasance suna ta'addi. = --Qur'an 5:78
    They used not to prevent one another from wrongdoing that they did. How wretched was that which they were doing. <> Sun kasance bã su hana juna daga abin ƙi, wanda suka aikata. Haƙĩƙa abin da suka kasancesunã aikatãwa yã munana. = --Qur'an 5:79
    You see many of them becoming allies of those who disbelieved. How wretched is that which they have put forth for themselves in that Allah has become angry with them, and in the punishment they will abide eternally. <> Kana ganin mãsu yawa daga gare su, sunã jiɓintar waɗanda suka kãfirta. Haƙĩƙa tir da abin da rãyukansu suka gabãtar sabõda su, watau Allah Yã yi fushi da su, kuma a cikin azãba su mãsu dawwama ne = --Qur'an 5:80
    And if they had believed in Allah and the Prophet and in what was revealed to him, they would not have taken them as allies; but many of them are defiantly disobedient. <> Kuma dã sun kasance sunã ĩmãni da Allah da Annabi da abin da aka saukar zuwa gare shi, dã ba su riƙe su masõya ba. Kuma amma mãsu yawa daga gare su, fãsiƙai ne. = --Qur'an 5:81
    You will surely find the most intense of the people in animosity toward the believers [to be] the Jews and those who associate others with Allah; and you will find the nearest of them in affection to the believers those who say, "We are Christians." That is because among them are priests and monks and because they are not arrogant. <> Lalle ne kana sãmun mafiya tsananin mutãne a adãwa ga waɗanda suka yi ĩmãni, Yahudu ne da waɗanda suka yi shirki. Kuma lalle ne kanã sãmun mafiya kusantarsu a sõyayya ga waɗanda suka yi ĩmãni su ne waɗanda suka ce: "Lalle mu ne Nasãra." Wancan kuwa sabõda akwai ¡issawa da ruhubãnãwa daga cikinsu. Kuma lalle ne su, bã su yin girman kai. = --Qur'an 5:82
    And when they hear what has been revealed to the Messenger, you see their eyes overflowing with tears because of what they have recognized of the truth. They say, "Our Lord, we have believed, so register us among the witnesses. <> Kuma idan suka ji abin da aka saukar zuwa ga Manzo, kanã ganin idanunsu sunã zubar da hawãye, sabõda abin da suka sani daga gaskiya, sunã cewa: "Yã Ubangijinmu! Mun yi ĩmãni, sai ka rubuta mu tãre da mãsu shaida. = --Qur'an 5:83
    And why should we not believe in Allah and what has come to us of the truth? And we aspire that our Lord will admit us [to Paradise] with the righteous people." <> "Kuma mene ne yake gare mu, bã zã mu yi ĩmãni daAllah ba, da kuma abin da ya zo mana daga gaskiya, kuma munã gurin Ubangijinmu Ya shigar da mu tãre da mutãne sãlihai?" = --Qur'an 5:84
    So Allah rewarded them for what they said with gardens [in Paradise] beneath which rivers flow, wherein they abide eternally. And that is the reward of doers of good. <> Sabõda haka, Allah Yã sãkã musu, dõmin abin da suka faɗa da gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙõramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu, kuma wannan ne sakamakon mãsu kyautatãwa. = --Qur'an 5:85
    But those who disbelieved and denied Our signs - they are the companions of Hellfire. <> Kuma waɗanda suka kãfirta kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu, waɗancan ne abõkan Wuta. = --Qur'an 5:86
    O you who have believed, do not prohibit the good things which Allah has made lawful to you and do not transgress. Indeed, Allah does not like transgressors. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku haramta abubuwa mãsu dãɗi da Allah Ya halatta muku, kuma kada ku ƙetare haddi. Lalle ne, Allah bã Ya son mãsu ƙetare haddi. = --Qur'an 5:87
    And eat of what Allah has provided for you [which is] lawful and good. And fear Allah, in whom you are believers. <> Kuma ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku, halat mai daɗi, kuma ku bi Allah da taƙawa, wanda yake ku, mãsu ĩmãni ne da shi. = --Qur'an 5:88
    Allah will not impose blame upon you for what is meaningless in your oaths, but He will impose blame upon you for [breaking] what you intended of oaths. So its expiation is the feeding of ten needy people from the average of that which you feed your [own] families or clothing them or the freeing of a slave. But whoever cannot find [or afford it] - then a fast of three days [is required]. That is the expiation for oaths when you have sworn. But guard your oaths. Thus does Allah make clear to you His verses that you may be grateful. <> Allah bã Ya kãmã ku sabõda yãsassa a cikin rantsuwõyinku, kuma amma Yanã kãmã ku da abin da kuka ƙudurta rantsuwõyi (a kansa). To, kaffãrarsa ita ce ciyar da miskĩni gõma daga matsakaicin abin da kuke ciyar da iyãlanku, kõ kuwa tufãtar da su, kõ kuwa 'yantãwar wuya. Sa'an nan wanda bai sãmu ba, sai azumin kwãna uku. wannan ne kaffãrar rantsuwõyinku, idan kun rantse. Kuma ku kiyãye rantsuwoyinku. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ãyoyinsa, tsammãninku kunã gõdewa. = --Qur'an 5:89
    O you who have believed, indeed, intoxicants, gambling, [sacrificing on] stone alters [to other than Allah], and divining arrows are but defilement from the work of Satan, so avoid it that you may be successful. <> Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, giya da cãca da refu da kiban ƙuri'a, ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku nĩsance shi, wa la'alla ku ci nasara. = --Qur'an 5:90
    Satan only wants to cause between you animosity and hatred through intoxicants and gambling and to avert you from the remembrance of Allah and from prayer. So will you not desist? <> Abin sani kawaĩ Shaiɗan yanã nufin ya aukar da adãwa da ƙeta a tsakãninku, a cikin giya da cãca, kuma ya kange ku daga ambaton Allah, kuma daga sallah. To, shin, ku mãsu hanuwa ne? = --Qur'an 5:91
    And obey Allah and obey the Messenger and beware. And if you turn away - then know that upon Our Messenger is only [the responsibility for] clear notification. <> Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga Manzo, kuma ku kiyãye. To, idan kun jũya, to, ku sani abin da kawai yake kan ManzonMu, iyarwa bayyananniya. = --Qur'an 5:92
    There is not upon those who believe and do righteousness [any] blame concerning what they have eaten [in the past] if they [now] fear Allah and believe and do righteous deeds, and then fear Allah and believe, and then fear Allah and do good; and Allah loves the doers of good. <> Bãbu laifi a kan waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, a cikin abin da suka ci, idan sun yi taƙawa kuma suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sa'an nan suka yi taƙawa kuma suka yi ĩmãni, sa'an nan kuma suka yi taƙawa kuma suka kyautata. Kuma Allah Yana son mãsu kyautatãwa. = --Qur'an 5:93
    O you who have believed, Allah will surely test you through something of the game that your hands and spears [can] reach, that Allah may make evident those who fear Him unseen. And whoever transgresses after that - for him is a painful punishment. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne, Allah zai jarraba ku da wani abu, daga farauta, hannuwanku da mãsunku sunã sãmun sa dõmin Allah Ya san wanda yake tsoron Sa a fake. To, wanda ya yi ta'addi a bãyan wannan, to, yanã da azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 5:94
    O you who have believed, do not kill game while you are in the state of ihram. And whoever of you kills it intentionally - the penalty is an equivalent from sacrificial animals to what he killed, as judged by two just men among you as an offering [to Allah] delivered to the Ka'bah, or an expiation: the feeding of needy people or the equivalent of that in fasting, that he may taste the consequence of his deed. Allah has pardoned what is past; but whoever returns [to violation], then Allah will take retribution from him. And Allah is Exalted in Might and Owner of Retribution. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kashe farauta alhãli kunã mãsu harama. Kuma wanda ya kashe shi daga gare ku, yanã mai ganganci, sai sakamako misãlin abin da ya kashe, daga dabbõbin ni'ima, ma'abuta ãdalci biyu daga cikinku sunã yin hukunci da shi. Ya zama hadaya mai isa ga Ka'aba ko kuwa kaffãra da abincin miskĩnai ko kuwa a matsayinsa ya yi azumi dõmin ya ɗanɗani masifar al'amarinsa. Allah Yã yafe laifi daga abin da ya gabãta. Kuma wanda ya kõma, to, Allah zai yi azãbar rãmuwa daga gare shi, kuma Allah Mabuwãyi ne, ma'abũcin azabãr rãmuwa. = --Qur'an 5:95
    Lawful to you is game from the sea and its food as provision for you and the travelers, but forbidden to you is game from the land as long as you are in the state of ihram. And fear Allah to whom you will be gathered. <> An halatta muku farautar ruwa da abincinsa dõmin jin dãɗi a gare ku, kuma dõmin matafiya. Kuma an haramta farautar tudu a kanku, matuƙar kun dawwama mãsu harama. Kuma ku bi Allah da taƙawa, wanda yake zuwa gare Shi ne ake tãra ku. = --Qur'an 5:96
    Allah has made the Ka'bah, the Sacred House, standing for the people and [has sanctified] the sacred months and the sacrificial animals and the garlands [by which they are identified]. That is so you may know that Allah knows what is in the heavens and what is in the earth and that Allah is Knowing of all things. <> Allah Ya sanya Ka'aba ¦aki Tsararre, ma'aunin addini ga mutane, kuma Yã sanya watã Mai alfarma da hadaya da rãtayõyin Allah Yã san abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, kuma cewa lalle Allah, ga dukkan, kõme, Masani ne. = --Qur'an 5:97
    Know that Allah is severe in penalty and that Allah is Forgiving and Merciful. <> Ku sani cewa lalle Allah Mai tsananin uƙuba ne, kuma lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 5:98
    Not upon the Messenger is [responsibility] except [for] notification. And Allah knows whatever you reveal and whatever you conceal. <> Bãbu abin da yake a kan Manzo, sai iyarwa, kuma Allah Yanã sanin abin da kuke bayyanãwa da abin da kuke ɓõyewa. = --Qur'an 5:99
    Say, "Not equal are the evil and the good, although the abundance of evil might impress you." So fear Allah, O you of understanding, that you may be successful. <> Ka ce: "Mummuna da mai kyau bã su daidaita, kuma kõ dã yawan mummuan yã bã ka sha'awa. Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, yã ma'abuta hankula ko la'alla zã ku ci nasara." = --Qur'an 5:100
    O you who have believed, do not ask about things which, if they are shown to you, will distress you. But if you ask about them while the Qur'an is being revealed, they will be shown to you. Allah has pardoned that which is past; and Allah is Forgiving and Forbearing. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku yi tambaya ga abubuwa, idan an bayyana muku (hukuncinsu) su ɓãta muku rai. Kuma idan kuka yi tambaya a gare su a lõkacin da ake saukar da Alƙur'ãni, zã a bayyana maku. Allah Yã yãfe laifi daga gare su, Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri. = --Qur'an 5:101
    A people asked such [questions] before you; then they became thereby disbelievers. <> Lalle ne wasu mutãne sun tambaye su daga gabãninku, sa'an nan kuma suka wãyi gari da su sanã kãfirai. = --Qur'an 5:102
    Allah has not appointed [such innovations as] bahirah or sa'ibah or wasilah or ham. But those who disbelieve invent falsehood about Allah, and most of them do not reason. <> Kuma Allah bai sanya wata bahĩra ba, kuma haka sã'iba, kuma haka wasĩla, kuma haka hãmi, amma waɗanda suka kãfirta, su suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma mafi yawansu bã su hankalta. = --Qur'an 5:103
    And when it is said to them, "Come to what Allah has revealed and to the Messenger," they say, "Sufficient for us is that upon which we found our fathers." Even though their fathers knew nothing, nor were they guided? <> Kuma idan aka ce musu: "Ku zo zuwa ga abin da Allah Ya saukar, kuma zuwa ga Manzo," sai su ce: "Mai isarmu shi ne abin da muka iske ubanninmu a kansa." Shin, kuma kõ dã ubanninsu sun kasance bã su sanin kõme kuma bã su shiryuwa? = --Qur'an 5:104
    O you who have believed, upon you is [responsibility for] yourselves. Those who have gone astray will not harm you when you have been guided. To Allah is you return all together; then He will inform you of what you used to do. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku lazimci rãyukanku, wanda ya ɓace bã zai cuce ku ba idan kun shiryu, zuwa ga Allah makõmarku take gabã ɗaya. Sa'an nan Ya bã ku lãbari ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa. = --Qur'an 5:105
    O you who have believed, testimony [should be taken] among you when death approaches one of you at the time of bequest - [that of] two just men from among you or two others from outside if you are traveling through the land and the disaster of death should strike you. Detain them after the prayer and let them both swear by Allah if you doubt [their testimony, saying], "We will not exchange our oath for a price, even if he should be a near relative, and we will not withhold the testimony of Allah. Indeed, we would then be of the sinful." <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Shaidar tsakãninku, idan mutuwa ta halarci ɗayanku, a lõkacin wasiyya, maza biyu ne ma'abuta ãdalci daga gare ku, kõ kuwa wasu biyu daga wasunku idan kun tafi a cikin ƙasa sa'an nan masĩfarmutuwa ta sãme ku. Kunã tsare su daga bãyan salla har su yi rantsuwa da Allah; idan kun yi shakka: "Bã mu sayen kuɗi da shi, kõ dã ya kasance ma'abucin zumunta kuma bã mu ɓõye shaidar Allah. Lalle ne mu, a lõkacin, haƙĩƙa, munã daga mãsu zunubi." = --Qur'an 5:106
    But if it is found that those two were guilty of perjury, let two others stand in their place [who are] foremost [in claim] from those who have a lawful right. And let them swear by Allah, "Our testimony is truer than their testimony, and we have not transgressed. Indeed, we would then be of the wrongdoers." <> To, idan aka gane cewa lalle sũ, sun cancanci zunubi to sai wasu biyu su tsayu matsayibsu daga waɗanda suka karɓa daga gare su, mutãne biyu mafiya cancanta, sa'an nan su yi rantsuwa da Allah: "Lalle ne shaidarmu ce mafi gaskiya daga shaidarsu, kuma ba mu yi zãlunci ba. Lalle mu, a lõkacin haƙĩƙa, munã daga azzãlumai." = --Qur'an 5:107
    That is more likely that they will give testimony according to its [true] objective, or [at least] they would fear that [other] oaths might be taken after their oaths. And fear Allah and listen; and Allah does not guide the defiantly disobedient people. <> Wannan ne mafi kusantar su zo da shaida a kan fuskarta kõ kuwa su yi tsõron a tũre rantsuwõyi a bãyan rantsuwõyinsu. Kuma ku bi Allah da taƙawa kuma ku saurara, kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fãsiƙai. = --Qur'an 5:108
    [Be warned of] the Day when Allah will assemble the messengers and say, "What was the response you received?" They will say, "We have no knowledge. Indeed, it is You who is Knower of the unseen" <> A ranar da Allah Yake tãra manzanni sa'an nan Ya ce: "Mene ne aka karɓa muku?" (zã) su ce: "Bãbu ilmi a gare mu. Lalle ne Kai, Kai ne Masanin abubuwan fake." = --Qur'an 5:109
    [The Day] when Allah will say, "O Jesus, Son of Mary, remember My favor upon you and upon your mother when I supported you with the Pure Spirit and you spoke to the people in the cradle and in maturity; and [remember] when I taught you writing and wisdom and the Torah and the Gospel; and when you designed from clay [what was] like the form of a bird with My permission, then you breathed into it, and it became a bird with My permission; and you healed the blind and the leper with My permission; and when you brought forth the dead with My permission; and when I restrained the Children of Israel from [killing] you when you came to them with clear proofs and those who disbelieved among them said, "This is not but obvious magic." <> A lõkacin da Allah Ya ce: "Yã Ĩsã ɗan Maryama! Ka tuna ni'ima Ta a kanka, kuma a kan mahaifiyarka, a lõkacin da Na ƙarfafa ka da Rũhul ¡udusi, kanã yiwa mutãne magana a cikin shimfiɗar jariri, da kuma kanã dattijo. Kuma a lõkacin da Na sanar da kai rubutu da hikima da Attaura da Injĩla, kuma a lõkacin da kake yin halitta daga lãkã kamar surar tsuntsu da izinĩNa, sa'an nan ka hura a cikinta sai ta zama tsuntsu da izinĩNa, kuma kanã warkar da haifaffen makaho da kuturu, da izinĩNa, kuma a lõkacin da kake fitar da matattu da izinĩNa, kuma a lõkacin da Na kange Banĩ Isrã'ĩla daga gare ka, a lõkacin da ka je musu da hujjõji bayyanannu, sai waɗanda suka kãfirta daga cikinsu suka ce: 'Wannan bã kõme ba ne, fãce sihiri bayyananne.' = --Qur'an 5:110
    And [remember] when I inspired to the disciples, "Believe in Me and in My messenger Jesus." They said, "We have believed, so bear witness that indeed we are Muslims [in submission to Allah]." <> "Kuma a lõkacin da Na yi wahayi zuwa ga Hawãriyãwa cewa ku yi ĩmãni da Ni, kuma da ManzoNa. Suka ce: "Mun yi ĩmãni, kuma ka shaida da cewa lalle mu, mãsu sallamãwa ne." = --Qur'an 5:111
    [And remember] when the disciples said, "O Jesus, Son of Mary, can your Lord send down to us a table [spread with food] from the heaven? [Jesus] said," Fear Allah, if you should be believers." <> A lõkacin da Hawarãyãwa suka ce: "Ya Ĩsa ɗan Maryam! shin, Ubangijinka Yanã iyãwa Ya saukar da kaɓaki a kanmu daga samã?" (Ĩsã) Ya ce: "Ku bi Allah da taƙawa idan kun kasance muminai." = --Qur'an 5:112
    They said, "We wish to eat from it and let our hearts be reassured and know that you have been truthful to us and be among its witnesses." <> Suka ce: "Munã nufin mu ci daga gare shi ne, kuma zukãtanmu su natsu kuma mu san cewa lalle ne, kã yi mana gaskiya, kuma mu kasance daga mãsu shaida a kansa." = --Qur'an 5:113
    Said Jesus, the son of Mary, "O Allah, our Lord, send down to us a table [spread with food] from the heaven to be for us a festival for the first of us and the last of us and a sign from You. And provide for us, and You are the best of providers." <> Ĩsã ɗan Maryam ya ce: "Yã Allah. Ubangijinmu! Ka saukar da kaɓaki a kanmu daga sama dõmin ya zama ĩdi ga na farkonmu da na ƙarshenmu, kuma ya zama ãyã daga gare Ka. Ka azurta mu, kuma Kai ne Mafĩfĩcin mãsu azurtawa." = --Qur'an 5:114
    Allah said, "Indeed, I will sent it down to you, but whoever disbelieves afterwards from among you - then indeed will I punish him with a punishment by which I have not punished anyone among the worlds." <> Allah Ya ce: "Lalle ne Nĩ mai saukar da shi ne a kanku sa'an nan wanda ya kãfirta daga gare ku, to, lalle ne Nĩ, Inã azabta shi, da wata azãba wadda bã Ni azabta ta ga kõwa daga tãlikai." = --Qur'an 5:115
    And [beware the Day] when Allah will say, "O Jesus, Son of Mary, did you say to the people, 'Take me and my mother as deities besides Allah?'" He will say, "Exalted are You! It was not for me to say that to which I have no right. If I had said it, You would have known it. You know what is within myself, and I do not know what is within Yourself. Indeed, it is You who is Knower of the unseen. <> Kuma a lõkacin da Allah Ya ce: "Yã Ĩsã ɗan Maryama! Shin, kai ne ka ce wa mutãne, 'Ku riƙe ni, ni da uwata, abubuwan bautãwa biyu, baicin Allah?" (Ĩsã) Ya ce: "Tsarkinka yã tabbata! Bã ya kasancewa a gare ni, in faɗi abin da bãbu wani hakki a gare ni. Idan nã kasance nã faɗe shi, to lalle Ka san shi, Kanã sanin abin da ke a cikin raina, kuma bã ni sanin abin da ke a cikin nufinKa. Lalle ne Kai Masanin abubuwan fake ne." = --Qur'an 5:116
    I said not to them except what You commanded me - to worship Allah, my Lord and your Lord. And I was a witness over them as long as I was among them; but when You took me up, You were the Observer over them, and You are, over all things, Witness. <> "Ban faɗa musu ba fãce abin da Ka umurce ni da shi; watau: 'Ku bauta wa Allah Ubangijina kuma Ubangijinku;' kuma nã kasance mai shaida a kansu matuƙar nã dawwama a cikinsu, sa'an nan a lõkacin da Ka karɓi raina Kã kasance Kai ne mai tsaro a kansu, kuma Kai, a kan dukkan kõme, Halartacce ne. = --Qur'an 5:117
    If You should punish them - indeed they are Your servants; but if You forgive them - indeed it is You who is the Exalted in Might, the Wise. <> "Idan Ka azabta su, to lalle ne su, bãyinKa ne, kuma idan Ka gãfarta musu, to, lalle ne Kai ne Mabuwayi Mai hikima." = --Qur'an 5:118
    Allah will say, "This is the Day when the truthful will benefit from their truthfulness." For them are gardens [in Paradise] beneath which rivers flow, wherein they will abide forever, Allah being pleased with them, and they with Him. That is the great attainment. <> Allah Ya ce: "Wannan ce rãnar da mãsu gaskiya, gaskiyarsu take amfãninsu. Sunã da gidãjen Aljanna, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu har abada. Allah Yã yarda da su, kuma sun yarda da Shi. wannan ne babban rabo mai girma." = --Qur'an 5:119
    To Allah belongs the dominion of the heavens and the earth and whatever is within them. And He is over all things competent. <> Allah ne da mallakar sammai da ƙasa da abin da ke a cikinsu kuma shi, a kan dukkan kõme Mai ĩkon yi ne. = --Qur'an 5:120
    [All] praise is [due] to Allah, who created the heavens and the earth and made the darkness and the light. Then those who disbelieve equate [others] with their Lord. <> Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya halitta sammai da ƙasa, kuma Ya sanya duffai da haske, sa'an nan kuma waɗanda suka kãfirta, da Ubangijinsu suke karkacewa. = --Qur'an 6:1
    It is He who created you from clay and then decreed a term and a specified time [known] to Him; then [still] you are in dispute. <> Shi ne wanda Ya halitta ku daga lãkã, sa'an nan kuma Ya yanka ajali alhãli wani ajali ambatacce yanã wurinSa. Sa'an nan kuma ku kunã yin shakka. = --Qur'an 6:2
    And He is Allah, [the only deity] in the heavens and the earth. He knows your secret and what you make public, and He knows that which you earn. <> Kuma Shĩ ne Allah a cikin sammai, kuma a cikin ƙasa Yanã sanin asĩrinku da bayyanenku, kuma Yanã sanin abin da kuke yi na tsirfa. = --Qur'an 6:3
    And no sign comes to them from the signs of their Lord except that they turn away therefrom. <> Kuma wata ãyã daga Ubangijinsu ba zã ta jẽ musu ba, fãce su kasance, daga gare ta, mãsu bijirẽwa. = --Qur'an 6:4
    For they had denied the truth when it came to them, but there is going to reach them the news of what they used to ridicule. <> Sabõda haka, lalle sun ƙaryata (Manzo) game da gaskiya, a lõkacin da ta jẽ musu, to lãbãrun abin da suka kasance sunã izgili da shi, zã su jẽ musu. = --Qur'an 6:5
    Have they not seen how many generations We destroyed before them which We had established upon the earth as We have not established you? And We sent [rain from] the sky upon them in showers and made rivers flow beneath them; then We destroyed them for their sins and brought forth after them a generation of others. <> Shin, ba su gani ba, da yawa Muka halakar da wani ƙarni daga gabãninsu, Mun mallaka musu, a ckikin ƙasa, abin da ba Mu mallaka muku ba kuma Muka saki sama a kansu tanã ta zuba, kuma Muka sanya kõguna sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sa'an nan Muka halakã su sabõda zunubansu kuma Muka ƙãga halittar wani ƙarni na dabam daga bayansu? = --Qur'an 6:6
    And even if We had sent down to you, [O Muhammad], a written scripture on a page and they touched it with their hands, the disbelievers would say, "This is not but obvious magic." <> Kuma dã Mun sassaukar da wani littãfi, zuwa gare ka, a cikin takarda, sa'an nan suka taɓa shi da hannuwansu, lalle dã waɗanda suka kãfirta sun ce: "Wannan bai zama ba, face sihiri bayyananne." = --Qur'an 6:7
    And they say, "Why was there not sent down to him an angel?" But if We had sent down an angel, the matter would have been decided; then they would not be reprieved. <> Suka ce: "Don me ba a saukar da wani malã'ika ba a gare shi?" to dã Mun saukar da malã'ika haƙĩƙa dã an hukunta al'amarin sa'an nan kuma ba zã a yi musu jinkiri ba. = --Qur'an 6:8
    And if We had made him an angel, We would have made him [appear as] a man, and We would have covered them with that in which they cover themselves. <> Kuma dã Mun sanya malã'ika ya zama manzo lalle ne dã Mun mayar da shi mutum, kuma dã Mun rikita musu abin da suke rikitãwa. = --Qur'an 6:9
    And already were messengers ridiculed before you, but those who mocked them were enveloped by that which they used to ridicule. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili da manzanni daga gabaninka, sai waɗanda suka yi izgilin, abin da suka kasance sunã izgili da shi ya fãɗa musu. = --Qur'an 6:10
    Say, "Travel through the land; then observe how was the end of the deniers." <> Ka ce: "Ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan kuma ku dũba yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance." = --Qur'an 6:11
    Say, "To whom belongs whatever is in the heavens and earth?" Say, "To Allah." He has decreed upon Himself mercy. He will surely assemble you for the Day of Resurrection, about which there is no doubt. Those who will lose themselves [that Day] do not believe. <> Ka ce: "Na wãne ne abin da yake a cikin sammai da ƙasa?" Ka ce: "Na Allah ne." Yã wajabta rahama ga kanSa. Lalle ne Yanã tãra ku zuwa ga Rãnar ¡iyãma, babu shakka a gare Shi. Waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, to, sũ ba zã su yi ĩmani ba." = --Qur'an 6:12
    And to Him belongs that which reposes by night and by day, and He is the Hearing, the Knowing. <> "Kuma Shĩ ne da mallakar abin da ya yi kawaici a cikin dare da yini, kuma Shi ne Mai ji, Masani." = --Qur'an 6:13
    Say, "Is it other than Allah I should take as a protector, Creator of the heavens and the earth, while it is He who feeds and is not fed?" Say, [O Muhammad], "Indeed, I have been commanded to be the first [among you] who submit [to Allah] and [was commanded], 'Do not ever be of the polytheists.' " <> Ka ce: "Shin, wanin Allah nike riƙo majiɓinci, (alhãli Allah ne) Mai ƙãga halittar sammai da ƙasa, kuma Shi, Yanã ciyarwa, kuma ba a ciyar da Shi?" Ka ce: "Lalle ne nĩ, an umurce ni da in kasance farkon wanda ya sallama, kuma kada lalle ku kasance daga mãsu shirki." = --Qur'an 6:14
    Say, "Indeed I fear, if I should disobey my Lord, the punishment of a tremendous Day." <> Kace: "Lalle ne nĩ inã tsõron azãbar Yini Mai girma, idan nã sãɓã wa Ubangijina." = --Qur'an 6:15
    He from whom it is averted that Day - [Allah] has granted him mercy. And that is the clear attainment. <> "Wanda aka jũyar da shi daga gare shi, a wannan Rãnar, to, lalle ne, (Allah) Yã yi masa rahama, Kuma wannan ne tsĩra bayyananniya." = --Qur'an 6:16
    And if Allah should touch you with adversity, there is no remover of it except Him. And if He touches you with good - then He is over all things competent. <> "Idan Allah Ya shãfe ka da wata cũta, to, babu mai kuranyẽwa gare ta, fãce Shĩ, kuma idanYa shãfe ka da wani alhẽri to shĩ ne, a kan kõme, Mai ĩkon yi." = --Qur'an 6:17
    And He is the subjugator over His servants. And He is the Wise, the Acquainted [with all]. <> "Kuma Shĩ ne mai Tanƙwasa a kan bayinSa, kuma Shi ne Mai hikima, Masani." = --Qur'an 6:18
    Say, "What thing is greatest in testimony?" Say, "Allah is witness between me and you. And this Qur'an was revealed to me that I may warn you thereby and whomever it reaches. Do you [truly] testify that with Allah there are other deities?" Say, "I will not testify [with you]." Say, "Indeed, He is but one God, and indeed, I am free of what you associate [with Him]." <> Ka ce: "Wane abu ne mafi girma ga shaida?" Ka ce: "Allah ne shaida a tsakãnina da tsakaninku. Kuma an yiwo wahayin wannan Alƙur'ãni dõmin in yi muku gargaɗi da shi, da wanda lãbãri ya kai gare shi. Shin lalle ne ku, haƙĩƙa, kunã shaidar cẽwa, lalle ne tãre da Allah akwai wasu abũbuwan bautawa?" Ka ce: "Bã zan yi shaidar (haka) ba." Ka ce: "Abin sani, Shi ne Abin bautãwa Guda kumã lalle ne nĩ barrantacce ne daga abin da kuke yi na shirki." = --Qur'an 6:19
    Those to whom We have given the Scripture recognize it as they recognize their [own] sons. Those who will lose themselves [in the Hereafter] do not believe. <> Waɗanda Muka bã su Littãfi sunã sanin sa kamar yadda suke sanin ɗiyansu. Waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, to, sũ bã su yin ĩmãni. = --Qur'an 6:20
    And who is more unjust than one who invents about Allah a lie or denies His verses? Indeed, the wrongdoers will not succeed. <> Wãne ne mafi zãlunci daga wanda yake ƙirƙira karya ga Allah, kõ kuwa ya ƙaryata game da ãyõyinsa? Lalle ne shĩ, azzalumai bã zã su ci nasara ba. = --Qur'an 6:21
    And [mention, O Muhammad], the Day We will gather them all together; then We will say to those who associated others with Allah, "Where are your 'partners' that you used to claim [with Him]?" <> Kuma rãnar da Muka tãra su gabã ɗaya, sa'an nan Mu ce wa waɗanda suka yi shirki: "Inã abõkan tãrayyarku waɗanda kuka kasance kunã riyãwa?" = --Qur'an 6:22
    Then there will be no [excuse upon] examination except they will say, "By Allah, our Lord, we were not those who associated." <> Sa'an nan kuma fitinarsu ba ta kasance ba, fãce dõmin sun ce: "Munã rantsuwa da Allah Ubangijinmu, ba mu kasance mãsu yin shirki ba." = --Qur'an 6:23
    See how they will lie about themselves. And lost from them will be what they used to invent. <> Ka dũba yadda suka ƙaryata kansu! Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙira ƙaryarsa, ya ɓace daga gare su. = --Qur'an 6:24
    And among them are those who listen to you, but We have placed over their hearts coverings, lest they understand it, and in their ears deafness. And if they should see every sign, they will not believe in it. Even when they come to you arguing with you, those who disbelieve say, "This is not but legends of the former peoples." <> Kuma daga cikinsu akwai wanda yake saurãre gare ka. Kuma Mun sanya abũbuwan rufi a kan zukãtansu dõmin kada su fahimcẽ shi kuma a cikin kunnuwansu (Mun sanya) wani nauyi. Kuma idan sun ga kõwace ãyã bã zã su yi ĩmãni da ita ba har idan sunjẽ maka sunã jãyayya da kai, waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: "Wannan bai zama ba fãce tãtsũniyõyin mutãnen farko." = --Qur'an 6:25
    And they prevent [others] from him and are [themselves] remote from him. And they do not destroy except themselves, but they perceive [it] not. <> Kuma sunã hanãwa daga gare shi, kuma sunã nĩsanta daga gare shi, kuma bã su halakarwa, fãce kansu, kuma bã su sansancẽwa. = --Qur'an 6:26
    If you could but see when they are made to stand before the Fire and will say, "Oh, would that we could be returned [to life on earth] and not deny the signs of our Lord and be among the believers." <> Kuma dã kanã gani, a lõkacin da aka tsayar da su a kan wuta, sai suka ce: "Yã kaitõnmu! Dã ana mayar da mu, kuma bã zã mu ƙaryata ba daga ãyõyin Ubangijinmu, kuma zã mu kasance Daga mũminai." = --Qur'an 6:27
    But what they concealed before has [now] appeared to them. And even if they were returned, they would return to that which they were forbidden; and indeed, they are liars. <> Ã'aha, abin da suka kasance suna ɓõyẽwa, daga gabãni, ya bayyana a gare su. Kuma dã an mayar da su, lalle dã sun kõma ga abin da aka hana su daga barinsa. Kuma lalle ne sũ, haƙĩƙa, maƙaryata ne. = --Qur'an 6:28
    And they say, "There is none but our worldly life, and we will not be resurrected." <> Kuma suka ce: "Ba ta zama ba, fãce rayuwarmu ta duniya, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba." = --Qur'an 6:29
    If you could but see when they will be made to stand before their Lord. He will say, "Is this not the truth?" They will say, "Yes, by our Lord." He will [then] say, "So taste the punishment because you used to disbelieve." <> Kuma dã kana gani, a lõkacin da aka tsayar da su ga UbangiJinsu, Ya ce: "Ashe wannan bai zama gaskiya ba?" Suka ce: "Nã'am, muna rantsuwa da Ubangijinmu!" Ya ce: "To ku ɗanɗani azaba sabõda abin da kuka kasance kuna yi na kãfirci." = --Qur'an 6:30
    Those will have lost who deny the meeting with Allah, until when the Hour [of resurrection] comes upon them unexpectedly, they will say, "Oh, [how great is] our regret over what we neglected concerning it," while they bear their burdens on their backs. Unquestionably, evil is that which they bear. <> Lalle ne waɗanda suka ƙaryata game da gamuwa da Allah sun yi hasara, har idan Sa'a ta je musu kwatsam, sai su ce: "Yã nadãmarmu a kan abin da muka yi sakaci a cikinta!" Alhãli kuwa su suna ɗaukar kayansu masu nauyi a kan bayayyakinsu. To, abin da suke ɗauka yã mũnana. = --Qur'an 6:31
    And the worldly life is not but amusement and diversion; but the home of the Hereafter is best for those who fear Allah, so will you not reason? <> Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba, fãce wãsa da shagala, kuma lalle ne, Lãhira ce mafi alhẽri ga waɗanda suka yi taƙawa. Shin, ba za ku yi hankali ba? = --Qur'an 6:32
    We know that you, [O Muhammad], are saddened by what they say. And indeed, they do not call you untruthful, but it is the verses of Allah that the wrongdoers reject. <> Lalle ne Muna sani cewa haƙĩƙa, abin da suke faɗa yana ɓãta maka rai. To, lalle ne su, bã su ƙaryata ka (a cikin zukatansu) kuma amma azzãlumai da ãyõyin Allah suke musu. = --Qur'an 6:33
    And certainly were messengers denied before you, but they were patient over [the effects of] denial, and they were harmed until Our victory came to them. And none can alter the words of Allah. And there has certainly come to you some information about the [previous] messengers. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an ƙaryata manzanni daga gabãninka, sai suka yi haƙuri a kan abin da aka ƙaryata su, kuma aka cũtar da su, har taimakonMu ya je musu, kuma babu mai musanyãwa ga kalmõmin Allah. Kuma lalle ne (abin da yake natsar da kai) ya zo maka daga lãbãrin (annabãwan) farko. = --Qur'an 6:34
    And if their evasion is difficult for you, then if you are able to seek a tunnel into the earth or a stairway into the sky to bring them a sign, [then do so]. But if Allah had willed, He would have united them upon guidance. So never be of the ignorant. <> Kuma idan yã kasance cewa finjirewarsu tã yi nauyi a gare ka, to, idan kana iyãwa, ka nemi wani ɓullõ a cikin ƙasa, kõ kuwa wani tsãni a cikin sama dõmin ka zo musu da wata ãyã, (sai ka yi). Kuma dã Allah Yã so haƙĩƙa dã Yãtãra su a kan shiriya. Sabõda haka, kada lalle ka kasance daga jãhilai. = --Qur'an 6:35
    Only those who hear will respond. But the dead - Allah will resurrect them; then to Him they will be returned. <> Abin sani kawai, waɗanda suke saurare ne suke karɓãwa, kuma matattu Allah Yake tãyar da su, Sa'an nan kuma zuwa gare Shi ake mayar da su. = --Qur'an 6:36
    And they say, "Why has a sign not been sent down to him from his Lord?" Say, "Indeed, Allah is Able to send down a sign, but most of them do not know." <> Kuma suka ce: "Don me ba a saukar da ãyã ba, a kansa, daga Ubangjinsa?" Ka ce: "Lalle ne Allah Mai ĩko ne a kan Yasaukar da ãyã, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba." = --Qur'an 6:37
    And there is no creature on [or within] the earth or bird that flies with its wings except [that they are] communities like you. We have not neglected in the Register a thing. Then unto their Lord they will be gathered. <> Kuma bãbu wata dabba a cikin ƙasa kuma bãbu wani tsuntsu wanda yake tashi da fukafukinsa fãce al'umma ne misãlanku. Ba Mu yi sakacin barin kõme ba a cikin Littãfi, sa'an nan kuma zuwa ga Ubangjinsu ake tãra su. = --Qur'an 6:38
    But those who deny Our verses are deaf and dumb within darknesses. Whomever Allah wills - He leaves astray; and whomever He wills - He puts him on a straight path. <> Kuma waɗanda suka ƙaryata gameda ãyõyinMu, kurãme ne kuma bebãye, acikin duffai. Wanda Allah Ya so Yanã ɓatar da shi, kuma wanda Ya so zai sanya shi a kan hanya madaidaiciya. = --Qur'an 6:39
    Say, "Have you considered: if there came to you the punishment of Allah or there came to you the Hour - is it other than Allah you would invoke, if you should be truthful?" <> Ka ce: "Shĩn, kun gan ku, idan azãbar Allah ta zo muku, kõ Sã'ar Tashin Kiyãma ta zo muku, shin wanin Allah kuke kira, idan dai kun kasance mãsu gaskiya?" = --Qur'an 6:40
    No, it is Him [alone] you would invoke, and He would remove that for which you invoked Him if He willed, and you would forget what you associate [with Him]. <> "Ã'a, Shĩ dai kuke kira sai Ya kuranye abin da kuke kira zuwa gare Shi, idan Ya so, kuma kunã mantãwar abin da kuke yin shirkin tãre da shi." = --Qur'an 6:41
    And We have already sent [messengers] to nations before you, [O Muhammad]; then We seized them with poverty and hardship that perhaps they might humble themselves [to Us]. <> Kuma lalle Mun aika zuwa ga al'ummai daga gabãninka, sai Muka kãmã su da tsanani da cũta, tsammãninsu zã su ƙanƙan da kai, = --Qur'an 6:42
    Then why, when Our punishment came to them, did they not humble themselves? But their hearts became hardened, and Satan made attractive to them that which they were doing. <> To, don me, a lõkacin da tsananinMu ya jẽ musu ba su yi tawãlu'i ba? Kuma amma zukatansu sun ƙẽƙashe kuma shaiɗan yã ƙawãta musu abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 6:43
    So when they forgot that by which they had been reminded, We opened to them the doors of every [good] thing until, when they rejoiced in that which they were given, We seized them suddenly, and they were [then] in despair. <> Sa'an nan kuma alõkacin da suka manta da abin da aka tunãtar da su da shi, sai Muka bũɗe, a kansu, ƙõfõfin dukkan kõme, har a lõkacin da suka yi farin ciki da abin da aka ba su, Muka kãmã su, kwatsam, sai gã su sun yi tsuru tsuru. = --Qur'an 6:44
    So the people that committed wrong were eliminated. And praise to Allah, Lord of the worlds. <> Sai aka katse ƙarshen mutãnen, waɗanda suka yi zãlunci. Kuma gõdiya tã tabbata ga Allah Ubangijin tãlikai. = --Qur'an 6:45
    Say, "Have you considered: if Allah should take away your hearing and your sight and set a seal upon your hearts, which deity other than Allah could bring them [back] to you?" Look how we diversify the verses; then they [still] turn away. <> Ka ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya riƙe jinku, da gannanku, kuma Ya sanya hãtimi a kan zukãtanku, wane abin bauttãwa ne, wanin Allah, zai jẽ muku da shi?" Ka dũba yadda Muke sarrafaãyõyi, Sa'an nan kuma sũ, sunã finjirẽwa. = --Qur'an 6:46
    Say, "Have you considered: if the punishment of Allah should come to you unexpectedly or manifestly, will any be destroyed but the wrongdoing people?" <> Ka ce: "Shin, kun gan ku, idan azãbar Allah ta jẽ muku, kwatsam, kõ kuwa bayyane, shin, anã halakãwa, fãce dai mutãne azzãlumai?" = --Qur'an 6:47
    And We send not the messengers except as bringers of good tidings and warners. So whoever believes and reforms - there will be no fear concerning them, nor will they grieve. <> Kuma bã Mu aikãwa da manzãnni fãce mãsu bayar da bushãra, kuma mãsu gargaɗi. To, wanda ya yi ĩmãni kuma yagyãra aiki, to, babu tsõro a kansu, kuma ba su yin baƙin ciki. = --Qur'an 6:48
    But those who deny Our verses - the punishment will touch them for their defiant disobedience. <> Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, azãba tanã shãfar su sabõda abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci. = --Qur'an 6:49
    Say, [O Muhammad], "I do not tell you that I have the depositories [containing the provision] of Allah or that I know the unseen, nor do I tell you that I am an angel. I only follow what is revealed to me." Say, "Is the blind equivalent to the seeing? Then will you not give thought?" <> Ka ce: "Ba zan ce muku, a wurina akwai taskõkin Allah ba. Kuma ba ni sanin gaibi, kuma ba ni gaya muku cẽwa ni malã'ika ne. Ba ni bi, fãce abin da ake yiwo wahayi zuwa gare ni." Ka ce: "Shin, makãho da mai gani sunã daidaita? Shin fa, ba ku yin tunãni?" = --Qur'an 6:50
    And warn by the Qur'an those who fear that they will be gathered before their Lord - for them besides Him will be no protector and no intercessor - that they might become righteous. <> Kuma ka yi gargaɗi da shi ga waɗanda suke jin tsõron a tãra su zuwa ga Ubangijinsu, ba su da wani masõyi baicinSa, kuma babu mai cẽto, tsammãninsu, sunã yin taƙawa. = --Qur'an 6:51
    And do not send away those who call upon their Lord morning and afternoon, seeking His countenance. Not upon you is anything of their account and not upon them is anything of your account. So were you to send them away, you would [then] be of the wrongdoers. <> Kuma kada ka kõri waɗanda suke kiran Ubangijinsu sãfe da maraice, sunã nufin yardarSa, babu wani abu daga hisãbinsu a kanka, kuma babu wani abu daga hisãbinka a kansu, har ka kõre su ka kasance daga azzãlumai. = --Qur'an 6:52
    And thus We have tried some of them through others that the disbelievers might say, "Is it these whom Allah has favored among us?" Is not Allah most knowing of those who are grateful? <> Kuma kamar wannan ne, Muka fitini sãshensu da sãshe, dõmin su ce: "Shin waɗannan ne Allah Ya yi falala a kansu daga tsakãninmu?" Shin, Allah bai zama Mafi sani ba ga mãsu gõdiya? = --Qur'an 6:53
    And when those come to you who believe in Our verses, say, "Peace be upon you. Your Lord has decreed upon Himself mercy: that any of you who does wrong out of ignorance and then repents after that and corrects himself - indeed, He is Forgiving and Merciful." <> Kuma idan waɗanda suke yin ĩmãni da ãyõyinMu suka jẽ maka, sai ka ce: "Aminci ya tabbata a gareku; Ubangjinku Ya wajabta rahama ga kanSa, cẽwa lalle ne wanda ya aikata aibi da jãhilci daga cikinku, sa'an nan kuma ya tũba daga bãyansa, kuma ya gyãra, to, lalle Shi, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai." = --Qur'an 6:54
    And thus do We detail the verses, and [thus] the way of the criminals will become evident. <> Kuma kamar wannan ne Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, kuma dõmin hanyar mãsu laifi ta bayyana. = --Qur'an 6:55
    Say, "Indeed, I have been forbidden to worship those you invoke besides Allah." Say, "I will not follow your desires, for I would then have gone astray, and I would not be of the [rightly] guided." <> Ka ce: "Lalle ne ni, an hana ni in bauta wa waɗanda kuke kira daga baicin Allah." Ka cc: "Ba ni bin son zũciyõyinku, (dõmin in nã yi haka) lalle ne, nã ɓace. A sa'an nan, kuma ban zama daga shiryayyu ba." = --Qur'an 6:56
    Say, "Indeed, I am on clear evidence from my Lord, and you have denied it. I do not have that for which you are impatient. The decision is only for Allah. He relates the truth, and He is the best of deciders." <> Ka ce: "Lalle ne inã kan hujja daga Ubangjina, kuma kun ƙaryata (ni) game da Shi; abin da kuke nẽman gaugãwarsa, bã ya wurina, hukunci kuwa bai zama ba fãce, ga Allah, Yanã bãyar da lãbãrin gaskiya, kuma shĩ ne mafi alhẽrin mãsu rarrabẽwa." = --Qur'an 6:57
    Say, "If I had that for which you are impatient, the matter would have been decided between me and you, but Allah is most knowing of the wrongdoers." <> Ka ce: "Lalle ne, dã a wurina akwai abin da kuke nẽman gaugãwa da shi, haƙĩƙa dã an hukunta al'amarin, a tsakãnina da tsakãninku, kuma Allah Shĩ ne Mafi sani ga azzũlumai." = --Qur'an 6:58
    And with Him are the keys of the unseen; none knows them except Him. And He knows what is on the land and in the sea. Not a leaf falls but that He knows it. And no grain is there within the darknesses of the earth and no moist or dry [thing] but that it is [written] in a clear record. <> Kuma a wurinSa mabũdan gaibi suke, babu wanda yake sanin su fãce Shi, kuma Yanã sanin abin da ke a cikin tudu da ruwa, kuma wani ganye ba ya fãɗuwa, fãce Yã san shi, kuma bãbu wata ƙwãya a cikin duffan ƙasã, kuma babu ɗanye, kuma babu ƙẽƙasasshe, fãce yanã a cikin wani Littãfi mai bayyanãwa. = --Qur'an 6:59
    And it is He who takes your souls by night and knows what you have committed by day. Then He revives you therein that a specified term may be fulfilled. Then to Him will be your return; then He will inform you about what you used to do. <> Kuma Shĩ ne wanda Yake karɓar rãyukanku da dare, kuma Yanã sanin abin da kuka yãga da rãna, sa'an nan Yanã tãyar da ku a cikinsa, dõmin a hukunta ajali ambatacce sa'an nan kuma zuwa gare shi makõmarku take, sa'an nan kuma Ya ba ku lãbari da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. = --Qur'an 6:60
    And He is the subjugator over His servants, and He sends over you guardian-angels until, when death comes to one of you, Our messengers take him, and they do not fail [in their duties]. <> Kuma Shĩ ne Mai rinjãya bisa ga bãyinSa, kuma Yanã aikan mãsu tsaro a kanku, har idan mutuwa ta jẽ wa ɗayanku, sai manzanninMu su karɓi ransa alhãli su ba su yin sakaci. = --Qur'an 6:61
    Then they His servants are returned to Allah, their true Lord. Unquestionably, His is the judgement, and He is the swiftest of accountants. <> Sa'an nan kuma a mayar da su zuwa ga Allah Ubangjinsu na gaskiya. To! A gare shi hukunci yake, kuma Shi ne Mafi gaugãwar mãsu bincike. = --Qur'an 6:62
    Say, "Who rescues you from the darknesses of the land and sea [when] you call upon Him imploring [aloud] and privately, 'If He should save us from this [crisis], we will surely be among the thankful.' " <> Ka ce: "Wane ne Yake tsĩrar da ku daga duhũhuwan tududa ruwa, kunã kiran Sa bisa ga ƙanƙan da kai Kuma a ɓõye: 'Lalle ne idan Ka tsĩrar da mu daga wannan (masĩfa), haƙĩƙa, muna kasancẽwa daga mãsu gõdiya?'" = --Qur'an 6:63
    Say, "It is Allah who saves you from it and from every distress; then you [still] associate others with Him." <> Ka ce: "Allah ne Yake tsĩrar da ku daga gare ta, kuma daga dukan baƙin ciki sa'an nan kuma ku, kunã yin shirki!" = --Qur'an 6:64
    Say, "He is the [one] Able to send upon you affliction from above you or from beneath your feet or to confuse you [so you become] sects and make you taste the violence of one another." Look how We diversify the signs that they might understand. <> Ka ce: "Shĩ ne Mai ĩko a kan Ya aika da wata azãba a kanku daga bisanku, kõ kuwa daga ƙarƙashin ƙafãfunku, kõ kuwa Ya gauraya ku ƙungiyõyi, kuma Ya ɗanɗanã wa sãshenku masĩfar sãshe." "Ka dũba yadda Muke sarrafa ãyõyi, tsammãninsu sunã fahimta!" = --Qur'an 6:65
    But your people have denied it while it is the truth. Say, "I am not over you a manager." <> Kuma mutãnenka sun ƙaryata (ka) game da Shi, alhãli kuwa Shi ne gaskiya. Ka ce: "Nĩban zama wakĩli a kanku ba." = --Qur'an 6:66
    For every happening is a finality; and you are going to know. <> "Akwai matabbata ga dukan lãbãri, kuma zã ku sani." = --Qur'an 6:67
    And when you see those who engage in [offensive] discourse concerning Our verses, then turn away from them until they enter into another conversation. And if Satan should cause you to forget, then do not remain after the reminder with the wrongdoing people. <> Kuma idan kã ga waɗanda suke kũtsawa a cikin ãyõyinMu, to, ka bijire daga gare su, sai sun kũtsa a cikin wani lãbãri waninsa. Kuma imma dai shaiɗan lalle ya mantar da kai, to, kada ka zauna a bayan tunãwa tãre da mutãne azzãlumai. = --Qur'an 6:68
    And those who fear Allah are not held accountable for the disbelievers at all, but [only for] a reminder - that perhaps they will fear Him. <> Kuma babu wani abu daga hisãbinsu (mãsu kutsãwa a cikin ayõyin Allah (a kan mãsu taƙawa amma akwai tunãtarwa (a kansu), tsãmmãninsu (mãsu kutsawar) zã su yi taƙawa. = --Qur'an 6:69
    And leave those who take their religion as amusement and diversion and whom the worldly life has deluded. But remind with the Qur'an, lest a soul be given up to destruction for what it earned; it will have other than Allah no protector and no intercessor. And if it should offer every compensation, it would not be taken from it. Those are the ones who are given to destruction for what they have earned. For them will be a drink of scalding water and a painful punishment because they used to disbelieve. <> Kuma ka bar waɗanda suka riƙi addĩninsu abin wãsa da wargi alhãli rãyuwar dũniya tã rũɗe su, kuma ka tunãtar game da shi (Alƙur'ãni): Kada a jẽfa raia cikin halaka sabõda abin da ya tsirfanta; ba shi da wani majiɓinci baicin Allah, kuma babu wani mai cẽto; kuma, kõ ya daidaita dukan fansa, ba zã a karɓa ba daga gare shi. Waɗancan ne aka yanke wa tsammãni sabõda abin da suka tsirfanta; sunã da wani abin shã daga ruwan zãfi, da wata azãba mai raɗaɗi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci. = --Qur'an 6:70
    Say, "Shall we invoke instead of Allah that which neither benefits us nor harms us and be turned back on our heels after Allah has guided us? [We would then be] like one whom the devils enticed [to wander] upon the earth confused, [while] he has companions inviting him to guidance, [calling], 'Come to us.' " Say, "Indeed, the guidance of Allah is the [only] guidance; and we have been commanded to submit to the Lord of the worlds. <> Ka ce: "Shin, zã mu yi kiran abin da bã ya amfãninmu, baicin Allah, kuma bã ya cũtar damu, kuma a mayar da mu a kan dugãduganmu, a bayan Allah Yã shiryar da mu kamar wanda shaiɗãnu suka kãyar da shi a cikin ƙasa, yanã mai ɗĩmuwa, yanã da abõkaisunã kiran sa zuwa ga shiriya, 'Ka zo mana'" Kace: "Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya. Kuma an umurce mu, mu sallama wa Ubangijin tãlikai." = --Qur'an 6:71
    And to establish prayer and fear Him." And it is He to whom you will be gathered. <> "Kuma (an ce mana): Ku tsai da salla kuma ku bĩ shi (Allah) da taƙawa kuma Shi ne wanda Yake zuwa gare Shi ake tãra ku." = --Qur'an 6:72
    And it is He who created the heavens and earth in truth. And the day He says, "Be," and it is, His word is the truth. And His is the dominion [on] the Day the Horn is blown. [He is] Knower of the unseen and the witnessed; and He is the Wise, the Acquainted. <> Kuma Shĩ ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa da mulkinSa, kuma a Rãnar da Yake cẽwa: "Ka kasance," sai abu ya yi ta kasancẽwa. MaganarSa ce gaskiya, kuma gare Shi mulki yake a Rãnar da ake bũsa a cikin ƙaho. Masanin fake da bayyane ne, Kuma Shi ne Mai hikima Masani. = --Qur'an 6:73
    And [mention, O Muhammad], when Abraham said to his father Azar, "Do you take idols as deities? Indeed, I see you and your people to be in manifest error." <> Kuma a lõkacin da Ibrãhĩma ya ce wa ubansa Ãzara: "Shin, kanã riƙon gumãka abũbuwan bautãwa? Lalle nĩ, inã ganin ka kai damutã- nenka, a cikin ɓata bayyananniya." = --Qur'an 6:74
    And thus did We show Abraham the realm of the heavens and the earth that he would be among the certain [in faith] <> Kuma kamar wancan ne, Muke nũna wa Ibrãhĩma mulkin sammai da ƙasa, kuma dõmin ya kasance daga mãsu yaƙĩni. = --Qur'an 6:75
    So when the night covered him [with darkness], he saw a star. He said, "This is my lord." But when it set, he said, "I like not those that disappear." <> To, a lõkacin da dare ya rufe a kansa, ya ga wani taurãro, ya ce: "Wannan ne, ubangijina?" Sa'an nan a lõkacin da ya faɗi, ya ce: "Ba ni son mãsu fãɗuwa." = --Qur'an 6:76
    And when he saw the moon rising, he said, "This is my lord." But when it set, he said, "Unless my Lord guides me, I will surely be among the people gone astray." <> Sa'an nan a lõkacin da ya ga watã yanã mai bayyana, ya ce: "Wannan ne Ubangijina?" Sa'an nan a lõkacin da ya fãɗi, ya ce: "Lalle ne idan Ubangijina bai shiryar da ni ba, haƙĩƙa, inã kasancẽwa daga mutãne ɓatattu." = --Qur'an 6:77
    And when he saw the sun rising, he said, "This is my lord; this is greater." But when it set, he said, "O my people, indeed I am free from what you associate with Allah. <> Sa'an nan a lõkacin da ya ga rãnã tanã bayyana, ya ce: "Wannan shĩ ne Ubangijina, wannan ne mafi girma?" Sa'an nan a lõkacin da ta fãɗi, ya ce: "Ya mutãnena! Lalle ne ni barrantacce nake daga abin da kuke yi na shirki." = --Qur'an 6:78
    Indeed, I have turned my face toward He who created the heavens and the earth, inclining toward truth, and I am not of those who associate others with Allah." <> "Lalle ne nĩ, na fuskantar da fuskata ga wanda, Ya ƙãga halittar sammai da ƙasa, inã mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bã ni cikin mãsu shirki." = --Qur'an 6:79
    And his people argued with him. He said, "Do you argue with me concerning Allah while He has guided me? And I fear not what you associate with Him [and will not be harmed] unless my Lord should will something. My Lord encompasses all things in knowledge; then will you not remember? <> Kuma mutãnensa suka yi musu da shi. Ya ce: "Shin kunã musu da ni a cikin sha'anin Allah, alhãli kuwa Yã shiryai da ni? Kuma bã ni tsõron abin da kuke yin shirki da shi, fãce idan Ubangijina Yã so wani abu. Ubangijina Ya yalwaci dukkan kõme da ilmi. Shin, ba zã ku yi tunãni ba?" = --Qur'an 6:80
    And how should I fear what you associate while you do not fear that you have associated with Allah that for which He has not sent down to you any authority? So which of the two parties has more right to security, if you should know? <> "Kuma yãyã nake jin tsõron abin da kuka yi shirki da shi, kuma ba ku tsõron cẽwa lalle ne kũ, kun yi shirki da Allah, abin da (Allah) bai saukar da wata hujja ba game da shi? To, wane ɓangare daga sãshen biyu ne mafi cancanta da aminci, idan kun kasance kunã sani?" = --Qur'an 6:81
    They who believe and do not mix their belief with injustice - those will have security, and they are [rightly] guided. <> "Waɗanda suka yi ĩmãni, kuma ba su gauraya ĩmãninsu da zãlunci ba, waɗannan sunã da aminci, kuma sũ ne shiryayyu." = --Qur'an 6:82
    And that was Our [conclusive] argument which We gave Abraham against his people. We raise by degrees whom We will. Indeed, your Lord is Wise and Knowing. <> Kuma waccan ita ce hujjarMu, Mun bayãr da ita ga Ibrãhĩma a kan mutãnensa. Munã ɗaukaka wanda Muka so da darajõji. Lalle ne Ubangijinka Mai hikima ne, Masani. = --Qur'an 6:83
    And We gave to Abraham, Isaac and Jacob - all [of them] We guided. And Noah, We guided before; and among his descendants, David and Solomon and Job and Joseph and Moses and Aaron. Thus do We reward the doers of good. <> Kuma Muka bã shi Is'hãƙa da Yãƙubu, dukansu Mun shiryar, kuma Nũhu Mun shiryar da shi a gabãni, kuma daga zuriyarsa akwai Dãwũda da Sulaimãnu da Ayyũba, da Yũsufu da Mũsã da Hãrũna, kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. = --Qur'an 6:84
    And Zechariah and John and Jesus and Elias - and all were of the righteous. <> Da Zakariyya da Yahaya da Isa da Ilyasu dukansu daga sãlihai suke. = --Qur'an 6:85
    And Ishmael and Elisha and Jonah and Lot - and all [of them] We preferred over the worlds. <> Da Ismã'la da Ilyasa, a da Yũnusa da Luɗu, kuma dukansu Mun fĩfĩtã su a kan tãlikai. = --Qur'an 6:86
    And [some] among their fathers and their descendants and their brothers - and We chose them and We guided them to a straight path. <> Kuma daga ubanninsu, da zũriyarsu, da 'yan'uwansu, kuma Muka zãɓe su, kuma Muka shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya. = --Qur'an 6:87
    That is the guidance of Allah by which He guides whomever He wills of His servants. But if they had associated others with Allah, then worthless for them would be whatever they were doing. <> Wancan ne shiryarwar Allah, Yanã shiryar da wanda Yake so daga bayinSa. Kuma dã sun yi shirki dã haƙĩƙa abin da suka kasance sunã, aikatãwa yã lãlãce. = --Qur'an 6:88
    Those are the ones to whom We gave the Scripture and authority and prophethood. But if the disbelievers deny it, then We have entrusted it to a people who are not therein disbelievers. <> Waɗancan ne waɗanda Muka bai wa Littãfi da hukunci da Annabci. To idan waɗannan (mutãne) sun kãfirta da ita, to, haƙĩƙa, Mun wakkala wasu mutãne gare ta, ba su zama game da ita kãfirai ba. = --Qur'an 6:89
    Those are the ones whom Allah has guided, so from their guidance take an example. Say, "I ask of you for this message no payment. It is not but a reminder for the worlds." <> Waɗancan ne Allah Ya shiryar, sabõda haka ka yi kõyi da shiryarsu. Ka ce: "Ba ni tambayar ku wata ijãra. Shĩ (Alƙur'ãni) bai zama ba fãce tunãtarwa ga tãlikai." = --Qur'an 6:90
    And they did not appraise Allah with true appraisal when they said, "Allah did not reveal to a human being anything." Say, "Who revealed the Scripture that Moses brought as light and guidance to the people? You [Jews] make it into pages, disclosing [some of] it and concealing much. And you were taught that which you knew not - neither you nor your fathers." Say, "Allah [revealed it]." Then leave them in their [empty] discourse, amusing themselves. <> Kuma ba su ƙaddara Allah a kan hakkin ƙaddara shi ba, a lõkacin da suka ce: "Allah bai saukar da kõme ba ga wani mutum." Ka ce: "Wãne ne ya saukar da Littãfi wanda Mũsã ya zo da shi, yanã haske da shiriya ga mutãne, kunã sanya shi takardu, kũna bayyana su, kuma kunã ɓõye mai yawa, kuma an sanar da ku abin da ba ku sani ba, ku da ubanninku?" Ka ce: "Allah," sa'an nan ka bar su a cikin sharhõliyarsu sunã wãsã. = --Qur'an 6:91
    And this is a Book which We have sent down, blessed and confirming what was before it, that you may warn the Mother of Cities and those around it. Those who believe in the Hereafter believe in it, and they are maintaining their prayers. <> Kuma wannan Littãfi ne, Mun saukar da shi, mai albarka ne, mai gaskata wanda yake a gabansa ne, kuma dõmin ka yi gargaɗi ga Uwar Alƙaryu (Makka) da wanda yake gefenta. Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da Lãhira sunã ĩmãni da shi (Alƙur'ãni), kuma sũ, a kan sallarsu, sunã tsarẽwa. = --Qur'an 6:92
    And who is more unjust than one who invents a lie about Allah or says, "It has been inspired to me," while nothing has been inspired to him, and one who says, "I will reveal [something] like what Allah revealed." And if you could but see when the wrongdoers are in the overwhelming pangs of death while the angels extend their hands, [saying], "Discharge your souls! Today you will be awarded the punishment of [extreme] humiliation for what you used to say against Allah other than the truth and [that] you were, toward His verses, being arrogant." <> Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ce: "An yi wahayi zuwa gare ni," alhãli kuwa ba a yi wahayin kõme ba zuwa gare shi, da wanda ya ce: "zan saukar da misãlin abin da Allah Ya saukar?" Kuma dã kã gani, a lõkacin da azzãlumai suke cikin mãyen mutuwa, kuma malã'iku sunã mãsu shimfiɗa hannuwansu, (sunã ce musu) "Ku fitar da kanku; a yau anã sãka muku da azãbar wulãƙanci sabõda abin da kuka kasance kunã faɗa, wanin gaskiya, ga Allah kuma kun kasance daga ãyõyinSa kunã yin girman kai." = --Qur'an 6:93
    [It will be said to them], "And you have certainly come to Us alone as We created you the first time, and you have left whatever We bestowed upon you behind you. And We do not see with you your 'intercessors' which you claimed that they were among you associates [of Allah]. It has [all] been severed between you, and lost from you is what you used to claim." <> Kuma lalle ne haƙĩƙa, kun zo Mana ɗai ɗai, kamar yadda Muka halittã ku a farkon lõkaci. Kuma kun bar abin da Muka mallaka muku a bayan bayayyakinku, kuma ba Mu gani a tãre da kũ ba, macẽtanku waɗanda kuka riya cẽwa lalle ne sũ, a cikinku mãsu tãrayya ne. Lalle ne, hãƙĩƙa, kõme yã yanyanke a tsakãninku, kuma abin da kuka kasance kunã riyãwa ya ɓace daga gare ku. = --Qur'an 6:94
    Indeed, Allah is the cleaver of grain and date seeds. He brings the living out of the dead and brings the dead out of the living. That is Allah; so how are you deluded? <> Lalle ne, Allah ne Mai tsãgewar ƙwãyar hatsi da kwalfar gurtsu. Yanã fitar da mai rai daga mamaci, kuma (Shi) Mai fitar da mamaci ne daga mai rai, wannan ne Allah. To, yãya ake karkatar da ku? = --Qur'an 6:95
    [He is] the cleaver of daybreak and has made the night for rest and the sun and moon for calculation. That is the determination of the Exalted in Might, the Knowing. <> Mai tsãgẽwar sãfiya, kuma Ya sanya dare mai natsuwa, kuma da rãna da watã a bisa lissãfi. vwannan ne ƙaddarãwar Mabuwãyi Masani. = --Qur'an 6:96
    And it is He who placed for you the stars that you may be guided by them through the darknesses of the land and sea. We have detailed the signs for a people who know. <> Kuma Shi ne Ya sanya muku taurãri dõmin ku shiryu da su a cikin duffan tudu da ruwa. Lalle ne Mun bayyana ãyõyi daki-daki, ga mutãne waɗanda suke sani. = --Qur'an 6:97
    And it is He who produced you from one soul and [gave you] a place of dwelling and of storage. We have detailed the signs for a people who understand. <> Kuma Shi ne Ya ƙãga halittarku daga rai guda, sa'an nan da mai tabbata da wanda ake ajẽwa. Lalle ne Mun bayyanã ãyõyi daki-daki, ga mutãne waɗanda suke fahimta. = --Qur'an 6:98
    And it is He who sends down rain from the sky, and We produce thereby the growth of all things. We produce from it greenery from which We produce grains arranged in layers. And from the palm trees - of its emerging fruit are clusters hanging low. And [We produce] gardens of grapevines and olives and pomegranates, similar yet varied. Look at [each of] its fruit when it yields and [at] its ripening. Indeed in that are signs for a people who believe. <> Kuma Shi ne Ya saukar da ruwa daga sama, Muka fitar da tsiron dukkan kõme game dã shi, sa'an nan Muka fitar da kõre daga gare shi, Muna fitar da kwãya ɗamfararriya daga gare shi (kõren), kuma daga dabĩno daga hirtsinta akwai dumbuje-dumbuje makusanta, kuma (Muka fitar) da gõnaki na inabõbi da zãitũni da rummãni, mãsu kamã da jũna da wasun mãsu kama da jũna. Ku dũba zuwa 'ya'yan itãcensa, idan ya yi 'ya'yan, da nunarsa. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyõyi ga waɗanda suke yin ĩmãni. = --Qur'an 6:99
    But they have attributed to Allah partners - the jinn, while He has created them - and have fabricated for Him sons and daughters. Exalted is He and high above what they describe <> Kuma suka sanya wa Allah abõkan tãrayya, aljannu, alhãli kuwa (Shi) Ya halitta su. Kuma sun ƙirƙira masa ɗiya da 'yã'ya, bã da ilmi ba. TsarkinSa yã tabbata! Kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke sifantãwa. = --Qur'an 6:100
    [He is] Originator of the heavens and the earth. How could He have a son when He does not have a companion and He created all things? And He is, of all things, Knowing. <> Mafarin halittar sammai da ƙasa. Yãya ɗã zai zama a gare Shi alhãli kuwa mãta ba ta kasance ba, a gare Shi, kuma Ya halitta dukkan, kõme, kuma Shĩ, game da dukan kõme, Masani ne? = --Qur'an 6:101
    That is Allah, your Lord; there is no deity except Him, the Creator of all things, so worship Him. And He is Disposer of all things. <> Wancan ne Allah Ubangijinku. Bãbu wani abin bautãwa fãce Shĩ, Mahaliccin dukan kõme. Sabõda haka ku bauta Masa kuma Shi ne wakĩli a kan dukan, kõme. = --Qur'an 6:102
    Vision perceives Him not, but He perceives [all] vision; and He is the Subtle, the Acquainted. <> Gannai bã su iya riskuwarSa, kuma Shĩ Yanã riskuwar gannai, kuma Shĩ ne Mai tausasãwa, Masani. = --Qur'an 6:103
    There has come to you enlightenment from your Lord. So whoever will see does so for [the benefit of] his soul, and whoever is blind [does harm] against it. And [say], "I am not a guardian over you." <> Lalle ne abũbuwan lũra sun je muku daga Ubangijinku, to, wanda ya kula, to, dõmin kansa, kuma wanda ya makanta, to, laifi yanã a kansa, kuma nĩ, a kanku, bã mai tsaro ba ne. = --Qur'an 6:104
    And thus do We diversify the verses so the disbelievers will say, "You have studied," and so We may make the Qur'an clear for a people who know. <> Kamar wannan ne Muke sarrafa ãyõyi, kuma dõmin su ce: "Kã karanta!" Kuma dõmin Mu bayyana shi ga mutãne waɗanda sunã sani. = --Qur'an 6:105
    Follow, [O Muhammad], what has been revealed to you from your Lord - there is no deity except Him - and turn away from those who associate others with Allah. <> Ka bi abin da aka yi wahayi zuwa gare ka daga Ubangijinka; babu wani abin bautãwa fãce Shi, kuma ka bijire daga mãsu shirki. = --Qur'an 6:106
    But if Allah had willed, they would not have associated. And We have not appointed you over them as a guardian, nor are you a manager over them. <> Kuma dã Allah Yã so, dã ba su yi shirki ba, kuma ba Mu, sanya ka mai tsaro a kansu ba, kuma ba kai ne wakĩli a kansu ba. = --Qur'an 6:107
    And do not insult those they invoke other than Allah, lest they insult Allah in enmity without knowledge. Thus We have made pleasing to every community their deeds. Then to their Lord is their return, and He will inform them about what they used to do. <> Kuma kada ku zãgi waɗanda suke kira, baicin Allah, har su zãgi Allah bisa zãlunci, ba, da ilmi ba. Kamar wannan ne Muka ƙawãta ga kõwace al'umma aikinsu, sa'an nan zuwa ga Ubangijinsu makõmarsu take, sa'an nan Ya ba su lãbari da abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 6:108
    And they swear by Allah their strongest oaths that if a sign came to them, they would surely believe in it. Say, "The signs are only with Allah." And what will make you perceive that even if a sign came, they would not believe. <> Kuma suka yi rantsuwa da Allah iyakar rantsuwõyinsu (cẽwa) lalle ne idan wata ãyã ta jẽmusu, haƙĩƙa, sunã yin ĩmãni da ita. Ka ce: "Abin sani kawai, ãyõyi a wurin Allah suke. Kuma mẽne nezai sanya ku ku sansance cẽwa, lalle ne su, idan ãyõyin sun je, ba zã su yi ĩmãni ba?" = --Qur'an 6:109
    And We will turn away their hearts and their eyes just as they refused to believe in it the first time. And We will leave them in their transgression, wandering blindly. <> Kuma Munã jujjũya zukãtansu da ganansu, kamar yadda ba su yi ĩmãni da shi ba a farkon lõkaci kuma Munã barin su a cikin kũtsãwarsu, sunã ɗĩmuwa. = --Qur'an 6:110
    And even if We had sent down to them the angels [with the message] and the dead spoke to them [of it] and We gathered together every [created] thing in front of them, they would not believe unless Allah should will. But most of them, [of that], are ignorant. <> Kuma dã a ce, lalle Mũ Mun saukar da Malã'iku zuwa gare su, kuma matattu suka yi musu magana, kuma Muka tãra dukkan kõme a kansu, gungu-gungu, ba su kasance sunã iya yin ĩmãni ba, sai fa idan Allah Yã so, Kuma amma mafi yawansu sunã jãhiltar haka. = --Qur'an 6:111
    And thus We have made for every prophet an enemy - devils from mankind and jinn, inspiring to one another decorative speech in delusion. But if your Lord had willed, they would not have done it, so leave them and that which they invent. <> Kuma kamar wancan ne Muka sanya wa kõwane Annabi maƙiyi; shaiɗãnun mutãne da aljannu, sãshensu yanã yin ishãra zuwa sãshe da ƙawãtaccen zance bisa ga rũɗi. Kuma dã Ubangijinka Yã so, dã ba su aikatã shi ba, don haka ka bar su da abin da, suke ƙirƙirãwa. = --Qur'an 6:112
    And [it is] so the hearts of those who disbelieve in the Hereafter will incline toward it and that they will be satisfied with it and that they will commit that which they are committing. <> Kuma dõmin zukãtan waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba su karkata saurãrẽ zuwa gareshi, kuma dõmin su yarda da shi, kuma dõmin su kamfaci abin da suke mãsu kamfata. = --Qur'an 6:113
    [Say], "Then is it other than Allah I should seek as judge while it is He who has revealed to you the Book explained in detail?" And those to whom We [previously] gave the Scripture know that it is sent down from your Lord in truth, so never be among the doubters. <> Shin fa, wanin Allah nake nẽma ya zama mai hukunci, alhãli kuwa Shĩ ne wanda Ya saukar muku da Littãfi abin rabẽwadaki-daki? Kuma waɗanda Muka bai wa Littãfi sunã sanin cẽwa lalleshi (Alƙur'ãni) abin saukarwa ne daga Ubangijinka, da gaskiya? Sabõda haka kada ku kasance daga mãsu shakka. = --Qur'an 6:114
    And the word of your Lord has been fulfilled in truth and in justice. None can alter His words, and He is the Hearing, the Knowing. <> Kuma kalmar Ubangijinka tã cika, tanã gaskiya da ãdalci. Babu mai musanyãwa ga kalmõminSa, kuma Shi ne Maiji, Masani. = --Qur'an 6:115
    And if you obey most of those upon the earth, they will mislead you from the way of Allah. They follow not except assumption, and they are not but falsifying. <> Kuma idan ka bi mafiya yawan waɗanda suke a cikin ƙasa da ɗã'a sunã ɓatar da kai daga hanyar Allah. Ba su bin kõme sai fãce ƙaddari-faɗi suke yi. = --Qur'an 6:116
    Indeed, your Lord is most knowing of who strays from His way, and He is most knowing of the [rightly] guided. <> Lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Mafi sani ga wanda yake ɓacẽwa daga hanyarsa kuma Shi ne mafi sani ga masu shiryuwa. = --Qur'an 6:117
    So eat of that [meat] upon which the name of Allah has been mentioned, if you are believers in His verses. <> Sabõda haka ku ci daga abin da aka ambaci sũnan Allah kansa, idan kun kasance mãsu ĩmãni da ãyõyinSa. = --Qur'an 6:118
    And why should you not eat of that upon which the name of Allah has been mentioned while He has explained in detail to you what He has forbidden you, excepting that to which you are compelled. And indeed do many lead [others] astray through their [own] inclinations without knowledge. Indeed, your Lord - He is most knowing of the transgressors. <> Kuma mẽne ne ya sãme ku, bã zã ku ci ba daga abin da aka ambaci sũnan Allah a kansa, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Ya rarrabe, muku daki-daki, abin da Ya haramta a kanku, fãce fa abin da aka bukãtar da ku bisa lalũra zuwa gare shi? Kuma lalle ne mãsu yawa sunã ɓatarwa, da son zũciyõyinsu, ba da wani ilmi ba. Lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Mafi sani ga mãsu ta'addi. = --Qur'an 6:119
    And leave what is apparent of sin and what is concealed thereof. Indeed, those who earn [blame for] sin will be recompensed for that which they used to commit. <> Kuma ku bar bayyanannen zunubi da ɓõyayyensa. Lalle ne waɗanda suke tsiwurwurin zunubi za a sãka musu da abin da suka kasance sunã kamfata. = --Qur'an 6:120
    And do not eat of that upon which the name of Allah has not been mentioned, for indeed, it is grave disobedience. And indeed do the devils inspire their allies [among men] to dispute with you. And if you were to obey them, indeed, you would be associators [of others with Him]. <> Kada ku ci daga abin da ba a ambaci sũnan Allah ba a kansa. Kuma lalle ne shĩ fãsiƙanci ne. Kuma lalle ne, shaiɗãnu, haƙĩƙa, suna yin ishãra zuwa ga masõyansu, dõmin su yi jãyayya da ku. Kuma idan kuka yi musu ɗã'a, lalle ne kũ, haƙĩƙa, mãsu shirki ne. = --Qur'an 6:121
    And is one who was dead and We gave him life and made for him light by which to walk among the people like one who is in darkness, never to emerge therefrom? Thus it has been made pleasing to the disbelievers that which they were doing. <> Shin, kuma wanda ya kasance matacce sa'an nan Muka rãyar da shi, kuma Muka sanya wani haske dõminsa, yanã tafiya da shi, yanã zama kamar wanda misãlinsa yanã cikin duffai, shĩ kuma ba mai fita ba daga gare su? Kamar wancan ne aka ƙawãta wa kãfirai abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 6:122
    And thus We have placed within every city the greatest of its criminals to conspire therein. But they conspire not except against themselves, and they perceive [it] not. <> Kuma kamar wancan ne Mun sanya a cikin kõwace alƙarya, shugabanni sũ ne mãsu laifinta dõmin su yi mãkirci a cikinta, alhãli kuwa ba su yin makirci fãce ga rayukansu, kuma ba su sansancẽwa. = --Qur'an 6:123
    And when a sign comes to them, they say, "Never will we believe until we are given like that which was given to the messengers of Allah." Allah is most knowing of where He places His message. There will afflict those who committed crimes debasement before Allah and severe punishment for what they used to conspire. <> Kuma idan wata ãyã ta je musu sai su ce: "Ba zã mu yi ĩmãni ba, sai an kãwo mana kamar abin da aka kãwo wa manzannin Allah." Allah Mafi sanin inda Yake sanya manzancinSa. Wani wulaƙanci a wurin Allah da wata azãba mai tsanani zã su sãmi waɗanda suka yi laifi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na mãkirci. = --Qur'an 6:124
    So whoever Allah wants to guide - He expands his breast to [contain] Islam; and whoever He wants to misguide - He makes his breast tight and constricted as though he were climbing into the sky. Thus does Allah place defilement upon those who do not believe. <> Dõmin haka wanda Allah Ya yi nufin ya shiryar da shi sai ya bũɗa ƙirjinsa dõmĩn Musulunci, kuma wanda Ya yi nufin Ya ɓatar da shi, sai Ya sanya ƙirjinsa mai ƙunci matsattse, kamar dai yanã tãkãwa ne a ckin sama. Kamar wannan ne Allah Yake sanyãwar ƙazanta a kan waɗanda bã su yin ĩmãni. = --Qur'an 6:125
    And this is the path of your Lord, [leading] straight. We have detailed the verses for a people who remember. <> Wannan ita ce hanya ta Ubangijinka madaidaiciya. Lalle ne Mun bayyana ãyõyi daki-daki ga mutãne mãsu karɓar tunãtarwa. = --Qur'an 6:126
    For them will be the Home of Peace with their Lord. And He will be their protecting friend because of what they used to do. <> Sunã da gidan aminci a wurin Ubangjinsu, kuma Shĩ ne Majiɓincinsu, sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 6:127
    And [mention, O Muhammad], the Day when He will gather them together [and say], "O company of jinn, you have [misled] many of mankind." And their allies among mankind will say, "Our Lord, some of us made use of others, and we have [now] reached our term, which you appointed for us." He will say, "The Fire is your residence, wherein you will abide eternally, except for what Allah wills. Indeed, your Lord is Wise and Knowing." <> Kuma rãnar da yake tãra su gaba ɗaya (Yanã cẽwa): "Yã jama'ar aljannu! Lalle ne kun yawaita kanku daga mutãne." Kuma majiɓantansu daga mutãne suka ce: "Yã Ubangjinmu! Sãshenmu ya ji dãɗi da sãshe, kuma mun kai ga ajalinmu wanda Ka yanka mana!" (Allah) Ya ce: "Wuta ce mazaunarku, kunã madawwama acikinta, sai abin da Allah Ya so. Lalle ne Ubangijinka Mai hikima ne, Masani." = --Qur'an 6:128
    And thus will We make some of the wrongdoers allies of others for what they used to earn. <> Kuma kamar wancan ne Muke jiɓintar da sãshen azzãlumai ga sãshe, sabõda abin da suka kasance sunã tãrãwa. = --Qur'an 6:129
    "O company of jinn and mankind, did there not come to you messengers from among you, relating to you My verses and warning you of the meeting of this Day of yours?" They will say, "We bear witness against ourselves"; and the worldly life had deluded them, and they will bear witness against themselves that they were disbelievers. <> Yã jama'ar aljannu da mutãne! Shin, manzanni daga gare ku ba su jẽ muku ba sunã lãbarta ãyõyiNa a kanku, kuma sunã yi muku gargaɗin haɗuwa da wannan yini nãku? Suka ce: "Mun yi shaida a kan kãwunanmu." Kuma rãyuwar dũniya tã rũɗẽ su. Kuma suka yi shaida a kan kãwunansu cẽwa lalle ne sũ, sun kasance kãfirai. = --Qur'an 6:130
    That is because your Lord would not destroy the cities for wrongdoing while their people were unaware. <> Wanan kuwa sabõda Ubangijinka bai kasance Mai halaka alƙaryõyi sabõda wani zãlunci ba ne, alhãli kuwa mutãnensu sunã jãhilai. = --Qur'an 6:131
    And for all are degrees from what they have done. And your Lord is not unaware of what they do. <> Kuma ga kõwanne, akwai darajõji daga abin da suka aikata. Kuma Ubangijinka bai zama mai shagala ba daga abin da suke aikatãwa. = --Qur'an 6:132
    And your Lord is the Free of need, the possessor of mercy. If He wills, he can do away with you and give succession after you to whomever He wills, just as He produced you from the descendants of another people. <> Kuma Ubangijinika Wadãtacce ne Ma'abũcin rahama. Idan Yã so zai tafi da ku, kuma Ya musanya daga bãyanku, abin da Yake so, kamar yadda Ya ƙãga halittarku daga zũriyar wasu mutãne na dabam. = --Qur'an 6:133
    Indeed, what you are promised is coming, and you will not cause failure [to Allah]. <> Lalle ne abin da ake yi muku wa'adi lalle mai zuwa ne kuma ba ku zama mãsu buwãya ba, = --Qur'an 6:134
    Say, "O my people, work according to your position; [for] indeed, I am working. And you are going to know who will have succession in the home. Indeed, the wrongdoers will not succeed. <> Ka ce: "Yã ku mutãnena! Ku yi aiki a kan halinku, lalle ne nĩ mai aiki ne, sa'an nan da sannu zã ku san wanda ãƙibar gida zã ta kasance a gare shi. Lalle ne shi, azzãlumai bã zã su ci nasarã ba." = --Qur'an 6:135
    And the polytheists assign to Allah from that which He created of crops and livestock a share and say, "This is for Allah," by their claim, "and this is for our partners [associated with Him]." But what is for their "partners" does not reach Allah, while what is for Allah - this reaches their "partners." Evil is that which they rule. <> Kuma sun sanya wani rabõ ga Allah daga abin da Ya halitta daga shũka da dabbõbi, sai suka ce: "Wannan na Allah ne," da riyãwarsu "Kuma wannan na abũbuwan shirkinmu ne." Sa'an nan = --Qur'an 6:136
    And likewise, to many of the polytheists their partners have made [to seem] pleasing the killing of their children in order to bring about their destruction and to cover them with confusion in their religion. And if Allah had willed, they would not have done so. So leave them and that which they invent. <> Kuma kamar wancan ne abũbuwan shirkinsu suka ƙãwata wa mãsu yawa, daga mãsu shirkin; kashewar 'ya'yansu, dõmin su halaka su kuma dõmin su rikitar da addininsu a gare su, Kuma dã Allah Yã so dã ba su aikatã shi ba. Sabõda haka ka bar su da abin da suke ƙirƙirãwa. = --Qur'an 6:137
    And they say, "These animals and crops are forbidden; no one may eat from them except whom we will," by their claim. And there are those [camels] whose backs are forbidden [by them] and those upon which the name of Allah is not mentioned - [all of this] an invention of untruth about Him. He will punish them for what they were inventing. <> Kuma sukace: "Waɗannan dabbõbi da shũka hanannu ne; bãbu mai ɗanɗanar su fãce wanda muke so," ga riyãwarsu. Da wasu dabbõbi an hana bãyayyakinsu, da wasu dabbõbi bã su ambatar sũnan Allah a kansu, bisa ƙirƙiren ƙarya gare Shi. Zai sãka musu da abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa. = --Qur'an 6:138
    And they say, "What is in the bellies of these animals is exclusively for our males and forbidden to our females. But if it is [born] dead, then all of them have shares therein." He will punish them for their description. Indeed, He is Wise and Knowing. <> Kuma suka ce: "Abin da yake a cikin cikkunan waɗannan dabbõbi kẽɓantacce ne ga mazanmu, kuma hananne ne a kan mãtan aurenmu. Kuma idan ya kasance mũshe, to, a cikinsa sũ abõkan tãrayya ne, zai sãka musu sifantãwarsu. Lalle ne Shĩ, Mai hikima ne, Masani." = --Qur'an 6:139
    Those will have lost who killed their children in foolishness without knowledge and prohibited what Allah had provided for them, inventing untruth about Allah. They have gone astray and were not [rightly] guided. <> Lalle ne waɗanda suka kashe ɗiyansu sabõda wauta, ba da ilmi ba, sun yi hasãra! Kuma suka haramta abin da Allah Ya azurta su, bisa ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne sun ɓace, kuma ba su kasance mãsu shiryuwa ba. = --Qur'an 6:140
    And He it is who causes gardens to grow, [both] trellised and untrellised, and palm trees and crops of different [kinds of] food and olives and pomegranates, similar and dissimilar. Eat of [each of] its fruit when it yields and give its due [zakah] on the day of its harvest. And be not excessive. Indeed, He does not like those who commit excess. <> Kuma Shĩ ne Wanda Ya ƙãga halittar gõnaki mãsu rumfuna da wasun mãsu rumfuna da dabĩnai da shũka, mai sãɓãwa ga 'yã'yansa na ci, da zaituni da rummãni mai kama da jũna da wanin mai kama da jũna. Ku ci daga 'ya'yan itãcensa, idan ya yi 'yã'yan, kuma ku bãyar da hakkinSa a rãnar girbinsa, kuma kada ku yi ɓarna. Lalle ne Shĩ, ba Ya son mafarauta. = --Qur'an 6:141
    And of the grazing livestock are carriers [of burdens] and those [too] small. Eat of what Allah has provided for you and do not follow the footsteps of Satan. Indeed, he is to you a clear enemy. <> Kuma daga dabbõbi (Ya ƙãga halittar) mai ɗaukar kãya da ƙanãna; Ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku, kuma kada ku bi zambiyõyin shaiɗan: LalLe ne shi, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne. = --Qur'an 6:142
    [They are] eight mates - of the sheep, two and of the goats, two. Say, "Is it the two males He has forbidden or the two females or that which the wombs of the two females contain? Inform me with knowledge, if you should be truthful." <> Nau'õ'i takwas daga tumãkai biyu, kuma daga awãkai biyu; ka ce: Shin mazan biyu ne Ya haramta ko mãtan biyu, ko abin da mahaifar mãtan biyu suka tattara a kansa? Ku bã ni lãbãri da ilmi, idan kun kasance mãsu gaskiya. = --Qur'an 6:143
    And of the camels, two and of the cattle, two. Say, "Is it the two males He has forbidden or the two females or that which the wombs of the two females contain? Or were you witnesses when Allah charged you with this? Then who is more unjust than one who invents a lie about Allah to mislead the people by [something] other than knowledge? Indeed, Allah does not guide the wrongdoing people." <> Kuma daga rãƙuma akwai nau'i biyu, kuma daga shãnu biyu; ka ce: Shin, mazan biyu ne Ya hana ko mãtan biyu Ya hana, kõ abin da mahaifar mãtan biyu suka tattara a kansa? Kõ kun kasance halarce ne a lõkacin da Allah Ya yi muku wasiyya da wannan? To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, dõmin ya ɓatar da mutãne bã da wani ilmi ba? Lalle ne, Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai. = --Qur'an 6:144
    Say, "I do not find within that which was revealed to me [anything] forbidden to one who would eat it unless it be a dead animal or blood spilled out or the flesh of swine - for indeed, it is impure - or it be [that slaughtered in] disobedience, dedicated to other than Allah. But whoever is forced [by necessity], neither desiring [it] nor transgressing [its limit], then indeed, your Lord is Forgiving and Merciful." <> Ka ce: "Bã ni sãmu, a cikin abin da aka yõ wahayi zuwa gare Ni, abin haramtãwa a kan wani mai ci wanda yake cin sa fãce idan ya kasance mũshe kõ kuwa jini abin zubarwa kõ kuwa nãman alade, to lalle ne shi ƙazanta ne, kõ kuwa fãsiƙanci wanda aka kurũrũta, dõmin wanin Allah da shi." Sa'an nan wanda larũra ta kãmã shi, bã mai fita jama'a ba, kuma bã mai ta'addi ba, to, lalle Ubangijinka Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 6:145
    And to those who are Jews We prohibited every animal of uncloven hoof; and of the cattle and the sheep We prohibited to them their fat, except what adheres to their backs or the entrails or what is joined with bone. [By] that We repaid them for their injustice. And indeed, We are truthful. <> Kuma a kan waɗanda suka tũba (Yahũdu) Mun haramta dukan mai akaifa, kuma daga shãnu da bisãshe Mun haramta musu kitsattsansu fãce abin da bãyukansu suka ɗauka, kõ kuwa kãyan ciki, kõ kuwa abin da ya garwaya da ƙashĩ wannan ne Muka sãka musu sabõda zãluncinsu, kuma Mu, haƙĩƙa, Mãsu gaskiya ne. = --Qur'an 6:146
    So if they deny you, [O Muhammad], say, "Your Lord is the possessor of vast mercy; but His punishment cannot be repelled from the people who are criminals." <> To, idan sun ƙaryatã ka, sai ka ce: "Ubangijinku Ma'abũcin rahama ne Mai yalwa; kuma bã a mayar da azãbarSa daga mutãne mãsu laifi." = --Qur'an 6:147
    Those who associated with Allah will say, "If Allah had willed, we would not have associated [anything] and neither would our fathers, nor would we have prohibited anything." Likewise did those before deny until they tasted Our punishment. Say, "Do you have any knowledge that you can produce for us? You follow not except assumption, and you are not but falsifying." <> Waɗanda suka yi shirki zã su ce: "Dã Allah Yã so dã ba mu yi shirki ba, kuma dã ubanninmu ba su yi ba, kuma dã ba mu haramta wani abu ba." Kamar wannan ne mutãnen da suke a gabãninsu suka ƙaryata, har suka ɗanɗani azãbarMu. Ka ce: "Shin, kunã da wani ilmi a wurinku dõmin ku fito mana da shi? Bã ku bin kõme fãce zato kuma ba ku zama ba fãce ƙiri-faɗi kawai kuke yi." = --Qur'an 6:148
    Say, "With Allah is the far-reaching argument. If He had willed, He would have guided you all." <> Ka ce: "To Allah ne da hujja isasshiya, sabõda haka: Dã Yã so, dã Yã shiryar da ku gabã ɗaya." = --Qur'an 6:149
    Say, [O Muhammad], "Bring forward your witnesses who will testify that Allah has prohibited this." And if they testify, do not testify with them. And do not follow the desires of those who deny Our verses and those who do not believe in the Hereafter, while they equate [others] with their Lord. <> Ka ce: "Ku kãwo shaidunku, waɗanda suke bãyar da shaidar cẽwa Allah ne Ya haramta wannan." To idan sun kãwo shaida kada ka yi shaida tãre da su. Kuma kada ka bi son zũciyõyin waɗanda suka ƙaryata, game da ãyõyinMu, da waɗanda bã su yin ĩmãni da Lãhira, alhãli kuwa sũ daga Ubangijinsu suna karkacẽwa. = --Qur'an 6:150
    Say, "Come, I will recite what your Lord has prohibited to you. [He commands] that you not associate anything with Him, and to parents, good treatment, and do not kill your children out of poverty; We will provide for you and them. And do not approach immoralities - what is apparent of them and what is concealed. And do not kill the soul which Allah has forbidden [to be killed] except by [legal] right. This has He instructed you that you may use reason." <> Ka ce: "Ku zo, in karanta abin da Ubangijinku Ya haramta." wãjibi ne a kanku kada ku yi shirkin kõme da Shi, kuma ga mahaifa biyu (ku kyautata) kyautatãwa, kuma kada ku kashe ɗiyanku sabõda talauci, Mũ ne Muke azurta ku, kũ da su, kuma kada ku kusanci abũbuwa alfãsha, abin da ya bayyana daga gare ta da abin da ya ɓõyu, kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta, fãce da hakki. Wannan ne (Allah) Ya yi muku wasiyya da Shi: Tsammãninku, kunã hankalta. = --Qur'an 6:151
    And do not approach the orphan's property except in a way that is best until he reaches maturity. And give full measure and weight in justice. We do not charge any soul except [with that within] its capacity. And when you testify, be just, even if [it concerns] a near relative. And the covenant of Allah fulfill. This has He instructed you that you may remember. <> Kada ku kusanci dũkiyar marãya fãce da wadda take ita ce mafi kyau, har ya kai ga ƙarfinsa. Kuma ku cika mũdu da sikẽli da ãdalci, bã Mu kallafã wa rai fãce iyãwarsa. Kuma idan kun faɗi magana, to, ku yi ãdalci, kuma ko dã yã kasance ma'abũcin zumunta ne. Kuma da alkawarin Allah ku cika. wannan ne Ya yi muku wasiyya da shi: Tsammãninku, kunã tunãwa. = --Qur'an 6:152
    And, [moreover], this is My path, which is straight, so follow it; and do not follow [other] ways, for you will be separated from His way. This has He instructed you that you may become righteous. <> Kuma lalle wannan ne tafarkĩNa, yana madaidaici: Sai ku bĩ shi, kuma kada ku bi wasu hanyõyi, su rarrabu da ku daga barin hanyãTa. Wannan ne Allah Ya yi muku wasiyya da shi tsammãninku, kunã yin taƙawa. = --Qur'an 6:153
    Then We gave Moses the Scripture, making complete [Our favor] upon the one who did good and as a detailed explanation of all things and as guidance and mercy that perhaps in [the matter of] the meeting with their Lord they would believe. <> Sa'an nan kuma Mun bai wa Mũsã Littãfi, yanã cikakke bisa ga wanda ya kyautata (hukuncin Allah) da rarrabẽwa, daki-daki, ga kõwane abu, da shiriya da rahama, tsammãninsu, sunã yin ĩmãni da haɗuwa da Ubangijinsu. = --Qur'an 6:154
    And this [Qur'an] is a Book We have revealed [which is] blessed, so follow it and fear Allah that you may receive mercy. <> Kuma wannan Littãfi ne, Mun saukar da shi, mai albarka ne, sai ku bĩ shi kuma ku yi taƙawa, tsammãninku, anã jin ƙanku. = --Qur'an 6:155
    [We revealed it] lest you say, "The Scripture was only sent down to two groups before us, but we were of their study unaware," <> (Dõmin) kada ku ce: "Abin sani kawai, an saukar da littãfi a kan ƙungiya biyu daga gabãninmu, kuma lalle ne mũ, mun kasance, daga karatunsu, haƙĩƙa, gãfilai." = --Qur'an 6:156
    Or lest you say, "If only the Scripture had been revealed to us, we would have been better guided than they." So there has [now] come to you a clear evidence from your Lord and a guidance and mercy. Then who is more unjust than one who denies the verses of Allah and turns away from them? We will recompense those who turn away from Our verses with the worst of punishment for their having turned away. <> Kõ kuwa ku ce: "Dã dai lalle mũ an saukar da Littãfi a kanmu, haƙĩƙa, dã mun kasance mafiya, shiryuwa daga gare su." To, lalle ne wata hujja bayyananniya, daga Ubangijinku, tã zo muku, da shiriya da rahama. To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙaryata game da ãyõyin Allah, kuma ya finjire daga barinsu? Zã Mu sãka wa waɗanda suke finjirẽwa daga barin ãyõyinMu da mugunyar azãba, sabõda abin da suka kasance sunã yi na hinjirẽwa. = --Qur'an 6:157
    Do they [then] wait for anything except that the angels should come to them or your Lord should come or that there come some of the signs of your Lord? The Day that some of the signs of your Lord will come no soul will benefit from its faith as long as it had not believed before or had earned through its faith some good. Say, "Wait. Indeed, we [also] are waiting." <> Shin, sunã jiran (wani abu), fãce dai malã'iku su je musu kõ kuwa Ubangijinka Ya je, kõ kuwa sãshen ãyõyin Ubangijinka ya je. A rãnar da sãshen ãyõyin Ubangijinka yake zuwa, ĩmãnin rai wanda bai kasance yã yi ĩmãnin ba a gabãni, kõ kuwa ya yi tsiwirwirin wani alhẽri, bã ya amfãninsa. Ka ce: "Ku yi jira: Lalle ne mũ, mãsu jira ne." = --Qur'an 6:158
    Indeed, those who have divided their religion and become sects - you, [O Muhammad], are not [associated] with them in anything. Their affair is only [left] to Allah; then He will inform them about what they used to do. <> Lalle ne waɗanda suka rarraba addininsu, kuma suka kasance ƙungiyã-ƙungiyã, kai ba ka zama daga gare su ba, a cikin kõme: abin sani kawai al'amarinsu zuwa ga Allah yake. Sa'an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 6:159
    Whoever comes [on the Day of Judgement] with a good deed will have ten times the like thereof [to his credit], and whoever comes with an evil deed will not be recompensed except the like thereof; and they will not be wronged. <> Wanda ya zo da kyakkyãwan aiki guda, to, yanã da gõma ɗin misãlansa. Kuma wanda ya zo da mũgun aiki gũda, to, bã zã a sãka masa ba fãce da misãlinsa. Kuma sũ bã a zãluntar su. = --Qur'an 6:160
    Say, "Indeed, my Lord has guided me to a straight path - a correct religion - the way of Abraham, inclining toward truth. And he was not among those who associated others with Allah." <> Ka ce: "Lalle nĩ, Ubangijina Yã shiryar da ni zuwa ga tafarki madaidaici, addĩni, ƙĩmantãwa (ga abũbuwa), mai aƙĩdar Ibrãhĩm, mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba." = --Qur'an 6:161
    Say, "Indeed, my prayer, my rites of sacrifice, my living and my dying are for Allah, Lord of the worlds. <> Ka ce: "Lalle ne sallãta, da baikõna, da rãyuwãta, da mutuwãta, na Allah ne Ubangijin tãlikai." = --Qur'an 6:162
    No partner has He. And this I have been commanded, and I am the first [among you] of the Muslims." <> "Bãbu abõkin tãrayya a gare Shi. Kuma da wancan aka umurce ni, kuma ni ne farkon mãsu sallamãwa." = --Qur'an 6:163
    Say, "Is it other than Allah I should desire as a lord while He is the Lord of all things? And every soul earns not [blame] except against itself, and no bearer of burdens will bear the burden of another. Then to your Lord is your return, and He will inform you concerning that over which you used to differ." <> Ka ce: "Shin wanin Allah nake nẽma ya zama Ubangiji, alhãli kuwa Shĩ ne Ubangijin dukan kõme? Kuma wani rai bã ya yin tsirfa fãce dõmin kansa, kuma mai ɗaukar nauyi, bã ya ɗaukar nauyin wani, sa'an nan kuma kõmawarku zuwa ga Ubangijinku take; Sa'an nan Yã bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance, a cikinsa, kunã sãɓã wa jũnã?" = --Qur'an 6:164
    And it is He who has made you successors upon the earth and has raised some of you above others in degrees [of rank] that He may try you through what He has given you. Indeed, your Lord is swift in penalty; but indeed, He is Forgiving and Merciful. <> "Kuma Shĩ ne wanda Ya sanya ku mãsu maye wa jũnaga ƙasa. Kuma Ya ɗaukaka sãshenku bisa ga sãshe da darajõji; dõmin Ya jarraba ku a cikin abin da Ya bã ku." Lalle ne, Ubangijinka Mai gaggãwar uƙkũba ne, kuma lalle ne Shi, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 6:165
    Alif, Lam, Meem, Sad. <> A. L̃. M̃. Ṣ̃. = --Qur'an 7:1
    [This is] a Book revealed to you, [O Muhammad] - so let there not be in your breast distress therefrom - that you may warn thereby and as a reminder to the believers. <> Littãfi ne aka saukar zuwa gare ka, kada wani ƙunci ya kasance a cikin ƙirjinka daga gare shi, dõmin ka yi gargaɗi da shi. Kuma tunãtarwa ne ga mũminai. = --Qur'an 7:2
    Follow, [O mankind], what has been revealed to you from your Lord and do not follow other than Him any allies. Little do you remember. <> Ku bi abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, kuma kada ku dinga bin wasu majiɓinta baicinSa. Kaɗan ƙwarai kuke tunãwa. = --Qur'an 7:3
    And how many cities have We destroyed, and Our punishment came to them at night or while they were sleeping at noon. <> Kuma da yawa wata alƙarya Muka halaka ta, sai azãbarMu ta jẽ mata da dare kõ kuwa sunã mãsu ƙailũla. = --Qur'an 7:4
    And their declaration when Our punishment came to them was only that they said, "Indeed, we were wrongdoers!" <> Sa'an nan bãbu abin da yake da'awarsu, a lõkacin da azãbarMu ta jẽ musu, fãce suka ce: "Lalle ne mũ muka kasance mãsu zãlunci," = --Qur'an 7:5
    Then We will surely question those to whom [a message] was sent, and We will surely question the messengers. <> Sa'an nan lalle ne Munã tambayar waɗanda aka aika zuwa gare su, kuma lalle Munã tambayar Manzannin. = --Qur'an 7:6
    Then We will surely relate [their deeds] to them with knowledge, and We were not [at all] absent. <> Sa'an nan haƙĩƙa Munã bã su lãbãri da ilmi kuma ba Mu kasance mãsu fakowa ba. = --Qur'an 7:7
    And the weighing [of deeds] that Day will be the truth. So those whose scales are heavy - it is they who will be the successful. <> Kuma awo a rãnar nan ne gaskiya. To, wanda sikẽlansasuka yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu cin nasara. = --Qur'an 7:8
    And those whose scales are light - they are the ones who will lose themselves for what injustice they were doing toward Our verses. <> Kuma wanda sikẽlansa suka yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasarar rayukansu, sabõda abin da suka kasance, da ãyõyinMu, sunã yi na zãlunci. = --Qur'an 7:9
    And We have certainly established you upon the earth and made for you therein ways of livelihood. Little are you grateful. <> Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun sarautar da ku, a cikin ƙasa, kuma Mun sanya muku abũbuwan rãyuwa, a cikinta; kaɗan ƙwarai kuke gõdẽwa. = --Qur'an 7:10
    And We have certainly created you, [O Mankind], and given you [human] form. Then We said to the angels, "Prostrate to Adam"; so they prostrated, except for Iblees. He was not of those who prostrated. <> Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halittã ku sa'an nan kuma Mun sũrantã ku, sa'an nan kumaMun ce wa malã'iku: "Ku yi sujada ga Ãdam." Sai suka yi sujada fãce Iblĩs, bai kasance daga mãsuyin sujadar ba. = --Qur'an 7:11
    [Allah] said, "What prevented you from prostrating when I commanded you?" [Satan] said, "I am better than him. You created me from fire and created him from clay." <> Ya ce: "Mẽne ne ya hana ka, ba ka yi sujada ba, alõkacin da Na umurce ka?" Ya ce: "Nĩ ne mafĩfĩci daga gare shi, Ka halitta ni daga wuta alhãli kuwa Kã halitta shi daga lãka." = --Qur'an 7:12
    [Allah] said, "Descend from Paradise, for it is not for you to be arrogant therein. So get out; indeed, you are of the debased. <> Ya ce: "To, ka sauka daga gare ta; dõmin bã, ya kasancẽwa a gare ka ga ka yi girman kai a cikinta. Sai ka fita. Lalle ne kanã daga mãsu ƙasƙanci." = --Qur'an 7:13
    [Satan] said, "Reprieve me until the Day they are resurrected." <> Ya ce: "Ka yi mini jinkiri zuwa ga rãnar da ake tãyar da su." = --Qur'an 7:14
    [Allah] said, "Indeed, you are of those reprieved." <> Ya ce: "Lalle ne, kanã daga waɗanda aka yi wa jinkiri." = --Qur'an 7:15
    [Satan] said, "Because You have put me in error, I will surely sit in wait for them on Your straight path. <> Ya ce: "To inã rantsuwa da halakarwar da Ka yi mini, lalle ne, inã zaune musu tafarkinKa madaidaici." = --Qur'an 7:16
    Then I will come to them from before them and from behind them and on their right and on their left, and You will not find most of them grateful [to You]." <> "Sa'an nan kuma haƙĩƙa, Inã je musu daga gaba gare su, kuma daga bãya gare su, kuma daga jihõhin damansu da jihõhin hagunsu; Kuma bã zã ka sãmi mafi yawansu mãsu gõdiya ba." = --Qur'an 7:17
    [Allah] said, "Get out of Paradise, reproached and expelled. Whoever follows you among them - I will surely fill Hell with you, all together." <> Ya ce: "Ka fita daga gare ta kanã abin zargi kõrarre. Lalle ne wanda ya bĩ ka daga gare su, haƙĩƙa, zã Ni cika jahannama daga gare ku, gabã ɗaya." = --Qur'an 7:18
    And "O Adam, dwell, you and your wife, in Paradise and eat from wherever you will but do not approach this tree, lest you be among the wrongdoers." <> "Kuma ya Ãdam! Ka zauna kai da matarka a Aljanna sai ku ci daga inda kuka so; kuma kada ku kusanci wannan itãciya, har ku kasance daga azzãlumai." = --Qur'an 7:19
    But Satan whispered to them to make apparent to them that which was concealed from them of their private parts. He said, "Your Lord did not forbid you this tree except that you become angels or become of the immortal." <> Sai Shaiɗan ya sanya musu waswãsi dõmin ya bayyana musu abin da aka rufe daga barinsu, daga al'aurarsu, kuma ya ce: "Ubangijinku bai hanã ku daga wannan itãciya ba fãce dõmin kada ku kasance malã'iku biyu ko kuwa ku kasance daga madawwama." = --Qur'an 7:20
    And he swore [by Allah] to them, "Indeed, I am to you from among the sincere advisors." <> Kuma ya yi musu rantsuwa; Lalle ne nĩ, a gare ku, haƙĩƙa, daga mãsu nasĩha ne. = --Qur'an 7:21
    So he made them fall, through deception. And when they tasted of the tree, their private parts became apparent to them, and they began to fasten together over themselves from the leaves of Paradise. And their Lord called to them, "Did I not forbid you from that tree and tell you that Satan is to you a clear enemy?" <> Sai ya saukar da su da rũɗi. Sa'an nan a lõkacin da suka ɗanɗani itãciyar, al'aurarsu ta bayyana gare su, kuma suka shiga sunã lĩƙawar ganye a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ubangjinsu Ya kira su: "Shin, Ban hanã ku ba daga waccan itãciya, kuma Na ce muku lalle ne Shaiɗan, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne?" = --Qur'an 7:22
    They said, "Our Lord, we have wronged ourselves, and if You do not forgive us and have mercy upon us, we will surely be among the losers." <> Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Mun zãlunci kanmu. Kuma idan ba Ka gãfarta mana ba, kuma Ka yi mana rahama, haƙĩƙa, Munã kasancẽwa daga mãsu hasãra." = --Qur'an 7:23
    [Allah] said, "Descend, being to one another enemies. And for you on the earth is a place of settlement and enjoyment for a time." <> Ya ce: "Ku sauka, sãshenku zuwa ga sãshe yanã maƙiyi, kuma kunã da matabbata a cikin ƙasa, da ɗan jin dãɗi zuwa ga wani lõkabi." = --Qur'an 7:24
    He said, "Therein you will live, and therein you will die, and from it you will be brought forth." <> Ya ce: "A cikinta kuke rãyuwa, kuma a cikinta kuke mutuwa, kuma daga gare ta ake fitar da ku." = --Qur'an 7:25
    O children of Adam, We have bestowed upon you clothing to conceal your private parts and as adornment. But the clothing of righteousness - that is best. That is from the signs of Allah that perhaps they will remember. <> Yã ɗiyan Ãdam! Lalle ne Mun saukar da wata tufa a kanku, tanã rufe muku al'aurarku, kuma da ƙawã. Kuma tufar taƙawa wancan ce mafi alhẽri. Wancan daga ãyõyin Allah ne, tsammãninsu sunã tunãwa! = --Qur'an 7:26
    O children of Adam, let not Satan tempt you as he removed your parents from Paradise, stripping them of their clothing to show them their private parts. Indeed, he sees you, he and his tribe, from where you do not see them. Indeed, We have made the devils allies to those who do not believe. <> Yã ɗiyan Ãdam! Kada Shaiɗan, lalle, ya fitine ku, kamar yadda ya fitar da iyãyenku, biyu daga Aljanna, yanã fizge tufarsu daga gare su, dõmin ya nũna musu al'aurarsu. Lalle ne shĩ, yanã ganin ku, shi da rundunarsa, daga inda bã ku ganin su. Lalle ne Mũ, Mun sanyaShaiɗan majiɓinci ga waɗanda bã su yin ĩmãni. = --Qur'an 7:27
    And when they commit an immorality, they say, "We found our fathers doing it, and Allah has ordered us to do it." Say, "Indeed, Allah does not order immorality. Do you say about Allah that which you do not know?" <> Kuma idan suka aikata alfãsha su ce: "Mun sãmi ubanninmu akanta." Kuma Allah ne Ya umurce mu da ita."Ka ce: "Lalle ne, Allah bã Ya umurni da alfãsha. Shin kunã faɗar abin da bã ku da saninsa ga Allah?" = --Qur'an 7:28
    Say, [O Muhammad], "My Lord has ordered justice and that you maintain yourselves [in worship of Him] at every place [or time] of prostration, and invoke Him, sincere to Him in religion." Just as He originated you, you will return [to life] - <> Ka ce: "Ubangjina Yã yi umurni da ãdalci; kuma ku tsayar da fuskõkinku a wurin kõwane masallãci, kuma ku rõƙẽ Shi, kunã mãsu tsarkake addini gare Shi. Kamar yadda Ya fãra halittarku kuke kõmãwa." = --Qur'an 7:29
    A group [of you] He guided, and a group deserved [to be in] error. Indeed, they had taken the devils as allies instead of Allah while they thought that they were guided. <> Wata ƙungiya (Allah) Yã shiryar, kuma wata ƙungiya ɓata tã wajaba a kansu; lalle ne sũ, sun riƙi shaiɗanu majiɓinta, baicin Allah, kuma sunã zaton, lalle sũ, mãsu shiryuwa ne. = --Qur'an 7:30
    O children of Adam, take your adornment at every masjid, and eat and drink, but be not excessive. Indeed, He likes not those who commit excess. <> Yã ɗiyan Ãdam! Ku riƙi ƙawarku a wurin kõwane masallãci kuma ku ci, kuma ku sha; Kuma kada ku yi ɓarna. Lalle ne Shĩ (Allah), bã Ya son mãsu ɓarna. = --Qur'an 7:31
    Say, "Who has forbidden the adornment of Allah which He has produced for His servants and the good [lawful] things of provision?" Say, "They are for those who believe during the worldly life [but] exclusively for them on the Day of Resurrection." Thus do We detail the verses for a people who know. <> Ka ce: "Wãne ne ya haramta ƙawar Allah, wadda Ya fitar sabõda bãyinSa, da mãsu dãɗi daga abinci?" Ka ce: "Sũ, dõmin waɗanda suka yi ĩmani suke a cikin rãyuwar dũniya, suna keɓantattu a Rãnar Kiyãma. "Kamar wannan ne Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, ga mutãnen da suke sani. = --Qur'an 7:32
    Say, "My Lord has only forbidden immoralities - what is apparent of them and what is concealed - and sin, and oppression without right, and that you associate with Allah that for which He has not sent down authority, and that you say about Allah that which you do not know." <> Ka ce: "Abin sani kawai, Ubangijina Yã hana abũbuwanalfãsha; abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya ɓõyu, da zunubi da rarraba jama'a, bã da wani hakki ba, kuma da ku yi shirki da Allah ga abin da bai saukar da wani dalĩli ba gare shi, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba, ga Allah." = --Qur'an 7:33
    And for every nation is a [specified] term. So when their time has come, they will not remain behind an hour, nor will they precede [it]. <> Kuma ga kõwace al'umma akwai ajali. Sa'an nan idan ajalinsu ya je, bã zã a yi musu jinkiri ba, sa'a guda, kuma bã zã su gabãce shi ba. = --Qur'an 7:34
    O children of Adam, if there come to you messengers from among you relating to you My verses, then whoever fears Allah and reforms - there will be no fear concerning them, nor will they grieve. <> Yã ɗiyan Ãdam! Ko dai wasu manzanni, daga cikinku, su jẽ muku, sunã gaya muku ayõyiNato, wanda ya yi taƙawa, kuma ya gyara aikinsa, to, bãbu tsoro a kansu, kuma bã su yin baƙin ciki. = --Qur'an 7:35
    But the ones who deny Our verses and are arrogant toward them - those are the companions of the Fire; they will abide therein eternally. <> Kuma waɗanda suka ƙaryatã game da ãyõyinMu, kuma suka yi girman kai daga gare su, waɗannan sũ ne abõkan wuta, sũ, a cikinta madawwama ne. = --Qur'an 7:36
    And who is more unjust than one who invents about Allah a lie or denies His verses? Those will attain their portion of the decree until when Our messengers come to them to take them in death, they will say, "Where are those you used to invoke besides Allah?" They will say, "They have departed from us," and will bear witness against themselves that they were disbelievers. <> To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ƙaryata game da ãyõyinSa? Waɗannan rabonsu daga Littãfi yanã sãmunsu, har a lõkacin da ManzanninMu suka je musu, sunã karɓar rãyukansu, su ce: "Ĩnã abin da kuka kasance kunã kira, baicin Allah?" Su ce: "Sun ɓace daga gare mu, "Kuma su yi shaida a kansu cẽwa lalle sũ, sun kasance kãfirai." = --Qur'an 7:37
    [Allah] will say, "Enter among nations which had passed on before you of jinn and mankind into the Fire." Every time a nation enters, it will curse its sister until, when they have all overtaken one another therein, the last of them will say about the first of them "Our Lord, these had misled us, so give them a double punishment of the Fire. He will say, "For each is double, but you do not know." <> Ya ce: "Ku shiga a cikin al'ummai waɗanda, haƙĩƙa, sun shige daga gabãninku, daga aljannu da mutãne, a cikin Wuta. A kõ da yaushe wata al'umma ta shiga sai ta la'ani 'yar'uwarta, har idan suka riski jũna, a cikinta, gabã ɗaya, ta ƙarshensu ta ce wa ta farkonsu: "Ya Ubangijinmu! Waɗannan ne suka ɓatar da mu, sai Ka kãwo musu azãba ninki daga wuta." Ya ce: "Ga kõwane akwai ninki; kuma amma ba ku sani ba." = --Qur'an 7:38
    And the first of them will say to the last of them, "Then you had not any favor over us, so taste the punishment for what you used to earn." <> Kuma ta farkonsu ta ce wa ta ƙarshe: "To, bã ku da wata falala a kanmu, sai ku ɗanɗana azãba sabõda abin da kuka kasance kunã tãrãwa!" = --Qur'an 7:39
    Indeed, those who deny Our verses and are arrogant toward them - the gates of Heaven will not be opened for them, nor will they enter Paradise until a camel enters into the eye of a needle. And thus do We recompense the criminals. <> Lalle ne waɗanda suka ƙaryatã game da ãyõyinMu, kuma suka yi girman kai daga barinsu, bã zã a bubbuɗe musu kõfõfin sama ba, kuma bã su shiga Aljanna sai raƙumi ya shiga kafar allũra, kuma kamar wannan ne Muke sãka wa mãsu laifi. = --Qur'an 7:40
    They will have from Hell a bed and over them coverings [of fire]. And thus do We recompense the wrongdoers. <> Sunã da wata shimfiɗa daga Jahannama kuma daga samansu akwai wasu murafai. Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa azzãlumai. = --Qur'an 7:41
    But those who believed and did righteous deeds - We charge no soul except [within] its capacity. Those are the companions of Paradise; they will abide therein eternally. <> Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, bã Mu ƙallafa wa rai fãce iyãwarsa, Waɗannan ne abõkan Aljanna, sũ, a cikinta, madawwma ne. = --Qur'an 7:42
    And We will have removed whatever is within their breasts of resentment, [while] flowing beneath them are rivers. And they will say, "Praise to Allah, who has guided us to this; and we would never have been guided if Allah had not guided us. Certainly the messengers of our Lord had come with the truth." And they will be called, "This is Paradise, which you have been made to inherit for what you used to do." <> Kuma Muka fitar da abin da yake a cikin ƙirãzansu, daga ƙiyayya, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, kuma suka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya shiryar da mu ga wannan. Kuma ba mu kasance munã iya shiryuwa ba, bã dõmin Allah Ya shiryar da mu ba. Lalle ne haƙĩƙa, Manzannin Ubangjinmu, sun jẽ mana da gaskiya." Kuma aka kira su, cẽwa: "Waccan Aljlnna an gãdar da ku ita, sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa." = --Qur'an 7:43
    And the companions of Paradise will call out to the companions of the Fire, "We have already found what our Lord promised us to be true. Have you found what your Lord promised to be true?" They will say, "Yes." Then an announcer will announce among them, "The curse of Allah shall be upon the wrongdoers." <> Kuma 'yan Aljanna suka kirãyi 'yan Wuta suka ce: "Lalle ne mun sãmi abin da Ubangijinmu Ya yi mana wa'adi, gaskiya ne. To, shin, kun sãmi abin da Ubangijinku Ya yi muku wa'adi, gaskiya?" Suka ce: "Na'am." Sai mai sanarwa ya yi yẽkuwa, cẽwa: "La'anar Allah ta tabbata a kan azzãlumai." = --Qur'an 7:44
    Who averted [people] from the way of Allah and sought to make it [seem] deviant while they were, concerning the Hereafter, disbelievers. <> "Waɗanda suke kangẽwa daga hanyar Allah, kuma sunã nẽman ta ta zama karkatacciya,. kuma sũ, game da Lãhira, kãfirai ne." = --Qur'an 7:45
    And between them will be a partition, and on [its] elevations are men who recognize all by their mark. And they call out to the companions of Paradise, "Peace be upon you." They have not [yet] entered it, but they long intensely. <> Kuma a tsakãninsu akwai wani shãmaki, kuma a kan A'arãf akwai wasu maza sunã sanin kõwa da alãmarsu; Kuma suka kirãyi abõkan Aljamia cẽwa: "Aminci ya tabbata a kanku: "Ba su shige ta ba, alhãli kuwa sũ, sunã tsammãni. = --Qur'an 7:46
    And when their eyes are turned toward the companions of the Fire, they say, "Our Lord, do not place us with the wrongdoing people." <> Kuma idan an jũyar da gannansu wajen abõkan wuta, su ce: "Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanyã mu tãre da mutãne azzãlumai." = --Qur'an 7:47
    And the companions of the Elevations will call to men [within Hell] whom they recognize by their mark, saying, "Of no avail to you was your gathering and [the fact] that you were arrogant." <> Kuma abõkan A'araf suka kirãyi wasu maza, sunã sanin su da alãmarsu, suka ce: "Tãrawar dũkiyarku da abin da kuka kasance kunã yi na girman kai, bai wadãtar ba daga barinku?" = --Qur'an 7:48
    [Allah will say], "Are these the ones whom you [inhabitants of Hell] swore that Allah would never offer them mercy? Enter Paradise, [O People of the Elevations]. No fear will there be concerning you, nor will you grieve." <> "Shin, waɗannan ne waɗanda kuka yi rantsuwa, Allah bã zai sãme su da rahama ba? Ku shiga Aljanna, bãbu tsõro akanku, kuma ba ku zama kunã baƙin ciki ba." = --Qur'an 7:49
    And the companions of the Fire will call to the companions of Paradise, "Pour upon us some water or from whatever Allah has provided you." They will say, "Indeed, Allah has forbidden them both to the disbelievers." <> Kuma 'yan wuta suka kirãyi 'yan Aljanna cẽwa: "Ku zubo a kaumu daga ruwa kõ kuwa daga abin da Allah Ya azurta ku." Su ce: "Lalle ne Allah Ya haramtã su a kan kãfirai." = --Qur'an 7:50
    Who took their religion as distraction and amusement and whom the worldly life deluded." So today We will forget them just as they forgot the meeting of this Day of theirs and for having rejected Our verses. <> "Waɗanda suka riƙi addininsu abin shagala da wãsa, kuma rãyuwar dũniya ta rũɗe su." To, a yau Munã mantãwa da su, kamar yadda suka manta da haɗuwa da yininsu wannan, da kuma abin da suka kasance da ãyoyinMu sunã musu. = --Qur'an 7:51
    And We had certainly brought them a Book which We detailed by knowledge - as guidance and mercy to a people who believe. <> Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun jẽ musu da Littãfi, Mun bayyana Shi, daki-daki, a kan ilmi, yanã shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin ĩmani. = --Qur'an 7:52
    Do they await except its result? The Day its result comes those who had ignored it before will say, "The messengers of our Lord had come with the truth, so are there [now] any intercessors to intercede for us or could we be sent back to do other than we used to do?" They will have lost themselves, and lost from them is what they used to invent. <> Shin, sunã jira, fãce fassararsa, a rãnar da fassararsa take zuwa, waɗanda saka manta da Shi daga gabãni, sunã cẽwa: "Lalle ne, Manzannin Ubangijin mu svun jẽ da gaskiya. To, shin, munã da wasu mãsu cẽto, su yi cẽto gare mu, kõ kuwa a mayar da mũ, har mu aikata wanin wanda muka kasance muna aikatãwa?" Lalle ne sun yi hasãrar rãyukansu, kuma abin da suka kasance sunã ƙĩrƙirawa yã ɓace musu. = --Qur'an 7:53
    Indeed, your Lord is Allah, who created the heavens and earth in six days and then established Himself above the Throne. He covers the night with the day, [another night] chasing it rapidly; and [He created] the sun, the moon, and the stars, subjected by His command. Unquestionably, His is the creation and the command; blessed is Allah, Lord of the worlds. <> Lalle ne Ubangijinku Allah ne, wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin kwãnaki shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, Yanã sanya dare ya rufa yini, yanã nẽman sa da gaggawa, kuma rãnã da watã da taurãri hõrarru ne da umurninSa. To, Shĩ ne da halittar kuma da umurnin. Albarkar Allah Ubangijin halittu tã bayyana! = --Qur'an 7:54
    Call upon your Lord in humility and privately; indeed, He does not like transgressors. <> Ku kirãyi Ubangijinku da ƙanƙan da kai, da kuma a ɓõye: lalle ne Shĩ, bã Yã son mãsuwuce iyãka. = --Qur'an 7:55
    And cause not corruption upon the earth after its reformation. And invoke Him in fear and aspiration. Indeed, the mercy of Allah is near to the doers of good. <> Kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa a bãyan gyaranta. Kuma ku kirãye shi sabõda tsõro da tsammãni; lalle ne rahamar Allah makusanciya ce daga mãsu kyautatãwa. = --Qur'an 7:56
    And it is He who sends the winds as good tidings before His mercy until, when they have carried heavy rainclouds, We drive them to a dead land and We send down rain therein and bring forth thereby [some] of all the fruits. Thus will We bring forth the dead; perhaps you may be reminded. <> Kuma Shĩ ne wanda Yake aika iskõki, sunã bishãra gaba ga rahamarSa, har idan sun ɗauki gizãgizai mãsu nauyi, sai Mu kõra su ga wani gari matacce, sa'an nan Mu saukar da ruwa gare shi, sa'an nan Mu fitar, game da shi, daga dukkan 'ya'yan itĩce. Kamar wancan ne Muke fitar da matattu; tsammãninku, kunã tunãni. = --Qur'an 7:57
    And the good land - its vegetation emerges by permission of its Lord; but that which is bad - nothing emerges except sparsely, with difficulty. Thus do We diversify the signs for a people who are grateful. <> Kuma gari mai kyau, tsirinsa yanã fita da iznin Ubangijinsa, kuma wanda ya mũnana, (tsirinsa) bã ya fita, fãce da wahala; kamar wannan ne, Muka sarrafa ãyõyi dõmin mutãne waɗanda suke gõdẽwa. = --Qur'an 7:58
    We had certainly sent Noah to his people, and he said, "O my people, worship Allah; you have no deity other than Him. Indeed, I fear for you the punishment of a tremendous Day. <> Lalle ne, haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnẽnsa, sai ya ce: "Yã mutãnẽna! Ku bauta waAllah! Bã ku da wani abin bautãwa waninSa. Lalle ne nĩ, inã yimuku tsõron azãbar wani Yini mai girma." = --Qur'an 7:59
    Said the eminent among his people, "Indeed, we see you in clear error." <> Mashawarta daga mutãnensa suka ce: "Lalle ne mu, haƙĩƙa, Munã ganin ka a cikin ɓata bayyananniya." = --Qur'an 7:60
    [Noah] said, "O my people, there is not error in me, but I am a messenger from the Lord of the worlds." <> Ya ce: "Yã mutãnena! Bãbu ɓata guda gare ni, kuma amma nĩ Manzo ne daga ubangijin halittu!" = --Qur'an 7:61
    I convey to you the messages of my Lord and advise you; and I know from Allah what you do not know. <> "Inã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina; kuma inã yi muku nasĩha, kuma inã sani, daga Allah, abin da ba ku sani ba. = --Qur'an 7:62
    Then do you wonder that there has come to you a reminder from your Lord through a man from among you, that he may warn you and that you may fear Allah so you might receive mercy." <> "Shin, kunã mãmãkin cẽwa ambato yã zo muku daga Ubangijinku a kan wani namiji, daga gare ku, dõmin ya yi muku gargaɗi, kuma dõmin ku yi taƙawa, kuma tsammãninku anã jin ƙanku?" = --Qur'an 7:63
    But they denied him, so We saved him and those who were with him in the ship. And We drowned those who denied Our signs. Indeed, they were a blind people. <> Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan Muka tsĩrar da shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgin; kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata shi game da ãyõyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance wasu mutãne ɗĩmautattu. = --Qur'an 7:64
    And to the 'Aad [We sent] their brother Hud. He said, "O my people, worship Allah; you have no deity other than Him. Then will you not fear Him?" <> Kuma zuwa ga Ãdãwa, ɗan'uwansu Hudu, ya ce: "Ya mutãnena! Ku bautã wa Allah! Bã ku da wani abin bautã wa, waninSa. Shin fa, bã zã ku yi taƙawa ba?" = --Qur'an 7:65
    Said the eminent ones who disbelieved among his people, "Indeed, we see you in foolishness, and indeed, we think you are of the liars." <> Mashawarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa suka ce: "Lalle ne mũ, haƙĩƙka, Munã ganin ka a cikin wata wauta! Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, Munã zaton ka daga maƙaryata." = --Qur'an 7:66
    [Hud] said, "O my people, there is not foolishness in me, but I am a messenger from the Lord of the worlds." <> Ya ce: "Yã mutãnena! Bãbu wata wauta a gare ni, kuma amma nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu!" = --Qur'an 7:67
    I convey to you the messages of my Lord, and I am to you a trustworthy adviser. <> Inã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina, kuma nĩ, gare ku, mai nasĩha ne amintacce. = --Qur'an 7:68
    Then do you wonder that there has come to you a reminder from your Lord through a man from among you, that he may warn you? And remember when He made you successors after the people of Noah and increased you in stature extensively. So remember the favors of Allah that you might succeed. <> "Shin, kuma kun yi mãmãki cẽwa ambato daga Ubangijinku ya zo muku a kan wani namiji daga gare ku, dõmin ya yi muku gargaɗi? Kuma ku tunã a lõkacin da Ya sanyã ku mãsu mayẽwa daga bãyan mutãnen Nũhu, kuma Ya ƙãra muku zãti a cikin halitta. Sabõda haka ku tuna ni'imõmin Allah; tsammãninku kunã cin nasara." = --Qur'an 7:69
    They said, "Have you come to us that we should worship Allah alone and leave what our fathers have worshipped? Then bring us what you promise us, if you should be of the truthful." <> Suka ce: "Shin, kã zo mana ne dõmin mu bauta wa Allah Shi kaɗai, kuma mu bar abin da ubanninmu suka kasance sunã bauta wa? To, ka zõ mana da abin da kake yi mana wa'adi da shi idan kã kasance daga mãsu gaskiya." = --Qur'an 7:70
    [Hud] said, "Already have defilement and anger fallen upon you from your Lord. Do you dispute with me concerning [mere] names you have named them, you and your fathers, for which Allah has not sent down any authority? Then wait; indeed, I am with you among those who wait." <> Ya ce: "Haƙĩƙa azãba da fushi sun auku a kanku daga Ubangijinku! Shin, kunã jãyayya da ni a cikin wasu sunãye waɗanda kũ ne kuka yi musu sunãyen, kũ da ubanninku, Allah bai saukar da wani dalili ba a gare su? To, ku yi jira. Lalle ne ni, tãre da ku mai jira ne." = --Qur'an 7:71
    So We saved him and those with him by mercy from Us. And We eliminated those who denied Our signs, and they were not [at all] believers. <> To, sai Muka tsĩrar da shi, shĩ da waɗanda suke tãre da shi sabõda wata rahama daga gare Mu, kuma Muka katse ƙarshen waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma ba su kasance mũminaiba. = --Qur'an 7:72
    And to the Thamud [We sent] their brother Salih. He said, "O my people, worship Allah; you have no deity other than Him. There has come to you clear evidence from your Lord. This is the she-camel of Allah [sent] to you as a sign. So leave her to eat within Allah 's land and do not touch her with harm, lest there seize you a painful punishment. <> Kuma zuwa ga Samũdãwa ɗan'uwansu, Sãlihu, ya ce: "Yã mutãnena! Ku bauta wa Allah; bã ku da wani abin bauta wa wanninSa. Haƙĩƙa hujja bayyananniya tã zo muku daga Ubangijinku! wannan rãƙumar Allah ce, a gare ku, wata ãyã ce. Sai ku bar ta ta ci, a cikin ƙasar Allah, kuma kada ku shãfe ta da wata cũta har azãba mai raɗaɗi ta kãmã ku." = --Qur'an 7:73
    And remember when He made you successors after the 'Aad and settled you in the land, [and] you take for yourselves palaces from its plains and carve from the mountains, homes. Then remember the favors of Allah and do not commit abuse on the earth, spreading corruption." <> "Kuma ku tuna a lõkacin da Ya sanyã ku mamaya daga bãyan Ãdãwa kuma Ya zaunar da ku a cikin ƙasa, kunã riƙon manyan gidãje daga tuddanta, kuma kunã sassaƙar ɗãkuna daga duwãtsu; sabõda haka ku tuna ni'imõmin Allah, kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa kuna mãsu fasãdi." = --Qur'an 7:74
    Said the eminent ones who were arrogant among his people to those who were oppressed - to those who believed among them, "Do you [actually] know that Salih is sent from his Lord?" They said, "Indeed we, in that with which he was sent, are believers." <> Mashawarta waɗanda suka yi girman kai daga mutanensa suka ce ga waɗanda aka raunanar, ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare su: "Shin, kunã sanin cẽwaSãlihu manzo ne daga Ubangijinsa?" Suka ce: "Lalle ne mũ, da abin daaka aiko shi, mãsu ĩmãni ne." = --Qur'an 7:75
    Said those who were arrogant, "Indeed we, in that which you have believed, are disbelievers." <> Waɗanda suka yi girman kai suka ce: "Lalle ne mu, ga abin da kuka yi ĩmãni da shi kãfirai ne." = --Qur'an 7:76
    So they hamstrung the she-camel and were insolent toward the command of their Lord and said, "O Salih, bring us what you promise us, if you should be of the messengers." <> Sai suka sõke rãƙumar, kuma suka kangare daga barin umurnin Ubangijinsu, kuma suka ce: "Yã Sãlihu! Ka zõ mana da abin da kake yi mana wa'adi da shi, idan kã kasance daga manzanni!" = --Qur'an 7:77
    So the earthquake seized them, and they became within their home [corpses] fallen prone. <> Sai tsãwa ta kãmã su, sabõda haka suka wãyi gari a cikin gidansu guggurfãne! = --Qur'an 7:78
    And he turned away from them and said, "O my people, I had certainly conveyed to you the message of my Lord and advised you, but you do not like advisors." <> Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: "Ya mutãnena! Lalle ne, haƙĩƙa, nã iyar muku damanzancin Ubangijina. Kuma nã yi muku nasĩha kuma amma bã ku son mãsu nasĩha!" = --Qur'an 7:79
    And [We had sent] Lot when he said to his people, "Do you commit such immorality as no one has preceded you with from among the worlds? <> Da Lũɗu, a lõkacin daya ce wa mutãnensa: "Shin, kunã jẽ wa alfãsha, bãbu kõwa da ya gabãce ku da ita daga halittu?" = --Qur'an 7:80
    Indeed, you approach men with desire, instead of women. Rather, you are a transgressing people." <> "Lalle ne ku, haƙĩƙa kunã jẽ wa maza da sha'awa, baicin mata; Ã'a, kũ mutãne ne maɓarnata." = --Qur'an 7:81
    But the answer of his people was only that they said, "Evict them from your city! Indeed, they are men who keep themselves pure." <> Kuma bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa, fãce ɗai suka ce: "Ku fitar da su daga alƙaryarku: lalle ne sũ, wasumutãne ne mãsu da'awar tsarki!" = --Qur'an 7:82
    So We saved him and his family, except for his wife; she was of those who remained [with the evildoers]. <> Sai Muka tsĩrar da shi, shĩ da iyãlansa, fãce matarsa, ta kasance daga mãsu wanzuwa. = --Qur'an 7:83
    And We rained upon them a rain [of stones]. Then see how was the end of the criminals. <> Kuma Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa; Sai ka dũba yadda ãƙibar mãsu laifi ta kasance! = --Qur'an 7:84
    And to [the people of] Madyan [We sent] their brother Shu'ayb. He said, "O my people, worship Allah; you have no deity other than Him. There has come to you clear evidence from your Lord. So fulfill the measure and weight and do not deprive people of their due and cause not corruption upon the earth after its reformation. That is better for you, if you should be believers. <> Kuma zuwa Madayana ɗan'uwansu Shu'aibu, ya ce: "Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah; bã ku da wani abin bauta wa waninSa. Lalle ne, wata hujja bayyananniya daga Ubangijinku tã zõ muku! Sai ku cika mũdu da sikeli kumakada ku nakasa wa mutãne kãyansu, kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa a bãyan gyaranta. Wannan ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance mũminai." = --Qur'an 7:85
    And do not sit on every path, threatening and averting from the way of Allah those who believe in Him, seeking to make it [seem] deviant. And remember when you were few and He increased you. And see how was the end of the corrupters. <> "Kuma kada ku zauna ga kõwane tafarki kunã ƙyacẽwa, kuma kunã kangẽwa, daga hanyar Allah, ga wanda ya yi ĩmãni da shi, kuma kunã nẽman ta ta zama karkatacciya, kuma ku tuna, a lõkacin da kuka kasance kaɗan, sai Ya yawaita ku, kuma ku dũba yadda ãƙibar mãsu fasãdi ta kasance:" = --Qur'an 7:86
    And if there should be a group among you who has believed in that with which I have been sent and a group that has not believed, then be patient until Allah judges between us. And He is the best of judges." <> "Kuma idan wata ƙungiya daga gare ku ta kasance ta yi ĩmãni da abin da aka aiko ni da shi, kuma wata ƙungiya ba ta yi ĩmãni ba, to, ku yi haƙuri, har Allah Ya yi hukunci a tsakãninmu; kuma Shi ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci." = --Qur'an 7:87
    Said the eminent ones who were arrogant among his people, "We will surely evict you, O Shu'ayb, and those who have believed with you from our city, or you must return to our religion." He said, "Even if we were unwilling?" <> Mashawarta waɗanda suka kangare daga mutãnensa, suka ce: "Lalle ne, Munã fitar da kai, Yã Shu'aibu, kai da waɗanda suka yi Ĩmãni tãre da kai, daga alƙaryarmu; kõ kuwa lalle ku kõmo a cikin addininmu." Ya ce: "Ashe! Kuma kõ dã mun kasance mãsu ƙĩ?" = --Qur'an 7:88
    We would have invented against Allah a lie if we returned to your religion after Allah had saved us from it. And it is not for us to return to it except that Allah, our Lord, should will. Our Lord has encompassed all things in knowledge. Upon Allah we have relied. Our Lord, decide between us and our people in truth, and You are the best of those who give decision." <> "Lalle ne mun ƙirƙira ƙarya ga Allah idan mun kõma a cikin addininku a bãyan lõkacin da Allah ya tsĩrar da mu daga gare shi, kuma bã ya kasancewa a gare mu, mu kõma a cikinsa, fãce idan Al1ah, Ubangijinmu Ya so. Ubangijinmu Yã yalwaci dukan kõme ga ilmi. Ga Allah muka dõgara. Yã Ubangijinmu! Ka yi hukunci a tsakãninmu da tsakanin mutãnenmu da gaskiya, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci." = --Qur'an 7:89
    Said the eminent ones who disbelieved among his people, "If you should follow Shu'ayb, indeed, you would then be losers." <> Kuma mashawarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: "Lalle ne, idan kun bi Shu'aibu haƙĩƙa kũ, a lõkacin nan, mãsu hasãra ne." = --Qur'an 7:90
    So the earthquake seized them, and they became within their home [corpses] fallen prone. <> Sai tsãwa ta kãma su, sabõda haka suka wãyi gari, a cikin gidansu, sunã guggurfãne. = --Qur'an 7:91
    Those who denied Shu'ayb - it was as though they had never resided there. Those who denied Shu'ayb - it was they who were the losers. <> Waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu kamar ba su zauna ba a cikinta, waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu, sun kasance sũ nemãsu hasãra! = --Qur'an 7:92
    And he turned away from them and said, "O my people, I had certainly conveyed to you the messages of my Lord and advised you, so how could I grieve for a disbelieving people?" <> Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: "Yã mutãnena! Haƙĩƙa, nã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina, kuma nã yi muku nasĩha! To, yãya zan yi baƙin ciki a kan mutãne kãfirai?" = --Qur'an 7:93
    And We sent to no city a prophet [who was denied] except that We seized its people with poverty and hardship that they might humble themselves [to Allah]. <> Kuma ba Mu aika wani Annabi a cikin wata alƙarya ba, fãce Mun kãma mutãnenta da azãba da cũta, tsammãninsu sunã yin ƙasƙantar da kai. = --Qur'an 7:94
    Then We exchanged in place of the bad [condition], good, until they increased [and prospered] and said, "Our fathers [also] were touched with hardship and ease." So We seized them suddenly while they did not perceive. <> Sa'an nan kuma Muka musanya mai kyau a matsayin mummũna, har su yi yawa, kuma su ce: "Cũta da azãba sun shãfi ubanninmu." (sai su kõma wa kãfirci). Sai Mu kãmã su kwatsam! alhãli kuwa sũ, bã su sansancẽwa." = --Qur'an 7:95
    And if only the people of the cities had believed and feared Allah, We would have opened upon them blessings from the heaven and the earth; but they denied [the messengers], so We seized them for what they were earning." <> Kuma dã lalle mutãnen alƙaryu sun yi ĩmãni kuma suka yi taƙawa dã haƙĩƙa Mun bũɗe albarkõki a kansu daga sama da ƙasa, kuma amma sun ƙaryata, don haka Muka kãma su da abin da suka kasance sunã tãrãwa. = --Qur'an 7:96
    Then, did the people of the cities feel secure from Our punishment coming to them at night while they were asleep? <> Shin, mutãnen alƙaryu sun amince wa azãbar Mu ta jẽ musu da dare, alhãli kuwa sunã barci? = --Qur'an 7:97
    Or did the people of the cities feel secure from Our punishment coming to them in the morning while they were at play? <> Kõ kuwa mutãnen alƙaryu sun amince wa azãbarMu ta jẽ musu da hantsi, alhãli kuwa sunã wãsa? = --Qur'an 7:98
    Then did they feel secure from the plan of Allah? But no one feels secure from the plan of Allah except the losing people. <> Shin fa, sun amince wa makarun Allah? To, bãbu mai amince wa makarun Allah fãce mutãne mãsu hasãra! = --Qur'an 7:99
    Has it not become clear to those who inherited the earth after its [previous] people that if We willed, We could afflict them for their sins? But We seal over their hearts so they do not hear. <> Shin, kuma bai shiryar da waɗanda suke gãdon ƙasa ba daga bãyan mutãnenta cẽwa da Munã so, dã Mun sãme su da zunubansu, kuma Mu rufe a kan zukãtansu, sai su zama bã su ji? = --Qur'an 7:100
    Those cities - We relate to you, [O Muhammad], some of their news. And certainly did their messengers come to them with clear proofs, but they were not to believe in that which they had denied before. Thus does Allah seal over the hearts of the disbelievers. <> Waɗancan alƙaryu Munã gaya maka daga lãbãransu, kuma lalle ne, haƙĩƙa manzanninMu sun jẽ musu da hujjõji bayyanannnu; to, ba su kasance sunã yin ĩmãnida abin da suka ƙaryata daga gabãni ba. Kamar wancan ne Allah Yake rufẽwa a kan zukãtan kãfirai. = --Qur'an 7:101
    And We did not find for most of them any covenant; but indeed, We found most of them defiantly disobedient. <> Kuma ba Mu sãmi wani alkawari ba ga mafi yawansu, kuma lalle ne, Mun sãmi mafi yawansu, haƙĩƙa, fãsiƙai. = --Qur'an 7:102
    Then We sent after them Moses with Our signs to Pharaoh and his establishment, but they were unjust toward them. So see how was the end of the corrupters. <> Sa'an nan kuma Mun aika Musa, daga bãyansu, da ãyõyinMu zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka yi zãlunci game da su. To, dũbi yadda ãƙibar maɓarnata take. = --Qur'an 7:103
    And Moses said, "O Pharaoh, I am a messenger from the Lord of the worlds <> Kuma Musa ya ce: "Ya Fir'auna! Lalle ne nĩ, manzo ne daga Ubangijin halittu." = --Qur'an 7:104
    [Who is] obligated not to say about Allah except the truth. I have come to you with clear evidence from your Lord, so send with me the Children of Israel." <> "Tabbatacce ne a kan kada in faɗi kõme ga Allah fãce gaskiya. Lalle ne, nã zo muku da hujja bayyananniya daga Ubangijinku; Sai ka saki Banĩ Isrã'ila tãreda ni." = --Qur'an 7:105
    [Pharaoh] said, "If you have come with a sign, then bring it forth, if you should be of the truthful." <> Ya ce: "Idan kã kasance kã zo da wata ãyã, to, ka kãwõ ta, idan kã kasance daga mãsu gaskiya." = --Qur'an 7:106
    So Moses threw his staff, and suddenly it was a serpent, manifest. <> Sai ya jẽfa sandarsa, sai gã ta kumurci bayyananne! = --Qur'an 7:107
    And he drew out his hand; thereupon it was white [with radiance] for the observers. <> Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu dũbi! = --Qur'an 7:108
    Said the eminent among the people of Pharaoh, "Indeed, this is a learned magician <> Mashãwarta daga mutãnen Fir'auna suka ce: "Lalle ne, wannan, haƙĩƙa, matsafi ne mai ilmi." = --Qur'an 7:109
    Who wants to expel you from your land [through magic], so what do you instruct?" <> " Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku: To, mẽne ne kuke shawartawa?" = --Qur'an 7:110
    They said, "Postpone [the matter of] him and his brother and send among the cities gatherers <> Suka ce: "Ka jinkirtar da shĩ, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika da mãsu gayyar mutãne a cikin garũruwa. = --Qur'an 7:111
    Who will bring you every learned magician." <> "Su zõ maka da duka matsafi, mai ilmi." = --Qur'an 7:112
    And the magicians came to Pharaoh. They said, "Indeed for us is a reward if we are the predominant." <> Kuma matsafa suka jẽ wa fir'aunã suka ce: "Lalle ne, shin, Munã da ijãra, idan mun kasance mũ ne marinjaya?" = --Qur'an 7:113
    He said, "Yes, and, [moreover], you will be among those made near [to me]." <> Ya ce: "Na, am kuma lalle ne kunã a cikin makusanta." = --Qur'an 7:114
    They said, "O Moses, either you throw [your staff], or we will be the ones to throw [first]." <> Suka ce: "Ya Mũsã! Kõ dai ka jẽfa, kõ kuwa mu kasance, mũ ne, mãsu jẽfãwa?" = --Qur'an 7:115
    He said, "Throw," and when they threw, they bewitched the eyes of the people and struck terror into them, and they presented a great [feat of] magic. <> Ya ce: "Ku jẽfa." To a 1õkacin da suka jẽfa, suka sihirce idãnun mutãne kuma suka tsõratar da su; Kuma suka jẽ da tsafi mai girma." = --Qur'an 7:116
    And We inspired to Moses, "Throw your staff," and at once it devoured what they were falsifying. <> Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa: "Ka jẽfa sandarka." Sai gã ta tanã lãƙumar abin da suke ƙarya da shi! = --Qur'an 7:117
    So the truth was established, and abolished was what they were doing. <> Gaskiya ta auku, kuma abin da suke aikatãwa ya ɓãci. = --Qur'an 7:118
    And Pharaoh and his people were overcome right there and became debased. <> Sai aka rinjãye su a can, kuma suka jũya sunã ƙasƙantattu. = --Qur'an 7:119
    And the magicians fell down in prostration [to Allah]. <> Kuma aka jẽfar da matsafan, sunã mãsu sujada. = --Qur'an 7:120
    They said, "We have believed in the Lord of the worlds, <> Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halittu." = --Qur'an 7:121
    The Lord of Moses and Aaron." <> "Ubangijin Mũsã da Harũna." = --Qur'an 7:122
    Said Pharaoh, "You believed in him before I gave you permission. Indeed, this is a conspiracy which you conspired in the city to expel therefrom its people. But you are going to know. <> Fir'auna ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni da shi a gabãnin inyi izni a gare ku? Lalle ne, wannan, haƙĩƙa, mãkirci ne kuka mãkirta a cikin birni, dõmin ku fitar da mutãnensa daga gare shi; To, da sannu zã ku sani." = --Qur'an 7:123
    I will surely cut off your hands and your feet on opposite sides; then I will surely crucify you all." <> "Lalle ne, inã karkãtse hannãyenku da ƙafãfunku daga sãɓãni, sa'an nan kuma, haƙĩƙa, inã tsĩre, ku gabã ɗaya." = --Qur'an 7:124
    They said, "Indeed, to our Lord we will return. <> Suka ce: "Lalle ne mu, zuwa ga Ubangijinmu, mãsu jũyãwa ne." = --Qur'an 7:125
    And you do not resent us except because we believed in the signs of our Lord when they came to us. Our Lord, pour upon us patience and let us die as Muslims [in submission to You]." <> "Kuma bã ka zargin kõme daga gare mu fãce dõmin mun yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinmu a lõkacin da suka zõ mana! Ya Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu, kuma Ka cika mana munã Musulmai! " = --Qur'an 7:126
    And the eminent among the people of Pharaoh said," Will you leave Moses and his people to cause corruption in the land and abandon you and your gods?" [Pharaoh] said, "We will kill their sons and keep their women alive; and indeed, we are subjugators over them." <> Kuma mashawarta daga mutãnen Fir'auna suka ce: "Shin, zã ka bar Mũsã da mutãnensa dõmin su yi ɓarna a cikin ƙasa, kuma ya bar ka, kai da gumãkanka?" Ya ce: "Zã mu yayyanka ɗiyansu maza kuma mu rãya mãtansu; kuma lalle ne mũ, a bisa gare su, marinjãya ne." = --Qur'an 7:127
    Said Moses to his people, "Seek help through Allah and be patient. Indeed, the earth belongs to Allah. He causes to inherit it whom He wills of His servants. And the [best] outcome is for the righteous." <> Mũsã ya ce wa mutãnensa: "Ku nẽmi taimako da Allah, kuma ku yi haƙuri; Lalle ne ƙasa ta Allah ce, Yãna gãdar da ita ga wanda Yake so daga bãyinSa, kuma ãƙiba ta mãsu taƙawa ce." = --Qur'an 7:128
    They said, "We have been harmed before you came to us and after you have come to us." He said, "Perhaps your Lord will destroy your enemy and grant you succession in the land and see how you will do." <> Suka ce: "An cũtar da mu daga gabãnin ka zõ mana, kuma daga bãyan da kã zõ mana." Ya ce: "Akwai tsammãnin Ubangijinku, Ya halaka maƙiyanku, kuma Ya sanya ku, ku maye a cikin ƙasa, sa'an nan Ya dũba yadda kuke aikatãwa." = --Qur'an 7:129
    And We certainly seized the people of Pharaoh with years of famine and a deficiency in fruits that perhaps they would be reminded. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun kãma mutãnen Fir'auna da tsananin shẽkaru (fari) da nakasa daga 'ya'yan itãce; Tsammãninsu sunã tunãwa. = --Qur'an 7:130
    But when good came to them, they said, "This is ours [by right]." And if a bad [condition] struck them, they saw an evil omen in Moses and those with him. Unquestionably, their fortune is with Allah, but most of them do not know. <> Sa'an nan idan wani alhẽri ya jẽ musu, sai su ce: "Masĩfa ta sãme su, sai su yi shu'umci da Mũsã da wanda yake tãre da shi, To, shu'umcinsu a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawansu bã su sani!" = --Qur'an 7:131
    And they said, "No matter what sign you bring us with which to bewitch us, we will not be believers in you." <> Kuma suka ce: "Kõ me ka zõ mana da shi daga ãyã, dõmin ka sihirce mu da ita, to, baza mu zama, sabõda kai, mãsu ĩmãni ba." = --Qur'an 7:132
    So We sent upon them the flood and locusts and lice and frogs and blood as distinct signs, but they were arrogant and were a criminal people. <> Sai Muka aika a kansu da cikõwa, da fãra, da ƙwarƙwata da kwãɗi, da jini; ãyõyi abũbuwan rarrabẽwa; Sai suka kangare, kuma suka kasance mutãne mãsu laifi. = --Qur'an 7:133
    And when the punishment descended upon them, they said, "O Moses, invoke for us your Lord by what He has promised you. If you [can] remove the punishment from us, we will surely believe you, and we will send with you the Children of Israel." <> Kuma a lõkacin da masĩfa ta auku a kansu, sukan ce: "Yã Mũsã! Ka rõƙa mana Ubangijinka, sabõda abin da Ya yi alkwari a wurinka, lalle ne idan ka kau da azãbar daga barinmu, haƙĩƙa Munã ĩmãni sabõda kai, kuma munã sakin Banĩ Isrã'ila tĩre da kai." = --Qur'an 7:134
    But when We removed the punishment from them until a term which they were to reach, then at once they broke their word. <> To, a lõkacin da Muka kuranye azãba daga barinsu zuwa a wani ajali wanda suke mãsu iske shi ne, sai gã su sunã warwarẽwa! = --Qur'an 7:135
    So We took retribution from them, and We drowned them in the sea because they denied Our signs and were heedless of them. <> Sai Muka yi azãbar rãmuwa, daga gare su, sabõda haka Muka nutsar da su a cikin tẽku, dõmin lalle ne sũ, sun ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma sun kasance daga barinsu, gãfilai. = --Qur'an 7:136
    And We caused the people who had been oppressed to inherit the eastern regions of the land and the western ones, which We had blessed. And the good word of your Lord was fulfilled for the Children of Israel because of what they had patiently endured. And We destroyed [all] that Pharaoh and his people were producing and what they had been building. <> Kuma Muka gãdar da mutãnen, waɗanda sun kasance anã raunana su, a gabacin ƙasa da yammacinta, wadda Muka sanya albarka a cikinta, kuma kalmar Ubangijinka mai kyau ta cika a kan Banĩ Isrã'ĩla, sabõda abin dasuka yi na haƙuri. Kuma Muka murtsuke abin da Fir'auna da mutãnensa suka kasance sunã sanã'antawa, da abin da suka kasance sunã shimfiɗãwa. = --Qur'an 7:137
    And We took the Children of Israel across the sea; then they came upon a people intent in devotion to [some] idols of theirs. They said, "O Moses, make for us a god just as they have gods." He said, "Indeed, you are a people behaving ignorantly. <> Kuma Muka ƙẽtarar da Banĩ Isra'ila ga tẽku, sai suka jẽ a kan wasu mutãne waɗanda sunã lizimta da ibãda a kan wasu gumãka, nãsu suka ce: "Yã Mũsã! Ka sanya mana wani abin bautawa kamar yadda suke da abũbuwan bautãwa " Ya ce: "Lalle ne kũ, mutãne ne kunã jahilta." = --Qur'an 7:138
    Indeed, those [worshippers] - destroyed is that in which they are [engaged], and worthless is whatever they were doing." <> "Lalle ne waɗannan, abin da suke a cikinsa halakakke ne, kuma abin da suka kasance sunã aikãtawa ƙarya ne." = --Qur'an 7:139
    He said, "Is it other than Allah I should desire for you as a god while He has preferred you over the worlds?" <> Ya ce: "Shin, wanin Allah nike nẽma muku ya zama abin bautãwa, alhãli kuwa Shĩ (Allah) Ya fĩfĩta ku a kan halittu?" = --Qur'an 7:140
    And [recall, O Children of Israel], when We saved you from the people of Pharaoh, [who were] afflicting you with the worst torment - killing your sons and keeping your women alive. And in that was a great trial from your Lord. <> Kuma a lõkacin da Muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, sunã tayã muku mugunyar azãba. sunã karkashe ɗiyanku maza, kuma sunã rãyar da matanku. Kuma a cikin wancan akwai jarrabãwa daga Ubangijinku, Mai girma. = --Qur'an 7:141
    And We made an appointment with Moses for thirty nights and perfected them by [the addition of] ten; so the term of his Lord was completed as forty nights. And Moses said to his brother Aaron, "Take my place among my people, do right [by them], and do not follow the way of the corrupters." <> Kuma Muka yi wa'adi ga Mũsã da dare talãtin kuma Muka cikã su da gõma, sai miƙatin Ubangijinsa ya cika dare arba'in. Kuma Mũsã ya ce wa ɗan'uwansa, Hãrũna: "Ka maye mini a cikin mutãnena, kuma ka gyãra, kuma kada ka bi hanyar mãsu fasãdi." = --Qur'an 7:142
    And when Moses arrived at Our appointed time and his Lord spoke to him, he said, "My Lord, show me [Yourself] that I may look at You." [Allah] said, "You will not see Me, but look at the mountain; if it should remain in place, then you will see Me." But when his Lord appeared to the mountain, He rendered it level, and Moses fell unconscious. And when he awoke, he said, "Exalted are You! I have repented to You, and I am the first of the believers." <> Kuma a lõkacin da Mũsã ya jẽ ga mĩkatinMu, kuma Ubangijinsa Ya yi masa magana, shi Mũsã ya ce: "Yã Ubangijina! Ka nũna mini in yi dũbi zuwa gare Ka!" Ya ce: "Bã zã ka gan Ni ba, kuma amma ka dũba zuwa ga dũtse, to, idan ya tabbata a wurinsa, to, zã ka gan Ni." Sa'an nan a lõkacin da Ubangijinsa, Ya kuranye zuwa ga dũtsen, Ya sanyã shi niƙaƙƙe. Kuma Mũsã ya fãɗi sõmamme. To, a lõkacin da ya farka, ya ce: "TsarkinKa ya tabbata! Nã tũba zuwa gare Ka, kuma ni ne farkon mũminai." = --Qur'an 7:143
    [Allah] said, "O Moses, I have chosen you over the people with My messages and My words [to you]. So take what I have given you and be among the grateful." <> Ya ce: "Ya Mũsã! Lalle ne Nĩ, Nã zãɓe ka bisa ga mutãne da manzanciNa, kuma da maganãTa. Sabõda haka ka riƙi abin da Nã bã ka, kuma ka kasance daga mãsu gõdiya." = --Qur'an 7:144
    And We wrote for him on the tablets [something] of all things - instruction and explanation for all things, [saying], "Take them with determination and order your people to take the best of it. I will show you the home of the defiantly disobedient." <> Kuma Muka rubũta masa a cikin alluna daga kõwane abu, wa'azi da rarrabẽwa ga dukan kõwane abu: "Sai ka riƙe su da ƙarfi, kuma ka umurci mutãnenka, su yi riƙo ga abin da yake mafi kyawunsu; zã Ni nũna muku gidan fãsiƙai." = --Qur'an 7:145
    I will turn away from My signs those who are arrogant upon the earth without right; and if they should see every sign, they will not believe in it. And if they see the way of consciousness, they will not adopt it as a way; but if they see the way of error, they will adopt it as a way. That is because they have denied Our signs and they were heedless of them. <> Zã Ni karkatar da waɗanda suke yin girman kai a cikin ƙasa, bã da wani hakki ba, daga ãyõyiNa. Kuma idan sun ga dukan ãyã, bã zã su yi ĩmãni da ita ba, kuma idan sun ga hanyar shiriya, bã zã su riƙe ta hanya ba, kuma idan sun ga hanyar ɓata, sai su riƙe ta hanya. Wancan ne, dõmin lalle ne su, sun ƙaryata da ãyõyinMu, kuma sun kasance, daga barinsu gãfilai. = --Qur'an 7:146
    Those who denied Our signs and the meeting of the Hereafter - their deeds have become worthless. Are they recompensed except for what they used to do? <> Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu da gamuwa da Lãhira, ayyukansu sun ɓãci. Shin, ana saka musu, fãce da abin da suka kasance suna aikatãwa? = --Qur'an 7:147
    And the people of Moses made, after [his departure], from their ornaments a calf - an image having a lowing sound. Did they not see that it could neither speak to them nor guide them to a way? They took it [for worship], and they were wrongdoers. <> Kuma mutãnen Mũsã suka riƙi maraƙi, jikin mutãne, yanã rũri, daga bãyan tafiyarsa, daga kãyan ƙawarsu. Shin, ba su ganĩ ba, cẽwa lalle ne shi, bã ya yi musu magana, kuma bã ya shiryar da su ga hanya, sun riƙa shi, kuma sun kasance mãsu zãlunci. = --Qur'an 7:148
    And when regret overcame them and they saw that they had gone astray, they said, "If our Lord does not have mercy upon us and forgive us, we will surely be among the losers." <> Kuma a lõkacin da suka yi nadãma, kuma suka ga cẽwalalle ne sũ haƙĩƙa sun ɓace, suka ce: "Haƙĩƙa, idan UbangijinMu bai yi mana rahama ba, kuma Ya gãfarta mana, lalle ne munã kasancẽwa daga mãsu hasãra." = --Qur'an 7:149
    And when Moses returned to his people, angry and grieved, he said, "How wretched is that by which you have replaced me after [my departure]. Were you impatient over the matter of your Lord?" And he threw down the tablets and seized his brother by [the hair of] his head, pulling him toward him. [Aaron] said, "O son of my mother, indeed the people oppressed me and were about to kill me, so let not the enemies rejoice over me and do not place me among the wrongdoing people." <> Kuma a lõkacin da Mũsã ya kõma zuwa ga mutãnensa, yanã mai fushi, mai baƙin ciki, ya ce: "Tir da abin da kuka yi mini wakilci, a bãyanã! Shin, kun nẽmi gaggawar umurnin Ubangijinku ne?" Kuma ya jefar da Allunan, kuma ya yi riƙo ga kan ɗan'uwansa yana jan sa zuwa gare shi. Ya ce: "Yã ɗan'uwata! Lalle ne mutãnen, sun ɗauke ni mai rauni, kuma sun yi kusa su kashe ni, sabõda haka kada ka dãrantar da maƙiya game da ni, kuma kada ka sanya ni tãre da mutãne azzãlumai." = --Qur'an 7:150
    [Moses] said, "My Lord, forgive me and my brother and admit us into Your mercy, for You are the most merciful of the merciful." <> Ya ce: "Yã Ubangijina! Ka gãfarta mini, nĩ da ɗan'uwana, kuma Ka shigar da mu a cikin rahamarKa, alhãli kuwa Kai ne Mafi rahamar mãsu rahama!" = --Qur'an 7:151
    Indeed, those who took the calf [for worship] will obtain anger from their Lord and humiliation in the life of this world, and thus do We recompense the inventors [of falsehood]. <> Lalle ne waɗanda suka riƙi maraƙin, wani fushi daga Ubangijinsu da wani walãkanci a cikin rãyuwar dũniya, zã su sãme su: Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu ƙirƙira ƙarya. = --Qur'an 7:152
    But those who committed misdeeds and then repented after them and believed - indeed your Lord, thereafter, is Forgiving and Merciful. <> Kuma waɗanda suka aikata miyãgun ayyuka, sa'an nan suka tũba daga bãyansu kuma sukayi ĩmãni, lalle ne Ubangijinka daga bãyansu, haƙĩƙa, Mai gãfarane, Mai jin ƙai. = --Qur'an 7:153
    And when the anger subsided in Moses, he took up the tablets; and in their inscription was guidance and mercy for those who are fearful of their Lord. <> Kuma a lõkacin da fushin ya kwanta daga barin Mũsã, sai ya riƙi Allunan, kuma a cikin kwafensu akwai shiriya da rahama ga waɗanda suke sũ, ga Ubangijinsu, mãsu jin tsõro ne. = --Qur'an 7:154
    And Moses chose from his people seventy men for Our appointment. And when the earthquake seized them, he said, "My Lord, if You had willed, You could have destroyed them before and me [as well]. Would You destroy us for what the foolish among us have done? This is not but Your trial by which You send astray whom You will and guide whom You will. You are our Protector, so forgive us and have mercy upon us; and You are the best of forgivers. <> Kuma Mũsã ya zãɓi mutãnensa, namiji saba'in dõmin miƙãtinMu. To, a lõkacin da tsãwa ta kãma su, ya ce: "Yã Ubangijina! Dã Kã so, dã Kã halakar da su daga gabãni, sũ da ni. Shin zã Kahalaka mu, sabõda abin da wãwãyen daga gare mu suka aikata? Ba ta zama ba fãce fitinarKa Kanã ɓatarwa, da ita, wanda Kake so kuma kanã shiryarwa da ita, wanda Kake so; Kai ne Majiɓincinmu. Sai Ka gãfarta mana; kuma Ka yi mana rahama, alhãli kuwa Kai ne Mafi alhẽrin mãsu gãfara." = --Qur'an 7:155
    And decree for us in this world [that which is] good and [also] in the Hereafter; indeed, we have turned back to You." [Allah] said, "My punishment - I afflict with it whom I will, but My mercy encompasses all things." So I will decree it [especially] for those who fear Me and give zakah and those who believe in Our verses - <> "Kuma Ka rubũta mana alhẽri a cikin wannan dũniya, kuma a cikin Lãhira. Lalle ne mũ, mun tũba zuwa gare Ka." Ya ce: "AzãbaTa Inã sãmu, da ita, wanda Nike so, kuma rahamaTa, ta yalwaci dukan kõme. Sa'an nan zã Ni rubũta ta ga waɗanda suke yin taƙawa, kuma sunã bãyar da zakka, da waɗanda suke, game da ãyõyinMu mũminai ne." = --Qur'an 7:156
    Those who follow the Messenger, the unlettered prophet, whom they find written in what they have of the Torah and the Gospel, who enjoins upon them what is right and forbids them what is wrong and makes lawful for them the good things and prohibits for them the evil and relieves them of their burden and the shackles which were upon them. So they who have believed in him, honored him, supported him and followed the light which was sent down with him - it is those who will be the successful. <> "Waɗanda suke sunã bin Manzo, Annabi, Ummiyyi wanda suke sãmun sa rubũce a wurinsu, a cikin Attaura da Linjĩla. = --Qur'an 7:157
    Say, [O Muhammad], "O mankind, indeed I am the Messenger of Allah to you all, [from Him] to whom belongs the dominion of the heavens and the earth. There is no deity except Him; He gives life and causes death." So believe in Allah and His Messenger, the unlettered prophet, who believes in Allah and His words, and follow him that you may be guided. <> Ka ce: "Yã kũ mutãne! Lalle ne nĩ manzon Allah nezuwa gare ku, gabã ɗaya. (Allah) Wanda Yake Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa; Bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Yanã rãyarwa, kuma Yanã matarwa, sai ku yi ĩmãni daAllah da ManzonSa, Annabi, Ummiyyi, wanda yake yin ĩmãni da Allah da kalmominSa; ku bĩ shi, tsammãninku, kunã shiryuwa." = --Qur'an 7:158
    And among the people of Moses is a community which guides by truth and by it establishes justice. <> Kuma daga mutãnen Mũsã akwai al'umma, sunã shiryarwa da gaskiya, kuma da ita suke yin ãdalci. = --Qur'an 7:159
    And We divided them into twelve descendant tribes [as distinct] nations. And We inspired to Moses when his people implored him for water, "Strike with your staff the stone," and there gushed forth from it twelve springs. Every people knew its watering place. And We shaded them with clouds and sent down upon them manna and quails, [saying], "Eat from the good things with which We have provided you." And they wronged Us not, but they were [only] wronging themselves. <> Kuma Muka yayyanka su sibɗi gõma shã biyu, al'ummai. Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã a lõkacin da mutãnensasuka nẽme shi, ga shãyarwa, cẽwa: "Ka dõki dũtsen da sandarka."Sai marmaro gõma shã biyu suka ɓuɓɓuga daga gare shi: Lalle ne kõwaɗanne mutãne sun san mashãyarsu. Kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kansu."Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku."Kuma ba su zãluncẽ Mu ba; kuma amma rãyukansu suke zãlunta. = --Qur'an 7:160
    And [mention, O Muhammad], when it was said to them, "Dwell in this city and eat from it wherever you will and say, 'Relieve us of our burdens,' and enter the gate bowing humbly; We will [then] forgive you your sins. We will increase the doers of good [in goodness and reward]." <> Kuma a lõkacin da aka ce masu: "Ku zauna ga wannan alƙarya, kuma ku ci daga gare ta, inda kuka so, kuma ku ce: 'Saryarwa,' kuma ku shiga kõfa kuna mãsu sujada; Mu gãfarta muku laifuffukanku, kuma zã Mu ɗãra wa mãsu kyautatãwa." = --Qur'an 7:161
    But those who wronged among them changed [the words] to a statement other than that which had been said to them. So We sent upon them a punishment from the sky for the wrong that they were doing. <> Sai waɗanda suka yi zãlunci daga gare su, suka musanya magana watar wadda aka ce musu, sai Muka aika azãba a kansu, daga sama, sabõda abin da suka kasance sunã yi na zãlunci. = --Qur'an 7:162
    And ask them about the town that was by the sea - when they transgressed in [the matter of] the sabbath - when their fish came to them openly on their sabbath day, and the day they had no sabbath they did not come to them. Thus did We give them trial because they were defiantly disobedient. <> Kuma ka tambaye su daga alƙarya wadda ta kasance kusa ga tẽku, a lõkacin da suke ƙẽtare haddi a cikin Asabar, a lõkacin da kĩfãyensu, suke je musu a rãnar Asabar ɗinsu jẽre. Kuma a rãnar da ba su yi Asabar ba, bã su zuwa gare su; Kamar wancan ne Muke jarraba su da abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci. = --Qur'an 7:163
    And when a community among them said, "Why do you advise [or warn] a people whom Allah is [about] to destroy or to punish with a severe punishment?" they [the advisors] said, "To be absolved before your Lord and perhaps they may fear Him." <> Kuma a lõkacin da wata al'umma daga gare su ta ce: "Don me kuke yin wa'azi ga mutãne waɗanda Allah Yake Mai halaka su kõ kuwa Mai yi musu azãba, azãba mai tsanani?" Suka ce: "Dõmin nẽman hanzari zuwa ga Ubangijinku, kuma tsammãninsu, sunã yin taƙawa." = --Qur'an 7:164
    And when they forgot that by which they had been reminded, We saved those who had forbidden evil and seized those who wronged, with a wretched punishment, because they were defiantly disobeying. <> To, a lõkacin da suka manta da abin da aka tunãtar da su da shi, Mun tsĩrar da waɗanda suke hani daga cũta, kuma Muka kãma waɗanda suka yi zãlunci, da azãba mai tsanani dõmin abin da suka kasance sunã yi, na fasiƙanci. = --Qur'an 7:165
    So when they were insolent about that which they had been forbidden, We said to them, "Be apes, despised." <> Sa'an nan a lõkacin da suka yi girman kai daga barin abin da aka hana su daga gare shi, Muka ce musu: "Ku kasance birai ƙasƙantattu." = --Qur'an 7:166
    And [mention] when your Lord declared that He would surely [continue to] send upon them until the Day of Resurrection those who would afflict them with the worst torment. Indeed, your Lord is swift in penalty; but indeed, He is Forgiving and Merciful. <> Kuma a lõkacin da Ubangijinku Ya sanar, lalle ne, zã Ya aika a kansu (Yahũd), zuwa, Rãnar¡iyãma, wanda zai ɗanɗana musu mummunar azãba, lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Mai gaggawar uƙũba ne, kuma shĩ haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 7:167
    And We divided them throughout the earth into nations. Of them some were righteous, and of them some were otherwise. And We tested them with good [times] and bad that perhaps they would return [to obedience]. <> Kuma Muka yayyanka su, a cikin ƙasa, al'ummõmi, daga gare su akwai sãlihai, kuma daga gare su akwai wanda bã haka ba. Muka jarrabe su da abũbuwan alhẽri da na musĩfa; Tsammãninsu, sunã kõmõwa. = --Qur'an 7:168
    And there followed them successors who inherited the Scripture [while] taking the commodities of this lower life and saying, "It will be forgiven for us." And if an offer like it comes to them, they will [again] take it. Was not the covenant of the Scripture taken from them that they would not say about Allah except the truth, and they studied what was in it? And the home of the Hereafter is better for those who fear Allah, so will you not use reason? <> Sai wasu' yan bãya suka maye daga bãyansu, sun gaji Littãfin, sunã karɓar sifar wannan ƙasƙantacciya, sunã cẽwa: "Zã a gãfarta mana. "Iadan kuma wata sifa irinta ta zo, za su karɓe ta. Shin, ba a karɓi alkawarin Littãfi ba a kansu cẽwa kada su faɗa ga Allah, fãce gaskiya, alhãli kuwa sun karanta abin da yake a cikinsa, kuma Gidan Lãhira ne mafi alhẽriga wanda ya yi taƙawa? Shin, bã zã ku hankalta ba? = --Qur'an 7:169
    But those who hold fast to the Book and establish prayer - indeed, We will not allow to be lost the reward of the reformers. <> Kuma waɗanda suke riƙẽwa da laittãfi kuma suka tsayar da salla, lalle ne Mũ, bã Mu tõzarta lãdar mãsu gyãrãwa. = --Qur'an 7:170
    And [mention] when We raised the mountain above them as if it was a dark cloud and they were certain that it would fall upon them, [and Allah said], "Take what We have given you with determination and remember what is in it that you might fear Allah." <> Kuma a lõkacin da muka ɗaukaka dũtse sama da su, kumar dai shi girgije ne, kuma suka haƙƙaƙe, lalle ne shĩ, mai fãɗuwa ne a gare su, (aka ce): "Ku karɓi abin da Muka kãwo muku da ƙarfi, kuma ku tuna abin da yake a cikinsa, tsammãninku kunã yin taƙawa." = --Qur'an 7:171
    And [mention] when your Lord took from the children of Adam - from their loins - their descendants and made them testify of themselves, [saying to them], "Am I not your Lord?" They said, "Yes, we have testified." [This] - lest you should say on the day of Resurrection, "Indeed, we were of this unaware." <> Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya karɓi (alkawari) daga ɗiyan Ãdam, daga bãyayyakinsu, a zuriyarsu, kuma Ya shaidar da su a kan rãyukansu, (Ya ce): "Shin, bã Nĩ ne Ubangijinku ba?" Suka ce: "Na'am! Mun yi shaida!" (ya ce): "Kada ku ce a Rãnar Kiyãma: Lalle ne mũ, daga wannan, gafalallu ne." = --Qur'an 7:172
    Or [lest] you say, "It was only that our fathers associated [others in worship] with Allah before, and we were but descendants after them. Then would You destroy us for what the falsifiers have done?" <> Kõ kuwa ku ce: "Abin sani kawai, ubanninmu suka yi shirki daga farko, kuma mũ, mun kasance zũriya daga bãyansu. Shin fa, Kanã halaka mu, sabõda abin da mãsu ɓãtãwa suka aikata?" = --Qur'an 7:173
    And thus do We [explain in] detail the verses, and perhaps they will return. <> Kuma kamar haka Muke rarrabe ãyõyi, daki-daki; tsammãninsu, sunã kõmõwa. = --Qur'an 7:174
    And recite to them, [O Muhammad], the news of him to whom we gave [knowledge of] Our signs, but he detached himself from them; so Satan pursued him, and he became of the deviators. <> Ka karanta a kansu lãbãrin wanda Muka kãwo masa ãyõyinMu, sai ya sãɓule daga gare su, sai shaidan ya bi shi, sai ya kasance a cikin halakakku. = --Qur'an 7:175
    And if We had willed, we could have elevated him thereby, but he adhered [instead] to the earth and followed his own desire. So his example is like that of the dog: if you chase him, he pants, or if you leave him, he [still] pants. That is the example of the people who denied Our signs. So relate the stories that perhaps they will give thought. <> Kuma dã Mun so, da Mun ɗaukakã shi da su, kuma amma shĩ, ya nẽmi dawwama a cikin ƙasa, kuma ya bi son zũciyarsa. To, misãlinsa kamar misãlin kare ne, idan ka yi ɗauki a kansa ya yi lallage, kõ kuwa ka bar shi sai ya yi lallage, wannan ne misãlin mutãne waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu: Ka jẽranta karãtun lãbãrun; tsammãninsu sunã tunãni. = --Qur'an 7:176
    How evil an example [is that of] the people who denied Our signs and used to wrong themselves. <> Tir da zama misãli, mutãnen da suka ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma kansu suka kasance sunã zãlunta. = --Qur'an 7:177
    Whoever Allah guides - he is the [rightly] guided; and whoever He sends astray - it is those who are the losers. <> Wanda Allah Ya shiryar, to, shĩ ne Mai shiryuwa, kuma wanda Ya ɓatar, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra. = --Qur'an 7:178
    And We have certainly created for Hell many of the jinn and mankind. They have hearts with which they do not understand, they have eyes with which they do not see, and they have ears with which they do not hear. Those are like livestock; rather, they are more astray. It is they who are the heedless. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sabõda Jahannama, mãsu yawa daga aljannu da mutãne, sunã da zukãta, ba su fahimta da su, kuma sunã da idãnu, bã su gani da su, kuma sunã da kunnuwa, ba su ji da su; waɗancan kamar bisãshe suke. Ã'a, sũ ne mafi ɓacẽwa; Waɗancan sũ ne gafalallu. = --Qur'an 7:179
    And to Allah belong the best names, so invoke Him by them. And leave [the company of] those who practice deviation concerning His names. They will be recompensed for what they have been doing. <> Kuma Allah Yanã da sũnãye mãsu kyau. Sai ku rõƙe shi da su, kuma ku bar waɗanda suke yin ilhãdi a cikin sũnãyenSa: zã a sãka musu abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 7:180
    And among those We created is a community which guides by truth and thereby establishes justice. <> Kuma daga waɗanda Muka halitta akwai wata al'umma, sunã shiryarwa da gaskiya, kuma, da ita suke yin ãdalci. = --Qur'an 7:181
    But those who deny Our signs - We will progressively lead them [to destruction] from where they do not know. <> Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba. = --Qur'an 7:182
    And I will give them time. Indeed, my plan is firm. <> Kuma Inã yi musu jinkiri, lalle ne kaidĩNa, mai ƙarfi ne. = --Qur'an 7:183
    Then do they not give thought? There is in their companion [Muhammad] no madness. He is not but a clear warner. <> Shin, ba su yi tunĩni ba, cẽwa bãbu wata hauka ga ma'abucinsu? shĩ bai zama ba fãce mai gargaɗi mai bayyanãwa. = --Qur'an 7:184
    Do they not look into the realm of the heavens and the earth and everything that Allah has created and [think] that perhaps their appointed time has come near? So in what statement hereafter will they believe? <> Shin, ba su yi dũbi ba a cikin mulkin sammai da ƙasa, da kuma abin da Allah Ya halitta daga kõme, kuma akwai tsammãni kasancewar ajalinsu, haƙĩƙa, ya kusanta? To, da wane lãbãri a bãyansa suke yin ĩmãni? = --Qur'an 7:185
    Whoever Allah sends astray - there is no guide for him. And He leaves them in their transgression, wandering blindly. <> Wanda Allah Ya ɓatar to bãbu mai shiryarwa a gare shi: kuma Yanã barin su, a cikin ɓatarsu sunã ɗimuwa. = --Qur'an 7:186
    They ask you, [O Muhammad], about the Hour: when is its arrival? Say, "Its knowledge is only with my Lord. None will reveal its time except Him. It lays heavily upon the heavens and the earth. It will not come upon you except unexpectedly." They ask you as if you are familiar with it. Say, "Its knowledge is only with Allah, but most of the people do not know." <> Sunã tambayar ka daga Sa'a, a yaushe tabbatarta take? Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Ubangijina yake. Bãbu mai bayyana ta ga lõkacinta fãce shĩ Tã yi nauyi a cikin sammai da ƙasa. Bã zã ta zo muku ba fãce kwatsam." sunã tambayar ka, kamar kai masani ne gare ta. Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawan mutãne bã su sani." = --Qur'an 7:187
    Say, "I hold not for myself [the power of] benefit or harm, except what Allah has willed. And if I knew the unseen, I could have acquired much wealth, and no harm would have touched me. I am not except a warner and a bringer of good tidings to a people who believe." <> Ka ce: "Bã ni mallaka wa raina wani amfãni, kuma haka ban tunkuɗe wata cũta, fãceabin da Allah Ya so. Kuma dã na kasance inã sanin gaibi, dã lalle ne, nã yawaita daga alhẽri kuma cũta bã zã ta shãfe ni ba, nĩ ban zama ba fĩce mai gargaɗi, kumamai bãyar da bishãra ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni." = --Qur'an 7:188
    It is He who created you from one soul and created from it its mate that he might dwell in security with her. And when he covers her, she carries a light burden and continues therein. And when it becomes heavy, they both invoke Allah, their Lord, "If You should give us a good [child], we will surely be among the grateful." <> Shĩ ne wanda Ya halitta ku daga rai guda, kumaYa sanya, daga gare ta, ma'auranta, dõmin ya natsu zuwa gare ta. Sa'an nan a lõkacin da ya rufe ta, ta yi ciki, ciki sassauƙa, sai ta shũɗe dashi. Sa'an nan a lõkacin da ya yi nauyi, sai suka rõƙi Allah, Ubangijinsu: "Lalle ne idan Ka bã mu abin ƙwarai, haƙĩƙa, zã mu kasance dagamãsu gõdiya." = --Qur'an 7:189
    But when He gives them a good [child], they ascribe partners to Him concerning that which He has given them. Exalted is Allah above what they associate with Him. <> To, a lõkacin da Ya bã su abin ƙwarai, suka sanya Masa abõkan tarayya a cikin abin da Ya ba su. To, Allah Yã tsarkaka daga abin da suke yi na shirki. = --Qur'an 7:190
    Do they associate with Him those who create nothing and they are [themselves] created? <> Shin, sunã shirki da abin da bã ya halittar kõme, kuma sũne ake halittãwa? = --Qur'an 7:191
    And the false deities are unable to [give] them help, nor can they help themselves. <> Kuma ba su iya bãyar da taimako gare su, kuma kansu ma, bã su iya taimaka! = --Qur'an 7:192
    And if you [believers] invite them to guidance, they will not follow you. It is all the same for you whether you invite them or you are silent. <> Kuma idan kun kirãye su zuwa ga shiriya, bã zã su bĩ ku ba, daidai ne a gare ku, shin, kun kirãye su, kõ kuwa kũ mãsu kawaici ne! = --Qur'an 7:193
    Indeed, those you [polytheists] call upon besides Allah are servants like you. So call upon them and let them respond to you, if you should be truthful. <> Lalle ne waɗannan da kuke kira, baicin Allah, bãyĩ ne misãlanku: to, ku kirãye su, sa'an nan su karɓa muku, idan kun kasance mãsu gaskiya! = --Qur'an 7:194
    Do they have feet by which they walk? Or do they have hands by which they strike? Or do they have eyes by which they see? Or do they have ears by which they hear? Say, [O Muhammad], "Call your 'partners' and then conspire against me and give me no respite. <> Shin sunã da ƙafãfu da suke yin tafia da su? Kõ sunã da hannãye da suke damƙa da su? Kõ sunã da idãnu da suke gani da su? Ko sunã da kunnuwa da suke saurãre da su? Ka ce: "Ku kirãwo abũbuwan shirkinku sa'an nan kuma ku yi mini kaidi, sa'an nan kada ku saurãra mini." = --Qur'an 7:195
    Indeed, my protector is Allah, who has sent down the Book; and He is an ally to the righteous. <> "Lalle ne, Majiɓincĩna Allah ne Wanda Ya saukar da Littãfi kuma Shĩ ne Yake jiɓintar sãlihai," = --Qur'an 7:196
    And those you call upon besides Him are unable to help you, nor can they help themselves." <> "Kuma waɗanda kuke kira, baicinSa, bã su iya taimakõn ku, kuma kansu ma, bã su iya taimaka." = --Qur'an 7:197
    And if you invite them to guidance, they do not hear; and you see them looking at you while they do not see. <> Kuma idan ka kirãye su zuwa ga shiriya, bã zã su ji ba, kuma kanã ganin su, sunã dũbi zuwa gare ka, alhãli kuwa sũ, bã su gani. = --Qur'an 7:198
    Take what is given freely, enjoin what is good, and turn away from the ignorant. <> Ka riƙi abin da ya sauƙaƙa; Kuma ka yi umurni da alhẽri, Kuma ka kau da kai daga jãhilai. = --Qur'an 7:199
    And if an evil suggestion comes to you from Satan, then seek refuge in Allah. Indeed, He is Hearing and Knowing. <> Kuma imma wata fizga daga Shaiɗan ta fizge ka, sai ka nẽmi tsari ga Allah. Lalle ne shi, Mai jĩ ne, Masani. = --Qur'an 7:200
    Indeed, those who fear Allah - when an impulse touches them from Satan, they remember [Him] and at once they have insight. <> Lalle ne waɗanda suka yi taƙawa idan wani tãshin hankali daga Shaiɗan ya shãfe su, sai su tuna (Allah) sai gã su, sun zama masu basĩra. = --Qur'an 7:201
    But their brothers - the devils increase them in error; then they do not stop short. <> Kuma 'yan'uwan su (shaiɗanu) sunã taimakon su a cikin ɓata, sa'an nan kuma bã su taƙaitãwa. = --Qur'an 7:202
    And when you, [O Muhammad], do not bring them a sign, they say, "Why have you not contrived it?" Say, "I only follow what is revealed to me from my Lord. This [Qur'an] is enlightenment from your Lord and guidance and mercy for a people who believe." <> Kuma idan ba ka je musu da wata ãyã ba, su ce: "Don me ba ka ƙãga ta ba?" Ka ce: "Abin sani kawai, inã biyar abin da aka yõ wahayi zuwa gare ni ne, daga Ubangjina. Wannan abũbuwan kula ne daga Ubangijinku, da shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin imãni." = --Qur'an 7:203
    So when the Qur'an is recited, then listen to it and pay attention that you may receive mercy. <> Kuma idan an karanta Alƙur'ãni sai ku saurara gare shi, kuma ku yi shiru; Tsammãninku, anã yi muku rahama. = --Qur'an 7:204
    And remember your Lord within yourself in humility and in fear without being apparent in speech - in the mornings and the evenings. And do not be among the heedless. <> Kuma ka ambaci Ubangijinka, a cikin ranka da ƙanƙan da kai, da tsõro, kuma kõmabãyan bayyanawa na magana, da sãfe da marece, kuma kada ka kasance daga gafalallu. = --Qur'an 7:205
    Indeed, those who are near your Lord are not prevented by arrogance from His worship, and they exalt Him, and to Him they prostrate. <> Lalle ne, waɗanda ke wurin Ubangijinka bã su yin girman kai ga bauta Masa, kuma sunã tsarake shi da tasbĩhi, kuma a gare shi suke yin sujada. = --Qur'an 7:206
    They ask you, [O Muhammad], about the bounties [of war]. Say, "The [decision concerning] bounties is for Allah and the Messenger." So fear Allah and amend that which is between you and obey Allah and His Messenger, if you should be believers. <> Suna tambayar ka ga ganĩma. ka ce: "Ganĩma ta Allah daManzonSa ce. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku gyãra abin da yake a tsakãninku, kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, idan kun kasance mũminai." = --Qur'an 8:1
    The believers are only those who, when Allah is mentioned, their hearts become fearful, and when His verses are recited to them, it increases them in faith; and upon their Lord they rely - <> Abin sani kawai, nũminai sũ ne waɗanda suke idan an ambaci, Allah, zukãtansu su firgita, kuma idan an karanta ãyõyinSa a kansu, su ƙãrã musu wani ĩmãni, kuma ga Ubangijinsu suke dõgara. = --Qur'an 8:2
    The ones who establish prayer, and from what We have provided them, they spend. <> Waɗanda suke tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azũrtã su sunã ciyarwa. = --Qur'an 8:3
    Those are the believers, truly. For them are degrees [of high position] with their Lord and forgiveness and noble provision. <> Waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya. Sunã da darajõji a wurin Ubangijinsu, da wata gãfara da arziki na karimci. = --Qur'an 8:4
    [It is] just as when your Lord brought you out of your home [for the battle of Badr] in truth, while indeed, a party among the believers were unwilling, <> Kamar yadda Ubangijinka Ya fitar da kai daga gidanka da gaskiya, alhãli kuwa lalle wani ɓangare na mũminai, haƙĩƙa, sunã ƙyãma. = --Qur'an 8:5
    Arguing with you concerning the truth after it had become clear, as if they were being driven toward death while they were looking on. <> Sunã jãyayya da kai a cikin (sha'anin) gaskiya a bãyan tã bayYanã, kamar dai lalle anã kõra su zuwa ga mutuwa ne alhãli kuwa sunã kallo. = --Qur'an 8:6
    [Remember, O believers], when Allah promised you one of the two groups - that it would be yours - and you wished that the unarmed one would be yours. But Allah intended to establish the truth by His words and to eliminate the disbelievers <> Kuma a lõkacin da Allah Yake yi muku alkawari da ɗayan ƙungiya biyu, cẽwa lalle ita tãku ce: kuma kunã gũrin cẽwa lalle ƙungiya wadda bã ta da ƙaya ta kasance gare ku, kuma Allah Yanã nufin Ya tabbatar da gaskiya da kalmõminSa, kuma Ya kãtse ƙarshen kãfirai; = --Qur'an 8:7
    That He should establish the truth and abolish falsehood, even if the criminals disliked it. <> Dõmin Ya tabbatar da gaskiya, kuma Ya ɓãta ƙarya, kuma kõdã mãsu laifi sun ƙi. = --Qur'an 8:8
    [Remember] when you asked help of your Lord, and He answered you, "Indeed, I will reinforce you with a thousand from the angels, following one another." <> A lõkacin da kuke nẽman Ubangijinku tairnako, sai Ya karɓa muku cẽwa: "Lalle ne Nĩ, Mai taimakon ku ne da dubu daga malã'iku, jẽre." = --Qur'an 8:9
    And Allah made it not but good tidings and so that your hearts would be assured thereby. And victory is not but from Allah. Indeed, Allah is Exalted in Might and Wise. <> Kuma Allah bai sanya shi ba fãce Dõmin bishãra, kuma dõmin zukãtanku su natsu da shi, kuma taimakon, bai zama ba fãce daga wurin Allah; Lalle ne Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima. = --Qur'an 8:10
    [Remember] when He overwhelmed you with drowsiness [giving] security from Him and sent down upon you from the sky, rain by which to purify you and remove from you the evil [suggestions] of Satan and to make steadfast your hearts and plant firmly thereby your feet. <> A lõkacin da (Allah) Yake rufe ku da gyangyaɗi, ɗõmin aminci daga gare Shi, kuma Yanã saukar da ruwa daga sama, a kanku, dõmin Ya tsarkake ku da shi, kuma Ya tafiyar da ƙazantar Shaiɗan daga barinku, kuma dõmin Ya ɗaure a kan zukãtanku, kuma Ya tabbatar da ƙafãfu da shi. = --Qur'an 8:11
    [Remember] when your Lord inspired to the angels, "I am with you, so strengthen those who have believed. I will cast terror into the hearts of those who disbelieved, so strike [them] upon the necks and strike from them every fingertip." <> A lõkacin da Ubangijinka Yake yin wahayi zuwa ga Malã'iku cẽwa: "Lalle ne Ni, Inã tãre da ku, sai ku tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni: Zã Ni jẽfa tsõro a cikin zukãtan waɗanda suka kãfirta, sai ku yi dũka bisa ga wuyõyi kuma ku yi dũka daga gare su ga dukkan yãtsu. = --Qur'an 8:12
    That is because they opposed Allah and His Messenger. And whoever opposes Allah and His Messenger - indeed, Allah is severe in penalty. <> Wancan ne, dõmin lalle ne sũ, sunã sãɓa wa Allah da ManzonSa. Kuma wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, to, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne. = --Qur'an 8:13
    "That [is yours], so taste it." And indeed for the disbelievers is the punishment of the Fire. <> Wancan ne: "Ku ɗanɗane shi, kuma lalle ne akwai azãbar wuta ga kãfirai." = --Qur'an 8:14
    O you who have believed, when you meet those who disbelieve advancing [for battle], do not turn to them your backs [in flight]. <> Yã kũ wacɗanda suka yiĩmãni! Idan kun haɗu da waɗanda suka kãfirta ga yãƙi, to, kada ku jũya musu bãyayyakinku. = --Qur'an 8:15
    And whoever turns his back to them on such a day, unless swerving [as a strategy] for war or joining [another] company, has certainly returned with anger [upon him] from Allah, and his refuge is Hell - and wretched is the destination. <> Kuma duka wanda ya jũya musu bãyansa a yinin nan, fãce wanda ya karkata dõmin kõɗayya, kõ kuwa wanda ya jẽ dõmin haɗuwa da wata ƙungiya, to, lalle ne ya kõma da fushi daga Allah, kuma matattararsa Jahannama, kuma tir da makõma ita! = --Qur'an 8:16
    And you did not kill them, but it was Allah who killed them. And you threw not, [O Muhammad], when you threw, but it was Allah who threw that He might test the believers with a good test. Indeed, Allah is Hearing and Knowing. <> To, bã kũ ne kuka kashe su ba; kuma amma Allah ne Ya kashe su: kuma ba ka yi jĩfa ba a lõkacin da ka yi jĩfa; kuma amma Allah ne Ya yi jĩfar. Kuma dõminYa jarraba Musulmi da jarrabãwa mai kyau daga gare shi. Kuma Allah Mai ji ne, Masani. = --Qur'an 8:17
    That [is so], and [also] that Allah will weaken the plot of the disbelievers. <> Wancan ne, kuma lalle ne, Allah Mai raunana kaidin kãfirai ne. = --Qur'an 8:18
    If you [disbelievers] seek the victory - the defeat has come to you. And if you desist [from hostilities], it is best for you; but if you return [to war], We will return, and never will you be availed by your [large] company at all, even if it should increase; and [that is] because Allah is with the believers. <> Idan kun yi alfãnun cin nasara to lalle nasarar tã je muku, kuma idan kun hanu, to Shi ne Mafi alhẽri a gare ku, kuma idan kun kõma zã Mu kõma, kuma jama'arku bã zã ta wadãtar muku da kõme ba, kõ dã tã yi yawa. Kuma lalle ne cẽwa Allah Yanã tãre da mũminai! = --Qur'an 8:19
    O you who have believed, obey Allah and His Messenger and do not turn from him while you hear [his order]. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, kuma kada ku jũya daga barinSa, alhãli kunã ji. = --Qur'an 8:20
    And do not be like those who say, "We have heard," while they do not hear. <> Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka ce: "Mun ji, alhãli kuwa sũ bã su ji." = --Qur'an 8:21
    Indeed, the worst of living creatures in the sight of Allah are the deaf and dumb who do not use reason. <> Lalle ne, mafi sharrin dabbõbi a wurin Allah, sũ ne kurãme, bẽbãye, waɗanda bã, su yin hankali. = --Qur'an 8:22
    Had Allah known any good in them, He would have made them hear. And if He had made them hear, they would [still] have turned away, while they were refusing. <> Dã Allah Yã san wani alhẽri a cikinsu, dã Yã jiyar da su, kuma kõ da Yãjiyar da su, haƙĩƙa, dã sun jũya, alhãli sũ, sunã mãsu hinjirẽwa. = --Qur'an 8:23
    O you who have believed, respond to Allah and to the Messenger when he calls you to that which gives you life. And know that Allah intervenes between a man and his heart and that to Him you will be gathered. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku karɓa wa Allah, kuma ku karɓa wa Manzo, idan Ya kirãye ku zuwa ga abin da Yake rãyar da ku; Kuma ku sani cẽwa Allah Yanã shãmakacẽwa a tsakãnin mutum da zũciyarsa, kuma lalle ne Shĩ, a zuwa gare Shi ake tãra ku. = --Qur'an 8:24
    And fear a trial which will not strike those who have wronged among you exclusively, and know that Allah is severe in penalty. <> Kuma ku ji tsõron fitina wadda bã ta sãmun waɗanda suka yi zãlunci daga gare ku kẽɓe, kuma ku sani, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne. = --Qur'an 8:25
    And remember when you were few and oppressed in the land, fearing that people might abduct you, but He sheltered you, supported you with His victory, and provided you with good things - that you might be grateful. <> Ku tuna a lõkacin da kuke kaɗan, waɗanda ake raunanarwã a cikin ƙasa kunã tsõron mutãne su cafe ku, sai Ya tattara ku (a wurin natsuwa, Maɗina), kuma Ya ƙarfafã ku da taimakonSa kuma Ya azurtã ku daga abũbuwa mãsu dãɗi; Tsammãninku, kunã gõdẽwa. = --Qur'an 8:26
    O you who have believed, do not betray Allah and the Messenger or betray your trusts while you know [the consequence]. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku yaudari Allah da ManzonSa, kuma ku yaudari amãnõninku, alhãli kuwa kunã sane. = --Qur'an 8:27
    And know that your properties and your children are but a trial and that Allah has with Him a great reward. <> Kuma ku sani cẽwa abin sani kawai, dũkiyõyinku da 'ya'yanku, wata fitina ce, kuma lalle ne Allah, a wurinSa, akwai ijãra mai girma. = --Qur'an 8:28
    O you who have believed, if you fear Allah, He will grant you a criterion and will remove from you your misdeeds and forgive you. And Allah is the possessor of great bounty. <> Ya kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun bi Allah da taƙawa, zai sanyã muku mararraba (da tsõro) kuma Ya kankare ƙanãnan zunubanku daga barinku. Kuma Ya gãfartã muku. Kuma Allah ne Ma'abũcin falalã Mai girma. = --Qur'an 8:29
    And [remember, O Muhammad], when those who disbelieved plotted against you to restrain you or kill you or evict you [from Makkah]. But they plan, and Allah plans. And Allah is the best of planners. <> Kuma a lõkacin da waɗanda suka kãfirta sukẽ yin mãkirci game da kai, dõmin su tabbatar da kai, kõ kuwa su kashe ka, kõ kuwa su fitar da kai, sunã mãkirci kuma Allah Yanã mayar musa da mãkirci kuma Allah ne Mafificin mãsu mãkirci. = --Qur'an 8:30
    And when Our verses are recited to them, they say, "We have heard. If we willed, we could say [something] like this. This is not but legends of the former peoples." <> Kuma idan aka karanta, ãyõyinMu a kansu, sukan ce: "Lalle ne mun ji dã muna so, haƙĩƙa, da mun faɗi irin wannan; wannan bai zama ba fãce tãtsunãyõyin mutãnen farko." = --Qur'an 8:31
    And [remember] when they said, "O Allah, if this should be the truth from You, then rain down upon us stones from the sky or bring us a painful punishment." <> A lõkacin da suka ce: "Yã Allah! Idan wannan ya kasancc shĩ ne gaskiya daga wurinKa, sai Ka yi ruwan duwãtsu, a kanmu, daga sama, kõ kuwa Kazõ mana da wata azãba, mai raɗaɗi." = --Qur'an 8:32
    But Allah would not punish them while you, [O Muhammad], are among them, and Allah would not punish them while they seek forgiveness. <> Kuma Allah bai kasance Yanã yi musu azãba ba alhãli kuwa kai kanã cikinsu, kuma Allah bai kasance Mai yi musu azãba ba alhãli kuwa sunã yin istigfãri. = --Qur'an 8:33
    But why should Allah not punish them while they obstruct [people] from al-Masjid al- Haram and they were not [fit to be] its guardians? Its [true] guardians are not but the righteous, but most of them do not know. <> Kuma mẽne ne a gare su da Allah ba zai yi musu azãba ba, alhãli kuwa sũ, sunã kangẽwa daga Masallaci Mai alfarma kuma ba su kasance majiɓintanSa ba? Bãbu majiɓintanSa fãce mãsu taƙawa. Kuma mafi yawansu ba su sani ba. = --Qur'an 8:34
    And their prayer at the House was not except whistling and handclapping. So taste the punishment for what you disbelieved. <> Kuma sallarsu a wurin ¦ãkin ba ta kasance ba fãce shẽwa da yãyã; sai ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci. = --Qur'an 8:35
    Indeed, those who disbelieve spend their wealth to avert [people] from the way of Allah. So they will spend it; then it will be for them a [source of] regret; then they will be overcome. And those who have disbelieved - unto Hell they will be gathered. <> Lalle ne waɗanda suka kãfirta, sunã ciyar da dũkiyõyinsu, dõmin su kange daga hanyar Allah; to, zã a su ciyar da ita, sa' an nan kuma ta kasance nadãma a kansu, sa'an nan kuma a rinjãye su. Kuma waɗanda suka kãfirta zuwa ga Jahannama ake tãra su; = --Qur'an 8:36
    [This is] so that Allah may distinguish the wicked from the good and place the wicked some of them upon others and heap them all together and put them into Hell. It is those who are the losers. <> Dõmin Allah Ya rarrabe mummũna daga mai kyau, kuma Ya sanya mummũnan, sãshensa a kan sãshe, sa'an nan Ya shirga shi gabã daya, sa'an nan Ya sanyã shi a cikin Jahannama. Waɗannan sũ ne mãsu hasãra. = --Qur'an 8:37
    Say to those who have disbelieved [that] if they cease, what has previously occurred will be forgiven for them. But if they return [to hostility] - then the precedent of the former [rebellious] peoples has already taken place. <> Ka ce wa waɗanda suka kãfirta, idan sun hanu, zã a gãfarta musu abin da ya riga ya shige, kuma idan sun kõma, to, hanyar kãfiran farko, haƙĩƙa, ta shũɗe. = --Qur'an 8:38
    And fight them until there is no fitnah and [until] the religion, all of it, is for Allah. And if they cease - then indeed, Allah is Seeing of what they do. <> Kuma ku yãƙe su har wata fitina bã zã ta kasance ba, kuma addini dukansa ya kasance na Allah. To, idan sun hanu to lalle ne, Allah ia abin da kuke aikatãwa Mai gani ne. = --Qur'an 8:39
    But if they turn away - then know that Allah is your protector. Excellent is the protector, and Excellent is the helper. <> Kuma idan sun jũya, to, ku sani cẽwa lalle Allah ne Majiɓincinku: Mãdalla da Majiɓinci, kuma mãdalla da Mai taimako, Shĩ. = --Qur'an 8:40
    And know that anything you obtain of war booty - then indeed, for Allah is one fifth of it and for the Messenger and for [his] near relatives and the orphans, the needy, and the [stranded] traveler, if you have believed in Allah and in that which We sent down to Our Servant on the day of criterion - the day when the two armies met. And Allah, over all things, is competent. <> Kuma ka sani, abin sani kawai, abin da kuka sãmi ganĩma daga wani abu, to, lalle ne Allah Yanã da humusinsa kuma da Manzo, kuma da mãsu zumunta, da marãyu da miskĩnai da ɗan hanya, idan kun kasance kun yi ĩmãni da Allah da abin da Muka saukar a kan bãwanMu a Rãnar Rarrabẽwa, a Rãnar da jama'a biyu suka haɗu, kuma Allah ne, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi. = --Qur'an 8:41
    [Remember] when you were on the near side of the valley, and they were on the farther side, and the caravan was lower [in position] than you. If you had made an appointment [to meet], you would have missed the appointment. But [it was] so that Allah might accomplish a matter already destined - that those who perished [through disbelief] would perish upon evidence and those who lived [in faith] would live upon evidence; and indeed, Allah is Hearing and Knowing. <> A lõkacin da kuke a gãɓa ta kusa sũ kuma sunã a gãɓa tanẽsa, kuma ãyarin yana a wuri mafi gangarãwa daga gare ku, kuma dã kun yi wa jũna wa'adi, dã kun sãɓa ga wa'adin; kuma amma dõmin Allah Ya hukunta abin da yake ya kasance abin aikatãwa. Dõmin wanda yake halaka ya halaka daga shaida, kuma mai rãyuwa ya rãyu daga shaida, kuma lalle Allah ne, haƙĩƙa, Mai ji Masani. = --Qur'an 8:42
    [Remember, O Muhammad], when Allah showed them to you in your dream as few; and if He had shown them to you as many, you [believers] would have lost courage and would have disputed in the matter [of whether to fight], but Allah saved [you from that]. Indeed, He is Knowing of that within the breasts. <> A lõkacin da Allah Yake nũna maka sũ sunã kaɗan, a cikin barcinka, kuma dã Ya nũna maka su sunã da, yawa, lalle ne dã kun ji tsõro, kuma lalle ne dã kun yi jãyayya a cikin al'amarin, kuma amma Allah Yã tsare ku: Lalle Shĩ ne Masani ga abin da yake a cikin ƙirãza. = --Qur'an 8:43
    And [remember] when He showed them to you, when you met, as few in your eyes, and He made you [appear] as few in their eyes so that Allah might accomplish a matter already destined. And to Allah are [all] matters returned. <> Kuma a lõkacin da Yake nũna muku su, a lõkacin da kuka haɗu, a cikin idanunku sunã kaɗan, kuma Ya ƙarantar da ku a cikin idanunsu dõmin Allah Ya hukunta wani al'amari wanda ya kasance abin aikatãwa. Kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'umurra. = --Qur'an 8:44
    O you who have believed, when you encounter a company [from the enemy forces], stand firm and remember Allah much that you may be successful. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun haɗu da wata ƙungiyar yãƙi, to, ku tabbata, kuma ku ambaci Allah da yawa, tsammãninku kunã cin nasara. = --Qur'an 8:45
    And obey Allah and His Messenger, and do not dispute and [thus] lose courage and [then] your strength would depart; and be patient. Indeed, Allah is with the patient. <> Kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, kuma kada ku yi jãyayya har ku raunana kuma iskarku ta tafi, kuma ku yi haƙuri. Lalle ne Allah Yanã tãre da mãsu haƙuri. = --Qur'an 8:46
    And do not be like those who came forth from their homes insolently and to be seen by people and avert [them] from the way of Allah. And Allah is encompassing of what they do. <> Kada ku kasance kamar waɗanda suka fita daga gidãjensu, sunã mãsu alfahari da yin riya ga mutãne, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma Allah ne ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa. = --Qur'an 8:47
    And [remember] when Satan made their deeds pleasing to them and said, "No one can overcome you today from among the people, and indeed, I am your protector." But when the two armies sighted each other, he turned on his heels and said, "Indeed, I am disassociated from you. Indeed, I see what you do not see; indeed I fear Allah. And Allah is severe in penalty." <> Kuma a lõkacin da Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, kuma ya ce: "Bãbu marinjayi a gareku a yau daga mutãne, kuma nĩ maƙwabci ne gare ku." To, a lõkacin da ƙungiya biyu suka haɗu, ya kõma a kan digãdigansa, kuma ya ce: "Lalle ne nĩ barrantacce ne daga gare ku! Nĩ inã ganin abin da bã ku gani; ni inã tsõron Allah: Kuma Allah Mai tsananin uƙũba ne." = --Qur'an 8:48
    [Remember] when the hypocrites and those in whose hearts was disease said, "Their religion has deluded those [Muslims]." But whoever relies upon Allah - then indeed, Allah is Exalted in Might and Wise. <> A lõkacin da munãfukai da waɗanda suke akwai cũtã a cikin zukãtansu, suke cẽwa: "Addĩnin waɗannan yã rũɗe su" Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, lalle ne Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima. = --Qur'an 8:49
    And if you could but see when the angels take the souls of those who disbelieved... They are striking their faces and their backs and [saying], "Taste the punishment of the Burning Fire. <> Kuma dã kã gani, a lõkacin da Malã'iku suke karɓar rãyukan waɗanda suka kãfirta, sunã dukar fuskõkinsu da ɗuwãwunsu, kuma suna cẽwa: "Ku ɗanɗani azãbar Gõbara." = --Qur'an 8:50
    That is for what your hands have put forth [of evil] and because Allah is not ever unjust to His servants." <> "Wancan sabõda abin da hannãyenku suka gabãtar ne. Kuma lalle ne, Allah bai zama Mai zãlunci ba ga, bãyinSa." = --Qur'an 8:51
    [Theirs is] like the custom of the people of Pharaoh and of those before them. They disbelieved in the signs of Allah, so Allah seized them for their sins. Indeed, Allah is Powerful and severe in penalty. <> "Kamar al'ãdar mutãnen Fir'auna da waɗanda suke gabãninsu, sun kãfirta da ãyõyin Allah, sai Allah Ya kãma su da zunubansu. Lalle Allah ne Mai ƙarfi, Mai tsananin uƙũba. = --Qur'an 8:52
    That is because Allah would not change a favor which He had bestowed upon a people until they change what is within themselves. And indeed, Allah is Hearing and Knowing. <> "Wancan ne, dõmin lalle ne, Allah bai kasance Mai canza wata ni'ima wadda ya ni'imtar da ita a kan wasu mutãne ba fãce sun sãke abin da yake ga rãyukansu, kuma dõmin lalle Allah ne Mai jĩ, Masani." = --Qur'an 8:53
    [Theirs is] like the custom of the people of Pharaoh and of those before them. They denied the signs of their Lord, so We destroyed them for their sins, and We drowned the people of Pharaoh. And all [of them] were wrongdoers. <> Kamar al'adar mutãnen Fir'auna da waɗanda suke a gabãninsu, sun ƙaryata game da ãyõyin Ubangijinsu, sai Muka halaka su, sabõda zunubansu, kuma Muka nutsar da mutãnen Fir'auna. Kuma dukansu sun kasance ne mãsu zãlunci. = --Qur'an 8:54
    Indeed, the worst of living creatures in the sight of Allah are those who have disbelieved, and they will not [ever] believe - <> Lalle mafi sharrin dabbõbi a wurin Allah, sũ ne waɗanda suka kãfirta, sa'an nan bã zã su yi ĩmãni ba. = --Qur'an 8:55
    The ones with whom you made a treaty but then they break their pledge every time, and they do not fear Allah. <> Waɗanda ka yi ƙullin alkawari da su, daga gare su, sa'an nan kuma sunã warwarewar alkawarinsu a kõwane lõkaci kuma sũ, bã su yin taƙawa. = --Qur'an 8:56
    So if you, [O Muhammad], gain dominance over them in war, disperse by [means of] them those behind them that perhaps they will be reminded. <> To, in dai ka kãma su a cikin yãƙi, sai ka kõre waɗanda suke a bãyansu, game da su, tsammãninsu, zã su dinga tunãwa. = --Qur'an 8:57
    If you [have reason to] fear from a people betrayal, throw [their treaty] back to them, [putting you] on equal terms. Indeed, Allah does not like traitors. <> Kuma in ka ji tsõron wata yaudara daga wasu mutãne, to, ka jẽfar da alkawarin, zuwa gare su, a kan daidaita: Lalle ne Allah, bã Ya son mayaudara. = --Qur'an 8:58
    And let not those who disbelieve think they will escape. Indeed, they will not cause failure [to Allah]. <> Kuma waɗanda suka kãfirta kada su yi zaton sun tsẽre: Lalle ne sũ, bã zã su gãgara ba. = --Qur'an 8:59
    And prepare against them whatever you are able of power and of steeds of war by which you may terrify the enemy of Allah and your enemy and others besides them whom you do not know [but] whom Allah knows. And whatever you spend in the cause of Allah will be fully repaid to you, and you will not be wronged. <> Kuma ku yi tattali, dõminsu, abin da kuka sãmi ĩkon yi na wani ƙarfi, kuma da ajiye dawaki, kunã tsoratarwa, game da shi, ga maƙiyin Allah kuma maƙiyinku da wasu, baicin su, ba ku san su ba, Allah ne Yake sanin su, kuma abin da kuka ciyar daga wani abu a cikin hanyar Allah, zã a cika muku sakamakonsa, kuma kũ ba a zãluntar ku. = --Qur'an 8:60
    And if they incline to peace, then incline to it [also] and rely upon Allah. Indeed, it is He who is the Hearing, the Knowing. <> Kuma idan sun karkata zuwa ga zaman lãfiya, to, ka karkata zuwa gare shi, kuma ka dõgara ga Allah: Lalle ne Shĩ, Mai ji ne Masani. = --Qur'an 8:61
    But if they intend to deceive you - then sufficient for you is Allah. It is He who supported you with His help and with the believers <> Kuma idan sun yi nufin su yaudare ka, to, lalle ma'ishinka Allah ne, Shĩ ne wanda Ya ƙarfafa ka da taimakonSa, kuma da mũminai. = --Qur'an 8:62
    And brought together their hearts. If you had spent all that is in the earth, you could not have brought their hearts together; but Allah brought them together. Indeed, He is Exalted in Might and Wise. <> Kuma Ya sanya sõyayya a tsakãnin zukãtansu. Dã kã ciyar da abin da yake cikin ƙasa, gabã ɗaya, dã ba ka sanya sõyayya a tsakãnin zukãtansu ba, kuma amma Allah Yã sanya sõyayya a tsakãninsu. Lalle Shi ne Mabuwãyi, Mai hikima. = --Qur'an 8:63
    O Prophet, sufficient for you is Allah and for whoever follows you of the believers. <> Ya kai Annabi! Ma'ishinka Allah ne, kai da wanda ya biye maka daga mũminai. = --Qur'an 8:64
    O Prophet, urge the believers to battle. If there are among you twenty [who are] steadfast, they will overcome two hundred. And if there are among you one hundred [who are] steadfast, they will overcome a thousand of those who have disbelieved because they are a people who do not understand. <> Ya kai Annabi! Ka kwaɗaitar da mũminai a kan yãƙi. Idan mutum ashirin mãsu haƙuri sun kasance daga gare ku, zã su rinjãyi mẽtan kuma idan ɗari suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi dubu daga waɗanda suka kãfirta, dõmin sũ, mutãne ne bã su fahimta. = --Qur'an 8:65
    Now, Allah has lightened [the hardship] for you, and He knows that among you is weakness. So if there are from you one hundred [who are] steadfast, they will overcome two hundred. And if there are among you a thousand, they will overcome two thousand by permission of Allah. And Allah is with the steadfast. <> A yanzu Allah Yã sauƙaƙe daga gare ku, kuma Yã sani cẽwa lalle ne akwai mãsu rauni a cikinku. To, idan mutum ɗari, mãsu haƙuri, suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi mẽtan, kuma idan dubu suka kasance daga gare ku, zã su rinjãyi dubu biyu, da iznin Allah. Kuma Allah Yanã tãre da mãsu haƙuri. = --Qur'an 8:66
    It is not for a prophet to have captives [of war] until he inflicts a massacre [upon Allah 's enemies] in the land. Some Muslims desire the commodities of this world, but Allah desires [for you] the Hereafter. And Allah is Exalted in Might and Wise. <> Bã ya kasancewa ga wani annabi, kãmammu su kasance a gare shi sai (bãyan) yã zubar da jinainai a cikin ƙasa. Kunã nufin sifar dũniya kuma Allah Yanãnufin Lãhira. Kuma Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima. = --Qur'an 8:67
    If not for a decree from Allah that preceded, you would have been touched for what you took by a great punishment. <> Bã dõmin wani Littãfi daga Allah ba, wanda ya gabãta, dã azãba mai girma daga Allah tã shãfe ku a cikin abin da kuka kãma. = --Qur'an 8:68
    So consume what you have taken of war booty [as being] lawful and good, and fear Allah. Indeed, Allah is Forgiving and Merciful. <> Sabõda haka, ku ci daga abin da kuka sãmu ganĩma, Yanã halal mai kyau. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai. = --Qur'an 8:69
    O Prophet, say to whoever is in your hands of the captives, "If Allah knows [any] good in your hearts, He will give you [something] better than what was taken from you, and He will forgive you; and Allah is Forgiving and Merciful." <> Ya kai Annabi! Ka ce wa wanda yake a cikin hannãyenku daga kãmammu: "Idan Allah Ya san akwai wani alhẽri a cikin zukãtanku, zai kawo muku mafi alhẽri daga abin da aka karɓa daga gare ku, kuma Ya yi muku gãfara. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai." = --Qur'an 8:70
    But if they intend to betray you - then they have already betrayed Allah before, and He empowered [you] over them. And Allah is Knowing and Wise. <> Kuma idan sun yi nufin yaudararka, to, haƙĩƙa, sun yaudari Allahdaga gabãni sai Ya bãyar da dãmã daga gare su: Kuma Allah ne Masani, Mai hikima. = --Qur'an 8:71
    Indeed, those who have believed and emigrated and fought with their wealth and lives in the cause of Allah and those who gave shelter and aided - they are allies of one another. But those who believed and did not emigrate - for you there is no guardianship of them until they emigrate. And if they seek help of you for the religion, then you must help, except against a people between yourselves and whom is a treaty. And Allah is Seeing of what you do. <> Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihãdi da dũkiyõyinsuda rãyukansu, a cikin hanyar Allah, da waɗanda suka bãyar da masauki, kuma suka yi taimako. Waɗancan, sãshensu waliyyai ne ga sãshe. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma ba su yi hijira ba, bã ku da wani abu daga waliccinsu, sai sun yi hijira. Kuma idan suka nẽme ku taimako a cikin addini, to taimako yã wajaba a kanku, fãce a kan mutãne waɗanda a tsakãninku da tsakãninsu akwai wani alkwari. Kuma Allah ne, ga abin da kuke aikatãwa, Mai gani. = --Qur'an 8:72
    And those who disbelieved are allies of one another. If you do not do so, there will be fitnah on earth and great corruption. <> Kuma waɗanda suka kãfirta sãshensu ne waliyyan sãshe, idan ba ku aikata shi ba, wata fitina zã ta kasance a cikin ƙasa, da fasãdi babba. = --Qur'an 8:73
    But those who have believed and emigrated and fought in the cause of Allah and those who gave shelter and aided - it is they who are the believers, truly. For them is forgiveness and noble provision. <> Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka yi hijira, kuma suka yi Jihãdi, a cikin hanyar Allah, kuma da waɗanda suka bãyar da masauki, kuma suka yi tamiako, waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya, sunãda gãfara da wani abinci na karimci. = --Qur'an 8:74
    And those who believed after [the initial emigration] and emigrated and fought with you - they are of you. But those of [blood] relationship are more entitled [to inheritance] in the decree of Allah. Indeed, Allah is Knowing of all things. <> Kuma waɗanda suka yi ĩmãni daga bãya, kuma suka yi hijira kuma suka yi jihãdi tãre da ku, to, waɗannan daga gare ku suke. Kuma ma'abũta zumunta, sãshensu ne waliyyan sãshe a cikin Littãfin Allah. Lalle Allah ne ga dukkan kõme Masani. = --Qur'an 8:75
    [This is a declaration of] disassociation, from Allah and His Messenger, to those with whom you had made a treaty among the polytheists. <> Barranta daga Allah da ManzonSa zuwa ga waɗanda kuka yi wa alkawari daga mãsu shirki = --Qur'an 9:1
    So travel freely, [O disbelievers], throughout the land [during] four months but know that you cannot cause failure to Allah and that Allah will disgrace the disbelievers. <> Sabõda haka ku yi tafiya a cikin ƙasa watã huɗu, kuma ku sani lalle kũ, bã mãsu buwãyar Allah ba ne, kuma lalle Allah ne Mai kunyatar da kãfirai. = --Qur'an 9:2
    And [it is] an announcement from Allah and His Messenger to the people on the day of the greater pilgrimage that Allah is disassociated from the disbelievers, and [so is] His Messenger. So if you repent, that is best for you; but if you turn away - then know that you will not cause failure to Allah. And give tidings to those who disbelieve of a painful punishment. <> Kuma da yẽkuwa daga Allah da ManzonSa zuwa ga mutãne, a Rãnar Haji Babba cẽwa lallene Allah Barrantacce ne daga mãsu shirki, kuma ManzonSa (haka). To, idan kun tũba to shi ne mafi alhẽri a gare ku, kuma idan kun jũya, to, ku sani lalle ne kũ, bã mãsu buwãyar Allah ba ne. Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka kãfirta, da azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 9:3
    Excepted are those with whom you made a treaty among the polytheists and then they have not been deficient toward you in anything or supported anyone against you; so complete for them their treaty until their term [has ended]. Indeed, Allah loves the righteous [who fear Him]. <> Sai waɗanda kuka yi wani alkawari daga mãsu shirki, sa'an nan kuma ba su rage ku da kõme ba, kuma ba su taimaki kõwa a kanku ba, to, ku cika alkawarin, zuwa gare su, har ga iyakar yarjẽjẽyarsu. Lalle ne Allah Yanã son mãsu taƙawa. = --Qur'an 9:4
    And when the sacred months have passed, then kill the polytheists wherever you find them and capture them and besiege them and sit in wait for them at every place of ambush. But if they should repent, establish prayer, and give zakah, let them [go] on their way. Indeed, Allah is Forgiving and Merciful. <> Kuma idan watanni, mãsu alfarma suka shige, to, ku yãki mushirikai inda kuka sãmẽ su, kuma ku kãmã su, kuma ku tsare su, kuma ku zaune musu dukkan madãkata. To, idan sun tũba, kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka to ku sakar musu da hanyarsu. Lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai. = --Qur'an 9:5
    And if any one of the polytheists seeks your protection, then grant him protection so that he may hear the words of Allah. Then deliver him to his place of safety. That is because they are a people who do not know. <> Idan wani daga mushirikai ya nemi maƙwabtakarka to, ka ba shi maƙwabtakar har ya ji, maganar Allah, sa'an nan ka isar da shi ga wurin amincewarsa. Wancan fa domin lalle ne su, mutãne ne waɗanda ba su sani ba. = --Qur'an 9:6
    How can there be for the polytheists a treaty in the sight of Allah and with His Messenger, except for those with whom you made a treaty at al-Masjid al-Haram? So as long as they are upright toward you, be upright toward them. Indeed, Allah loves the righteous [who fear Him]. <> Yãya wani alkawari a wurin Allah a wurin ManzonSa yake kasancẽwa ga mushirikai, fãce ga waɗanda kuka yi wa alkawari wurin Masallaci Mai alfarma? To matuƙar sun tsaya sõsai gare ku, sai ku tsayu sõsai gare su. Lalle ne Allah Yanã son mãsu taƙawa. = --Qur'an 9:7
    How [can there be a treaty] while, if they gain dominance over you, they do not observe concerning you any pact of kinship or covenant of protection? They satisfy you with their mouths, but their hearts refuse [compliance], and most of them are defiantly disobedient. <> Yãya, alhãli idan sun ci nasara a kanku, bã zã su tsare wata zumun ta ba a cikinku, kuma haka wata amãna, sunã yardar da ku da bãkunansu kuma zukãtansu sunã ƙi? Kuma mafi yawansu fãsiƙai ne. = --Qur'an 9:8
    They have exchanged the signs of Allah for a small price and averted [people] from His way. Indeed, it was evil that they were doing. <> Sun saya da ãyõyin Allah, 'yan kuɗi kaɗan, sa'an nan suka kange daga hanyar Allah. Lalle ne sũ, abin da suka kasance sunã aikatãwa yã mũnana. = --Qur'an 9:9
    They do not observe toward a believer any pact of kinship or covenant of protection. And it is they who are the transgressors. <> Bã su tsaron wata zumunta a cikin mũminai, kuma haka bãsu tsaron wata amãna. Kuma waɗannan ne mãsu ta'adi. = --Qur'an 9:10
    But if they repent, establish prayer, and give zakah, then they are your brothers in religion; and We detail the verses for a people who know. <> Sa'an nan idan sun tũba kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka, to, 'yan'uwanku ne a cikin addini, kuma Munã rarrabe ãyõyi daki-daki, ga mutãne waɗanda suke sani. = --Qur'an 9:11
    And if they break their oaths after their treaty and defame your religion, then fight the leaders of disbelief, for indeed, there are no oaths [sacred] to them; [fight them that] they might cease. <> Kuma idan suka warware rantsuwõyin amãna daga bãyan alkawarinsu, kuma suka yi sũka a cikin addininku, to, ku yaki shũgabannin kãfirci. Lalle ne sũ, bãbu rantsuwõyin amãna a gare su. Tsammãninsu sunã hanuwa. = --Qur'an 9:12
    Would you not fight a people who broke their oaths and determined to expel the Messenger, and they had begun [the attack upon] you the first time? Do you fear them? But Allah has more right that you should fear Him, if you are [truly] believers. <> Shin, bã ku yaƙin mutãne, waɗanda suka warware rantsuwõyinsu, kuma suka yi niyya ga fitar da Manzo, kuma sũ ne suka fãra muku, tun a farkon lõkaci? Shin kunã tsõron su ne? To, Allah ne marfi cancantar ku ji tsõronSa, idan kun kasance mũminai! = --Qur'an 9:13
    Fight them; Allah will punish them by your hands and will disgrace them and give you victory over them and satisfy the breasts of a believing people <> Ku yãƙe su, Allah Ya yi musu azabã da hannãyenku, kuma Ya kunyatar da su, kuma Ya taimake ku, kuma Ya warkar da ƙirãzan mutãne mũminai. = --Qur'an 9:14
    And remove the fury in the believers' hearts. And Allah turns in forgiveness to whom He wills; and Allah is Knowing and Wise. <> Kuma Ya tafĩ da fushin zukãtansu, kuma Ya karɓi tũba a kan wanda Ya so. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima. = --Qur'an 9:15
    Do you think that you will be left [as you are] while Allah has not yet made evident those among you who strive [for His cause] and do not take other than Allah, His Messenger and the believers as intimates? And Allah is Acquainted with what you do. <> Kõ kunã zaton a bar ku, tun Allah bai bayyana waɗanda suka yi jihãdi ba daga gare ku, kuma sũ ba su riƙi wani shigeba, baicin Allah da ManzonSa da mũminai? Kuma Allah ne Mai jarrabãwa ga abin da kuke aikatãwa. = --Qur'an 9:16
    It is not for the polytheists to maintain the mosques of Allah [while] witnessing against themselves with disbelief. [For] those, their deeds have become worthless, and in the Fire they will abide eternally. <> Bã ya kasancewa ga mãsu shirki su rãya masallatan Allah, alhãli kuwa sunã mãsu bãyar da shaida a kan rãyukansu da kafirci, waɗannan ayyukansu sun ɓãci, kuma a cikin wutã sũ madawwama = --Qur'an 9:17
    The mosques of Allah are only to be maintained by those who believe in Allah and the Last Day and establish prayer and give zakah and do not fear except Allah, for it is expected that those will be of the [rightly] guided. <> Abin sani kawai, mai rãya masallãtan Allah, shĩ ne wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya tsayar da salla kuma ya bãyar da zakka, kuma bai ji tsõron kõwa ba fãce Allah. To, akwai tsammãnin waɗannan su kasance daga shiryayyu. = --Qur'an 9:18
    Have you made the providing of water for the pilgrim and the maintenance of al-Masjid al-Haram equal to [the deeds of] one who believes in Allah and the Last Day and strives in the cause of Allah? They are not equal in the sight of Allah. And Allah does not guide the wrongdoing people. <> Shin, kun sanya shãyar da mahajjata da rãyar da Masallaci Mai alfarma kamar wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya yi jihãɗi a cikin hanyar Allah? Bã su daidaita a wurin Allah. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai. = --Qur'an 9:19
    The ones who have believed, emigrated and striven in the cause of Allah with their wealth and their lives are greater in rank in the sight of Allah. And it is those who are the attainers [of success]. <> Waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihãdi, a cikin hanyar Allah, da dũkiyõyinsu, da rãyukansu, sũ ne mafi girma ga daraja, a wurin Allah, kuma waɗannan sũ ne mãsu babban rabo. = --Qur'an 9:20
    Their Lord gives them good tidings of mercy from Him and approval and of gardens for them wherein is enduring pleasure. <> Ubangijinsu Yanã yi musu bishãra da wata rahama daga gare shi, da yarda, da gidãjen Aljanna. sunã da, a cikinsu, ni'ima zaunanniya. = --Qur'an 9:21
    [They will be] abiding therein forever. Indeed, Allah has with Him a great reward. <> Sunã madawwamã a cikinsu, har abada. Lalle ne Allah a wurinSa akwai lãda mai girma. = --Qur'an 9:22
    O you who have believed, do not take your fathers or your brothers as allies if they have preferred disbelief over belief. And whoever does so among you - then it is those who are the wrongdoers. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi ubanninku da 'yan'uwanku masõya, idan sun nũna son kãfirci a kan ĩmãni. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, waɗannan sũ ne azzãlumai. = --Qur'an 9:23
    Say, [O Muhammad], "If your fathers, your sons, your brothers, your wives, your relatives, wealth which you have obtained, commerce wherein you fear decline, and dwellings with which you are pleased are more beloved to you than Allah and His Messenger and jihad in His cause, then wait until Allah executes His command. And Allah does not guide the defiantly disobedient people." <> Ka ce: "Idan ubanninku da ɗiyanku da 'yan'uwanku da mãtanku da danginku da dũkiyõyi, waɗanda kuka yi tsiwirwirinsu, da fatauci wanda kuke tsõron tasgaronsa, da gidaje waɗanda kuke yarda da su, sun kasance mafiya sõyuwa a gare ku daga Allah da ManzonSa, da yin jihãdi ga hanyarSa, to, ku yi jira har Allah Ya zo da umurninSa! Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fãsiƙai." = --Qur'an 9:24
    Allah has already given you victory in many regions and [even] on the day of Hunayn, when your great number pleased you, but it did not avail you at all, and the earth was confining for you with its vastness; then you turned back, fleeing. <> Lalle ne, haƙĩƙa, Allah Yã taimake ku a cikin wurãre mãsu yawa, da Rãnar Hunainu, a lõkacin da yawanku ya bã ku sha'awa, sai bai amfãnar da ku da kõme ba, kuma ƙasa ta yi ƙunci a kanku da yalwarta, sa'an nan kuma kuka jũya kunã mãsu bãyar da bãya. = --Qur'an 9:25
    Then Allah sent down His tranquillity upon His Messenger and upon the believers and sent down soldiers angels whom you did not see and punished those who disbelieved. And that is the recompense of the disbelievers. <> Sa'an nan kuma Allah Ya saukar da natsuwarSa a kan ManzonSa kuma a kan mũminai, kuma Ya saukar da rundunõni waɗanda ba ku gan su ba, kuma Ya azabtar da waɗanda suka kãfirta: Wancan ne sakamakon kãfirai. = --Qur'an 9:26
    Then Allah will accept repentance after that for whom He wills; and Allah is Forgiving and Merciful. <> Sa'an nan kuma Allah Ya karɓi tũba daga bãyan wancana kan wanda Ya so. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai rahama. = --Qur'an 9:27
    O you who have believed, indeed the polytheists are unclean, so let them not approach al-Masjid al-Haram after this, their [final] year. And if you fear privation, Allah will enrich you from His bounty if He wills. Indeed, Allah is Knowing and Wise. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, mushirikai najasa ne, sabõda haka kada su kusanci Masallaci Mai alfarma a bãyan shẽkararsu wannan. Kuma idan kun ji tsõron talauci to, da sannu Allah zai wadãta ku daga falalarSa, idan Ya so. Lalle Allah ne Masani, mai hikima. = --Qur'an 9:28
    Fight those who do not believe in Allah or in the Last Day and who do not consider unlawful what Allah and His Messenger have made unlawful and who do not adopt the religion of truth from those who were given the Scripture - [fight] until they give the jizyah willingly while they are humbled. <> Ku yãƙi waɗanda bã su yin ĩmãni da Allah kuma bã su ĩmãni da Rãnar Lãhira kumabã su haramta abin da Allah da ManzonSa suka haramta, kuma bã su yin addini, addinin gaskiya, daga waɗanda aka bai wa Littãfi, har sai sun bãyar da jizya daga, hannu, kuma sunã ƙasƙantattu. = --Qur'an 9:29
    The Jews say, "Ezra is the son of Allah "; and the Christians say, "The Messiah is the son of Allah." That is their statement from their mouths; they imitate the saying of those who disbelieved [before them]. May Allah destroy them; how are they deluded? <> Kuma Yahũdãwa suka ce: "Uzairu ɗan Allah ne."Kuma Nasãra suka ce: "Masĩhu ɗan Allah ne." Wancan zancensu ne da bãkunansu. Sunã kamã da maganar waɗanda suka kãfirta daga gabãni. Allah Yã la'ance su! Yãya aka karkatar da su? = --Qur'an 9:30
    They have taken their scholars and monks as lords besides Allah, and [also] the Messiah, the son of Mary. And they were not commanded except to worship one God; there is no deity except Him. Exalted is He above whatever they associate with Him. <> Sun riƙi mãlamansu (Yahũdu) da ruhubãnãwansu (Nasãra) Ubannangiji, baicin Allah, kuma sun riƙi Masĩhu ɗan Maryama (haka). Kuma ba a umurce su ba fãce da su bautã wa Ubangiji Guda. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. TsarkinSa ya tabbata daga barin abin da suke yin shirki da shi. = --Qur'an 9:31
    They want to extinguish the light of Allah with their mouths, but Allah refuses except to perfect His light, although the disbelievers dislike it. <> Sunã nufin su bice hasken Allah da bãkunãnsu. Kuma Allah Yanã ki, fãce dai Ya cika haskenSa, kuma kõ da kãfirai sun ƙi. = --Qur'an 9:32
    It is He who has sent His Messenger with guidance and the religion of truth to manifest it over all religion, although they who associate others with Allah dislike it. <> Shi ne wanda Ya aiko manzonSa da shiriya da addinin gaskiya, dõmin ya bayyanl shi a kan addini dukansa, kuma kõ dã mushirikai sun ƙi. = --Qur'an 9:33
    O you who have believed, indeed many of the scholars and the monks devour the wealth of people unjustly and avert [them] from the way of Allah. And those who hoard gold and silver and spend it not in the way of Allah - give them tidings of a painful punishment. <> Yã waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne mãsu yawa daga Ahbãr da Ruhbãnãwa haƙĩƙa sunã cin dũkiyar mutãne da ƙarya, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma waɗanda suke taskacẽwar zĩnãriya da azurfa, kuma bã su ciyar da ita a cikin hanyar Allah, to, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 9:34
    The Day when it will be heated in the fire of Hell and seared therewith will be their foreheads, their flanks, and their backs, [it will be said], "This is what you hoarded for yourselves, so taste what you used to hoard." <> A Rãnar da ake ƙõna shi a kanta a cikin wutar Jahannama, sai a yi lalas da ita ga gõshinansu da sãshinansu da bãyayyakinsu, (a ce musu): "Wannan ne abin da kuka taskace dõmin rãyukanku. To, ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã sanyãwa a taska." = --Qur'an 9:35
    Indeed, the number of months with Allah is twelve [lunar] months in the register of Allah [from] the day He created the heavens and the earth; of these, four are sacred. That is the correct religion, so do not wrong yourselves during them. And fight against the disbelievers collectively as they fight against you collectively. And know that Allah is with the righteous [who fear Him]. <> Lallai ne ƙidãyayyun watanni a wurin Allah watã gõma shã biyu ne a cikin Littãfin Allah, a Rãnar da Ya halicci sammai da ƙasa daga cikinsu akwai huɗu mãsu alfarma. Wannan ne addini madaidaici. Sabõda haka kada ku zãlunci kanku a cikinsu. Kuma ku yãƙi mushirikai gabã ɗaya, kamar yadda suke yãƙar ku gabã ɗaya. Kuma ku sani cẽwa lallai ne Allah Yanã tãre da mãsu taƙawa. = --Qur'an 9:36
    Indeed, the postponing [of restriction within sacred months] is an increase in disbelief by which those who have disbelieved are led [further] astray. They make it lawful one year and unlawful another year to correspond to the number made unlawful by Allah and [thus] make lawful what Allah has made unlawful. Made pleasing to them is the evil of their deeds; and Allah does not guide the disbelieving people. <> Abin sani kawai, "Jinkirtãwa" ƙãri ne a cikin kãfirci, anã ɓatar da waɗanda suka kãfirta game da shi. Sunã halattar da watã a wata shẽkara kuma su haramtar da shi a wata shẽkara dõmin su dãce da adadin abin da Allah Ya haramta. Sabõda haka sunã halattar da abin da Allah Ya haramtar. An ƙawãce musu mũnanan ayyukansu. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne kãfirai. = --Qur'an 9:37
    O you who have believed, what is [the matter] with you that, when you are told to go forth in the cause of Allah, you adhere heavily to the earth? Are you satisfied with the life of this world rather than the Hereafter? But what is the enjoyment of worldly life compared to the Hereafter except a [very] little. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Mẽne ne a gare ku, idan ance muku, "Ku fita da yãƙi a cikin hanyar Allah," sai ku yi nauyi zuwa ga ƙasa. Shin, kun yarda da rãyuwar dũniya ne daga ta Lãhira? To jin dãɗin rãyuwar dũniya bai zama ba a cikin Lãhira, fãce kaɗan. = --Qur'an 9:38
    If you do not go forth, He will punish you with a painful punishment and will replace you with another people, and you will not harm Him at all. And Allah is over all things competent. <> Idan ba ku fita da yãƙi ba, Allah zai azabta ku da azãba mai raɗaɗi, kuma Ya musanya wasu mutãne, wasunku (a maimakonku). Kuma bã zã ku cũtar da Shida kõme ba. Kuma Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne. = --Qur'an 9:39
    If you do not aid the Prophet - Allah has already aided him when those who disbelieved had driven him out [of Makkah] as one of two, when they were in the cave and he said to his companion, "Do not grieve; indeed Allah is with us." And Allah sent down his tranquillity upon him and supported him with angels you did not see and made the word of those who disbelieved the lowest, while the word of Allah - that is the highest. And Allah is Exalted in Might and Wise. <> Idan ba ku taimake shi ba, to, lalle ne Allah Yã taimake shi, a lõkacin da waɗanda suka kãfirta suka fitar da shi, Yanã na biyun biyu, a lõkacin da suke cikin kõgon dũtse, a lõkacin da yake cẽwa da sãhibinsa: "Kada ka yi baƙin ciki, lalle ne Allah Yanã tãre da mu." Sai Allah Ya saukar da natsuwarSa a kansa, kuma Ya taimake shi da waɗansu rundunõni, ba ku gan su ba, kuma Ya sanya kalmar waɗanda suka kãfirta maƙasƙanciya, kuma kalmar Allah ita ce maɗaukakiya. Kuma Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima. = --Qur'an 9:40
    Go forth, whether light or heavy, and strive with your wealth and your lives in the cause of Allah. That is better for you, if you only knew. <> Ku fita da yãƙi kunã mãsu sauƙãƙan kãyã da mãsu nauyi, kuma ku yi jihãdi da dũkiyõyinku da kuma rãyukanku a cikin hanyar Allah. Wancan ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kunã sani. = --Qur'an 9:41
    Had it been an easy gain and a moderate trip, the hypocrites would have followed you, but distant to them was the journey. And they will swear by Allah, "If we were able, we would have gone forth with you," destroying themselves [through false oaths], and Allah knows that indeed they are liars. <> Dã yã kasance wata siffar dũniya ce: makusanciya, da tafiya matsakaiciya, dã sun bĩ ka, kuma amma fagen yã yi musu nĩsa. Kuma zã su yi ta yin rantsuwa da Allah, "Dã mun sãmi dãma, dã mun tafi tare da ku." Sunã halakar da kansu (da rantsuwar ƙarya) ne, kuma Allah Yanã sanin lalle, haƙĩƙa, sumaƙaryata ne.' = --Qur'an 9:42
    May Allah pardon you, [O Muhammad]; why did you give them permission [to remain behind]? [You should not have] until it was evident to you who were truthful and you knew [who were] the liars. <> Allah Ya yãfe maka laifi. Dõmin me ka yi musu izinin zama? Sai waɗanda suka yi gaskiya ssun bayyana a gare ka, kuma ka san maƙaryata. = --Qur'an 9:43
    Those who believe in Allah and the Last Day would not ask permission of you to be excused from striving with their wealth and their lives. And Allah is Knowing of those who fear Him. <> Waɗanda suke yin ĩmãnida Allah da Rãnar Lãhira, bã zã su nẽmi izininka ga yin, jihãdida dũkiyõyinsu da rãyukansu ba. Kuma Allah ne Masani ga mãsu taƙawa. = --Qur'an 9:44
    Only those would ask permission of you who do not believe in Allah and the Last Day and whose hearts have doubted, and they, in their doubt, are hesitating. <> Abin sani kawai, waɗanda bã sa ĩmãni da Allah, da Rãnar Lãhira, kuma zukãtansu suka yi shakka, sũ ne ke nẽman izininka, sa'an nan a cikin shakkarsu sunã ta yin kai kãwo. = --Qur'an 9:45
    And if they had intended to go forth, they would have prepared for it [some] preparation. But Allah disliked their being sent, so He kept them back, and they were told, "Remain [behind] with those who remain." <> Kuma dã sun yi nufin fita, dã sun yi wani tattali sabõda shi, kuma amma Allah Ya ƙi zãburarsu, sai Ya nauyayar da zamansu. Kuma aka ce ku zauna tãre da mãsu zama. = --Qur'an 9:46
    Had they gone forth with you, they would not have increased you except in confusion, and they would have been active among you, seeking [to cause] you fitnah. And among you are avid listeners to them. And Allah is Knowing of the wrongdoers. <> Dã sun fita a cikinku bã zã su ƙãre ku da kõme ba fãce da ɓarna, kuma lalle dã sun yi gaggãwar sanya annamĩmanci a tsakãninku, sunã nẽma muku fitina. Kuma a cikinku akwai 'yan rahõto sabõda su. Kuma Allah ne Masani ga azzãlumai, = --Qur'an 9:47
    They had already desired dissension before and had upset matters for you until the truth came and the ordinance of Allah appeared, while they were averse. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa sun nẽmi fitina daga gabãni, kuma, suka jũya maka al'amari, har gaskiya ta zo, kuma umurnin Allah Ya bayyana, alhãli sunã mãsu ƙyãma, = --Qur'an 9:48
    And among them is he who says, "Permit me [to remain at home] and do not put me to trial." Unquestionably, into trial they have fallen. And indeed, Hell will encompass the disbelievers. <> Kuma daga cikinsu akwai mai cẽwa, "Ka yi mini izinin zama, kuma kada ka fitine ni." To, a cikin fitinar suka fãɗa. Kuma lalle ne Jahannama, haƙĩƙa, mai ƙẽwayẽwa ce ga kãfirai. = --Qur'an 9:49
    If good befalls you, it distresses them; but if disaster strikes you, they say, "We took our matter [in hand] before," and turn away while they are rejoicing. <> Idan wani alhẽri ya sãme ka, zai ɓãta musu rai, kuma idan wata masifa ta sãme ka sai su ce: "Haƙĩƙa, mun riƙe al'amarinmu daga gabãni."Kuma sujũya, alhãli kuwa sunã mãsu farin ciki. = --Qur'an 9:50
    Say, "Never will we be struck except by what Allah has decreed for us; He is our protector." And upon Allah let the believers rely. <> Ka ce: "Bãbu abin da yake sãmun mu fãce abin da Allah Ya rubũta sahõda mu. Shĩ ne Majiɓincinmu. Kuma ga Allah, sai mũminai su dõgara." = --Qur'an 9:51
    Say, "Do you await for us except one of the two best things while we await for you that Allah will afflict you with punishment from Himself or at our hands? So wait; indeed we, along with you, are waiting." <> Ka ce: "Shin, kunã dãko ne da mu? Fãce dai da ɗayan abũbuwan biyu mãsu kyau, alhãli kuwa mũ, munã dãko da ku, AllahYa sãme ku da wata azãba daga gare Shi, kõ kuwa da hannayenmu. To, ku yi dãko. Lalle ne mũ, tãre da ku mãsu dãkon ne." = --Qur'an 9:52
    Say, "Spend willingly or unwillingly; never will it be accepted from you. Indeed, you have been a defiantly disobedient people." <> Ka ce: "Ku ciyar a kan yarda kõ kuwa a kan tĩlas. Bã zã a karɓa daga gare ku ba. Lalle ne kũ, kun kasance mutãne fãsiƙai." = --Qur'an 9:53
    And what prevents their expenditures from being accepted from them but that they have disbelieved in Allah and in His Messenger and that they come not to prayer except while they are lazy and that they do not spend except while they are unwilling. <> Kuma bãbu abin da ya hana a karɓi ciyarwarsu daga gare su fãce dõmin sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa, kuma bã su zuwa ga salla fãce Luma sunã mãsu kasãla, kuma bã su ciyarwa fãce sunã mãsu ƙyãma. = --Qur'an 9:54
    So let not their wealth or their children impress you. Allah only intends to punish them through them in worldly life and that their souls should depart [at death] while they are disbelievers. <> Sabõda haka, kada dũkiyõyinsu su bã ka sha'awa, kuma haka 'ya'yansu. Abin sani kawai, Allah Yanã nufin Ya yi musu azãba, da su a cikin rãyuwar dũniya, kuma rãyukansu su fita alhãli kuwa sunã kãfirai. = --Qur'an 9:55
    And they swear by Allah that they are from among you while they are not from among you; but they are a people who are afraid. <> Kuma sunã rantsuwa da Allah cẽwa, lalle ne sũ, haƙĩƙa, daga gare ku suke, alhãli kuwa ba su zamo daga gare ku ba. Kuma amma sũ mutãne ne mãsu tsõro. = --Qur'an 9:56
    If they could find a refuge or some caves or any place to enter [and hide], they would turn to it while they run heedlessly. <> Dã sunã sãmun mafaka kõ kuwa waɗansu ɓulõli, kõ kuwa wani mashigi, da sun, jũya zuwa gare shi, kuma suna gaggawar shiga. = --Qur'an 9:57
    And among them are some who criticize you concerning the [distribution of] charities. If they are given from them, they approve; but if they are not given from them, at once they become angry. <> Kuma daga cikinsu akwai wanda yake zunɗen ka a kan sha'anin dũkiyõyin sadaka, sai idan an bã su daga cikinta, su yarda, kuma idan ba a bã su ba daga cikinta sai su zamo sunã mãsu fushi. = --Qur'an 9:58
    If only they had been satisfied with what Allah and His Messenger gave them and said, "Sufficient for us is Allah; Allah will give us of His bounty, and [so will] His Messenger; indeed, we are desirous toward Allah," [it would have been better for them]. <> Kuma dã dai su lalle sun yarda da abin da Allah Ya bã su, da ManzonSa kuma suka ce: "Ma'ishinmu Allah ne, zai kãwo mana daga falalarSa kuma ManzõnSa (zai bã mu). Lalle ne mũ, zuwa ga Allah mãsu kwaɗayi ne." = --Qur'an 9:59
    Zakah expenditures are only for the poor and for the needy and for those employed to collect [zakah] and for bringing hearts together [for Islam] and for freeing captives [or slaves] and for those in debt and for the cause of Allah and for the [stranded] traveler - an obligation [imposed] by Allah. And Allah is Knowing and Wise. <> Abin sani kawai, dũkiyõyin sadaka na faƙĩrai ne da miskinai da mãsu aiki a kansu, da waɗanda ake lallãshin zukãtansu, kuma a cikin fansar wuyõyi, da mabarta, da a cikin hanyar Allah da ɗan hanya (matafiyi). Farilla daga Allah. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima. = --Qur'an 9:60
    And among them are those who abuse the Prophet and say, "He is an ear." Say, "[It is] an ear of goodness for you that believes in Allah and believes the believers and [is] a mercy to those who believe among you." And those who abuse the Messenger of Allah - for them is a painful punishment. <> Kuma daga cikinsu akwai waɗanda suke cũtar Annabi, kuma sunã cẽwa "Shi kunne ne." Ka ce: "Kunnen alhẽri gare ku, Yanã ĩmãni da Allah, kuma Yanã yarda da mũminai, kuma rahama ne ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare ku."Kuma waɗanda suke cũtar Manzon Allah sunã da azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 9:61
    They swear by Allah to you [Muslims] to satisfy you. But Allah and His Messenger are more worthy for them to satisfy, if they should be believers. <> Sunã rantsuwa da Allah sabõda ku, dõmin su yardar da ku. Kuma Allah da ManzonSa ne mafi cancantar su yardar da Shi, idan sun kasance mũminai. = --Qur'an 9:62
    Do they not know that whoever opposes Allah and His Messenger - that for him is the fire of Hell, wherein he will abide eternally? That is the great disgrace. <> Shin, ba su sani ba cẽwa "Lalle ne wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, haƙĩƙa Yanã da wutar Jahannama, Yanã madawwami a cikinta? Waccan ita ce wulãkantãwa babba!" = --Qur'an 9:63
    They hypocrites are apprehensive lest a surah be revealed about them, informing them of what is in their hearts. Say, "Mock [as you wish]; indeed, Allah will expose that which you fear." <> Munãfukai sunã tsõron a saukar da wata sũra a kansu, wadda take bã su lãbãri ga abin da yake cikin zukãtansu. Ka ce: "Ku yi izgili. Lalle ne, Allah ne Mai fitai da abin da kuke tsõro." = --Qur'an 9:64
    And if you ask them, they will surely say, "We were only conversing and playing." Say, "Is it Allah and His verses and His Messenger that you were mocking?" <> Kuma lalle ne, idan ka tambaye, su haƙĩƙa, sunã cẽwa, "Abin sani kawai, mun kasance munã hĩra kuma munã wãsã. Ka ce: "Shin da Allah, da kuma ãyõyinSa da ManzonSa kuka kasance kunã izgili?" = --Qur'an 9:65
    Make no excuse; you have disbelieved after your belief. If We pardon one faction of you - We will punish another faction because they were criminals. <> "Kada ku kãwo wani uzuri, haƙĩƙa, kun kãfirta a bãyanĩmãninku. Idan Mun yãfe laifi ga wata ƙungiya daga gare ku, zã Mu azabta wata ƙungiya sabõda, lalle, sun kasance mãsu laifi." = --Qur'an 9:66
    The hypocrite men and hypocrite women are of one another. They enjoin what is wrong and forbid what is right and close their hands. They have forgotten Allah, so He has forgotten them [accordingly]. Indeed, the hypocrites - it is they who are the defiantly disobedient. <> Munãfukai maza da munãfukai mãtã, sãshensu daga sãshe, sunã umurni da abin ƙi kuma sunã hani daga alhẽri. Kuma sunã damƙẽwar hannayensu. Sun mance Allah, sai Ya mantã da su. Lalle ne munãfukai sũ ne fãsiƙai. = --Qur'an 9:67
    Allah has promised the hypocrite men and hypocrite women and the disbelievers the fire of Hell, wherein they will abide eternally. It is sufficient for them. And Allah has cursed them, and for them is an enduring punishment. <> Allah yã yi wa'adi ga munãfukai maza da munãfukai mãtã da kãfirai da wutar Jahannama, sunã madawwama a cikinta. Ita ce ma'ishiyarsu. Kuma Allah Yã la'ance su, kuma sunã da azãba zaunanniya. = --Qur'an 9:68
    [You disbelievers are] like those before you; they were stronger than you in power and more abundant in wealth and children. They enjoyed their portion [of worldly enjoyment], and you have enjoyed your portion as those before you enjoyed their portion, and you have engaged [in vanities] like that in which they engaged. [It is] those whose deeds have become worthless in this world and in the Hereafter, and it is they who are the losers. <> Kamar waɗanda suke a gabãninku, sun kasance mafi tsananin ƙarfi daga gare ku, kuma mafi yawan dũkiyõyi da ɗiya. Sai suka ji daɗi da rabonsu, sai kuka ji daɗi da rabonku kamar yadda waɗanda suke a gabãninku suka ji dãɗi, da rabonsu, kuma kuka kũtsa kamar kũtsãwarsu. Waɗancan ayyukansu sun ɓãci a dũniya da Lãhira, kuma waɗannan sũ ne mãsu hasãra. = --Qur'an 9:69
    Has there not reached them the news of those before them - the people of Noah and [the tribes of] 'Aad and Thamud and the people of Abraham and the companions of Madyan and the towns overturned? Their messengers came to them with clear proofs. And Allah would never have wronged them, but they were wronging themselves. <> Shin lãbarin waɗanda suke a gabãninsu bai je musu ba, mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdãwa da mutãnen Ibrãhĩm da Ma'abũta Madyana da waɗanda aka birkice? Manzanninsu sun jẽ musu da ãyõyayi bayanannu. To, Allah bai kasance Yanã zãluntar su ba, amma sun kasance rãyukansu suke zãlunta. = --Qur'an 9:70
    The believing men and believing women are allies of one another. They enjoin what is right and forbid what is wrong and establish prayer and give zakah and obey Allah and His Messenger. Those - Allah will have mercy upon them. Indeed, Allah is Exalted in Might and Wise. <> Kuma mummunai maza da mummunai mãtã sãshensu majiɓincin sãshe ne, sunã umurni da alhẽri kuma sunã hani daga abin da bã a so, kuma sunã tsayar da salla, kuma sunã bãyar da zakka, kuma sunãɗã'a ga Allah da ManzonSa. Waɗannan Allah zai yi musu rahama. Lalle Allah ne Mabuwãyi, Mai hikima. = --Qur'an 9:71
    Allah has promised the believing men and believing women gardens beneath which rivers flow, wherein they abide eternally, and pleasant dwellings in gardens of perpetual residence; but approval from Allah is greater. It is that which is the great attainment. <> Kuma Allah Yã yi wa'adi ga mummunai maza da mummunai mãtã da gidãjen Aljanna ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwamã a cikinsu, da wurãren zama mãsu dãɗi a cikin gidãjen Aljannar. Kuma yarda daga Allah ce mafi girma. Wancan shi ne babban rabo, mai girma. = --Qur'an 9:72
    O Prophet, fight against the disbelievers and the hypocrites and be harsh upon them. And their refuge is Hell, and wretched is the destination. <> Ya kai Annabi! Ka yãƙi kãfirai da munãfukai kuma ka tsaurara a kansu. Kuma matattararsu Jahannama ce. Tir da ta zama makõmar! = --Qur'an 9:73
    They swear by Allah that they did not say [anything against the Prophet] while they had said the word of disbelief and disbelieved after their [pretense of] Islam and planned that which they were not to attain. And they were not resentful except [for the fact] that Allah and His Messenger had enriched them of His bounty. So if they repent, it is better for them; but if they turn away, Allah will punish them with a painful punishment in this world and the Hereafter. And there will not be for them on earth any protector or helper. <> Sunã rantsuwa da Allah, ba su faɗa ba, alhãli kuwa lalle ne, haƙĩƙa, sun faɗi kalmar kãfirci, kuma; sun kãfirta a bãyan musuluntarsu, kuma sun yi himma ga abin da ba su sãmu ba. Kuma ba su zargi kõme ba fãce dõmin Allah da ManzonSa Ya wadãtar da su daga falalarSa. To, idan sun tũba zai kasance mafi alhẽri gare su, kuma idan sun jũya bãya, Allah zaiazabtã su da azãba mai raɗaɗi a cikin dũniya da Lãhira, kuma bã su da wani masõyi kõ wani mataimaki a cikin kasa. = --Qur'an 9:74
    And among them are those who made a covenant with Allah, [saying], "If He should give us from His bounty, we will surely spend in charity, and we will surely be among the righteous." <> Kuma daga cikinsu akwai wadɗanda suka yi wa Allah alkawari, "Lalle ne idan ya kãwo mana daga falalarSa, haƙĩƙa, munãbãyar da sadaka, kuma lalle ne munã kasancẽwa, daga sãlihai." = --Qur'an 9:75
    But when he gave them from His bounty, they were stingy with it and turned away while they refused. <> To, a lõkacin da Ya bã su daga falalarSa, sai suka yi rõwa da shi, kuma suka jũya bãya sunã mãsu bijirẽwa, = --Qur'an 9:76
    So He penalized them with hypocrisy in their hearts until the Day they will meet Him - because they failed Allah in what they promised Him and because they [habitually] used to lie. <> Sai Ya biyar musu da munãfunci a cikin zukatansu har zuwa ga Rãnar da suke haɗuwa da Shi sabõda sãɓã wa Allah a abin da suka yi Masa alkawari, kuma sabõda abin da suka kasance sunã yi na ƙarya. = --Qur'an 9:77
    Did they not know that Allah knows their secrets and their private conversations and that Allah is the Knower of the unseen? <> Shin, ba su sani ba cẽwa lalle ne Allah Yanã sanin asĩrinsuda gãnawarsu, kuma lalle Allah ne Masanin abũbuwan fake? = --Qur'an 9:78
    Those who criticize the contributors among the believers concerning [their] charities and [criticize] the ones who find nothing [to spend] except their effort, so they ridicule them - Allah will ridicule them, and they will have a painful punishment. <> Waɗanda suke aibanta mãsu yin alhẽri daga mummunaia cikin dũkiyõyin sadaka, da waɗanda ba su sãmu fãce iyãkar ƙõƙarinsu, sai sanã yi musu izgili. Allah Yanã yin izgili gare su. Kuma sunã da azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 9:79
    Ask forgiveness for them, [O Muhammad], or do not ask forgiveness for them. If you should ask forgiveness for them seventy times - never will Allah forgive them. That is because they disbelieved in Allah and His Messenger, and Allah does not guide the defiantly disobedient people. <> Kõ kã nẽma musu gãfara ko ba ka nẽma musu ba, idan ka nẽma musu gãfara sau saba'in, to, Allah bã zai gãfarta musu ba. Sabõda sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne fãsiƙai. = --Qur'an 9:80
    Those who remained behind rejoiced in their staying [at home] after [the departure of] the Messenger of Allah and disliked to strive with their wealth and their lives in the cause of Allah and said, "Do not go forth in the heat." Say, "The fire of Hell is more intensive in heat" - if they would but understand. <> Waɗanda aka bari sun yi farin ciki da zamansu a bãyan Manzon Allah, kuma suka ƙi su yi jihãdi da dũkiyõyinsu da rãyukansu a cikin hanyar Allah, kuma suka ce: "Kada ku fita zuwa yãƙi a cikin zãfi."Ka ce: "Wutar Jahannama ce mafi tsanlnin zãfi." Dã sun kasance sunã fahimta! = --Qur'an 9:81
    So let them laugh a little and [then] weep much as recompense for what they used to earn. <> Sabõda haka su yi dãriya kaɗan, kuma su yi kũkada yawa a kan sãkamako ga abin da suka kasance sunã tsirfatãwa. = --Qur'an 9:82
    If Allah should return you to a faction of them [after the expedition] and then they ask your permission to go out [to battle], say, "You will not go out with me, ever, and you will never fight with me an enemy. Indeed, you were satisfied with sitting [at home] the first time, so sit [now] with those who stay behind." <> To, idan Allah Ya mayar da kai zuwa ga wata ƙungiyã daga gare su sa'an nan suka nẽme ka izni dõmin su fita, to, ka ce: "Bã zã ku fita tãre da nĩ ba har abada, kuma bã zã ku yi yãƙi tãre da nĩ ba a kan wani maƙiyi. Lalle ne kũ, kun yarda da zama a farkon lõkaci, sai ku zauna tãre da mãtã mãsu zaman gida." = --Qur'an 9:83
    And do not pray [the funeral prayer, O Muhammad], over any of them who has died - ever - or stand at his grave. Indeed, they disbelieved in Allah and His Messenger and died while they were defiantly disobedient. <> Kuma kada ka yi salla a kan kõwa daga cikinsu wanda ya mutu, har abada, kuma kada ka tsaya a kan kabarinsa. Lalle ne sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa, kuma sun mutu alhãli kuwa sunã fãsiƙai. = --Qur'an 9:84
    And let not their wealth and their children impress you. Allah only intends to punish them through them in this world and that their souls should depart [at death] while they are disbelievers. <> Kuma kada dũkiyõyinsu da ɗiyansu su bã ka sha'awa. Abin sani kawai, Allah Yanã nufin Ya yi musu azãba da su a cikin dũniya, kuma rãyukansu su fita alhãli kuwa sunã kãfirai. = --Qur'an 9:85
    And when a surah was revealed [enjoining them] to believe in Allah and to fight with His Messenger, those of wealth among them asked your permission [to stay back] and said, "Leave us to be with them who sit [at home]." <> Kuma idan aka saukar da wata sũra cẽwa; Ku yi ĩmãni da Allah kuma ku yi jihãdi tãre da ManzionSa. Sai mawadãta daga gare su su nẽmi izninka, kuma su ce: Ka bar mu mu kasance tãre da mazauna. = --Qur'an 9:86
    They were satisfied to be with those who stay behind, and their hearts were sealed over, so they do not understand. <> Sun yarda da su kasance tãre da mãtã mãsu zama (a cikin gidãje). Kuma aka rufe a kan zukãtansu, sabõda haka, sũ, bã su fahimta. = --Qur'an 9:87
    But the Messenger and those who believed with him fought with their wealth and their lives. Those will have [all that is] good, and it is those who are the successful. <> Amma Manzon Allah da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sun yi jihãdi da dũkiyõyinsu da rãyukansu. Kuma waɗannan sunã da ayyukan alhẽri, kuma waɗannan sũ ne mãsu cin nasara. = --Qur'an 9:88
    Allah has prepared for them gardens beneath which rivers flow, wherein they will abide eternally. That is the great attainment. <> Allah yã yi musu tattalin gidãjen Aljanna, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwamã a cikinsu. Wancan ne babban rabo mai girma. = --Qur'an 9:89
    And those with excuses among the bedouins came to be permitted [to remain], and they who had lied to Allah and His Messenger sat [at home]. There will strike those who disbelieved among them a painful punishment. <> Kuma mãsu uzuri daga ƙauyãwa zuka zo dõmin a yi musu izini, kuma waɗanda suka yi wa Allah da ManzonSa ƙarya, suka yi zamansu. wata azãba mai raɗaɗi zã ta sãmi waɗanda suka kãfirta daga gare su. = --Qur'an 9:90
    There is not upon the weak or upon the ill or upon those who do not find anything to spend any discomfort when they are sincere to Allah and His Messenger. There is not upon the doers of good any cause [for blame]. And Allah is Forgiving and Merciful. <> Bãbu laifi a kan maraunana kuma haka majinyata, kuma bãbu laifi a kan waɗanda bã su sãmun abin da suke ciyarwa idan sun yi nasĩha ga Allah da ManzonSa. Kuma bãbu wani laifi a kan mãsu kyautatãwa. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai tausayi. = --Qur'an 9:91
    Nor [is there blame] upon those who, when they came to you that you might give them mounts, you said, "I can find nothing for you to ride upon." They turned back while their eyes overflowed with tears out of grief that they could not find something to spend [for the cause of Allah]. <> Kuma bãbu (laifi) a kan waɗanda idan sun je maka dõmin ka ɗauke su ka ce: "Bã ni da abin da nake ɗaukar ku a kansa," suka jũya alhãli kuwa idãnunsu sunã zubar da hawãye dõmin baƙin ciki cẽwa ba su sãmi abin da suke ciyarwa ba. = --Qur'an 9:92
    The cause [for blame] is only upon those who ask permission of you while they are rich. They are satisfied to be with those who stay behind, and Allah has sealed over their hearts, so they do not know. <> Abin sani kawai, laifi Yanã a kan waɗanda suke nẽman izininka alhãli kuwa sũ mawadãta ne. Sun yarda su kasance tãre da mãtã mamaya (gidãje), kuma Allah Yã danne a kan zukãtansu, dõmin haka sũ, bã su gãnẽwa. = --Qur'an 9:93
    They will make excuses to you when you have returned to them. Say, "Make no excuse - never will we believe you. Allah has already informed us of your news. And Allah will observe your deeds, and [so will] His Messenger; then you will be taken back to the Knower of the unseen and the witnessed, and He will inform you of what you used to do." <> Sunã kãwo uzurinsu zuwa gare ku idan kun kõma zuwa gare su Ka ce: "Kada ku kãwo wani uzuri, bã zã mu amince muku ba. Haƙĩƙa, Allah Yã bã mu lãbãri daga lãbãrunku, Allah zai ga aikinku kuma ManzonSa (zai gani). Sa'an nan kuma a mayar da ku zuwa ga Masanin gaibi da bayyane, sai Ya bã ku lãbarin abin da kuka kasance kunã aikatãwa." = --Qur'an 9:94
    They will swear by Allah to you when you return to them that you would leave them alone. So leave them alone; indeed they are evil; and their refuge is Hell as recompense for what they had been earning. <> Zã su yi rantsuwa da Allah a gare ku idan kun jũya zuwa gare su, dõmin ku kau da kai daga gare su. To, ku kau da kai daga gare su don kõ sũ ƙarantã ne, kuma Jahannama ce matattararsu bisa ga sãkamakon abin da suka kasance sunã tsirfatãwa. = --Qur'an 9:95
    They swear to you so that you might be satisfied with them. But if you should be satisfied with them - indeed, Allah is not satisfied with a defiantly disobedient people. <> Sunã rantsuwã gare ku dõmin ku yarda da su. To, idan kun yarda da su, to, lalle ne Allah bã shi yarda da mutãne fãsiƙai. = --Qur'an 9:96
    The bedouins are stronger in disbelief and hypocrisy and more likely not to know the limits of what [laws] Allah has revealed to His Messenger. And Allah is Knowing and Wise. <> ¡auyãwã ne mafi tsananin kãfirci da munãfinci, kuma sũne mafi kamanta ga, rashin sanin haddõjin abin da Allah Ya saukar a kan ManzonSa. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima. = --Qur'an 9:97
    And among the bedouins are some who consider what they spend as a loss and await for you turns of misfortune. Upon them will be a misfortune of evil. And Allah is Hearing and Knowing. <> Kuma daga ƙauyãwã akwai waɗanda suke riƙon abin da suke ciyarwa a kan tãra ce, kuma sunã saurãron aukuwar masĩfa a gare ku, aukuwar mummunar masĩfa ta tabbata a kansu. Kuma Allah ne Mai ji, Masani. = --Qur'an 9:98
    But among the bedouins are some who believe in Allah and the Last Day and consider what they spend as means of nearness to Allah and of [obtaining] invocations of the Messenger. Unquestionably, it is a means of nearness for them. Allah will admit them to His mercy. Indeed, Allah is Forgiving and Merciful. <> Kuma daga ƙauyãwã akawi waɗanda suke yin ĩmanida Allah da Rãnar Lãhira, kuma sunã riƙon abin da suke ciyarwa (tamkar) waɗansu ibãdõdin nẽman kusanta ne a wurin Allah da addu'õ'in ManzonSa. To, lalle ne ita (ciyarwar nan) ibãdar nẽman kusanta ce a gare su. Allah zai shigar da su a cikin RahamarSa. Lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai. = --Qur'an 9:99
    And the first forerunners [in the faith] among the Muhajireen and the Ansar and those who followed them with good conduct - Allah is pleased with them and they are pleased with Him, and He has prepared for them gardens beneath which rivers flow, wherein they will abide forever. That is the great attainment. <> Kuma mãsu tsẽrẽwa na farko daga Muhãjirina da Ansar da waɗanda suka bi su da kyautatãwa, Allah Ya yarda daga gare su su kuma sun yarda daga gare Shi, kuma Ya yi mãsu tattalin gidãjen Aljanna; ¡õramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, suna madawwamã a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo mai girma. = --Qur'an 9:100
    And among those around you of the bedouins are hypocrites, and [also] from the people of Madinah. They have become accustomed to hypocrisy. You, [O Muhammad], do not know them, [but] We know them. We will punish them twice [in this world]; then they will be returned to a great punishment. <> Kuma daga waɗanda suke a gẽfenku daga ƙauyãwa akwai munãfukai, haka kuma daga mutãnen Madnĩa. Sun gõge a kan munãfunci, bã ka sanin su, Mũ ne Muke sanin su. zã Mu yi musu azãba sau biyu, sa'an nan a mayar da su zuwa ga azãba mai girma. = --Qur'an 9:101
    And [there are] others who have acknowledged their sins. They had mixed a righteous deed with another that was bad. Perhaps Allah will turn to them in forgiveness. Indeed, Allah is Forgiving and Merciful. <> Kuma da waɗansu, sun yi furuci da laifinsu, sun haɗa aiki na ƙwarai da wani mummuna. Akwai tsammãnin Allah Ya karɓi tũba a kansu. Lallai Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai. = --Qur'an 9:102
    Take, [O, Muhammad], from their wealth a charity by which you purify them and cause them increase, and invoke [Allah 's blessings] upon them. Indeed, your invocations are reassurance for them. And Allah is Hearing and Knowing. <> Ka karɓi sadaka daga dũkiyõyinsu kana tsarkake su, kuma kana tabbatar da kirkinsu da ita. Kuma ka yi musu addu'a. Lallai addu'õ'inKa natsuwã ne a gare su. Kuma Allah ne Mai ji, Masani. = --Qur'an 9:103
    Do they not know that it is Allah who accepts repentance from His servants and receives charities and that it is Allah who is the Accepting of repentance, the Merciful? <> Shin, ba su sani ba cẽwa lallai Allah, ne Yake karɓar tũbã daga bãyinSa, kuma Yanã karɓar sadakõkinsu, kuma lalle Allah ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai? = --Qur'an 9:104
    And say, "Do [as you will], for Allah will see your deeds, and [so, will] His Messenger and the believers. And you will be returned to the Knower of the unseen and the witnessed, and He will inform you of what you used to do." <> Kuma ka ce: "Ku yi aiki, sa'an nan Allah zai ga aikinku, da ManzonSa da Muminai kuma zã a mayar da ku zuwa ga masanin fake da bayyane, sa'an nan Ya bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa." = --Qur'an 9:105
    And [there are] others deferred until the command of Allah - whether He will punish them or whether He will forgive them. And Allah is Knowing and Wise. <> Kuma da waɗansu waɗanda aka jinkirtar ga umurnin Allah, kõ dai Ya yi musu azãba kõ kuma Ya karɓi tũba a kansu. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima. = --Qur'an 9:106
    And [there are] those [hypocrites] who took for themselves a mosque for causing harm and disbelief and division among the believers and as a station for whoever had warred against Allah and His Messenger before. And they will surely swear, "We intended only the best." And Allah testifies that indeed they are liars. <> Kuma waɗanda suka riƙi wani masallãci dõmin cũta da kãfirci da nẽman rarrabẽwa a tsakãnin muminai da fakẽwã ga taimakon wanda ya yãƙi Allah da ManzonSa daga gabãni, kuma haƙĩƙa sunã yin rantsuwa cẽwa, "Ba mu yi nufin kõmai ba fãce alhẽri", alhãli kuwa Allah Yanã yin shaida cẽwa, su, haƙĩƙa, maƙaryata ne. = --Qur'an 9:107
    Do not stand [for prayer] within it - ever. A mosque founded on righteousness from the first day is more worthy for you to stand in. Within it are men who love to purify themselves; and Allah loves those who purify themselves. <> Kada ka tsaya a cikinsa har abada. Lalle ne, Masallaci wanda aka yi harsãshinsa a kan taƙawa tun farkon yini, shĩ ne mafi cancantar ka tsaya a cikinsa. A cikinsa akwai waɗansu maza sunã son su tsarkaka. Kuma Allah Yanã son mãsu nẽman tsarkakuwa. = --Qur'an 9:108
    Then is one who laid the foundation of his building on righteousness [with fear] from Allah and [seeking] His approval better or one who laid the foundation of his building on the edge of a bank about to collapse, so it collapsed with him into the fire of Hell? And Allah does not guide the wrongdoing people. <> Shin, wanda ya sanya harsãshin gininsa a kan taƙawa daga Allah da yarda, shi ne mafi alhẽri kõ kuwa wanda ya sanya harsãshin gininsa a kan gãɓar rãmi mai tusgãwa? Sai ya rũsa da shi a cikin wutar Jahannama. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai. = --Qur'an 9:109
    Their building which they built will not cease to be a [cause of] skepticism in their hearts until their hearts are stopped. And Allah is Knowing and Wise. <> Gininsu, wanda suka gina, bã zai gushe ba Yanã abin shakka a cikin zukãtansu fãce idan zukãtansu sun yanyanke. Kuma Allah ne Masani, Mai Hikima. = --Qur'an 9:110
    Indeed, Allah has purchased from the believers their lives and their properties [in exchange] for that they will have Paradise. They fight in the cause of Allah, so they kill and are killed. [It is] a true promise [binding] upon Him in the Torah and the Gospel and the Qur'an. And who is truer to his covenant than Allah? So rejoice in your transaction which you have contracted. And it is that which is the great attainment. <> Lalle ne, Allah Ya saya daga mummunai, rãyukansu da dũkiyõyinsu, da cẽwa sunã da Aljanna, sunã yin yãƙi a cikin hanyar Allah, sabõda haka sunã kashẽwa anã kashẽ su. (Allah Yã yi) wa'adi a kanSa, tabbace a cikin Attaura da Linjĩla da Alƙur'ãni. Kuma wãne ne mafi cikãwa da alkawarinsa daga Allah? Sabõda haka ku yi bushãra da cinikinku wanda kuka ƙulla da Shi. Kuma wancan shi ne babban rabo, mai girma. = --Qur'an 9:111
    [Such believers are] the repentant, the worshippers, the praisers [of Allah], the travelers [for His cause], those who bow and prostrate [in prayer], those who enjoin what is right and forbid what is wrong, and those who observe the limits [set by] Allah. And give good tidings to the believers. <> Mãsu tũba, mãsu bautãwa, mãsu gõdẽwa, mãsu tafiya, mãsu ruku'i, mãsu sujada mãsu umurni da alhẽri da mãsu hani daga abin da aka ƙi da mãsu tsarẽwaã ga iyãkõkin Allah. Kuma ka bãyar da bushãra ga muminai. = --Qur'an 9:112
    It is not for the Prophet and those who have believed to ask forgiveness for the polytheists, even if they were relatives, after it has become clear to them that they are companions of Hellfire. <> Bã ya kasancẽwa ga Annabi da waɗanda suka yi ĩmãni, su yi istigifãri ga mushirikai, kuma kõ dã sun kasance ma'abũta zumunta ne daga bãyan sun bayyana a gare su, cẽwa lalle ne, sũ, 'yan Jahĩm ne. = --Qur'an 9:113
    And the request of forgiveness of Abraham for his father was only because of a promise he had made to him. But when it became apparent to Abraham that his father was an enemy to Allah, he disassociated himself from him. Indeed was Abraham compassionate and patient. <> Kuma istigifãrin Ibrãhĩm ga ubansa bai kasance ba fãce sabõda wani wa'adi ne da ya ƙulla alƙawarinsa da shi, sa'an nan a lõkacin da ya bayyana a gare shi (Ibrãhĩm) cẽwa lalle ne shĩ (ubansa) maƙiyi ne ga Allah, sai ya barranta daga gare shi. Lalle ne Ibrahim, haƙĩƙa, mai yawan addu'a ne, mai haƙuri. = --Qur'an 9:114
    And Allah would not let a people stray after He has guided them until He makes clear to them what they should avoid. Indeed, Allah is Knowing of all things. <> Kuma Allah bai kasance mai ɓatar da mutãne a bãyan Yã shiryar da su ba, sai Ya bayyanã musu abin da zã su yi taƙawa da shi. Lalle ne Alllh, ga kõme, Masani ne. = --Qur'an 9:115
    Indeed, to Allah belongs the dominion of the heavens and the earth; He gives life and causes death. And you have not besides Allah any protector or any helper. <> Lalle ne Allah Yanã da mulkin sammai da ƙasa, Yanã rãyarwa kuma Yanã matarwa. Kuma bã ku da wani masõyi, kuma bã ku da mataimaki, baicin Allah. = --Qur'an 9:116
    Allah has already forgiven the Prophet and the Muhajireen and the Ansar who followed him in the hour of difficulty after the hearts of a party of them had almost inclined [to doubt], and then He forgave them. Indeed, He was to them Kind and Merciful. <> Lalle ne, haƙĩƙa, Allah Ya karɓi tũbar Anbabi da Muhãjirĩna da Ansãr waɗanda suka bĩ shi, a cikin sã'ar tsanani, daga bãya zukãtan wani ɓangare daga gare su sun yi kusa su karkata, sa'an nan (Allah) Ya karɓi tũbarsu. Lalle, Shĩ ne Mai tausayi, Mai jin ƙai gare su. = --Qur'an 9:117
    And [He also forgave] the three who were left behind [and regretted their error] to the point that the earth closed in on them in spite of its vastness and their souls confined them and they were certain that there is no refuge from Allah except in Him. Then He turned to them so they could repent. Indeed, Allah is the Accepting of repentance, the Merciful. <> Kuma (Allah) Yã karɓi tũba a kan ukun nan waɗanda aka jinkirtar har ƙasa da yalwarta ta yi ƙunci a kansu, kuma rãyukansu suka yi ƙunci a kansu, kuma suka yi zaton bãbu wata mafakã daga Allah fãce (kõmãwa) zuwa gare Shi. Sa'an nan Allah Ya karɓi tũbarsu, dõmin su tabbata a kan tũba. Lalle Allah ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai. = --Qur'an 9:118
    O you who have believed, fear Allah and be with those who are true. <> Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, kuma ku kasance tãre da mãsu gaskiya. = --Qur'an 9:119
    It was not [proper] for the people of Madinah and those surrounding them of the bedouins that they remain behind after [the departure of] the Messenger of Allah or that they prefer themselves over his self. That is because they are not afflicted by thirst or fatigue or hunger in the cause of Allah, nor do they tread on any ground that enrages the disbelievers, nor do they inflict upon an enemy any infliction but that is registered for them as a righteous deed. Indeed, Allah does not allow to be lost the reward of the doers of good. <> Bã ya kasancẽwa ga mutãnen Madĩna da wanda yake a gẽfensu, daga ƙauyãwã, su sãba daga bin Manzon Allah, kuma kada su yi gudu da rãyukansu daga ransa. Wancan, sabõda ƙishirwa bã ta sãmun su, haka kuma wata wahala, haka kuma wata yunwa, a cikin hanyai Allah, kuma bã su tãkin wani matãki wanda yake takaitar da kãfirai kuma bã su sãmun wani sãmu daga maƙiyi fãce an rubuta musu da shi, lãdar aiki na ƙwarai. Lallai ne Allah bã Ya tõzarta lãdar mãsu kyautatãwa. = --Qur'an 9:120
    Nor do they spend an expenditure, small or large, or cross a valley but that it is registered for them that Allah may reward them for the best of what they were doing. <> Kuma bã su ciyar da wata ciyarwa, ƙarama kõ babba, kuma bã su kẽta wani rafi sai an rubutã musu, dõmin Allah Ya sãka musu da mafi kyãwon abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 9:121
    And it is not for the believers to go forth [to battle] all at once. For there should separate from every division of them a group [remaining] to obtain understanding in the religion and warn their people when they return to them that they might be cautious. <> Kuma bã ya kasancẽwã ga muminai su fita zuwa yãƙi gabã ɗaya. Sabõda haka, don me ne wata jama'a daga kowane ɓangare daga gare su ba ta fita (zuwa nẽman ilimi ba) dõmin su nẽmi ilimi ga fahimtar addĩni kuma dõmin su yi gargaɗi ga mutãnensu idan sun kõma zuwa gare su, tsammãninsu, sunã yin sauna? = --Qur'an 9:122
    O you who have believed, fight those adjacent to you of the disbelievers and let them find in you harshness. And know that Allah is with the righteous. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yãƙi waɗanda suke kusantar ku daga kãfirai. Kuma su sami tsanani daga gare ku. Kuma ku sani cẽwa Allah Yanã tãre da mãsu taƙawa. = --Qur'an 9:123
    And whenever a surah is revealed, there are among the hypocrites those who say, "Which of you has this increased faith?" As for those who believed, it has increased them in faith, while they are rejoicing. <> Kuma idan aka saukar da wata sũra, to, daga gare su akwai waɗanda suke cẽwa: "Wãne a cikinku wannan sũra ta ƙãra masa ĩmãni?" To amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sũ, sunã yin bushãra (da ita). = --Qur'an 9:124
    But as for those in whose hearts is disease, it has [only] increased them in evil [in addition] to their evil. And they will have died while they are disbelievers. <> Amma kuma waɗanda suke a cikin zukãtansu akwai cũta, to, tã ƙãra musu ƙazanta zuwa ga ƙazantarsu, kuma su mutu alhãlin kuwa sunã kãfirai. = --Qur'an 9:125
    Do they not see that they are tried every year once or twice but then they do not repent nor do they remember? <> Shin, bã su ganin cẽwa anã fitinar su a cikin kõwace shẽkara: Sau ɗaya kõ kuwa sau biyu, sa'an nan kuma bã su tũba, kuma ba su zama sunã tunãni ba? = --Qur'an 9:126
    And whenever a surah is revealed, they look at each other, [saying], "Does anyone see you?" and then they dismiss themselves. Allah has dismissed their hearts because they are a people who do not understand. <> "Kuma idan haƙĩƙa, aka saukar da wata sũra, sai sãshensu ya yi dũbi zuwa ga wani sãshe, (su ce): "Shin, wani mutum yanã ganin ku?" Sa'an nan kuma sai su jũya. Allah Ya jũyar da zukãtansu, dõmin, haƙĩƙa sũ mutãne ne, bã su fahimta. = --Qur'an 9:127
    There has certainly come to you a Messenger from among yourselves. Grievous to him is what you suffer; [he is] concerned over you and to the believers is kind and merciful. <> Lalle ne, haƙĩƙa, Manzo daga cikinku yã je muku. Abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa. Mai kwaɗayi ne sabõda ku. Ga muminai Mai tausayi ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 9:128
    But if they turn away, [O Muhammad], say, "Sufficient for me is Allah; there is no deity except Him. On Him I have relied, and He is the Lord of the Great Throne." <> To, idan sun jũya, sai ka ce: Ma'ishĩna Allah ne. Bãbu abin bautãwa fãce shi. A gare Shi nake dõgara. Kuma Shi ne Ubangijin Al'arshi mai girma. = --Qur'an 9:129
    Alif, Lam, Ra. These are the verses of the wise Book <> A. L̃.R. Waɗancan ãyõyin littãfi ne kyautatacce. = --Qur'an 10:1
    Have the people been amazed that We revealed [revelation] to a man from among them, [saying], "Warn mankind and give good tidings to those who believe that they will have a [firm] precedence of honor with their Lord"? [But] the disbelievers say, "Indeed, this is an obvious magician." <> Shin, yã zama abin mãmaki ga mutãne dõmin Mun yi wahayi zuwa ga wani namiji daga gare su cẽwa, "Ka yi gargaɗi ga mutãne kuma ka yi bushãra ga waɗanda suka yi ĩmãni da cẽwa: Lalle ne sunã da abin gabãtarwar gaskiya a wurin Ubangijinsu."Kãfirai suka ce: "Lalle ne wannan, haƙĩƙa, masihirci ne bayyananne." = --Qur'an 10:2
    Indeed, your Lord is Allah, who created the heavens and the earth in six days and then established Himself above the Throne, arranging the matter [of His creation]. There is no intercessor except after His permission. That is Allah, your Lord, so worship Him. Then will you not remember? <> Lalle Allah ne Ubangijinku wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwãna shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi Yanã gudãnar da al'amari. Bãbu wani macẽci fãce a bayan izninSa. Wannan ne Allah, Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Shin fa, ba ku tunãni? = --Qur'an 10:3
    To Him is your return all together. [It is] the promise of Allah [which is] truth. Indeed, He begins the [process of] creation and then repeats it that He may reward those who have believed and done righteous deeds, in justice. But those who disbelieved will have a drink of scalding water and a painful punishment for what they used to deny. <> zuwa gare Shi makõmarku take gabã ɗaya, wa'adin Allah gaskiya ne. Haƙĩƙa, Shi ne Yake fara halitta, sa'an nan kuma Ya mayar da ita dõmin Ya sãka wa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai da ãdalci, kuma waɗanda suka kãfirta sunã da abin sha daga ruwan zãfi, da azãba mai raɗaɗi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci. = --Qur'an 10:4
    It is He who made the sun a shining light and the moon a derived light and determined for it phases - that you may know the number of years and account [of time]. Allah has not created this except in truth. He details the signs for a people who know <> Shĩ ne wanda Ya sanya muku rãnã, babban haske, da watã mai haske, kuma Ya ƙaddara shi ga Manzilõli, dõmin ku san ƙidãyar shẽkaru da lissãfi. Allah bai halitta wannan ba, fãce da gaskiya, Yanã bayyana ãyõyi daki-daki dõmin mutãne waɗanda suke sani. = --Qur'an 10:5
    Indeed, in the alternation of the night and the day and [in] what Allah has created in the heavens and the earth are signs for a people who fear Allah <> Lalle ne a cikin sãɓãwar dare da yini, da abin da Allah Ya halitta a cikin sammai da ƙasa, haƙĩƙaakwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin taƙawa. = --Qur'an 10:6
    Indeed, those who do not expect the meeting with Us and are satisfied with the life of this world and feel secure therein and those who are heedless of Our signs <> Lalle ne waɗanda ba su ƙaunar gamuwa da Mũ, kuma suka yarda da rãyuwar dũniya kuma suka natsu da ita, da waɗanda suke gafalallu ne daga ãyõyinMu, = --Qur'an 10:7
    For those their refuge will be the Fire because of what they used to earn. <> Waɗannan matattãrarsu Jahannama ce sabõda abin da suka kasance sunã tsirfãtawa. = --Qur'an 10:8
    Indeed, those who have believed and done righteous deeds - their Lord will guide them because of their faith. Beneath them rivers will flow in the Gardens of Pleasure <> Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, Ubangijinsu Yanã shiryar da su sabõda ĩmãninsu, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, a cikin gidãjen Aljannar ni'ima. = --Qur'an 10:9
    Their call therein will be, "Exalted are You, O Allah," and their greeting therein will be, "Peace." And the last of their call will be, "Praise to Allah, Lord of the worlds!" <> Kiransu a cikinta, "TsarkinKa yã Allah!" Kuma gaisuwarsu a cikinta,"Salãmun", kuma ƙarshen kiransu, cẽwa, "Gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu." = --Qur'an 10:10
    And if Allah was to hasten for the people the evil [they invoke] as He hastens for them the good, their term would have been ended for them. But We leave the ones who do not expect the meeting with Us, in their transgression, wandering blindly <> Kuma dã Allah Yana gaggãwa ga mutãne da sharri kamar yadda Yake gaggauta musu da alhẽri, haƙĩƙa dã an hukunta ajalinsu zuwa gare su. Sabõda haka Munã barin waɗanda ba su ƙaunar gamuwa da Mu, a cikin kangararsu sunã ta ɗimuwa. = --Qur'an 10:11
    And when affliction touches man, he calls upon Us, whether lying on his side or sitting or standing; but when We remove from him his affliction, he continues [in disobedience] as if he had never called upon Us to [remove] an affliction that touched him. Thus is made pleasing to the transgressors that which they have been doing <> Kuma idan cũta ta shãfi mutum, sai ya kirãye Mu, yanã (kwance) ga sãshensa kõ kuwa zaune, kõ kuwa a tsaye. To, a lõkacin, da Muka kuranye cũtar daga gare shi, sai ya shũɗe kamar ɗai bai kirãye Mu ba zuwa ga wata cũta wadda ta shãfe shi. Kamar wannan ne aka ƙawãta ga maɓannata, abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 10:12
    And We had already destroyed generations before you when they wronged, and their messengers had come to them with clear proofs, but they were not to believe. Thus do We recompense the criminal people <> Kuma, haƙĩƙa, Mun halakar da al'ummomi daga gabãninku, a lõkacin da suka yi zãlunci, kuma manzanninsu suka jẽ musu da hujjõji bayyanannu, amma ba su kasance sunã ĩmãni ba. Kamar wannan ne, Muke sãkãwa ga mutãne mãsu laifi. = --Qur'an 10:13
    Then We made you successors in the land after them so that We may observe how you will do. <> Sa'an nan kuma Muka sanya ku mãsu mayẽwa a cikin ƙasa daga bãyansu, dõmin Mu ga yãya kuke aikatãwa. = --Qur'an 10:14
    And when Our verses are recited to them as clear evidences, those who do not expect the meeting with Us say, "Bring us a Qur'an other than this or change it." Say, [O Muhammad], "It is not for me to change it on my own accord. I only follow what is revealed to me. Indeed I fear, if I should disobey my Lord, the punishment of a tremendous Day." <> Kuma idan anã karatun ãyõyĩnMu bayyanannu a kansu, sai waɗanda bã su ƙaunar gawuwa da Mu, su ce: "Ka zo da wani Alƙur'ãni, wanin wannan, ko kuwa ka musunyã shi." Ka ce: "Bã ya kasancẽwa a gare ni in musanyã shi da kaina. Bã ni biyar kõme fãce abin da aka yiwo wahayi zuwa gare ni. Kuma, haƙĩƙa ni inã tsõro idan na sãɓã wa Ubangijina, ga azãbar wani yini mai girma." = --Qur'an 10:15
    Say, "If Allah had willed, I would not have recited it to you, nor would He have made it known to you, for I had remained among you a lifetime before it. Then will you not reason?" <> Ka ce: "Dã Allah Ya so dã ban karanta shi ba a kanku, kuma dã ban sanar da kũ ba gameda shi, dõmin lalle ne nã zauna a cikinku a zãmani mai tsawo daga gabãnin (fãra saukar) sa. Shin fa, bã ku hankalta?" = --Qur'an 10:16
    So who is more unjust than he who invents a lie about Allah or denies His signs? Indeed, the criminals will not succeed <> "Sabõda haka wãne ne mafi Zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kõ kuwa ya ƙaryata ãyõyinSa? Haƙĩƙa, mãsu laifibã su cin nasara!" = --Qur'an 10:17
    And they worship other than Allah that which neither harms them nor benefits them, and they say, "These are our intercessors with Allah " Say, "Do you inform Allah of something He does not know in the heavens or on the earth?" Exalted is He and high above what they associate with Him <> Kuma sunã bautã wa, baicin Allah, abin da bã ya cũtar dasu kuma bã ya amfãninsu, kuma sunã cẽwa: "Waɗannan ne macẽtanmu a wurin Allah."Ka ce: "Shin, kunã bai wa Allah lãbãri ne, ga abin da bai sani ba, a cikin sammai ko a cikin ƙasa? TsarkinSa ya tabbata kuma Yã ɗaukaka daga gabin da duk suke yin shirki da Shi." = --Qur'an 10:18
    And mankind was not but one community [united in religion], but [then] they differed. And if not for a word that preceded from your Lord, it would have been judged between them [immediately] concerning that over which they differ. <> Kuma mutãne ba su kasance ba fãce al'umma guda, sa'an nan kuma suka sãɓã wa jũna, kuma ba dõmin wata kalma ba wadda ta gabãta daga Ubangijinka, dã an yi hukunci a tsakãninsu a kan abin da yake a cikinsa suke sãɓã wa jũna. = --Qur'an 10:19
    And they say, "Why is a sign not sent down to him from his Lord?" So say, "The unseen is only for Allah [to administer], so wait; indeed, I am with you among those who wait." <> Kuma sunã cẽwa: "Don me ba a saukar da wata ãyã ba a gare shi, daga Ubangijinsa?" To, ka ce: "Abin sani kawai, gaibi ga Allah yake. Sai ku yi jira. Lalle ne nĩ, tãre da ku, inã daga mãsu jira." = --Qur'an 10:20
    And when We give the people a taste of mercy after adversity has touched them, at once they conspire against Our verses. Say, "Allah is swifter in strategy." Indeed, Our messengers record that which you conspire <> Kuma idan Muka ɗanɗanã wa mutãne wata rahama, a bãyan wata cũta tã shãfe su, sai gã su da mãkirci a cikin ãyõyinMu. Ka ce: "Allah ne mafi gaggãwar (sakamakon) mãkirci." Lalle ne ManzanninMu sunã rubũta abin da kuke yi na mãkirci. = --Qur'an 10:21
    It is He who enables you to travel on land and sea until, when you are in ships and they sail with them by a good wind and they rejoice therein, there comes a storm wind and the waves come upon them from everywhere and they assume that they are surrounded, supplicating Allah, sincere to Him in religion, "If You should save us from this, we will surely be among the thankful." <> Shĩ ne wanda Yake tafiyar da ku a cikin tudu da (kuma) tẽku, sai idan kun kasance a cikin jirãge, su gudãna tãre da su da iska mai dãɗi, kuma su yi farin ciki da ita, sai wata gũguwa ta je wa jirãgen, kuma tãguwar ruwa ta jẽ musu daga kõwane wuri, kuma su tabbata cẽwa sũ, an kẽwaye su, sai su kirãyi Allah, sunã mãsu tsarkake addini gare Shi, (sunã cẽwa): Lalle ne idanKa kuɓutar da mu daga wannan, haƙĩƙa munã kasancẽwa daga mãsu gõdiya. = --Qur'an 10:22
    But when He saves them, at once they commit injustice upon the earth without right. O mankind, your injustice is only against yourselves, [being merely] the enjoyment of worldly life. Then to Us is your return, and We will inform you of what you used to do. <> To, a lõkacin da Ya kuɓutar da su, sai, gã su sunã zãlunci a cikin ƙasa, bã da wanĩ hakki ba. Yã ku mutãne! Abin sani kawai, zãluncinku a kanku yake, a bisa rãyuwar dũniya. Sa'an nan kuma zuwa gare Mu makõmarku take, sa'an nan Mu bã ku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa, = --Qur'an 10:23
    The example of [this] worldly life is but like rain which We have sent down from the sky that the plants of the earth absorb - [those] from which men and livestock eat - until, when the earth has taken on its adornment and is beautified and its people suppose that they have capability over it, there comes to it Our command by night or by day, and We make it as a harvest, as if it had not flourished yesterday. Thus do We explain in detail the signs for a people who give thought. <> Abin sani kawai, misãlin rãyuwar dũniya kamar ruwa ne Muka saukar da shi daga sama, sa'an nan tsiron ƙasa ya garwaya da shi. Daga abin da mutãne da dabbõbi suke ci, har idan ƙasa ta riƙi zinãriyarta kuma ta yi ƙawa, kuma mutãnenta suka zaci cẽwa sũ ne mãsu ĩkon yi a kanta, sai umurninMu ya je mata da dare kõ kuma da rãna, sai Mu maishẽta girbabba kamar ba ta wadãta ba a jiya. Kamar wannan ne Muke rarrabe ãyõyi, daki-daki, ga mutãne waɗanda suke tunãni. = --Qur'an 10:24
    And Allah invites to the Home of Peace and guides whom He wills to a straight path <> Kuma Allah Yanã kira zuwa ga gidan aminci, kuma, Yanã shiryar da wanda Yake so zuwa ga tafarki madaidaici. = --Qur'an 10:25
    For them who have done good is the best [reward] and extra. No darkness will cover their faces, nor humiliation. Those are companions of Paradise; they will abide therein eternally <> Waɗanda suka kyautata yi, sunã da abu mai kyãwo kuma da ƙari, wata ƙũra bã ta rufe fuskõkinsu, kuma haka wani ƙasƙanci. waɗancan ne abokan Aljanna, sunã madawwama a cikinta. = --Qur'an 10:26
    But they who have earned [blame for] evil doings - the recompense of an evil deed is its equivalent, and humiliation will cover them. They will have from Allah no protector. It will be as if their faces are covered with pieces of the night - so dark [are they]. Those are the companions of the Fire; they will abide therein eternally. <> Kuma waɗanda suka yi tsirfar mũnanan ayyuka, sakamakon mummuna da kamarsa yake, kuma ƙasƙanci yanã rufe su. Bã su da wani matsari daga Allah, kamar an rufe fuskokinsu da guntãyen ƙirãruwa daga dare mai duhu. Waɗannan ne abõkan wuta, sunã madawwama a cikinta. = --Qur'an 10:27
    And [mention, O Muhammad], the Day We will gather them all together - then We will say to those who associated others with Allah, "[Remain in] your place, you and your 'partners.' " Then We will separate them, and their "partners" will say, "You did not used to worship us, <> Kuma a rãnar da Muke tãra su gabã ɗaya, sa'an nan kuma Mu ce wa waɗanda suka yi shirki, "Ku kãma matsayinku, kũ da abũbuwan shirkĩnku." Sa'an nan Mu rarrabe a tsakãninsu, kuma abũbuwan shirkinsu su ce: "Bã mũ kuka kasance kunã bauta wa ba." = --Qur'an 10:28
    And sufficient is Allah as a witness between us and you that we were of your worship unaware." <> "To, kuma Allah Yã isa zama shaida a tsakãninmu da tsakãninku. Haƙĩƙa mun kasance ba mu san kõme ba na bautãwarku a gare mu!" = --Qur'an 10:29
    There, [on that Day], every soul will be put to trial for what it did previously, and they will be returned to Allah, their master, the Truth, and lost from them is whatever they used to invent. <> A can ne kõwane rai yake jarraba abin da ya bãyar bãshi, kuma aka mayar da su zuwa ga Allah, Majiɓincinsu Tabbatacce kuma, abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa ya ɓace musu. = --Qur'an 10:30
    Say, "Who provides for you from the heaven and the earth? Or who controls hearing and sight and who brings the living out of the dead and brings the dead out of the living and who arranges [every] matter?" They will say, "Allah," so say, "Then will you not fear Him?" <> Ka ce: "Wãne ne Yake azurtã ku daga sama da ƙasa? Shin kõ kuma Wãne ne Yake mallakar jĩ da ganĩ, kuma Wãne ne Yake fitar da mai rai daga mamaci, kuma Ya fitar da mamaci daga mai rai, Kuma Wãne ne Yake shirya al'amari?" To, zã su ce: "Allah ne." To, ka ce: "Shin fa, bã zã ku yi taƙawa ba?" = --Qur'an 10:31
    For that is Allah, your Lord, the Truth. And what can be beyond truth except error? So how are you averted? <> To, Wancan ne Allah, Ubangijinku Tobbatacce. To, mẽne ne a bãyan gaskiya fãce ɓãta? To, yãya ake karkatar da ku? = --Qur'an 10:32
    Thus the word of your Lord has come into effect upon those who defiantly disobeyed - that they will not believe. <> Kamar wancan ne kalmar Ubangijinka, ta tabbata a kan waɗanda suka yi fãsiƙanci, cẽwa haƙĩƙa sũ, bã zã su yi ĩmãni ba. = --Qur'an 10:33
    Say, "Are there of your 'partners' any who begins creation and then repeats it?" Say, "Allah begins creation and then repeats it, so how are you deluded?" <> Ka ce: "Shin, daga abũbuwan shirkinku akwai wanda yake fãra halitta, sa'an nan kuma ya mayar da ita?" Ka ce: "Allah ne Yake fãra halitta, sa'an nan kuma Ya mayar da ita. To, yãyã akejũyar da ku?" = --Qur'an 10:34
    Say, "Are there of your 'partners' any who guides to the truth?" Say, "Allah guides to the truth. So is He who guides to the truth more worthy to be followed or he who guides not unless he is guided? Then what is [wrong] with you - how do you judge?" <> Ka ce: "Shin, daga abũbuwan shirkinku akwai wanda yake shiryarwa zuwa ga gaskiya?" Ka ce: "Allah ne Yake shiryarwa zuwa ga gaskiya. Shin fa, wanda Yake shiryarwa ne mafi cancantar a bi Shi, ko kuwa wanda bã ya shiryarwa fãce dai a shiryar da shi? To, mẽne ne a gare ku? Yãya kuke yin hukunci?" = --Qur'an 10:35
    And most of them follow not except assumption. Indeed, assumption avails not against the truth at all. Indeed, Allah is Knowing of what they do. <> Kuma mafi yawansu bã su biyar kõme fãce zato. Lalle ne zato bã ya wadãtar da kõme daga gaskiya. Lalle Allah ne Masani ga abin da suke aikatãwa. = --Qur'an 10:36
    And it was not [possible] for this Qur'an to be produced by other than Allah, but [it is] a confirmation of what was before it and a detailed explanation of the [former] Scripture, about which there is no doubt, from the Lord of the worlds. <> Kuma wannan Alƙur'ãni bai kasance ga a ƙirƙira shi ba daga wanin Allah, kuma amma shi gaskatawar wannan ne da yake a gabãninsa da bayãnin hukuncin littãffan Allah, Bãbu shakka a cikinsa, daga Ubangijin halittu yake. = --Qur'an 10:37
    Or do they say [about the Prophet], "He invented it?" Say, "Then bring forth a surah like it and call upon [for assistance] whomever you can besides Allah, if you should be truthful." <> Kõ sunã cẽwa, "Yã ƙirƙira shi?" Ka ce: "Ku zo da sũra guda misãlinsa, kuma ku kirãyi wanda kuka iya duka, baicin Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya." = --Qur'an 10:38
    Rather, they have denied that which they encompass not in knowledge and whose interpretation has not yet come to them. Thus did those before them deny. Then observe how was the end of the wrongdoers. <> Ã'a, sun ƙaryata game da abin da ba su kẽwaye da saninsa ba, kuma fassararsa ba ta riga ta jẽ musu ba. Kamar waɗancan ne waɗanda suke a gabãninsu. Sai ka dũba, yãya ãƙibar azzãlumai ta kasance? = --Qur'an 10:39
    And of them are those who believe in it, and of them are those who do not believe in it. And your Lord is most knowing of the corrupters <> Kuma daga cikinsu akwai wanda yake yin ĩmãni da Shi, kuma daga cikinsu akwai wanda bã ya yin ĩmãni da Shi. Kuma Ubangijinka ne Mafi sani ga maɓarnata. = --Qur'an 10:40
    And if they deny you, [O Muhammad], then say, "For me are my deeds, and for you are your deeds. You are disassociated from what I do, and I am disassociated from what you do." <> Kuma idan sun ƙaryata ka, to, ka ce: "Inã da aikĩna kuma kunã da aikinku, kũ kuɓutattu ne daga abin da nake aikatãwa kuma ni kuɓutacce ne daga abin da kuke aikatãwa." = --Qur'an 10:41
    And among them are those who listen to you. But can you cause the deaf to hear, although they will not use reason? <> Kuma daga cikinsu akwai waɗanda suke saurare zuwa gare ka. Shin fa, kai kana jiyar da kurma, kuma kõ dã sun kasance bã su hankalta? = --Qur'an 10:42
    And among them are those who look at you. But can you guide the blind although they will not [attempt to] see? <> Kuma daga cikinsu akwai wanda yake tsõkaci zuwa gare ka. Shin fa, kai kana shiryar da makãfi, kuma kõ dã sun kasance bã su gani? = --Qur'an 10:43
    Indeed, Allah does not wrong the people at all, but it is the people who are wronging themselves. <> Lalle ne Allah ba Ya zãluntar mutãne da kõme, amma mutãnen ne ke zãluntar kansu. = --Qur'an 10:44
    And on the Day when He will gather them, [it will be] as if they had not remained [in the world] but an hour of the day, [and] they will know each other. Those will have lost who denied the meeting with Allah and were not guided <> Kuma rãnar da Yake tãra su, kamar ba su zauna ba fãce sa'a guda daga yini. Sunã gãne jũna a tsakãninsu. Haƙĩƙa, waɗanda suka ƙaryata game da gamuwa da Allah sun yi hasãra. Kuma ba su kasance mãsu shiryuwa ba. = --Qur'an 10:45
    And whether We show you some of what We promise them, [O Muhammad], or We take you in death, to Us is their return; then, [either way], Allah is a witness concerning what they are doing <> Kuma imma dai, haƙĩƙa, Mu nũna maka sãshen abin da Muke yi musu alkawari, kõ kuwa Mu karɓi ranka, to, zuwa gare Mu makõmarsu take. Sa'an nan kuma Allah ne shaida a kan abin da suke aikatãwa. = --Qur'an 10:46
    And for every nation is a messenger. So when their messenger comes, it will be judged between them in justice, and they will not be wronged <> Kuma ga kõwace al'umma akwai Manzo. Sa'an nan idan Manzonsu ya je, sai a yi hukunci a tsakãninsu da ãdalci, kuma sũ, bã a zãluntar su. = --Qur'an 10:47
    And they say, "When is [the fulfillment of] this promise, if you should be truthful?" <> Kuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi zai auku, idan kun kasance mãsu gaskiya?" = --Qur'an 10:48
    Say, "I possess not for myself any harm or benefit except what Allah should will. For every nation is a [specified] term. When their time has come, then they will not remain behind an hour, nor will they precede [it]." <> Ka ce: "Ba na mallaka wa kaina wata cũta, haka kuma wani amfãni, sai abin da Allah Ya so. Ga kõwace al'umma akwai ajali, idan ajalinsu ya zo, to, bã zã su yi jinkiri daga gare shi ba, kõ dã sã'ã guda, kuma bã zã su gabãta ba." = --Qur'an 10:49
    Say, "Have you considered: if His punishment should come to you by night or by day - for which [aspect] of it would the criminals be impatient?" <> Ka ce: "Shin, kun gani, idan azãbarSa ta zo muku da dare ko da rãna? Mẽne ne daga gare shimãsu laifi suke nẽman gaggãwarsa?" = --Qur'an 10:50
    Then is it that when it has [actually] occurred you will believe in it? Now? And you were [once] for it impatient <> Shin sa'an nan kuma idan har ya auku, kun yi ĩmãni da shi? Ashe? Yanzu kuwa, alhãli kun kasance game da shi kunã nẽman gaggãwar aukuwarsa? = --Qur'an 10:51
    Then it will be said to those who had wronged, "Taste the punishment of eternity; are you being recompensed except for what you used to earn?" <> Sa'an nan kuma aka ce ga waɗanda suka yi zãlunci, "Ku ɗanɗani azãbar dawwama! Shin, anã sãka muku fãce da abin da kuka kasance kuna aikatãwa?" = --Qur'an 10:52
    And they ask information of you, [O Muhammad], "Is it true?" Say, "Yes, by my Lord. Indeed, it is truth; and you will not cause failure [to Allah]." <> Kuma sunã tambayar ka: Shin gaskiya ne? Ka ce: "Ĩ, ina rantsuwa da Ubangijĩna. Lalle gaskiya ne, kuma ba ku zama mãsu buwãya ba." = --Qur'an 10:53
    And if each soul that wronged had everything on earth, it would offer it in ransom. And they will confide regret when they see the punishment; and they will be judged in justice, and they will not be wronged <> Kuma dã kõwane rai wanda ya yi zãlunci yã mallaki duka abin da yake a cikin ƙasa, to, dã yã yi fansa da shi. Kuma suka dinga nadãma a lõkacin da suka ga azãba. Sa'an nan aka yi hukunci a tsakãninsu da ãdalci, kuma bã zã a zãlunce su ba. = --Qur'an 10:54
    Unquestionably, to Allah belongs whatever is in the heavens and the earth. Unquestionably, the promise of Allah is truth, but most of them do not know <> To! Haƙĩƙa Allah Ya mallaki abin da yake a cikin sammai da ƙasa. To! Haƙĩƙa wa'adin Allah gaskiya ne. Amma kuma mafi yawansu ba su sani ba. = --Qur'an 10:55
    He gives life and causes death, and to Him you will be returned <> Shi ne Yake rãyarwa kuma Yake matarwa. Kuma zuwa gare Shi ne ake mayar da ku. = --Qur'an 10:56
    O mankind, there has to come to you instruction from your Lord and healing for what is in the breasts and guidance and mercy for the believers. <> Ya ku mutãne! Lalle wa'azi yã jẽ muku daga Ubangijinku, da waraka ga abin da yake a cikin ƙirãza, da shiriya da rahama ga muminai. = --Qur'an 10:57
    Say, "In the bounty of Allah and in His mercy - in that let them rejoice; it is better than what they accumulate." <> Ka ce: "Da falalar Allah da rahamarSa. Sai su yi farin ciki da wannan." Shĩ ne mafi alhẽri daga abin da suke tãrãwa. = --Qur'an 10:58
    Say, "Have you seen what Allah has sent down to you of provision of which you have made [some] lawful and [some] unlawful?" Say, "Has Allah permitted you [to do so], or do you invent [something] about Allah?" <> Ka ce: "Shin, kun ga abin da Allah Ya saukar sabõda ku na arziki, sai kuka sanya hukuncin haramci da halacci a gare shi?" Ka ce: "Shin, Allah ne Ya yi muku izni, ko ga Allah kuke ƙirƙirãwar ƙarya?" = --Qur'an 10:59
    And what will be the supposition of those who invent falsehood about Allah on the Day of Resurrection? Indeed, Allah is full of bounty to the people, but most of them are not grateful." <> Kuma mẽne ne zaton waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, a Rãnar ¡iyãma? Lalle haƙĩƙa, Allah Ma, abũcin falala ne a kan mutãne, amma kuma mafi yawansu bã su gõdẽwa. = --Qur'an 10:60
    And, [O Muhammad], you are not [engaged] in any matter or recite any of the Qur'an and you [people] do not do any deed except that We are witness over you when you are involved in it. And not absent from your Lord is any [part] of an atom's weight within the earth or within the heaven or [anything] smaller than that or greater but that it is in a clear register. <> Kuma ba ka kasance a cikin wani sha'ani ba, kuma ba ka karanta wani abin karatu daga gare shi ba, kuma ba ku aikata wani aiki ba, fãce Mun kasance Halarce a lõkacin da kuke zubuwa a cikinsa. Kuma wani ma'aunin zarra bã zai yi nĩsa ba daga Ubangijinka a cikin ƙasa, haka kuma a cikin sama, kuma bãbu wanda yake mafi ƙaranci daga haka, kuma bãbu mafi girma, fãce yana a cikin littãfi bayyananne. = --Qur'an 10:61
    Unquestionably, [for] the allies of Allah there will be no fear concerning them, nor will they grieve <> To, Lalle ne masõyan Allah bãbu tsõro a kansu, kuma bã zã su kasance sunã yin baƙin ciki ba. = --Qur'an 10:62
    Those who believed and were fearing Allah <> Waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka kasance sunã yin taƙawa. = --Qur'an 10:63
    For them are good tidings in the worldly life and in the Hereafter. No change is there in the words of Allah. That is what is the great attainment. <> Sunã da bushãra a cikin rãyuwar dũniya da ta Lãhira. Bãbu musanyãwa ga kalmõmin Allah. Wancan shi ne babban rabo mai girma, = --Qur'an 10:64
    And let not their speech grieve you. Indeed, honor [due to power] belongs to Allah entirely. He is the Hearing, the Knowing. <> Kada maganarsu ta sanya ka a cikin baƙin ciki. Lalle ne alfarma ga Allah take gaba ɗaya. Shi ne Mai jĩ, Masani. = --Qur'an 10:65
    Unquestionably, to Allah belongs whoever is in the heavens and whoever is on the earth. And those who invoke other than Allah do not [actually] follow [His] "partners." They follow not except assumption, and they are not but falsifying <> To! Haƙĩƙa Allah Yanã da mulkin wanda ke a cikin sammai da wanda ke a cikin ƙasa kuma waɗanda suke kiran wanin Allah, bã su biyar waɗansu abõkan tarẽwa (ga Allah a MulkinSa). Bã su biyar kõme fãce zato. Kuma ba su zama ba fãce sunã ƙiri faɗi kawai. = --Qur'an 10:66
    It is He who made for you the night to rest therein and the day, giving sight. Indeed in that are signs for a people who listen. <> Shĩ ne wanda Ya sanya muku dare, dõmin ku natsu a cikinsa, da yini mai sanya a yi gani. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda sukẽ ji. = --Qur'an 10:67
    They have said, "Allah has taken a son." Exalted is He; He is the [one] Free of need. To Him belongs whatever is in the heavens and whatever is in the earth. You have no authority for this [claim]. Do you say about Allah that which you do not know? <> Suka ce: "Allah Ya riƙi ɗa." Tsarkinsa yã tabbata! Shi ne wadãtacce Yanã da mallakar abin da yake, a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, A wurinku bãbu wani dalĩli game da wannan! Shin, kunã faɗar abin da ba ku sani ba game da Allah? = --Qur'an 10:68
    Say, "Indeed, those who invent falsehood about Allah will not succeed." <> Ka ce: "Haƙĩƙa waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, bã zã su ci nasara ba." = --Qur'an 10:69
    [For them is brief] enjoyment in this world; then to Us is their return; then We will make them taste the severe punishment because they used to disbelieve <> Jin dãɗi ne a cikin dũniya, sa'an nan kuma makõmarsu zuwa gare Mu take, sa'an nan Mu ɗanɗana musu azãba mai tsanani sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci. = --Qur'an 10:70
    And recite to them the news of Noah, when he said to his people, "O my people, if my residence and my reminding of the signs of Allah has become burdensome upon you - then I have relied upon Allah. So resolve upon your plan and [call upon] your associates. Then let not your plan be obscure to you. Then carry it out upon me and do not give me respite. <> Kuma ka karanta musu lãbãrin Nũhu, a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, "Ya mutãnẽna! Idan matsayĩna da tunãtarwata ameda ãyõyin Allah sun kasance sun yi nauyi a kanku, to, ga Allah na dõgara. Sai ku tãra al'amarinku, kũ da abũbuwan shirkinku, sa'annan kuma kada al'amarinku ya kasance rufaffe a kanku, sa'an nan kuma ku kashe ni, kada ku yi mini jinkiri." = --Qur'an 10:71
    And if you turn away [from my advice] then no payment have I asked of you. My reward is only from Allah, and I have been commanded to be of the Muslims." <> "Kuma idan kuka jũya bãya, to, ban tambaye ku wata ijãra ba. ljãrata ba ta zama ba fãce daga Allah, kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa." = --Qur'an 10:72
    And they denied him, so We saved him and those with him in the ship and made them successors, and We drowned those who denied Our signs. Then see how was the end of those who were warned. <> Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan Muka kuɓutar da shi da wanda yake tãre da shi, a cikin jirgi, kuma Muka sanya su mãsu mayẽwa, kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata ãyõyinMu. Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance. = --Qur'an 10:73
    Then We sent after him messengers to their peoples, and they came to them with clear proofs. But they were not to believe in that which they had denied before. Thus We seal over the hearts of the transgressors <> Sa'an nan kuma Muka aika waɗansu Manzanni daga bãyansa zuwa ga mutãnensu, suka jẽmusu da hujjõji bayyanannu, to, ba su kasance zã su yi ĩmãni ba sabõda sun ƙaryata shi a gabani. Kamar wannan ne Muke rufẽwa a kan zukãtan mãsu ta'addi. = --Qur'an 10:74
    Then We sent after them Moses and Aaron to Pharaoh and his establishment with Our signs, but they behaved arrogantly and were a criminal people <> Sa'an nan kuma a bãyansu Muka aika Mũsa da Hãrũna zuwa ga Fir'auna da mashãwartansa, tãre da ãyõyinMu. Sai suka kangara kuma sun kasance mutãne mãsu laifi. = --Qur'an 10:75
    So when there came to them the truth from Us, they said, "Indeed, this is obvious magic." <> Sa'an nan a lõkacin da gaskiya ta jẽ musu daga gare Mu, suka ce: "Wannan haƙĩƙa sihiri ne bayyananne." = --Qur'an 10:76
    Moses said, "Do you say [thus] about the truth when it has come to you? Is this magic? But magicians will not succeed." <> Mũsã ya ce: " Shin, kunã cẽwa ga gaskiya a lõkacin data zo muku? Shin, sihiri ne wannan? Lalle masihirci, bã ya cin nasara." = --Qur'an 10:77
    They said, "Have you come to us to turn us away from that upon which we found our fathers and so that you two may have grandeur in the land? And we are not believers in you." <> Suka ce: "Shin, ka zo mana ne dõmin ka jũyar da mu daga abin da muka iske ubanninmu a kansa, kuma girma ya kasance gare ku, ku biyu a cikin ƙasa? Bã zã mu zama mãsu ĩmãni ba sabõda ku." = --Qur'an 10:78
    And Pharaoh said, "Bring to me every learned magician." <> Kuma Fir'auna ya ce: "Ku zo mini da dukan masihirci, masani." = --Qur'an 10:79
    So when the magicians came, Moses said to them, "Throw down whatever you will throw." <> To, a lõkacin da masihirta suka je, Mũsã ya ce musu,"Ku jẽfa abin da kuke jẽfãwa." = --Qur'an 10:80
    And when they had thrown, Moses said, "What you have brought is [only] magic. Indeed, Allah will expose its worthlessness. Indeed, Allah does not amend the work of corrupters. <> To, a lõkacin da suka jẽfa, Mũsa ya ce: "Abin da kuka zo da shi sihiri ne. Lalle ne Allah zai ɓãta shi. Haƙĩƙa Allah bã Ya gyãra aikin maɓarnata. = --Qur'an 10:81
    And Allah will establish the truth by His words, even if the criminals dislike it." <> "Kuma Allah Yanã tabbatar da gaskiya da kalmõminSa, kõ dã mãsu laifi sun ƙi." = --Qur'an 10:82
    But no one believed Moses, except [some] youths among his people, for fear of Pharaoh and his establishment that they would persecute them. And indeed, Pharaoh was haughty within the land, and indeed, he was of the transgressors <> Sa'an nan bãbu wanda ya yi ĩmãni da Mũsa fãce zuriya daga mutãnensa, a kan tsõron kada Fir'auna da shũgabanninsu su fitinẽ su. Lalle, haƙĩƙa, Fir'auna marinjãyi ne a cikin ƙasa, kuma lalle shĩ haƙĩƙa, yanã daga mãsu ɓarna. = --Qur'an 10:83
    And Moses said, "O my people, if you have believed in Allah, then rely upon Him, if you should be Muslims." <> Kuma Mũsã ya ce: "Yã kũ mutãnena! Idan kun kasance kun yi ĩmãni da Allah, to, a gare Shi sai ku dõgara, idan kun kasance Musulmi." = --Qur'an 10:84
    So they said, "Upon Allah do we rely. Our Lord, make us not [objects of] trial for the wrongdoing people <> Sai suka ce: "Ga Allah muka dõgara. Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanyã mu fitina ga mutãne azzãlumai. = --Qur'an 10:85
    And save us by Your mercy from the disbelieving people." <> "Kuma Ka kuɓutar da mu dõmin RahamarKa, daga mutãne kãfirai." = --Qur'an 10:86
    And We inspired to Moses and his brother, "Settle your people in Egypt in houses and make your houses [facing the] qiblah and establish prayer and give good tidings to the believers." <> Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã da ɗan'uwansa, cẽwa: Kũ biyu, ku zaunar da mutãnenku a Masar a cikin wasu gidãje. Kuma ku sanya gidãjenku su fuskanci Alƙibla, kuma ku tsayar da salla. Kuma ku bãyar da bushãra ga mãsu ĩmãni. = --Qur'an 10:87
    And Moses said, "Our Lord, indeed You have given Pharaoh and his establishment splendor and wealth in the worldly life, our Lord, that they may lead [men] astray from Your way. Our Lord, obliterate their wealth and harden their hearts so that they will not believe until they see the painful punishment." <> Sai MũSã ya ce: "Yã Ubangijinmu! Haƙĩƙa Kai ne Ka bai wa Fir'auna da majalisarsa ƙawa da dũkiyõyi a cikin rãyuwar dũniya, yã Ubangijinmu, dõmin su ɓatar (damutãne) daga hanyarKa. Yã Ubangijinmu! Ka shãfe a kan dũkiyarsu kuma Ka yi ɗauri a kan zukãtansu yadda bã zã su yi ĩmãni ba har su ga azãba mai raɗaɗi." = --Qur'an 10:88
    [Allah] said, "Your supplication has been answered." So remain on a right course and follow not the way of those who do not know." <> (Allah) Yã ce: "Lalle ne an karɓi addu'arku. Sai ku daidaitu kuma kada ku bi hanyar waɗanda ba su sani ba." = --Qur'an 10:89
    And We took the Children of Israel across the sea, and Pharaoh and his soldiers pursued them in tyranny and enmity until, when drowning overtook him, he said, "I believe that there is no deity except that in whom the Children of Israel believe, and I am of the Muslims." <> Kuma Muka ƙẽtãrar da Banĩ Isrã'ila tẽku sai Fir'auna da rundunarsa suka bĩ su bisa ga zãlunci da ƙẽtare haddi, har a lõkacin da nutsẽwa ta riske shi ya ce: "Nã yi ĩmãni cẽwa, haƙĩƙa, bãbu abin bautawa fãce wannan da Banũ Isrã'il suka yi ĩmãni da Shi, kumanĩ, ina daga Musulmi." = --Qur'an 10:90
    Now? And you had disobeyed [Him] before and were of the corrupters? <> Ashe! A yanzu! Alhãli kuwa, haƙĩƙa ka sãɓa a gabãni, kuma ka kasance daga mãsu ɓarna? = --Qur'an 10:91
    So today We will save you in body that you may be to those who succeed you a sign. And indeed, many among the people, of Our signs, are heedless <> To, a yau Munã kuɓutar da kai game da jikinka, dõmin ka kasance ãyã ga waɗanda suke a bãyanka. Kuma lalle ne mãsu yawa daga mutãne, haƙĩƙa, gafalallu ne ga ãyõyinMu. = --Qur'an 10:92
    And We had certainty settled the Children of Israel in an agreeable settlement and provided them with good things. And they did not differ until [after] knowledge had come to them. Indeed, your Lord will judge between them on the Day of Resurrection concerning that over which they used to differ <> Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun zaunar da Banĩ Isrã'ilamazaunar gaskiya kuma Muka arzũta su daga abũbuwa mãsu dãɗi. Sa'an nan ba su sãɓa ba har ilmi ya jẽ musu. Lalle ne Ubangijinka Yanã yin hukunci a tsakãninsu a Rãnar Kiyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna. = --Qur'an 10:93
    So if you are in doubt, [O Muhammad], about that which We have revealed to you, then ask those who have been reading the Scripture before you. The truth has certainly come to you from your Lord, so never be among the doubters. <> To, idan ka kasance a cikin shakka daga abin da Muka saukar zuwa gare ka, sai ka tambayi waɗanda suke karatun Littãfi daga gabaninka. Lalle ne, haƙĩƙa, gaskiya tã jẽ maka daga Ubangijinka dõmin haka kada ka kasance daga mãsu kõkanto. = --Qur'an 10:94
    And never be of those who deny the signs of Allah and [thus] be among the losers. <> Kuma kada ka kasance daga waɗanda suke ƙaryatãwa game da ãyõyin Allah, har ka kasance daga mãsu hasãra. = --Qur'an 10:95
    Indeed, those upon whom the word of your Lord has come into effect will not believe, <> Lalle ne waɗanda kalmar Ubangijinka ta wajaba a kansu, bã zã su yi ĩmãni ba. = --Qur'an 10:96
    Even if every sign should come to them, until they see the painful punishment. <> Kuma kõ dã kõwace ãyã ta jẽ musu, sai sun ga azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 10:97
    Then has there not been a [single] city that believed so its faith benefited it except the people of Jonah? When they believed, We removed from them the punishment of disgrace in worldly life and gave them enjoyment for a time. <> To, dõmin me wata alƙarya ba ta kasance ta yi ĩmãniba har ĩmãninta ya amfãne ta, fãcemutãnen Yũnus? A lõkacin da suka yi ĩmãni, Munjanye azãbar wulãkanci daga gare su a cikin rãyuwar dũniya. Kuma Muka jiyar da su dãɗi zuwa wani lõkaci. = --Qur'an 10:98
    And had your Lord willed, those on earth would have believed - all of them entirely. Then, [O Muhammad], would you compel the people in order that they become believers? <> Kuma dã Ubangijinka Ya so, dã waɗanda suke a cikin ƙasa sun yi ĩmãni dukansu gabã ɗaya. Shin, kai kanã tĩlasta mutãnene har su kasance mãsu ĩmãni? = --Qur'an 10:99
    And it is not for a soul to believe except by permission of Allah, and He will place defilement upon those who will not use reason. <> Kuma ba ya kasancẽwa ga wani rai ya yi ĩmãni fãce da iznin Allah, kuma (Allah) Yanã sanya ƙazanta a kan waɗanda bã su yin hankali. = --Qur'an 10:100
    Say, "Observe what is in the heavens and earth." But of no avail will be signs or warners to a people who do not believe <> Ka ce: "Ku dũbi abin da yake cikin sammai da ƙasa."Kuma ãyõyi da gargaɗi bã su wadãtarwa ga mutãne waɗanda bã su yin ĩmãni. = --Qur'an 10:101
    So do they wait except for like [what occurred in] the days of those who passed on before them? Say, "Then wait; indeed, I am with you among those who wait." <> To, Shin sunã jiran wani abu fãce kamar misãlin kwãnukan waɗanda suka shũɗe daga gabãninsu? Ka ce: "Ku yi jira! Lalle nĩ tãre da ku, inã daga mãsu jira." = --Qur'an 10:102
    Then We will save our messengers and those who have believed. Thus, it is an obligation upon Us that We save the believers <> Sa'an nan kuma Munã kuɓutar da manzanninMu da waɗanda suka yi ĩmãni, kamar wannan ne, tabbatacce ne a gare Mu, Mu kuɓutar da mãsu ĩmãni. = --Qur'an 10:103
    Say, [O Muhammad], "O people, if you are in doubt as to my religion - then I do not worship those which you worship besides Allah; but I worship Allah, who causes your death. And I have been commanded to be of the believers <> Ka ce: "Yã kũ mutãne! Idan kun kasance a cikin kõkanto daga addinĩna, to bã ni bauta wa, waɗanda kuke, bautã wa, baicin Allah, kuma amma ina bauta wa Allah wanda Yake karɓar rãyukanku. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu ĩmãni." = --Qur'an 10:104
    And [commanded], 'Direct your face toward the religion, inclining to truth, and never be of those who associate others with Allah; <> "Kuma (an ce mini): Ka tsayar da fuskarka ga addini, kanã karkatl zuwa ga gaskiya, kuma kada ka kasance daga mãsu shirka. = --Qur'an 10:105
    And do not invoke besides Allah that which neither benefits you nor harms you, for if you did, then indeed you would be of the wrongdoers.'" <> "Kuma kada ka kirãyi, baicin Allah, abin da bã ya amfãnin ka kuma bã ya cũtar ka. To, idan ka aikata haka, sa'an nan lalle kai, a lõkacin, kanã daga mãsu zãlunci." = --Qur'an 10:106
    And if Allah should touch you with adversity, there is no remover of it except Him; and if He intends for you good, then there is no repeller of His bounty. He causes it to reach whom He wills of His servants. And He is the Forgiving, the Merciful <> Kuma idan Allah Ya shãfe ka da wata cũta, to, bãbu mai yãyẽ ta fãce shi, kuma idan Yanã nufin ka da wani alhẽri, to, bãbumai mayar da falalarSa. Yanã sãmun wanda Yake so daga cikin bãyinSa da shi. Kuma Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai. = --Qur'an 10:107
    Say, "O mankind, the truth has come to you from your Lord, so whoever is guided is only guided for [the benefit of] his soul, and whoever goes astray only goes astray [in violation] against it. And I am not over you a manager." <> Ka ce: "Yã ku mutãne! Lalle ne gaskiya, ta zo muku daga Ubangijinku. To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai, kuma wanda ya ɓace yana ɓacewa ne a kansa kawai. Kuma ban zama wakĩli a kanku ba." = --Qur'an 10:108
    And follow what is revealed to you, [O Muhammad], and be patient until Allah will judge. And He is the best of judges. <> Kuma ka bi abin da ake yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ka yi haƙuri har Allah Ya yi hukunci. Kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci. = --Qur'an 10:109
    Alif, Lam, Ra. [This is] a Book whose verses are perfected and then presented in detail from [one who is] Wise and Acquainted. <> A. L̃.R. Littãfi ne an kyautata ãyõyinsa, sa'an nan an bayyanã su daki-daki, daga wurin Mai hikima, Mai ƙididdigewa. = --Qur'an 11:1
    [Through a messenger, saying], "Do not worship except Allah. Indeed, I am to you from Him a warner and a bringer of good tidings," <> Kada ku bautã wa kõwa fãce Allah. Lalle ne ni a gare ku mai gargaɗi ne kuma mai bushãrã daga gare Shi. = --Qur'an 11:2
    And [saying], "Seek forgiveness of your Lord and repent to Him, [and] He will let you enjoy a good provision for a specified term and give every doer of favor his favor. But if you turn away, then indeed, I fear for you the punishment of a great Day. <> Kuma ku nẽmi gãfara gun Ubangijinku. Sa'an nan ku tũba zuwa gare Shi, Ya jiyar da ku dãɗi, jiyarwa mai kyau zuwa ga ajali ambatacce, kuma Ya bai wa dukkan ma'abucin, girma girmansa. Amma idan kun jũya, to, lalle nĩ, inã tsõron azãbar yini mai girma a kanku. = --Qur'an 11:3
    To Allah is your return, and He is over all things competent." <> Zuwa ga Allah makõmarku take, kuma Shĩ a kan kõmeMai ĩkon yi ne. = --Qur'an 11:4
    Unquestionably, they the disbelievers turn away their breasts to hide themselves from Him. Unquestionably, [even] when they cover themselves in their clothing, Allah knows what they conceal and what they declare. Indeed, He is Knowing of that within the breasts. <> To, lalle sũ sunã karkatar da ƙirjinsu dõmin su ɓõye daga gare shi. To, a lõkacin da suke lulluɓẽwa da tufãfinsu Yanã sanin abin da suke ɓoyewa da abin da suke bayyanãwa. Lalle Shi Masani ne ga abin da yake a cikin ƙirãzã. = --Qur'an 11:5
    And there is no creature on earth but that upon Allah is its provision, and He knows its place of dwelling and place of storage. All is in a clear register. <> Kuma bãbu wata dabba a cikin ƙasa fãce ga Allah arzikinta yake, kuma Yanã sanin matabbatarta da ma'azarta, duka sunã cikin littãfi bayyananne. = --Qur'an 11:6
    And it is He who created the heavens and the earth in six days - and His Throne had been upon water - that He might test you as to which of you is best in deed. But if you say, "Indeed, you are resurrected after death," those who disbelieve will surely say, "This is not but obvious magic." <> Kuma shi ne wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwanaki shida, kuma Al'arshinSa ya kasance akan ruwa, dõmin Ya jarrabã ku, wannan ne daga cikinku mafi kyãwon aiki. Kuma haƙĩƙa idan ka ce: "Lalle kũ waɗanda ake tãyarwa ne a bãyan mutuwa," haƙĩƙa waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: "Wannan bai zama ba fãce sihiri bayyananne." = --Qur'an 11:7
    And if We hold back from them the punishment for a limited time, they will surely say, "What detains it?" Unquestionably, on the Day it comes to them, it will not be averted from them, and they will be enveloped by what they used to ridicule. <> Kuma lalle ne idan Mun jinkirta da azãba gare su zuwa ga wani lõkaci ƙidãyayye, haƙĩƙa sunãcẽwa me yake tsare ta? To, a rãnar da zã ta je musu, ba ta zama abin karkatarwa ba daga gare su. Kuma abin da suka kasance suna yin izgili da shi, yã wajaba a kansu. = --Qur'an 11:8
    And if We give man a taste of mercy from Us and then We withdraw it from him, indeed, he is despairing and ungrateful. <> Kuma lalle ne idan Mun ɗanɗana wa mutum wata rahama daga gare Mu, sa'an nan kuma Muka zãre ta daga gare shi, lalle ne shĩ, hakĩka, mai yanke tsammãnine, mai yawan kãfrci. = --Qur'an 11:9
    But if We give him a taste of favor after hardship has touched him, he will surely say, "Bad times have left me." Indeed, he is exultant and boastful - <> Kuma lalle ne idan Mun ɗanɗana masa ni'ima a bãyan cũta ta shãfe shi, Yana cẽwa mũnanan halaye sun tafi daga wurina. Lalle shi mai farin ciki ne, mai alfahari. = --Qur'an 11:10
    Except for those who are patient and do righteous deeds; those will have forgiveness and great reward. <> Sai waɗanda suka yi haƙuri kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai. Waɗannan sunã da gãfara da lãda mai girma. = --Qur'an 11:11
    Then would you possibly leave [out] some of what is revealed to you, or is your breast constrained by it because they say, "Why has there not been sent down to him a treasure or come with him an angel?" But you are only a warner. And Allah is Disposer of all things. <> Sabõda haka tsammãninka kai mai barin sãshen abin da aka yi wahayi zuwa gare ka ne, kuma mai ƙuntata ƙirjinka da shi ne dõmin sun ce: "Dõmin me ba a saukar masa da wata taska ba, kõ kuma Malã'ika ya zo tãre de shi?" Kai mai gargaɗi ne kawai. Kuma Allah ne wakili a kan kõme. = --Qur'an 11:12
    Or do they say, "He invented it"? Say, "Then bring ten surahs like it that have been invented and call upon [for assistance] whomever you can besides Allah, if you should be truthful." <> Kõ sunã cewa: "Yã ƙirƙira shi ne."Ka ce: "Sai ku zo da sũrõri gõma misãlinsa ƙirƙirarru, kuma ku kirãyi wanda kuke iyãwa, baicin Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya." = --Qur'an 11:13
    And if they do not respond to you - then know that the Qur'an was revealed with the knowledge of Allah and that there is no deity except Him. Then, would you [not] be Muslims? <> To, idan ba su amsa muku ba, to, ku sani cẽwa an saukar da shi kawai ne da sanin Allah, kuma cẽwa bãbu abin bauta wa fãce Shi. To, shin, kũ mãsu sallamãwa ne?, = --Qur'an 11:14
    Whoever desires the life of this world and its adornments - We fully repay them for their deeds therein, and they therein will not be deprived. <> Wanda ya kasance yã yi nufin rãyuwar dũniya da ƙawarta, Munã cika musu ayyukansu zuwa gare su a cikinta, kuma a cikinta bã zã a rage su ba. = --Qur'an 11:15
    Those are the ones for whom there is not in the Hereafter but the Fire. And lost is what they did therein, and worthless is what they used to do. <> Waɗannan ne waɗanda bã su da kõme a cikin Lãhira fãce wuta, kuma abin da suka sanã'anta a cikinta (dũniya) yã ɓãci, kuma abin da suka kasance sunã aikatãwa ɓãtacce ne. = --Qur'an 11:16
    So is one who [stands] upon a clear evidence from his Lord [like the aforementioned]? And a witness from Him follows it, and before it was the Scripture of Moses to lead and as mercy. Those [believers in the former revelations] believe in the Qur'an. But whoever disbelieves in it from the [various] factions - the Fire is his promised destination. So be not in doubt about it. Indeed, it is the truth from your Lord, but most of the people do not believe. <> Shin, wanda ya kasance a kan hujja bayyananna daga Ubangijinsa, kuma wata shaida tanã biyar sa daga gare Shi, kuma a gabãninsa akwai littãfin Mũsãabin kõyi da rahama? Waɗannan sunã yin ĩmãni da shi, kuma wanda ya kãfirta da shi daga ƙungiyõyi, to, wutã ce makõmarsa. Sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga gare shi. Lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinka, amma kuma mafi yawan mutãne bã su yin ĩmãni. = --Qur'an 11:17
    And who is more unjust than he who invents a lie about Allah? Those will be presented before their Lord, and the witnesses will say, "These are the ones who lied against their Lord." Unquestionably, the curse of Allah is upon the wrongdoers. <> Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah? Waɗannan anã gitta su ga Ubangijinsu, kuma mãsu shaida su ce: "Waɗannan ne suka yi ƙarya ga Ubangijinsu. To, la'anar Allah ta tabbata a kan azzãlumai." = --Qur'an 11:18
    Who averted [people] from the way of Allah and sought to make it [seem] deviant while they, concerning the Hereafter, were disbelievers. <> Waɗanda suke kangẽwa daga hanyar Allah kuma sunã nẽman ta karkace, kuma sũ ga Lãhira sunã kãfirta. = --Qur'an 11:19
    Those were not causing failure [to Allah] on earth, nor did they have besides Allah any protectors. For them the punishment will be multiplied. They were not able to hear, nor did they see. <> Waɗannan ne ba su kasance mabuwãya ba a cikin ƙasa, kuma waɗansu masõya ba su kasance ba a gare su, baicin Allah. Anã ninka musu azãba, ba su kasance sunã iya ji ba, kuma ba su kasance sunã gani ba. = --Qur'an 11:20
    Those are the ones who will have lost themselves, and lost from them is what they used to invent. <> Waɗannan ne wɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirawa ya ɓace musu. = --Qur'an 11:21
    Assuredly, it is they in the Hereafter who will be the greatest losers. <> Bãbu makawã cẽwa, haƙĩƙa, sũ a lãhira, sũ ne mafi hasãra. = --Qur'an 11:22
    Indeed, they who have believed and done righteous deeds and humbled themselves to their Lord - those are the companions of Paradise; they will abide eternally therein. <> Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi tawãlu'i zuwa ga Ubangijinsu, waɗannan ne abõkan Aljanna, sunã madawwama a cikinta. = --Qur'an 11:23
    The example of the two parties is like the blind and deaf, and the seeing and hearing. Are they equal in comparison? Then, will you not remember? <> Misãlin ɓangaren biyu kamar makãho ne da kurmã, da mai gani da mai ji. Shin, sunã daidaita ga misãli? Ashe, bã ku yin tunãni? = --Qur'an 11:24
    And We had certainly sent Noah to his people, [saying], "Indeed, I am to you a clear warner <> Kuma haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutanensa, (ya ce): "Lalle ne ni, a gare ku mai gargaɗi bayyananne ne." = --Qur'an 11:25
    That you not worship except Allah. Indeed, I fear for you the punishment of a painful day." <> "Kada ku bautã wa kõwa fãce Allah. Lalle nĩ, inã jin tsõron azãbar yini mai raɗaɗi a kanku." = --Qur'an 11:26
    So the eminent among those who disbelieved from his people said, "We do not see you but as a man like ourselves, and we do not see you followed except by those who are the lowest of us [and] at first suggestion. And we do not see in you over us any merit; rather, we think you are liars." <> Sai mashãwarta waɗanda suka kãfirta, daga mutãnensa, suka ce: "Bã mu ganin ka fãce mutum kake kamarmu, kuma ba mu ganin wani ya bĩ ka fãce waɗanda suke sũ ƙasƙantattunmu ne marasa tunani. Kuma bã mu ganin wata falalã agare ka a kanmu. Ã'a, Munã zaton ku maƙaryata ne." = --Qur'an 11:27
    He said, "O my people have you considered: if I should be upon clear evidence from my Lord while He has given me mercy from Himself but it has been made unapparent to you, should we force it upon you while you are averse to it? <> Ya ce: "Ya mutãnena! Shin, kun gani idan na kasance a kan wata hujja bayyananna daga Ubangijina, kuma Yã bã ni wata Rahama daga wurinSa, Sa'an nan aka rufe ta (ita Rahamar) daga gare ku, shin, zã mu tĩlasta mukuita, alhãli kuwa kũ mãsu ƙi gare ta ne? = --Qur'an 11:28
    And O my people, I ask not of you for it any wealth. My reward is not but from Allah. And I am not one to drive away those who have believed. Indeed, they will meet their Lord, but I see that you are a people behaving ignorantly. <> "Kuma yã mutãnena! Bã zan tambaye ku wata dũkiya ba akansa, ijãrata ba ta zama ba, fãce daga Allah, kuma ban zama mai kõrar waɗanda suka yĩ ĩmãni ba. Haƙĩƙa sũ, mãsu haɗuwa da Ubangijinsu ne, kuma amma ni, inã ganin ku mutãne ne jãhilai." = --Qur'an 11:29
    And O my people, who would protect me from Allah if I drove them away? Then will you not be reminded? <> "Kuma ya mutãnena! Wãne ne yake taimakõna daga Allah idan na kõre su? Ashe, bã ku tunãni?" = --Qur'an 11:30
    And I do not tell you that I have the depositories [containing the provision] of Allah or that I know the unseen, nor do I tell you that I am an angel, nor do I say of those upon whom your eyes look down that Allah will never grant them any good. Allah is most knowing of what is within their souls. Indeed, I would then be among the wrongdoers." <> "Kuma bã ni ce muku a wurĩna taskõkin Allah suke kuma bã inã sanin gaibi ba ne. Kuma ba inã cẽwa ni Malã'ika ba ne. Kuma ba ni cẽwa ga waɗanda idãnunku suke wulãkantãwa, Allah bã zai bã su alhẽri ba. Allah ne Mafi sani ga abin da yake cikin zukatansu. Lalle ne ni, idan (nã yi haka) dã ina daga cikin azzalumai." = --Qur'an 11:31
    They said, "O Noah, you have disputed us and been frequent in dispute of us. So bring us what you threaten us, if you should be of the truthful." <> Suka ce: "Yã Nũhu, lalle ne kã yi jayayya da mu, sa'an nan kã yawaita yi mana jidãli, to, ka zõ mana da abin da kake yi mana wa'adi idan kã kasance daga mãsu gaskiya." = --Qur'an 11:32
    He said, "Allah will only bring it to you if He wills, and you will not cause [Him] failure. <> Ya ce: "Allah kawai ne Yake zo muku da shi idan Ya so. Kuma ba ku zama mabuwãya ba." = --Qur'an 11:33
    And my advice will not benefit you - although I wished to advise you - If Allah should intend to put you in error. He is your Lord, and to Him you will be returned." <> "Kuma nasĩhãta bã zã ta amfãne ku ba, idan nã yi nufin in yi muku nasĩha, idan Allah Yakasance Yanã nufin Ya halaka ku. Shĩ ne Ubangijinku, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku." = --Qur'an 11:34
    Or do they say [about Prophet Muhammad], "He invented it"? Say, "If I have invented it, then upon me is [the consequence of] my crime; but I am innocent of what [crimes] you commit." <> Ko sunã cẽwa: (Nũhu) ya ƙirƙira shi. Ka ce: "Idan nĩ (Nũhu) na ƙirƙira shi to, laifĩnã a kaina yake, kuma nĩ mai barrantã ne daga abin da kuke yi na laifi." = --Qur'an 11:35
    And it was revealed to Noah that, "No one will believe from your people except those who have already believed, so do not be distressed by what they have been doing. <> Kuma aka yi wahayi zuwa ga Nũhu cẽwa: Lalle ne bãbu mai yin ĩmãni daga mutãnenka fãce wanda ya riga ya yi ĩmãnin, sabõdahaka kada ka yi baƙin ciki da abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 11:36
    And construct the ship under Our observation and Our inspiration and do not address Me concerning those who have wronged; indeed, they are [to be] drowned." <> Kuma ka sassaƙa jirgi da kyau a kan idanunMu da wahayinMu, kuma kada ka yi Mini magana a cikin sha'anin waɗanda suka kãfirta, lalle ne sũ, waɗanda akenutsarwa ne. = --Qur'an 11:37
    And he constructed the ship, and whenever an assembly of the eminent of his people passed by him, they ridiculed him. He said, "If you ridicule us, then we will ridicule you just as you ridicule. <> Kuma Yanã sassaƙa jirgin cikin natsuwa, kuma a kõ yaushe waɗansu shugabanni daga mutãnensa suka shũɗe a gabansa, sai su yi izgili gare shi. Ya ce: "Idan kun yi izgili gare mu, to, haƙĩƙa mũ mã zã mu yi izgili gare ku, kamar yadda kuke yin izgili. = --Qur'an 11:38
    And you are going to know who will get a punishment that will disgrace him [on earth] and upon whom will descend an enduring punishment [in the Hereafter]." <> "Sa'an nan da sannu zã ku san wanda azãba zã ta zo masa, ta wulakantã shi (a dũniya), kuma wata azãba zaunanna ta sauka a kansa (a Lãhira)." = --Qur'an 11:39
    [So it was], until when Our command came and the oven overflowed, We said, "Load upon the ship of each [creature] two mates and your family, except those about whom the word has preceded, and [include] whoever has believed." But none had believed with him, except a few. <> Har a lõkacin da umurninMu ya je, kuma tandã ta ɓulɓula. Muka ce: "Ka ɗauka, a cikinta, daga kõme, ma'aura biyu, da kuma iyalanka, fãce wanda magana ta gabãta a kansa, da wanda ya yi ĩmãni." Amma kuma bãbu waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi fãce kaɗan." = --Qur'an 11:40
    And [Noah] said, "Embark therein; in the name of Allah is its course and its anchorage. Indeed, my Lord is Forgiving and Merciful." <> Kuma ya ce: "Ku hau a cikinta, da sũnan Allah magudãnarta da matabbatarta. Lalle ne Ubangijĩna, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai." = --Qur'an 11:41
    And it sailed with them through waves like mountains, and Noah called to his son who was apart [from them], "O my son, come aboard with us and be not with the disbelievers." <> Kuma ita tanã gudãna da su a cikin tãguwar ruwa kamai duwãtsu, sai Nũhu ya kirãyi ɗansa alhãli, kuwa ya kasance can wuri mai nĩsa. "Yã ƙaramin ɗãnã! zo ka hau tãre da mu, kuma kada ka kasance tãre da kãfirai!" = --Qur'an 11:42
    [But] he said, "I will take refuge on a mountain to protect me from the water." [Noah] said, "There is no protector today from the decree of Allah, except for whom He gives mercy." And the waves came between them, and he was among the drowned. <> Ya ce: "Zan tattara zuwa ga wani dũtse ya tsare ni daga ruwan." (Nũhu) ya ce: "Bãbu mai tsarẽwa a yau daga umurnin Allah fãce wanda Ya yi wa rahama." Sai taguwar ruwa ta shãmakace a tsakãninsu, sai ya kasance daga waɗanda aka nutsar. = --Qur'an 11:43
    And it was said, "O earth, swallow your water, and O sky, withhold [your rain]." And the water subsided, and the matter was accomplished, and the ship came to rest on the [mountain of] Judiyy. And it was said, "Away with the wrongdoing people." <> Kuma aka ce: "Yã ƙasa! Ki haɗiye ruwanki, kuma yã sama! Ki kãme."Kuma aka faƙar da ruwan kuma aka hukunta al'amarin, kuma Jirgin ya daidaita a kan Jũdiyyi, kuma aka ce: "Nĩsa ya tabbata ga mutãne azzãlumai." = --Qur'an 11:44
    And Noah called to his Lord and said, "My Lord, indeed my son is of my family; and indeed, Your promise is true; and You are the most just of judges!" <> Kuma Nũhu ya kira Ubangijinsa, sa'an nan ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne ɗãna na daga iyãlĩna! Kuma haƙĩƙa wa'adinKa gaskiya ne, kuma Kai ne Mafi hukuncin mãsu yin hukunci." = --Qur'an 11:45
    He said, "O Noah, indeed he is not of your family; indeed, he is [one whose] work was other than righteous, so ask Me not for that about which you have no knowledge. Indeed, I advise you, lest you be among the ignorant." <> Ya ce: "Yã Nũhu! Lalle ne shi bã ya a ciki iyãlanka, lalle ne shĩ, aiki ne wanda ba na ƙwarai ba, sabõda haka kada ka tambaye Ni abin da bã ka da ilmi a kansa. Haƙĩƙa, Nĩ Inã yi maka gargaɗi kada ka kasance daga jãhilai." = --Qur'an 11:46
    [Noah] said, "My Lord, I seek refuge in You from asking that of which I have no knowledge. And unless You forgive me and have mercy upon me, I will be among the losers." <> Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, inã nẽman tsari gare Ka da in tambaye Ka abin da bã ni da wani ilmi a kansa. Idan ba Ka gãfarta mini ba, kuma Ka yi mini rahama, zan kasance daga mãsu hasãra." = --Qur'an 11:47
    It was said, "O Noah, disembark in security from Us and blessings upon you and upon nations [descending] from those with you. But other nations [of them] We will grant enjoyment; then there will touch them from Us a painful punishment." <> Aka ce: "Ya Nũhu! Ka sauka da aminci da, a gare Mu da albarka a kanka, kuma rahama ta tabbata a kan waɗansu al'ummõmi daga waɗanda suke tãre da kai. Da waɗansu al'ummõmi da zã Mu jiyar da su dãɗi, sa'an nan kuma azãba mai raɗaɗi ta shafe su daga gare Mu." = --Qur'an 11:48
    That is from the news of the unseen which We reveal to you, [O Muhammad]. You knew it not, neither you nor your people, before this. So be patient; indeed, the [best] outcome is for the righteous. <> Waccan ƙissa tanã daga lãbãran gaibi, Munã yin wahayinsu zuwa gare ka (Muhammadu). Ba ka kasance kanã sanin su ba, haka kuma mutãnenka ba su sani ba daga gabãnin wannan. Sai ka yi haƙuri. Lalle ne ãƙiba tanã ga mãsu taƙawa, = --Qur'an 11:49
    And to 'Aad [We sent] their brother Hud. He said, "O my people, worship Allah; you have no deity other than Him. You are not but inventors [of falsehood]. <> Kuma zuwa ga Ãdãwa, (Mun aika) ɗan'uwansu Hũdu. Ya ce: "Yã kũ mutãnena! Ku bauta wa Allah. Ba ku da wani abin bautãwa fãce Shi. Ba ku kasance ba fãce kunã mãsu ƙirƙirãwa. = --Qur'an 11:50
    O my people, I do not ask you for it any reward. My reward is only from the one who created me. Then will you not reason? <> "Yã ku mutãnena! Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa, ijãrata ba ta zama ba, fãce ga wanda Ya ƙãga halittata. Shin fa, bã ku hankalta?" = --Qur'an 11:51
    And O my people, ask forgiveness of your Lord and then repent to Him. He will send [rain from] the sky upon you in showers and increase you in strength [added] to your strength. And do not turn away, [being] criminals." <> "Kuma, ya mutãnena! Ku nẽmi Ubangijinku gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare Shi, zai saki sama a kanku, tanã mai yawan zubar da ruwa, kuma Ya ƙãra muku wani ƙarfi ga ƙarfinku. Kuma kada ku jũya kunã mãsu laifi." = --Qur'an 11:52
    They said, "O Hud, you have not brought us clear evidence, and we are not ones to leave our gods on your say-so. Nor are we believers in you. <> Suka ce: "Yã Hũdu! Ba ka zo mana da wata hujja bayyananna ba, kuma ba mu zama mãsu barin abũbuwan bautawarmu ba dõmin maganarka, kuma ba mu zama mãsu yin ĩmãni da kai ba." = --Qur'an 11:53
    We only say that some of our gods have possessed you with evil." He said, "Indeed, I call Allah to witness, and witness [yourselves] that I am free from whatever you associate with Allah <> "Bã mu cẽwa, sai dai kurum sashen abũbuwan bautawarmu ya sãme ka da cũtar hauka." Yace: "Lalle ne nĩ, inã shaida waAllah, kuma ku yi shaidar cẽwa" lalle ne nĩ mai barranta ne dagb abin da kuke yin shirki da shi." = --Qur'an 11:54
    Other than Him. So plot against me all together; then do not give me respite. <> "Baicin Allah: Sai ku yi mini kaidi gabã ɗaya, sa'an nan kuma kada ku yi mini jinkiri." = --Qur'an 11:55
    Indeed, I have relied upon Allah, my Lord and your Lord. There is no creature but that He holds its forelock. Indeed, my Lord is on a path [that is] straight." <> "Haƙĩƙa, ni na dõgara ga Allah, Ubangijĩna kuma Ubangijinku. Bãbu wata dabba fãce Shi ne Mai riko ga kwarkwaɗarta. Haƙĩƙa, Ubangijĩna Yanã (kan) tafarki madaidaici." = --Qur'an 11:56
    But if they turn away, [say], "I have already conveyed that with which I was sent to you. My Lord will give succession to a people other than you, and you will not harm Him at all. Indeed my Lord is, over all things, Guardian." <> "To! Idan kun jũya, haƙĩƙa, nã iyar muku abin da aka aiko ni da shi zuwa gare ku. Kuma Ubangijĩna Yanã musanya waɗansu mutãne, waɗansunku su maye muku. Kuma bã ku cũtar Sa da kõme. Lalle Ubangijina a kan dukkan kõme, Matsari ne." = --Qur'an 11:57
    And when Our command came, We saved Hud and those who believed with him, by mercy from Us; and We saved them from a harsh punishment. <> Kuma a lõkacin da umurninmu ya je, Muka kuɓutar da Hũdu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sabõdawata rahama daga gare Mu. Kuma Muka kuɓutr da su daga azãba mai kauri. = --Qur'an 11:58
    And that was 'Aad, who rejected the signs of their Lord and disobeyed His messengers and followed the order of every obstinate tyrant. <> Haka Ãdãwa suka kasance, sun yi musun ãyõyin Ubangijinsu, kuma sun sãɓa wa ManzanninSa, kuma sun bi umurnin dukan mai girman kai, makangari. = --Qur'an 11:59
    And they were [therefore] followed in this world with a curse and [as well] on the Day of Resurrection. Unquestionably, 'Aad denied their Lord; then away with 'Aad, the people of Hud. <> Kuma an biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyada Rãnar Kiyãma. To! Lalle ne Ãdãwa sun kãfirta da Ubangijinsu. To, Nĩsa ya tabbata ga Ãdãwa, mutãnen Hũdu! = --Qur'an 11:60
    And to Thamud [We sent] their brother Salih. He said, "O my people, worship Allah; you have no deity other than Him. He has produced you from the earth and settled you in it, so ask forgiveness of Him and then repent to Him. Indeed, my Lord is near and responsive." <> Kuma zuwa ga Samũdãwa (an aika) ɗan'uwansu Sãlihu. Ya ce: "Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa fãce Shi. Shĩ ne Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma Ya sanya ku mãsu yin kyarkyara a cikinta. Sai ku nẽme Shi gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare Shi. Lalle Ubangijina Makusanci ne Mai karɓãwa." = --Qur'an 11:61
    They said, "O Salih, you were among us a man of promise before this. Do you forbid us to worship what our fathers worshipped? And indeed we are, about that to which you invite us, in disquieting doubt." <> Suka ce: "Ya Sãlihu! Haƙĩƙa, kã kasance a cikinmu, wanda ake fatan wani alhẽri da shi a gabãnin wannan. Shin kana hana mu bauta wa abin da ubanninmu suke bauta wa? Kuma haƙĩƙa mũ, munã cikin shakka daga abin da kake kiran mu gare shi, mai sanya kõkanto." = --Qur'an 11:62
    He said, "O my people, have you considered: if I should be upon clear evidence from my Lord and He has given me mercy from Himself, who would protect me from Allah if I disobeyed Him? So you would not increase me except in loss. <> Ya ce: "Ya mutãnẽna! Kun gani? Idan na kasance a kan hujja bayyananna daga Ubangijina, kuma Ya bã ni rahama daga gare Shi, to, wane ne zai taimake ni daga Allah idan nã sãɓa Masa? Sa'an nan bã zã ku ƙãre ni da kõme ba fãce hasãra." = --Qur'an 11:63
    And O my people, this is the she-camel of Allah - [she is] to you a sign. So let her feed upon Allah 's earth and do not touch her with harm, or you will be taken by an impending punishment." <> "Kuma ya mutãnena! wannan rãƙumar Allah ce, tanã ãyã a gare ku. Sai ku bar ta ta ci a cikin ƙasar Allah, kuma kada ku shãfe ta da wata cũta kar azãba makusanciya ta kãma ku." = --Qur'an 11:64
    But they hamstrung her, so he said, "Enjoy yourselves in your homes for three days. That is a promise not to be denied." <> Sai suka sõke ta. Sai ya ce: "Kuji dãɗi a cikin gidãjenku kwãna uku. Wannan wa'adi ne bã abin ƙaryatãwa ba." = --Qur'an 11:65
    So when Our command came, We saved Salih and those who believed with him, by mercy from Us, and [saved them] from the disgrace of that day. Indeed, it is your Lord who is the Powerful, the Exalted in Might. <> To, a lõkacin da umurninMu ya je, muka kuɓutar da Sãlihu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sabõda wata rahama daga gare Mu, kuma daga wulãkancin rãnar nan. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMai ƙarfi, Mabuwãyi. = --Qur'an 11:66
    And the shriek seized those who had wronged, and they became within their homes [corpses] fallen prone <> Sai tsãwa ta kãma waɗanda suka yi zãlunci, sai suka wãyi gari sunã guggurfãne a cikin gidãjensu. = --Qur'an 11:67
    As if they had never prospered therein. Unquestionably, Thamud denied their Lord; then, away with Thamud. <> Kamar dai ba su zauna a cikinta ba. To! Lalle ne samũdãwa sun kãfirce wa Ubangijinsu. To, Nĩsa ya tabbata ga Samũdãwa. = --Qur'an 11:68
    And certainly did Our messengers come to Abraham with good tidings; they said, "Peace." He said, "Peace," and did not delay in bringing [them] a roasted calf. <> Kuma haƙĩƙa, manzanninMu sun je wa Ibrãhim da bushãra suka ce: "Aminci." Ya ce: "Aminci (ya tabbata a gare ku)." Sa'an nan bai yi jinkiri ba ya je da maraƙi ƙawãtacce. = --Qur'an 11:69
    But when he saw their hands not reaching for it, he distrusted them and felt from them apprehension. They said, "Fear not. We have been sent to the people of Lot." <> Sa'an nan a lõkacin da ya ga hannayensu bã su sãduwa zuwa gare shi (maraƙin), sai ya yi ƙyãmarsu, kuma ya ji tsõronsu. Suka ce, "Kada kaji tsõro lalle ne mũ, an aiko mu ne zuwa ga mutãnen Lũɗu" = --Qur'an 11:70
    And his Wife was standing, and she smiled. Then We gave her good tidings of Isaac and after Isaac, Jacob. <> Kuma mãtarsa tanã tsaye. Ta yi dãriya. Sai Muka yi mata bushãra (da haihuwar) Is'hãƙa, kuma a bayan Is'hãƙa, Yãƙũbu. = --Qur'an 11:71
    She said, "Woe to me! Shall I give birth while I am an old woman and this, my husband, is an old man? Indeed, this is an amazing thing!" <> Sai ta ce: "Yã kaitõna! Shin, zan haihu ne alhãli kuwa inã tsõhuwa, kuma ga mijĩna tsõho ne? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu ne mai ban mãmãki." = --Qur'an 11:72
    They said, "Are you amazed at the decree of Allah? May the mercy of Allah and His blessings be upon you, people of the house. Indeed, He is Praiseworthy and Honorable." <> Suka ce: "Shin kinã mãmaki ne daga al'amarin Allah? Rahamar Allah da albarkarSa su tabbata a kanku, ya mutãnen babban gida! Lalle ne Shĩ abin gõdewa ne, Mai girma." = --Qur'an 11:73
    And when the fright had left Abraham and the good tidings had reached him, he began to argue with Us concerning the people of Lot. <> To, a lõkacin da firgita ta tafi daga Ibrãhĩm, kuma bushãra tã je masa, Yanã mai jayayya a gare Mu, sabõda mutãnen Lũɗu! = --Qur'an 11:74
    Indeed, Abraham was forbearing, grieving and [frequently] returning [to Allah]. <> Lalle Ibrãhĩm, haƙĩƙa mai haƙuri ne, mai yawan addu'a, mai tawakkali. = --Qur'an 11:75
    [The angels said], "O Abraham, give up this [plea]. Indeed, the command of your Lord has come, and indeed, there will reach them a punishment that cannot be repelled." <> Ya Ibrãhĩm! Ka bijira daga wannan. Lalle shi, haƙĩƙa, umurnin Ubangijinka ne ya zo, kuma lalle ne sũ, abin da yake mai je musu azãba ce wadda bã a iya hanãwa. = --Qur'an 11:76
    And when Our messengers, [the angels], came to Lot, he was anguished for them and felt for them great discomfort and said, "This is a trying day." <> Kuma a lõkacin da manzanninMu suka je wa Lũɗu aka ɓãta masa rai game da su, ya, ƙuntata rai sabõda su. Ya ce: "Wannan yini ne mai tsananin masĩfa." = --Qur'an 11:77
    And his people came hastening to him, and before [this] they had been doing evil deeds. He said, "O my people, these are my daughters; they are purer for you. So fear Allah and do not disgrace me concerning my guests. Is there not among you a man of reason?" <> Kuma mutãnensa suka je masa sunã gaggãwa zuwa gare shi, kuma a gabãni, sun kasance sunã aikatãwar mũnãnan ayyuka. Ya ce: "Yã mutãnẽna! waɗannan, 'yã'yã na sũ ne mafiya tsarki a gare ku. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku wulãkantã ni a cikin bãƙĩna. Shin, bãbu wani namiji shiryayye daga gare ku?" = --Qur'an 11:78
    They said, "You have already known that we have not concerning your daughters any claim, and indeed, you know what we want." <> Suka ce: "Lalle, haƙĩƙa kã sani, bã mu da wani hakki a cikin 'ya'yanka, kuma lalle kai haƙĩƙa, kanã sane da abin da muke nufi." = --Qur'an 11:79
    He said, "If only I had against you some power or could take refuge in a strong support." <> Ya ce: "Dã dai inã da wani ƙarfi game da ku, kõ kuwa inã da gõyon bãya daga wani rukuni mai ƙarfi?" = --Qur'an 11:80
    The angels said, "O Lot, indeed we are messengers of your Lord; [therefore], they will never reach you. So set out with your family during a portion of the night and let not any among you look back - except your wife; indeed, she will be struck by that which strikes them. Indeed, their appointment is [for] the morning. Is not the morning near?" <> (Manzannin) Suka ce: "Yã Lũɗu! Lalle mũ, manzannin Ubangijinka ne. Bã zã su iya sãduwa zuwa gare ka ba. Sai ka yi tafiyarka a wani yankin dare da iyãlinka, kuma kada wani daga gare ku ya waiwaya fãce mãtarka. Lalle ne abin da ya same su mai sãmunta ne. Lalle wa'adinsu lõkacin sãfiya ne. Shin lõkacin sãfiya bã kusa ba ne?" = --Qur'an 11:81
    So when Our command came, We made the highest part [of the city] its lowest and rained upon them stones of layered hard clay, [which were] <> Sa'an nan a lõkacin da umurninMu ya je, Muka sanya na samanta ya zama na ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu a kanta (ƙasar Lũɗu) daga taɓocũrarre. = --Qur'an 11:82
    Marked from your Lord. And Allah 's punishment is not from the wrongdoers [very] far. <> Alamtacce a wurin Ubangijinka. Kuma ita (ƙasar Lũɗu) ba ta zama mai nĩsa ba daga azzãlumai (kuraishãwa). = --Qur'an 11:83
    And to Madyan [We sent] their brother Shu'ayb. He said, "O my people, worship Allah; you have no deity other than Him. And do not decrease from the measure and the scale. Indeed, I see you in prosperity, but indeed, I fear for you the punishment of an all-encompassing Day. <> Kuma zuwa ga Madyana (Mun aika) ɗan'uwansu Shu'aibu. Ya ce: "Ya Mutãnena! Ku bauta wa Allah. Ba ku da wani abin bautãwa fãce shi kuma kada ku rage mũdu da sikẽli. Lalle nĩ, inã ganin ku da wadãta. Kuma lalle inã ji muku tsõron azãbar yini mai kẽwayẽwa." = --Qur'an 11:84
    And O my people, give full measure and weight in justice and do not deprive the people of their due and do not commit abuse on the earth, spreading corruption. <> "Ya mutãnẽna! Ku cika mũdu da sikẽli da ãdalci, kuma kada ku naƙasta wa mutãne kãyansu, kuma kada ku yi ɓarnã a cikin ƙasa kunã mãsu fasãdi." = --Qur'an 11:85
    What remains [lawful] from Allah is best for you, if you would be believers. But I am not a guardian over you." <> "Falalar Allah mai wanzuwa ita ce mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance muminai, kuma ni bã mai tsaro ne a kanku ba." = --Qur'an 11:86
    They said, "O Shu'ayb, does your prayer command you that we should leave what our fathers worship or not do with our wealth what we please? Indeed, you are the forbearing, the discerning!" <> Suka ce: "Yã Shu'aibu! Shin sallarka ce take umurtar ka ga mu bar abin da ubanninmu suke bautãwa, kõ kuwa mu bar aikata abin da muke so a cikin dũkiyõyinmu? Lalle, haƙĩƙa kai ne mai haƙuri shiryayye!" = --Qur'an 11:87
    He said, "O my people, have you considered: if I am upon clear evidence from my Lord and He has provided me with a good provision from Him...? And I do not intend to differ from you in that which I have forbidden you; I only intend reform as much as I am able. And my success is not but through Allah. Upon him I have relied, and to Him I return. <> Ya ce: "Ya mutãnena! Kun gani idan no kasance a kan hujja bayyananniya daga Ubangijina, kuma Ya azurta nĩ da arzikimai kyãwo daga gare Shi? Kuma bã ni nufin in sãɓa muku zuwa ga abin da nake hana ku daga gare shi. Bã ni nufin kõme fãce gyãrã, gwargwadon da na sãmi dãma. Kuma muwãfaƙãta ba ta zama ba fãce daga Allah. A gare shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi na wakkala." = --Qur'an 11:88
    And O my people, let not [your] dissension from me cause you to be struck by that similar to what struck the people of Noah or the people of Hud or the people of Salih. And the people of Lot are not from you far away. <> "Kuma ya mutãnena! Kada sãɓa mini ya ɗauke ku ga misãlin abin da ya sãmi mutãnen Nũhu kõ kuwa mutãnen Hũdu kõ kuwa mutãnen Sãlihu ya sãme ku. Mutãnen Lũɗu ba su zama a wuri mai nĩsa ba daga gare ku." = --Qur'an 11:89
    And ask forgiveness of your Lord and then repent to Him. Indeed, my Lord is Merciful and Affectionate." <> "Kuma ku nẽmi Ubangijinku gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare shi. Lalle Ubangijĩna Mai Jin ƙai ne, Mai nũna sõyayya." = --Qur'an 11:90
    They said, "O Shu'ayb, we do not understand much of what you say, and indeed, we consider you among us as weak. And if not for your family, we would have stoned you [to death]; and you are not to us one respected." <> Suka ce: "Yã Shu'aibu! Bã mu fahimta da yawa daga abin da kake faɗi, kuma munã ganin ka mai rauni a cikinmu. Kuma bã dõmin jama'arka ba dã mun jẽfe ka, sabõda ba ka zama mai daraja a gunmu ba." = --Qur'an 11:91
    He said, "O my people, is my family more respected for power by you than Allah? But you put Him behind your backs [in neglect]. Indeed, my Lord is encompassing of what you do. <> Ya ce: "Ya mutãnena! Ashe, jama'ãta ce mafi daraja a gare ku daga Allah, kuma kun riƙẽ Shi a bãyanku abin jẽfarwa? Lallene Ubangijĩna Mai kẽwayẽwa nega abin da kuke aikatãwa." = --Qur'an 11:92
    And O my people, work according to your position; indeed, I am working. You are going to know to whom will come a punishment that will disgrace him and who is a liar. So watch; indeed, I am with you a watcher, [awaiting the outcome]." <> "Kuma ya mutãnena! Ku yi aiki a kan hãlinku. Lalle nĩmai aiki ne. Da sannu zã ku san wãne ne azãba zã ta zo masa, ta wulakanta shi, kuma wãne ne maƙaryaci. Kuma ku yi jiran dãko, lalle ni mai dãko ne tãre da ku." = --Qur'an 11:93
    And when Our command came, We saved Shu'ayb and those who believed with him, by mercy from Us. And the shriek seized those who had wronged, and they became within their homes [corpses] fallen prone <> Kuma a lõkacin da umurninMu yã je, Muka kuɓutar da Shu'aibu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sabõda wata rahama daga gare, Mu. Kuma tsãwa ta kama waɗanda suka yi zãlunci. Sai suka wãyi gari guggurfãne a cikin gidãjensu. = --Qur'an 11:94
    As if they had never prospered therein. Then, away with Madyan as Thamud was taken away. <> Kamar ba su zaunã ba a cikinsu. To, halaka ta tabbata ga Madyana kamar yadda Samũdãwa suka halaka. = --Qur'an 11:95
    And We did certainly send Moses with Our signs and a clear authority <> Kuma haƙĩƙa Mun aiki Mũsã da ãyõyinMu, da dalĩli bayyananne. = --Qur'an 11:96
    To Pharaoh and his establishment, but they followed the command of Pharaoh, and the command of Pharaoh was not [at all] discerning. <> Zuwa ga Fir'auna da majalisarsa. Sai suka bi umurnin Fir'auna, amma al'amarin Fir'auna bai zama shiryayye ba. = --Qur'an 11:97
    He will precede his people on the Day of Resurrection and lead them into the Fire; and wretched is the place to which they are led. <> Yanã shũgabantar mutãnensa a Rãnar Kiyãma, har ya tuzgar da su a wuta. Kuma tir da irin tuzgãwarsu. = --Qur'an 11:98
    And they were followed in this [world] with a curse and on the Day of Resurrection. And wretched is the gift which is given. <> Kuma aka biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyada Rãnar Kiyãma. Tir da kyautar da ake yi musu. = --Qur'an 11:99
    That is from the news of the cities, which We relate to you; of them, some are [still] standing and some are [as] a harvest [mowed down]. <> Wancan Yanã daga lãbãran alƙaryõyi. Munã bã ka lãbãrinsu, daga gare su akwai wanda ke tsaye da kuma girbabbe. = --Qur'an 11:100
    And We did not wrong them, but they wronged themselves. And they were not availed at all by their gods which they invoked other than Allah when there came the command of your Lord. And they did not increase them in other than ruin. <> Kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun zãlunci kansu sa'an nan abũbuwan bautawarsu waɗanda suke kiran su, baicin Allah, ba su wadãtar musu kõme ba a lõkacin da umurnin Ubangijinka ya je, kuma (gumãkan) ba su ƙãra musu wani abu ba fãce hasãra. = --Qur'an 11:101
    And thus is the seizure of your Lord when He seizes the cities while they are committing wrong. Indeed, His seizure is painful and severe. <> Kuma kamar wancan ne kãmun Ubangijinka, idan Ya kãma alƙaryõyi alhãli kuwa sunã mãsu zãlunci. Lalle kamũnSa mai raɗaɗi ne, mai tsanani. = --Qur'an 11:102
    Indeed in that is a sign for those who fear the punishment of the Hereafter. That is a Day for which the people will be collected, and that is a Day [which will be] witnessed. <> Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga wanda ya ji tsõron azãbar Lãhira. Wancan yini ne wanda ake tãra mutãne a cikinsa kuma wancan yini ne abin halarta. = --Qur'an 11:103
    And We do not delay it except for a limited term. <> Ba Mu jinkirtã shi ba fãce dõmin ajali ƙidãyayye. = --Qur'an 11:104
    The Day it comes no soul will speak except by His permission. And among them will be the wretched and the prosperous. <> Rãnar da za ta zo wani rai ba ya iya magana fãce da izninSa. Sa'an nan daga cikinsu akwai shaƙiyyi da mai arziki. = --Qur'an 11:105
    As for those who were [destined to be] wretched, they will be in the Fire. For them therein is [violent] exhaling and inhaling. <> To, amma waɗanda suka yi shaƙãwa, to, sunã a cikin wuta. Sunã mãsu ƙãra da shẽka acikinta. = --Qur'an 11:106
    [They will be] abiding therein as long as the heavens and the earth endure, except what your Lord should will. Indeed, your Lord is an effecter of what He intends. <> Suna madawwama a cikinta matuƙar sammai da ƙasa sun dawwama, fãce abin da Ubangijinka Ya so. Lalle Ubangijinka Mai aikatãwa ne ga abin da Yake nufi. = --Qur'an 11:107
    And as for those who were [destined to be] prosperous, they will be in Paradise, abiding therein as long as the heavens and the earth endure, except what your Lord should will - a bestowal uninterrupted. <> Amma waɗanda suka yi arziki to, sunã a cikin Aljanna sunã madawwama, a cikinta, matuƙar sammai da ƙasa sun dawwama, fãce abin da Ubangijinka Ya so. Kyauta wadda bã ta yankẽwa. = --Qur'an 11:108
    So do not be in doubt, [O Muhammad], as to what these [polytheists] are worshipping. They worship not except as their fathers worshipped before. And indeed, We will give them their share undiminished. <> Sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga abin da waɗannan suke bautawa. Bã su wata ibãda fãce kamar yadda ubanninsu ke aikatãwa a gabani. Kuma haƙĩƙa Mũ, Mãsu cika musu rabon su ne, bã tãre da nakasãwa ba. = --Qur'an 11:109
    And We had certainly given Moses the Scripture, but it came under disagreement. And if not for a word that preceded from your Lord, it would have been judged between them. And indeed they are, concerning the Qur'an, in disquieting doubt. <> Kuma haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi, sai aka sãɓã wa jũna a cikinsa. Kuma bã dõmin wata kalma wadda ta gabãta daga Ubangijinka ba, haƙĩƙa, dã an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma haƙĩƙa, sunã a cikin wata shakka, game da shi, mai sanya kõkanto. = --Qur'an 11:110
    And indeed, each [of the believers and disbelievers] - your Lord will fully compensate them for their deeds. Indeed, He is Acquainted with what they do. <> Kuma lalle, haƙĩƙa, Ubangijinka Mai cika wa kõwa (sakamakon) ayyukansa ne. Lalle Shĩ, Mai ƙididdigewa ne ga abin da suke aikatãwa. = --Qur'an 11:111
    So remain on a right course as you have been commanded, [you] and those who have turned back with you [to Allah], and do not transgress. Indeed, He is Seeing of what you do. <> Sai ka daidaitu kamar yadda aka umurce ka, kai da waɗanda suka tũba tãre da kai kunã bã mãsu ƙẽtara haddi ba. Lalle shĩ, Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa. = --Qur'an 11:112
    And do not incline toward those who do wrong, lest you be touched by the Fire, and you would not have other than Allah any protectors; then you would not be helped. <> Kada ku karkata zuwa ga waɗanda suka yi zãlunci har wuta ta shãfe ku. Kuma bã ku da waɗansu majiɓinta baicin Allah, sa'an nan kuma bã zã a taimake ku ba. = --Qur'an 11:113
    And establish prayer at the two ends of the day and at the approach of the night. Indeed, good deeds do away with misdeeds. That is a reminder for those who remember. <> Kuma ka tsai da salla a gẽfe guda biyu na yini da wani yanki daga dare. Lalle ne ayyukan ƙwarai sunã kõre mũnãnan ayyuka. wancan ne tunãtarwa ga mãsu tunãwa. = --Qur'an 11:114
    And be patient, for indeed, Allah does not allow to be lost the reward of those who do good. <> Kuma ka yi haƙuri. Allah bã Ya tõzartar da lãdar mãsu kyautatãwa. = --Qur'an 11:115
    So why were there not among the generations before you those of enduring discrimination forbidding corruption on earth - except a few of those We saved from among them? But those who wronged pursued what luxury they were given therein, and they were criminals. <> To, don me mãsu hankali ba su kasance daga mutãnen ƙarnõnin da suke a gabãninku ba, sunã hani daga ɓarna a cikin ƙasa? fãce kaɗan daga wanda Muka kuɓutar daga gare su (sun yi hanin). Kuma waɗanda suka yi zãlunci suka bin abin da aka ni'imtar da su a cikinsa, suka kasance mãsu laifi. = --Qur'an 11:116
    And your Lord would not have destroyed the cities unjustly while their people were reformers. <> Kuma Ubangijinka bai kasance Yanã halakar da alƙaryu sabõda wani zãlunci ba, alhãli mutãnensu sunã mãsu gyãrãwa. = --Qur'an 11:117
    And if your Lord had willed, He could have made mankind one community; but they will not cease to differ. <> Kuma dã Ubangijinka Ya so, dã Yã sanya mutãne al'umma guda. Kuma bã zã su gushe ba sunã mãsu sãɓã wa jũna. = --Qur'an 11:118
    Except whom your Lord has given mercy, and for that He created them. But the word of your Lord is to be fulfilled that, "I will surely fill Hell with jinn and men all together." <> Sai wanda Ubangijinka Ya yi wa rahama, kuma dõmin wannan ne Ya halicce su. Kuma kalmar "Ubangijinka" Lalle ne zã Ni cika Jahannama da aljannu da mutãne gaba ɗaya" ta cika. = --Qur'an 11:119
    And each [story] We relate to you from the news of the messengers is that by which We make firm your heart. And there has come to you, in this, the truth and an instruction and a reminder for the believers. <> Kuma dũbi dai Munã bã da lãbãri a gare ka daga lãbarun Manzanni, abin da Muke tabbatar da zuciyarka da shi. Kuma gaskiya ta zo maka a cikin wannan da wa'azi da tunãtarwã ga mãsu ĩmãni. = --Qur'an 11:120
    And say to those who do not believe, "Work according to your position; indeed, we are working. <> kuma kace wa waɗanda bã su yin ĩmãni, "Ku yi aiki a kan hãlinku, lalle mũ mãsu aiki ne. = --Qur'an 11:121
    And wait, indeed, we are waiting." <> "Kuma ku yi Jiran dãko, lalle mu mãsu Jiran dãko ne." = --Qur'an 11:122
    And to Allah belong the unseen [aspects] of the heavens and the earth and to Him will be returned the matter, all of it, so worship Him and rely upon Him. And your Lord is not unaware of that which you do. <> Kuma ga Allah gaibin sammai da ƙasa yake. Kuma zuwa gare Shi ake mayar da dukan al'amari. Sabõda haka ku bauta Masa kuma ku dõgara a kanSa. Kuma Ubangijinka bai zama Mai gafala daga abin da kuke aikatãwa ba. = --Qur'an 11:123
    Alif, Lam, Ra. These are the verses of the clear Book. <> A. L̃.R. Waɗancan ãyoyin Littãfi mai bayyanãwa ne. = --Qur'an 12:1
    Indeed, We have sent it down as an Arabic Qur'an that you might understand. <> Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi, yanã abin karantãwa na Lãrabci; tsammãninkũ, kunã hankalta. = --Qur'an 12:2
    We relate to you, [O Muhammad], the best of stories in what We have revealed to you of this Qur'an although you were, before it, among the unaware. <> Mũ, Munã bãyar da lãbãri a gare ka, mafi kyãwon lãbãri ga abin da Muka yi wahayin wannan Alƙur'ãni zuwa gare ka. Kuma lalle ne kã kasance a gabãninsa, haƙĩƙa, daga gafalallu. = --Qur'an 12:3
    [Of these stories mention] when Joseph said to his father, "O my father, indeed I have seen [in a dream] eleven stars and the sun and the moon; I saw them prostrating to me." <> A lõkacin da Yũsufu ya ce wa ubansa, "Yã bãba! Lalle ne nĩ, nã ga taurãri gõma shã ɗaya, da rãnã da watã. Na gan su sunã mãsu sujada a gare ni." = --Qur'an 12:4
    He said, "O my son, do not relate your vision to your brothers or they will contrive against you a plan. Indeed Satan, to man, is a manifest enemy. <> Ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Kada ka faɗi mafarkinka ga 'yan'uwanka, har su ƙulla maka wani kaidi. Lalle ne Shaidan ga mutum, haƙĩƙa, maƙiyi ne bayyanãnne. = --Qur'an 12:5
    And thus will your Lord choose you and teach you the interpretation of narratives and complete His favor upon you and upon the family of Jacob, as He completed it upon your fathers before, Abraham and Isaac. Indeed, your Lord is Knowing and Wise." <> "Kuma kãmar wancan ne, Ubangijinka Yake zãɓen ka, kuma Ya sanar da kai daga fassarar lãbãrai, kuma ya cika ni'imõminSa a kanka, kuma a kan gidan Yãƙũba kãmar yadda ya cika su a kan ubanninka biyu, a gabãni, Ibrãhĩm da Is'hãƙa. Lalle Ubangijinka ne Masani, Mai hikima." = --Qur'an 12:6
    Certainly were there in Joseph and his brothers signs for those who ask, <> Lalle ne, haƙĩƙa, ãyõyi sun kasance ga Yũsufu da 'yan'uwansa dõmin mãsu tambaya. = --Qur'an 12:7
    When they said, "Joseph and his brother are more beloved to our father than we, while we are a clan. Indeed, our father is in clear error. <> A lõkacin da suka ce: lalle ne Yũsufu da ɗan'uwansa ne mafiya sõyuwa ga ubanmu daga gare mu, alhãli kuwa mũ jama'a guda ne. Lalle ubanmu, haƙĩƙa, yanã cikin ɓata bayyananniya. = --Qur'an 12:8
    Kill Joseph or cast him out to [another] land; the countenance of your father will [then] be only for you, and you will be after that a righteous people." <> Ku kashe Yũsufu, kõ kuwa ku jẽfa shi a wata ƙasa, fuskar ubanku ta wõfinta sabõda ku, kuma ku kasance a bãyansa mutãne sãlihai. = --Qur'an 12:9
    Said a speaker among them, "Do not kill Joseph but throw him into the bottom of the well; some travelers will pick him up - if you would do [something]." <> Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Kada ku kashe Yũsufu. Ku jẽfa shi a cikin duhun rĩjiya, wasu matafiya su tsince shi, idan kun kasance mãsu aikatãwa ne." = --Qur'an 12:10
    They said, "O our father, why do you not entrust us with Joseph while indeed, we are to him sincere counselors? <> Suka ce: "Yã bãbanmu! Mẽne ne a gare ka ba ka amince mana ba a kan Yũsufu, alhãlikuwa lalle ne mũ, haƙãƙa mãsu nashĩha muke a gare shi?" = --Qur'an 12:11
    Send him with us tomorrow that he may eat well and play. And indeed, we will be his guardians. <> "Ka bar shi tãre da mu a gõbe, ya ji dãɗi, kuma ya yi wãsa. Kuma lalle ne mu, a gare shi, mãsu tsaro ne." = --Qur'an 12:12
    [Jacob] said, "Indeed, it saddens me that you should take him, and I fear that a wolf would eat him while you are of him unaware." <> Ya ce: "Lalle ne ni, haƙãƙa yanã ɓãta mini rai ku tafii da shi, Kuma inã tsõron kerkẽci ya cinye shi, alhãli ku kuwa kunã mãsu shagala daga gare shi." = --Qur'an 12:13
    They said, "If a wolf should eat him while we are a [strong] clan, indeed, we would then be losers." <> Suka ce: "Haƙĩƙa idan kerkẽci ya cinye shi, alhãli kuwa munã dangin jũna, lalle ne mũ, a sa'an nan, hakĩka, mun zama mãsu hasãra." = --Qur'an 12:14
    So when they took him [out] and agreed to put him into the bottom of the well... But We inspired to him, "You will surely inform them [someday] about this affair of theirs while they do not perceive [your identity]." <> To, a lõkacin da suka tafi da shi, kuma suka yi niyyar su sanya shi a cikin duhun rĩjiya, Muka yi wahayi zuwa gare shi, "Lalle ne, kanã bã su lãbari game da wannan al'amari nãsu, kuma sũ ba su sani ba." = --Qur'an 12:15
    And they came to their father at night, weeping. <> Kuma suka je wa ubansu da dare sunã kũka. = --Qur'an 12:16
    They said, "O our father, indeed we went racing each other and left Joseph with our possessions, and a wolf ate him. But you would not believe us, even if we were truthful." <> Suka ce: "Yã bãbanmu! Lalle ne, mun tafi munã tsẽre, kuma muka bar Yusufu a wurin kãyanmu, sai kerkẽci ya cinye shi, kuma kai, bã mai amincẽwa da mu ba ne, kuma kõ dã mun kasance mãsu gaskiya!"_ = --Qur'an 12:17
    And they brought upon his shirt false blood. [Jacob] said, "Rather, your souls have enticed you to something, so patience is most fitting. And Allah is the one sought for help against that which you describe." <> Kuma suka je, a jikin rigarsa akwai wani jinin ƙarya. Ya ce: "Ã'a, zukatanku suka ƙawãta muku wani al'amari. Sai haƙuri mai kyau! Kuma Allah ne wanda ake nẽman taimako (a gunSa) a kan abin da kuke siffantãwa." = --Qur'an 12:18
    And there came a company of travelers; then they sent their water drawer, and he let down his bucket. He said, "Good news! Here is a boy." And they concealed him, [taking him] as merchandise; and Allah was knowing of what they did. <> Kuma wani ãyari ya je, sai suka aika mai nẽman musu rũwa, sai ya zura gugansa, ya ce: "Yã bushãrata! Wannan yãro ne." Kuma suka ɓõye shi yanã abin sayarwa. Kuma Allah ne Masani ga abin da suke aikatãwa. = --Qur'an 12:19
    And they sold him for a reduced price - a few dirhams - and they were, concerning him, of those content with little. <> Kuma suka sayar da shi da 'yan kuɗi kaɗan, dirhamõmi ƙidãyayyu, Kuma sun kasance, a wurinsa, daga mãsu isuwa da abu kaɗan. = --Qur'an 12:20
    And the one from Egypt who bought him said to his wife, "Make his residence comfortable. Perhaps he will benefit us, or we will adopt him as a son." And thus, We established Joseph in the land that We might teach him the interpretation of events. And Allah is predominant over His affair, but most of the people do not know. <> Kuma wanda ya saye shi daga Masar ya ce wa mãtarsa, "Ki girmama mazauninsa, akwai tsammãnin ya amfãne mu, kõ kuwa mu riƙe shi ɗã."Kuma kamar wancan ne Muka tabbatar ga Yũsufu, a cikin ƙasa kuma dõmin Mu sanar da shi daia fassarar lũbũru, kuma Allah ne Marinjãyi a kan al'amarinSa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba." = --Qur'an 12:21
    And when Joseph reached maturity, We gave him judgment and knowledge. And thus We reward the doers of good. <> Kuma a lõkacin da ya isa mafi ƙarfinsa, Muka bã shi hukunci da ilmi. Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. = --Qur'an 12:22
    And she, in whose house he was, sought to seduce him. She closed the doors and said, "Come, you." He said, "[I seek] the refuge of Allah. Indeed, he is my master, who has made good my residence. Indeed, wrongdoers will not succeed." <> Kuma wadda yake a cikin ɗãkinta, ta nẽme shi ga kansa, kuma ta kukkulle ƙõfõfi, kuma ta ce, "Yã rage a gare ka!" ya ce: "Ina neman tsarin Allah! Lalle shĩne Ubangijina. Yã kyautata mazaunina. Lalle ne shĩ, mãsu zãlunci ba su cin nasara!" = --Qur'an 12:23
    And she certainly determined [to seduce] him, and he would have inclined to her had he not seen the proof of his Lord. And thus [it was] that We should avert from him evil and immorality. Indeed, he was of Our chosen servants. <> Kuma lalle ne, tã himmantu da shi. Kuma yã himmantu da ita in bã dõmin ya ga dalĩlin Ubangijinsa ba. Kãmar haka dai, dõmin Mu karkatar da mummũnan aiki da alfãsha daga gare shi. Lalle ne shi, daga bãyinMu zaɓaɓɓu yake. = --Qur'an 12:24
    And they both raced to the door, and she tore his shirt from the back, and they found her husband at the door. She said, "What is the recompense of one who intended evil for your wife but that he be imprisoned or a painful punishment?" <> Kuma suka yi tsẽre zuwa ga ƙõfa. Sai ta tsãge rigarsa daga bãya, kuma suka iske mijinta a wurin ƙõfar. Ta ce: "Mẽnene sakamakon wanda ya yi nufin cũta game da iyãlinka? Fãce a ɗaure shi, ko kuwa a yi masa wata azãba mai raɗaɗi." = --Qur'an 12:25
    [Joseph] said, "It was she who sought to seduce me." And a witness from her family testified. "If his shirt is torn from the front, then she has told the truth, and he is of the liars. <> Ya ce: "Ita ce ta nẽme ni a kaina."Kuma wani mai shaida daga mutãnenta ya bãyar da shaida: "Idan rigarsa ta kasance an tsage ta daga gaba, to, tã yi gaskiya, kuma shĩ ne daga maƙaryata." = --Qur'an 12:26
    But if his shirt is torn from the back, then she has lied, and he is of the truthful." <> "Kuma idan rigarsa ta kasance an tsãge ta daga bãya, to, tã yi ƙarya, kuma shĩ ne daga mãsu gaskiya." = --Qur'an 12:27
    So when her husband saw his shirt torn from the back, he said, "Indeed, it is of the women's plan. Indeed, your plan is great. <> Sa'an nan a lõkacin da ya ga rĩgarsa an tsãge ta daga bãya, ya ce: "Lalle ne shi, daga kaidinku ne, mata! Lalle ne kaidinku mai girma ne!" = --Qur'an 12:28
    Joseph, ignore this. And, [my wife], ask forgiveness for your sin. Indeed, you were of the sinful." <> "Yusufu! Ka kau da kai daga wannan. Kuma ki nẽmi gãfara dõmin laifinki. Lalle ne ke, kin kasance daga mãsu kuskure." = --Qur'an 12:29
    And women in the city said, "The wife of al-'Azeez is seeking to seduce her slave boy; he has impassioned her with love. Indeed, we see her [to be] in clear error." <> Kuma waɗansu mãtã a cikin Birnin suka ce: "Matar Azĩz tanã nẽman hãdiminta daga kansa! Haƙĩƙa, yã rufe zũciyarta da so. Lalle ne mũ, Munã ganin taa cikin ɓata bayyanãnna." = --Qur'an 12:30
    So when she heard of their scheming, she sent for them and prepared for them a banquet and gave each one of them a knife and said [to Joseph], "Come out before them." And when they saw him, they greatly admired him and cut their hands and said, "Perfect is Allah! This is not a man; this is none but a noble angel." <> Sa'an nan a lõkacin da ta ji lãbãri game da mãkircinsu, sai ta aika kiran liyafa zuwa gare su, kuma ta yi tattalin abincin da ake dõgara wajen cinsa, kuma ta bai wa kõwace ɗaya daga cikinsu wuƙa, kuma ta ce: "Ka fito a kansu." To, a lõkacin da, suka gan shi, suka girmamã shi, kuma suka yanyanke hannãyensu, kuma suka ce: "Tsarki yanã ga Allah! Wannan bã mutum ba ne! Wannan bai zama ba fãce Malã'ika ne mai daraja!" = --Qur'an 12:31
    She said, "That is the one about whom you blamed me. And I certainly sought to seduce him, but he firmly refused; and if he will not do what I order him, he will surely be imprisoned and will be of those debased." <> Ta ce: "To wannan ne fa wanda kuka, zarge ni a cikinsa! Kuma lalle ne, haƙẽƙa na nẽme shi daga kansa, sai ya tsare gida, kuma nĩ inã rantsuwa, idan bai aikata abin da nake umurnin sa ba, haƙẽƙa anã ɗaure shi. Haƙĩƙa, yanã kasan, cewa daga ƙasƙantattu." = --Qur'an 12:32
    He said, "My Lord, prison is more to my liking than that to which they invite me. And if You do not avert from me their plan, I might incline toward them and [thus] be of the ignorant." <> Ya ce: "Yã Ubangijina! Kurkuku ne mafi sõyuwa a gare ni daga abin da suke kirã na zuwa gare shi. Kuma idan ba Ka karkatar da kaidinsu daga gare ni ba, zan karkata zuwa gare su, kuma in kasance daga jãhilai." = --Qur'an 12:33
    So his Lord responded to him and averted from him their plan. Indeed, He is the Hearing, the Knowing. <> Sai Ubangijinsa Ya karɓa masa sabõda haka Ya karkatar da kaidinsu daga gare shi. Lalle Shĩ ne Mai jĩ, Masani. = --Qur'an 12:34
    Then it appeared to them after they had seen the signs that al-'Azeez should surely imprison him for a time. <> Sa'an nan kuma ya bayyana a gare su a bãyan sun ga alãmõmin, lalle ne dai su ɗaure shi har zuwa wani lõkaci. = --Qur'an 12:35
    And there entered the prison with him two young men. One of them said, "Indeed, I have seen myself [in a dream] pressing wine." The other said, "Indeed, I have seen myself carrying upon my head [some] bread, from which the birds were eating. Inform us of its interpretation; indeed, we see you to be of those who do good." <> Kuma waɗansu samãri biyu suka shiga kurkuku tãre da shi. ¦ayansu ya ce: "Lalle ne nĩ, nã yi mafarkin gã ni inã mãtsar giya." Kuma ɗayan ya ce: "Lalle ne nĩ, nã yi Mafarkin gã ni inã ɗauke da waina a bisa kaina, tsuntsãye sunã ci daga gare ta. Ka bã mu lãbãri game da fassararsu. Lalle ne mũ, Munã ganin ka daga mãsu kyautatãwa." = --Qur'an 12:36
    He said, "You will not receive food that is provided to you except that I will inform you of its interpretation before it comes to you. That is from what my Lord has taught me. Indeed, I have left the religion of a people who do not believe in Allah, and they, in the Hereafter, are disbelievers. <> Ya ce: "Wani abinci bã zai zo muku ba wanda ake azurtã ku da shi fãce nã bã ku lãbãrin fassararsa, kãfin ya zo muku. Wannan kuwa yanã daga abin da Ubangijĩna Ya sanar da ni. Lalle ne nĩ nã bar addinin mutãne waɗanda ba su yi ĩmãni da Allah ba, kuma game da lãhira, sũ kãfirai ne." = --Qur'an 12:37
    And I have followed the religion of my fathers, Abraham, Isaac and Jacob. And it was not for us to associate anything with Allah. That is from the favor of Allah upon us and upon the people, but most of the people are not grateful. <> "Kuma na bi addinin iyayẽna, Ibrãhĩm da Is'hãka da Yãƙũba. Bã ya yiwuwa a gare mu mu yi shirka da Allah da kõme. Wannan yana daga falalar Allah a kanmu da mutãne, amma mafi yawan mutãne bã su gõdewa." = --Qur'an 12:38
    O [my] two companions of prison, are separate lords better or Allah, the One, the Prevailing? <> "Yã abõkaina biyu na kurkuku! Shin iyãyen giji dabam-dabam ne mafiya alhẽri kõ kuwa Allah Makaɗaici Mai tanƙwasãwa?" = --Qur'an 12:39
    You worship not besides Him except [mere] names you have named them, you and your fathers, for which Allah has sent down no authority. Legislation is not but for Allah. He has commanded that you worship not except Him. That is the correct religion, but most of the people do not know. <> "Ba ku bauta wa kõme, baicinSa, fãce waɗansu sũnãye waɗanda kuka ambace su, kũ da ubanninku. Allah bai saukar da wani dalĩli ba game da su. Bãbu hukunci fãce na Allah. Ya yi umurnin kada ku bauta wa kõwa fãce Shi. Wancan ne addini madaidaici, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba." = --Qur'an 12:40
    O two companions of prison, as for one of you, he will give drink to his master of wine; but as for the other, he will be crucified, and the birds will eat from his head. The matter has been decreed about which you both inquire." <> "Yã abõkaina biyu, na kurkuku! Amma ɗayanku, to, zai shãyar da uban gidansa giya, kuma gudan, to, zã a tsĩrẽ shi, sa'an nan tsuntsãye su ci daga kansa. An hukunta al'amarin, wanda a cikinsa kuke yin fatawa." = --Qur'an 12:41
    And he said to the one whom he knew would go free, "Mention me before your master." But Satan made him forget the mention [to] his master, and Joseph remained in prison several years. <> Kuma ya ce da wanda ya tabbatar da cẽwa shi mai kuɓuta ne daga gare su, "Ka ambacẽ ni a wurin uban gidanka." Sai Shaiɗan ya mantar da shi tunãwar Ubangijinsa, sabõda haka ya zauna a cikin kurkuku 'yan shekaru. = --Qur'an 12:42
    And [subsequently] the king said, "Indeed, I have seen [in a dream] seven fat cows being eaten by seven [that were] lean, and seven green spikes [of grain] and others [that were] dry. O eminent ones, explain to me my vision, if you should interpret visions." <> Kuma sarki ya ce: "Lalle ne, nã yi mafarki; nã ga shãnu bakwai mãsu ƙiba, waɗansu bakwai rãmammu, sunã cin su, da zangarku bakwai kõre-kõre da waɗansu ƙeƙasassu. Yã kũ jama'a! Ku yi mini fatawa a cikin mafarkĩna, idan kun kasance ga mafarki kunã fassarawa." = --Qur'an 12:43
    They said, "[It is but] a mixture of false dreams, and we are not learned in the interpretation of dreams." <> Suka ce: "Yãye-yãyen mafarki ne, kuma ba mu zamo masana ga fassarar yãye-yãyen mafarki ba." = --Qur'an 12:44
    But the one who was freed and remembered after a time said, "I will inform you of its interpretation, so send me forth." <> Kuma wannan da ya kuɓuta daga cikinsu ya ce: a bãyan yã yi tunãni a lõkaci mai tsawo, "Nĩ, inã bã ku lãbãri game da fassararsa. Sai ku aike ni." = --Qur'an 12:45
    [He said], "Joseph, O man of truth, explain to us about seven fat cows eaten by seven [that were] lean, and seven green spikes [of grain] and others [that were] dry - that I may return to the people; perhaps they will know [about you]." <> "Yã Yũsufu! Yã kai mai yawan gaskiya! Ka yi mana fatawa a cikin shãnu bakwai mãsu ƙiba, waɗansu bakwai rãmammu sunã cin su, da zangarku bakwai kõrãye da waɗansu ƙẽƙasassu, tsammãnĩna in kõma ga mutãne, tsammãninsu zã su sani." = --Qur'an 12:46
    [Joseph] said, "You will plant for seven years consecutively; and what you harvest leave in its spikes, except a little from which you will eat. <> Ya ce: "Kunã shũka, shẽkara bakwai tutur, sa'an nan abin da kuka girbe, sai ku bar shi, a cikin zanganniyarsa, sai kaɗan daga abin da kuke ci." = --Qur'an 12:47
    Then will come after that seven difficult [years] which will consume what you saved for them, except a little from which you will store. <> "Sa'an nan kuma waɗansu bakwai mãsu tsanani su zo daga hãyan wancan, su cinye abin da kuka gabãtar dõminsu, fãce kaɗan daga abin da kuke ãdanãwa." = --Qur'an 12:48
    Then will come after that a year in which the people will be given rain and in which they will press [olives and grapes]." <> "Sa'an nan kuma wata shẽkara ta zo daga bãyan wancan, a cikinta ake yi wa mutãne ruwa mai albarka, kuma a cikinta suke mãtsar abin sha." = --Qur'an 12:49
    And the king said, "Bring him to me." But when the messenger came to him, [Joseph] said, "Return to your master and ask him what is the case of the women who cut their hands. Indeed, my Lord is Knowing of their plan." <> Kuma sarkin ya ce: "Ku zo mini da shi." To, a lõkacin da manzo ya je masa (Yũsufu), ya ce: "Ka kõma zuwa ga uban gidanka, sa' an nan ka tambaye shi; Mẽnene hãlin mãtãyen nan waɗanda suka yanyanke hannãyensu? Lalle ne Ubangijĩna ne Masani game da kaidinsu." = --Qur'an 12:50
    Said [the king to the women], "What was your condition when you sought to seduce Joseph?" They said, "Perfect is Allah! We know about him no evil." The wife of al-'Azeez said, "Now the truth has become evident. It was I who sought to seduce him, and indeed, he is of the truthful. <> Ya ce: "Mẽne ne babban al'amarinku, a lõkacin da kaka nẽmi Yũsufu daga kansa?" Suka ce: "Tsarki ga Allah yake! Ba mu san wani mummũnan aiki a kansaba." Mãtar Azĩz ta ce: "Yanzu fagaskiya ta bayyana. Nĩ ce nã nẽme shi daga kansa. Kuma lalle ne shĩ, haƙĩƙa, yanã daga mãsu gaskiya. = --Qur'an 12:51
    That is so al-'Azeez will know that I did not betray him in [his] absence and that Allah does not guide the plan of betrayers. <> "Wancan ne, dõmin ya san cẽwa lalle ne ni ban yaudareshi ba a ɓõye, kuma lalle Allah bã Ya shiryar da kaidin mayaudara." = --Qur'an 12:52
    And I do not acquit myself. Indeed, the soul is a persistent enjoiner of evil, except those upon which my Lord has mercy. Indeed, my Lord is Forgiving and Merciful." <> "Kuma bã ni kuɓutar da kaina. Lalle ne rai, haƙĩƙa, mai yawan umurni ne da mummũnan aiki, fãce abin da Ubangjina Ya yi na; rahama. Lalle Ubangjina Mai gãfara ne, Mai jin ƙai." = --Qur'an 12:53
    And the king said, "Bring him to me; I will appoint him exclusively for myself." And when he spoke to him, he said, "Indeed, you are today established [in position] and trusted." <> Kuma sarkin ya ce: "Ku zo mini da shi in kẽɓe shi ga kaina." To, a lõkacin da Yũsufu ya yi masa magana sai ya ce: "Lalle ne kai a yau, a gunmu, mai daraja ne, amintacce." = --Qur'an 12:54
    [Joseph] said, "Appoint me over the storehouses of the land. Indeed, I will be a knowing guardian." <> Ya ce: "Ka sanya ni a kan taskõkin ƙasa. Lalle ne nĩ, mai tsarẽwa ne, kuma masani." = --Qur'an 12:55
    And thus We established Joseph in the land to settle therein wherever he willed. We touch with Our mercy whom We will, and We do not allow to be lost the reward of those who do good. <> Kuma kamar wancan ne Muka bãyar da ĩko ga Yũsufu a cikin ƙasa yanã sauka a inda duk yake so. Munã sãmun wanda Muke so da rahamar Mu, kuma bã Mu tõzartar da lãdar mãsu kyautatawa. = --Qur'an 12:56
    And the reward of the Hereafter is better for those who believed and were fearing Allah. <> Kuma lalle lãdar Lãhira ce mafi alhẽri ga waɗandasuka yi ĩmãni, kuma suka kasance mãsu taƙawa. = --Qur'an 12:57
    And the brothers of Joseph came [seeking food], and they entered upon him; and he recognized them, but he was to them unknown. <> Kuma 'yan'uwan Yũsufu suka jẽ, sa'an nan suka shiga a gare shi, sai ya gãne su, alhãli kuwa su, sunã mãsu musunsa. = --Qur'an 12:58
    And when he had furnished them with their supplies, he said, "Bring me a brother of yours from your father. Do not you see that I give full measure and that I am the best of accommodators? <> Kuma a lõkacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, ya ce: "Ku zo mini da wani ɗan'uwa nãku daga ubanku. Ba ku gani ba cẽwa lalle ne nĩ, inã cika ma'auni, kuma nĩ ne mafi alhẽrin mãsu saukarwa?" = --Qur'an 12:59
    But if you do not bring him to me, no measure will there be [hereafter] for you from me, nor will you approach me." <> "Sa'an nan idan ba ku zo mini da shĩ ba, to, bãbu awoa gare ku a wurĩna, kuma kada ku, kasance ni." = --Qur'an 12:60
    They said, "We will attempt to dissuade his father from [keeping] him, and indeed, we will do [it]." <> Suka ce: "Zã mu nẽme shi daga ubansa. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu aikatãwa ne." = --Qur'an 12:61
    And [Joseph] said to his servants, "Put their merchandise into their saddlebags so they might recognize it when they have gone back to their people that perhaps they will [again] return." <> Kuma ya ce wa yaransa, "Ku sanya hajjarsu a cikin kãyansu, tsammãninsu sunã gãne ta idan sun jũya zuwa ga mutãnensu, tsammã ninsu, zã su kõmo." = --Qur'an 12:62
    So when they returned to their father, they said, "O our father, [further] measure has been denied to us, so send with us our brother [that] we will be given measure. And indeed, we will be his guardians." <> To, a lõkacin da suka kõma zuwa ga ubansu, suka ce: "Yã bãbanmu! An hana mu awo sai ka aika ɗan'uwanmu tãre da mu. Zã mu yi awo. Kuma lalle ne, haƙĩƙa mũ, mãsu lũra da Shi ne." = --Qur'an 12:63
    He said, "Should I entrust you with him except [under coercion] as I entrusted you with his brother before? But Allah is the best guardian, and He is the most merciful of the merciful." <> Ya ce: "Ashe, zã ni amince muku a kansa? Fãce dai kamar yadda na amince muku a kan ɗan'uwansa daga gabãni, sai dai Allah ne Mafĩfĩcin mãsu tsari, kuma Shĩ ne Mafi rahamar mãsu rahama." = --Qur'an 12:64
    And when they opened their baggage, they found their merchandise returned to them. They said, "O our father, what [more] could we desire? This is our merchandise returned to us. And we will obtain supplies for our family and protect our brother and obtain an increase of a camel's load; that is an easy measurement." <> Kuma a lõkacin da suka bũɗe kãyansu, suka sãmi hajjarsu an mayar musu da ita, suka ce: "Yã bãbanmu! Ba mu zãlunci! Wannan hajjarmu ce an mayar mana da ita, kuma mu nẽmo wa iyalinmu abinci, kuma mu kiyãye ɗan'uwanmu, kuma mu ƙãra awon kãyan rãƙumi guda, wancan awo ne mai sauki." = --Qur'an 12:65
    [Jacob] said, "Never will I send him with you until you give me a promise by Allah that you will bring him [back] to me, unless you should be surrounded by enemies." And when they had given their promise, he said, "Allah, over what we say, is Witness." <> Ya ce: "Bã zan sake shi tãre da kũ ba, sai kun kawo mini alkawarinku baga Allah, haƙĩƙa, kunã dawo mini da shi, sai fa idan an kẽwaye ku." To, a, lõkacinda suka yi mãsa alkawari, ya ce: "Allah ne wakĩli a kan abin da muke faɗa." = --Qur'an 12:66
    And he said, "O my sons, do not enter from one gate but enter from different gates; and I cannot avail you against [the decree of] Allah at all. The decision is only for Allah; upon Him I have relied, and upon Him let those who would rely [indeed] rely." <> Kuma ya ce: "Yã ɗiyana! Kada ku shiga ta ƙõfa guda, ku shiga ta ƙõfõfi dabam-dabam, kuma bã na wadãtar muku kõme daga Allah. Bãbu hukunci fãce daga Allah, a gare Shi na dõgara, kuma a gare Shi mãsu dõgara sai su dõgara." = --Qur'an 12:67
    And when they entered from where their father had ordered them, it did not avail them against Allah at all except [it was] a need within the soul of Jacob, which he satisfied. And indeed, he was a possessor of knowledge because of what We had taught him, but most of the people do not know. <> Kuma a lõkacin da suka shiga daga inda ubansu ya umurce su wani abu bai kasance yanã wadãtarwa ga barinsu daga Allah ba fãce wata bukata ce a ran Yãƙũbu, ya bayyana ta. Kuma lalle ne shĩ, haƙĩƙa, ma'abũcin wani ilmi ne ga abin da Muka sanar da shi, kuma mafi yawan mutãne ba su sani ba. = --Qur'an 12:68
    And when they entered upon Joseph, he took his brother to himself; he said, "Indeed, I am your brother, so do not despair over what they used to do [to me]." <> Kuma a lõkacin da suka shiga wajen Yũsufu, ya tattara ɗan'uwansa zuwa gare shi, ya ce: "Lalle nĩ ne ɗan'uwanka, sabõda haka kada ka yi baƙin ciki da abin da suka kasance sunã aikatãwa." = --Qur'an 12:69
    So when he had furnished them with their supplies, he put the [gold measuring] bowl into the bag of his brother. Then an announcer called out, "O caravan, indeed you are thieves." <> Sa'an nan a lõkacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, sai ya sanya ma'auni a cikin kãyan ɗan'uwansa sa'an nan kuma mai yẽkuwa ya yi yẽkuwa," Yã kũ ãyari! lalle ne, haƙĩƙa kũ ɓarãyi ne." = --Qur'an 12:70
    They said while approaching them, "What is it you are missing?" <> Suka ce: kuma suka fuskanta zuwa gare su: "Mẽne ne kuke nẽma?" = --Qur'an 12:71
    They said, "We are missing the measure of the king. And for he who produces it is [the reward of] a camel's load, and I am responsible for it." <> Suka ce: "Munã nẽman ma'aunin sarki. Kuma wanda ya zo da shi, yanã da kãyan rãkumi ɗaya, kuma ni ne lãmuni game da shi." = --Qur'an 12:72
    They said, "By Allah, you have certainly known that we did not come to cause corruption in the land, and we have not been thieves." <> Suka ce: "Tallahi! Lalle ne, haƙĩƙa, kun sani, ba mu zodon mu yi ɓarna a cikin ƙasa ba, kuma ba mu kasance ɓarãyi ba." = --Qur'an 12:73
    The accusers said, "Then what would be its recompense if you should be liars?" <> Suka ce: "To mẽne ne sakamakonsa idan, kun kasance maƙaryata?" = --Qur'an 12:74
    [The brothers] said, "Its recompense is that he in whose bag it is found - he [himself] will be its recompense. Thus do we recompense the wrongdoers." <> Suka ce: "Sakamakonsa, wanda aka same shi a cikin kãyansa, to, shi ne sakamakonsa, kamar wancan ne muke sãka wa azzãlumai." = --Qur'an 12:75
    So he began [the search] with their bags before the bag of his brother; then he extracted it from the bag of his brother. Thus did We plan for Joseph. He could not have taken his brother within the religion of the king except that Allah willed. We raise in degrees whom We will, but over every possessor of knowledge is one [more] knowing. <> To, sai ya fãra (bincike) da jikunansu a gabãnin jakar ɗan'uwansa. Sa'an nan ya fitar da ita daga jakar ɗan'uwansa. Kamar wancan muka shirya wa Yũsufu. Bai kasance ya kãma ɗan'uwansa a cikin addinin (dõkõkin) sarki ba, fãce idan Allah Ya so. Munã ɗaukaka darajõji ga wanda Muka so, kuma a saman kõwane ma'abũcin ilmi akwai wani masani. = --Qur'an 12:76
    They said, "If he steals - a brother of his has stolen before." But Joseph kept it within himself and did not reveal it to them. He said, "You are worse in position, and Allah is most knowing of what you describe." <> Suka ce: "Idan ya yi sãta, to, lalle ne wani ɗan'uwansa yã taɓa yin sãta a gabãninsa." Sai Yũsufu ya bõye ta a cikin ransa. Kuma bai bayyana ta ba a gare su, ya ce: "Kũ ne mafi sharri ga wuri. Kuma Allah ne Mafi sani daga abin da kuke siffantãwa." = --Qur'an 12:77
    They said, "O 'Azeez, indeed he has a father [who is] an old man, so take one of us in place of him. Indeed, we see you as a doer of good." <> Suka ce: "Yã kai Azĩzu! Lalle ne yanã da wani ubã, tsoho mai daraja, sabõda haka ka kãma ɗayanmu amatsayinsa. Lalle ne mũ, muna ganin ka daga mãsu kyautatãwa." = --Qur'an 12:78
    He said, "[I seek] the refuge of Allah [to prevent] that we take except him with whom we found our possession. Indeed, we would then be unjust." <> Ya ce: "Allah Ya tsare mu daga mu kãma wani fãce wanda muka sãmi kãyanmu a wurinsa. Lalle ne mũ, a lõkacin nan, haƙĩƙa, azzãlumai ne." = --Qur'an 12:79
    So when they had despaired of him, they secluded themselves in private consultation. The eldest of them said, "Do you not know that your father has taken upon you an oath by Allah and [that] before you failed in [your duty to] Joseph? So I will never leave [this] land until my father permits me or Allah decides for me, and He is the best of judges. <> Sabõda haka, a lõkacin da suka yanke tsammãni daga gare shi, sai suka fita sunã mãsu gãnãwa. Babbansu ya ce: "Shin, ba ku sani ba cẽwa lalle ne ubanku yariƙi alkawari daga Allah a kanku, kuma daga gabanin haka akwai abin da kuka yi na sakaci game da Yũsufu? Sabõda haka, bã zan gushe daga ƙasar nan ba fãce ubana yã yi mini izni, kõ kuwa Allah Ya yi hukunci a gare ni, kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mahukunta." = --Qur'an 12:80
    Return to your father and say, "O our father, indeed your son has stolen, and we did not testify except to what we knew. And we were not witnesses of the unseen, <> "Ku kõma zuwa ga ubanku, ku gaya masa: Yã bãbanmu, lalle ne ɗanka yã yi sãta, kuma ba mu yi shaida ba fãce da abin da muka sani, kuma ba mu kasance mun san gaibu ba." = --Qur'an 12:81
    And ask the city in which we were and the caravan in which we came - and indeed, we are truthful," <> "Kuma ka tambayi alƙarya wadda muka kasance a cikinta da ãyari wanda muka gabãto acikinsa, kuma lalle ne haƙĩƙa, mũ mãsu gaskiya ne." = --Qur'an 12:82
    [Jacob] said, "Rather, your souls have enticed you to something, so patience is most fitting. Perhaps Allah will bring them to me all together. Indeed it is He who is the Knowing, the Wise." <> Ya ce: "Ã'a, zukatanku sun ƙawãta wani al'amari a gare ku. Sai haƙuri mai kyãwo, akwai tsammãnin Allah Ya zo mini da su gabã ɗaya (Yũsufu da 'yan'uwansa). Lalle ne Shĩ ne Masani, Mai hikima." = --Qur'an 12:83
    And he turned away from them and said, "Oh, my sorrow over Joseph," and his eyes became white from grief, for he was [of that] a suppressor. <> Kuma ya jũya daga gare su, kuma ya ce: "Yã baƙin cikina a kan Yũsufu!" Kuma idãnunsa suka yi fari sabõda huznu sa'an nan yanã ta haɗẽwar haushi. = --Qur'an 12:84
    They said, "By Allah, you will not cease remembering Joseph until you become fatally ill or become of those who perish." <> Suka ce: "Tallahi! Bã zã ka gushe ba, kanã ambaton Yũsufu, har ka kasance Mai rauni ƙwarai, kõ kuwa ka kasance daga mãsu halaka." = --Qur'an 12:85
    He said, "I only complain of my suffering and my grief to Allah, and I know from Allah that which you do not know. <> Ya ce: "Abin sani kawai, inã kai ƙarar baƙin cikĩna da sunõna zuwa ga Allah, kuma na san abin da ba ku sani ba daga Allah." = --Qur'an 12:86
    O my sons, go and find out about Joseph and his brother and despair not of relief from Allah. Indeed, no one despairs of relief from Allah except the disbelieving people." <> "Yã ɗiyãna! Sai ku tafi ku nẽmo lãbãrin Yũsufu da ɗan'uwansa. Kada ku yanke tsammãni daga rahamar Allah. Lalle ne, bãbu Mai yanke tsammãni daga rahamar Allah fãce mutãne kãfirai." = --Qur'an 12:87
    So when they entered upon Joseph, they said, "O 'Azeez, adversity has touched us and our family, and we have come with goods poor in quality, but give us full measure and be charitable to us. Indeed, Allah rewards the charitable." <> Sa'an nan a lõkacin da suka shiga gare shi suka ce: "Yã kai Azĩzu! Cũta ta shãfe mu, mũ da iyãlinmu, kuma mun zo da wata hãja maras kuma. Sai ka cika mana ma'auni, kuma ka yi sadaka a gare mu. Lalle ne Allah Yanã sãka wa mãsu yin sadaka. " = --Qur'an 12:88
    He said, "Do you know what you did with Joseph and his brother when you were ignorant?" <> Ya ce: "Shin, kan san abin da kuka aikata ga Yũsufu da ɗan'uwansa a lõkacin da kuke jãhilai?" = --Qur'an 12:89
    They said, "Are you indeed Joseph?" He said "I am Joseph, and this is my brother. Allah has certainly favored us. Indeed, he who fears Allah and is patient, then indeed, Allah does not allow to be lost the reward of those who do good." <> Saka ce: "Shin kõ, lalle ne, kai ne Yũsufu?" Ya ce: "Nĩ ne Yũsufu, kuma wamian shĩ ne ɗan'uwãna. Hƙĩƙa Allah Yã yi falala a gare mu. Lalle ne, shi wanda ya bi Allah da taƙawa, kuma ya yi haƙuri, to, Lalle ne Allah bã Ya tõzarta lãdar mãsu kyautatãwa." = --Qur'an 12:90
    They said, "By Allah, certainly has Allah preferred you over us, and indeed, we have been sinners." <> Suka ce: "Tallahi! Lalle ne haƙĩƙa, Allah Yã zãɓe ka akannmu, kuma lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, mãsu kuskure." = --Qur'an 12:91
    He said, "No blame will there be upon you today. Allah will forgive you; and He is the most merciful of the merciful." <> Ya ce: "Bãbu zargi akanku a yau, Allah Yanã gãfartã muku, kuma Shĩ ne Mafi rahamar mãsu rahama." = --Qur'an 12:92
    Take this, my shirt, and cast it over the face of my father; he will become seeing. And bring me your family, all together." <> "Ku tafi da rĩgãta wannan, sa'an nan ku jẽfa ta a kan fuskar mahaifina, zai kõma mai gani. Kuma ku zo mini da iyãlinku bãki ɗaya." = --Qur'an 12:93
    And when the caravan departed [from Egypt], their father said, "Indeed, I find the smell of Joseph [and would say that he was alive] if you did not think me weakened in mind." <> Kuma, a lõkacin da ãyari ya bar (Masar) ubansa ya ce: "Lalle ne nĩ inã shãƙar iskar Yũsufu, bã dõmin kanã ƙaryata ni ba." = --Qur'an 12:94
    They said, "By Allah, indeed you are in your [same] old error." <> Suka ce: "Tallahi lalle ne, kai, haƙĩƙa, kanã a cikin ɓatarka daɗaɗɗa." = --Qur'an 12:95
    And when the bearer of good tidings arrived, he cast it over his face, and he returned [once again] seeing. He said, "Did I not tell you that I know from Allah that which you do not know?" <> Sa'an nan a lõkacin da mai bãyar da bushãra ya je, sai ya jẽfa ta a kan fuskarsa, sai ya kõma mai gani. Ya ce: "Shin, ban gaya muku ba, lalle ne, ni inã sanin abin da ba ku sani ba, daga Allah?" = --Qur'an 12:96
    They said, "O our father, ask for us forgiveness of our sins; indeed, we have been sinners." <> Suka ce: "Yã ubanmu! ka nẽma mana gãfara ga zunubanmu, lalle ne mũ, mun kasance mãsu kuskure." = --Qur'an 12:97
    He said, "I will ask forgiveness for you from my Lord. Indeed, it is He who is the Forgiving, the Merciful." <> Ya ce: "Da sannu zã ni nẽma muku gãfara daga Ubangijina. Shi ne Mai gãfara, Mai jin ƙai." = --Qur'an 12:98
    And when they entered upon Joseph, he took his parents to himself and said, "Enter Egypt, Allah willing, safe [and secure]." <> Sa'an nan a lõkacin da suka shiga gun Yũsufu, yã tattara mahaifansa biyu a gare shi, kuma ya ce: "Ku shiga Masar in Allah Ya so, kuna amintattu." = --Qur'an 12:99
    And he raised his parents upon the throne, and they bowed to him in prostration. And he said, "O my father, this is the explanation of my vision of before. My Lord has made it reality. And He was certainly good to me when He took me out of prison and brought you [here] from bedouin life after Satan had induced [estrangement] between me and my brothers. Indeed, my Lord is Subtle in what He wills. Indeed, it is He who is the Knowing, the Wise. <> Kuma ya ɗaukaka iyãyensa biyu a kan karaga, sa'an nan suka fãɗi a gare shi, suna mãsu sujada. Kuma ya ce: "Ya bãbãna! Wannan ita ce fassarar mafarkin nan nãwa. Lalle ne Ubangijina Ya sanya shi ya tabbata sõsai, kuma lalle ne Ya kyautata game da ni a lõkacin da Ya fitar da ni daga kurkuku. Kuma Ya zo da ku daga ƙauye, a bãyan Shaiɗan yã yi fisgar ɓarna a tsakãnĩna da tsakãnin 'yan'uwana, Lalle ne Ubangijina Mai tausasawa ne ga abin da Yake so. Lalle ne Shĩ, Shĩ ne Masani, Mai hikima." = --Qur'an 12:100
    My Lord, You have given me [something] of sovereignty and taught me of the interpretation of dreams. Creator of the heavens and earth, You are my protector in this world and in the Hereafter. Cause me to die a Muslim and join me with the righteous." <> "Yã Ubangijina lalle ne Kã bã ni daga mulki, kuma Kã sanar da ni daga fassarar lãbaru. Ya Mahaliccin sammai da ƙasa! Kai ne Majiɓincĩna a dũniya da Lãhira Ka karɓi raina inã Musulmi, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai." = --Qur'an 12:101
    That is from the news of the unseen which We reveal, [O Muhammad], to you. And you were not with them when they put together their plan while they conspired. <> Wannan daga lãbarun gaibi ne, Munã yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lõkacin da suke yin niyyar zartar da al'amarinsu, alhãli sunã yin mãkirci. = --Qur'an 12:102
    And most of the people, although you strive [for it], are not believers. <> Kuma mafi yawan mutãne ba su zama mãsu ĩmãni ba, kõ da kã yi kwaɗayin haka. = --Qur'an 12:103
    And you do not ask of them for it any payment. It is not except a reminder to the worlds. <> Kuma bã ka tambayar su wata lãdã a kansa. Shĩ bai zama ba fãce ambato dõmin halittu. = --Qur'an 12:104
    And how many a sign within the heavens and earth do they pass over while they, therefrom, are turning away. <> Kuma da yawa, wata ãyã a cikin sammai da ƙasa sunã shũɗẽwa a kanta kuma sũ, sunã bijirẽwa daga gare ta. = --Qur'an 12:105
    And most of them believe not in Allah except while they associate others with Him. <> Kuma mafi yawansu ba su yin ĩmãni da Allah fãce kuma sunã mãsu shirki. = --Qur'an 12:106
    Then do they feel secure that there will not come to them an overwhelming [aspect] of the punishment of Allah or that the Hour will not come upon them suddenly while they do not perceive? <> Shin fa, sun amince cẽwa wata masĩfa daga azãbar Allah ta zo musu ko kuwa Tãshin ¡iyãma ta zo musu kwatsam, alhãli sũ ba su sani ba? = --Qur'an 12:107
    Say, "This is my way; I invite to Allah with insight, I and those who follow me. And exalted is Allah; and I am not of those who associate others with Him." <> Ka ce: "Wannan ce hanyãta; inã kira zuwa ga Allah a kan basĩra, nĩ da waɗanda suka bĩ ni, kuma tsarki ya tabbata ga Allah! Nĩ kuma, ban zama daga mãsu shirki ba." = --Qur'an 12:108
    And We sent not before you [as messengers] except men to whom We revealed from among the people of cities. So have they not traveled through the earth and observed how was the end of those before them? And the home of the Hereafter is best for those who fear Allah; then will you not reason? <> Kuma ba Mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã wahayi zuwa gare su, daga mutãnen ƙauyuka. Shin fa, ba su yi tafiya a cikin ƙasa ba, dõmin su dũbayadda ãƙibar waɗanda suka kasance daga gabãninsu ta zama? Kuma lalle ne gidan Lãhira shĩ ne mafi alhẽri ga waɗanda suka yi taƙawa? Shin fa, bã ku hankalta? = --Qur'an 12:109
    [They continued] until, when the messengers despaired and were certain that they had been denied, there came to them Our victory, and whoever We willed was saved. And Our punishment cannot be repelled from the people who are criminals. <> Har a lõkacin da Manzanni suka yanke tsammãni, kuma suka yi zaton cẽwa an jingina suga ƙarya, sai taimakonMu ya je masu, Sa'an nan Mu tsẽrar da wanda Muke so, kuma bã a mayar da azãbarMu daga mutãne mãsu laifi. = --Qur'an 12:110
    There was certainly in their stories a lesson for those of understanding. Never was the Qur'an a narration invented, but a confirmation of what was before it and a detailed explanation of all things and guidance and mercy for a people who believe. <> Lalle ne haƙĩƙa abin kula yã kasance a cikin ƙissoshinsu ga masu hankali. Bai kasance wani ƙirƙiran lãbãri ba kuma amma shi gaskatãwa ne ga, abin da yake a gaba gare shi, da rarrabẽwar dukan abũbuwa, da shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suka yi ĩmãni. = --Qur'an 12:111
    Alif, Lam, Meem, Ra. These are the verses of the Book; and what has been revealed to you from your Lord is the truth, but most of the people do not believe. <> A. L̃. M̃.R. Waɗancan ayõyin littãfi ne kuma abin da aka saukar gare ka daga Ubangijinka ne gaskiya, kuma amma mafi yawan mutãne bã su yin ĩmãni. = --Qur'an 13:1
    It is Allah who erected the heavens without pillars that you [can] see; then He established Himself above the Throne and made subject the sun and the moon, each running [its course] for a specified term. He arranges [each] matter; He details the signs that you may, of the meeting with your Lord, be certain. <> Allah Shi ne wanda Ya ɗaukaka sammai, bã da ginshiƙai ba waɗanda kuke ganin su. Sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, kuma Ya hõre rãnã da watã, kõwane yanã gudãna zuwa ga ajali ambatacce. Yanã shirya al'amari, Yanã rarrabe ãyõyi daki-daki, mai yiwuwa ne ku yi yaƙĩni da haɗuwa da Ubangijinku. = --Qur'an 13:2
    And it is He who spread the earth and placed therein firmly set mountains and rivers; and from all of the fruits He made therein two mates; He causes the night to cover the day. Indeed in that are signs for a people who give thought. <> Kuma shĩ, ne wanda Ya shimfiɗa kasa, kuma Ya sanya duwãtsu da kõguna a cikinta, kuma daga dukan 'ya'yan itãce Ya sanya ma'aura biyu cikinsu. Yanã sanya dare ya rufe yini. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin tunãni. = --Qur'an 13:3
    And within the land are neighboring plots and gardens of grapevines and crops and palm trees, [growing] several from a root or otherwise, watered with one water; but We make some of them exceed others in [quality of] fruit. Indeed in that are signs for a people who reason. <> Kuma a cikin ƙasa akwai yankuna mãsu maƙwabtaka, da gõnaki na inabõbi da shũka da dabĩnai iri guda, da waɗanda bã iri guda ba, anã shayar da su da ruwa guda. Kuma Munã fĩfĩta sãshensa a kan sãshe a wajen ci. Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga muiãne waɗanda suke hankalta. = --Qur'an 13:4
    And if you are astonished, [O Muhammad] - then astonishing is their saying, "When we are dust, will we indeed be [brought] into a new creation?" Those are the ones who have disbelieved in their Lord, and those will have shackles upon their necks, and those are the companions of the Fire; they will abide therein eternally. <> Kuma idan ka yi mãmãki, to, mãmãkin kam shi ne maganarsu, "Shin, idan muka kasance turɓãya, zã mu zama a cikin wata halitta sãbuwa?" Waɗancan ne waɗanda suka kãfirta da Ubangijinsu, kuma waɗanda akwai ƙuƙumai a cikin wuyõyinsu, kuma waɗancan ne abõkan wuta. Sũ, a cikinta, mãsu dawwama ne. = --Qur'an 13:5
    They impatiently urge you to bring about evil before good, while there has already occurred before them similar punishments [to what they demand]. And indeed, your Lord is full of forgiveness for the people despite their wrongdoing, and indeed, your Lord is severe in penalty. <> Kuma sunã nẽman ka da gaggãwa da azãba a gabãnin rahama, alhãli kuwa abũbuwan misãli sun gabãta a gabãninsu. Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Ma'abũcin gãfara ne ga mutãne a kan zãluncinsu, kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Mai tsananin uƙũba ne. = --Qur'an 13:6
    And those who disbelieved say, "Why has a sign not been sent down to him from his Lord?" You are only a warner, and for every people is a guide. <> Kuma waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa don me ba a saukar da wata ãyã a gare shi ba daga Ubangijinsa? Abin sani kawai, kai dai mai gargaɗi ne kuma a cikin kõwaɗanne mutãne akwai mai shiryarwa. = --Qur'an 13:7
    Allah knows what every female carries and what the wombs lose [prematurely] or exceed. And everything with Him is by due measure. <> Allah Yanã sanin abin da kõwace mace take ɗauke da shi a cikinta da abin da mahaifu suke ragẽwa da abin da suke ƙãrãwa. Kuma dukkan kõme, a wurinSa, da gwargwado yake. = --Qur'an 13:8
    [He is] Knower of the unseen and the witnessed, the Grand, the Exalted. <> Shi ne Masanin fake da bayyane, Mai girma, Maɗaukaki. = --Qur'an 13:9
    It is the same [to Him] concerning you whether one conceals [his] speech or one publicizes it and whether one is hidden by night or conspicuous [among others] by day. <> Daidai ne daga gare ku, wanda ya asirta magana da wanda ya bayyana game da ita, da wanda yake shi mai nẽman ɓõyewa ne da dare, da mai bayyana a cikin tafiyarsa a hanya da rãna. = --Qur'an 13:10
    For each one are successive [angels] before and behind him who protect him by the decree of Allah. Indeed, Allah will not change the condition of a people until they change what is in themselves. And when Allah intends for a people ill, there is no repelling it. And there is not for them besides Him any patron. <> (Kowannenku) Yanã da waɗansu malã'iku mãsu maye wa jũna a gaba gare shi da bãya gare shi, sunã tsare shi daga umurnin Allah. Lalle ne Allah bã Ya canja abin da yake ga, mutãne sai sun canja abin da yake ga zukatansu. Kuma idan Allah Ya yi nufin wata azãba game da mutãne, to, bãbu mai mayar da ita, kuma bã su da wani majiɓinci baicin Shi. = --Qur'an 13:11
    It is He who shows you lightening, [causing] fear and aspiration, and generates the heavy clouds. <> Shĩ ne Wanda Yake nũna muku walƙiya dõmin tsõro da tsammãni, kuma Ya ƙãga halittar girãgizai mãsu nauyi. = --Qur'an 13:12
    And the thunder exalts [Allah] with praise of Him - and the angels [as well] from fear of Him - and He sends thunderbolts and strikes therewith whom He wills while they dispute about Allah; and He is severe in assault. <> Kuma arãdu tanã tasbĩhi game da gõde Masa, da malã'iku dõmin tsoronsa. Kuma Yanã aiko tsãwawwaki, sa'an nan Ya sãmi wanda Yake so da su alhãli kuwa sũ, sunã jãyayya a cikin (al'amarin) Allah kuma shĩ ne mai tsananin hĩla. = --Qur'an 13:13
    To Him [alone] is the supplication of truth. And those they call upon besides Him do not respond to them with a thing, except as one who stretches his hands toward water [from afar, calling it] to reach his mouth, but it will not reach it [thus]. And the supplication of the disbelievers is not but in error [i.e. futility]. <> Yanã da kiran gaskiya, kuma waɗanda (kãfirai) suke kira baicinsa, bã su karɓa musu da kõme fãce kamar mai shimfiɗa tãfukansa Zuwa ga ruwa (na girgije) dõmin (ruwan) ya kai ga bãkinsa, kuma shi bã mai kaiwa gare shi ba. Kuma kiran kãfirai (ga wanin Allah) bai zama ba fãce yanã a cikin ɓata. = --Qur'an 13:14
    And to Allah prostrates whoever is within the heavens and the earth, willingly or by compulsion, and their shadows [as well] in the mornings and the afternoons. <> Kuma sabõda Allah wanda yake a cikin sammai da ƙasa suke yin sujada, so da ƙi, kuma da inuwõyinsu, a sãfe da maraice. = --Qur'an 13:15
    Say, "Who is Lord of the heavens and earth?" Say, "Allah." Say, "Have you then taken besides Him allies not possessing [even] for themselves any benefit or any harm?" Say, "Is the blind equivalent to the seeing? Or is darkness equivalent to light? Or have they attributed to Allah partners who created like His creation so that the creation [of each] seemed similar to them?" Say, "Allah is the Creator of all things, and He is the One, the Prevailing." <> Ka ce: "Wãne ne Ubangijin sammai da ƙasa?" Ka ce: "Allah". Ka ce: "Ashe fa, kun riƙi waɗansu masõya baicin Shi, waɗanda ba su mallaka wa kansu wani amfãni ba kuma haka bã su tũre wata cũta?" Ka ce: "Shin makãho da mai gani sunã daidaita? Kõ shin duhu da haske sunã daidaita? ko sun sanya ga Allah waɗansu abõkan tãrayya waɗanda suka yi halitta kamar halittarSa sa'an nan halittar ta yi kama da jũna a gare su?" Ka ce: "Allah ne Mai halitta kõme kuma Shĩ ne Maɗaukaki, Marinjãyi." = --Qur'an 13:16
    He sends down from the sky, rain, and valleys flow according to their capacity, and the torrent carries a rising foam. And from that [ore] which they heat in the fire, desiring adornments and utensils, is a foam like it. Thus Allah presents [the example of] truth and falsehood. As for the foam, it vanishes, [being] cast off; but as for that which benefits the people, it remains on the earth. Thus does Allah present examples. <> Ya saukar da ruwa daga sama, sai magudanai suka gudãna da gwargwadonsu, Sa'an nan kõgi ya ɗauki kumfa mai ƙãruwa, kuma daga abin da suke zuga a kansa (azurfa ko zinari kõ ƙarfe) a cikin wuta dõmin nẽman ado kõ kuwa kãyan ɗãki akwai kumfa misãlinsa (kumfar ruwa). Kamar wancan ne Allah Yake bayyana gaskiya da ƙarya. To, amma kumfa, sai ya tafi ƙẽƙasasshe, kumaamma abin da yake amfãnin mutãne sai ya zauna a cikin ƙasa. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana misãlai. = --Qur'an 13:17
    For those who have responded to their Lord is the best [reward], but those who did not respond to Him - if they had all that is in the earth entirely and the like of it with it, they would [attempt to] ransom themselves thereby. Those will have the worst account, and their refuge is Hell, and wretched is the resting place. <> Ga waɗanda suka karɓa wa Ubangijinsu akwai abu mafi kyau a gare su, kuma waɗanda suke ba su karɓa Masa ba, to, lalle dã sunã da abin da yake a cikin ƙasa gaba ɗaya da misãlinsa tãre da shi, haƙĩƙa, dã sun yi fansa da shi. Waɗancan sunã da mummunan bincike kuma matabbatarsu Jahannama ce, kuma tir da ita ta zama shimfida. = --Qur'an 13:18
    Then is he who knows that what has been revealed to you from your Lord is the truth like one who is blind? They will only be reminded who are people of understanding - <> Shin, fa, wanda yake sanin cẽwa lalle abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka ne gaskiya yanã zama kamar wanda yake makãho? Abin sani kawai masu hankali sũ ke yin tunãni. = --Qur'an 13:19
    Those who fulfill the covenant of Allah and do not break the contract, <> Sũ ne waɗanda suke cikãwa da alkawarin Allah, kuma bã su warware alkawari. = --Qur'an 13:20
    And those who join that which Allah has ordered to be joined and fear their Lord and are afraid of the evil of [their] account, <> Kuma sũ ne waɗanda suke sãdar da abin da Allah Ya yi umurni da shi dõmin a sãdar da shi kuma sunã tsõron Ubangijinsu, kuma sunã tsõron mummũnan bincike. = --Qur'an 13:21
    And those who are patient, seeking the countenance of their Lord, and establish prayer and spend from what We have provided for them secretly and publicly and prevent evil with good - those will have the good consequence of [this] home - <> Kuma waɗanda suka yi haƙuri dõmin nẽman yardar Ubangijinsu, kuma suka tsayar da salla, kuma suka ciyar da abin da Muka azurta su da shi, a asirce da bayyane, kuma sunã tunkuɗe mummunan aiki da mai kyau. Waɗancan sunã da ãƙibar gida mai kyau. = --Qur'an 13:22
    Gardens of perpetual residence; they will enter them with whoever were righteous among their fathers, their spouses and their descendants. And the angels will enter upon them from every gate, [saying], <> Gidãjen Aljannar zama sunã shigarsu, sũ da waɗandasuka kyautatu daga iyãyensu, da mãtansu da zũriyarsu. Kuma malã'iku sunã shiga zuwa gunsu ta kõwace kõfa. = --Qur'an 13:23
    "Peace be upon you for what you patiently endured. And excellent is the final home." <> "Aminci ya tabbata a kanku sabõda abin da kuka yi wa haƙuri. Sãbõda haka madalla da ni'imar ãƙibar gida." = --Qur'an 13:24
    But those who break the covenant of Allah after contracting it and sever that which Allah has ordered to be joined and spread corruption on earth - for them is the curse, and they will have the worst home. <> Kuma waɗanda suka warware alkawarin Allah daga bãyan ƙulla shi, kuma sunã yanke abin da Allah Ya yi umurui da shi dõmin a sãdar da shi kuma sunã ɓarna a cikin ƙasar. Waɗancan sunã da wata la'ana, kuma sunã da mũnin gida. = --Qur'an 13:25
    Allah extends provision for whom He wills and restricts [it]. And they rejoice in the worldly life, while the worldly life is not, compared to the Hereafter, except [brief] enjoyment. <> Allah ne Yake shimfiɗa arziki ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuntatãwa. Kuma sun yi farin ciki da rãyuwar dũniya, alhalikuwa rãyuwar dũniya ba ta zama ba dangane ga ta Lãhira fãce jin dãɗi kaɗan. = --Qur'an 13:26
    And those who disbelieved say, "Why has a sign not been sent down to him from his Lord?" Say, [O Muhammad], "Indeed, Allah leaves astray whom He wills and guides to Himself whoever turns back [to Him] - <> Kuma wanɗanda suka kãfirta, sunã cẽwa, "Don me ba a saukar da wata ãyã ba a kansa daga Ubangijinsa?" Ka ce: "Lalle ne Allah Yanã ɓatar da wanda Yake so kuma Yanã shiryar da wanda ya tũba zuwa gare shi." = --Qur'an 13:27
    Those who have believed and whose hearts are assured by the remembrance of Allah. Unquestionably, by the remembrance of Allah hearts are assured." <> Waɗanda suka yi ĩmãni kuma zukãtansu sukan natsu da ambaton Allah. To, da ambaton Allah zukãta suke natsuwa. = --Qur'an 13:28
    Those who have believed and done righteous deeds - a good state is theirs and a good return. <> Waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata aiki nagari, farin ciki yã tabbata a gare su, da kyakkyawar makõma. = --Qur'an 13:29
    Thus have We sent you to a community before which [other] communities have passed on so you might recite to them that which We revealed to you, while they disbelieve in the Most Merciful. Say, "He is my Lord; there is no deity except Him. Upon Him I rely, and to Him is my return." <> Kamar wancan ne Muka aika ka a cikin al'umma wanda take waɗansu al'ummai sun shũɗe daga gabaninta, dõmin ka karanta musu abin da Muka yi wahayi zuwa a gare ka, alhãli kuwa sũ, sunãkãfirta da Rahaman. Ka ce: "Shi ne Ubangijĩna, bãbu abin, bautãwa fãce Shi, a gare Shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi tũbãta take." = --Qur'an 13:30
    And if there was any qur'an by which the mountains would be removed or the earth would be broken apart or the dead would be made to speak, [it would be this Qur'an], but to Allah belongs the affair entirely. Then have those who believed not accepted that had Allah willed, He would have guided the people, all of them? And those who disbelieve do not cease to be struck, for what they have done, by calamity - or it will descend near their home - until there comes the promise of Allah. Indeed, Allah does not fail in [His] promise. <> Kuma dã lalle an saukar da wani littafi abin karatu wanda ake tafiyar da duwãtsu game da shi, kõ kuma aka yanyanke ƙasa da shi, ko kuwa aka yi magana da matattu da shi (dã ba su yi ĩmãni ba). Ã'a ga Allah al'amari yake gabã ɗaya! Shin fa, waɗanda suka yi ĩmãni ba su yanke tsammãni ba da cẽwa da Allah Yã so, dã Yã shiryar da mutãne gabã ɗaya? Kuma waɗanda suka yi kãfirci ba zã su gushe ba wata masĩfa tanã samun su sabõda abin da suka aikata, kõ kuwa ka saukã kusa da gidãjẽnsu, har wa'adin Allah ya zo. Kuma lalle ne Allah bã ya sãɓã wa lõkacin alkawari. = --Qur'an 13:31
    And already were [other] messengers ridiculed before you, and I extended the time of those who disbelieved; then I seized them, and how [terrible] was My penalty. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili da Manzanni kãfinka, sai Na yi jinkiri ga waɗanda suka kãfirta, sa'an nan Na kãma su. To, yãya uƙũbãta take? = --Qur'an 13:32
    Then is He who is a maintainer of every soul, [knowing] what it has earned, [like any other]? But to Allah they have attributed partners. Say, "Name them. Or do you inform Him of that which He knows not upon the earth or of what is apparent of speech?" Rather, their [own] plan has been made attractive to those who disbelieve, and they have been averted from the way. And whomever Allah leaves astray - there will be for him no guide. <> Shin fa, wanda shĩ Yake tsaye a kan kõwane rai game da abin da ya tanada (zai zama kamar wanda ba haka ba)? Kuma suka sanya abõkan tãrayya ga Allah! Ka ce: "Ku ambaci sũnãyensu."Ko kunã bai wa Allah lãbãri ne game da abin da bai sani ba a cikin ƙasa? Kõ da bayyananniyar magana kuke yin shirka, (banda a cikin zũciya)? Ã'a, an dai ƙawãta wa waɗanda suka kafirta mãkircinsu kuma an kange su daga hanya. Kuma wanda Allah Ya ɓatar to, bãbu wani mai shiryarwa a gare shi!" = --Qur'an 13:33
    For them will be punishment in the life of [this] world, and the punishment of the Hereafter is more severe. And they will not have from Allah any protector. <> Sunã da wata azãba a cikin rãyuwar dũniya, kuma haƙĩƙa azãbar Lãhira ce mafi tsanani kuma bãbu wani mai tsare su daga Allah. = --Qur'an 13:34
    The example of Paradise, which the righteous have been promised, is [that] beneath it rivers flow. Its fruit is lasting, and its shade. That is the consequence for the righteous, and the consequence for the disbelievers is the Fire. <> Misãlin Aljanna wadda aka yi alkawarinta ga mãsu taƙawa, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinta. Abincinta yana madawwami da inuwarta. Waccan ce ãƙibar waɗanda suka yi taƙawa, kuma ãƙibar kãfirai, ita ce wuta, = --Qur'an 13:35
    And [the believers among] those to whom We have given the [previous] Scripture rejoice at what has been revealed to you, [O Muhammad], but among the [opposing] factions are those who deny part of it. Say, "I have only been commanded to worship Allah and not associate [anything] with Him. To Him I invite, and to Him is my return." <> Kuma waɗanda Muka bã su Littãfi sunã farin ciki da abin da aka saukar zuwa gare ka, kuma daga ƙungiyõyi akwai mai musun sãshensa. Ka ce: "Abin sani kawai, an umurce ni da in bauta wa Allah kuma kada in yi shirka da Shi, zuwa gare Shi nake kira, kuma zuwa gare Shi makõmata take." = --Qur'an 13:36
    And thus We have revealed it as an Arabic legislation. And if you should follow their inclinations after what has come to you of knowledge, you would not have against Allah any ally or any protector. <> Kuma kamar wancan ne Muka saukar da shi, Hukunci a cikin Lãrabci. Kuma lalle ne idan kã bi son zuciyõyinsu a bãyan abin da ya zo maka na ilmi, bãbu wani masõyi a gare ka mai kãre ka daga Allah, kuma bãbu matsari. = --Qur'an 13:37
    And We have already sent messengers before you and assigned to them wives and descendants. And it was not for a messenger to come with a sign except by permission of Allah. For every term is a decree. <> Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika waɗansu manzanni, daga gabãninka, kuma Muka sanya mãtan aure a gare su da zũriyya, kuma ba ya kasancẽwa ga wani Manzo ya zo da wata ãyã, sai da iznin Allah. Ga kõwane ajali akwai littãfi. = --Qur'an 13:38
    Allah eliminates what He wills or confirms, and with Him is the Mother of the Book. <> Allah Yanã shafe abin da Yake so, kuma Yanã tabbatarwa kuma a wurinsa asalin Littãfin yake. = --Qur'an 13:39
    And whether We show you part of what We promise them or take you in death, upon you is only the [duty of] notification, and upon Us is the account. <> Kuma imma lalle Mu nũna maka sãshen abin da Muke yi musu wa'adi, kõ kuwa lalle Mu karɓi ranka to abin sani kawai iyarwa ce a kanka, kuma hisãbi yana gare Mu. = --Qur'an 13:40
    Have they not seen that We set upon the land, reducing it from its borders? And Allah decides; there is no adjuster of His decision. And He is swift in account. <> Shin, kuma ba su gani ba cẽwa lalle ne, Muna jẽ wa ƙasar (su), Munã rage ta daga gẽfunanta? Kuma Allah ne Yake yin hukuncinsa. Babu mai bincike ga hukuncinsa. Kuma shĩ ne Mai gaggãwar sakamako. = --Qur'an 13:41
    And those before them had plotted, but to Allah belongs the plan entirely. He knows what every soul earns, and the disbelievers will know for whom is the final home. <> Kuma lalle ne waɗanda suke a gabãninsu sun yi mãkirci. To, ga Allah mãkircin yake gabã ɗaya. Ya san abin da kõwane rai yake tãnada. Kuma kãfirai zã su sani, ga wane ãƙibar gida take. = --Qur'an 13:42
    And those who have disbelieved say, "You are not a messenger." Say, [O Muhammad], "Sufficient is Allah as Witness between me and you, and [the witness of] whoever has knowledge of the Scripture." <> Kuma waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: "Ba a aiko ka ba." Ka ce, "Allah Yã isa zama shaida a tsakãnina da tsakãninku da wanda yake a wurinsa akwai ilmin Littãfi." = --Qur'an 13:43
    Alif, Lam, Ra. [This is] a Book which We have revealed to you, [O Muhammad], that you might bring mankind out of darknesses into the light by permission of their Lord - to the path of the Exalted in Might, the Praiseworthy - <> A. L̃.R. Littãfi ne mun saukar da shi zuwa gare ka dõmin ka fitar da mutãne daga duhunhuna zuwa ga haske, da iznin Ubangijinsu, zuwa ga tafarkin Mabuwãyi, Abin gõdẽwa. = --Qur'an 14:1
    Allah, to whom belongs whatever is in the heavens and whatever is on the earth. And woe to the disbelievers from a severe punishment <> Allah wanda Yake Yanã da abin da ke cikin sammai da cikin ƙasa. Kuma bone yã tabbata ga kãfirai daga azãba mai tsanani. = --Qur'an 14:2
    The ones who prefer the worldly life over the Hereafter and avert [people] from the way of Allah, seeking to make it (seem) deviant. Those are in extreme error. <> Waɗanda suka fi son rãyuwar dũniya fiye da ta Lãhira, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah, kuma sunã nẽman ta karkace. Waɗancan na a cikin ɓata mai nĩsa. = --Qur'an 14:3
    And We did not send any messenger except [speaking] in the language of his people to state clearly for them, and Allah sends astray [thereby] whom He wills and guides whom He wills. And He is the Exalted in Might, the Wise. <> Kuma ba Mu aika wani Manzo ba fãce da harshen mutãnensa dõmin ya bayyanã musu. Sa'an nan Allah Ya ɓatar da wanda Yake so kuma Ya shiryar da wanda Yake so, Kuma shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima. = --Qur'an 14:4
    And We certainly sent Moses with Our signs, [saying], "Bring out your people from darknesses into the light and remind them of the days of Allah." Indeed in that are signs for everyone patient and grateful. <> Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika Mũsã game, da ãyõin Mu cẽwa, "Ka fitar da mutãnenkadaga duhu zuwa ga haske. Kuma ka tunar musu da kwãnukan (masĩfun) Allah." Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi dõmin dukan mai yawan haƙuri, mai gõdiya. = --Qur'an 14:5
    And [recall, O Children of Israel], when Moses said to His people, "Remember the favor of Allah upon you when He saved you from the people of Pharaoh, who were afflicting you with the worst torment and were slaughtering your [newborn] sons and keeping your females alive. And in that was a great trial from your Lord. <> Kuma a lõkacin da Mũsã yace wa mutãnensa, "Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da Ya tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, sunã yi muku mummunar azãba, kuma sunã yanyanka ɗiyanku, kuma sunã rãyar da mãtanku. Kuma a cikin wancan akwai jarrabãwa mai girmã daga Ubangijinku." = --Qur'an 14:6
    And [remember] when your Lord proclaimed, 'If you are grateful, I will surely increase you [in favor]; but if you deny, indeed, My punishment is severe.' " <> Kuma a lõkacin da Ubangijinku Ya sanar, "Lalle ne idan kun gõde, haƙĩƙa, Inã ƙãramuku, kuma lalle ne idan kun kãfirta haƙĩƙa azãbãta, tabbas, mai tsanani ce." = --Qur'an 14:7
    And Moses said, "If you should disbelieve, you and whoever is on the earth entirely - indeed, Allah is Free of need and Praiseworthy." <> Kuma Mũsã ya ce: "Idan kun kãfirta kũ da waɗanda suke a cikin ƙasa, gabã ɗaya, to, lalle ne Allah haƙĩƙa Mawadãci ne, Mai yawan gõdiya." = --Qur'an 14:8
    Has there not reached you the news of those before you - the people of Noah and 'Aad and Thamud and those after them? No one knows them but Allah. Their messengers brought them clear proofs, but they returned their hands to their mouths and said, "Indeed, we disbelieve in that with which you have been sent, and indeed we are, about that to which you invite us, in disquieting doubt." <> Shin lãbãrin waɗanda suke a gabãninku, mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdawa bai zomuku ba? Kuma da waɗanda suke daga bãyansu bãbu wanda yake sanin su fãce Allah? Manzanninsu sun jẽ musu da hujjõji mabayyana, sai suka mayar da hannayensu a cikin bãkunansu, kuma suka ce: "Lalle ne mũ, mun kãfirta da abinda aka aiko ku da shi. Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa munã a cikin shakkada abin do kuke kiran mu zuwa gare shi, mai sanya kõkanto." = --Qur'an 14:9
    Their messengers said, "Can there be doubt about Allah, Creator of the heavens and earth? He invites you that He may forgive you of your sins, and He delays your death for a specified term." They said, "You are not but men like us who wish to avert us from what our fathers were worshipping. So bring us a clear authority." <> Manzanninsu suka ce "Ashe, akwai shakka a cikin (sha'anin) Allah, Mai ƙãga halittar sammai da ƙasa Yanã kiran ku dõmin Ya gãfarta muku zunubanku, kuma Ya jinkirtã muku zuwa ga ajali ambatacce?" Suka ce: "Ba ku zama ba fãce mutãne misãlinmu kuma nufinku ku kange mu daga abin da iyãyenmu suka kasance sunã bautãwa sai ku zo mana da dalĩli mabayyani." = --Qur'an 14:10
    Their messengers said to them, "We are only men like you, but Allah confers favor upon whom He wills of His servants. It has never been for us to bring you evidence except by permission of Allah. And upon Allah let the believers rely. <> Manzanninsu suka ce musu, "Bã mu zama ba fãce mutãne misã, linku, kuma amma Allah Yanã yin falala a kan wanda Yake so daga bãyinsa, kuma bã ya kasancẽwa a gare mu, mu zo muku da wani dalĩli fãce da iznin Allah. Kuma ga Allah sai mũminai su dõgara. = --Qur'an 14:11
    And why should we not rely upon Allah while He has guided us to our [good] ways. And we will surely be patient against whatever harm you should cause us. And upon Allah let those who would rely [indeed] rely." <> "Kuma mẽne ne a gare mu, bã zã mu dõgara ga Allah ba, alhãli kuwa haƙĩƙa Yã shiryar da mu ga hanyõyinmu? Kuma lalle ne munã yin haƙuri a kan abin da kuka cũtar da mu, kuma ga Allah sai mãsu dõgaro su dõgara." = --Qur'an 14:12
    And those who disbelieved said to their messengers, "We will surely drive you out of our land, or you must return to our religion." So their Lord inspired to them, "We will surely destroy the wrongdoers. <> Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa Manzanninsu, "Lalle ne munã fitar da ku daga ƙasarmu, kõ kuwa haƙĩƙa, kunã kõmowã acikin addininmu." Sai Ubangijinsu Ya yi wahayi zuwa gare su, "Lalle ne, Munã halakar da azzãlumai." = --Qur'an 14:13
    And We will surely cause you to dwell in the land after them. That is for he who fears My position and fears My threat." <> Kuma haƙĩƙa, Munã zaunar da ku ga ƙasa a bãyansu. Wancan ne abin gargaɗi ga wanda ya ji tsõron matsayiNa, kuma ya ji tsõron ƙyacẽwãTa. = --Qur'an 14:14
    And they requested victory from Allah, and disappointed, [therefore], was every obstinate tyrant. <> Kuma suka yi addu'ar alfãnu. Kuma kõwane kangararre mai tsaurin kai ya tãɓe. = --Qur'an 14:15
    Before him is Hell, and he will be given a drink of purulent water. <> Daga bãyansa akwai Jahannama, kuma anã shãyar da shi daga wani ruwa, surkin jini. = --Qur'an 14:16
    He will gulp it but will hardly [be able to] swallow it. And death will come to him from everywhere, but he is not to die. And before him is a massive punishment. <> Yanã kwankwaɗarsa, kuma bã ya jin sauƙin haɗiyarsa, kuma mutuwa ta jẽ masa daga kõwane wuri kuma bai zama mai mutuwa ba, kuma daga bãyansa akwai azãba mai kauri. = --Qur'an 14:17
    The example of those who disbelieve in their Lord is [that] their deeds are like ashes which the wind blows forcefully on a stormy day; they are unable [to keep] from what they earned a [single] thing. That is what is extreme error. <> Misãlin waɗanda suka kãfirta da Ubangijinsu, ayyukansu sun yi kama da tõka wadda iska ta yi tsananin bugãwa da ita a cikin yini mai gũguwa. Ba su iya amfãni daga abin da suka yi tsirfa a kan kõme. Wancan ita ce ɓata mai nĩsa. = --Qur'an 14:18
    Have you not seen that Allah created the heavens and the earth in truth? If He wills, He can do away with you and produce a new creation. <> Shin, ba ka gani ba cẽwa lalle ne Allah Yã halicci sammai bakwai da ƙasa da mallakarSa. Idan Yã so zai tafiyar da ku, kuma Ya zo da wata halitta sãbuwa. = --Qur'an 14:19
    And that is not difficult for Allah. <> Kuma wancan bai zama mabuwãyi ba ga Allah. = --Qur'an 14:20
    And they will come out [for judgement] before Allah all together, and the weak will say to those who were arrogant, "Indeed, we were your followers, so can you avail us anything against the punishment of Allah?" They will say, "If Allah had guided us, we would have guided you. It is all the same for us whether we show intolerance or are patient: there is for us no place of escape." <> Kuma suka bayyana ga Allah gabã daya, sai mãsu rauni suka ce wa waɗanda suka kangara, "Lalle ne mũ, mun kasance mãsu bi a gare ku, to, shin, kũ mãsu kãrewa ga barinmu ne daga azãbar Allah daga wani abu?" Suka ce: "Dã Allah Ya shiryar da mu, dã mun shiryar da ku, daidai ne a kanmu, mun yi rãki ko mun yi haƙuri ba mu da wata mafaka." = --Qur'an 14:21
    And Satan will say when the matter has been concluded, "Indeed, Allah had promised you the promise of truth. And I promised you, but I betrayed you. But I had no authority over you except that I invited you, and you responded to me. So do not blame me; but blame yourselves. I cannot be called to your aid, nor can you be called to my aid. Indeed, I deny your association of me [with Allah] before. Indeed, for the wrongdoers is a painful punishment." <> Kuma Shaiɗan ya ce a lõkacin da aka ƙãre al'amarin, "Lalle ne Allah Ya yi muku wa'adi, wa'adin gaskiyã, kuma na yi muku wa'adi, sa'an nan na sãɓã muku. Kuma bãbu wani dalĩli a gare ni a kanku fãce na kirã ku, sa'an nan kun karɓã mini. Sabõda haka kada ku zarge ni, kuma ku zargi kanku. Ban zama mai amfaninku ba, kuma ba ku zama mãsu amfãnĩna ba. Lalle na barranta da abin da kuka haɗã ni da shi gabanin wannan (matsayi). Lalle azzãlumai sunã da azãba mai raɗaɗi." = --Qur'an 14:22
    And those who believed and did righteous deeds will be admitted to gardens beneath which rivers flow, abiding eternally therein by permission of their Lord; and their greeting therein will be, "Peace!" <> Kuma aka shigar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, a gidãjen Aljanna, kõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu sunã madawwamã a cikinsu da iznin Ubangijinsu, gaisuwarsu a cikinta "Salãm", (wãtau Aminci). = --Qur'an 14:23
    Have you not considered how Allah presents an example, [making] a good word like a good tree, whose root is firmly fixed and its branches [high] in the sky? <> Shin, ba ka ganĩ ba, yadda Allah Ya buga wani mĩsali, kalma mai kyau kamar itãciya ce mai kyau, asalinta yanã tabbatacce, kuma rẽshenta yanã cikin sama? = --Qur'an 14:24
    It produces its fruit all the time, by permission of its Lord. And Allah presents examples for the people that perhaps they will be reminded. <> Tanã bãyar da abincinta a kõwane lõkaci da iznin Ubangijinta! Kuma Allah Yanã buga misãli ga mutãne, mai yiwuwã ne, sunã tunãwa. = --Qur'an 14:25
    And the example of a bad word is like a bad tree, uprooted from the surface of the earth, not having any stability. <> Kuma misalin kalma mummũnã kamar itãciya mummũnã ce, an tumɓuke ta daga bisa ga ƙasa, bã ta da wata tabbata. = --Qur'an 14:26
    Allah keeps firm those who believe, with the firm word, in worldly life and in the Hereafter. And Allah sends astray the wrongdoers. And Allah does what He wills. <> Allah Yanã tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni da magana tabbatacciya a cikin rãyuwar dũniya, da cikin Lãhira, Kuma Allah Yanã ɓatar da azzãlumai, kuma Allah Yanã aikata abin da Yake so. = --Qur'an 14:27
    Have you not considered those who exchanged the favor of Allah for disbelief and settled their people [in] the home of ruin? <> Shin ba ka lura ba da waɗanda suka musanya ni'imar Allah da kãfirci kuma suka saukar da mutãnensu a gidan halakã? = --Qur'an 14:28
    [It is] Hell, which they will [enter to] burn, and wretched is the settlement. <> Sunã ƙõnuwa a wutar jahannama, kuma tir da matabbatarsu. = --Qur'an 14:29
    And they have attributed to Allah equals to mislead [people] from His way. Say, "Enjoy yourselves, for indeed, your destination is the Fire." <> Kuma suka sanya wa Allah kĩshiyõyi, dõmin ɓatarwa daga hanyarSa, Ka ce: "Ku ji dãɗi, sa'an nan, lalle ne, makõmarku Wutar ce." = --Qur'an 14:30
    [O Muhammad], tell My servants who have believed to establish prayer and spend from what We have provided them, secretly and publicly, before a Day comes in which there will be no exchange, nor any friendships. <> Ka ce wa bãyĩNa waɗanda suka yi ĩmãni su tsayar da salla kuma su ciyar daga abin da Muka azurtã su, a asirce da bayyane, daga gabãnin wani wuni ya zo, bãbu ciniki a ciki, kuma bãbu abõtaka. = --Qur'an 14:31
    It is Allah who created the heavens and the earth and sent down rain from the sky and produced thereby some fruits as provision for you and subjected for you the ships to sail through the sea by His command and subjected for you the rivers. <> Allah ne wanda Ya halicci sammai da ƙasa kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya fitar game da shi, daga 'ya'yan itãce arziki dõminku kuma Ya hõrẽ jirgin ruwa dõmin ya yi gudu a cikin tẽku da umurninSa, kuma Ya hõrẽ muku kõguna. = --Qur'an 14:32
    And He subjected for you the sun and the moon, continuous [in orbit], and subjected for you the night and the day. <> Kuma Ya hõrẽ muku rãnã da watã sunã madawwama biyu, kuma Ya hõrẽ muku dare da wuni. = --Qur'an 14:33
    And He gave you from all you asked of Him. And if you should count the favor of Allah, you could not enumerate them. Indeed, mankind is [generally] most unjust and ungrateful. <> Kuma Ya bã ku dukkan abin da kuka rõƙe Shi kuma idan kun ƙidaya, ni'imar Allah bã zã ku lissafe ta ba. Lalle ne mutum, haƙĩƙa, mai yawan zãlunci ne, mai yawan kãfirci. = --Qur'an 14:34
    And [mention, O Muhammad], when Abraham said, "My Lord, make this city [Makkah] secure and keep me and my sons away from worshipping idols. <> Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Yã Ubangijina! Ka sanyã wannan gari amintacce kuma Ka nĩsanta ni, nĩ da ɗiyãna daga bauta wa gumãka. = --Qur'an 14:35
    My Lord, indeed they have led astray many among the people. So whoever follows me - then he is of me; and whoever disobeys me - indeed, You are [yet] Forgiving and Merciful. <> "Yã Ubangijina! Lalle ne sũ, sun ɓatar da mãsu yawa daga mutãne sa'an nan wanda ya bĩ ni, to, lalle shi, yanã daga gare ni, kuma wanda ya sãɓa mini, to, lalle ne Kai Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 14:36
    Our Lord, I have settled some of my descendants in an uncultivated valley near Your sacred House, our Lord, that they may establish prayer. So make hearts among the people incline toward them and provide for them from the fruits that they might be grateful. <> "Yã Ubangijinmu! Lalle ne ni, na zaunar da zuriyata ga rãfi wanda ba ma'abũcin shũka ba, a wurin ¦ãkinka mai alfarma. Yã Ubangijinmu! Dõmin su tsayar da salla. Sai Ka sanya zukãta daga mutãne sunã gaggãwar bẽgenzuwa gare su, kuma ka azurtã su daga 'ya'yan itãce, mai yiwuwã ne sunã gõdẽwã." = --Qur'an 14:37
    Our Lord, indeed You know what we conceal and what we declare, and nothing is hidden from Allah on the earth or in the heaven. <> "Yã Ubangijinmu! Lalle ne Kai Kanã sanin abin da muke ɓõyẽwa, da abin da muke bayyanãwa. Kuma bãbu abin da yake ɓõyẽwa ga A1lah, daga wani abu a cikin ƙasa, kuma bãbu a cikin sama." = --Qur'an 14:38
    Praise to Allah, who has granted to me in old age Ishmael and Isaac. Indeed, my Lord is the Hearer of supplication. <> "Gõdiyã ta tabbata ga Allah wanda Yake Ya bã ni inã a cikin tsufa Ismã'ila da Is'hãƙa. Lalle ne Ubangijina, haƙĩƙa, Mai jin addu'a ne." = --Qur'an 14:39
    My Lord, make me an establisher of prayer, and [many] from my descendants. Our Lord, and accept my supplication. <> "Yã Ubangijina! Ka sanyã ni mai tsayar da salla. Kuma daga zũriyyata. Yã Ubangijinmu! Kuma Ka karɓi addu'ata." = --Qur'an 14:40
    Our Lord, forgive me and my parents and the believers the Day the account is established." <> "Yã Ubangijinmu! Ka yi gãfara gare ni, kuma ga mahaifãna, kuma da mũminai, a rãnar da hisãbi yake tsayãwa." = --Qur'an 14:41
    And never think that Allah is unaware of what the wrongdoers do. He only delays them for a Day when eyes will stare [in horror]. <> "Kuma kada ka yi zaton Allah Mai shagalã ne daga abin da azzalumai suke aikatãwã. Abin sani kawai, Yanã jinkirta musu ne zuwa ga wani wuni, wanda idãnuwa suke fita turu- turu a cikinsa." = --Qur'an 14:42
    Racing ahead, their heads raised up, their glance does not come back to them, and their hearts are void. <> "Sunã mãsu gaggãwa, mãsu ɗaukaka kãwunansu zuwa sama ƙiftawar ganinsu ba ta kõmãwa gare su. Kuma zukãtansu wõfintattu." = --Qur'an 14:43
    And, [O Muhammad], warn the people of a Day when the punishment will come to them and those who did wrong will say, "Our Lord, delay us for a short term; we will answer Your call and follow the messengers." [But it will be said], "Had you not sworn, before, that for you there would be no cessation? <> Kuma ka yi gargaɗi ga mutãne ga rãnar da azãba take jẽ musu, sai waɗanda suka yi zãlunci su ce: "Yã Ubangijinmu! Ka yi mana jinkiri zuwa ga wani ajali makusanci, mu karɓa wa kiranKa, kuma mu bi Manzanni."(Allah Ya ce musu) "Ashe, ba ku kasance kun yi rantsuwã ba daga gabãni, cẽwa bã ku da wata gushẽwa? = --Qur'an 14:44
    And you lived among the dwellings of those who wronged themselves, and it had become clear to you how We dealt with them. And We presented for you [many] examples." <> "Kuma kuka zaunã a cikin gidãjen waɗanda suka zãlunci kansu, kuma ya bayyana a gare ku yadda Muka aikatã game da su, kuma Muka buga muku misãlai." = --Qur'an 14:45
    And they had planned their plan, but with Allah is [recorded] their plan, even if their plan had been [sufficient] to do away with the mountains. <> Kuma lalle sun yi mãkirci irin makircinSu kuma a wurin Allah makircinsu, yake, kuma lalle ne makircinsu yã kasance, haƙĩƙa, duwãtsu sunã gushẽwã sabõda shi. = --Qur'an 14:46
    So never think that Allah will fail in His promise to His messengers. Indeed, Allah is Exalted in Might and Owner of Retribution. <> Sabõda haka, kada ka ƙarfafa zaton Allah Mai sãɓa wa'adinSa ne ga ManzanninSa. Lalle ne Allah ne Mabuwãyi, Ma'abũcin azãbar rãmuwa. = --Qur'an 14:47
    [It will be] on the Day the earth will be replaced by another earth, and the heavens [as well], and all creatures will come out before Allah, the One, the Prevailing. <> A rãnar da ake musanya ƙasa bã ƙasar nan ba, da sammai kuma su bayyana ga Allah Makaɗaici, Mai tanƙwasãwa. = --Qur'an 14:48
    And you will see the criminals that Day bound together in shackles, <> Kuma kana ganin mãsu laifi, a rãnar nan, sunã waɗanda aka yi wa ciri daidai a cikin marũruwa. = --Qur'an 14:49
    Their garments of liquid pitch and their faces covered by the Fire. <> Rigunansu daga farar wutã ne, kuma wuta ta rufe fuskõkinsu. = --Qur'an 14:50
    So that Allah will recompense every soul for what it earned. Indeed, Allah is swift in account. <> Dõmin Allah Ya sãkã wa kõwane rai da abin da ya tsuwurwurta. Lalle ne, Allah Mai gaggãwar hisãbi ne. = --Qur'an 14:51
    This [Qur'an] is notification for the people that they may be warned thereby and that they may know that He is but one God and that those of understanding will be reminded. <> Wannan iyarwa ce ga mutãne, kuma dõmin a yi musu gargaɗi da shi, kuma dõmin su sani cẽwa, abin sani kawai, shĩ ne abin bautawa guda. Kuma dõmin masu hankali su riƙa tunãwa. = --Qur'an 14:52
    Alif, Lam, Ra. These are the verses of the Book and a clear Qur'an. <> A. L̃.R. Waɗancan ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa. = --Qur'an 15:1
    Perhaps those who disbelieve will wish that they had been Muslims. <> Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi. = --Qur'an 15:2
    Let them eat and enjoy themselves and be diverted by [false] hope, for they are going to know. <> Ka bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa'an nan da sannu zã su sani. = --Qur'an 15:3
    And We did not destroy any city but that for it was a known decree. <> Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne. = --Qur'an 15:4
    No nation will precede its term, nor will they remain thereafter. <> Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba. = --Qur'an 15:5
    And they say, "O you upon whom the message has been sent down, indeed you are mad. <> Suka ce: "Yã kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur'ãni) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne." = --Qur'an 15:6
    Why do you not bring us the angels, if you should be among the truthful?" <> "Dõmin me bã zã ka zo mana da malã'ĩku ba idan ka kasance daga mãsu gaskiya?" = --Qur'an 15:7
    We do not send down the angels except with truth; and the disbelievers would not then be reprieved. <> Bã Mu sassaukar da malã'iku fãce da gaskiya, bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba. = --Qur'an 15:8
    Indeed, it is We who sent down the Qur'an and indeed, We will be its guardian. <> Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lal1e Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi. = --Qur'an 15:9
    And We had certainly sent [messengers] before you, [O Muhammad], among the sects of the former peoples. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyõyin farko, gabãninka. = --Qur'an 15:10
    And no messenger would come to them except that they ridiculed him. <> Kuma wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu, izgili a gare shi. = --Qur'an 15:11
    Thus do We insert denial into the hearts of the criminals. <> Kamar wancan ne Muke shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi. = --Qur'an 15:12
    They will not believe in it, while there has already occurred the precedent of the former peoples. <> Bã su yin ĩmãni da shi, kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige. = --Qur'an 15:13
    And [even] if We opened to them a gate from the heaven and they continued therein to ascend, <> Kuma dã Mun bũɗe wata ƙõfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sunã tãkãwa. = --Qur'an 15:14
    They would say, "Our eyes have only been dazzled. Rather, we are a people affected by magic." <> Lalle ne dã sun ce: "Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. Ã'a, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce." = --Qur'an 15:15
    And We have placed within the heaven great stars and have beautified it for the observers. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun sanya waɗansu masaukai a, cikin sama, kuma Muka ƙawãta ta ga masu kallo. = --Qur'an 15:16
    And We have protected it from every devil expelled [from the mercy of Allah] <> Kuma Muka kiyãye ta daga dukan Shaiɗani wanda ake jĩfa. = --Qur'an 15:17
    Except one who steals a hearing and is pursued by a clear burning flame. <> Fãce wanda ya sãci saurãre sai wutar yũlã bayyananniya ta bĩ shi. = --Qur'an 15:18
    And the earth - We have spread it and cast therein firmly set mountains and caused to grow therein [something] of every well-balanced thing. <> Kuma ƙasa Mun mĩkẽ ta kuma Mun jẽfa duwãtsu tabbatattu a cikinta kuma Mun tsirar a cikinta, daga dukan abu wanda ake aunãwa da sikẽli. = --Qur'an 15:19
    And We have made for you therein means of living and [for] those for whom you are not providers. <> Kuma Muka sanyã muku, a cikinta, abũbuwan rãyuwã da wanda ba ku zamã mãsu ciyarwa gare shi ba. = --Qur'an 15:20
    And there is not a thing but that with Us are its depositories, and We do not send it down except according to a known measure. <> Kuma bãbu wani abu fãce a wurinMu, akwai taskõkĩnsa kuma ba Mu saukar da shi ba fãce kan gwargwado sananne. = --Qur'an 15:21
    And We have sent the fertilizing winds and sent down water from the sky and given you drink from it. And you are not its retainers. <> Kuma Muka aika iskõki mãsu barbarar jũna sa'an nan Muka saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka shãyar da ku shi, kuma ba ku zama mãsu taskacẽwa a gare shi ba. = --Qur'an 15:22
    And indeed, it is We who give life and cause death, and We are the Inheritor. <> Kuma lalle ne Mu Muke rãyarwa, kuma Muke kashẽwa kuma Mũ ne magada. = --Qur'an 15:23
    And We have already known the preceding [generations] among you, and We have already known the later [ones to come]. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun san mãsu gabãta daga cikinku, kuma Mun san mãsu jinkiri. = --Qur'an 15:24
    And indeed, your Lord will gather them; indeed, He is Wise and Knowing. <> Kuma lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Yake tãra su, lalle Shĩ ne Mai hikima, Masani. = --Qur'an 15:25
    And We did certainly create man out of clay from an altered black mud. <> Kuma lalle ne Mun halicci mutum daga ƙeƙasasshiyar lãka, daga baƙin yumɓu wanda ya canja. = --Qur'an 15:26
    And the jinn We created before from scorching fire. <> Kuma Aljani Mun haliccẽ shi daga gabãni, daga wutar iskar zafi. = --Qur'an 15:27
    And [mention, O Muhammad], when your Lord said to the angels, "I will create a human being out of clay from an altered black mud. <> Kuma a lõkacin da Ubangijinka ya ce wa malã'iku: "Lalle Nĩ mai halittar wani jiki ne daga ƙẽƙasasshen yumɓu wanda ya canja." = --Qur'an 15:28
    And when I have proportioned him and breathed into him of My [created] soul, then fall down to him in prostration." <> "To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada." = --Qur'an 15:29
    So the angels prostrated - all of them entirely, <> Sai malã'iku suka yi sujada dukkansu gaba ɗaya. = --Qur'an 15:30
    Except Iblees, he refused to be with those who prostrated. <> Fãce Iblĩs, ya ƙi kasancẽwa daga mãsu yin sujadar. = --Qur'an 15:31
    [Allah] said, O Iblees, what is [the matter] with you that you are not with those who prostrate?" <> Ya ce: "Yã Iblĩs mẽne ne a gare ka, ba ka kasance tãre da mãsu yin sujuda ba?" = --Qur'an 15:32
    He said, "Never would I prostrate to a human whom You created out of clay from an altered black mud." <> Ya ce: "Ban kasance inã yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga bũsasshen yumɓun lãka wadda ta canja." = --Qur'an 15:33
    [Allah] said, "Then get out of it, for indeed, you are expelled. <> Ya ce: "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai abin jĩfa ne." = --Qur'an 15:34
    And indeed, upon you is the curse until the Day of Recompense." <> "Kuma lalle ne akwai la'ana a kanka har ya zuwa rãnar sakamako." = --Qur'an 15:35
    He said, "My Lord, then reprieve me until the Day they are resurrected." <> Ya ce: "Yã Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rãnar da ake tãshin su." = --Qur'an 15:36
    [Allah] said, "So indeed, you are of those reprieved <> Ya ce: "To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri." = --Qur'an 15:37
    Until the Day of the time well-known." <> "Zuwa ga Yinin Lõkacin nan sananne." = --Qur'an 15:38
    [Iblees] said, "My Lord, because You have put me in error, I will surely make [disobedience] attractive to them on earth, and I will mislead them all <> Ya ce: "Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya." = --Qur'an 15:39
    Except, among them, Your chosen servants." <> "Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake." = --Qur'an 15:40
    [Allah] said, "This is a path [of return] to Me [that is] straight. <> Ya ce: "Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici." = --Qur'an 15:41
    Indeed, My servants - no authority will you have over them, except those who follow you of the deviators. <> "Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu." = --Qur'an 15:42
    And indeed, Hell is the promised place for them all. <> Kuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma'a1kawartarsu gabã ɗaya. = --Qur'an 15:43
    It has seven gates; for every gate is of them a portion designated." <> Tanã da ƙõfõfi bakwai, ga kõwace ƙõfa akwai wani juz'i daga gare su rababbe. = --Qur'an 15:44
    Indeed, the righteous will be within gardens and springs. <> Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna mai idandunan ruwa. = --Qur'an 15:45
    [Having been told], "Enter it in peace, safe [and secure]." <> "Ku shigẽ ta da aminci, kunã amintattu." = --Qur'an 15:46
    And We will remove whatever is in their breasts of resentment, [so they will be] brothers, on thrones facing each other. <> Kuma Muka ɗẽbe abinda ke a cikin zukãtansu na daga ƙullin zũci, suka zama 'yan'uwa a kan gadãje, sunã mãsu fuskantar junã. = --Qur'an 15:47
    No fatigue will touch them therein, nor from it will they [ever] be removed. <> Wata wahala bã zã ta shãfe su bã a cikinta kuma ba su zama mãsu fita daga, cikinta ba. = --Qur'an 15:48
    [O Muhammad], inform My servants that it is I who am the Forgiving, the Merciful. <> Ka bai wa bãyiNa lãbari cẽwa lalle ne Ni, Mai gãfarane, Mai jin ƙai. = --Qur'an 15:49
    And that it is My punishment which is the painful punishment. <> Kuma azãbãTa ita ce azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 15:50
    And inform them about the guests of Abraham, <> Kuma ka bã su lãbãrin bãƙin Ibrãhĩm. = --Qur'an 15:51
    When they entered upon him and said, "Peace." [Abraham] said, "Indeed, we are fearful of you." <> A lõkacin da suka shiga gunsa, sai suka ce: "Sallama." Ya ce: "Lalle mũ, daga gare ku, mãsu firgita ne." = --Qur'an 15:52
    [The angels] said, "Fear not. Indeed, we give you good tidings of a learned boy." <> Suka ce: "Kada ka firgita. Lalle ne mũ, munã yi makabushãra game da wani yãro masani." = --Qur'an 15:53
    He said, "Have you given me good tidings although old age has come upon me? Then of what [wonder] do you inform?" <> Ya ce: "Shin kun bã ni bushãra ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara?" = --Qur'an 15:54
    They said, "We have given you good tidings in truth, so do not be of the despairing." <> Suka ce: "Munã yi maka bushãra da gaskiya ne, sabõda haka, kada da kasance daga mãsu yanke tsammãni." = --Qur'an 15:55
    He said, "And who despairs of the mercy of his Lord except for those astray?" <> Ya ce: "Kuma wãne ne yake yanke tsammãni daga rahamar Ubangijinsa, fãce ɓatattu?" = --Qur'an 15:56
    [Abraham] said, "Then what is your business [here], O messengers?" <> Ya ce: "To, mẽne ne babban al'amarinku? Yã kũ manzanni!" = --Qur'an 15:57
    They said, "Indeed, we have been sent to a people of criminals, <> Suka ce: "Lalle ne mũ, an aika mu zuwa ga wasu mutãne mãsu laifi." = --Qur'an 15:58
    Except the family of Lot; indeed, we will save them all <> "Fãce mutãnen Lũɗu, lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu tsĩrar dasu ne gabã ɗaya." = --Qur'an 15:59
    Except his wife." Allah decreed that she is of those who remain behind. <> "Fãce mãtarsa mun ƙaddara cẽwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka." = --Qur'an 15:60
    And when the messengers came to the family of Lot, <> To, a lõkacin da mazannin suka jẽ wa mutãnen Lũɗu, = --Qur'an 15:61
    He said, "Indeed, you are people unknown." <> Ya ce: "Lalle ne ku mutãne ne waɗanda ba a sani ba." = --Qur'an 15:62
    They said, "But we have come to you with that about which they were disputing, <> Suka ce: "Ã'a, mun zo maka sabõda abin da suka kasance sunã shakka a cikinsa." = --Qur'an 15:63
    And we have come to you with truth, and indeed, we are truthful. <> "Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne." = --Qur'an 15:64
    So set out with your family during a portion of the night and follow behind them and let not anyone among you look back and continue on to where you are commanded." <> "Sai ka yi tafiya da iyãlinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bãyansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka aumurce ku." = --Qur'an 15:65
    And We conveyed to him [the decree] of that matter: that those [sinners] would be eliminated by early morning. <> Kuma Muka hukunta wancan al'amarin zuwa gare shi cẽwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankẽwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga asuba. = --Qur'an 15:66
    And the people of the city came rejoicing. <> Kuma mutãnen alƙaryar suka je sunã mãsu bushãra. = --Qur'an 15:67
    [Lot] said, "Indeed, these are my guests, so do not shame me. <> Ya ce: "Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni." = --Qur'an 15:68
    And fear Allah and do not disgrace me." <> "Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki." = --Qur'an 15:69
    They said, "Have we not forbidden you from [protecting] people?" <> Suka ce: "Ashe ba mu hana ka daga tãlikai ba?" = --Qur'an 15:70
    [Lot] said, "These are my daughters - if you would be doers [of lawful marriage]." <> Ya ce: "Ga waɗannan, 'ya'yãna idan kun kasance mãsu aikatãwa ne." = --Qur'an 15:71
    By your life, [O Muhammad], indeed they were, in their intoxication, wandering blindly. <> Rantsuwa da rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa. = --Qur'an 15:72
    So the shriek seized them at sunrise. <> Sa'an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã. = --Qur'an 15:73
    And We made the highest part [of the city] its lowest and rained upon them stones of hard clay. <> Sa'an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu. = --Qur'an 15:74
    Indeed in that are signs for those who discern. <> Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali. = --Qur'an 15:75
    And indeed, those cities are [situated] on an established road. <> Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a gẽfen wata hanyã tabbatacciya. = --Qur'an 15:76
    Indeed in that is a sign for the believers. <> Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni. = --Qur'an 15:77
    And the companions of the thicket were [also] wrongdoers. <> Kuma lalle ne ma'abũta Al'aika sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci! = --Qur'an 15:78
    So We took retribution from them, and indeed, both [cities] are on a clear highway. <> Sai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a gẽfen wani tafarki mabayyani. = --Qur'an 15:79
    And certainly did the companions of Thamud deny the messengers. <> Kuma lalle ne haƙĩƙa ma'abũta Hijiri sun ƙaryata Manzanni. = --Qur'an 15:80
    And We gave them Our signs, but from them they were turning away. <> Kuma Kuka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirẽwa daga gare su. = --Qur'an 15:81
    And they used to carve from the mountains, houses, feeling secure. <> Kuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu. = --Qur'an 15:82
    But the shriek seized them at early morning. <> Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga asuba. = --Qur'an 15:83
    So nothing availed them [from] what they used to earn. <> Sa'an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba. = --Qur'an 15:84
    And We have not created the heavens and earth and that between them except in truth. And indeed, the Hour is coming; so forgive with gracious forgiveness. <> Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã'a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau. = --Qur'an 15:85
    Indeed, your Lord - He is the Knowing Creator. <> Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani. = --Qur'an 15:86
    And We have certainly given you, [O Muhammad], seven of the often repeated [verses] and the great Qur'an. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗanda ake maimaita karatunsu da Alƙur'ãni mai girma. = --Qur'an 15:87
    Do not extend your eyes toward that by which We have given enjoyment to [certain] categories of the disbelievers, and do not grieve over them. And lower your wing to the believers <> Kada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau'i-nau'i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni. = --Qur'an 15:88
    And say, "Indeed, I am the clear warner" - <> Kuma ka ce: "Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyananne." = --Qur'an 15:89
    Just as We had revealed [scriptures] to the separators <> Kamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa, = --Qur'an 15:90
    Who have made the Qur'an into portions. <> Waɗanda suka sanya Alƙur'ãni tãtsuniyõyi. = --Qur'an 15:91
    So by your Lord, We will surely question them all <> To, rantsuwa da Ubangijinka! Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya. = --Qur'an 15:92
    About what they used to do. <> Daga abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 15:93
    Then declare what you are commanded and turn away from the polytheists. <> Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki. = --Qur'an 15:94
    Indeed, We are sufficient for you against the mockers <> Lalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu izgili. = --Qur'an 15:95
    Who make [equal] with Allah another deity. But they are going to know. <> Waɗanda suke sanyãwar wani abin bautãwa na dabam tare da Allah, sa'an nan da sannu zã su sani. = --Qur'an 15:96
    And We already know that your breast is constrained by what they say. <> Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cẽwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã (na izgili). = --Qur'an 15:97
    So exalt [Allah] with praise of your Lord and be of those who prostrate [to Him]. <> Sabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada. = --Qur'an 15:98
    And worship your Lord until there comes to you the certainty (death). <> Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka. = --Qur'an 15:99
    The command of Allah is coming, so be not impatient for it. Exalted is He and high above what they associate with Him. <> Al'amarin Allah yã zo, sabõda haka kada ku nẽmi hanzartãwarsa. Tsarkin Allah ya tabbata, kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka. = --Qur'an 16:1
    He sends down the angels, with the inspiration of His command, upon whom He wills of His servants, [telling them], "Warn that there is no deity except Me; so fear Me." <> Yanã sassaukar da malã'iku da Rũhi daga umurninSaa kan wanda Yake so daga bãyinSa, cẽwa ku yi gargaɗi cẽwa: Lalle ne shĩ, bãbu abin bautãwa fãce Ni, sabõda haka ku bĩ Ni da taƙawa. = --Qur'an 16:2
    He created the heavens and earth in truth. High is He above what they associate with Him. <> Ya halicci sammai da ƙasa da gaskiya. Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka. = --Qur'an 16:3
    He created man from a sperm-drop; then at once, he is a clear adversary. <> Ya halicci mutum daga maniyyi, sai gã shi yanã mai husũma bayyananniya. = --Qur'an 16:4
    And the grazing livestock He has created for you; in them is warmth and [numerous] benefits, and from them you eat. <> Da dabbõbin ni'ima, Ya halicce su dõminku. A cikinsu akwai abin yin ɗumi da waɗansu amfãnõni, kuma daga gare su kuke ci. = --Qur'an 16:5
    And for you in them is [the enjoyment of] beauty when you bring them in [for the evening] and when you send them out [to pasture]. <> Kuma kunã da kyau a cikinsu a lõkacin da suke kõmõwa daga kĩwo da maraice da lõkacin da suke sakuwã. = --Qur'an 16:6
    And they carry your loads to a land you could not have reached except with difficulty to yourselves. Indeed, your Lord is Kind and Merciful. <> Kuma sunã ɗaukar kãyanku mãsu nauyi zuwa ga wani gari, ba ku kasance mãsu isa gare shi ba, fãce da tsananin wahalar rãyuka, Lalle ne Ubangijinka ne, haƙĩƙa, Mai tausayi, Maijin ƙai. = --Qur'an 16:7
    And [He created] the horses, mules and donkeys for you to ride and [as] adornment. And He creates that which you do not know. <> Kuma da dawãki da alfadarai da jãkuna, dõmin ku hau su, kuma da ƙawa. Kuma Yana halitta abin da ba ku sani ba. = --Qur'an 16:8
    And upon Allah is the direction of the [right] way, and among the various paths are those deviating. And if He willed, He could have guided you all. <> Kuma ga Allah madaidaiciyar hanya take kuma daga gare ta akwai mai karkacẽwa. Kuma da Yã so, dã Ya shiryar da ku gabã ɗaya. = --Qur'an 16:9
    It is He who sends down rain from the sky; from it is drink and from it is foliage in which you pasture [animals]. <> Shĩ ne Wanda Ya saukar da ruwa daga sama dõminku, daga gare shi akwai abin sha, kuma daga gare shi itãce yake, a cikinsa kuke yin kĩwo. = --Qur'an 16:10
    He causes to grow for you thereby the crops, olives, palm trees, grapevines, and from all the fruits. Indeed in that is a sign for a people who give thought. <> Yanã tsirar da shũka game da shi, dõminku zaitũni da dabĩnai da inabai, kuma daga dukan 'yã'yan itãce. Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke yin tunãni. = --Qur'an 16:11
    And He has subjected for you the night and day and the sun and moon, and the stars are subjected by His command. Indeed in that are signs for a people who reason. <> Kuma Ya hõrẽ muku dare da wuni da rãnã da watã kuma taurãri hõrarru ne da umurninSa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke hankalta. = --Qur'an 16:12
    And [He has subjected] whatever He multiplied for you on the earth of varying colors. Indeed in that is a sign for a people who remember. <> Kuma abin da Ya halitta muku a cikin ƙasa, yana mai sãɓãnin launukansa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke tunãwa. = --Qur'an 16:13
    And it is He who subjected the sea for you to eat from it tender meat and to extract from it ornaments which you wear. And you see the ships plowing through it, and [He subjected it] that you may seek of His bounty; and perhaps you will be grateful. <> Kuma Shĩ ne Ya hõrẽ tẽku dõmin ku ci wani nama sãbõ daga gare shi, kuma kunã fitarwa, daga gare shi, ƙawã wadda kuke yin ado da ita. Kuma kuna ganin jirãge sunã yankan ruwa a cikinsa kuma dõmin ku yi nẽman (fatauci) daga falalarSa. Kuma mai yiwuwa ne kuna gõdẽwa. = --Qur'an 16:14
    And He has cast into the earth firmly set mountains, lest it shift with you, and [made] rivers and roads, that you may be guided, <> Kuma Ya jẽfa, a cikin ƙasa, tabbatattun duwatsu dõmin kada ta karkata da ku, da kõguna da hanyõyi, ɗammãninku kunã shiryuwa. = --Qur'an 16:15
    And landmarks. And by the stars they are [also] guided. <> Kuma da waɗansu alãmõmi, kuma da taurãri sunã mãsu nẽman shiryuwa (ga tafiyarsu ta fatauci). = --Qur'an 16:16
    Then is He who creates like one who does not create? So will you not be reminded? <> Shin, wanda Yake yin halitta yanã yin kama da wanda ba ya yin halitta? Shin fa, bã ku tunãwa? = --Qur'an 16:17
    And if you should count the favors of Allah, you could not enumerate them. Indeed, Allah is Forgiving and Merciful. <> Kuma idan kun ƙidãya ni'imar Allah, bã ku iya lissafa ta. Lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 16:18
    And Allah knows what you conceal and what you declare. <> Kuma Allah Yanã sanin abin da kuke asirtãwa da abin da kuke bayyanãwa. = --Qur'an 16:19
    And those they invoke other than Allah create nothing, and they [themselves] are created. <> Kuma waɗanda suke kira, baicin Allah, ba su halicci kõme ba, kuma sũ ne ake halittawa. = --Qur'an 16:20
    They are, [in fact], dead, not alive, and they do not perceive when they will be resurrected. <> Matattũ ne, bã su da rai, kuma ba su san a wane lõkaci ake tãyar da su ba. = --Qur'an 16:21
    Your god is one God. But those who do not believe in the Hereafter - their hearts are disapproving, and they are arrogant. <> Abin bautawarku, abin bautãwa ne guda, to, waɗanda ba su yin ĩmãni da Lãhira, zukãtansu mãsu musu ne, kuma su makangara ne. = --Qur'an 16:22
    Assuredly, Allah knows what they conceal and what they declare. Indeed, He does not like the arrogant. <> Haƙĩƙa, lalle ne, Allah Yanã sanin abin da suke asirtãwa da abin da suke bayyanãwa. Lalle ne Shi, bã Ya Son mãsu girman kai. = --Qur'an 16:23
    And when it is said to them, "What has your Lord sent down?" They say, "Legends of the former peoples," <> Idan aka ce musu: "Mẽne ne Ubangijinku Ya saukar?" Sai su ce: "Tãtsũniyõyin mutãnen farko." = --Qur'an 16:24
    That they may bear their own burdens in full on the Day of Resurrection and some of the burdens of those whom they misguide without knowledge. Unquestionably, evil is that which they bear. <> Dõmin su ɗauki zunubansu cikakku a Rãnar ¡iyãma, kuma daga zunuban waɗanda suke ɓatarwa bã da wani ilmi ba. To, abin da suke ɗauka na zunubi ya mũnana. = --Qur'an 16:25
    Those before them had already plotted, but Allah came at their building from the foundations, so the roof fell upon them from above them, and the punishment came to them from where they did not perceive. <> Lalle ne waɗanda suke a gabãninsu sun yi mãkirci, sai Allah Ya je wa gininsu daga harsãshensa, sai rufi ya fãɗa a kansu daga bisansu, kuma azãba ta jẽ musu daga inda ba su sani ba. = --Qur'an 16:26
    Then on the Day of Resurrection He will disgrace them and say, "Where are My 'partners' for whom you used to oppose [the believers]?" Those who were given knowledge will say, "Indeed disgrace, this Day, and evil are upon the disbelievers" - <> Sa'an nan a Rãnar ¡iyãma (Allah) Yanã kunyatã su, kuma Yanã cẽwa: "Inã abõkan tãrayyaTa, waɗanda kuka kasance kunã gãbã a cikin ɗaukaka sha'aninsu?" Waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: "Lalle ne wulãkanci a yau da cũta sun tabbata a kan kãfirai." = --Qur'an 16:27
    The ones whom the angels take in death [while] wronging themselves, and [who] then offer submission, [saying], "We were not doing any evil." But, yes! Indeed, Allah is Knowing of what you used to do. <> Waɗanda malãiku suke karɓar rãyukansu sunã mãsu zãluntar kansu. Sai suka jẽfa nẽman sulhu (suka ce) "Ba mu kasance muna aikata wani mummũnan aiki ba." Kayya! Lalle Allah ne Masani ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa. = --Qur'an 16:28
    So enter the gates of Hell to abide eternally therein, and how wretched is the residence of the arrogant. <> Sai ku shiga ƙõfõfin Jahannama, kunã madawwama a cikinta. Sa'an nan tir da mazaunin mãsu girman kai. = --Qur'an 16:29
    And it will be said to those who feared Allah, "What did your Lord send down?" They will say, "[That which is] good." For those who do good in this world is good; and the home of the Hereafter is better. And how excellent is the home of the righteous - <> Kuma aka ce wa waɗanda suka yi taƙawa, "Mẽne ne Ubangijinku Ya saukar?" Suka ce, "Alhẽri Ya saukar, ga waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya akwai wani abu mai kyau, kuma haƙĩƙa, Lãhira ce mafi alhẽri." Kuma haƙĩƙa, mãdalla da gidan mãsu taƙawa. = --Qur'an 16:30
    Gardens of perpetual residence, which they will enter, beneath which rivers flow. They will have therein whatever they wish. Thus does Allah reward the righteous - <> Gidãjen Aljannar zama sunã shigarsu, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã da abin da suke so a cikinsu. Kamar haka Allah ke sãkã wa mãsu taƙawa. = --Qur'an 16:31
    The ones whom the angels take in death, [being] good and pure; [the angels] will say, "Peace be upon you. Enter Paradise for what you used to do." <> Waɗanda malã'iku suke karɓar rãyukansu sunã mãsu jin dãɗin rai, malã'ikun sunã cẽwa. "Aminci ya tabbata a kanku. Ku shiga Aljanna sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa." = --Qur'an 16:32
    Do the disbelievers await [anything] except that the angels should come to them or there comes the command of your Lord? Thus did those do before them. And Allah wronged them not, but they had been wronging themselves. <> Shin sunã jiran wani abu? Fãce malã'iku su jẽ musu kõ kuwa umurnin Ubangijinka. Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu, suka aikata. Kuma Allah bai zãlunce su ba, kuma amma kansu suka kasance sunã zãlunta. = --Qur'an 16:33
    So they were struck by the evil consequences of what they did and were enveloped by what they used to ridicule. <> Sai mũnãnan abũbuwan da suka aikata ya sãme su, kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili ya wajaba a kansu. = --Qur'an 16:34
    And those who associate others with Allah say, "If Allah had willed, we would not have worshipped anything other than Him, neither we nor our fathers, nor would we have forbidden anything through other than Him." Thus did those do before them. So is there upon the messengers except [the duty of] clear notification? <> Kuma waɗanda suka yi shirki suka ce: "Dã Allah Yã so, dã bamu bautã wa kõme ba, baicinSa, mũ ko ubannimmu kuma dã ba mu haramta kõme ba, baicin abin da Ya haramta." Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu suka aikata. To, shin, akwai wani abu a kan Manzanni, fãce iyarwa bayyananniyã? = --Qur'an 16:35
    And We certainly sent into every nation a messenger, [saying], "Worship Allah and avoid Taghut." And among them were those whom Allah guided, and among them were those upon whom error was [deservedly] decreed. So proceed through the earth and observe how was the end of the deniers. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kõwace al'umma da wani Manzo (ya ce): "Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci ¦ãgũtu." To, daga gare su akwai wanda Allah Ya shiryar, kuma daga cikinsu akwai wanda ɓata ta wajaba a kansa. Sai ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance. = --Qur'an 16:36
    [Even] if you should strive for their guidance, [O Muhammad], indeed, Allah does not guide those He sends astray, and they will have no helpers. <> Idan ka yi kwaɗayi a kan shiryuwarsu, to, lalle ne, Allah bã Ya shiryar da wanda yake ɓatarwa, kuma bã su da waɗansu mataimaka. = --Qur'an 16:37
    And they swear by Allah their strongest oaths [that] Allah will not resurrect one who dies. But yes - [it is] a true promise [binding] upon Him, but most of the people do not know. <> Kuma suka rantse da Allah iyãkar rantsuwarsu (cẽwa) Allah bã ya tãyar da wanda yake mutuwa! Na'am, Yanã tãyarwa. Wa'adi ne (Allah) Ya yi a kanSa tabbatacce, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba. = --Qur'an 16:38
    [It is] so He will make clear to them [the truth of] that wherein they differ and so those who have disbelieved may know that they were liars. <> Dõmin Ya bayyana musu abin da suke sãɓã wa jũna a cikinsa, kuma dõmin waɗanda suka kãfirta su sani cẽwa lalle sũ ne suka kasance maƙaryatã. = --Qur'an 16:39
    Indeed, Our word to a thing when We intend it is but that We say to it, "Be," and it is. <> Abin sani kawai, MaganarMu ga wani abu idan Mun nufe shi, Mu ce masa, "Ka kasance; sai yanã kasancẽwa. = --Qur'an 16:40
    And those who emigrated for [the cause of] Allah after they had been wronged - We will surely settle them in this world in a good place; but the reward of the Hereafter is greater, if only they could know. <> Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin sha'anin Allah daga bãyan an zãlunce su, haƙĩƙa Munã zaunar da su a cikin dũniya da alhẽri kuma lalle lãdar Lãhira ce mafi girmã, dã sun kasance sunã sani. = --Qur'an 16:41
    [They are] those who endured patiently and upon their Lord relied. <> Waɗanda suka yi haƙuri, kuma ga Ubangijinsu suke dõgara. = --Qur'an 16:42
    And We sent not before you except men to whom We revealed [Our message]. So ask the people of the message if you do not know. <> Kuma ba Mu aika daga gabaninka ba, fãce waɗansu mazãje Muna yin wahayi zuwa gare su. Sai ku tambayi mutãnen Ambato idan kun kasance ba ku sani ba. = --Qur'an 16:43
    [We sent them] with clear proofs and written ordinances. And We revealed to you the message that you may make clear to the people what was sent down to them and that they might give thought. <> Da hujjõji bayyanannu da littattafai kuma Mun saukar da Ambato zuwa gare ka, dõmin ka bayyana wa mutãne abin da aka sassaukar zuwa gare su, kuma don ɗammãninsu su yi tunãni. = --Qur'an 16:44
    Then, do those who have planned evil deeds feel secure that Allah will not cause the earth to swallow them or that the punishment will not come upon them from where they do not perceive? <> Shin fa, waɗanda suka yi mãkircin mũnãnan ayyuka sun amince da Allah, bã zai shafe ƙasa da su ba ko kuwa azãba bã zã ta je musu daga inda ba su sani ba? = --Qur'an 16:45
    Or that He would not seize them during their [usual] activity, and they could not cause failure? <> Ko kuwa Ya kama su a cikin jujjuyawarsu? Sabõda haka ba su zama masu buwãya ba. = --Qur'an 16:46
    Or that He would not seize them gradually [in a state of dread]? But indeed, your Lord is Kind and Merciful. <> Ko kuwa Ya kama su a kan naƙasa? To, lalle ne Ubangijinka haƙĩƙa Mai tausayi ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 16:47
    Have they not considered what things Allah has created? Their shadows incline to the right and to the left, prostrating to Allah, while they are humble. <> Shin, ba su Iura ba da abin da Allah Ya halitta kõ mene ne inuwõyinsu suna karkata daga dãma da wajãjen hagu, suna masu sujada ga Allah, alhãli suna masu ƙasƙantar da kai? = --Qur'an 16:48
    And to Allah prostrates whatever is in the heavens and whatever is on the earth of creatures, and the angels [as well], and they are not arrogant. <> Kuma ga Allah, abin da yake a cikin sammai da ƙasa na dabba da mala'iku, suke yin sujada, kuma bã su kangara. = --Qur'an 16:49
    They fear their Lord above them, and they do what they are commanded. <> Suna tsõron Ubangijinsu daga bisansu, kuma suna aikata abin da ake umuruin su. = --Qur'an 16:50
    And Allah has said, "Do not take for yourselves two deities. He is but one God, so fear only Me." <> Kuma Allah Ya ce: "Kada ku riƙi abũbuwan bautãwa biyu. Abin sani kawai, wanda ake bautãwa guda ne, sa'an nan sai kuji tsõroNa, Ni kawai." = --Qur'an 16:51
    And to Him belongs whatever is in the heavens and the earth, and to Him is [due] worship constantly. Then is it other than Allah that you fear? <> Kuma Yana da abin da yake a cikin sammai da ƙasa, kuma Yana da addini wanda yake dawwamamme. Shin fa, wanin Allah kuke bĩ da taƙãwa? = --Qur'an 16:52
    And whatever you have of favor - it is from Allah. Then when adversity touches you, to Him you cry for help. <> Kuma abin da yake a gare ku na ni'ima, to, daga Allah ne. Sa'an nan kuma idan cũta ta shãfeku, to, zuwa gare Shi kuke hargõwa. = --Qur'an 16:53
    Then when He removes the adversity from you, at once a party of you associates others with their Lord <> sa'an nan idan Ya kuranye cũtar daga gare ku, sai gã wani ɓangare daga gare ku game da Ubangijinsu sunã shirki. = --Qur'an 16:54
    So they will deny what We have given them. Then enjoy yourselves, for you are going to know. <> Dõmin su kãfirta da abin da Muka bã su. To, ku ji dãɗi, sa'an nan da sannu zã ku sani. = --Qur'an 16:55
    And they assign to what they do not know a portion of that which We have provided them. By Allah, you will surely be questioned about what you used to invent. <> Kuma sunã sanya rabõ ga abin da ba su sani ba daga abin da Muka azurtã su. Ranstuwa da Allah! Lalle ne zã a tambaye ku daga abin da kuka kasance kunã ƙirƙirãwa. = --Qur'an 16:56
    And they attribute to Allah daughters - exalted is He - and for them is what they desire. <> Kuma sunã danganta 'ya'ya mãta ga Allah. Tsarkinsa yã tabbata! Kuma sũ ne da abin da suke sha'awa. = --Qur'an 16:57
    And when one of them is informed of [the birth of] a female, his face becomes dark, and he suppresses grief. <> Kuma idan aka yi wa ɗayansu bushãra da mace sai fuskarsa ta wuni baƙa ƙirin, alhãli kuwa yanã mai cike da baƙin ciki. = --Qur'an 16:58
    He hides himself from the people because of the ill of which he has been informed. Should he keep it in humiliation or bury it in the ground? Unquestionably, evil is what they decide. <> Yanã ɓõyẽwa daga mutãne dõmin mũnin abin da aka yimasa bushãra da shi. Shin, zai riƙe shi a kan wulãkanci kõ zai turbuɗe shi a cikin turɓãya To, abin da suke hukuntãwa ya mũnana. = --Qur'an 16:59
    For those who do not believe in the Hereafter is the description of evil; and for Allah is the highest attribute. And He is Exalted in Might, the Wise. <> Ga waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba akwai sifar cũta kuma ga Allah akwai sifa mafi ɗaukaka. Kuma shi ne Mabuwãyi, Mai hikima. = --Qur'an 16:60
    And if Allah were to impose blame on the people for their wrongdoing, He would not have left upon the earth any creature, but He defers them for a specified term. And when their term has come, they will not remain behind an hour, nor will they precede [it]. <> Kuma dã Allah Yanã kãma mutãne da zãluncinsu, dã bai bar wata dabba ba a kan ƙasa. Kuma amma Yanã jinkirta musu zuwa ga ajali ambatacce. Sa'an nan idan ajalinsu ya zo, bã zã a yi musu jinkiri ba kõ da sa'a guda, kuma bã zã su gabãta ba. = --Qur'an 16:61
    And they attribute to Allah that which they dislike, and their tongues assert the lie that they will have the best [from Him]. Assuredly, they will have the Fire, and they will be [therein] neglected. <> Kuma sunã sanyã wa Allah abin da suke ƙi, kuma harsunansu na siffanta ƙarya cẽwa lalle ne sunã da abũbuwa mãsu kyau. Bãbu shakka lalle ne sunã da wuta, kuma lalle sũ, waɗanda ake ƙyãlẽwa ne (a cikinta). = --Qur'an 16:62
    By Allah, We did certainly send [messengers] to nations before you, but Satan made their deeds attractive to them. And he is the disbelievers' ally today [as well], and they will have a painful punishment. <> Rantsuwar Allah! Lalle ne haƙĩƙa Mun aika zuwa ga al'ummomi daga gabãninka, sai Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, sabõda haka shĩ ne majiɓincinsu, a yau, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 16:63
    And We have not revealed to you the Book, [O Muhammad], except for you to make clear to them that wherein they have differed and as guidance and mercy for a people who believe. <> Lalle ba Mu saukar da Littafi ba a kanka, fãce dõmin ka bayyanã musu abin da suka sãɓã wa jũna a cikinsa, kuma dõmin shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni. = --Qur'an 16:64
    And Allah has sent down rain from the sky and given life thereby to the earth after its lifelessness. Indeed in that is a sign for a people who listen. <> Kuma Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya rãyar da ƙasa da shi a bãyan mutuwarta. Lalle ne a cikin wannan haƙĩƙa akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke saurãre. = --Qur'an 16:65
    And indeed, for you in grazing livestock is a lesson. We give you drink from what is in their bellies - between excretion and blood - pure milk, palatable to drinkers. <> Kuma lalle ne, kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'ima; Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikin cikunansu, daga tsakãnin tukar tumbi da jini nõno tsantsan mai sauƙin haɗiya ga mãsu shã. = --Qur'an 16:66
    And from the fruits of the palm trees and grapevines you take intoxicant and good provision. Indeed in that is a sign for a people who reason. <> Kuma daga 'ya'yan itãcen dabĩno da inabi. Kunã sãmudaga gare shi, abin mãye da abinci mai kyau. Lalle a cikin wannan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke hankalta. = --Qur'an 16:67
    And your Lord inspired to the bee, "Take for yourself among the mountains, houses, and among the trees and [in] that which they construct. <> Kuma Ubangjinka Yã yi wahayi zuwa ga ƙudan zuma cẽwa: "Ki riƙi gidãje daga duwãtsu, kuma daga itãce, kuma daga abin da suke ginãwa." = --Qur'an 16:68
    Then eat from all the fruits and follow the ways of your Lord laid down [for you]." There emerges from their bellies a drink, varying in colors, in which there is healing for people. Indeed in that is a sign for a people who give thought. <> "Sa'an nan ki ci daga dukan 'ya'yan itãce, sabõda haka ki shiga hanyõyin Ubangijinka, sunã hõrarru." Wani abin shã yanã fita daga cikunanta, mai sãɓãwar launukansa a cikinsa akwai wata warkewa ga mutãne. Lalle ne, a cikin wannan, haƙĩƙa, akwaiãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin tunãni. = --Qur'an 16:69
    And Allah created you; then He will take you in death. And among you is he who is reversed to the most decrepit [old] age so that he will not know, after [having had] knowledge, a thing. Indeed, Allah is Knowing and Competent. <> Kuma Allah ne Ya halicce ku, sa'an nan Yanã karɓar rãyukanku, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwã zuwa ga mafi ƙasƙncin rãyuwa, dõmin kada ya san kõme a bãyan dã ya zama mai ilmi. Lalle Allah ne Masani Mai ĩkon yi. = --Qur'an 16:70
    And Allah has favored some of you over others in provision. But those who were favored would not hand over their provision to those whom their right hands possess so they would be equal to them therein. Then is it the favor of Allah they reject? <> Kuma Allah Ya fifita sãshenku a kan sãshe a arziki. Sa'an nan waɗanda aka fĩfĩta ba su zama mãsu mayar da arzikinsu a kan abin da hannãyensu na dãma suka mallaka ba, har su zama daidai a cikinsa. Shin fa, da ni'imar Allah suke musu? = --Qur'an 16:71
    And Allah has made for you from yourselves mates and has made for you from your mates sons and grandchildren and has provided for you from the good things. Then in falsehood do they believe and in the favor of Allah they disbelieve? <> Kuma Allah Yã sanya muku mãtan aure daga kãwunanku, kuma Ya sanya muku daga mãtan aurenku ɗiyã da jĩkõki, kuma Ya arzũta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi. Shin fa, da ƙarya suke yin ĩmãni, kuma da ni'imar Allah sũ, suke kãfirta? = --Qur'an 16:72
    And they worship besides Allah that which does not possess for them [the power of] provision from the heavens and the earth at all, and [in fact], they are unable. <> Kuma sunã bautã wa, baicin Allah, abin da yake bã ya mallakar wani arziki dõminsu, daga sammai da ƙasa game da kõme, kuma bã su iyawa (ga aikata kõme). = --Qur'an 16:73
    So do not assert similarities to Allah. Indeed, Allah knows and you do not know. <> Sa'an nan kada ku bãyar da waɗansu misãlai ga Allah. Lalle ne Allah Yanã sani, kuma kũ, ba ku sani ba. = --Qur'an 16:74
    Allah presents an example: a slave [who is] owned and unable to do a thing and he to whom We have provided from Us good provision, so he spends from it secretly and publicly. Can they be equal? Praise to Allah! But most of them do not know. <> Allah Yã buga wani misali da wani bãwa wanda bã ya iya sãmun ĩko a kan yin kõme, da (wani bãwa) wanda Muka azurtã shi daga gare Mu da arziki mai kyau. Sa'an nan shĩ yanã ciyarwa daga arzikin, a asirce da bayyane. Shin sunã daidaita? Gõdiya ta tabbata ga Allah. Ã'a mafi yawansu ba su sani ba. = --Qur'an 16:75
    And Allah presents an example of two men, one of them dumb and unable to do a thing, while he is a burden to his guardian. Wherever he directs him, he brings no good. Is he equal to one who commands justice, while he is on a straight path? <> Kuma Allah Ya buga wani misãli, maza biyu, ɗayansu bẽbe ne, ba ya iya sãmun ikon yin kõme, kuma shi nauyi ne a kan mai mallakarsa, inda duk ya fuskantar da shi, bã ya zuwa da wani alhẽri. Shin, yanã daidaita, shi da (namiji na biyu) wanda yake umurni da a yi ãdalci kuma yanã a kan tafarki madaidaici? = --Qur'an 16:76
    And to Allah belongs the unseen [aspects] of the heavens and the earth. And the command for the Hour is not but as a glance of the eye or even nearer. Indeed, Allah is over all things competent. <> Kuma ga Allah gaibin sammai da ƙasa yake, kuma al'amarin Sã'a bai zama ba fãce kamar walƙãwar gani, kõ kuwa shĩ ne mafi kusa! Lalle Allah a kan dukan kõme Mai ikon yi ne. = --Qur'an 16:77
    And Allah has extracted you from the wombs of your mothers not knowing a thing, and He made for you hearing and vision and intellect that perhaps you would be grateful. <> Kuma Allah ne Ya fitar da ku daga cikunan iyãyenku, ba da kunã sanin kõme ba, kuma Ya sanya muku ji da gannai da zukãta, tsammãninku zã ku gõde. = --Qur'an 16:78
    Do they not see the birds controlled in the atmosphere of the sky? None holds them up except Allah. Indeed in that are signs for a people who believe. <> Shin ba su ga tsuntsãye ba sunã hõrarru cikin sararin sama bãbu abin da yake riƙe su fãce Allah? Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni. = --Qur'an 16:79
    And Allah has made for you from your homes a place of rest and made for you from the hides of the animals tents which you find light on your day of travel and your day of encampment; and from their wool, fur and hair is furnishing and enjoyment for a time. <> Kuma Allah ne Ya sanya muku daga gidajenku wurin natsuwa, kuma Ya sanya muku daga fatun dabbõbin ni'ima wasu gidãje kunã ɗaukar su da sauƙi a rãnar tafiyarku da rãnar zamanku, kuma daga sũfinsu da gãshinsu da gẽzarsu (Allah) Ya sanya muku kãyan ɗãki da na jin dãɗi zuwa ga wani lõƙaci. = --Qur'an 16:80
    And Allah has made for you, from that which He has created, shadows and has made for you from the mountains, shelters and has made for you garments which protect you from the heat and garments which protect you from your [enemy in] battle. Thus does He complete His favor upon you that you might submit [to Him]. <> Kuma Allah ne Ya sanyã muku inuwa daga abin da Ya halitta, kuma Ya sanyã muku ɗãkuna daga duwãtsu, kuma Ya sanyã muku waɗansu riguna sunã tsare muku zãfi, da waɗansu rĩguna sunã tsare muku makãminku. Kamar wancan ne (Allah) Yake cika ni'imarSa a kanku, tsammãnin ku, kuna sallamawa. = --Qur'an 16:81
    But if they turn away, [O Muhammad] - then only upon you is [responsibility for] clear notification. <> To, idan sun jũya, to, abin da ya wajaba a kanka, shi ne iyarwã kawai, bayyananniyã. = --Qur'an 16:82
    They recognize the favor of Allah; then they deny it. And most of them are disbelievers. <> Suna sanin ni'imar Allah, sa'an nan kuma sunã musunta, kuma mafi yawansu kãfirai ne. = --Qur'an 16:83
    And [mention] the Day when We will resurrect from every nation a witness. Then it will not be permitted to the disbelievers [to apologize or make excuses], nor will they be asked to appease [Allah]. <> Kuma a rãnar da Muke tãyar da mai shaida daga kõwace al'umma, sa'an nan kuma bã zã a yi izni ba ga waɗanda suka kãfirta, kuma ba su zama ana nẽman kõmawarsu ba. = --Qur'an 16:84
    And when those who wronged see the punishment, it will not be lightened for them, nor will they be reprieved. <> Kuma idan waɗanda suka yi zãlunci suka ga azãba, sa'an nan bã za a saukake ta daga gare su ba, kuma bã su zama anã yi musu jinkiri ba. = --Qur'an 16:85
    And when those who associated others with Allah see their "partners," they will say," Our Lord, these are our partners [to You] whom we used to invoke besides You." But they will throw at them the statement, "Indeed, you are liars." <> Kuma idan waɗanda suka yi shirka suka ga abũbuwan shirkarsu sai su ce: "Yã Ubangijinmu! Waɗannan ne abũbuwanshirkarmu waɗanda muka kasance munã kira baicinKa". Sai su jẽfamagana zuwa gare su, "Lalle ne ku, haƙĩƙa, maƙaryata ne." = --Qur'an 16:86
    And they will impart to Allah that Day [their] submission, and lost from them is what they used to invent. <> Kuma su shiga nẽman sulhu zuwa ga Allah a rãnar nan, kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa ya ɓace daga gare su. = --Qur'an 16:87
    Those who disbelieved and averted [others] from the way of Allah - We will increase them in punishment over [their] punishment for what corruption they were causing. <> Waɗanda suka kãfirta kuma suka kange daga hanyar, Allah, Mun ƙãra musu wata azãba bisa ga azãbar, sabõda abin da suka kasance sunã yi na fasãdi. = --Qur'an 16:88
    And [mention] the Day when We will resurrect among every nation a witness over them from themselves. And We will bring you, [O Muhammad], as a witness over your nation. And We have sent down to you the Book as clarification for all things and as guidance and mercy and good tidings for the Muslims. <> Kuma a rãnar da Muke tãyar da shaidu a cikin kõwace al'umma a kansu daga kãwunansu, kuma Muka zo da kai kanã mai bãyar da shaida a kan waɗannan, kuma Mun saussaukar da Littãli a kanka dõmin yin bãyani ga dukkan kõme da shiriya da rahama da bushãra ga mãsu mĩƙa wuya (Musulmi). = --Qur'an 16:89
    Indeed, Allah orders justice and good conduct and giving to relatives and forbids immorality and bad conduct and oppression. He admonishes you that perhaps you will be reminded. <> Lalle Allah nã yin umurni da ãdalci da kyautatãwa, da bai wa ma'abũcin zumunta, kuma yanã hani ga alfãsha da abin da aka ƙi da rarrabe jama'a. Yanã yi muku gargaɗi, ɗammãnin ku, kunã tunãwa. = --Qur'an 16:90
    And fulfill the covenant of Allah when you have taken it, [O believers], and do not break oaths after their confirmation while you have made Allah, over you, a witness. Indeed, Allah knows what you do. <> Kuma ku cika da alkãwarin Allah idan kun yi alkawari, kuma kada ku warware rantsuwõyinku a bãyan ƙarfafa su, alhãli kuma haƙĩƙa kun sanya Allah Mai lãmuncẽwa a kanku. Kuma lalle Allah ne Yake sanin abin da kuke aikatãwa. = --Qur'an 16:91
    And do not be like she who untwisted her spun thread after it was strong [by] taking your oaths as [means of] deceit between you because one community is more plentiful [in number or wealth] than another community. Allah only tries you thereby. And He will surely make clear to you on the Day of Resurrection that over which you used to differ. <> Kuma kada ku kasance kamar wadda ta warware zarenta a bãyan tukka, ya zama warwararku, kunã riƙon rantsuwõyinku dõmin yaudara a tsakãninku, dõmin kasancẽwar wata al'umma tãfi rĩba daga wata al'umma! Abin sani kawai Allah Yanã jarrabar ku da shi, kuma lalle ne yanã bayyana muku a Rãnar ¡iyãma, abin da kuka kasance, a cikinsa, kunã sãɓã wajũna. = --Qur'an 16:92
    And if Allah had willed, He could have made you [of] one religion, but He causes to stray whom He wills and guides whom He wills. And you will surely be questioned about what you used to do. <> Kuma dã Allah Ya so, haƙĩ ƙa, dã Ya sanya ku al'umma gudã, kuma Yanã ɓatar da wanda Ya so. kuma Yanã shiryar da wanda Ya so. Lalle ne anã tambayarku abin da kuka kasance kunã aikatãwa. = --Qur'an 16:93
    And do not take your oaths as [means of] deceit between you, lest a foot slip after it was [once] firm, and you would taste evil [in this world] for what [people] you diverted from the way of Allah, and you would have [in the Hereafter] a great punishment. <> Kada ku riƙi rantsuwõyinku dõmin yaudara a tsakãninku, har ƙafa ta yi sulɓi a bãyan tabbatarta, kuma ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kange daga hanyar Allah. Kuma kunã da wata azãba mai girma. = --Qur'an 16:94
    And do not exchange the covenant of Allah for a small price. Indeed, what is with Allah is best for you, if only you could know. <> Kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da alkawarin Allah. Lalle ne abin da yake a wurin Allah shi ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kunã sani. = --Qur'an 16:95
    Whatever you have will end, but what Allah has is lasting. And We will surely give those who were patient their reward according to the best of what they used to do. <> Abin da yake a wurinku yanã ƙãrẽwa, kuma abin da yake a wurin Allah ne mai wanzuwã. Kuma lalle ne, Munã sãka wa waɗanda suka yi haƙuri da lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 16:96
    Whoever does righteousness, whether male or female, while he is a believer - We will surely cause him to live a good life, and We will surely give them their reward [in the Hereafter] according to the best of what they used to do. <> Wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ kuwa mace, alhãli yanã mũmini, to, haƙĩƙa Munã rãyar da shi, rãyuwa mai dãɗi. Kuma haƙĩƙa Munã sãkã musu lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 16:97
    So when you recite the Qur'an, [first] seek refuge in Allah from Satan, the expelled [from His mercy]. <> Sa'an nan idan ka karantã Alƙur'ãni, sai ka nẽmi tsari ga Allah daga shaiɗan jẽfaffe. = --Qur'an 16:98
    Indeed, there is for him no authority over those who have believed and rely upon their Lord. <> Lalle ne shi, bã shi da wani ƙarfi a kan waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sunã dõgara ga Ubangijinsu. = --Qur'an 16:99
    His authority is only over those who take him as an ally and those who through him associate others with Allah. <> Abin sani kawai ƙarfinsa yanã a kan waɗanda suke jiɓintar sa, kuma waɗanda suke sũ, game da shi, mãsu shirki ne. = --Qur'an 16:100
    And when We substitute a verse in place of a verse - and Allah is most knowing of what He sends down - they say, "You, [O Muhammad], are but an inventor [of lies]." But most of them do not know. <> Kuma idan Muka musanya wata ãyã a matsayin wata ãyã, kuma Allah ne Mafi sani ga abin da Yake saukarwa sai su ce: "Abin sani kawai, kai, aƙirƙiri ne." Ã'a, mafi yawansu bã swa sani. = --Qur'an 16:101
    Say, [O Muhammad], "The Pure Spirit has brought it down from your Lord in truth to make firm those who believe and as guidance and good tidings to the Muslims." <> Ka ce: "Rũhul ¡udusi ne ya sassaukar da shi, daga Ubangijinka da gaskiya, dõmin ya tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma (dõmin) shiriya da bushãra ga Musulmi." = --Qur'an 16:102
    And We certainly know that they say, "It is only a human being who teaches the Prophet." The tongue of the one they refer to is foreign, and this Qur'an is [in] a clear Arabic language. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa Munã sanin (cẽwa) lalle ne sũ, sunã cẽwa, "Abin sani kawai wani mutum ne yake karantar da shi." Harshen wanda suke karkatai da maganar zuwa gare shi, Ba'ajame ne, kuma wannan (Alƙur'ãni) harshe ne Balãrabe bayyananne. = --Qur'an 16:103
    Indeed, those who do not believe in the verses of Allah - Allah will not guide them, and for them is a painful punishment. <> Lalle ne waɗanda bã su yin ĩmãni da ãyõyin Allah, Allahbã zai shiryar da su ba, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 16:104
    They only invent falsehood who do not believe in the verses of Allah, and it is those who are the liars. <> Abin sani kawai waɗanda bã su yin ĩmãni da ãyõyin Allah, sũ ne suke ƙirƙira ƙarya. Kuma waɗannan sũ ne maƙaryata. = --Qur'an 16:105
    Whoever disbelieves in Allah after his belief... except for one who is forced [to renounce his religion] while his heart is secure in faith. But those who [willingly] open their breasts to disbelief, upon them is wrath from Allah, and for them is a great punishment; <> Wanda ya kãfirta da Allah daga bãyan ĩmãninsa, fãce wanda aka tĩlasta alhãli kuwa zũciyarsa tanã natse da ĩmãni kuma wanda ya yi farin ciki da kãfirci, to, akwai fushi a kansa daga Allah, kuma sunã da wata azãba mai girma. = --Qur'an 16:106
    That is because they preferred the worldly life over the Hereafter and that Allah does not guide the disbelieving people. <> Waɗancan ne kãfirai dõmin sun fĩfĩta son dũniya a kan Lãhira, kuma lalle ne Allah bã Ya shiryar da mutãne kãfirai. = --Qur'an 16:107
    Those are the ones over whose hearts and hearing and vision Allah has sealed, and it is those who are the heedless. <> Waɗancan ne waɗanda Allah Ya bice hasken zukãtansu da jinsu da gannansu. Kuma waɗancan sũ ne gafalallu. = --Qur'an 16:108
    Assuredly, it is they, in the Hereafter, who will be the losers. <> Bãbu shakka lalle ne a Lãhira sũ ne mãsu hasãra. = --Qur'an 16:109
    Then, indeed your Lord, to those who emigrated after they had been compelled [to renounce their religion] and thereafter fought [for the cause of Allah] and were patient - indeed, your Lord, after that, is Forgiving and Merciful <> Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka yi hijirã daga bãyan an fitine su, sa'an nan kuma suka yi jihãdi, kuma suka yi haƙuri, lalle ne Ubangijinka, daga bãyanta haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 16:110
    On the Day when every soul will come disputing for itself, and every soul will be fully compensated for what it did, and they will not be wronged. <> A rãnar da kõwane rai zai je yanã jãyayyar tunkuɗẽwa daga kansa, kuma a cika wa kõwane rai (sakamakon) abin da ya aikata, kuma sũ bã zã a zãlunce su ba. = --Qur'an 16:111
    And Allah presents an example: a city which was safe and secure, its provision coming to it in abundance from every location, but it denied the favors of Allah. So Allah made it taste the envelopment of hunger and fear for what they had been doing. <> Kuma Allah Ya buga misãli, wata alƙarya ta kasance amintacciyã, natsattsiyã, arzikinta yanã je mata a wadãce daga kõwane wuri sai ta kãfirta da ni'imõmin Allah, sabõda haka Allah ya ɗanɗana mata tufãfin yunwa da tsõro, sabõda abin da suka kasance sunã sanã'antãwa. = --Qur'an 16:112
    And there had certainly come to them a Messenger from among themselves, but they denied him; so punishment overtook them while they were wrongdoers. <> Kuma lalle ne haƙĩƙa wani Manzo daga gare su, ya jẽmusu, sai suka ƙaryata shi, sabõda haka azãba ta kãma su, alhãli kuwa sũ ne mãsu zãlunci. = --Qur'an 16:113
    Then eat of what Allah has provided for you [which is] lawful and good. And be grateful for the favor of Allah, if it is [indeed] Him that you worship. <> Sa'an nan ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku da shi, halas, kuma mai dãɗi, kuma ku gõde wa ni'imar Allah idan kun kasance shi kuke bautãwa. = --Qur'an 16:114
    He has only forbidden to you dead animals, blood, the flesh of swine, and that which has been dedicated to other than Allah. But whoever is forced [by necessity], neither desiring [it] nor transgressing [its limit] - then indeed, Allah is Forgiving and Merciful. <> Abin sani kawai (Allah) Ya haramta muku mussai da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah game da shi. Sa'an nan wanda aka tĩlastaa kan jama'a kuma baicin mai zãlunci, to, lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai. = --Qur'an 16:115
    And do not say about what your tongues assert of untruth, "This is lawful and this is unlawful," to invent falsehood about Allah. Indeed, those who invent falsehood about Allah will not succeed. <> Kuma kada ku ce, dõmin abin da harsunanku suke siffantawa da ƙarya, "Wannan halas ne, kuma wannan harãmun ne." Dõmin ku ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne, waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah bã zã su ci nasara ba. = --Qur'an 16:116
    [It is but] a brief enjoyment, and they will have a painful punishment. <> Jin dãɗi ne kaɗan. Kuma sunã da wata azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 16:117
    And to those who are Jews We have prohibited that which We related to you before. And We did not wrong them [thereby], but they were wronging themselves. <> Kuma kan waɗanda suka tũba (Yãhũdu) Mun haramta abin da Muka bãyar da lãbari a gare ka daga gabãni, kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun kasance kansu suke zãlunta. = --Qur'an 16:118
    Then, indeed your Lord, to those who have done wrong out of ignorance and then repent after that and correct themselves - indeed, your Lord, thereafter, is Forgiving and Merciful. <> Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka aikata mummunan aiki da jãhilci, sa'an nan suka tũba daga bãyan wancan, kuma suka gyãra, lalle ne Ubangijinka, daga bãyanta haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 16:119
    Indeed, Abraham was a [comprehensive] leader, devoutly obedient to Allah, inclining toward truth, and he was not of those who associate others with Allah. <> Lalle ne Ibrãhĩm ya kasance shũgaba, mai ƙasƙantar da kai ga Allah, mai karkatã zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba. = --Qur'an 16:120
    [He was] grateful for His favors. Allah chose him and guided him to a straight path. <> Mai gõdiya ga ni'imominSa (Allah), Ya zãɓe shi, kuma Ya shiryar da shi zuwa ga tafarki madaidaici. = --Qur'an 16:121
    And We gave him good in this world, and indeed, in the Hereafter he will be among the righteous. <> Kuma Muka ba shi alhẽri a cikin dũniya, Kuma lalle shĩ, a Lãhira, yanã daga sãlihai. = --Qur'an 16:122
    Then We revealed to you, [O Muhammad], to follow the religion of Abraham, inclining toward truth; and he was not of those who associate with Allah. <> Sa'an nan kuma Muka yi wahayi zuwa gare ka (cẽwa), "Ka bi aƙĩdar Ibrahĩm, mai karkatã zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.' = --Qur'an 16:123
    The sabbath was only appointed for those who differed over it. And indeed, your Lord will judge between them on the Day of Resurrection concerning that over which they used to differ. <> Abin sani kawai, an sanya Asabar a kan waɗanda suka sãɓã wajũna a cikin sha'aninsa. Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Yanã yin hukunci a tsakaninsu a Rãnar ¡iyãma a cikin abin da suka kasance a cikinsa sunã sãɓã wa jũnã. = --Qur'an 16:124
    Invite to the way of your Lord with wisdom and good instruction, and argue with them in a way that is best. Indeed, your Lord is most knowing of who has strayed from His way, and He is most knowing of who is [rightly] guided. <> Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa'azi mai kyau kuma ka yi jãyayya da su da magana wadda take mafi kyau. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMafi sani ga wanda ya ɓãce daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa. = --Qur'an 16:125
    And if you punish [an enemy, O believers], punish with an equivalent of that with which you were harmed. But if you are patient - it is better for those who are patient. <> Kuma idan kuka sãka wa uƙũba to ku sãka wa uƙũba da misãlin abin da aka yi muku uƙũbar da shi. Kuma idan kun yi haƙuri, lalle shĩ ne mafi alhẽri ga mãsu haƙuri. = --Qur'an 16:126
    And be patient, [O Muhammad], and your patience is not but through Allah. And do not grieve over them and do not be in distress over what they conspire. <> Kuma ka yi haƙuri, kuma haƙurinka bã zai zama ba fãce dõmin Allah, kuma kada ka yi baƙin ciki sabo da su, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke yi na mãkirci. = --Qur'an 16:127
    Indeed, Allah is with those who fear Him and those who are doers of good. <> Lalle Allah Yanã tãre da waɗanda suka yi taƙawa da waɗanda suke sũ mãsu kyautatãwa ne. = --Qur'an 16:128
    Exalted is He who took His Servant by night from al-Masjid al-Haram to al-Masjid al-Aqsa, whose surroundings We have blessed, to show him of Our signs. Indeed, He is the Hearing, the Seeing. <> Tsarki ya tabbata ga wanda Ya yi tafiyar dare da bãwanSa da dare daga Masallaci mai alfarma zuwa ga Masallaci mafi nĩsa wanda Muka sanya albarka a gefensa dõmin Mu nũna masa daga ãyõyinMu. Lalle ne Shi shĩ ne Mai ji, Mai gani. = [17:1] Tsarki ta tabbata ga wanda Ya kirawo bawanSa (Muhammad) da dare, daga Masallaci mai Alfarma (na Makka) zuwa ga Masallaci mafi nisa,*wanda Muka sanya albarka geyaye da shi, domin Mu nuna masa wasu ayoyinMu. Shi ne Mai ji, Mai gani. --Qur'an 17:1
    And We gave Moses the Scripture and made it a guidance for the Children of Israel that you not take other than Me as Disposer of affairs, <> Kuma Mun bai wa Mũsã littafi, kuma Mun sanya shi shiriya ga Banĩ Isrã'ila, cẽwa kada ku riƙi wani wakĩli baiciNa. = [17:2] Haka kuma muka baiwa Musa littafi, kuma muka sanya shi shiriya ga Bani Isra’ila, da cewa: “Kada ku riqi wani wakili baiciNa.” --Qur'an 17:2
    O descendants of those We carried [in the ship] with Noah. Indeed, he was a grateful servant. <> Zuriyar waɗanda Muka ɗauka tãre da Nũhu. Lalle ne shi ya kasance wani bãwa mai gõdiya. = [17:3] Zuriyar wadanda muka dauka tare da Nuhu; ya kasance bawa mai godiya. --Qur'an 17:3
    And We conveyed to the Children of Israel in the Scripture that, "You will surely cause corruption on the earth twice, and you will surely reach [a degree of] great haughtiness. <> Kuma Mun hukunta zuwa ga Bani Isrã'ĩla a cikin Littãfi, cewa lalle ne, kunã yin ɓarna a cikin ƙasa sau biyu, kuma lalle ne kunã zãlunci, zãlunci mai girma. = [17:4] Mun yi jawabi zuwa ga Bani Isra’ila a cikin littafi da cewa: “Zaku yi barna a cikin qasa sau biyu. Kuma an qaddara ku fada ga mafi girman kai. --Qur'an 17:4
    So when the [time of] promise came for the first of them, We sent against you servants of Ours - those of great military might, and they probed [even] into the homes, and it was a promise fulfilled. <> To idan wa'adin na farkonsu yajẽ, za Mu aika, a kanku waɗansu bãyi Nãmu, ma'abũta yãƙi mafĩ tsanani, har su yi yãwo a tsakãnin gidãjenku, kuma yã zama wa'adi abin aikatawa. = [17:5] “Sa’ad da wa’adin farko ta auku, za mu aika a kanku wadansu bayinmu masu yawan iko, kuma za su shiga gidajenku a kan farmaki. Wannan ambata ce wanda lalle ne ta auku. --Qur'an 17:5
    Then We gave back to you a return victory over them. And We reinforced you with wealth and sons and made you more numerous in manpower <> Sa'an nan kuma Mu nwayar da ɗauki a gare ku a kansu, kuma Mu taimake ku da dũkiyõyi da ɗiya kuma Mu sanya ku mafiya yawan mãsu fita yãƙi. = [17:6] “Sa’annan daga baya, za mu sa ku rama a kansu, kuma mu arzuta ku da dinbin dukiyoyi da yara; kuma mu sanya ku mafiya rinjaya. --Qur'an 17:6
    [And said], "If you do good, you do good for yourselves; and if you do evil, [you do it] to yourselves." Then when the final promise came, [We sent your enemies] to sadden your faces and to enter the temple in Jerusalem, as they entered it the first time, and to destroy what they had taken over with [total] destruction. <> Idan kun kyautata, kun kyautata dõmin kanku, kuma idan kun mũnana to dõmĩnsu. Sa'an nan idan wa'adin na ƙarshe ya jẽ, (za su je) dõmin su baƙanta fuskokinku, kuma su shiga masallaci kamar yadda suka shige shi a farkon lõkaci, kuma dõmin su halakar da abin da suka rinjaya a kansa, halakarwa. = [17:7] “Idan kuka kyautata, kun kyautata domin kanku, amma idan kuka yi mumunar aiki kun yi don kanku. Sa’annan idan wa’adin qarshe (ta biyu) ta zo, za su kayar da ku kuma su shiga masallaci, kamar yadda suka shiga daga farko. Za su shafe duk wani arzikin da kuka tanada.” --Qur'an 17:7
    [Then Allah said], "It is expected, [if you repent], that your Lord will have mercy upon you. But if you return [to sin], We will return [to punishment]. And We have made Hell, for the disbelievers, a prison-bed." <> Akwai tsammãnin Ubangijinku Ya yi muku rahama. Kuma idan kun sãke Mu sãke. Kuma Mun sanya Jahannama matsara ga kãfirai. = [17:8] Akwai tsammanin Ubangijinku zai yi maku rahamah. Amma idan kuka koma zuwa ga qetare iyaka, za mu saka da azaba. Kuma mun sanya jahannamah makomar kafirai. --Qur'an 17:8
    Indeed, this Qur'an guides to that which is most suitable and gives good tidings to the believers who do righteous deeds that they will have a great reward. <> Lalle ne wannan Alƙur'ãni yanã shiryarwa ga (hãlayen) waɗanda suke mafi daidaita kuma yanã bãyar da bushãra ga mũminai waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai (cẽwa) "Lalle ne sunã da wata ijãra. mai girma." = [17:9] Wannan Alqurani yana shiryarwa zuwa ga tafarki mafi daidaitawa, kuma yana bayar da bishara ga muminai wadanda suke aikata ayyuka na qwarai, cewa an yi masu ajiyan wata ladan ijara mai girma. --Qur'an 17:9
    And that those who do not believe in the Hereafter - We have prepared for them a painful punishment. <> Kuma lalle ne, waɗanda ba su yin ĩmãni da Lãhira, Mun yimusu tattalin wata azãba mai raɗaɗi. = [17:10] Amma ga wadanda ba su yi imani da Lahira ba, mun shirya masu azaba mai radadi. --Qur'an 17:10
    And man supplicates for evil as he supplicates for good, and man is ever hasty. <> Kuma mutum yanã yin addu'a da sharri kamar addu'arsa da alhẽri, kuma mutum ya kasance mai gaggãwa. = [17:11] Mutum yakan yi addu’a ga abin da zai cuce shi, yana tsammanin cewa addu’a ce ga abin alheri. Mutum ba shi da haquri. --Qur'an 17:11
    And We have made the night and day two signs, and We erased the sign of the night and made the sign of the day visible that you may seek bounty from your Lord and may know the number of years and the account [of time]. And everything We have set out in detail. <> Kuma Mun sanya dare da rãna, ãyõyi biyu, sa'an nan Muka shãfe ãyar dare, kuma Muka sanya ãyar rãna mai sanyãwa a yi gani, dõmin ku nẽmi falala daga Ubangijinku, kuma dõmin ku san ƙidãyar shẽkara da lissafi. Kuma dukan kõme Mun bayyana shi daki-dakin bayyanãwa. = [17:12] Mun sanya dare da rana ayoyi biyu. Sa’annan muka shafe dare da duhu, kuma muka sanya ayar rana da haske, domin ku nemi falala daga Ubangijinku. Kuma domin ku san qidayar shekara da lissafi. Ta haka muka bayyana kome dalla-dalla. --Qur'an 17:12
    And [for] every person We have imposed his fate upon his neck, and We will produce for him on the Day of Resurrection a record which he will encounter spread open. <> Kuma kõwane mutum Mun lazimta masa abin rekõdinsa a cikin wuyansa, kuma Mu fitar masa a Rãnar ¡iyãma da littãfi wanda zai haɗu da shi buɗaɗɗe. = [17:13] Kowane mutum mun lazimta masa abin rekondinsa a wuyansa. A Ranar Qiyamah za mu ba shi littafin rekodinsa wanda zai tarad da shi a fili. --Qur'an 17:13
    [It will be said], "Read your record. Sufficient is yourself against you this Day as accountant." <> "Karanta Littãfinka. Ranka ya isa ya zama mai hisãbi a kanka a yau." = [17:14] Karanta littafinka. A yau, kai ne maishin hisabin kanka. --Qur'an 17:14
    Whoever is guided is only guided for [the benefit of] his soul. And whoever errs only errs against it. And no bearer of burdens will bear the burden of another. And never would We punish until We sent a messenger. <> Wanda ya nẽmi shiryuwa, to, ya nẽmi shiryuwa ne dõminkansa kawai kuma wanda ya ɓace, to, ya ɓace ne a kansa kawai kuma rai mai ɗaukar nauyi bã ya ɗaukar nauyin wani ran, kuma ba Mu zama mãsu yin azãba ba, sai Mun aika wani Manzo. = [17:15] Wanda ya nemi shiryuwa, to, ya nemi shiryuwa ne domin kansa, kuma wanda ya bata ya bata domin kansa. Babu wani mai laifi da zai dauki laifin wani dabam. Ba mu yin azaba sai mun aika da manzo tukunna. --Qur'an 17:15
    And when We intend to destroy a city, We command its affluent but they defiantly disobey therein; so the word comes into effect upon it, and We destroy it with [complete] destruction. <> Kuma idan Mun yi nufin Mu halakar da wata alƙarya, sai Mu umurci mawadãtanta, har su yi fãsicci a cikinta, sa'an nan maganar azãba ta wajaba a kanta, sa'an nan Mu darkãke ta, darkãkẽwa. = [17:16] Idan muka nufa mu halakar da wata al’qarya, sai mu bari manyanta su aikata almundahana a cikinta. To, sa’ad da suka cancanci azaba, sai mu halakar da ita gaba daya. --Qur'an 17:16
    And how many have We destroyed from the generations after Noah. And sufficient is your Lord, concerning the sins of His servants, as Acquainted and Seeing. <> Kuma da yawa Muka halakar da al'ummomi a bãyan Nũhu. Kuma Ubangijinka Ya isa ya zama Mai ƙididdigewa ga zunubban bãyinSa, Mai gani. = [17:17] Sau da yawa mun halakar da al’ummomi a byan Nuhu. Ubangijinka Shi ne mafi iya tafiyad da zunuban bayinSa; Shi Masani ne, Mai gani. --Qur'an 17:17
    Whoever should desire the immediate - We hasten for him from it what We will to whom We intend. Then We have made for him Hell, which he will [enter to] burn, censured and banished. <> Wanda ya kasance yanã nufin mai gaggãwa, sai Mu gaggauta masa a cikinta, abin da Muke so ga wanda Muke nufi, sa'an nan kuma Mu sanya masa Jahannama, ya ƙõnu da ita, yanã abin zargi kuma abin tunkuɗewa. = [17:18] Wanda ya zabi wannan rayuwa mai saurin qarewa ya zama masa abin fifitawa, sai mu hanzarta zuwa gare shi abin da muka yi nufin mu ba shi, sa’annan mu saka shi a Jahannama, wurin da zai sha wuya na dauwama, yana abin rainawa da abin kadawa. --Qur'an 17:18
    But whoever desires the Hereafter and exerts the effort due to it while he is a believer - it is those whose effort is ever appreciated [by Allah]. <> Kuma wanda ya nufi Lãhira, kuma ya yi aiki sabõda ita irin aikinta alhãli kuwa yanã mũmĩni, to, waɗannan aikinsu ya kasance gõdadde. = [17:19] Amma ga wadanda suka zabi Lahira a matsayin abin fifiko, kuma suka aikata ayyuka na qwarai, alhali suna mu’minai, to, ayyukansu za su kasance anin yabawa. --Qur'an 17:19
    To each [category] We extend - to these and to those - from the gift of your Lord. And never has the gift of your Lord been restricted. <> Dukkansu Munã taimakon waɗannan da waɗancan daga kyautar Ubangijinka, kuma kyautar Ubangijinka ba ta kasance hananna ba. = [17:20] Kowane daga cikinsu muna tanadawa; muna tanadad wa wadancan da wadannan daga karimcin Ubangijinka. Karimcin Ubangijinka ba ta surewa. --Qur'an 17:20
    Look how We have favored [in provision] some of them over others. But the Hereafter is greater in degrees [of difference] and greater in distinction. <> Ka duba yadda Muka fĩfĩtar da sãshensu a kan sãshe! Kuma lalle ne Lãhira ce mafi girman darajõji, kuma mafi girman fĩfĩtãwa. = [17:21] Ku duba yadda muka fifita wasu mutane a kan wasu (a nan duniya). Kuma Lahira ce mafi bambamcin daraja kuma mafi girman fifitawa. --Qur'an 17:21
    Do not make [as equal] with Allah another deity and [thereby] become censured and forsaken. <> Kada ka sanya wani abin bautawa na daban tãre da Allah har ka zauna kana abin zargi, yarɓaɓɓe. = [17:22] Kada ku sanya wani abin bauta na dabam tare da ALLAH, har ka zama abin rainawa da abin kunyatawa. --Qur'an 17:22
    And your Lord has decreed that you not worship except Him, and to parents, good treatment. Whether one or both of them reach old age [while] with you, say not to them [so much as], "uff," and do not repel them but speak to them a noble word. <> Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa kõwa fãce Shi, kum game da mahaifa biyu ku kyautata kyautatawa, ko dai ɗayansu ya kai ga tsũfa a wurinka ko dukansu biyu, to, kada ka ce musu 'tir' kuma kada ka tsãwace su kuma ka faɗa musu magana mai karimci. = [17:23] Ubangijinka Ya hukunta cewa kada ku bautawa kowa sai Shi, kuma ku kyautawa iyayenku. Muddin dayansu ko biyunsu suna da rai, kada ku taba ce masu “Tir” (na nuna dan alamar fushi da su), kuma kada ku yi masu kuwa; ku yi masu magana mai karimci. --Qur'an 17:23
    And lower to them the wing of humility out of mercy and say, "My Lord, have mercy upon them as they brought me up [when I was] small." <> Kuma ka sassauta musu fikãfikan tausasãwa na rahama. Kuma ka ce: "Ya Ubangijina! Ka yi musu rahama, kamar yadda suka yi rẽnõna, ina ƙarami." = [17:24] Kuma ku sassauta masu fikafikan tawali’u da rahamah, kuma ku ce, “Ubangijina, Ka yi masu rahamah, kamar yadda suka yi mani reno ina qarami.” --Qur'an 17:24
    Your Lord is most knowing of what is within yourselves. If you should be righteous [in intention] - then indeed He is ever, to the often returning [to Him], Forgiving. <> Ubangijinku ne Mafi sani ga abin da yake a cikin rãyukanku. Idan kun kasance sãlihai to lalle ne shĩ Ya kasance ga mãsu kõmawa gare Shi, Mai gãfara. = [17:25] Ubangijinku ne mafi sani ga abin da ke sadarin zukatarku. Idan kuka kasance salihai, to, Shi mai gafara ne ga masu tuba. --Qur'an 17:25
    And give the relative his right, and [also] the poor and the traveler, and do not spend wastefully. <> Kuma ka bai wa ma'abũcin zumunta hakkinsa da miskĩna da ɗan hanya. Kuma kada ka bazzara dũkiyarka, bazzarãwa. = [17:26] Ku ba da haqqin da ya wajabta ga dangi, da mabukaci, da matalauci, da matafiya kan hanya, amma kada ku yi birbishin, bazzarawa. --Qur'an 17:26
    Indeed, the wasteful are brothers of the devils, and ever has Satan been to his Lord ungrateful. <> Lalle ne mubazzarai sun kasance 'yan'uwan shaiɗanu. Kuma Shaiɗan ya kasance ga Ubangijinsa, mai yawan kãfirci. = [17:27] Mubazzarai ‘yan’uwan shaidanu ne, kuma shaidan ba ya godiya ga Ubangijinsa. --Qur'an 17:27
    And if you [must] turn away from the needy awaiting mercy from your Lord which you expect, then speak to them a gentle word. <> Ko dai ka kau da kai daga gare su dõmin nẽman rahama daga Ubangijinka, wadda kake fãtanta, to sai ka gaya musu magana mai laushi. = [17:28] Ko da za ka kau da kai daga gare su, domin neman rahamah daga Ubangijinka, wanda kake fatanta, to, sai ka yi masu magana mai laushi. --Qur'an 17:28
    And do not make your hand [as] chained to your neck or extend it completely and [thereby] become blamed and insolvent. <> Kuma kada ka sanya hannunka ƙuƙuntacce zuwa ga wuyanka, kuma kada ka shimfiɗa shi dukan shimfiɗãwa har ka zama abin zargi, wanda ake yanke wa. = [17:29] Kada ka sanya hannunka a kan maqo zuwa ga wuyarka, ko kuma ka yi wautan bode su, har ka zama abin zargi da nadama. --Qur'an 17:29
    Indeed, your Lord extends provision for whom He wills and restricts [it]. Indeed He is ever, concerning His servants, Acquainted and Seeing. <> Lalle ne Ubangijinka Yanã shimfiɗa arzĩki ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuƙuntãwa. Lalle Shi, Yã kasance Mai sani ga bãyinSa, Mai gani. = [17:30] Ubangijinka ne mai qara arziki ga wanda ya zaba, kuma da hanawa. Shi ne masani ga bayinSa, Mai gani. --Qur'an 17:30
    And do not kill your children for fear of poverty. We provide for them and for you. Indeed, their killing is ever a great sin. <> Kuma kada ku kashe 'yã'yanku dõmin tsõron talauci. Mu ne ke arzũta su, su da ku. Lalle ne kashe su yã kasance kuskure babba. = [17:31] Kuma kada ku kashe ‘ya’yanku domin tsoron talauci. Mu ne ke arzuta su, su da ku. Kashe su babban laifi ne. --Qur'an 17:31
    And do not approach unlawful sexual intercourse. Indeed, it is ever an immorality and is evil as a way. <> Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfãsha ce kuma tã mũnãna ga zama hanya. = [17:32] Kuma kada ku kusanci yin zina; yinta babbar alfasha ce, kuma mumunar debi’a. --Qur'an 17:32
    And do not kill the soul which Allah has forbidden, except by right. And whoever is killed unjustly - We have given his heir authority, but let him not exceed limits in [the matter of] taking life. Indeed, he has been supported [by the law]. <> Kuma kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da haƙƙi, kuma wanda aka kashe, yanã wanda aka zãlunta to, haƙĩƙa Mun sanya hujja ga waliyyinsa, sai dai kada ya ƙẽtare haddi a cikin kashẽwar. Lalle shĩ ya kasance wanda ake taimako. = [17:33] Kuma kada ku yi wa kowace rai kisa – domin ALLAH Ya tsarkakata – sai dai a kan haqqi. Wanda aka kashe a kan zalunci, to, mun baiwa waliyyinsa izini ya nemi hukuncin adalci. Amma sai dai kada ya wuce iyaka wurin ramuwar kisa, za taimaka masa. --Qur'an 17:33
    And do not approach the property of an orphan, except in the way that is best, until he reaches maturity. And fulfill [every] commitment. Indeed, the commitment is ever [that about which one will be] questioned. <> Kuma kada ku kusanci dũkiyar marãya fãce dai da sifa wadda take ita ce mafi kyau, har ya isa ga mafi ƙarfinsa. Kuma ku cika alkawari. Lalle alkawari yã kasance abin tambayãwa ne. = [17:34] Kuma kada ku taba kudin marayu sai dai domin amfaninsu, har su kai ga balaga. Ku cika alkawarinku, saboda daukan alkawari babban alhaki ne. --Qur'an 17:34
    And give full measure when you measure, and weigh with an even balance. That is the best [way] and best in result. <> Kuma ku cika mũdu idan kun yi awo, kuma ku auna nauyi da sikẽli madaidaici. Wancan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara. = [17:35] Kuma ku cika mudu idan kun yi awo a kasuwanci, kuma ku auna nauyi na sikeli ta adalci. Wannan shi ne mafi alheri, kuma mafi adalci. --Qur'an 17:35
    And do not pursue that of which you have no knowledge. Indeed, the hearing, the sight and the heart - about all those [one] will be questioned. <> Kuma kada ka bi abin da bã ka da ilmi game da shi. Lalle ne jĩ da gani da zũciya, dukan waɗancan (mutum) yã kasance daga gare shi wanda ake tambaya. = [17:36] Kada ka bi abin da ba ka da ilmi game da shi. Lalle, ji da gani da tunani, kowanensu kai ke da alhakin amfani da su. --Qur'an 17:36
    And do not walk upon the earth exultantly. Indeed, you will never tear the earth [apart], and you will never reach the mountains in height. <> Kuma kada ka yi tafiya a cikin ƙasa da alfahari. Lalle kai bã zã ka hũda ƙasa ba kuma bã zã ka kai a duwãtsu ba ga tsawo. = [17:37] Kada ka yi tafiya da nuna alfahari a kan qasa – domin ba za ka iya huda hanya cikin qasa ba, ko ka yi tsawo kamar tsaunika. --Qur'an 17:37
    All that - its evil is ever, in the sight of your Lord, detested. <> Dukan wancan mli mũninsa yã kasance abin ƙyãma a wurin Ubangijinka. = [17:38] Dukan dabi’u marasa kyau an la’ancesu a wurin Ubangijinka. --Qur'an 17:38
    That is from what your Lord has revealed to you, [O Muhammad], of wisdom. And, [O mankind], do not make [as equal] with Allah another deity, lest you be thrown into Hell, blamed and banished. <> Wancan yãnã daga abin da Ubangijinka Ya yi wahayi zuwa gare ka na hikima. Kuma kada ka sanya wani abin bautãwa na daban tãre da Allah har a jẽfa ka a cikin Jahannama kanã wanda ake zargi, wanda ake tunkuɗẽwa = [17:39] Wannan yana daga abin da Ubangijinka Ya yi wahayi zuwa gare ka na hikimah. Kada ka sanya wani abin bautawa na dabam tare da ALLAH, har a jefa ka cikin jahannamah, ka zama abin zargi da kadawa. --Qur'an 17:39
    Then, has your Lord chosen you for [having] sons and taken from among the angels daughters? Indeed, you say a grave saying. <> Shin fa, Ubangijinku Ya zãɓe ku da ɗiya maza ne, kuma Ya riƙi 'ya'ya mãta daga malã'iku? Lalle ne kũ, haƙĩƙa, kunã faɗar magana mai girma! = [17:40] Shin, Ubangijinku Ya baku yara maza, alhali Yana baiwa kanSa mala’iku a matsayin ‘ya’ya mata?! Ta yaya za ku furta irin wannan sabo? --Qur'an 17:40
    And We have certainly diversified [the contents] in this Qur'an that mankind may be reminded, but it does not increase the disbelievers except in aversion. <> Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun sarrafa bayãni a cikin wannan Alƙur'ãni dõmin su yi tunãni, kuma bã ya ƙãra musu kõme fãce gudu. = [17:41] Mun sarrafa bayanai a cikin wannan Alqurani (da misalai dabam dabam), domin su yi tunani. Amma bai qara masu kome ba sai qyama. --Qur'an 17:41
    Say, [O Muhammad], "If there had been with Him [other] gods, as they say, then they [each] would have sought to the Owner of the Throne a way." <> Ka ce: "Dã akwai waɗansu abũbuwan bautãwa tãre da shi, kamar yadda suka faɗa, a lõkacin, dã (abũbuwan bautãwar) sun nẽmi wata hanya zuwa ga Ma'abũcin Al'arshi." = [17:42] Ka ce, “Idan da akwai wadansu abubuwan bautawa tare da Shi, kamar yadda suke fada, da sun yi yunqurin tunbuke Mamallakin Al’arshi.” --Qur'an 17:42
    Exalted is He and high above what they say by great sublimity. <> TsarkinSa yã tabbata kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke faɗã, ɗaukaka mai girma. = [17:43] TsarkinSa ya tabbata, Shi ne Mafi daukaka, nesa bisa ga abin da suke furtawa. --Qur'an 17:43
    The seven heavens and the earth and whatever is in them exalt Him. And there is not a thing except that it exalts [Allah] by His praise, but you do not understand their [way of] exalting. Indeed, He is ever Forbearing and Forgiving. <> Sammai bakwai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sunã yi Masa tasbĩhi. Kuma bãbu wani abu fãce yanã tasbĩhi game da gõde Masa, kuma amma ba ku fahimtar tasbĩhinsu. Lalle ne shĩ, Ya kasance Mai haƙuri ne, Mai gãfara. = [17:44] Masu yi maSa tasbihi su ne sammai bakwai, da qasa, da kome da ke cikinsu. Babu wani abin da baya yi maSa tasbihi, amma ba ku fahimtar tasbihinsu. Shi Ya kasance Mai haquri ne, Mai gafara. --Qur'an 17:44
    And when you recite the Qur'an, We put between you and those who do not believe in the Hereafter a concealed partition. <> Kuma idan ka karanta Alƙur'ani, sai Mu sanya a tsakãninka da tsakanin waɗanda bã su yin ĩmãni da Lãhira wani shãmaki mai suturcẽwa. = [17:45] Kumar idan ka karanta Aqurani, sai Mu sanya a tsakaninka da wadanda ba su yi imani da Lahira ba wani shamaki wanda ba iya gani. --Qur'an 17:45
    And We have placed over their hearts coverings, lest they understand it, and in their ears deafness. And when you mention your Lord alone in the Qur'an, they turn back in aversion. <> Kuma Mu sanya marufai a kan zukãtansu dõmin kada su fahimce shi, da, wani nauyi a cikin kunnuwansu, kuma idan ka ambaci Ubangijinka, a cikin Alƙur'ãni shĩ kaɗai, sai su jũya a kan bayayyakinsu dõmin gudu. = [17:46] Kuma Mu sanya marufuna a kan zukatansu, domin kada su fahimce shi, da wani nauyi a cikin kunnuwarsu. Kuma idan ka ambaci Ubangijinka, da yin amfani da Alqurani shi kadai,* sai su gudu a cikin qyama. --Qur'an 17:46
    We are most knowing of how they listen to it when they listen to you and [of] when they are in private conversation, when the wrongdoers say, "You follow not but a man affected by magic." <> Mũ ne Mafi sani game da abin da suke saurãre da shi a lõkacin da suke yin saurãren zuwa gare ka, kuma a lõkacin da suke mãsu gãnãwa a tsakãninsu a lõkacin da azzãlumai suke cẽwa, "Bã ku biyar kõwa fãce wani namiji sihirtacce." = [17:47] Mu ne Mafi sani game da abin da suke saurare, a lokacin da suke sauraronka, kuma da lokacin da suke ganawa a tsakaninsu na boye – azzalumai sai su ce, “Kana bin mahaukaci ne mai dabo.” --Qur'an 17:47
    Look how they strike for you comparisons; but they have strayed, so they cannot [find] a way. <> Ka dũba yadda suka buga maka misãlai, sai suka ɓace bã su iya sãmun hanya. = [17:48] Ka lura yadda suke misilta ka, kuma yadda wannan ke sa wa suna kaucewa a kan hanya. --Qur'an 17:48
    And they say, "When we are bones and crumbled particles, will we [truly] be resurrected as a new creation?" <> Kuma suka ce: "Shin, idan mun kasance ƙasũsuwa da, niƙaƙƙun gaɓãɓuwa ashe, lalle ne mũ haƙĩƙa, waɗanda ake tãyarwa ne a wata halitta sãbuwa?" = [17:49] Kuma sun ce, “Shin, idan mun koma ga qasusuwa da niqaqqun gababuwa, za tayar da mu halittu sabuwa?!” --Qur'an 17:49
    Say, "Be you stones or iron <> Ka ce: "Ku kasance duwãtsu ko kuwa baƙin ƙarfe." = [17:50] Ka ce, “Ko da kun zama dutsuna ne ko qarfe. --Qur'an 17:50
    Or [any] creation of that which is great within your breasts." And they will say, "Who will restore us?" Say, "He who brought you forth the first time." Then they will nod their heads toward you and say, "When is that?" Say, "Perhaps it will be soon - <> "Kõ kuwa wata halitta daga abin da yake da girma a cikin ƙirazanku." To zã su ce "Wãne ne zai mayar da mu?" Ka ce: "Wanda Ya ƙaga halittarku a fabkon lõkaci." To, zã su gyaɗa kansu zuwa gare ka, kuma sunã cẽwa, "A yaushene shi?" Ka ce: "Akwai tsammãninsa ya kasance kusa." = [17:51] “Ko da kun zama kowane irin halitta ne wanda kuke ganin babu daman iyawa.” Za su ce, “Wane ne zai mayar da mu?” Ka ce, “Wanda Ya qaga halittarku da farko.” To za su kada kansu su ce, “A yaushe wannan zai kasance?” Ka ce, “Zai yuwu yana kusa fiye da yadda kuke zato.” --Qur'an 17:51
    On the Day He will call you and you will respond with praise of Him and think that you had not remained [in the world] except for a little." <> "A rãnar da Yake kiran ku, sa'an nan ku riƙa karɓãwa game dã gõde Masa, kuma kunã zaton ba ku zauna ba fãce kaɗan." = [17:52] A ranar da zai kira ku, za ku amsa ne da yi maSa godiya, sa’annan kuma za ku ankara da cewan dadewanku a wannan rayuwar dan kadan ne. --Qur'an 17:52
    And tell My servants to say that which is best. Indeed, Satan induces [dissension] among them. Indeed Satan is ever, to mankind, a clear enemy. <> Kuma ka cẽ wa bãyiNa, su faɗi kalma wadda take mafi kyau. Lalle ne Shaiɗan yanã sanya ɓarna a tsakãninsu. Lalle ne Shaiɗan ya kasance ga mutum, maƙiyi bayyananne. = [17:53] Ka gaya wa bayiNa su yi wa junansu magana wanda take mafi kyau, saboda kullum shaidan zai nemi ya dasa qiyayya a tsakaninsu. Lalle ne, shaidan babban maqiyin mutum ne. --Qur'an 17:53
    Your Lord is most knowing of you. If He wills, He will have mercy upon you; or if He wills, He will punish you. And We have not sent you, [O Muhammad], over them as a manager. <> Ubangijinku ne Mafi sani game da ku. Idan Ya so, zai yi muku rahama, kõ kuwa idan Yã so zai azabtãku. Kuma ba Mu aika ka kanã wakĩli a kansu ba. = [17:54] Ubangijinku ne Mafi sani game da ku. Idan Ya so zai yi maku rahamah, ko kuwa idan Ya so zai azabta ku. Bamu aike ka ka zama wakili a kansu ba. --Qur'an 17:54
    And your Lord is most knowing of whoever is in the heavens and the earth. And We have made some of the prophets exceed others [in various ways], and to David We gave the book [of Psalms]. <> Kuma Ubangijinka ne Mafi sani game da wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun fĩfĩta sãshen Annabãwa a kan sãshe kuma Mun bai wa Dãwũda zabũra. = [17:55] Ubangijinka ne Mafi sani game da kowa da yake cikin sammai da qasa. Daidai da wannan ilmin, mun fifita wadansu annabawa a kan wadansu. Misali, mun baiwa Dawuda Zabura. --Qur'an 17:55
    Say, "Invoke those you have claimed [as gods] besides Him, for they do not possess the [ability for] removal of adversity from you or [for its] transfer [to someone else]." <> Ka ce: "Ku kirãyi waɗanda kuka riya, baicinSa." To, ba su mallakar kuranyẽwar cũta daga gare ku, kuma haka jũyarwa." = [17:56] Ka ce, “Ku kira duk wanda kuka riya baicinSa.” Ba su da iko su warkar da cutarku, ko su hana su. --Qur'an 17:56
    Those whom they invoke seek means of access to their Lord, [striving as to] which of them would be nearest, and they hope for His mercy and fear His punishment. Indeed, the punishment of your Lord is ever feared. <> Waɗancan, waɗanda suke kiran, sunã nẽman tsãni zuwa ga Ubangijinsu. Waɗanne ne suke mafĩfĩta a kusanta? Kuma sunã fãtan sãmun rahamarSa, kuma sunã tsõron azãbarSa. Lalle ne azãbar Ubangijinka ta kasance abar tsõro ce. = [17:57] Ko wadanda suke kira suma suna neman hanya ne zuwa ga Ubangijinsu. Suna qoqarin wadanne ne zai fi kusanta. Kuma suna fatan su samu rahamarSa, da jin tsoron azabarSa. Lalle ne, azabar Ubangijinka abin tsoro ne. --Qur'an 17:57
    And there is no city but that We will destroy it before the Day of Resurrection or punish it with a severe punishment. That has ever been in the Register inscribed. <> Kuma bãbu wata alƙarya fãce, Mu ne mãsu halaka ta a gabãnin Rãnar ¡iyãma kõ kuwa Mũ mãsu azãbta ta ne da azãba mai tsanani. Wancan ya kasance a cikin littãfi rubũtacce. = [17:58] Kuma babu wata alqaryah wanda baza mu halaka ta ba kafin Ranar Alqiyamah, ko kuwa mu sanya azaba mai tsanani a kansu. An riga an rubuta wannan a cikin littafi. --Qur'an 17:58
    And nothing has prevented Us from sending signs except that the former peoples denied them. And We gave Thamud the she-camel as a visible sign, but they wronged her. And We send not the signs except as a warning. <> Kuma bãbu abin da ya hana Mu, Mu aika da ãyõyi fãce sabõda mutãnen farko sun ƙaryata game da su. Kuma Mun bai wa Samũdãwa tãguwa, ãyã bayyananna, sai suka yi zãlunci game da ita. Kuma bã Mu aikãwa da ãyõyi fãce dõmin tsõratarwa. = [17:59] Babu abin da ya hana mu, mu aika da mu’ijizai sai domin mutanen zamanin farko sun qaryata su. Misali, mun baiwa Samudawa raqumi, wani bayyananna (mu’ijiza), amma sai suka aikata zalunci game da ita. Ba mu aikawa da mu’ijiza sai kawai domin qarfafa girmamawa. --Qur'an 17:59
    And [remember, O Muhammad], when We told you, "Indeed, your Lord has encompassed the people." And We did not make the sight which We showed you except as a trial for the people, as was the accursed tree [mentioned] in the Qur'an. And We threaten them, but it increases them not except in great transgression. <> Kuma a lõkacin da Muka ce maka, "Lalle ne Ubangijinka Yã kẽwaye mutãne." Kuma ba Mu sanya abin da ya gani wanda Muka nũna maka ba, fãce dõmin fitina ga mutãne, da itãciya wadda aka la'anta a cikin Alƙur'ani. Kuma Munã tsõratar da su, sa'an nan (tsõratarwar) bã ta ƙãra su fãce da kangara mai girma. = [17:60] Kuma a lokacin da muka sanar da kai cewa Ubangijinka ne mai cikkaken iko da mutane, kuma muka sanya mafalkin da muka nuna maka domin gwagi ga mutane, da itaciya wanda aka la’anta a cikin Alqurani.*Muka nuna masu hujjoji masu qarfi domin a qarfafa masu girmamawa, amma duk wannan ya qara masu tumbe ne kawai. --Qur'an 17:60
    And [mention] when We said to the angles, "Prostrate to Adam," and they prostrated, except for Iblees. He said, "Should I prostrate to one You created from clay?" <> Kuma a lõkacin da Muka cẽ wa malã'iku, "Ku yi sujada ga Ãdamu," sai suka yi sujada, fãce Ibilĩsa, ya ce: "shin, zan yi sujada ga wanda ka halitta shi yanã lãka?" = [17:61] Kuma a lokacin da muka ce wa mala’iku, “Ku yi sujadah ga Adam” sai suka yi sujadah, banda Iblis, ya ce, “Shin, zan yi sujadah ga wanda ka halitta shi da laka?” --Qur'an 17:61
    [Iblees] said, "Do You see this one whom You have honored above me? If You delay me until the Day of Resurrection, I will surely destroy his descendants, except for a few." <> Ya ce: "Shin, kã gan ka! Wannan wanda ka girmama a kaina, lalle ne idan ka jinkirtã mini zuwa ga Rãnar ¡iyãma lalle ne, zan tumɓuke zuriyarsa, fãce kaɗan." = [17:62] Ya ce, “Ka gan ka..! wannan wanda ka daukaka a kai na, idan ka jinkirta mini zuwa Ranar Alqiyamah, to zan mallaki zuriyarsa, illa qalilan.” --Qur'an 17:62
    [Allah] said, "Go, for whoever of them follows you, indeed Hell will be the recompense of you - an ample recompense. <> Ya ce: "Ka tafi. Sa'an nan wanda ya bĩ ka daga gare su, to, Jahannama ce sakamakonku, (Mu ba ku shi) sakamako cikakke." = 17:63] Ya ce, Sai ka tafi; kai da wadanda suka bi ka Jahannama ce sakamakonku; sakamakon da ya dace. --Qur'an 17:63
    And incite [to senselessness] whoever you can among them with your voice and assault them with your horses and foot soldiers and become a partner in their wealth and their children and promise them." But Satan does not promise them except delusion. <> "Kuma ka rikitar da wanda ka sãmi ĩko a kansa, daga gare su, da sautinka, kuma ka yi hari a kansu da dawãkinka da dãkãrunka kuma ka yi tãrẽwa da su a cikin dũkiyõyi da ɗiyã, kumaka yi musu wa'adi. Alhãli kuwa Shaiɗan bã ya yi musu wa'adin kõme fãce da ruɗi." = [17:64] Kana iya ka rikitar da wanda ka sami iko a kansa, a cikinsu, da sautinka, kuma ka shirya dukan dakarunka da mutanenka a kansu, kuma ka sami kaso a cikin dukiyoyisu da yaransu, kuma ka yi masu alkawari. Alhali kuwa duk abin da shaidan ya yi alkawari da shi ba kome ne ba sai rudi. --Qur'an 17:64
    Indeed, over My [believing] servants there is for you no authority. And sufficient is your Lord as Disposer of affairs. <> "Lalle ne bãyiNa, bã ka da wani ƙarfi a kansu. Kuma Ubangijinka Ya isa Ya zama wakĩli." = [17:65] “Amma ga bayiNa, baka da wani iko a kansu.” Ubangijinka Ya isa Ya zama Wakili. --Qur'an 17:65
    It is your Lord who drives the ship for you through the sea that you may seek of His bounty. Indeed, He is ever, to you, Merciful. <> Ubangijinku ne Yake gudãnar da jirgi a cikin tẽku, dõmin ku nema daga falalarSa. Lalle ne Shĩ, Yã kasance a gare ku Mai jin ƙai. = [17:66] Ubangijinku ne Yake gudanar da girajen ruwa a teku, domin ku nemi daga falalarSa. Shi ne Mafi jin qai a gare ku. --Qur'an 17:66
    And when adversity touches you at sea, lost are [all] those you invoke except for Him. But when He delivers you to the land, you turn away [from Him]. And ever is man ungrateful. <> Kuma idan cũta ta shãfe ku, a cikin tẽku, sai wanda kuke kira ya ɓace fãce Shi. To, a lõkacin da Ya tsira da ku zuwa, ga tudu sai kuka bijire. Kuma mutum ya kasance mai yawan butulci. = [17:67] Kuma idan masifa ta shafe ku a tsakiyar teku, sai ku manta da abubuwan da kuke kira na bautarku sai Shi kadai. Amma da zaran Ya tsirad da ku zuwa tudu, sai ku koma bijirewa. Lalle ne, mutum ya kasance mai yawan butulci. --Qur'an 17:67
    Then do you feel secure that [instead] He will not cause a part of the land to swallow you or send against you a storm of stones? Then you would not find for yourselves an advocate. <> Shin fa kun amince cẽwa (Allah) bã Ya shãfe gẽfen ƙasa game da ku kõ kuwa Ya aika da iska mai tsakuwa a kanku, sa'an nan kuma bã zã ku sãmi wani wakĩli ba dõminku? = [17:68] To shin, kun tabbatar ne cewa ba zai sa qasa, a tudu, ta hadeye ku ba? Ko kuwa Ya aika da iskan hadari mai tsakuwa a kanku, sa’annan ba za ku sami wani wakili mai kareku ba? --Qur'an 17:68
    Or do you feel secure that He will not send you back into the sea another time and send upon you a hurricane of wind and drown you for what you denied? Then you would not find for yourselves against Us an avenger. <> Ko kun amince ga Ya mayar da ku a cikin tẽkun a wani lõkaci na dabam, sa'an na Ya aika wata gũguwa mai karya abũbuwa daga iska, har ya nutsar da ku sabõda abin da kuka yi na kãfirci? Sa'an nan kuma bã ku sãmun mai bin hakki sabõda ku, a kanMu, game da Shi. = [17:69] Ko kun tabbatar ne cewa ba zai mayar da ku ba zuwa tekun a wani lokaci, sa’annan Ya aika da ambariyar ruwa wanda zai nutsar da ku saboda kafircinku? Idan hakan ya auku, ba za mu ba ku wata dama kuma ba. --Qur'an 17:69
    And We have certainly honored the children of Adam and carried them on the land and sea and provided for them of the good things and preferred them over much of what We have created, with [definite] preference. <> Kuma lalle ne Mun girmama 'yan Adam, kuma Muka ɗauke su a cikin ƙasa da tẽku kuma Muka azurta su daga abũbuwa mãsu dãɗi kuma Muka fĩfĩta su a kan mãsu yawa daga waɗanda Muka halitta, fĩfĩtãwa. = [17:70] Mun daukaka bil’Adama, kuma muka tanadad masu da abubuwan hawa a kan qasa da teku. Kuma muka arzuta su da abubuwa masu dadi, kuma muka yi masu yawan fifiko daga sauran abin da muka halitta. --Qur'an 17:70
    [Mention, O Muhammad], the Day We will call forth every people with their record [of deeds]. Then whoever is given his record in his right hand - those will read their records, and injustice will not be done to them, [even] as much as a thread [inside the date seed]. <> A rãnar da Muke kiran kõwane mutãne da lĩmãminsu to, wanda aka bai wa littafinsa a dã, mansa, to, waɗannan sunã karãtun littãfinsu, kuma bã a zãluntar su da zaren bãkin gurtsin dabĩno. = [17:71] Wata rana za mu kira kowane mutane, tare da limaminsu. Wadanda aka bai wa littafinsa na ayyukan qwarai a damansu, za su karanta rubutaccen littafinsu kuma ba za zalunce su ba ko kadan. --Qur'an 17:71
    And whoever is blind in this [life] will be blind in the Hereafter and more astray in way. <> Kuma wanda ya kasance makãho a cikin wannan sabõda haka shi a Lãhira makãho ne kuma mafi ɓata ga hanya. = [17:72] Amma ga wadanda su makafi ne a nan rayuwa, za su kasance makafi a Lahira; wanda ya fi muni. --Qur'an 17:72
    And indeed, they were about to tempt you away from that which We revealed to you in order to [make] you invent about Us something else; and then they would have taken you as a friend. <> Kuma lalle ne sun yi kusa haƙĩƙa, su fitinẽ ka daga abin da Muka yi wahayi zuwa gare ka, dõmin ka ƙirƙira waninsa a gare Mu, a lõkacin, haƙĩƙa, dã sun riƙe ka masoyi. = [17:73] Sun yi kusan su juyad da kai daga ayoyin da muka yi wahayi zuwa gare ka. Sun so ka qirqira wani abu dabam, domin su riqe ka aboki. --Qur'an 17:73
    And if We had not strengthened you, you would have almost inclined to them a little. <> Kuma bã dõmin Mun tabbatar da kai ba, lalle ne, haƙĩƙa, dã kã yi kusa ka karkata zuwa gare su ta wani abu kaɗan. = [17:74] Ba domin mun qarfafa ka ba, ka kusan ka dan karkata zuwa gare su. --Qur'an 17:74
    Then [if you had], We would have made you taste double [punishment in] life and double [after] death. Then you would not find for yourself against Us a helper. <> A lõkacin, lalle ne, dã Mun ɗanɗana maka ninkin azãbar rãyuwa da ninkin azãbar mutuwa, sa'an nan kuma bã zã ka sãmi mataimaki ba a kanMu. = [17:75] Da kuwa ka aikata haka, da mun dandana maka ninkin azabar rayuwa da ninkin azaba bayan mutuwa, sa’annan da ba ka sami kowa ya taimaka maka a kanMu ba. --Qur'an 17:75
    And indeed, they were about to drive you from the land to evict you therefrom. And then [when they do], they will not remain [there] after you, except for a little. <> Kuma lalle ne, sun yi kusa, haƙĩƙa, su tãyar da hankalinka daga ƙasar, dõmin su fitar da kai daga gare ta. Kuma a lõkacin, bã zã su zauna ba a kan sãɓãninka fãce kaɗan. = [17:76] Kuma sun yi kusa su kore ka daga qasa saboda su rabu da kai, domin su koma bijirewa da zaran ka tafi. --Qur'an 17:76
    [That is Our] established way for those We had sent before you of Our messengers; and you will not find in Our way any alteration. <> Hanyar waɗanda, haƙĩƙa, Muka aika a gabãninka, daga ManzanninMu, kuma bã zã ka sãmi jũyarwa ba ga hanyarMu. = [17:77] Sharadin wannan daidai ne da batun dukan manzanninMu da muka aika a gabaninka, kuma za ka ga cewa sunnarMu bata canzawa. --Qur'an 17:77
    Establish prayer at the decline of the sun [from its meridian] until the darkness of the night and [also] the Qur'an of dawn. Indeed, the recitation of dawn is ever witnessed. <> Ka tsayar da salla a karkatar rãnã zuwa ga duhun dare da lõkacin fitar alfijir lalle ne karãtun fitar alfijir ya kasance wanda ake halarta. = [17:78] Ku tsayar da Sallah a karkatar rana, zuwa ga duhun dare; da yin karatun Alquranin alfijir. Lalle ne, karatun Alqurani alfijir ya kasance wanda ake halarta. --Qur'an 17:78
    And from [part of] the night, pray with it as additional [worship] for you; it is expected that your Lord will resurrect you to a praised station. <> Kuma da dare, sai ka yi hĩra da shi (Alƙur'ãni) akan ƙãri gare ka. Akwai tsammãnin Ubangijinka Ya tãyar da kai a wani matsayi gõdadde. = [17:79] Kuma da dare, sai ka yi nafila saboda qarin lada, akwai fatan Ubangijinka zai daga ka zuwa wani daraja mai daukaka. --Qur'an 17:79
    And say, "My Lord, cause me to enter a sound entrance and to exit a sound exit and grant me from Yourself a supporting authority." <> Kuma ka ce: "Yã Ubangijĩna! Ka shigar, da ni shigar gaskiya, kuma Ka fitar da ni fitar gaskiya. Kuma Ka sanya mini, daga gunKa, wani ƙarfi mai taimako." = [17:80] Kuma ka ce, “Ubangijina, ka shigar da ni shigar gaskiya, kuma ka sa na fita, fitar gaskiya, kuma Ka sanya mini daga wurinKa taimako mai qarfi.” --Qur'an 17:80
    And say, "Truth has come, and falsehood has departed. Indeed is falsehood, [by nature], ever bound to depart." <> Kuma ka ce: "Gaskiya tã zo, kuma ƙarya ta lãlãce. Lalle ne ƙarya ta kasance lãlãtacciya." = [17:81] Ka zayyanar, “Gaskiya ta bayyana, kuma qariya ta bace; lalle ne, qarya ta kasance abin bacewa ne.” --Qur'an 17:81
    And We send down of the Qur'an that which is healing and mercy for the believers, but it does not increase the wrongdoers except in loss. <> Kuma Munã sassaukarwa daga Alƙur'ãni, abin da yake waraka ne da rahama ga mũminai. Kuma bã ya ƙãra wa azzãlumai (kõme) fãce hasãra. = [17:82] Muna saukarwa daga Alqurani abin da yake waraka ne da rahamah ga muminai. Sa’annan kuma, baya qara wa azzalumai kome sai hasara. --Qur'an 17:82
    And when We bestow favor upon the disbeliever, he turns away and distances himself; and when evil touches him, he is ever despairing. <> Kuma idan Muka yi ni'ima a kan mutum, sai ya hinjire, kuma ya nĩsanta da gefensa, kuma idan sharri ya shãfe shi, sai ya kasance mai yanke ƙauna. = [17:83] Idan muka yi ni’ima a kan mutum, sai ya hinjire babu kulawa. Amma idan masifa ta same shi, sai ya yanke qauna. --Qur'an 17:83
    Say, "Each works according to his manner, but your Lord is most knowing of who is best guided in way." <> Ka ce: "Kõwa ya yi aiki a kan hanyarsa. Sa'an nan Ubangijinka ne Mafi sani ga wanda yake mafi shiryuwa ga hanya." = [17:84] Ka ce, “Kowa yana aiki daidai da ra’ayinsa ne, sa’annan Ubangijinka ne Mafi sani ga wadanda shiryayyu ne a kan hanya madaidaici.” --Qur'an 17:84
    And they ask you, [O Muhammad], about the soul. Say, "The soul is of the affair of my Lord. And mankind have not been given of knowledge except a little." <> Sunã tambayar ka ga rũhi. Ka ce: "Rũhi daga al'amarin Ubangijina ne, kuma ba a bã ku (kõme) ba daga ilmi fãce kaɗan." = [17:85] Suna tambayarka ga ruhi. Ka ce, “Ruhi daga al’amarin Ubangijina ne. Kuma ilmin da ake baku kadan ne.” --Qur'an 17:85
    And if We willed, We could surely do away with that which We revealed to you. Then you would not find for yourself concerning it an advocate against Us. <> Kuma lalle ne idan Mun so, haƙĩƙa, Munã tafiya da abinda Muka yi wahayi zuwa gare ka. Sa'an nan kuma bã za ka sãmi wani wakĩli ba dõminka game da shi a kanMu. = 17:86] Idan mun so, sai mu karbe abin da muka yi wahayi zuwa gare ka, sa’annan ba za ka sami wani wakilin da zai kare ka ba a kanMu. --Qur'an 17:86
    Except [We have left it with you] as a mercy from your Lord. Indeed, His favor upon you has ever been great. <> Fãce da rahama daga Ubangijinka. Lalle ne falalarSa ta kasance mai girma a kanka. = [17:87] Wannan rahamah ce daga Ubangijinka. FalalarSa ta kasance mai yawa a kanka. --Qur'an 17:87
    Say, "If mankind and the jinn gathered in order to produce the like of this Qur'an, they could not produce the like of it, even if they were to each other assistants." <> Ka ce: "Lalle ne idan mutãne da aljannu sun tãru a kan su zo da misãlin wannan Alƙur'ãni bã zã su zo da misãlinsa ba, kuma kõ dã sãshinsu yã kasance, mataimaki ga sãshi." = [17:88] Ka ce, “Idan da dukan mutane da aljannu za su taru su hada kai domin su zo da misalin wannan Alqurani, ba za su iya kawo misalinsa ba, kome taimakon da za su yi ga junansu.” --Qur'an 17:88
    And We have certainly diversified for the people in this Qur'an from every [kind] of example, but most of the people refused [anything] except disbelief. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun caccanza dõmin mutãne, a cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane misãli sai mafi yawan mutãne suka ƙi (kõme) fãce kãfirci, = [17:89] Mun sarrafa wa mutane a cikin wannan Alqurani kowane irin misalai, amma akasarin mutane sun nace a kan yin kafirci. --Qur'an 17:89
    And they say, "We will not believe you until you break open for us from the ground a spring. <> Kuma suka ce: "Bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka sai kã ɓuɓɓugar da idan ruwa daga ƙasa. = [17:90] Kuma suka ce, “Ba za mu imani ba dominka sai ka sa idon ruwa ta bulbule daga qasa. --Qur'an 17:90
    Or [until] you have a garden of palm tress and grapes and make rivers gush forth within them in force [and abundance] <> "Kõ kuma wata gõna daga dabĩnai da inabi ta kasance a gare ka. Sa'an nan ka ɓuɓɓugar da ƙõramu a tsakãninta ɓuɓɓugarwa." = [17:91] Ko kuma ka mallaki gonar dabinai da inabi, sa’annan da qoramun ruwa na gudana a tsakanin ta. --Qur'an 17:91
    Or you make the heaven fall upon us in fragments as you have claimed or you bring Allah and the angels before [us] <> "Kõ kuwa ka kãyar da sama a kanmu kaɓukka kõ kuwa ka zo da Allah, da malã'iku banga-banga." = [17:92] Ko kuwa ka sa duwatsu daga sama, kamar yadda kake fadi, su fado a kanmu. Ko kuma ka zo da ALLAH da mala’iku a gaban idanuwanmu. --Qur'an 17:92
    Or you have a house of gold or you ascend into the sky. And [even then], we will not believe in your ascension until you bring down to us a book we may read." Say, "Exalted is my Lord! Was I ever but a human messenger?" <> "Kõ kuwa wani gida na zĩnãriya ya kasance a gare ka, kõ kuwa ka tãka a cikin sama. Kuma bã zã mu yi ĩmãni ba ga tãkawarka, sai ka sassaukõ da wani littãfi a kanmu, munã karantã shi." Ka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijĩna! Ban kasance ba fãce mutum, Manzo." = [17:93] Ko kuwa ka mallaki wani gidan qasaita na zinariya, ko kuma ka hau cikin sama. Kuma ba za mu yi imani ba da takawarka, sai idan ka zo mana da wani littafin da za mu karanta.”* Ka ce, “Tsarki ya tabbata ga Ubangijina. Shin, ni wani abu ne ban da mutum manzo?” --Qur'an 17:93
    And what prevented the people from believing when guidance came to them except that they said, "Has Allah sent a human messenger?" <> Kuma bãbu abin da ya hana mutãne su yi ĩmãni, a lõkacin da shiriya ta jẽ musu, fãce sunce, "Shin, Allah zai aiko mutum ya zamo yana Manzo." = [17:94] Babu abin da ya hana mutane su yi imani sa’ad da shiriya ta zo masu, sai dai cewarsu, “Shin, ALLAH Ya aika da mutum a matsayin manzo?” --Qur'an 17:94
    Say, "If there were upon the earth angels walking securely, We would have sent down to them from the heaven an angel [as a] messenger." <> Ka ce: "Dã malã'iku sun kasance a cikin ƙasa, kuma sunã tafiya, sunã masu natsuwa, lalle ne dã mun saukar da malã'ika daga sama ya zama manzo a kansu." = [17:95] Ka ce, “Idan da mala’iku ne suke da zama a qasa, suna tafiya, da sanaki, da mun saukar da mala’ika daga sama ya zama masu manzo.” --Qur'an 17:95
    Say, "Sufficient is Allah as Witness between me and you. Indeed he is ever, concerning His servants, Acquainted and Seeing." <> Ka ce: "Allah Yã isa zama shaida a tsakãnina da ku. Lalle Shi Ya kasance ga bãyinsa, mai ƙididdigewa ne Mai gani." = [17:96] Ka ce, “ALLAH Ya isa zama shaida tsakanina da ku. Shi Mai cikakken sanin bayinSa ne, Mai gani. --Qur'an 17:96
    And whoever Allah guides - he is the [rightly] guided; and whoever He sends astray - you will never find for them protectors besides Him, and We will gather them on the Day of Resurrection [fallen] on their faces - blind, dumb and deaf. Their refuge is Hell; every time it subsides We increase them in blazing fire. <> Kuma wanda Allah Ya shiryar, to, shĩ ne shiryayye, kuma wanda Ya ɓatar to bã zã ka sãmi waɗansu masõya gare su ba baicinSa. Kuma Munã tãra su a Rãnar ¡iyãma a kan fuskõkinsu, sunã makãfi, kuma bẽbãye da kurãme. Matattararsu Jahannama ce, kõ da yaushe ta bice, sai Mu ƙãra musu wata wuta mai tsanani. = [17:97] Kuma wanda ALLAH Ya shiriyar, to, shi ne shiriyayye na gaske. Kuma wanda ya batar, to, ba za ka sami wadansu masoya a gare su ba baicinSa. Za mu tara su a Ranar Alqiyamah na tilastawa; suna makafi, bebaye, da kurame. Masaukinsu Jahannama; a duk lokacin da ta huce, sai mu qara zafin wutansu. --Qur'an 17:97
    That is their recompense because they disbelieved in Our verses and said, "When we are bones and crumbled particles, will we [truly] be resurrected [in] a new creation?" <> Wancan ne sãkamakonsu sabõda lalle sũ, sun kãfirta da ãyõ yinMu, kuma suka ce: "Shin idan muka kasance ƙasũsuwa da nĩƙaƙƙun gaɓũɓuwa, shin lalle mũ, haƙĩ ka, waɗanda ake tãyarwa ne a cikin wata halitta sãbuwa?" = [17:98] Irin sakamakonsu da ya dace kenan, tun da sun kafirta da ayoyinmu. Kuma suka ce, “Shin, idan muka kasance qasusuwa da niqaqun gabubuwa, za tayar da mu cikin wata sabuwar halitta?” --Qur'an 17:98
    Do they not see that Allah, who created the heavens and earth, is [the one] Able to create the likes of them? And He has appointed for them a term, about which there is no doubt. But the wrongdoers refuse [anything] except disbelief. <> Shin, kuma ba su ganĩ ba (cẽwa) lalle ne Allah, wandaYa halicci sammai da ƙasa, Mai ikon yi ne a kan Ya halicci misãlinsu? Kuma Ya sanya wani ajali wanda bãbu kõkwanto a cikinsa? Sai azzãlumai suka ƙi fãce kãfirci. = [17:99] Shin, ba su gani ba ne cewan ALLAH wanda Ya halicci sammai da qasa Mai ikon yi ne bisa sake halittan misalinsu? Ya sanya ajali wanda babu fashi a cikinta. Amma duk da haka, azzalumai sun nace a kan kafirci. --Qur'an 17:99
    Say [to them], "If you possessed the depositories of the mercy of my Lord, then you would withhold out of fear of spending." And ever has man been stingy. <> Ka ce: "Dã dai kũ, kunã mallakar taskõkin rahamar Ubangijĩna, a lõkacin, haƙĩƙa dã kun kãme dõmin tsõron ƙãrẽwar taskõkin. Kuma mutum yã kasance mai ƙwauro ne." = [17:100] Ka zayyana, “Idan da kun mallaki dukiyar rahamar Ubangijina, da kun riqe su baku bayar ba, domin tsoron za ku qarad da su. Mutum marowaci ne.” --Qur'an 17:100
    And We had certainly given Moses nine evident signs, so ask the Children of Israel [about] when he came to them and Pharaoh said to him, "Indeed I think, O Moses, that you are affected by magic." <> Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun bai wa Mũsã ãyõyi guda tara bayyanannu, sai ka tambayi Banĩ Isrã'ila, a lõkacin da ya jẽ musu, sai Fir'auna ya ce masa, "Lalle nĩ, inã zaton ka, ya Mũsã, sihirtacce." = [17:101] Mun bai wa Musa ayoyi guda tara bayyanannu – ka tambayi Bani Isra’ila. Sa’ad da ya je zuwa gare su, sai Fir’auna ya ce masa, “Ina ganin cewan kai, Musa, masihiri ne.” --Qur'an 17:101
    [Moses] said, "You have already known that none has sent down these [signs] except the Lord of the heavens and the earth as evidence, and indeed I think, O Pharaoh, that you are destroyed." <> Ya ce: "lalle ne haƙĩƙa ka sani bãbu wanda ya saukar da waɗannan, fãce Ubangijin sammai da ƙasa dõmĩn su zama abũbuwan lũra. Kuma lalle ne ni, haƙĩƙa, ina zaton ka, yã Fir'auna, halakakke." = [17:102] Ya ce, “Kai ma ka san babu mai iya tabbatar da wadannan sai, ainihin, Ubangijin sammai da qasa. Ni ma ina ganin cewan kai, Fir’auna tababbe ne.” --Qur'an 17:102
    So he intended to drive them from the land, but We drowned him and those with him all together. <> Sai ya yi nufin fitar da su daga ƙasar, sai Muka nutsar da shi, shi da wanda yake tãre da shi gabã ɗaya. = [17:103] Sa’annan ya bi su, sa’ad da yake koransu a qasar, sai muka nutsar da shi, shi tare da wadanda suka goya masa baya, dukansu. --Qur'an 17:103
    And We said after Pharaoh to the Children of Israel, "Dwell in the land, and when there comes the promise of the Hereafter, We will bring you forth in [one] gathering." <> Kuma Muka ce: daga bãyansa ga Banĩ Isrã'ĩla, "Ku zauni ƙasar. Sa'an nan idan wa'adin ƙarshe ya zo, zã Mu jẽ da ku jama'a-jama'a." = [17:104] Kuma muka ce, daga bayansa, wa bani Isra’ila, “Ku je ku zauna a cikin qasar. Sa’annan idan wa’adin qarshe ya zo, za mu tara ku duka a qungiya guda.” --Qur'an 17:104
    And with the truth We have sent the Qur'an down, and with the truth it has descended. And We have not sent you, [O Muhammad], except as a bringer of good tidings and a warner. <> Kuma da gaskiya Muka saukar da shi, kuma da gaskiya ya sauka. Kuma ba Mu aike ka ba fãce kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. = [17:105] Kuma da gaskiya muka saukar da shi, kuma da gaskiya ya sauka. Ba mu aike ka ba sai a matsayin mai ba da bishara, kuma mai gargadi. --Qur'an 17:105
    And [it is] a Qur'an which We have separated [by intervals] that you might recite it to the people over a prolonged period. And We have sent it down progressively. <> Kuma yanã abin karãtu Mun rarraba shi dõmin ka karanta shi ga mutane a kan jinkiri kuma Mun sassaukar da shi sassaukarwa. = [17:106] Kuma Alqurani wanda mun saukar a hankali, domin ka karanta shi ga mutane a kan tsowon lokaci, ko da yake mun saukar da shi gaba daya ne. --Qur'an 17:106
    Say, "Believe in it or do not believe. Indeed, those who were given knowledge before it - when it is recited to them, they fall upon their faces in prostration, <> Ka ce: "Ku yi ĩmãni da Shi, ko kuwa kada ku yi ĩmãni, lalle ne waɗanda aka bai wa ilmi daga gabãninsa, idan anã karãtunsa a kansu, sunã fãɗuwa ga haɓõɓinsu, sunã mãsu sujada." = [17:107] Ka zayyana, “Ku yi imani da shi, ko kuwa kada ku yi imani da shi.” Wadanda aka bai wa ilmi daga gabaninsa, idan aka karanta masu shi, za su fadi ga hababansu, suna sujadah. --Qur'an 17:107
    And they say, "Exalted is our Lord! Indeed, the promise of our Lord has been fulfilled." <> "Kuma sunã cẽwa: Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle ne wa'adin Ubangijinmu ya kasance, haƙĩƙa, abin aikatãwa." = [17:108] Kuma suna cewa, “Tsaki ya tabbata ga Ubangijinmu. Lalle ne, wannan ya cika wa’adin Ubangijinmu.” --Qur'an 17:108
    And they fall upon their faces weeping, and the Qur'an increases them in humble submission. <> Kuma sunã fãɗuwa ga haɓõɓinsu sunã kũka, kuma yanã ƙara musu tsõro. = [17:109] Suna fadiwa ga hababansu, suna sujadah da kuka, domin ya qara masu girmamawa. --Qur'an 17:109
    Say, "Call upon Allah or call upon the Most Merciful. Whichever [name] you call - to Him belong the best names." And do not recite [too] loudly in your prayer or [too] quietly but seek between that an [intermediate] way. <> Ka ce: "Ku kirayi Allah kõ kuwa ku kirãyi Mai rahama. Kõwane kuka kira to Yanã da sũnãye mafi kyau. Kuma, kada ka bayyana ga sallarka, kuma kada ka ɓõye ta. Ka nẽmi hanya a tsakãnin wancan." = [17:110] Ka ce, “Ku kira Shi ALLAH, ko ku kira Shi Alrahaman; kowane suna kuka kira, to, Shi ne Mai sunaye Mafi kyau.” Kuma kada ka bayyana Sallarka da qarfi, ko kuma ka boye ta; ka nemi matsakaicin murya. --Qur'an 17:110
    And say, "Praise to Allah, who has not taken a son and has had no partner in [His] dominion and has no [need of a] protector out of weakness; and glorify Him with [great] glorification." <> Kuma ka ce: "Gõdiyã ta tabbata ga Allah wanda bai riƙi ɗã ba kuma abõkin tãrayya bai kasance a gare Shi ba a cikin mulkinSa, kuma wani masõyi sabõda wulãkancin bai kasance a gare Shi ba." Kuma ka girmama Shi, girmamãwa. = [17:111] Kuma ka zayyana: “Godiya ta tabbata ga ALLAH, wanda bai haifi da ba, kuma ba Shi da abokin tarayya a cikin mulkinSa, kuma ba Ya bukatan wani masoyi saboda rashin qarfi,” kuma ka girmama Shi kullum. --Qur'an 17:111
    [All] praise is [due] to Allah, who has sent down upon His Servant the Book and has not made therein any deviance. <> Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya saukar da Littafi a kan bãwansa kuma bai sanya karkata ba a gare shi. = [18:1] Godiya ta tabbata ga ALLAH wanda ya saukar da littafi a kan bawanSa kuma bai sanya karkata ba a gare shi. --Qur'an 18:1
    [He has made it] straight, to warn of severe punishment from Him and to give good tidings to the believers who do righteous deeds that they will have a good reward <> Madaidaici, dõmin Ya yi gargaɗi da azãba mai tsanani daga gare shi, kuma Ya yi bushãra ga mũminai, waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai da (cẽwa) sunã da wata lãdã mai kyau. = [18:2] Madaidaicin (littafi) domin Ya yi gargadi game da azaba mai radadi daga wurinSa, kuma Ya yi bishara ga muminai wadanda suke aikata ayyuka na qwarai, da cewa suna da lada mai karimci. --Qur'an 18:2
    In which they will remain forever <> Sunã mãsu zama a cikinta har abada. = [18:3] Suna masu zama a cikinta na har abada. --Qur'an 18:3
    And to warn those who say, "Allah has taken a son." <> Kuma Ya yi gargaɗi ga waɗanda suka ce: "Allah yanã da ɗa." = [18:4] Kuma Ya yi gargadi ga wadanda suka ce, “ALLAH Ya haifi da!” --Qur'an 18:4
    They have no knowledge of it, nor had their fathers. Grave is the word that comes out of their mouths; they speak not except a lie. <> Ba su da wani ilmi game da wannan magana, kuma iyãyensu bã su da shi, abin da ke fita daga bãkunansu ya girma ga ya zama kalmar faɗa! Ba su faɗan kõme fãce ƙarya. = [18:5] Ba su da wani ilmi game da wannan furcin, kuma iyayensu ba su da shi. Abin da ke fita daga bakinsu yin sabo ne! Abin da suke furtawa babban qarya ne. --Qur'an 18:5
    Then perhaps you would kill yourself through grief over them, [O Muhammad], if they do not believe in this message, [and] out of sorrow. <> To, kã yi kusa ka halaka ranka a gurabbansu, wai dõmin ba su yi ĩmãni da wannan lãbãri ba sabõda baƙin ciki. = [18:6] Za ka kusan ka zargi kanka dangane da gurabbansu na wannan hadith, da bijirewa da shi; za ka kusan baqin ciki. --Qur'an 18:6
    Indeed, We have made that which is on the earth adornment for it that We may test them [as to] which of them is best in deed. <> Lalle ne Mũ, Mun sanya abin da ke kan ƙasa wata ƙawa ce gare ta, dõmin Mu jarraba su; wanne daga cikinsu zai zama mafi kyau ga aiki. = [18:7] Mun qawaita kome a qasa, domin mu jarrabe su, sa’annan ya bambanta a cikinsu wadanda suke ayyuka na qwarai. --Qur'an 18:7
    And indeed, We will make that which is upon it [into] a barren ground. <> Kuma lalle Mũ, Mãsu sanya abin da ke a kanta (ya zama) turɓãya ƙeƙasasshiya ne. = [18:8] Kuma lalle ne, za mu shafe kome da ke kanta, ta rage cikakken bakarare. --Qur'an 18:8
    Or have you thought that the companions of the cave and the inscription were, among Our signs, a wonder? <> Ko kuwa kã yi zaton cẽwa ma'abũta kõgo da allo sun kasance abin mãmãki daga ãyõyin Allah? = [18:9] To, mene ne kuwa ka ke tsamanin abin da yasa muke gaya maka game da as’hab el kahf, da lambobin da ke alaqa da su? Suna cikin mu’ijizanMu na ban mamaki. --Qur'an 18:9
    [Mention] when the youths retreated to the cave and said, "Our Lord, grant us from Yourself mercy and prepare for us from our affair right guidance." <> A lõkacin da samarin suka tattara zuwa ga kõgon, sai suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka bã mu wata rahama daga gare Ka, kuma Ka sauƙaƙe mana (sãmun) shiriya daga al'amarinmu." = [18:10] Sa’ad da samarin suka yi hijira a cikin ‘kahf’ (kogo), sai suka ce,“Ubangijinmu, ka bamu rahamah daga gare Ka, kuma Ka sa mana albarkacinKa a kan al’amarinmu da shiriyarKa.” --Qur'an 18:10
    So We cast [a cover of sleep] over their ears within the cave for a number of years. <> Sai Muka yi dũka a kan kunnunwansu, a cikin kõgon, shẽkaru mãsu yawa. = [18:11] Sai muka rufe kunnuwarsu a cikin kogo na qudirin lambobin shekaru. --Qur'an 18:11
    Then We awakened them that We might show which of the two factions was most precise in calculating what [extent] they had remained in time. <> Sa'an nan Muka tãyar da su, dõmin Mu san wane ɗayan ƙungiyõyin biyu suka fi lissãfi ga abin da suka zauna na lõkacin. = [18:12] Sa’annan muka tayar da su, domin mu ga kowane dayan gungiyoyin biyu zai iya lissafin adadin lokacin da suka tsaya a wurin. --Qur'an 18:12
    It is We who relate to you, [O Muhammad], their story in truth. Indeed, they were youths who believed in their Lord, and We increased them in guidance. <> Mu ne ke jẽranta maka lãbãrinsu da gaskiya. Lalle ne sũ, waɗansu samãri ne. Sun yi ĩmãni da Ubangijinsu, kuma Muka ƙãra musu wata shiriya. = [18:13] Mu ne ke baka wannan labarin, da gaskiya. Lalle ne, su wasu samari ne wanda suka yi imani da Ubangijinsu, kuma muka qara masu shiriya. --Qur'an 18:13
    And We made firm their hearts when they stood up and said, "Our Lord is the Lord of the heavens and the earth. Never will we invoke besides Him any deity. We would have certainly spoken, then, an excessive transgression. <> Kuma Muka ɗaure a kan zukãtansu, a lõkacin da suka tsayu, sa'an nan suka ce: "Ubangijinmu Shĩ ne Ubangijin sammai daƙasa. Bã zã mu kirãyi waninSa abin bautawa ba. (Idan mun yi haka) lalle ne, haƙĩƙa, mun faɗi abin da ya ƙẽtare haddi a sa'an nan." = [18:14] Kuma muka qarfafa masu zukatansu sa’ad da suka yi tsayin daka suka ce: “Ubangijinmu kadai Shi ne Ubangijin sammai da qasa. Ba za mu bautawa wani baicinSa ba. Idan muka yi haka, za mu bata. --Qur'an 18:14
    These, our people, have taken besides Him deities. Why do they not bring for [worship of] them a clear authority? And who is more unjust than one who invents about Allah a lie?" <> "Ga waɗannan mutãnenmu sun riƙi waninSa abin bautãwa! Don me bã su zuwa da wata hujja bayyananna a kansu (waɗanda ake bautawar)? To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙãga ƙarya ga Allah?" = [18:15] Ga mutanenmu suna sanya wasu abin bautawa baicinSa. Idan da ma za su bada wani hujja bayyananna a kan dalilin abin da suke bautawa! To, wane ne mafi zalunci da wanda ya qaga qarya ya dangana su ga ALLAH? --Qur'an 18:15
    [The youths said to one another], "And when you have withdrawn from them and that which they worship other than Allah, retreat to the cave. Your Lord will spread out for you of His mercy and will prepare for you from your affair facility." <> "Kuma idan kun nĩsance su sũ da abin da suke bautãwa, fãce Allah, to, ku tattara zuwa ga kõgon sai Ubangijinku Ya watsa muku daga rahamarSa kuma Ya sauƙaƙe muku madõgara daga al'amarinku." = [18:16] “Tun da kuna nufin ku nisance su, su da abin da suke bautawa baicin ALLAH,* bari mu fake a cikin kogo. Ubangijinku Ya sanya maku rahamarSa kuma Ya nuna maku madaidaicin shawararku.” --Qur'an 18:16
    And [had you been present], you would see the sun when it rose, inclining away from their cave on the right, and when it set, passing away from them on the left, while they were [laying] within an open space thereof. That was from the signs of Allah. He whom Allah guides is the [rightly] guided, but he whom He leaves astray - never will you find for him a protecting guide. <> Kuma kanã ganin rãnã idan ta fito tanã karkata daga kõgonsu wajen dãma kuma idan ta fãɗi tanã gurgura su wajen hagu, kuma su, sunã a cikin wani fili daga gare shi. Wannan abu yanã daga ãyõyin Allah. Wanda Allah Ya shiryar, to shĩ ne mai shiryuwa, kuma wanda Allah Ya ɓatar to bã zã ka sãmar masa wani majiɓinci mai shiryarwa ba. = [18:17] Kuma (da kuna wurin) za ku ga rana idan ta fito tana karkata daga kogonsu ta hannun dama, kuma idan ta fadi, tana haska masu daga hagu, da suke ta yin barcinsu a fili. Wannan abu yana daya daga cikin mu’ijizan ALLAH.* Wanda ALLAH Ya shiriyar shi ne shiriyayyen gaskiya, kuma wanda Ya batar, to, ba za ka samar masa wani majibinci mai shiryarwa ba. --Qur'an 18:17
    And you would think them awake, while they were asleep. And We turned them to the right and to the left, while their dog stretched his forelegs at the entrance. If you had looked at them, you would have turned from them in flight and been filled by them with terror. <> Kuma kanã zaton su farkakku ne, alhãli kuwa sũ mãsu barci ne. Munã jũya su wajen dãma da wajen hagu, kuma karensu yanã shimfiɗe da zirã'õ'in ƙafãfuwansa ga farfãjiya (ta kõgon). Dã ka lẽka (a kan) su (dã) lalle ne, ka jũya daga gare su a guje kuma (dã) lalle ne ka cika da tsõro daga gare su. = [18:18] Kuma (da kun kasance wurin) za ku zaton su farkakku ne, alhali kuwa su masu barci ne. muna juya su zuwa dama da ta hagu, kuma karensu yana miqan qafafuwansa a tsakaninsu. Da kun kallesu, da za ku sheqa a guje daga gare su, saboda tsoro. --Qur'an 18:18
    And similarly, We awakened them that they might question one another. Said a speaker from among them, "How long have you remained [here]?" They said, "We have remained a day or part of a day." They said, "Your Lord is most knowing of how long you remained. So send one of you with this silver coin of yours to the city and let him look to which is the best of food and bring you provision from it and let him be cautious. And let no one be aware of you. <> Kuma kamar wannan ne Muka tãyar da su, dõmin su tambayi jũna a tsakãninsu. Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Mẽne ne lõkacin da kuka zauna?" suka ce: "Mun zauna yini ɗaya ko sãshen yini." Suka ce: "Ubangijinku ne Mafi sani ga abin da kuka zauna. To, ku aika da ɗayanku, game da azurfarku wannan, zuwa ga birnin. Sai ya dũba wanne ne mafi tsarki ga abin dafãwa, sai ya zo muku da abinci daga gare shi. Kuma sai ya yi da hankali, kada ya sanar da ku ga wani mutum." = [18:19] Kuma ta haka ne muka tayar da su, domin su tambayi junansu,“Wani mai magana daga cikinsu ya ce, “Tun yaushe ne kuke nan?” Suka ce,“Muna nan na yini daya ko sahen yini,” suka amsa. “Ubangijinku ne mafi sani ga tun yaushe muke nan, to, bari mu aiki dayanku da wannan azurfarku zuwa cikin gari. Bari ya je ya nemo mana mafi tsakin abin dafawa, ya saya mana. Amma sai ya yi a hankali, kada ya ja hankali game da ku ga wani. --Qur'an 18:19
    Indeed, if they come to know of you, they will stone you or return you to their religion. And never would you succeed, then - ever." <> "Lalle ne sũ idan sun kãmã ku, zã su jẽfẽ ku, kõ kuwa su mayar da ku a cikin addininsu kuma bã zã ku sãmi babban rabo, ba, a sa'an nan har abada." = [18:20] “Idan suka kama ku, za su jefe ku, ko kuwa su tilasta ku, domin ku koma zuwa addininsu, sa’annan ba za ku ci nasara ba.” --Qur'an 18:20
    And similarly, We caused them to be found that they [who found them] would know that the promise of Allah is truth and that of the Hour there is no doubt. [That was] when they disputed among themselves about their affair and [then] said, "Construct over them a structure. Their Lord is most knowing about them." Said those who prevailed in the matter, "We will surely take [for ourselves] over them a masjid." <> Kuma kamar wancan ne, Muka nũna su (gare su) dõmin su san lalle wa'adin Allah gaskiya ne, kuma lalle ne Sa'a bãbu shakka a cikinta. A lõkacin da suke jãyayyar al'amarinsu a tsakãninsu sai suka ce: "Ku gina wani gini a kansu, Ubangijinsu ne Mafi sani game da su." Waɗanda suka rinjãya a kan al'amarinsu suka ce: "Lalle mu riƙi masãllãci a kansu." = [18:21] Sai muka yi sanadin a gano su, domin mu bari kowa ya san cewa wa’adin ALLAH gaskiya ne, kuma mu cire shakka game da qarshen duniya --Qur'an 18:21
    They will say there were three, the fourth of them being their dog; and they will say there were five, the sixth of them being their dog - guessing at the unseen; and they will say there were seven, and the eighth of them was their dog. Say, [O Muhammad], "My Lord is most knowing of their number. None knows them except a few. So do not argue about them except with an obvious argument and do not inquire about them among [the speculators] from anyone." <> Zã su ce: "Uku ne da na huɗunsu karensu."Kuma sunã cẽwa, "Biyar ne da na shidansu karensu," a kan jĩfa a cikin duhu. Kuma sunã cẽwa, "Bakwaine da na takwas ɗinsu karensu."Ka ce: "Ubangijĩna ne Mafi saniga ƙidãyarsu, bãbu wanda ya san su fãce kaɗan."Kada ka yi jãyayya bayyananna. Kuma kada ka yi fatawa ga kõwa daga gare su a cikin al'amarinsu. = [18:22] Wadansu za su ce, “Da su uku ne; karensu ne na hudunsu,” alhali kuwa wasu za su ce su, “Biyar ne; karensu ne na shida,” da suke ta cinci. Wadansu suna cewa, “Bakwai ne, da na takwas dinsu karensu. Ka ce,“Ubangijina ne mafi sani adadin lambarsu.” Kadan ne kawai suka san adadin lambarsu daidai. Saboda haka, kada ka yi jayayya da su; ku yarda da su kawai. Kuma kada ka yi fatawa ga kowa game da wannan. --Qur'an 18:22
    And never say of anything, "Indeed, I will do that tomorrow," <> Kuma kada lalle ka ce ga wani abu, "Lalle ni, mai aikatãwa ne ga wancan a gõbe." = [18:23] Kada ka ce za ka aikata wani abu nan gaba, --Qur'an 18:23
    Except [when adding], "If Allah wills." And remember your Lord when you forget [it] and say, "Perhaps my Lord will guide me to what is nearer than this to right conduct." <> Fãce idan Allah Ya so. Kuma ka ambaci Ubangijinka idan ka manta, kuma ka ce: "¦ammãni ga Ubangijĩna, Ya shiryar da ni ga abin da yake shi ne mafi kusa ga wannan na shiriya." = [18:24] ba tare da ka ce, “Insha ALLAH.” Idan ka manta baka ce hakan ba, sai ka tuna Ubangijinka nan da nan kuma ka ce, “Ubangijina Ya shiriyar da ni domin in gyara wani sa’a.” --Qur'an 18:24
    And they remained in their cave for three hundred years and exceeded by nine. <> Kuma suka zauna a cikin kõgonsu shẽkaru ɗarĩ uku kuma suka daɗa tara. = [18:25] Sun tsaya a cikin kogonsu shekaru dari uku, aka qara da tara.* --Qur'an 18:25
    Say, "Allah is most knowing of how long they remained. He has [knowledge of] the unseen [aspects] of the heavens and the earth. How Seeing is He and how Hearing! They have not besides Him any protector, and He shares not His legislation with anyone." <> Ka ce: "Allah ne Mafi sani ga abin da suka zauna. Shĩ ne da (sanin) gaibin sammai da ƙasa. Mũne ne ya yi ganinSa da jinSa! Bã su da wani majiɓinci baicinSa kuma bã Ya tãrayya da kõwa a cikin hukuncinsa." = [18:26] Ka ce, “ALLAH ne mafi sanin adadin lokutan da suka tsaya a wurin.” Shi ne da sanin gaibun sammai da qasa. Da izininSa za ka iya gani; da izininSa za ka iya ji. Babu wani majibinci baicinSa, kuma ba Ya tarayya da kowa a cikin hukuncinSa. --Qur'an 18:26
    And recite, [O Muhammad], what has been revealed to you of the Book of your Lord. There is no changer of His words, and never will you find in other than Him a refuge. <> Ka karanta abin da aka yi wahayi zuwa gare ka, na littãfin Ubangijinka. Bãbu mai musanyãwa ga kalmõminSa kuma bã zã kã sãmi wata madõgara ba daga waninsa. = [18:27] Ka karanta abin da aka yi wahayi zuwa gare ka na littafin Ubangijinka. Babu wani abu mai kau da kalmominSa, kuma ba za ka sami wata madogara ba baicin shi. --Qur'an 18:27
    And keep yourself patient [by being] with those who call upon their Lord in the morning and the evening, seeking His countenance. And let not your eyes pass beyond them, desiring adornments of the worldly life, and do not obey one whose heart We have made heedless of Our remembrance and who follows his desire and whose affair is ever [in] neglect. <> Ka haƙurtar da ranka tãre da waɗanda ke kiran Ubangijinsu, sãfe da maraice, sunã nufin yardarSa. Kuma kada idãnunka su jũya daga barinsu, kanã nufin ƙawar rãyuwar dũniya. Kuma kada ka biwanda Muka shagaltar da zũciyarsa daga hukuncinMu, kuma ya bi son zuciyarsa, alhãli kuwa al'amarinsa ya kasance yin ɓarna. = [18:28] Ka yi haqurin tilasta kanka da zama tare da wadanda ke kiran Ubangijinsu safe da maraice, suna neman yardanSa. Kuma kada idanunka su juya ga barinsu, kana neman wuqiniyan rayuwar duniya. Kumar kada ka bi wanda muka shagaltar da zuciyarsa daga hukuncinMu; wanda yake bin son zuciyarsa, kuma wanda ya rikitad da al’amarinsa. --Qur'an 18:28
    And say, "The truth is from your Lord, so whoever wills - let him believe; and whoever wills - let him disbelieve." Indeed, We have prepared for the wrongdoers a fire whose walls will surround them. And if they call for relief, they will be relieved with water like murky oil, which scalds [their] faces. Wretched is the drink, and evil is the resting place. <> Kuma ka ce: "Gaskiya daga Ubangijinku take." Sabõda haka wanda ya so, to, ya yi ĩmãni, kuma wanda ya so, to, ya kãfirta. Lalle ne Mũ, Mun yi tattali dõmin azzãlumai wata wuta wadda shãmakunta, sun ƙẽwaye da su. Kuma idan sun nẽmi taimako sai a taimake su da wani ruwa kamar dabzar mai, yanã sõye fuskõki. Tir da abin shansu, kuma wutar ta yi mũnin zama mahũtarsu. = [18:29] Ka zayyana: “Wannan shi ne gaskiya daga Ubangijinku,” saboda haka wanda ya so, to, ya yi imani, kuma wanda ya so, to, ya kafirta. Mun shirya wa azzalumai wuta, wanda shamakunta zai kewaye su. Idan suka yi kukan neman taimako, za ba su wani abu na ruwa-ruwa, kamar dabzar mai na acid mai qona fuskoki. Tir da abin shansu na zullumi! Kuma tir da makoman zullumi! --Qur'an 18:29
    Indeed, those who have believed and done righteous deeds - indeed, We will not allow to be lost the reward of any who did well in deeds. <> Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai lalle ne Mũ bã Mu tõzartar da lãdar wanda ya kyautata aiki. = [18:30] Amma ga wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyuka na qwarai, ba rasa baiwa lada ga wadanda suka kyautata ayyukan qwarai. --Qur'an 18:30
    Those will have gardens of perpetual residence; beneath them rivers will flow. They will be adorned therein with bracelets of gold and will wear green garments of fine silk and brocade, reclining therein on adorned couches. Excellent is the reward, and good is the resting place. <> Waɗannan sunã da gidãjen Aljannar zama, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, anã sanya musu ƙawa, a cikinsu, daga mundãye na zinariya, kuma sunã tufantar waɗansu tũfãfi kõre, na alharĩni raƙĩƙi da alharini mai kauri sunã kishingiɗe a cikinsu, a kan, karagu. Mãdalla da sakamakonsu. Kuma Aljanna ta kyautatu da zama wurin hutãwa. = [18:31] Wadannan sun cancanci gidajen Aljannah wurin da qoramu suke gudana daga qarqashinsu. Za qawaita masu a wurin da suluwan zinariya, kuma za su sa tufafin siliki da karammiski masu ruwan kore, kuma za su huta a kan karagu suna holewa. Sambarika da sakamakonsu; kuma sambarika da qasaitacen wurin mahuta! --Qur'an 18:31
    And present to them an example of two men: We granted to one of them two gardens of grapevines, and We bordered them with palm trees and placed between them [fields of] crops. <> Kuma ka buga musu misãli da waɗansu maza biyu. Mun sanya wa ɗayansu gõnaki biyu na inabõbi, kuma Muka kẽwayesu da itãcen dabĩnai, kuma Muka sanya shũka a tsakãninsu (sũ gõnakin). = [18:32] Kuma ka buga masu misali da wasu mutane biyu: mun baiwa dayansu gonaki biyu na inabobi, kuma muka kewaye su da itacen dabinai, kuma muka sanya wasu shuke-shuke a tsakanin gonakin. --Qur'an 18:32
    Each of the two gardens produced its fruit and did not fall short thereof in anything. And We caused to gush forth within them a river. <> Kõwace gõna daga biyun, tã bãyar da amfãninta, kuma ba ta yi zãluncin kõme ba daga gare shi. Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙoramu a tsakãninsu. = [18:33] Kowace gona daga biyun, ta bayar da amfaninta a cikin lokaci, da kariminci, saboda mun sanya qorami ta gudana a tsakaninsu. --Qur'an 18:33
    And he had fruit, so he said to his companion while he was conversing with him, "I am greater than you in wealth and mightier in [numbers of] men." <> Kuma ɗan ĩtãce ya kasance gare shi. Sai ya ce wa abõkinsa, alhali kuwa yanã muhãwara da shi, "Nĩ ne mafĩfĩci daga gare ka a wajen dũkiya, kuma mafi izza a wajen jama'a." = [18:34] Wata rana, bayan girbi, ya yi alfaharin gayawa abokinsa cewa: “Ni ne mafificin wadata a kanka, kuma ni ne mafi mutunci daga wurin mutane.” --Qur'an 18:34
    And he entered his garden while he was unjust to himself. He said, "I do not think that this will perish - ever. <> Kuma ya shiga gõnarsa, alhãli yanã mai zãlunci ga kansa, ya ce: "Bã ni zaton wannan zã ta halaka har abada." = [18:35] Kuma sa’ad da ya shiga gonansa, sai ya zalunci kansa da cewa, “Ba ni zaton wannan zai taba qarewa ba. --Qur'an 18:35
    And I do not think the Hour will occur. And even if I should be brought back to my Lord, I will surely find better than this as a return." <> "Kuma bã ni zaton sa'a mai tsayuwa ce, kuma lalle ne, idan an mayar da ni zuwa ga Ubangijiĩna, to, lalle ne, zan sãmi abin da yake mafi alhẽri daga gare ta ya zama makõma." = [18:36] Kumar ba ni zaton sa’a (Alqiyamah) mai tsayuwa ce. Kuma ko da an mayar da ni ne ga Ubangijina, zan ( koma samun dabara) in mallaki abin da ya dara wannan a can.” --Qur'an 18:36
    His companion said to him while he was conversing with him, "Have you disbelieved in He who created you from dust and then from a sperm-drop and then proportioned you [as] a man? <> Abõkinsa ya ce masa, alhãli kuwa yanã muhãwara da shi, "Ashe kã kãfirta da wanda Ya halitta ka daga turɓaya, sa'an nan daga ɗigon maniyi, sa, an nan Ya daidaita ka, ka zama mutum?" = [18:37] Abokinsa ya ce masa, sa’ad da yake muhawara da shi, “Shin ka kafirta ne ga wanda Ya halitta ka daga turbaya, sa’annan daga digon maniyi, sa’annan Ya daidaita ka, ka zama mutum? --Qur'an 18:37
    But as for me, He is Allah, my Lord, and I do not associate with my Lord anyone. <> "Amma ni, shĩ ne Allah Ubangijina, kuma bã zan tãra kõwa da Ubangijina ba" = [18:38] “Ni kam, ALLAH ne Ubangijina, kuma ba zan yi shirka da kowane abu ba da Ubangijina. --Qur'an 18:38
    And why did you, when you entered your garden, not say, 'What Allah willed [has occurred]; there is no power except in Allah '? Although you see me less than you in wealth and children, <> "Kuma don me, a lõkacin da ka shiga gõnarka, ka, ce, 'Abin da Allah ya so (shi ke tabbata) bãbu wani ƙarfi fãce game da Allah.' Idan ka gan ni, ni ne mafi ƙaranci daga gare ka a wajen dũkiya da ɗiya." = [18:39] “Sa’ad da ka shiga gonarka, da ya kamata ka ce, Ma Sha ALLAH. La Quwwata Illa Bi’ALLAH. Za ka ga cewa ni ba ni da dukiya da yara kamar ka. --Qur'an 18:39
    It may be that my Lord will give me [something] better than your garden and will send upon it a calamity from the sky, and it will become a smooth, dusty ground, <> "To, akwai fãtan Ubangijĩna Ya ba ni abin da yake mafi alhẽri daga gõnarka, kuma ya aika azãba a kanta (ita gõnarka) daga sama, sai ta wãyi gari turɓãya mai santsi." = [18:40] To, amma Ubangijina zai iya ya bani gona fiye da naka. Kuma zai iya ya aika da goguwar iskan hadari daga sama wanda za ta shafe gonarka, ta bar shi bakarare. --Qur'an 18:40
    Or its water will become sunken [into the earth], so you would never be able to seek it." <> "Kõ kuma ruwanta ya wãyi gari faƙaƙƙe, sabõda haka, bã zã ka iya nẽmo shi ba dõminta." = [18:41] “Ko kuma, ruwanta ta nutsad da zurufi, inda ba za ka iya kaiwa ba.” --Qur'an 18:41
    And his fruits were encompassed [by ruin], so he began to turn his hands about [in dismay] over what he had spent on it, while it had collapsed upon its trellises, and said, "Oh, I wish I had not associated with my Lord anyone." <> Kuma aka halaka dukan 'ya'yan itãcensa, sai ya wãyi gari yanã jũyar da tãfunansa biyu, sabõda abin da ya kashe a cikinta, alhãli kuwa ita tanã kwance a kan rassanta, kuma yanã cẽwa, "Kaitõna, dã dai ban tãra wani da Ubangijina ba!" = [18:42] Kuma haka ne, an shafe gonarsa, sai ya yai gari yana nadama, yana koke saboda abin da ya kashe a banza a cikinta, sa’ad da aka bari gonansa bakarare. Daga qarshe sai ya ce, “Kaitona, da ma ban yi shirkanta gona na da Ubangijina ba.” --Qur'an 18:42
    And there was for him no company to aid him other than Allah, nor could he defend himself. <> Kuma wata jama'a ba ta kasance a gare shi ba, waɗanda ke taimakon sa, baicin Allah, kuma bai kasance mai taimakon kansa ba. = [18:43] kuma da babu wani mai tallafa masa ga ALLAH, kuma ba wanda ya iya ya basi wani taimako. --Qur'an 18:43
    There the authority is [completely] for Allah, the Truth. He is best in reward and best in outcome. <> A can taimako da jiɓinta ga Allah yake. Shĩ ne kawai Gaskiya, shĩ ne Mafĩfĩci ga lãda kumaMafĩ fĩci ga ãƙiba. = [18:44] Dalili shi ne taimakon gaskiya da jibinta daga ALLAH yake; Yana ba da mafificin lada, kuma da mafificin aqiba. --Qur'an 18:44
    And present to them the example of the life of this world, [its being] like rain which We send down from the sky, and the vegetation of the earth mingles with it and [then] it becomes dry remnants, scattered by the winds. And Allah is ever, over all things, Perfect in Ability. <> Ka buga musu misãlin rãyuwar dũniya, kamar ruwane wanda Muka saukar da shi daga sama sa'an nan tsirin ƙasa ya garwaya da shi, sa'an nan ya wãyi gari dudduga, iska tanã shiƙar sa. Kuma Allah Ya kasance Mai yawan ĩkon yi ne a kan dukan kõme. = [18:45] Ka buga masu misalin rayuwar duniya, kamar ruwa ne wanda muka sakar daga sama domin ya fito da tsiro a qasa, sa’annan suka koma baro wanda tafi da hurin iska. Kuma ALLAH Ya kasance mai yawan ikon yi a kan dukan kome. --Qur'an 18:45
    Wealth and children are [but] adornment of the worldly life. But the enduring good deeds are better to your Lord for reward and better for [one's] hope. <> Dũkiya da ɗiya, sũ ne ƙawar rãyuwar dũniya, kuma ayyuka mãsu wanzuwa na ƙwarai sun fi zama alhẽri a wurin Ubangijinka ga lãda kuma sun fi alhẽri ga bũri. = [18:46] Kudi da yara su ne qawar rayuwar duniya, amma ayyuka na qwarai sun fi zama alheri daga Ubangijinka ga lada, kuma mafi alheri ga buri. --Qur'an 18:46
    And [warn of] the Day when We will remove the mountains and you will see the earth prominent, and We will gather them and not leave behind from them anyone. <> Kuma a rãnar da Muke tafiyar da duwãtsu, kuma ka ga ƙasa bayyane, kuma Mu tãra su har ba Mu bar kõwa ba daga gare su. = [18:47] Akwai ranar da za mu shafe tsaunika, kuma za ku ga qasa bakarareya. Sa,annan mu tara su duka, ba za mu bar ko dayansu ba. --Qur'an 18:47
    And they will be presented before your Lord in rows, [and He will say], "You have certainly come to Us just as We created you the first time. But you claimed that We would never make for you an appointment." <> Kuma a gittã su ga Ubangijinka sunã sahu guda, (Mu ce musu), "Lalle ne haƙĩƙa kun zo Mana, kamar yadda Muka halitta ku a farkon lõkaci. Ã'a, kun riya cẽwa bã zã Mu sanya mukuwani lõkacin haɗuwa ba." = [18:48] Za gufanad da su a gaban Ubangijinka a cikin sahu guda. Kun zo mana yasu-yasunku, kamar yadda muka halicce ku farkon lokaci. Lalle ne, da abin da kuka riya cewan ba zai taba faruwa ba kenan. --Qur'an 18:48
    And the record [of deeds] will be placed [open], and you will see the criminals fearful of that within it, and they will say, "Oh, woe to us! What is this book that leaves nothing small or great except that it has enumerated it?" And they will find what they did present [before them]. And your Lord does injustice to no one. <> Kuma aka aza littãfin ayyuka, sai ka ga mãsu laifi sunã mãsu jin tsõro daga abin da ke cikinsa, kuma sunã cẽwa "Kaitonmu! Mẽne ne ga wannan littãfi, bã ya barin ƙarama, kuma bã ya barin babba, fãce yã ƙididdige ta?" Kuma suka sãmi abin da suka aikata halarce. Kuma Ubangijinka bã Ya zãluntar kõwa. = [18:49] Za gabatar da littafin ayyuka, kuma za ka ga mai laifi yana fargaban abin da ya qumsa. Za su ce, “Kaitonmu. Yahya aka yi wannan littafin bai bar kome ba, qarami ko babba, ba tare da ya qidaya shi ba?” Za su tarad da kome da suka aikata an gabatar da shi. Ubangijinka ba ya zaluntar kowa. --Qur'an 18:49
    And [mention] when We said to the angels, "Prostrate to Adam," and they prostrated, except for Iblees. He was of the jinn and departed from the command of his Lord. Then will you take him and his descendants as allies other than Me while they are enemies to you? Wretched it is for the wrongdoers as an exchange. <> Kuma a lõkacin da Muka ce wa malãiku, "Ku yi sujada ga Ãdamu." Sai suka yi sujada fãce Iblĩsa, yã kasance daga aljannu sai ya yi fãsiƙanci ga barin umurnin Ubangijinsa, To fa, ashe, kunã riƙon sa, shi da zũriyarsa, su zama majiɓinta baicin Ni, alhãli kuwa su maƙiya ne a gare ku? Tir da ya zama musanya ga azzãlumai. = [18:50] Sa’ad da muka ce wa mala’iku, “Ku yi sujadah ga Adam.” Sai suka yi sujadah, ban da Iblis. Sai ya kasance aljanni, saboda ya finjire bin umurnin Ubangijinsa --Qur'an 18:50
    I did not make them witness to the creation of the heavens and the earth or to the creation of themselves, and I would not have taken the misguiders as assistants. <> Ban shaida musu halittar sammai da ƙasa ba, kuma ban (shaida musu) halittar rãyukansu ba kuma ban kasance mai riƙon mãsu ɓatarwa (da wani) su zama mataimaka ba. = [18:51] Ban bari su shaida game da halittar sammai da qasa ba, ko kuma halittar kansu. Kuma bana bari mugu ya yi aiki a cikin masarautaNa. --Qur'an 18:51
    And [warn of] the Day when He will say, "Call 'My partners' whom you claimed," and they will invoke them, but they will not respond to them. And We will put between them [a valley of] destruction. <> Kuma da rãnar da Allah Yake cẽwa, "Ku kirãyi abõkan tarayyãTa, waɗanda kuka riya." Sai su kirãye su, sai bã zã su karɓa musu ba, kuma Mu sanya Maubiƙa (Mahalaka) a tsakãninsu, = [18:52] Akwai ranar da zai ce, “Ku kira abokan tarayyaTa, wanda kuke riya su ne baicin Ni,” za su kira su, amma ba za su amsa masu ba. Shamakin‘maubiqa’ zai rabe su daga junansu. --Qur'an 18:52
    And the criminals will see the Fire and will be certain that they are to fall therein. And they will not find from it a way elsewhere. <> Kuma mãsu laifi suka ga wutã suka tabbata lalle ne, sũ mãsu, auka mata ne, kuma ba su sãmi majũya ba daga gare ta. = [18:53] Masu laifi za su ga wuta, kuma za su tabbatar cewa za su fada ne a cikinta. Ba za su sami kubucewa ba daga gare ta. --Qur'an 18:53
    And We have certainly diversified in this Qur'an for the people from every [kind of] example; but man has ever been, most of anything, [prone to] dispute. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun jujjũya, a cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane irin misãli ga mutãne (dõmin su gãne, su bi sharĩ'a), kuma mutum yã kasance mafi yawan abu ga jidãli. = [18:54] Mun bada kowane irin misali a cikin wannan Alqurani ga mutane, amma mutum ya kasance halitta mafi yawan jayayya. --Qur'an 18:54
    And nothing has prevented the people from believing when guidance came to them and from asking forgiveness of their Lord except that there [must] befall them the [accustomed] precedent of the former peoples or that the punishment should come [directly] before them. <> Kuma bãbu abin da ya hana mutãne su yi ĩmãni a lõkacinda shiriya ta zo musu, kuma su nẽmi gãfara daga Ubangijinsu, fãce hanyar farko ta je musu kõ kuma azãba ta jẽ musu nau'i-nau'i. = [18:55] Babu abin da ya hana mutum daga yin imani, sa’ad da shiriya ya je masu, kuma daga neman gafara daga Ubangijinsu, sai dai cewa sun nemi su ga (irin mu’ijizai) kamar na mutanen da, ko kuwa su ga azaba tukuna. --Qur'an 18:55
    And We send not the messengers except as bringers of good tidings and warners. And those who disbelieve dispute by [using] falsehood to [attempt to] invalidate thereby the truth and have taken My verses, and that of which they are warned, in ridicule. <> Kuma ba Mu aika Manzanni ba fãce sunã mãsu bãyar da bushãra kuma mãsu gargaɗi, kuma waɗanda suka kãfirta sunã jidãli da ƙarya dõmin su ɓãta gaskiya da ita, kuma suka riƙi ãyõyiNa da abin da aka yi musu gargaɗi da shi abin izgili. = [18:56] Mu kan aika da manzanni ne kawai domin su ba da bushara, kuma da gargadi. Wadanda suka kafirta suna jayayya da qarya daomin su kayar da gaskiya, kuma suna daukan ayoyiNa da gargadiNa a banza. --Qur'an 18:56
    And who is more unjust than one who is reminded of the verses of his Lord but turns away from them and forgets what his hands have put forth? Indeed, We have placed over their hearts coverings, lest they understand it, and in their ears deafness. And if you invite them to guidance - they will never be guided, then - ever. <> Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda aka tunãtar game da ãyõyin Ubangijinsa, sai ya bijire daga barinsu, kuma ya manta abin da hannãyensa suka gabãtar? Lalle ne Mũ, Mun sanya abũbuwan rufi a kan zukãtansu dõmin kada su fahimcẽ shi, kuma a cikin kunnuwansu (Mun sanya) wani nauyi, kuma idan kã kĩrayẽ su zuwa ga shiriya, to, bã zã su shiryu ba, a sa'an nan, har abada. = [18:57] Wane ne mafi zalunci da wanda aka tunatar game da ayoyin Ubangijinsa, sai ya bijire da barinsu, ba tare da sanin abin da suke yi ba. Saboda haka, muka sanya abubuwan rufi a kan zukatansu domin kada su fahimce shi (Alqur’ani), kuma a cikin kunnuwansu. Ta haka ne, duk kome da za ka yi, ka shiriyad da su, ba za su shiryu ba, har abada. --Qur'an 18:57
    And your Lord is the Forgiving, full of mercy. If He were to impose blame upon them for what they earned, He would have hastened for them the punishment. Rather, for them is an appointment from which they will never find an escape. <> Kuma Ubangijinka Mai gãfara ne, Ma'abũcin rahama. Dã Yanã kãma su sabõda abin da suka sanã'anta, lalle ne, dã Ya gaggauta azãba a gare su. Ã'a, sunã da lõkacin alkawari, (wanda) bã zã su sãmi wata makõma ba, baicinSa. = [18:58] Duk da haka, Ubangijinka mai gafara ne, mai yawan rahamah. Idan da zai kama su saboda abin da suka aikata, da ya shafe su nan da nan. Amma a maimakon haka, sai Ya jinkirta masu sai qayyadadden lokaci, sa’an da aka qaddarta; sa’annan ba za su kubuta ba. --Qur'an 18:58
    And those cities - We destroyed them when they wronged, and We made for their destruction an appointed time. <> Kuma waɗancan alƙaryu Mun halaka su, a lõkacin da suka yi zãlunci, kuma Muka sanya lõkacin alkawarin, ga halaka su. = [18:59] Alqaryu masu yawa wanda muka halaka saboda zaluncinsu, sai da muka sanya qayyadadden lokaci na halaka su. --Qur'an 18:59
    And [mention] when Moses said to his servant, "I will not cease [traveling] until I reach the junction of the two seas or continue for a long period." <> Kuma a lõkacin da Mũsã ya ce wa yãronsa, "Bã zan gushe ba sai na isa mahaɗar tẽku biyu, kõ in shũɗe da tafiya shekara da shẽkaru." = [18:60] A lokacin da Musa ya ce wa bawansa, “Ba zan huta ba sai na isa wurin da rafi biyu suka game, kome nisan shi.” --Qur'an 18:60
    But when they reached the junction between them, they forgot their fish, and it took its course into the sea, slipping away. <> To, a lõkacin da suka isa mahaɗar tsakãninsu sai suka manta kĩfinsu, sai ya kãma tafarkinsa a cikin tẽku kamar bĩga. = [18:61] A lokacin da suka kai dam da wurin da magamar tsakaninsu, sai suka manta da kifinsu, sai ta kama hanyan komawa zuwa rafi, a labe. --Qur'an 18:61
    So when they had passed beyond it, [Moses] said to his boy, "Bring us our morning meal. We have certainly suffered in this, our journey, [much] fatigue." <> To, a lõkacin da suka wuce ya ce wa yãronsa, "Ka kãwo mana kãlãcinmu. Lalle ne haƙĩƙa mun haɗu da wahala daga tafiyarmu wannan." = [18:62] A lokacin da suka wuce wurin, sai ya ce wa bawansa, “Ka kawo mana kalacinmu. Tafiyar nan ta gajiyar da mu matuqa.” --Qur'an 18:62
    He said, "Did you see when we retired to the rock? Indeed, I forgot [there] the fish. And none made me forget it except Satan - that I should mention it. And it took its course into the sea amazingly". <> (Yãron) ya ce: "Kã gani! A lõkacin da muka tattara zuwa ga falalen nan to, lalle nĩ, na manta kĩfin, kuma bãbu abin da yamantar da nĩ shi, fãce Shaiɗan, dõmin kada in tuna shi, sai ya kama tafarkinsa a cikin tẽku, da mãmãki!" = [18:63] Ya ce, “Ka tuna sa’ad da muka zauna kusa da wani dutse bayan can? Ban ba da hankali ga kifin ba. Iblis ne ya sa na manta da ita, sai ta kama hanyanta komawa zuwa ruwa, ta garibi.” --Qur'an 18:63
    [Moses] said, "That is what we were seeking." So they returned, following their footprints. <> Ya ce: "Wancan ne abin da muka kasance munã biɗã." Sai suka kõma a kan gurãbunsu, sunã bĩbiya. = [18:64] (Musa) ya ce, “To, daidan wurin da muke nema kenan.” Sai suka koma bin sawun qafansu baya. --Qur'an 18:64
    And they found a servant from among Our servants to whom we had given mercy from us and had taught him from Us a [certain] knowledge. <> Sai suka sãmi wani bãwa daga bãyinMu, Mun bã shi wata rahama daga wurinMu, kuma Mun sanar da shi wani ilmi daga gunMu. = [18:65] Sai suka sami daya daga bayinMu, wanda muka bashi wata rahamah daga wurinMu, kuma muka koya masa wani ilmi daga wurinMu. --Qur'an 18:65
    Moses said to him, "May I follow you on [the condition] that you teach me from what you have been taught of sound judgement?" <> Mũsã ya ce masa, "Ko in bĩ ka a kan ka sanar da ni daga abin da aka sanar da kai na shiriya?" = [18:66] Musa ya ce masa, “Ko in bi ka, domin ka koya mani daga abin da aka koya maka na shiriya?” --Qur'an 18:66
    He said, "Indeed, with me you will never be able to have patience. <> Ya ce: "Lalle ne kai bã zã ka iya yin haƙuri tãre da nĩ, ba." = [18:67] Ya ce, “Ba za ka iya yin juriya tare da ni ba.” --Qur'an 18:67
    And how can you have patience for what you do not encompass in knowledge?" <> "Kuma yãya zã ka yi haƙuri a kan abin da ba ka kẽwayeda shi ba ga jarrabãwa?" = [18:68] Ta yaya za ka iya juriya ga abin da baka sani ba?” --Qur'an 18:68
    [Moses] said, "You will find me, if Allah wills, patient, and I will not disobey you in [any] order." <> Ya ce: "Za ka sãme ni, in Allah Yã so mai haƙuri kuma bã zan sãɓa maka ba ga wani umurni." = [18:69] Ya ce, “Insha ALLAH, za ka ga cewa ni mai haquri ne. Ba zan qi bin umurnin da ka yi mani ba.” --Qur'an 18:69
    He said, "Then if you follow me, do not ask me about anything until I make to you about it mention." <> Ya ce: "To idan ka bĩ ni to kada ka tambaye ni daga kõme sai na lãbarta maka ambato daga gare shi." = [18:70] Ya ce, “Idan ka bi ni, to, kada ka tambaye ni game da kome, sai idan na ga daman in gaya maka game da shi.” --Qur'an 18:70
    So they set out, until when they had embarked on the ship, al-Khidh r tore it open. [Moses] said, "Have you torn it open to drown its people? You have certainly done a grave thing." <> Sai suka tafi har a lõkacin da suka hau a cikin jirgi, ya hũje shi, ya ce, "Kã hũje shi dõmin ya nutsar da mutãnensa? Lalle ne, haƙĩƙa, kã zo da wani babban abu!" = [18:71] Sai suka tafi. A lokacin da suka hau cikin girgi, sai ya huda ta. Ya ce, “Ka huda ta ne domin ta nutsar da mutanenta? Lalle, ka aikata mumunan abu.” --Qur'an 18:71
    [Al-Khidh r] said, "Did I not say that with me you would never be able to have patience?" <> Ya ce: "Ashe ban ce, lalle kai, bã za ka iya yin haƙuri tãre da ni ba?" = [18:72] Ya ce, “Ashe, ban ce ba za ka iya juriya tare da ni ba?” --Qur'an 18:72
    [Moses] said, "Do not blame me for what I forgot and do not cover me in my matter with difficulty." <> Ya ce: "Kada ka kãma ni da abin da na manta kuma kada ka kallafa mini tsanani ga al'amarĩna." = [18:73] Ya ce, “Ka yi haquri. Kada ka hukunta ni bisa ga mantuwana; kuma kada ka kallafa mini tsanani ga al’amarina.” --Qur'an 18:73
    So they set out, until when they met a boy, al-Khidh r killed him. [Moses] said, "Have you killed a pure soul for other than [having killed] a soul? You have certainly done a deplorable thing." <> Sai suka tafi, har suka haɗu da wani yãro, sai ya kashe shi. Ya ce: "Ashe kã kashe rai tsarkakakke, bã da wani rai ba? Lalle ne haƙĩƙa ka zo da wani abu na ƙyãma." = [18:74] Sai suka tafi. Da suka hadu da yaro qarami, sai ya kashe shi. Ya ce,“Don me ka kashe irin wannan mutum mara laifi? Lalle, ka aikata qazamin aiki.” --Qur'an 18:74
    [Al-Khidh r] said, "Did I not tell you that with me you would never be able to have patience?" <> Ya ce: "Shin, ban ce maka ba, lalle ne kai bã zã ka iya yin haƙuri tãre da nĩ ba?" = [18:75] Ya ce, “Ashe ban gaya maka ba cewa ba za ka iya juriya tare da ni ba?” --Qur'an 18:75
    [Moses] said, "If I should ask you about anything after this, then do not keep me as a companion. You have obtained from me an excuse." <> Ya ce: "Idan na tambaye ka daga wani abu a bãyanta, to, kada ka abũce ni. Lalle ne, kã isa ga iyakar uzuri daga gare ni." = [18:76] Ya ce, “Idan na sake tambayar ka wani abu kuma, to, kada ka bar ni tare da kai. Ka ga yawan uzuri daga gare ni.” --Qur'an 18:76
    So they set out, until when they came to the people of a town, they asked its people for food, but they refused to offer them hospitality. And they found therein a wall about to collapse, so al-Khidh r restored it. [Moses] said, "If you wished, you could have taken for it a payment." <> Sai suka tafi, har a lõkacin da suka je wa mutãnen wata alƙarya, suka nẽmi mutãnenta da su bã su abinci, sai suka ƙi su yi musu liyãfa. Sai suka sãmi wani bango a cikinta yanã nufin ya karye, sai (Halliru) ya tãyar da shi mĩƙe. (Mũsã) ya ce: "Dã kã so, lalle ne dã kã karɓi ijãra a kansa." = [18:77] Sai suka tafi. Har da suka kai ga mutanen wata alqarya, suka nemi mtanenta da su basu abinci, sai suka qi su yi masu liyafa. Jim kadan, sai suka ga wani bango a cikinta ta kusan ta fadi, sai ya gyara ta. Ya ce, “Ai da ka nemi su biya ka ujiri a kansa!” --Qur'an 18:77
    [Al-Khidh r] said, "This is parting between me and you. I will inform you of the interpretation of that about which you could not have patience. <> Ya ce: "Wannan shi ne rabuwar tsakanina da tsakaninka. Zã ni gaya maka fassarar abin da ba ka iya yin haƙuri ba a kansa." = [18:78] Ya ce, “Yanzu ya wajabta mu rabu. Amma zan byyana maka kome da baka iya yin juriya ba a kansa. --Qur'an 18:78
    As for the ship, it belonged to poor people working at sea. So I intended to cause defect in it as there was after them a king who seized every [good] ship by force. <> "Amma Jirgin, to, ya zama na waɗansu matalauta ne sunã aiki a cikin tẽku, sai na yi niyyar in aibanta shi, alhãli kuwa wani sarki ya kasance a gaba gare su, yanã karɓẽwar kõwane jirgi (lãfiyayye) da ƙwãce. = [18:79] Amma bisa ga girgin, ta kasance na wadansu matalauta ne masu kamun kifi, kuma na so in aibanta ta. Saboda akwai wani sarki a gaba zuwa gare su, wanda yana qwatar kowane girgi, da qarfi. --Qur'an 18:79
    And as for the boy, his parents were believers, and we feared that he would overburden them by transgression and disbelief. <> "Kuma amma yaron, to, uwãyensa sun kasance mũminai, to, sai muka ji tsõron ya kallafa musu kangara da kãfirci." = [18:80] “Kuma yaron, iyayensa muminai ne na qwarai, kuma mun ga cewa zai kallafa masu da bijirewa da kafirci.* --Qur'an 18:80
    So we intended that their Lord should substitute for them one better than him in purity and nearer to mercy. <> "Sai muka yi nufin Ubangijinsu Ya musanya musu mafi alhẽri daga gare shi ga tsarkakuwa, kuma mafi kusantar tausayi." = [18:81] “Sai muka yi nufin cewa Ubangijinsu, Ya musanya masu wani da mafi alheri da shi; wanda ya fi kirki da tausayi. --Qur'an 18:81
    And as for the wall, it belonged to two orphan boys in the city, and there was beneath it a treasure for them, and their father had been righteous. So your Lord intended that they reach maturity and extract their treasure, as a mercy from your Lord. And I did it not of my own accord. That is the interpretation of that about which you could not have patience." <> "Kuma amma bangon, to, yã kasance na waɗansu yãra biyu ne, marãyu a cikin birnin, kuma akwai wata taska tãsu a ƙarƙashinsa, kuma ubansu ya kasance sahĩhin mutum ne, dõmin haka Ubangijinka Ya yi nufin su isa iyãkar ƙarfinsu, kuma sũ, su fitar da taskarsu, sabõda rahama ne daga Ubangijinka. Kuma ban yi shi ba daga umurnĩna. Wancan shĩ ne fassarar abin da ba ka iya yin haƙuri ba a kansa." = [18:82] Amma dangane da banon, ya kasance na wadansu yara biyu ne, marayu a cikin birnin. Qarqashinta, akwai dukiya wanda na su ne. kuma babansu ya kasance salihin mutum ne, saboda haka Ubangijinka Ya nufe su, su yi girma kuma su kai ga iyakn qarfinsu, sa’annan, su cire dukiyarsu. Saboda wannan rahamah ne daga Ubangijinka. Ban aikata kowanensu bisa son ra’ayin kaina ba. To, bayanin abin da baka iya ka haqura a kansa ba kenan.” --Qur'an 18:82
    And they ask you, [O Muhammad], about Dhul-Qarnayn. Say, "I will recite to you about him a report." <> Kuma suna tambayar ka daga zulƙarnaini, ka ce: "Zan karanta muku ambato daga gare shi." = [18:83] Kuma suna tambayar ka game da Zul-Qarnain. Ka ce, “Zan karanta maku wasu labarunsa.” --Qur'an 18:83
    Indeed We established him upon the earth, and We gave him to everything a way. <> Lalle ne Mũ Mun bã shi mulki a cikin ƙasa kuma Muka bã shi daga kõwane abu, hanya (zuwa ga murãdinsa). = [18:84] Lalle ne, Mun ba shi mulki a cikin qasa, kuma muka ba shi hanyoyin abubuwa dabam dabam. --Qur'an 18:84
    So he followed a way <> Sai ya bi hanya. = [18:85] Sa’annan, ya bi hanya guda. --Qur'an 18:85
    Until, when he reached the setting of the sun, he found it [as if] setting in a spring of dark mud, and he found near it a people. Allah said, "O Dhul-Qarnayn, either you punish [them] or else adopt among them [a way of] goodness." <> Har a lõkacin da ya isa ga mafãɗar rãnã, kuma ya sãme ta tanã ɓacẽwa a cikin wani ruwa mai baƙar lãkã, kuma ya sãmi waɗansu mutãne a wurinta. Muka ce: "Yã Zulƙarnaini imma dai ka azabtar kuma imma ka riƙi kyautatãwa a cikinsu." = [18:86] Sa’ad da ya kai nesa da yamma, sai ya ga rana na fadiwa a cikin qaton teku, kuma ya sami mutane daga wurin. Muka ce, “Ya Zul-Qqrnain, (ka yi mulki yadda kake so); imma za ka azabtar, ko ka kyautata zuwa gare su.” --Qur'an 18:86
    He said, "As for one who wrongs, we will punish him. Then he will be returned to his Lord, and He will punish him with a terrible punishment. <> Ya ce: "Amma wanda ya yi zãlunci, to zã mu azabta shi, sa'an nan a mayar da shi zuwa ga Ubangijinsa, sai kuma Ya yi masa azãba, azãba abar ƙyãma." = [18:87] Ya ce, “Bisa ga wadanda suke zalunci, za mu azabta su, sa’annan, idan suka koma ga Ubangijinsu, sai kuma Ya qara masu azaba mai muni. --Qur'an 18:87
    But as for one who believes and does righteousness, he will have a reward of Paradise, and we will speak to him from our command with ease." <> "Kuma amma wanda ya yi ĩmãni kuma ya aikata aikin ƙwarai to, zã mu yi sakamako a gare shi (watau kyauta) mai kyau, kuma zã mu gaya masa sauƙi daga umurninmu." = [18:88] “Amma ga wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyuka na qwarai, suna samun kyakkyawan lada; za mu kyautata masu.” --Qur'an 18:88
    Then he followed a way <> Sa'an nan kuma ya bi hanya. = [18:89] Sa’annan kuma ya bi wani hanya. --Qur'an 18:89
    Until, when he came to the rising of the sun, he found it rising on a people for whom We had not made against it any shield. <> Har a lõkacin da ya isa ga mafitar rãnã, ya sãme ta tanã fita a kan waɗansu mutãne (waɗanda) ba Mu sanya musu wata kãriya ba daga barinta. = [18:90] Sa’ad da ya kai nesa da gabas, ya ga inda rana ke fitowa a kan mutane wanda ba su da abin da za su tsare kansu daga ita. --Qur'an 18:90
    Thus. And We had encompassed [all] that he had in knowledge. <> Kamar wancan alhãli kuwa haƙĩƙa, Mun kẽwaye da jarrabãwa ga abin da ke gunsa. = [18:91] Tun asali, mu ne mafi sani ga kome da ya gani. --Qur'an 18:91
    Then he followed a way <> Sa'an nan kuma ya bi hanya. = [18:92] Sa’annan ya bi wani hanya. --Qur'an 18:92
    Until, when he reached [a pass] between two mountains, he found beside them a people who could hardly understand [his] speech. <> Har a lõkacin da ya isa a tsakãnin duwãtsu biyu, ya sãmi waɗansu mutãne daga gabãninsu. Ba su yi kusa su fahimci magana ba. = [18:93] Sa’ad da ya kai ga kwari tsakanin kawarai, sai ya tarad da mutanen da daqyar ake fahimtar yarensu. --Qur'an 18:93
    They said, "O Dhul-Qarnayn, indeed Gog and Magog are [great] corrupters in the land. So may we assign for you an expenditure that you might make between us and them a barrier?" <> Suka ce: "Yã Zulƙarnaini! Lalle ne Yãjũja da Majũja mãsu ɓarna ne a cikin ƙasa. To, ko zã mu Sanya harãji sabõda kai, a kan ka sanya wani danni a tsakãninmu da tsakãninsu?" = [18:94] Suka ce, “Ya Zul-Qarnain, lalle ne, Ya’juj da Ma’juj masu barna ne a cikin qasa. To, ko mu biya ka domin ka sanya shingen danni tsakaninmu da su?” --Qur'an 18:94
    He said, "That in which my Lord has established me is better [than what you offer], but assist me with strength; I will make between you and them a dam. <> Ya ce: "Abin da Ubangijĩna Ya mallaka mini, a cikinsa yã fi zama alhẽri. Sai ku taimakeni da ƙarfi, in sanya babbar katanga a tsakãninku da tsakãninsu." = [18:95] Ya ce, “Ubangijina Ya mallaka mini karimci mai yawa. Idan kuka bani hadin kai, zan gina datsiya tsakaninku da su. --Qur'an 18:95
    Bring me sheets of iron" - until, when he had leveled [them] between the two mountain walls, he said, "Blow [with bellows]," until when he had made it [like] fire, he said, "Bring me, that I may pour over it molten copper." <> "Ku kãwo mini guntãyen baƙin ƙarfe". (Suka kai masa) har a lõkacin da ya daidaita a tsakãnin duwãtsun biyu (ya sanya wutã a cikin ƙarfen) ya ce: "Ku hũra (da zugãzugai)." Har a lõkacin da ya mayar da shi wutã, ya ce: "Ku kãwo mini gaci (narkakke) in zuba a kansa." = [18:96] “Ku kawo mini qarafuna masu yawa.” Sa’alin da ya cike gurbin tsakanin kawaran biyu, ya ce, “Ku hura.” Da ya yi jan zafi, ya ce, “Ku taya ni kwarara kwalta a kansa.” --Qur'an 18:96
    So Gog and Magog were unable to pass over it, nor were they able [to effect] in it any penetration. <> Dõmin haka bã za su iya hawansa ba, kuma bã zã su iya hujẽwa gare shi ba. = [18:97] Ta haka ne, ba za su iya hawanta ba, kuma ba za su iya huda ramuka a cikinta ba. --Qur'an 18:97
    [Dhul-Qarnayn] said, "This is a mercy from my Lord; but when the promise of my Lord comes, He will make it level, and ever is the promise of my Lord true." <> Ya ce: "Wannan wata rahama ce daga Ubangijĩna. Sai idan wa'adin Ubangijĩna ya zo, ya mayar da shi niƙaƙƙe. Kuma wa'adin Ubangijĩna ya kasance tabbatacce." = [18:98] Ya ce, “Wannan wata rahamah ce daga Ubangijina. Sai idan wa’adin Ubangijina ya zo, zai sa datsiyan ta marmashe. Kuma wa’adin Ubangijina gaskiya ne.” --Qur'an 18:98
    And We will leave them that day surging over each other, and [then] the Horn will be blown, and We will assemble them in [one] assembly. <> Kuma Muka bar sãshensu a rãnar nan, yanã garwaya a cikin sãshe, kuma aka bũsa a cikin ƙaho sai muka tãra su, tãrãwa. = [18:99] A lokacin ne, za mu bari su yi shigan farmakin juna, sa’anna a busa qaho, kuma mu tara su duka gaba daya. --Qur'an 18:99
    And We will present Hell that Day to the Disbelievers, on display - <> Kuma Muka gitta Jahannama, a rãnar nan ga kãfirai gittãwa. = [18:100] Kuma mu gabatar da Jahannama, a ranar, ga kafirai gittawa. --Qur'an 18:100
    Those whose eyes had been within a cover [removed] from My remembrance, and they were not able to hear. <> Waɗanda idãnunsu suka kasance a cikin rufi daga tunã Ni, kuma sun kasance bã su iya saurãrãwa. = [18:101] Wadanda idanunsu suka kasance a rufe da tunawa da Ni. Kuma sun kasance ba su iya saurarawa ba. --Qur'an 18:101
    Then do those who disbelieve think that they can take My servants instead of Me as allies? Indeed, We have prepared Hell for the disbelievers as a lodging. <> Shin fa, waɗanda suka kãfirta sun yi zaton (daidai ne) su riƙi waɗansu bãyĩNa, majiɓinta baiciNa? Lalle ne, Mun yi tattalin Jahannama ta zama liyãfa ga kãfirai. = [18:102] Shin, wadanda suka kafirta suna zoton za su tsira ne da sanya bayiNa majibinta baici Na? lalle, mun shirya Jahannama ta zama liyafa ga kafirai wurin zama na dindin. --Qur'an 18:102
    Say, [O Muhammad], "Shall we [believers] inform you of the greatest losers as to [their] deeds? <> Ka ce: "Kõ mu gaya muku game da mafĩfita hasãra ga ayyuka?" = [18:103] Ka ce, Ko in gaya maku game da mafifita hasara ga ayyuka?” --Qur'an 18:103
    [They are] those whose effort is lost in worldly life, while they think that they are doing well in work." <> "Waɗanda aikinsu ya ɓace a cikin rãyuwar dũniya, alhãli kuwa sunã zaton lalle ne sũ, sunã kyautata, (abin da suke gani) aikin ƙwarai?" = [18:104] Su ne wadanda ayyukansu a cikin wannan rayuwar duniya suke kan bata, amma suna zaton suna kyautata ayyukan qwarai.” --Qur'an 18:104
    Those are the ones who disbelieve in the verses of their Lord and in [their] meeting Him, so their deeds have become worthless; and We will not assign to them on the Day of Resurrection any importance. <> Waɗancan ne waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Ubangijinsu, da kuma haɗuwa da Shi, sai ayyukansu suka ɓãci. Sabõda haka bã zã Mu tsayar musu da awo ba a Rãnar ¡iyãma. = [18:105] Wadannan su ne suka kafirta da ayoyin Ubangijinsu kuma da haduwa da Shi. Saboda haka, ayyukansu duk abanza ne; kuma a Ranar Alqiyamah, awonsu ba za su yi nauyi ba. --Qur'an 18:105
    That is their recompense - Hell - for what they denied and [because] they took My signs and My messengers in ridicule. <> Wancan ne sakamakonsu shĩ ne Jahannama, sabõda kãfircinsu, kuma suka riƙi ãyõyiNa da ManzanniNa abin izgili. = [18:106] Sakamakonsu shi ne Jahannama, saboda kafircinsu, kuma saboda sun mayar da ayoyiNa da manzanniNa abin yin ba’a. --Qur'an 18:106
    Indeed, those who have believed and done righteous deeds - they will have the Gardens of Paradise as a lodging, <> Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, Aljannar Firdausi ta kasance ita ce liyãfa a gare su. = [18:107] Amma ga wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyuka na qwarai, to, sun cancanci Aljannar Firdausi ta zama liyafa a gare su. --Qur'an 18:107
    Wherein they abide eternally. They will not desire from it any transfer. <> Suna madawwama a cikinta, bã su nẽman makarkata daga barinta. = [18:108] Suna madauwama a cikinta; ba za su bukaci wani musayanta ba. --Qur'an 18:108
    Say, "If the sea were ink for [writing] the words of my Lord, the sea would be exhausted before the words of my Lord were exhausted, even if We brought the like of it as a supplement." <> Ka ce: "Dã tẽku ta kasance tawada ga (rubũtun) kalmõmin Ubangijina, lalle ne dã tẽkun ta ƙãre a gabãnin kalmõmin Ubangijĩna su ƙãre, kuma kõda mun jẽ da misãlinsa dõmin ƙari." = [18:109] Ka ce, “Idan da ruwan teku tawada ce ga (abin rubutun) kalmomin Ubangijina, da tekun ta qare, kalmomin Ubangijina basu qare ba, kuma ko da mun ninka misalin tawadar ne.” --Qur'an 18:109
    Say, "I am only a man like you, to whom has been revealed that your god is one God. So whoever would hope for the meeting with his Lord - let him do righteous work and not associate in the worship of his Lord anyone." <> Ka ce: "Nĩ, mutum ne kawai kamarku, anã yin wahayi zuwa gare ni cewa: Lalle ne, Abin bautawarku, Abin bautawa Guda ne, sabõda haka wanda ya kasance yanã fãtan haɗuwa da Ubangijinsa, to, sai ya yi aiki na ƙwarai. Kuma kada ya haɗa kõwa ga bauta wa Ubangijinsa." = [18:110] Ka ce, “Ni mutum ne kawai kamarku, ana yin wahayi zuwa gare ni cewa: Abin bautawarku Daya ne. Saboda haka, wadanda suke fatan su hadu da Ubangijinsu, to sai su aikata ayyuka na qwarai, kuma kada su hada kowa ga bauta ga UbangijinSa.” --Qur'an 18:110
    Kaf, Ha, Ya, 'Ayn, Sad. <> K̃.H. Y.I. Ṣ̃. = --Qur'an 19:1
    [This is] a mention of the mercy of your Lord to His servant Zechariah <> Ambaton rahamar Ubangijinka ne ga BawanSa Zakariyya. = --Qur'an 19:2
    When he called to his Lord a private supplication. <> A lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, kira ɓõyayye. = --Qur'an 19:3
    He said, "My Lord, indeed my bones have weakened, and my head has filled with white, and never have I been in my supplication to You, my Lord, unhappy. <> Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, ƙashi na daga gare ni ya yi rauni, kuma kaina ya kunnu da furfura, kuma ban kasance marashin arziki ba game da kiranKa, yã Ubangiji!" = --Qur'an 19:4
    And indeed, I fear the successors after me, and my wife has been barren, so give me from Yourself an heir <> "Kuma lalle nĩ, na ji tsõron dangi a bãyãna, kuma mãtãta ta kasance bakarãriya! Sai ka bã ni wani mataimaki daga wajenKa." = --Qur'an 19:5
    Who will inherit me and inherit from the family of Jacob. And make him, my Lord, pleasing [to You]." <> "Ya gãjẽ ni, kuma ya yi gãdo daga gidan Yãƙũba. Kuma Ka sanya shi yardajje, yã Ubangiji!" = --Qur'an 19:6
    [He was told], "O Zechariah, indeed We give you good tidings of a boy whose name will be John. We have not assigned to any before [this] name." <> (Allah Ya karɓa) "Yã zakariyya! Lalle ne Mũ, Munã yi maka bushãra da wani yãro, sunansa Yahaya. Ba Mu sanya masa wani takwara ba a gabãni." = --Qur'an 19:7
    He said, "My Lord, how will I have a boy when my wife has been barren and I have reached extreme old age?" <> Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Yãya wani yãro zai kasance a gare ni, alhãli kuwa mãtãta ta kasance bakarãriya, kuma gã shi nã kai ga matuƙa ta tsũfa?" = --Qur'an 19:8
    [An angel] said, "Thus [it will be]; your Lord says, 'It is easy for Me, for I created you before, while you were nothing.' " <> Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinka Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne, kuma haƙĩƙa Na halitta ka a gabãnin haka, alhãli ba ka kasance kõme ba." = --Qur'an 19:9
    [Zechariah] said, "My Lord, make for me a sign." He said, "Your sign is that you will not speak to the people for three nights, [being] sound." <> Ya ce: "Yã Ubangijina! Ka sanya mini alãma." Ya ce: "Alamarka ita ce ka kãsa yi wa mutãne magana a darũruwa uku daidai." = --Qur'an 19:10
    So he came out to his people from the prayer chamber and signaled to them to exalt [Allah] in the morning and afternoon. <> Sai ya fita a kan mutãnensa daga masallãci, sa'an nan ya yi ishãra zuwa gare su da cẽwa, "Ku yi tasbĩhi sãfe da yamma." = --Qur'an 19:11
    [Allah] said, "O John, take the Scripture with determination." And We gave him judgement [while yet] a boy <> Yã Yahaya! Ka kãma littãfi da ƙarfi. Kuma Muka bã shi hukunci yanã yãro. = --Qur'an 19:12
    And affection from Us and purity, and he was fearing of Allah <> Kuma (Muka sanya shi) abin girmamãwa daga gunMu, kuma mai albarka, kuma ya kasance mai ɗã'ã da taƙawa. = --Qur'an 19:13
    And dutiful to his parents, and he was not a disobedient tyrant. <> Kuma mai biyayya ga mahaifansa biyu, kuma bai kasance mai girman kai mai sãɓo ba. = --Qur'an 19:14
    And peace be upon him the day he was born and the day he dies and the day he is raised alive. <> Kuma aminci ya tabbata a gare shi a rãnar da aka haife shi da rãnar da yake mutuwa da rãnar da ake tãyar da shi yanã mai rai. = --Qur'an 19:15
    And mention, [O Muhammad], in the Book [the story of] Mary, when she withdrew from her family to a place toward the east. <> Kuma ka ambaci Maryamu a cikin Littãfi, a lõkacin da ta tsallake daga mutãnenta a wani wuri, a gẽfen gabas. = --Qur'an 19:16
    And she took, in seclusion from them, a screen. Then We sent to her Our Angel, and he represented himself to her as a well-proportioned man. <> Sa'an nan ta riƙi wani shãmaki daga barinsu. Sai Muka aika rũhinMu zuwa gare ta. Sai ya bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaci. = --Qur'an 19:17
    She said, "Indeed, I seek refuge in the Most Merciful from you, [so leave me], if you should be fearing of Allah." <> Ta ce: "Lalle nĩ inã nẽman tsari ga Mai, rahama daga gare ka, idan ka kasance mai tsaron addini!" = --Qur'an 19:18
    He said, "I am only the messenger of your Lord to give you [news of] a pure boy." <> Ya ce: "Abin sani kawai, ni Manzon Ubangijinki ne dõmin in bãyar da wani yãro tsarkakke gare ki." = --Qur'an 19:19
    She said, "How can I have a boy while no man has touched me and I have not been unchaste?" <> Ta ce: "A inã yãro zai kasance a gare ni alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba, kuma ban kasance kãruwa ba?" = --Qur'an 19:20
    He said, "Thus [it will be]; your Lord says, 'It is easy for Me, and We will make him a sign to the people and a mercy from Us. And it is a matter [already] decreed.' " <> Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinki Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne. Kuma dõmin Mu sanya shi wata alãma ga mutãne, kuma wata rahama ce daga gare Mu.' Kuma abin yã kasance wani al'amari hukuntacce." = --Qur'an 19:21
    So she conceived him, and she withdrew with him to a remote place. <> Sai ta yi cikinsa, sai ta tsallake da shi ga wani wuri mai nĩsa. = --Qur'an 19:22
    And the pains of childbirth drove her to the trunk of a palm tree. She said, "Oh, I wish I had died before this and was in oblivion, forgotten." <> Sai nãƙuda ta kai ta zuwa ga wani kututturen dabĩniya, ta ce "Kaitona, dã dai na mutu a gabãnin wannan kuma na kasance wani abu wulakantacce wanda aka manta!" = --Qur'an 19:23
    But he called her from below her, "Do not grieve; your Lord has provided beneath you a stream. <> Sai (yãron da ta haifa) ya kira ta daga ƙarƙashinta, "Kada ki yi baƙin ciki! Haƙĩƙa Ubangijinki Ya sanya wani marmaro a ƙarƙashinki. = --Qur'an 19:24
    And shake toward you the trunk of the palm tree; it will drop upon you ripe, fresh dates. <> "Kuma ki girgiza zuwa gare ki game da kututturen dabĩnon ya zuba a kanki yanã 'ya'yan dabĩno, ruɗabi nunannu." = --Qur'an 19:25
    So eat and drink and be contented. And if you see from among humanity anyone, say, 'Indeed, I have vowed to the Most Merciful abstention, so I will not speak today to [any] man.' " <> "Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idãnunki. To, idan kin ga wani aya daga mutãne, sai ki ce, 'Lalle nĩ, na yi alwãshin azumi dõmin Mai rahama sabõda haka bã zan yi wa wani mutum magana ba." = --Qur'an 19:26
    Then she brought him to her people, carrying him. They said, "O Mary, you have certainly done a thing unprecedented. <> Sai ta je wa mutãnenta tanã auke da shi. Suka ce: "Yã Maryamu! Lalle ne, haƙĩƙa kin zo da wani abu mai girma! = --Qur'an 19:27
    O sister of Aaron, your father was not a man of evil, nor was your mother unchaste." <> "Yã 'yar'uwar Hãrũna! Ubanki bai kasance mutumin alfãsha ba, kuma uwarki ba ta kasance kãruwa ba." = --Qur'an 19:28
    So she pointed to him. They said, "How can we speak to one who is in the cradle a child?" <> Sai ta yi ishãra zuwa gare shi, suka ce: "Yãya zã mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfiar tsumma yanã jãrĩri?" = --Qur'an 19:29
    [Jesus] said, "Indeed, I am the servant of Allah. He has given me the Scripture and made me a prophet. <> Ya ce: "Lalle ne, nĩ bãwan Allah ne Allah Yã bã ni Littãfi kuma Ya sanya ni Annabi." = --Qur'an 19:30
    And He has made me blessed wherever I am and has enjoined upon me prayer and zakah as long as I remain alive <> "Kuma Yã sanya ni mai albarka a inda duk na kasance kuma Ya umurce ni da yin salla da zakka matuƙar inã da rai." = --Qur'an 19:31
    And [made me] dutiful to my mother, and He has not made me a wretched tyrant. <> "Kuma mai biyayya ga uwãta, kuma bai sanya ni mai kaushin zũciya ba marashin alhẽri." = --Qur'an 19:32
    And peace is on me the day I was born and the day I will die and the day I am raised alive." <> "Kuma aminci ya tabbata a gare ni a rãnar da aka haife ni da rãnar da nake mutũwa da rãnar da ake tãyar da ni inã mai rai." = --Qur'an 19:33
    That is Jesus, the son of Mary - the word of truth about which they are in dispute. <> Wancan ne Ĩsã ɗan Maryamu, maganar gaskiya wadda suke shakka a cikinta. = --Qur'an 19:34
    It is not [befitting] for Allah to take a son; exalted is He! When He decrees an affair, He only says to it, "Be," and it is. <> Bã ya kasancẽwa ga Allah Ya riƙi wani ɗã. Tsarki ya tabbata a gare shi! Idan Yã hukunta wani al'amari sai kawai Ya ce masa, "Kasance." Sai ya dinga kasan cẽwa. = --Qur'an 19:35
    [Jesus said], "And indeed, Allah is my Lord and your Lord, so worship Him. That is a straight path." <> "Kuma lalle Allah ne Ubangijina kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan shi ne tafarki madaidaici." = --Qur'an 19:36
    Then the factions differed [concerning Jesus] from among them, so woe to those who disbelieved - from the scene of a tremendous Day. <> Sai ƙungiyõyin suka sãɓã wa jũna a tsakãninsu. To, bõne ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga halartar yini mai girma. = --Qur'an 19:37
    How [clearly] they will hear and see the Day they come to Us, but the wrongdoers today are in clear error. <> Mẽne ne ya yi jinsu, kuma mẽne ne ya yi ganinsu a rãnar da suke zo Mana! Amma azzãlumai sunã a cikin ɓata bayyananna. = --Qur'an 19:38
    And warn them, [O Muhammad], of the Day of Regret, when the matter will be concluded; and [yet], they are in [a state of] heedlessness, and they do not believe. <> Kuma ka yi musu gargaɗi da rãnar nadãma a lõkacin da aka hukunta al'amari alhãli kuwa sunã a cikin ɓãta, kuma sũ bã su yin ĩmãni. = --Qur'an 19:39
    Indeed, it is We who will inherit the earth and whoever is on it, and to Us they will be returned. <> Lalle ne Mũ, Mũ ne ke gãdon ƙasa da wanda yake a kanta, kuma zuwa gare Mu ake mayar da su. = --Qur'an 19:40
    And mention in the Book [the story of] Abraham. Indeed, he was a man of truth and a prophet. <> Kuma ambaci Ibrãhĩm a cikin Littafi. Lalle shi ya kasance mai yawan gaskatãwa, Annabi. = --Qur'an 19:41
    [Mention] when he said to his father, "O my father, why do you worship that which does not hear and does not see and will not benefit you at all? <> A lõkacin da ya ce wa ubansa, "Yã bãba! Don me kake bauta wa abin da bã ya ji, kuma bã ya ga ni, kuma ba ya wadãtar da kõme daga barinka?" = --Qur'an 19:42
    O my father, indeed there has come to me of knowledge that which has not come to you, so follow me; I will guide you to an even path. <> "Yã bãba! Lalle ni, haƙĩƙa abin da bai je maka ba na ilmi ya zo mini, sabõda haka ka bĩ ni in shiryar da kai wani tafarki madaidaici." = --Qur'an 19:43
    O my father, do not worship Satan. Indeed Satan has ever been, to the Most Merciful, disobedient. <> "Yã bãba! Kada ka bauta wa Shaiɗan. Lalle Shaiɗan ya kasance mai saɓãwa ga Mai rahama." = --Qur'an 19:44
    O my father, indeed I fear that there will touch you a punishment from the Most Merciful so you would be to Satan a companion [in Hellfire]." <> "Yã bãba! Lalle ne ni inã tsõron wata azãba daga Mai rahama ta shãfe ka, har ka zama masõyi ga Shaiɗan." = --Qur'an 19:45
    [His father] said, "Have you no desire for my gods, O Abraham? If you do not desist, I will surely stone you, so avoid me a prolonged time." <> Ya ce: "Ashe, mai gudu ne kai daga gumãkãna? Yã Ibrãĩm! Lalle ne, idan ba ka hanu ba, haƙĩ ƙa, zan jẽfe ka. Kuma ka ƙaurace mini tun kanã mai mutunci." = --Qur'an 19:46
    [Abraham] said, "Peace will be upon you. I will ask forgiveness for you of my Lord. Indeed, He is ever gracious to me. <> Ya ce: "Aminci ya tabbata a gare ka! zan nẽmi Ubangijina Ya gãfarta maka. Lalle Shi Ya kasance Mai girmamãwa gare ni." = --Qur'an 19:47
    And I will leave you and those you invoke other than Allah and will invoke my Lord. I expect that I will not be in invocation to my Lord unhappy." <> "Kuma inã nĩsantar ku da abin da kuke kira, baicin Allah kuma inã kiran Ubangijina, tsammãnin kada in zama marashin arziki game da kiran Ubangijina." = --Qur'an 19:48
    So when he had left them and those they worshipped other than Allah, We gave him Isaac and Jacob, and each [of them] We made a prophet. <> To, sa'ad da ya nĩsance su da abin da suke bautãwa baicin Allah, Muka bã shi Is'hãƙa da Ya'aƙuba alhãli kuwa kõwanensu Mun mayar da shi Annabi. = --Qur'an 19:49
    And We gave them of Our mercy, and we made for them a reputation of high honor. <> Kuma Muka yi musu kyauta daga RahamarMu, kuma Muka sanya musu harshen gaskiya maɗaukaki. = --Qur'an 19:50
    And mention in the Book, Moses. Indeed, he was chosen, and he was a messenger and a prophet. <> Kuma ka ambaci Mũsã a cikin Littãfi. Lalle ne shi, yã kasance zãɓaɓɓe, kuma yã kasance Manzo, Annabi. = --Qur'an 19:51
    And We called him from the side of the mount at [his] right and brought him near, confiding [to him]. <> Kuma Muka kira shi daga gẽfen dũtse na dãma kuma Muka kusanta shi yanã abõkin gãnãwa. = --Qur'an 19:52
    And We gave him out of Our mercy his brother Aaron as a prophet. <> Kuma Muka yi masa kyauta daga RahamarMu da ɗan'uwansa Hãrũna, ya zama Annabi. = --Qur'an 19:53
    And mention in the Book, Ishmael. Indeed, he was true to his promise, and he was a messenger and a prophet. <> Kuma ka ambaci Ismã'ila a cikin Littãfi. Lalle shi, yã kasance mai gaskiyar alkawari, kuma yã kasance Manzo, Annabi. = --Qur'an 19:54
    And he used to enjoin on his people prayer and zakah and was to his Lord pleasing. <> Kuma yã kasance yanã umurnin mutãnens da salla da zakka. Kuma yã kasance yardajje a wurin Ubangijinsa. = --Qur'an 19:55
    And mention in the Book, Idrees. Indeed, he was a man of truth and a prophet. <> Kuma ka ambaci Idrĩsa a cikin Littãfi. Lalle shi, ya kasance mai yawan gaskatãwa, Annabi. = --Qur'an 19:56
    And We raised him to a high station. <> Muka ɗaukaka shi a wuri maɗaukaki. = --Qur'an 19:57
    Those were the ones upon whom Allah bestowed favor from among the prophets of the descendants of Adam and of those We carried [in the ship] with Noah, and of the descendants of Abraham and Israel, and of those whom We guided and chose. When the verses of the Most Merciful were recited to them, they fell in prostration and weeping. <> Waɗancan sũ ne waɗanda Allah Ya yi wa ni'ima daga Annabãwa daga zurriyar Ãdamu, kuma daga waɗanda muka ɗauka tãre da Nũhu, kuma daga zurriyar Ibrãhĩm da Isrã'ila, kuma daga waɗanda Muka shiryar kuma Muka zãɓe su. Idan anã karãtun ãyõyin Mai rahama a kansu, sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma mãsu kũka. = --Qur'an 19:58
    But there came after them successors who neglected prayer and pursued desires; so they are going to meet evil - <> Sai waɗansu 'yan bãya suka maye a bãyansu suka tõzarta salla, kuma suka bi sha'awõwinsu. To, da sannu zã su hau da wani sharri. = --Qur'an 19:59
    Except those who repent, believe and do righteousness; for those will enter Paradise and will not be wronged at all. <> Fãce wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai. To, waɗannan sunã shiga Aljanna, kuma bã a zãluntar su da kõme. = --Qur'an 19:60
    [Therein are] gardens of perpetual residence which the Most Merciful has promised His servants in the unseen. Indeed, His promise has ever been coming. <> Gidãjen Aljannar zama wadda Mai rahama ya yi alkawarin bãyarwa ga bãyinSa (mãsu aikin ĩmãni) a fake. Lalle ne shĩ, alkawarin ya kasance abin riskuwa. = --Qur'an 19:61
    They will not hear therein any ill speech - only [greetings of] peace - and they will have their provision therein, morning and afternoon. <> Bã su jin yasassar magana a cikinta, fãce sallama. Kuma sunã da abinci, a cikinta, sãfe da maraice. = --Qur'an 19:62
    That is Paradise, which We give as inheritance to those of Our servants who were fearing of Allah. <> Wancan Aljannar ce wadda Muke gãdar da wanda ya kasance mai aiki da taƙawa daga bãyiNa. = --Qur'an 19:63
    [Gabriel said], "And we [angels] descend not except by the order of your Lord. To Him belongs that before us and that behind us and what is in between. And never is your Lord forgetful - <> (Sunã mãsu cẽwa) "Kuma bã mu sauka Fãce da umuruin Ubangijinka (Muhammad). Shĩ ne da mulkin abin da ke a gaba gare mu da abin da ke a bãyanmu da abin da ke a tsakãnin wannan." Kuma (Ubangijinka bai kasance wanda ake mantãwa ba. = --Qur'an 19:64
    Lord of the heavens and the earth and whatever is between them - so worship Him and have patience for His worship. Do you know of any similarity to Him?" <> Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu. sai ka bauta Masa, kuma ka yi haƙuri ga bautarsa. Shin kã san wani takwara a gare shi? = --Qur'an 19:65
    And the disbeliever says, "When I have died, am I going to be brought forth alive?" <> Kuma mutum yana cẽwa, "Shin idan na mutu lalle ne haƙĩ ƙa da sannu zã a fitar da ni inã mai rai?" = --Qur'an 19:66
    Does man not remember that We created him before, while he was nothing? <> Shin, kuma mutum bã zai tuna ba cẽwa lalle ne Mun halitta shi a gabãni, alhãli kuwa bai kasance kõme ba? = --Qur'an 19:67
    So by your Lord, We will surely gather them and the devils; then We will bring them to be present around Hell upon their knees. <> To, Munã rantsuwa da Ubangijinka, lalle ne, Muna tãyar da su da kuma shaianun sa'an nan, kuma lalle Muna halatar da su da kuma Shaiɗanun sa'an nan, kuma, lalle Muna halatar da su a gẽfen Jahannama sunã gurfãne. = --Qur'an 19:68
    Then We will surely extract from every sect those of them who were worst against the Most Merciful in insolence. <> Sa'an nan kuma lalle Munã fizge wanda yake mafi tsananin girman kai ga Mai rahama daga kõwace ƙungiya. = --Qur'an 19:69
    Then, surely it is We who are most knowing of those most worthy of burning therein. <> Sa'an nan kuma lalle Mũ ne Mafi sani ga waɗanda suke sũ ne mafiya cancantar ƙõnuwa da ita. = --Qur'an 19:70
    And there is none of you except he will come to it. This is upon your Lord an inevitability decreed. <> Kuma bãbu kõwa daga gare ku sai mai tuzga mata. Yã kasance wajibi ga Ubangijinka, hukuntacce. = --Qur'an 19:71
    Then We will save those who feared Allah and leave the wrongdoers within it, on their knees. <> Sa'an nan kuma Mu tsẽrar da waɗanda suka yi aiki da taƙawa, kuma Mu bar azzãlumai a cikinta gurfãne. = --Qur'an 19:72
    And when Our verses are recited to them as clear evidences, those who disbelieve say to those who believe, "Which of [our] two parties is best in position and best in association?" <> Kuma idan anã karatun ãyõyinMu, bayyanannu a kansu, sai waɗanda suka kãfirta su ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, "Wanne daga ƙungiyõyin biyu ya fi zama mafi alhẽri ga matsayi, kuma mafi kyaun majalisa?" = --Qur'an 19:73
    And how many a generation have We destroyed before them who were better in possessions and [outward] appearance? <> Kuma da yawa daga mutãnen ƙarni Muka halakar a gabãninsu sũ (waɗandaMuka halakar) in ne mafi kyaun kãyan ãki da magãnã. = --Qur'an 19:74
    Say, "Whoever is in error - let the Most Merciful extend for him an extension [in wealth and time] until, when they see that which they were promised - either punishment [in this world] or the Hour [of resurrection] - they will come to know who is worst in position and weaker in soldiers." <> Ka ce: "Wanda ya kasance a cikin ɓata sai Mai rahama Ya yalwata masa yalwatãwa, har idan sun ga abin da ake yi musu wa'adi, imma azãba kõ sã'a, to zã su sani, wane ne yake shĩ ne, mafi sharri ga wuri, kuma mafi rauni ga runduna!" = --Qur'an 19:75
    And Allah increases those who were guided, in guidance, and the enduring good deeds are better to your Lord for reward and better for recourse. <> Kuma Allah na ƙãra wa wa ɗanda suka nẽmi shiryuwa da shiriya. Kuma ayyuka mãsu wanzuwa na ƙwarai ne mafi alhẽri awurin Ubangijinka ga lãda, kuma mafi alhẽri ga makõma. = --Qur'an 19:76
    Then, have you seen he who disbelieved in Our verses and said, "I will surely be given wealth and children [in the next life]?" <> Shin, ka ga wanda ya kãfirta da ayõyinMu, kuma ya ce: "Lalle ne zã a bã ni dũkiya da ɗiya?" = --Qur'an 19:77
    Has he looked into the unseen, or has he taken from the Most Merciful a promise? <> Shin, yã tsinkãyi gaibi ne, kõ kuwa yã ɗauki wani alkawari daga Mai rahama ne? = --Qur'an 19:78
    No! We will record what he says and extend for him from the punishment extensively. <> Ã'aha! zã mu rubũta abin da yake faɗa, kuma Mu yalwata masa, daga azãba, yalwatãwa. = --Qur'an 19:79
    And We will inherit him [in] what he mentions, and he will come to Us alone. <> Kuma Mu gãde shi ga abin da yake faɗa, kuma ya zo Mana yanã shi kɗai. = --Qur'an 19:80
    And they have taken besides Allah [false] deities that they would be for them [a source of] honor. <> Kuma suka riƙi gumãka, baicin Allah, dõmin su kãsance mataimaka a gare su. = --Qur'an 19:81
    No! Those "gods" will deny their worship of them and will be against them opponents [on the Day of Judgement]. <> Ã'aha! Zã su kãfirta da ibãdarsu, kuma su kasance maƙiya a kansu. = --Qur'an 19:82
    Do you not see that We have sent the devils upon the disbelievers, inciting them to [evil] with [constant] incitement? <> Shin, ba ka gani ba cẽwa Mun saki shaiɗanu a kan kãfirai sunã shũshũta su ga zunubi shũshũtãwa? = --Qur'an 19:83
    So be not impatient over them. We only count out to them a [limited] number. <> Sabõda haka kada ka yi gaggawa a kansu, Munã yi musu ƙidãyar ajali ne kawai, ƙidãyãwa. = --Qur'an 19:84
    On the Day We will gather the righteous to the Most Merciful as a delegation <> A rãnar da Muka tãra mãsu taƙawa zuwa ga Mai rahama sunã bãƙin girma. = --Qur'an 19:85
    And will drive the criminals to Hell in thirst <> Kuma Munã kõra mãsu laifi zuwa Jahannama, gargaãwa. = --Qur'an 19:86
    None will have [power of] intercession except he who had taken from the Most Merciful a covenant. <> Ba su mal1akar cẽto fãce wanda ya riƙi alkawari a wurin Mai rahama. = --Qur'an 19:87
    And they say, "The Most Merciful has taken [for Himself] a son." <> Kuma suka ce: "Mai rahama Yã riƙi ã!" = --Qur'an 19:88
    You have done an atrocious thing. <> Lalle ne haƙĩƙa kun zo da wani abu mai girman mũni. = --Qur'an 19:89
    The heavens almost rupture therefrom and the earth splits open and the mountains collapse in devastation <> Sammai sunã kusa su tsattsage sabõda shi, kuma ƙasa ke kẽce kuma duwãtsu su faɗi sunã karyayyu. = --Qur'an 19:90
    That they attribute to the Most Merciful a son. <> Dõmin sun yi da'awar ɗã ga Mai rahama. = --Qur'an 19:91
    And it is not appropriate for the Most Merciful that He should take a son. <> Alhãli bã ya kamata ga Mai rahama ya riƙi wani ɗã. = --Qur'an 19:92
    There is no one in the heavens and earth but that he comes to the Most Merciful as a servant. <> Dukkan wanda yake a cikin sammai da ƙasa bai zama ba fãce mai jẽ wa Mai rahama ne yanã bãwã. = --Qur'an 19:93
    He has enumerated them and counted them a [full] counting. <> Lalle ne haƙĩƙa Yã lissafe su, kuma ya ƙidãye su, ƙidãya. = --Qur'an 19:94
    And all of them are coming to Him on the Day of Resurrection alone. <> Kuma dukan kõwanensu mai jẽ Masa ne a Rãnar ¡iyãma yanã shi kaɗai. = --Qur'an 19:95
    Indeed, those who have believed and done righteous deeds - the Most Merciful will appoint for them affection. <> Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, Mai rahama zai sanya musu so. = --Qur'an 19:96
    So, [O Muhammad], We have only made Qur'an easy in the Arabic language that you may give good tidings thereby to the righteous and warn thereby a hostile people. <> Sa'an nan Ibin sani kawai Mun sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) a harshenka, dõmin ka yi bushãra da shi ga mãsu aiki da taƙawa kuma ka yi gargaɗi da shi ga mutãne mãsu tsananin husũma. = --Qur'an 19:97
    And how many have We destroyed before them of generations? Do you perceive of them anyone or hear from them a sound? <> Kuma da yawa Muka halakar da mutãnen ƙarnõni a gabãninsu. Shin kanã jin mõtsin wani guda daga gare su, kõ kuwa kanã jin wata ɗuriya tãsu? = --Qur'an 19:98
    Ta, Ha. <> ¦.H. = --Qur'an 20:1
    We have not sent down to you the Qur'an that you be distressed <> Ba Mu saukar da Alƙur'ãni a gare ka dõmin ka wahala ba. = --Qur'an 20:2
    But only as a reminder for those who fear [Allah] - <> Fãce dõmin tunãtarwa ga wanda ke tsõron Allah. = --Qur'an 20:3
    A revelation from He who created the earth and highest heavens, <> (An saukar da shi) saukarwa daga wanda Ya halitta ƙasa da sammai maɗaukaka. = --Qur'an 20:4
    The Most Merciful [who is] above the Throne established. <> Mai rahama, Ya daidaita a kan Al'arshi. = --Qur'an 20:5
    To Him belongs what is in the heavens and what is on the earth and what is between them and what is under the soil. <> Abin da yake a cikin sammai nãSa ne, da abin da yake a cikin ƙasa da abin da yake a tsakãninsu da abin da ke ƙarƙashin turɓãya. = --Qur'an 20:6
    And if you speak aloud - then indeed, He knows the secret and what is [even] more hidden. <> Kuma idan ka bayyana da magana, to, lalle Shi, Yanã sanin asĩri da mafi bõyuwa. = --Qur'an 20:7
    Allah - there is no deity except Him. To Him belong the best names. <> Allah bãbu abin bautãwa fãce Shi. Yanã da sunãye mafiya kyau. = --Qur'an 20:8
    And has the story of Moses reached you? - <> Kuma shin, lãbarin Mũsã yãje maka? = --Qur'an 20:9
    When he saw a fire and said to his family, "Stay here; indeed, I have perceived a fire; perhaps I can bring you a torch or find at the fire some guidance." <> A lõkacin da ya ga wata wuta, sai ya ce wa iyãlinsa, "Ku dãkata. Lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wuta tsammãnĩna in zo mukuda makãmashi daga gare ta, kõ kuwa in sãmi wata shiriya a kan wutar." = --Qur'an 20:10
    And when he came to it, he was called, "O Moses, <> Sa'an nan a lõkacin da ya je mata, aka kira shi, "Ya Mũsã!" = --Qur'an 20:11
    Indeed, I am your Lord, so remove your sandals. Indeed, you are in the sacred valley of Tuwa. <> "Lalle ne, Nĩ ne Ubangijnka, sai ka ɗẽbe takalmanka Lalle ne kanã a rãfin nan abin tsarkakẽwa, ¦uwa." = --Qur'an 20:12
    And I have chosen you, so listen to what is revealed [to you]. <> "Kuma Nĩ Nã zãɓe ka. Sai ka saurãra ga abin da ake yin wahayi." = --Qur'an 20:13
    Indeed, I am Allah. There is no deity except Me, so worship Me and establish prayer for My remembrance. <> "Lalle, Nĩ Ni ne Allah. Bãbu abin bautawa fãce Ni. Sai ka bauta Mini, kuma ka tsayar da salla dõmin tuna Ni." = --Qur'an 20:14
    Indeed, the Hour is coming - I almost conceal it - so that every soul may be recompensed according to that for which it strives. <> "Lalle ne Sa'a mai zuwa ce, lnã kusa da In ɓõye ta dõmin a sãka wa dukan rai da abin da yake aikatãwa." = --Qur'an 20:15
    So do not let one avert you from it who does not believe in it and follows his desire, for you [then] would perish. <> "Sabõda haka, kada wanda bã ya yin ĩmãni da ita kumaya bi son zuciyarsa, ya taushe ka daga gare ta har ka halaka." = --Qur'an 20:16
    And what is that in your right hand, O Moses?" <> "Kuma wãce ce waccan ga dãmanka yã Mũsa!" = --Qur'an 20:17
    He said, "It is my staff; I lean upon it, and I bring down leaves for my sheep and I have therein other uses." <> Ya ce: "Ita sandãta ce, inã dõgara a kanta, kuma inã kakkaɓar ganye da ita a kan ƙananan bisãshẽna kuma inã da waɗansu bukãtõci na dabam a gare ta." = --Qur'an 20:18
    [Allah] said, "Throw it down, O Moses." <> Ya ce: "Ka yi jĩfa da ĩta, yã Mũsã!" = --Qur'an 20:19
    So he threw it down, and thereupon it was a snake, moving swiftly. <> Sai ya jẽfa ta. Sai gã ta dabbar macĩjiya, tanã tafiya da gaggãwa. = --Qur'an 20:20
    [Allah] said, "Seize it and fear not; We will return it to its former condition. <> Ya ce: "Ka kãma ta kuma kada ka ji tsõro. Za Mu mayar da ita ga hãlinta na farko." = --Qur'an 20:21
    And draw in your hand to your side; it will come out white without disease - another sign, <> "Kuma ka haɗa hannunka zuwa ga damtsenka, ya fita yanã fari, bãbu sõfane, wata ãyã ta dabam." = --Qur'an 20:22
    That We may show you [some] of Our greater signs. <> "Dõmin Mu nũna maka daga ãyõyinMu manya." = --Qur'an 20:23
    Go to Pharaoh. Indeed, he has transgressed." <> "Ka tafi zuwa ga Fĩr'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi (da girman kai)." = --Qur'an 20:24
    [Moses] said, "My Lord, expand for me my breast [with assurance] <> Ya ce: "Ya Ubangiji! Ka buɗa mini, ƙirjĩna. = --Qur'an 20:25
    And ease for me my task <> "Kuma ka sauƙaƙe mini al'amarĩna." = --Qur'an 20:26
    And untie the knot from my tongue <> "Kuma Ka warware mini wani ƙulli daga harshẽna." = --Qur'an 20:27
    That they may understand my speech. <> "Su fahimci maganãta." = --Qur'an 20:28
    And appoint for me a minister from my family - <> "Kuma Ka sanya mini wani mataimaki daga mutãnena." = --Qur'an 20:29
    Aaron, my brother. <> "Hãrũna ɗan'uwana." = --Qur'an 20:30
    Increase through him my strength <> "Ka ƙarfafa halittata da shi." = --Qur'an 20:31
    And let him share my task <> "Kuma Ka shigar da shi a cikin al'amarina." = --Qur'an 20:32
    That we may exalt You much <> "Dõmin mu tsarkake Ka da yawa." = --Qur'an 20:33
    And remember You much. <> "Kuma mu tuna Ka da yawa." = --Qur'an 20:34
    Indeed, You are of us ever Seeing." <> "Lalle Kai, Ka kasance Mai gani gare mu." = --Qur'an 20:35
    [Allah] said, "You have been granted your request, O Moses. <> Ya ce: "Lalle ne, an bã ka rõƙonka, yã Mũsã!" = --Qur'an 20:36
    And We had already conferred favor upon you another time, <> "Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun yi wata baiwa gare ka a wani lõkacin na dabam." = --Qur'an 20:37
    When We inspired to your mother what We inspired, <> "A lõkacin da Muka yi wahayin abin da aka yi wahayi zuwa ga uwarka." = --Qur'an 20:38
    [Saying], 'Cast him into the chest and cast it into the river, and the river will throw it onto the bank; there will take him an enemy to Me and an enemy to him.' And I bestowed upon you love from Me that you would be brought up under My eye. <> "Cẽwa, Ki jẽfa shi a cikin akwatin nan, sa'an nan ki jẽfa shi a cikin kõgi, sa'an nan kogin ya jefa shi a gãɓa, wani maƙiyi Nãwa kuma maƙiyi nãsa ya ɗauke shi.' Kuma Na jẽfa wani so daga gare Ni a kanka. Kuma dõmin a riƙe ka da kyau a kan ganiNa." = --Qur'an 20:39
    [And We favored you] when your sister went and said, 'Shall I direct you to someone who will be responsible for him?' So We restored you to your mother that she might be content and not grieve. And you killed someone, but We saved you from retaliation and tried you with a [severe] trial. And you remained [some] years among the people of Madyan. Then you came [here] at the decreed time, O Moses. <> "A sa'ad da 'yar'uwrka ke tafiya har ta ce, shin, in shiryar da ku ga wanda ke rẽnonsa?' Sai Muka mayar da kai zuwa ga uwarka dõmin idonta ya yi sanyi kuma bã zã ta yi baƙin ciki ba. Kuma kã kashe wani rai, sa'an nan Muka tsẽrar da kai daga baƙin ciki, kuma Muka fitine ka da waɗansu fitinõni. Sa'an nan ka zauna shẽkaru a cikin mutãnen Madyana. Sa'an nan kuma ka zo a kan wata ƙaddara, yã Mũsã! = --Qur'an 20:40
    And I produced you for Myself. <> "Kuma Na zãɓe ka dõmin Kaina." = --Qur'an 20:41
    Go, you and your brother, with My signs and do not slacken in My remembrance. <> "Ka tafi kai da ɗan'uwanka game da ãyõyiNa, kuma kada ku yi rauni ga ambatõNa." = --Qur'an 20:42
    Go, both of you, to Pharaoh. Indeed, he has transgressed. <> "Ku tafi kũ biyu zuwa ga Fir'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi (ga girman kai)." = --Qur'an 20:43
    And speak to him with gentle speech that perhaps he may be reminded or fear [Allah]." <> "Sai ku gaya masa magana mai laushi, tsammãninsa yanã tunãwa kõ kuwa ya ji tsõro." = --Qur'an 20:44
    They said, "Our Lord, indeed we are afraid that he will hasten [punishment] against us or that he will transgress." <> Su biyu suka ce: "Ya Ubangijinmu! Lalle ne munã tsõron ya yi gaggawa a kanmu, kõ ya ƙẽtare haddi." = --Qur'an 20:45
    [Allah] said, "Fear not. Indeed, I am with you both; I hear and I see. <> Ya ce: "Kada ku ji tsõro. Lalle Nĩ, Inã tãre da ku, Inaji, kuma Inã gani." = --Qur'an 20:46
    So go to him and say, 'Indeed, we are messengers of your Lord, so send with us the Children of Israel and do not torment them. We have come to you with a sign from your Lord. And peace will be upon he who follows the guidance. <> "Sai ku jẽ masa sa'an nan ku ce, Lalle mũ, Manzanni biyune na Ubangijinka, sai ka saki Banĩ Isrã'ĩla tãre da mu. Kuma kada ka yi musu azãba. Haƙĩƙa mun zomaka da wata ãyã daga, Ubangijinka. Kuma aminci ya tabbata ga wanda ya bi shiriya." = --Qur'an 20:47
    Indeed, it has been revealed to us that the punishment will be upon whoever denies and turns away.' " <> "Lalle mũ, haƙĩƙa, an yi wahayi zuwa gare mu, cẽwaazãba tanã a kan wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya." = --Qur'an 20:48
    [Pharaoh] said, "So who is the Lord of you two, O Moses?" <> Ya ce: "To, wãne ne Ubangijinku? Ya Mũsã!" = --Qur'an 20:49
    He said, "Our Lord is He who gave each thing its form and then guided [it]." <> Ya ce: "Ubangijinmu Shi ne wanda Ya bai wa dukan kõme halittarsa, sa'an nan Ya shiryar." = --Qur'an 20:50
    [Pharaoh] said, "Then what is the case of the former generations?" <> Ya ce: "To, mẽne hãlin ƙarnõnin farko?" = --Qur'an 20:51
    [Moses] said, "The knowledge thereof is with my Lord in a record. My Lord neither errs nor forgets." <> Ya ce: "Saninsu yanã a wurin Ubangijĩna, Ubangijĩna bã Ya ɓacẽwa kuma bã Ya mantuwa." = --Qur'an 20:52
    [It is He] who has made for you the earth as a bed [spread out] and inserted therein for you roadways and sent down from the sky, rain and produced thereby categories of various plants. <> "Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma Ya shigar muku da hanyõyi a cikinta, kuma Ya saukar da ruwa daga sama." Sa'an nan game da shi Muka fitar da nau'i-nau'i daga tsirũruwa dabam-dabam. = --Qur'an 20:53
    Eat [therefrom] and pasture your livestock. Indeed, in that are signs for those of intelligence. <> Ku ci kuma ku yi kiwon dabbõbin ni'imarku. Lalle ne, a cikin wannan akwai ãyõyi ga masu hankali. = --Qur'an 20:54
    From the earth We created you, and into it We will return you, and from it We will extract you another time. <> Daga gare ta Muka halitta ku, kuma a cikinta Muke mayar da ku, kuma daga gare ta Muke fitar da ku a wani lõkaci na dabam. = --Qur'an 20:55
    And We certainly showed Pharaoh Our signs - all of them - but he denied and refused. <> Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun nũna masa ãyõyinMu dukansu sai ya ƙaryata, kuma ya ƙiya! = --Qur'an 20:56
    He said, "Have you come to us to drive us out of our land with your magic, O Moses? <> Ya ce: "Shin kã zo mana ne dõmin ka fitar da mu daga ƙasarmu game da sihirinka, yã Mũsã?" = --Qur'an 20:57
    Then we will surely bring you magic like it, so make between us and you an appointment, which we will not fail to keep and neither will you, in a place assigned." <> "To, lalle ne munã zo maka da wani sihiri irinsa. Sai ka sanya wani wa'adi a tsakãninmu da tsakãninka bã mu sãɓa masa mũ kai kuma, bã ka sãɓãwa, a wani wuri mai dãcẽwa." = --Qur'an 20:58
    [Moses] said, "Your appointment is on the day of the festival when the people assemble at mid-morning." <> Ya ce: "Wa'adinku shi ne rãnar ƙawa kuma a tãra mutãne da hantsi." = --Qur'an 20:59
    So Pharaoh went away, put together his plan, and then came [to Moses]. <> Sai Fir'auna ya jũya, sa'an nan ya tãra mugunyar dabãrarsa, sa'an nan kuma ya zo. = --Qur'an 20:60
    Moses said to the magicians summoned by Pharaoh, "Woe to you! Do not invent a lie against Allah or He will exterminate you with a punishment; and he has failed who invents [such falsehood]." <> Mũsã ya ce musu, "Kaitõnku! Kada ku ƙirƙira ƙarya ga Allah har Ya tumɓuke ku da wata azãba. Kuma wanda ya ƙirƙira ƙarya, yã tãɓe." = --Qur'an 20:61
    So they disputed over their affair among themselves and concealed their private conversation. <> Sai suka yi jãyayya ga al'amarinsu a tsakãninsu kuma suka asirta gãnawa. = --Qur'an 20:62
    They said, "Indeed, these are two magicians who want to drive you out of your land with their magic and do away with your most exemplary way. <> Suka ce: "Lalle ne waɗannan biyun, haƙĩƙa masihirta ne sunã nufin su fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinsu kuma su tafi da tabĩ'arku mafĩficiya." = --Qur'an 20:63
    So resolve upon your plan and then come [forward] in line. And he has succeeded today who overcomes." <> "Sai ku haɗa dabãrarku sa'an nan kuma ku tafi a sahu guda, kuma haƙĩƙa, wanda ya rinjãya, a yau, ya rabbanta." = --Qur'an 20:64
    They said, "O Moses, either you throw or we will be the first to throw." <> Suka ce: "Ya Mũsã! Imma ka jefa, ko kuma mu kasance farkon mai jẽfawa." = --Qur'an 20:65
    He said, "Rather, you throw." And suddenly their ropes and staffs seemed to him from their magic that they were moving [like snakes]. <> Ya ce: "Ã'a, ku jẽfa." Sai gã igiyoyinsu da sandunansu anã sũranta su a gare shi, daga sihirinsu, lalle sunã tafiya da sauri. = --Qur'an 20:66
    And he sensed within himself apprehension, did Moses. <> Sai Mũsã ya ji tsõro a cikin ransa. = --Qur'an 20:67
    Allah said, "Fear not. Indeed, it is you who are superior. <> Muka ce: "Kada ka ji tsõro. lalle kai ne mafi ɗaukaka." = --Qur'an 20:68
    And throw what is in your right hand; it will swallow up what they have crafted. What they have crafted is but the trick of a magician, and the magician will not succeed wherever he is." <> "Kuma ka jẽfa abin da ke a cikin hannun dãmanka, ta cafe abin da suka aikata. Lalle ne abin da suka aikata mãkircin masihirci ne kuma masihirci bã ya cin nasara a duk inda ya je." = --Qur'an 20:69
    So the magicians fell down in prostration. They said, "We have believed in the Lord of Aaron and Moses." <> Sai aka jẽfar da masihirtan sunã mãsu sujada, suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin Hãrũna da Mũsã." = --Qur'an 20:70
    [Pharaoh] said, "You believed him before I gave you permission. Indeed, he is your leader who has taught you magic. So I will surely cut off your hands and your feet on opposite sides, and I will crucify you on the trunks of palm trees, and you will surely know which of us is more severe in [giving] punishment and more enduring." <> Ya ce: "Kun yi ĩmãni sabõda shi a gabãnin in yi muku izni? Lalle shĩ, haƙĩƙa, babbanku ne wanda ya sanar da ku sihirin! To, lalle ne zan kakkãtse hannayenku da ƙafãfunku a tarnaƙi kuma lalle zan tsĩre ku a cikin kututturan itãcen dabĩno, kuma lalle zã ku sani wanenmu ne mafi tsananin azãba kuma wãne ne mafi wanzuwar (azãba)." = --Qur'an 20:71
    They said, "Never will we prefer you over what has come to us of clear proofs and [over] He who created us. So decree whatever you are to decree. You can only decree for this worldly life. <> Suka ce: "Bã zã mu fĩfĩta ka ba faufau a kan abin da ya zo mana na hujjõji. Munã rantsuwa da wanda Ya ƙãga halittarmu sai ka hukunta abin da kake mai hukuntãwa, ai kanã ƙãre wannan rãyuwar dũniya kawai ne." = --Qur'an 20:72
    Indeed, we have believed in our Lord that He may forgive us our sins and what you compelled us [to do] of magic. And Allah is better and more enduring." <> "Lalle mũ, mun yi ĩmãni da Ubangijinmu dõmin Ya gãfarta mana laifuffukanmu da abin da ka tĩlasta mu a kansa na sihiri. Kuma Allah ne Mafi alhẽri, kumaMafi wanzuwa." = --Qur'an 20:73
    Indeed, whoever comes to his Lord as a criminal - indeed, for him is Hell; he will neither die therein nor live. <> Lalle shĩ wanda ya je wa Ubangijinsa yanã mai laifi, to lalle ne yanã da Jahannama, bã ya mutuwa a cikinta kuma bã ya rãyuwa. = --Qur'an 20:74
    But whoever comes to Him as a believer having done righteous deeds - for those will be the highest degrees [in position]: <> Kuma wanda ya je Masa yanã mai ĩmãni, alhãli kuwaya aikata aikin ƙwarai to waɗannan sunã da darajõji maɗaukaka. = --Qur'an 20:75
    Gardens of perpetual residence beneath which rivers flow, wherein they abide eternally. And that is the reward of one who purifies himself. <> Gidãjen Aljannar zama kõguna na gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu. Kuma wannan ne sakamakon wanda ya tsarkaku. = --Qur'an 20:76
    And We had inspired to Moses, "Travel by night with My servants and strike for them a dry path through the sea; you will not fear being overtaken [by Pharaoh] nor be afraid [of drowning]." <> Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa, "Ka yi tafiyar dare da bãyiNa. Sa'an nan ka dõka musu hanya a cikin tẽku tana ƙẽƙasasshiya, bã ka tsõron riskuwa, kuma bã ka fargabar nutsẽwa." = --Qur'an 20:77
    So Pharaoh pursued them with his soldiers, and there covered them from the sea that which covered them, <> Sai Fir'auna ya bi su game da rundunarsa. Sai abin da ya rufe su daga tẽku ya rufe su. = --Qur'an 20:78
    And Pharaoh led his people astray and did not guide [them]. <> Kuma Fir'auna ya ɓatar da mutãnensa, kuma bai shiryar (dasu) ba. = --Qur'an 20:79
    O Children of Israel, We delivered you from your enemy, and We made an appointment with you at the right side of the mount, and We sent down to you manna and quails, <> Yã Banĩ Isrã'ĩla! Lalle Mun tsẽrar da ku daga maƙiyinku, kuma mun yi muku wa'adi a gẽfen Dũtsen nan na dãma, kuma Mun sassaukar da darɓa da tattabaru dõminku. = --Qur'an 20:80
    [Saying], "Eat from the good things with which We have provided you and do not transgress [or oppress others] therein, lest My anger should descend upon you. And he upon whom My anger descends has certainly fallen." <> Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurtã ku kuma kada ku ƙẽtare haddi a cikinsa har hushĩNa ya sauka a kanku. Kuma wanda hushĩNa ya sauka a kansa, to, lalle ne, ya fãɗi. = --Qur'an 20:81
    But indeed, I am the Perpetual Forgiver of whoever repents and believes and does righteousness and then continues in guidance. <> Kuma lalle Nĩ haƙĩƙa Mai gãfara ne ga wanda ya tũba kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai, sa'an nan kuma ya nẽmi shiryuwa. = --Qur'an 20:82
    [Allah] said, "And what made you hasten from your people, O Moses?" <> "Kuma mẽne ne ya gaggautar da kai ga barin mutãnenka? Yã Mũsã!" = --Qur'an 20:83
    He said, "They are close upon my tracks, and I hastened to You, my Lord, that You be pleased." <> Ya ce: "Su ne waɗannan a kan sãwũna, kuma na yi gaggãwa zuwa gare Ka, yã Ubangiji! Dõmin Ka yarda." = --Qur'an 20:84
    [Allah] said, "But indeed, We have tried your people after you [departed], and the Samiri has led them astray." <> Ya ce: "To, lalle ne, haƙĩƙa, Mun fitini, mutãnenka daga bayãnka, kuma sãmiri ya ɓatar da su." = --Qur'an 20:85
    So Moses returned to his people, angry and grieved. He said, "O my people, did your Lord not make you a good promise? Then, was the time [of its fulfillment] too long for you, or did you wish that wrath from your Lord descend upon you, so you broke your promise [of obedience] to me?" <> Sai Mũsã ya kõma zuwa ga mutãnensa yanã mai hushi, mai baƙin ciki, ya ce: "Yã mutãnẽna! shin, Ubangijinku bai yi muku wa'adi ba, wa'adi mai kyau? Shin, lõkacin ya yi tsãwo a kanku ne, kõ kun yi nufi ne wani hushi ya sauka a kanku daga Ubangijinku, sabõda haka kuka sãɓã wa alkawarĩna?" = --Qur'an 20:86
    They said, "We did not break our promise to you by our will, but we were made to carry burdens from the ornaments of the people [of Pharaoh], so we threw them [into the fire], and thus did the Samiri throw." <> Suka ce: "Ba mu sãɓa wa alkawarinka ba da ĩkonmu kuma amma an ɗõra mana waɗansu kãya masu nauyi daga abin ƙawar mutãnen ne, sai muka jẽfar da su. Sa'an nan kamar haka ne sãmiri ya jẽfa." = --Qur'an 20:87
    And he extracted for them [the statue of] a calf which had a lowing sound, and they said, "This is your god and the god of Moses, but he forgot." <> "Sai ya fitar musu da wani maraƙi, jikin mutãne, yanã rũri, sa'an nan suka ce: wannan ne gunkinku kuma gunkin Mũsã, sai ya manta." = --Qur'an 20:88
    Did they not see that it could not return to them any speech and that it did not possess for them any harm or benefit? <> Shin, to, bã su ganin cẽwabã ya mayar musu da magana, kuma bã ya mallakar wata cũta a gare su, kuma bã ya mallakar amfãni? = --Qur'an 20:89
    And Aaron had already told them before [the return of Moses], "O my people, you are only being tested by it, and indeed, your Lord is the Most Merciful, so follow me and obey my order." <> Kuma, haƙĩƙa, Hãrũna yã ce musu daga gabãni, "Yã mutãnẽna! Lalle an fitinẽ ku da shi ne kawai. Kuma lalle Ubangijinku Mai rahama ne, sai ku bi ni, kuma ku yi ɗã'ã ga umurnĩna." = --Qur'an 20:90
    They said, "We will never cease being devoted to the calf until Moses returns to us." <> Suka ce: "Ba zã mu gushe ba faufau a kansa munã mãsu lazimta, sai Mũsã ya kõmo zuwa gare mu." = --Qur'an 20:91
    [Moses] said, "O Aaron, what prevented you, when you saw them going astray, <> (Mũsã) ya ce: "Yã Hãrũna! Mẽ ya hane ka, sa'ad da kagan su sun ɓace." = --Qur'an 20:92
    From following me? Then have you disobeyed my order?" <> "Ba ka bĩ ni ba! Shin, to, ka sãɓã wa umurnina ne?" = --Qur'an 20:93
    [Aaron] said, "O son of my mother, do not seize [me] by my beard or by my head. Indeed, I feared that you would say, 'You caused division among the Children of Israel, and you did not observe [or await] my word.' " <> (Hãrũna) ya ce: "Yã ɗãn'uwãna! Kada ka yi kãmu ga gẽmũna kõ ga kaina. Lalle nĩ, nã ji tsõron ka ce: Ka rarraba a tsakãnin Banĩ Isrã'ĩla kuma ba ka tsare maganata ba." = --Qur'an 20:94
    [Moses] said, "And what is your case, O Samiri?" <> (Mũsã) ya ce: "Mẽne ne babban al'amarinka? Ya Sãmiri!" = --Qur'an 20:95
    He said, "I saw what they did not see, so I took a handful [of dust] from the track of the messenger and threw it, and thus did my soul entice me." <> (Sãmiri) ya ce: "Nã ga abin da ba su gan shi ba shi, sai na yi damƙa, damƙa guda daga kufan sãwun Manzon, sa'an nan na jẽfa ta. Kuma haka dai raina ya ƙawãta mini." = --Qur'an 20:96
    [Moses] said, "Then go. And indeed, it is [decreed] for you in [this] life to say, 'No contact.' And indeed, you have an appointment [in the Hereafter] you will not fail to keep. And look at your 'god' to which you remained devoted. We will surely burn it and blow it into the sea with a blast. <> (Mũsã) ya ce: "To, ka tafi, sabõda haka lalle ne kanã da a cikin rãyuwarka, ka ce 'Bãbu shãfa' kuma kanã da wani ma'alkawarta, bã zã a sãɓa maka gare ta ba. Kuma ka dũba zuwa ga gunkinka wanda ka yini a kansa kanã mai lazimta. Lalle ne muna ƙõne shi, sa'an nan kuma munã shẽƙe shi, a cikin tẽku, shẽƙẽwa." = --Qur'an 20:97
    Your god is only Allah, except for whom there is no deity. He has encompassed all things in knowledge." <> Abin sani kawai abin bautãwarku Allah kawai ne wanda bãbu wani abin bautãwa, fãce Shi kuma Yã yalwaci dukkan kõme da ilmi. = --Qur'an 20:98
    Thus, [O Muhammad], We relate to you from the news of what has preceded. And We have certainly given you from Us the Qur'an. <> Kamar wancan ne Muke lãbartãwa a gare ka, daga lãbãran abin da ya gabãta, alhãli kuwa haƙĩƙa, Mun bã ka zikiri (Alƙur'ãni) daga gunMu. = --Qur'an 20:99
    Whoever turns away from it - then indeed, he will bear on the Day of Resurrection a burden, <> Wanda ya kau da kai daga gare shi, to, lalle shĩ, yanãɗaukar wani nauyi a Rãnar ¡iyãma. = --Qur'an 20:100
    [Abiding] eternally therein, and evil it is for them on the Day of Resurrection as a load - <> Sunã madawwama a cikinsa, kuma yã mũnana ya zama abin ɗauka, a Rãnar ¡iyãma. = --Qur'an 20:101
    The Day the Horn will be blown. And We will gather the criminals, that Day, blue-eyed. <> A Rãnar da ake hũrãwa a cikin ƙãho kuma Munã tãra mãsu laifi, a rãnar nan, sunã mãsu shũɗãyen idãnu. = --Qur'an 20:102
    They will murmur among themselves, "You remained not but ten [days in the world]." <> Suna ɓõye magana a tsakãninsu, (Sunã ce wa jũna) "Ba ku zauna ba (a cikin dũniya) fãce kwãna gõma." = --Qur'an 20:103
    We are most knowing of what they say when the best of them in manner will say, "You remained not but one day." <> Mu ne mafi sani ga abin da suke faɗa a sa'ad da mafĩficinsu ga hanya ke cẽwa, "Ba ku zauna ba fãce a yini guda." = --Qur'an 20:104
    And they ask you about the mountains, so say, "My Lord will blow them away with a blast. <> Kuma sunã tambayar ka daga duwãtsu sai ka ce: "Ubangijina Yana shẽƙe su shẽƙẽwa, = --Qur'an 20:105
    And He will leave the earth a level plain; <> Sa'an nan Yanã barin (wurinsu) faƙo mai santsi. = --Qur'an 20:106
    You will not see therein a depression or an elevation." <> "Bã ka ganin karkata a cikinsa, kuma bã ka ganin wani tudu." = --Qur'an 20:107
    That Day, everyone will follow [the call of] the Caller [with] no deviation therefrom, and [all] voices will be stilled before the Most Merciful, so you will not hear except a whisper [of footsteps]. <> A rãnar nan sunã biyar mai kira, bãbu karkata a gare shi, kuma sautuka suka yi kawaici ga Mai rahama, bã ka sauraren kõme fãce sautin tafiya. = --Qur'an 20:108
    That Day, no intercession will benefit except [that of] one to whom the Most Merciful has given permission and has accepted his word. <> A yinin nan cẽto bã ya yin amfãni fãce wanda Mai rahama Ya yi masa izni kuma Ya yarda da shi, da magan = --Qur'an 20:109
    Allah knows what is [presently] before them and what will be after them, but they do not encompass it in knowledge. <> Yanã sanin abin da ke a gaba gare su da abin da ke bãyansu, kuma bã su kẽwayẽwa da shi ga sani. = --Qur'an 20:110
    And [all] faces will be humbled before the Ever-Living, the Sustainer of existence. And he will have failed who carries injustice. <> Kuma fuskõki suka ƙanƙan da kai ga Rãyayye, Tsayayye, alhãli kuwa wanda ya ɗauko wani zãlunci ya tãɓe. = --Qur'an 20:111
    But he who does of righteous deeds while he is a believer - he will neither fear injustice nor deprivation. <> Kuma wanda ya aikata wani abu daga ayyukan ƙwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bã ya tsõron wani zãlunci ko wata naƙasa. = --Qur'an 20:112
    And thus We have sent it down as an Arabic Qur'an and have diversified therein the warnings that perhaps they will avoid [sin] or it would cause them remembrance. <> Kuma haka Muka saukar da shi, Alƙur'ãni, yanã abin karantãwa, da Larabci kuma Muka jujjuya misãlai, a cikinsa, na tsõratarwa, tsammãninsu, sunã yin taƙawa ko ya sabbaba musu wata wa'aztuwa. = --Qur'an 20:113
    So high [above all] is Allah, the Sovereign, the Truth. And, [O Muhammad], do not hasten with [recitation of] the Qur'an before its revelation is completed to you, and say, "My Lord, increase me in knowledge." <> Sa'an nan Allah Mamallaki, Tabbatacce Yã ɗaukaka. Kuma kada ka yi gaggãwa da Alƙur'ãni a gabãnin a ƙãre wahayinsa zuwa gare ka. Kuma ka ce: "Yã Ubangiji! Ka ƙãra mini ilmi." = --Qur'an 20:114
    And We had already taken a promise from Adam before, but he forgot; and We found not in him determination. <> Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun yi alkawari zuwa ga Ãdamu a gabãnin wannan, sai ya manta, kuma ba Mu sãmi ƙarfin zũciya a gare shiba. = --Qur'an 20:115
    And [mention] when We said to the angels, "Prostrate to Adam," and they prostrated, except Iblees; he refused. <> Kuma sa'ad da Muka ce wa malã'iku, "Ku yi sujada ga Ãdamu." Sai suka yi sujada, fãce Iblĩsa, yã ƙiya. = --Qur'an 20:116
    So We said, "O Adam, indeed this is an enemy to you and to your wife. Then let him not remove you from Paradise so you would suffer. <> Sai Muka ce: "Ya Ãdamu! Lalle ne wannan maƙiyi ne gare ka da kuma ga mãtarka, sabõda haka kada ya fitar da ku daga Aljanna har ku wahala." = --Qur'an 20:117
    Indeed, it is [promised] for you not to be hungry therein or be unclothed. <> Lalle ne kã sãmu bã zã ka ji yunwa ba a cikinta, kuma bã zã ka yi tsiraici ba. = --Qur'an 20:118
    And indeed, you will not be thirsty therein or be hot from the sun." <> "Lalle kai, bã zã ka ji ƙishirwa ba, kuma bã zã ka shiga hantsi ba." = --Qur'an 20:119
    Then Satan whispered to him; he said, "O Adam, shall I direct you to the tree of eternity and possession that will not deteriorate?" <> Sai shaiɗan ya sanya waswãsi zuwa gare shi, ya ce: "Yã Ãdamu! Shin, in shiryar da kai ga itãciyar dawwama da mulki wanda bã ya ƙãrẽwa?" = --Qur'an 20:120
    And Adam and his wife ate of it, and their private parts became apparent to them, and they began to fasten over themselves from the leaves of Paradise. And Adam disobeyed his Lord and erred. <> Sai suka ci daga gare ta, sabõda haka al'aurunsu suka bayyana, kuma suka shiga sunã lulluɓãwa a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ãdamu ya sãɓã wa Ubangijinsa, sabõda haka ya ɓace. = --Qur'an 20:121
    Then his Lord chose him and turned to him in forgiveness and guided [him]. <> Sa'an nan kuma Ubangjinsa Ya zãɓẽ shi, Ya karɓi tũba gare shi, kuma Ya shiryar (da shi). = --Qur'an 20:122
    [Allah] said, "Descend from Paradise - all, [your descendants] being enemies to one another. And if there should come to you guidance from Me - then whoever follows My guidance will neither go astray [in the world] nor suffer [in the Hereafter]. <> Ya ce: "Ku sauka kũ biyu daga gare ta gabã ɗaya, sãshenku yanã maƙiyi ga sãshe. To, imma dai wata shitiya ta jẽ muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiryarwãta, to, bã ya ɓacẽwa, kuma bã ya wahala." = --Qur'an 20:123
    And whoever turns away from My remembrance - indeed, he will have a depressed life, and We will gather him on the Day of Resurrection blind." <> "Kuma wanda ya bijire daga ambatõNa (Alƙur'ãni) to, lalle ne rãyuwa mai ƙunci ta tabbata a gare shi, kuma Munã tãyar da shi a Rãnar ¡iyãma yanã makãho." = --Qur'an 20:124
    He will say, "My Lord, why have you raised me blind while I was [once] seeing?" <> Ya ce: "Ya Ubangiji! Don me Ka tãyar da ni makãho alhãli kuwa nã kasance mai gani?" = --Qur'an 20:125
    [Allah] will say, "Thus did Our signs come to you, and you forgot them; and thus will you this Day be forgotten." <> Ya ce: "Kamar wancan ne ãyõyinMu suka jẽ maka sai ka mance su, kuma kamar hakar a yau ake mance ka." = --Qur'an 20:126
    And thus do We recompense he who transgressed and did not believe in the signs of his Lord. And the punishment of the Hereafter is more severe and more enduring. <> Kuma kamar haka Muke sãka wa wanda ya yawaita, kuma bai yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinsa ba. Kuma lalle ne azãbar Lãhira ce mafi tsanani, kuma mafi wanzuwa = --Qur'an 20:127
    Then, has it not become clear to them how many generations We destroyed before them as they walk among their dwellings? Indeed in that are signs for those of intelligence. <> Shin, to, bai shiryar da su ba cẽwa da yawa Muka halakarda (kãfirai) daga ƙarnuka, a gabãninsu, sunã tafiya a cikin masaukansu? Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu hankula. = --Qur'an 20:128
    And if not for a word that preceded from your Lord, punishment would have been an obligation [due immediately], and [if not for] a specified term [decreed]. <> Kuma bã dõmin wata kalma ba wadda ta gabãta daga Ubangijinka, da kuma ajali ambatacce haƙĩƙa, dã azãbarta kasance mai lazimta. = --Qur'an 20:129
    So be patient over what they say and exalt [Allah] with praise of your Lord before the rising of the sun and before its setting; and during periods of the night [exalt Him] and at the ends of the day, that you may be satisfied. <> Sai ka yi haƙuri a kan abin da suke cẽwa, kuma ka yi tasbĩhi da gõdẽ wa Ubangijinka a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta, kuma daga sã'õ'in dare sai ka yi tasbĩhi da sãsannin yini, tsammãninka zã ka sãmi yarda. = --Qur'an 20:130
    And do not extend your eyes toward that by which We have given enjoyment to [some] categories of them, [its being but] the splendor of worldly life by which We test them. And the provision of your Lord is better and more enduring. <> Kuma kada ka mĩƙar da idãnunka zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi da shi, nau'i-nau'i daga gare su, kamar huren rãyuwar dũniya yake, dõmin Mu fitine su a cikinsa, alhãli kuwa arzikin Ubangijinka, ne mafi alhẽri kuma mafi wanzuwa. = --Qur'an 20:131
    And enjoin prayer upon your family [and people] and be steadfast therein. We ask you not for provision; We provide for you, and the [best] outcome is for [those of] righteousness. <> Kuma ka umurci iyãlanka da salla, kuma ka yi haƙuri a kanta. Bã Mu tambayar ka wani arziki Mu ne Muke azurta ka. Kuma ãƙiba mai kyau tanã ga taƙawa. = --Qur'an 20:132
    And they say, "Why does he not bring us a sign from his Lord?" Has there not come to them evidence of what was in the former scriptures? <> Kuma suka ce: "Don me bã ya zo mana da wata ãyã daga Ubangijinsa?" Shin, kuwa hujjar abin da ke a cikin littattafan farko, ba ta jẽ musu ba? = --Qur'an 20:133
    And if We had destroyed them with a punishment before him, they would have said, "Our Lord, why did You not send to us a messenger so we could have followed Your verses before we were humiliated and disgraced?" <> Kuma dã dai Mun halaka sũ da wata azãba daga gabãninsa, lalle ne dã sun ce: "Yã Ubangijinmu! Dã Kã aiko da wani Manzo zuwa gare mu har mu bibiyi ãyõyinKa daga gabãnin mu ƙasƙanta, kuma mu wulãkantu!" = --Qur'an 20:134
    Say, "Each [of us] is waiting; so wait. For you will know who are the companions of the sound path and who is guided." <> Ka ce: "Kõwa mai tsumãye ne. Sai ku yi tsumãye. Sa'an nan zã ku san su wa ne ma'abũta tafarki madaidaici, kuma wane ne ya nẽmi shiryuwa." = --Qur'an 20:135
    [The time of] their account has approached for the people, while they are in heedlessness turning away. <> Hisãbin mutãne ya kusanta gare su, ahãli kuwa sunã a cikin gafala, sunã mãsu bijirẽwa. = --Qur'an 21:1
    No mention comes to them anew from their Lord except that they listen to it while they are at play <> Wani ambatõ daga Ubangijinsu sãbo, bã ya zuwa gare su fãce sun saurãre shi, alhãli kuwa sunã mãsu yin wãsa. = --Qur'an 21:2
    With their hearts distracted. And those who do wrong conceal their private conversation, [saying], "Is this [Prophet] except a human being like you? So would you approach magic while you are aware [of it]?" <> Sanã mãsu shagaltacin zukãtansu, kuma su asirta gãnãwa: Waɗanda suka yi zãlunce (sunã cẽwa) "Wannan bã Kõwa ba ne fãce mutum misãlinku. Shin, to, kunã jẽ wa sihiri, ahãli kuwa kũ, kunã fahimta?" = --Qur'an 21:3
    The Prophet said, "My Lord knows whatever is said throughout the heaven and earth, and He is the Hearing, the Knowing." <> Ya ce: "Ubangijina Yanã sanin magana a cikin sama da ƙasa kuma Shi ne Mai ji, Masani." = --Qur'an 21:4
    But they say, "[The revelation is but] a mixture of false dreams; rather, he has invented it; rather, he is a poet. So let him bring us a sign just as the previous [messengers] were sent [with miracles]." <> Ã'a, suka ce: "Yãye-yãyen mafarki ne. Ã'a, yã ƙirƙira shi ne. Ã'a, shi mawãƙi ne. Sai ya zo mana da wata ãyã kamar yadda aka aiko manzanni na farko." = --Qur'an 21:5
    Not a [single] city which We destroyed believed before them, so will they believe? <> Wata alƙarya da Muka halaka ta a gabãninsu, ba ta yi ĩmãni ba. Shin, to, sũ, sunã yin ĩmãni? = --Qur'an 21:6
    And We sent not before you, [O Muhammad], except men to whom We revealed [the message], so ask the people of the message if you do not know. <> Kuma ba Mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã yin wahayi zuwa gare su. Ku tambayi ma'abũta ambato idan kun kasance ba ku sani ba. = --Qur'an 21:7
    And We did not make the prophets forms not eating food, nor were they immortal [on earth]. <> Kuma ba Mu sanya su jiki, bã su cin abin ci ba, kuma ba su kasance madawwama ba. = --Qur'an 21:8
    Then We fulfilled for them the promise, and We saved them and whom We willed and destroyed the transgressors. <> Sa'an nan kuma Muka gaskata musu alkawari; sai Muka tsẽrar da su da wanda Muke so, kuma Muka halakar da mãsu yawaitãwa. = --Qur'an 21:9
    We have certainly sent down to you a Book in which is your mention. Then will you not reason? <> Lalle haƙĩƙa Mun saukar da wani littãfi zuwa gare ku, a cikinsa akwai ambatonku. Shin, to, bã ku hankalta? = --Qur'an 21:10
    And how many a city which was unjust have We shattered and produced after it another people. <> Kuma da yawa Muka karya wata alƙarya tã kasance mai zãlunci, kuma Muka ƙãga halittar waɗansu mutãne na dabam a bãyanta. = --Qur'an 21:11
    And when its inhabitants perceived Our punishment, at once they fled from it. <> Sai a lõkacin da suka hangi azãbarMu, sai gã su sunã gudu daga gare ta. = --Qur'an 21:12
    [Some angels said], "Do not flee but return to where you were given luxury and to your homes - perhaps you will be questioned." <> "Kada ku yi gudu. Ku kõmo zuwa ga abin da aka ni'imtar da ku a cikinsa da gidãjenku tsammãninku anã tambayar ku." = --Qur'an 21:13
    They said, "O woe to us! Indeed, we were wrongdoers." <> Suka ce: "Kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance mãsu zãlunci." = --Qur'an 21:14
    And that declaration of theirs did not cease until We made them [as] a harvest [mowed down], extinguished [like a fire]. <> Sa'an nan waccan ba ta gushe ba, ita ce da'awarsu har Muka mayar da su girbabbu, bitattu. = --Qur'an 21:15
    And We did not create the heaven and earth and that between them in play. <> Kuma ba Mu halitta sama da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu Muna Mãsu wãsã ba. = --Qur'an 21:16
    Had We intended to take a diversion, We could have taken it from [what is] with Us - if [indeed] We were to do so. <> Da Mun yi nufin Mu riƙi wani abin wãsa dã Mun riƙe shi daga gunMu, idan Mun kasance mãsu aikatãwa. = --Qur'an 21:17
    Rather, We dash the truth upon falsehood, and it destroys it, and thereupon it departs. And for you is destruction from that which you describe. <> Ã'a, Munã jĩfa da gaskiya a kan ƙarya, sai ta darkãke ta, sai ga tã halakakka. Kuma bone yã tabbata a gare ku sabõda abin da kuke siffantãwa. = --Qur'an 21:18
    To Him belongs whoever is in the heavens and the earth. And those near Him are not prevented by arrogance from His worship, nor do they tire. <> Kuma shĩ ne da mallakar wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma waɗanda suke wurinSa (watau malã'iku), bã su yin girman kai ga ibãdarSa. kuma bã su gajiya. = --Qur'an 21:19
    They exalt [Him] night and day [and] do not slacken. <> Sunã tasbĩhi dare da rãnã, bã su yin rauni. = --Qur'an 21:20
    Or have men taken for themselves gods from the earth who resurrect [the dead]? <> Kõ (kãfirai) sun riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa ne ga ƙasã, su ne mãsu tãyarwa (gare su)? = --Qur'an 21:21
    Had there been within the heavens and earth gods besides Allah, they both would have been ruined. So exalted is Allah, Lord of the Throne, above what they describe. <> Dã waɗansu abũbuwan bautawa sun kasance a cikinsu (sama da ƙasa) fãce Allah, haƙĩƙa dã su biyun sun ɓãci. Sabõda haka tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin Al'arshi daga abin da suke siffantãwa. = --Qur'an 21:22
    He is not questioned about what He does, but they will be questioned. <> Bã a tambayar Sa ga abin da Yake aikatãwa, alhãli kuwa sũanã tambayar su. = --Qur'an 21:23
    Or have they taken gods besides Him? Say, [O Muhammad], "Produce your proof. This [Qur'an] is the message for those with me and the message of those before me." But most of them do not know the truth, so they are turning away. <> Kõ sun riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa baicinSa? Ka ce: "Ku kãwo hujjarku, wannan shi ne ambaton wanda yake tãre da ni, kuma shi ne ambaton wanda yake a gabãnĩna. Ã'a, mafi yawansubã su sanin gaskiya, sabõda haka sũ mãsu bijirẽwa ne." = --Qur'an 21:24
    And We sent not before you any messenger except that We revealed to him that, "There is no deity except Me, so worship Me." <> Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba a gabãninka fãce Munã yin wahayi zuwa gare shi, cẽwa "Lalle ne Shi, bãbu abin bautãwa fãce Nĩ, sai ku bauta Mini." = --Qur'an 21:25
    And they say, "The Most Merciful has taken a son." Exalted is He! Rather, they are [but] honored servants. <> Kuma suka ce: "Mai rahama ya riƙi ɗã." Tsarkinsa, ya tabbata! Ã'a, (malã'iku) bãyi ne mãsu daraja. = --Qur'an 21:26
    They cannot precede Him in word, and they act by His command. <> Bã su gabãtarSa da magana, kuma su da umurninSa suke aiki. = --Qur'an 21:27
    He knows what is [presently] before them and what will be after them, and they cannot intercede except on behalf of one whom He approves. And they, from fear of Him, are apprehensive. <> Yanã sanin abin da yake gaba gare su da abin da yake a bãyansu, kuma bã su yin cẽto fãce ga wanda Ya yarda, kuma sũmasu sauna ne sabõda tsõronSa. = --Qur'an 21:28
    And whoever of them should say, "Indeed, I am a god besides Him"- that one We would recompense with Hell. Thus do We recompense the wrongdoers. <> Kuma wanda ya ce daga gare su, "Lalle nĩ abin bautãwa ne baicinSa," to, wannan Munã sãkã masa da, Jahannama. Kamar haka Muke sãkã wa azzãlumai. = --Qur'an 21:29
    Have those who disbelieved not considered that the heavens and the earth were a joined entity, and We separated them and made from water every living thing? Then will they not believe? <> Shin kuma waɗanda suka kãfirta ba, su gani da cẽwa lalle sammai da ƙasa sun kasance ɗinke, sai Muka bũɗe su, kuma Muka sanya dukan kome mai rai daga ruwa? Shin, bã zã su yi ĩmãni ba? = --Qur'an 21:30
    And We placed within the earth firmly set mountains, lest it should shift with them, and We made therein [mountain] passes [as] roads that they might be guided. <> Kuma Mun sanya tabbatattun duwãtsu a cikin ƙasa dõmin kada ta karkata da su kuma Mun sanya ranguna, hanyõyi, a cikinsu (duwãtsun), tsammãninsu sunã shiryuwa. = --Qur'an 21:31
    And We made the sky a protected ceiling, but they, from its signs, are turning away. <> Kuma Mun sanya sama rufi tsararre, alhãli kuwa su daga ãyõyinta mãsu bijirẽwa ne. = --Qur'an 21:32
    And it is He who created the night and the day and the sun and the moon; all [heavenly bodies] in an orbit are swimming. <> Kuma shĩ ne wanda Ya halitta dare da yini da rãnã da watã dukansu a cikin wani sarari suKe iyo. = --Qur'an 21:33
    And We did not grant to any man before you eternity [on earth]; so if you die - would they be eternal? <> Kuma ba Mu sanya dawwama ga wani mutum ba, a gabãninka. Shin to idan ka mutu to sũ ne madawwama? = --Qur'an 21:34
    Every soul will taste death. And We test you with evil and with good as trial; and to Us you will be returned. <> Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma Munã jarraba ku da sharri da alhẽri dõmin fitina. Kuma zuwa gare Mu ake mayar da ku. = --Qur'an 21:35
    And when those who disbelieve see you, [O Muhammad], they take you not except in ridicule, [saying], "Is this the one who insults your gods?" And they are, at the mention of the Most Merciful, disbelievers. <> Kuma idan waɗanda suka kãfirta suka gan ka, bã su riƙon ka fãce da izgili (sunã cẽwa), "Shin, wannan ne ke ambatar gumãkanku?" Alhãli kuwa sũ, ga ambatar Mai rahama, mãsu kãfirta ne. = --Qur'an 21:36
    Man was created of haste. I will show you My signs, so do not impatiently urge Me. <> An halitta mutum daga gaggãwa, zan nũna muku ãyõyiNa. Sabõda haka kada ku nẽmiyin gaggãwa. = --Qur'an 21:37
    And they say, "When is this promise, if you should be truthful?" <> Kuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi zai tabbata, idan kun kasance mãsu gaskiya?" = --Qur'an 21:38
    If those who disbelieved but knew the time when they will not avert the Fire from their faces or from their backs and they will not be aided... <> Dã waɗanda suka kãfirta sunã sanin lõkacin da bã su kange wuta daga fuskõkinsu, kuma haka daga bãyayyakinsu, alhãli kuwa ba su zama ana taimakon su ba. = --Qur'an 21:39
    Rather, it will come to them unexpectedly and bewilder them, and they will not be able to repel it, nor will they be reprieved. <> Ã'a, tanã jẽ musu bisa ga auke sai ta ɗimautar da su, sa'an nan bã su iya mayar da ita, kuma ba su zama anã yi musu jinkiri ba. = --Qur'an 21:40
    And already were messengers ridiculed before you, but those who mocked them were enveloped by what they used to ridicule. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili ga waɗansu Manzanni daga gabãninka, sai abin da suka kasance sunã izgili da shi ya auku ga waɗanda suka yi izgilin daga gare su. = --Qur'an 21:41
    Say, "Who can protect you at night or by day from the Most Merciful?" But they are, from the remembrance of their Lord, turning away. <> Ka ce: "Wãne ne yake tsare ku a dare da yini daga Mai rahama?" Ã'a, sũ mãsu bijirẽwa ne daga ambaton Ubangijinsu. = --Qur'an 21:42
    Or do they have gods to defend them other than Us? They are unable [even] to help themselves, nor can they be protected from Us. <> Ko kuwa sunã da waɗansu abũbuwan bautãwa waɗanda ke tsare su, daga gare Mu? Bã su iya taimakon kansu kuma ba su kasance anã abũtar su ba daga gareMu. = --Qur'an 21:43
    But, [on the contrary], We have provided good things for these [disbelievers] and their fathers until life was prolonged for them. Then do they not see that We set upon the land, reducing it from its borders? So it is they who will overcome? <> Ã'a, Mun yalwata wa waɗannan da ubanninsu ni'imarMu, har rãyuwa ta yi tsawo a kansu. Shin, to, bã su ganin cẽwa lalle Mũ, Munã je wa ƙasarsu, Munã rage ta daga sãsanninta? Shin, to, su ne marinjaya? = --Qur'an 21:44
    Say, "I only warn you by revelation." But the deaf do not hear the call when they are warned. <> Ka ce: "Abin sani, inã yi muku gargaɗi kawai da wahayi," kuma kurma ba ya jin kira a lõkacin da ake yi musu gargaɗi. = --Qur'an 21:45
    And if [as much as] a whiff of the punishment of your Lord should touch them, they would surely say, "O woe to us! Indeed, we have been wrongdoers." <> Kuma haƙĩƙa idan wata iska daga azãbar Ubangiji ta shãfe su, haƙĩƙa sunã cẽwa, "Yã kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance mãsu zãlunci." = --Qur'an 21:46
    And We place the scales of justice for the Day of Resurrection, so no soul will be treated unjustly at all. And if there is [even] the weight of a mustard seed, We will bring it forth. And sufficient are We as accountant. <> Kuma Munã aza ma'aunan ãdalci ga Rãnar ¡iyãma, sabõda haka ba a zãluntar rai da kõme. Kuma kõ dã ya kasance nauyin ƙwãya daga kõmayya ne Mun zo da ita. Kuma Mun isa zama Mãsu hisãbi. = --Qur'an 21:47
    And We had already given Moses and Aaron the criterion and a light and a reminder for the righteous <> Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun kãwo wa Mũsã da Hãrũna Rarrabewa da haske da ambato ga mãsu aiki da taƙawa. = --Qur'an 21:48
    Who fear their Lord unseen, while they are of the Hour apprehensive. <> Waɗanda suke tsãron Ubangijinsu a fake, alhãli kuwa sũ, mãsu sauna ne daga Sa'a. = --Qur'an 21:49
    And this [Qur'an] is a blessed message which We have sent down. Then are you with it unacquainted? <> Kuma wannan ambato ne mai albarka Mun saukar da shi. Shin, to, kũ mãsu musu ne gare shi? = --Qur'an 21:50
    And We had certainly given Abraham his sound judgement before, and We were of him well-Knowing <> Kuma lalle haƙĩƙa Mun kãwo wa Ibrãhĩm shiryuwarsa daga gabãni, kuma Mun kasance Masana gare shi. = --Qur'an 21:51
    When he said to his father and his people, "What are these statues to which you are devoted?" <> Ya ce wa ubansa da mutanensa, "Mẽne ne waɗannan mutummutumai waɗanda kuke mãsu lazimta a kansu?" = --Qur'an 21:52
    They said, "We found our fathers worshippers of them." <> Suka ce: "Mun sãmi Ubanninmu mãsu lazimta a kansu." = --Qur'an 21:53
    He said, "You were certainly, you and your fathers, in manifest error." <> Ya ce: "Lalle, haƙĩƙa, kun kasance kũ da Ubanninku a cikin ɓata bayyananna." = --Qur'an 21:54
    They said, "Have you come to us with truth, or are you of those who jest?" <> Suka ce: "Shin kã zo mana da gaskiya ne, Kõ kuwa kai kanã daga mãSu wãsã ne?" = --Qur'an 21:55
    He said, "[No], rather, your Lord is the Lord of the heavens and the earth who created them, and I, to that, am of those who testify. <> Ya ce: "Ã'a, Ubangijinku Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa, wanda Ya ƙãga halittarsu. Kuma Ni inã daga mãsu shaida a kan haka." = --Qur'an 21:56
    And [I swear] by Allah, I will surely plan against your idols after you have turned and gone away." <> "Kuma inã rantsuwa da Allah, lalle zan yi wani shiri ga gumãkanku a bãyan kun jũya kunã mãsu bãyar da bãya." = --Qur'an 21:57
    So he made them into fragments, except a large one among them, that they might return to it [and question]. <> Sai ya sanya su guntu-guntu fãce wani babba gare su, tsammãninsũ sunã Kõmãwa zuwa gare shi. = --Qur'an 21:58
    They said, "Who has done this to our gods? Indeed, he is of the wrongdoers." <> Suka ce: "Wane ne ya aikata wannan ga gumãkanmu? Lalle shĩ, haƙĩƙa, yanã daga azzãlumai." = --Qur'an 21:59
    They said, "We heard a young man mention them who is called Abraham." <> Suka ce: "Mun ji wani saurayi yanã ambatar su. Anã ce masa Ibrahĩm." = --Qur'an 21:60
    They said, "Then bring him before the eyes of the people that they may testify." <> Suka ce: "To, ku zo da shi a kan idanun mutãne, tsammãnin su zã su bãyar da shaida." = --Qur'an 21:61
    They said, "Have you done this to our gods, O Abraham?" <> Suka ce: "Shin kai ne ka aikata wannan ga gumãkanmu? Yã Ibrahĩm!" = --Qur'an 21:62
    He said, "Rather, this - the largest of them - did it, so ask them, if they should [be able to] speak." <> Ya ce: "Ã'a, babbansu, wannan, shĩ ya aikata, shi. Sai ku tambaye su idan sun kasance sunã yin magana." = --Qur'an 21:63
    So they returned to [blaming] themselves and said [to each other], "Indeed, you are the wrongdoers." <> Sai suka kõma wa jũnansu suka ce: "Lalle ne kũ, kũ ne azzãlumai." = --Qur'an 21:64
    Then they reversed themselves, [saying], "You have already known that these do not speak!" <> Sa'an nan kuma aka sunkuyar da su a kan kãwunansu (sukace,) "Lalle, haƙĩƙa, kã sani waɗannan bã su yin magana." = --Qur'an 21:65
    He said, "Then do you worship instead of Allah that which does not benefit you at all or harm you? <> Ya ce: "Shin to, kunã bautã wa abin da, bã ya, amfãnin ku da Kõme kuma bã ya cũtar da ku baicin Allah?" = --Qur'an 21:66
    Uff to you and to what you worship instead of Allah. Then will you not use reason?" <> "Tir da ku, kuma da abin da kuke bauta wa, baicin Allah! Shin to, bã ku hankalta?" = --Qur'an 21:67
    They said, "Burn him and support your gods - if you are to act." <> Suka ce: "Ku ƙõne shi kuma ku taimaki gumãkanku, idan kun kasance mãsu aikatãwa." = --Qur'an 21:68
    Allah said, "O fire, be coolness and safety upon Abraham." <> Muka ce: "Yã wuta! Ki kasance sanyi da aminci ga Ibrahĩm." = --Qur'an 21:69
    And they intended for him harm, but We made them the greatest losers. <> Kuma suka yi nufin wani mũgun shiri da shi, sai Mukasanya su mafiya hasãra. = --Qur'an 21:70
    And We delivered him and Lot to the land which We had blessed for the worlds. <> Kuma Muka tsẽrar da shi da Lũɗu zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta ga tãlikai. = --Qur'an 21:71
    And We gave him Isaac and Jacob in addition, and all [of them] We made righteous. <> Kuma Muka ba shi Is'haka da Ya'aƙuba a kan daɗi alhãli kuwa dukansu Mun sanya su sãlihai. = --Qur'an 21:72
    And We made them leaders guiding by Our command. And We inspired to them the doing of good deeds, establishment of prayer, and giving of zakah; and they were worshippers of Us. <> Kuma Muka sanya su shugabanni, sunã shiryarwa da umurninMu. Kuma Muka yi wahayi zuwa gare su da ayyukan alhẽri da tsayar da salla da bãyar da zakka. Kuma sun kasance mãsu bauta gare Mu. = --Qur'an 21:73
    And to Lot We gave judgement and knowledge, and We saved him from the city that was committing wicked deeds. Indeed, they were a people of evil, defiantly disobedient. <> Kuma Lũɗu Mun bã shi hukunci da ilmi. Kuma Mun tsĩrar da shi daga alƙaryar nan wadda ke aikata mũnãnan ayyuka. Lallesũ, sun kasance mutãnen mũgun aiki, fãsiƙai. = --Qur'an 21:74
    And We admitted him into Our mercy. Indeed, he was of the righteous. <> Kuma Muka shigar da shi a cikin rahamarMu. Lalle ne shĩ, yanã daga sãlihai. = --Qur'an 21:75
    And [mention] Noah, when he called [to Allah] before [that time], so We responded to him and saved him and his family from the great flood. <> Kuma Nũhu, a sa'ad da ya yi kira a gabãni, sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka tsirar da shi da mutãnensa daga baƙin ciki mai girma. = --Qur'an 21:76
    And We saved him from the people who denied Our signs. Indeed, they were a people of evil, so We drowned them, all together. <> Kuma Muka taimake shi daga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata da ãyõyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance mutãnen mugun aiki. Sai Muka nutsar da su gabã ɗaya. = --Qur'an 21:77
    And [mention] David and Solomon, when they judged concerning the field - when the sheep of a people overran it [at night], and We were witness to their judgement. <> Kuma Dãwũda da Sulaimãn sa'ad da suke yin hukunci a cikin sha'anin shũka a lõkacin da tumãkin mutãne suka yi kiĩwon dare a cikinsa. Kuma Mun kasance Mãsu halarta ga hukuncinsu. = --Qur'an 21:78
    And We gave understanding of the case to Solomon, and to each [of them] We gave judgement and knowledge. And We subjected the mountains to exalt [Us], along with David and [also] the birds. And We were doing [that]. <> Sai Muka fahimtar da ita (mats'alar) ga Sulaiman. Kuma dukansu Mun bã su hukunci da ilmi kuma Muka hõre duwatsu tãre da Dãwũda, sunã tasbĩhi, da tsuntsãye. Kuma Mun kasance Mãsu aikatãwa. = --Qur'an 21:79
    And We taught him the fashioning of coats of armor to protect you from your [enemy in] battle. So will you then be grateful? <> Kuma Muka sanar da shi sana'ar wata tufa sabõda ku dõmin ya tsare ku daga makãminku. To, shin, ku mãsu gõdẽwa ne? = --Qur'an 21:80
    And to Solomon [We subjected] the wind, blowing forcefully, proceeding by his command toward the land which We had blessed. And We are ever, of all things, Knowing. <> Kuma (Muka hõre) wa Sulaimãn iska mai tsananin bugãwa, tanã gudãna da umuruinsa zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta. Kuma Mun kasance Masana ga dukkan Kõme. = --Qur'an 21:81
    And of the devils were those who dived for him and did work other than that. And We were of them a guardian. <> Kuma daga Shaiɗannu (Mun hõre) wanda ke nutso sabõda shi. Kuma sunã yin wani aiki baicin wancan. Kuma Mun kasance Mãsu tsaro a gare su. = --Qur'an 21:82
    And [mention] Job, when he called to his Lord, "Indeed, adversity has touched me, and you are the Most Merciful of the merciful." <> Kuma da Ayyũba a sã'ad da ya yi kiran Ubangijinsa, (ya ce:) "Lalle nĩ, cũta ta shãfe ni, alhãli kuwa Kai ne Mafi rahamar mãsu rahama." = --Qur'an 21:83
    So We responded to him and removed what afflicted him of adversity. And We gave him [back] his family and the like thereof with them as mercy from Us and a reminder for the worshippers [of Allah]. <> Sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka kuranye abin da ke a gare shi na cũta, kuma Muka kãwo masa mutãnesa da kwatank wacinsu tãre da su, sabõda rahama daga wurinMu da tunãtarwa ga mãsu ibãda. = --Qur'an 21:84
    And [mention] Ishmael and Idrees and Dhul-Kifl; all were of the patient. <> Kuma da Ismãĩla da Idrĩsa da Zulkifli, dukansu sunã daga mãsu haƙuri. = --Qur'an 21:85
    And We admitted them into Our mercy. Indeed, they were of the righteous. <> Kuma Muka shigar da su a cikin rahamarMu. Lalle ne, sunã daga sãlihai. = --Qur'an 21:86
    And [mention] the man of the fish, when he went off in anger and thought that We would not decree [anything] upon him. And he called out within the darknesses, "There is no deity except You; exalted are You. Indeed, I have been of the wrongdoers." <> Kuma mai kifi a sã'ad da ya tafi yanã mai hushi, sai ya yi zaton cẽwa ba zã Mu ƙuƙunta masa ba. Sai ya yi kira a cikin duffai cẽwa, "Bãbu abĩn bautãwa fãce Kai. Tsarki ya tabbata a gare Ka. Lalle ne nĩ, na kasance daga azzãlumai." = --Qur'an 21:87
    So We responded to him and saved him from the distress. And thus do We save the believers. <> Sai Muka karɓa masa kuma Muka tsĩrar da shi daga baƙin ciki. Kamar haka ne Muke tsĩrarda masu ĩmãni. = --Qur'an 21:88
    And [mention] Zechariah, when he called to his Lord, "My Lord, do not leave me alone [with no heir], while you are the best of inheritors." <> Kuma da Zakariyya a sa'ad da ya kirãyi Ubangijinsa cẽwa, "Ya Ubangiji! Kada Ka bar ni makaɗaici alhãli kuwa Kai ne Mafi alhẽrin mãsu gãdo." = --Qur'an 21:89
    So We responded to him, and We gave to him John, and amended for him his wife. Indeed, they used to hasten to good deeds and supplicate Us in hope and fear, and they were to Us humbly submissive. <> Sai Muka karɓa masa kuma Muka kyautata masa mãtarsa. Lalle ne sũ, sun kasance sunã gudun tsẽre zuwa ga ayyukan alhẽri. Kuma sunã kiran Mu a kan kwaɗayi da fargaba. Kuma sun kasance mãsu saunar (aikata sãɓo) gare Mu. = --Qur'an 21:90
    And [mention] the one who guarded her chastity, so We blew into her [garment] through Our angel [Gabriel], and We made her and her son a sign for the worlds. <> Kuma da wadda ta tsare farJinta daga alfãsha. Sai Muka hũra a cikinta daga rũhinMu. Kuma Muka sanya ta ita da ɗanta wata ãyã ga dũniya. = --Qur'an 21:91
    Indeed this, your religion, is one religion, and I am your Lord, so worship Me. <> Lalle ne wannan ita ce al'ummarku ta zama al'umma guda, kuma Nĩ ne Ubangijinku. Sai ku bauta Mini. = --Qur'an 21:92
    And [yet] they divided their affair among themselves, [but] all to Us will return. <> Kuma suka kakkãtse al'amarinsu a tsakaninsu. Dukan Kõwanensu mãsu Kõmõwa zuwa gare Ni = --Qur'an 21:93
    So whoever does righteous deeds while he is a believer - no denial will there be for his effort, and indeed We, of it, are recorders. <> Dõmin wanda ya aikata daga ayyukan kwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bãbu musu ga aikinsa, kuma Mu Mãsu rubũtãwa gare shi ne. = --Qur'an 21:94
    And there is prohibition upon [the people of] a city which We have destroyed that they will [ever] return <> Kuma hananne ne a kan wata alƙarya da Muka halakar cẽwa lalle sũ, bã su kõmõwa. = --Qur'an 21:95
    Until when [the dam of] Gog and Magog has been opened and they, from every elevation, descend <> Har sa'ad da aka bũde Yãjũju da Mãjũju alhãli kuwa sunã gaggãwa daga kõwane tudun ƙasa. = --Qur'an 21:96
    And [when] the true promise has approached; then suddenly the eyes of those who disbelieved will be staring [in horror, while they say], "O woe to us; we had been unmindful of this; rather, we were wrongdoers." <> Kuma wa'adin nan tabbatacce ya kusanto, sai gã ta idãnun waɗanda suka kãfirta sunã bayyanannu, (sunã cẽwa), "Yã kaitonmu! Haƙĩƙa mun kasance a cikin gafala daga wannan! Ã'a, mun kasance dai mãsu zãlunci!" = --Qur'an 21:97
    Indeed, you [disbelievers] and what you worship other than Allah are the firewood of Hell. You will be coming to [enter] it. <> (A ce musu) "Lalle ne, kũ da abin da kuke bautãwa, baicin Allah makãmashin Jahannama ne. Kũ mãsu tusgãwa gare ta ne." = --Qur'an 21:98
    Had these [false deities] been [actual] gods, they would not have come to it, but all are eternal therein. <> Dã waɗannan (abũbuwanbautãwar) sun kasance abũbuwan bautãwar gaskiya ne, dã ba su tusga mata ba, alhãli kuwa dukansu madawwama a cikinta ne. = --Qur'an 21:99
    For them therein is heavy sighing, and they therein will not hear. <> Sunã da wata hargõwa a cikinta, alhãli kuwa sũ, a cikinta, bã su saurãren kõme. = --Qur'an 21:100
    Indeed, those for whom the best [reward] has preceded from Us - they are from it far removed. <> Lalle ne waɗanda kalmar yabo tã gabãta a garẽ su daga garẽ Mu, waɗannan waɗanda ake nĩsantarwa daga barinta ne. = --Qur'an 21:101
    They will not hear its sound, while they are, in that which their souls desire, abiding eternally. <> Bã su jin sautin mõtsinta alhãli kuwa sũ madawwamãne a cikin abin da rãyukansu suka yi marmarinsa. = --Qur'an 21:102
    They will not be grieved by the greatest terror, and the angels will meet them, [saying], "This is your Day which you have been promised" - <> Firgitar nan mafi girma, bã zã ta baƙantã musu rai ba. Kuma malã'iku na yi musu marãba (sunã cẽwa) "Wannan yininku nẽ wanda kuka kasance anã yi muku wa'adi da shi." = --Qur'an 21:103
    The Day when We will fold the heaven like the folding of a [written] sheet for the records. As We began the first creation, We will repeat it. [That is] a promise binding upon Us. Indeed, We will do it. <> A rãnar da Muke naɗe sãma kamar neɗẽwar takarda ga abũbuwan rubũtãwa kamar yadda Muka fãra a farKon halitta Muke mãyar da ita. Wa'adi ne a Kanmu. Lalle ne Mun kasance Mãsu aikatãwa. = --Qur'an 21:104
    And We have already written in the book [of Psalms] after the [previous] mention that the land [of Paradise] is inherited by My righteous servants. <> Kuma lalle haƙĩƙa Mun rubũta a cikin Littãfi baicin Ambato (Lauhul Mahfũz) cẽwa ƙasã, bayĩNa sãlihai, sunã gãdonta. = --Qur'an 21:105
    Indeed, in this [Qur'an] is notification for a worshipping people. <> Lalle ne a cikin wannan (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, akwai iyarwa (ga maganar da ta gabãta ga waɗansu mutãne mãsu ibãda. = --Qur'an 21:106
    And We have not sent you, [O Muhammad], except as a mercy to the worlds. <> Kuma ba Mu aike ka ba fãce dõmin wata rahama ga talikai. = --Qur'an 21:107
    Say, "It is only revealed to me that your god is but one God; so will you be Muslims [in submission to Him]?" <> Ka ce: "Abin sani kawai, anã yin wahayi zuwa gare ni ne, cẽwa, lalle ne, Abin bautãwarku, Abin bautãwa ne Guda. To shin kũ mãsu mĩƙa wuya ne?" = --Qur'an 21:108
    But if they turn away, then say, "I have announced to [all of] you equally. And I know not whether near or far is that which you are promised. <> Sa'an nan idan suka jũya, to, ka ce: "Nã sanar da ku, a kan daidaita, kuma ban sani ba, shin, abin da ake yi muku wa'adi makusanci ne Kõ kuwa manĩsanci?" = --Qur'an 21:109
    Indeed, He knows what is declared of speech, and He knows what you conceal. <> "Lalle ne Shĩ (Allah) Yanã sanin bayyane daga magana, kuma Yanã sanin abin da kuke ɓõyẽwa. = --Qur'an 21:110
    And I know not; perhaps it is a trial for you and enjoyment for a time." <> "Kuma ban sani ba, tsammãninsa ya zama fitina a gare ku, kõ kuma don jin dãɗi, zuwa ga wani ɗan lõkaci." = --Qur'an 21:111
    [The Prophet] has said, "My Lord, judge [between us] in truth. And our Lord is the Most Merciful, the one whose help is sought against that which you describe." <> Ya ce: "Yã Ubangiji! Ka yi hukunci da gaskiya. Kuma Ubangijinmu Mai rahama ne Wanda ake nẽman taimakonSa a kan abinda kuke siffantãwa." = --Qur'an 21:112
    O mankind, fear your Lord. Indeed, the convulsion of the [final] Hour is a terrible thing. <> Yã ku mutãne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa. Lalle ne girgizar ƙasa ta tsayuwar Sa'a wata aba ce mai girma. = --Qur'an 22:1
    On the Day you see it every nursing mother will be distracted from that [child] she was nursing, and every pregnant woman will abort her pregnancy, and you will see the people [appearing] intoxicated while they are not intoxicated; but the punishment of Allah is severe. <> A rãnar da kuke ganin ta dukan mai shãyar da mãma tanã shagala daga abin da ta shãyar, kuma dukan mai ciki tanã haihuwar cikinta, kuma kanã ganin mutãne sunã mãsu mãyẽ alhãli kuwa su bã mãsu mãye ba, amma azãbar Allah ce mai tsanani. = --Qur'an 22:2
    And of the people is he who disputes about Allah without knowledge and follows every rebellious devil. <> Akwai daga mutãne wanda yake yin musũ ga sha'anin Allah bã da wani ilmi ba, kuma yanã biyar kõwane Shaiɗan mai taurin kai. = --Qur'an 22:3
    It has been decreed for every devil that whoever turns to him - he will misguide him and will lead him to the punishment of the Blaze. <> An wajabta masa cẽwa wanda ya jiɓince shi, to, lalle ne sai ya ɓatar da shi, kuma ya shiryar da shi zuwa ga azãbar sa'ĩr. = --Qur'an 22:4
    O People, if you should be in doubt about the Resurrection, then [consider that] indeed, We created you from dust, then from a sperm-drop, then from a clinging clot, and then from a lump of flesh, formed and unformed - that We may show you. And We settle in the wombs whom We will for a specified term, then We bring you out as a child, and then [We develop you] that you may reach your [time of] maturity. And among you is he who is taken in [early] death, and among you is he who is returned to the most decrepit [old] age so that he knows, after [once having] knowledge, nothing. And you see the earth barren, but when We send down upon it rain, it quivers and swells and grows [something] of every beautiful kind. <> Ya ku mutãne! Idan kun kasance a cikin shakka a Tãshin ¡iyãma, to, lalle ne Mũ, Man halittaku daga turɓaya, sa'an nan kuma daga gudãjin jini, sa'an nan kuma daga taõka wadda ake halittãwa da wadda ba a halittawa dõmin, Mu bayyana muku. Kuma Munã tab batar da abin da Muke so a cikin mahaifa zuwa ga wani ajali ambatacce, sa'an nan kuma Munã fitar da ku kunã jãrĩri, sa'an nan kuma dõmin ku kai ga cikar ƙarfinku. Kuma daga cikin ku akwai wanda ke mutuwa, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwa zuwa ga mafi ƙasƙancin rãyuwa dõmin kada ya san kõme a bãyan ya sani. Kuma kanã ganin ƙasa shiru, sa'an nan idan Muka saukar da ruwa a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura, kuma ta tsirar da tsirrai daga kõwane nau'i mai ban sha'awa. = --Qur'an 22:5
    That is because Allah is the Truth and because He gives life to the dead and because He is over all things competent <> Wancan ne dõmin lalle Allah Shi ne Gaskiya, kuma lalle ne shi Yake rãyar da matattu, kuma lalle Shi Mai ikon yi ne a kan kõme. = --Qur'an 22:6
    And [that they may know] that the Hour is coming - no doubt about it - and that Allah will resurrect those in the graves. <> Kuma lalle ne Sa'ar Tãshin ¡iyãma mai zuwa ce, bãbu shakka a cikinta kuma lalle ne Allah Yanã tãyar da waɗanda suke a cikin ƙaburbura. = --Qur'an 22:7
    And of the people is he who disputes about Allah without knowledge or guidance or an enlightening book [from Him], <> Kuma daga mutãne akwai mai yin musu ga Allah bã da wani ilmi ba kuma bã da wata shiriya ba, kuma bã da wani littãfi mai haskakãwa ba. = --Qur'an 22:8
    Twisting his neck [in arrogance] to mislead [people] from the way of Allah. For him in the world is disgrace, and We will make him taste on the Day of Resurrection the punishment of the Burning Fire [while it is said], <> Yanã mai karkatar da sãshensa dõmin ya ɓatar (da wasu) daga tafarkin Allah! Yanã da wani wulãkanci a dũniya, kuma Munã ɗanɗana masa azãbar gõbara a Rãnar ¡iyãma. = --Qur'an 22:9
    "That is for what your hands have put forth and because Allah is not ever unjust to [His] servants." <> (A ce masa): "Wancan azaba sabõda abin da hannayenka biyu suka gabatar ne, kuma lalle ne Allah bai zama Mai zãlunci ga bãyinSa ba." = --Qur'an 22:10
    And of the people is he who worships Allah on an edge. If he is touched by good, he is reassured by it; but if he is struck by trial, he turns on his face [to the other direction]. He has lost [this] world and the Hereafter. That is what is the manifest loss. <> Kuma daga mutãne akwai mai bauta wa Allah a kan wani gefe. Sa'an nan idan wani alhẽri ya sãme shi, sai ya natsu da shi, kuma idan wata fitina ta sãme shi, sai ya jũya bãya a kan fuskarsa. Yã yi hasãrar dũniya da Lãhira. Waccan ita ce hasãra bayyananna. = --Qur'an 22:11
    He invokes instead of Allah that which neither harms him nor benefits him. That is what is the extreme error. <> Yanã kiran baicin Allah, abin da bã ya cũtarsa da abin da bã ya amfãninsa! waccan ita ce ɓata mai nĩsa. = --Qur'an 22:12
    He invokes one whose harm is closer than his benefit - how wretched the protector and how wretched the associate. <> Yanã kiran wanda yake lalle cũtarwarsa ce mafi kusa daga amfãninsa! Lalle ne, tir da shi ya zama majiɓinci, kuma tir da ya zama abõkin zama! = --Qur'an 22:13
    Indeed, Allah will admit those who believe and do righteous deeds to gardens beneath which rivers flow. Indeed, Allah does what He intends. <> Lalle ne Allah Yanã shigar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a cikin gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Lalle ne Allah Yanã aikata abin da Yake nufi. = --Qur'an 22:14
    Whoever should think that Allah will not support [Prophet Muhammad] in this world and the Hereafter - let him extend a rope to the ceiling, then cut off [his breath], and let him see: will his effort remove that which enrages [him]? <> Wanda ya kasance yanã zaton cẽwa Allah bã zai taimake shi ba a cikin dũniya da Lãhira to sai ya mĩƙa wata igiya zuwa sama, sa'an nan kuma ya yanke ta, sa'an nan ya dũba. Shin, ko lalle kaidinsa zai gusar da abin da yake ji na takaici? = --Qur'an 22:15
    And thus have We sent the Qur'an down as verses of clear evidence and because Allah guides whom He intends. <> Kuma kamar haka Muka saukar da shi (Alƙur'ãni) yanã ãyõyi bayyanannu. Kuma lalle ne Allah Yanã shiryar da wanda Yake nufi. = --Qur'an 22:16
    Indeed, those who have believed and those who were Jews and the Sabeans and the Christians and the Magians and those who associated with Allah - Allah will judge between them on the Day of Resurrection. Indeed Allah is, over all things, Witness. <> Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni da waɗanda suka tũba (Yahũdu) da waɗanda suka karkace (Saba'ãwa) da Nasãra da Majũsãwa da waɗanda suka yi shirka, lalle ne Allah Yanã yin hukunci a tsakãninsu a Ranãr ¡iyãma. Lalle ne Allah Mahalarci ne a kan dukkan kõme. = --Qur'an 22:17
    Do you not see that to Allah prostrates whoever is in the heavens and whoever is on the earth and the sun, the moon, the stars, the mountains, the trees, the moving creatures and many of the people? But upon many the punishment has been justified. And he whom Allah humiliates - for him there is no bestower of honor. Indeed, Allah does what He wills. <> Ashe, ba ka gani ba, lalle Allah, wanda yake a cikin sammai da wanda yake a cikin ƙasa yanã yin sujada a gare shi, da kuma rãna da watã da taurãri da duwãtsu da itãce da dabbõbi, da kuma mãsu yawa daga mutãne? Kuma waɗansu mãsu yawa azãba tã tabbata a kansu. Kuma wanda Allah Ya wulãkantar, to, bã ya da wani mai girmamãwa. Kuma Lalle ne Allah Yanã aikata abin da Yake so. = --Qur'an 22:18
    These are two adversaries who have disputed over their Lord. But those who disbelieved will have cut out for them garments of fire. Poured upon their heads will be scalding water <> waɗannan ƙungiyõyi biyu ne mãsu husũma, sun yi husũma ga sha'anin Ubangijinsu. To, waɗanda suka kãfirta an yanka musu waɗansu tufafi daga wata irin wuta, anã zuba tafasasshen ruwa daga bisa kãwunansu. = --Qur'an 22:19
    By which is melted that within their bellies and [their] skins. <> Da shĩ ake narkar da abin da yake a cikin cikunansu da fãtun jikinsu. = --Qur'an 22:20
    And for [striking] them are maces of iron. <> Kuma sunã da waɗansu gwalmõmin dũka na baƙin ƙarfe. = --Qur'an 22:21
    Every time they want to get out of Hellfire from anguish, they will be returned to it, and [it will be said], "Taste the punishment of the Burning Fire!" <> A kõyaushe suka yi nufin fita daga gare ta, daga baƙin ciki, sai a mayar da su a cikinta, (a ce musu) "Ku ɗanɗani azãbar gõbara." = --Qur'an 22:22
    Indeed, Allah will admit those who believe and do righteous deeds to gardens beneath which rivers flow. They will be adorned therein with bracelets of gold and pearl, and their garments therein will be silk. <> Lalle ne, Allah Yana shigar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a cikin gidãjen Aljanna, ƙoramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, anã ƙawãta su, a cikinsu, da waɗansu mundãye na zĩnãri da lu'u-lu'u. Kuma tufãfinsu a cikinsu alharĩni ne. = --Qur'an 22:23
    And they had been guided [in worldly life] to good speech, and they were guided to the path of the Praiseworthy. <> Kuma an shiryar da su zuwa ga mai kyau na zance kuma an shiryar da su zuwa ga, hanyar wanda ake gode wa. = --Qur'an 22:24
    Indeed, those who have disbelieved and avert [people] from the way of Allah and [from] al-Masjid al-Haram, which We made for the people - equal are the resident therein and one from outside; and [also] whoever intends [a deed] therein of deviation [in religion] or wrongdoing - We will make him taste of a painful punishment. <> Lalle ne waɗanda suka kãfirta kuma suka taushe (mutãne) daga hanyar Allah da masallaci mai alfarma wanda Muka sanya shi ga mutãne alhãli kuwa mazauni a ciki da baƙauye daidai suke kuma wanda ya yi nufin karkatar da gaskiya a cikinsa da zãlunci zã Mu ɗanɗana masa daga wata azãba mai raɗadi. = --Qur'an 22:25
    And [mention, O Muhammad], when We designated for Abraham the site of the House, [saying], "Do not associate anything with Me and purify My House for those who perform Tawaf and those who stand [in prayer] and those who bow and prostrate. <> Kuma a lõkacin da Muka iyãkance wa Ibrãhim wurin ¦akin (Muka ce masa), "Kada ka haɗa kõme da Ni ga bauta, kuma ka tsarkake ¦ãkiNa dõmin mãsu ɗawãfi da mãsu tsayuwa da mãsu ruku'u da mãsu sujada. = --Qur'an 22:26
    And proclaim to the people the Hajj [pilgrimage]; they will come to you on foot and on every lean camel; they will come from every distant pass - <> "Kuma ka yi yẽkuwa ga mutãne da wajabcin Hajji su je maka suna mãsu tafiya da ƙafãfu da kuma a kan kõwane maɗankwarin rãƙumi mãsu zuwa daga kõwane rango mai zurfi." = --Qur'an 22:27
    That they may witness benefits for themselves and mention the name of Allah on known days over what He has provided for them of [sacrificial] animals. So eat of them and feed the miserable and poor. <> "Dõmin su halarci abũbuwan amfãni a gare su, kuma su ambãci sunan Allah a cikin 'yan kwãnuka sanannu sabõda abin da Ya azurta su da shĩ daga dabbõbin jin dãɗi. Sai ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da matsattse matalauci." = --Qur'an 22:28
    Then let them end their untidiness and fulfill their vows and perform Tawaf around the ancient House." <> "Sa'an nan kuma sai su ƙãre ibãdarsu da gusar da ƙazanta, knma sai su cika alkawuransu kuma sai su yi ɗawãfi (sunã gẽwaya) ga ¦ãkin nin 'yantacce." = --Qur'an 22:29
    That [has been commanded], and whoever honors the sacred ordinances of Allah - it is best for him in the sight of his Lord. And permitted to you are the grazing livestock, except what is recited to you. So avoid the uncleanliness of idols and avoid false statement, <> Wancan ne. Kuma wanda ya girmama hukunce-hukuncen Allah to shĩ ne mafĩfĩci a gare shi, a wurin Ubangijinsa. Kuma an halatta muku dabbõbin ni'ima fãce abin da ake karantãwa a kanku. Sabõda haka ku nĩsanci ƙazanta daga gumãka kuma ku nĩsanci ƙazanta daga shaidar zur. = --Qur'an 22:30
    Inclining [only] to Allah, not associating [anything] with Him. And he who associates with Allah - it is as though he had fallen from the sky and was snatched by the birds or the wind carried him down into a remote place. <> Kuna mãsu tsayuwa ga gaskiya dõmin Allah, ba masu yin shirka da Shi ba. Kuma wanda ya yi shirka da Allah, to, yanã kamar abin da ya fãɗo daga sama, sa'an nan tsuntsãye su cafe shi, ko iska ta fãɗa da shi a cikin wani wuri mai nisa. = --Qur'an 22:31
    That [is so]. And whoever honors the symbols of Allah - indeed, it is from the piety of hearts. <> Wancan ne. Kuma wanda ya girmama ibãdõdin Allah, to, lalle ne ita (girmamãwar) tanã daga ayyukan zukãta na ibãda. = --Qur'an 22:32
    For you the animals marked for sacrifice are benefits for a specified term; then their place of sacrifice is at the ancient House. <> Kuna da waɗansu abũbuwan amfãni a cikinta (dabbar hadaya) har ya zuwa ga wani ajali ambatacce, sa'an nan kuma wurin halattãta zuwa ga ¦ãkin 'yantacce ne. = --Qur'an 22:33
    And for all religion We have appointed a rite [of sacrifice] that they may mention the name of Allah over what He has provided for them of [sacrificial] animals. For your god is one God, so to Him submit. And, [O Muhammad], give good tidings to the humble [before their Lord] <> Kuma ga kõwace al'umma Mun sanya ibãdar yanka, dõmin su ambaci sũnan Allah a kan abin da Ya azurta su da shi daga dabbõbin ni'ima. Sa'an nan kuma Abin bautawarku Abin bautawa ne Guda, sai ku sallama Masa. Kuma ka yi bushãra ga mãsu ƙanƙantar da kai. = --Qur'an 22:34
    Who, when Allah is mentioned, their hearts are fearful, and [to] the patient over what has afflicted them, and the establishers of prayer and those who spend from what We have provided them. <> Waɗanda suke idan an ambaci Allah sai zukãtansu su firgita, da mãsu haƙuri a kan abin da ya sãme su, da mãsu tsayar da salla, kuma sunã ciyarwa daga abin da Muka azurta su. = --Qur'an 22:35
    And the camels and cattle We have appointed for you as among the symbols of Allah; for you therein is good. So mention the name of Allah upon them when lined up [for sacrifice]; and when they are [lifeless] on their sides, then eat from them and feed the needy and the beggar. Thus have We subjected them to you that you may be grateful. <> Kuma rãƙuman, Mun sanya su a gare ku, a ibãdõjin Allah. Kunã da wani alhẽri babba a cikinsu. Sai ku ambaci sũnan Allah a kansu sunã tsaye a kan ƙafãfu uku. Sa'an nan idan sãsanninsu suka fãɗi, to, ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da mai wadar zũci da mai bara. Kamar haka Muka hõre muku su, tsammãninku kunã gõdẽwa. = --Qur'an 22:36
    Their meat will not reach Allah, nor will their blood, but what reaches Him is piety from you. Thus have We subjected them to you that you may glorify Allah for that [to] which He has guided you; and give good tidings to the doers of good. <> Nãmõminsu bã za su sãmi Allah ba haka jinainansu amma taƙawa daga gare ku tanã, sãmun Sa. Kamar haka Ya hõre su sabõda ku dõmin ku girmama Allah sabõda shiriyar da Ya yi muku. Kuma ka yi bushãra ga mãsu kyautata yi. = --Qur'an 22:37
    Indeed, Allah defends those who have believed. Indeed, Allah does not like everyone treacherous and ungrateful. <> Lalle ne, Allah Yanã yin faɗa sabõda waɗanda suka yi ĩmãni. Lalle ne Allah bã Ya son dukkan mayaudari, mai yawan kãfirci. = --Qur'an 22:38
    Permission [to fight] has been given to those who are being fought, because they were wronged. And indeed, Allah is competent to give them victory. <> An yi izni ga waɗanda ake yãƙar su da cẽwa lalle an zãlunce su, kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai ĩkon yi ne a kan taimakonsu. = --Qur'an 22:39
    [They are] those who have been evicted from their homes without right - only because they say, "Our Lord is Allah." And were it not that Allah checks the people, some by means of others, there would have been demolished monasteries, churches, synagogues, and mosques in which the name of Allah is much mentioned. And Allah will surely support those who support Him. Indeed, Allah is Powerful and Exalted in Might. <> Waɗanda aka fitina daga gidajensu bã da wani hakki ba fãce sunã cẽwa, Ubangijinmu Allah ne."Kuma ba dõmin tunkuɗẽwar Allah ga mutãne ba, sãshensu da sãshe, haƙĩƙa, da an rũsa sauma'õ'in (Ruhbãnãwa) dã majãmi'õ'in Nasãra da gidãjen ibãdar Yahudu da masallatai waɗanda ake ambatar Allah a cikinsu da yawa. Kuma lalle, haƙĩƙa, Allah Yanã taimakon wanda yake taimakon Sa. Lalle Allah ne haƙĩƙa Mai ƙarfi Mabuwãyi. = --Qur'an 22:40
    [And they are] those who, if We give them authority in the land, establish prayer and give zakah and enjoin what is right and forbid what is wrong. And to Allah belongs the outcome of [all] matters. <> Waɗanda suke idan Muka bã su ĩko a cikin ƙasa sai su tsai da salla, kuma su baybr da zakka kuma su yi umurni da abin da aka sani, kuma su hana daga abin da ba a sani ba. Kuma ãƙibar al'amura ga Allah take. = --Qur'an 22:41
    And if they deny you, [O Muhammad] - so, before them, did the people of Noah and 'Aad and Thamud deny [their prophets], <> Kuma idan sun ƙaryata ka, to lalle haƙĩƙa, mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdawa, sun ƙaryata a gabaninsu. = --Qur'an 22:42
    And the people of Abraham and the people of Lot <> Da mutãnen Ibrahim da mutãnen Lũɗu. = --Qur'an 22:43
    And the inhabitants of Madyan. And Moses was denied, so I prolonged enjoyment for the disbelievers; then I seized them, and how [terrible] was My reproach. <> Da mãsu Madyana, kuma an ƙaryata Mũsã. Sai Na jinkirtawa kãfiran, sa'an nan kuma Na kãma su. To, yãya musũNa (gare su) ya kasance? = --Qur'an 22:44
    And how many a city did We destroy while it was committing wrong - so it is [now] fallen into ruin - and [how many] an abandoned well and [how many] a lofty palace. <> Sa'an nan da yawa daga alƙarya, Muka halaka ta, alhãli kuwa tanã mai zalũnci sai ta zama fãɗaɗɗa a kan rassanta, da yawa daga rĩjiya wadda aka wõfintar, da kuma gidãjen sarauta maɗaukaka. = --Qur'an 22:45
    So have they not traveled through the earth and have hearts by which to reason and ears by which to hear? For indeed, it is not eyes that are blinded, but blinded are the hearts which are within the breasts. <> Shin, to, ba su yi tafiya ba a cikin ƙasa dõmin zukãta waɗanda zã su yi hankali da su da kunnuwa da za su yi saurãre da su su kasance a gare su? Dõmin lalle ne idãnun ba su makanta, amma zukãta waɗanda ke a cikin ƙirãza sũ ke makanta. = --Qur'an 22:46
    And they urge you to hasten the punishment. But Allah will never fail in His promise. And indeed, a day with your Lord is like a thousand years of those which you count. <> Kuma sunã nẽman ka yi gaggãwa da azãba, alhãli kuwa Allah bã zai sãɓa wa'adinSa ba kuma lalle ne, yini ɗaya a wurin Ubangijinka kamar shẽkara dubu yake daga abin da kuke ƙidãyãwa. = --Qur'an 22:47
    And for how many a city did I prolong enjoyment while it was committing wrong. Then I seized it, and to Me is the [final] destination. <> Kuma da yawa daga alƙarya, Na yi jinkirin azãba gare ta (da laifinta) sa'an nan Na kãma ta, kuma zuwa gare Ni makõma take. = --Qur'an 22:48
    Say, "O people, I am only to you a clear warner." <> Ka ce: "Ya ku mutãne! Nĩ wani mai gargaɗi ne kawai zuwa gare ku, mai bayyanawa." = --Qur'an 22:49
    And those who have believed and done righteous deeds - for them is forgiveness and noble provision. <> To, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, sunã da gãfara da arziki na karimci. = --Qur'an 22:50
    But the ones who strove against Our verses, [seeking] to cause failure - those are the companions of Hellfire. <> Kuma waɗanda suka yi aikin ɓãtãwa a cikin ayõyinMu, sunã mãsu gajiyarwa, waɗancan 'yan Jahĩm ne. = --Qur'an 22:51
    And We did not send before you any messenger or prophet except that when he spoke [or recited], Satan threw into it [some misunderstanding]. But Allah abolishes that which Satan throws in; then Allah makes precise His verses. And Allah is Knowing and Wise. <> Kuma ba Mu aika wani manzo ba a gabãninka, kuma ba Mu umurci wani Annabi ba fãce idan ya yi bũri, sai Shaiɗan ya jẽfa (wani abu) a cikin bũrinsa, sa'an nan Allah Ya shãfe abin da Shaiɗan ke jefãwa. Sa'an nan kuma Allah Ya kyautata ãyõyinSa. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima. = --Qur'an 22:52
    [That is] so He may make what Satan throws in a trial for those within whose hearts is disease and those hard of heart. And indeed, the wrongdoers are in extreme dissension. <> Dõmin Ya sanya abin da Shaiɗan ke jẽfãwa ya zama fitina ga waɗanda a cikin zukãtansu akwai cũta, da mãsu ƙẽƙasassun zukãtansu. Kuma lalle ne azzãlumai haƙĩƙa, sunã a cikin sãɓãnimai nĩsa. = --Qur'an 22:53
    And so those who were given knowledge may know that it is the truth from your Lord and [therefore] believe in it, and their hearts humbly submit to it. And indeed is Allah the Guide of those who have believed to a straight path. <> Kuma dõmin waɗanda aka bai wa ilmi su sani lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinka dõmin su yi ĩmãni da shi sabõda zukãtansu su natsu gare shi. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai shiryar da waɗanda suka yi ĩmãni ne zuwa ga hanya madaidaiciya. = --Qur'an 22:54
    But those who disbelieve will not cease to be in doubt of it until the Hour comes upon them unexpectedly or there comes to them the punishment of a barren Day. <> Kuma waɗanda suka kãfirta bã zã su gushe ba sunã a cikin shakka daga gare shi, har Sa'a ta jẽ musu bisa ga abke, kõ kuwa azãbar wani yini bakarãre ta jẽ musu. = --Qur'an 22:55
    [All] sovereignty that Day is for Allah; He will judge between them. So they who believed and did righteous deeds will be in the Gardens of Pleasure. <> Mulki a rãnar nan ga Allah yake, Yanã hukunci a tsakãninsu. To, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã a cikin gidãjen Aljannar ni'ima. = --Qur'an 22:56
    And they who disbelieved and denied Our signs - for those there will be a humiliating punishment. <> Kuma waɗandra suka kãfirta kuma suka ƙaryata, game da ãyõyinMu, to, waɗannan sunã da azãba mai wulãkantarwa. = --Qur'an 22:57
    And those who emigrated for the cause of Allah and then were killed or died - Allah will surely provide for them a good provision. And indeed, it is Allah who is the best of providers. <> Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin tafarkin Allah sa'an nan kuma aka kashe su, kõ suka mutu, lalle ne Allah Yanã azurta su da arziki mai kyau. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu azurtãwa. = --Qur'an 22:58
    He will surely cause them to enter an entrance with which they will be pleased, and indeed, Allah is Knowing and Forbearing. <> Lalle ne, Yanã shigar da su a wata mashiga wadda zã su yarda da ita. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa Masani ne, Mai haƙuri. = --Qur'an 22:59
    That [is so]. And whoever responds [to injustice] with the equivalent of that with which he was harmed and then is tyrannized - Allah will surely aid him. Indeed, Allah is Pardoning and Forgiving. <> Wancan! Kuma wanda ya rãma azãba da misãlin abin da aka yi masa, sa'an nan kuma aka zãlunce shi, lalle ne Allah Yanã taimakon sa. Lalle ne Allah haƙĩƙa Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara. = --Qur'an 22:60
    That is because Allah causes the night to enter the day and causes the day to enter the night and because Allah is Hearing and Seeing. <> Wancan! sabõda Allah Yanã shigar da dare a cikin yini, kuma Yanã shigar da yini a cikin dare, kuma lalle, Allah Mai jĩ ne, Mai gani. = --Qur'an 22:61
    That is because Allah is the Truth, and that which they call upon other than Him is falsehood, and because Allah is the Most High, the Grand. <> Wancan! sabõda lalle ne Allah, shĩ ne Gaskiya, kuma lalle ne, abin da suke kira waninSa shi ne ƙarya. Kuma lalle ne Allah, Shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma. = --Qur'an 22:62
    Do you not see that Allah has sent down rain from the sky and the earth becomes green? Indeed, Allah is Subtle and Acquainted. <> Ashe, ba ka gani ba, lalle ne, Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sai ƙasa ta wãyi gari kõriya? Lalle Allah Mai tausasawa ne, Mai ƙididdigewa. = --Qur'an 22:63
    To Him belongs what is in the heavens and what is on the earth. And indeed, Allah is the Free of need, the Praiseworthy. <> Abin da ke a cikin sammai, da abin da ke a cikin ƙasa, Nasa ne, kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Shi ne wadatacce, Gõdadde. = --Qur'an 22:64
    Do you not see that Allah has subjected to you whatever is on the earth and the ships which run through the sea by His command? And He restrains the sky from falling upon the earth, unless by His permission. Indeed Allah, to the people, is Kind and Merciful. <> Shin ba ka gani ba, lalle ne Allah Ya hõre muku abin da yake a cikin ƙasa, kuma jirãge sunã gudãna a cikin tẽku, da umurninSa kuma Yanã riƙe sama dõmin kada ta fãɗi a kan ƙasa fãce da izninsa? Lalle ne Allah ga mutãne haƙĩƙa, Mai tausayi ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 22:65
    And He is the one who gave you life; then He causes you to die and then will [again] give you life. Indeed, mankind is ungrateful. <> Kuma shĩ ne wanda Ya rãya ku, sa'an nan kuma Yanã matar da ku, sa'an nan kuma Yanã rãyar da ku. Lalle mutum, haƙĩƙa, mai kãfirci ne. = --Qur'an 22:66
    For every religion We have appointed rites which they perform. So, [O Muhammad], let the disbelievers not contend with you over the matter but invite them to your Lord. Indeed, you are upon straight guidance. <> Ga kõwace al'umma Mun sanya wurin yanka, su ne masu yin baiko gare Shi, sabõda haka, kada su yi maka jãyayya a cikin al'amarin (hadaya). Kuma ka yi kira zuwa ga Ubangijinka lalle kai kana a kan shiriya madaidaiciya. = --Qur'an 22:67
    And if they dispute with you, then say, "Allah is most knowing of what you do. <> Kuma idan sun yi maka jidãli, sai ka ce: "Allah ne Mafi sani game da abin da kuke aikatãwa." = --Qur'an 22:68
    Allah will judge between you on the Day of Resurrection concerning that over which you used to differ." <> "Allah ne zai yi hukunci a tsakãninku, a Rãnar ¡iyãma a cikin abin da kuka kasance a cikinsa kunã sãɓawa jũna." = --Qur'an 22:69
    Do you not know that Allah knows what is in the heaven and earth? Indeed, that is in a Record. Indeed that, for Allah, is easy. <> Ashe, ba ka sani ba, lalle ne Allah Yanã sanin abin da yake a cikin sama da ƙasa? Lalle ne wancan yanã cikin Littafi lalle wancan ga Allah mai sauƙi ne. = --Qur'an 22:70
    And they worship besides Allah that for which He has not sent down authority and that of which they have no knowledge. And there will not be for the wrongdoers any helper. <> Kuma sunã bautãwa baicin Allah, abin da (Allah) bai saukar da wani dalili ba game da shi, kuma abin da bã su da wani ilmi game da shi, kuma bãbu wani mai taimako ga azzãlumai. = --Qur'an 22:71
    And when Our verses are recited to them as clear evidences, you recognize in the faces of those who disbelieve disapproval. They are almost on the verge of assaulting those who recite to them Our verses. Say, "Then shall I inform you of [what is] worse than that? [It is] the Fire which Allah has promised those who disbelieve, and wretched is the destination." <> Kuma idan anã karanta ãyõyinMu bayyanannu a kansu kanã sanin abin ƙyãma a cikin fuskõkin waɗanda suka kãfirta sunã kusa su yi danƙa ga waɗanda ke karãtun ayõyinMu a kansu. Ka ce: "Shin to in gaya muku abin da yake mafi sharri daga wannan? (Ita ce) Wuta." Allah Yã yi alkawarinta ga waɗanda suka kãfirta. Kuma makõmarsu ta mũnana. = --Qur'an 22:72
    O people, an example is presented, so listen to it. Indeed, those you invoke besides Allah will never create [as much as] a fly, even if they gathered together for that purpose. And if the fly should steal away from them a [tiny] thing, they could not recover it from him. Weak are the pursuer and pursued. <> "Ya ku mutãne! An buga wani misãli, sai ku saurãra zuwa gare shi. Lalle ne waɗanda kuke kira baicin Allah, bã zã su halitta ƙudã ba, kõ da sun tãru gare shi, kuma idan ƙudãn ya ƙwãce musu wani abu, bã zã su kuɓutar da shi ba daga gare shi. Mai nẽma da wanda ake nẽman gare shi sun raunana." = --Qur'an 22:73
    They have not appraised Allah with true appraisal. Indeed, Allah is Powerful and Exalted in Might. <> Ba su ƙaddara wa Allah hakkin girmanSa ba. Lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi. = --Qur'an 22:74
    Allah chooses from the angels messengers and from the people. Indeed, Allah is Hearing and Seeing. <> Allah nã zãɓen Manzanni daga malã'iku kuma daga mutãne. Lalle Allah, Mai ji ne, Mai gani. = --Qur'an 22:75
    He knows what is [presently] before them and what will be after them. And to Allah will be returned [all] matters. <> Yanã sanin abin da ke gaba gare su da abin da ke bãyansu, kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'amura. = --Qur'an 22:76
    O you who have believed, bow and prostrate and worship your Lord and do good - that you may succeed. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi rukũ'i, kuma ku yi sujada, kuma ku bauta wa Ubangijinku, kuma ku aikata alhẽri, tsammãninku, ku sami babban rabo. = --Qur'an 22:77
    And strive for Allah with the striving due to Him. He has chosen you and has not placed upon you in the religion any difficulty. [It is] the religion of your father, Abraham. Allah named you "Muslims" before [in former scriptures] and in this [revelation] that the Messenger may be a witness over you and you may be witnesses over the people. So establish prayer and give zakah and hold fast to Allah. He is your protector; and excellent is the protector, and excellent is the helper. <> Kuma ku yi jihãdi a cikin (al'amarin) Allah, hakkin JihãdinSa. shĩ ne Ya zãɓe ku alhãli kuwa bai sanya wani ƙunci ba a kanku a cikin addĩni. Bisa ƙudurcẽwar ubanku Ibrãhĩm, shĩ ne ya yi muku sũna Musulmi daga gabãnin haka. Kuma a cikin wannan (Littãfi ya yi muku sũna Musulmi), dõmin Manzo ya kasance mai shaida a kanku, kũ kuma ku kasancemãsu shaida a kan mutãne. Sabõda haka ku tsayar da salla kuma ku bãyar da zakka kuma ku amince da Allah, Shi ne Majiɓincinku. Sãbõda haka mãdalla da Shi Ya zama Majiɓinci, mãdalla da Shi ya zama Mai taimako. = --Qur'an 22:78
    Certainly will the believers have succeeded: <> Lalle ne, Mũminai sun sãmi babban rabõ. = --Qur'an 23:1
    They who are during their prayer humbly submissive <> Waɗanda suke a cikin sallarsu mãsu tawãli'u ne. = --Qur'an 23:2
    And they who turn away from ill speech <> Kuma waɗanda suke, sũdaga barin yasassar magana, mãsu kau da kai ne. = --Qur'an 23:3
    And they who are observant of zakah <> Kuma waɗanda suke ga zakka mãsu aikatãwa ne. = --Qur'an 23:4
    And they who guard their private parts <> Kuma waɗanda suke ga farjõjinsu mãsu tsarẽwa ne. = --Qur'an 23:5
    Except from their wives or those their right hands possess, for indeed, they will not be blamed - <> Fãce a kan mãtan aurensu, kõ kuwa abin da hannayen dãmansu suka mallaka to lalle sũ bã waɗanda ake zargi, ba, ne. = --Qur'an 23:6
    But whoever seeks beyond that, then those are the transgressors - <> Sabõda haka wanda ya nẽmi abin da ke bãyan wancan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙẽtarẽwar haddi. = --Qur'an 23:7
    And they who are to their trusts and their promises attentive <> Kuma waɗanda suke, sũga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne. = --Qur'an 23:8
    And they who carefully maintain their prayers - <> Kuma da waɗanda suke, sũ a kan sallõlinsu sunã tsarẽwa. = --Qur'an 23:9
    Those are the inheritors <> Waɗannan, sũ ne magãda. = --Qur'an 23:10
    Who will inherit al-Firdaus. They will abide therein eternally. <> Waɗanda suke gãdõn (Aljannar) Firdausi, su a cikinta madawwama ne. = --Qur'an 23:11
    And certainly did We create man from an extract of clay. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta mutum daga wani tsantsa daga lãka. = --Qur'an 23:12
    Then We placed him as a sperm-drop in a firm lodging. <> Sa'an nan kuma Muka sanya shi, ɗigon maniyyi a cikin matabbata natsattsiya. = --Qur'an 23:13
    Then We made the sperm-drop into a clinging clot, and We made the clot into a lump [of flesh], and We made [from] the lump, bones, and We covered the bones with flesh; then We developed him into another creation. So blessed is Allah, the best of creators. <> Sa'an nan kuma Muka halitta shi gudan jini, sa'an nan Muka halitta gudan jinin tsõka, sa'an nan Muka halitta tsõkar ta zama ƙasũsuwa, sa'an nan Muka tufãtar da ƙasũsuwan da wani nãma sa'an nan kuma Muka ƙãga shi wata halitta dabam. Sabõda haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne Mafi kyaun mãsu halittawa. = --Qur'an 23:14
    Then indeed, after that you are to die. <> Sa'an nan kuma ku, bãyan wannan, lalle ne masu mutuwa ne. = --Qur'an 23:15
    Then indeed you, on the Day of Resurrection, will be resurrected. <> Sa'an nan kuma lalle ne kũ a Rãnar ¡iyãma, za a iãyar da ku, = --Qur'an 23:16
    And We have created above you seven layered heavens, and never have We been of [Our] creation unaware. <> Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta, a samanku, hanyõyi bakwai, kuma ba Mu kasance, daga barin halittar, Mãsu shagala ba. = --Qur'an 23:17
    And We have sent down rain from the sky in a measured amount and settled it in the earth. And indeed, We are Able to take it away. <> Muka saukar da ruwa daga sama bisa gwargwado, sa'an nan Muka zaunar da shi a cikin ƙasa alhãli, lalle ne Mũ, a kan tafiyar da shi, Mãsu iyãwa ne. = --Qur'an 23:18
    And We brought forth for you thereby gardens of palm trees and grapevines in which for you are abundant fruits and from which you eat. <> Sai Muka ƙãga muku, game da shi (ruwan), gõnaki daga daĩnai da inabõbi, kunã da, a cikinsu, 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, kuma daga gare su kuke ci. = --Qur'an 23:19
    And [We brought forth] a tree issuing from Mount Sinai which produces oil and food for those who eat. <> Da wata itãciya, tanã fita daga dũtsin Sainã'a, tanã tsira da man shãfãwa, da man miya dõmin masu cĩ. = --Qur'an 23:20
    And indeed, for you in livestock is a lesson. We give you drink from that which is in their bellies, and for you in them are numerous benefits, and from them you eat. <> Kuma lalle ne kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'imõmi Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikinsu, kuma kunã da a cikinsu abũbuwan amfãni mãsu yawa, kuma daga gare su kuke cĩ = --Qur'an 23:21
    And upon them and on ships you are carried. <> Kuma a kansu da a kan jirgin ruwa ake ɗaukar ku. = --Qur'an 23:22
    And We had certainly sent Noah to his people, and he said, "O my people, worship Allah; you have no deity other than Him; then will you not fear Him?" <> Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnensa, sai ya ce: "Yã mutãnẽna! Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa waninsa. Shin, to, bã za ku yi taƙawa ba?" = --Qur'an 23:23
    But the eminent among those who disbelieved from his people said, "This is not but a man like yourselves who wishes to take precedence over you; and if Allah had willed [to send a messenger], He would have sent down angels. We have not heard of this among our forefathers. <> Sai mashãwarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: "Wannan ba kõwa ba ne, fãce mutum misãlinku, yanã nufin ya ɗaukaka a kanku. Dã Allah Yã so, lalle ne dã Yã saukar da Malã'iku, Ba muji (kõme) ba, game da wannan, a cikin ubanninmu na farko." = --Qur'an 23:24
    He is not but a man possessed with madness, so wait concerning him for a time." <> "Shi bai zamo kõwa ba fãce wani namiji ne, a gare shi akwai hauka, sai ku yi jinkiri da shi har wani lõkaci." = --Qur'an 23:25
    [Noah] said, "My Lord, support me because they have denied me." <> Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimakeni sabõda sun ƙaryatani." = --Qur'an 23:26
    So We inspired to him, "Construct the ship under Our observation, and Our inspiration, and when Our command comes and the oven overflows, put into the ship from each [creature] two mates and your family, except those for whom the decree [of destruction] has proceeded. And do not address Me concerning those who have wronged; indeed, they are to be drowned. <> Sai Muka yi wahayi zuwa gare shi. "Ka sana'anta jirgin bisa ga idonMu, da wahayinMu. To, idan umuminMu ya jẽ, kuma tandã ta ɓuɓɓuga da ruwa, to, ka shigar a cikinta daga kõme, ma'aura biyu, da iyãlanka, sai wanda Magana ta gabãta a kansa, daga gare su, kuma kada ka rõƙẽ Ni (sabõda wani) a cikin waɗanda suka yi zãlunci, lalle ne sũ waɗanda ake nutsarwa ne. = --Qur'an 23:27
    And when you have boarded the ship, you and those with you, then say, 'Praise to Allah who has saved us from the wrongdoing people.' <> "Sa'an nan idan ka daidaitu kai da waɗanda ke tãre da kai a kan jirgin, sai ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya tsĩrar damu daga mutãne azzãlumai." = --Qur'an 23:28
    And say, 'My Lord, let me land at a blessed landing place, and You are the best to accommodate [us].' " <> "Kuma ka ce: 'Ya Ubangijĩna! Ka saukar da ni, saukarwa mai albarka. Kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu saukarwa.'" = --Qur'an 23:29
    Indeed in that are signs, and indeed, We are ever testing [Our servants]. <> Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi, ko da yake Mun kasance, haƙẽƙa' Mãsu jarrabãwa. = --Qur'an 23:30
    Then We produced after them a generation of others. <> Sa'an nan kuma Muka ƙãga wani ƙarni na waɗansu dabam daga bãyansu. = --Qur'an 23:31
    And We sent among them a messenger from themselves, [saying], "Worship Allah; you have no deity other than Him; then will you not fear Him?" <> Sai Muka aika a cikinsu Manzo daga gare su. "Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa, sai Shi. Shin to, bã zã ku yi taƙawa ba?" = --Qur'an 23:32
    And the eminent among his people who disbelieved and denied the meeting of the Hereafter while We had given them luxury in the worldly life said, "This is not but a man like yourselves. He eats of that from which you eat and drinks of what you drink. <> Mashãwarta daga mutãnensa, waɗanda suka kãfirta kuma suka ƙaryata game da haɗuwa da Lãhira, kuma Muka ni'imtar da su a cikin rãyuwar dũniya, suka ce: "Wannan bã kõwa ba fãce wani mutum ne kamarku, yanã cĩ daga abin da kuke cĩ daga gare shi, kuma yanã shã daga abin da kuke shã." = --Qur'an 23:33
    And if you should obey a man like yourselves, indeed, you would then be losers. <> "Kuma lalle ne idan kun yi ɗã' a ga mutum misãlinku, lalle ne, a lõkacin nan, haƙĩƙa, kũ mãsu hasãra ne." = --Qur'an 23:34
    Does he promise you that when you have died and become dust and bones that you will be brought forth [once more]? <> "Shin, yanã yi muku wa'adin (cẽwa) lalle kũ, idan kun mutu kuma kuka kasance turɓãya da ɓasũsuwa lalle ne kũ waɗanda ake fitarwa ne?" = --Qur'an 23:35
    How far, how far, is that which you are promised. <> "Faufau faufau ga abin da ake yi muku wa'adi da shi." = --Qur'an 23:36
    Life is not but our worldly life - we die and live, but we will not be resurrected. <> "Rãyuwa ba ta zama ba fãce rãyuwarmu ta dũniya, munã mutuwa kuma munã rãyuwa, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba." = --Qur'an 23:37
    He is not but a man who has invented a lie about Allah, and we will not believe him." <> "Bai zama kõwa ba fãce namiji, ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma ba mu zama, sabõda shi, mãsu ĩmãni ba." = --Qur'an 23:38
    He said, "My Lord, support me because they have denied me." <> Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni sabõda sun ƙaryatã ni." = --Qur'an 23:39
    [Allah] said, "After a little, they will surely become regretful." <> Ya ce: "Daga abu kaɗan, lalle ne zã su wãyi gari sunã mãsu nadãma." = --Qur'an 23:40
    So the shriek seized them in truth, and We made them as [plant] stubble. Then away with the wrongdoing people. <> Sai tsãwa ta kãma su da gaskiya, sai Muka sanya su tunkuɓa. Sabõda haka nĩsa ya tabbataga mutãne azzãlumai! = --Qur'an 23:41
    Then We produced after them other generations. <> Sa'an kuma Muka ƙãga halittar wasu ƙarnõni dabam daga bayãnsu. = --Qur'an 23:42
    No nation will precede its time [of termination], nor will they remain [thereafter]. <> Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba. = --Qur'an 23:43
    Then We sent Our messengers in succession. Every time there came to a nation its messenger, they denied him, so We made them follow one another [to destruction], and We made them narrations. So away with a people who do not believe. <> Sa'an nan kuma Muka aika da ManzanninMu jẽre a kõda yaushe Manzon wata al'umma ya jẽ mata, sai su ƙaryata shi, sabõda haka Muka biyar da sãshensu ga sãshe, kuma Muka sanya su lãbãrun hĩra. To, nĩsa ya tabbata ga mutãne (waɗanda) bã su yin ĩmãni! = --Qur'an 23:44
    Then We sent Moses and his brother Aaron with Our signs and a clear authority <> Sa'an nan kuma Muka aika Mũsã da ɗan'uwansa Hãrũna, game da ãyõyinMu da, dalĩli bayyananne. = --Qur'an 23:45
    To Pharaoh and his establishment, but they were arrogant and were a haughty people. <> Zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka kangara, alhãli sun kasance mutãne ne marinjãya. = --Qur'an 23:46
    They said, "Should we believe two men like ourselves while their people are for us in servitude?" <> Sai suka ce: "Shin, zã Mu yi ĩmãni sabõda wasu mutãne biyu misãlinmu, alhãli kuwa mutãnensu a gare mu, mãsu bauta ne." = --Qur'an 23:47
    So they denied them and were of those destroyed. <> Sai suka ƙaryata su sabõda haka suka kasance halakakku. = --Qur'an 23:48
    And We certainly gave Moses the Scripture that perhaps they would be guided. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi tsammaninsu zã su shiryu. = --Qur'an 23:49
    And We made the son of Mary and his mother a sign and sheltered them within a high ground having level [areas] and flowing water. <> Kuma Mun sanya ¦an Maryama, shi da uwarsa wata ãyã Kuma Muka tattara su zuwa ga wani tsauni ma'abũcin natsuwa da marẽmari. = --Qur'an 23:50
    [Allah said], "O messengers, eat from the good foods and work righteousness. Indeed, I, of what you do, am Knowing. <> Yã ku Manzanni! Ku ci daga abũbuwa mãsu dãɗi kuma ku aikata aikin ƙwarai. Lalle Nĩga abin da kuke aikatãwa, Masani ne. = --Qur'an 23:51
    And indeed this, your religion, is one religion, and I am your Lord, so fear Me." <> Kuma lalle ne, wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Nĩ, Ubangijinku ne, sai ku bĩ Ni da taƙawa. = --Qur'an 23:52
    But the people divided their religion among them into sects - each faction, in what it has, rejoicing. <> Sai (al'ummar) suka yanyanke al'amarinsu a tsakãninsu guntu-guntu, kõwace ƙungiya sunã mãsu farin ciki da abin da yake a gare su. = --Qur'an 23:53
    So leave them in their confusion for a time. <> To, ka bar su a cikin ɓatarsu har a wani lõkaci. = --Qur'an 23:54
    Do they think that what We extend to them of wealth and children <> Shin, sunã zaton cẽwa abin da Muke taimakon su da shi daga dũkiya da ɗiya, = --Qur'an 23:55
    Is [because] We hasten for them good things? Rather, they do not perceive. <> Munã yi musu gaggãwa ne a cikin alhẽrõri? = --Qur'an 23:56
    Indeed, they who are apprehensive from fear of their Lord <> Lalle ne waɗanda suke mãsu sauna sabo da tsõron Ubangijinsu, = --Qur'an 23:57
    And they who believe in the signs of their Lord <> Da waɗanda suke, game da ãyõyin Ubangijinsu sunã ĩmãni, = --Qur'an 23:58
    And they who do not associate anything with their Lord <> Da waɗanda suke game da Ubangijinsu bã su yin shirki, = --Qur'an 23:59
    And they who give what they give while their hearts are fearful because they will be returning to their Lord - <> Da waɗanda ke bãyar da abin da suka bãyar, alhãli kuwa zukãtansu sunã tsõrace dõmin sunã kõmãwa zuwa ga Ubangijinsu, = --Qur'an 23:60
    It is those who hasten to good deeds, and they outstrip [others] therein. <> Waɗancan sunã gaggãwar tsẽre a cikin ayyukan alhẽri, alhãli kuwa sunã mãsu tsẽrẽwa zuwa gare su (ayyukan alhẽri). = --Qur'an 23:61
    And We charge no soul except [with that within] its capacity, and with Us is a record which speaks with truth; and they will not be wronged. <> Kuma bã Mu kallafa wa rai fãce abin iyawarsa, kuma a wurinMu akwai wani Littãfi wanda yake magana da gakiya, kuma sũ bã a zãluntar su. = --Qur'an 23:62
    But their hearts are covered with confusion over this, and they have [evil] deeds besides disbelief which they are doing, <> Ã'a, zukãtansu sunã cikin jãhilci daga wannan (magana), kuma sunã da waɗansu ayyuka, baicin wancan, sũ a gare su, mãsu aikatãwa ne. = --Qur'an 23:63
    Until when We seize their affluent ones with punishment, at once they are crying [to Allah] for help. <> Har idan Mun kãma mani'imtansu da azãba, sai gã su sunã hargõwa. = --Qur'an 23:64
    Do not cry out today. Indeed, by Us you will not be helped. <> Kada ku yi hargowa a yau, lalle ne kũ, daga gare Mu bã a taimakon ku. = --Qur'an 23:65
    My verses had already been recited to you, but you were turning back on your heels <> Lalle ne, ãyõyĩNa sun kasance anã karãtun su a kanku, sai kuka kasance, a kan dugãduganku, kunã kõmãwa bãya. = --Qur'an 23:66
    In arrogance regarding it, conversing by night, speaking evil. <> Kunã mãsu girman kai gare shi (Annabi), da hĩrã kunã alfãsha. = --Qur'an 23:67
    Then have they not reflected over the Qur'an, or has there come to them that which had not come to their forefathers? <> Shin fa, ba su yi ta'ammalin maganar (Alƙur'ãni) ba, kõ abin da bai jẽ wa ubanninsu na farko ba ne ya jẽ musu? = --Qur'an 23:68
    Or did they not know their Messenger, so they are toward him disacknowledging? <> Kõ ba su san Manzonsu ba ne dõmin haka suke mãsu musu a gare shi? = --Qur'an 23:69
    Or do they say, "In him is madness?" Rather, he brought them the truth, but most of them, to the truth, are averse. <> Kõ sunã cẽwa, "Akwai hauka gare shi?" Ã'a, yã zo musu da gaskiya, alhãli kuwa mafi yawansu, ga gaskiya, mãsu ƙi ne. = --Qur'an 23:70
    But if the Truth had followed their inclinations, the heavens and the earth and whoever is in them would have been ruined. Rather, We have brought them their message, but they, from their message, are turning away. <> Kuma dã gaskiya (Alƙur'ãni) yã bi son zuciyoyinsu, haƙĩƙa dã sammai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sun ɓãci. Ã'a, Mun tafo musu da ambaton (darajar) su, sa'an nan sũ daga barin ambaton su mãsu bijirẽwa ne, bijirẽwa. = --Qur'an 23:71
    Or do you, [O Muhammad], ask them for payment? But the reward of your Lord is best, and He is the best of providers. <> Kõ kanã tambayar su wani harãji ne (a kan iyar da Manzanci a gare su)? To, harãjin Ubangijinka ne mafi alhẽri kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu ciyarwa. = --Qur'an 23:72
    And indeed, you invite them to a straight path. <> Kuma lalle ne kai haƙĩƙa kanã kiran su zuwa ga hanya madaidaiciya. = --Qur'an 23:73
    But indeed, those who do not believe in the Hereafter are deviating from the path. <> Kuma lalle waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba mãsu karkacẽwa daga hanya ne. = --Qur'an 23:74
    And even if We gave them mercy and removed what was upon them of affliction, they would persist in their transgression, wandering blindly. <> Kuma dã Mun ji tausayinsu, kuma Muka kuranye musu abin da yake tãre da su na cũta, lalle ne dã sun yi zurfi a cikin ɓatarsu, sunã ɗimuwa. = --Qur'an 23:75
    And We had gripped them with suffering [as a warning], but they did not yield to their Lord, nor did they humbly supplicate, [and will continue thus] <> Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã kãma su da azãba sai dai ba su saukar da kai ba, ga Ubangijinsu, kama bã su yin tawãli'u. = --Qur'an 23:76
    Until when We have opened before them a door of severe punishment, immediately they will be therein in despair. <> Har idan Mun bũɗe, akansu, wata ƙõfa mai azãba mai tsanani sai gã su a cikinta sunã mãsu mugi. = --Qur'an 23:77
    And it is He who produced for you hearing and vision and hearts; little are you grateful. <> Kuma Shi ne Wanda Ya ƙãga halittar ji da gani da zukãta dominku. Kaɗan ƙwarai kuke gõdẽwa. = --Qur'an 23:78
    And it is He who has multiplied you throughout the earth, and to Him you will be gathered. <> Kuma Shĩ ne Ya halitta ku a cikin ƙasa, kuma zuwa gare Shi ake tãyar da ku. = --Qur'an 23:79
    And it is He who gives life and causes death, and His is the alternation of the night and the day. Then will you not reason? <> Kuma Shĩ ne Wanda Yake rãyarwa, kuma Yanã matarwa, kuma a gare Shi ne sãɓawar dare da yini take. Shin, to, bã zã ku hankalta ba? = --Qur'an 23:80
    Rather, they say like what the former peoples said. <> Ã'a, sun faɗi misãlin abin da na farko suka faɗa. = --Qur'an 23:81
    They said, "When we have died and become dust and bones, are we indeed to be resurrected? <> Suka ce: "Shin idan mun mutu kuma muka kasance turɓaya da ƙasũsuwa shin lal1e ne mu haƙĩƙa waɗanda ake tãyarwa ne? = --Qur'an 23:82
    We have been promised this, we and our forefathers, before; this is not but legends of the former peoples." <> "Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi, mũ da ubanninmu ga wannan a gabãni, wannan abu bai zama kõme ba, fãce tãtsũniyõyin na farko." = --Qur'an 23:83
    Say, [O Muhammad], "To whom belongs the earth and whoever is in it, if you should know?" <> Ka ce: "Wane ne da mulkin ƙasa da wanda ke a cikinta, idan kun kasance kunã sani?" = --Qur'an 23:84
    They will say, "To Allah." Say, "Then will you not remember?" <> Zã su ce: "Ta Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku yi tunãni ba?" = --Qur'an 23:85
    Say, "Who is Lord of the seven heavens and Lord of the Great Throne?" <> Ka ce: "Wãne ne Ubangijin sammai bakwai kuma Ubangijin Al'arshi mai girma?" = --Qur'an 23:86
    They will say, "[They belong] to Allah." Say, "Then will you not fear Him?" <> Zã su ce: "Na Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku bĩ Shi da taƙawa ba?" = --Qur'an 23:87
    Say, "In whose hand is the realm of all things - and He protects while none can protect against Him - if you should know?" <> Ka ce: "Wãne ne ga hannunsa mallakar kõwane abu take alhãli kuwa shi yanã tsarẽwar wani, kuma ba a tsare kõwa daga gare shi, idan kun kasance kunã sani?" = --Qur'an 23:88
    They will say, "[All belongs] to Allah." Say, "Then how are you deluded?" <> Zã su ce: "Ga Allah yake." Ka ce: "To, yãya ake sihirce ku?" = --Qur'an 23:89
    Rather, We have brought them the truth, and indeed they are liars. <> Ã'a, Mun zo musu da gaskiya, kuma lalle ne sũ, haƙĩƙa, maƙaryata ne. = --Qur'an 23:90
    Allah has not taken any son, nor has there ever been with Him any deity. [If there had been], then each deity would have taken what it created, and some of them would have sought to overcome others. Exalted is Allah above what they describe [concerning Him]. <> Allah bai riƙi wani abin haihuwa ba, kuma bãbu wani abin bautãwa tãre da Shi. Idan haka ne (akwai abin bautawa tare da Shi), lalle ne dã kõwane abin bautawar ya tafi da abin da ya halitta, kuma lalle ne, dã waɗansu sun rinjãya a kan waɗansu, tsarki ya tabbata ga Allah, daga abin da suke siffantãwa. = --Qur'an 23:91
    [He is] Knower of the unseen and the witnessed, so high is He above what they associate [with Him]. <> Masanin ɓõye da bayyane. sa'an nan Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka. = --Qur'an 23:92
    Say, [O Muhammad], "My Lord, if You should show me that which they are promised, <> Ka ce: "Yã Ubangijina! Ko dai Ka nũna mini abin da ake yi musu wa'adi da shi." = --Qur'an 23:93
    My Lord, then do not place me among the wrongdoing people." <> "Yã Ubangijina, to, kada Ka sanya ni a cikin mutãne azzãlumai." = --Qur'an 23:94
    And indeed, We are able to show you what We have promised them. <> Kuma lalle ne Mũ haƙĩƙa Mãsu iyawa ne a kan Mu nũna maka abin da Muke yi musu wa'adi da shi. = --Qur'an 23:95
    Repel, by [means of] what is best, [their] evil. We are most knowing of what they describe. <> Ka tunkuɗe cũta da wadda take ita ce mafi kyau. Mũ neMafi sani game da abin da suke siffantãwa. = --Qur'an 23:96
    And say, "My Lord, I seek refuge in You from the incitements of the devils, <> Ka ce: "Yã Ubangijĩna, inã nẽman tsari da Kai daga fizge-fizgen Shaiɗãnu." = --Qur'an 23:97
    And I seek refuge in You, my Lord, lest they be present with me." <> "Kuma inã nẽman tsari da Kai, ya Ubangijĩna! Dõmin kada su halarto ni, " = --Qur'an 23:98
    [For such is the state of the disbelievers], until, when death comes to one of them, he says, "My Lord, send me back <> Har idan mutuwa ta jẽ wa ɗayansu, sai ya ce: "Yã Ubangijina, Ku mayar da ni (dũniya)." = --Qur'an 23:99
    That I might do righteousness in that which I left behind." No! It is only a word he is saying; and behind them is a barrier until the Day they are resurrected. <> "Tsammãnina in aikata aiki na ƙwarai cikin abin da na bari." Kayya! Lalle ne ita kalma ce, shĩ ne mafaɗinta, alhãli kuwa a bãya gare su akwai wani shãmaki har rãnar da zã a tãyar da su. = --Qur'an 23:100
    So when the Horn is blown, no relationship will there be among them that Day, nor will they ask about one another. <> Sa'an nan idan an yi bũsa a cikin ƙaho, to, bãbu dangantakõki a tsakãninsu a rãnar nan kuma bã zã su tambayi jũnansu ba. = --Qur'an 23:101
    And those whose scales are heavy [with good deeds] - it is they who are the successful. <> To, wadanda sikẽlinsu ya yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo. = --Qur'an 23:102
    But those whose scales are light - those are the ones who have lost their souls, [being] in Hell, abiding eternally. <> Kuma waɗanda sikẽlinsu ya yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu sunã madawwama a cikin Jahannama. = --Qur'an 23:103
    The Fire will sear their faces, and they therein will have taut smiles. <> Fuskokinsu sunã balbalar wuta, kuma su a cikinta mãsu yãgaggun leɓɓa daga haƙõra ne. = --Qur'an 23:104
    [It will be said]. "Were not My verses recited to you and you used to deny them?" <> "Shin, ayõyĩNa ba su kasance anã karanta su a kanku ba sai kuka kasance game da su kunã ƙaryatãwa?" = --Qur'an 23:105
    They will say, "Our Lord, our wretchedness overcame us, and we were a people astray. <> Suka ce: "Yã Ubangijinmu, shaƙãwamiu ce ta rinjãya a kanmu, kuma mun kasance mutãne ɓatattu." = --Qur'an 23:106
    Our Lord, remove us from it, and if we were to return [to evil], we would indeed be wrongdoers." <> "Yã Ubangjinmu! Ka fitar da mu daga gare ta, sa'an nan idan mun kõma, to, lalle ne, mũ ne mãsu zãlunci." = --Qur'an 23:107
    He will say, "Remain despised therein and do not speak to Me. <> Ya ce: "Ku tafi (da wulãkanci) a cikinta. Kada ku yi Mini magana." = --Qur'an 23:108
    Indeed, there was a party of My servants who said, 'Our Lord, we have believed, so forgive us and have mercy upon us, and You are the best of the merciful.' <> Lalle ne waɗansu ƙungiyoyi daga bãyiNa sun kasance sunã cẽwa, "Yã Ubangijinmu! Mun yi ĩmãni, sai Ka gãfarta mana, kuma Ka yi mana rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu tausayi." = --Qur'an 23:109
    But you took them in mockery to the point that they made you forget My remembrance, and you used to laugh at them. <> Sai kuka riƙe su lẽburõri har suka mantar da ku ambatõNa kuma kun kasance, daga gare su kuke yin dãriya. = --Qur'an 23:110
    Indeed, I have rewarded them this Day for their patient endurance - that they are the attainers [of success]." <> Lalle ne Nĩ Inã sãka musu a yau, sabõda abin da suka yi wa haƙuri. Dõmin lalle ne sũ sũ ne mãsu sãmun babban rabo. = --Qur'an 23:111
    [Allah] will say, "How long did you remain on earth in number of years?" <> Ya ce: "Nawa kuka zauna a cikin ƙasa na ƙidãyar shẽkaru?" = --Qur'an 23:112
    They will say, "We remained a day or part of a day; ask those who enumerate." <> Suka ce: "Mun zauna a yini ɗaya ko rabin yini, sai ka tambayi mãsu ƙidãyãwa." = --Qur'an 23:113
    He will say, "You stayed not but a little - if only you had known. <> Ya ce: "Ba ku zauna ba fãce kaɗan, dã dai kun kasance kunã sani." = --Qur'an 23:114
    Then did you think that We created you uselessly and that to Us you would not be returned?" <> "Shin, to, kun yi zaton cẽwa Mun halitta ku ne da wãsa kuma lalle ku, zuwa gare Mu, bã zã ku kõmo ba?" = --Qur'an 23:115
    So exalted is Allah, the Sovereign, the Truth; there is no deity except Him, Lord of the Noble Throne. <> Allah Mamallaki gaskiya, Yã ɗaukaka. Bãbu abin bautãwa, fãce Shi. Shĩ ne Ubangijin Al'arshi, mai daraja. = --Qur'an 23:116
    And whoever invokes besides Allah another deity for which he has no proof - then his account is only with his Lord. Indeed, the disbelievers will not succeed. <> Kuma wanda ya kira, tãre da Allah, waɗansu abũbuwan bautãwa na dabam, bã yanã da wani dalĩli game da shĩ (kiran) ba, to hisãbinsa yanã wurin Ubangijinsa kawai. Lalle ne, kãfirai bã su cin nasara. = --Qur'an 23:117
    And, [O Muhammad], say, "My Lord, forgive and have mercy, and You are the best of the merciful." <> Kuma ka ce: "Yã Ubangijina! Ka yi gãfara, Ka yi rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu rahama." = --Qur'an 23:118
    [This is] a surah which We have sent down and made [that within it] obligatory and revealed therein verses of clear evidence that you might remember. <> (Wannan) sũra ce. Mun saukar da ita, kuma Mun wajabta ta, kuma Mun saukar da ãyõyi bayyanannu a cikinta, dõmin ku riƙa tunãwa. = --Qur'an 24:1
    The [unmarried] woman or [unmarried] man found guilty of sexual intercourse - lash each one of them with a hundred lashes, and do not be taken by pity for them in the religion of Allah, if you should believe in Allah and the Last Day. And let a group of the believers witness their punishment. <> Mazinãciya da mazinãci, to, ku yi bũlãla ga kõwane ɗaya daga gare su, bũlãla ɗari. Kuma kada tausayi ya kãma ku game da su a cikin addinin Allah idan kun kasance kunã yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma wani yankin jama, a daga mũminai, su halarci azãbarsu. = --Qur'an 24:2
    The fornicator does not marry except a [female] fornicator or polytheist, and none marries her except a fornicator or a polytheist, and that has been made unlawful to the believers. <> Mazinãci bã ya aure fãce da mazinãciya kõ mushirika, kuma mazinãciya bãbu mai aurenta fãce mazinãci kõ mushiriki. Kuma an haramta wannan a kan mũminai. = --Qur'an 24:3
    And those who accuse chaste women and then do not produce four witnesses - lash them with eighty lashes and do not accept from them testimony ever after. And those are the defiantly disobedient, <> Kuma waɗanda ke jĩfar mãtã masu kãmun kai, sa'an nan kuma ba su jẽ da shaidu huɗu ba to, ku yi musu bũlãla, bũlãla tamãnin, kuma kada ku karɓi wata shaida tãsu, har abada. Waɗancan su ne fãsiƙai. = --Qur'an 24:4
    Except for those who repent thereafter and reform, for indeed, Allah is Forgiving and Merciful. <> Fãce waɗanda suka tũbadaga bãyan wannan, kuma suka gyãru, to lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 24:5
    And those who accuse their wives [of adultery] and have no witnesses except themselves - then the witness of one of them [shall be] four testimonies [swearing] by Allah that indeed, he is of the truthful. <> Kuma waɗanda ke jĩfar mãtan aurensu kuma waɗansu shaidu ba su kasance a gare su ba, fãce dai kansu, to, shaidar ɗayansu, shaida huɗu ce da Allah, 'Lalle shĩ, haƙĩƙa, yanã daga magasganta.' = --Qur'an 24:6
    And the fifth [oath will be] that the curse of Allah be upon him if he should be among the liars. <> Kuma ta biyar cẽwa 'La'anar Allah ta tabbata a kansa, idan ya kasance daga maƙaryata.' = --Qur'an 24:7
    But it will prevent punishment from her if she gives four testimonies [swearing] by Allah that indeed, he is of the liars. <> Kuma yanã tunkuɗe mata azãba ta yi shaida, shaida huɗu da Allah, 'Lalle shĩ haƙĩƙa, yanã daga maƙaryata.' = --Qur'an 24:8
    And the fifth [oath will be] that the wrath of Allah be upon her if he was of the truthful. <> Kuma tã biyar cẽwa 'Hushin Allah ya tabbata a kanta idan ya kasance daga magasganta.' = --Qur'an 24:9
    And if not for the favor of Allah upon you and His mercy... and because Allah is Accepting of repentance and Wise. <> Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku, da rahamarSa, kuma cẽwa Allah Mai karɓar tũba ne, Mai hikima! = --Qur'an 24:10
    Indeed, those who came with falsehood are a group among you. Do not think it bad for you; rather it is good for you. For every person among them is what [punishment] he has earned from the sin, and he who took upon himself the greater portion thereof - for him is a great punishment. <> Lalle ne waɗanda suka zo da ƙiren ƙarya waɗansu jama'a ne daga gare ku, kada ku yi zatonsa sharri ne a gare ku. Ã'a, alhẽri ne gare ku. Kõwane mutum daga gare su na da sakamakon abin da ya sanã'anta na zunubi, kuma wanda ya jiɓinci girmansa, daga gare su, yanã da azãba mai girma. = --Qur'an 24:11
    Why, when you heard it, did not the believing men and believing women think good of one another and say, "This is an obvious falsehood"? <> Don me a lõkacin da kuka ji shi mũminai maza da mũminai mãta ba su yi zaton alhẽri game da kansu ba kuma su ce: "Wannan ƙiren ƙarya ne bayyananne?" = --Qur'an 24:12
    Why did they [who slandered] not produce for it four witnesses? And when they do not produce the witnesses, then it is they, in the sight of Allah, who are the liars. <> Don me ba su zo da shaidu huɗu a kansa ba? To idan ba su kãwo shaidun nan ba to, waɗannan, a wurin Allah, sũ ne maƙaryata. = --Qur'an 24:13
    And if it had not been for the favor of Allah upon you and His mercy in this world and the Hereafter, you would have been touched for that [lie] in which you were involved by a great punishment <> Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa a cikin dũniya da Lãhira. Lalle ne, dã azãba mai girma ta shãfe ku a cikin abin da kuka kũtsa da magana a cikinsa. = --Qur'an 24:14
    When you received it with your tongues and said with your mouths that of which you had no knowledge and thought it was insignificant while it was, in the sight of Allah, tremendous. <> A lõkacin da kuke marãbarsa da harsunanku kuma kunã cẽwa da bakunanku abin da bã ku da wani ilmi game da shi, kuma kunã zaton sa mai sauƙi alhãli kuwa, shi a wurin Allah, babba ne. = --Qur'an 24:15
    And why, when you heard it, did you not say, "It is not for us to speak of this. Exalted are You, [O Allah]; this is a great slander"? <> Kuma don me a lõkacin da kuka ji shi, ba ku ce ba, "Bã ya yiwuwa a gare mu, mu yi magana a game da wannan. Tsarki ya tabbata a gare Ka, wannan ƙiren ƙarya ne mai girma"? = --Qur'an 24:16
    Allah warns you against returning to the likes of this [conduct], ever, if you should be believers. <> Allah Yanã yi muku wa'azi, kada ku kõma ga irinsa, har abada, idan kun kasance mũminai. = --Qur'an 24:17
    And Allah makes clear to you the verses, and Allah is Knowing and Wise. <> Kuma Allah Yanã bayyana muku ãyõyinSa, kuma Allah Masani ne, Mai hikima. = --Qur'an 24:18
    Indeed, those who like that immorality should be spread [or publicized] among those who have believed will have a painful punishment in this world and the Hereafter. And Allah knows and you do not know. <> Lalle ne waɗanda ke son alfãsha ta wãtsu ga waɗanda suka yi ĩmãni sunã da azãba mai raɗaɗi a cikin dũniya da Lãhira. KumaAllah, Shi ne Ya sani, alhãli kuwa, kũ ba ku sani ba. = --Qur'an 24:19
    And if it had not been for the favor of Allah upon you and His mercy... and because Allah is Kind and Merciful. <> Kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa. Kuma lalle ne Allah Mai tausayi ne, Mai jin ƙai! = --Qur'an 24:20
    O you who have believed, do not follow the footsteps of Satan. And whoever follows the footsteps of Satan - indeed, he enjoins immorality and wrongdoing. And if not for the favor of Allah upon you and His mercy, not one of you would have been pure, ever, but Allah purifies whom He wills, and Allah is Hearing and Knowing. <> Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni, kada ku bi hanyõyin Shaiɗan. Kuma wanda ke bin hanyõyin Shaiɗan, to, lalle ne shi, yanã umurni da yin alfãsha da abin da ba a sani ba, kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa, bãbu wani mutum daga gare ku da zai tsarkaka har abada, kuma amma Allah Yanã tsarkake wanda Yake so kuma Allah Mai ji ne, Masani. = --Qur'an 24:21
    And let not those of virtue among you and wealth swear not to give [aid] to their relatives and the needy and the emigrants for the cause of Allah, and let them pardon and overlook. Would you not like that Allah should forgive you? And Allah is Forgiving and Merciful. <> Kuma kada ma'abũta falala daga gare ku da mawadãta su rantse ga rashin su bãyar da alhẽri ga ma'abũta zumunta da miskĩnai da muhãjirai, a cikin hanyar Allah. Kuma su yãfe, kuma su kau da kai. shin, bã ku son Allah Ya gãfarta muku, alhãli Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai? = --Qur'an 24:22
    Indeed, those who [falsely] accuse chaste, unaware and believing women are cursed in this world and the Hereafter; and they will have a great punishment <> Lalle ne waɗannan da suke jĩfar mãtã mãsu kãmun kai gãfilai mũminai, an la'ane su, a cikin dũniya da Lãhira, kuma sunãda azãba mai girma. = --Qur'an 24:23
    On a Day when their tongues, their hands and their feet will bear witness against them as to what they used to do. <> A rãnar da harsunansu da hannãyensu, da ƙafãfunsu suke bãyar da shaida a kansu, game da abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 24:24
    That Day, Allah will pay them in full their deserved recompense, and they will know that it is Allah who is the perfect in justice. <> a rãnar dl Allah Yake cika musu sakamakonsu tabbatacce kuma sunã sanin (cẽwa) lalle Allah, Shi ne Gaskiya bayyananna. = --Qur'an 24:25
    Evil words are for evil men, and evil men are [subjected] to evil words. And good words are for good men, and good men are [an object] of good words. Those [good people] are declared innocent of what the slanderers say. For them is forgiveness and noble provision. <> Miyãgun mãtã dõmin miyagun maza suke, kuma miyãgun maza dõmin miyãgun mãtã suke kuma tsarkãkan mãtã dõmin tsarkãkan maza suke kuma tsarkãkan maza dõmin tsarkãkan mãtã suke. waɗancan sũ ne waɗanda ake barrantãwa daga abin da (mãsu ƙazafi) suke faɗa kuma sunã da gãfara da arziki na karimci. = --Qur'an 24:26
    O you who have believed, do not enter houses other than your own houses until you ascertain welcome and greet their inhabitants. That is best for you; perhaps you will be reminded. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku shiga gidãje waɗanda bã gidãjenku ba sai kun sãmi izni, kuma kun yi sallama a kan ma'abũtansu. Wannan ne mafi alhẽri gare ku, tsammaninku, zã ku tuna. = --Qur'an 24:27
    And if you do not find anyone therein, do not enter them until permission has been given you. And if it is said to you, "Go back," then go back; it is purer for you. And Allah is Knowing of what you do. <> To, idan ba ku sãmi kõwa a cikinsu ba, to, kada ku shige su, sai an yi muku izni. Kuma idan an ce muku, "Ku kõma." Sai ku kõma, shi ne mafi tsarkaka a gare ku. Kuma Allah game da abin da kuke aikatãwa, Masani ne. = --Qur'an 24:28
    There is no blame upon you for entering houses not inhabited in which there is convenience for you. And Allah knows what you reveal and what you conceal. <> Bãbu laifi a kanku, ga ku shiga gidãje waɗanda bã zaunannu ba, a cikinsu akwai waɗansu kãya nãku. Kuma Allah Yanã sanin abin da kuke nũnãwa, da abin dakuke ɓãyẽwa. = --Qur'an 24:29
    Tell the believing men to reduce [some] of their vision and guard their private parts. That is purer for them. Indeed, Allah is Acquainted with what they do. <> Ka ce wa mũminai maza su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjõjinsu. wannan shĩ ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah, Mai ƙididdigewa ne ga abin da suke sanã'antãwa. = --Qur'an 24:30
    And tell the believing women to reduce [some] of their vision and guard their private parts and not expose their adornment except that which [necessarily] appears thereof and to wrap [a portion of] their headcovers over their chests and not expose their adornment except to their husbands, their fathers, their husbands' fathers, their sons, their husbands' sons, their brothers, their brothers' sons, their sisters' sons, their women, that which their right hands possess, or those male attendants having no physical desire, or children who are not yet aware of the private aspects of women. And let them not stamp their feet to make known what they conceal of their adornment. And turn to Allah in repentance, all of you, O believers, that you might succeed. <> Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjõjinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu fãce abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su dõka da mayãfansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nũna ƙawarsu fãce ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan mazansu, ko 'yan'uwansu, ko ɗiyan 'yan'uwansu mãtã, kõ mãtan ƙungiyarsu, ko abin da hannãyensu na dãma suka mallaka, ko mabiya wasun mãsu bukãtar mãta daga maza, kõ jãrirai waɗanda. bã su tsinkãya a kan al'aurar mãtã. Kuma kada su yi dũka da ƙafãfunsu dõmin a san abin da suke ɓõyẽwa daga ƙawarsu. Kuma ku tũba zuwa ga Allah gabã ɗaya, yã ku mũminai! Tsammãninku, ku sãmi babban rabo. = --Qur'an 24:31
    And marry the unmarried among you and the righteous among your male slaves and female slaves. If they should be poor, Allah will enrich them from His bounty, and Allah is all-Encompassing and Knowing. <> Kuma ku aurar da gwaurãye daga gare ku, da sãlihai daga bãyinku, da kuyanginku. Idan sun kasance matalauta Allah zai wadãtar da su daga falalarSa. Kuma Allah Mawadãci ne, Masani. = --Qur'an 24:32
    But let them who find not [the means for] marriage abstain [from sexual relations] until Allah enriches them from His bounty. And those who seek a contract [for eventual emancipation] from among whom your right hands possess - then make a contract with them if you know there is within them goodness and give them from the wealth of Allah which He has given you. And do not compel your slave girls to prostitution, if they desire chastity, to seek [thereby] the temporary interests of worldly life. And if someone should compel them, then indeed, Allah is [to them], after their compulsion, Forgiving and Merciful. <> Kuma waɗannan da ba su sãmi aure ba su kãme kansu har Allah Ya wadãtar da su daga, falalarsa. Kuma waɗanda ke nẽman fansa daga abin da hannuwanku na dãma suka mallaka, to, ku ɗaura musu fansã idan kun san akwai wani alhẽri a cikinsu kuma ku bã su wani abu daga dũkiyar Allah wannan da Ya bã ku. Kuma kada ku tĩlasta kuyanginku a kan yin zina, idan sun yi nufin tsaron kansu, dõmin ku nẽmi rãyuwar dũniya, kuma wanda ya tĩlasta su to, lalle Allah, a bãyan tĩlasta su, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 24:33
    And We have certainly sent down to you distinct verses and examples from those who passed on before you and an admonition for those who fear Allah. <> Kuma lalle ne Mun saukar zuwa gare ku, ãyõyi mãsu bayyanãwa, da misãli daga waɗanda suka shige daga gabãninku, da wa'azi ga mãsu taƙawa. = --Qur'an 24:34
    Allah is the Light of the heavens and the earth. The example of His light is like a niche within which is a lamp, the lamp is within glass, the glass as if it were a pearly [white] star lit from [the oil of] a blessed olive tree, neither of the east nor of the west, whose oil would almost glow even if untouched by fire. Light upon light. Allah guides to His light whom He wills. And Allah presents examples for the people, and Allah is Knowing of all things. <> Allah ne Hasken sammai da ƙasa, misãlin HaskenSa, kamar tãgã, a cikinta akwai fitila, fitilar a cikin ƙarau, ƙarau ɗin kamar shi taurãro ne mai tsananin haske, anã kunna shi daga wata itãciya mai albarka, ta zaitũni, bã bagabashiya ba kuma bã bayammaciya ba, manta na kusa ya yi haske, kuma kõ wuta ba ta shãfe shi ba, haske a kan haske, Allah na shiryar da wanda Yake so zuwa ga HaskenSa. Kuma Allah na buga misãlai ga mutãne, kuma Allah game da dukan kõme, Masani ne. = --Qur'an 24:35
    [Such niches are] in mosques which Allah has ordered to be raised and that His name be mentioned therein; exalting Him within them in the morning and the evenings <> A cikin waɗansu gidãje waɗanda Allah Yã yi umurnin a ɗaukaka kuma a ambaci sũnansa a cikinsu, sunã yin tasbĩhi a gare Shi a cikinsu, sãfe da maraice. = --Qur'an 24:36
    [Are] men whom neither commerce nor sale distracts from the remembrance of Allah and performance of prayer and giving of zakah. They fear a Day in which the hearts and eyes will [fearfully] turn about - <> Waɗansu maza, waɗanda wani fatauci bã ya shagaltar da su, kuma sayarwa bã ta shagaltar da su daga ambaton Allah, da tsai da salla da bãyar da zakka, sunã tsõron wani yini wanda zukãta sunã bibbirkita a cikinsa, da gannai. = --Qur'an 24:37
    That Allah may reward them [according to] the best of what they did and increase them from His bounty. And Allah gives provision to whom He wills without account. <> Dõmin Allah Ya sãka musu da mafi kyaun abin da suka aikata, kuma Ya ƙãra musu daga falalarsa. Kuma Allah Yanã azurta wanda Yake so, bã da lissafi ba. = --Qur'an 24:38
    But those who disbelieved - their deeds are like a mirage in a lowland which a thirsty one thinks is water until, when he comes to it, he finds it is nothing but finds Allah before Him, and He will pay him in full his due; and Allah is swift in account. <> Kuma waɗanda suka ƙãfirta ayyukansu sunã kamar ƙawalwalniyã ga faƙo, mai ƙishirwa yanã zaton sa ruwa, har idan ya jẽ masa bai iske shi kõme ba, kuma ya sãmi Allah a wurinsa, sai Ya cika masa hisãbinsa. Kuma Allah Mai gaggãwar sakamako ne. = --Qur'an 24:39
    Or [they are] like darknesses within an unfathomable sea which is covered by waves, upon which are waves, over which are clouds - darknesses, some of them upon others. When one puts out his hand [therein], he can hardly see it. And he to whom Allah has not granted light - for him there is no light. <> Kõ kuwa kamar duffai a cikin tẽku mai zurfi, tãguwar ruwa tanã rufe da shi, daga bisansa akwai wata tãguwa, daga bisansa akwai wani girgije, duffai sãshensu a bisa sãshe, idan ya fitar da tãfinsa ba ya kusa ya gan shi. Kuma wanda Allah bai sanya masa haske ba, to, bã ya da wani haske. = --Qur'an 24:40
    Do you not see that Allah is exalted by whomever is within the heavens and the earth and [by] the birds with wings spread [in flight]? Each [of them] has known his [means of] prayer and exalting [Him], and Allah is Knowing of what they do. <> Shin, ba ka gani ba (cẽwa) lalle ne Allah, Wanda yake a cikin sammai da ƙasa sunã yi Masa tasbĩhi, kuma tsuntsaye sunã mãsu sanwa, kõwane lalle ya san sallarsa da tasbĩhinsa kuma Allah Masani ne ga abin da suke aikatãwa? = --Qur'an 24:41
    And to Allah belongs the dominion of the heavens and the earth, and to Allah is the destination. <> Mulkin sammai da ƙasa ga Allah kawai yake, kuma zuwa ga Allah makõma take. = --Qur'an 24:42
    Do you not see that Allah drives clouds? Then He brings them together, then He makes them into a mass, and you see the rain emerge from within it. And He sends down from the sky, mountains [of clouds] within which is hail, and He strikes with it whom He wills and averts it from whom He wills. The flash of its lightening almost takes away the eyesight. <> Ashe, ba ka ganĩ ba, lalle ne Allah Yanã kõra girgije, sa'an nan kuma Ya haɗa a tsakãninsa sa'an nan kuma Ya sanya shi mai hauhawar jũna? Sai ka ga ruwa yanã fita daga tsattsakinsa, kuma Ya saukar daga waɗansu duwãtsu a cikinsa na ƙanƙarã daga sama, sai ya sãmu wanda Yake so da shi, kuma Ya karkatar da shi daga barin wanda Yake so. Hasken walƙiyarsa Yanã kusa ya tafi da gannai. = --Qur'an 24:43
    Allah alternates the night and the day. Indeed in that is a lesson for those who have vision. <> Allah Yanã jũyar da dare da yini. Lalle ne a cikin wannan akwai abin kula ga ma'abũta gannai. = --Qur'an 24:44
    Allah has created every [living] creature from water. And of them are those that move on their bellies, and of them are those that walk on two legs, and of them are those that walk on four. Allah creates what He wills. Indeed, Allah is over all things competent. <> Kuma Allah ne Ya halitta kõwace dabba daga ruwa. To, daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya a kan cikinsu, kuma daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya a kan ƙafãfu biyu, kuma daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya akan huɗu. Allah Yãna halitta abin da Yake so, lalle Allah, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi ne. = --Qur'an 24:45
    We have certainly sent down distinct verses. And Allah guides whom He wills to a straight path. <> Lalle ne haƙĩƙa Mun saukar da ãyõyi, mãsu bayyanãwa. Kuma Allah Yanã shiryar da wanda Yake so zuwa ga hanya madaidaiciya. = --Qur'an 24:46
    But the hypocrites say, "We have believed in Allah and in the Messenger, and we obey"; then a party of them turns away after that. And those are not believers. <> Kuma sunã cẽwa, "Mun yi ĩmãni da Allah da kuma Manzo, kuma mun yi ɗã'ã." Sa'an nan kuma wata ƙungiya daga gare su, su jũya daga bãyan wancan. Kuma waɗancan ba mũminai ba ne. = --Qur'an 24:47
    And when they are called to [the words of] Allah and His Messenger to judge between them, at once a party of them turns aside [in refusal]. <> Kuma idan aka kirã su zuwa ga Allah da ManzonSa, dõmin Ya yi hukunci a tsakãninsu, sai gã wata ƙnngiya daga gare su sunã mãsu bijirewa. = --Qur'an 24:48
    But if the right is theirs, they come to him in prompt obedience. <> Kuma idan hakki ya kasance a gare su, zã su jẽ zuwa gare shi, snnã mãsu mĩƙa wuya. = --Qur'an 24:49
    Is there disease in their hearts? Or have they doubted? Or do they fear that Allah will be unjust to them, or His Messenger? Rather, it is they who are the wrongdoers. <> Shin, a cikin zukãtansu akwai cũta ne, ko kuwa sunã tsõron Allah Ya yi zãlunci a kansu da ManzonSa? Ã'a, waɗancan sũ ne azzãlumai. = --Qur'an 24:50
    The only statement of the [true] believers when they are called to Allah and His Messenger to judge between them is that they say, "We hear and we obey." And those are the successful. <> Maganar mũminai, idan aka kira su zuwa ga Allah da ManzonSa dõmin Ya yi hukunci a tsakãninsu takan kasance kawai su ce "Mun ji, kuma mun yi ɗã'ã, Kuma waɗannan sũ ne mãsu cin nasara." = --Qur'an 24:51
    And whoever obeys Allah and His Messenger and fears Allah and is conscious of Him - it is those who are the attainers. <> Kuma wanda ya yi ɗã'ã ga Allah da ManzonSa, kuma ya ji tsõron Allah, ya kuma bĩ Shi da taƙawa to waɗannan sũ ne mãsu babban rabo. = --Qur'an 24:52
    And they swear by Allah their strongest oaths that if you ordered them, they would go forth [in Allah 's cause]. Say, "Do not swear. [Such] obedience is known. Indeed, Allah is Acquainted with that which you do." <> Kuma suka rantse da Allah iyãkar rantsuwarsu, 'Lalle ne idan ka umurce su haƙĩƙa sunã fita.' Ka ce, "Kada ku rantse, ɗã'ã sananna ce! Lalle ne, Allah Mai ƙididdigewã ne ga abin da kuke aikatãwã." = --Qur'an 24:53
    Say, "Obey Allah and obey the Messenger; but if you turn away - then upon him is only that [duty] with which he has been charged, and upon you is that with which you have been charged. And if you obey him, you will be [rightly] guided. And there is not upon the Messenger except the [responsibility for] clear notification." <> Ka ce: "Ku yi ɗã'ã ga Allah kuma ku yi ɗã'ã ga Manzo. To, idan kun jũya, to, a kansa akwai abin da aka aza masa kawai, kuma a kanku akwai abin da aka aza muku kawai, Kuma idan kun yi masa ɗã'ã za ku shiryu. Kuma bãbu abin da yake a kan Manzo fãce iyarwa bayyananna." = --Qur'an 24:54
    Allah has promised those who have believed among you and done righteous deeds that He will surely grant them succession [to authority] upon the earth just as He granted it to those before them and that He will surely establish for them [therein] their religion which He has preferred for them and that He will surely substitute for them, after their fear, security, [for] they worship Me, not associating anything with Me. But whoever disbelieves after that - then those are the defiantly disobedient. <> Allah Ya yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare. Ku, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle zai shugabantar da su a cikin ƙasa kamar yadda Ya shugabantar da waɗanda suke daga gabãninsu, kuma lalle ne zai tabbatar musu da addininsu wanda Ya yardar musu, kuma lalle ne Yanã musanya musu daga bãyan tsõronsu da aminci, sunã bauta Mini bã su haɗa kõme da Nĩ. Kuma wanda ya kãfirta a bãyan wannan, to, waɗancan, su ne fãsiƙai. = --Qur'an 24:55
    And establish prayer and give zakah and obey the Messenger - that you may receive mercy. <> Kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka, kuma ku yi ɗã'ã ga Manzo, tsammãninku a yi muku rahama. = --Qur'an 24:56
    Never think that the disbelievers are causing failure [to Allah] upon the earth. Their refuge will be the Fire - and how wretched the destination. <> Kada lalle ka yi zaton waɗanda suka kãfirta zã su buwãya a cikin ƙasa, kuma makõmarsu wuta ce, kuma lalle ne makomar tã mũnana. = --Qur'an 24:57
    O you who have believed, let those whom your right hands possess and those who have not [yet] reached puberty among you ask permission of you [before entering] at three times: before the dawn prayer and when you put aside your clothing [for rest] at noon and after the night prayer. [These are] three times of privacy for you. There is no blame upon you nor upon them beyond these [periods], for they continually circulate among you - some of you, among others. Thus does Allah make clear to you the verses; and Allah is Knowing and Wise. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Waɗannan da hannuwanku na dãma suka mallaka da waɗanda ba su isa mafarki ba daga cikinku, su nẽmi izni sau uku; daga gabãnin sallar alfijir da lõkacin da kuke ajiye tufãfinku sabõda zãfin rãnã, kuma daga bãyan sallar ishã'i. Sũ ne al'aurõri uku a gare ku. Bãbu laifi a kanku kuma bãbu a kansu a bãyansu. Sũ mãsu kẽwaya ne a kanku sãshenku a kan sãshe. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa a gare ku. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima. = --Qur'an 24:58
    And when the children among you reach puberty, let them ask permission [at all times] as those before them have done. Thus does Allah make clear to you His verses; and Allah is Knowing and Wise. <> Kuma idan yãra daga cikinku suka isa mafarki to su nẽmi izni, kamar yadda waɗanda suke a gabãninsu suka nẽmi iznin. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa a gare ku, kuma Allah Masani ne, Mai hikima. = --Qur'an 24:59
    And women of post-menstrual age who have no desire for marriage - there is no blame upon them for putting aside their outer garments [but] not displaying adornment. But to modestly refrain [from that] is better for them. And Allah is Hearing and Knowing. <> Kuma tsõfaffi daga mãtã, waɗanda bã su fatan wani aure to, bãbu laifi a kansu su ajiye tufãfinsu, bã sunã mãsu fitar da ƙawa ba, kuma su tsare mutuncinsu shĩ ne mafi alhẽri a gare su. Kuma Allah Mai jĩ ne, Masani. = --Qur'an 24:60
    There is not upon the blind [any] constraint nor upon the lame constraint nor upon the ill constraint nor upon yourselves when you eat from your [own] houses or the houses of your fathers or the houses of your mothers or the houses of your brothers or the houses of your sisters or the houses of your father's brothers or the houses of your father's sisters or the houses of your mother's brothers or the houses of your mother's sisters or [from houses] whose keys you possess or [from the house] of your friend. There is no blame upon you whether you eat together or separately. But when you enter houses, give greetings of peace upon each other - a greeting from Allah, blessed and good. Thus does Allah make clear to you the verses [of ordinance] that you may understand. <> Bãbu laifi a kan makãho, kuma bãbu laifi a kan gurgu, kuma bãbu laifi a kan majiyyaci, kuma bãbu laifi a kan kõwanenku, ga ku ci (abinci) daga gidãjenku, kõ daga gidãjen ubanninku, kõ daga gidãjen uwãyenku, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku mazã, kõ daga gidãjen 'yan'uwanku mãtã, kõ daga gidãjen baffanninku, kõ daga gidãjen gwaggwanninku, kõ daga gidãjen kãwunnanku, kõ daga gidãjen innõninku kõ abin da kuka mallaki mabũɗansa kõ abõkinku bãbu laifi a gare ku ku ci gabã ɗaya, kõ dabam- dabam. To, idan kun shiga wasu gidãje, ku yi sallama a kan kãwunanku, gaisuwã ta daga wurin Allah mai albarka, mai dãɗi. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ãyõyinSa, tsammãninku ku yi hankali. = --Qur'an 24:61
    The believers are only those who believe in Allah and His Messenger and, when they are [meeting] with him for a matter of common interest, do not depart until they have asked his permission. Indeed, those who ask your permission, [O Muhammad] - those are the ones who believe in Allah and His Messenger. So when they ask your permission for something of their affairs, then give permission to whom you will among them and ask forgiveness for them of Allah. Indeed, Allah is Forgiving and Merciful. <> Waɗanda ke mũminai sõsai, su ne waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, kuma idan sun kasance tãre da shi, a kan wani al'amari na aikin gayya, bã su tafiya sai sun nẽme shi izni. Lalle ne, waɗanda suke biɗar ka izni waɗancan sũ ne suke yin ĩmãni da Allah da ManzonSa. To, idan sun nẽme ka izni sabõda wani sha'aninsu, to, ka yi izni ga wanda ka so daga gare su, kuma ka nẽmã musu gãfara daga Allah. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 24:62
    Do not make [your] calling of the Messenger among yourselves as the call of one of you to another. Already Allah knows those of you who slip away, concealed by others. So let those beware who dissent from the Prophet's order, lest fitnah strike them or a painful punishment. <> Kada ku sanya kiran Manzo a tsakãninku kamar kiran sãshenku ga sãshe. Lalle ne Allah Yanã sanin waɗanda ke sancẽwa daga cikinku da saɗãɗe. To, waɗanda suke sãɓãwa daga umurninSa, su yi saunar wata fitina ta sãme su, kõ kuwa wata azãba mai raɗãɗi ta sãme su. = --Qur'an 24:63
    Unquestionably, to Allah belongs whatever is in the heavens and earth. Already He knows that upon which you [stand] and [knows] the Day when they will be returned to Him and He will inform them of what they have done. And Allah is Knowing of all things. <> To! Lalle Allah ne Yake da mulkin abin da ke a cikin sammai da ƙasa, haƙĩƙa, Yanã sanin abin da kuke a kansa kuma a rãnar da ake mayar da su zuwa gare shi, sai Yanã bã su lãbãri game da abin da suka aikata. Kuma Allah, ga dukkan kõme, Masani ne. = --Qur'an 24:64
    Blessed is He who sent down the Criterion upon His Servant that he may be to the worlds a warner - <> Albarka ta tabbata ga wanda Ya saukar da (Littãfi) mai rarrabẽwa a kan bãwanSa, dõmin ya kasance mai gargaɗi ga halitta. = --Qur'an 25:1
    He to whom belongs the dominion of the heavens and the earth and who has not taken a son and has not had a partner in dominion and has created each thing and determined it with [precise] determination. <> wanda Yake da mulkin sammai da ƙasa kuma bai riƙi abin haihuwa ba, kuma abõkin tãrayya bai kasance a gare Shi ba a cikin mulkinSa kuma Ya halitta dukan kowane abu, sa'an nan Ya ƙaddara shi ƙaddarãwa. = --Qur'an 25:2
    But they have taken besides Him gods which create nothing, while they are created, and possess not for themselves any harm or benefit and possess not [power to cause] death or life or resurrection. <> Kuma suka riƙi abũbuwan bautawa, baicin Shi, bã su yin halittar kõme alhãli sũ ne ake halittãwa kuma bã su mallakar wa kansu wata cũta ko wani amfãni, kuma bã su mallakar mutuwa kuma bã su mallakar rãyarwa, kuma bã su mallakar tãyarwa. = --Qur'an 25:3
    And those who disbelieve say, "This [Qur'an] is not except a falsehood he invented, and another people assisted him in it." But they have committed an injustice and a lie. <> Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Wannan bã kõme ba ne fãce ƙiron ƙarya da (Muhammadu) ya ƙirƙira shi, kuma waɗansu mutãne na dabam suka taimake shi a kansa." To, lalle ne sun jẽ wa zãlunci da karkacẽwar magana. = --Qur'an 25:4
    And they say, "Legends of the former peoples which he has written down, and they are dictated to him morning and afternoon." <> Kuma suka ce: "Tatsũniyõyi ne na farko ya rurrbũta, sai sũ ake shibtarsu a gare shi sãfe da yamma." = --Qur'an 25:5
    Say, [O Muhammad], "It has been revealed by He who knows [every] secret within the heavens and the earth. Indeed, He is ever Forgiving and Merciful." <> Ka ce: "wanda Yake sanin asĩri a cikin, sammai da ƙasane Ya saukar da shi. Lalle ne shĩ Ya kasance Mai gãfara, Mai, jin ƙai." = --Qur'an 25:6
    And they say, "What is this messenger that eats food and walks in the markets? Why was there not sent down to him an angel so he would be with him a warner? <> Kuma suka ce: "Mẽne ne ga wannan Manzo, yanã cin abinci, kuma yanã tafiya a cikin kãsuwanni! Don me ba a saukar da malã'ika zuwa gare shi ba, dõmin ya kasance mai gargaɗi tãre da shi? = --Qur'an 25:7
    Or [why is not] a treasure presented to him [from heaven], or does he [not] have a garden from which he eats?" And the wrongdoers say, "You follow not but a man affected by magic." <> "Kõ kuwa a jẽfo wata taska zuwa gare shi, kõ kuwa wata gõna ta kasance a gare shi, yanã ci daga gare ta?" Kuma azzãlumai suka ce: "Bã ku bin kõwa, fãce mutum sihirtacce:" = --Qur'an 25:8
    Look how they strike for you comparisons; but they have strayed, so they cannot [find] a way. <> Ka dũba yadda suka buga maka misãlai sai suka ɓace, dõmin haka bã su iya bin tafarki. = --Qur'an 25:9
    Blessed is He who, if He willed, could have made for you [something] better than that - gardens beneath which rivers flow - and could make for you palaces. <> Albarka ta tabbata ga wanda idan Ya so, Yã sanya maka mafi alhẽri daga wannan (abu): gõnaki, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, kuma Ya sanya maka manyan gidãje. = --Qur'an 25:10
    But they have denied the Hour, and We have prepared for those who deny the Hour a Blaze. <> Ã'a, sun ƙaryata game da Sã'a, alhãli kuwa Mun yi tattalin wuta mai tsanani ga wanda ya ƙaryata (manzanni) game da Sa'a. = --Qur'an 25:11
    When the Hellfire sees them from a distant place, they will hear its fury and roaring. <> Idan ta gan su daga wani wuri mai nĩsa, sai su ji sautin fushi da wani rũri nãta. = --Qur'an 25:12
    And when they are thrown into a narrow place therein bound in chains, they will cry out thereupon for destruction. <> Kuma idan an jẽfa su a wani wuri mai ƙunci daga gare ta, sunã waɗanda aka ɗaure ciki daidai, sai su kirãyi halaka a can. = --Qur'an 25:13
    [They will be told], "Do not cry this Day for one destruction but cry for much destruction." <> Kada ku kirãyi halaka guda, kuma ku kirãyi halaka mai yawa. = --Qur'an 25:14
    Say, "Is that better or the Garden of Eternity which is promised to the righteous? It will be for them a reward and destination. <> Ka ce: "Shin, wancan ne mafi alhẽri, kõ kuwa Aljannar dawwama wadda aka yi wa'adi ga mãsu taƙawa? Tã zama, a gare su, sakamako da makõma." = --Qur'an 25:15
    For them therein is whatever they wish, [while] abiding eternally. It is ever upon your Lord a promise [worthy to be] requested. <> "Sunã da abin da suke so, a cikinta sunã madawwama. Wannan ya kasance wa'adi abin tambaya a kan Ubangijinka." = --Qur'an 25:16
    And [mention] the Day He will gather them and that which they worship besides Allah and will say, "Did you mislead these, My servants, or did they [themselves] stray from the way?" <> Kuma rãnar da Yake tãra su da abin da suke bauta wa, baicin Allah sai Ya ce: "Shin kũ nekuka ɓatar, da bãyiNa, waɗannan, ko kuwa su ne suka ɓata daga hanya?" = --Qur'an 25:17
    They will say, "Exalted are You! It was not for us to take besides You any allies. But You provided comforts for them and their fathers until they forgot the message and became a people ruined." <> suka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka, bã ya kasancẽwa agare mu, mu riƙi waɗansu majiɓinta, baicin Kai, kuma amma Kã jiyar da su dãɗi sũ da ubanninsu har suka manta da Tunãtarwa, kuma sun kasance mutãne ne halakakku." = --Qur'an 25:18
    So they will deny you, [disbelievers], in what you say, and you cannot avert [punishment] or [find] help. And whoever commits injustice among you - We will make him taste a great punishment. <> To, lalle ne, sun ƙaryata game da abin da kuke cẽwa, sabõda haka bã ku iya karkatarwa ga (maganarsu), kuma ba ku iya taimako (ga hana azãba), kuma wanda ya yi zãlunci a cikinku zã Mu ɗanɗana masa azãba mai girma. = --Qur'an 25:19
    And We did not send before you, [O Muhammad], any of the messengers except that they ate food and walked in the markets. And We have made some of you [people] as trial for others - will you have patience? And ever is your Lord, Seeing. <> Kuma ba Mu aika ba, a gabãninka daga Manzanni, fãce lalle sũ haƙĩƙa sunã cin abinci kuma sunã tafiya a cikin kasuwõyi. Kuma Mun sanya sãshen mutãne fitina ga sãshe. Shin kunã yin haƙuri? Kuma Ubangijia Ya kasance Mai gani. = --Qur'an 25:20
    And those who do not expect the meeting with Us say, "Why were not angels sent down to us, or [why] do we [not] see our Lord?" They have certainly become arrogant within themselves and [become] insolent with great insolence. <> Kuma waɗanda bã su fatan haɗuwa da Mu suka ce: "Don me ba a saukar da malã'ĩku ba a kanmu, kõ kuwa mu ga Ubangijinmu?" Lalle ne sun kangara a cikin rãyukansu, kuma suka yi tsaurin kai, tsaurin kai mai girma. = --Qur'an 25:21
    The day they see the angels - no good tidings will there be that day for the criminals, and [the angels] will say, "Prevented and inaccessible." <> A rãnar da suke ganin malã'iku bãbu bushãra a yinin nan ga mãsu laifi kuma sunã cẽwa,"Allah Ya kiyãshe mu!" = --Qur'an 25:22
    And We will regard what they have done of deeds and make them as dust dispersed. <> Kuma Muka gabãta zuwa ga abin da suka aikata daga aiki, sai Muka sanya shi ƙũra wãtsattsiya. = --Qur'an 25:23
    The companions of Paradise, that Day, are [in] a better settlement and better resting place. <> Ma'abũta Aljanna a rãnar nan sũ ne mafi alhẽri ga matabbata kuma mafi kyaun wurin ƙailũla. = --Qur'an 25:24
    And [mention] the Day when the heaven will split open with [emerging] clouds, and the angels will be sent down in successive descent. <> Kuma a rãnar da sama take tsattsãgewa tãre da gizãgizai, kuma a saukar da malã'iku, saukarwa. = --Qur'an 25:25
    True sovereignty, that Day, is for the Most Merciful. And it will be upon the disbelievers a difficult Day. <> Mulki a rãnar nan, na gaskiya, yanã ga Mai rahama, kuma ya zama yini, a kan kãfirai, mai tsanani. = --Qur'an 25:26
    And the Day the wrongdoer will bite on his hands [in regret] he will say, "Oh, I wish I had taken with the Messenger a way. <> Kuma rãnar da azzãlumi yake cĩzo a kan hannayensa, yanã cẽwa "Ya kaitõna! (A ce dai) na riƙi hanya tãre da Manzo! = --Qur'an 25:27
    Oh, woe to me! I wish I had not taken that one as a friend. <> "Ya kaitõna! (A ce dai) ban riƙi wãne masõyi ba! = --Qur'an 25:28
    He led me away from the remembrance after it had come to me. And ever is Satan, to man, a deserter." <> "Lalle ne, haƙĩƙa ya ɓatar da ni daga Tunãwa a bãyan (Tunãwar) ta je mini."Kuma Shaiɗan ya zama mai zumɓulẽwa ga mutum. = --Qur'an 25:29
    And the Messenger has said, "O my Lord, indeed my people have taken this Qur'an as [a thing] abandoned." <> Kuma Manzo ya ce: "Ya Ubangijĩna! Lalle mutãnena sun riƙi wannan Alƙur'ãni abin ƙauracẽwa!" = --Qur'an 25:30
    And thus have We made for every prophet an enemy from among the criminals. But sufficient is your Lord as a guide and a helper. <> Kuma kamar haka ne, Muka sanya maƙiyi daga mãsu laifi ga kõwane Annabi. Kuma Ubangijinka Ya isa ga zama Mai Shiryarwa, kuma Mai taimako. = --Qur'an 25:31
    And those who disbelieve say, "Why was the Qur'an not revealed to him all at once?" Thus [it is] that We may strengthen thereby your heart. And We have spaced it distinctly. <> Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Don me ba a saukar da Alƙur'ãni a kansa ba, jimla guda?" kamar wancan! Dõmin Mu ƙarfafa zũciyarka game da shi, kuma Mun jẽranta karanta shi da hankali jẽrantawa. = --Qur'an 25:32
    And they do not come to you with an argument except that We bring you the truth and the best explanation. <> Kuma bã zã su zo maka da wani misãli ba, fãce Mun je maka da gaskiya da mafi kyau ga fassara. = --Qur'an 25:33
    The ones who are gathered on their faces to Hell - those are the worst in position and farthest astray in [their] way. <> Waɗanda ake tãyarwa a kan fuskõkinsu, zuwa ga Jahannama, waɗancan sũ ne mafi sharri ga wuri, kuma mafi ɓacẽwa ga hanya. = --Qur'an 25:34
    And We had certainly given Moses the Scripture and appointed with him his brother Aaron as an assistant. <> Kuma lalle ne, Mun bai wa Mũsã Littãfi, kuma Mun sanya ɗan'uwansa, Hãrũna, mataimaki tãre da shi. = --Qur'an 25:35
    And We said, "Go both of you to the people who have denied Our signs." Then We destroyed them with [complete] destruction. <> Sai Muka ce: "Ku tafi, kũ biyu, zuwa ga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata game da ãyõ yinMu." sai Muka darkãke su, darkãkewa. = --Qur'an 25:36
    And the people of Noah - when they denied the messengers, We drowned them, and We made them for mankind a sign. And We have prepared for the wrongdoers a painful punishment. <> Kuma mutãnen Nũhu, a lõkacin da suka ƙaryata Manzanni, Muka nutsar da su, kuma Muka sanya su wata ãya ga mutãne, kuma Muka yi tattalin azãba mai raɗaɗi ga azzãlumai. = --Qur'an 25:37
    And [We destroyed] 'Aad and Thamud and the companions of the well and many generations between them. <> Da Ãdãwa da Samũdãwa, da mutanen Rassi, da waɗansu al'ummomi, a tsakãnin wannan, mãsu yawa. = --Qur'an 25:38
    And for each We presented examples [as warnings], and each We destroyed with [total] destruction. <> Kuma kõwannensu Mun buga masa misãlai, kuma kõwanne Mun halakar da (shi), halakarwa. = --Qur'an 25:39
    And they have already come upon the town which was showered with a rain of evil. So have they not seen it? But they are not expecting resurrection. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, (¡uraishi) sun jẽ a kan alƙaryar nan wadda aka yi wa ruwa, ruwan azãba. Shin, ba su kasance sun gan ta ba? Ã'a, sun kasance bã su ƙaunar tãyarwa (a ¡iyãma). = --Qur'an 25:40
    And when they see you, [O Muhammad], they take you not except in ridicule, [saying], "Is this the one whom Allah has sent as a messenger? <> Kuma idan sun gan ka, bã su rikon ka fãce da izgili, (sunã cẽwa) "Shin, wannan ne wanda Allah Ya aiko, Manzo? = --Qur'an 25:41
    He almost would have misled us from our gods had we not been steadfast in [worship of] them." But they are going to know, when they see the punishment, who is farthest astray in [his] way. <> "Lalle ne, yã yi kusa ya ɓatar da mu daga Ubangijinmu, in bã dõmin da muka yi haƙuri a kansu ba."Kuma zã su sani a lõkacin da suke ganin azãba, wãne ne mafi ɓacẽwa ga hanya! = --Qur'an 25:42
    Have you seen the one who takes as his god his own desire? Then would you be responsible for him? <> Shin, kã ga wanda ya riƙi UbangiJinsa son zuciyarsa? shin, to, kai ne ke kasancẽwa mai tsaro a kansa? = --Qur'an 25:43
    Or do you think that most of them hear or reason? They are not except like livestock. Rather, they are [even] more astray in [their] way. <> Ko kanã zaton cẽwa mafi yawansu sunã ji, kõ kuwa sunã hankali? sũ ba su zama ba fãce dabbõbin gida suke. Ã'a, sũ ne mafi ɓacẽwa ga hanya. = --Qur'an 25:44
    Have you not considered your Lord - how He extends the shadow, and if He willed, He could have made it stationary? Then We made the sun for it an indication. <> Ashe, ba ka dũba ba zuwa ga Ubangijinka, yadda Ya miƙe inuwa? Kuma dã Yã so dã Yã bar ta tsaye cif, sa'an nan Muka sanya rãnã mai nũni a kanta. = --Qur'an 25:45
    Then We hold it in hand for a brief grasp. <> Sa'an nan Muka karɓe ta (inuwa) zuwa gare Mu, karɓa mai sauƙi. = --Qur'an 25:46
    And it is He who has made the night for you as clothing and sleep [a means for] rest and has made the day a resurrection. <> Kuma shĩ ne wanda Ya sanya muku dare ya zama tũfa da barci ya zama hũtãwa, dã yini ya zama lokacin tãshi (kamar Tashin ¡iyãma). = --Qur'an 25:47
    And it is He who sends the winds as good tidings before His mercy, and We send down from the sky pure water <> Kuma Shi ne Ya aika iskõkin bushãra gaba ga rahamarSa, kuma Muka saukar da ruwa mai tsarkakẽwa daga sama. = --Qur'an 25:48
    That We may bring to life thereby a dead land and give it as drink to those We created of numerous livestock and men. <> Dõmin Mu rãyar, game da shi, gari matacce, kuma Mu shayar da shi dabbõbi da mutãne mãsu yawa daga abin da Muka halitta. = --Qur'an 25:49
    And We have certainly distributed it among them that they might be reminded, but most of the people refuse except disbelief. <> Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun sarrafa shi (Alƙur'ãni) a tsakãninsu, dõmin su yi tunãni, sai dai mafi yawan mutãnen sun ƙi fãce kãfirci. = --Qur'an 25:50
    And if We had willed, We could have sent into every city a warner. <> Kuma da Mun so, haƙĩƙa dã Mun aika da mai gargaɗi a ciƙin kõwace alƙarya. = --Qur'an 25:51
    So do not obey the disbelievers, and strive against them with the Qur'an a great striving. <> Sabõda haka kada ka yi ɗã'ã ga kãfirai, ka yãke su, da shi, yãƙi mai girma. = --Qur'an 25:52
    And it is He who has released [simultaneously] the two seas, one fresh and sweet and one salty and bitter, and He placed between them a barrier and prohibiting partition. <> Kuma shĩ ne Ya garwaya tẽkuna biyu, wannan mai dãdi, mai sauƙin haɗiya, kuma wannan gishiri gurɓatacce, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãninsu da kãriya mai shãmakacẽwa. = --Qur'an 25:53
    And it is He who has created from water a human being and made him [a relative by] lineage and marriage. And ever is your Lord competent [concerning creation]. <> Kuma Shi ne Ya halitta mutum daga ruwa, sai Ya sanya shi nasaba da surukuta, kuma Ubangijinka Ya kasance Mai ĩkon yi. = --Qur'an 25:54
    But they worship rather than Allah that which does not benefit them or harm them, and the disbeliever is ever, against his Lord, an assistant [to Satan]. <> Kuma sunã bauta wa, baicin Allah, abin da bã ya amfãnin su, kuma bã ya cũtar su, kuma kãfiri ya kasance mai taimakon (Shaiɗan) a kan Ubangijinsa. = --Qur'an 25:55
    And We have not sent you, [O Muhammad], except as a bringer of good tidings and a warner. <> Ba Mu aika ka ba sai kana mai bãyar da bushãra, kuma mai gargaɗi. = --Qur'an 25:56
    Say, "I do not ask of you for it any payment - only that whoever wills might take to his Lord a way." <> Ka ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa fãce wanda ya so ya riƙi wata hanya zuwa ga Ubangijinsa." = --Qur'an 25:57
    And rely upon the Ever-Living who does not die, and exalt [Allah] with His praise. And sufficient is He to be, with the sins of His servants, Acquainted - <> Kuma ka dõgara a kan Rãyayye wanda bã Ya mutuwa, kuma ka yi tasbĩhi game da gõde Masa. Kuma Yã isa zama Mai ƙididdigewa ga laifuffukan bãyinSa. = --Qur'an 25:58
    He who created the heavens and the earth and what is between them in six days and then established Himself above the Throne - the Most Merciful, so ask about Him one well informed. <> Wanda Ya halitta sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, a cikin kwãnuka shida sa'an nan Yã daidaitu a kan Al'arshi Mai rahama, sai ka tambayi mai bãyar da lãbãri game da Shi. = --Qur'an 25:59
    And when it is said to them, "Prostrate to the Most Merciful," they say, "And what is the Most Merciful? Should we prostrate to that which you order us?" And it increases them in aversion. <> Idan aka ce musu, "Ku yi sujada ga Mai rahama." Sai su ce: "Mene ne Mai rahama? Ashe zã mu yi sujada ga abin da kuke umurnin mu?"Kuma wannan (magana ta ƙãra musu gudu. = --Qur'an 25:60
    Blessed is He who has placed in the sky great stars and placed therein a [burning] lamp and luminous moon. <> Albarka ta tabbata ga Wanda Ya sanya masaukai (na tafiyar wata) a cikin sama kuma Ya sanya fitila da watã mai haskakewa a cikinta. = --Qur'an 25:61
    And it is He who has made the night and the day in succession for whoever desires to remember or desires gratitude. <> Kuma Shĩ ne wanda Ya sanya dare da yini a kan mayẽwa, ga wanda yake son ya yi tunãni, kõ kuwa ya yi nufin ya gõde. = --Qur'an 25:62
    And the servants of the Most Merciful are those who walk upon the earth easily, and when the ignorant address them [harshly], they say [words of] peace, <> Kuma bãyin Mai rahama su ne waɗanda ke yin tafiya a kan ƙasa da sauƙi, kuma idan jãhilai sun yi musu magana, sai su ce: "Salãma" (a zama lafiya). = --Qur'an 25:63
    And those who spend [part of] the night to their Lord prostrating and standing [in prayer] <> Kuma waɗanda suke kwãna sunã mãsu sujada da tsayi a wurin Ubangijinsu. = --Qur'an 25:64
    And those who say, "Our Lord, avert from us the punishment of Hell. Indeed, its punishment is ever adhering; <> Kuma waɗanda suke cẽwa "Ya Ubangijinmu! Ka karkatar da azãbar Jahannama daga gare mu. Lalle ne, azãbarta tã zama tãra = --Qur'an 25:65
    Indeed, it is evil as a settlement and residence." <> "Lalle ne ita ta mũnana ta zama wurin tabbata da mazauni." = --Qur'an 25:66
    And [they are] those who, when they spend, do so not excessively or sparingly but are ever, between that, [justly] moderate <> Kuma waɗanda suke idan sun ciyar, bã su yin ɓarna, kuma bã su yin ƙwauro, kuma (ciyarwarsu) sai ta kasance a tsakãnin wancan da tsakaitãwa. = --Qur'an 25:67
    And those who do not invoke with Allah another deity or kill the soul which Allah has forbidden [to be killed], except by right, and do not commit unlawful sexual intercourse. And whoever should do that will meet a penalty. <> Kuma waɗanda bã su kiran wani ubangiji tãre da Allah, kuma bã su kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da hakki kuma bã su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan, zai gamu da laifuffuka, = --Qur'an 25:68
    Multiplied for him is the punishment on the Day of Resurrection, and he will abide therein humiliated - <> A riɓanya masa azãba a Rãnar ¡iyãma. Kuma ya tabbata a cikinta yanã wulakantacce. = --Qur'an 25:69
    Except for those who repent, believe and do righteous work. For them Allah will replace their evil deeds with good. And ever is Allah Forgiving and Merciful. <> Sai wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai to, waɗancan Allah Yanã musanya miyãgun ayyukansu da mãsu kyau. Allah Ya kasance Mai gãfara Mai jin ƙai. = --Qur'an 25:70
    And he who repents and does righteousness does indeed turn to Allah with [accepted] repentance. <> Kuma wanda ya tũba, kuma ya aikata aiki mai kyau, to, lalle ne sai ya tũba zuwa gaAllah. = --Qur'an 25:71
    And [they are] those who do not testify to falsehood, and when they pass near ill speech, they pass by with dignity. <> Kuma waɗanda suke bã su yin shaidar zur, kuma idan sun shũɗe ga yasassar magana sai su shũɗe suna mãsu mutumci. = --Qur'an 25:72
    And those who, when reminded of the verses of their Lord, do not fall upon them deaf and blind. <> Kuma waɗanda suke idan an tunãtar da su da ãyõyin Allah, bã su saukar da kai, sunã kurame da makãfi. = --Qur'an 25:73
    And those who say, "Our Lord, grant us from among our wives and offspring comfort to our eyes and make us an example for the righteous." <> Kuma waɗanda suke cẽwa "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu sanyin idãnu daga mãtanmu da zũriyarmu, kuma Ka sanya mu shũgabanni ga mãsu taƙawa." = --Qur'an 25:74
    Those will be awarded the Chamber for what they patiently endured, and they will be received therein with greetings and [words of] peace. <> Waɗannan anã sãka musu da bẽne, sabõda haƙurin da suka yi, kuma a haɗa su, a cikinsa, da gaisuwa da aminci. = --Qur'an 25:75
    Abiding eternally therein. Good is the settlement and residence. <> Suna madawwama a cikinsa. Ya yi kyau ga zama matabbaci da mazauni. = --Qur'an 25:76
    Say, "What would my Lord care for you if not for your supplication?" For you [disbelievers] have denied, so your denial is going to be adherent. <> Ka ce: "Ubangijĩna ba Ya kula da ku in bã dõmin addu'arku ba. To, lalle ne, kun ƙaryata, sabõda haka al'amarin zã ya zama malizimci." = --Qur'an 25:77
    Ta, Seen, Meem. <> ¦. S̃. M̃. = --Qur'an 26:1
    These are the verses of the clear Book. <> Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne. = --Qur'an 26:2
    Perhaps, [O Muhammad], you would kill yourself with grief that they will not be believers. <> Tsammãninka kai mai halakar da ranka ne, dõmin ba su kasance mũminai ba! = --Qur'an 26:3
    If We willed, We could send down to them from the sky a sign for which their necks would remain humbled. <> Idan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai. = --Qur'an 26:4
    And no revelation comes to them anew from the Most Merciful except that they turn away from it. <> Kuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance daga barinta sunã mãsu bijirẽwa. = --Qur'an 26:5
    For they have already denied, but there will come to them the news of that which they used to ridicule. <> To, lalle ne, sun ƙaryata, to, lãbãran abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi zã ya je musu. = --Qur'an 26:6
    Did they not look at the earth - how much We have produced therein from every noble kind? <> Shin, ba su dũba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan nau'i mai kyau? = --Qur'an 26:7
    Indeed in that is a sign, but most of them were not to be believers. <> Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mũminai ba. = --Qur'an 26:8
    And indeed, your Lord - He is the Exalted in Might, the Merciful. <> Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai rahama. = --Qur'an 26:9
    And [mention] when your Lord called Moses, [saying], "Go to the wrongdoing people - <> Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya kirãyi Mũsã, "Ka je wa mutãnen nan azzãlumai. = --Qur'an 26:10
    The people of Pharaoh. Will they not fear Allah?" <> "Mutãnen Fir'auna bã zã su yi taƙawa ba?" = --Qur'an 26:11
    He said, "My Lord, indeed I fear that they will deny me <> Ya ce: "Ya Ubangijĩna, nĩ inã tsõron su ƙaryata ni. = --Qur'an 26:12
    And that my breast will tighten and my tongue will not be fluent, so send for Aaron. <> "Kuma ƙirjĩna ya yi ƙunci kuma harshẽna bã zai saku ba sabõda haka ka aika zuwa ga Harũna. = --Qur'an 26:13
    And they have upon me a [claim due to] sin, so I fear that they will kill me." <> "Kuma sunã da wani laifi a kaina, sabõda haka inã tsõron kada su kashe ni." = --Qur'an 26:14
    [Allah] said, "No. Go both of you with Our signs; indeed, We are with you, listening. <> Ya ce: "Kayya! Ku tafi, kũ biyu, da ÃyõyinMu. Lalle ne, Munã tãre da ku Munã Mãsu saurãre." = --Qur'an 26:15
    Go to Pharaoh and say, 'We are the messengers of the Lord of the worlds, <> "Sai ku je wa Fir'auna, sa'an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin halitta ne." = --Qur'an 26:16
    [Commanded to say], "Send with us the Children of Israel."'" <> "Ka saki Banĩ Isrã'ila tãre da mu." = --Qur'an 26:17
    [Pharaoh] said, "Did we not raise you among us as a child, and you remained among us for years of your life? <> Ya ce: "Shin, ba mu yi rẽnonka ba a cikinmu kanã jãrĩri, kuma ka zauna a cikinmu shẽkarudaga lõkacin rãyuwarka?" = --Qur'an 26:18
    And [then] you did your deed which you did, and you were of the ungrateful." <> "Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhãli kai kanã daga butulai?" = --Qur'an 26:19
    [Moses] said, "I did it, then, while I was of those astray. <> Ya ce: "Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin hushi." = --Qur'an 26:20
    So I fled from you when I feared you. Then my Lord granted me wisdom and prophethood and appointed me [as one] of the messengers. <> "Sabõda haka na gudu daga gãre ku a lõkacin da na ji tsõronku, sai Ubangijĩna Ya bã ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni." = --Qur'an 26:21
    And is this a favor of which you remind me - that you have enslaved the Children of Israel?" <> "Kuma waccan ni'ima ce, kanã gõrint a kaina, dõmin kã bautar da Banĩ Isrã'ĩla." = --Qur'an 26:22
    Said Pharaoh, "And what is the Lord of the worlds?" <> Fir'auna ya ce: "Kuma mene ne Ubangijin halittu?" = --Qur'an 26:23
    [Moses] said, "The Lord of the heavens and earth and that between them, if you should be convinced." <> Ya ce: "Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu ƙarfin ĩmãni." = --Qur'an 26:24
    [Pharaoh] said to those around him, "Do you not hear?" <> Ya ce wa waɗanda suke a gẽfensa, "Bã za ku saurãra ba?" = --Qur'an 26:25
    [Moses] said, "Your Lord and the Lord of your first forefathers." <> Ya ce: "Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko." = --Qur'an 26:26
    [Pharaoh] said, "Indeed, your 'messenger' who has been sent to you is mad." <> Ya ce: "Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne." = --Qur'an 26:27
    [Moses] said, "Lord of the east and the west and that between them, if you were to reason." <> Ya ce: "Ubangijin mafitar rãnã da maɓũyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan kun kasance kunã hankalta." = --Qur'an 26:28
    [Pharaoh] said, "If you take a god other than me, I will surely place you among those imprisoned." <> Ya ce: "Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautãwa wanĩna haƙĩƙa, inã sanyã ka daga ɗaurarru." = --Qur'an 26:29
    [Moses] said, "Even if I brought you proof manifest?" <> Ya ce: "Ashe, kuma kõ dã nã zõ maka da wani, abu mai bayyanãwa?" = --Qur'an 26:30
    [Pharaoh] said, "Then bring it, if you should be of the truthful." <> Ya ce: "To, ka zõ da shi idan ka kasance daga, mãsu gaskiya." = --Qur'an 26:31
    So [Moses] threw his staff, and suddenly it was a serpent manifest. <> Sai ya jẽfa sandarsa, sai ga ta kumurci bayyananne. = --Qur'an 26:32
    And he drew out his hand; thereupon it was white for the observers. <> Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu kallo. = --Qur'an 26:33
    [Pharaoh] said to the eminent ones around him, "Indeed, this is a learned magician. <> (Fir'auna) ya ce ga mashãwarta a gẽfensa, "Lalle ne, wannan haƙĩƙa, masihirci ne, mai ilmi! = --Qur'an 26:34
    He wants to drive you out of your land by his magic, so what do you advise?" <> "Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mẽne ne kuke shãwartãwa?" = --Qur'an 26:35
    They said, "Postpone [the matter of] him and his brother and send among the cities gatherers <> Suka ce: "Ka jinkirtar da shi, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika mãsu gayya a cikin birãne." = --Qur'an 26:36
    Who will bring you every learned, skilled magician." <> "Zã su zõ maka da dukkan mai yawan sihiri masani." = --Qur'an 26:37
    So the magicians were assembled for the appointment of a well-known day. <> Sai aka tãra masihirta dõmin ajalin yini sananne. = --Qur'an 26:38
    And it was said to the people, "Will you congregate <> Kuma aka ce wa mutãne "Kõ kũ mãsu tãruwã ne? = --Qur'an 26:39
    That we might follow the magicians if they are the predominant?" <> "Tsammãninmu mu bi masihirta, idan sun kasance sũ ne marinjãya." = --Qur'an 26:40
    And when the magicians arrived, they said to Pharaoh, "Is there indeed for us a reward if we are the predominant?" <> To, a lõkacin da masihirta suka jẽ suka ce wa Fir'auna,"Shin, lalle ne, haƙĩƙa munã da ijãra idan mun kasance mũ ne marinjãya?" = --Qur'an 26:41
    He said, "Yes, and indeed, you will then be of those near [to me]." <> Ya ce: "Na'am! Kuma lalle ne, kũ ne a lõkacin haƙĩƙa muƙarrabai." = --Qur'an 26:42
    Moses said to them, "Throw whatever you will throw." <> Mũsã ya ce musu, "Ku jẽfa abin da kuke mãsu jẽfãwa." = --Qur'an 26:43
    So they threw their ropes and their staffs and said, "By the might of Pharaoh, indeed it is we who are predominant." <> Sai suka jẽfa igiyõyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: "Da ƙarfin Fir'auna lalle ne mũ, haƙĩƙa, mũ ne marinjãya." = --Qur'an 26:44
    Then Moses threw his staff, and at once it devoured what they falsified. <> Sai Mũsa ya jẽfa sandarsa, sai ga ta tanã harhaɗe abin da suke yi na ƙarya. = --Qur'an 26:45
    So the magicians fell down in prostration [to Allah]. <> Sai aka jẽfar da masihirta sunã mãsu sujada. = --Qur'an 26:46
    They said, "We have believed in the Lord of the worlds, <> Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halitta." = --Qur'an 26:47
    The Lord of Moses and Aaron." <> "Ubangijin Mũsa da Hãrũna." = --Qur'an 26:48
    [Pharaoh] said, "You believed Moses before I gave you permission. Indeed, he is your leader who has taught you magic, but you are going to know. I will surely cut off your hands and your feet on opposite sides, and I will surely crucify you all." <> Ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni sabõda shĩ, a gabãnin in yi muku izni? Lalle ne shi, haƙĩƙa babbanku ne wanda ya kõya muku sihirin, to, zã ku sani. Lalle ne haƙĩƙa, zan kakkãtse hannuwanku da kafãfunku a tarnaƙi, kuma haƙĩƙa, zan tsĩrẽ ku gabã ɗaya." = --Qur'an 26:49
    They said, "No harm. Indeed, to our Lord we will return. <> Suka ce: "Bãbu wata cũta! Lalle ne mũ mãsu jũyãwa ne zuwa ga Ubangijinmu." = --Qur'an 26:50
    Indeed, we aspire that our Lord will forgive us our sins because we were the first of the believers." <> "Lalle ne mu munã kwaɗayin Ubangijinmu, Ya gãfarta mana kurakuranmu dõmin mun kasance farkon mãsu ĩmãni." = --Qur'an 26:51
    And We inspired to Moses, "Travel by night with My servants; indeed, you will be pursued." <> Kuma Muka aika zuwa ga Mũsã cẽwa ka yi tafiyar dare da bãyiNa, lalle ne kũ waɗanda ake biyã ne. = --Qur'an 26:52
    Then Pharaoh sent among the cities gatherers <> Sai Fir'auna ya aika mãsu gayya a cikin birãne. = --Qur'an 26:53
    [And said], "Indeed, those are but a small band, <> "Lalle ne, waɗannan, haƙĩƙa, ƙungiya ce kaɗan." = --Qur'an 26:54
    And indeed, they are enraging us, <> "Kuma lalle ne sũ, a gare Mu, Mãsu fusãtarwa ne." = --Qur'an 26:55
    And indeed, we are a cautious society... " <> "Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa gabã ɗaya mãsu sauna ne." = --Qur'an 26:56
    So We removed them from gardens and springs <> Sai Muka fitar da su daga gonaki da marẽmari. = --Qur'an 26:57
    And treasures and honorable station - <> Da taskõki da mazauni mai kyau. = --Qur'an 26:58
    Thus. And We caused to inherit it the Children of Israel. <> Kamar haka! Kuma Muka gãdar da su ga Banĩ Isrãĩla. = --Qur'an 26:59
    So they pursued them at sunrise. <> Sai suka bĩ su sunã mãsu fita a lõkacin hũdõwar rãnã. = --Qur'an 26:60
    And when the two companies saw one another, the companions of Moses said, "Indeed, we are to be overtaken!" <> Sa'an nan a lõkacin da jama'a biyu suka ga jũna, sai abõkan Mũsã suka ce: "Lalle ne mũ haƙĩ ƙa, waɗanda ake riska ne." = --Qur'an 26:61
    [Moses] said, "No! Indeed, with me is my Lord; He will guide me." <> Ya ce: "Kayya! Lalle ne Ubangijina Yanã tare da ni, zai shiryar da ni." = --Qur'an 26:62
    Then We inspired to Moses, "Strike with your staff the sea," and it parted, and each portion was like a great towering mountain. <> Sai Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa "Ka dõki tẽku da sandarka." Sai tẽku ta tsãge, kõwane tsãgi ya kasance kamar falalen dũtse mai girma. = --Qur'an 26:63
    And We advanced thereto the pursuers. <> Kuma Muka kusantar da waɗansu mutãne a can. = --Qur'an 26:64
    And We saved Moses and those with him, all together. <> Kuma Muka tsĩrar da Mũsã da waɗanda suke tãre da shi gabã ɗaya. = --Qur'an 26:65
    Then We drowned the others. <> Sa'an nan kuma Muka nutsar da waɗansu mutãnen. = --Qur'an 26:66
    Indeed in that is a sign, but most of them were not to be believers. <> Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba. = --Qur'an 26:67
    And indeed, your Lord - He is the Exalted in Might, the Merciful. <> Kuma lalle ne Ubangijinka, kaƙĩƙa, Shĩ ne Mabũwayi, Mai jin ƙai. = --Qur'an 26:68
    And recite to them the news of Abraham, <> Kuma ka karanta, a kansu, lãbãrin Ibrãhĩm. = --Qur'an 26:69
    When he said to his father and his people, "What do you worship?" <> A sã'ilin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bauta wa?" = --Qur'an 26:70
    They said, "We worship idols and remain to them devoted." <> Suka ce: "Munã bauta wa gumãka, sabõda haka munã yini mãsu lazimta a gare su." = --Qur'an 26:71
    He said, "Do they hear you when you supplicate? <> Ya ce: "Shin, sunã jin ku, a lõkacin da kuke kira?" = --Qur'an 26:72
    Or do they benefit you, or do they harm?" <> "Kõ kuwa sunã amfãnin ku, kõ sunã cũtar ku?" = --Qur'an 26:73
    They said, "But we found our fathers doing thus." <> Suka ce: "Ã'a mun sãmĩ ubanninmu, kamar haka ne suke aikatãwa." = --Qur'an 26:74
    He said, "Then do you see what you have been worshipping, <> Ya ce: "Shin to, kun ga abin da kuka kasance kunã bautã wa?" = --Qur'an 26:75
    You and your ancient forefathers? <> "Kũ da ubanninku mafi daɗẽwa?" = --Qur'an 26:76
    Indeed, they are enemies to me, except the Lord of the worlds, <> "To lalle ne, sũ maƙiya ne a gare ni, fãce Ubangijin halittu." = --Qur'an 26:77
    Who created me, and He [it is who] guides me. <> "Wanda Ya halitta ni, sa'an nan Yanã shiryar da ni." = --Qur'an 26:78
    And it is He who feeds me and gives me drink. <> "Kuma Wanda Yake Shĩ ne Yake ciyar da ni, kuma Yanã shãyar da ni." = --Qur'an 26:79
    And when I am ill, it is He who cures me <> "Kuma idan na yi jiyya, to, Shĩ ne Yake warkar da ni." = --Qur'an 26:80
    And who will cause me to die and then bring me to life <> "Kuma wanda Yake matar da ni, sa'an nan Ya rãyar da ni." = --Qur'an 26:81
    And who I aspire that He will forgive me my sin on the Day of Recompense." <> "Kuma wanda Yake inã kwaɗayin Ya gãfarta mini kurãkuraina, a rãnar sãkamako." = --Qur'an 26:82
    [And he said], "My Lord, grant me authority and join me with the righteous. <> "Ya Ubangijĩna! Ka ba ni hukunci, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai." = --Qur'an 26:83
    And grant me a reputation of honor among later generations. <> "Kuma Ka sanya mini harshen gaskiya a cikin mutãnen ƙarshe." = --Qur'an 26:84
    And place me among the inheritors of the Garden of Pleasure. <> "Kuma Ka sanya ni daga magãdan Aljannar ni'ima." = --Qur'an 26:85
    And forgive my father. Indeed, he has been of those astray. <> "Kuma Ka gãfarta wa ubãna, lalle ne shi, ya kasance daga ɓatattu." = --Qur'an 26:86
    And do not disgrace me on the Day they are [all] resurrected - <> "Kuma kada Ka kunyata ni a rãnar da ake tãyar da su." = --Qur'an 26:87
    The Day when there will not benefit [anyone] wealth or children <> "A rãnar da dũkiya bã ta amfãni, kuma ɗiya bã su yi." = --Qur'an 26:88
    But only one who comes to Allah with a sound heart." <> "Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki." = --Qur'an 26:89
    And Paradise will be brought near [that Day] to the righteous. <> Kuma aka kusantar da Aljanna ga mãsu taƙawa. = --Qur'an 26:90
    And Hellfire will be brought forth for the deviators, <> Kuma aka fitar da wutã babba dõmin halakakku. = --Qur'an 26:91
    And it will be said to them, "Where are those you used to worship <> Kuma aka ce musu, "Inã abin da kuka kasance kunã bautawa?" = --Qur'an 26:92
    Other than Allah? Can they help you or help themselves?" <> "Baicin Allah? Shin sunã tamakon ku kõ kuwa sunã tsare kansu?" = --Qur'an 26:93
    So they will be overturned into Hellfire, they and the deviators <> Sai aka kikkife su a cikinta, su da halakakkun. = --Qur'an 26:94
    And the soldiers of Iblees, all together. <> Da rundunar Ibilĩsa gabã ɗaya. = --Qur'an 26:95
    They will say while they dispute therein, <> Suka ce: alhãli sunã a cikinta sunã yin husũma, = --Qur'an 26:96
    "By Allah, we were indeed in manifest error <> "Rantsuwa da Allah! Lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, a cikin ɓata bayyananna." = --Qur'an 26:97
    When we equated you with the Lord of the worlds. <> "A lõkacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu. = --Qur'an 26:98
    And no one misguided us except the criminals. <> "Kuma bãbu abin da ya ɓatar da mu fãce mãsu laifi." = --Qur'an 26:99
    So now we have no intercessors <> "Sabõda haka bã mu da waɗansu macẽta." = --Qur'an 26:100
    And not a devoted friend. <> "Kuma bã mu da abõki, masõyi." = --Qur'an 26:101
    Then if we only had a return [to the world] and could be of the believers... " <> "Sabõda haka dã lalle munã da (dãmar) kõmawa, dõmin mu kasance daga mũminai!" = --Qur'an 26:102
    Indeed in that is a sign, but most of them were not to be believers. <> Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, bã su kasance mũminai ba. = --Qur'an 26:103
    And indeed, your Lord - He is the Exalted in Might, the Merciful. <> Kuma lalle ne, Ubangijinka, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. = --Qur'an 26:104
    The people of Noah denied the messengers <> Mutãnen Nũhu sun ƙaryata Manzanni. = --Qur'an 26:105
    When their brother Noah said to them, "Will you not fear Allah? <> A lõkacin da ɗan'uwansu, Nũhu, ya ce musu, "Shin, bã zã ku yi taƙawa ba?" = --Qur'an 26:106
    Indeed, I am to you a trustworthy messenger. <> "Lalle ne, zuwa gare ku, ni Manzo ne amintacce." = --Qur'an 26:107
    So fear Allah and obey me. <> "To, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." = --Qur'an 26:108
    And I do not ask you for it any payment. My payment is only from the Lord of the worlds. <> "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãtã ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu." = --Qur'an 26:109
    So fear Allah and obey me." <> "Sabõda haka, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." = --Qur'an 26:110
    They said, "Should we believe you while you are followed by the lowest [class of people]?" <> Suka ce: "Ashe, zã mu yi ĩmãni sabõda kai alhãli kuwa mafiya ƙasƙanci sun bi ka?" = --Qur'an 26:111
    He said, "And what is my knowledge of what they used to do? <> Ya ce: "Kuma bã ni da sani ga abin da suka kasance sanã aikatãwa." = --Qur'an 26:112
    Their account is only upon my Lord, if you [could] perceive. <> "Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa." = --Qur'an 26:113
    And I am not one to drive away the believers. <> "Ban zama mai kõre mũminai ba." = --Qur'an 26:114
    I am only a clear warner." <> "Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa." = --Qur'an 26:115
    They said, "If you do not desist, O Noah, you will surely be of those who are stoned." <> Suka ce: "Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, (daga maganarka,) haƙĩƙa, kanã kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa" = --Qur'an 26:116
    He said, "My Lord, indeed my people have denied me. <> Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne mutãnena sun ƙaryatã ni." = --Qur'an 26:117
    Then judge between me and them with decisive judgement and save me and those with me of the believers." <> "Sai ka yi hukunci, a tsakãnĩna da tsakãninsu tabbataccen hukanci, kuma ka tsĩrar da ni, da waɗanda suke tãre da ni daga mũminai." = --Qur'an 26:118
    So We saved him and those with him in the laden ship. <> Sai Muka tsĩrar da shi, shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgi wanda aka yi wa lõdi. = --Qur'an 26:119
    Then We drowned thereafter the remaining ones. <> Sa'an nan Muka nutsar a bãyan haka, da sauran. = --Qur'an 26:120
    Indeed in that is a sign, but most of them were not to be believers. <> Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba. = --Qur'an 26:121
    And indeed, your Lord - He is the Exalted in Might, the Merciful. <> Kuma Lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Rahama. = --Qur'an 26:122
    'Aad denied the messengers <> Ãdãwa sun ƙaryata Manzanni. = --Qur'an 26:123
    When their brother Hud said to them, "Will you not fear Allah? <> A lõkacin da ɗan'uwansu, Hũdu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?" = --Qur'an 26:124
    Indeed, I am to you a trustworthy messenger. <> "Lalle ne ni, zuwa gare ku, haƙĩƙa, Manzo ne, amintacce." = --Qur'an 26:125
    So fear Allah and obey me. <> "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." = --Qur'an 26:126
    And I do not ask you for it any payment. My payment is only from the Lord of the worlds. <> "Kuma bã ni tambayar wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba, fãce daga Ubangijin halittu." = --Qur'an 26:127
    Do you construct on every elevation a sign, amusing yourselves, <> "Shin, kunã yin ginin sitadiyo a kõwane tsauni ne, kunã yin wãsa?" = --Qur'an 26:128
    And take for yourselves palaces and fortresses that you might abide eternally? <> "Kuma kunã riƙon matsãrar ruwa, tsammãninku, ku dawwama?" = --Qur'an 26:129
    And when you strike, you strike as tyrants. <> "Kuma idan kun yi damƙa, sai ku yi damƙar kunã mãsu tanƙwasãwa." = --Qur'an 26:130
    So fear Allah and obey me. <> "To ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." = --Qur'an 26:131
    And fear He who provided you with that which you know, <> "Ku ji tsõron wanda Ya taimake ku da abin da kuka sani." = --Qur'an 26:132
    Provided you with grazing livestock and children <> "Ya taimake ku da dabbõbin ni'ima da ɗiya." = --Qur'an 26:133
    And gardens and springs. <> "Da gõnaki da marẽmari." = --Qur'an 26:134
    Indeed, I fear for you the punishment of a terrible day." <> "Lalle ne nĩ, inã ji muku tsõron azãbar wani yini mai girma." = --Qur'an 26:135
    They said, "It is all the same to us whether you advise or are not of the advisors. <> Suka ce: "Daidai ne a kanmu: Kã yi wa'azi kõ ba ka kasance daga mãsu wa'azi ba." = --Qur'an 26:136
    This is not but the custom of the former peoples, <> "Wannan abu bai zamõ ba fãce hãlãyen mutãnen farko." = --Qur'an 26:137
    And we are not to be punished." <> "Kuma mũ ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba." = --Qur'an 26:138
    And they denied him, so We destroyed them. Indeed in that is a sign, but most of them were not to be believers. <> Sabõda haka suka ƙaryata shi, sai Muka halakar da sũ. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba. = --Qur'an 26:139
    And indeed, your Lord - He is the Exalted in Might, the Merciful. <> Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. = --Qur'an 26:140
    Thamud denied the messengers <> Samũdãwa sun ƙaryata Manzanni. = --Qur'an 26:141
    When their brother Salih said to them, "Will you not fear Allah? <> A lõkacin da ɗan'uwansu Sãlihu ya ce: "Shin, bã zã ku bi Allah da taƙawa ba?" = --Qur'an 26:142
    Indeed, I am to you a trustworthy messenger. <> "Lalle ne nĩ zuwã gare ku, Manzo ne, amintacce." = --Qur'an 26:143
    So fear Allah and obey me. <> "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã. = --Qur'an 26:144
    And I do not ask you for it any payment. My payment is only from the Lord of the worlds. <> "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba fãce da a Ubangijin halittu." = --Qur'an 26:145
    Will you be left in what is here, secure [from death], <> "Shin, anã barin ku a cikin abin da yake a nan, kunã amintattu?" = --Qur'an 26:146
    Within gardens and springs <> "A cikin gõnaki da marẽmari." = --Qur'an 26:147
    And fields of crops and palm trees with softened fruit? <> "Da shuke-shuke da dabĩ nai, 'ya'yan itãcensu hirtsi mãsu narkẽwa a ciki?" = --Qur'an 26:148
    And you carve out of the mountains, homes, with skill. <> "Kuma kunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, kunã mãsu alfãhari?" = --Qur'an 26:149
    So fear Allah and obey me. <> "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." = --Qur'an 26:150
    And do not obey the order of the transgressors, <> "Kada ku yi ɗã'ã ga umurnin maɓarnata." = --Qur'an 26:151
    Who cause corruption in the land and do not amend." <> "Waɗanda suke yin ɓarna a cikin ƙasa, kuma bã su kyautatãwa." = --Qur'an 26:152
    They said, "You are only of those affected by magic. <> Suka ce: "Kai daga mãsu sihiri kurum kake." = --Qur'an 26:153
    You are but a man like ourselves, so bring a sign, if you should be of the truthful." <> "Bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu. To, kã zo da wata ãyã idan kã kasance daga mãsu gaskiya." = --Qur'an 26:154
    He said, "This is a she-camel. For her is a [time of] drink, and for you is a [time of] drink, [each] on a known day. <> Ya ce: "Wannan rãkuma ce tanã da shan yini, kuma kunã da shan yini sasanne." = --Qur'an 26:155
    And do not touch her with harm, lest you be seized by the punishment of a terrible day." <> "Kada ku shãfe ta da cũta har azãbar yini mai girmã ta shãfe ku." = --Qur'an 26:156
    But they hamstrung her and so became regretful. <> Sai suka sõke ta sa'an nan suka wãyi gari sunã mãsu nadãma. = --Qur'an 26:157
    And the punishment seized them. Indeed in that is a sign, but most of them were not to be believers. <> Sabõda haka azãba ta kãma su. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba. = --Qur'an 26:158
    And indeed, your Lord - He is the Exalted in Might, the Merciful. <> Lalle ne Ubangijinka, haƙĩ ƙa, Shĩ ne Mabuwayi, Mai jin ƙai. = --Qur'an 26:159
    The people of Lot denied the messengers <> Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata Manzanni. = --Qur'an 26:160
    When their brother Lot said to them, "Will you not fear Allah? <> A lõkacin da ɗan'uwansu, Lũɗu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?" = --Qur'an 26:161
    Indeed, I am to you a trustworthy messenger. <> "Lalle ne nĩ, zuwa gare ku, Manzõ ne, amintacce." = --Qur'an 26:162
    So fear Allah and obey me. <> "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." = --Qur'an 26:163
    And I do not ask you for it any payment. My payment is only from the Lord of the worlds. <> "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra, Ijãrãta ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu." = --Qur'an 26:164
    Do you approach males among the worlds <> "Shin kunã jẽ wa maza daga cikin talikai?" = --Qur'an 26:165
    And leave what your Lord has created for you as mates? But you are a people transgressing." <> "Kuma kunã barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga mãtanku? Ã'a, ku mutãne ne mãsu ƙẽtarẽwa!" = --Qur'an 26:166
    They said, "If you do not desist, O Lot, you will surely be of those evicted." <> Suka ce: "Lalle ne haƙĩƙa idan ba ka hanu ba, yã Lũɗu! Tĩlas ne kanã kasancẽwa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari)." = --Qur'an 26:167
    He said, "Indeed, I am, toward your deed, of those who detest [it]. <> Ya ce: "Lalle ne ga aikinku, haƙĩƙa, inã daga mãsu ƙinsa." = --Qur'an 26:168
    My Lord, save me and my family from [the consequence of] what they do." <> "Ya Ubangijina! Ka tsĩrar da ni da iyãlĩna daga abin da suke aikatãwa." = --Qur'an 26:169
    So We saved him and his family, all, <> Sabõda haka Muka tsĩrar da shi, Shi da mutãnensa gabã ɗaya. = --Qur'an 26:170
    Except an old woman among those who remained behind. <> Fãce wata tsõhuwa a cikin mãsu wanzuwa. = --Qur'an 26:171
    Then We destroyed the others. <> Sa'an nan kuma Muka darkãke wasu. = --Qur'an 26:172
    And We rained upon them a rain [of stones], and evil was the rain of those who were warned. <> Kuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana. = --Qur'an 26:173
    Indeed in that is a sign, but most of them were not to be believers. <> Lalle ne ga wannan, akwai ãyã, kuma mafi yawansu bã su kasance mãsu ĩmãni ba. = --Qur'an 26:174
    And indeed, your Lord - He is the Exalted in Might, the Merciful. <> Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. = --Qur'an 26:175
    The companions of the thicket denied the messengers <> Ma'abũta ƙunci sun ƙaryata Manzanni. = --Qur'an 26:176
    When Shu'ayb said to them, "Will you not fear Allah? <> A lõkacin da Shu'aibu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?" = --Qur'an 26:177
    Indeed, I am to you a trustworthy messenger. <> "Lalle ne ni, zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce." = --Qur'an 26:178
    So fear Allah and obey me. <> "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa kuma ku yi mini ɗã'ã." = --Qur'an 26:179
    And I do not ask you for it any payment. My payment is only from the Lord of the worlds. <> "Kuma ba ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu." = --Qur'an 26:180
    Give full measure and do not be of those who cause loss. <> "Ku cika mũdu, kuma kada ku kasance daga mãsu sanyãwar hasãra (ga mutãne)." = --Qur'an 26:181
    And weigh with an even balance. <> "Kuma ku yi awo da sikẽli daidaitacce." = --Qur'an 26:182
    And do not deprive people of their due and do not commit abuse on earth, spreading corruption. <> "Kuma kada ku nakasa wa mutãne abũbuwansu kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa kuna mãsu ɓarna." = --Qur'an 26:183
    And fear He who created you and the former creation." <> "Kuma ku ji tsõron Allah wanda Ya halitta ku, kũ da jama'ar farko." = --Qur'an 26:184
    They said, "You are only of those affected by magic. <> Suka ce: "Kai dai daga waɗanda suke sihirtattu kawai ne." = --Qur'an 26:185
    You are but a man like ourselves, and indeed, we think you are among the liars. <> "Kuma bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu kuma lalle ne munã zaton ka, haƙĩƙa, daga maƙaryata." = --Qur'an 26:186
    So cause to fall upon us fragments of the sky, if you should be of the truthful." <> "To ka jẽfo wani ɓaɓɓake daga sama a kanmu, idan ka kasance daga mãsu gaskiya." = --Qur'an 26:187
    He said, "My Lord is most knowing of what you do." <> Ya ce: "Ubangijĩna ne Mafi sani ga abin da kuke aikatãwa." = --Qur'an 26:188
    And they denied him, so the punishment of the day of the black cloud seized them. Indeed, it was the punishment of a terrible day. <> Sai suka ƙaiyatã shi, sabõda haka, azãbar rãnar girgije ta kãma su. Lalle ne ita, tã kasance azãbar yini mai girma. = --Qur'an 26:189
    Indeed in that is a sign, but most of them were not to be believers. <> Lalle a cikin wancan haƙĩka akwai ãya, amma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba. = --Qur'an 26:190
    And indeed, your Lord - He is the Exalted in Might, the Merciful. <> Kuma lalle Ubangijĩnka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. = --Qur'an 26:191
    And indeed, the Qur'an is the revelation of the Lord of the worlds. <> Kuma lalle shi (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, saukarwar Ubangijinhalittu ne. = --Qur'an 26:192
    The Trustworthy Spirit has brought it down <> Rũhi amintacce ne ya sauka da shi. = --Qur'an 26:193
    Upon your heart, [O Muhammad] - that you may be of the warners - <> A kan zũciyarka, dõmin ka kasance daga mãsu gargaɗi. = --Qur'an 26:194
    In a clear Arabic language. <> Da harshe na Larabci mai bayãni. = --Qur'an 26:195
    And indeed, it is [mentioned] in the scriptures of former peoples. <> Kuma lalle shin, haƙĩƙa, yanã a cikin litattafan (Manzannin) farko. = --Qur'an 26:196
    And has it not been a sign to them that it is recognized by the scholars of the Children of Israel? <> Ashe, bai kasance ãyã ba a gare su, ya zama Mãlaman Banĩ Isrã'ĩla sun san shi? = --Qur'an 26:197
    And even if We had revealed it to one among the foreigners <> Kuma dã mun saukar da shi a kan sãshen Ajamãwa, = --Qur'an 26:198
    And he had recited it to them [perfectly], they would [still] not have been believers in it. <> Ya karanta shi a kansu, ba su kasance sabõda shi mãsu ĩmãni ba. = --Qur'an 26:199
    Thus have We inserted disbelief into the hearts of the criminals. <> Kamar wancan ne! Muka shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi. = --Qur'an 26:200
    They will not believe in it until they see the painful punishment. <> Bã zã su yi ĩmãni da shĩ ba sai sun ga azãbar nan mai raɗadi. = --Qur'an 26:201
    And it will come to them suddenly while they perceive [it] not. <> Sai ta taho musu kwatsam, alhãli kuwa sũ, ba su sansance ba. = --Qur'an 26:202
    And they will say, "May we be reprieved?" <> Sai su ce: "Shin, mu waɗanda ake yi wa jinkiri ne?" = --Qur'an 26:203
    So for Our punishment are they impatient? <> Ashe, to, da azãbarMu suke nẽman gaggãwa? = --Qur'an 26:204
    Then have you considered if We gave them enjoyment for years <> Ashe, to, kã gani, idan Muka jĩshe su daɗi a shẽkaru, = --Qur'an 26:205
    And then there came to them that which they were promised? <> Sa'an nan abin da suka kasance anã yi musu wa'adi (da shi) ya jẽ musu, = --Qur'an 26:206
    They would not be availed by the enjoyment with which they were provided. <> Abin da suka kasance anã jĩshe su dãɗin bã zai tunkuɗe azãba ba daga gare su. = --Qur'an 26:207
    And We did not destroy any city except that it had warners <> Kuma bã Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da mãsu gargaɗi. = --Qur'an 26:208
    As a reminder; and never have We been unjust. <> Dõmin tunãtarwa, kuma ba Mu kasance Mãsu zãlunci ba. = --Qur'an 26:209
    And the devils have not brought the revelation down. <> Kuma (Alƙur'ãni) Shaiɗãnu ba su ɗõra sauka da shĩba. = --Qur'an 26:210
    It is not allowable for them, nor would they be able. <> Kuma bã ya kamãta a gare su (su Shaiɗãnu su sauka da shi), kuma ba su iyãwa. = --Qur'an 26:211
    Indeed they, from [its] hearing, are removed. <> Lalle ne sũ, daga saurãre, haƙĩƙa, waɗanda aka nĩsantar ne. = --Qur'an 26:212
    So do not invoke with Allah another deity and [thus] be among the punished. <> Sabõda haka, kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah, sai ka kasance daga waɗanda ake yi wa azãba. = --Qur'an 26:213
    And warn, [O Muhammad], your closest kindred. <> Kuma ka yi gargaɗi ga danginka mafiya kusanci. = --Qur'an 26:214
    And lower your wing to those who follow you of the believers. <> Kuma ka sassauta fikãfikanka ga wanda ya bĩ ka daga mũminai. = --Qur'an 26:215
    And if they disobey you, then say, "Indeed, I am disassociated from what you are doing." <> Sa'an nan idan suka sãɓã maka to ka ce: "Lalle nĩ, barrantacce ne daga abin da kuko aikatãwa." = --Qur'an 26:216
    And rely upon the Exalted in Might, the Merciful, <> Kuma ka dõgara ga Mabuwãyi, Mai jin ƙai. = --Qur'an 26:217
    Who sees you when you arise <> Wanda Yake ganin ka a lõkacin da kake tãshi tsaye. = --Qur'an 26:218
    And your movement among those who prostrate. <> Da jujjuyãwarka a cikin mãsu yin sujada. = --Qur'an 26:219
    Indeed, He is the Hearing, the Knowing. <> Lalle Shi, Shi ne Mai ji, Masani. = --Qur'an 26:220
    Shall I inform you upon whom the devils descend? <> Shin, (kunã so) in gaya muku a kan wanda Shaiɗãnnu kan sauka? = --Qur'an 26:221
    They descend upon every sinful liar. <> Sukan sauka a kan dukkan maƙaryaci, mai zunubi. = --Qur'an 26:222
    They pass on what is heard, and most of them are liars. <> Sunã jẽfa (abin da suka) ji, alhãli kuwa mafi yawansu maƙaryata ne. = --Qur'an 26:223
    And the poets - [only] the deviators follow them; <> Kuma mawãƙa halakakku ne ke bin su. = --Qur'an 26:224
    Do you not see that in every valley they roam <> Shin, ba ku cẽwa, lalle ne sũ, cikin kõwane rango sunã yin ɗimuwa (su ƙẽtare haddi) ba? = --Qur'an 26:225
    And that they say what they do not do? - <> Kuma lalle ne, sũ, sunã faɗin abin da bã su aikatãwa? = --Qur'an 26:226
    Except those [poets] who believe and do righteous deeds and remember Allah often and defend [the Muslims] after they were wronged. And those who have wronged are going to know to what [kind of] return they will be returned. <> Fãce waɗanda suka yi ĩmãni suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka ambaci Allah da yawa, kuma suka rãma zãlunci, daga bãyan an zãlunce su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci, zã su sani a wace majũya suke jũyãwa. = --Qur'an 26:227
    Ta, Seen. These are the verses of the Qur'an and a clear Book <> ¦. S̃. Waɗancan ãyõyinAlƙur'ãni ne da Littãfi mai bayyanawa. = --Qur'an 27:1
    As guidance and good tidings for the believers <> Shiriya ce da bushãra ga mũminai. = --Qur'an 27:2
    Who establish prayer and give zakah, and of the Hereafter they are certain [in faith]. <> Waɗanda suke tsayar da salla kuma su bãyar da zakka, alhãli kuwa sũ, game da Lãhira, to, sũ, sunã yin yaƙĩni. = --Qur'an 27:3
    Indeed, for those who do not believe in the Hereafter, We have made pleasing to them their deeds, so they wander blindly. <> Lalle ne waɗanda suke bã su yin ĩmãni da Lãhira, Mun ƙawãta musu ayyukansu, sabõda haka sunã ɗimuwa. = --Qur'an 27:4
    Those are the ones for whom there will be the worst of punishment, and in the Hereafter they are the greatest losers. <> Waɗannan ne waɗanda suke sunã da mugunyar azãba (a dũniya), kuma sũ, a Lãhira, sũ ne mafiya hasãra. = --Qur'an 27:5
    And indeed, [O Muhammad], you receive the Qur'an from one Wise and Knowing. <> Kuma lalle ne haƙĩƙa, anã haɗa ka da Alƙur'ãni daga gun Mai hikima, Masani. = --Qur'an 27:6
    [Mention] when Moses said to his family, "Indeed, I have perceived a fire. I will bring you from there information or will bring you a burning torch that you may warm yourselves." <> A lõkacin da Mũsã ya ce wa iyãlinsa "Lalle ni, na tsinkãyi wata wuta, ni mai zo muku daga gare ta ne, da wani lãbari, ko kuwa mai zo muku ne da Yũla, makãmashi, tsammãninku, ku ji ɗimi." = --Qur'an 27:7
    But when he came to it, he was called, "Blessed is whoever is at the fire and whoever is around it. And exalted is Allah, Lord of the worlds. <> To, a lõkacin da ya jẽ mata, sai aka kira shi cẽwa, "An tsarkake wanda yake cikin (wurin) wutar da yanda yake a gẽfenta kuma tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin halittu." = --Qur'an 27:8
    O Moses, indeed it is I - Allah, the Exalted in Might, the Wise." <> "Yã Mũsã lalle ne shi, Nĩ ne Allah, Mabuwãyi, Mai hikima." = --Qur'an 27:9
    And [he was told], "Throw down your staff." But when he saw it writhing as if it were a snake, he turned in flight and did not return. [Allah said], "O Moses, fear not. Indeed, in My presence the messengers do not fear. <> "Kuma ka jẽfa sandarka." To, a lõkacin da ya gan ta tanã girgiza kamar dai ita ƙaramin macĩji ne, sai ya jũya yanã mai bãyar da bãya, kuma bai kõma ba, "Yã Musã! Kada ka ji tsõro lalle Ni, Manzanni bã sujin tsõro a wuriNa." = --Qur'an 27:10
    Otherwise, he who wrongs, then substitutes good after evil - indeed, I am Forgiving and Merciful. <> "Sai wanda ya yi zãlunci, sa'an nan ya musanya kyau a bãyan cũta, to, lalle Nĩ, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai." = --Qur'an 27:11
    And put your hand into the opening of your garment [at the breast]; it will come out white without disease. [These are] among the nine signs [you will take] to Pharaoh and his people. Indeed, they have been a people defiantly disobedient." <> "Kuma ka shigar da hannunka a cikin wuyan rĩgarka, ya fita fari, bãbu wata cũta, a cikinwasu ãyõyi tara zuwa ga Fir'auna da mutãnensa. Lalle ne sũ, sun kasance mutãne ne fãsiƙai." = --Qur'an 27:12
    But when there came to them Our visible signs, they said, "This is obvious magic." <> To, a lõkacin da ãyõyinMu suka jẽ musu, sunã mãsu wãyar da kai suka ce wannan sihiri ne bayyananne. = --Qur'an 27:13
    And they rejected them, while their [inner] selves were convinced thereof, out of injustice and haughtiness. So see how was the end of the corrupters. <> Kuma suka yi musunsu, alhãli zukãtansu sun natsu da su dõmin zãlunci da girman kai. To, ka dũbi yadda ãƙibar maɓarnata ta kasance. = --Qur'an 27:14
    And We had certainly given to David and Solomon knowledge, and they said, "Praise [is due] to Allah, who has favored us over many of His believing servants." <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Dãwũda da Sulaimãn ilmi kuma suka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah, Wanda Ya fĩfĩta mu a kan mãsu yawa daga bãyinSa mũminai." = --Qur'an 27:15
    And Solomon inherited David. He said, "O people, we have been taught the language of birds, and we have been given from all things. Indeed, this is evident bounty." <> Kuma sulaimãn ya gãji Dãwũda ya ce: "Yã ku mutãne! An sanar da mu maganar tsuntsãye, kuma an bã mu daga kõwane abu. Lalle ne wannan haƙĩƙa shi ne falalar (Allah) bayyananna." = --Qur'an 27:16
    And gathered for Solomon were his soldiers of the jinn and men and birds, and they were [marching] in rows. <> Kuma aka tattara, dõmin Sulaimãn, rundunõninsa, daga aljannu da mutãne da tsuntsãye, to, sũ anã kange su (ga tafiya). = --Qur'an 27:17
    Until, when they came upon the valley of the ants, an ant said, "O ants, enter your dwellings that you not be crushed by Solomon and his soldiers while they perceive not." <> Har a lõkacin da suka je a kan rãfin turũruwa wata turũruwa ta ce, "Yã kũ jama'ar turũruwa! Ku shiga gidãjenku, kada Sulaimãn da rundunõninsa su kakkarya ku, alhãli kuwa sũ, ba su sani ba." = --Qur'an 27:18
    So [Solomon] smiled, amused at her speech, and said, "My Lord, enable me to be grateful for Your favor which You have bestowed upon me and upon my parents and to do righteousness of which You approve. And admit me by Your mercy into [the ranks of] Your righteous servants." <> Sai ya yi murmushi yanã mai dãriya daga maganarta, kuma ya ce, "Yã Ubangijĩna! Ka cũsa mini in gõde wa ni'imarKa wadda Ka ni'imta ta a gare ni da kuma ga mahaifãna biyu, kuma in aikata aiki na ƙwarai, wanda Kake yarda da shi, kuma Ka shigar da ni, sabõda rahamarKa, a cikin bãyinKa sãlihai." = --Qur'an 27:19
    And he took attendance of the birds and said, "Why do I not see the hoopoe - or is he among the absent? <> Kuma ya binciki tsuntsãye, sai ya ce: "Me ya kãre ni bã ni ganin hudhudu, kõ ya kasance daga mãsu fakuwa ne?" = --Qur'an 27:20
    I will surely punish him with a severe punishment or slaughter him unless he brings me clear authorization." <> "Lalle ne zã ni azabta shi azãba mai tsanani kõ kuwa lalle in yanka shi, kõ kuwa lalle ya zo mini da dalĩli bayyananne." = --Qur'an 27:21
    But the hoopoe stayed not long and said, "I have encompassed [in knowledge] that which you have not encompassed, and I have come to you from Sheba with certain news. <> Sai ya zauna bã nẽsa ba, sa'an nan ya ce: "Nã san abin da ba ka sani ba, kuma na zo maka daga Saba da wani lãbari tabbatacce." = --Qur'an 27:22
    Indeed, I found [there] a woman ruling them, and she has been given of all things, and she has a great throne. <> "Lalle ni nã sãmi wata mace wadda tanã mulkinsu kuma an bã ta daga dukkan kõme, kuma tanã da gadon sarauta mai girma. = --Qur'an 27:23
    I found her and her people prostrating to the sun instead of Allah, and Satan has made their deeds pleasing to them and averted them from [His] way, so they are not guided, <> "Na sãme ta ita da mutãnenta, sunã yin sujada ga rãnã, baicin Allah, kuma Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, sabõda haka ya karkatar da su daga hanya, sa'an nan sũ, ba su shiryuwa." = --Qur'an 27:24
    [And] so they do not prostrate to Allah, who brings forth what is hidden within the heavens and the earth and knows what you conceal and what you declare - <> "Ga su yi sujada ga Allah Wanda Yake fitar da abin da yake a ɓõye, a cikin sammai da ƙasa, kuma Yã san abin da kuke ɓõyẽwada abin da kuke bayyanãwa." = --Qur'an 27:25
    Allah - there is no deity except Him, Lord of the Great Throne." <> "Allah bãbu abin bautãwa fãce shĩ Ubangijin Al'arshi, mai girma." = --Qur'an 27:26
    [Solomon] said, "We will see whether you were truthful or were of the liars. <> Ya ce: "Za mu dũba shin kã yi gaskiya ne, kõ kuwa kã kasance daga maƙaryata?" = --Qur'an 27:27
    Take this letter of mine and deliver it to them. Then leave them and see what [answer] they will return." <> "Ka tafi da takardata wannan, sa'an nan ka jẽfa ta zuwa gare su, sa'an nan kuma ka jũya daga barinsu, sa'an nan ka ga mẽne ne suke mayarwa." = --Qur'an 27:28
    She said, "O eminent ones, indeed, to me has been delivered a noble letter. <> Ta ce: "Yã kũ mashawarta! Lalle ne, an jẽfo, zuwa gareni, wata takarda mai girma." = --Qur'an 27:29
    Indeed, it is from Solomon, and indeed, it reads: 'In the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful, <> "Lalle ita daga Sulaiman take, kuma lalle ita da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai ne." = --Qur'an 27:30
    Be not haughty with me but come to me in submission [as Muslims].' " <> "Kada ku yi girman kai a gare ni, kuma ku zo mini kunã mãsu sallamãwa." = --Qur'an 27:31
    She said, "O eminent ones, advise me in my affair. I would not decide a matter until you witness [for] me." <> Ta ce: "Yã ku mashawarta! Ku yi Mini fatawa ga al'amarĩna, ban kasance mai yanke wani al'amari ba, sai kun halarta." = --Qur'an 27:32
    They said, "We are men of strength and of great military might, but the command is yours, so see what you will command." <> Suka ce: "Mũ ma'abũta ƙarfi ne, kuma ma'abbũta yãƙi mai tsanani ne, kuma al'amari yã kõma zuwa gare ki, sabõda haka ki dũbamẽne ne zã ki yi umurui (da shi)?" = --Qur'an 27:33
    She said, "Indeed kings - when they enter a city, they ruin it and render the honored of its people humbled. And thus do they do. <> Ta ce: "Lalle sarakuna idan sun shiga wata alƙarya, sai su ɓãta ta, kuma su sanya mãsu darajar mutãnenta ƙasƙantattu. Kuma kamar wancan ne suke likatãwa." = --Qur'an 27:34
    But indeed, I will send to them a gift and see with what [reply] the messengers will return." <> "Kuma lalle nĩ mai aikãwa ce zuwa gare su da kyauta, sa'an nan mai dũbawa ce: Da me manzannin zã su kõmo." = --Qur'an 27:35
    So when they came to Solomon, he said, "Do you provide me with wealth? But what Allah has given me is better than what He has given you. Rather, it is you who rejoice in your gift. <> To, a lõkacin da ya jẽ wa Sulaiman ya ce: "Shin, za ku ƙãra ni da dũkiya ne? To, abin daAllah Ya bã ni, shi ne mafi alhẽridaga abin da Ya bã ku. A'a, kũ nekuke yin farin ciki da kyautarku." = --Qur'an 27:36
    Return to them, for we will surely come to them with soldiers that they will be powerless to encounter, and we will surely expel them therefrom in humiliation, and they will be debased." <> "Ka kõma zuwa gare su. Sa'an nan lalle munã je musu da rundunõni, bãbu wata tãɓukawa gare su game da su, kuma lalle munã fitar da su daga gare ta, sunã mafi wulãkantuwa, kuma sunã ƙasƙantattu." = --Qur'an 27:37
    [Solomon] said, "O assembly [of jinn], which of you will bring me her throne before they come to me in submission?" <> Ya ce: "Yã ku mashãwarta! Wannenku zai zo mini da gadonta a gabãnin su zo, sunã mãsu sallamãwa?" = --Qur'an 27:38
    A powerful one from among the jinn said, "I will bring it to you before you rise from your place, and indeed, I am for this [task] strong and trustworthy." <> Wani mai ƙarfi daga aljannu ya ce: "Nĩ inã zo maka da shi a gabãnin ka tãshi daga matsayinka. Kuma llale nĩ a gare shi, haƙĩƙa, mai ƙarfi ne amintacce." = --Qur'an 27:39
    Said one who had knowledge from the Scripture, "I will bring it to you before your glance returns to you." And when [Solomon] saw it placed before him, he said, "This is from the favor of my Lord to test me whether I will be grateful or ungrateful. And whoever is grateful - his gratitude is only for [the benefit of] himself. And whoever is ungrateful - then indeed, my Lord is Free of need and Generous." <> Wanda yake a wurinsa akwai wani ilmi daga Littafin ya ce: "Ni inã zo maka da shi a gabãnin ƙyaftãwar ganinka ta kõma gare ka." To, a lõkacin da ya gan shi matabbaci a wurinsa, ya ce: "Wannan daga falalar Ubangijĩna yake, dõmin Ya jarraba ni: Shin, zan gõde ne, kõ kuwa zan butulce! Kuma wanda ya gõde, to, yanã gõdẽwa ne dõmin kansa, kuma wanda ya kãfirta, to, lalle Ubangijina Wadãtacce ne, Karĩmi." = --Qur'an 27:40
    He said, "Disguise for her her throne; we will see whether she will be guided [to truth] or will be of those who is not guided." <> Ya ce: "Ku canza kamar gadonta gare ta, mu gani, shin zã ta shiryu, kõ kuwa tanã kasancẽwa daga waɗanda bã su shiryuwa." = --Qur'an 27:41
    So when she arrived, it was said [to her], "Is your throne like this?" She said, "[It is] as though it was it." [Solomon said], "And we were given knowledge before her, and we have been Muslims [in submission to Allah]. <> To a lõkacin da ta jẽ aka ce "Shin, kamar wannan gadon sarautarki yake?" Ta ce: "Kamar dai shĩne. Kuma an bã mu ilmi daga gabãninta kuma mun kasance mãsu sallamãwar (al'amari ga Allah)." = --Qur'an 27:42
    And that which she was worshipping other than Allah had averted her [from submission to Him]. Indeed, she was from a disbelieving people." <> Kuma abin da ta kasance tanã bautãwa, baicin Allah, ya kange ta. Lalle ita, tã kasance daga mutãne kãfirai. = --Qur'an 27:43
    She was told, "Enter the palace." But when she saw it, she thought it was a body of water and uncovered her shins [to wade through]. He said, "Indeed, it is a palace [whose floor is] made smooth with glass." She said, "My Lord, indeed I have wronged myself, and I submit with Solomon to Allah, Lord of the worlds." <> Aka ce mata, "Ki shiga a gidan sarauta." To, a lõkacin da ta gan shi, ta yi zatona wai gurbi ne, kuma ta kuranye daga ƙwaurinta. Ya ce: "Lalle ne shi, gidan sarauta ne mai santsi daga madũbai." Ta ce: "Yã Ubangijĩna! Bã a rõƙon Allah sai da sunãyensa mãsu kyau, tis'in da taran nan, sai dai a dunƙule kamar a ce, "Inã rõƙon Allah da sunãyenSa da na sani da waɗanda ban sani ba." Lalle nĩ, na zãlunci kaina, kuma nã sallama al'amari tãre da Sulaiman ga Allah, Ubangijin halittu." = --Qur'an 27:44
    And We had certainly sent to Thamud their brother Salih, [saying], "Worship Allah," and at once they were two parties conflicting. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, mun aika zuwa Samũdãwa da ɗan'uwansu, Salihu (ya ce), "Ku bauta wa Allah." Sai gã su ƙungiyõyi biyu sunã ta husũma. = --Qur'an 27:45
    He said, "O my people, why are you impatient for evil instead of good? Why do you not seek forgiveness of Allah that you may receive mercy?" <> Ya ce: "Yã mutãnẽna! Don me kuke nẽman gaggãwa game da mũnanãwa, a gabãnin kyautatãwa. Don me bã ku nẽman Allah gãfara, tsammãninku, zã a yi muku rahama?" = --Qur'an 27:46
    They said, "We consider you a bad omen, you and those with you." He said, "Your omen is with Allah. Rather, you are a people being tested." <> Suka ce: "Munã shu'umci da kai, kuma da wanda ke tãre da kai." Ya ce: "Shu'umcinku a wurin Allah yake. Ã'a, kũ mutãne ne, anã fitinar ku." = --Qur'an 27:47
    And there were in the city nine family heads causing corruption in the land and not amending [its affairs]. <> Kuma waɗansu jama'a tara sun kasance a cikin birnin, sunã yin ɓarna, kuma bã su kyautatãwa. Suka ce: "Ku yi rantsuwa da Allah, lalle zã mu kwãnan masa, shi da mutãnensa sa'an nan mu ce wa waliyyinsa. 'Ba mu halarci halakar mutãnensa ba kuma mũ, haƙĩ ƙa, mãsu gaskiya ne'." = --Qur'an 27:48
    They said, "Take a mutual oath by Allah that we will kill him by night, he and his family. Then we will say to his executor, 'We did not witness the destruction of his family, and indeed, we are truthful.' " <> Kuma suka ƙulla mãkirci, kuma Muka ƙulla sakamakon mãkirci, alhãli sũ ba su sani ba. = --Qur'an 27:49
    And they planned a plan, and We planned a plan, while they perceived not. <> Ka dũba yadda ãƙibar mãkircinsu ta kasance lalle Mũ Mun darkãke su da mutãnensu, gabã ɗaya. = --Qur'an 27:50
    Then look how was the outcome of their plan - that We destroyed them and their people, all. <> Waɗancan, gidãjensu ne, wõfintattu sabõda zãluncin da suka yi, lalle ne a wancan akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke sani. = --Qur'an 27:51
    So those are their houses, desolate because of the wrong they had done. Indeed in that is a sign for people who know. <> Muka tsĩrar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sun kasance sunã taƙawa. = --Qur'an 27:52
    And We saved those who believed and used to fear Allah. <> Da Lũdu, a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, "Shin kunã jẽ wa alfasha ne, alhãli, kuwa kunã gani?" = --Qur'an 27:53
    And [mention] Lot, when he said to his people, "Do you commit immorality while you are seeing? <> "Shin lalle kũ haƙĩƙa kunã je wa maza da sha'awa baicin mãtã? Ã'a, kũ wasu irin mutãne ne kuna aikin jãhilci." = --Qur'an 27:54
    Do you indeed approach men with desire instead of women? Rather, you are a people behaving ignorantly." <> 49. = --Qur'an 27:55
    But the answer of his people was not except that they said, "Expel the family of Lot from your city. Indeed, they are people who keep themselves pure." <> Bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa fãce suka ce "Ku fitar da mutãnen Lũɗu daga alƙaryarku, lalle sũ, wasu irin mutãne ne mãsu da'awar sunã da tsarki." = --Qur'an 27:56
    So We saved him and his family, except for his wife; We destined her to be of those who remained behind. <> Sai Muka tsĩrar da shi, shi da mutãnensa, fãce mãtarsa, Mun ƙaddara ta a cikin mãsu wanzuwa. = --Qur'an 27:57
    And We rained upon them a rain [of stones], and evil was the rain of those who were warned. <> Kuma Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa. To, ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana. = --Qur'an 27:58
    Say, [O Muhammad], "Praise be to Allah, and peace upon His servants whom He has chosen. Is Allah better or what they associate with Him?" <> Ka ce: "Godiya ta tabbata ga A1lah, kuma aminci ya tabbata bisa ga bãyinSa, waɗanda Ya zãɓa." Shin Allah ne Mafi alhẽri koabin da suke yin shirki da Shi? = --Qur'an 27:59
    [More precisely], is He [not best] who created the heavens and the earth and sent down for you rain from the sky, causing to grow thereby gardens of joyful beauty which you could not [otherwise] have grown the trees thereof? Is there a deity with Allah? [No], but they are a people who ascribe equals [to Him]. <> Kõ wãne ne Ya halitta sammai da ƙasa kuma Ya saukar muku, daga, sama, wani ruwa, Muka tsirar, game da shi, gõnaki mãsu sha'awa, ba ya kasancẽwa gare ku, ku tsirar da itãcensu? Shin, akwai abin bautãwa tãre da Allah? Ã'a, sũ mutãne ne suna daidaitãwa (Allah da wani). = --Qur'an 27:60
    Is He [not best] who made the earth a stable ground and placed within it rivers and made for it firmly set mountains and placed between the two seas a barrier? Is there a deity with Allah? [No], but most of them do not know. <> Kõ kuwa wãne ne Ya sanya ƙasa tabbatacciya, kuma Ya sanya kõguna a tsakãninta kuma Ya sanya mata manyan duwãtsu tabatattu, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãnin tẽkuna biyu? Shin akwai wani abin bautãwa tãre da Allah. Ã'a, mafi yawansu ba su sanĩ ba. = --Qur'an 27:61
    Is He [not best] who responds to the desperate one when he calls upon Him and removes evil and makes you inheritors of the earth? Is there a deity with Allah? Little do you remember. <> Kõ wãne ne yake karɓã, kuma ya sanya ku mamãyan ƙasa? Shin akwai wani abin bautawa tãre da Allah? Kaɗan ƙwarai kuke yin tunãni. = --Qur'an 27:62
    Is He [not best] who guides you through the darknesses of the land and sea and who sends the winds as good tidings before His mercy? Is there a deity with Allah? High is Allah above whatever they associate with Him. <> Kõ wãne ne yake shiryarwa a cikin duffan ƙasa da tẽku, kuma wãne ne Yake aikõwar iskõki dõmin bãyar da bushãra a gaba ga rahamarSa? Ashe akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? tsarki yã tabbata ga Allah daga barin abin da suke shirki da Shi. = --Qur'an 27:63
    Is He [not best] who begins creation and then repeats it and who provides for you from the heaven and earth? Is there a deity with Allah? Say, "Produce your proof, if you should be truthful." <> Kõ wãne ne yake fã ra halitta sa'an nan kuma ya mayar da ita, kuma Wãne ne Ya azurta ku daga sama da ƙasa? Ashe, akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? Ka ce: "Ku kãwo dalĩlinku idan kun kasance mãsu gaskiya." = --Qur'an 27:64
    Say, "None in the heavens and earth knows the unseen except Allah, and they do not perceive when they will be resurrected." <> Ka ce: "Bãbu wanda ya san gaibi a cikin sammai da ƙasa fãce Allah. Kuma bã su sansancẽwar a yaushe ne zã a tãyar da su." = --Qur'an 27:65
    Rather, their knowledge is arrested concerning the Hereafter. Rather, they are in doubt about it. Rather, they are, concerning it, blind. <> Ã'a, saninsu ya kai a cikin Lãhira Ã'a, sunã cikin shakka daga gare ta. Ã'a, sũ da gare ta makãfin zũci ne. = --Qur'an 27:66
    And those who disbelieve say, "When we have become dust as well as our forefathers, will we indeed be brought out [of the graves]? <> Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Shin idan mun kasance turɓaya, mu da ubanninmu, shin, haƙĩƙa, waɗanda ake fitarwa ne?" = --Qur'an 27:67
    We have been promised this, we and our forefathers, before. This is not but legends of the former peoples." <> "Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi ga wannan, mũ da ubanninmu, daga gabãnin haka. Wannan bã kõme ba ne fãce tãtsũniyõyin farko." = --Qur'an 27:68
    Say, [O Muhammad], "Travel through the land and observe how was the end of the criminals." <> Ka ce: "Ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba, yãya ãƙibar mãsu laifi take?" = --Qur'an 27:69
    And grieve not over them or be in distress from what they conspire. <> Kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke ƙullãwa na mãkirci. = --Qur'an 27:70
    And they say, "When is [the fulfillment of] this promise, if you should be truthful?" <> Kuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi (zai auku), idan kun kasance mãsu gaskiya?" = --Qur'an 27:71
    Say, "Perhaps it is close behind you - some of that for which you are impatient. <> Ka ce: "Akwai fatan sãshen abin da kuke, nẽman gaggãwarsa, ya kasance yã kuturta a gare ku." = --Qur'an 27:72
    And indeed, your Lord is full of bounty for the people, but most of them do not show gratitude." <> Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa Mai falala ne a kanmutãne kuma amma mafi yawansu, bã su gõdẽwa. = --Qur'an 27:73
    And indeed, your Lord knows what their breasts conceal and what they declare. <> Kuma lalle Ubangijinka, haƙĩƙa Yanã sanin abin da ƙirãzansu suke, ɓõyẽwa, da abin da suke hayyanãwa. = --Qur'an 27:74
    And there is nothing concealed within the heaven and the earth except that it is in a clear Register. <> Kuma bãbu wata (mas'ala) mai bõyuwa, a cikin sama da ƙasa fãce tanã a cikin littafi bayyananne. = --Qur'an 27:75
    Indeed, this Qur'an relates to the Children of Israel most of that over which they disagree. <> Lalle ne wannan Alƙur'ãni yanã gaya wa Banĩ Isrãĩla mafi yawan abin da sũ suke sãɓa wa jũnansu a ciki. = --Qur'an 27:76
    And indeed, it is guidance and mercy for the believers. <> Kuma lalle shi haƙĩƙa shiriya ce da rahama ga mũminai. = --Qur'an 27:77
    Indeed, your Lord will judge between them by His [wise] judgement. And He is the Exalted in Might, the Knowing. <> "Lalle Ubangijinka Yanã yin hukunci a tsakãninsu da hukuncinsa, kuma Shi ne Mabuwãyi, Masani." = --Qur'an 27:78
    So rely upon Allah; indeed, you are upon the clear truth. <> Sabõda haka, ka dõgara ga Allah, lalle ne, kai ne a kan gaskiya bayyananniya. = --Qur'an 27:79
    Indeed, you will not make the dead hear, nor will you make the deaf hear the call when they have turned their backs retreating. <> Lalle ne kai, bã ka jiyar da matattu, kuma bã ka sa kurãme su ji kiranka, idan sun jũya sunã mãsu bãyar da bãya. = --Qur'an 27:80
    And you cannot guide the blind away from their error. You will only make hear those who believe in Our verses so they are Muslims [submitting to Allah]. <> Kuma kai ba ka zama mai shiryar da ɗimammu daga ɓata ba. Bã ka jiyarwa fãce wanda yake yin ĩmãni da ãyõyinMu. To, sũ ne mãsu sallamãwa (al'amari zuwa ga Allah). = --Qur'an 27:81
    And when the word befalls them, We will bring forth for them a creature from the earth speaking to them, [saying] that the people were, of Our verses, not certain [in faith]. <> Kuma idan magana ta auku a kansu, Munã fitar musu da wata dabba daga ƙasa, tanã yi musu magana, cẽwa "Lalle mutãne sun kasance game da ayoyinMu, ba su yin ĩmãnin yaƙĩni." = --Qur'an 27:82
    And [warn of] the Day when We will gather from every nation a company of those who deny Our signs, and they will be [driven] in rows <> Kuma a rãnar da Muke tãrãwa daga kõwace al'umma, wata ƙungiya daga waɗanda suke ƙaryata ãyõyinMu, sai ga su anã kangesu. (ga kõra) = --Qur'an 27:83
    Until, when they arrive [at the place of Judgement], He will say, "Did you deny My signs while you encompassed them not in knowledge, or what [was it that] you were doing?" <> Har idan sun zo, (Allah) zai ce, "Ashe kun ƙaryata ãyõyinNa, kuma ba ku kẽwaye su da sani ba? To, mẽne ne kuka kasance kunã aikatãwa?" = --Qur'an 27:84
    And the decree will befall them for the wrong they did, and they will not [be able to] speak. <> Kuma magana ta auku a kansu, sabõda zãluncin da suka yi. To, sũ bã su da ta cẽwa. = --Qur'an 27:85
    Do they not see that We made the night that they may rest therein and the day giving sight? Indeed in that are signs for a people who believe. <> Shin, ba su gani ba, cẽwa, lalle Mũ, Mun sanya dare dõmin su natsu a cikinsa, kuma da yini mai sanya gani? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi! Dõmin mutãne waɗanda suka yi ĩmãni. = --Qur'an 27:86
    And [warn of] the Day the Horn will be blown, and whoever is in the heavens and whoever is on the earth will be terrified except whom Allah wills. And all will come to Him humbled. <> Kuma da rãnar da ake hũsa a cikin ƙaho, sai wandayake a cikin sammai da waɗanda suke a cikin ƙasa su firgita, fãce wanda Allah Ya so, kuma dukansu, su je Masa sunã ƙasƙantattu. = --Qur'an 27:87
    And you see the mountains, thinking them rigid, while they will pass as the passing of clouds. [It is] the work of Allah, who perfected all things. Indeed, He is Acquainted with that which you do. <> Kuma kanã ganin duwãtsu, kanã zaton su sandararru, alhãli kuwa sũ sunã shũɗẽwa shũɗewar girgije, bisa sanã'ar Allah wanda Ya kyautata kõwane abu. Lalle Shi, Mai lãbartãwa ne game da abin da kuke aikatãwa. = --Qur'an 27:88
    Whoever comes [at Judgement] with a good deed will have better than it, and they, from the terror of that Day, will be safe. <> Wanda ya zo da kyakkyawan aiki guda, to, yanã da mafi alhẽri daga gare shi. Kuma sũ daga wata firgita, a yinin nan, amintattu ne. = --Qur'an 27:89
    And whoever comes with an evil deed - their faces will be overturned into the Fire, [and it will be said], "Are you recompensed except for what you used to do?" <> Kuma wanda ya zo da mugun aiki, to, an kife fuskõkinsu a cikin wuta. Ko zã a sãka muku fãce da abin da kuka kasance kũnã aikatãwa? = --Qur'an 27:90
    [Say, O Muhammad], "I have only been commanded to worship the Lord of this city, who made it sacred and to whom [belongs] all things. And I am commanded to be of the Muslims [those who submit to Allah] <> (Ka ce): "An umurce ni, in bauta wa Ubangijin wannan Gari, Wanda Ya mayar da shi Hurumi, kuma Yanã da dukan kõme. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa." = --Qur'an 27:91
    And to recite the Qur'an." And whoever is guided is only guided for [the benefit of] himself; and whoever strays - say, "I am only [one] of the warners." <> "Kuma inã karanta Alƙur'ãni." To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai. Kuma wanda ya ɓãce, to, ka ce: "Ni daga mãsu gargaɗi kawai nake." = --Qur'an 27:92
    And say, "[All] praise is [due] to Allah. He will show you His signs, and you will recognize them. And your Lord is not unaware of what you do." <> Kuma ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah. Zai nũna muku ãyõyinSa, har ku sansu." Kuma Ubangijinka bai zama Mai shagala daga barin abin da kuke aikatãwa ba. = --Qur'an 27:93
    Ta, Seen, Meem. <> ¦. S̃. M̃. = --Qur'an 28:1
    These are the verses of the clear Book. <> Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne. = --Qur'an 28:2
    We recite to you from the news of Moses and Pharaoh in truth for a people who believe. <> Munã karantãwa a kanka daga lãbarin Mũsã da Fir'auna da gaskiya dõmin mutãne waɗanda suke yin ĩmãni. = --Qur'an 28:3
    Indeed, Pharaoh exalted himself in the land and made its people into factions, oppressing a sector among them, slaughtering their [newborn] sons and keeping their females alive. Indeed, he was of the corrupters. <> Lalle ne Fir'auna ya ɗaukaka a cikin ƙasa, kuma ya sanya mutãnenta ƙungiya-ƙungiya, yanã raunanar da wata jama'a daga gare su; yanã yanyanka ɗiyansu maza kuma yanã rãyar da mãtan. Lalle shĩ ya kasance daga mãsu ɓarna. = --Qur'an 28:4
    And We wanted to confer favor upon those who were oppressed in the land and make them leaders and make them inheritors <> Kuma Munã nufin Mu yi falala ga waɗanda aka raunanar a cikin ƙasar, kuma Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su magãda. = --Qur'an 28:5
    And establish them in the land and show Pharaoh and [his minister] Haman and their soldiers through them that which they had feared. <> Kuma Mu tabbatar da su a cikin ƙasar, kuma Mu nũna wa Fir'auna da Hãmãna da rundunõninsu abin da suka kasance sunã sauna daga gare su. = --Qur'an 28:6
    And We inspired to the mother of Moses, "Suckle him; but when you fear for him, cast him into the river and do not fear and do not grieve. Indeed, We will return him to you and will make him [one] of the messengers." <> Kuma Muka yi wahayi zuwa ga uwar Mũsa, cẽwa ki shãyar da shi, sai idan kin ji tsõro game da shi, to, ki jẽfa shi a cikin kõgi, kuma kada ki ji tsõro, kuma kada ki yi baƙin ciki. Lalle ne Mũ, Mãsu mayar da shi ne zuwa gare ki, kuma Mãsu sanya shi ne a cikin Manzanni = --Qur'an 28:7
    And the family of Pharaoh picked him up [out of the river] so that he would become to them an enemy and a [cause of] grief. Indeed, Pharaoh and Haman and their soldiers were deliberate sinners. <> Sai mutãnen Fir'auna suka tsince shi, dõmin ya kasance maƙiyi da baƙin ciki a gare su. Lalle ne Fir'auna da Hãmãna da rundunõninsu, sun kasance mãsu aikin ganganci. = --Qur'an 28:8
    And the wife of Pharaoh said, "[He will be] a comfort of the eye for me and for you. Do not kill him; perhaps he may benefit us, or we may adopt him as a son." And they perceived not. <> Kuma matar Fir'auna ta ce ("Ka bar shi yanã) sanyin ido a gare ni da gare ka! Kada ka kashe shi, akwai fatan ya amfane mu, kõ mu riƙe Shi ɗã," alhãli kuwa sũ ba su sansance ba. = --Qur'an 28:9
    And the heart of Moses' mother became empty [of all else]. She was about to disclose [the matter concerning] him had We not bound fast her heart that she would be of the believers. <> Kuma zuciyar uwar Mũsã ta wãyi gari yõfintatta. Lalle ne, haƙĩƙa, ta yi kusa ta bayyanar da shi, bã dõmin Mun ɗaure zũciyarta ba, dõmin ta kasance daga mũminai. = --Qur'an 28:10
    And she said to his sister, "Follow him"; so she watched him from a distance while they perceived not. <> Kuma ta ce wa 'yar'uwarsa, "Ki bĩ shi." Sabõda haka sai ta lẽƙe shi daga gẽfe, alhãli sũ ba Su sani ba. = --Qur'an 28:11
    And We had prevented from him [all] wet nurses before, so she said, "Shall I direct you to a household that will be responsible for him for you while they are to him [for his upbringing] sincere?" <> Kuma Muka hana masa mãsu shãyai da mãma, a gabãnin haka sai ta ce: "Kõ in nũnamuku mutãnen wani gida, su yi muku renonsa alhãli kuwa su mãsu nasĩha ne a, gare shi?" = --Qur'an 28:12
    So We restored him to his mother that she might be content and not grieve and that she would know that the promise of Allah is true. But most of the people do not know. <> Sai Muka mayar da shi zuwa ga uwarsa dõmin idanunta su yi sanyi, kuma bã zã ta yi baƙin ciki ba, kuma dõmin ta san cẽwa lalle wa'adin Allah gaskiya ne, amma kuma mafi yawansu ba su sani ba. = --Qur'an 28:13
    And when he attained his full strength and was [mentally] mature, We bestowed upon him judgement and knowledge. And thus do We reward the doers of good. <> Kuma a lõkacin da ya kai ƙarfinsa, kuma ya daidaita, Mun bã shi hukunci da ilmi kuma kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. = --Qur'an 28:14
    And he entered the city at a time of inattention by its people and found therein two men fighting: one from his faction and one from among his enemy. And the one from his faction called for help to him against the one from his enemy, so Moses struck him and [unintentionally] killed him. [Moses] said, "This is from the work of Satan. Indeed, he is a manifest, misleading enemy." <> Kuma sai ya shiga garin a lõkacin da mutãnen garin suka shagala, sai ya sãmu, a cikin garin, waɗansu maza biyu sunã faɗa, wannan daga ƙungiyarsa, kuma ɗayan daga maƙiyansa, sai wannann da yake daga ƙungiyarsa ya nẽmi ãgajinsa, sai Mũsã ya yi masa ƙulli, ya kashe shi. Ya ce: "Wannan aikin Shaiɗan ne, dõmin shi maƙiyi ne mai ɓatarwa, bayyananne!" = --Qur'an 28:15
    He said, "My Lord, indeed I have wronged myself, so forgive me," and He forgave him. Indeed, He is the Forgiving, the Merciful. <> Ya ce: "Ya Uhangijĩna! Lalle na zãlunci kaina, sai Ka yi mini gãfara." Sai Ya gãfarta masa, dõmin Shĩ ne Mai yawan gãfara, Mai jin ƙai. = --Qur'an 28:16
    He said, "My Lord, for the favor You bestowed upon me, I will never be an assistant to the criminals." <> Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Dõmin abin da Ka ni'imta shi a kaina, sahõda haka bã zan kasance mai taimako ga mãsu laifi ba." = --Qur'an 28:17
    And he became inside the city fearful and anticipating [exposure], when suddenly the one who sought his help the previous day cried out to him [once again]. Moses said to him, "Indeed, you are an evident, [persistent] deviator." <> Sai ya wãyi gari a cikin birnin yanã mai tsõro, yanã sauna. Sai ga wanda ya nẽmi taimako daga gare shi a jiya, yanã nẽman ãgajinsa. Mũsã ya ce masa, "Lalle kai ɓatacce ne, bayyananne." = --Qur'an 28:18
    And when he wanted to strike the one who was an enemy to both of them, he said, "O Moses, do you intend to kill me as you killed someone yesterday? You only want to be a tyrant in the land and do not want to be of the amenders." <> To, a lõkacin da Mũsã ya yi nufin ya damƙi wanda yake maƙiyi ne a gare su, (mai nẽman ãgajin) ya ce, "Ya Mũsã! Shin kanãnufin ka kashe ni ne kamar yadda ka kashe wani rai jiya? Ba ka son kõme fãce ka kasance mai tanƙwasawa a cikin ƙasa kuma bã ka nufin ka kasance daga mãsu kyautatãwa." = --Qur'an 28:19
    And a man came from the farthest end of the city, running. He said, "O Moses, indeed the eminent ones are conferring over you [intending] to kill you, so leave [the city]; indeed, I am to you of the sincere advisors." <> Kuma wani mutum ya zo daga mafi nĩsan birnin yanã taliya da gaggãwa, ya ce: "Ya Mũsã! Lalle mashãwarta sunã shãwara game da kai dõmin su kashe ka sabõda haka ka fita. Lalle nĩ, mai nasĩha ne a gare ka." = --Qur'an 28:20
    So he left it, fearful and anticipating [apprehension]. He said, "My Lord, save me from the wrongdoing people." <> Sai ya fita daga gare ta, yanã mai jin tsõro yanã sauna. Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Kã tsẽrar da ni daga mutãne azzãlumai." = --Qur'an 28:21
    And when he directed himself toward Madyan, he said, "Perhaps my Lord will guide me to the sound way." <> Kuma a lõkacin da ya fuskanci wajen Madyana, ya ce: "Inã fatan Ubangijĩna Ya shiryar da ni a kan madaidaiciyar hanya." = --Qur'an 28:22
    And when he came to the well of Madyan, he found there a crowd of people watering [their flocks], and he found aside from them two women driving back [their flocks]. He said, "What is your circumstance?" They said, "We do not water until the shepherds dispatch [their flocks]; and our father is an old man." <> Kuma a lõkacin da ya isa mashãyar Madyana, ya sãmi wata jam'ar mutãne sunã shãyarwa, kuma a bãyansu ya sãmi waɗansu mãtã biyu sunã kõrar (tumãkinsu). Ya ce: "Mẽne ne shã'aninku?" Suka ce, "Bã zã mu iya shãyãrwa ba sai makiyãya sun fita, kuma ubanmu tsõho ne mai daraja." = --Qur'an 28:23
    So he watered [their flocks] for them; then he went back to the shade and said, "My Lord, indeed I am, for whatever good You would send down to me, in need." <> Sai ya shãyar musu, sa'an nan kuma ya jũya zuwa ga inuwa, sa'an nan ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne, ga abin da Ka saukar zuwa gare ni na alhẽri ni mai bukãta ne." = --Qur'an 28:24
    Then one of the two women came to him walking with shyness. She said, "Indeed, my father invites you that he may reward you for having watered for us." So when he came to him and related to him the story, he said, "Fear not. You have escaped from the wrongdoing people." <> Sai ɗayansu ta je masa, tanã tafiya a kan jin kunya, ta ce, "Ubãna yanã kiran ka, dõmin ya sãka maka ijãrar abin da ka shãyar sabõda mu." To, a lõkacin da ya je masa, ya gaya masa lãbãrinsa, ya ce: "Kada ka ji tsõro, kã tsĩra daga mutãne azzãlumai." = --Qur'an 28:25
    One of the women said, "O my father, hire him. Indeed, the best one you can hire is the strong and the trustworthy." <> ¦ayarsu ta ce, "Yã Bãba! Ka bã shi aikin ijãra, lalle ne mafi alhẽrin wanda ka bai wa aikin ijãra shi ne mai ƙarfi amintacce." = --Qur'an 28:26
    He said, "Indeed, I wish to wed you one of these, my two daughters, on [the condition] that you serve me for eight years; but if you complete ten, it will be [as a favor] from you. And I do not wish to put you in difficulty. You will find me, if Allah wills, from among the righteous." <> Ya ce: "Lalle ne inã nufin in aurar da kai ɗayan 'yã'yãna biyu, waɗannan, a kan ka yi mini aikin ijãra shẽkara takwas to, idan ka cika gõma, to, daga, gare ka yake. Ba ni so in tsanantã maka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga sãlihai." = --Qur'an 28:27
    [Moses] said, "That is [established] between me and you. Whichever of the two terms I complete - there is no injustice to me, and Allah, over what we say, is Witness." <> Ya ce: "Wannan yanã a tsakanina da tsakãninka kõwane ɗayan adadin biyun na ƙãre, to, bãbu wani zãlunci a kaina. Kuma Allah ne Wakili ga abin da muke faɗa." = --Qur'an 28:28
    And when Moses had completed the term and was traveling with his family, he perceived from the direction of the mount a fire. He said to his family, "Stay here; indeed, I have perceived a fire. Perhaps I will bring you from there [some] information or burning wood from the fire that you may warm yourselves." <> To, a lokacin da Mũsã ya ƙãre adadin kuma yanã tafiya da iyãlinsa, sai ya tsinkãyi wata Wutã daga gẽfen dũtse (¦ũr). Ya cewa iyãlinsa, "Ku dãkata, lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wutã, tsammãnĩna ni, mai zo muku ne daga gare ta da wani lãbãrĩ, kõ kuwa da guntun makãmashi daga Wutar don kõ ku ji ɗimi." = --Qur'an 28:29
    But when he came to it, he was called from the right side of the valley in a blessed spot - from the tree, "O Moses, indeed I am Allah, Lord of the worlds." <> To, a lõkacin da ya jẽ wurinta (Wutar) aka kirã shi, daga gẽfen rãfin na dãma, a cikin wurin nan mai albarka, daga itãciyar (cẽwa) "Ya Mũsã! Lalle Nĩ ne Allah Ubangijin halittu." = --Qur'an 28:30
    And [he was told], "Throw down your staff." But when he saw it writhing as if it was a snake, he turned in flight and did not return. [Allah said], "O Moses, approach and fear not. Indeed, you are of the secure. <> "Kuma ka jẽfa sandarka." To, a lõkacin da ya gan ta, tanã girgiza kamar ƙaramar macijiya, ya jũya yanã mai bãyar da bãya, bai kõma ba. "Ya Mũsã! Ka fuskanto, kuma kada ka ji tsõro lalle ne kanã daga waɗanda ke amintattu." = --Qur'an 28:31
    Insert your hand into the opening of your garment; it will come out white, without disease. And draw in your arm close to you [as prevention] from fear, for those are two proofs from your Lord to Pharaoh and his establishment. Indeed, they have been a people defiantly disobedient." <> "Ka shigar da hannunka a cikin wuyan rĩgarka, ya fita fari, ba da wata cũta ba, kuma ka haɗa hannuwanka ga kãfaɗunka, dõmin tsõro (ya gushe daga gare ka). To, waɗannan abũbuwa dalĩlai biyu ne daga Ubangijinka zuwa ga Fir'auna da 'yan Majalisarsa. Lalle sun kasance mutãne ne fãsiƙai." = --Qur'an 28:32
    He said, "My Lord, indeed, I killed from among them someone, and I fear they will kill me. <> Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle nã kashe wani rai daga gare su, dõmin haka inã tsõron kada su kashe ni." = --Qur'an 28:33
    And my brother Aaron is more fluent than me in tongue, so send him with me as support, verifying me. Indeed, I fear that they will deny me." <> "Kuma ɗan'uwana Hãrũna shĩ ne mafi fasãha daga gareni, ga harshe, sabõda haka Ka aika shi tãre da ni, yanã mai taimako, yanã gaskata ni, lalle ne inã tsõron su ƙaryata ni." = --Qur'an 28:34
    [Allah] said, "We will strengthen your arm through your brother and grant you both supremacy so they will not reach you. [It will be] through Our signs; you and those who follow you will be the predominant." <> Ya ce: "Zã Mu ƙarfafa damtsenka game da ɗan'uwanka kuma Mu sanya muku wani dalĩli, sabõda haka bã zã su sãdu zuwa gareku ba, tãre da ãyõyinMu, kũ da waɗanda suka bĩ ku ne marinjãya." = --Qur'an 28:35
    But when Moses came to them with Our signs as clear evidences, they said, "This is not except invented magic, and we have not heard of this [religion] among our forefathers." <> To, a lõkacin da Mũsã ya jẽ musu da ãyõyinMu bayyanannu, suka ce: "Wannan ba kõme ba sai sihiri, wanda aka ƙãga, kuma ba mu ji wannan ba daga wajen ubanninmu na farko." = --Qur'an 28:36
    And Moses said, "My Lord is more knowing [than we or you] of who has come with guidance from Him and to whom will be succession in the home. Indeed, wrongdoers do not succeed." <> Kuma Mũsã ya ce: "Ubangijĩna ne Mafi sanin wanda ya zo da shiriya daga gare Shi, da wanda ãƙibar gida take kasancẽwa agare shi. Lalle ne mãsu zãlunci bã su cin nasara." = --Qur'an 28:37
    And Pharaoh said, "O eminent ones, I have not known you to have a god other than me. Then ignite for me, O Haman, [a fire] upon the clay and make for me a tower that I may look at the God of Moses. And indeed, I do think he is among the liars." <> Kuma Fir'auna ya ce: "Yã ku mashãwarta! Ban san kunã da wani abin bautãwa baicina ba, sabõda haka ka hũra mini wuta, ya Hãmãnu! a kan lãka (dõmin a yi tũbali), sa'an nan ka sanya mini bẽne tsammãnĩna zan ninƙãya zuwa ga Ubangijin Mũsã kuma lalle ne ni, haƙĩƙa, inã zaton sa daga maƙaryata." = --Qur'an 28:38
    And he was arrogant, he and his soldiers, in the land, without right, and they thought that they would not be returned to Us. <> Kuma ya kangare, shi da rundunõninsa a cikin ƙasa, bã da haƙƙi ba kuma suka zaci cẽwa sũ, bã zã a mayar da su zuwa gare Mu ba. = --Qur'an 28:39
    So We took him and his soldiers and threw them into the sea. So see how was the end of the wrongdoers. <> Sai Muka kãma shi, shĩ da rundunõninsa sai Muka jẽfa su a cikin kõgi. Sai ka dũbi yaddaãƙibar azzãlumai ta kasance. = --Qur'an 28:40
    And We made them leaders inviting to the Fire, and on the Day of Resurrection they will not be helped. <> Kuma Muka sanya su shũgabanni, sunã kira zuwa ga wuta, kuma a Rãnar ¡iyãma bã zã a taimake su ba. = --Qur'an 28:41
    And We caused to overtake them in this world a curse, and on the Day of Resurrection they will be of the despised. <> Kuma Muka biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyakuma a Rãnar ¡iyãma sunã daga waɗanda aka mũnana halittarsu. = --Qur'an 28:42
    And We gave Moses the Scripture, after We had destroyed the former generations, as enlightenment for the people and guidance and mercy that they might be reminded. <> Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã Littãfi daga bãyan Mun halakar da ƙarnõnin farko, dõmin su zama abũbuwan kula ga mutãne, da shiriya da rahama, tsammãninsu sunã tunãwa. = --Qur'an 28:43
    And you, [O Muhammad], were not on the western side [of the mount] when We revealed to Moses the command, and you were not among the witnesses [to that]. <> Kuma ba ka kasance ba ga gẽfen rãfi na yamma a lõkacin da Muka hukunta al'amaru zuwa ga Mũsã, kuma ba ka kasance daga halartattu ba. = --Qur'an 28:44
    But We produced [many] generations [after Moses], and prolonged was their duration. And you were not a resident among the people of Madyan, reciting to them Our verses, but We were senders [of this message]. <> Kuma amma Mũ, Mun ƙãga halittawar wasu ƙarnõni har lõkatan rãyuwa suka yi tsawo a kansu. Kuma ba ka kasance mazauni ba a cikin mutãnen Madyana, kanã karanta musu ãyõyinMu, amma Mũ Mun kasãnce mãsu aikãwa (da kai game da waɗancan lãbarai). = --Qur'an 28:45
    And you were not at the side of the mount when We called [Moses] but [were sent] as a mercy from your Lord to warn a people to whom no warner had come before you that they might be reminded. <> Kuma ba ka kasance ga gẽfen dũtse ba a lõkacin da Muka yi kira, kuma amma dõmin rahama daga Ubangijinka, dõmin ka yi gargaɗi ga mutãne waɗanda suke wani mai gargaɗi a gabãninka bai je musu ba, tsammãninsu sunã tunãwa. = --Qur'an 28:46
    And if not that a disaster should strike them for what their hands put forth [of sins] and they would say, "Our Lord, why did You not send us a messenger so we could have followed Your verses and been among the believers?"... <> Kuma bã dõmin wata masĩfa ta sãme su ba sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, su ce: "Yã Ubangijinmu! Don me ba Ka aiko wani Manzo zuwa gare mu ba, har mu dinga bĩn ãyõyinKa, kuma mu kasance daga mũminai?" = --Qur'an 28:47
    But when the truth came to them from Us, they said, "Why was he not given like that which was given to Moses?" Did they not disbelieve in that which was given to Moses before? They said, "[They are but] two works of magic supporting each other, and indeed we are, in both, disbelievers." <> Sa'an nan a lõkacin da gaskiya ta jẽ musu daga wurinMu, suka ce: "Don me ba a bã shi kamar abin da aka bai wa Mũsã ba?" Shin kuma ba su kãfirta ba da abin da aka bai wa Mũsã a gabãnin (wannan)? suka ce: "Sihirõri biyu ne suka taimaki jũna," kuma suka ce: "Lalle ne mũ, mãsu kãfirta ne ga dukansu?" = --Qur'an 28:48
    Say, "Then bring a scripture from Allah which is more guiding than either of them that I may follow it, if you should be truthful." <> Ka ce: "To ku zo da wani littãfi daga, wurin Allah, wanda yake shi ne mafi shiryarwa daga gare su, in bĩ shi, idan kunkasance mãsu gaskiya." = --Qur'an 28:49
    But if they do not respond to you - then know that they only follow their [own] desires. And who is more astray than one who follows his desire without guidance from Allah? Indeed, Allah does not guide the wrongdoing people. <> To, idan ba su karɓa maka ba to sai ka sani sunã bin son zuciyarsu ne kawai, kuma wãne ne mafi ɓata daga wanda ya bi son zuciyarsa, bã tãre da wata shiriya daga Allah ba? Lalle ne, Allah bã ya shiryar da mutãne azzãlumai. = --Qur'an 28:50
    And We have [repeatedly] conveyed to them the Qur'an that they might be reminded. <> Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun sãdar da magana sabõda su, tsammãninsu, suna tunãni. = --Qur'an 28:51
    Those to whom We gave the Scripture before it - they are believers in it. <> Waɗanda Muka bã su littãfi daga gabãninsa (Alƙur'ãni), su mãsu ĩmãni ne da shi. = --Qur'an 28:52
    And when it is recited to them, they say, "We have believed in it; indeed, it is the truth from our Lord. Indeed we were, [even] before it, Muslims [submitting to Allah]." <> Kuma idan anã karanta shi a kansu, sai su ce: "Mun yi ĩmãni da shi, lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinmu. Lalle mũ, mun kasance a gabãninsa masu sallamãwa." = --Qur'an 28:53
    Those will be given their reward twice for what they patiently endured and [because] they avert evil through good, and from what We have provided them they spend. <> Waɗancan anã ba su lãdarsu sau biyu, sabõda haƙurin da suka yi, kuma da kyautatãwa suna tunkuɗewar mũnanãwa kuma daga abin da Muka azũrtã susunã ciyarwa. = --Qur'an 28:54
    And when they hear ill speech, they turn away from it and say, "For us are our deeds, and for you are your deeds. Peace will be upon you; we seek not the ignorant." <> Kuma idan sun ji yãsassar magana sukan kau da kai daga barinta, kuma sukan ce, "Ayyukanmu sunã a gare mu, kuma ayyukanku sunã a gare ku, aminci ya tabbata a kanmu bã mu nẽman jãhilai (da husũma)." = --Qur'an 28:55
    Indeed, [O Muhammad], you do not guide whom you like, but Allah guides whom He wills. And He is most knowing of the [rightly] guided. <> Lalle ne kai bã ka shiryar da wanda ka so, amma kuma Allah Yanã shiryar da wanda Yake so, kuma Shi ne Mafi sani daga mãsu shiryuwa. = --Qur'an 28:56
    And they say, "If we were to follow the guidance with you, we would be swept from our land." Have we not established for them a safe sanctuary to which are brought the fruits of all things as provision from Us? But most of them do not know. <> Kuma suka ce: "Idan mun bi shiriya tãre da kai anã fizge mu daga ƙasamiu." Shin, ba Mu tabbatar musu da mallakar Hurumi ba, ya zama amintacce, anã jãwõwa zuwa gare shi, 'ya'yan itãcen kõwane iri, bisa ga azurtãwa daga gare Mu? Amma kuma mafi yawansu ba su sani ba. = --Qur'an 28:57
    And how many a city have We destroyed that was insolent in its [way of] living, and those are their dwellings which have not been inhabited after them except briefly. And it is We who were the inheritors. <> Kuma da yawa Muka halakar da wata alƙarya wadda ta yi butulci ga rãyuwarta. To, waɗancan gidãjensu ne, ba a zaune su ba, a bãyansu, fãce kaɗan. Kuma mun kasance Mũ ne Magãda. = --Qur'an 28:58
    And never would your Lord have destroyed the cities until He had sent to their mother a messenger reciting to them Our verses. And We would not destroy the cities except while their people were wrongdoers. <> Kuma Ubangijinka bai kasance Mai halaka alƙaryu ba, sai Ya aika a cikin hedkwatarsu da wani Manzo yanã karanta ãyõyinMu a kansu. Kuma ba Mu kasance Mãsu halaka alƙaryu ba, fãce mutanensu sun kasance mãsu zãlunci. = --Qur'an 28:59
    And whatever thing you [people] have been given - it is [only for] the enjoyment of worldly life and its adornment. And what is with Allah is better and more lasting; so will you not use reason? <> Kuma abin da aka bã su daga kõme, to, jin dãɗin rayuwar dũniya ne da ƙawarta. Kuma abin da ke wurin Allah, shĩ ne mafi alhẽri, knma mafi wanzuwa. Shin bã ku hankalta? = --Qur'an 28:60
    Then is he whom We have promised a good promise which he will obtain like he for whom We provided enjoyment of worldly life [but] then he is, on the Day of Resurrection, among those presented [for punishment in Hell]? <> Shin fa, wanda Muka yi wa wa'adi, wa'adi mai kyau, sa'an nan shĩ mai haɗuwa da shi ne, yanã zama kamar wanda Muka jiyar da shi ɗan dãɗi, dãɗin rãyuwar dũniya, sa'an nan shi a Rãnar ¡iyãma yanã daga mãsu shiga wuta? = --Qur'an 28:61
    And [warn of] the Day He will call them and say, "Where are My 'partners' which you used to claim?" <> Kuma rãnar da (Allah) Yake kiran su sa'an nan Ya ce: "Inã abõkan tãrayyaTa, waɗanda kuka kasance kunã riyãwa?" = --Qur'an 28:62
    Those upon whom the word will have come into effect will say, "Our Lord, these are the ones we led to error. We led them to error just as we were in error. We declare our disassociation [from them] to You. They did not used to worship us." <> Waɗanda magana ta wajaba a kansu, su ce: "Yã Ubangijinmu! Waɗannan sũ ne waɗanda muka halakar mun halakar da su kamar yadda muka halaka. Mun barranta zuwa gare Ka, ba su kasance mũ suke bautã wa ba." = --Qur'an 28:63
    And it will be said, "Invoke your 'partners' " and they will invoke them; but they will not respond to them, and they will see the punishment. If only they had followed guidance! <> Kuma a ce ku kirãwo abõkan tãrayyar ɗinku, sai su kira su, sai ba su amsa ba, kuma su ga azãbar. Dã dai lalle su sun kasance snnã shiryuwa! = --Qur'an 28:64
    And [mention] the Day He will call them and say, "What did you answer the messengers?" <> Kuma rãnar da Yake kiran su, sa'an nan Ya ce: "Mẽne nekuka karɓa wa Mananni?" = --Qur'an 28:65
    But the information will be unapparent to them that Day, so they will not [be able to] ask one another. <> Sai lãbãru su ɓace musu a rãnar nan sa'an nan bã zã su tambayi jũnaosu ba. = --Qur'an 28:66
    But as for one who had repented, believed, and done righteousness, it is promised by Allah that he will be among the successful. <> To, amma wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni' ya aikata aiki na ƙwarai, to, akwai fãtan su kasance daga mãsu cin nasara. = --Qur'an 28:67
    And your Lord creates what He wills and chooses; not for them was the choice. Exalted is Allah and high above what they associate with Him. <> Kuma Ubangijinka Yanã halitta abin da Yake so kuma Yake zãɓi. Zãɓi bai kasance a gare su ba. Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma (Allah) Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka. = --Qur'an 28:68
    And your Lord knows what their breasts conceal and what they declare. <> Kuma Ubangijinka Yanã sanin abin da zukãtansu ke ɓõyẽwa, da abin da suke bayyanãwa. = --Qur'an 28:69
    And He is Allah; there is no deity except Him. To Him is [due all] praise in the first [life] and the Hereafter. And His is the [final] decision, and to Him you will be returned. <> Kuma Shĩ ne Allah, bãbu abin bautãwa fãce Shi. Kuma Shi ne abin gõdiya a cikin ta farko (dũniya), da ta ƙarshe (Lãhira). Kuma Shi ne da hukunci, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku. = --Qur'an 28:70
    Say, "Have you considered: if Allah should make for you the night continuous until the Day of Resurrection, what deity other than Allah could bring you light? Then will you not hear?" <> Ka ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya sanya dare tutur a kanku har zuwa Rãnar ¡iyãma, wane abin bautãwa wanin Allah zai zo muku da haske? Shin, bã ku ji?" = --Qur'an 28:71
    Say, "Have you considered: if Allah should make for you the day continuous until the Day of Resurrection, what deity other than Allah could bring you a night in which you may rest? Then will you not see?" <> Ka ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya sanya yini a kanku tutur zuwa Rãnar ¡iyãma, wane abin bautãwa, wanin Allah, zai zo muku da dare wanda kunã natsuwa a cikinsa? Shin fa, bã ku gani?" = --Qur'an 28:72
    And out of His mercy He made for you the night and the day that you may rest therein and [by day] seek from His bounty and [that] perhaps you will be grateful. <> "Kuma daga rahamarSa Ya sanya muku dare da yini dõmin ku natsu a cikinsa, kuma dõmin ku nẽma daga falalarSa, kuma tsammãninku zã ku gõde." = --Qur'an 28:73
    And [warn of] the Day He will call them and say, "Where are my 'partners' which you used to claim?" <> Kuma a rãnar da Yake kiran su ya ce: "Inã abõkan tarayya Ta, waɗanda kuka kasance kunã riyãwa" = --Qur'an 28:74
    And We will extract from every nation a witness and say, "Produce your proof," and they will know that the truth belongs to Allah, and lost from them is that which they used to invent. <> Kuma Muka zãre mai shaida daga kõwace al'umma, sa'an nan Muka ce: "Ku kãwo dalilinku." Sai suka san cẽwa lalle gaskiya ga Allah take. Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya ya ɓace daga barinsu. = --Qur'an 28:75
    Indeed, Qarun was from the people of Moses, but he tyrannized them. And We gave him of treasures whose keys would burden a band of strong men; thereupon his people said to him, "Do not exult. Indeed, Allah does not like the exultant. <> Lalle ne ¡ãrũna ya kasance daga mutãnen Mũsã, sai ya fita daga tsãrinsu alhãli Mun bã shi taskõkin abin da yake mabũɗansa sunã nauyi ga jama'a ma'abũta ƙarfi a lõkacin da mutãnensa suka ce masa, "Kada ka yi annashuwa, lalle ne Allah bã Ya son mãsu annashuwa." = --Qur'an 28:76
    But seek, through that which Allah has given you, the home of the Hereafter; and [yet], do not forget your share of the world. And do good as Allah has done good to you. And desire not corruption in the land. Indeed, Allah does not like corrupters." <> "Kuma ka biɗã a cikin abin da Allah Ya bã ka, gidan Lãhira, kuma kada ka manta da rabonka daga dũniya. Kuma ka kyautata, kamar yadda Allah Ya kyautata zuwa gare ka, kuma kada ka nẽmi ɓarna a cikin ƙasa, lalle ne Allah bã Ya son mãsu barna." = --Qur'an 28:77
    He said, "I was only given it because of knowledge I have." Did he not know that Allah had destroyed before him of generations those who were greater than him in power and greater in accumulation [of wealth]? But the criminals, about their sins, will not be asked. <> Ya ce: "An bã ni shi a kan wani ilmi wanda yake gare ni ne kawai." Shin, kuma bai sani ba cẽwa lalle Allah haƙiƙa Ya halakar a gabaninsa, daga ƙarnõni, wanda yake Shi ne mafi tsananin ƙarfi daga gare shi, kuma mafi yawan tãrawar dũkiya, kuma bã zã a tambayi mãsu laifi daga zunubansu ba? = --Qur'an 28:78
    So he came out before his people in his adornment. Those who desired the worldly life said, "Oh, would that we had like what was given to Qarun. Indeed, he is one of great fortune." <> Sai (¡ãrũna) ya fita a kan mutãnensa a cikin adonsa. Waɗanda suke nufin rãyuwar dũniya suka ce: "Inã dai munã da kwatancin abin da aka bai wa ¡ãrũna! Lalle shĩ haƙĩƙa ma'abũcin rabo babba ne." = --Qur'an 28:79
    But those who had been given knowledge said, "Woe to you! The reward of Allah is better for he who believes and does righteousness. And none are granted it except the patient." <> Kuma waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: "Kaitonku! sakamakon Allah ne mafi alhẽri a wanda ya yi tunãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai, kuma bãbu wanda ake haɗãwa da ita fãce mai ha ƙuri." = --Qur'an 28:80
    And We caused the earth to swallow him and his home. And there was for him no company to aid him other than Allah, nor was he of those who [could] defend themselves. <> Sai Muka shãfe ƙasa da shi da kuma gidansa. To, waɗansu jama'a ba su kasance gare shi ba, waɗanda suke taimakon sa, baicin Allah, kuma shi bai kasance daga mãsu taimakon kansu ba. = --Qur'an 28:81
    And those who had wished for his position the previous day began to say, "Oh, how Allah extends provision to whom He wills of His servants and restricts it! If not that Allah had conferred favor on us, He would have caused it to swallow us. Oh, how the disbelievers do not succeed!" <> Kuma waɗanda suka yi bũrin matsayinsa a jiya suka wãyi gari sunã cẽwa, "Wai! Allah Yanã shimfiɗa arziki, ga wanda Yake so daga bãyinsa, kuma Yanã ƙuntatãwa. Bã dõmin Allah Ya yi mana falala ba dã Yã shãfe ƙasa da mu. Wai! lalle ne shi, kãfirai bã su cin nasara." = --Qur'an 28:82
    That home of the Hereafter We assign to those who do not desire exaltedness upon the earth or corruption. And the [best] outcome is for the righteous. <> Wancan gidan Lãhira Munã sanya shi ga waɗanda suke bã su nufin ɗaukaka a cikin rãyuwar dũniya kuma bã su son ɓarna. Kuma ãkiba ga mãsu taƙawa take. = --Qur'an 28:83
    Whoever comes [on the Day of Judgement] with a good deed will have better than it; and whoever comes with an evil deed - then those who did evil deeds will not be recompensed except [as much as] what they used to do. <> Wanda ya zo da abu mai kyau, to, yana da mafi alhẽri daga gare shi, kuma wanda ya zo da mũgun abu, to, bã zã a sãkawa waɗanda suka aikata miyãgun ayyuka ba, fãce da abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 28:84
    Indeed, [O Muhammad], He who imposed upon you the Qur'an will take you back to a place of return. Say, "My Lord is most knowing of who brings guidance and who is in clear error." <> Lalle ne wanda Ya faralta Alƙur'ãni a kanka, haƙĩƙa, Mai Mayar da kai ne zuwa ga makõma. ka ce: "Ubangijĩna ne Mafi sani ga wanda ya zo da shiriya, da kuma wanda yake a cikin ɓata bayyananna." = --Qur'an 28:85
    And you were not expecting that the Book would be conveyed to you, but [it is] a mercy from your Lord. So do not be an assistant to the disbelievers. <> Kuma ba ka kasance kanã fãtan a jẽfa Littafin nan zuwa gare ka ba, fãce dai dõmin rahama daga Ubangijinka. Sabõda haka kada ka zama mai taimako ga kãfirai. = --Qur'an 28:86
    And never let them avert you from the verses of Allah after they have been revealed to you. And invite [people] to your Lord. And never be of those who associate others with Allah. <> Kuma kada lalle su karkatar da kai daga barin ãyõyin Allah, a bãyãn har an saukar da su uwa gare ka. Ka yi kira zuwa ga Ubangijinka, kuma kada lalle ka kasance daga mãsu shirka. = --Qur'an 28:87
    And do not invoke with Allah another deity. There is no deity except Him. Everything will be destroyed except His Face. His is the judgement, and to Him you will be returned. <> Kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. Kõwane abu mai halaka ne fãce fuskarSa. Shi ne da hukunci kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku. = --Qur'an 28:88
    Alif, Lam, Meem <> A. L̃. M̃. = --Qur'an 29:1
    Do the people think that they will be left to say, "We believe" and they will not be tried? <> Ashe, mutãne sun yi zaton a bar su su ce: "Mun yi ĩmãni," alhãli kuwa bã zã a fitine su ba?" = --Qur'an 29:2
    But We have certainly tried those before them, and Allah will surely make evident those who are truthful, and He will surely make evident the liars. <> Kuma lalle Mun fitini waɗanda ke a gabãninsu, dõmin lalle Allah Ya san waɗanda suka yi gaskiya, kuma lalle Ya san maƙaryata. = --Qur'an 29:3
    Or do those who do evil deeds think they can outrun Us? Evil is what they judge. <> Kõ waɗanda ke aikata miyãgun ayyuka sun yi zaton su tsẽre Mana? Abin da suke hukuntãwa ya mũnana. = --Qur'an 29:4
    Whoever should hope for the meeting with Allah - indeed, the term decreed by Allah is coming. And He is the Hearing, the Knowing. <> Wanda ya kasance yanã fãtan gamuwa da Al1ah to lalle ajalin Allah mai zuwa ne, kuma (Allah) Shĩ ne Mai ji, Masani. = --Qur'an 29:5
    And whoever strives only strives for [the benefit of] himself. Indeed, Allah is free from need of the worlds. <> Kuma wanda ya yi jihãdi, to, yanã yin jihãdin ne dõmin kansa. lalle Allah haƙĩƙa waɗatacce ne daga barin tãlikai. = --Qur'an 29:6
    And those who believe and do righteous deeds - We will surely remove from them their misdeeds and will surely reward them according to the best of what they used to do. <> Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle Munã kankare musu miyãgun ayyukansu, kuma lalle Munã sãka musu da mafi kyaun abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 29:7
    And We have enjoined upon man goodness to parents. But if they endeavor to make you associate with Me that of which you have no knowledge, do not obey them. To Me is your return, and I will inform you about what you used to do. <> Kuma Mun yi wa mutum wasiyyar kyautatãwa ga uwayensa, kuma idan sun tsananta maka dõmin ka yi shirki da Ni game da abin da bã ka da ilmi gare shi, to, kada ka yi musu ɗã'ã. Zuwa gare Ni makõmarku take sa'an nan In bã ku lãbari ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa. = --Qur'an 29:8
    And those who believe and do righteous deeds - We will surely admit them among the righteous [into Paradise]. <> Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle Munã shigar da su a cikin mutãnen kirki. = --Qur'an 29:9
    And of the people are some who say, "We believe in Allah," but when one [of them] is harmed for [the cause of] Allah, they consider the trial of the people as [if it were] the punishment of Allah. But if victory comes from your Lord, they say, "Indeed, We were with you." Is not Allah most knowing of what is within the breasts of all creatures? <> Kuma daga cikin mutãne akwai mai cẽwa, 'Mun yi ĩmãni da Allah" sa'an nan idan aka cũce shi wajen aikin Allah, sai ya sanya fitinar mutãne kamar azãbar Allah kuma lalle idan taimakon Ubangijinka ya zo, haƙĩƙa, ya kan ce: "Lalle mũ mun kasance tãre da ku." shin, Allah bai zama Mafi sani ba ga abin da ke a cikin ƙirãzan halittunSa? = --Qur'an 29:10
    And Allah will surely make evident those who believe, and He will surely make evident the hypocrites. <> Kuma lalle Allah na sanin waɗanda suka yi ĩmãni kuma lalle Yanã sanin munfukai. = --Qur'an 29:11
    And those who disbelieve say to those who believe, "Follow our way, and we will carry your sins." But they will not carry anything of their sins. Indeed, they are liars. <> Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, "Ku bi hanyarmu, kuma Mu ɗauki laifuffukanku," alhãli kõwa ba su zamo mãsu ɗauka da a kõme ba daga laifuffukansu. Lalle sũ maƙaryata ne. = --Qur'an 29:12
    But they will surely carry their [own] burdens and [other] burdens along with their burdens, and they will surely be questioned on the Day of Resurrection about what they used to invent. <> Kuma lalle sunã ɗaukar kãyan nauyinsu da waɗansu nauyãyan kãya tãre da kãyan nauyinsu, kuma lalle zã a tambaye su a Rãnar ¡iyama game da abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya. = --Qur'an 29:13
    And We certainly sent Noah to his people, and he remained among them a thousand years minus fifty years, and the flood seized them while they were wrongdoers. <> Kuma lalle Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnensa, sai ya zauna a cikinsu shẽkara dubu fãce shẽkara hamsin, sa'an nan cikowar (¦ũfãna) ta kãmã su, alhãli kuwa sũ ne mãsu zãlunci. = --Qur'an 29:14
    But We saved him and the companions of the ship, and We made it a sign for the worlds. <> Sa'an nan Muka tsĩrar da shi da mutãnen jirgin, kuma Muka sanya jirgin ya zama wata ãyã ga tãlikai. = --Qur'an 29:15
    And [We sent] Abraham, when he said to his people, "Worship Allah and fear Him. That is best for you, if you should know. <> Da Ibrãhĩm a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, "Ku bautã wa Allah ku bĩ Shi da taƙawa. Wannan Shĩ ne alhẽri a gare ku idan kun kasance kunã sani. = --Qur'an 29:16
    You only worship, besides Allah, idols, and you produce a falsehood. Indeed, those you worship besides Allah do not possess for you [the power of] provision. So seek from Allah provision and worship Him and be grateful to Him. To Him you will be returned." <> "Abin da dai kuke bautãwa, baiein Allah, gumaka ne, kuma kun ƙirƙira ƙarya. Lalle waɗannan da kuke bauta wa baicin Allah, bã su mallakã muku arziki. Sabõda haka ku nẽmi arziki a wurin Allah kawai, kuma ku bauta Masa, kuma ku yi gõdiya zuwa gare Shi. Zuwa gare Shi ake mayar da ku. = --Qur'an 29:17
    And if you [people] deny [the message] - already nations before you have denied. And there is not upon the Messenger except [the duty of] clear notification. <> "Kuma idan kun ƙaryata, to, lalle waɗansu al'ummõmi a gabãninku sun ƙaryata, kuma bãbu abin da ke kan Manzo, fãce iyar da manzanci, iyarwa bayyananna." = --Qur'an 29:18
    Have they not considered how Allah begins creation and then repeats it? Indeed that, for Allah, is easy. <> Shin, ba su ga yadda Allah ke fãra yin halitta ba, sa'an nan kuma Ya mayar da ita? Lalle wannan abu ne mai sauƙi ga Allah. = --Qur'an 29:19
    Say, [O Muhammad], "Travel through the land and observe how He began creation. Then Allah will produce the final creation. Indeed Allah, over all things, is competent." <> Ka ce: "Ku yi tafiya cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba yadda (Allah) Ya fãra yin halitta, sa'an nan kuma Allah Yanã ƙãga wata halittar mayarwa. Lalle Allah Mai ikon yi ne a kan kõme. = --Qur'an 29:20
    He punishes whom He wills and has mercy upon whom He wills, and to Him you will be returned. <> "Yanã azabta wanda Ya so, kuma Yanã jin ƙan wanda Ya so. Kuma zuwa gare shi ake jũyaku." = --Qur'an 29:21
    And you will not cause failure [to Allah] upon the earth or in the heaven. And you have not other than Allah any protector or any helper. <> "Kuma ba ku zamo mãsu buwãya ba a cikin ƙasã, kuma haka a cikin sama kuma bã ku da wani majiɓinci wanda ba Allah ba, kuma ha ku da wani mataimaki." = --Qur'an 29:22
    And the ones who disbelieve in the signs of Allah and the meeting with Him - those have despaired of My mercy, and they will have a painful punishment. <> Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah da gamuwa da shi, waɗannan sun yanke ƙauna daga rahamaTa kuma waɗannan sunã da wata azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 29:23
    And the answer of Abraham's people was not but that they said, "Kill him or burn him," but Allah saved him from the fire. Indeed in that are signs for a people who believe. <> Sa'an nan bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa (Ibrãhĩm) fãce dai suka ce: "Ku kashe shi kõ, ku ƙõnã shi," Sai Allah Ya tsĩrar da shi daga wutã. Lallea cikin wannan akwai ayõyi ga mutãnen da ke yin ĩmãni. = --Qur'an 29:24
    And [Abraham] said, "You have only taken, other than Allah, idols as [a bond of] affection among you in worldly life. Then on the Day of Resurrection you will deny one another and curse one another, and your refuge will be the Fire, and you will not have any helpers." <> Kuma Ibrahĩm ya ce "Bãbu abin da kuka yi sai dai kub bar Allah kun riƙi gumãka sabõda sõyayyar tsakãninku a cikin rãyuwar dũniya, a'an nan a Rãnar ¡iyãma sãshinku zai kãfirce wa sãshi, kuma makõmarku ita ce wutã kuma bã ku da waɗansu mataimaka." = --Qur'an 29:25
    And Lot believed him. [Abraham] said, "Indeed, I will emigrate to [the service of] my Lord. Indeed, He is the Exalted in Might, the Wise." <> Sai Lũɗu ya yi ĩmãni da shi. Kuma Ibrãhĩm ya ce: "Lallenĩ mai ƙaura ne zuwa ga Ubangijina. Lalle Shĩ Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima." = --Qur'an 29:26
    And We gave to Him Isaac and Jacob and placed in his descendants prophethood and scripture. And We gave him his reward in this world, and indeed, he is in the Hereafter among the righteous. <> Kuma Muka bã shi Ishãƙa da Ya'aƙũba, kuma Muka sanya Annabci da littãfi a cikin zuriyarsa. Kuma Mun bã shi sakamakonsa a dũniya, kuma lalle shĩ a Lãhira, tabbas, yanã a cikin sãlihai. = --Qur'an 29:27
    And [mention] Lot, when he said to his people, "Indeed, you commit such immorality as no one has preceded you with from among the worlds. <> Da Lũɗu, a lõkacin daya ce wa mutãnensa, "Lalle kũ, haƙĩƙa kunã jẽ wa alfãsha wadda wani mahalũƙi daga cikin dũniya bai riga ku gare ta ba. = --Qur'an 29:28
    Indeed, you approach men and obstruct the road and commit in your meetings [every] evil." And the answer of his people was not but they said, "Bring us the punishment of Allah, if you should be of the truthful." <> "Ashe, lalle kũ kunã je wa maza, kuma ku yi fashin hanya kuma ku je, a cikin majalisarku da abin da bã shi da kyau? To, jawãbin mutãnensa bai kasance ba fãce dai sun ce: 'Ka zo mana da azãbar Allah, idan ka kasance daga mãsu gaskiya.'" = --Qur'an 29:29
    He said, "My Lord, support me against the corrupting people." <> Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni a kan mutãnen nan maɓarnata." = --Qur'an 29:30
    And when Our messengers came to Abraham with the good tidings, they said, "Indeed, we will destroy the people of that Lot's city. Indeed, its people have been wrongdoers." <> Kuma a lõkacin da ManzanninMu suka jẽ wa Ibrãhĩm da bushãra suka ce: "Lalle mu mãsu halaka mutãnen, wannan alƙarya ne. Lalle mutãnenta sun kasance mãsu zãlunci." = --Qur'an 29:31
    [Abraham] said, "Indeed, within it is Lot." They said, "We are more knowing of who is within it. We will surely save him and his family, except his wife. She is to be of those who remain behind." <> Ya ce: "Lalle akwai Lũɗu a cikinta!" Suka ce: "Mũ ne mafiya sani ga waɗanda suke a cikinta, lalle munã tsĩrar da shi da mutãnensa, fãce fa mãtarsa ta kasance a cikin mãsu wanzuwa." = --Qur'an 29:32
    And when Our messengers came to Lot, he was distressed for them and felt for them great discomfort. They said, "Fear not, nor grieve. Indeed, we will save you and your family, except your wife; she is to be of those who remain behind. <> Kuma a lõkacin da ManzanninMu suka je wa Lũɗu ya ɓãta rai sabõda su, kuma yã ƙuntata ga kirji sabõda su. Kuma suka ce: "Kada ka ji tsõro kuma kada ka yi baƙin ciki lalle mũ mãsu tsĩrar da kai ne da iyãlanka, fãce dai matarka ta kasance daga mãsu wanzuwa. = --Qur'an 29:33
    Indeed, we will bring down on the people of this city punishment from the sky because they have been defiantly disobedient." <> "Lalle mũ, mãsu saukar da azãba ne daga sama a kan mutãnen wannan alƙarya sabõda abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci." = --Qur'an 29:34
    And We have certainly left of it a sign as clear evidence for a people who use reason. <> Kuma lalle Mun bar wata ãyã bayyananna daga gare ta ga mutãne mãsu hankalta. = --Qur'an 29:35
    And to Madyan [We sent] their brother Shu'ayb, and he said, "O my people, worship Allah and expect the Last Day and do not commit abuse on the earth, spreading corruption." <> Kuma zuwa ga Madyana, Mun aika ɗan'uwansu shu'aibu, sai ya ce: "Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah kuma ku yi fatan (rahamar) Rãnar Lãhira, kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasã, alhãli kuwa kunã mãsu lãlãtarwa." = --Qur'an 29:36
    But they denied him, so the earthquake seized them, and they became within their home [corpses] fallen prone. <> Sai suka ƙaryata shi, sabõda haka tsãwa ta kãmã su, dõmin haka suka wãyi gari sunã guggurfãne. = --Qur'an 29:37
    And [We destroyed] 'Aad and Thamud, and it has become clear to you from their [ruined] dwellings. And Satan had made pleasing to them their deeds and averted them from the path, and they were endowed with perception. <> Da Ãdawa da Samũdãwa alhãli kuwa lalle alãmun azãba sun bayyana a gare su daga gidãjensu kuma Shaiɗan ya ƙawãta musu ayyukansu, sabõda haka ya kange su daga hanyar Allah, kuma sun kasance mãsu basĩra! = --Qur'an 29:38
    And [We destroyed] Qarun and Pharaoh and Haman. And Moses had already come to them with clear evidences, and they were arrogant in the land, but they were not outrunners [of Our punishment]. <> Kuma ¡ãrũna da Fir'auna da Hãmãna, kuma lalle Mũsaya je musu da hujjõji, sai suka yi girman kai a cikin ƙasã kuma ba su kasance mãsu tsẽrẽwa ba. = --Qur'an 29:39
    So each We seized for his sin; and among them were those upon whom We sent a storm of stones, and among them were those who were seized by the blast [from the sky], and among them were those whom We caused the earth to swallow, and among them were those whom We drowned. And Allah would not have wronged them, but it was they who were wronging themselves. <> Sabõda haka kõwanensu Mun kama shi da laifinsa. Watau daga cikinsu akwai wanda Muka aika iskar tsakuwa a kansa kuma daga cikinsu akwai wanda tsãwa ta kãmã, kuma daga cikinsu akwai wanda Muka birkice ƙasã da shi kuma daga cikinsu akwai wanda Muka nutsar. Bã ya yiwuwa ga Allah Ya zãlunce su, amma sun kasance kansu suke zãlunta. = --Qur'an 29:40
    The example of those who take allies other than Allah is like that of the spider who takes a home. And indeed, the weakest of homes is the home of the spider, if they only knew. <> Misãlin waɗanda suka riƙi waɗansu masõya waɗanda bã Allah ba, kamar misãlin gizõgizo ne wanda ya riƙi wani ɗan gida, alhãli kuwa lalle mafi raunin gidãje, shĩ ne gidan gizogizo, dã sun kasance sunã sane. = --Qur'an 29:41
    Indeed, Allah knows whatever thing they call upon other than Him. And He is the Exalted in Might, the Wise. <> Lalle Allah Yanã sane da abin da suke kira wanda bã Shi ba na wani abu duka kuma shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima. = --Qur'an 29:42
    And these examples We present to the people, but none will understand them except those of knowledge. <> Kuma waɗancan misãlan Munã bayyana su ga mutãne kuma bãbu mai hankalta da su sai mãsu ilmi. = --Qur'an 29:43
    Allah created the heavens and the earth in truth. Indeed in that is a sign for the believers. <> Allah Ya halitta sammai da ƙasa da gaskiya. Lalle cikin wancan akwai ãyã ga mũminai. = --Qur'an 29:44
    Recite, [O Muhammad], what has been revealed to you of the Book and establish prayer. Indeed, prayer prohibits immorality and wrongdoing, and the remembrance of Allah is greater. And Allah knows that which you do. <> Ka karanta abin da ake yin wahayi zuwa gare ka daga Littãfi, kuma ka tsayar da salla. Lalle salla tanã hanãwa daga alfãsha da abni ƙyãma, kuma lalle ambaton Allah ya fi girma, kuma Allah Yanã sane da abin da kuke aikatãwa. = --Qur'an 29:45
    And do not argue with the People of the Scripture except in a way that is best, except for those who commit injustice among them, and say, "We believe in that which has been revealed to us and revealed to you. And our God and your God is one; and we are Muslims [in submission] to Him." <> Kada ku yi jayayya da mazowa Littãfi sai fa da magana wadda ta fi kyau, sai fa waɗanda suka yi zãlunci daga gare su, kuma ku ce, "Mun yi ĩmãni da abin da aka saukar a gare mu kuma aka saukar a gare ku, kuma Abin bautãwarmu da Abin bautãwarku Guda ne, kama mũ mãsu sallamãwa ne a gare shi." = --Qur'an 29:46
    And thus We have sent down to you the Qur'an. And those to whom We [previously] gave the Scripture believe in it. And among these [people of Makkah] are those who believe in it. And none reject Our verses except the disbelievers. <> Kuma kamar haka Muka saukar da Littafi a gare ka, to, waɗannan da Muka bai wa Littãfi sanã ĩmãni da shi, daga cikin wãɗannan akwai mai ĩmãni da shi, kuma bãbu mai musun ãyõyinMu, fãce kãfirai. = --Qur'an 29:47
    And you did not recite before it any scripture, nor did you inscribe one with your right hand. Otherwise the falsifiers would have had [cause for] doubt. <> Kuma ba ka kasance kana karãtun wani littãfi ba a gabãninsa, kuma bã ka rubũtunsa da dãmanka dã haka yã auku, dã mãsu ɓarnã sun yi shakka. = --Qur'an 29:48
    Rather, the Qur'an is distinct verses [preserved] within the breasts of those who have been given knowledge. And none reject Our verses except the wrongdoers. <> Ã'a, shĩ ãyõyi ne bayyanannu a cikin ƙirãzan waɗanda aka bai wa ilmi. Kuma bãbu mai musun ãyõyinMu fãce azzãlumai. = --Qur'an 29:49
    But they say, "Why are not signs sent down to him from his Lord?" Say, "The signs are only with Allah, and I am only a clear warner." <> Kuma suka ce: "Don me ba a saukar masa da ãyõi ba daga Ubangijinsa? "Ka ce: "Su ãyõyi a wurin Allah kawai suke, kuma lalle ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyanãwa." = --Qur'an 29:50
    And is it not sufficient for them that We revealed to you the Book which is recited to them? Indeed in that is a mercy and reminder for a people who believe. <> Shin bai ishe su ba cẽwa lalle Mũ, Mun saukar da Littãfin akanka, anã karanta shi a kansu? Lalle a cikin wancan haƙĩƙa akwai rahama da tunãtawa ga mutanen da ke yin ĩmãni. = --Qur'an 29:51
    Say, "Sufficient is Allah between me and you as Witness. He knows what is in the heavens and earth. And they who have believed in falsehood and disbelieved in Allah - it is those who are the losers." <> Ka ce: "Allah Yã isa shaida a tsakãnĩna da tsakãnĩnku Yanã sane da abin da ke a cikin sammai da ƙasã, kuma waɗanda suka yi ĩmãni da ɗarya kuma suka kãfirta da Allah, waɗannan sũ nemãsu hasãra." = --Qur'an 29:52
    And they urge you to hasten the punishment. And if not for [the decree of] a specified term, punishment would have reached them. But it will surely come to them suddenly while they perceive not. <> Kuma suna nẽman ka da gaggauta azãba, to, bã dõmin ajali ƙayyadadde ba, dã azãba ta jẽ musu kuma lalle dã tanã iske su bisa ia abke, alhãli kuwa sũ ba su sani ba. = --Qur'an 29:53
    They urge you to hasten the punishment. And indeed, Hell will be encompassing of the disbelievers <> Sunã nẽman ka da gaggauta azãba, kuma lalle Jahannama, tabbas, mai kẽwayewa ce gakãfirai. = --Qur'an 29:54
    On the Day the punishment will cover them from above them and from below their feet and it is said, "Taste [the result of] what you used to do." <> Rãnar da azãba ke rufe su daga samansu da kuma ƙasan ƙafafunsu kuma Ya ce: "Ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã aikatãwa." = --Qur'an 29:55
    O My servants who have believed, indeed My earth is spacious, so worship only Me. <> Yã bãyiNa, waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle fa ƙasãTa mai yalwã ce, sabãda haka ku bauta Mini. = --Qur'an 29:56
    Every soul will taste death. Then to Us will you be returned. <> Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne, sa'an nan zuwa gare Mu ake mayar da ku. = --Qur'an 29:57
    And those who have believed and done righteous deeds - We will surely assign to them of Paradise [elevated] chambers beneath which rivers flow, wherein they abide eternally. Excellent is the reward of the [righteous] workers <> Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle zã Mu zaunar da su daga cikin Aljanna a gidãjen bẽne, ƙoramu nã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu. To, madalla da sakamakon mãsu aikin ƙwarai. = --Qur'an 29:58
    Who have been patient and upon their Lord rely. <> Waɗanda suka yi haƙuri, kuma sunã dõgara ga Ubangijinsu kawai. = --Qur'an 29:59
    And how many a creature carries not its [own] provision. Allah provides for it and for you. And He is the Hearing, the Knowing. <> Kuma da yawa dabba wadda bã ta ɗaukar abincinta Allah Yanã ciyar da ita tãre da ku, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai ilmi. = --Qur'an 29:60
    If you asked them, "Who created the heavens and earth and subjected the sun and the moon?" they would surely say, "Allah." Then how are they deluded? <> Lalle idan ka tambaye su: "Wãne ne ya halitta sammai da ƙasã kuma ya hõre rãnã da watã?" Lalle sunã cẽwa Allah ne. TO, yãya ake karkatar da su? = --Qur'an 29:61
    Allah extends provision for whom He wills of His servants and restricts for him. Indeed Allah is, of all things, Knowing. <> A1lah ne ke shimfiɗa arziki ga wanda Yake so daga cikin bãyinsa kuma Yanã ƙuntãtãwa ga (wanda, Yake so). Lalle Allah, Masani ne ga dukan kõme. = --Qur'an 29:62
    And if you asked them, "Who sends down rain from the sky and gives life thereby to the earth after its lifelessness?" they would surely say " Allah." Say, "Praise to Allah "; but most of them do not reason. <> Kuma lalle idan ka tambaye su. "Wãne ne ya saukar da ruwa daga sama, har ya rãyar da ƙasã game da shi a bãyan mutuwarta?" Lalle sunã cẽwa, "Allah ne." Ka ce: "Gõdiya tã tabbata ga Allah." Ã'a, mafi yawansu bã su hankalta. = --Qur'an 29:63
    And this worldly life is not but diversion and amusement. And indeed, the home of the Hereafter - that is the [eternal] life, if only they knew. <> Kuma wannan rãyuwa ta dũniya ba ta zamo ba, fãce abar shagala da wãsã kuma lalle Lãhira tabbas, ita ce rãyuwa, dã sun kasance sunã sani. = --Qur'an 29:64
    And when they board a ship, they supplicate Allah, sincere to Him in religion. But when He delivers them to the land, at once they associate others with Him <> To, a lõkacin da suka shiga cikin jirgin ruwa, sun kirãyi Allah sunã mãsu tsarkake addini a gare shi, to, a lõkacin da Ya tsĩrar da su zuwa ga tudun ƙasã, sai gã su sunã shirki. = --Qur'an 29:65
    So that they will deny what We have granted them, and they will enjoy themselves. But they are going to know. <> Dõmin su kãfirce wa abin da Muka bã su kuma dõmin su ji dãɗi sa'an nan kuma zã su sani. = --Qur'an 29:66
    Have they not seen that We made [Makkah] a safe sanctuary, while people are being taken away all around them? Then in falsehood do they believe, and in the favor of Allah they disbelieve? <> Shin, ba su ga cẽwa, lalle Mun sanya Hurumi amintacce ba alhãli kuwa anã fisge mutãne a gẽfensu? Shin, da ɓãtaccen abu suke ĩmãni kuma da ni'imarAllah suka kãfirta? = --Qur'an 29:67
    And who is more unjust than one who invents a lie about Allah or denies the truth when it has come to him? Is there not in Hell a [sufficient] residence for the disbelievers? <> Kuma wãne ne ya fi zãlunci bisa ga wanda ya ƙirƙira ƙarya ya jingina ta ga Allah, kõ kuma ya ƙaryata gaskiya a lõkacin da ta je masa? Ashe a cikin Jahannama bãbu mazauna ga kãfirai? = --Qur'an 29:68
    And those who strive for Us - We will surely guide them to Our ways. And indeed, Allah is with the doers of good. <> Kuma wadannan da suka yi ƙõƙari ga nẽman yardarMu, lalle Munã shiryar da su ga hanyõyinMu, kuma lalle Allah, tabbas, Yanã tãre da mãsu kyautatãwa (ga addĩninsu). = --Qur'an 29:69
    Alif, Lam, Meem. <> A. L̃. M̃. = --Qur'an 30:1
    The Byzantines have been defeated <> An rinjãyi Rũmawa. = --Qur'an 30:2
    In the nearest land. But they, after their defeat, will overcome. <> A cikin mafi kusantar ƙasarsu, kuma sũ, a bãyan rinjãyarsu, zã sn rinjãya. = --Qur'an 30:3
    Within three to nine years. To Allah belongs the command before and after. And that day the believers will rejoice <> A cikin'yan shẽkaru. Al'amari na Allah ne a gabãnin kõme da bãyansa, kuma a rãnar nan mũminai zã su yi farin ciki. = --Qur'an 30:4
    In the victory of Allah. He gives victory to whom He wills, and He is the Exalted in Might, the Merciful. <> Da taimakon Allah Yanã taimakon wanda Yake so. Kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. = --Qur'an 30:5
    [It is] the promise of Allah. Allah does not fail in His promise, but most of the people do not know. <> Wa'adin Allah, Allah bã ya sãɓãwa ga wa'adinsa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba. = --Qur'an 30:6
    They know what is apparent of the worldly life, but they, of the Hereafter, are unaware. <> Sunã sanin bayyanannar rãyuwar dũniya, alhãli kuwa sũ shagalallu ne daga rãyuwar Lãhira. = --Qur'an 30:7
    Do they not contemplate within themselves? Allah has not created the heavens and the earth and what is between them except in truth and for a specified term. And indeed, many of the people, in [the matter of] the meeting with their Lord, are disbelievers. <> Shin, ba su yi tunãni ba a cikin zukãtansu cẽwa Allah bai halitta sammai da ƙasa ba da abin da ke tsakãninsu, fãce da gaskiya da ajali ambatacce? Kuma lalle mãsu yawa daga mutãne kãfirai ne ga gamuwa da Ubangijinsu? = --Qur'an 30:8
    Have they not traveled through the earth and observed how was the end of those before them? They were greater than them in power, and they plowed the earth and built it up more than they have built it up, and their messengers came to them with clear evidences. And Allah would not ever have wronged them, but they were wronging themselves. <> Shin, kuma ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã dõmin su gani yadda aƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Sun kasance mafiya ƙarfi daga gare su kuma suka nõmi ƙasa suka rãya ta fiye da yadda suka raya ta, kuma manzanninsu suka je musu da hujjoji bayyanannu. Sabo da haka Allah ba Ya yiwuwa Ya zãlunce su, amma kansu suka kasance sunã zãlunta. = --Qur'an 30:9
    Then the end of those who did evil was the worst [consequence] because they denied the signs of Allah and used to ridicule them. <> Sa'an nan ãƙibar waɗannan da suka aikata mũgun aiki ta kasance mafi muni, wãtau sun ƙaryata game da ãyõyin Allah, kuma suka kasance sunã izgili da su. = --Qur'an 30:10
    Allah begins creation; then He will repeat it; then to Him you will be returned. <> Allah ne ke fãra yin halitta, sa'an nan Ya sãke ta sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku. = --Qur'an 30:11
    And the Day the Hour appears the criminals will be in despair. <> Kuma a rãnar da sa'a ke tsayuwa, mãsu laifi zã su kãsa magana. = --Qur'an 30:12
    And there will not be for them among their [alleged] partners any intercessors, and they will [then] be disbelievers in their partners. <> Kuma bã su da mãsu cẽto daga abũbuwan shirkinsu, kuma snn kasance mãsu kãfircẽwadaga abũbuwan shirkinsu. = --Qur'an 30:13
    And the Day the Hour appears - that Day they will become separated. <> Kuma a rãnar da Sa'a ke tsayuwa, a rãnar nan mutãne ke farraba. = --Qur'an 30:14
    And as for those who had believed and done righteous deeds, they will be in a garden [of Paradise], delighted. <> To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai to sũ anã faranta musu rãyuka, a cikin wani lambu. = --Qur'an 30:15
    But as for those who disbelieved and denied Our verses and the meeting of the Hereafter, those will be brought into the punishment [to remain]. <> Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata, game da ãyõyinMu da kuma haɗuwa da Rãnar Lãhira, to, waɗancan anã halartar da su a cikin azãba. = --Qur'an 30:16
    So exalted is Allah when you reach the evening and when you reach the morning. <> Sabõda haka tsarkakẽwa ta tabbata ga Allah a lõkacin da kuke shiga maraice, da lõkacin da kuke shiga sãfiya. = --Qur'an 30:17
    And to Him is [due all] praise throughout the heavens and the earth. And [exalted is He] at night and when you are at noon. <> Kuma Shĩ ne da gõdiya, a cikin sammai da ƙasã kuma da lõkacin yamma da lõkacin zawãli. = --Qur'an 30:18
    He brings the living out of the dead and brings the dead out of the living and brings to life the earth after its lifelessness. And thus will you be brought out. <> Yanã fitar da mai rai daga matacce kuma Yanã fitar da matacce daga mai rai, kuma Yanã rãyar da ƙasa a bãyan mutuwarta. Kuma haka ake fitar da ku. = --Qur'an 30:19
    And of His signs is that He created you from dust; then, suddenly you were human beings dispersing [throughout the earth]. <> Kuma akwai daga ãyõyinSa, Ya halitta ku daga turɓãya, sai gã ku kun zama mutum, kunã wãtsuwa. = --Qur'an 30:20
    And of His signs is that He created for you from yourselves mates that you may find tranquillity in them; and He placed between you affection and mercy. Indeed in that are signs for a people who give thought. <> Kuma akwai daga ãyõyinsa, Ya halitta muku mãtan aure daga kanku, dõmin ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya sõyayya da rahama a tsakãninku. Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin tunãni. = --Qur'an 30:21
    And of His signs is the creation of the heavens and the earth and the diversity of your languages and your colors. Indeed in that are signs for those of knowledge. <> Kuma akwai daga ãyõyinSa halittar sammai da ƙasã da sãɓã, war harsunanku, da launukanku. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mãsu ilmi. = --Qur'an 30:22
    And of His signs is your sleep by night and day and your seeking of His bounty. Indeed in that are signs for a people who listen. <> Kuma akwai daga cikin ãyõyinSa, barcinku a cikin dare da rãna, da nẽmanku ga falalarsa. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu saurãrãwa. = --Qur'an 30:23
    And of His signs is [that] He shows you the lightning [causing] fear and aspiration, and He sends down rain from the sky by which He brings to life the earth after its lifelessness. Indeed in that are signs for a people who use reason. <> Kuma akwai daga cikin ãyõyinSa, Ya nũna muku walƙiya a kan tsõro da ɗammãni kuma Ya dinga saukar da ruwa daga sama Sa'an nan Ya rãyar da ƙasã game da shi a bãyan mutuwarta. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu hankaltawa. = --Qur'an 30:24
    And of His signs is that the heaven and earth remain by His command. Then when He calls you with a [single] call from the earth, immediately you will come forth. <> Kuma akwai daga ãyõyinsa, tsayuwar sama da asƙã bisa umurninsa, sa'an nan idan Ya kira ku, kira ɗaya, daga ƙasã, sai gã ku kunã fita. = --Qur'an 30:25
    And to Him belongs whoever is in the heavens and earth. All are to Him devoutly obedient. <> Kuma wanda ke cikin sammai da ƙasã Nãsa ne shi kaɗai. Dukansu mãsu tawãli'u ne a gare Shi. = --Qur'an 30:26
    And it is He who begins creation; then He repeats it, and that is [even] easier for Him. To Him belongs the highest attribute in the heavens and earth. And He is the Exalted in Might, the Wise. <> Kuma Shĩ ne Wanda Ya fãra halitta, sa'an nan Ya sãke ta kuma sakẽwarta tã fi sauƙi a gare shi. Kuma Yanã da misãli wanda ya fi ɗaukaka a cikin sammai da ƙasã kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. = --Qur'an 30:27
    He presents to you an example from yourselves. Do you have among those whom your right hands possess any partners in what We have provided for you so that you are equal therein [and] would fear them as your fear of one another [within a partnership]? Thus do We detail the verses for a people who use reason. <> Ya bũga muku wani misãli daga kanku. Kõ kunã da abõkan tarẽwa, daga cikin bãyin da hannãyenku na dãma suka mallaka, a cikin arzikinku, watau ku zama daidai a ciki kunã tsõron su kamar tSõronku ga kanku? Haka dai Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, ga mutãne mãsu hankaltawa. = --Qur'an 30:28
    But those who wrong follow their [own] desires without knowledge. Then who can guide one whom Allah has sent astray? And for them there are no helpers. <> Ã'aha! waɗanda suka yi zã1unci sun bi son zũciyõyinsu, bã tãre da wani ilmi ba. To wãne ne zai shiryar da wanda Allah Ya ɓatar, kuma bã su da waɗansu mataimaka? = --Qur'an 30:29
    So direct your face toward the religion, inclining to truth. [Adhere to] the fitrah of Allah upon which He has created [all] people. No change should there be in the creation of Allah. That is the correct religion, but most of the people do not know. <> Sabõda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini, kanã mai karkata zuwa ga gaskiya, halittar Allah da Ya halitta mutãne a kanta. Bãbu musanyãwa ga halittar Allah, wannan shĩ ne addini madaidaici kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba. = --Qur'an 30:30
    [Adhere to it], turning in repentance to Him, and fear Him and establish prayer and do not be of those who associate others with Allah <> Kunã mãsu mai da al'amari gare Shi, kuma ku bĩ Shi dataƙawa, kuma ku tsayar da salla, kuma kada ku kasance daga mushirikai. = --Qur'an 30:31
    [Or] of those who have divided their religion and become sects, every faction rejoicing in what it has. <> Wãtau waɗanda suka rarrabe addininsu kuma suka kasance ƙungiya-ƙungiya, kõwace ƙungiya tanã mai farin ciki da abin da ke a gare ta kawai. = --Qur'an 30:32
    And when adversity touches the people, they call upon their Lord, turning in repentance to Him. Then when He lets them taste mercy from Him, at once a party of them associate others with their Lord, <> Kuma idan cũta ta shãfi mutãne, sai su kirãyi Ubangijinsu, sunã mãsu mai da al'amari gare Shi, sa'an nan idan Ya ɗanɗana musu wata rahama daga gare Shi, sai gã wani ɓangare daga gare su sunã shirki da Ubangijinsu. = --Qur'an 30:33
    So that they will deny what We have granted them. Then enjoy yourselves, for you are going to know. <> Dõmin su kãfirta dl abin da Muka bã su. To ku ji dãɗi kaɗan Sa'an nan zã ku, sani. = --Qur'an 30:34
    Or have We sent down to them an authority, and it speaks of what they were associating with Him? <> Kõ Mun saukar da wani dalĩ li a gare su? Shi kuwa yanã magana da abin da suka kasance sunã shirkin da shi? = --Qur'an 30:35
    And when We let the people taste mercy, they rejoice therein, but if evil afflicts them for what their hands have put forth, immediately they despair. <> Kuma idan Muka ɗanɗana wa mutãne wata rahama, sai su yi farin ciki da ita kuma idan cũta ta sãme su, sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, sai gã su sunã yanke ƙauna, = --Qur'an 30:36
    Do they not see that Allah extends provision for whom He wills and restricts [it]? Indeed, in that are signs for a people who believe. <> Shin, kuma ba su gani ba cẽwa Allah na shimfida arziki ga wanda Yake so kuma Yanã ƙuntatãwa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin ĩmãni. = --Qur'an 30:37
    So give the relative his right, as well as the needy and the traveler. That is best for those who desire the countenance of Allah, and it is they who will be the successful. <> Sabõda haka ka bai wa zumu hakkinsa da miskĩnai da ɗan hanya, wannan shĩ ne alhẽri ga waɗanda ke nufin yardar Allah kuma waɗancan sũ ne mãsu sãmun babban rabo. = --Qur'an 30:38
    And whatever you give for interest to increase within the wealth of people will not increase with Allah. But what you give in zakah, desiring the countenance of Allah - those are the multipliers. <> Kuma abin da kuka bãyar na riba dõmin ya ƙãru a cikin dũkiyar mutãne to, bã zai ƙãru ba, a wurin Allah. Kuma abin da kuka bãyar na zakka, kanã nufin yardar Allah to (mãsu yin haka) waɗancan sũ ne mãsu ninkãwa (ga dũkiyarsu). = --Qur'an 30:39
    Allah is the one who created you, then provided for you, then will cause you to die, and then will give you life. Are there any of your "partners" who does anything of that? Exalted is He and high above what they associate with Him. <> Allah ne Wanda Ya halitta ku, sa'an nan Ya azurta ku, sa'an nan Ya matar da ku, sa'an nan Ya rãyar da ku. Ashe, daga cikin abũbuwan shirkinku akwai wanda ke aikata wani abu daga waɗannan ahũbuwa? Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma Ya ɗaukaka bisa ga abin da suke yi na shirki. = --Qur'an 30:40
    Corruption has appeared throughout the land and sea by [reason of] what the hands of people have earned so He may let them taste part of [the consequence of] what they have done that perhaps they will return [to righteousness]. <> ¥arnã tã bayyana a cikin ƙasa da tẽku, sabõda abin da hannãyen mutãne suka aikata. Dõmin Allah Ya ɗanɗana musu sãshin abin da suka aikata, ɗammãninsu zã su kõmo. = --Qur'an 30:41
    Say, [O Muhammad], "Travel through the land and observe how was the end of those before. Most of them were associators [of others with Allah]. <> Ka ce: "Ku tafi a cikin ƙasã sa'an nan ku dũbi yadda ãƙibar waɗanda suka kasance a gabãninku ta kasance. Mafi yawansu sun kasance mãsu yin shirki." = --Qur'an 30:42
    So direct your face toward the correct religion before a Day comes from Allah of which there is no repelling. That Day, they will be divided. <> Sabõda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini madaidaici a gabãnin wani yini ya zo, bãbu makawa gare Shi daga Allah, a rãnar nan mutãne sunã tsãgẽwa (su rabu biyu). = --Qur'an 30:43
    Whoever disbelieves - upon him is [the consequence of] his disbelief. And whoever does righteousness - they are for themselves preparing, <> Wanda ya kãfirta, to, kãfircinsa na kansa, kuma wanda ya aikata aikin ƙwarai, to, sabõda kansu suke yin shimfiɗa. = --Qur'an 30:44
    That He may reward those who have believed and done righteous deeds out of His bounty. Indeed, He does not like the disbelievers. <> Dõmin Ya sãkã wa waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, daga falalarSa. Lalle Allah bã Ya son kafirai. = --Qur'an 30:45
    And of His signs is that He sends the winds as bringers of good tidings and to let you taste His mercy and so the ships may sail at His command and so you may seek of His bounty, and perhaps you will be grateful. <> Kuma akwai daga ãyõyinSa, ya aika iskõki mãsu bãyar da bushãra kuma dõmin Ya ɗanɗana muku daga rahamarSa, kuma dõmin jirãgen ruwa su gudãna da umurninSa, kuma dõmin ku nẽma daga falalarSa, fãtanku zã ku gode. = --Qur'an 30:46
    And We have already sent messengers before you to their peoples, and they came to them with clear evidences; then We took retribution from those who committed crimes, and incumbent upon Us was support of the believers. <> Kuma lalle Mun aiki waɗansu Manzanni a gabãninka, zuwa ga mutãnensu sai suka je musu da hujjõji, bayyanannu, sa'an nan Muka azabtar da waɗanda suka yi laifi, kuma ya kasance tabbatacce taimakon mũminai wajibi ne a kan mu. = --Qur'an 30:47
    It is Allah who sends the winds, and they stir the clouds and spread them in the sky however He wills, and He makes them fragments so you see the rain emerge from within them. And when He causes it to fall upon whom He wills of His servants, immediately they rejoice <> Allah ne Wanda ke aika iskõki, sai su mõtsar da girgije, sa'an nan Ya shimfiɗa shi a cikin sama yadda Yake so, kuma Ya sanya shi wani ɓaɓɓake, sa'an nan ka ga ruwa na fita daga tsakãninsa. Sa'an nan idan Allah Ya sãmi waɗanda Ya so daga bãyinsa, Sai gã su suna bushãra da shi. = --Qur'an 30:48
    Although they were, before it was sent down upon them - before that, in despair. <> Kuma kõ da sun kasance a gabãnin a saukar da shi a kansu, kusa-kusa, sunã baƙin ciki hai bã su iya magana. = --Qur'an 30:49
    So observe the effects of the mercy of Allah - how He gives life to the earth after its lifelessness. Indeed, that [same one] will give life to the dead, and He is over all things competent. <> Sai ka dũbi alãmõmin rahamar Allah yadda Yake rãyar da ƙasã a bãyan mutuwarta. Lalle wannan (Mai wannan aiki), tabbas, Mai rãyar da halitta ne, kuma Shi Mai ikon yi ne a kan kõme. = --Qur'an 30:50
    But if We should send a [bad] wind and they saw [their crops] turned yellow, they would remain thereafter disbelievers. <> Kuma lalle idan Mun aika wata iska, suka ganta fatsifatsi, lalle zã su yini a bãyansa sunã kãfirta. = --Qur'an 30:51
    So indeed, you will not make the dead hear, nor will you make the deaf hear the call when they turn their backs, retreating. <> Sabõda haka, kai, bã ka jiyar da matattu kira, kuma bã ka jiyar da kurãme kira idan sun jũya bãya sunã gudu. = --Qur'an 30:52
    And you cannot guide the blind away from their error. You will only make hear those who believe in Our verses so they are Muslims [in submission to Allah]. <> Kuma ba ka zamo mai shiryar da makãfi ba daga ɓatarsu, bã ka jiyarwa fãce wanda ke yin ĩmãni da ãyõyinMu, watau sũ ne mãsu mĩƙa wuya, su sallama. = --Qur'an 30:53
    Allah is the one who created you from weakness, then made after weakness strength, then made after strength weakness and white hair. He creates what He wills, and He is the Knowing, the Competent. <> Allah ne Ya halitta ku daga rauni, sa'an nan Ya sanya wani ƙarfi a bayan wani rauni, sa'an nan Ya sanya wani rauni da furfura a bãyan wani ƙarfi, Allah na halitta abin da Ya so, kuma Shĩ ne Mai ilmi, Mai ĩkon yi, = --Qur'an 30:54
    And the Day the Hour appears the criminals will swear they had remained but an hour. Thus they were deluded. <> Kuma a rãnar da Sa'a ke tsayuwa, mãsu laifi na rantsuwã: Ba su zauna a cikin kabari ba fãce sã'a guda. Kamar haka suka kasance anã karkatar da su. = --Qur'an 30:55
    But those who were given knowledge and faith will say, "You remained the extent of Allah 's decree until the Day of Resurrection, and this is the Day of Resurrection, but you did not used to know." <> Kuma waɗanda aka bai wa ilmi da ĩmãni suka ce: "Lalle, haƙĩƙa kun zauna a cikin Littãfin Allah, har zuwa rãnar tãyarwa, to, kuma wannan ita ce rãnar tãyarwar, kuma amma kũ, kun kasance ba ku sani ba." = --Qur'an 30:56
    So that Day, their excuse will not benefit those who wronged, nor will they be asked to appease [Allah]. <> To, a rãnar da uzurin waɗanda suka yi zãlunci bã ya amfaninsu, kuma bã a neman yardarsu. = --Qur'an 30:57
    And We have certainly presented to the people in this Qur'an from every [kind of] example. But, [O Muhammad], if you should bring them a sign, the disbelievers will surely say, "You [believers] are but falsifiers." <> Kuma lalle tabbas Mun buga kõwane irin misãli ga mutãne a cikin wannan Alƙur'ãni, kuma lalle idan kã je musu da kõwace ãyã, lalle, waɗanda suka kãfirta zã su ce "Kũ, bã kõme kuke ba fãce mãsu barua." = --Qur'an 30:58
    Thus does Allah seal the hearts of those who do not know. <> Kamar haka Allah Yake shãfe haske a kan zukãtan waɗanda ba su sani ba. = --Qur'an 30:59
    So be patient. Indeed, the promise of Allah is truth. And let them not disquiet you who are not certain [in faith]. <> Sabõda haka ka yi haƙuri lalle wa'adin Allah gaskiya ne, kuma kada waɗanda bã su da yaƙĩni su sassabce maka hankali. = --Qur'an 30:60
    Alif, Lam, Meem. <> A. L̃. M̃. = --Qur'an 31:1
    These are verses of the wise Book, <> Waɗancan ãyõyin Littãfin ne mai hikima. = --Qur'an 31:2
    As guidance and mercy for the doers of good <> Shiriya da rahama ne ga mãsu kyautatawa. = --Qur'an 31:3
    Who establish prayer and give zakah, and they, of the Hereafter, are certain [in faith]. <> Waɗanda ke tsai da salla kuma sunã ɓãyar da zakka kuma sũ, sunã yin ĩmãnin yaƙĩni, ga lãhira. = --Qur'an 31:4
    Those are on [right] guidance from their Lord, and it is those who are the successful. <> Waɗannan sunã a kan shiriya ta daga Ubangijinsu kuma waɗannan sũ ne mãsu babban rabo. = --Qur'an 31:5
    And of the people is he who buys the amusement of speech to mislead [others] from the way of Allah without knowledge and who takes it in ridicule. Those will have a humiliating punishment. <> Kuma akwai daga cikin mutãne wanda ke sayen tãtsuniyõyi dõmin ya ɓatar da mutãne daga hanyar Allah, bã da wani ilmi ba, kuma ya riƙe ta abin izgili! Waɗancan sunã da wata azãba mai wulãkantãwa. = --Qur'an 31:6
    And when our verses are recited to him, he turns away arrogantly as if he had not heard them, as if there was in his ears deafness. So give him tidings of a painful punishment. <> Kuma idan an karanta ãyõyinMu a gare shi, sai ya jũya bãya, yanã mai girman kai, kamar dai bai saurãre su ba kamar dai akwai wanĩ danni a kan kunnuwansa! To, ka yi masa bushãra da azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 31:7
    Indeed, those who believe and do righteous deeds - for them are the Gardens of Pleasure. <> Lalle, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljannar ni'ima. = --Qur'an 31:8
    Wherein they abide eternally; [it is] the promise of Allah [which is] truth. And He is the Exalted in Might, the Wise. <> Sunã dawwama a cikinsu Allah Yã yi alkawarin, Ya tabbatar da shi. Kuma shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima. = --Qur'an 31:9
    He created the heavens without pillars that you see and has cast into the earth firmly set mountains, lest it should shift with you, and dispersed therein from every creature. And We sent down rain from the sky and made grow therein [plants] of every noble kind. <> (Allah) Ya halitta sammai, bã da ginshiƙi wanda kuke gani ba, kuma Yã jẽfa duwatsu mãsu kafuwa a cikin ƙasã, dõmin kada ta karkata da ku kuma Ya wãtsa daga kowanc irin dabba a cikinta, kuma Mun saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka tsirar a cikinta, daga kõwane nau'i biyu (nami; i da mace) mai ban sha'awa. = --Qur'an 31:10
    This is the creation of Allah. So show Me what those other than Him have created. Rather, the wrongdoers are in clear error. <> Wannan shĩ ne halittar Allah. To ku nũna mini, "Mẽne ne waɗanan da ba Shi ba suka halitta? Ã'a, azzalumai sunã a cikin ɓata bayyananna." = --Qur'an 31:11
    And We had certainly given Luqman wisdom [and said], "Be grateful to Allah." And whoever is grateful is grateful for [the benefit of] himself. And whoever denies [His favor] - then indeed, Allah is Free of need and Praiseworthy. <> Kuma lalle haƙĩƙa Mun bai wa Luƙmãn hikima. (Muka ce masa) Ka gõde wa Allah, kuma wanda ya gõde, to yanã gõdẽwa ne dõmin kansa kawai kuma wanda ya kãfirta, to, lalle, Allah Mawadãci ne, Gõdadde. = --Qur'an 31:12
    And [mention, O Muhammad], when Luqman said to his son while he was instructing him, "O my son, do not associate [anything] with Allah. Indeed, association [with him] is great injustice." <> Kuma a lõkacin da Luƙmãn ya ce wa ɗansa, alhãli kuwa yanã yi masa wa'azi, "Yã ƙaramin ɗãna! Kada ka yi shirki game da Allah. Lalle shirki wani zãlunci ne mai girma." = --Qur'an 31:13
    And We have enjoined upon man [care] for his parents. His mother carried him, [increasing her] in weakness upon weakness, and his weaning is in two years. Be grateful to Me and to your parents; to Me is the [final] destination. <> Kuma Mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu; uwarsa tã ɗauke shi a cikin rauni a kan wani rauni, kuma yãyensa a cikin shekaru biyu (Muka ce masa) "Ka gõde Mini da kuma mahaifanka biyu. Makõma zuwa gare Ni kawai take." = --Qur'an 31:14
    But if they endeavor to make you associate with Me that of which you have no knowledge, do not obey them but accompany them in [this] world with appropriate kindness and follow the way of those who turn back to Me [in repentance]. Then to Me will be your return, and I will inform you about what you used to do. <> "Kuma idan mahaifanka suka tsananta maka ga ka yi shirki game da Ni, ga abin da bã ka da ilmi gare shi, to, kada ka yi musu ɗã'a. Kuma ka abũce su a cikin dũniya gwargwadon sharĩ'a, kuma ka bi hanyar wanda ya mayar da al'amari zuwa gare Ni, sa'an nan zuwa gare Ni makõmarku take sa'an nan In bã ku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa." = --Qur'an 31:15
    [And Luqman said], "O my son, indeed if wrong should be the weight of a mustard seed and should be within a rock or [anywhere] in the heavens or in the earth, Allah will bring it forth. Indeed, Allah is Subtle and Acquainted. <> "Yã ƙaramin ɗãna! Lalle ita idan gwargwadon ƙwãyar kõmayya ce ta kasance, to, ta kasance a cikin wani falalen dũtse, kõ a cikin sammai, kõ a cikin ƙasã, Allah zai kãwo ta Lalle Allah Mai tausasãwa ne, Masani." = --Qur'an 31:16
    O my son, establish prayer, enjoin what is right, forbid what is wrong, and be patient over what befalls you. Indeed, [all] that is of the matters [requiring] determination. <> "Yã ƙaramin ɗãna! Ka tsai da salla, kuma ka yi umurni da abin da aka sani, kuma ka yi hani daga abin da ba a sani ba, kuma ka yi haƙuri a kan abin da ya sãme ka. Lalle, wancan yanã daga muhimman al'amura." = --Qur'an 31:17
    And do not turn your cheek [in contempt] toward people and do not walk through the earth exultantly. Indeed, Allah does not like everyone self-deluded and boastful. <> "Kada ka karkatar da kundukukinka ga mutãne, kada ka yi tafiya a cikin ƙasã kanã mai nũna fãɗin rai. Lalle, Allah bã Ya son dukan mai tãƙama, mai alfahari." = --Qur'an 31:18
    And be moderate in your pace and lower your voice; indeed, the most disagreeable of sounds is the voice of donkeys." <> "Kuma ka tsakaita a tafiyarka, kuma ka runtse ga sautinka. Lalle mafi mũnin sautuka haƙĩƙa shĩ ne sautin jãkuna. " = --Qur'an 31:19
    Do you not see that Allah has made subject to you whatever is in the heavens and whatever is in the earth and amply bestowed upon you His favors, [both] apparent and unapparent? But of the people is he who disputes about Allah without knowledge or guidance or an enlightening Book [from Him]. <> Ashe, ba ku gani ba, cẽwa Allah Yã hõre muku abin da ke a cikin sammai da abin da ke a cikin ƙasã, kuma Ya zuba ni'imõminsa a kanku, bayyanannu da ɓõyayyu? Kuma akwai daga mutãne wanda ke yin jidãli ga al'amarin Allah, bã da wani ilmi ba, kuma bã da wata shiriya ba, kumã ba da wani littãfi mai haskakãwa ba. = --Qur'an 31:20
    And when it is said to them, "Follow what Allah has revealed," they say, "Rather, we will follow that upon which we found our fathers." Even if Satan was inviting them to the punishment of the Blaze? <> Kuma idan aka ce musu, "Ku bi abin da Allah ya saukar," sai su ce: "Ã'a, munã bin abin da muka sãmi ubanninmu a kansa." shin kõ dã Shaiɗan nã kiran su ne zuwa ga azãbar sa'ir, = --Qur'an 31:21
    And whoever submits his face to Allah while he is a doer of good - then he has grasped the most trustworthy handhold. And to Allah will be the outcome of [all] matters. <> kuma wanda ya mĩka fuskarsa zuwa ga Allah, alhãli kuma yanã mai kyautatãwa, to, lalle ya yi riƙo ga igiya amintacciya. Kuma zuwa ga Allah ãƙibar al'amura take. = --Qur'an 31:22
    And whoever has disbelieved - let not his disbelief grieve you. To Us is their return, and We will inform them of what they did. Indeed, Allah is Knowing of that within the breasts. <> Kuma wanda ya kãfirta, to, kada kãfircinsa ya baƙanta maka rai, zuwa gare Mu makõmarsu take, sa'an nan Mu bã su lãbari game da abin da suka aikata. Lalle Allah, Masani ne ga abin da ke a cikin ƙirãza. = --Qur'an 31:23
    We grant them enjoyment for a little; then We will force them to a massive punishment. <> Munã jĩshe su dãdi kaɗan sa'an nan Mu tĩlasta su ga shiga zuwa azãba kakkaura. = --Qur'an 31:24
    And if you asked them, "Who created the heavens and earth?" they would surely say, "Allah." Say, "[All] praise is [due] to Allah "; but most of them do not know. <> Kuma lalle, idan ka tambaye su, "Wãne ne ya halĩtta sammai da kasa?" Lalle zã su ce: "Allah ne." Ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah" Ã'a, mafi yawansu ba su sani ba. = --Qur'an 31:25
    To Allah belongs whatever is in the heavens and earth. Indeed, Allah is the Free of need, the Praiseworthy. <> Abin da yake a cikin sammai da ƙasa duka na Allah kawai ne. Lalle, Allah Shĩ ne Mawadãci, Gõdadde. = --Qur'an 31:26
    And if whatever trees upon the earth were pens and the sea [was ink], replenished thereafter by seven [more] seas, the words of Allah would not be exhausted. Indeed, Allah is Exalted in Might and Wise. <> Kuma dã dai abin da ke a cikin ƙasa duka, na itãce, ya zama alƙalumma, kuma tẽku tanã yi masa tawada, a bayansa da waɗansu tẽkuna bakwai kalmõmin Allah ba zã su ƙãre ba. Lalle, Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima. = --Qur'an 31:27
    Your creation and your resurrection will not be but as that of a single soul. Indeed, Allah is Hearing and Seeing. <> Halittarku bã ta zama ba, kuma tãyar da ku bai zama ba, fãce kamar rai guda. Lalle, Allah Mai jĩ ne, Mai gani. = --Qur'an 31:28
    Do you not see that Allah causes the night to enter the day and causes the day to enter the night and has subjected the sun and the moon, each running [its course] for a specified term, and that Allah, with whatever you do, is Acquainted? <> Ashe, ba ku ga, lalle, Allah Yanã shigar da dare a cikin rãna ba, kuma Yanã shigar da rãna a cikin dare kuma Yã hõre rãnã da watã kõwane yanã gudãna zuwa a ajali ambatacce kuma lalle Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa? = --Qur'an 31:29
    That is because Allah is the Truth, and that what they call upon other than Him is falsehood, and because Allah is the Most High, the Grand. <> Wannan fa dõmin Allah Shĩ ne Gaskiya, kuma abin da suke kira wanda bã Shi ba, shi ne ƙaryã, kuma lalle, A1lah shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma. = --Qur'an 31:30
    Do you not see that ships sail through the sea by the favor of Allah that He may show you of His signs? Indeed in that are signs for everyone patient and grateful. <> Ashe, ba ka ga lalle jirgin ruwa nã gudãna ba a cikin tẽku da ni'imar Allah dõmin Ya nũna muku daga ãyõyinSa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga dukan mai haƙuri, mai gõdiya. = --Qur'an 31:31
    And when waves come over them like canopies, they supplicate Allah, sincere to Him in religion. But when He delivers them to the land, there are [some] of them who are moderate [in faith]. And none rejects Our signs except everyone treacherous and ungrateful. <> Kuma idan tãguwar ruwa, kamar duwatsu, ta rufe su, sai su kira Allah sunã tsarkakẽwar addini a gare shi. To, a lõkacin da Ya tsĩrar da su zuwa ga tudu, sai daga cikinsu akwai mai taƙaitãwa kuma bãbu mai musun ãyõyinMu fãce dukkan mayaudari mai yawan kãfirci. = --Qur'an 31:32
    O mankind, fear your Lord and fear a Day when no father will avail his son, nor will a son avail his father at all. Indeed, the promise of Allah is truth, so let not the worldly life delude you and be not deceived about Allah by the Deceiver. <> Ya ku mutãne! Ku bauta wa Ubangijinku da taƙawa, kuma ku ji tsõron wani yini, rãnar da wani mahaifi bã ya sãka wa abin haifuwarsa da kõme kuma wani abin haifuwa bã ya sãka wa mahaifinsa da kõme. Lalle wa'adin Allah gaskiya ne. Sabõda haka, kada wata rãyuwa ta kusa ta rũde ku, kuma kada marũɗin nan ya rũɗẽ ku game da Allah. = --Qur'an 31:33
    Indeed, Allah [alone] has knowledge of the Hour and sends down the rain and knows what is in the wombs. And no soul perceives what it will earn tomorrow, and no soul perceives in what land it will die. Indeed, Allah is Knowing and Acquainted. <> Lalle, Allah a wurinsa kawai sanin sa'a yake, kuma Yanã saukar da girgije, kuma Yanã sanin abin da yake a cikin mahaiffannai kuma wani rai bai san abin da yake aikatãwa a gõbe ba, kuma wani rai bai san a wace ƙasã yake mutuwa ba. Lalle Allah Masani ne Mai ƙididdidigẽwa. = --Qur'an 31:34
    Alif, Lam, Meem. <> A. L̃. M̃. = --Qur'an 32:1
    [This is] the revelation of the Book about which there is no doubt from the Lord of the worlds. <> Saukar da Littafin bãbu shakka a gare shi, daga Ubangijin tãlikai yake. = --Qur'an 32:2
    Or do they say, "He invented it"? Rather, it is the truth from your Lord, [O Muhammad], that you may warn a people to whom no warner has come before you [so] perhaps they will be guided. <> Kõ sunã cẽwa (Muhammadu ne) ya ƙirƙira shi? Ã'a, shĩ ne gaskiya daga Ubangijinka, dõmin ka yi gargaɗi ga mutãne waɗanda wani mai gargaɗi bai je musu ba a gabãninka, fãtan zã su shiryu. = --Qur'an 32:3
    It is Allah who created the heavens and the earth and whatever is between them in six days; then He established Himself above the Throne. You have not besides Him any protector or any intercessor; so will you not be reminded? <> Allah ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu a cikin kwãnuka shida, sa'an nan Ya daidaita a kan Al'arshi. Bã ku da, baicin Shi, wani majiɓinci kuma babu wani maceci. Shin, bã zã ku yi tunãni ba? = --Qur'an 32:4
    He arranges [each] matter from the heaven to the earth; then it will ascend to Him in a Day, the extent of which is a thousand years of those which you count. <> Yanã shirya al'amari daga sama zuwa ga ƙasã, sa'an nan ya tãka zuwa gare Shi a cikin yini, wanda gwargwadonsa shẽkaru dubu ne ga abin da kuke lissafãwa. = --Qur'an 32:5
    That is the Knower of the unseen and the witnessed, the Exalted in Might, the Merciful, <> Wannan shĩ ne Masanin fake da bayyane, Mabuwãyi, Mai jinƙai. = --Qur'an 32:6
    Who perfected everything which He created and began the creation of man from clay. <> Wanda Ya kyautata kõme, Wanda Ya halitta shi. Shi ne kuma Ya fãra halittar mutum daga lãka. = --Qur'an 32:7
    Then He made his posterity out of the extract of a liquid disdained. <> Sa'an nan Ya sanya ɗiyansa daga wani asali na wani ruwa wulãkantacce. = --Qur'an 32:8
    Then He proportioned him and breathed into him from His [created] soul and made for you hearing and vision and hearts; little are you grateful. <> Sa'an nan Ya daidaita shi, kuma Ya hũra a cikinsa, daga ruhinSa kuma Ya sanya muku ji, da ganunuwa da zukãta. Gõdiyarku kaɗan ce ƙwarai. = --Qur'an 32:9
    And they say, "When we are lost within the earth, will we indeed be [recreated] in a new creation?" Rather, they are, in [the matter of] the meeting with their Lord, disbelievers. <> Kuma suka ce: "Shin, idan mun ɓace a cikin ƙasã, shin, lalle mu, tabbas ne munã zama a cikin wata halitta sãbuwa?" Ã'a, su game da gamuwa da Ubangijinsu kãfirai = --Qur'an 32:10
    Say, "The angel of death will take you who has been entrusted with you. Then to your Lord you will be returned." <> Ka ce: "Mala, ikin mutuwa ne. wanda aka wakkala a gare ku, shĩ ne ke karɓar rãyukanku. Sa'an nan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku." = --Qur'an 32:11
    If you could but see when the criminals are hanging their heads before their Lord, [saying], "Our Lord, we have seen and heard, so return us [to the world]; we will work righteousness. Indeed, we are [now] certain." <> Kuma da kã gani a lõkacin da mãsu laifi suke mãsu sunkuyar da kawunansu a wurin Ubangijinsu, "Ya Ubangijinmu! Mun gani, kuma mun ji, to, Ka mayar da mu mu aikata aiki na ƙwarai. Lalle mũ mãsu yaƙĩni ne." = --Qur'an 32:12
    And if We had willed, We could have given every soul its guidance, but the word from Me will come into effect [that] "I will surely fill Hell with jinn and people all together. <> Kuma dã Mun so dã Mun bai wa kõwane rai shiriyarsa to, amma magana ta tabbata daga gare Ni! Lalle ne Inã cika Jahannama daga aljannu da mutãne gabã ɗaya. = --Qur'an 32:13
    So taste [punishment] because you forgot the meeting of this, your Day; indeed, We have [accordingly] forgotten you. And taste the punishment of eternity for what you used to do." <> To, ku ɗanɗana sabõda abin da kuka manta na haɗuwa da ranarku wannan. Lalle Mũ mã Mun manta da ku, kuma ku dãnɗani azãbar dawwama sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa. = --Qur'an 32:14
    Only those believe in Our verses who, when they are reminded by them, fall down in prostration and exalt [Allah] with praise of their Lord, and they are not arrogant. <> Waɗanda ke ĩmãni da ãyõyinMu kawai, sũ ne waɗanda idan aka karanta musu ãyõyinMu sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma su yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu, alhãli kuwa su bã su yin girman kai. = --Qur'an 32:15
    They arise from [their] beds; they supplicate their Lord in fear and aspiration, and from what We have provided them, they spend. <> Sãsanninsu nã nĩsanta daga wurãren kwanciya, sunã kiran Ubangijinsu bisa ga tsõro da ɗammãni, kuma sunã ciryawa daga abin da Muka azurta su. = --Qur'an 32:16
    And no soul knows what has been hidden for them of comfort for eyes as reward for what they used to do. <> Sabõda haka wani rai bai san abin da aka ɓõye musu ba, na sanyin idãnu, dõmin sakamako ga abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 32:17
    Then is one who was a believer like one who was defiantly disobedient? They are not equal. <> Shin, wanda ya zama mũmini yanã kamar wanda ya zama fãsiƙi? Bã zã su yi daidai ba. = --Qur'an 32:18
    As for those who believed and did righteous deeds, for them will be the Gardens of Refuge as accommodation for what they used to do. <> Amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwafai, to, sunã da gidãjen Aljannar makõma, a kan liyãfa sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 32:19
    But as for those who defiantly disobeyed, their refuge is the Fire. Every time they wish to emerge from it, they will be returned to it while it is said to them, "Taste the punishment of the Fire which you used to deny." <> Kuma waɗanda suka yi fãsiƙanci to makõmarsu ita ce wuta, kõ da yaushe suka yi nufin su fita daga gare ta, sai a mayar da su a cikinta, kuma a ce musu: "Ku ɗanɗana azãbai wutã, wadda kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita." = --Qur'an 32:20
    And we will surely let them taste the nearer punishment short of the greater punishment that perhaps they will repent. <> Kuma lalle Munã ɗanɗana musu daga azãba, mafi ƙasƙanci, kãfin a kai ga azãba mafi girma, dõmin fãtan za su kõmo. = --Qur'an 32:21
    And who is more unjust than one who is reminded of the verses of his Lord; then he turns away from them? Indeed We, from the criminals, will take retribution. <> Kuma wãne ne ya fi zãlunci bisa ga wanda aka tunãtar da ãyõyin Ubangijinsa, sa'an na ya bijire daga barinsu? Lalle Mũ, Mãsu yin azãbar rãmuwa ne ga mãsu laifi. = --Qur'an 32:22
    And We certainly gave Moses the Scripture, so do not be in doubt over his meeting. And we made the Torah guidance for the Children of Israel. <> Kuma lalle haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã Littafi, sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga haɗuwa da shi. Kuma Mun sanya shi ya zama shiriya ga Banĩ Isrã'ĩla. = --Qur'an 32:23
    And We made from among them leaders guiding by Our command when they were patient and [when] they were certain of Our signs. <> Kuma Mun sanya shugabanni daga cikinsu, sunã shiryarwa da umurninMu, a lõkacin da suka yi haƙuri, kuma sun kasance sunã yin yaƙĩni da ãyõyinMu. = --Qur'an 32:24
    Indeed, your Lord will judge between them on the Day of Resurrection concerning that over which they used to differ. <> Lalle Ubangijinka shĩ ne zai rarrabe a tsakãninsu a Rãnar ¡iyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna a cikinsa. = --Qur'an 32:25
    Has it not become clear to them how many generations We destroyed before them, [as] they walk among their dwellings? Indeed in that are signs; then do they not hear? <> Shin, ba ya shiryar da su cẽwa da yawa Muka halakara gabãninsu, daga al'ummõmi sunã tafiya a cikin masaukansu? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi. Shin, ba su jĩ ne? = --Qur'an 32:26
    Have they not seen that We drive the water [in clouds] to barren land and bring forth thereby crops from which their livestock eat and [they] themselves? Then do they not see? <> Shin, kuma ba su gani ba cẽwa lalle Mũ, Munã kõra ruwa zuwa ga ƙasã ƙeƙasasshiya, sa'an nan Mu fitar, game da shi, wata shũka wadda dabbõbinsu, da su kansu ke ci daga gare ta? Ashe fa ba su gani ba? = --Qur'an 32:27
    And they say, "When will be this conquest, if you should be truthful?" <> Kuma sunã cẽwa, "Yaushe wannan hukunci yake, aukuwa idan kun kasance mãsu gaskiya?" = --Qur'an 32:28
    Say, [O Muhammad], "On the Day of Conquest the belief of those who had disbelieved will not benefit them, nor will they be reprieved." <> Ka ce: "Ranar hukuncin nan, ĩmãnin waɗanda suka kãfirta bã zai amfãne su ba (a cikinta) kuma bã zã a yi musu jinkiri ba." = --Qur'an 32:29
    So turn away from them and wait. Indeed, they are waiting. <> Sabõda haka ka kau da kai daga barinsu, kuma, ka yi jira lalle, sũ ma mãsu jira ne. = --Qur'an 32:30
    O Prophet, fear Allah and do not obey the disbelievers and the hypocrites. Indeed, Allah is ever Knowing and Wise. <> Yã kai Annabi! Ka bi Allah da taƙawa, kuma kada ka yi ɗã'ã ga kãfirai da munãfukai. Lalle, Allah Ya kasance Mai ilmi, Mai hikima. = --Qur'an 33:1
    And follow that which is revealed to you from your Lord. Indeed Allah is ever, with what you do, Acquainted. <> Kuma ka bi abin da aka yi wahayi da shi zuwa gare ka daga Ubangijinka. Lalle, Allah Ya kasance Mai labartawa ga abin da kuke aikatawa. = --Qur'an 33:2
    And rely upon Allah; and sufficient is Allah as Disposer of affairs. <> Ka dõgara ga Allah. Kuma Allah Ya isa Ya zama wakĩli. = --Qur'an 33:3
    Allah has not made for a man two hearts in his interior. And He has not made your wives whom you declare unlawful your mothers. And he has not made your adopted sons your [true] sons. That is [merely] your saying by your mouths, but Allah says the truth, and He guides to the [right] way. <> Allah bai sanya zũciya biyu ba ga wani namiji a cikinsa, kuma bai sanya mãtanku waɗanda kuke yin zihãri daga gare su, su zama uwãyenku ba, kuma bai sanya ɗiyan hankãkarku su zama ɗiyanku ba. wannan abu nãku, maganarku ce da bãkunanku alhãli kuwa Allah na faɗar gaskiya, kuma Shĩ ne ke shiryarwa ga hanyar ƙwarai. = --Qur'an 33:4
    Call them by [the names of] their fathers; it is more just in the sight of Allah. But if you do not know their fathers - then they are [still] your brothers in religion and those entrusted to you. And there is no blame upon you for that in which you have erred but [only for] what your hearts intended. And ever is Allah Forgiving and Merciful. <> Ku kira su ga ubanninsu, shi ne mafi ãdalci a wurin Allah. To, idan ba ku san ubanninsu ba, to, 'yan'uwanku ga addini da dĩmajojinku. Kuma bãbu laifi a gare ku ga abin da kuka yi kuskure da shi, kuma amma (akwai laifi) ga abin da zukãtanku suka ganganta, kuma Allah Ya kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai. = --Qur'an 33:5
    The Prophet is more worthy of the believers than themselves, and his wives are [in the position of] their mothers. And those of [blood] relationship are more entitled [to inheritance] in the decree of Allah than the [other] believers and the emigrants, except that you may do to your close associates a kindness [through bequest]. That was in the Book inscribed. <> Annabi ne mafi cancanta ga mũminai bisa ga su kansu, kuma mãtansa uwãyensu ne. Kuma ma'abuta zumunta waɗansunsu sun fi waɗansu a cikin Littãfin Allah bisa ga mũminai da Muhãjirai, fãce fa idan kun aikata wani alhẽri zuwa ga majiɓintanku. Wancan yã kasance a cikin Littafi, rubũtacce. = --Qur'an 33:6
    And [mention, O Muhammad], when We took from the prophets their covenant and from you and from Noah and Abraham and Moses and Jesus, the son of Mary; and We took from them a solemn covenant. <> Kuma a lõkacin da Muka riƙi alkawarin Annabawa daga gare su, kuma daga gare ka, kuma daga Nũhu da Ibrãhĩm da Mũsa da kuma Ĩsã ɗan Maryama, kuma Muka riƙi wani alkawari mai kauri daga gare su. = --Qur'an 33:7
    That He may question the truthful about their truth. And He has prepared for the disbelievers a painful punishment. <> Dõmin Ya tambayi mãsu gaskiya a kan gaskiyarsu, kuma Yã yi tattalin wata azãba mai raɗaɗi ga kãfirai. = --Qur'an 33:8
    O you who have believed, remember the favor of Allah upon you when armies came to [attack] you and We sent upon them a wind and armies [of angels] you did not see. And ever is Allah, of what you do, Seeing. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da waɗansu rundunõni suka zo muku, sai Muka aika wata iskã a kansu da waɗansu rundunõni waɗanda ba ku gani ba, Kuma Allah Yã kasance Mai gani ga abin da kuke aikatãwa. = --Qur'an 33:9
    [Remember] when they came at you from above you and from below you, and when eyes shifted [in fear], and hearts reached the throats and you assumed about Allah [various] assumptions. <> A lõkacin da suka zo muku daga samanku da kuma ƙasa daga gare ku, kuma a lõkacin da gannai suka karkata kuma zukãta suka kai ga maƙõsai, kuma kuka yi zaton zace-zace, game da Allah. = --Qur'an 33:10
    There the believers were tested and shaken with a severe shaking. <> A can aka jarrabi mũminai, kuma aka yi girgiza da su, girgiza mai tsanani. = --Qur'an 33:11
    And [remember] when the hypocrites and those in whose hearts is disease said, "Allah and His Messenger did not promise us except delusion," <> Kuma a lõkacin da munafukai da waɗanda akwai cũta a cikin zukãtansu ke cẽwa, Allah da ManzonSa, "Ba su yi mana wa'adin kõme ba, fãce rũɗi." = --Qur'an 33:12
    And when a faction of them said, "O people of Yathrib, there is no stability for you [here], so return [home]." And a party of them asked permission of the Prophet, saying, "Indeed, our houses are unprotected," while they were not exposed. They did not intend except to flee. <> Kuma a lõkacin da wata ƙungiya daga gare su, ta ce, "Ya mutãnen Yasriba! Bã ku da wani matsayi, sabõda haka ku kõma." Kuma wata ƙungiya daga gare su na nẽman izni ga Annabi sunãcẽwa, "Lalle gidãjenmu kuranye suke," alhãli kuwa bã kuranye suke ba, bã su da nufin kome fãce gudu. = --Qur'an 33:13
    And if they had been entered upon from all its [surrounding] regions and fitnah had been demanded of them, they would have done it and not hesitated over it except briefly. <> Kuma dã an shige ta (Madĩna) a kansu, daga sasanninta, sa'an nan aka tambaye su fitina (kãfirci), lalle dã sun jẽ mata, kuma dã ba su zauna a cikinta (Madĩna) ba fãce kaɗan. = --Qur'an 33:14
    And they had already promised Allah before not to turn their backs and flee. And ever is the promise to Allah [that about which one will be] questioned. <> Kuma lalle haƙĩƙa, sun kasance sunã yi wa Allah alkawari, a gabãnin wannan; Bã zã su jũya dõmin gudu ba, kuma alkawarin Allah ya kasance abin tambaya. = --Qur'an 33:15
    Say, [O Muhammad], "Never will fleeing benefit you if you should flee from death or killing; and then [if you did], you would not be given enjoyment [of life] except for a little." <> Ka ce: "Gudun nan bã zai amfãne ku ba daga mutuwa ko kisa. Kuma har in kun gudu, bã zã a jĩshe ku dãɗĩ ba fãce kaɗan." = --Qur'an 33:16
    Say, "Who is it that can protect you from Allah if He intends for you an ill or intends for you a mercy?" And they will not find for themselves besides Allah any protector or any helper. <> Ka ce: "Wãne ne wanda yake tsare ku daga Allah, idan Yã yi nufin wata cũta game da ku?" Kuma bã zã su sãmar wa kansu wani majiɓinci ba, banda Allah, kuma bã zã su sãmar wa kansu wani mataimaki ba. = --Qur'an 33:17
    Already Allah knows the hinderers among you and those [hypocrites] who say to their brothers, "Come to us," and do not go to battle, except for a few, <> Lalle Allah Ya san mãsu hana mutãne fita daga cikinku, da mãsu cẽwa ga 'yan'uwansu,"Ku zo nan a wurinmu." Kuma bã zã su shiga yãƙi ba fãce kaɗan. = --Qur'an 33:18
    Indisposed toward you. And when fear comes, you see them looking at you, their eyes revolving like one being overcome by death. But when fear departs, they lash you with sharp tongues, indisposed toward [any] good. Those have not believed, so Allah has rendered their deeds worthless, and ever is that, for Allah, easy. <> Suna mãsu rõwa gare ku, sa'an nan idan tsõro ya zo, sai ka gan su sunã kallo zuwa gare ka, idãnunsu sunã kẽwaya, kamar wanda ake rufe hankalinsa sabõda mutuwa. Sa'an nan idan tsõron ya tafi, sai su yi muku miyãgun maganganu da harussa mãsu kaifi, sunã mãsu rõwa a kan dũkiya. Waɗannan, ba su yi ĩmani ba, sabõda hakaAllah Ya ɓãta ayyukansu. Kuma wannan ya kasance mai sauƙi ga Allah. = --Qur'an 33:19
    They think the companies have not [yet] withdrawn. And if the companies should come [again], they would wish they were in the desert among the bedouins, inquiring [from afar] about your news. And if they should be among you, they would not fight except for a little. <> Sunã zaton ƙungiyõyin kãfirai ba su tafi ba. Kuma idan ƙungiyõyin kãfirai sun zo, sunã gũrin da dai sun zama a karkara a cikin ƙauyãwa, sunã tambayar lãbãranku. Kuma kõ dã sun kasance a cikinku, bã zã su yi yãƙi ba, fãce kaɗan. = --Qur'an 33:20
    There has certainly been for you in the Messenger of Allah an excellent pattern for anyone whose hope is in Allah and the Last Day and [who] remembers Allah often. <> Lalle, abin kõyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah, ga wanda ya kasanee yanã fãtan rahamar Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya ambaci Allah da yawa. = --Qur'an 33:21
    And when the believers saw the companies, they said, "This is what Allah and His Messenger had promised us, and Allah and His Messenger spoke the truth." And it increased them only in faith and acceptance. <> Kuma a lõkacin da mũminai suka ga ƙungiyõyin kãfirai, sai suka ce, "Wannan ne abin da Allah da ManzonSa suka yi mana wa'adi, Allah da ManzonSa sunyi gaskiya." Kuma wannan bai ƙãra musu kõme ba fãce ĩmãni da sallamãwa. = --Qur'an 33:22
    Among the believers are men true to what they promised Allah. Among them is he who has fulfilled his vow [to the death], and among them is he who awaits [his chance]. And they did not alter [the terms of their commitment] by any alteration - <> Daga mũminai akwai waɗansu mazãje da suka gaskata abin da suka yi wa Allah alkwari a kansa, sa'an nan a cikinsu, akwai wanda ya biya bukãtarsa, kuma daga cikinsu akwai wanda ke jira. Kuma ba su musanya ba, musanyawa. = --Qur'an 33:23
    That Allah may reward the truthful for their truth and punish the hypocrites if He wills or accept their repentance. Indeed, Allah is ever Forgiving and Merciful. <> Dõmin Allah Ya sãka wa masu gaskiya da gakiyarsu, kuma Ya azabtar da munafukai idan Ya so, ko Ya karɓi tũba a kansu. Lalle, Allah Ya kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai. = --Qur'an 33:24
    And Allah repelled those who disbelieved, in their rage, not having obtained any good. And sufficient was Allah for the believers in battle, and ever is Allah Powerful and Exalted in Might. <> Kuma Allah Yã mayar da waɗanda suka kãfirta da fushinsu, ba su sãmi wani alhẽri ba. Allah Ya isar wa mũminai daga barin yãƙi. Kuma Allah Ya kasance Mai ƙarfi, Mabuwãyi. = --Qur'an 33:25
    And He brought down those who supported them among the People of the Scripture from their fortresses and cast terror into their hearts [so that] a party you killed, and you took captive a party. <> Kuma Ya saukar da waɗannan da suka taimake su daga mazõwa Littãfi, daga birãnensu, kuma Ya jẽfa tsõro a cikin zukatansu; wata ƙungiya kunã kashẽwa, kuma kunã kãma wata ƙungiyar. = --Qur'an 33:26
    And He caused you to inherit their land and their homes and their properties and a land which you have not trodden. And ever is Allah, over all things, competent. <> Kuma Ya gãdar da ku gõnakinsu da gidãjensu da dũkiyõyinsu, da wata ƙasa wadda ba ku taɓa tãkarta bã. Kuma Allah ya kasance Mai ĩkon yi ne a kan kõme. = --Qur'an 33:27
    O Prophet, say to your wives, "If you should desire the worldly life and its adornment, then come, I will provide for you and give you a gracious release. <> Yã kai Annabi! Ka ce wa matanka, "Idan kun kasance kunã nufin rãyuwar dũniya da ƙawarta, to, ku zo in yi muku kyautar ban kwãna kuma in sake ku, saki mai kyau." = --Qur'an 33:28
    But if you should desire Allah and His Messenger and the home of the Hereafter - then indeed, Allah has prepared for the doers of good among you a great reward." <> "Kuma idan kun kasance kunã nufin Allah da Manzonsa da gidan Lãhria, to, lalle, Allah Yã yi tattalin wani sakamako mai girma ga mãsu kyautatãwa daga gare ku." = --Qur'an 33:29
    O wives of the Prophet, whoever of you should commit a clear immorality - for her the punishment would be doubled two fold, and ever is that, for Allah, easy. <> Yã mãtan Annabi! Wadda ta zo da alfãsha bayyananna daga cikinku zã a ninka mata azãba ninki biyu. Kuma wancan yã kasance mai sauƙi ga Allah. = --Qur'an 33:30
    And whoever of you devoutly obeys Allah and His Messenger and does righteousness - We will give her her reward twice; and We have prepared for her a noble provision. <> Kuma wadda ta yi tawãli'u daga cikinku ga Allah da ManzonSa, kuma ta aikata aiki na ƙwarai, zã Mu bã ta sakamakonta ninki biyu, kuma Mun yi mata tattalin arziki ma karimci. = --Qur'an 33:31
    O wives of the Prophet, you are not like anyone among women. If you fear Allah, then do not be soft in speech [to men], lest he in whose heart is disease should covet, but speak with appropriate speech. <> Yã mãtan Annabĩ! Ba ku zama kamar kõwa ba daga mãtã, idan kun yi taƙawa, sabõda haka, kada ku sassautar da magana, har wanda ke da cũta a cikin zuciyarsa ya yi ɗammani, kuma ku faɗi magana ta alheri. = --Qur'an 33:32
    And abide in your houses and do not display yourselves as [was] the display of the former times of ignorance. And establish prayer and give zakah and obey Allah and His Messenger. Allah intends only to remove from you the impurity [of sin], O people of the [Prophet's] household, and to purify you with [extensive] purification. <> Kuma ku tabbata a cikin gidãjenku, kuma kada ku yi fitar gãye-gãye irin fitar gãye-gãye ta jãhiliyyar farko. Kuma ku tsaĩ da salla, kuma ku bãyar da zakka, ku yi ɗã, ã ga Allah da ManzonSa. Allah na nufin Ya tafiyar da ƙazamta kawai daga gare ku, yã mutãnen Babban Gida! Kuma Ya tsarkake ku, tsarkakẽwa. = --Qur'an 33:33
    And remember what is recited in your houses of the verses of Allah and wisdom. Indeed, Allah is ever Subtle and Acquainted [with all things]. <> Kuma ku tuna abin da ake karantawa a cikin ɗãkunanku daga ãyõyin Allah da hukunci. Lalle Allah Yã kasance Mai tausasãwa Mai labartawa. = --Qur'an 33:34
    Indeed, the Muslim men and Muslim women, the believing men and believing women, the obedient men and obedient women, the truthful men and truthful women, the patient men and patient women, the humble men and humble women, the charitable men and charitable women, the fasting men and fasting women, the men who guard their private parts and the women who do so, and the men who remember Allah often and the women who do so - for them Allah has prepared forgiveness and a great reward. <> Lalle, Musulmi maza da Musulmi mãtã da muminai maza da muminai mãtã, da mãsu tawãli'u maza da mãsu tawãlĩu mãtãda mãsu gaskiya maza da mãsu gaskiya mãtã, da mãsu haƙuri maza da mãsu haƙuri mãtã, da mãsu tsõron Allah maza da mãsu tsõron Allah mãtã, da mãsu sadaka maza da mãsu sadaka mãtã, da mãsu azumi maza da mãsu azumi mãtã da mãsu tsare farjõjinsu maza da mãsu tsare farjõjinsu mãtã, da mãsu ambaton Allah da yawa maza da mãsu ambatonsa mãtã, Allah Ya yi musu tattalin wata gãfara da wani sakamako mai girma. = --Qur'an 33:35
    It is not for a believing man or a believing woman, when Allah and His Messenger have decided a matter, that they should [thereafter] have any choice about their affair. And whoever disobeys Allah and His Messenger has certainly strayed into clear error. <> Kuma ba ya halatta ga mũmini kuma haka ga mũmina, a lõkacin da Allah da Manzonsa Ya hukunta wani umurni, wani zãɓi daga al'amarinsu ya kasance a gare su. Kuma wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa, to, yã ɓace, ɓacẽwa bayyananna. = --Qur'an 33:36
    And [remember, O Muhammad], when you said to the one on whom Allah bestowed favor and you bestowed favor, "Keep your wife and fear Allah," while you concealed within yourself that which Allah is to disclose. And you feared the people, while Allah has more right that you fear Him. So when Zayd had no longer any need for her, We married her to you in order that there not be upon the believers any discomfort concerning the wives of their adopted sons when they no longer have need of them. And ever is the command of Allah accomplished. <> Kuma a lõkacin da kake cẽwa ga wanda Allah Ya yi ni'ima a gare shi kai kuma ka yi ni'ima a gare shi, "Ka riƙe mãtarka, kuma ka bi Allah da taƙawa," kuma kana ɓõyẽwa a cikin ranka abin da Allah zai bayyana shi, kanã tsõron mutãne, alhãli kuwa Allah ne Mafi cancantar ka ji tsõronSa. to a lõkacin da zaidu ya ƙãre bukãtarsa daga gare ta, Mun aurar da kai ita, dõmin kada wani ƙunci ya kasance a kan mũminai a cikin (auren mãtan) ɗiyan hankãkarsu, idan sun ƙãre bukãta daga gare su. Kuma umurnin Allah yã kasance abin aikatãwa. = --Qur'an 33:37
    There is not to be upon the Prophet any discomfort concerning that which Allah has imposed upon him. [This is] the established way of Allah with those [prophets] who have passed on before. And ever is the command of Allah a destiny decreed. <> Wani ƙunci bai kasance a kan Annabi ba ga abin da Allah Ya faralta a kansa, a kan ƙã'idar, Allah a cikin (Annabãwa) waɗanda suka shige daga gabãninsa. Kuma umurnin Allah yã kasance abin ƙaddarãwa tabbatacce. = --Qur'an 33:38
    [Allah praises] those who convey the messages of Allah and fear Him and do not fear anyone but Allah. And sufficient is Allah as Accountant. <> Waɗanda ke iyar da Manzancin Allah, kuma sunã tsõronSa, kuma bã su tsõron kõwa fãce Allah, Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai hisabi. = --Qur'an 33:39
    Muhammad is not the father of [any] one of your men, but [he is] the Messenger of Allah and last of the prophets. And ever is Allah, of all things, Knowing. <> Muhammadu bai kasance uban kõwa ba daga mazanku, kuma amma shĩ yã kasance Manzon Allah kuma cikon Annabãwa. Kuma Allah Ya kasance Masani ga kõme. = --Qur'an 33:40
    O you who have believed, remember Allah with much remembrance <> Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ambaci Allah, ambata mai yawa. = --Qur'an 33:41
    And exalt Him morning and afternoon. <> Kuma ku tsarkake shi, a sãfiya da maraice. = --Qur'an 33:42
    It is He who confers blessing upon you, and His angels [ask Him to do so] that He may bring you out from darknesses into the light. And ever is He, to the believers, Merciful. <> (Allah) Shĩ ne Wanda ke tsarkake ku, da mala'ikunSa (sunã yi muku addu'a), dõmin Ya fitar da ku daga duffai zuwa ga haske. Kuma (Allah) Yã kasance Mai Jĩn ƙai ga mũminai. = --Qur'an 33:43
    Their greeting the Day they meet Him will be, "Peace." And He has prepared for them a noble reward. <> Gaisuwarsu a rãnar da suke haɗuwa da shi "Salãm", kuma Yã yi musu tattalin wani sakamako na karimci. = --Qur'an 33:44
    O Prophet, indeed We have sent you as a witness and a bringer of good tidings and a warner. <> Yã kai Annabi! Lalle Mũ Mun aike ka kanã mai shaida, kuma mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. = --Qur'an 33:45
    And one who invites to Allah, by His permission, and an illuminating lamp. <> Kuma mai kira zuwa ga Allah da izninSa, kuma fitila mai haskakãwa. = --Qur'an 33:46
    And give good tidings to the believers that they will have from Allah great bounty. <> Kuma ka yi bushãra ga mũminai cẽwa, sũnã da falalamai girma daga Allah. = --Qur'an 33:47
    And do not obey the disbelievers and the hypocrites but do not harm them, and rely upon Allah. And sufficient is Allah as Disposer of affairs. <> Kuma kada ka yi ɗã'a ga kãfirai da munãfukai, kuma ka ƙyã1e cũtarsu (gare ka), kuma ka dõgara ga Allah. Allah Yã isa zama wakĩli. = --Qur'an 33:48
    O You who have believed, when you marry believing women and then divorce them before you have touched them, then there is not for you any waiting period to count concerning them. So provide for them and give them a gracious release. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! idan kun auri mũminai mãtã, sa'an nan kuka sake su a gabãnin ku shãfe su, to, bã ku da wata idda da zã ku lissafa a kansu, kuma ku yi musu kyautar jin dãɗi kuma ku sake su saki mai kyau. = --Qur'an 33:49
    O Prophet, indeed We have made lawful to you your wives to whom you have given their due compensation and those your right hand possesses from what Allah has returned to you [of captives] and the daughters of your paternal uncles and the daughters of your paternal aunts and the daughters of your maternal uncles and the daughters of your maternal aunts who emigrated with you and a believing woman if she gives herself to the Prophet [and] if the Prophet wishes to marry her, [this is] only for you, excluding the [other] believers. We certainly know what We have made obligatory upon them concerning their wives and those their right hands possess, [but this is for you] in order that there will be upon you no discomfort. And ever is Allah Forgiving and Merciful. <> Yã kai Annabi! Lalle Mũ, Mun halatta maka mãtanka waɗanda ka bai wa sadãkõkinsu da abin da hannun dãmanka ya mallaka daga abin da Allah Ya bã ka na ganĩma, da 'yã'yan baffanka, da 'ya'yan goggonninka da 'yã'yan kãwunka da 'yã'yan innõninka waɗanda suka yi hijira tãre da kai, da wata mace mũmina idan ta bãyar da kanta ga Annabi, idan shi Annabi yanã nufin ya aure ta (hãlin wannan hukunci) kẽɓe yake gare ka, banda gamũminai. Lalle Mun san abin da Muka faralta a kansu (smũminai) game da mãtansuda abin da hannayensu suka mallaka. Do min kada wani ƙunci ya kasance a kanka, kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai. = --Qur'an 33:50
    You, [O Muhammad], may put aside whom you will of them or take to yourself whom you will. And any that you desire of those [wives] from whom you had [temporarily] separated - there is no blame upon you [in returning her]. That is more suitable that they should be content and not grieve and that they should be satisfied with what you have given them - all of them. And Allah knows what is in your hearts. And ever is Allah Knowing and Forbearing. <> Kanã iya jinkirtar da wadda ka ga dãmã daga gare su, kuma kanã tãro wadda kake so zuwa gare ka. Kuma wadda ka nẽma daga waɗanda ka nĩsantar, to, bãbu laifi agare ka. Wannan yã fi kusantar da sanyaya idãnunsu, kuma bã zã su yi baƙin ciki ba, kuma su yarda da abin da ka bã su, sũ duka. Kuma Allah Yanã sane da abin da yake a cikin zukãtanku. Kuma Allah Ya kasance Masani, Mai haƙuri. = --Qur'an 33:51
    Not lawful to you, [O Muhammad], are [any additional] women after [this], nor [is it] for you to exchange them for [other] wives, even if their beauty were to please you, except what your right hand possesses. And ever is Allah, over all things, an Observer. <> Waɗansu mãtã bã su halatta a gare ka a bãyan haka, kuma ba zã ka musanya su da mãtan aure ba, kuma kõ kyaunsu yã bã ka sha'awa, fãce dai abin da hannun dãmanka ya mallaka. Kuma Allah Yã kasance Mai tsaro ga dukan kõme. = --Qur'an 33:52
    O you who have believed, do not enter the houses of the Prophet except when you are permitted for a meal, without awaiting its readiness. But when you are invited, then enter; and when you have eaten, disperse without seeking to remain for conversation. Indeed, that [behavior] was troubling the Prophet, and he is shy of [dismissing] you. But Allah is not shy of the truth. And when you ask [his wives] for something, ask them from behind a partition. That is purer for your hearts and their hearts. And it is not [conceivable or lawful] for you to harm the Messenger of Allah or to marry his wives after him, ever. Indeed, that would be in the sight of Allah an enormity. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada kũ shiga gidãjen Annabi, fãce fa idan an yi izni a gare ku zuwa ga wani abinci, bã da kun tsaya jiran nunarsa ba, kuma amma idan an kira ku, to, ku shiga, sa'an nan idan kun ci, to ku wãtse, kuma bã da kun tsaya kunã masu hĩra da wani Iãbãri ba. Lalle wannan yanã cũtar da Annabi, to, yanã jin kunyarku, alhãli kuwa Allah bã Ya jin kunya daga gaskiya. Kuma idan zã ku tambaye su waɗansu kãyã, to, ku tambaye su daga bãyan shãmaki. Wannan ya fi muku tsarki ga zukãtanku da zukãtansu. Kuma bã ya halatta a gare ku, ku cũci Manzon Allah, kuma bã ya halatta ku auri mãtansa a bãyansa har abada. lalle wannan a gare ku yã kasance babban abu a wurin Allah. = --Qur'an 33:53
    Whether you reveal a thing or conceal it, indeed Allah is ever, of all things, Knowing. <> Idan kun bayyana wani abu, kõ kuma kuka ɓõye shi, to, lalle Allah Ya kasance Masani ga kõme. = --Qur'an 33:54
    There is no blame upon women concerning their fathers or their sons or their brothers or their brothers' sons or their sisters' sons or their women or those their right hands possess. And fear Allah. Indeed Allah is ever, over all things, Witness. <> Bãbu laifi a kansu game da ubanninsu, kuma bãbu game da ɗiyansu, kuma bãbu game da 'yan'uwansu maza, kuma bãbu game da ɗiyan 'yan'uwansu maza, kuma bãbu game da ɗiyan 'yan'uwansu mãtã, kuma bãbu game da mãtan mũminai, kuma bãbu game da abin da hannãyensu suka mallaka, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Yã kasance Mahalarci a kan kõme. = --Qur'an 33:55
    Indeed, Allah confers blessing upon the Prophet, and His angels [ask Him to do so]. O you who have believed, ask [Allah to confer] blessing upon him and ask [Allah to grant him] peace. <> Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi. = --Qur'an 33:56
    Indeed, those who abuse Allah and His Messenger - Allah has cursed them in this world and the Hereafter and prepared for them a humiliating punishment. <> Lalle waɗanda ke cũtar Allah da MauzonSa Allah Yã la'ane su, a cikin dũniya da Lãhira, kuma Yã yi musu tattalin azãba mai wulãkantarwa. = --Qur'an 33:57
    And those who harm believing men and believing women for [something] other than what they have earned have certainly born upon themselves a slander and manifest sin. <> Kuma waɗanda suke cũtar mũminai maza dã muminai mãtã, bã da wani abu da suka aikata ba to, lalle sun ɗauki ƙiren ƙarya da zunubi bayyananne. = --Qur'an 33:58
    O Prophet, tell your wives and your daughters and the women of the believers to bring down over themselves [part] of their outer garments. That is more suitable that they will be known and not be abused. And ever is Allah Forgiving and Merciful. <> Yã kai Annabi! Ka ce wa mãtan aurenka da 'yã'yanka da mãtan mũminai su kusantar da ƙasã daga manyan tufãfin da ke a kansu. Wancan ya fi sauƙi ga a gane su dõmin kada a cũce su. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai Jin ƙai. = --Qur'an 33:59
    If the hypocrites and those in whose hearts is disease and those who spread rumors in al-Madinah do not cease, We will surely incite you against them; then they will not remain your neighbors therein except for a little. <> Lalle, idan munãfukai da waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukãtansu, da mãsu tsẽgumi a cikin Madĩna, ba su hanu ba (daga hãlãyensu), lalle, zã Mu shũshũta ka a gare su, sa'an nan bã zã su yi maƙwabtaka da kai ba, a cikinta, fãce kaɗan. = --Qur'an 33:60
    Accursed wherever they are found, [being] seized and massacred completely. <> Sunã la'anannu, inda duka aka sãme su a kãmã su, kuma a karkashe su karkashẽwa. = --Qur'an 33:61
    [This is] the established way of Allah with those who passed on before; and you will not find in the way of Allah any change. <> A kan hanyar Allah (ta gyaran jama'a) a cikin waɗanda suka shũɗe gabãninka, kuma bã zã ka sãmi musanyãwa ba ga hanyar Allah. = --Qur'an 33:62
    People ask you concerning the Hour. Say," Knowledge of it is only with Allah. And what may make you perceive? Perhaps the Hour is near." <> Sunã tambayar ka ga Sã'a. Ka ce: "Saninta yanã wurin Allah kawai." Kuma me yã sanar da kai cẽwa anã tsammãnin sa'a ta kasance kusa? = --Qur'an 33:63
    Indeed, Allah has cursed the disbelievers and prepared for them a Blaze. <> Lalle Allah Yã la'ani kãfirai, kuma Yã yi musu tattalin wata wuta mai ƙũna. = --Qur'an 33:64
    Abiding therein forever, they will not find a protector or a helper. <> Sunã madawwama a cikinta har abada, bã su sãmun majiɓinci, kuma bã su sãmun mataimaki. = --Qur'an 33:65
    The Day their faces will be turned about in the Fire, they will say, "How we wish we had obeyed Allah and obeyed the Messenger." <> Rãnar da ake jũya fuskõkinsu a cikin wuta sunã cẽwa, "Kaitonmu, sabõda, rashin biyarmu ga Allah da rashin biyarmu ga Manzo!" = --Qur'an 33:66
    And they will say, "Our Lord, indeed we obeyed our masters and our dignitaries, and they led us astray from the [right] way. <> Kuma suka ce: "Yã Ubangijinmu! Lalle mũ mun bi shugabanninmu da manyanmu! Sai suka ɓatar da mu daga hanya! = --Qur'an 33:67
    Our Lord, give them double the punishment and curse them with a great curse." <> "Yã Ubangijinmu! Ka ba su ninki biyu na azãba, kuma ka la'ane su, la'ana mai girma." = --Qur'an 33:68
    O you who have believed, be not like those who abused Moses; then Allah cleared him of what they said. And he, in the sight of Allah, was distinguished. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kasance kamar waɗanda suka cũci Mũsã sa'an nan Allah Ya barrantar da shi daga abin da suka ce. Kuma ya kasance mai daraja a wurin Allah. = --Qur'an 33:69
    O you who have believed, fear Allah and speak words of appropriate justice. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma ku faɗi magana madaidaiciya. = --Qur'an 33:70
    He will [then] amend for you your deeds and forgive you your sins. And whoever obeys Allah and His Messenger has certainly attained a great attainment. <> Ya kyautata muku ayyukanku, kuma Ya gãfarta zunubanku. Kuma wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, to, lalle, yã rabbanta, babban rabo mai girma. = --Qur'an 33:71
    Indeed, we offered the Trust to the heavens and the earth and the mountains, and they declined to bear it and feared it; but man [undertook to] bear it. Indeed, he was unjust and ignorant. <> Lalle Mũ, Mun gitta amãna ga sammai da ƙasã da duwãtsu, sai suka ƙi ɗaukarta kuma sukaji tsõro daga gare ta, kuma mutum ya ɗauke ta, lalle shĩ (mutum) ya kasance mai yawan zãlunci, mai yawan jãhilci. = --Qur'an 33:72
    [It was] so that Allah may punish the hypocrite men and hypocrite women and the men and women who associate others with Him and that Allah may accept repentance from the believing men and believing women. And ever is Allah Forgiving and Merciful. <> Dõmin Allah Ya azabta munãfukai maza da munãfukai mãtã, da mushirikai maza da mushirikai mãtã, kuma Allah Yã karɓi tũba ga mũminai maza da mũminai mãtã. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai. = --Qur'an 33:73
    [All] praise is [due] to Allah, to whom belongs whatever is in the heavens and whatever is in the earth, and to Him belongs [all] praise in the Hereafter. And He is the Wise, the Acquainted. <> Gõdiya ta tabbata ga Allah, wanda Yake abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã Nãsa ne, kuma shĩ ne Mai hikima, Mai labartawa. = --Qur'an 34:1
    He knows what penetrates into the earth and what emerges from it and what descends from the heaven and what ascends therein. And He is the Merciful, the Forgiving. <> Yã san abin da yake shiga a cikin ƙasã da abin da yake fita daga gare ta, da abin da yake sauka daga sama da abin da yake hawa a cikinta, kuma Shĩ ne Mai jin ƙai, Mai gãfara. = --Qur'an 34:2
    But those who disbelieve say, "The Hour will not come to us." Say, "Yes, by my Lord, it will surely come to you. [Allah is] the Knower of the unseen." Not absent from Him is an atom's weight within the heavens or within the earth or [what is] smaller than that or greater, except that it is in a clear register - <> Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Sã'a bã zã ta zo mana ba." Ka ce: "Kayya! Na rantse da Ubangijĩna, lalle, zã ta zõ muku." Masanin gaibi, gwargwadon zarra bã ta nĩsanta daga gare Shi a cikin sammai kuma bã ta nĩsanta a cikin ƙasã, kuma bãbu mafi ƙaranci daga wancan kuma bãbu mafi girma fãce yanã a cikin Littãfi bayyananne. = --Qur'an 34:3
    That He may reward those who believe and do righteous deeds. Those will have forgiveness and noble provision. <> Dõmin Ya sãkã wa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Waɗancan suna da wata gãfara da wani arziki mai karimci. = --Qur'an 34:4
    But those who strive against Our verses [seeking] to cause failure - for them will be a painful punishment of foul nature. <> Kuma waɗanda suka yi mãkirci ga ãyõyinMu, sunã mãsu gajiyarwa, waɗannan sunã da wata azãba daga azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 34:5
    And those who have been given knowledge see that what is revealed to you from your Lord is the truth, and it guides to the path of the Exalted in Might, the Praiseworthy. <> Kuma waɗanda aka bai wa ilmi sunã ganin abin nan da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, shi ne gaskiya, kuma yanã shiryarwa zuwa ga hanyar Mabuwãyi, Gõdadde. = --Qur'an 34:6
    But those who disbelieve say, "Shall we direct you to a man who will inform you [that] when you have disintegrated in complete disintegration, you will [then] be [recreated] in a new creation? <> Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Shin zã mu nũna muku wani namiji wanda yake gaya muku wai idan an tsattsãge ku, kõwace irin tsattsãgẽwa, lalle kũ, tabbas, kunã a cikin wata halitta sãbuwa.?" = --Qur'an 34:7
    Has he invented about Allah a lie or is there in him madness?" Rather, they who do not believe in the Hereafter will be in the punishment and [are in] extreme error. <> "Ya ƙãga ƙarya ga Allah ne kõ kuwa akwai wata hauka a gare shi?" Ã'a, waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba, sunã a cikin azãba da ɓãta mai nĩsa. = --Qur'an 34:8
    Then, do they not look at what is before them and what is behind them of the heaven and earth? If We should will, We could cause the earth to swallow them or [could] let fall upon them fragments from the sky. Indeed in that is a sign for every servant turning back [to Allah]. <> Ashe fa, ba su yi dũbi ba zuwa ga abin da ke a gaba gare su da abin da ke a bãyansu daga sama da ƙasã? idan Mun so, sai Mu shãfe ƙasã da su, kõ kuma Mu kãyar da wani ɓaɓɓake daga sama a kansu. Lalle, a cikin wancan akwai ãyã ga dukan bãwã mai maida al'amarinsa ga Allah. = --Qur'an 34:9
    And We certainly gave David from Us bounty. [We said], "O mountains, repeat [Our] praises with him, and the birds [as well]." And We made pliable for him iron, <> Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun bai wa Dãwũda wata falala dagagare Mu. Yã duwatsu, ku konkõma sautin tasbihi tãre da shi kuma da tsuntsãye. Kuma Muka tausasa masa baƙin ƙarfe. = --Qur'an 34:10
    [Commanding him], "Make full coats of mail and calculate [precisely] the links, and work [all of you] righteousness. Indeed I, of what you do, am Seeing." <> Ka aikata sulkuna kuma ka ƙaddara lissãfi ga tsãrawa, kuma ka aikata aikin ƙwarai. Lalle NĩMai gani ne ga abin da kuke aikatãwa. = --Qur'an 34:11
    And to Solomon [We subjected] the wind - its morning [journey was that of] a month - and its afternoon [journey was that of] a month, and We made flow for him a spring of [liquid] copper. And among the jinn were those who worked for him by the permission of his Lord. And whoever deviated among them from Our command - We will make him taste of the punishment of the Blaze. <> Kuma ga Sulaimãn, Mun hõre masa iska, tafiyarta ta safiya daidai da wata, kuma ta maraice daidai da wata. Kuma Muka gudãnar masa da marmaron gaci, kuma daga aljannu (Muka hõre masa) waɗanda ke aiki a gaba gare shi, da iznin Ubangijinsa. Wanda ya karkata daga cikinsu, daga umurninMu, sai Mu ɗanɗana masa daga azãbar sa'ĩr. = --Qur'an 34:12
    They made for him what he willed of elevated chambers, statues, bowls like reservoirs, and stationary kettles. [We said], "Work, O family of David, in gratitude." And few of My servants are grateful. <> Sunã aikata masa abin da yake so, na masallatai da mutummutumai da akussa kamar kududdufai, da tukwãne kafaffu. Ku aikata gõdiya, yã ɗiyan Dãwũda, kuma kaɗan ne mai gõdiya daga bãyĩNa. = --Qur'an 34:13
    And when We decreed for Solomon death, nothing indicated to the jinn his death except a creature of the earth eating his staff. But when he fell, it became clear to the jinn that if they had known the unseen, they would not have remained in humiliating punishment. <> Sa'an nan a lõkacin da Muka hukunta mutuwa a kansa bãbu abin da ya ja hankalinsu, a kan mutuwarsa, fãce dabbar ƙasa (gara) wadda take cin sandarsa. To a lõkacin da ya fãɗi, sai aljannu suka bayyana (ga mutãne) cẽwa dã sun kasance sun san gaibi, dã ba su zauna ba a cikin azãba mai wulãkantarwa. = --Qur'an 34:14
    There was for [the tribe of] Saba' in their dwelling place a sign: two [fields of] gardens on the right and on the left. [They were told], "Eat from the provisions of your Lord and be grateful to Him. A good land [have you], and a forgiving Lord." <> Lalle, haƙĩƙa, akwai ãyã ga saba'ãwa a cikin mazauninsu: gõnakin lambu biyu, dama da hagu. "Ku ci daga arzikin Ubangijinku, kuma ku yi gõdiya gare shi. Gari mai dãɗin zama, da Ubangiji Mai gãfara." = --Qur'an 34:15
    But they turned away [refusing], so We sent upon them the flood of the dam, and We replaced their two [fields of] gardens with gardens of bitter fruit, tamarisks and something of sparse lote trees. <> Sai suka bijire sabõda haka Muka saki Mãlãlin Arimi (dam) a kansu, kuma Muka musanya musu gõnakinsu biyu da waɗansu gõnaki biyu mãsu 'ya'yan itãce kaɗan: talãkiya da gõriba da wani abu na magarya kaɗan. = --Qur'an 34:16
    [By] that We repaid them because they disbelieved. And do We [thus] repay except the ungrateful? <> Wancan, da shi Muka yi musu sakamako sabõda kãfircinsu. Kuma lalle, bã Mu yi wa kõwa irin wannan sakamako, fãce kafirai. = --Qur'an 34:17
    And We placed between them and the cities which We had blessed [many] visible cities. And We determined between them the [distances of] journey, [saying], "Travel between them by night or day in safety." <> Kuma Muka sanya, a tsakaninsu da tsakãnin garũruwan da Muka Sanya albarka a cikinsu, waɗansu garũruwa mãsuganin jũna kuma Muka ƙaddara tafiya a cikinsu, "Ku yi tafiya a cikinsu, darũruwa da rãnaiku, kunã amintattu." = --Qur'an 34:18
    But [insolently] they said, "Our Lord, lengthen the distance between our journeys," and wronged themselves, so We made them narrations and dispersed them in total dispersion. Indeed in that are signs for everyone patient and grateful. <> Sai suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka nĩsantar da tsakãnin tafiyõyinmu," kuma suka zãlunci kansu, sabõda haka Muka sanya su lãbãran hĩra kuma Muka kekkẽce su kõwace, irin kekkẽcewa. Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga dukan mai yawan haƙuri, mai yawan gõdiya. = --Qur'an 34:19
    And Iblees had already confirmed through them his assumption, so they followed him, except for a party of believers. <> Kuma lalle, haƙĩƙa, Iblĩs ya gaskata zatonsa a kansu, sai suka bi shi fãce wani ɓangare na mũminai. = --Qur'an 34:20
    And he had over them no authority except [it was decreed] that We might make evident who believes in the Hereafter from who is thereof in doubt. And your Lord, over all things, is Guardian. <> Kuma bã ya da wani dalĩli a kansu fãce dai dõmin Mu san wanda yake yin ĩmãni da Lãhira daga wanda yake a cikin shakka daga gare ta. Kuma Ubangijinka, a kan kõme, Mai tsaro ne. = --Qur'an 34:21
    Say, [O Muhammad], "Invoke those you claim [as deities] besides Allah." They do not possess an atom's weight [of ability] in the heavens or on the earth, and they do not have therein any partnership [with Him], nor is there for Him from among them any assistant. <> Ka ce: "Ku kirãyi waɗanda kuka riya (cẽwa abũbuwan bautãwa ne) baicin Allah, bã su Mallakar ma'aunin zarra a cikin sammai, kuma bã su Mallakarsa a cikin ƙasa kuma bã su da wani rabon tãrẽwa a cikinsu (sammai da ƙasa), kuma bã Shi da wani mataimaki daga gare su. = --Qur'an 34:22
    And intercession does not benefit with Him except for one whom He permits. [And those wait] until, when terror is removed from their hearts, they will say [to one another], "What has your Lord said?" They will say, "The truth." And He is the Most High, the Grand. <> "Kuma wani cẽto bã ya amfãni a wurinSa face fa ga wanda Ya yi izni a gare shi. Har a lõkacin da aka kuranye tsõro daga zukãtansu, sai su ce, 'Mẽne ne Ubangijinku Ya ce?' Suka ce: 'Gaskiya', kuma shi ne Maɗaukaki, Mai girma," = --Qur'an 34:23
    Say, "Who provides for you from the heavens and the earth?" Say, "Allah. And indeed, we or you are either upon guidance or in clear error." <> Ka ce: "Wãne ne yake azurta ku daga sama da ƙasa?" Ka ce: "Allah kuma lalle mũ kõ ku, wani yanã a kan shiriya, kõ yana a cikin ɓata bayyananniya." = --Qur'an 34:24
    Say, "You will not be asked about what we committed, and we will not be asked about what you do." <> Ka ce: "Bã zã a tambaye ku ba ga abin da muka aikata daga laifi, kuma bã zã a tambaye mu daga abin da kuke aikatawa ba." = --Qur'an 34:25
    Say, "Our Lord will bring us together; then He will judge between us in truth. And He is the Knowing Judge." <> Ka ce: "Ubangijinmu zai tãra tsakãninmu, sa'an nan Ya yi hukunci a tsakaninmu da gaskiya. Kuma Shĩ ne Mahukunci, Masani." = --Qur'an 34:26
    Say, "Show me those whom you have attached to Him as partners. No! Rather, He [alone] is Allah, the Exalted in Might, the Wise." <> Ka ce: "Ku nũna mini waɗanda kuka riskar da Shi, su zama abõkan tãrayya. Ã'a, Shĩ ne Allah, Mabuwãyi, Mai hikima." = --Qur'an 34:27
    And We have not sent you except comprehensively to mankind as a bringer of good tidings and a warner. But most of the people do not know. <> Kuma ba Mu aika ka ba fãce zuwa ga mutãne gabã ɗaya, kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba. = --Qur'an 34:28
    And they say, "When is this promise, if you should be truthful?" <> Sunã cẽwa, "Yaushe ne wannan wa'adi zai auku idan kun kasance mãsu gaskiya?" = --Qur'an 34:29
    Say, "For you is the appointment of a Day [when] you will not remain thereafter an hour, nor will you precede [it]." <> Ka ce: "Kunã da mi'ãdin wani yini wanda bã ku jinkirta daga gare shi kõ da sa'a ɗaya, kuma bã ku gabãta." = --Qur'an 34:30
    And those who disbelieve say, "We will never believe in this Qur'an nor in that before it." But if you could see when the wrongdoers are made to stand before their Lord, refuting each other's words... Those who were oppressed will say to those who were arrogant, "If not for you, we would have been believers." <> Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Bã zã mu yi ĩmanida wannan Alƙur'ãni ba, kuma bã zã mu yi ĩmani da abin da yakea gabãninsa ba (na waɗansu littattafan sama)." Kuma dã kã gani a lõkacin da azzãlumai suke abin tsayarwa wurin Ubangijinka, sashensu na mayar wa sãshe maganar maraunana (mabiya) suke cẽwa makangara (shũgabanni) "Ba dõminku ba, lalle, dã mun kasance mũminai." = --Qur'an 34:31
    Those who were arrogant will say to those who were oppressed, "Did we avert you from guidance after it had come to you? Rather, you were criminals." <> Makangara suka ce wa maraunana, "Ashe, mũ ne muka kange ku daga shiriya a bãyan ya zo muku? Ã, a' kun dai kasance mãsu laifi." = --Qur'an 34:32
    Those who were oppressed will say to those who were arrogant, "Rather, [it was your] conspiracy of night and day when you were ordering us to disbelieve in Allah and attribute to Him equals." But they will [all] confide regret when they see the punishment; and We will put shackles on the necks of those who disbelieved. Will they be recompensed except for what they used to do? <> Kuma maraunana suka ce wa makangara. "Ã'a, (ku tuna) mãkircin dare da na rãna a lõkacin da kuke umurnin mu da mu kãfirta da Allah, kuma mu sanya Masa abõkan tãrayya." Kuma suka assirtar da nadãma a lõkacin da suka ga azãba. Kuma Muka sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyin waɗanda suka kãfirta. Lalle, bã zã a yi musu sakamako ba fãce da abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 34:33
    And We did not send into a city any warner except that its affluent said, "Indeed we, in that with which you were sent, are disbelievers." <> Kuma ba mu aika wani mai gargaɗi ba a cikin wata alƙarya fãce mani'imtanta (shũgabanni) sunce, "Lalle mũ, mãsu kãfirta ne da abin da aka aiko ku da shi." = --Qur'an 34:34
    And they said, "We are more [than the believers] in wealth and children, and we are not to be punished." <> Kuma suka ce: "Mũ ne mafiya yawa ga dũkiya da ɗiya, kuma mu ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba." = --Qur'an 34:35
    Say, "Indeed, my Lord extends provision for whom He wills and restricts [it], but most of the people do not know." <> Ka ce: "Lalle, Ubangijĩna Yanã shimfiɗa arziki ga wanda Ya so, kuma Yanã ƙuntatãwa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba." = --Qur'an 34:36
    And it is not your wealth or your children that bring you nearer to Us in position, but it is [by being] one who has believed and done righteousness. For them there will be the double reward for what they did, and they will be in the upper chambers [of Paradise], safe [and secure]. <> Kuma dũkiyarku ba ta zamo ba, haka ɗiyanku ba su zamo abin da yake kusantar da ku ba a wurinMu, kusantarwar muƙãmi fãce wanda, ya yi ĩmãni kuma ya aikata aikin ƙwarai. To, waɗannan sunã da sakamakon ninkawa sabõda abin da suka aikata. Kuma su amintattu ne a cikin bẽnãye. = --Qur'an 34:37
    And the ones who strive against Our verses to cause [them] failure - those will be brought into the punishment [to remain]. <> Kuma waɗanda suke mãkirci a cikin ãyõyinMu, sunã nẽman gajiyarwa, waɗannan abin halartãwa ne a cikin azãba. = --Qur'an 34:38
    Say, "Indeed, my Lord extends provision for whom He wills of His servants and restricts [it] for him. But whatever thing you spend [in His cause] - He will compensate it; and He is the best of providers." <> Ka ce: "Lalle, Ubangijĩna Yanã shimfida arziki ga wanda Ya so daga bãyinSa, kuma Yanã ƙuntatãwa a gare shi, kuma abin da kuka ciyar daga wani abu, to, Shĩ ne zai musanya shi, kuma Shĩ ne Mafi fĩcin mãsu azurtawa." = --Qur'an 34:39
    And [mention] the Day when He will gather them all and then say to the angels, "Did these [people] used to worship you?" <> Kuma rãnar da Allah Ya ke tãra su gabã ɗaya, sa'an nan Ya ce wa Malã'iku, "Shin, waɗannan kũ ne suka kasance sunã bauta wa?" = --Qur'an 34:40
    They will say, "Exalted are You! You, [O Allah], are our benefactor not them. Rather, they used to worship the jinn; most of them were believers in them." <> Sukace: "Tsarki ya tabbata a gare Ka. Kai ne Majiɓincinmu, bã su ba. Ã'a, sun kasance sunã bauta wa aljannu. Mafi yawansu, da sũ suka yi ĩmani." = --Qur'an 34:41
    But today you do not hold for one another [the power of] benefit or harm, and We will say to those who wronged, "Taste the punishment of the Fire, which you used to deny." <> Sabõda haka, a yau sãshenku bã ya mallakar wani amfãni ga wani sãshen, kuma bã ya mallakar wata cũta, kuma Munã cẽwa ga waɗanda suka yi zalunci, Ku ɗanɗani azabar wutã wadda "kuka kasance game da ita, kunã ƙaryatãwa." = --Qur'an 34:42
    And when our verses are recited to them as clear evidences, they say, "This is not but a man who wishes to avert you from that which your fathers were worshipping." And they say, "This is not except a lie invented." And those who disbelieve say of the truth when it has come to them, "This is not but obvious magic." <> Kuma idan an karanta ãyõyinMu bayyanannu a kansu, sai su ce: "Wannan bai zama ba fãce namiji ne yanã son ya kange ku daga abin da ubanninku suka kasance sunã bauta wa." Kuma su ce: "Wannan bai zama ba fãce ƙiren ƙarya da aka ƙãga." Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: ga gaskiya a lõkacin da ta je musu: "Wannan bã kõme ba fãce sihiri ne bayyananne." = --Qur'an 34:43
    And We had not given them any scriptures which they could study, and We had not sent to them before you, [O Muhammad], any warner. <> Kuma ba Mu bã su waɗansu littattafai ba waɗanda suke karãtun su, kuma ba Mu aika wani mai gargaɗi ba zuwa gare su a gabãninka! = --Qur'an 34:44
    And those before them denied, and the people of Makkah have not attained a tenth of what We had given them. But the former peoples denied My messengers, so how [terrible] was My reproach. <> Kuma waɗanda suke a gabãninsu, sun ƙaryata, alhãli kuwa ba su kai ushurin-ushurin abin da Muka bã su ba, sai suka ƙaryata ManzanniNa! To, yãya musũNa (ga maƙaryata) ya kasance? = --Qur'an 34:45
    Say, "I only advise you of one [thing] - that you stand for Allah, [seeking truth] in pairs and individually, and then give thought." There is not in your companion any madness. He is only a warner to you before a severe punishment. <> Ka ce: "Ina yi muku wa'azi ne kawai da kalma guda! watau ku tsayu dõmin Allah, bibbiyu da ɗaiɗai, sa'an nan ku yi tunãni, bãbu wata hauka ga ma'abũcinku. Shĩ bai zama ba fãce mai gargaɗi ne a gare ku a gaba ga wata azãba mai tsanani. = --Qur'an 34:46
    Say, "Whatever payment I might have asked of you - it is yours. My payment is only from Allah, and He is, over all things, Witness." <> Ka ce: "Abin da na rõƙe ku na wani sakamako, to, amfãninsa nãku ne. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Allah, kuma shi Mahalarci ne a kan dukan kõme." = --Qur'an 34:47
    Say, "Indeed, my Lord projects the truth. Knower of the unseen." <> Ka ce: "Lalle Ubangijina Yanã jẽfa gaskiya. (Shi) Masanin abũbuwan fake ne." = --Qur'an 34:48
    Say, "The truth has come, and falsehood can neither begin [anything] nor repeat [it]." <> Ka ce: "Gaskiya ta zo, kuma ƙarya bã ta iya fara (kome) kuma bã ta iya mayarwa." = --Qur'an 34:49
    Say, "If I should err, I would only err against myself. But if I am guided, it is by what my Lord reveals to me. Indeed, He is Hearing and near." <> Ka ce: "Idan na ɓace, to, inã ɓacẽwa ne kawai a kan kaina. Kuma idan na shiryu, to, sabõda abin da Ubangijina Yake yõwar wahayi ne zuwa a gare ni. Lalle Shĩ Mai ji ne, Makusanci." = --Qur'an 34:50
    And if you could see when they are terrified but there is no escape, and they will be seized from a place nearby. <> Kuma dã kã gani, a lõkacin da suka firgita, to, bãbu kuɓuta, kuma aka kãma su daga wuri makusanci. = --Qur'an 34:51
    And they will [then] say, "We believe in it!" But how for them will be the taking [of faith] from a place far away? <> Kuma suka ce: "Mun yi ĩmãni da Shi." To inã zã su sãmu kãmãwa daga wuri mai nisa? = --Qur'an 34:52
    And they had already disbelieved in it before and would assault the unseen from a place far away. <> Kuma lalle sun kãfirta da Shi a gabãnin haka, kuma sunã jĩfa da jãhilci daga wuri mai nĩsa. = --Qur'an 34:53
    And prevention will be placed between them and what they desire, as was done with their kind before. Indeed, they were in disquieting denial. <> Kuma an shãmakance a tsakãninsu da tsakãnin abin da suke marmari, kamar yadda aka aikata da irin ƙungiyõyinsu a gabãninsu. Lalle sũ sun kasance a cikin shakka mai sanya kõkanto. = --Qur'an 34:54
    [All] praise is [due] to Allah, Creator of the heavens and the earth, [who] made the angels messengers having wings, two or three or four. He increases in creation what He wills. Indeed, Allah is over all things competent. <> Gõdiya ta tabbata ga Allah, Mai fãra halittar sammai da ƙasã, Mai sanya malã'iku manzanni mãsu fukãfukai, bibbiyu, da uku-uku da hurhuɗu. Yanã ƙãrãwar abin da Ya ke so a cikin halittar. Lalle Allah Mai ĩkon yi ne a kan kõme. = --Qur'an 35:1
    Whatever Allah grants to people of mercy - none can withhold it; and whatever He withholds - none can release it thereafter. And He is the Exalted in Might, the Wise. <> Abin da Allah Ya buɗa wa mutãne daga rahama, to, bãbu mai riƙewa a gare shi, kuma abin da Ya riƙe, to, bãbu mai saki a gare shi, waninSa, kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima. = --Qur'an 35:2
    O mankind, remember the favor of Allah upon you. Is there any creator other than Allah who provides for you from the heaven and earth? There is no deity except Him, so how are you deluded? <> Yã kũ mutãne! Ku tuna ni'imar Allah a kanku. Shin, akwai wani mai halitta wanin Allah da zai azurta ku daga sama da, ƙasã? Bãbu wani abin bautãwa, fãce Shi. To, yãya ake karkatar da ku? = --Qur'an 35:3
    And if they deny you, [O Muhammad] - already were messengers denied before you. And to Allah are returned [all] matters. <> Kuma idan sun ƙaryata ka, to, lalle, an ƙaryata waɗansu Manzanni a gabãninka, kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'amura. = --Qur'an 35:4
    O mankind, indeed the promise of Allah is truth, so let not the worldly life delude you and be not deceived about Allah by the Deceiver. <> Yã kũ mutãne! Lalle wa'adin Allah gaskiya ne, sabõda haka kada rãyuwar dũniya ta rũɗar da ku, kuma kada marũɗi ya rũɗe ku game da Allah. = --Qur'an 35:5
    Indeed, Satan is an enemy to you; so take him as an enemy. He only invites his party to be among the companions of the Blaze. <> Lalle Shaiɗan maƙiyi ne a gare ku, sai ku riƙe shi maƙiyi. Yanã kiran ƙungiyarsa kawai ne, dõmin su kasance 'yan sa'ir. = --Qur'an 35:6
    Those who disbelieve will have a severe punishment, and those who believe and do righteous deeds will have forgiveness and great reward. <> Waɗanda suka kãfirta suna da azãba mai tsanani kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wata gãfara da sakamako mai girma. = --Qur'an 35:7
    Then is one to whom the evil of his deed has been made attractive so he considers it good [like one rightly guided]? For indeed, Allah sends astray whom He wills and guides whom He wills. So do not let yourself perish over them in regret. Indeed, Allah is Knowing of what they do. <> Shin to, wanda aka ƙawãta masa aikinsa, har ya gan shi mai kyau (yanã daidai da waninsa)? Sabõda haka, lalle, Allah Yanã ɓatar da wanda Yake so, kuma Yanã shiryar da wanda Yake so, sabõda haka kada ranka ya halaka a kansu dômin baƙin ciki. Lalle Allah Masani ne ga abin da suke sanã'antawa. = --Qur'an 35:8
    And it is Allah who sends the winds, and they stir the clouds, and We drive them to a dead land and give life thereby to the earth after its lifelessness. Thus is the resurrection. <> Kuma Allah ne Ya aika da iskõki har su mõtsar da girgije, sa'an nan Mu kõra shi zuwa ga gari matacce, sa'an nan Mu rãyar da ƙasã game da shi a bayan mutuwarta. Kamar wancan ne Tãshin ¡iyãma yake. = --Qur'an 35:9
    Whoever desires honor [through power] - then to Allah belongs all honor. To Him ascends good speech, and righteous work raises it. But they who plot evil deeds will have a severe punishment, and the plotting of those - it will perish. <> Wanda ya kasance yanã nẽman wata izza, to, Allah ne da izza gabã ɗaya. zuwa gare Shi magana mai dãɗi ke hawa, kuma aiki na ƙwarai Yanã ɗaukar ta Kuma waɗanda ke yin mãkircin mũnanan ayyuka, sunã da wata azãba mai tsanani, kuma mãkircin waɗannan yanã yin tasgaro. = --Qur'an 35:10
    And Allah created you from dust, then from a sperm-drop; then He made you mates. And no female conceives nor does she give birth except with His knowledge. And no aged person is granted [additional] life nor is his lifespan lessened but that it is in a register. Indeed, that for Allah is easy. <> Kuma Allah ne Ya halitta ku daga turɓãya, sa'an nan daga ɗigon maniyyi, sa'an nan Ya sanya ku surkin maza da mãtã. Kuma wata mace bã ta yin ciki, kuma bã ta haihuwa, fãce da saninSa, kuma bã zã a rãyar da wanda ake rãyarwa ba, kuma bã zã a rage tsawon ransa ba fãce yanã a cikin Littãfi. Lalle, wancan mai sauki ne ga Allah. = --Qur'an 35:11
    And not alike are the two bodies of water. One is fresh and sweet, palatable for drinking, and one is salty and bitter. And from each you eat tender meat and extract ornaments which you wear, and you see the ships plowing through [them] that you might seek of His bounty; and perhaps you will be grateful. <> Kuma kõguna biyu ba su daidaita: Wannan mai ruwan dãɗi, mai zãƙi, mai sauƙin haɗiya kuma wannan mai ruwan gishiri mai zartsi, kuma daga kõwane, kunã cin wani nama sãbo, kuma kunã fitar da kawa wadda kuke tufantarta, kuma kanã ganin jirãge a cikinsa sunã mãsu gudãna, dõmin ku nẽmo daga falalarSa, kuma ɗammãninku zã ku dinga gõdẽwa. = --Qur'an 35:12
    He causes the night to enter the day, and He causes the day to enter the night and has subjected the sun and the moon - each running [its course] for a specified term. That is Allah, your Lord; to Him belongs sovereignty. And those whom you invoke other than Him do not possess [as much as] the membrane of a date seed. <> Yanã shigar da dare a cikin rãna, kuma Yanã shigar da rãna a cikin dare. Kuma Ya hõre rãnã da watã kõwannensu yanã gudãna zuwa ga ajali ambatacce Wannan Shĩ ne Allah, Ubangijinku, gare Shi mulki yake, kuma waɗanda kuke kira waninSa bã su mallakar kõ fãtar gurtsun dabĩno. = --Qur'an 35:13
    If you invoke them, they do not hear your supplication; and if they heard, they would not respond to you. And on the Day of Resurrection they will deny your association. And none can inform you like [one] Acquainted [with all matters]. <> Idan kun kira su, bã zã su ji kiranku ba, kuma kõ sun jiya, bã zã su karɓa muku ba, kuma a Rãnar ¡iyãma zã su kãfirce wa shirkinku, kuma bãbu mai bã ka lãbãri, kamar wanda ya sani. = --Qur'an 35:14
    O mankind, you are those in need of Allah, while Allah is the Free of need, the Praiseworthy. <> Yã kũ mutãne! Kũ ne mãsu bukãta zuwa ga Allah, kuma Allah, Shĩ ne Mawadãci, Gõdadde. = --Qur'an 35:15
    If He wills, He can do away with you and bring forth a new creation. <> Idan Ya so, zai tafi da ku, kuma Ya zo da wata halitta sãbuwa. = --Qur'an 35:16
    And that is for Allah not difficult. <> Kuma wancan bai zama mabuwãyi ba ga Allah. = --Qur'an 35:17
    And no bearer of burdens will bear the burden of another. And if a heavily laden soul calls [another] to [carry some of] its load, nothing of it will be carried, even if he should be a close relative. You can only warn those who fear their Lord unseen and have established prayer. And whoever purifies himself only purifies himself for [the benefit of] his soul. And to Allah is the [final] destination. <> Kuma wani rai mai ɗaukar nauyi, bai ɗaukar nauyin wani rai. Kuma idan ran da aka nauyaya wa kãya ya yi kira (ga wani mataimaki) zuwa ga kãyansa, bã zã a dauki kõme ba daga gare shi, kuma kõ dã (wanda ake kiran) yã kasance makusancin zumunta ne. Kanã gargaɗi kawai ne ga waɗanda ke tsoron Ubangijinsu a fake, kuma suka tsayar da salla. Kuma wanda ya tsarkake, to, yanã tsarkaka ne dõmin kansa. Kuma zuwa ga Allah kawai makõma take. = --Qur'an 35:18
    Not equal are the blind and the seeing, <> Kuma makãho bã ya daidaita da mai gani. = --Qur'an 35:19
    Nor are the darknesses and the light, <> Kuma duffai bã su daidaita, kuma haske bã ya daidaita. = --Qur'an 35:20
    Nor are the shade and the heat, <> Kuma inuwa bã ta daidaita, kuma iskar zãfi bã ta daidaita. = --Qur'an 35:21
    And not equal are the living and the dead. Indeed, Allah causes to hear whom He wills, but you cannot make hear those in the graves. <> Kuma rãyayyu bã su daidaita kuma matattu ba su daidaita. Lalle Allah Yanã jiyar da wa'azi ga wanda Ya so, kuma ba ka jiyar da waɗanda suke a cikin kaburbura. = --Qur'an 35:22
    You, [O Muhammad], are not but a warner. <> Ba ka zama ba fãce mai gargaɗi kawai. = --Qur'an 35:23
    Indeed, We have sent you with the truth as a bringer of good tidings and a warner. And there was no nation but that there had passed within it a warner. <> Lalle Mũ Mun aike ka da gaskiya, kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. Kuma bãbu wata al'umma fãce wani mai gargaɗi yã shũɗe a cikinta. = --Qur'an 35:24
    And if they deny you - then already have those before them denied. Their messengers came to them with clear proofs and written ordinances and with the enlightening Scripture. <> Kuma idan sunã ƙaryata ka, to, haƙĩƙa, waɗanda suke a gabãninsu sun ƙaryata. Manzanninsu sun jẽ musu da hujjõji, kuma da takardu, kuma da Littafi mai haske. = --Qur'an 35:25
    Then I seized the ones who disbelieved, and how [terrible] was My reproach. <> Sa'an nan Na kãma waɗanda suka kãfirta. To, yãya musũNa yake? = --Qur'an 35:26
    Do you not see that Allah sends down rain from the sky, and We produce thereby fruits of varying colors? And in the mountains are tracts, white and red of varying shades and [some] extremely black. <> Ba ka gani ba, lalle Allah Ya saukar da ruwa daga sama? Sai Muka fitar, game da shi,'yã'yan itãce mãsu sãɓanin launuka kuma daga duwatsu akwai zane-zane, farfaru da jãjãye, mãsu sãɓanin launin, da mãsu launin baƙin ƙarfe, baƙãƙe. = --Qur'an 35:27
    And among people and moving creatures and grazing livestock are various colors similarly. Only those fear Allah, from among His servants, who have knowledge. Indeed, Allah is Exalted in Might and Forgiving. <> Kuma daga mutãne da dabbõbi da bisãshen gida, mãsu sãɓãnin launinsu kamar wancan. Malamai kawai ke tsõron Allah daga cikin bãyinSa. Lalle, Allah, Mabuwãyi ne, Mai gãfara. = --Qur'an 35:28
    Indeed, those who recite the Book of Allah and establish prayer and spend [in His cause] out of what We have provided them, secretly and publicly, [can] expect a profit that will never perish - <> Lalle waɗanda ke karãtun Littãfin Allah kuma suka tsayar da salla, kuma suka ciyar daga abin da Muka azurta su da shi, a asirce da bayyane, sunã fãtan (sãmun) wani fatauci ne wanda bã ya yin tasgaro. = --Qur'an 35:29
    That He may give them in full their rewards and increase for them of His bounty. Indeed, He is Forgiving and Appreciative. <> Dõmin (Allah) zai cika musu sakamakonsu, kuma Ya ƙarã musu daga falalarSa. Lalle Shi Mai gãfara ne, Mai gõdiya. = --Qur'an 35:30
    And that which We have revealed to you, [O Muhammad], of the Book is the truth, confirming what was before it. Indeed, Allah, of His servants, is Acquainted and Seeing. <> Kuma abin da Muka yi wahayi zuwa gare ka, daga Littãfi, = --Qur'an 35:31
    Then we caused to inherit the Book those We have chosen of Our servants; and among them is he who wrongs himself, and among them is he who is moderate, and among them is he who is foremost in good deeds by permission of Allah. That [inheritance] is what is the great bounty. <> Sa'an nan Mun gãdar da Littãfin, ga waɗanda Muka zãɓa daga bãyinMu, sa'an nan daga cikinsu, akwai mai zãlunci ga kansa, kuma daga cikinsu akwai mai tsakaitãwa, kuma daga cikinsu akwai mai tsẽrẽwa da ayyukan alhẽri da iznin Allah. Waccan ita ce falalar (Allah) mai girma. = --Qur'an 35:32
    [For them are] gardens of perpetual residence which they will enter. They will be adorned therein with bracelets of gold and pearls, and their garments therein will be silk. <> Gidãjen Aljannar zamã sunã shigar su. Anã ƙawãce su a cikinsu, da ƙawã ta mundãye daga zĩnãriya da lu'ulu'u, kuma tufãfinsu, a cikinsu alharĩni ne. = --Qur'an 35:33
    And they will say, "Praise to Allah, who has removed from us [all] sorrow. Indeed, our Lord is Forgiving and Appreciative - <> Kuma suka ce: "Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya tafiyar da baƙin ciki daga gare mu. Lalle Ubangijinmu, haƙĩƙa Mai gafarane, Mai godiya." = --Qur'an 35:34
    He who has settled us in the home of duration out of His bounty. There touches us not in it any fatigue, and there touches us not in it weariness [of mind]." <> "Wanda Ya saukar da mu a gidan zamã, daga falalarSa, wata wahala bã ta shãfar mu a cikinsa, kuma wata kãsãwa bã ta shãfar mu a cikinsa." = --Qur'an 35:35
    And for those who disbelieve will be the fire of Hell. [Death] is not decreed for them so they may die, nor will its torment be lightened for them. Thus do we recompense every ungrateful one. <> Kuma waɗanda suka kãfirta sunã da wutar Jahannama, bã a yin hukunci a kansu balle su mutu kuma bã a sauƙaƙa musu daga azãbarta. Kamar haka Muke sãka wa kõwane mai yawan kãfirci. = --Qur'an 35:36
    And they will cry out therein, "Our Lord, remove us; we will do righteousness - other than what we were doing!" But did We not grant you life enough for whoever would remember therein to remember, and the warner had come to you? So taste [the punishment], for there is not for the wrongdoers any helper. <> Kuma sũ, sunã hargõwar nẽman ãgaji a cikinta. (Sunã cẽwa) "Yã Ubangijinmu! Ka fitar da mu, mu aikata aiki mai kyau, wanin wanda muka kasance munã aikatãwa." Ashe, kuma, ba Mu rãyar da ku ba, abin da mai tunãni zai iya yin tunãni a ciki, kuma mai gargaɗi yã jẽ muku? To, ku ɗanɗana, sabõda haka bãbu wani mataimaki, ga azzãlumai. = --Qur'an 35:37
    Indeed, Allah is Knower of the unseen [aspects] of the heavens and earth. Indeed, He is Knowing of that within the breasts. <> Lalle Allah ne Masanin gaibin sammai da ƙasã. Lalle Shĩ ne Masani ga abin da yake ainihin zukata. = --Qur'an 35:38
    It is He who has made you successors upon the earth. And whoever disbelieves - upon him will be [the consequence of] his disbelief. And the disbelief of the disbelievers does not increase them in the sight of their Lord except in hatred; and the disbelief of the disbelievers does not increase them except in loss. <> Shĩ ne Wanda Ya sanya ku mãsu maye wa junã, a cikin ƙasã. To, wanda ya kãfirta, to, kãfircinsa yanã a kansa. Kuma kãfircin kãfirai bã ya kãra musu kõme fãce baƙin jini, kuma kãfircin kãfirai bã ya kãra musu kõme face hasãra. = --Qur'an 35:39
    Say, "Have you considered your 'partners' whom you invoke besides Allah? Show me what they have created from the earth, or have they partnership [with Him] in the heavens? Or have We given them a book so they are [standing] on evidence therefrom? [No], rather, the wrongdoers do not promise each other except delusion." <> Ka ce: "Shin, kun ga abũbuwan shirkinku, waɗanda kuke kira, wasun Allah? Ku nũna mini, mẽne ne suka halitta daga ƙasã? Kõ sunã da tãrayya ne a cikin sammai? Kõ kuma Mun bã su wani littãfi ne sabõda haka sunã a kan wata hujja ce daga gare shi? Ã'a, azzãlumai bã su yin wani wa'adi, sãshensu zuwa ga sãshe, fãce rũɗi." = --Qur'an 35:40
    Indeed, Allah holds the heavens and the earth, lest they cease. And if they should cease, no one could hold them [in place] after Him. Indeed, He is Forbearing and Forgiving. <> Lalle Allah Yanã riƙe sammai da ƙasã dõmin kada su gushe. Kuma haƙĩƙa, idan sun gushe, bãbu wani baicinSa da zai riƙe su. Lalle Shi Yã kasance Mai haƙuri, Mai gãfara. = --Qur'an 35:41
    And they swore by Allah their strongest oaths that if a warner came to them, they would be more guided than [any] one of the [previous] nations. But when a warner came to them, it did not increase them except in aversion. <> Kuma suka yi rantsuwa da Allah, mafi nauyin rantsuwarsu, "Lalle, idan wani mai gargaɗi ya zo musu tabbas zã su kasance mafi shiryuwa, daga ɗayan al'ummõmi." To, a lõkacin da mai gargaɗi ya jẽ musu, bai ƙarã su da kõme ba fãce gudu. = --Qur'an 35:42
    [Due to] arrogance in the land and plotting of evil; but the evil plot does not encompass except its own people. Then do they await except the way of the former peoples? But you will never find in the way of Allah any change, and you will never find in the way of Allah any alteration. <> Dõmin nũna girman kai a cikin ƙasã da mãkircin cũta. Kuma mãkirci na cũta bã ya fãdãwa fãce a kan mutãnensa. To shin sunã jiran (wani abu ne) fãce dai hanyar (kãfiran) farko. To, bã zã ka sãmi musanya ba ga hanyar Allah. Kuma bã zã ka sãmi jũyarwa ba ga hanyar Allah. = --Qur'an 35:43
    Have they not traveled through the land and observed how was the end of those before them? And they were greater than them in power. But Allah is not to be caused failure by anything in the heavens or on the earth. Indeed, He is ever Knowing and Competent. <> Ashe, kuma ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã, dõmin su dũba yadda ãƙibar waɗannan da suke a gabãninsu ta kasance? Alhãli kuwa sun kasance mafĩfĩta ƙarfi daga gare su? Kuma Allah bai kasance wani abu nã iya rinjãyarSa ba, a cikin sammai, kuma haka a cikin kaƙã. Lalle Shi ne Ya kasance Masani, Mai ĩkon yi. = --Qur'an 35:44
    And if Allah were to impose blame on the people for what they have earned, He would not leave upon the earth any creature. But He defers them for a specified term. And when their time comes, then indeed Allah has ever been, of His servants, Seeing. <> Kuma dã Allah Yanã kãma mutãne sabõda abin da suka aikata, dã bai bar wata dabba ba a kanta (kasã). Amma Yanã jinkirta musu zuwa ga ajalin da aka ambatã. Sa'an nan idan ajalinsu ya zo, to, lalle Allah yã kasance Mai gani ga bãyinSa. = --Qur'an 35:45
    Ya, Seen. <> Y. S̃. = --Qur'an 36:1
    By the wise Qur'an. <> Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni Mai hikima. = --Qur'an 36:2
    Indeed you, [O Muhammad], are from among the messengers, <> Lalle kai, haƙĩƙa kanã cikinManzanni. = --Qur'an 36:3
    On a straight path. <> A kan hanya madaidaiciya. = --Qur'an 36:4
    [This is] a revelation of the Exalted in Might, the Merciful, <> (Allah Ya saukar da Al-kur'ãni) saukarwar Mabuwãyi, Mai jin ƙai. = --Qur'an 36:5
    That you may warn a people whose forefathers were not warned, so they are unaware. <> Dõmin ka yi gargaɗi ga waɗansu mutãne da ba a yi gargaɗi ga ubanninsu ba, sabõda haka sũmasu rafkana ne. = --Qur'an 36:6
    Already the word has come into effect upon most of them, so they do not believe. <> Lalle, haƙĩƙa, kalma tã wajaba a kan mafi yawansu, dõmin sũ, bã zã su yi ĩmãni ba. = --Qur'an 36:7
    Indeed, We have put shackles on their necks, and they are to their chins, so they are with heads [kept] aloft. <> Lalle Mũ, Mun sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyinsu, sa'an nan sũ (ƙuƙumman sun kai) har zuwa ga haɓõɓinsu, sabõda haka, sũ banƙararru ne. = --Qur'an 36:8
    And We have put before them a barrier and behind them a barrier and covered them, so they do not see. <> Kuma Muka sanya wata tõshiya a gaba gare su, da wata tõshiya a bãyansu, sabõda haka Muka rufe su, sai suka zama bã su gani. = --Qur'an 36:9
    And it is all the same for them whether you warn them or do not warn them - they will not believe. <> Kuma daidai yake a gare su, shin, ka yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, sũ bã zã su yi ĩmãni ba. = --Qur'an 36:10
    You can only warn one who follows the message and fears the Most Merciful unseen. So give him good tidings of forgiveness and noble reward. <> Kanã yin gargaɗi kawai ga wanda ya bi Alƙur'ãni ne, kuma ya ji tsõron mai rahama a fake. To, ka yi masa bushãra da gãfara da wani sakamako na karimci. = --Qur'an 36:11
    Indeed, it is We who bring the dead to life and record what they have put forth and what they left behind, and all things We have enumerated in a clear register. <> Lalle Mũ, Mũ ne ke rãyar da matattu kuma Mu rubũta abin da suka gabãtar, da gurãbunsu, kuma kõwane abu Mun ƙididdige shi, a cikin babban Littãfi Mabayyani. = --Qur'an 36:12
    And present to them an example: the people of the city, when the messengers came to it - <> Kuma ka buga musu misãli: Waɗansu ma'abũta alƙarya, a lõkacin da Manzanni suka jẽ mata. = --Qur'an 36:13
    When We sent to them two but they denied them, so We strengthened them with a third, and they said, "Indeed, we are messengers to you." <> A lõkacin da Muka aika (Manzannin) biyu zuwa gare su, sai suka ƙaryata su, sa'an nan Muka ƙarfafa (su) da na uku, sai suka ce: "Lalle mũ, Manzanni ne zuwa gare ku." = --Qur'an 36:14
    They said, "You are not but human beings like us, and the Most Merciful has not revealed a thing. You are only telling lies." <> Suka ce: "Kũ ba ku zamo bafãce mutãne ne kamarmu kuma Mai rahama bai saukar da kõme ba, ba ku zamo ba fãce ƙarya kuke yi." = --Qur'an 36:15
    They said, "Our Lord knows that we are messengers to you, <> Suka ce: "Ubangijinmu Yã sani, lalle mũ, haƙiƙa Manzanni nezuwa gare ku." = --Qur'an 36:16
    And we are not responsible except for clear notification." <> "Kuma bãbu abin da ke kanmu, fãce iyar da manzanci bayyananne." = --Qur'an 36:17
    They said, "Indeed, we consider you a bad omen. If you do not desist, we will surely stone you, and there will surely touch you, from us, a painful punishment." <> Suka ce: "Lalle mũ munã shu'umci da ku! Haƙĩƙa idan ba ku, hanu ba, haƙĩƙa, zã mu jẽfe ku, kuma haƙĩƙa wata azãba mai raɗaɗi daga gare mu zã ta shãfe ku." = --Qur'an 36:18
    They said, "Your omen is with yourselves. Is it because you were reminded? Rather, you are a transgressing people." <> Suka ce: "Shu'umcinku, yanã tãre da ku. Ashe, dõmin an tunãtar da ku? Ã'a, kũ dai mutãne ne mãsu ƙẽtare haddi." = --Qur'an 36:19
    And there came from the farthest end of the city a man, running. He said, "O my people, follow the messengers. <> Kuma wani mutum daga mafi nĩsan birnin ya je, yanã tafiya da gaggãwa, ya ce: "Ya mutãnẽna! Ku bi Manzannin nan. = --Qur'an 36:20
    Follow those who do not ask of you [any] payment, and they are [rightly] guided. <> "Ku bi waɗanda bã su tambayar ku wata ijãra kuma sũ shiryayyu ne." = --Qur'an 36:21
    And why should I not worship He who created me and to whom you will be returned? <> "Kuma mene ne a gare ni, bã zan bauta wa Wanda Ya ƙãga halittata ba, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku?" = --Qur'an 36:22
    Should I take other than Him [false] deities [while], if the Most Merciful intends for me some adversity, their intercession will not avail me at all, nor can they save me? <> "Shin, zan riƙi waninSa abũbuwan bautãwa? Idan Mai rahama Ya nufe ni da wata cũta, to cẽtonsu bã ya amfanĩna da kõme, kuma bã za su iya tsãmar da ni bã." = --Qur'an 36:23
    Indeed, I would then be in manifest error. <> "Lalle nĩ, a lõkacin nan, tabbas, inã a cikin ɓata bayyananna." = --Qur'an 36:24
    Indeed, I have believed in your Lord, so listen to me." <> "Lalle ni, nã yi ĩmãni da Ubangijinku, sabõda haka ku saurãre ni." = --Qur'an 36:25
    It was said, "Enter Paradise." He said, "I wish my people could know <> Aka ce (masa), "Ka shiga Aljanna." Ya ce, "Dã dai a ce mutãnẽna sunã iya sani." = --Qur'an 36:26
    Of how my Lord has forgiven me and placed me among the honored." <> "Game da gãfarar da Ubangijjĩna ya yi mini, kuma Ya sanya ni a cikin waɗanda aka girmama." = --Qur'an 36:27
    And We did not send down upon his people after him any soldiers from the heaven, nor would We have done so. <> Kuma ba Mu saukar da waɗansu runduna ba daga sama a kan (halaka) mutãnensa, daga bãyansa, kuma bã zã Mu kasance. Mãsu saukarwa ba. = --Qur'an 36:28
    It was not but one shout, and immediately they were extinguished. <> Ba ta kasance ba face tsawa guda, sa'an nan sai gã su sõmammu. = --Qur'an 36:29
    How regretful for the servants. There did not come to them any messenger except that they used to ridicule him. <> Yã nadãma a kan bãyĩNa! Wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu yi masa izgili. = --Qur'an 36:30
    Have they not considered how many generations We destroyed before them - that they to them will not return? <> Ba su gani ba, da yawa Muka halakar da (mutãnen) ƙarnõni a gabãninsu kuma cẽwa su bã zã su kõmo ba? = --Qur'an 36:31
    And indeed, all of them will yet be brought present before Us. <> Kuma lalle bãbu kõwa fãce waɗanda ake halartarwa ne a wurinMu. = --Qur'an 36:32
    And a sign for them is the dead earth. We have brought it to life and brought forth from it grain, and from it they eat. <> Kuma ãyã ce a gare su: ¡asã matacciya, Mu rãyar da ita, Mu fitar da ƙwãya daga gare ta, sai gã shi daga gare ta suke ci. = --Qur'an 36:33
    And We placed therein gardens of palm trees and grapevines and caused to burst forth therefrom some springs - <> Kuma Muka sanya, a cikinta (ƙasã), waɗansu gõnaki na dabĩno da inabõbi, kuma Muka ɓuɓɓugar da ruwa daga marẽmari a cikinta. = --Qur'an 36:34
    That they may eat of His fruit. And their hands have not produced it, so will they not be grateful? <> Dõmin su ci 'ya'yan itãcensa, alhãli kuwa hannãyensu ba su aikata shi ba. Shin, to, bã zã su gõdẽ ba? = --Qur'an 36:35
    Exalted is He who created all pairs - from what the earth grows and from themselves and from that which they do not know. <> Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya halitta nau'uka, namiji da mace, dukansu, daga abin da ƙasã ke tsirarwa, kuma daga kansu, kuma daga abin da ba su sani ba. = --Qur'an 36:36
    And a sign for them is the night. We remove from it [the light of] day, so they are [left] in darkness. <> Kuma ãyã ce a gare su: Dare Muna feɗe rãna daga gare shi, sai gã su sunã mãsu shiga duhu. = --Qur'an 36:37
    And the sun runs [on course] toward its stopping point. That is the determination of the Exalted in Might, the Knowing. <> Kuma rãnã tanã gudãna zuwa ga wani matabbaci nãta. Wannan ƙaddarãwar Mabuwãyi ne, Masani. = --Qur'an 36:38
    And the moon - We have determined for it phases, until it returns [appearing] like the old date stalk. <> Kuma da watã Mun ƙaddara masa manzilõli, har ya kõma kamar tsumagiyar murlin dabĩno wadda ta tsũfa. = --Qur'an 36:39
    It is not allowable for the sun to reach the moon, nor does the night overtake the day, but each, in an orbit, is swimming. <> Rãnã bã ya kamãta a gare ta, ta riski watã. Kuma dare bã ya kamãta a gare shi ya zama mai tsẽre wa yini, kuma dukansua cikin sarari guda suke yin iyo. = --Qur'an 36:40
    And a sign for them is that We carried their forefathers in a laden ship. <> Kuma ãyã ce a gare su. Lalle Mũ, Mun ɗauki zuriyarsu a cikin jirgin, wanda aka yi wa lõdi. = --Qur'an 36:41
    And We created for them from the likes of it that which they ride. <> Kuma Muka halitta musu, daga irinsa, abin da suke hawa. = --Qur'an 36:42
    And if We should will, We could drown them; then no one responding to a cry would there be for them, nor would they be saved <> Kuma idan Mun so, zã Mu nutsar da su, har bãbu kururuwar neman ãgaji, a gare su, kuma ba su zama anã tsirar da su ba. = --Qur'an 36:43
    Except as a mercy from Us and provision for a time. <> Sai fa bisa ga wata rahama daga gare Mu, da jiyarwa dãɗi zuwa ga wani ɗan lõkaci. = --Qur'an 36:44
    But when it is said to them, "Beware of what is before you and what is behind you; perhaps you will receive mercy... " <> Kuma idan aka ce musu, "Ku kãre abin da ke a gaba gare ku da abin da yake a bãyanku, dõmin tsammãninku a ji tausayinku." = --Qur'an 36:45
    And no sign comes to them from the signs of their Lord except that they are from it turning away. <> Kuma wata ãyã daga ãyõyin Ubangijinsu bã ta zuwa a gare su, sai sun kasance sunã mãsu bijirẽwa daga gare ta. = --Qur'an 36:46
    And when it is said to them, "Spend from that which Allah has provided for you," those who disbelieve say to those who believe, "Should we feed one whom, if Allah had willed, He would have fed? You are not but in clear error." <> Kuma idan aka ce musu, "Ku ciyar daga abin da Allah Ya azurta ku," sai waɗanda suka kãfirta su ce ga waɗanda suka yi ĩmãni, "Ashe, zã mu ciyar da wanda idan Allah Ya so Yanã ciyar da shi? Ba ku zama ba fãce a cikin ɓata bayyananniya." = --Qur'an 36:47
    And they say, "When is this promise, if you should be truthful?" <> Kuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi yake (aukuwa) idan kun kasance mãsu gaskiya?" = --Qur'an 36:48
    They do not await except one blast which will seize them while they are disputing. <> Bã su jiran (kõme) fãce wata tsãwa guda, zã ta kãma su, alhãli kuwa sunã yin husũma. = --Qur'an 36:49
    And they will not be able [to give] any instruction, nor to their people can they return. <> Bã zã su iya yin wasiyya ba, kuma bã zã su iya kõmãwa zuwa ga iyãlansu ba. = --Qur'an 36:50
    And the Horn will be blown; and at once from the graves to their Lord they will hasten. <> Kuma aka yi bũsa a cikin ƙaho, to, sai gã su, daga kaburbura zuwa ga Ubangijinsu, sunã ta gudu. = --Qur'an 36:51
    They will say, "O woe to us! Who has raised us up from our sleeping place?" [The reply will be], "This is what the Most Merciful had promised, and the messengers told the truth." <> Suka ce: "Yã bonenmu! Wãne ne ya tãyar da mu daga barcinmu?" "Wannan shi ne abin da Mai rahama ya yi wa'adi da shi, kuma Manzanni sun yi gaskiya." = --Qur'an 36:52
    It will not be but one blast, and at once they are all brought present before Us. <> Ba ta kasance ba fãce wata tsãwa ce guda, sai gã su duka, sunã abin halartarwa a gare Mu. = --Qur'an 36:53
    So today no soul will be wronged at all, and you will not be recompensed except for what you used to do. <> To, a yau, bã zã a zãlunci wani rai da kõme ba. Kuma bã zã a sãkã muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. = --Qur'an 36:54
    Indeed the companions of Paradise, that Day, will be amused in [joyful] occupation - <> Lalle, 'yan Aljanna, a yau, sunã cikin shagali, sunã mãsu nishãɗi. = --Qur'an 36:55
    They and their spouses - in shade, reclining on adorned couches. <> Sũ da mãtan aurensu sunã cikin inuwõwi, a kan karagai, sunã mãsu gincira. = --Qur'an 36:56
    For them therein is fruit, and for them is whatever they request [or wish] <> Sunã da, 'ya'yan itãcen marmari a cikinta kuma sunã sãmun abin da suke kiran a kãwo. = --Qur'an 36:57
    [And] "Peace," a word from a Merciful Lord. <> "Aminci," da magana, daga Ubangiji Mai jin ƙai. = --Qur'an 36:58
    [Then He will say], "But stand apart today, you criminals. <> "Ku rarrabe dabam, a yau, yã kũ mãsu laifi!" = --Qur'an 36:59
    Did I not enjoin upon you, O children of Adam, that you not worship Satan - [for] indeed, he is to you a clear enemy - <> "Ashe, ban yi muku umurni na alkawari ba, yã ɗiyan Ãdamu? Cẽwa kada ku bauta wa Shaiɗan, lalle shĩ, maƙiyi ne a gareku bayyananne?" = --Qur'an 36:60
    And that you worship [only] Me? This is a straight path. <> "Kuma ku bauta Mini. Wannan ita ce hanya madaidaciya." = --Qur'an 36:61
    And he had already led astray from among you much of creation, so did you not use reason? <> "Kuma lalle haƙĩƙa, (Shaiɗan) yã ɓatar da jama'a mãsu yawa daga gare ku. Ashe to ba ku kasance kunã yin hankali ba?" = --Qur'an 36:62
    This is the Hellfire which you were promised. <> "Wannan ita ce Jahannama wadda kuka kasance anã yi muku wa'adi da ita." = --Qur'an 36:63
    [Enter to] burn therein today for what you used to deny." <> "Ku shigẽ ta a yau, sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci." = --Qur'an 36:64
    That Day, We will seal over their mouths, and their hands will speak to Us, and their feet will testify about what they used to earn. <> A yau, Munã sanya hãtimin rufi a kan bãkunansu, kuma hannãyensu su yi Mana magana, kuma ƙafãfunsu su yi shaidu da abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 36:65
    And if We willed, We could have obliterated their eyes, and they would race to [find] the path, and how could they see? <> Dã Mun so, dã Mun shãfe gani daga idãnunsu, sai su yi tsẽre ga hanya, to, yaya zã su yi gani? = --Qur'an 36:66
    And if We willed, We could have deformed them, [paralyzing them] in their places so they would not be able to proceed, nor could they return. <> Kuma da Mun so, da Mun juyar da halittarsu a kan halinsu, saboda haka ba zã su iya shuɗewa ba, kuma ba zã su komo ba. = --Qur'an 36:67
    And he to whom We grant long life We reverse in creation; so will they not understand? <> Kuma wanda Muka rãya shi, Manã sunkuyar da shi ga halittarsa. Ashe, bã su hankalta? = --Qur'an 36:68
    And We did not give Prophet Muhammad, knowledge of poetry, nor is it befitting for him. It is not but a message and a clear Qur'an <> Ba Mu sanar da shi (Annabi) wãkã ba, kuma wãkã ba ta kamãta da shi (Annabi) ba. Shi (Al-ƙur'ãni) bai zama ba fãce tunãtarwa ce, da abin karãtu bayyananne. = --Qur'an 36:69
    To warn whoever is alive and justify the word against the disbelievers. <> Dõmin ya yi gargaɗi ga wanda ya kasance mai rai, kuma magana ta wajaba a kan kãfirai. = --Qur'an 36:70
    Do they not see that We have created for them from what Our hands have made, grazing livestock, and [then] they are their owners? <> Shin, ba su gani ba (cẽwa) lalle Mun halitta musu dabbõbi daga abin da HannayenMu suka aikata, sai sunã mallakar su? = --Qur'an 36:71
    And We have tamed them for them, so some of them they ride, and some of them they eat. <> Kuma Muka hõre su, sabõda su, sabõda haka daga gare su abin hawansu yake, kuma daga gare su suke ci. = --Qur'an 36:72
    And for them therein are [other] benefits and drinks, so will they not be grateful? <> Kuma sunã da waɗansu amfãnõni a cikinsu, da abũbuwan shã. Ashe fa, bã zã; su gõdẽ ba? = --Qur'an 36:73
    But they have taken besides Allah [false] deities that perhaps they would be helped. <> Kuma suka riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa wanin Allah, ɗammãninsu zã su taimake su. = --Qur'an 36:74
    They are not able to help them, and they [themselves] are for them soldiers in attendance. <> Bã zã su iya taimakonsu ba, alhãli kuwa sũ runduna ce wadda ake halartarwa (a cikin wutã). = --Qur'an 36:75
    So let not their speech grieve you. Indeed, We know what they conceal and what they declare. <> Sabõda haka, kada maganarsu ta ɓãta maka rai. Lalle Mũ, Munã sanin abin da suke asirtãwa da abin da suke bayyanãwa. = --Qur'an 36:76
    Does man not consider that We created him from a [mere] sperm-drop - then at once he is a clear adversary? <> Ashe, kuma mutum bai ga (cẽwa) lalle Mũ, Mun halitta shi daga maniyyi ba, sai gã shi mai yawan husũma, mai bayyanãwar husũmar. = --Qur'an 36:77
    And he presents for Us an example and forgets his [own] creation. He says, "Who will give life to bones while they are disintegrated?" <> Kuma ya buga Mana wani misãli, kuma ya manta da halittarsa, ya ce: "Wãne ne ke rãyar da ƙasũsuwa alhãli kuwa sunã rududdugaggu?" = --Qur'an 36:78
    Say, "He will give them life who produced them the first time; and He is, of all creation, Knowing." <> Ka ce: "Wanda ya ƙãga halittarsu a farkon lõkaci Shĩ ke rãyar da su, kuma Shi, game da kõwace halitta, Mai ilmi ne." = --Qur'an 36:79
    [It is] He who made for you from the green tree, fire, and then from it you ignite. <> "Wanda ya sanya muku wutã daga itãce kõre, sai gã ku kunã kunnãwa daga gare shi." = --Qur'an 36:80
    Is not He who created the heavens and the earth Able to create the likes of them? Yes, [it is so]; and He is the Knowing Creator. <> "Shin, kuma Wanda Ya halitta sammai da ƙasã bai zama Mai ĩkon yi ba ga Ya halitta kwatankwacinsu? Na'am, zai iya! Kuma Shĩ Mai yawan halittãwa ne, Mai ilmi." = --Qur'an 36:81
    His command is only when He intends a thing that He says to it, "Be," and it is. <> UmurninSa idan Yã yi nufin wani abu sai Ya ce masa kawai, "Ka kasance," sai yana kasancewa (kamar yadda Yake nufi). = --Qur'an 36:82
    So exalted is He in whose hand is the realm of all things, and to Him you will be returned. <> Sabõda haka, tsarki yã tabbata ga Wanda mallakar kõwane abu take ga HannãyenSa, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku. = --Qur'an 36:83
    By those [angels] lined up in rows <> Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi). = --Qur'an 37:1
    And those who drive [the clouds] <> Sa'an nan mãsu yin tsãwa dõmin gargaɗi. = --Qur'an 37:2
    And those who recite the message, <> Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa. = --Qur'an 37:3
    Indeed, your God is One, <> Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne. = --Qur'an 37:4
    Lord of the heavens and the earth and that between them and Lord of the sunrises. <> Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã. = --Qur'an 37:5
    Indeed, We have adorned the nearest heaven with an adornment of stars <> Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri. = --Qur'an 37:6
    And as protection against every rebellious devil <> Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai. = --Qur'an 37:7
    [So] they may not listen to the exalted assembly [of angels] and are pelted from every side, <> Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe. = --Qur'an 37:8
    Repelled; and for them is a constant punishment, <> Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya. = --Qur'an 37:9
    Except one who snatches [some words] by theft, but they are pursued by a burning flame, piercing [in brightness]. <> Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi. = --Qur'an 37:10
    Then inquire of them, [O Muhammad], "Are they a stronger [or more difficult] creation or those [others] We have created?" Indeed, We created men from sticky clay. <> Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri. = --Qur'an 37:11
    But you wonder, while they mock, <> Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili. = --Qur'an 37:12
    And when they are reminded, they remember not. <> Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa. = --Qur'an 37:13
    And when they see a sign, they ridicule <> Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili. = --Qur'an 37:14
    And say, "This is not but obvious magic. <> Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne." = --Qur'an 37:15
    When we have died and become dust and bones, are we indeed to be resurrected? <> "Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne? = --Qur'an 37:16
    And our forefathers [as well]?" <> "Ashe kõ da ubanninmu na farko?" = --Qur'an 37:17
    Say, "Yes, and you will be [rendered] contemptible." <> Ka ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu." = --Qur'an 37:18
    It will be only one shout, and at once they will be observing. <> Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi. = --Qur'an 37:19
    They will say, "O woe to us! This is the Day of Recompense." <> Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako." = --Qur'an 37:20
    [They will be told], "This is the Day of Judgement which you used to deny." <> Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa. = --Qur'an 37:21
    [The angels will be ordered], "Gather those who committed wrong, their kinds, and what they used to worship <> Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa. = --Qur'an 37:22
    Other than Allah, and guide them to the path of Hellfire <> Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm. = --Qur'an 37:23
    And stop them; indeed, they are to be questioned." <> Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne. = --Qur'an 37:24
    [They will be asked], "What is [wrong] with you? Why do you not help each other?" <> Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna? = --Qur'an 37:25
    But they, that Day, are in surrender. <> Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne. = --Qur'an 37:26
    And they will approach one another blaming each other. <> Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna. = --Qur'an 37:27
    They will say, "Indeed, you used to come at us from the right." <> Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)." = --Qur'an 37:28
    The oppressors will say, "Rather, you [yourselves] were not believers, <> Suka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba. = --Qur'an 37:29
    And we had over you no authority, but you were a transgressing people. <> "Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka." = --Qur'an 37:30
    So the word of our Lord has come into effect upon us; indeed, we will taste [punishment]. <> "Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne." = --Qur'an 37:31
    And we led you to deviation; indeed, we were deviators." <> "Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu." = --Qur'an 37:32
    So indeed they, that Day, will be sharing in the punishment. <> To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar. = --Qur'an 37:33
    Indeed, that is how We deal with the criminals. <> Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi. = --Qur'an 37:34
    Indeed they, when it was said to them, "There is no deity but Allah," were arrogant <> Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai. = --Qur'an 37:35
    And were saying, "Are we to leave our gods for a mad poet?" <> Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci? = --Qur'an 37:36
    Rather, the Prophet has come with the truth and confirmed the [previous] messengers. <> Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni. = --Qur'an 37:37
    Indeed, you [disbelievers] will be tasters of the painful punishment, <> Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne. = --Qur'an 37:38
    And you will not be recompensed except for what you used to do - <> Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. = --Qur'an 37:39
    But not the chosen servants of Allah. <> Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. = --Qur'an 37:40
    Those will have a provision determined - <> Waɗannan sunã da abinci sananne. = --Qur'an 37:41
    Fruits; and they will be honored <> 'Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa. = --Qur'an 37:42
    In gardens of pleasure <> A cikin gidãjen Aljannar ni'ima. = --Qur'an 37:43
    On thrones facing one another. <> A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna. = --Qur'an 37:44
    There will be circulated among them a cup [of wine] from a flowing spring, <> Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari. = --Qur'an 37:45
    White and delicious to the drinkers; <> Farã mai dãɗi ga mashãyan. = --Qur'an 37:46
    No bad effect is there in it, nor from it will they be intoxicated. <> A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba, = --Qur'an 37:47
    And with them will be women limiting [their] glances, with large, [beautiful] eyes, <> Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu. = --Qur'an 37:48
    As if they were [delicate] eggs, well-protected. <> Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye. = --Qur'an 37:49
    And they will approach one another, inquiring of each other. <> Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna. = --Qur'an 37:50
    A speaker among them will say, "Indeed, I had a companion [on earth] <> Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)." = --Qur'an 37:51
    Who would say, 'Are you indeed of those who believe <> Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?" = --Qur'an 37:52
    That when we have died and become dust and bones, we will indeed be recompensed?'" <> "Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?" = --Qur'an 37:53
    He will say, "Would you [care to] look?" <> (Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?" = --Qur'an 37:54
    And he will look and see him in the midst of the Hellfire. <> Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim. = --Qur'an 37:55
    He will say, "By Allah, you almost ruined me. <> Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni." = --Qur'an 37:56
    If not for the favor of my Lord, I would have been of those brought in [to Hell]. <> "Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)." = --Qur'an 37:57
    Then, are we not to die <> "Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba." = --Qur'an 37:58
    Except for our first death, and we will not be punished?" <> "Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?" = --Qur'an 37:59
    Indeed, this is the great attainment. <> Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma. = --Qur'an 37:60
    For the like of this let the workers [on earth] work. <> Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa. = --Qur'an 37:61
    Is Paradise a better accommodation or the tree of zaqqum? <> Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm? = --Qur'an 37:62
    Indeed, We have made it a torment for the wrongdoers. <> Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai. = --Qur'an 37:63
    Indeed, it is a tree issuing from the bottom of the Hellfire, <> Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm. = --Qur'an 37:64
    Its emerging fruit as if it was heads of the devils. <> Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne. = --Qur'an 37:65
    And indeed, they will eat from it and fill with it their bellies. <> To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta. = --Qur'an 37:66
    Then indeed, they will have after it a mixture of scalding water. <> Sa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi. = --Qur'an 37:67
    Then indeed, their return will be to the Hellfire. <> Sa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take. = --Qur'an 37:68
    Indeed they found their fathers astray. <> Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu. = --Qur'an 37:69
    So they hastened [to follow] in their footsteps. <> Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa. = --Qur'an 37:70
    And there had already strayed before them most of the former peoples, <> Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu. = --Qur'an 37:71
    And We had already sent among them warners. <> Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu. = --Qur'an 37:72
    Then look how was the end of those who were warned - <> Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance. = --Qur'an 37:73
    But not the chosen servants of Allah. <> Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. = --Qur'an 37:74
    And Noah had certainly called Us, and [We are] the best of responders. <> Kuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu. = --Qur'an 37:75
    And We saved him and his family from the great affliction. <> Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba. = --Qur'an 37:76
    And We made his descendants those remaining [on the earth] <> Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa. = --Qur'an 37:77
    And left for him [favorable mention] among later generations: <> Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe. = --Qur'an 37:78
    "Peace upon Noah among the worlds." <> Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu. = --Qur'an 37:79
    Indeed, We thus reward the doers of good. <> Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. = --Qur'an 37:80
    Indeed, he was of Our believing servants. <> Lalle shi, yanã daga bãyinMu mũminai. = --Qur'an 37:81
    Then We drowned the disbelievers. <> Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu. = --Qur'an 37:82
    And indeed, among his kind was Abraham, <> Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake. = --Qur'an 37:83
    When he came to his Lord with a sound heart <> A lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya. = --Qur'an 37:84
    [And] when he said to his father and his people, "What do you worship? <> A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa?" = --Qur'an 37:85
    Is it falsehood [as] gods other than Allah you desire? <> "Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?" = --Qur'an 37:86
    Then what is your thought about the Lord of the worlds?" <> "To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?" = --Qur'an 37:87
    And he cast a look at the stars <> Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri. = --Qur'an 37:88
    And said, "Indeed, I am [about to be] ill." <> Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne." = --Qur'an 37:89
    So they turned away from him, departing. <> Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya. = --Qur'an 37:90
    Then he turned to their gods and said, "Do you not eat? <> Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba? = --Qur'an 37:91
    What is [wrong] with you that you do not speak?" <> "Me ya sãme ku, bã ku magana?" = --Qur'an 37:92
    And he turned upon them a blow with [his] right hand. <> Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma. = --Qur'an 37:93
    Then the people came toward him, hastening. <> Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa. = --Qur'an 37:94
    He said, "Do you worship that which you [yourselves] carve, <> Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa, = --Qur'an 37:95
    While Allah created you and that which you do?" <> "Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?" = --Qur'an 37:96
    They said, "Construct for him a furnace and throw him into the burning fire." <> Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm." = --Qur'an 37:97
    And they intended for him a plan, but We made them the most debased. <> Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci. = --Qur'an 37:98
    And [then] he said, "Indeed, I will go to [where I am ordered by] my Lord; He will guide me. <> Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni." = --Qur'an 37:99
    My Lord, grant me [a child] from among the righteous." <> "Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne." = --Qur'an 37:100
    So We gave him good tidings of a forbearing boy. <> Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri. = --Qur'an 37:101
    And when he reached with him [the age of] exertion, he said, "O my son, indeed I have seen in a dream that I [must] sacrifice you, so see what you think." He said, "O my father, do as you are commanded. You will find me, if Allah wills, of the steadfast." <> To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri." = --Qur'an 37:102
    And when they had both submitted and he put him down upon his forehead, <> To, a lõkacin da suka yi sallama, (Ibrahĩm) ya kãyar da shi ga gẽfen gõshinsa. = --Qur'an 37:103
    We called to him, "O Abraham, <> Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm!" = --Qur'an 37:104
    You have fulfilled the vision." Indeed, We thus reward the doers of good. <> "Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. = --Qur'an 37:105
    Indeed, this was the clear trial. <> Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna. = --Qur'an 37:106
    And We ransomed him with a great sacrifice, <> Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma. = --Qur'an 37:107
    And We left for him [favorable mention] among later generations: <> Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe. = --Qur'an 37:108
    "Peace upon Abraham." <> Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm. = --Qur'an 37:109
    Indeed, We thus reward the doers of good. <> Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. = --Qur'an 37:110
    Indeed, he was of Our believing servants. <> Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai. = --Qur'an 37:111
    And We gave him good tidings of Isaac, a prophet from among the righteous. <> Kuma Muka yi masa bushãra Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne. = --Qur'an 37:112
    And We blessed him and Isaac. But among their descendants is the doer of good and the clearly unjust to himself. <> Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin). = --Qur'an 37:113
    And We did certainly confer favor upon Moses and Aaron. <> Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna. = --Qur'an 37:114
    And We saved them and their people from the great affliction, <> Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma. = --Qur'an 37:115
    And We supported them so it was they who overcame. <> Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya. = --Qur'an 37:116
    And We gave them the explicit Scripture, <> Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni. = --Qur'an 37:117
    And We guided them on the straight path. <> Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya. = --Qur'an 37:118
    And We left for them [favorable mention] among later generations: <> Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe. = --Qur'an 37:119
    "Peace upon Moses and Aaron." <> Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna. = --Qur'an 37:120
    Indeed, We thus reward the doers of good. <> Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. = --Qur'an 37:121
    Indeed, they were of Our believing servants. <> Lalle, sunã daga bãyinMu mũminai. = --Qur'an 37:122
    And indeed, Elias was from among the messengers, <> Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. = --Qur'an 37:123
    When he said to his people, "Will you not fear Allah? <> A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?" = --Qur'an 37:124
    Do you call upon Ba'l and leave the best of creators - <> "Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?" = --Qur'an 37:125
    Allah, your Lord and the Lord of your first forefathers?" <> "Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko?" = --Qur'an 37:126
    And they denied him, so indeed, they will be brought [for punishment], <> Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã). = --Qur'an 37:127
    Except the chosen servants of Allah. <> Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. = --Qur'an 37:128
    And We left for him [favorable mention] among later generations: <> Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe. = --Qur'an 37:129
    "Peace upon Elias." <> Aminci ya tabbata ga Ilyãs. = --Qur'an 37:130
    Indeed, We thus reward the doers of good. <> Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. = --Qur'an 37:131
    Indeed, he was of Our believing servants. <> Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai. = --Qur'an 37:132
    And indeed, Lot was among the messengers. <> Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. = --Qur'an 37:133
    [So mention] when We saved him and his family, all, <> A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya. = --Qur'an 37:134
    Except his wife among those who remained [with the evildoers]. <> Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba). = --Qur'an 37:135
    Then We destroyed the others. <> Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen. = --Qur'an 37:136
    And indeed, you pass by them in the morning <> Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci. = --Qur'an 37:137
    And at night. Then will you not use reason? <> Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba? = --Qur'an 37:138
    And indeed, Jonah was among the messengers. <> Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. = --Qur'an 37:139
    [Mention] when he ran away to the laden ship. <> A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi. = --Qur'an 37:140
    And he drew lots and was among the losers. <> Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya. = --Qur'an 37:141
    Then the fish swallowed him, while he was blameworthy. <> Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi. = --Qur'an 37:142
    And had he not been of those who exalt Allah, <> To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba, = --Qur'an 37:143
    He would have remained inside its belly until the Day they are resurrected. <> Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su. = --Qur'an 37:144
    But We threw him onto the open shore while he was ill. <> Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya. = --Qur'an 37:145
    And We caused to grow over him a gourd vine. <> Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi. = --Qur'an 37:146
    And We sent him to [his people of] a hundred thousand or more. <> Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka). = --Qur'an 37:147
    And they believed, so We gave them enjoyment [of life] for a time. <> Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci. = --Qur'an 37:148
    So inquire of them, [O Muhammad], "Does your Lord have daughters while they have sons? <> Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?" = --Qur'an 37:149
    Or did We create the angels as females while they were witnesses?" <> Kõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce? = --Qur'an 37:150
    Unquestionably, it is out of their [invented] falsehood that they say, <> To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa. = --Qur'an 37:151
    " Allah has begotten," and indeed, they are liars. <> "Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne. = --Qur'an 37:152
    Has He chosen daughters over sons? <> Shin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza? = --Qur'an 37:153
    What is [wrong] with you? How do you make judgement? <> Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannanhukunci)? = --Qur'an 37:154
    Then will you not be reminded? <> Shin, bã ku tunãni? = --Qur'an 37:155
    Or do you have a clear authority? <> Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne? = --Qur'an 37:156
    Then produce your scripture, if you should be truthful. <> To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya. = --Qur'an 37:157
    And they have claimed between Him and the jinn a lineage, but the jinn have already known that they [who made such claims] will be brought to [punishment]. <> Kuma suka sanya nasaba a tsakãninSa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)" = --Qur'an 37:158
    Exalted is Allah above what they describe, <> Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa. = --Qur'an 37:159
    Except the chosen servants of Allah [who do not share in that sin]. <> Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. = --Qur'an 37:160
    So indeed, you [disbelievers] and whatever you worship, <> To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa, = --Qur'an 37:161
    You cannot tempt [anyone] away from Him <> Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi. = --Qur'an 37:162
    Except he who is to [enter and] burn in the Hellfire. <> Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm. = --Qur'an 37:163
    [The angels say], "There is not among us any except that he has a known position. <> "Kuma bãbu kõwa daga cikinmu, fãce yanã da matsayi sananne." = --Qur'an 37:164
    And indeed, we are those who line up [for prayer]. <> "Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)." = --Qur'an 37:165
    And indeed, we are those who exalt Allah." <> "Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi." = --Qur'an 37:166
    And indeed, the disbelievers used to say, <> Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa, = --Qur'an 37:167
    "If we had a message from [those of] the former peoples, <> "Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko." = --Qur'an 37:168
    We would have been the chosen servants of Allah." <> "Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake." = --Qur'an 37:169
    But they disbelieved in it, so they are going to know. <> Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani. = --Qur'an 37:170
    And Our word has already preceded for Our servants, the messengers, <> Kuma lalle, haƙĩƙa kalmarMu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni. = --Qur'an 37:171
    [That] indeed, they would be those given victory <> Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako. = --Qur'an 37:172
    And [that] indeed, Our soldiers will be those who overcome. <> Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya. = --Qur'an 37:173
    So, [O Muhammad], leave them for a time. <> Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci. = --Qur'an 37:174
    And see [what will befall] them, for they are going to see. <> Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani. = --Qur'an 37:175
    Then for Our punishment are they impatient? <> Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa? = --Qur'an 37:176
    But when it descends in their territory, then evil is the morning of those who were warned. <> To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana. = --Qur'an 37:177
    And leave them for a time. <> Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci. = --Qur'an 37:178
    And see, for they are going to see. <> Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa. = --Qur'an 37:179
    Exalted is your Lord, the Lord of might, above what they describe. <> Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa. = --Qur'an 37:180
    And peace upon the messengers. <> Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni. = --Qur'an 37:181
    And praise to Allah, Lord of the worlds. <> Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu. = --Qur'an 37:182
    Sad. By the Qur'an containing reminder... <> Ṣ̃, Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni mai hukunce-hukunce. = --Qur'an 38:1
    But those who disbelieve are in pride and dissension. <> Ã'a, waɗanda suka kãfirta sunã cikin girman kai (ga rikon al'ãdunsu) da sãɓãni (tsakãnin jũnansu). = --Qur'an 38:2
    How many a generation have We destroyed before them, and they [then] called out; but it was not a time for escape. <> Da yawa Muka halakar da wani ƙarni, a gabãninsu, suka yi kira (nẽman cẽto), bãbu lõkacin kuɓucewa. = --Qur'an 38:3
    And they wonder that there has come to them a warner from among themselves. And the disbelievers say, "This is a magician and a liar. <> Kuma suka yi mãmãki dõmin Mai gargaɗi, daga cikinsu, ya je musu. Kuma kãfirai sukace, "Wannan mai sihiri ne, maƙaryaci." = --Qur'an 38:4
    Has he made the gods [only] one God? Indeed, this is a curious thing." <> "Shin, yã sanya gumãka duka su zama abin bautawa guda? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu ne mai ban mãmaki!" = --Qur'an 38:5
    And the eminent among them went forth, [saying], "Continue, and be patient over [the defense of] your gods. Indeed, this is a thing intended. <> Shũgabanni daga cikinsu, suka tafi (suka ce),"Ku yi tafiyarku, ku yi haƙuri a kan abũbuwan bautawarku. Lalle wannan, haƙiƙa, wani abu ne ake nufi!" = --Qur'an 38:6
    We have not heard of this in the latest religion. This is not but a fabrication. <> "Ba mu taɓa ji ba, game da wannan a cikin addinin ƙarshe. Wannan bai zama ba fãce ƙiren ƙarya." = --Qur'an 38:7
    Has the message been revealed to him out of [all of] us?" Rather, they are in doubt about My message. Rather, they have not yet tasted My punishment. <> "Shin, an saukar da Alƙur'ãni ne a kansa, a tsakãninmu (mũ kuma ba mu gani ba)?" Ã'a, su dai sunã cikin shakka daga hukunciNa Ã'a, ba su i da ɗanɗanar azãba ba. = --Qur'an 38:8
    Or do they have the depositories of the mercy of your Lord, the Exalted in Might, the Bestower? <> Ko kuma a wurinsu ne ake ajiye taskõkin rahamar Ubangijinka, Mabuwãyi, Mai yawan kyauta? = --Qur'an 38:9
    Or is theirs the dominion of the heavens and the earth and what is between them? Then let them ascend through [any] ways of access. <> Kõ kuma sũ ne da mallakar sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu? To sai su hau a cikin sammai (dõmin, su hana saukar Alƙur'ãni ga Muhammadu). = --Qur'an 38:10
    [They are but] soldiers [who will be] defeated there among the companies [of disbelievers]. <> Rundunõni ne abin da ke can, rusassu, na ƙungiyõyinsu. = --Qur'an 38:11
    The people of Noah denied before them, and [the tribe of] 'Aad and Pharaoh, the owner of stakes, <> Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, da Ãdãwa da Fir'auna mai turãkun (da suka kafe mulkinsa). = --Qur'an 38:12
    And [the tribe of] Thamud and the people of Lot and the companions of the thicket. Those are the companies. <> Da Samũdãwa da mutãnen Luɗu da ma'abũta ƙunci, waɗancan ne ƙungiyõyin. = --Qur'an 38:13
    Each of them denied the messengers, so My penalty was justified. <> Bãbu kõwa a cikinsu fãce ya ƙaryata Manzanni, sabõda haka azãbãTa ta wajaba. = --Qur'an 38:14
    And these [disbelievers] await not but one blast [of the Horn]; for it there will be no delay. <> Kuma waɗannan bã su jiran kõme fãce tsãwã guda, wadda bã ta da hani. = --Qur'an 38:15
    And they say, "Our Lord, hasten for us our share [of the punishment] before the Day of Account" <> Kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka gaggauta mana da rabonmu, a gabãnin rãnar bincike." = --Qur'an 38:16
    Be patient over what they say and remember Our servant, David, the possessor of strength; indeed, he was one who repeatedly turned back [to Allah]. <> Ka yi haƙuri bisa ga abin da suke faɗa (na izgili), kuma ka ambaci bãwanMu Dãwũda ma'abũcin ƙarfin ibãda. Lalle, shi, mai mayar da al'amari ga Allah ne. = --Qur'an 38:17
    Indeed, We subjected the mountains [to praise] with him, exalting [Allah] in the [late] afternoon and [after] sunrise. <> Lalle Mũ, Mun hõre duwãtsu tãre da shi, sunã yin tasbĩhi maraice da fitõwar rãnã. = --Qur'an 38:18
    And the birds were assembled, all with him repeating [praises]. <> Da tsuntsãye waɗanda ake tattarawa, kõwannensu mai kõmãwa ne a gare shi. = --Qur'an 38:19
    And We strengthened his kingdom and gave him wisdom and discernment in speech. <> Kuma Muka ƙarfafa mulkinsa, kuma Muka bã shi hikima da rarrabẽwar magana. = --Qur'an 38:20
    And has there come to you the news of the adversaries, when they climbed over the wall of [his] prayer chamber - <> Kuma shin, lãbãrin mãsu husũma ya zo maka, a lõkacin da suka haura gãrun masallaci? = --Qur'an 38:21
    When they entered upon David and he was alarmed by them? They said, "Fear not. [We are] two adversaries, one of whom has wronged the other, so judge between us with truth and do not exceed [it] and guide us to the sound path. <> A lõkacin da suka shiga ga Dãwũda, sai ya firgita daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro, masu husuma biyu ne; sãshenmu ya zãlunci sãshe. Sabõda haka, ka yi hakunci a tsakãninmu da gaskiya. Kada ka ƙẽtare haddi kuma ka shiryar da mu zuwa, ga tsakar hanya." = --Qur'an 38:22
    Indeed this, my brother, has ninety-nine ewes, and I have one ewe; so he said, 'Entrust her to me,' and he overpowered me in speech." <> "Lalle wannan dan'uwãna ne, yanã da tunkiya casa'in da tara, kuma inã da tunkiya guda, sai ya ce: 'Ka lãmunce mini ita. Kuma ya buwãye ni ga magana." = --Qur'an 38:23
    [David] said, "He has certainly wronged you in demanding your ewe [in addition] to his ewes. And indeed, many associates oppress one another, except for those who believe and do righteous deeds - and few are they." And David became certain that We had tried him, and he asked forgiveness of his Lord and fell down bowing [in prostration] and turned in repentance [to Allah]. <> (Dãwũda) ya ce: "Lalle, haƙiƙa ya zãlunce ka game da tambayar tunkiyarka zuwa ga tumakinsa. Kuma lalle ne mãsu yawa daga abõkan tarayya, haƙiƙa, sãshensu na zambatar sãshe fãce waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai." Kuma Dãwũda ya tabbata cẽwa Mun fitine shi ne, sabõda haka, ya nẽmi Ubangijinsa gãfara, kuma ya fãɗi yanã mai sujada, kuma ya mayar da al'amari ga Allah. = --Qur'an 38:24
    So We forgave him that; and indeed, for him is nearness to Us and a good place of return. <> Sabõda haka Muka gãfarta masa wancan, kuma lalle yanã da wata kusantar daraja a wurinMu, da kyaun makõma. = --Qur'an 38:25
    [We said], "O David, indeed We have made you a successor upon the earth, so judge between the people in truth and do not follow [your own] desire, as it will lead you astray from the way of Allah." Indeed, those who go astray from the way of Allah will have a severe punishment for having forgotten the Day of Account. <> Yã Dãwũda! Lalle Mũ Mun sanya ka Halĩfa a cikin ƙasã. To, ka yi hukunci tsakãnin mutãne da gaskiya, kuma kada ka biye wa son zũciyar, har ya ɓatar dakai daga hanyar Allah. Lalle waɗanda ke ɓacẽwa daga hanyar Allah sunã da wata azãba mai tsanani dõmin abin da suka manta, a rãnar hisãbi = --Qur'an 38:26
    And We did not create the heaven and the earth and that between them aimlessly. That is the assumption of those who disbelieve, so woe to those who disbelieve from the Fire. <> Kuma ba Mu halitta sama da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu ba a kan ƙarya. Wannan shĩ ne zaton waɗanda suka kãfirta. To, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga wutã. = --Qur'an 38:27
    Or should we treat those who believe and do righteous deeds like corrupters in the land? Or should We treat those who fear Allah like the wicked? <> Kõ zã Mu sanya waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai kamar waɗanda suke mãsu barna ne a cikin ƙasa? Ko kuma za Mu sanya masu bin Allah da taƙawa kamar fãjirai makarkata? = --Qur'an 38:28
    [This is] a blessed Book which We have revealed to you, [O Muhammad], that they might reflect upon its verses and that those of understanding would be reminded. <> (Wannan) Littãfi ne, Mun saukar da shi zuwa gare ka, yanã, mai albarka, dõmin su lũra da ãyõyinsa, kuma don mãsu hankali su riƙa yin tunãni. = --Qur'an 38:29
    And to David We gave Solomon. An excellent servant, indeed he was one repeatedly turning back [to Allah]. <> Kuma Muka bai wa Dãwũda Sulaimãn. Mãdalla da bãwanMu, shi. Lalle shi (Sulaimãn) mai mayar da al'amari ne ga Allah. = --Qur'an 38:30
    [Mention] when there were exhibited before him in the afternoon the poised [standing] racehorses. <> A lõkacin da aka gitta masa dawãki mãsu asali, a lõkacin maraice. = --Qur'an 38:31
    And he said, "Indeed, I gave preference to the love of good [things] over the remembrance of my Lord until the sun disappeared into the curtain [of darkness]." <> Sai ya ce: "Lalle nĩ, na fĩfĩta son dũkiya daga tunãwar Ubangijina, har (rãnã) ta faku da shãmaki!" = --Qur'an 38:32
    [He said], "Return them to me," and set about striking [their] legs and necks. <> "Ku mayar da su a gare ni." Sai ya shiga yankansu da takõbi ga ƙwabrukansu da wuyõyinsu. = --Qur'an 38:33
    And We certainly tried Solomon and placed on his throne a body; then he returned. <> Kuma lalle haƙĩƙa, Mun fitini Sulaiman kuma Muka jẽfa wani jikin mutum a kan karagarsa. Sa'an nan ya mayar da al'amari zuwa gare Mu. = --Qur'an 38:34
    He said, "My Lord, forgive me and grant me a kingdom such as will not belong to anyone after me. Indeed, You are the Bestower." <> Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka gãfarta mini, kuma Ka bã ni mulki wanda bã ya kamãta da kõwa daga bãyãna. Lalle Kai, Kai ne Mai yawan kyauta. = --Qur'an 38:35
    So We subjected to him the wind blowing by his command, gently, wherever he directed, <> Sabõda haka Muka hõre masa iska tanã gudu da umurninsa, tãna tãshi da sauƙi, inda ya nufa. = --Qur'an 38:36
    And [also] the devils [of jinn] - every builder and diver <> Da shaiɗanu dukan mai gini, da mai nutsa (a cikin kõguna.) = --Qur'an 38:37
    And others bound together in shackles. <> Waɗansu, ɗaɗɗaure a cikin marũruwa. = --Qur'an 38:38
    [We said], "This is Our gift, so grant or withhold without account." <> Wannan kyautarMu ce. Sai ka yi kyauta ga wanda kake so, ko kuma ka riƙe, bãbu wani bincike. = --Qur'an 38:39
    And indeed, for him is nearness to Us and a good place of return. <> Kuma lalle, haƙĩƙa yanã da kusantar daraja a wurinMu da kyaun makõma. = --Qur'an 38:40
    And remember Our servant Job, when he called to his Lord, "Indeed, Satan has touched me with hardship and torment." <> Kuma ka ambaci bãwanMu Ayyũba a lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, ya ce: "Lalle nĩ, Shaiɗan yã shãfe ni da wahala da kuma wata azãba." = --Qur'an 38:41
    [So he was told], "Strike [the ground] with your foot; this is a [spring for] a cool bath and drink." <> Ka shura da ƙafarka. Wannan abin wanka ne mai sanyi da abin shã. = --Qur'an 38:42
    And We granted him his family and a like [number] with them as mercy from Us and a reminder for those of understanding. <> Kuma Muka bã shi iyalansa da kwatankwacinsu tãre da su sabõda rahama daga gare Mu, da tunãtarwa ga mãsu hankali. = --Qur'an 38:43
    [We said], "And take in your hand a bunch [of grass] and strike with it and do not break your oath." Indeed, We found him patient, an excellent servant. Indeed, he was one repeatedly turning back [to Allah]. <> Kuma ka riƙi wata ƙulla da hannunka, ka yi dũka da ita kuma kada ka karya rantsuwarka. Lalle Mũ, Mun sãme shi mai haƙuri. Madalla da bãwa, shĩ Lalle shĩ mai mayar da al'amari ga Allah ne. = --Qur'an 38:44
    And remember Our servants, Abraham, Isaac and Jacob - those of strength and [religious] vision. <> Kuma ka ambaci bãyinMu: Ibrahĩm da ls'hãƙa da Ya'aƙũba, ma'abũta ƙarfin (ɗaukar umurninMu) da basĩra. = --Qur'an 38:45
    Indeed, We chose them for an exclusive quality: remembrance of the home [of the Hereafter]. <> Lalle Mũ, Mun keɓance su game da wata, tsattsarkar aba: Hukunce-hukuncen gidan dũniya (mai tunãtar da su Lãhira). = --Qur'an 38:46
    And indeed they are, to Us, among the chosen and outstanding. <> Kuma lalle sũ a wurinMu, tabbas, sunã daga zãɓaɓɓu, mafĩfĩta. = --Qur'an 38:47
    And remember Ishmael, Elisha and Dhul-Kifl, and all are among the outstanding. <> Kuma ka ambaci Isma'ĩla da llyãs da Zulkifli, kuma dukansu sunã daga zãɓaɓɓu. = --Qur'an 38:48
    This is a reminder. And indeed, for the righteous is a good place of return <> Wannan tunãtarwa ce, kuma lalle mãsu bin Allah da taƙawa, sunã da kyakkyawar makõma. = --Qur'an 38:49
    Gardens of perpetual residence, whose doors will be opened to them. <> Gidãjen Aljannar zama, alhãli kuwa tanã abar buɗe wa kõfõfi sabõda su. = --Qur'an 38:50
    Reclining within them, they will call therein for abundant fruit and drink. <> Sunã gingincire a cikinsu, sunã kira a cikinsu, ga 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, da abin shã. = --Qur'an 38:51
    And with them will be women limiting [their] glances and of equal age. <> Kuma a wurinsu akwai mãtan aure mãsu gajarta ganinsu ga mazansu, tsãrar jũna. = --Qur'an 38:52
    This is what you, [the righteous], are promised for the Day of Account. <> Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi ga rãnar hisãbi. = --Qur'an 38:53
    Indeed, this is Our provision; for it there is no depletion. <> Lalle wannan, haƙĩƙa, azurtarwarMu ce, bã ta ƙãrẽwa. = --Qur'an 38:54
    This [is so]. But indeed, for the transgressors is an evil place of return - <> Wannan shĩ ne kuma lalle makangara, haƙĩƙa, sunã da mafi sharrin makõma. = --Qur'an 38:55
    Hell, which they will [enter to] burn, and wretched is the resting place. <> Jahannama, sunã shigarta. To, shimfiɗar tã mũnana, ita. = --Qur'an 38:56
    This - so let them taste it - is scalding water and [foul] purulence. <> Wannan shĩ ne! To, su ɗanɗane shi: ruwan zãfi ne da ruɓaɓɓen jini. = --Qur'an 38:57
    And other [punishments] of its type [in various] kinds. <> Da wani daga siffarsa nau'i-nau'i. = --Qur'an 38:58
    [Its inhabitants will say], "This is a company bursting in with you. No welcome for them. Indeed, they will burn in the Fire." <> Wannan wani yanki ne mai kũtsawa tãre da ku, bãbu marãba a gare su, lalle sũ, mãsu shiga Wutã ne. = --Qur'an 38:59
    They will say, "Nor you! No welcome for you. You, [our leaders], brought this upon us, and wretched is the settlement." <> Suka ce: "Ã'a, ku ne bãbu marãba a gare ku, kũ ne kuka gabãtar da shi a gare mu." To, matabbatar tã mũnana (ita wutar). = --Qur'an 38:60
    They will say, "Our Lord, whoever brought this upon us - increase for him double punishment in the Fire." <> Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Wanda ya gabãtar da wannan a gare mu, to, Ka ƙãra masa azãba, ninki, a cikin wutã." = --Qur'an 38:61
    And they will say, "Why do we not see men whom we used to count among the worst? <> Kuma suka ce: "Mẽ ya sãme mu, bã mu ganin waɗansu mazãje, mun kasance munã ƙidãya su daga asharãrai?" = --Qur'an 38:62
    Is it [because] we took them in ridicule, or has [our] vision turned away from them?" <> "Shin, mun riƙe su abin izgili ne kõ idãnunmu sun karkata daga gare su ne?" = --Qur'an 38:63
    Indeed, that is truth - the quarreling of the people of the Fire. <> Lalle wannan, haƙĩƙa, gaskiya ne, husũmar mutãnen wutã. = --Qur'an 38:64
    Say, [O Muhammad], "I am only a warner, and there is not any deity except Allah, the One, the Prevailing. <> Ka ce: "Nĩ mai gargaɗikawai ne, kuma babu wani abin bautawa sai Allah, Makaɗaici, Mai tilastawa." = --Qur'an 38:65
    Lord of the heavens and the earth and whatever is between them, the Exalted in Might, the Perpetual Forgiver." <> "Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu Mabuwãyi, Mai gãfara." = --Qur'an 38:66
    Say, "It is great news <> Ka ce: "Shĩ (Alkur'ãni) babban lãbãri ne mai girma". = --Qur'an 38:67
    From which you turn away. <> "Kũ, mãsu bijirẽwa ne daga gare shi!" = --Qur'an 38:68
    I had no knowledge of the exalted assembly [of angels] when they were disputing [the creation of Adam]. <> "Wani ilmi bai kasance a gare ni ba game da jama'a (malã'iku) mafi ɗaukaka a lõkacin da suke yin husũma." = --Qur'an 38:69
    It has not been revealed to me except that I am a clear warner." <> "Ba a yi mini wahayin kõme ba face cẽwa ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyanãwa." = --Qur'an 38:70
    [So mention] when your Lord said to the angels, "Indeed, I am going to create a human being from clay. <> A lõkacin da Ubangijinka Ya ce wa malã'iku, "Lalle Nĩ Mai halitta mutum ne daga lãkã. = --Qur'an 38:71
    So when I have proportioned him and breathed into him of My [created] soul, then fall down to him in prostration." <> "Sa'an nan idan Nã daidaita shi, kuma Na hũra (wani abu) daga RuhĩNa a cikinsa to ku fãɗi kunã mãsu sujada a gare; shi." = --Qur'an 38:72
    So the angels prostrated - all of them entirely. <> Sai malã'ikun suka yi sujada dukansu, gabã ɗaya. = --Qur'an 38:73
    Except Iblees; he was arrogant and became among the disbelievers. <> Fãce Iblis, ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai. = --Qur'an 38:74
    [Allah] said, "O Iblees, what prevented you from prostrating to that which I created with My hands? Were you arrogant [then], or were you [already] among the haughty?" <> (Allah) Ya ce, "Yã Ibilis! Mẽ ya hana ka, ka yi sujada ga abin da Nã halitta da HannayeNa biyu? Shin, kã yi girman kai ne, kõ kuwa kã kasance daga maɗaukaka ne?" = --Qur'an 38:75
    He said, "I am better than him. You created me from fire and created him from clay." <> Ya ce, "Nĩ, mafifici ne daga gare shi: Kã halitta ni daga wutã, kuma Kã halitta shi daga lãkã." = --Qur'an 38:76
    [Allah] said, "Then get out of Paradise, for indeed, you are expelled. <> Ya ce, "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai la'ananne ne." = --Qur'an 38:77
    And indeed, upon you is My curse until the Day of Recompense." <> "Kuma lalle a kanka akwai la'anaTa har zuwa rãnar sakamako." = --Qur'an 38:78
    He said, "My Lord, then reprieve me until the Day they are resurrected." <> Ya ce, "Ya Ubangijina! To, Ka yi mini jinkiri zuwa ga rãnar da ake tãyar da su." = --Qur'an 38:79
    [Allah] said, "So indeed, you are of those reprieved <> Ya ce, "To, lalle kanã daga waɗanda aka yi wa jinkiri, = --Qur'an 38:80
    Until the Day of the time well-known." <> "Zuwa ga yinin lõkaci sananne." = --Qur'an 38:81
    [Iblees] said, "By your might, I will surely mislead them all <> Ya ce, "To, inã rantsuwa da buwãyarKa, lalle, inã ɓatar da su gabã ɗaya. = --Qur'an 38:82
    Except, among them, Your chosen servants." <> "Fãce bãyinKa tsarkakakku daga gare su." = --Qur'an 38:83
    [Allah] said, "The truth [is My oath], and the truth I say - <> (Allah) Ya ce, "To, (wannan magana ita ce) gaskiya. Kuma gaskiya Nake faɗa." = --Qur'an 38:84
    [That] I will surely fill Hell with you and those of them that follow you all together." <> "Lalle zã Ni cika Jahannama daga gare ka, kuma daga wanda ya bĩ ka daga gare su, gabã ɗaya" = --Qur'an 38:85
    Say, [O Muhammad], "I do not ask you for the Qur'an any payment, and I am not of the pretentious <> Ka ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra, a kansa kuma bã ni daga mãsu ƙãƙalen faɗarsa." = --Qur'an 38:86
    It is but a reminder to the worlds. <> "Shĩ (Alkur'ãn) bai zama ba fãce ambato ne ga dukan halitta." = --Qur'an 38:87
    And you will surely know [the truth of] its information after a time." <> "Kuma lalle zã ku san babban lãbãrinsa a bayan ɗan lõkaci." = --Qur'an 38:88
    The revelation of the Qur'an is from Allah, the Exalted in Might, the Wise. <> Saukar da Littãfin daga Allah ne, Mabuwãyi, Mai hikima. = --Qur'an 39:1
    Indeed, We have sent down to you the Book, [O Muhammad], in truth. So worship Allah, [being] sincere to Him in religion. <> Lalle Mũ Mun saukar da Littãfi zuwa gare ka, da gaskiya. Sabõda haka, ka bauta wa Allah kanã mai tsarkake addini a gare Shi. = --Qur'an 39:2
    Unquestionably, for Allah is the pure religion. And those who take protectors besides Him [say], "We only worship them that they may bring us nearer to Allah in position." Indeed, Allah will judge between them concerning that over which they differ. Indeed, Allah does not guide he who is a liar and [confirmed] disbeliever. <> To, addini tsarkakakke na Allah ne, kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majibinta, bã Shi ba, (sunã cẽwa) "Ba mu bauta musu ba fãce dõmin su kusantar da mu zuwa ga Allah, kusantar daraja." Lalle Allah nã yin hukunci a tsakãninsu ga abin da suka zama sunã sãɓãwa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai ƙarya, mai kãfirci. = --Qur'an 39:3
    If Allah had intended to take a son, He could have chosen from what He creates whatever He willed. Exalted is He; He is Allah, the One, the Prevailing. <> Dã Allah Yã yi nufin Ya riƙi ɗã, to, lalle sai Ya zãɓa daga abin da Yake halittãwa abin da Yake so. Tsarki ya tabbata a gare Shi. Shĩ ne Allah, Makaɗaici, Mai tĩlastãwa. = --Qur'an 39:4
    He created the heavens and earth in truth. He wraps the night over the day and wraps the day over the night and has subjected the sun and the moon, each running [its course] for a specified term. Unquestionably, He is the Exalted in Might, the Perpetual Forgiver. <> Ya halitta sammai da ƙasã da gaskiya. Yanã shigar da dare a kan rãna, kuma Yanã shigar da rãnã a kan dare kuma Yã hõre rãnã da watã, kõwannensu yanã gudãna zuwa ga ajali ambatacce. To, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai gãfara. = --Qur'an 39:5
    He created you from one soul. Then He made from it its mate, and He produced for you from the grazing livestock eight mates. He creates you in the wombs of your mothers, creation after creation, within three darknesses. That is Allah, your Lord; to Him belongs dominion. There is no deity except Him, so how are you averted? <> Yã halitta ku daga rai guda, sa'an nan Ya sanya ma'auranta daga gare shi. Kuma ya saukar muku daga dabbõbin gida nau'i takwas Yanã halitta ku a cikin cikunnan uwayenku, halitta a bãyan wata halitta, a cikin duffai uku. Wannan shĩ ne Allah Ubangijinku. Mulki a gare shi yake. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. To, yãya ake karkatar da ku? = --Qur'an 39:6
    If you disbelieve - indeed, Allah is Free from need of you. And He does not approve for His servants disbelief. And if you are grateful, He approves it for you; and no bearer of burdens will bear the burden of another. Then to your Lord is your return, and He will inform you about what you used to do. Indeed, He is Knowing of that within the breasts. <> Idan kun kãfirta to, lalle Allah Wadãtacce ne daga barinku, kuma bã Shi yarda da kãfirci ga bãyinSa, kuma idan kun gõde, Zai yarda da ita (gõdiyar) a gare ku, kuma wani rai mai ɗaukar nauyi, bã ya ɗaukar nauyin wani. Sa'an nan kuma makõmarku zuwa ga Ubangijinku take, dõmin Ya bã ku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. Lalle Shĩ, Masani ne ga abin da yake a ainihin zukata. = --Qur'an 39:7
    And when adversity touches man, he calls upon his Lord, turning to Him [alone]; then when He bestows on him a favor from Himself, he forgets Him whom he called upon before, and he attributes to Allah equals to mislead [people] from His way. Say, "Enjoy your disbelief for a little; indeed, you are of the companions of the Fire." <> Kuma idan wata cũta ta shãfi mutum, sai ya kira Ubangijinsa, yanã mai mai da al'amari zuwa gare Shi, sa'an nan idan Ya jũyar da cũtar da ni'ima ta daga gare Shi, sai ya manta da abin da ya kasance yanã kira zuwa gare shi a gabãnin haka, kuma ya sanya wa Allah waɗansu abõkan tarẽwa dõmin ya ɓatar (da su) daga hanyarSa. Ka ce (masa), "Ka ji dãɗi da kãfircinka, a ɗan lõkaci, lalle kai daga 'yan wutã ne." = --Qur'an 39:8
    Is one who is devoutly obedient during periods of the night, prostrating and standing [in prayer], fearing the Hereafter and hoping for the mercy of his Lord, [like one who does not]? Say, "Are those who know equal to those who do not know?" Only they will remember [who are] people of understanding. <> Shin, wanda yake mai tawãli'u sã'õ'in dare, yanã mai sujada kuma yanã mai tsayi ga salla, yanã tsõron Lãhira, kuma yanã fãtan rahamar Ubangijinsa, (yanã daidai da waninsa?) Ka ce: "Ashe, waɗanda suka sani, sunã daidaita da waɗanda ba su sani ba?" Mãsu hankali kawai ke yin tunãni. = --Qur'an 39:9
    Say, "O My servants who have believed, fear your Lord. For those who do good in this world is good, and the earth of Allah is spacious. Indeed, the patient will be given their reward without account." <> Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩNa waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Ubangijinku da taƙawa. Waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya sunã da sakamako mai kyau, kuma ƙasar Allah mai fãɗi ce. Mãsu haƙuri kawai ake cika wa ijãrarsu, bã da wani lissãfi ba. = --Qur'an 39:10
    Say, [O Muhammad], "Indeed, I have been commanded to worship Allah, [being] sincere to Him in religion. <> Ka ce: "Lalle nĩ, an umurce ni da in bauta wa Allah, inã tsarkake addini a gare Shi. = --Qur'an 39:11
    And I have been commanded to be the first [among you] of the Muslims." <> "Kuma an umurce ni da in kasance farkon mãsu miƙa wuya (ga umurnin Allah)." = --Qur'an 39:12
    Say, "Indeed I fear, if I should disobey my Lord, the punishment of a tremendous Day." <> Ka ce: "Lalle nĩ inã tsõro, idan na sãɓã wa Ubangijĩna, ga azãbar yini mai girma." = --Qur'an 39:13
    Say, "Allah [alone] do I worship, sincere to Him in my religion, <> Ka ce: "Allah nake bautã wa, inã mai tsarkake addinĩna a gare Shi. = --Qur'an 39:14
    So worship what you will besides Him." Say, "Indeed, the losers are the ones who will lose themselves and their families on the Day of Resurrection. Unquestionably, that is the manifest loss." <> "To, ku bauta wa abin da kuke so, waninSa." Ka ce: "Lalle mãsu hasãra, sũ ne waɗanda suka yi hasarar rãyukansu da iyãlansu, a Rãnar ¡iyãma. To, waccan fa, ita ce hasãra bayyananna." = --Qur'an 39:15
    They will have canopies of fire above them and below them, canopies. By that Allah threatens His servants. O My servants, then fear Me. <> Sunã da waɗansu inuwõwi na wutã daga samansu, kuma daga ƙasansu akwai waɗansu inuwõwi. Wancan Shĩ ne Allah ke tsõratar da bãyinSa da shi. Yã bãyĩNa! To, ku bĩ Ni da taƙawa. = --Qur'an 39:16
    But those who have avoided Taghut, lest they worship it, and turned back to Allah - for them are good tidings. So give good tidings to My servants <> Kuma waɗanda suka nĩsanci Shaiɗannu ga bauta musu, kuma suka mai da al'amari ga Allah, sunã da bushãra. To, ka bãyar da bushãra ga bãyiNa. = --Qur'an 39:17
    Who listen to speech and follow the best of it. Those are the ones Allah has guided, and those are people of understanding. <> Waɗanda ke sauraren magana, sa'an nan su bi mafi kyaunta. waɗancan sũ ne Allah Ya shiryar da su, kuma waɗancan su ne mãsu hankali, = --Qur'an 39:18
    Then, is one who has deserved the decree of punishment [to be guided]? Then, can you save one who is in the Fire? <> Shin fa, wanda kalmar azãba ta wajaba a kansa? Shin fa, kanã iya tsãmar da wanda ke a cikin wutã? = --Qur'an 39:19
    But those who have feared their Lord - for them are chambers, above them chambers built high, beneath which rivers flow. [This is] the promise of Allah. Allah does not fail in [His] promise. <> Amma waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa, sunã da bẽnãye, daga samansu akwai waɗansu bẽnãye ginannu, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Alkawarin Allah. Allah bã Ya sãɓã wa alkawarinSa. = --Qur'an 39:20
    Do you not see that Allah sends down rain from the sky and makes it flow as springs [and rivers] in the earth; then He produces thereby crops of varying colors; then they dry and you see them turned yellow; then He makes them [scattered] debris. Indeed in that is a reminder for those of understanding. <> Shin, ba ka gani ba cẽwa lalle Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Yã gudãnar da shi yanã marẽmari a cikin ƙasã sa'an nan Yã fitar da shũka game da shi, launukan shũkar mãsu sãɓãnin jũna sa'annan shũkar ta ƙeƙashe har ka gan ta fatsifatsi, sa'an nan Allah Ya sanya ta dandaƙaƙƙiya? Lalle ne ga wancan akwai tunãtarwa ga mãsu hankali (ga iyãwar gudãnar da ruwa a cikin gidãjen Aljanna). = --Qur'an 39:21
    So is one whose breast Allah has expanded to [accept] Islam and he is upon a light from his Lord [like one whose heart rejects it]? Then woe to those whose hearts are hardened against the remembrance of Allah. Those are in manifest error. <> Shin fa, wanda Allah Ya buɗa ƙirjinsa, dõmin Musulunci sa'an nan shi yanã a kan haske daga Ubangijinsa, (zai zama kamar waninsa)? To, bone yã tabbata ga maƙeƙasa zukãtansu daga ambaton Allah. Waɗancan sunã a cikin wata ɓata bayyananna. = --Qur'an 39:22
    Allah has sent down the best statement: a consistent Book wherein is reiteration. The skins shiver therefrom of those who fear their Lord; then their skins and their hearts relax at the remembrance of Allah. That is the guidance of Allah by which He guides whom He wills. And one whom Allah leaves astray - for him there is no guide. <> Allah Ya sassaukar da mafi kyaun lãbãri, Littãfi mai kama da jũna, wanda ake konkoma karãtunsa fãtun waɗanda ke tsõron Ubangijinsu, sunã tãƙura sabõda Shi, sa'an nan fãtunsu da zukãtansu su yi laushi zuwa ga ambaton Allah. Waccan ita ce shiryarwar Allah, Yanã shiryar da wanda Ya so game da ita. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani mai shiryarwa. = --Qur'an 39:23
    Then is he who will shield with his face the worst of the punishment on the Day of Resurrection [like one secure from it]? And it will be said to the wrongdoers, "Taste what you used to earn." <> Shin fa, wanda ke kãre mũguwar azãba da fuskarsa (yanã zama kamar waninsa) a Rãnar ƙiyãma? Kuma a ce wa azzãlumai, "Ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã aikatãwa." = --Qur'an 39:24
    Those before them denied, and punishment came upon them from where they did not perceive. <> Waɗanda ke a gabãninsu, sun ƙaryata, sai azãba ta jẽ musu daga inda ba su sani ba. = --Qur'an 39:25
    So Allah made them taste disgrace in worldly life. But the punishment of the Hereafter is greater, if they only knew. <> Sai Allah Ya ɗanɗana musu azãbar wulãkanci a cikin rãyuwar dũniya, kuma lalle azãbar Lãhira ita ce mafi girma, dã sun kasance sunã da sani. = --Qur'an 39:26
    And We have certainly presented for the people in this Qur'an from every [kind of] example - that they might remember. <> Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun buga wa mutãne a, cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane misãli, ɗammãninsu su yi tunãni. = --Qur'an 39:27
    [It is] an Arabic Qur'an, without any deviance that they might become righteous. <> Abin karantãwa ne na Lãrabci, ba mai wata karkata ba, ɗammãninsu, su yi taƙawa. = --Qur'an 39:28
    Allah presents an example: a slave owned by quarreling partners and another belonging exclusively to one man - are they equal in comparison? Praise be to Allah! But most of them do not know. <> Allah Yã buga misãli; wani mutum (bãwa) a cikinsa akwai mãsu tarayya, mãsu mũgun hãlin jãyayya, da wani mutum (bãwa) dukansa ga wani mutum. Shin, zã su daidaita ga misãli? Gõdiya ta tabbata ga Allah (a kan bayãni). Ã'a, mafi yawan mutãne ba su sani ba. = --Qur'an 39:29
    Indeed, you are to die, and indeed, they are to die. <> Lalle kai mai mutuwa ne, kuma su mã lalle mãsu mutuwa ne. = --Qur'an 39:30
    Then indeed you, on the Day of Resurrection, before your Lord, will dispute. <> Sa'an nan, lalle kũ, a Rãnar ¡iyãma, a wurin Ubangijinku, zã ku yi ta yin husũma. = --Qur'an 39:31
    So who is more unjust than one who lies about Allah and denies the truth when it has come to him? Is there not in Hell a residence for the disbelievers? <> To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya yi ƙarya ga Allah, kuma ya ƙaryata gaskiya a lõkacin da ta jẽ masa? Shin bãbu mazauni a cikin Jahannama ga kãfirai? = --Qur'an 39:32
    And the one who has brought the truth and [they who] believed in it - those are the righteous. <> Kuma wanda ya zo da gaskiya, kuma ya gaskata a game da ita, waɗancan sũ ne mãsu taƙawa. = --Qur'an 39:33
    They will have whatever they desire with their Lord. That is the reward of the doers of good - <> Sunã da abin da suke so wajen Ubangijinsu. Wancan shĩ ne sakamakon mãsu kyautatãwa. = --Qur'an 39:34
    That Allah may remove from them the worst of what they did and reward them their due for the best of what they used to do. <> Dõmin Allah Ya kankare musu mafi mũnin abin da suka aikata, kuma Ya sãkã musu ijãrarsu da mafi kyaun abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 39:35
    Is not Allah sufficient for His Servant [Prophet Muhammad]? And [yet], they threaten you with those [they worship] other than Him. And whoever Allah leaves astray - for him there is no guide. <> Ashe Allah bai zama Mai isa ga BãwanSa ba? Kuma sunã tsõratar da kai ga waɗanda suke waninSa, kuma wanda Allah Ya ɓatar to, bã, shi da mai shiryarwa. = --Qur'an 39:36
    And whoever Allah guides - for him there is no misleader. Is not Allah Exalted in Might and Owner of Retribution? <> Kuma wanda Allah Ya shiryar, to, bã shi da mai ɓatarwa. Ashe, Allah bai zama Mabuwãyi ba, Mai azãbar rãmuwa? = --Qur'an 39:37
    And if you asked them, "Who created the heavens and the earth?" they would surely say, "Allah." Say, "Then have you considered what you invoke besides Allah? If Allah intended me harm, are they removers of His harm; or if He intended me mercy, are they withholders of His mercy?" Say, "Sufficient for me is Allah; upon Him [alone] rely the [wise] reliers." <> Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wane ne ya halitta sammai da ƙasã?" Haƙĩƙa, zã su ce, "Allah ne." Ka ce: "Ashe, to, kun gani abin da kuke kira, waɗanda suke wanin Allah ne, idan Allah Ya nufe ni da wata cũta, shin sũ abũbuwan nan mãsu kuranye, cutarsa ne? Kõ kuma Ya nufe ni da wata rahama, shin, su abũbuwan nan mãsu kãme rahamarSa ne?" Ka ce: "Mai isata Allah ne, gare Shi mãsu tawakkali ke dõgara." = --Qur'an 39:38
    Say, "O my people, work according to your position, [for] indeed, I am working; and you are going to know <> Ka ce: "Yã mutãnena! Ku yi aiki a kan hãlinku, lalle nĩ, inã aiki a kan hãlĩna. Sa'an nan zã ku sani." = --Qur'an 39:39
    To whom will come a torment disgracing him and on whom will descend an enduring punishment." <> "Wanda azãba ta je masa, zã ta wulãkanta shi, kuma wata azãba mai dawwama za ta sauka a kansa." = --Qur'an 39:40
    Indeed, We sent down to you the Book for the people in truth. So whoever is guided - it is for [the benefit of] his soul; and whoever goes astray only goes astray to its detriment. And you are not a manager over them. <> Lalle Mũ Mun saukar da littãfi a gare ka dõmin mutãne da gaskiya. Sa'an nan wanda ya nẽmi shiriya, to, dõmin kansa, kuma wanda ya ɓace, to, yanã ɓacẽwa ne a kanta. Kuma ba ka zama wakĩli a kansu ba. = --Qur'an 39:41
    Allah takes the souls at the time of their death, and those that do not die [He takes] during their sleep. Then He keeps those for which He has decreed death and releases the others for a specified term. Indeed in that are signs for a people who give thought. <> Allah ne ke karɓar rãyuka a lõkacin mutuwarsu, da waɗannan da ba su mutu ba, a cikin barcinsu. Sa'an nan Ya riƙe wanda Ya hukunta mutuwa a kansa kuma Ya saki gudar, har zuwa ga ajali ambatacce. Lalle a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni. = --Qur'an 39:42
    Or have they taken other than Allah as intercessors? Say, "Even though they do not possess [power over] anything, nor do they reason?" <> Kõ kuma sun riƙi mãsu cẽto ne, waɗansun Allah? Ka ce: "Shin, kuma kõ dã sun kasance bã su da mallakar kõme, kuma bã su hankalta?" = --Qur'an 39:43
    Say, "To Allah belongs [the right to allow] intercession entirely. To Him belongs the dominion of the heavens and the earth. Then to Him you will be returned." <> Ka ce: "Cẽto gabã ɗaya ga Allah yake. Mulkin sammai da ƙasã Nãsa ne. Sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku." = --Qur'an 39:44
    And when Allah is mentioned alone, the hearts of those who do not believe in the Hereafter shrink with aversion, but when those [worshipped] other than Him are mentioned, immediately they rejoice. <> Kuma idan aka ambaci Allah Shi kaɗai zukãtan waɗanda ba su yi ĩmãni ba da Lãhira, su yi ƙiyãma, kuma idan an ambaci waɗanda suke kiran, wasunSa, sai gãsu sunã yin bushãrar farin ciki. = --Qur'an 39:45
    Say, "O Allah, Creator of the heavens and the earth, Knower of the unseen and the witnessed, You will judge between your servants concerning that over which they used to differ." <> Ka ce: "Ya Allah, Mai ƙãga halittar sammai da ƙasã, Masanin gaibi da bayyane! Kai ne ke yin hukunci a tsakãnin bãyinKa a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna a cikinsa." = --Qur'an 39:46
    And if those who did wrong had all that is in the earth entirely and the like of it with it, they would [attempt to] ransom themselves thereby from the worst of the punishment on the Day of Resurrection. And there will appear to them from Allah that which they had not taken into account. <> Kuma dã waɗanda suka yi zãlunci sunã da abin da ke cikin ƙasã gaba ɗaya, da misãlinsa a tãre da shi lalle dã sun yi fansa da shi daga mummunar azãba, a Rãnar ¡iyãma. Kuma abin da ba su kasance sunã zato ba, daga Allah, ya bayyana a gare su. = --Qur'an 39:47
    And there will appear to them the evils they had earned, and they will be enveloped by what they used to ridicule. <> Mũnãnan ayyuka da suka aikata, suka bayyana a gare su, kuma abin da suka kasance sunã yi, na izgili, ya wajaba a kansu. = --Qur'an 39:48
    And when adversity touches man, he calls upon Us; then when We bestow on him a favor from Us, he says, "I have only been given it because of [my] knowledge." Rather, it is a trial, but most of them do not know. <> To, idan wata cũta ta shãfi mutum, sai ya kirãye Mu, sa'an nan idan Muka canza masa ita, ya sãmi ni'ima daga gare Mu, sai ya ce: "An bã ni ita ne a kan wani ilmi nãwa kawai." Ã'a ita wannan (magana) fitina ce, kuma amma mafi yawansu ba su sani ba. = --Qur'an 39:49
    Those before them had already said it, but they were not availed by what they used to earn. <> Lalle waɗanda ke a gabãninsu, sun faɗe ta, sabõda haka abin da suka kasance sunã aikatãwa bai wadãtar da su da kõme ba. = --Qur'an 39:50
    And the evil consequences of what they earned struck them. And those who have wronged of these [people] will be afflicted by the evil consequences of what they earned; and they will not cause failure. <> Sai (sakamakon) mũnãnan abin da suka aikata ya same su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci daga waɗannan, (sakamakon) munãnan abin da suka aikata zai sãme su, kuma ba su zama mabuwãya ba. = --Qur'an 39:51
    Do they not know that Allah extends provision for whom He wills and restricts [it]? Indeed in that are signs for a people who believe. <> Ashe kuma ba su sani ba cẽwa Allah, na shimfiɗa arziƙi ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuƙuntawa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin ĩmãni. = --Qur'an 39:52
    Say, "O My servants who have transgressed against themselves [by sinning], do not despair of the mercy of Allah. Indeed, Allah forgives all sins. Indeed, it is He who is the Forgiving, the Merciful." <> Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩNa waɗanda suka yi barna a kan rãyukansu! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gãfarta zunubai gabã ɗaya. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai." = --Qur'an 39:53
    And return [in repentance] to your Lord and submit to Him before the punishment comes upon you; then you will not be helped. <> "Kuma ku mayar da al'amari zuwa ga Ubangijinku, kuma ku sallama Masa, a gabãnin azãba ta zo muku, sa'an nan kuwa bã zã a taimake ku ba." = --Qur'an 39:54
    And follow the best of what was revealed to you from your Lord before the punishment comes upon you suddenly while you do not perceive, <> "Kuma ku bi mafi kyaun abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, a gabãnin azãba ta zo muku, bisa auke, kuma kũ ba ku sani ba." = --Qur'an 39:55
    Lest a soul should say, "Oh [how great is] my regret over what I neglected in regard to Allah and that I was among the mockers." <> "Kada wani rai ya ce: 'Yã nadãmãta a kan abin da na yi sakaci a cikin sãshen Allah' kuma lalle na kasance, haƙĩƙa, daga mãsu izgili!"' = --Qur'an 39:56
    Or [lest] it say, "If only Allah had guided me, I would have been among the righteous." <> "Ko kuma (kada) ya ce: 'Da Allah Ya shiryar da ni, dã na kasance daga mãsu taƙawa.'" = --Qur'an 39:57
    Or [lest] it say when it sees the punishment, "If only I had another turn so I could be among the doers of good." <> "Ko kuma (kada (ya ce: a lõkacin da yake ganin azãba, 'Dã lalle a ce inã da wata kõmawa (zuwa dũniya) dõmin in kasance daga mãsu kyautatãwa.'" = --Qur'an 39:58
    But yes, there had come to you My verses, but you denied them and were arrogant, and you were among the disbelievers. <> "Na'am! Lalle ne ãyõyiNa sun jẽ maka, sai ka ƙaryata a game da su, kuma ka yi girman kai, kuma ka kasance daga kãfirai." = --Qur'an 39:59
    And on the Day of Resurrection you will see those who lied about Allah [with] their faces blackened. Is there not in Hell a residence for the arrogant? <> Kuma a Rãnar ¡iyãma kanã ganin waɗanda suka yi ƙarya ga Allah fuskõkinsu sunã mãsu yin baƙi. Ashe bãbu mazauni a cikin Jahannama ga mãsu girman kai? = --Qur'an 39:60
    And Allah will save those who feared Him by their attainment; no evil will touch them, nor will they grieve. <> Kuma Allah na tsĩrar da waɗanda suka yi taƙawa a game da wurin sãmun babban rabonsu, cũta bã zã tashãfe su ba, kuma ba su zama sunã baƙin ciki ba. = --Qur'an 39:61
    Allah is the Creator of all things, and He is, over all things, Disposer of affairs. <> Allah ne Mai halitta dukan kõme, kuma Shĩ ne Wakĩli a kan kõme. = --Qur'an 39:62
    To Him belong the keys of the heavens and the earth. And they who disbelieve in the verses of Allah - it is those who are the losers. <> Shĩ ke da mabũɗan sammai da ƙasã. Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah, waɗannan sũ nemãsu hasãra. = --Qur'an 39:63
    Say, [O Muhammad], "Is it other than Allah that you order me to worship, O ignorant ones?" <> Ka ce: "Shin, wanin Allah kuke umurni na da in bauta wa? Yã ku jãhilai!" = --Qur'an 39:64
    And it was already revealed to you and to those before you that if you should associate [anything] with Allah, your work would surely become worthless, and you would surely be among the losers." <> Kuma an yi wahayi zuwa gare ka da kuma zuwa ga waɗanda suke a gabãninka, "Lalle idan ka yi shirki haƙĩƙa aikinka zai ɓãci, kuma lalle zã ka kasance daga mãsu hasãra." = --Qur'an 39:65
    Rather, worship [only] Allah and be among the grateful. <> Ã'aha! Ka bauta wa Allah kaɗai, kuma ka kasance daga mãsu gõdiya. = --Qur'an 39:66
    They have not appraised Allah with true appraisal, while the earth entirely will be [within] His grip on the Day of Resurrection, and the heavens will be folded in His right hand. Exalted is He and high above what they associate with Him. <> Kuma ba su ƙaddara Allah a kan haƙĩƙanin ĩkon yinsa ba: ¡asã duka damƙarSa ce, a Rãnar ¡iyãma, kuma sammai abũbuwan naɗewa ne ga dãmanSa. Tsarki ya tabbata a gare Shi, kuma Ya ɗaukaka daga barin abin da suke shirki da shi. = --Qur'an 39:67
    And the Horn will be blown, and whoever is in the heavens and whoever is on the earth will fall dead except whom Allah wills. Then it will be blown again, and at once they will be standing, looking on. <> Kuma aka busa a cikin ƙaho, sai waɗanda ke a cikin sammai da ƙasã suka sũma sai wanda Allah Ya so (rashin sumansa) sa'an nan aka hũra a cikinsa, wata hũrãwa, sai gã su tsaitsaye, sunã kallo. = --Qur'an 39:68
    And the earth will shine with the light of its Lord, and the record [of deeds] will be placed, and the prophets and the witnesses will be brought, and it will be judged between them in truth, and they will not be wronged. <> Kuma ƙasã ta yi haske da hasken Ubangijinta, kuma aka aza littãfi, kuma aka zo da Annabãwa da mãsu shaida, kuma aka yi hukunci a tsakãninsu, da gaskiya, alhãli kuwa, sũ, bã zã a zãlunce su ba. = --Qur'an 39:69
    And every soul will be fully compensated [for] what it did; and He is most knowing of what they do. <> Kuma aka cika wa kõwane rai abin da ya aikata. Kuma (Allah) Shĩ ne Mafi sani game da abin da suke aikatãwa. = --Qur'an 39:70
    And those who disbelieved will be driven to Hell in groups until, when they reach it, its gates are opened and its keepers will say, "Did there not come to you messengers from yourselves, reciting to you the verses of your Lord and warning you of the meeting of this Day of yours?" They will say, "Yes, but the word of punishment has come into effect upon the disbelievers. <> Kuma aka kõra waɗanda suka kãfirta zuwa Jahannama, jama'a-jama'a har a lõkacin da suka je mata, sai aka buɗe ƙõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu, "Ashe, waɗansu Manzanni, daga cikinku ba su je muku ba, sunã karanta ãyõyin Ubangijinku a kanku, kuma sunã yi muku gargaɗin gamuwa da yininku wannan?" Suka ce, "Na'am, "kuma amma kalmar azãba ita ce ta wajaba a kan kãfirai!" = --Qur'an 39:71
    [To them] it will be said, "Enter the gates of Hell to abide eternally therein, and wretched is the residence of the arrogant." <> Aka ce, "Ku shiga ƙõfõfin Jahannama, kaunã madawwama a cikinta. Sa'an nan mazaunin makangara yã munana." = --Qur'an 39:72
    But those who feared their Lord will be driven to Paradise in groups until, when they reach it while its gates have been opened and its keepers say, "Peace be upon you; you have become pure; so enter it to abide eternally therein," [they will enter]. <> Kuma aka kõra waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa zuwa Aljanna jama'a-jama'a har a lõkacin da suka jẽ mata, alhãli kuwa an buɗe kõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu, "Aminci ya tabbata a gare ku, kun ji dãɗi, sabõda haka ku shige ta, kunã madawwama (a cikinta)." = --Qur'an 39:73
    And they will say, "Praise to Allah, who has fulfilled for us His promise and made us inherit the earth [so] we may settle in Paradise wherever we will. And excellent is the reward of [righteous] workers." <> Kuma suka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya yi mana gaskiya ga wa'adinSa, kuma Ya gãdar da mu ƙasã, munã zama a cikin Aljanna a inda muke so." To, madalla da ijãrar ma'aikata. = --Qur'an 39:74
    And you will see the angels surrounding the Throne, exalting [Allah] with praise of their Lord. And it will be judged between them in truth, and it will be said, "[All] praise to Allah, Lord of the worlds." <> Kuma kanã ganin malã'iku sunã mãsu tsayãwa da haƙƙoƙin da aka ɗõra musu daga kẽwayen Al'arshi, sunã tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu. Kuma aka yi hukunci a tsakãninsu da gaskiya. Kuma aka ce, "Gõdiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu." = --Qur'an 39:75
    Ha, Meem. <> Ḥ. M̃. = --Qur'an 40:1
    The revelation of the Book is from Allah, the Exalted in Might, the Knowing. <> Saukar da Littãfi daga Allah ne, Mabuwãyi, Masani. = --Qur'an 40:2
    The forgiver of sin, acceptor of repentance, severe in punishment, owner of abundance. There is no deity except Him; to Him is the destination. <> Mai gãfarta zunubi kuma Mai karɓar tũba Mai tsananin azãba, Mai wadãtarwa bãbu abin bautawa fãce Shi, zuwa gare Shi makõma take. = --Qur'an 40:3
    No one disputes concerning the signs of Allah except those who disbelieve, so be not deceived by their [uninhibited] movement throughout the land. <> Bãbu mai jãyayya a cikin ãyõyin Allah, fãce waɗanda suka kãfirta. Sabõda haka kada jũyãwarsu a cikin garũruwa ta rũɗe ka = --Qur'an 40:4
    The people of Noah denied before them and the [disbelieving] factions after them, and every nation intended [a plot] for their messenger to seize him, and they disputed by [using] falsehood to [attempt to] invalidate thereby the truth. So I seized them, and how [terrible] was My penalty. <> Mutãnen Nũhu sun ƙaryata a gabãninsu, da ƙungiyõyin da suke a bãyansu, kuma kõwace al'umma tã yi nufi game da Manzonsu, dõmin su kãmã shi. Kuma suka yi jãyayya da ƙarya dõmin su gusar da gaskiya da ita. Sai Na kãmã su. To, yãya azãbãTa take? = --Qur'an 40:5
    And thus has the word of your Lord come into effect upon those who disbelieved that they are companions of the Fire. <> Kuma kamar haka kalmar Ubangijinka ta wajaba a kan waɗanda suka kãfirta, dõmin sũ 'yan wutã ne. = --Qur'an 40:6
    Those [angels] who carry the Throne and those around it exalt [Allah] with praise of their Lord and believe in Him and ask forgiveness for those who have believed, [saying], "Our Lord, You have encompassed all things in mercy and knowledge, so forgive those who have repented and followed Your way and protect them from the punishment of Hellfire. <> Waɗanda ke ɗaukar Al'arshi da waɗanda ke kẽwayenta, sunã tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu, kuma sunã yin ĩmãni da Shi, kuma sunã yin istigfãri dõmin waɗanda suka yi ĩmãni, (sunã cẽwa), "Yã Ubangijinmu! Kã yalwaci dukan kõme da rahama da ilmi to Ka yi gãfara ga waɗanda suka tũba kuma suka bi hanyarKa, kuma Ka tsare musu azãbar Jahĩm." = --Qur'an 40:7
    Our Lord, and admit them to gardens of perpetual residence which You have promised them and whoever was righteous among their fathers, their spouses and their offspring. Indeed, it is You who is the Exalted in Might, the Wise. <> "Ya Ubangijinmu! Kuma Ka shigar da su a gidãjen Aljannar zama, wannan da Ka yi musu wa'adi, sũ da wanda ya kyautatu daga ubanninsu da mãtan aurensu da zurriyarsu. Lalle Kai, Kai ne Mabuwãyi, Mai hikima." = --Qur'an 40:8
    And protect them from the evil consequences [of their deeds]. And he whom You protect from evil consequences that Day - You will have given him mercy. And that is the great attainment." <> "Kuma Ka tsare su daga mũnãnan ayyuka, kuma wanda Ka tsare shi daga mũnãnan ayyuka a rãnarnan, to, lalle, Ka yi masa rahama kuma wancan shi ne babban rabo mai girma." = --Qur'an 40:9
    Indeed, those who disbelieve will be addressed, "The hatred of Allah for you was [even] greater than your hatred of yourselves [this Day in Hell] when you were invited to faith, but you refused." <> Lalle waɗanda suka kãfirta, anã kiran su, "Haƙĩƙa, ƙin Allah (a gare ku) shĩ ne mafi girma daga ƙinku ga kanku a lõkacin da ake kiran ku zuwa ga ĩmãni, sai kunã ta kãfircẽwa." = --Qur'an 40:10
    They will say, "Our Lord, You made us lifeless twice and gave us life twice, and we have confessed our sins. So is there to an exit any way?" <> Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Kã matar da mu sau biyu, kuma Kã rãyar da mu sau biyu, sabõda haka mun yarda da laifuffukan mu. To, shin, akwai wata hanya zuwa ga fita?" = --Qur'an 40:11
    [They will be told], "That is because, when Allah was called upon alone, you disbelieved; but if others were associated with Him, you believed. So the judgement is with Allah, the Most High, the Grand." <> Wancan sababinsa, lalle (shi ne) idan an kirãyi Allah Shi kaɗai, sai ku kãfirta, kuma idan aka yi shirki game da Shi, sai ku yi ĩmãni. To, hukuncin fa, na Allah Maɗaukaki, Mai girma ne. = --Qur'an 40:12
    It is He who shows you His signs and sends down to you from the sky, provision. But none will remember except he who turns back [in repentance]. <> Shĩ ne Wanda ke nũna muku ãyõyinSa, kuma Ya saukar da arziki daga sama sabõda ku, kuma bãbu mai yin tunãni fãce mai mayar da al'amari ga Allah. = --Qur'an 40:13
    So invoke Allah, [being] sincere to Him in religion, although the disbelievers dislike it. <> Sabõda haka ku kirãyi Allah, kunã mãsu tsarkake addini a gare Shi, kuma kõ dã kãfirai sun ƙi. = --Qur'an 40:14
    [He is] the Exalted above [all] degrees, Owner of the Throne; He places the inspiration of His command upon whom He wills of His servants to warn of the Day of Meeting. <> Mai ɗaukaka darajõji (dõmin mũminai), Mai Al'arshi, Yanã jẽfa rũhi daga al'amarinSa a kan wanda Ya so daga bãyinSa, dõmin ya yi gargaɗi kan rãnar gamuwa. = --Qur'an 40:15
    The Day they come forth nothing concerning them will be concealed from Allah. To whom belongs [all] sovereignty this Day? To Allah, the One, the Prevailing. <> Rãnar da suke bayyanannu, bãbu wani abu daga gare su wanda yake iya bõyuwa ga Allah. "Mulki ga wa ya ke a yau?" Yana ga Allah, Makaɗaici, Mai tĩlastãwa. = --Qur'an 40:16
    This Day every soul will be recompensed for what it earned. No injustice today! Indeed, Allah is swift in account. <> Yau anã sãka wa kõwane rai a game da abin da ya aikata, bãbu zãlunci a yau. Lalle Allah Mai gaggawar hisãbi ne. = --Qur'an 40:17
    And warn them, [O Muhammad], of the Approaching Day, when hearts are at the throats, filled [with distress]. For the wrongdoers there will be no devoted friend and no intercessor [who is] obeyed. <> Kuma ka yi musu gargaɗi kan rãnar (Sã'a) makusanciya, a lõkacin da zukãta suke mãsu cika da bakin ciki, ga maƙõsansu. Bãbu wani masõyi ga azzãlumai, kuma bãbu wani mai cẽto da zã a yi wa dã'a (ga cẽtonsu). = --Qur'an 40:18
    He knows that which deceives the eyes and what the breasts conceal. <> (Allah) Ya san yaudarar idãnu da abin da ƙirãza ke ɓõyẽwa. = --Qur'an 40:19
    And Allah judges with truth, while those they invoke besides Him judge not with anything. Indeed, Allah - He is the Hearing, the Seeing. <> Kuma Allah Shĩ ke yin hukunci da gaskiya, waɗannan da kuke kira, waninSa, bã su yin hukunci da kõme. Lalle Allah, Shĩ ne Mai ji, Mai gani. = --Qur'an 40:20
    Have they not traveled through the land and observed how was the end of those who were before them? They were greater than them in strength and in impression on the land, but Allah seized them for their sins. And they had not from Allah any protector. <> Ashe, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã, dõmin su dũba ga yadda ãƙibar waɗanda suka kasance a gabãninsu ta zama? Sun kasance sũ ne mafi tsananin ƙarfi daga gare su, da kufaifan aiki a cikin ƙasã, sai Allah Ya kãmã su da laifuffukansu. Kuma bã su da wani mai tsarẽwa daga Allah. = --Qur'an 40:21
    That was because their messengers were coming to them with clear proofs, but they disbelieved, so Allah seized them. Indeed, He is Powerful and severe in punishment. <> Wancan sababinsa, dõmin sũ Manzanninsu sun kasance sunã zuwa gare su da hujjõji bayyanannu, sai suka kãfirta, sai Allah Ya kãmã su. Lalle Shĩ Mai ƙarfi ne, Mai tsananin azãba. = --Qur'an 40:22
    And We did certainly send Moses with Our signs and a clear authority <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Mũsã a game da ãyõyinMu da wani dalĩli bayyananne. = --Qur'an 40:23
    To Pharaoh, Haman and Qarun; but they said, "[He is] a magician and a liar." <> Zuwa ga Fir'auna da Hãmãna da Kãrũna, sai suka ce: "Mai sihiri ne, maƙaryaci." = --Qur'an 40:24
    And when he brought them the truth from Us, they said, "Kill the sons of those who have believed with him and keep their women alive." But the plan of the disbelievers is not except in error. <> Sa'an nan, a lõkacin da ya jẽ musu da gaskiya daga wurinMu, suka ce: "Ku kashe ɗiyan waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, kuma ku rãyar da mãtansu." Kuma mugun shirin kãfirai, bai zama ba fãce a cikin bata. = --Qur'an 40:25
    And Pharaoh said, "Let me kill Moses and let him call upon his Lord. Indeed, I fear that he will change your religion or that he will cause corruption in the land." <> Kuma Fir'auna ya ce: "Ku bar ni in kashe Mũsã, kuma shĩ, ya kirãyi Ubangijinsa. Lalle ne nĩ, inã tsõron ya musanya addininku, kõ kuwa ya bayyana ɓarna a cikin kasã." = --Qur'an 40:26
    But Moses said, "Indeed, I have sought refuge in my Lord and your Lord from every arrogant one who does not believe in the Day of Account." <> Kuma Mũsã ya ce: "Lalle nĩ, nã nẽmi tsari da Ubangijĩna kuma Ubangijinku, daga dukan makangari, wanda bã ya ĩmani da rãnar Hisãbi." = --Qur'an 40:27
    And a believing man from the family of Pharaoh who concealed his faith said, "Do you kill a man [merely] because he says, 'My Lord is Allah' while he has brought you clear proofs from your Lord? And if he should be lying, then upon him is [the consequence of] his lie; but if he should be truthful, there will strike you some of what he promises you. Indeed, Allah does not guide one who is a transgressor and a liar. <> Kuma wani namiji mũmini daga dangin Fir'auna, yanã bõye ĩmãninsa, ya ce: "Ashe, za ku kashe mutum dõmin ya ce Ubangijina Allah ne, alhãli kuwa haƙĩƙa ya zo muku da hujjõji bayyanannu daga Ubangijinku? Idan yã kasance maƙaryaci ne, to, ƙaryarsa na kansa, kuma idan ya kasance mai gaskiya ne, sãshen abin da yake yi muku wa'adi zai sãme ku. Lalle ne Allah bã Ya shiryar da wanda yake mai barna, mai yawan ƙarya." = --Qur'an 40:28
    O my people, sovereignty is yours today, [your being] dominant in the land. But who would protect us from the punishment of Allah if it came to us?" Pharaoh said, "I do not show you except what I see, and I do not guide you except to the way of right conduct." <> "Yã kũ mutãnẽna! Kunã da mulki a yau, kuma kũ ne marinjãya a cikin kasã to wãne ne zai taimake mu daga azãbar Allah idan ta zo mana?" Fir'auna ya ce: "Bã ni nũnamuku kõme face abin da na gani, kuma ba ni shiryar da ku, sai ga hanyar shiryuwa." = --Qur'an 40:29
    And he who believed said, "O my people, indeed I fear for you [a fate] like the day of the companies - <> Kuma wannan da ya yi ĩmãni ya ce: "Ya mutãnẽnã! Lallene, nĩ, inã yi muku tsõron kwatankwacin rãnar ƙungiyõyi." = --Qur'an 40:30
    Like the custom of the people of Noah and of 'Aad and Thamud and those after them. And Allah wants no injustice for [His] servants. <> "Kwatankwacin al'adar mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdãwa da waɗanda ke a bãyansu. Kuma Allah bã Ya nufin zãlunci ga bãyinSa." = --Qur'an 40:31
    And O my people, indeed I fear for you the Day of Calling - <> "Kuma ya mutãnẽna! Lallenĩ, inã yi muku tsõron rãnar kiran jũna." = --Qur'an 40:32
    The Day you will turn your backs fleeing; there is not for you from Allah any protector. And whoever Allah leaves astray - there is not for him any guide. <> "A rãnar da zã ku jũya, kunã mãsu bãyar da bãya (gudãne) bã ku da wani mai tsaro daga Allah. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani mai shiryarwa." = --Qur'an 40:33
    And Joseph had already come to you before with clear proofs, but you remained in doubt of that which he brought to you, until when he died, you said, 'Never will Allah send a messenger after him.' Thus does Allah leave astray he who is a transgressor and skeptic." <> "Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Yusufu ya zo muku daga gabãni, da hujjõji bayyanannu, ba ku gushe ba kunã a cikin shakka daga abin da ya zo muku da shi, har a lõkacin da ya halaka kuka ce, 'Allah bã zai aiko wani Manzo ba, a bãyansa.' Kamar haka Allah ke ɓatar da wanda yake mai ɓarna, mai shakka." = --Qur'an 40:34
    Those who dispute concerning the signs of Allah without an authority having come to them - great is hatred [of them] in the sight of Allah and in the sight of those who have believed. Thus does Allah seal over every heart [belonging to] an arrogant tyrant. <> "Waɗanda kejayayya a cikin ãyõyin Allah, bã da wani dalĩli da ya zo musu ba. Jidalin ya girma ga zamansa abin ki a wurin Allah da wurin waɗanda suka yi ĩmãni. Kamar haka Allah ke bicẽwar haske a kan zũciyar dukan makangari, mai tĩlastãwa." = --Qur'an 40:35
    And Pharaoh said, "O Haman, construct for me a tower that I might reach the ways - <> Kuma Fir'auna ye ce, "Yã Hãmana! Ka gina mini bẽne, dammãnĩna zã ni isa ga ƙõfõfi." = --Qur'an 40:36
    The ways into the heavens - so that I may look at the deity of Moses; but indeed, I think he is a liar." And thus was made attractive to Pharaoh the evil of his deed, and he was averted from the [right] way. And the plan of Pharaoh was not except in ruin. <> "¡õfõfin sammai dõmin in yi ninƙaya zuwa ga abin bautãwar Mũsã. Kuma lalle nĩ haƙĩƙa inã zaton sa maƙaryaci." Kuma haka dai aka ƙawãce wa Fir'auna mũnãnan aikinsakuma aka danne shi daga barin tafarki. Kuma mugun nufin Fir'auna bai zama ba fãce yanã a cikin hasãra." = --Qur'an 40:37
    And he who believed said, "O my people, follow me, I will guide you to the way of right conduct. <> Kuma wannan da ya yi ĩmãni ya ce: "Ya mutãnẽna! Ku bĩ ni, in shiryar da ku tafarkin shiryuwa." = --Qur'an 40:38
    O my people, this worldly life is only [temporary] enjoyment, and indeed, the Hereafter - that is the home of [permanent] settlement. <> "Kuma ya mutãnẽna! Wannan rãyuwa ta dũniya dan jin dãɗi ne kawai, kuma lalle Lãhira ita ce gidan tabbata." = --Qur'an 40:39
    Whoever does an evil deed will not be recompensed except by the like thereof; but whoever does righteousness, whether male or female, while he is a believer - those will enter Paradise, being given provision therein without account. <> "Wanda ya aikata mummunan aiki to, ba za a sãka masa ba fãce da misãlinsa, kuma wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ mace alhãli kuwa shĩ mũmini ne, to, waɗannan sunã shiga Aljanna, anã ciyar da su a cikinta, bã da lissãfi ba." = --Qur'an 40:40
    And O my people, how is it that I invite you to salvation while you invite me to the Fire? <> "Kuma ya mutãnẽna! Me ya sãme ni, inã kiran ku zuwa ga tsĩra, kuma kunã kira na zuwa ga wutã?" = --Qur'an 40:41
    You invite me to disbelieve in Allah and associate with Him that of which I have no knowledge, and I invite you to the Exalted in Might, the Perpetual Forgiver. <> "Kuna kira na zuwa ga in kãfirta da Allah, kuma in yi shirki, game da Shi, da abin da bãbu wani ilmi game da shi gare ni, kuma ni inã kiran ku zuwa ga Mabuwãyi, Mai gãfara." = --Qur'an 40:42
    Assuredly, that to which you invite me has no [response to a] supplication in this world or in the Hereafter; and indeed, our return is to Allah, and indeed, the transgressors will be companions of the Fire. <> "Haƙƙan ne abin da kawai kuke kira na zuwa gare shi, bã ya da wani kira a cikin dũniya, kuma bã shi da shi a Lãhira kuma lalle makomarmu zuwa ga Allah take, kuma lalle mabarnata sũ ne 'yan wutã." = --Qur'an 40:43
    And you will remember what I [now] say to you, and I entrust my affair to Allah. Indeed, Allah is Seeing of [His] servants." <> "To zã ku ambaci abin da nake gaya muku, kuma inã fawwala al'amarina zuwa ga Allah. Lalle Allah Mai gani ne ga bãyinSa." = --Qur'an 40:44
    So Allah protected him from the evils they plotted, and the people of Pharaoh were enveloped by the worst of punishment - <> Sai Allah Ya tsare shi daga mũnãnan abũbuwa da suka yi na mãkirci, kuma mummunar azãba ta wajaba ga mutãnen Fir'auna. = --Qur'an 40:45
    The Fire, they are exposed to it morning and evening. And the Day the Hour appears [it will be said], "Make the people of Pharaoh enter the severest punishment." <> Wutã, anã gitta su a kanta, sãfe da maraice, kuma a rãnar da Sa'a take tsayuwa, anã cẽwa, "Ku shigar da mutãnen Fir'auna a mafi tsananin azãba." = --Qur'an 40:46
    And [mention] when they will argue within the Fire, and the weak will say to those who had been arrogant, "Indeed, we were [only] your followers, so will you relieve us of a share of the Fire?" <> Kuma a lõkacin da suke husũma a cikin wutã, sai raunãna (mabiya) su ce wa waɗanda suka kangara (shugabanni), "Lalle mũ, mun kasance mabiya gare ku, to, shin kũ mãsu wadãtar da mu ne daga barin wani rabo daga wutã?" = --Qur'an 40:47
    Those who had been arrogant will say, "Indeed, all [of us] are in it. Indeed, Allah has judged between the servants." <> Waɗanda suka kangara suka ce: "Lalle mũ duka munã a cikinta. Lalle ne, Allah Ya yi hukunci a tsakãnin bãyinSa." = --Qur'an 40:48
    And those in the Fire will say to the keepers of Hell, "Supplicate your Lord to lighten for us a day from the punishment." <> Kuma waɗanda suke a cikin wutã suka ce wa matsaran Jahannama, "Ku rõki Ubangijinku Ya sauƙaƙa mana, a yini ɗaya, daga azãba." = --Qur'an 40:49
    They will say, "Did there not come to you your messengers with clear proofs?" They will say, "Yes." They will reply, "Then supplicate [yourselves], but the supplication of the disbelievers is not except in error." <> Suka ce: "Ashe, Manzanninku ba su jẽ muku da hujjõji bayyanannu ba?" Suka ce: "Na'am, sun jẽ!" Suka ce: "To, ku rõƙa." Kuma rõƙon kãfirai bai zamo ba fãce a cikin ɓata. = --Qur'an 40:50
    Indeed, We will support Our messengers and those who believe during the life of this world and on the Day when the witnesses will stand - <> Lalle Mũ, hakĩka, Munã taimakon ManzanninMu da waɗanda suka yi ĩmãni, a cikin rãyuwar dũniya da rãnar da shaidu ke tsayãwa. = --Qur'an 40:51
    The Day their excuse will not benefit the wrongdoers, and they will have the curse, and they will have the worst home. <> Rãnar da uzurin azzãlumai bã ya amfãninsu, kuma sunã da la'ana, kuma sunã da mũnin gida. = --Qur'an 40:52
    And We had certainly given Moses guidance, and We caused the Children of Israel to inherit the Scripture <> Kuma lalle haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã shiriya, kuma Mun gãdar da Banĩ Isrã'ĩla Littãfi. = --Qur'an 40:53
    As guidance and a reminder for those of understanding. <> Shiryarwa da tunãwa ga ma'abũta hankali. = --Qur'an 40:54
    So be patient, [O Muhammad]. Indeed, the promise of Allah is truth. And ask forgiveness for your sin and exalt [Allah] with praise of your Lord in the evening and the morning. <> Sabõda haka, ka yi haƙuri, lalle wa'adin Allah gaskiya ne. Kuma ka nẽmi gãfara ga zunubinka, kuma ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, maraice da kuma wãyẽwar sãfiya. = --Qur'an 40:55
    Indeed, those who dispute concerning the signs of Allah without [any] authority having come to them - there is not within their breasts except pride, [the extent of] which they cannot reach. So seek refuge in Allah. Indeed, it is He who is the Hearing, the Seeing. <> Lalle waɗanda ke jãyayya a cikin ãyõyin Allah, bã game da wani dalĩli wanda ya jẽ musu ba, bãbu kõme a cikin kirãzansu, fãce girman kai, ba su zama mãsu isa ga gũrinsu ba, sabõda haka ka nẽmi tsari daga Allah. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai ji, Mai gani. = --Qur'an 40:56
    The creation of the heavens and earth is greater than the creation of mankind, but most of the people do not know. <> Lalle halittar sammai da ƙasã, ita ce mafi girma daga halittar mutãne, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba. = --Qur'an 40:57
    And not equal are the blind and the seeing, nor are those who believe and do righteous deeds and the evildoer. Little do you remember. <> Kuma makãho da mai gani bã su daidaita kuma waɗanda suka yi ĩmãni suka, aikata ayyukan ƙwarai da mai mũnanãwa bã su daidaita. Kaɗan ƙwarai, kuke yin tunãni. = --Qur'an 40:58
    Indeed, the Hour is coming - no doubt about it - but most of the people do not believe. <> Lalle Sa'a, haƙĩƙa mai zuwa ce, bãbu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutãne bã su yin ĩmãni. = --Qur'an 40:59
    And your Lord says, "Call upon Me; I will respond to you." Indeed, those who disdain My worship will enter Hell [rendered] contemptible. <> Kuma Ubangijinku ya ce: "Ku kira Ni in karɓa muku. Lalle waɗannan da ke kangara daga barin bauta Mini, za su shiga Jahannama sunã ƙasƙantattu." = --Qur'an 40:60
    It is Allah who made for you the night that you may rest therein and the day giving sight. Indeed, Allah is full of bounty to the people, but most of the people are not grateful. <> Allah ne Wanda Ya sanya muku dare dõmin ku natsu a cikinsa, da rãna mai gãnarwa. Lalle Allah, haƙĩƙa, Ma'abũcin falala ne a kan mutãne, kuma amma mafi yawan mutãne bã su gõdẽwa. = --Qur'an 40:61
    That is Allah, your Lord, Creator of all things; there is no deity except Him, so how are you deluded? <> Wancan shine Allah Ubangijinku, Mahaliccin dukan kõme, bãbu abin bautãwa fãce Shi. To, yãya ake karkatar da ku? = --Qur'an 40:62
    Thus were those [before you] deluded who were rejecting the signs of Allah. <> Kamar haka ake karkatar da waɗanda suka kasance sunã jãyayya game da ãyõyin Allah. = --Qur'an 40:63
    It is Allah who made for you the earth a place of settlement and the sky a ceiling and formed you and perfected your forms and provided you with good things. That is Allah, your Lord; then blessed is Allah, Lord of the worlds. <> Allah ne Ya sanya muku kasã tabbatacciya, da sama ginanniya, kuma Ya sũranta ku, sa'an nan Ya kyautata sũrõrinku,, kuma Ya azurta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi. Wancan Shĩne Allah Ubangijinku. To, albarkar Allah Ubangijin halittu tã bayyana. = --Qur'an 40:64
    He is the Ever-Living; there is no deity except Him, so call upon Him, [being] sincere to Him in religion. [All] praise is [due] to Allah, Lord of the worlds. <> Shĩ ne Mai rai, bãbu abin bautãwa fãce Shi. Sabõda haka ku kira Shi, kunã mãsu tsarkake addini a gare Shi. Gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu. = --Qur'an 40:65
    Say, [O Muhammad], "Indeed, I have been forbidden to worship those you call upon besides Allah once the clear proofs have come to me from my Lord, and I have been commanded to submit to the Lord of the worlds." <> Ka ce: "Lalle nĩ, an hana ni in bauta wa waɗanda kuke kira waɗansun Allah a lõkacin da hujjõji bayyanannu suka zo mini daga Ubangijina, kuma an umurce ni in sallama ga Ubangijin halittu." = --Qur'an 40:66
    It is He who created you from dust, then from a sperm-drop, then from a clinging clot; then He brings you out as a child; then [He develops you] that you reach your [time of] maturity, then [further] that you become elders. And among you is he who is taken in death before [that], so that you reach a specified term; and perhaps you will use reason. <> Shĩ ne Wanda Ya halitta ku daga turɓãya, sa'an nan daga maniyyi, sa'an nan daga sãren jini, sa'an nan Ya fitar da ku kunã jãrĩri, sa'an nan dõmin ku isa ga cikar ƙarfinku sa'an nan dõmin ku kasance tsõfaffi, kuma daga cikinku, akwai wanda ake karɓar ransa a gabãnin haka, kuma dõmin ku isa ga ajali ambatacce, kuma dammãninku ko zã ku hankalta. = --Qur'an 40:67
    He it is who gives life and causes death; and when He decrees a matter, He but says to it, "Be," and it is. <> Shi ne Wanda ke rayarwa kuma Yana kashewa. To, idan Ya hukunta wani al'amari, to, Yana cewa kawai gare shi, ka kasance sai yana kasancewa (kamar yadda ake bukatar sa.) = --Qur'an 40:68
    Do you not consider those who dispute concerning the signs of Allah - how are they averted? <> Ashe, ba ka gani ba ga waɗanda ke jãyayya a cikin ãyõyin Allah, yadda ake karkatar da su? = --Qur'an 40:69
    Those who deny the Book and that with which We sent Our messengers - they are going to know, <> Waɗanda suka ƙaryata, game da Littãfin, kuma da abin da Muka aika Manzanninmu da shi. To, za su sani. = --Qur'an 40:70
    When the shackles are around their necks and the chains; they will be dragged <> A lõkacin da ƙuƙumma suke a cikin wuyõyinsu, da sarƙõƙi anã jan su. = --Qur'an 40:71
    In boiling water; then in the Fire they will be filled [with flame]. <> A cikin ruwan zãfi, sa'an nan a cikin wutã anã babbaka su. = --Qur'an 40:72
    Then it will be said to them, "Where is that which you used to associate [with Him in worship] <> Sa'an nan a ce musu, "Ina abin da kuka kasance kunã shirki da shi" = --Qur'an 40:73
    Other than Allah?" They will say, "They have departed from us; rather, we did not used to invoke previously anything." Thus does Allah put astray the disbelievers. <> "Wanin Allah?" Suka ce: "Sun ɓace mana. Ã'a, ba mu kasance munã kiran kõme ba a gabani."Kamar wancan ne Allah Yake ɓatar da kãfirai. = --Qur'an 40:74
    [The angels will say], "That was because you used to exult upon the earth without right and you used to behave insolently. <> Wancan dõmin abin da kuka kasance ne kunã farin ciki da shi, a cikin ƙasã, bã da hakki ba, kuma da abin da kuka kasance kunã yi na nishãɗi. = --Qur'an 40:75
    Enter the gates of Hell to abide eternally therein, and wretched is the residence of the arrogant." <> Ku shiga kofõfin Jahannama kunã madawwama a cikinta. To, mazaunin mãsu girman kai yã mũnana. = --Qur'an 40:76
    So be patient, [O Muhammad]; indeed, the promise of Allah is truth. And whether We show you some of what We have promised them or We take you in death, it is to Us they will be returned. <> Sabõda haka ka yi haƙuri. Lalle wa'adin Allah gaskiya ne. To, kõ dai lalle Mu nũna maka sãshen abin da Muka yi musu wa'adi da shi kõ kuwa lalle Mu karɓi ranka, to, zuwa gare Mu ake mayar da su. = --Qur'an 40:77
    And We have already sent messengers before you. Among them are those [whose stories] We have related to you, and among them are those [whose stories] We have not related to you. And it was not for any messenger to bring a sign [or verse] except by permission of Allah. So when the command of Allah comes, it will be concluded in truth, and the falsifiers will thereupon lose [all]. <> Kuma lalle haƙĩƙa, Mun aika wasu Manzanni daga gabãninka, daga cikinsu akwai wanda Muka ƙissanta maka lãbãrinsa kuma daga cikinsu akwai wanda ba Mu ƙissanta lãbãrinsa ba a gare ka. Bã ya yiwuwa ga wani Manzo ya jẽ da wata ãyar mu'ujiza fãce da iznin Allah. Sa'an nan idan umurnin Allah ya jẽ, sai a yi hukunci da gaskiya, mãsu ɓãtãwa sun yi hasara a can. = --Qur'an 40:78
    It is Allah who made for you the grazing animals upon which you ride, and some of them you eat. <> Allah ne Wanda Ya sanya muku dabbõbi dõmin ku hau daga gare su, kuma daga gare su kuke ci. = --Qur'an 40:79
    And for you therein are [other] benefits and that you may realize upon them a need which is in your breasts; and upon them and upon ships you are carried. <> Kuma kunã da abũbuwan amfãni a cikinsu, kuma dõmin ku isar da wata buƙãta, a cikin ƙirãzanku a kansu kuma a kansu da a kan jirãge ake, ɗaukar ku. = --Qur'an 40:80
    And He shows you His signs. So which of the signs of Allah do you deny? <> Kuma Ya nũna muku ayõyinSa. To, wane ãyõyin Allah kuke musu? = --Qur'an 40:81
    Have they not traveled through the land and observed how was the end of those before them? They were more numerous than themselves and greater in strength and in impression on the land, but they were not availed by what they used to earn. <> Ashe fa, ba su yi tafiya a cikin ƙasã ba, dõmin su dũba yadda ãƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Sun kasance mafi yawa daga gare su. Kuma sun fi tsananin ƙarfi, da (yawan) gurãbun sanã'õ'i a cikin ƙasã. To, abin da suka kasance sunã aikatãwa bai wadãtar da su ba. = --Qur'an 40:82
    And when their messengers came to them with clear proofs, they [merely] rejoiced in what they had of knowledge, but they were enveloped by what they used to ridicule. <> A lõkacin da Manzanninsu suka jẽ musu da hujjõji bayyanannu, suka yi farin ciki da abin da ke wurinsu na ilmi kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi ya wajaba a kansu. = --Qur'an 40:83
    And when they saw Our punishment, they said," We believe in Allah alone and disbelieve in that which we used to associate with Him." <> Sa'an nan a lõkacin da suka ga azãbarMu, suka ce: "Mun yi ĩmãni da Allah, Shi kaɗai, kuma mun kãfirta da abin da muka kasance munã shirki da shi." = --Qur'an 40:84
    But never did their faith benefit them once they saw Our punishment. [It is] the established way of Allah which has preceded among His servants. And the disbelievers thereupon lost [all]. <> To ĩmaninsu bai kasance yanã amfaninsu ba a lõkacin da suka ga azãbarMu. Hanyar Allah wadda ta gabãta a cikin bãyinSa. Kuma kãfirai sun yi hasãra a can. = --Qur'an 40:85
    Ha, Meem. <> Ḥ. M̃. = --Qur'an 41:1
    [This is] a revelation from the Entirely Merciful, the Especially Merciful - <> Saukarwa (da Alƙur' ãni) dãga Mai rahama ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 41:2
    A Book whose verses have been detailed, an Arabic Qur'an for a people who know, <> Littãfi ne, an bayyana ãyõyinsa daki-daki, yanã abin karantãwa na Lãrabci, dõmin mutãnen dake sani = --Qur'an 41:3
    As a giver of good tidings and a warner; but most of them turn away, so they do not hear. <> Yanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. Sai mafi yawansu suka bijire. Sabõda haka sũ, bã su saurãrãwa. = --Qur'an 41:4
    And they say, "Our hearts are within coverings from that to which you invite us, and in our ears is deafness, and between us and you is a partition, so work; indeed, we are working." <> Kuma suka ce: "Zukatanmu nã a cikin kwasfa daga abin da kake Kiran mu zuwa gare shi, kuma a cikin kunnuwanmu akwai wani nauyi, kuma daga tsakaninmu da tsakaninka akwai wani shãmaki. sahõda haka ka yi aiki, lalle mũ mãsu aiki ne." = --Qur'an 41:5
    Say, O [Muhammad], "I am only a man like you to whom it has been revealed that your god is but one God; so take a straight course to Him and seek His forgiveness." And woe to those who associate others with Allah - <> Ka ce: "Nĩ mutum kawai ne kamarku, ãnã yin wahayi zuwa gare ni cẽwa abin bautãwarku, abin bautãwa guda ne. Sai ku daidaitu zuwa gare Shi, kuma ku nẽmi gafararSa." Kuma bone ya tabbata ga mãsu yin shirki. = --Qur'an 41:6
    Those who do not give zakah, and in the Hereafter they are disbelievers. <> Waɗanda bã su bãyar da zakka, kuma sũ a game da Lãhira su kafirai ne. = --Qur'an 41:7
    Indeed, those who believe and do righteous deeds - for them is a reward uninterrupted. <> Lalle wɗdanda suka yi ĩmãni, Kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bai yankẽwa. = --Qur'an 41:8
    Say, "Do you indeed disbelieve in He who created the earth in two days and attribute to Him equals? That is the Lord of the worlds." <> Ka ce: "Ashe lalle kũ, haƙĩƙa, kunã kafurta a game da wanda Ya halitta kasã a cikin kwanuka biyu, kuma kunã sanya Masa kĩshiyõyi? Wancan fa, shĩ ne Ubangijin halittu." = --Qur'an 41:9
    And He placed on the earth firmly set mountains over its surface, and He blessed it and determined therein its [creatures'] sustenance in four days without distinction - for [the information] of those who ask. <> Kuma Ya sanya, a cikinta, dũwatsu kafaffu daga samanta, kuma Ya sanya albarka a cikinta, kuma Ya ƙaddara abũbuwan cinta a cikinta a cikin kwanuka huɗu mãsu daidaita, dõmin matambaya. = --Qur'an 41:10
    Then He directed Himself to the heaven while it was smoke and said to it and to the earth, "Come [into being], willingly or by compulsion." They said, "We have come willingly." <> Sa'an nan Ya daidaita zuwa ga sama alhãli kuwa ita (a lõkacin) hayãƙi ce, sai Ya ce mata, ita da ƙasã "Ku zo, bisa ga yarda kõ a kan tĩlas." Suka ce: "Mun zo, munã mãsu ɗã'ã. " = --Qur'an 41:11
    And He completed them as seven heavens within two days and inspired in each heaven its command. And We adorned the nearest heaven with lamps and as protection. That is the determination of the Exalted in Might, the Knowing. <> Sai Ya hukunta su sammai bakwai a cikin kwãnuka biyu. Kuma Ya yi wahayi, a cikin kõwace sama da al'amarinta, kuma Muka kãwata sama ta kusa da fitilu kuma don tsari. Wancan ƙaddarãwar Mabuwãyi ne, Masani. = --Qur'an 41:12
    But if they turn away, then say, "I have warned you of a thunderbolt like the thunderbolt [that struck] 'Aad and Thamud. <> To, idan sun bijire sai ka ce: "Nã yi muku gargaɗi ga wata tsãwa kamar irin tsãwar Ãdãwa da samũdãwa." = --Qur'an 41:13
    [That occurred] when the messengers had come to them before them and after them, [saying], "Worship not except Allah." They said, "If our Lord had willed, He would have sent down the angels, so indeed we, in that with which you have been sent, are disbelievers." <> A lõkacin da Manzanninsu suka je musu daga gaba gare su kuma daga bãyansu, "Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah." suka ce: "Dã UbangiJinmu Yã so, lalle dã Ya saukar da malã' iku, sabõda haka lalle mũ, mãsu kafirta ne a game da abin da aka aiko ku da shi." = --Qur'an 41:14
    As for 'Aad, they were arrogant upon the earth without right and said, "Who is greater than us in strength?" Did they not consider that Allah who created them was greater than them in strength? But they were rejecting Our signs. <> To, amma Ãdãwa, sai suka yi girman kai a cikin kasã, bã da wani hakki ba, suka ce: "Wãne ne mafi tsananin ƙarfi daga gare mu?" Ashe, kuma ba su gani ba cẽwa Allah, wanda Ya halitta su Shĩne Mafi ƙarfi daga gare su, kuma sun kasance a game da ãyõyinMu suna yin musu? = --Qur'an 41:15
    So We sent upon them a screaming wind during days of misfortune to make them taste the punishment of disgrace in the worldly life; but the punishment of the Hereafter is more disgracing, and they will not be helped. <> Sai Muka aika, a kansu, da iska mai tsananin sauti da sanyi, a cikin kwãnuka na shu'umci, dõmin Mu ɗanɗana musu azãbar wulãƙanci, a cikin rãyuwar dũniya, kuma lalle azãbar Lãhira ita ce mafi wulãƙantarwa, kuma sũ bã zã a taimake su ba. = --Qur'an 41:16
    And as for Thamud, We guided them, but they preferred blindness over guidance, so the thunderbolt of humiliating punishment seized them for what they used to earn. <> Kuma amma Samũdãwa, sai Muka shiryar da su, sai suka fi son makanta a kan shiriya, dõmin haka tsawar azãbar wulãkanci, ta kamã su sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa (dõmin nẽman wata fã'ida). = --Qur'an 41:17
    And We saved those who believed and used to fear Allah. <> Kuma Muka tsĩrar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka kasance sunã yin taƙawa. = --Qur'an 41:18
    And [mention, O Muhammad], the Day when the enemies of Allah will be gathered to the Fire while they are [driven] assembled in rows, <> Kuma rãnar da ake tãra maƙiyan Allah zuwa wutã, to, sũ anã kakkange su. = --Qur'an 41:19
    Until, when they reach it, their hearing and their eyes and their skins will testify against them of what they used to do. <> Har idan sun jẽ mata, sai jinsu da ganinsu da fãtunsu, su yi shaida a kansu a game da abin da suka kasance sunã aikatawa. = --Qur'an 41:20
    And they will say to their skins, "Why have you testified against us?" They will say, "We were made to speak by Allah, who has made everything speak; and He created you the first time, and to Him you are returned. <> Kuma suka ce wa fãtunsu, "Don me kuka yi shaida a kanmu?" Suka ce: "Allah, Wanda ke sanya kõwane abu ya yi furuci, Shĩ ne Ya sanya mu mu yi furuci, kuma Shĩ ne Ya halitta ku can da farko, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku." = --Qur'an 41:21
    And you were not covering yourselves, lest your hearing testify against you or your sight or your skins, but you assumed that Allah does not know much of what you do. <> "Ba ku kasance kunã sani ba a ɓõye, cẽwa jinku zai yi shaida a kanku kuma ganinku zai yi, kuma fãtunku za su yi. Kuma amma kun yi zaton cẽwã Allah bai san abũbuwa mãsu yawa daga abin da kuke aikatãwa ba." = --Qur'an 41:22
    And that was your assumption which you assumed about your Lord. It has brought you to ruin, and you have become among the losers." <> "Kuma wancan zaton nãku wanda kuka yi zaton shi, game da Ubangijinku, ya halakar da ku, sai kuka wãyi gari a cikin mãsu hasãra." = --Qur'an 41:23
    So [even] if they are patient, the Fire is a residence for them; and if they ask to appease [Allah], they will not be of those who are allowed to appease. <> Sabõda haka idan sun yi hakuri, to, wutar, ita ce mazauni a gare su, kuma idan sun nẽmi yarda, to, ba su zama daga waɗanda ake yardwa ba. = --Qur'an 41:24
    And We appointed for them companions who made attractive to them what was before them and what was behind them [of sin], and the word has come into effect upon them among nations which had passed on before them of jinn and men. Indeed, they [all] were losers. <> Kuma Muka sallaɗar da mabiya a gare su, sai suka ƙawãta musu abin da ke a gabansu da abin da ke a bãyansu. Kuma kalmar azãba ta wajaba a kansu, a cikin wasu al'ummõmi da suka shũɗe a gabãninsu daga aljannu da mutãne. Lalle sũ, sun kasance mãsu hasãra. = --Qur'an 41:25
    And those who disbelieve say, "Do not listen to this Qur'an and speak noisily during [the recitation of] it that perhaps you will overcome." <> Kuma waɗanda suka kafirta suka cc, "Kada ku saurãra ga wannan Alkur' ãni, kuma ku yi ta yin kuwwa a ckin (lõkacin karãtun) sa, ɗammãninku zã ku rinjaya." = --Qur'an 41:26
    But We will surely cause those who disbelieve to taste a severe punishment, and We will surely recompense them for the worst of what they had been doing. <> Sabõda haka, lalle zã Mu ɗanɗana wa waɗanda suka kafirta wata azãba mai tsanani, kuma lalle zã Mu sãka musu da mafi mũnin abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 41:27
    That is the recompense of the enemies of Allah - the Fire. For them therein is the home of eternity as recompense for what they, of Our verses, were rejecting. <> Wancan shĩ ne sakamakon makiyan Allah, watau wuta. Sunã a gidan dawwama a cikinta, dõmin sakamako ga abin da suka kasance sunã yin musu game da ãyõyinMu. = --Qur'an 41:28
    And those who disbelieved will [then] say, "Our Lord, show us those who misled us of the jinn and men [so] we may put them under our feet that they will be among the lowest." <> Kuma waɗanda suka kafirta suka ce: "Yã Ubangijinmu! Ka nũnã mana wadannan biyun da suka batar da mu daga aljannu da mutãne, mu sanya su a karkashin, ƙafãfunmu, dõmin su kasance daga ƙaskantattu." = --Qur'an 41:29
    Indeed, those who have said, "Our Lord is Allah " and then remained on a right course - the angels will descend upon them, [saying], "Do not fear and do not grieve but receive good tidings of Paradise, which you were promised. <> Lalle waɗannan da suka ce: "Ubangjinmu, shĩ ne Allah," sa'an nan suka daidaitu, malã'iku na sassauka a kansu (a lõkacin saukar ajalinsu sunã ce musu) "Kada ku ji tsõro, kuma kada ku yi baƙin ciki, kuma ku yi bushãra da Aljanna, wadda kun kasance anã yi muku wa'adi da ita." = --Qur'an 41:30
    We [angels] were your allies in worldly life and [are so] in the Hereafter. And you will have therein whatever your souls desire, and you will have therein whatever you request [or wish] <> "Mũ ne majibintanku a cikin rãyuwar dũniya da kuma a cikin Lãhira, kuma a cikinta kunã da abin da rãyukanku ke sha'awa, kuma kunã da abin da kuke kira (akawo muku) a cikinta. = --Qur'an 41:31
    As accommodation from a [Lord who is] Forgiving and Merciful." <> "A kan liyãfa daga Mai gafara, Mai jin ƙai." = --Qur'an 41:32
    And who is better in speech than one who invites to Allah and does righteousness and says, "Indeed, I am of the Muslims." <> Kuma wãne ne mafi kyau ga magana daga wanda ya yi kira zuwa ga Allah, kuma ya aikata aiki na ƙwarai kuma ya ce: "Lalle nĩinã daga mãsu sallamãwar al'amari zuwa ga Allah?" = --Qur'an 41:33
    And not equal are the good deed and the bad. Repel [evil] by that [deed] which is better; and thereupon the one whom between you and him is enmity [will become] as though he was a devoted friend. <> Kuma kyautatãwa bã ta daidaita kuma haka mũnanãwa. Ka tunkuɗe cũta da abin da yake mafi kyau, sai ga shi wanda akwai ƙiyayya a tsakaninka da tsakaninsa, kamar dai shi majibinci ne, masoyi. = --Qur'an 41:34
    But none is granted it except those who are patient, and none is granted it except one having a great portion [of good]. <> Kuma bã za a cũsa wa kõwa wannan hãli ba fãce waɗanda suka yi haƙuri, kuma bã zã a cũsa shi ba fãce ga mai rabo mai gima. = --Qur'an 41:35
    And if there comes to you from Satan an evil suggestion, then seek refuge in Allah. Indeed, He is the Hearing, the Knowing. <> Kuma idan wata fizga ta fizge ka daga Shaiɗan, to ka nẽmi tsari ga Allah. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai ji, Masani. = --Qur'an 41:36
    And of His signs are the night and day and the sun and moon. Do not prostrate to the sun or to the moon, but prostate to Allah, who created them, if it should be Him that you worship. <> Kuma akwai daga ãyõyinSa, dare da yini, da rãnã da watã. Kada ku yi sujada ga rãnã, kuma kada ku yi ga watã. Kuma ku yi sujada ga Allah wanda Ya halitta su, idan kun kasance Shĩ ne kuke bauta wa. = --Qur'an 41:37
    But if they are arrogant - then those who are near your Lord exalt Him by night and by day, and they do not become weary. <> To, idan sun yi girman kai, to, waɗanda ke a wurin Ubangijinka, sunã tasbĩhi a gare Shi, a dare da rana, alhãli kuwa sũ, bã su ƙõsãwa. = --Qur'an 41:38
    And of His signs is that you see the earth stilled, but when We send down upon it rain, it quivers and grows. Indeed, He who has given it life is the Giver of Life to the dead. Indeed, He is over all things competent. <> Kuma akwai daga ãyõyinSa cẽwa lalle kai kanã ganin ƙasã ƙẽƙasasshiya, to, idan Mun saukar da ruwa a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura. Lalle wannan da Ya rãya ta, haƙĩƙa, Mai rãyar da matattu ne. Lalle Shĩ Mai ĩkon yi ne a kan kõwane abu. = --Qur'an 41:39
    Indeed, those who inject deviation into Our verses are not concealed from Us. So, is he who is cast into the Fire better or he who comes secure on the Day of Resurrection? Do whatever you will; indeed, He is Seeing of what you do. <> Lalle waɗannan da ke karkacẽwa a cikin ãyõyinMu, bã su fakuwa a gare Mu. Ashe fa, wanda ake jẽfãwa a cikin Wutã ne mafĩfĩci kõ kuwa wanda zai je amintacce a Rãnar ¡iyãma? Ku aikata abin da kuke so! Lalle Shĩ Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa. = --Qur'an 41:40
    Indeed, those who disbelieve in the message after it has come to them... And indeed, it is a mighty Book. <> Waɗannan da suka kãfirta game da Alkur'ãni a lõkacin da ya je musu, kuma lalle shi haƙĩƙa littãfi ne mabuwãyi. = --Qur'an 41:41
    Falsehood cannot approach it from before it or from behind it; [it is] a revelation from a [Lord who is] Wise and Praiseworthy. <> ¥arna bã zã ta je masa ba daga gaba gare shi. kuma bã zã ta zo ba daga bãya gare shi. Saukarwa ce daga Mai hikima, Gõdadde. = --Qur'an 41:42
    Nothing is said to you, [O Muhammad], except what was already said to the messengers before you. Indeed, your Lord is a possessor of forgiveness and a possessor of painful penalty. <> Bã zã a fada maka ba fãce abin da aka riga aka faɗa ga Manzannin da suke a gabãninka. Lalle Ubangijinka, haƙĩƙa, Ma'abũcin gãfara ne, kuma Ma'abũcin azãba mai raɗaɗi ne. = --Qur'an 41:43
    And if We had made it a non-Arabic Qur'an, they would have said, "Why are its verses not explained in detail [in our language]? Is it a foreign [recitation] and an Arab [messenger]?" Say, "It is, for those who believe, a guidance and cure." And those who do not believe - in their ears is deafness, and it is upon them blindness. Those are being called from a distant place. <> Kuma da Mun sanya shi abin karãtu na ajamanci, lalle dã sun ce, "Don me ba a bayyana ãyõyinsa ba? Ashe, zai yiwu a sãmi littãfi ba'ajame da Manzo Balãrabe?" Ka ce: "Shi, shiriya ne da warkewa ga waɗanda suka yi ĩmãni. Kuma wadanda ba su yi ĩmãni ba akwai wani nauyi a cikin kunnuwansu, kuma shi wata makanta ne a kansu. Waɗannan anã kiran su daga wuri mai nĩsa." = --Qur'an 41:44
    And We had already given Moses the Scripture, but it came under disagreement. And if not for a word that preceded from your Lord, it would have been concluded between them. And indeed they are, concerning the Qur'an, in disquieting doubt. <> Kuma lalle Mun bai wa Mũsã Littãfi, sai aka yi ɗãɓãni a cikinsa, Kuma ba dõmin wata kalma da tã gabata ba daga Ubangijinka, lalle dã an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma lalle sũ, haƙĩƙa sunã a cikin shakka daga, gare shi, mai sanya kõkanto. = --Qur'an 41:45
    Whoever does righteousness - it is for his [own] soul; and whoever does evil [does so] against it. And your Lord is not ever unjust to [His] servants. <> Wanda ya aikata aiki na ƙwarai to sabõda kansa ne, kuma wanda ya mũnanã, to, yanã akansa. Kuma Ubangiwinka, bã Mai zãlunci ga bãyinSa ne ba. = --Qur'an 41:46
    To him [alone] is attributed knowledge of the Hour. And fruits emerge not from their coverings nor does a female conceive or give birth except with His knowledge. And the Day He will call to them, "Where are My 'partners'?" they will say, "We announce to You that there is [no longer] among us any witness [to that]." <> Zuwa gare Shi ake mayar da sanin Sa'a. Kuma waɗansu 'yã'yan itãce bã su fita daga kwasfõfinsu, kuma wata mace bã ta yin ciki, kuma bã ta haihuwa, fãce da saninSa, kuma a rãnar da Yake kiran su (Ya ce): "Inã abõkan tãrayyaTa?" Sai su ce, "Mun sanar da Kai bãbu mai bãyar da shaida da haka nan daga gare mu." = --Qur'an 41:47
    And lost from them will be those they were invoking before, and they will be certain that they have no place of escape. <> Kuma abin da suka kasance sunã kira a gabãnin haka ya ɓace musu, kuma suka yi zaton cẽwa bã su da wata mafakã. = --Qur'an 41:48
    Man is not weary of supplication for good [things], but if evil touches him, he is hopeless and despairing. <> Mutum bã ya kõsãwa daga addu 'ar nẽman alhẽri kuma idan sharri ya shãfe shi, sai ya zama mai yanke kauna, Mai nũna kãsãwa. = --Qur'an 41:49
    And if We let him taste mercy from Us after an adversity which has touched him, he will surely say, "This is [due] to me, and I do not think the Hour will occur; and [even] if I should be returned to my Lord, indeed, for me there will be with Him the best." But We will surely inform those who disbelieved about what they did, and We will surely make them taste a massive punishment. <> Kuma lalle idan Mun ɗanɗana masa wata rahama daga gareMu, daga bãyan wata cũta ta shãfe shi, lalle zai ce, "Wannan (ni'ima) tãwa ce kuma bã ni zaton Sã'a mai tsayuwa ce, kuma lalle idan aka mayar da ni zuwa ga Ubangijĩna, haƙĩƙa, inã da makõma mafi kyau, a wurinSa." To, lalle zã Mu bã da lãbãri ga waɗanda suka kãfirta game da abin da suka aikata, kuma lalle Munã ɗanɗana musu daga azãba, Mai kauri. = --Qur'an 41:50
    And when We bestow favor upon man, he turns away and distances himself; but when evil touches him, then he is full of extensive supplication. <> Kuma idan Muka yi ni'ima ga mutum, sai ya bijire, kuma ya nĩsantar da gẽfensa, kuma idan sharri ya sãme shi, sai ya zama ma'abũcin addu'a mai fãɗi. = --Qur'an 41:51
    Say, "Have you considered: if the Qur'an is from Allah and you disbelieved in it, who would be more astray than one who is in extreme dissension?" <> Ka ce: "Ashe, kun gani! Idan (Alƙur'ãni) ya kasance daga Allah ne, sa'an nan kun kãfirta a game da Shi, wãne ne mafi ɓata daga wanda yake yanã a cikin sãɓani manisanci (daga gaskiya)?" = --Qur'an 41:52
    We will show them Our signs in the horizons and within themselves until it becomes clear to them that it is the truth. But is it not sufficient concerning your Lord that He is, over all things, a Witness? <> Zã Mu nũna musu ãyõyinMu a cikin sãsanni da kuma cikin rãyukansu, har ya bayyana a gare su cẽwã lalle (Alƙur'ãni), shi ne gaskiya. Ashe, kuma Ubangijinka bai isa ba, ga cẽwa lalle Shĩ halartacce ne a kan kowane abu ne? = --Qur'an 41:53
    Unquestionably, they are in doubt about the meeting with their Lord. Unquestionably He is, of all things, encompassing. <> To lalle sũ, sunã a cikin shakka daga gamuwa da Ubangijinsu. To, lalle Shĩ, Mai kẽwayẽwane ga dukan kõme ne. = --Qur'an 41:54
    Ha, Meem. <> Ḥ. M̃. = --Qur'an 42:1
    'Ayn, Seen, Qaf. <> Ĩ. Ṣ̃. = --Qur'an 42:2
    Thus has He revealed to you, [O Muhammad], and to those before you - Allah, the Exalted in Might, the Wise. <> Kamar wancãn (asĩrin) Allah, Mabuwayi, Mai hikima, ke yin wahayi zuwa gare ka da zuwa ga waɗanda ke gabãninka. = --Qur'an 42:3
    To Him belongs whatever is in the heavens and whatever is in the earth, and He is the Most High, the Most Great. <> (Allah) Shi ne da abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa, kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma. = --Qur'an 42:4
    The heavens almost break from above them, and the angels exalt [Allah] with praise of their Lord and ask forgiveness for those on earth. Unquestionably, it is Allah who is the Forgiving, the Merciful. <> Sammai nã kusan su tsãge daga bisansu, kuma malã'iku nã yin tasĩhi game da gõdẽ wa Ubangijinsu kuma sunã istigfãri dõmin wanda ke cikin ƙasa. To, lalle Allah Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai. = --Qur'an 42:5
    And those who take as allies other than Him - Allah is [yet] Guardian over them; and you, [O Muhammad], are not over them a manager. <> Kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majiɓinta waɗanda bã Shĩ ba Allah ne Mai tsaro a kansu, kuma kai, bã wakili ne a kansu ba. = --Qur'an 42:6
    And thus We have revealed to you an Arabic Qur'an that you may warn the Mother of Cities [Makkah] and those around it and warn of the Day of Assembly, about which there is no doubt. A party will be in Paradise and a party in the Blaze. <> Kuma kamar haka ne Muka yi wahayin abin karãntãwa (Alƙur'ãni) na Lãrabci zuwa gare ka, dõmin ka yi gargaɗi ga Uwar Alƙaryu (Makka) da wanda ke a kẽwayenta, kuma ka yi gargaɗi game da rãnar taruwa, bãbu shakka gare ta, wata ƙungiya tanã a cikin Aljanna kuma wata ƙungiya tãna a cikin sa'ĩr. = --Qur'an 42:7
    And if Allah willed, He could have made them [of] one religion, but He admits whom He wills into His mercy. And the wrongdoers have not any protector or helper. <> Kuma dã Allah Ya so, da Ya haɗã su al'umma guda, kuma Amma Yanã shigar da wanda Ya so a cikin rahamarSa alhãli kuwa azzãluMai bã su da, wani majiɓinci, kuma bã su da wani mataimaki. = --Qur'an 42:8
    Or have they taken protectors [or allies] besides him? But Allah - He is the Protector, and He gives life to the dead, and He is over all things competent. <> Kõ kuma sun riƙi waninSa majiɓinta? To Allah Shĩ ne Majiɓinci, kuma Shĩ ne ke rãyar da matattu alhãli kuwa Shĩ, Maiĩkon yi ne a kan dukan kõme. = --Qur'an 42:9
    And in anything over which you disagree - its ruling is [to be referred] to Allah. [Say], "That is Allah, my Lord; upon Him I have relied, and to Him I turn back." <> Kuma abin da kuka sãɓã wa jũna a cikinsa kõ mêne ne, to, hukuncinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah. Wancan Shĩ ne Allah Ubangijĩna, a gare Shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi nake mayar da al'amarĩna. = --Qur'an 42:10
    [He is] Creator of the heavens and the earth. He has made for you from yourselves, mates, and among the cattle, mates; He multiplies you thereby. There is nothing like unto Him, and He is the Hearing, the Seeing. <> (Shĩ ne) Mai ƙãga halittar sammai da ƙasa, Ya sanya muku ma'aura daga jinsinku, kuma (Ya sanya) daga dabbõbi maza da mãtã, Yanã halitta ku a cikinsu, wani abu bai zama kamar tamkarSa ba, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai gani. = --Qur'an 42:11
    To Him belong the keys of the heavens and the earth. He extends provision for whom He wills and restricts [it]. Indeed He is, of all things, Knowing. <> Shĩ ne da mabuɗan sammai da ƙasa Yanã shimfiɗa arziki ga wanda ya so kuma Yanã hukuntãwa. Lalle ne, Shĩ Masani ne ga dukan kõme. = --Qur'an 42:12
    He has ordained for you of religion what He enjoined upon Noah and that which We have revealed to you, [O Muhammad], and what We enjoined upon Abraham and Moses and Jesus - to establish the religion and not be divided therein. Difficult for those who associate others with Allah is that to which you invite them. Allah chooses for Himself whom He wills and guides to Himself whoever turns back [to Him]. <> Ya shar'anta muku, game da addini, abin da Ya yi wasiyya da shi ga Nũhu da abin da Muka yi wahayi da shi zuwa gare ka, da abin da Muka yi wasiyya da shi ga Ibrãhĩm da Mũsã da Ĩsã, cẽwa ku tsayar da addini sõsai kuma kada ku rarrabu a cikinsa. Abin da kuke kira zuwa gare shi, ya yi nauyi a kan mãsu shirki. Allah na zãɓen wanda Yake so zuwa gare Shi, kuma Yanã shiryar da wanda ke tawakkali gare Shi, ga hanyarSa. = --Qur'an 42:13
    And they did not become divided until after knowledge had come to them - out of jealous animosity between themselves. And if not for a word that preceded from your Lord [postponing the penalty] until a specified time, it would have been concluded between them. And indeed, those who were granted inheritance of the Scripture after them are, concerning it, in disquieting doubt. <> Kuma ba su rarraba ba fãce bãyan da ilmi ya jẽ musu, dõmin zãlunci a tsakãninsu kuma bã dõmin wata kalma tã gabata ba daga Ubangijinka, zuwa ga wani ajali ambatacce, dã an yi hukunci a tsakaninsu. Kuma lalle ne waɗanda aka gãdar wa Littafi daga bãyansu, haƙiƙa, sunã cikin shakka a gare shi, mai sanya kokanto. = --Qur'an 42:14
    So to that [religion of Allah] invite, [O Muhammad], and remain on a right course as you are commanded and do not follow their inclinations but say, "I have believed in what Allah has revealed of the Qur'an, and I have been commanded to do justice among you. Allah is our Lord and your Lord. For us are our deeds, and for you your deeds. There is no [need for] argument between us and you. Allah will bring us together, and to Him is the [final] destination." <> Sabõda haka, sai ka yi kira kuma kai ka daidaitu kamar yadda aka umurce ka, kuma kada ka bi son zũciyõyinsu, kumaka ce, "Nã yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar na littãfi, kuma an umurce ni da in yi ãdalci a tsakãninku. Allah ne Ubangijinmu, kuma Shĩ ne Ubangijinku, ayyukanmu nã gare mu, kuma ayyukanku nã gare ku, kuma bãbu wata hujja a tsakãninmu da tsakãninku. Allah zai tara mu, kuma zuwa gare Shi makõma take." = --Qur'an 42:15
    And those who argue concerning Allah after He has been responded to - their argument is invalid with their Lord, and upon them is [His] wrath, and for them is a severe punishment. <> Kuma waɗannan da ke jãyayya a cikin al'amarin Allah daga bãyan an karɓa masa, hujjarsu ɓãtãcciya ce a wurin Ubangijinsu, kuma akwai fushi a kansu, kuma sunã da wata azãba mai tsanani. = --Qur'an 42:16
    It is Allah who has sent down the Book in truth and [also] the balance. And what will make you perceive? Perhaps the Hour is near. <> Allah ne Wanda Ya saukar da Littãfi da gaskiya, da sikeli. Kuma me ya sanar da kai (cẽwa anã) tsammãnin Sa'ar kusa take? = --Qur'an 42:17
    Those who do not believe in it are impatient for it, but those who believe are fearful of it and know that it is the truth. Unquestionably, those who dispute concerning the Hour are in extreme error. <> Waɗanda ba su yi ĩmãnida ita ba, (sũ) ke nẽman gaggautõwarta. Alhãli kuwa waɗanda suka yi ĩmãni, mãsu tsõro ne daga gare ta, kuma sun sani, cẽwa ita gaskiya ce. To, lalle ne waɗanda ke shakka a cikin Sa'a, haƙĩƙa, sunã a cikin ɓata Mai nĩsa. = --Qur'an 42:18
    Allah is Subtle with His servants; He gives provisions to whom He wills. And He is the Powerful, the Exalted in Might. <> Allah Mai tausasãwa ne ga bãyinsa. Yanã azurta wanda yake so, alhãli kuma Shĩ ne Maiƙarfi, Mabuwãyi. = --Qur'an 42:19
    Whoever desires the harvest of the Hereafter - We increase for him in his harvest. And whoever desires the harvest of this world - We give him thereof, but there is not for him in the Hereafter any share. <> Wanda ya kasance yanã nufin nõman Lãhira zã Mu ƙãra masa a cikin nõmansa, kuma wanda ya kasance yanã nufin nõman dũniya, zã Mu sam masa daga gare ta, alhãli kuwa bã shi da wani rabo a cikin Lãhira. = --Qur'an 42:20
    Or have they other deities who have ordained for them a religion to which Allah has not consented? But if not for the decisive word, it would have been concluded between them. And indeed, the wrongdoers will have a painful punishment. <> Kõ sunã da waɗansu abõkan tãrayya (da Allah) waɗanda suka shar'anta musu, game da addini, abin da Allah bai yi izni ba da shi? Kuma bã dõmin kalmar hukunci ba, da lalle, an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma lalle azzãlumai sunã da azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 42:21
    You will see the wrongdoers fearful of what they have earned, and it will [certainly] befall them. And those who have believed and done righteous deeds will be in lush regions of the gardens [in Paradise] having whatever they will in the presence of their Lord. That is what is the great bounty. <> Kanã ganin azzãlumai sunã mãsu tsõro daga abin da suka sanã'anta alhãli kuwa shi abin tsoron, mai aukuwa ne gare su, kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai sunã a cikin fadamun Aljanna sunã da abin da suke so a wurin Ubangijinsu. Waccan fa ita ce falala mai girma. = --Qur'an 42:22
    It is that of which Allah gives good tidings to His servants who believe and do righteous deeds. Say, [O Muhammad], "I do not ask you for this message any payment [but] only good will through kinship." And whoever commits a good deed - We will increase for him good therein. Indeed, Allah is Forgiving and Appreciative. <> Wancan shĩ ne Allah ke bãyar da bushãra da shi ga bãyinSa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Ka ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa, fãce dai sõyayya ta cikin zumunta." Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, zã Mu ƙarã masa kyau a cikinsa, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai gõdiya. = --Qur'an 42:23
    Or do they say, "He has invented about Allah a lie"? But if Allah willed, He could seal over your heart. And Allah eliminates falsehood and establishes the truth by His words. Indeed, He is Knowing of that within the breasts. <> Kõ zã su ce: "Ya ƙirƙira ƙarya ga Allah ne?" To, idan Allah Ya so, zai yunƙe a kan zũciyarka, kuma Allah Yana shãfe ƙarya kuma Yana tabbatar da gaskiya da kalmõminSa. Lalle ne Shĩ Masani ne ga abin da ke cikin zukata. = --Qur'an 42:24
    And it is He who accepts repentance from his servants and pardons misdeeds, and He knows what you do. <> Kuma Shi ne ke karɓar tũba daga bãyinSa, kuma Yanã Yafe ƙananan laifuffuka, alhãli kuwa Yanã sanin abin da kuke aikatãwa. = --Qur'an 42:25
    And He answers [the supplication of] those who have believed and done righteous deeds and increases [for] them from His bounty. But the disbelievers will have a severe punishment. <> Kuma Yanã karɓa wa waɗannan da suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma Yanã ƙãra musu (sakamako) daga falalarSa. Kuma kãfirai sunã da wata azãba mai tsanani. = --Qur'an 42:26
    And if Allah had extended [excessively] provision for His servants, they would have committed tyranny throughout the earth. But He sends [it] down in an amount which He wills. Indeed He is, of His servants, Acquainted and Seeing. <> Kuma dã Allah Ya shimfiɗa arziki ga bãyinSa, dã sun yi zãluncin rarraba jama'a a cikin ƙasa, kuma amma Yanã sassaukarwa gwargwado ga abin da Yake so. Lalle ne Shĩ, game da bãyinSa, Mai labartawa ne, Mai gani. = --Qur'an 42:27
    And it is He who sends down the rain after they had despaired and spreads His mercy. And He is the Protector, the Praiseworthy. <> Kuma Shĩ ne ke sassaukar da girgije (ruwa) a bãyan sun yanke ƙauna kuma Yana wãtsa rahamarSa, alhãli kuwa Shĩ ne Majiɓinci, Mai gõdiya. = --Qur'an 42:28
    And of his signs is the creation of the heavens and earth and what He has dispersed throughout them of creatures. And He, for gathering them when He wills, is competent. <> Kuma akwai daga ãyõyinSa, halittar sammai da ƙasa da abin da Ya wãtsa a cikinsu na dabba alhãli kuwa Shĩ Mai ĩko ne ga tãra su, a lõkacin da Yake so. = --Qur'an 42:29
    And whatever strikes you of disaster - it is for what your hands have earned; but He pardons much. <> Kuma abin da ya sãme ku na wata masifa, to, game da abin da hannãyenku suka sana' anta ne kuma (Alah) Yanã Yafẽwar (waɗansu laifuffuka) mãsu yawa. = --Qur'an 42:30
    And you will not cause failure [to Allah] upon the earth. And you have not besides Allah any protector or helper. <> Kuma ba ku zama mãsu buwãya ba a cikin ƙasa kuma bã ku da wani majiɓinci, wanin Allah, kuma bã ku da wani mataimaki. = --Qur'an 42:31
    And of His signs are the ships in the sea, like mountains. <> Kuma akwai daga ãyõyinsa, jirãge mãsu gudãna a cikin tẽku kamar duwãtsu. = --Qur'an 42:32
    If He willed, He could still the wind, and they would remain motionless on its surface. Indeed in that are signs for everyone patient and grateful. <> Idan Ya so, sai Ya kwantar da iskar, sai jirãgen su yini sunã mãsu kawaici a kan bãyan tẽkun, Lalle ne ga wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga dukan mai haƙuri, Mai gõdiya. = --Qur'an 42:33
    Or He could destroy them for what they earned; but He pardons much. <> Kõ Ya halakã su (sũ jirãgen) sabõda abin da mãsu su suka sanã'anta, alhãli kuwa Yanã yãfe (laifuffuka) mãsu yawa. = --Qur'an 42:34
    And [that is so] those who dispute concerning Our signs may know that for them there is no place of escape. <> Kuma dõmin waɗanda ke jãyayya a cikin ãyõyinMu su sani (cẽwa) bã su da wata mafaka. = --Qur'an 42:35
    So whatever thing you have been given - it is but [for] enjoyment of the worldly life. But what is with Allah is better and more lasting for those who have believed and upon their Lord rely <> Sabõda haka abin da aka bã ku, kõ mẽne ne, to, jin dãɗin rayuwar dũniya ne, kuma abin da ke a wurin Allah Shĩ ne mafĩfĩci, kuma Shĩ ne mafi wanzuwa ga waɗanda suka yi ĩmãni kuma sunã dõgara a kan Ubangijinsu kawai. = --Qur'an 42:36
    And those who avoid the major sins and immoralities, and when they are angry, they forgive, <> Kuma waɗanda ke nisantar manyan zunubbai da ayyukan alfãsha, kuma idan sun yi fushi, sũ, sunã gãfartawa. = --Qur'an 42:37
    And those who have responded to their lord and established prayer and whose affair is [determined by] consultation among themselves, and from what We have provided them, they spend. <> Da waɗanda suka karɓa kira ga Ubangijinsu, kuma suka tsayar da salla, kuma al'amarinsu shãwara ne a tsakãninsu, kuma daga abin da Muka azurta su sunã ciyarwa. = --Qur'an 42:38
    And those who, when tyranny strikes them, they defend themselves, <> Da waɗanda idan zãlunci ya sãme su, sunã nẽman taimako (su rãma). = --Qur'an 42:39
    And the retribution for an evil act is an evil one like it, but whoever pardons and makes reconciliation - his reward is [due] from Allah. Indeed, He does not like wrongdoers. <> Kuma sakamakon cũta shĩ ne wata cũta kamarta, sai dai wanda Ya yãfe kuma ya kyautata, to lãdarsa nã ga Allah. Lalle ne, Shĩ (Allah) bã Ya son azzãlumai. = --Qur'an 42:40
    And whoever avenges himself after having been wronged - those have not upon them any cause [for blame]. <> Kuma Lalle ne, wanda ya nẽmi taimakon rãmãwa a bãyan an zãlunce shi, to waɗannan bãbu wata hanyar zargi a kansu. = --Qur'an 42:41
    The cause is only against the ones who wrong the people and tyrannize upon the earth without right. Those will have a painful punishment. <> lnda hanyar zargi kawai take, shĩ ne a kan waɗanda ke zãluntar mutãne kuma sunã ƙẽtare haddin shari'a cikin ƙasa bã tare da haƙƙi ba. Waɗannan sunã da azãba Mai raɗaɗi. = --Qur'an 42:42
    And whoever is patient and forgives - indeed, that is of the matters [requiring] determination. <> Kuma Lalle ne, wanda ya yi haƙuri kuma ya gãfarta (wa wanda ya zãlunce shi), to shĩ wancan aiki haƙĩƙa, yanã daga manyan al'amura (da Allah ke so). = --Qur'an 42:43
    And he whom Allah sends astray - for him there is no protector beyond Him. And you will see the wrongdoers, when they see the punishment, saying, "Is there for return [to the former world] any way?" <> Kuma wanda (Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani majiɓinci bãyanSa, kuma zã ka ga azzãlumai, a lõkacin da suka ga azãba, sunã cẽwa, "Shin, akwai hanya zuwa ga kõmãwa?" = --Qur'an 42:44
    And you will see them being exposed to the Fire, humbled from humiliation, looking from [behind] a covert glance. And those who had believed will say, "Indeed, the [true] losers are the ones who lost themselves and their families on the Day of Resurrection. Unquestionably, the wrongdoers are in an enduring punishment." <> Kuma kanã ganin su anã gitta su a kanta, sunã ƙasƙantattu sabõda wulãkanci, sunã hange daga gefen gani ɓoyayye. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sai su ce, "Lalle ne, mãsu hasãra, sũ ne waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu da iyãlansu a Rãnar ¡iyãma." To, lalle ne, azzãlumai sunã a cikin wata azãba zaunanniya. = --Qur'an 42:45
    And there will not be for them any allies to aid them other than Allah. And whoever Allah sends astray - for him there is no way. <> Kuma waɗansu majiɓinta ba su kasance ba a gare su, waɗanda ke iya taimakonsu, baicin Allah. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani gõdabe na tsĩra. = --Qur'an 42:46
    Respond to your Lord before a Day comes from Allah of which there is no repelling. No refuge will you have that day, nor for you will there be any denial. <> Ku karɓã wa Ubangijinku tun gabãnin wani yini ya zo, bãbu makawa gare shi daga Allah, bã ku da wata mafaka a rãnar nan, kuma bã ku iya yin wani musu. = --Qur'an 42:47
    But if they turn away - then We have not sent you, [O Muhammad], over them as a guardian; upon you is only [the duty of] notification. And indeed, when We let man taste mercy from us, he rejoices in it; but if evil afflicts him for what his hands have put forth, then indeed, man is ungrateful. <> To, idan sun bijire, to, ba Mu aike ka kanã mai tsaro a kansu ba, bãbu abin da ke a kanka fãce iyar da Manzanci. Kuma lalle ne, Mũ idan Mun ɗanɗana wa mutum wata rahama daga gare Mu, sai ya yi farin ciki da ita, kuma idan wata masĩfa ta sãme su sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, to, lalle ne mutum mai tsananin kãfirci ne. = --Qur'an 42:48
    To Allah belongs the dominion of the heavens and the earth; He creates what he wills. He gives to whom He wills female [children], and He gives to whom He wills males. <> Mulkin sammai da ƙasa na Allah kawai ne. Yanã halitta abin da Yake so. Yanã bãyar da 'ya'ya mãtã ga wanda yake so, kuma Yanã bãyar da ɗiya maza ga wanda Yake so. = --Qur'an 42:49
    Or He makes them [both] males and females, and He renders whom He wills barren. Indeed, He is Knowing and Competent. <> Kõ kuma Ya haɗa su maza da mãtã, kuma Yanã sanya wanda Ya so bakarãre. Lalle shi, Mai ilmi ne, Mai ĩkon yi. = --Qur'an 42:50
    And it is not for any human being that Allah should speak to him except by revelation or from behind a partition or that He sends a messenger to reveal, by His permission, what He wills. Indeed, He is Most High and Wise. <> Kuma bã ya kasancẽwa ga wani mutum Allah Ya yi masa magana fãce da wahayi, kõ daga bãYan wani shãmaki, kõ Ya aika wani Manzo, sa'an nan Ya yi wahayi, da izninsa ga abin da Yake so. Lalle Shĩ, Maɗaukaki ne Mai hikima. = --Qur'an 42:51
    And thus We have revealed to you an inspiration of Our command. You did not know what is the Book or [what is] faith, but We have made it a light by which We guide whom We will of Our servants. And indeed, [O Muhammad], you guide to a straight path - <> Kuma kamar wancan Mun aika wani rũhi (rai mai haɗa jama'a) zuwa gare ka, daga gare Mu. Ba ka kasance kã san abin da yake littãfi ba, kõ abin da Yake ĩmãni, kuma amma Mun sanya shi (rũhin, watau Alƙur'ãni) wani haske ne, Munã shiryar da wanda Muke so daga cikin bãyĩnMu game da shi. Kuma Lalle kai, haƙĩƙa, kanã shiryarwa zuwa ga hanya, madaidaiciya. = --Qur'an 42:52
    The path of Allah, to whom belongs whatever is in the heavens and whatever is on the earth. Unquestionably, to Allah do [all] matters evolve. <> Hanyar Allah wanda ke da mulkin abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa. To, zuwa ga Allah kawai al'amura ke kõmãwa. = --Qur'an 42:53
    Ha, Meem. <> Ḥ. M̃. = --Qur'an 43:1
    By the clear Book, <> Ina rantsuwa da Littãfi Mabayyani. = --Qur'an 43:2
    Indeed, We have made it an Arabic Qur'an that you might understand. <> Lalle Mũ, Mun sanya shi abin karãtu na Lãrabci, tsammãninku, kunã hankalta. = --Qur'an 43:3
    And indeed it is, in the Mother of the Book with Us, exalted and full of wisdom. <> Kuma lalle, shĩ, a cikin uwar littãfi a wurin Mu, haƙĩƙa, maɗaukaki ne, bayyananne. = --Qur'an 43:4
    Then should We turn the message away, disregarding you, because you are a transgressing people? <> Shin, zã Mu kau da kai daga saukar da hukunci daga gare ku ne dõmin kun kasance mutane mãsu ɓarna? = --Qur'an 43:5
    And how many a prophet We sent among the former peoples, <> Alhãli kuwa sau nawa Muka aika wani Annabi a cikin mutãnen fãrko! = --Qur'an 43:6
    But there would not come to them a prophet except that they used to ridicule him. <> Kuma wani Annabi bai je musu ba fãce sun kasance, game da shi, sunã mãsu yin izgili. = --Qur'an 43:7
    And We destroyed greater than them in [striking] power, and the example of the former peoples has preceded. <> Sai Muka halakar da waɗanda suke sũ ne mafiya ƙarfin damƙa daga gare su. Kuma abin misãlin mutãnen farkon ya shũɗe. = --Qur'an 43:8
    And if you should ask them, "Who has created the heavens and the earth?" they would surely say, "They were created by the Exalted in Might, the Knowing." <> Kuma lalle ne, idan ka tambaye su, "Wãne ne ya halitta sammai da ƙasa?" Lalle zã su ce, "Mabuwãyi Mai ilmi ne Ya halitta su." = --Qur'an 43:9
    [The one] who has made for you the earth a bed and made for you upon it roads that you might be guided <> Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa kuma Ya sanya muku hanyõyi a cikinta, tsammãninku za ku nẽmi shiryuwa.' = --Qur'an 43:10
    And who sends down rain from the sky in measured amounts, and We revive thereby a dead land - thus will you be brought forth - <> Kuma Wanda Ya saukar da ruwa daga sama, a kan wani gwargwado, sai Muka rãyar da gari matacce game da shi. Kamar haka nan ake fitar da ku (daga kabari). = --Qur'an 43:11
    And who created the species, all of them, and has made for you of ships and animals those which you mount. <> Kuma Wanda Ya halitta ma'aura dukansu, kuma Ya sanya muku, daga jirgi da dabbõbin ni'ima, abin da kuke hawa. = --Qur'an 43:12
    That you may settle yourselves upon their backs and then remember the favor of your Lord when you have settled upon them and say. "Exalted is He who has subjected this to us, and we could not have [otherwise] subdued it. <> Domin ku daidaitu a kan bãyansa, sa'an nan ku tuna ni'imar Ubangijinku a lõkacin da kuka daidaita a kansa kuma ku ce, "Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya hõre mana wannan alhãli kuwa ba mu kasance mãsu iya rinjãya gare Shi ba. = --Qur'an 43:13
    And indeed we, to our Lord, will [surely] return." <> "Kuma lalle mũ haƙĩƙa mãsu jũyãwa muke, zuwa ga Ubangijinmu." = --Qur'an 43:14
    But they have attributed to Him from His servants a portion. Indeed, man is clearly ungrateful. <> Kuma suka sanya Masa juz'i daga bãyinsa. Lalle ne mutum, haƙĩƙa, mai yawan kãfirci ne, mai bayyanãwar kãfircin. = --Qur'an 43:15
    Or has He taken, out of what He has created, daughters and chosen you for [having] sons? <> Kõ zã Ya ɗauki 'ya'ya mãtã daga abin da Yake halittawa ne, kuma Ya zãɓe ku da ɗiya maza? = --Qur'an 43:16
    And when one of them is given good tidings of that which he attributes to the Most Merciful in comparison, his face becomes dark, and he suppresses grief. <> Alhãli kuwa idan an bãyar da bushãra ga ɗayansu da abin da ya buga misãli da shi ga Mai rahama, sai fuskarsa ta yini tanã wadda aka baƙanta launinta, kuma yanã cike da baƙin ciki. = --Qur'an 43:17
    So is one brought up in ornaments while being during conflict unevident [attributed to Allah]? <> Ashe, kuma (Allah zai zãɓi) wanda ake rẽno a cikin ƙawa alhãli kuwa gã shi a husũma bã mai iya bayyanawar magana ba? = --Qur'an 43:18
    And they have made the angels, who are servants of the Most Merciful, females. Did they witness their creation? Their testimony will be recorded, and they will be questioned. <> Kuma suka mayar da malã'iku ('yã'ya) mãtã, alhãli kuwa sũ, waɗanda suke bãyin (Allah) Mai rahama ne! Shin, sun halarci halittarsu ne? zã a rubũta shaidarsu kuma a tambaye su. = --Qur'an 43:19
    And they said, "If the Most Merciful had willed, we would not have worshipped them." They have of that no knowledge. They are not but falsifying. <> Kuma suka ce: "Dã Mai rahama ya so, dã ba mu bauta musu ba." Bã su da wani ilmi game da wancan! Bãbu abin da suke yi fãce yanki-faɗi. = --Qur'an 43:20
    Or have We given them a book before the Qur'an to which they are adhering? <> Kõ Mun bã su wani littãfi ne a gabãninsa (Alƙur'ãni) sabõda haka da shĩ suke riƙe? = --Qur'an 43:21
    Rather, they say, "Indeed, we found our fathers upon a religion, and we are in their footsteps [rightly] guided." <> Ã'a, sun ce dai, "Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani addini (na al'ãda) kuma lalle mũ, a kan gurãbunsu muke mãsu nẽman shiryuwa." = --Qur'an 43:22
    And similarly, We did not send before you any warner into a city except that its affluent said, "Indeed, we found our fathers upon a religion, and we are, in their footsteps, following." <> Kuma kamar haka, ba Mu aika wani mai gargaɗi ba a gabãninka, a cikin wata alƙarya, fãce mani'imtanta sun ce, "Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani addini kuma lalle mũ, mãsu kõyi nea kan gurãbunsu." = --Qur'an 43:23
    [Each warner] said, "Even if I brought you better guidance than that [religion] upon which you found your fathers?" They said, "Indeed we, in that with which you were sent, are disbelievers." <> (Sai mai gargaɗin) ya ce: "Shin, ban zo muku da abin da ya fi zama shiriya daga abin da kuka sãmi ubanninku a kansa ba?" Suka ce, "Lalle mũ dai mãsu kafirta ne game da abin da aka aiko ku da shi." = --Qur'an 43:24
    So we took retribution from them; then see how was the end of the deniers. <> Sabõda haka Muka yi musu azãbar rãmuwa. To, ka dũbi yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa take. = --Qur'an 43:25
    And [mention, O Muhammad], when Abraham said to his father and his people, "Indeed, I am disassociated from that which you worship <> Kuma (ka ambaci) lõkacin da Ibrãhĩm ya ce wa ubansada mutãnensa, "Lalle nĩ mai barranta ne daga abin da kuke bautãwa." = --Qur'an 43:26
    Except for He who created me; and indeed, He will guide me." <> "Fãce wannan da Ya ƙãga halittata, to, lalle Shĩ ne zai shiryar da ni." = --Qur'an 43:27
    And he made it a word remaining among his descendants that they might return [to it]. <> Kuma (Ibrãhĩm) ya sanya (ita wannan magana) kalma mai wanzuwa a cikin zuriyarsa, tsammãninsu su kõmo daga ɓata. = --Qur'an 43:28
    However, I gave enjoyment to these [people of Makkah] and their fathers until there came to them the truth and a clear Messenger. <> Ã'a, Na jiyar da waɗannan mutãne dãɗi sũ da ubanninsu har gaskiya, da Manzo mai bayyanawar gaskiyar, ya zo musu. = --Qur'an 43:29
    But when the truth came to them, they said, "This is magic, and indeed we are, concerning it, disbelievers." <> Kuma a lõkacin da gaskiyar ta jẽ musu sai suka ce: "Wannan sihiri ne kuma mũ mãsu kãfirta da shi ne." = --Qur'an 43:30
    And they said, "Why was this Qur'an not sent down upon a great man from [one of] the two cities?" <> Kuma suka ce: "Don me ba a saukar da wannan Alƙur'ãni a kan wani mutum mai girma daga alƙaryun nan biyu ba?" = --Qur'an 43:31
    Do they distribute the mercy of your Lord? It is We who have apportioned among them their livelihood in the life of this world and have raised some of them above others in degrees [of rank] that they may make use of one another for service. But the mercy of your Lord is better than whatever they accumulate. <> Shin, sũ ne ke raba rahamar Ubangijinka? Mũ ne, Muka raba musu abincinsu a cikin rãyuwar dũniya, kuma Muka ɗaukaka waɗansunsu a kan waɗansu da darajõji dõmin waɗansunsu su riƙi waɗansu lẽburori kumarahamar Ubangijinka (ta Annabci), ita ce mafificiya daga abin da suke tãrãwa. = --Qur'an 43:32
    And if it were not that the people would become one community [of disbelievers], We would have made for those who disbelieve in the Most Merciful - for their houses - ceilings and stairways of silver upon which to mount <> Kuma bã dõmin mutane su kasance al'umma ɗaya ba, lalle ne, dã Mun sanya wa mãsu kãfircẽ wa Mai Rahama, a gidãjensu, rufi na azurfa, kuma da matãkalai, ya zama a kanta suke tãƙãwa. = --Qur'an 43:33
    And for their houses - doors and couches [of silver] upon which to recline <> Kuma a gidãjensu, Mu sanya) ƙyamãre da gadãje, a kansu suke kishingiɗa. = --Qur'an 43:34
    And gold ornament. But all that is not but the enjoyment of worldly life. And the Hereafter with your Lord is for the righteous. <> Da zĩnãriya. Kuma dukan wancan abu bai zama ba, sai jin dãɗin rãyuwar dũniya nekawai' alhãli kuwa Lãhira, a wurin Ubangijinka, ta mãsu taƙawa ce. = --Qur'an 43:35
    And whoever is blinded from remembrance of the Most Merciful - We appoint for him a devil, and he is to him a companion. <> Kuma wanda ya makanta daga barin hukuncin Mai rahama, to, zã Mu lulluɓe shi da shaiɗan, watau shĩ ne abõkinsa. = --Qur'an 43:36
    And indeed, the devils avert them from the way [of guidance] while they think that they are [rightly] guided <> Kuma lalle su haƙĩƙa sunã kange su daga hanya, kuma sunã Zaton cẽwa sũ mãsu shiryuwa ne. = --Qur'an 43:37
    Until, when he comes to Us [at Judgement], he says [to his companion], "Oh, I wish there was between me and you the distance between the east and west - how wretched a companion." <> Har a lõkacin da (abõkin Shaiɗan) ya zo Mana (ya mutu) sai ya ce: (wa Shaiɗan) "Dã dai a tsakãnina da tsakãninka akwai nĩsan gabas da yamma, sabõda haka, tir da kai ga zama abõkin mutum!" = --Qur'an 43:38
    And never will it benefit you that Day, when you have wronged, that you are [all] sharing in the punishment. <> Kuma (wannan magana) bã za ta amfãne ku ba, a yau, dõmin kun yi zãlunci, lalle ku mãsu tãrẽwa ne a cikin azãba. = --Qur'an 43:39
    Then will you make the deaf hear, [O Muhammad], or guide the blind or he who is in clear error? <> Shin to, kai kanã jiyar da kurma ne, ko kanã shiryar da makãho da wanda ke a cikin ɓata bayyananna? = --Qur'an 43:40
    And whether [or not] We take you away [in death], indeed, We will take retribution upon them. <> To, kõ dai Mu tafi da kai to, lalle Mũ, mãsu yin azãbarrãmu, wa ne a kansu. = --Qur'an 43:41
    Or whether [or not] We show you that which We have promised them, indeed, We are Perfect in Ability. <> Kõ kuma Mu nũna maka abin da Muka yi musu wa'adi, to, lalle Mũ, Mãsu ĩkon tasarrufi a kansu ne. = --Qur'an 43:42
    So adhere to that which is revealed to you. Indeed, you are on a straight path. <> Sabõda haka, ka yi riƙo ga abin da aka yi wahayi da shi zuwa gaie ka. Lalle ne kai, kanã a kan hanya madaidaiciyl. = --Qur'an 43:43
    And indeed, it is a remembrance for you and your people, and you [all] are going to be questioned. <> Kuma shi (abin wahayin) ambato (na ɗaukaka) ne a gare ka da kuma ga mutãnenka, kuma zã a tambaye ku. = --Qur'an 43:44
    And ask those We sent before you of Our messengers; have We made besides the Most Merciful deities to be worshipped? <> Kuma ka tambayi waɗanda Muka aika a gabãninka daga Manzannin Mu, "Shin, Mun sanya waɗansu gumãka, wasun (Allah), Mai rahama, anã bauta musu?" = --Qur'an 43:45
    And certainly did We send Moses with Our signs to Pharaoh and his establishment, and he said, "Indeed, I am the messenger of the Lord of the worlds." <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Mũsã, game da ãyõyin Mu, zuwa ga Fir'auna da mashãwartansa, sai ya ce: "Lalle nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu." = --Qur'an 43:46
    But when he brought them Our signs, at once they laughed at them. <> To, a lõkacin da ya jẽ musu da ãyõyinMu, sai gã su sunã yi musu dãriya. = --Qur'an 43:47
    And We showed them not a sign except that it was greater than its sister, and We seized them with affliction that perhaps they might return [to faith]. <> Kuma ba Mu nũna musu wata ãyã ba, fãce ita ce mafi girma daga 'yar'uwarta. Kuma Muka kãma su da azãba, tsammãninsu kõ sunã kõmõwa. = --Qur'an 43:48
    And they said [to Moses], "O magician, invoke for us your Lord by what He has promised you. Indeed, we will be guided." <> Kuma suka ce: "Yã kai mai sihiri! Ka rõƙa mana Ubangijinka da albarkacin abin da yi alkawari a wurinka, lalle mũ, haƙĩƙa, mãsu shiryuwa ne." = --Qur'an 43:49
    But when We removed from them the affliction, at once they broke their word. <> To, a lõkacin da duk Muka kuranye musu azãba, sai gã su sunã warware alkawarinsu. = --Qur'an 43:50
    And Pharaoh called out among his people; he said, "O my people, does not the kingdom of Egypt belong to me, and these rivers flowing beneath me; then do you not see? <> Kuma Fir'auna ya yi kira a cikin mutãnensa, ya ce: "Ya mutãnẽna! Ashe mulkin Masar bã a gare ni yake ba, kuma waɗannan kõguna sunã gudãna daga ƙarƙashĩna? Ashe, ba ku gani ba?" = --Qur'an 43:51
    Or am I [not] better than this one who is insignificant and hardly makes himself clear? <> "Kõ kuma bã nĩ ne mafĩfĩci ba daga wannan wanda yake shĩ wulakantacce ne kuma bã ya iya bayyanawar magana sai da ƙyar? = --Qur'an 43:52
    Then why have there not been placed upon him bracelets of gold or come with him the angels in conjunction?" <> "To, don me, ba a jẽfa mundãye na zĩnãriya a kansaba, kõ kuma malã'iku su taho tãre da shi haɗe?" = --Qur'an 43:53
    So he bluffed his people, and they obeyed him. Indeed, they were [themselves] a people defiantly disobedient [of Allah]. <> Sai ya sassabce hankalin mutãnensa, sabõda haka suka bĩ shi. Lalle sũ, sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai. = --Qur'an 43:54
    And when they angered Us, We took retribution from them and drowned them all. <> Sabõda haka a lõkacin da suka husãtar da Mu, Muka yi musu azãbar rãmuwa sai Muka nutsar da su gabã ɗaya. = --Qur'an 43:55
    And We made them a precedent and an example for the later peoples. <> Sai Muka sanya su magabãta kuma abin misãli ga mutãnen ƙarshe. = --Qur'an 43:56
    And when the son of Mary was presented as an example, immediately your people laughed aloud. <> Kuma a lõkacin da aka buga misãli da ¦an Maryama, sai gã mutãnenka daga gare shi (shi misalin) sunã dãriya da izgili. = --Qur'an 43:57
    And they said, "Are your gods better, or is he?" They did not present the comparison except for [mere] argument. But, [in fact], they are a people prone to dispute. <> Kuma suka ce: "Shin, gumãkanmu ne mafĩfĩta kõ shi (¦an Maryama)?" Ba su buga wannan misãli ba a gare ka fãce dõmin yin jidãli. Ã'a, sũ mutãne nemãsu husũma. = --Qur'an 43:58
    Jesus was not but a servant upon whom We bestowed favor, and We made him an example for the Children of Israel. <> Shi (¦an Maryama) bai zama ba fãce wani bãwa ne, Mun yi ni'ima a gare shi, kuma Muka sanya shi abin kõyi ga Banĩ Isrã'ĩla. = --Qur'an 43:59
    And if We willed, We could have made [instead] of you angels succeeding [one another] on the earth. <> Kuma dã Munã so lalle ne dã Mun sanya malã'iku, daga ci, kinku, a cikin ƙasa, sunã mayẽwa = --Qur'an 43:60
    And indeed, Jesus will be [a sign for] knowledge of the Hour, so be not in doubt of it, and follow Me. This is a straight path. <> Kuma lalle shĩ, haƙĩƙa, wani ilmi ne na Sa'a, sabõda haka, kada ku yi shakka a gare ta, kuma ku bĩ Ni. Wannan ita ce hanya madaidaiciya. = --Qur'an 43:61
    And never let Satan avert you. Indeed, he is to you a clear enemy. <> Kuma kada Shaiɗan ya taushe ku (daga hanyar). Lalle shĩ maƙiyi ne a gare ku, mai bayyanãwar ƙiyayya. = --Qur'an 43:62
    And when Jesus brought clear proofs, he said, "I have come to you with wisdom and to make clear to you some of that over which you differ, so fear Allah and obey me. <> Kuma a lõkacin da Ĩsã ya jẽ da hujjõji bayyanannu, ya ce: "Lalle ne nã zo muku da hikima kuma dõmin in bayyana muku, sãshen abin da kuke sãɓã wa jũna acikinsa, sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'a." = --Qur'an 43:63
    Indeed, Allah is my Lord and your Lord, so worship Him. This is a straight path." <> "Lalle ne, Allah Shĩ ne Ubangijina kuma Shi ne Ubangijinku sabõda haka ku bauta Masa. Wannan ita ce hanya madaidaiciya." = --Qur'an 43:64
    But the denominations from among them differed [and separated], so woe to those who have wronged from the punishment of a painful Day. <> Sai ƙungiyõyi suka sãɓa a tsakãninsu. To, bone yã tabbata ga waɗanda suka yi zãlunci daga azãbar yini mai raɗaɗi! = --Qur'an 43:65
    Are they waiting except for the Hour to come upon them suddenly while they perceive not? <> Shin sunã jiran wani abu ne? sai dai Sa'a ta jẽ musu bisaga abke, alhãli kuwa ba su sani ba. = --Qur'an 43:66
    Close friends, that Day, will be enemies to each other, except for the righteous <> Masõya a yinin nan, sãshensu zuwa ga sãshe maƙiya ne, fãce mãsu taƙawa (sũ kam mãsu son jũna ne). = --Qur'an 43:67
    [To whom Allah will say], "O My servants, no fear will there be concerning you this Day, nor will you grieve, <> Ya bãyĩNa! Bãbu tsõro a kanku a yau, kuma bã zã ku yi baƙin ciki ba. = --Qur'an 43:68
    [You] who believed in Our verses and were Muslims. <> Waɗanda suka yi ĩmãni da ãyõyinMu, kuma suka kasance mãsu sallamawar al'amari (ga Allah). = --Qur'an 43:69
    Enter Paradise, you and your kinds, delighted." <> Ku shiga Aljanna, kũ da mãtan aurenku, anã girmama ku. = --Qur'an 43:70
    Circulated among them will be plates and vessels of gold. And therein is whatever the souls desire and [what] delights the eyes, and you will abide therein eternally. <> Anã kẽwayãwa a kansu da akussa na zĩnãriya da kõfuna, alhãli kuwa a cikinsu akwai abin da rãyuka ke marmari kuma idãnu su ji dãɗi, kuma kũ, a cikinta (Aljannar), madawwama ne. = --Qur'an 43:71
    And that is Paradise which you are made to inherit for what you used to do. <> Kuma waccan ita ce Aljannar, wannan da aka gãdar da ku ita sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa. = --Qur'an 43:72
    For you therein is much fruit from which you will eat. <> Kunã sãmu, a cikinta, 'yã'yan itãcen marmari mãsu yawa, daga cikinsu kuke ci. = --Qur'an 43:73
    Indeed, the criminals will be in the punishment of Hell, abiding eternally. <> Lalle mãsu laifi madawwama ne a cikin azãbar Jahannama. = --Qur'an 43:74
    It will not be allowed to subside for them, and they, therein, are in despair. <> Bã a sauƙaƙar da ita (azãbar) daga gare su, alhãli kuwa sũ, a cikinta, mãsu kãsa magana ne. = --Qur'an 43:75
    And We did not wrong them, but it was they who were the wrongdoers. <> Kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sũ ne suka kasance azzãlumai. = --Qur'an 43:76
    And they will call, "O Malik, let your Lord put an end to us!" He will say, "Indeed, you will remain." <> Kuma suka yi kira, "Ya Mãliku! Ubangijinka Ya kashe mu mana " (Mãliku) ya ce: "Lalle kũ mazauna ne." = --Qur'an 43:77
    We had certainly brought you the truth, but most of you, to the truth, were averse. <> Lalle ne, haƙĩƙa, Mun jẽ muku da gaskiya, kuma amma mafi yawanku mãsu ƙi ga gaskiyar ne. = --Qur'an 43:78
    Or have they devised [some] affair? But indeed, We are devising [a plan]. <> Kõ kuma sun tukka wani al'amari ne? To, lalle Mũ, Mãsu tukkãwa ne. = --Qur'an 43:79
    Or do they think that We hear not their secrets and their private conversations? Yes, [We do], and Our messengers are with them recording. <> Ko sunã zaton lalle Mũ, bã Mu jin asĩrinsu da gãnãwarsu? Na'am! Kuma manzannin Mu na tãre da su sunã rubũtãwa. = --Qur'an 43:80
    Say, [O Muhammad], "If the Most Merciful had a son, then I would be the first of [his] worshippers." <> Ka ce: "Idan har akwai ɗã ga Mai rahama, to, nĩ ne farkon mãsu bauta (wa ɗan)." = --Qur'an 43:81
    Exalted is the Lord of the heavens and the earth, Lord of the Throne, above what they describe. <> Tsarkin Ubangijin sammai da ƙasa, Ubangijin Al'arshi, ya tabbata daga abin da suke sifantãwa. = --Qur'an 43:82
    So leave them to converse vainly and amuse themselves until they meet their Day which they are promised. <> Sabõda haka, ka ƙyãlẽ su, su kũtsa kuma su yi wãsã har su haɗu da yininsu, wanda ake yi musu wa'adi da shi. = --Qur'an 43:83
    And it is Allah who is [the only] deity in the heaven, and on the earth [the only] deity. And He is the Wise, the Knowing. <> Kuma Shĩ ne wanda ke abin bautãwa a sama kuma abin bautãwa a ƙasa, kuma, Shĩ ne Mai hikima, Masani. = --Qur'an 43:84
    And blessed is He to whom belongs the dominion of the heavens and the earth and whatever is between them and with whom is knowledge of the Hour and to whom you will be returned. <> Kuma albarkar wanda ke da mulkin sammai da ƙasã abin da ke a tsakãninsu tã bayyana, kuma a wurinSa ne ilmin Sa'a yake, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku. = --Qur'an 43:85
    And those they invoke besides Him do not possess [power of] intercession; but only those who testify to the truth [can benefit], and they know. <> Kuma waɗanda suke kira baicinSa ba su mallaki cẽto ba, fãce wanda ya yi shaida da gaskiya, kuma sũ, sunã sane (da haka). = --Qur'an 43:86
    And if you asked them who created them, they would surely say, "Allah." So how are they deluded? <> Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wãne ne ya halitta su?" Lalle ne zã su ce Allah ne. To, yãya ake jũyar da su? = --Qur'an 43:87
    And [Allah acknowledges] his saying, "O my Lord, indeed these are a people who do not believe." <> Kuma da (ilmin) maganarSa (Annabi) "Ya Ubangijĩna! Lalle waɗannan mutãne ne waɗanda bã zã su yi ĩmãni ba." = --Qur'an 43:88
    So turn aside from them and say, "Peace." But they are going to know. <> To, sai ka kau da kai daga gare su, kuma ka ce, "salãmã." Sa'an nan kuma zã su sani. = --Qur'an 43:89
    Ha, Meem. <> Ḥ. M̃. = --Qur'an 44:1
    By the clear Book, <> Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani. = --Qur'an 44:2
    Indeed, We sent it down during a blessed night. Indeed, We were to warn [mankind]. <> Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi. = --Qur'an 44:3
    On that night is made distinct every precise matter - <> A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne. = --Qur'an 44:4
    [Every] matter [proceeding] from Us. Indeed, We were to send [a messenger] <> Umurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMãsu aikãwã. = --Qur'an 44:5
    As mercy from your Lord. Indeed, He is the Hearing, the Knowing. <> Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani. = --Qur'an 44:6
    Lord of the heavens and the earth and that between them, if you would be certain. <> (Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka). = --Qur'an 44:7
    There is no deity except Him; He gives life and causes death. [He is] your Lord and the Lord of your first forefathers. <> Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko. = --Qur'an 44:8
    But they are in doubt, amusing themselves. <> A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka. = --Qur'an 44:9
    Then watch for the Day when the sky will bring a visible smoke. <> Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne. = --Qur'an 44:10
    Covering the people; this is a painful torment. <> Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi. = --Qur'an 44:11
    [They will say], "Our Lord, remove from us the torment; indeed, we are believers." <> Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne. = --Qur'an 44:12
    How will there be for them a reminder [at that time]? And there had come to them a clear Messenger. <> Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)? = --Qur'an 44:13
    Then they turned away from him and said, "[He was] taught [and is] a madman." <> Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa ne, mahaukaci." = --Qur'an 44:14
    Indeed, We will remove the torment for a little. Indeed, you [disbelievers] will return [to disbelief]. <> Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin). = --Qur'an 44:15
    The Day We will strike with the greatest assault, indeed, We will take retribution. <> Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne. = --Qur'an 44:16
    And We had already tried before them the people of Pharaoh, and there came to them a noble messenger, <> Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu. = --Qur'an 44:17
    [Saying], "Render to me the servants of Allah. Indeed, I am to you a trustworthy messenger," <> (Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku." = --Qur'an 44:18
    And [saying], "Be not haughty with Allah. Indeed, I have come to you with clear authority. <> "Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne." = --Qur'an 44:19
    And indeed, I have sought refuge in my Lord and your Lord, lest you stone me. <> "Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni." = --Qur'an 44:20
    But if you do not believe me, then leave me alone." <> "Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni." = --Qur'an 44:21
    And [finally] he called to his Lord that these were a criminal people. <> Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi. = --Qur'an 44:22
    [Allah said], "Then set out with My servants by night. Indeed, you are to be pursued. <> (Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)" = --Qur'an 44:23
    And leave the sea in stillness. Indeed, they are an army to be drowned." <> "Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa." = --Qur'an 44:24
    How much they left behind of gardens and springs <> Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari. = --Qur'an 44:25
    And crops and noble sites <> Da shuke-shuke da matsayi mai kyau. = --Qur'an 44:26
    And comfort wherein they were amused. <> Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu. = --Qur'an 44:27
    Thus. And We caused to inherit it another people. <> Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam. = --Qur'an 44:28
    And the heaven and earth wept not for them, nor were they reprieved. <> Sa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba. = --Qur'an 44:29
    And We certainly saved the Children of Israel from the humiliating torment - <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa. = --Qur'an 44:30
    From Pharaoh. Indeed, he was a haughty one among the transgressors. <> Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna. = --Qur'an 44:31
    And We certainly chose them by knowledge over [all] the worlds. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne. = --Qur'an 44:32
    And We gave them of signs that in which there was a clear trial. <> Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna = --Qur'an 44:33
    Indeed, these [disbelievers] are saying, <> Lalle waɗannan mutãne, haƙĩka, sunã cẽwa, = --Qur'an 44:34
    "There is not but our first death, and we will not be resurrected. <> "Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba." = --Qur'an 44:35
    Then bring [back] our forefathers, if you should be truthful." <> "Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya." = --Qur'an 44:36
    Are they better or the people of Tubba' and those before them? We destroyed them, [for] indeed, they were criminals. <> shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi. = --Qur'an 44:37
    And We did not create the heavens and earth and that between them in play. <> Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã. = --Qur'an 44:38
    We did not create them except in truth, but most of them do not know. <> Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba. = --Qur'an 44:39
    Indeed, the Day of Judgement is the appointed time for them all - <> Lalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya. = --Qur'an 44:40
    The Day when no relation will avail a relation at all, nor will they be helped - <> Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba. = --Qur'an 44:41
    Except those [believers] on whom Allah has mercy. Indeed, He is the Exalted in Might, the Merciful. <> fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. = --Qur'an 44:42
    Indeed, the tree of zaqqum <> Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã), = --Qur'an 44:43
    Is food for the sinful. <> Ita ce abincin mai laifi. = --Qur'an 44:44
    Like murky oil, it boils within bellies <> Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna. = --Qur'an 44:45
    Like the boiling of scalding water. <> Kamar tafasar ruwan zãfi. = --Qur'an 44:46
    [It will be commanded], "Seize him and drag him into the midst of the Hellfire, <> (A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm." = --Qur'an 44:47
    Then pour over his head from the torment of scalding water." <> "Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi." = --Qur'an 44:48
    [It will be said], "Taste! Indeed, you are the honored, the noble! <> (A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!" = --Qur'an 44:49
    Indeed, this is what you used to dispute." <> "Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi." = --Qur'an 44:50
    Indeed, the righteous will be in a secure place; <> Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce. = --Qur'an 44:51
    Within gardens and springs, <> A cikin gidãjen Aljanna da marẽmari. = --Qur'an 44:52
    Wearing [garments of] fine silk and brocade, facing each other. <> Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna. = --Qur'an 44:53
    Thus. And We will marry them to fair women with large, [beautiful] eyes. <> Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyaun idãnu, mãsu girmansu. = --Qur'an 44:54
    They will call therein for every [kind of] fruit - safe and secure. <> Sunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro). = --Qur'an 44:55
    They will not taste death therein except the first death, and He will have protected them from the punishment of Hellfire <> Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm. = --Qur'an 44:56
    As bounty from your Lord. That is what is the great attainment. <> Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma. = --Qur'an 44:57
    And indeed, We have eased the Qur'an in your tongue that they might be reminded. <> Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa. = --Qur'an 44:58
    So watch, [O Muhammad]; indeed, they are watching [for your end]. <> Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne. = --Qur'an 44:59
    Ha, Meem. <> Ḥ. M̃. = --Qur'an 45:1
    The revelation of the Book is from Allah, the Exalted in Might, the Wise. <> Saukar Littãfi daga Allah Mabuwãyi Mai hikima yake. = --Qur'an 45:2
    Indeed, within the heavens and earth are signs for the believers. <> Lalle ne a cikin sammai da ƙasa akwai ãyõyi ga mãsu ĩmãni. = --Qur'an 45:3
    And in the creation of yourselves and what He disperses of moving creatures are signs for people who are certain [in faith]. <> Kuma a cikin halittarku da abin da ke watsuwa na dabba akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yaƙĩni. = --Qur'an 45:4
    And [in] the alternation of night and day and [in] what Allah sends down from the sky of provision and gives life thereby to the earth after its lifelessness and [in His] directing of the winds are signs for a people who reason. <> Kuma da sãɓawar dare da yini da abin da Allah Ya saukar daga sama na arziki, sa'an nan Ya rãyar da ƙasa game da shi a bãyan mutuwarta, da jũyawar iskõki, akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin hankali. = --Qur'an 45:5
    These are the verses of Allah which We recite to you in truth. Then in what statement after Allah and His verses will they believe? <> Waɗancan ãyõyin Allah ne, Munã karanta su gare ka da gaskiya. To, da wane lãbãri bãyan Allah da ãyõyinSa suke yin ĩmãni? = --Qur'an 45:6
    Woe to every sinful liar <> Bone ya tabbata ga dukan mai yawan ƙiren ƙarya, mai laifi. = --Qur'an 45:7
    Who hears the verses of Allah recited to him, then persists arrogantly as if he had not heard them. So give him tidings of a painful punishment. <> Yanã jin ãyõyin Allah anã karanta su a kansa, sa'an nan ya dõge yanã makãngari, kamar bai jĩ su ba. To, ka yi masa bushara da azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 45:8
    And when he knows anything of Our verses, he takes them in ridicule. Those will have a humiliating punishment. <> Kuma har idan ya san wani abu daga ãyõyinMu, sai ya rika su da izgili. Waɗancan sunã da wata azãba mai wulãkantãwa (a dũniya). = --Qur'an 45:9
    Before them is Hell, and what they had earned will not avail them at all nor what they had taken besides Allah as allies. And they will have a great punishment. <> Gaba gare su (a Lãhira) akwai Jahannama, kuma abin da suka sanã'anta bã ya wadãtar da su daga kõme, kuma abũbuwan da suka riƙa majiɓinta, baicin Allah, bã su wãdatar da su daga kõme. Kuma sunã da wata azãba mai girma. = --Qur'an 45:10
    This [Qur'an] is guidance. And those who have disbelieved in the verses of their Lord will have a painful punishment of foul nature. <> Wannan (Alƙur'ãni) shi ne shiryuwa. Kuma waɗanda suka kãfirta game da ãyõyin Ubangijinsu, sunã da wata azãba ta wulãkanci mai raɗaɗi. = --Qur'an 45:11
    It is Allah who subjected to you the sea so that ships may sail upon it by His command and that you may seek of His bounty; and perhaps you will be grateful. <> Allah ne wanda Ya hõre muku tẽku dõmin jirgi ya gudãna a cikinta da umurninSa, kuma dõmin ku nẽma daga falalarSa, kuma tsammãninku zã ku gõde. = --Qur'an 45:12
    And He has subjected to you whatever is in the heavens and whatever is on the earth - all from Him. Indeed in that are signs for a people who give thought. <> Kuma Ya hõre muku abin da ke a cikin sammai da abin da ke a cikin ƙasa, gabã ɗaya daga gare Shi yake. Lalle ne, a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni. = --Qur'an 45:13
    Say, [O Muhammad], to those who have believed that they [should] forgive those who expect not the days of Allah so that He may recompense a people for what they used to earn. <> Ka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, su yi gãfara ga waɗanda bã su fãtan rahama ga kwãnukan Allah, dõmin (Allah) Ya sãka wa mutãne da abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 45:14
    Whoever does a good deed - it is for himself; and whoever does evil - it is against the self. Then to your Lord you will be returned. <> Wanda ya aikata aikin ƙwarai, to, dõmin kansã, kuma wanda ya mũnana aki, to, a kansa. Sa'an nan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku. = --Qur'an 45:15
    And We did certainly give the Children of Israel the Scripture and judgement and prophethood, and We provided them with good things and preferred them over the worlds. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai (wa Bãnĩ Isrã'ĩla Littãfi da hukunci da Annabci, Kuma Mun azurta su daga abũbuwa mãsudãɗi, Kuma Mun fĩfta su a kan mutãnen dũniya (a zãmaninsu). = --Qur'an 45:16
    And We gave them clear proofs of the matter [of religion]. And they did not differ except after knowledge had come to them - out of jealous animosity between themselves. Indeed, your Lord will judge between them on the Day of Resurrection concerning that over which they used to differ. <> Kuma Muka bã su hujjõji na umurni. Ba su sãɓa ba fãce bãyan ilmi ya jẽ musu, sabõda zãlunci a tsakãninsu. Lalle ne, Ubangijinka zai yi hukunci a tsakãninsu, a Rãnar ƙiyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa (jũna). = --Qur'an 45:17
    Then We put you, [O Muhammad], on an ordained way concerning the matter [of religion]; so follow it and do not follow the inclinations of those who do not know. <> Sa'an nan Muka sanya ka a kan wata sharĩ'a ta al'amarin. Sai ka bĩ ta, Kuma kada kã bi son zũciyõyin waɗannan daba su sani ba. = --Qur'an 45:18
    Indeed, they will never avail you against Allah at all. And indeed, the wrongdoers are allies of one another; but Allah is the protector of the righteous. <> Lalle ne sũ, bã zã su wadãtar da kai da kõme ba daga Allah. Kuma lalle ne azzãlumai sãshensu majiɓintan sãshe ne. Kuma Allah ne Majiɓincin mãsu taƙawa. = --Qur'an 45:19
    This [Qur'an] is enlightenment for mankind and guidance and mercy for a people who are certain [in faith]. <> wannan (Alkur'ãni) hukunce-hukuncen natsuwa ne ga mutãne, da shiryuwa, da rahama, ga mutãne waɗanda ke da yaƙĩni. = --Qur'an 45:20
    Or do those who commit evils think We will make them like those who have believed and done righteous deeds - [make them] equal in their life and their death? Evil is that which they judge. <> Kõ waɗanda suka yãgi miyãgun ayyuka sunã zaton Mu sanyã su kamar waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, su zama daidai ga rãyuwarsu da mutuwarsu? Abin da suke hukuntãwa yã mũnanã! = --Qur'an 45:21
    And Allah created the heavens and earth in truth and so that every soul may be recompensed for what it has earned, and they will not be wronged. <> Alhãli kuwa Allah ne Ya halitta sammai da ƙasã sabõda gaskiya, Kuma dõmin a sãka wa kõwane rai da abin da ya sanã'anta, kuma su, bã zã a zãlunce su ba. = --Qur'an 45:22
    Have you seen he who has taken as his god his [own] desire, and Allah has sent him astray due to knowledge and has set a seal upon his hearing and his heart and put over his vision a veil? So who will guide him after Allah? Then will you not be reminded? <> Shin, kã ga wanda ya riƙi son zũciyarsa sĩh ne abin bautawarsa, kuma Allah Ya ɓatar da shi a kan wani ilmi, Kuma Ya sa hatini a kan jinsa, da zũciyarsa, kuma Ya sa wata yãnã ã kan ganinsa? To, wãne ne zai shiryar da shi bãyan Allah? Shin to, bã zã ku yi tunãni ba? = --Qur'an 45:23
    And they say, "There is not but our worldly life; we die and live, and nothing destroys us except time." And they have of that no knowledge; they are only assuming. <> Kuma suka ce: "Bãbu kõme fãce rãyuwarmu ta dũniya; munã mutuwa kuma munã rãyuwa (da haihuwa) kuma bãbu abin da ke halaka mu sai zãmani." Alhãli kuwa (ko da suke faɗar maganar) bã su da wani ilmi game da wannan, bã su bin kõme face zato. = --Qur'an 45:24
    And when Our verses are recited to them as clear evidences, their argument is only that they say, "Bring [back] our forefathers, if you should be truthful." <> Kuma idan anã karanta ãyõyinMu bayyanannu a kansu, bãbu abin da ya kasance hujjarsu fãce suka ce: "Ku zo mana da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya." = --Qur'an 45:25
    Say, "Allah causes you to live, then causes you to die; then He will assemble you for the Day of Resurrection, about which there is no doubt, but most of the people do not know." <> Ka ce: "Allah ne ke rãyar da ku kuma Shĩ ne ke matarda ku, sa'an nan Ya tãra ku zuwa ga Rãnar ¡iyãma, bãbu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba." = --Qur'an 45:26
    And to Allah belongs the dominion of the heavens and the earth. And the Day the Hour appears - that Day the falsifiers will lose. <> "Kuma mulkin sammai da ƙasa na Allah ne, Shĩ kaɗai. Kuma rãnar da Sa'a ke tsayuwa, a rãnar nan mãsu ɓãtãwã (ga hujjõjin Allah dõmin su ki bin sharĩ'arSa) zã su yi hasãra." = --Qur'an 45:27
    And you will see every nation kneeling [from fear]. Every nation will be called to its record [and told], "Today you will be recompensed for what you used to do. <> Kuma zã ka ga kõwace al'umma tanã gurfãne, kõwace al'umma anã kiran ta zuwa ga littãfinta. (A ce musu) "A yau anã sãka muku da abin da kuka kasance kunã aikatãwa." = --Qur'an 45:28
    This, Our record, speaks about you in truth. Indeed, We were having transcribed whatever you used to do." <> "Wannan littãfinMu ne yanã yin magana a kanku da gas, kiya. Lalle Mũ, Mun kasanceMuna sauya rubũtun tamkar abin dakuka kasance kunã aikãtãwa." = --Qur'an 45:29
    So as for those who believed and did righteous deeds, their Lord will admit them into His mercy. That is what is the clear attainment. <> To, amma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, to, Ubangijinsu zai sanya su a cikin rahamarsa. Wannan shĩ ne babban rabo bayyananne. = --Qur'an 45:30
    But as for those who disbelieved, [it will be said], "Were not Our verses recited to you, but you were arrogant and became a people of criminals? <> Kuma amma waɗanda suka kãfirtã (Allah zai ce musu): "Shin, ãyõyĩNã ba su kasance anã karãnta su ã kanku ba sai kuka kangare, Kuma kuka kasance mutãne mãsu laifi?" = --Qur'an 45:31
    And when it was said, 'Indeed, the promise of Allah is truth and the Hour [is coming] - no doubt about it,' you said, 'We know not what is the Hour. We assume only assumption, and we are not convinced.' " <> "Kuma idan aka ce, lalle wa'ãdin Allah gaskiya ne, kuma Sa'a, bãbu shakka a cikinta sai kuka ce, 'Ba mu san abin da ake cẽwa Sa'a ba, bã mu zãto (game da ita) fãce zato mai rauni, Kuma ba mu zama mãsu yaƙni ba."' = --Qur'an 45:32
    And the evil consequences of what they did will appear to them, and they will be enveloped by what they used to ridicule. <> Kuma mũnanan abin da suka aikata ya bayyana a gare su, kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili ya wajaba a kansu. = --Qur'an 45:33
    And it will be said, "Today We will forget you as you forgot the meeting of this Day of yours, and your refuge is the Fire, and for you there are no helpers. <> Kuma aka ce: "A yau zã Mu manta da ku, kamar yadda kuka manta da gamuwa da yininku wannan. Kuma mãkõmarku wutã ce, Kuma bã ku da waɗansu mãsu taimako. = --Qur'an 45:34
    That is because you took the verses of Allah in ridicule, and worldly life deluded you." So that Day they will not be removed from it, nor will they be asked to appease [Allah]. <> "Wancan dõmin lalle kũ, kun riƙi ãyõyin Allah da izgili, Kuma rãyuwar dũniya ta rũɗe ku. To, a yau bã zã su fita daga gare ta ba, Kuma bã zã su zama waɗanda ake nẽman yardarsu ba." = --Qur'an 45:35
    Then, to Allah belongs [all] praise - Lord of the heavens and Lord of the earth, Lord of the worlds. <> Sabõda haka, gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin sammai, kuma Ubangijin ƙasã, Ubangijin halittu. = --Qur'an 45:36
    And to Him belongs [all] grandeur within the heavens and the earth, and He is the Exalted in Might, the Wise. <> Kuma gare Shi girma yake, a cikin sammai da ƙasã, kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Hikima. = --Qur'an 45:37
    Ha, Meem. <> Ḥ. M̃. = --Qur'an 46:1
    The revelation of the Book is from Allah, the Exalted in Might, the Wise. <> Saukar da littafi daga Allah, Mabuwãyi, Mai hikima yake. = --Qur'an 46:2
    We did not create the heavens and earth and what is between them except in truth and [for] a specified term. But those who disbelieve, from that of which they are warned, are turning away. <> Ba Mu halitta sammai da ƙasa ba, da abin da ke tsakãninsu, fãce da gaskiya da wani ajali ambatacce, kuma waɗanda suka kãfirta, mãsu bijirẽwa ne daga abin da aka yi musu gargaɗi (da shi). = --Qur'an 46:3
    Say, [O Muhammad], "Have you considered that which you invoke besides Allah? Show me what they have created of the earth; or did they have partnership in [creation of] the heavens? Bring me a scripture [revealed] before this or a [remaining] trace of knowledge, if you should be truthful." <> Ka ce: "Shin, kun gani, abin da kuke kira, wanda yake baicin Allah? Ku nũna mini, menene suka halitta daga ƙasa? Kõ kuwa sunã da tãrayya a cikin sammai? Ku zo mini da wani littãfi na gabãnin wannan (Alƙur'ãni) kõ wata alãma daga wani ilmi, idan kun kasance mãsu gaskiya." = --Qur'an 46:4
    And who is more astray than he who invokes besides Allah those who will not respond to him until the Day of Resurrection, and they, of their invocation, are unaware. <> Kuma wãne ne mafi ɓata daga wanda ke kiran wanin Allah wanda da bã zai karɓa masa ba, bar Rãnar Kyama, alhãli sũ (waɗanda ake kiran) shagaltattu ne daga kiransu? = --Qur'an 46:5
    And when the people are gathered [that Day], they [who were invoked] will be enemies to them, and they will be deniers of their worship. <> Kuma idan aka tãra mutãne sai su kasance maƙiya a gare su, alhãli sun kasance mãsu ƙi ga ibãdarsu. = --Qur'an 46:6
    And when Our verses are recited to them as clear evidences, those who disbelieve say of the truth when it has come to them, "This is obvious magic." <> Kuma idan anã karãtun ãyõòyinMu bayyanannu a kansu, sai waɗanda suka kãfirta ga gaskiya a lõkacin da ta jẽ musu, su ce, "Wannan sihiri ne bayyananne." = --Qur'an 46:7
    Or do they say, "He has invented it?" Say, "If I have invented it, you will not possess for me [the power of protection] from Allah at all. He is most knowing of that in which you are involved. Sufficient is He as Witness between me and you, and He is the Forgiving the Merciful." <> Kõkuwã sunã cẽwa: "Yã ƙirƙira shi (Alƙur'ãni) ne?" Ka ce: "Idan na ƙirƙira shi ne, to bã ku mallaka mini kõme daga Allah. Shĩ ne Mafi sani ga abin da kuke kũtsãwa a cikinsa na magana. (Allah) Yã isa Ya zama shaida a tsakãnĩnada tsakãninku. Kuma shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai." = --Qur'an 46:8
    Say, "I am not something original among the messengers, nor do I know what will be done with me or with you. I only follow that which is revealed to me, and I am not but a clear warner." <> Ka ce: "Ban kasance fãrau ba daga Manzanni, kuma ban san abin da zã a yi game da ni kõ game da ku (na gaibi) ba, bã ni bin kõme fãce abin da ake yin wahayi zuwa gare ni, kuma ban zama ba, fãce mai gargaɗi mai bayyanãwa." = --Qur'an 46:9
    Say, "Have you considered: if the Qur'an was from Allah, and you disbelieved in it while a witness from the Children of Israel has testified to something similar and believed while you were arrogant...?" Indeed, Allah does not guide the wrongdoing people. <> Ka ce: "Shin, kun gani, idan (Alƙur'ãni) ya kasance daga wurin Allah yake, kuma kuka kãfirta da shi, kuma wani mai shaida daga Banĩ Isrã'ĩla ya bãyar da shaida a kan kwatankwacinsa, sa'an nan ya yi ĩmãni, kuma kuka kangare? Lalle Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai." = --Qur'an 46:10
    And those who disbelieve say of those who believe, "If it had [truly] been good, they would not have preceded us to it." And when they are not guided by it, they will say, "This is an ancient falsehood." <> Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni: "Da (Alƙur'ãni) ya kasance, wani alhẽri ne," dã ba su riga muzuwa gare shi ba. Kuma tun da ba su shiryu game da shĩ ba, to, zã su ce, "Wannan ƙiren ƙarya ne daɗaɗɗe." = --Qur'an 46:11
    And before it was the scripture of Moses to lead and as a mercy. And this is a confirming Book in an Arabic tongue to warn those who have wronged and as good tidings to the doers of good. <> Alhãli kuwa a gabãninsa akwai littãfin Mũsã, wanda ya kasance abin kõyi, kuma rahama. Kuma wannan (Alƙur'ãni) littafi ne mai gaskatãwa (ga littafin Mũsã), a harshe na Larabci dõmin ya gargaɗi waɗanda suka yi zãlunci, kuma ya zama bushãra ga mãsu kyautatãwa. = --Qur'an 46:12
    Indeed, those who have said, "Our Lord is Allah," and then remained on a right course - there will be no fear concerning them, nor will they grieve. <> Lalle ne waɗanda suka ce: "Ubangijinmu Allah ne," sa'an nan suka daidaitu, to, bãbu wani tsõro a kansu, kuma bã zã su yi baƙin ciki ba. = --Qur'an 46:13
    Those are the companions of Paradise, abiding eternally therein as reward for what they used to do. <> Waɗannan 'yan Aljanna ne, sunã madawwama a cikinta, a kan sakamako ga abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 46:14
    And We have enjoined upon man, to his parents, good treatment. His mother carried him with hardship and gave birth to him with hardship, and his gestation and weaning [period] is thirty months. [He grows] until, when he reaches maturity and reaches [the age of] forty years, he says, "My Lord, enable me to be grateful for Your favor which You have bestowed upon me and upon my parents and to work righteousness of which You will approve and make righteous for me my offspring. Indeed, I have repented to You, and indeed, I am of the Muslims." <> Kuma Mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu da kyautatãwa, uwarsa tã yi cikinsa wahala, kuma ta haife shi wahala. cikinsa da yãyensa watã talãtin. Har a lõkacin da ya kai ga mafi ƙarfinsa, kuma ya kai shẽkara arba'in, ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka kange nidõmin in gõde wa ni'imarKa, wadda Ka ni'imta a kaina da kuma a kan mahaifãna biyu, kuma dõmin in aikata aikin ƙwarai wanda Kake yarda da shi, kuma Ka kyautata mini a cikin zuriyata. Lalle nĩ, nã tũba zuwa gare Ka, kuma lalle ni, inã daga mãsu sallamãwa (ga umurninKa)." = --Qur'an 46:15
    Those are the ones from whom We will accept the best of what they did and overlook their misdeeds, [their being] among the companions of Paradise. [That is] the promise of truth which they had been promised. <> Waɗancan ne waɗanda Muke karɓa, daga gare su, mafi kyaun abin da suka aikata, kuma Muke gãfarta mafi mũnanan ayyukansum (sunã) a cikin 'yan Aljanna, a kan wa'adin gaskiya wanda suka kasance anã yi musu alkawari (da shi). = --Qur'an 46:16
    But one who says to his parents, "Uff to you; do you promise me that I will be brought forth [from the earth] when generations before me have already passed on [into oblivion]?" while they call to Allah for help [and to their son], "Woe to you! Believe! Indeed, the promise of Allah is truth." But he says, "This is not but legends of the former people" - <> Kuma wanda ya ce wa mahaifansa biyu: "Tir gare ku! shin, kunã tsõratar da ni cẽwa zã a fitar da ni daga (kabari) ne, alhãli kuwa ƙarnõni na mutãne da yawa sun shũɗe a gabãnĩna (ba su kõmo ba)?" Kuma sũ (mahaifan) sunã nẽman Allah taimako (sunãce masa) "Kaitonka! Ka yi ĩmãni, lalle wa'adin Allah gaskiya ne." Sai shi kuma ya ce. "Wannan bã kõme ba ne fãce tãtsũniyõyin mutãnen farko." = --Qur'an 46:17
    Those are the ones upon whom the word has come into effect, [who will be] among nations which had passed on before them of jinn and men. Indeed, they [all] were losers. <> Waɗancan ne waɗanda kalmar azãba ta wajaba a kansu, a cikin al'ummõmi waɗanda suka shũɗe, (bã da daɗẽwa ba), a gabãninsu, daga aljannu da mutãne. Lalle sũ, sun kasance mãsu hasãra. = --Qur'an 46:18
    And for all there are degrees [of reward and punishment] for what they have done, and [it is] so that He may fully compensate them for their deeds, and they will not be wronged. <> Kuma ga kõwane nau'i, yanã da darajõji daga abinda suka aikata. Kuma dõmin (Allah) Ya cika musu (sakamakon) ayyukansu, alhãli kuwa sũ, bã zã a zãlunce su ba. = --Qur'an 46:19
    And the Day those who disbelieved are exposed to the Fire [it will be said], "You exhausted your pleasures during your worldly life and enjoyed them, so this Day you will be awarded the punishment of [extreme] humiliation because you were arrogant upon the earth without right and because you were defiantly disobedient." <> Kuma rãnar da ake gitta waɗanda suka kãflrta a kan wutã (a ce musu): "Kun tafiyar da abũbuwanku na jin dãɗi a cikin rayuwarku ta dũniya, kuma kun nẽmi jin dãdi da su, to, ayau anã sãka muka da azãbar wulãkanci, dõmin abin da kuka kasance kanã yi na gmian kai a cikin ƙasa, bã da wani hakki ba, kuma dõmin abin da kuka kasance kuna yi na fãsiƙansi." = --Qur'an 46:20
    And mention, [O Muhammad], the brother of 'Aad, when he warned his people in the [region of] al-Ahqaf - and warners had already passed on before him and after him - [saying], "Do not worship except Allah. Indeed, I fear for you the punishment of a terrible day." <> Kuma ka ambaci ɗan'uwan Ãdãwa a lõkacin da ya yi gargaɗi ga mutãnensa, a Tuddan Rairayi, alhãli kuwa waɗansu mãsu gargaɗi sun shũɗe agaba gare shi da bãya gare shi (da cẽwa) "Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah. Lalle nĩ inã tsõrata muku azãbar yini mai girma." = --Qur'an 46:21
    They said, "Have you come to delude us away from our gods? Then bring us what you promise us, if you should be of the truthful." <> Suka ce: "Shin, kã zo mana ne dõmin ka karkatar da mu daga gumãkaumu? To, ka zo mana da abin da kake yi mana wa'adin, idan kã kasance daga mãsu gaskiya." = --Qur'an 46:22
    He said, "Knowledge [of its time] is only with Allah, and I convey to you that with which I was sent; but I see you [to be] a people behaving ignorantly." <> Ya ce: "Ilimi a wurin Allah kawai yake, kuma inã iyar maku abin da aka aiko ni da shi, kuma amma inã ganin, kũ, wasu mutãne ne, kunã jãhiltar gaskiya." = --Qur'an 46:23
    And when they saw it as a cloud approaching their valleys, they said, "This is a cloud bringing us rain!" Rather, it is that for which you were impatient: a wind, within it a painful punishment, <> To, a lõkacin da suka ga azãbar, kumar hadari mai fuskantar rãfukansu, suka ce: "Wannan hadari ne mai yi mana ruwa. Ã'a, shĩ na abin da kuke nẽman gaggawar saukarsa; Iska ce, a cikinta akwai wata azaba mai raɗaɗi. = --Qur'an 46:24
    Destroying everything by command of its Lord. And they became so that nothing was seen [of them] except their dwellings. Thus do We recompense the criminal people. <> Tanã darkake kõwane abu da umurnin Ubangijinta. Sai suka wãyi gari, bã a ganin kõme fãce gidãjensu. Kamar wannan ne Muke sãka wa mutãne mãsu laifi. = --Qur'an 46:25
    And We had certainly established them in such as We have not established you, and We made for them hearing and vision and hearts. But their hearing and vision and hearts availed them not from anything [of the punishment] when they were [continually] rejecting the signs of Allah; and they were enveloped by what they used to ridicule. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun ba su ĩko ga abin da ba Mubã ku ĩko gare shi ba, kuma Muka sanya musu wani irin jĩ da gani dazukãta. Sai dai jnsu bai amfãne su ba, kuma zukãtansu ba su amfãne su ba ga kõme, dõmin sun kasance sunã musu game da ãyõyin Allah, kuma abin da suka kasance sunã aikatãwa na izgili game da shi ya wajaba a gare su. = --Qur'an 46:26
    And We have already destroyed what surrounds you of [those] cities, and We have diversified the signs [or verses] that perhaps they might return [from disbelief]. <> Kuma ne, lalle haƙĩƙa, Mun halakar da abin da yake kẽwayenku na alƙaryu kuma Muka jujjũya ãyõyi, tsammãninsu zã su kõmo. = --Qur'an 46:27
    Then why did those they took besides Allah as deities by which to approach [Him] not aid them? But they had strayed from them. And that was their falsehood and what they were inventing. <> To, don mẽne ne waɗanda suka riƙa, baicin Allah, abũbuwan yi. wa baiko, gumaka, ba su taimake su ba? Ã'a, sun ɓace musu Kuma wannan shi ne ƙiren ƙaryarsu da abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa. = --Qur'an 46:28
    And [mention, O Muhammad], when We directed to you a few of the jinn, listening to the Qur'an. And when they attended it, they said, "Listen quietly." And when it was concluded, they went back to their people as warners. <> Kuma a lõkcin da Muka jũya waɗansu jama'a na aljamiu zuwa gare ka sunã saurãren Alƙur'ãni. To, alõkacin da suka halarce shi suka ce: "Ku yi shiru." Sa'an nan da aka ƙãre, suka jũya zuwa ga jama'arsu sunã mãsu gargaɗi. = --Qur'an 46:29
    They said, "O our people, indeed we have heard a [recited] Book revealed after Moses confirming what was before it which guides to the truth and to a straight path. <> Suka ce: "Ya mutãnenmu! Lalle mũ, mun ji wani littãfi an saukar da shi a bãyãn Mũsã, mai gaskatãwa ga abin da ke a gaba da shi, yanã shiryarwa ga gaskiya da kuma zuwa ga hanya madaidaiciya. = --Qur'an 46:30
    O our people, respond to the Messenger of Allah and believe in him; Allah will forgive for you your sins and protect you from a painful punishment. <> "Yã mutãnenmu! Ku karɓa wa mai kiran Allah, kuma ku yi ĩmãni da Shi, Ya gãfarta muku daga zunubanku, kuma ya tserar da ku daga azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 46:31
    But he who does not respond to the Caller of Allah will not cause failure [to Him] upon earth, and he will not have besides Him any protectors. Those are in manifest error." <> "Kuma wanda bai karɓa wa mai kiran Allah ba to bai zama mai buwãya a cikin ƙasa ba, kuma ba ya da waɗansu majiɓinta, baicin Shi. Waɗannnan sunã a cikin ɓata bayyananna." = --Qur'an 46:32
    Do they not see that Allah, who created the heavens and earth and did not fail in their creation, is able to give life to the dead? Yes. Indeed, He is over all things competent. <> Shin, kuma ba su gani ba cẽwa: "Lalle Allah, Wanda Yã halitta sammai da ƙasa kuma bai kãsa ga halittarsu ba, Mai ĩkon yi ne a kan rãyar da matattu?" Na'am, lalle Shi, Mai ĩkon yi ne a kan kõme. = --Qur'an 46:33
    And the Day those who disbelieved are exposed to the Fire [it will be said], "Is this not the truth?" They will say, "Yes, by our Lord." He will say, "Then taste the punishment because you used to disbelieve." <> Kuma rãnar da ake gittar da waɗanda suka kãfirta a kan wutã, (a ce musu) "Ashe, wannan bã gaskiya ba ne?" Su ce: "Na'am, gaskiya ne, mun rantse da Ubangijinmu!" Sai Ya ce, "To, ku ɗanɗani azãbar sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci." = --Qur'an 46:34
    So be patient, [O Muhammad], as were those of determination among the messengers and do not be impatient for them. It will be - on the Day they see that which they are promised - as though they had not remained [in the world] except an hour of a day. [This is] notification. And will [any] be destroyed except the defiantly disobedient people? <> Sabõda haka, ka yi haƙuri kamar yadda mãsu ƙarfin niyya daga Manzanni suka yi haƙuri. Kuma kada ka yi musu gaggãwa. Kamar dai sũ, a rãnar da suke ganin (sakamako) abin da ake yi musu wa'adi ba su zauna ba, fãce sa'a guda daga yini. Iyarwa dai da Manzanci). Shin, akwai wanda za a halakar? (Bãbu), fãce mutãne fasiƙai. = --Qur'an 46:35
    Those who disbelieve and avert [people] from the way of Allah - He will waste their deeds. <> Waɗanda suka kãfirta kuma suka kange mutãne daga tafarkin Allah, (Allah) Ya ɓatar da ayyukansu. = --Qur'an 47:1
    And those who believe and do righteous deeds and believe in what has been sent down upon Muhammad - and it is the truth from their Lord - He will remove from them their misdeeds and amend their condition. <> Kuma waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi ĩmani da abinda aka sassaukar ga Muhammadu, alhãli kuwa shĩ ne gaskiya daga Ubangijinsu, (Allah) Yã karkare musu miyãgun ayyukansu, kuma Yã kyautata hãlãyensu. = --Qur'an 47:2
    That is because those who disbelieve follow falsehood, and those who believe follow the truth from their Lord. Thus does Allah present to the people their comparisons. <> Wannan kuwa sabõda lalle, waɗanda suka kãfirta sun bi ƙarya, kumar lalle waɗanda suka yi ĩmãni, sun bi gaskiya daga Ubangijinsu. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana wa mutãne misãlansu. = --Qur'an 47:3
    So when you meet those who disbelieve [in battle], strike [their] necks until, when you have inflicted slaughter upon them, then secure their bonds, and either [confer] favor afterwards or ransom [them] until the war lays down its burdens. That [is the command]. And if Allah had willed, He could have taken vengeance upon them [Himself], but [He ordered armed struggle] to test some of you by means of others. And those who are killed in the cause of Allah - never will He waste their deeds. <> Sabõda haka idan kun haɗu da waɗanda suka kãfirta, sai ku yi ta dũkan wuyõyinsu har a lõkacin da suka yawaita musu kisa, to, ku tsananta ɗaurinsu sa'an nan imma karimci a bãyan' haka kõ biyan fansa, har yãƙi ya saukar da kayansa mãsu nauyi. Wancan, dã Allah nã so da Ya ci nasara a kansu (ba tare da yaƙin ba) kuma amma (ya wajabta jihadi) dõmin Ya jarraba sãshenku da sãshe. Kuma waɗanda zaka kashe a cikin tafarkin Allah, to, bã ai ɓatar da ayyukansu ba. = --Qur'an 47:4
    He will guide them and amend their condition <> Zai shiryar da su, kuma Ya kyautata hãlãyensu. = --Qur'an 47:5
    And admit them to Paradise, which He has made known to them. <> Kuma Ya shigarda su Aljanna (wadda) Ya siffanta ta a gare su. = --Qur'an 47:6
    O you who have believed, if you support Allah, He will support you and plant firmly your feet. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Idan kun taimaki Allah, zai taimake ku, kuma Ya tabbatar da dugãduganku.. = --Qur'an 47:7
    But those who disbelieve - for them is misery, and He will waste their deeds. <> Kuma waɗanda suka kãfirta, to, ruɓushi ya tabbata a gare su, kuma (Allah) Ya ɓatar da ayyukansu. = --Qur'an 47:8
    That is because they disliked what Allah revealed, so He rendered worthless their deeds. <> Wannan, sabõda lalle sũ, sun ƙi abin da Allah Ya saukar dõmin haka Ya ɓata ayyukansu. = --Qur'an 47:9
    Have they not traveled through the land and seen how was the end of those before them? Allah destroyed [everything] over them, and for the disbelievers is something comparable. <> Shin, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasa, dõmin su gani yadda ãƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Allah Ya darkãke a kansu. Kuma akwai misãlan wannan ãƙibar ga kãfirai (na kõwane zãmani). = --Qur'an 47:10
    That is because Allah is the protector of those who have believed and because the disbelievers have no protector. <> Wancan! Sabõda lalle Allah ne Majiɓincin waɗanda suka yi ĩmãni, kuma lalle, kafirai bãbu wani majiɓinci a gare su. = --Qur'an 47:11
    Indeed, Allah will admit those who have believed and done righteous deeds to gardens beneath which rivers flow, but those who disbelieve enjoy themselves and eat as grazing livestock eat, and the Fire will be a residence for them. <> Lalle ne, Allah nã shigar da waɗanda suka yi ĩmani kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a gidãjen Aljanna, kõgunan ruwa na gudana daga ƙarƙashinsu, kuma waɗanda suka kãfirta sunã jin ɗan daɗi (adũniya) kuma sunã ci, kamar yadda dabbõbi ke ci, kuma wutã ita ce mazauni a gare su. = --Qur'an 47:12
    And how many a city was stronger than your city [Makkah] which drove you out? We destroyed them; and there was no helper for them. <> Kuma da yawa akwai alƙarya, ita ce mafi tsanani ga ƙarfi daga alƙaryarka wadda ta fitar da kai, Mun halaka ta, sa'an nan kuwa bãbu wani mai taimako a gare su. = --Qur'an 47:13
    So is he who is on clear evidence from his Lord like him to whom the evil of his work has been made attractive and they follow their [own] desires? <> Shin, wanda ya kasance a kan wata hujja daga Ubangijinsa, zai zama kamar wanda aka ƙawãce masa mugun aikinsa, kuma suka bibbiyi son zũciyõyinsu? = --Qur'an 47:14
    Is the description of Paradise, which the righteous are promised, wherein are rivers of water unaltered, rivers of milk the taste of which never changes, rivers of wine delicious to those who drink, and rivers of purified honey, in which they will have from all [kinds of] fruits and forgiveness from their Lord, like [that of] those who abide eternally in the Fire and are given to drink scalding water that will sever their intestines? <> Misãlin Aljanna, wadda aka yi wa'adinta ga mãsu taƙawa, a cikinta akwai waɗansu kõguna na ruwa ba mai sãkẽwa ba da waɗansu kõguna na madara wadda ɗanɗanonta bã ya canjãwa, da waɗansu kõguna na giya mai dãɗi ga mashãya, da waɗansu kõguna na zuma tãtacce kuma suna sãmu, a cikinta, daga kõwane irin 'ya'yan itãce, da wata gãfara daga Ubangijinsu. (Shin, mãsu wannan ni'ima nã daidaita) kamar wanda yake madawwami ne a cikin wutã kuma an shãyar da su wani ruwa mai zãfi har ya kakkãtse hanjinsu? = --Qur'an 47:15
    And among them, [O Muhammad], are those who listen to you, until when they depart from you, they say to those who were given knowledge, "What has he said just now?" Those are the ones of whom Allah has sealed over their hearts and who have followed their [own] desires. <> Kuma daga cikinsu akwai wanda ke saurare zuwa gare ka, har idan sun fita daga wurinka, su ce wa waɗanda aka bai wa ilmi "Mẽne ne (Muhammadu) ya fãɗa ɗazu?" Waɗannan ne waɗanda Allah Ya shãfe haske daga zukãtansu, kuma suka bi son zũciyõyinsu. = --Qur'an 47:16
    And those who are guided - He increases them in guidance and gives them their righteousness. <> Kuma waɗannan da suka nẽmi shiryuwa (Allah) Ya ƙara musu shiryuwarsu, kuma Yã bã su (sakamakon) taƙawarsu. = --Qur'an 47:17
    Then do they await except that the Hour should come upon them unexpectedly? But already there have come [some of] its indications. Then what good to them, when it has come, will be their remembrance? <> To shin sunã jiran (wani abu)? Fãce S'a ta jẽ musu bisa abke, dõmin lalle sharuɗɗanta sun zo. To, yãya tunãwarsu take, idan har ta jẽ musu? = --Qur'an 47:18
    So know, [O Muhammad], that there is no deity except Allah and ask forgiveness for your sin and for the believing men and believing women. And Allah knows of your movement and your resting place. <> Sabõda hakaa ka sani, cẽwa bãbu abin bautãwa fãce Allah, kuma ka nẽmi gãfara ga zunubin, ka, (kuma sabõda mũminai maza da mũminai mãtã kuma Allah Ya san majũyaiku da mazauninku. = --Qur'an 47:19
    Those who believe say, "Why has a surah not been sent down? But when a precise surah is revealed and fighting is mentioned therein, you see those in whose hearts is hypocrisy looking at you with a look of one overcome by death. And more appropriate for them [would have been] <> Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sunã cẽwa: "Don mẽne ne ba a saukar da wata sũra ba? "To idan aka saukar da wata sũra, bayyananna, kuma aka ambaci yãƙi a cikinta, zã ka ga waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukatansu sunã kallo zuwa gare ka, irin kallon wanda aka rufe da mãgãgi sabõda mutuwa. To, abin da yake mafĩfĩci a gare su: = --Qur'an 47:20
    Obedience and good words. And when the matter [of fighting] was determined, if they had been true to Allah, it would have been better for them. <> Yin ɗã'a da magana mai kyau. Sa'an nan idan al'marin ya ƙullu, to, dã sun yi wa Allah gaskiya, lalle dã ya kasance mafifi ci a gare su. = --Qur'an 47:21
    So would you perhaps, if you turned away, cause corruption on earth and sever your [ties of] relationship? <> To, shin, kunã fãtan idan kun jũya (daga umurnin) zã ku yi ɓarna a cikin ƙasã, kuma ku yan yanke zumuntarku? = --Qur'an 47:22
    Those [who do so] are the ones that Allah has cursed, so He deafened them and blinded their vision. <> Waɗannan sũ ne waɗanda Allah Ya la'anẽ su, sa'an nan Ya kurumtar da su, kuma Ya makantar da ganinsu. = --Qur'an 47:23
    Then do they not reflect upon the Qur'an, or are there locks upon [their] hearts? <> Shin to, bã zã su, kula da Alƙur'ãni ba, kõ kuwa a bin zukã tansu akwai makullansu? = --Qur'an 47:24
    Indeed, those who reverted back [to disbelief] after guidance had become clear to them - Satan enticed them and prolonged hope for them. <> lalle ne, waɗanda suka kõma bãya a kan dugãdugansu a bãyan shiryuwa tã bayyana a gare su, Shaiɗan ne ya ƙawãta musu (haka), kuma ya yi musu shibta. = --Qur'an 47:25
    That is because they said to those who disliked what Allah sent down, "We will obey you in part of the matter." And Allah knows what they conceal. <> Wancan, dõmin lalle sũ sun ce wa waɗanda suka ƙi abin da Allah Ya saukar: "Za mu yi muku ɗã'ã ga sãshen al'amarin," alhãli kuwa Allah Yanã sane da gãnawarsu ta asĩri. = --Qur'an 47:26
    Then how [will it be] when the angels take them in death, striking their faces and their backs? <> To, yãya hãlinsu yake a lõkacin da malã'iku ke karɓar rãyukansu, sunã dũkan fuskõkinsu da ɗuwaiwansu? = --Qur'an 47:27
    That is because they followed what angered Allah and disliked [what earns] His pleasure, so He rendered worthless their deeds. <> Wannan, dõmin lalle sũ sun bi abin da ya, fusãtar da Allah kuma sun ƙi yardarSa, sabõda haka Ya ɓãta ayyukansu. = --Qur'an 47:28
    Or do those in whose hearts is disease think that Allah would never expose their [feelings of] hatred? <> Ko kuwa waɗanda ke da wata cũta a cikin zukatansu suna zaton cẽwa Allah ba zai fitar da mugun ƙulle-ƙullen su (ga Musulunci) ba? = --Qur'an 47:29
    And if We willed, We could show them to you, and you would know them by their mark; but you will surely know them by the tone of [their] speech. And Allah knows your deeds. <> Kuma dã Munã so, dã lalle Mun nũna maka su. To, lalle kanã sanin su game da alãmarsu. Kuma lalle kanã sanin su ga shaguɓen magana, alhali kuwa Allah Yanã sanin ayyukanku. = --Qur'an 47:30
    And We will surely test you until We make evident those who strive among you [for the cause of Allah] and the patient, and We will test your affairs. <> Kuma lalle ne, Munã jarraba ku, har Mu san mãsu jihãdi daga cikinku da mãsu haƙuri kuma Muna jbrraba lãbãran ku. = --Qur'an 47:31
    Indeed, those who disbelieved and averted [people] from the path of Allah and opposed the Messenger after guidance had become clear to them - never will they harm Allah at all, and He will render worthless their deeds. <> Lalle ne, waɗanda suka kãfirta, kuma suka kange daga tafarkin Allah, kuma suka saɓa wa Manzon sa a bãyan shiriyar ta bayyana a gare su, bã za su cũci Allah da kõme ba, kuma zã Ya ɓãta ayyukansu. = --Qur'an 47:32
    O you who have believed, obey Allah and obey the Messenger and do not invalidate your deeds. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗa'a ga ManzonSa, kuma kada ku ɓãta ayyukanku. = --Qur'an 47:33
    Indeed, those who disbelieved and averted [people] from the path of Allah and then died while they were disbelievers - never will Allah forgive them. <> Lalle ne waɗanda suka kãfirta sa'an nan kuma suka kange (mutãne) daga tafarkin Allah, sa'an nan suka mutu, alhãli kuwa sunã kãfirai, to, Allah bã zai yi gãfara ba a gare su. = --Qur'an 47:34
    So do not weaken and call for peace while you are superior; and Allah is with you and will never deprive you of [the reward of] your deeds. <> Sabõda haka kada ku yi rauni, kuma (kada) ku yi kira zũwaga sulhi alhãli kuwa kũ ne mafiɗaukaka kuma Allah na tãre da ku, kuma bã, zai naƙasa muku ayyukanku ba. = --Qur'an 47:35
    [This] worldly life is only amusement and diversion. And if you believe and fear Allah, He will give you your rewards and not ask you for your properties. <> Rãyuwar dũniya, wãsã da abin shagala kawai ce, kuma idan kun yi ĩmãni, kuma kun yi taƙawa, Allah zai kãwo muku ijarõrinku, kuma bã zai tambaye ku dũkiyarku ba. = --Qur'an 47:36
    If He should ask you for them and press you, you would withhold, and He would expose your unwillingness. <> Dã Allah zai tambaye ku su (dũkiyõyin) har Ya wajabta muku bãyarwa, zã ku yi rõwa kuma Ya fitar da miyãgun ƙulle-ƙullenku. = --Qur'an 47:37
    Here you are - those invited to spend in the cause of Allah - but among you are those who withhold [out of greed]. And whoever withholds only withholds [benefit] from himself; and Allah is the Free of need, while you are the needy. And if you turn away, He will replace you with another people; then they will not be the likes of you. <> Ga ku, ya ku waɗannan! Anã kiran ku dõmin ku ciyar ga tafarkin Allah, sa'an nan daga cikinku akwai mai yin rõwa. Kuma wanda ke yin rõwa, to, yanã yin rõwar ne ga kansa. Kuma Allah ne wadãtacce alhãli kuwa kũ fãƙĩrai ne. Kuma idan kuka jũya (daga yi Masa ɗã'a), zai musanya waɗansu mutãne waɗansunku sa'an nan bã zã su kasance kwatankwacinku ba. = --Qur'an 47:38
    Indeed, We have given you, [O Muhammad], a clear conquest <> Lalle Mũ, Mun yi maka rinjãye (a kan maƙiyanka), rinjaye bayyananne. = --Qur'an 48:1
    That Allah may forgive for you what preceded of your sin and what will follow and complete His favor upon you and guide you to a straight path <> Dõmin Allah Ya shãfe abin da ya gabãta na laifinka da abin da ya jinkirta, kuma Ya cika ni'imarSa a kanka, kuma Ya shiryar da kai ga hanya madaidaiciya. = --Qur'an 48:2
    And [that] Allah may aid you with a mighty victory. <> Kuma Allah Ya taimake ka, taimako mabuwãyi. = --Qur'an 48:3
    It is He who sent down tranquillity into the hearts of the believers that they would increase in faith along with their [present] faith. And to Allah belong the soldiers of the heavens and the earth, and ever is Allah Knowing and Wise. <> Shĩ ne wanda Ya saukar da natsuwa a cikin zukãtan mũminai dõmin su ƙãra wani ĩmãni tãre da imãninsu, alhãli kuwa rundunõnin sammai da ƙasa, na Allah kawai ne, kuma Allah Ya kasance Masani, Mai hikima. = --Qur'an 48:4
    [And] that He may admit the believing men and the believing women to gardens beneath which rivers flow to abide therein eternally and remove from them their misdeeds - and ever is that, in the sight of Allah, a great attainment - <> Dõmin Ya shigar da mũminai maza da mũminai mãtã gidãjen Aljanna, kõgunan ruwa na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen, sunã madawwama a cikinsu kuma Ya kankare musu mũnãnan ayyukansu. wannan abu ya kasance a wurin Allah babban rabo, mai gimia. = --Qur'an 48:5
    And [that] He may punish the hypocrite men and hypocrite women, and the polytheist men and polytheist women - those who assume about Allah an assumption of evil nature. Upon them is a misfortune of evil nature; and Allah has become angry with them and has cursed them and prepared for them Hell, and evil it is as a destination. <> Kuma Ya yi azãba ga munãfikai maza da munãfikai mãtã da mushirikai maza da musbirikai mãtã, mãsu zaton mugun zato game da Allah, mugunyar masĩfa mai kẽwayẽwa ta tabbata a kansu, kuma Allah Ya yi hushi da su, kuma Ya la'ane su, kuma Ya yi musu tattlain Jahannama kuma ta mũnana ta zama makõma (gare su). = --Qur'an 48:6
    And to Allah belong the soldiers of the heavens and the earth. And ever is Allah Exalted in Might and Wise. <> Rundunõnin sammai da ƙasã na Allah kawai ne, kuma Allah Ya kasance Mabuwãyi, Mai hikima. = --Qur'an 48:7
    Indeed, We have sent you as a witness and a bringer of good tidings and a warner <> Lalle Mũ Mun aike ka, kanã mai shaida, kuma mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. = --Qur'an 48:8
    That you [people] may believe in Allah and His Messenger and honor him and respect the Prophet and exalt Allah morning and afternoon. <> Dõmin ku yi ĩmani da Allah da ManzonSa, kuma ku ƙarfafa shi, kuma ku girmama Shi, kuma ku tsarkake Shi (Allah) sãfiya da maraice. = --Qur'an 48:9
    Indeed, those who pledge allegiance to you, [O Muhammad] - they are actually pledging allegiance to Allah. The hand of Allah is over their hands. So he who breaks his word only breaks it to the detriment of himself. And he who fulfills that which he has promised Allah - He will give him a great reward. <> Lalle waɗanda ke yi maka mubãya'a, Allah kawai ne suke yi wa mubãya'a, Hannun Allah nã bisa hannayensu, sabõda haka wanda ya warware, to, yanã warwarẽwa ne a kan kansa kawai, kuma wanda ya cika ga alkawarin da ya yi wa Allah a kansa, to, (Allah) zai kãwo masa ijãra mai girma. = --Qur'an 48:10
    Those who remained behind of the bedouins will say to you, "Our properties and our families occupied us, so ask forgiveness for us." They say with their tongues what is not within their hearts. Say, "Then who could prevent Allah at all if He intended for you harm or intended for you benefit? Rather, ever is Allah, with what you do, Acquainted. <> Waɗanda aka bari daga ƙauyãwa zã su ce maka, "Dũkiyõyinmu da iyãlanmu sun shagaltar da mu, sai ka nẽma mana gãfara." Sunã faɗã, da harsunansu, abin da bã shĩ ne a cikin zukãtansu ba. Kace: "To, wãne ne ke mallakar wani abu daga Allah sabõda kũ, idan Yã yi nufin wata cũta agare ku kõ kuma (idan) Ya yi nufin wani amfãni a gare ku? Ã'a, Allah Ya kasance Mai labartawa ne ga abin da kuke aikatãwa." = --Qur'an 48:11
    But you thought that the Messenger and the believers would never return to their families, ever, and that was made pleasing in your hearts. And you assumed an assumption of evil and became a people ruined." <> Ã'a kun yi zaton Annabi da mũminai, bã za su kõmo zuwa ga iyãlansu ba, har abada. Kuma an ƙawãta wannan (tunãni) a cikin zukãtanku, kuma kun yi zato, zaton mugunta, kuma kun kasance mutãne halakakku. = --Qur'an 48:12
    And whoever has not believed in Allah and His Messenger - then indeed, We have prepared for the disbelievers a Blaze. <> Kuma wanda bai yi ĩmãni da Allah da kuma Manzonsa ba, to, lalle Mũ, Mun yi tattalin wutã mai tsananin ƙũna, dõmin kafirai. = --Qur'an 48:13
    And to Allah belongs the dominion of the heavens and the earth. He forgives whom He wills and punishes whom He wills. And ever is Allah Forgiving and Merciful. <> Mulkin sammai da ƙasã na Allah kawai ne, Yanã gãfartawa ga wanda Yake so, kuma Yanã azabta wanda Yake so alhãli kuwa Allah Ya kasance Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 48:14
    Those who remained behind will say when you set out toward the war booty to take it, "Let us follow you." They wish to change the words of Allah. Say, "Never will you follow us. Thus did Allah say before." So they will say, "Rather, you envy us." But [in fact] they were not understanding except a little. <> Waɗanda aka bari zã su ce idan kun tafi zuwa ga waɗansu ganĩmõmi dõmin ku karɓo su, "Ku bar mu, mu bĩ ku." Sunã son su musanya maganar Allah ne. Ka ce: "Bã zã ku bĩ mu ba. Kamar wannan ne Allah Ya ce, a gabãnin haka." Sa'an nan zã su ce: "Ã'a, kunã dai hãssadar mu ne." Ã'a, sun kasance bã su fahimtar (abũbuwa) sai kaɗan. = --Qur'an 48:15
    Say to those who remained behind of the bedouins, "You will be called to [face] a people of great military might; you may fight them, or they will submit. So if you obey, Allah will give you a good reward; but if you turn away as you turned away before, He will punish you with a painful punishment." <> Ka ce wa waɗanda aka bari daga ƙauyãwa: "Za a kira ku zuwa ga waɗansu mutãne mãsu tsananin yãƙi (dõmin) ku yãƙe su kõ kuwa su musulunta. To, idan kun yi ɗã'a, Allah zai kãwo muku wata ijãra mai kyau, kuma idan kuka jũya bãya kamar yadda kuka jũya a gabãnin wancan, zai azãbtã ku, azãba mai raɗadi." = --Qur'an 48:16
    There is not upon the blind any guilt or upon the lame any guilt or upon the ill any guilt [for remaining behind]. And whoever obeys Allah and His Messenger - He will admit him to gardens beneath which rivers flow; but whoever turns away - He will punish him with a painful punishment. <> Bãbu laifi a kan makãho, kuma bãbu laifi a kan gurgu, kuma bãbu laifi a kan majiyyaci. Kuma wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, (Allah) zai shigar da shi a gidãjen Aljanna, kõguna na gudãna daga ƙarƙashinsu. Kuma wanda ya jũya bãya, (Allah) zai azabtãshi, azãba mai raɗãɗi. = --Qur'an 48:17
    Certainly was Allah pleased with the believers when they pledged allegiance to you, [O Muhammad], under the tree, and He knew what was in their hearts, so He sent down tranquillity upon them and rewarded them with an imminent conquest <> Lalle ne haƙĩƙa, Allah Ya yarda da muminai a lõkacin da suke yi maka mubãya, a a ƙarƙashin itãciyar nan dõmin Yã san abin da ke cikin zukãtansu sai Yã saukar da natsuwa a kansu, kuma Ya sãka musu da wani cin nasara makusanci. = --Qur'an 48:18
    And much war booty which they will take. And ever is Allah Exalted in Might and Wise. <> Da waɗansu ganĩmõmi mãsu yawa da zã su karɓo su. Kuma Allah Yã kasance Mabuwayi, Mai hikima. = --Qur'an 48:19
    Allah has promised you much booty that you will take [in the future] and has hastened for you this [victory] and withheld the hands of people from you - that it may be a sign for the believers and [that] He may guide you to a straight path. <> Kuma Allah Yã yi muku wa'adin waɗansu ganĩmõmi mãsu yawa, waɗanda zã ku karɓo su, kuma Ya gaggauta muku wannan. Kuma Ya kange hannãyen mutãne daga gare ku, kuma dõmin ta kasance wata ãyã ce ga mũminai, kuma Yã shiryar da ku ga hanya madaidaiciya. = --Qur'an 48:20
    And [He promises] other [victories] that you were [so far] unable to [realize] which Allah has already encompassed. And ever is Allah, over all things, competent. <> Da waɗansu (ganĩmõmin) da bã ku da ĩko a kansu lalle Allah Ya kẽwaye su da saninSa, kuma Allah Ya kasance Mai ikon yi ne a kan dukan kõme. = --Qur'an 48:21
    And if those [Makkans] who disbelieve had fought you, they would have turned their backs [in flight]. Then they would not find a protector or a helper. <> Kuma dã waɗanda suka kãfirta sun yãke ku, dã sun jũyar da ɗuwaiwai (dõmin gudu) sa'an nan bã zã su sãmi majiɓinci ba, kuma bã zã su sãmi mataimaki ba. = --Qur'an 48:22
    [This is] the established way of Allah which has occurred before. And never will you find in the way of Allah any change. <> Hanyar Allah wadda ta shũɗe daga gabãnin wannan, kuma bã zã ka sãmi musanya ba ga hanyar Allah (ta taimakon mũminai akan mai zãluntarsu). = --Qur'an 48:23
    And it is He who withheld their hands from you and your hands from them within [the area of] Makkah after He caused you to overcome them. And ever is Allah of what you do, Seeing. <> Kuma Shĩ ne Ya kange hannayensu daga gare ku, kuma da hannayenku daga gare su, a cikin Makka, bãyan Ya rinjãyar da ku a kansu. Kuma Allah Ya kasance Mai gani ga abin da kuke aikatãwa. = --Qur'an 48:24
    They are the ones who disbelieved and obstructed you from al-Masjid al-Haram while the offering was prevented from reaching its place of sacrifice. And if not for believing men and believing women whom you did not know - that you might trample them and there would befall you because of them dishonor without [your] knowledge - [you would have been permitted to enter Makkah]. [This was so] that Allah might admit to His mercy whom He willed. If they had been apart [from them], We would have punished those who disbelieved among them with painful punishment <> Sũ ne waɗanda suka kãfirta kuma suka kange ku daga Masallacin Harami, da hadaya tanã tsare (sun hana ta) ta isa ga wurinta. Kuma bã dõmin waɗansu maza mũminai da waɗansu mãtã mũminai ba ba ku sansu ba ku tãkã su har wani aibi ya sãme ku daga gare su, bã da sani ba, (dã Allah Yã yi muku iznin yãƙi), dõmin Allah Ya shigar da wanda Yake so a cikin rahamarSa. Da (mũminai) sun tsabbace dã Mun azabtar da waɗanda suka kãfirta daga gare su da azãba mai raɗiɗi. = --Qur'an 48:25
    When those who disbelieved had put into their hearts chauvinism - the chauvinism of the time of ignorance. But Allah sent down His tranquillity upon His Messenger and upon the believers and imposed upon them the word of righteousness, and they were more deserving of it and worthy of it. And ever is Allah, of all things, Knowing. <> A lõkacin da waɗanda suka kãfirta suka sanya hanãnar ƙabĩ lanci a cikin zukãtansu hanãnar ƙabĩlanci irin na Jãhiliyya sai Allah Ya saukar da natsuwarSa a kan ManzonSa, kuma da a kan mũminai kuma Ya lazimta musu kalmar taƙawa alhãli kuwa sun kasance mafi dãcẽwa da ita kuma ma'abutanta. Kuma Allah ya kasance Masani game da dukan kõme. = --Qur'an 48:26
    Certainly has Allah showed to His Messenger the vision in truth. You will surely enter al-Masjid al-Haram, if Allah wills, in safety, with your heads shaved and [hair] shortened, not fearing [anyone]. He knew what you did not know and has arranged before that a conquest near [at hand]. <> Lalle ne haƙĩƙa Allah Ya gaskata wa ManzonSa mafarkinsa da gaskiya: Lalle zã ku shiga Masallacin Harami, in Allah Ya so, kunã mãsu natsuwa, mãsu aske kawunanku da mãsu suisuye, bã ku jin tsõro, dõmin (Allah) Ya san abin da ba ku sani ba, sa'an nan Ya sanya wani cin nasara makusanci a bãyan wannan. = --Qur'an 48:27
    It is He who sent His Messenger with guidance and the religion of truth to manifest it over all religion. And sufficient is Allah as Witness. <> Shĩ ne wanda Ya aiki ManzonSa da shiriya da addinin gaskiya dõmin Ya rinjãyar da shi a kan addinai dukansu. Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai shaida. = --Qur'an 48:28
    Muhammad is the Messenger of Allah; and those with him are forceful against the disbelievers, merciful among themselves. You see them bowing and prostrating [in prayer], seeking bounty from Allah and [His] pleasure. Their mark is on their faces from the trace of prostration. That is their description in the Torah. And their description in the Gospel is as a plant which produces its offshoots and strengthens them so they grow firm and stand upon their stalks, delighting the sowers - so that Allah may enrage by them the disbelievers. Allah has promised those who believe and do righteous deeds among them forgiveness and a great reward. <> Muhammadu Manron Allah ne. Kuma waɗannan da ke tãre da shi mãsu tsanani ne a kan kãfirai, mãsu rahama ne a tsakãninsu, kanã ganin su sunã mãsu rukũ'i mãsu sujada, sunã nẽman falala daga Ubangijinsu, da yardarSa. Alãmarsu tanã a cikin fuskõkinsu, daga kufan sujuda. Wannan shĩ ne siffarsu a cikin Attaura. Kuma siffarsu, a cikin Injĩla ita ce kamar tsiron shũka wanda ya fitar da rẽshensa, sa'an nan ya ƙarfafa shi, ya yi kauri, sa'an nan ya daidaita a kan ƙafãfunsa, yanã bãyar da sha'awa ga mãsu shũkar' dõmin (Allah) Ya fusãtar da kãfirai game da su. Kuma Allah Ya yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, daga cikinsu, da gãfara da ijãra mai girma. = --Qur'an 48:29
    O you who have believed, do not put [yourselves] before Allah and His Messenger but fear Allah. Indeed, Allah is Hearing and Knowing. <> Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku gabãta (da kõme) gaba ga Allah da ManzonSa. Kuma ku yi ɗã'ã ga Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai ji ne, Masani. = --Qur'an 49:1
    O you who have believed, do not raise your voices above the voice of the Prophet or be loud to him in speech like the loudness of some of you to others, lest your deeds become worthless while you perceive not. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku ɗaukaka saututtukanku bisa sautin Annabi, kuma kada ku bayyana sauti gare shi a magana, kamar bayyanãwar sãshenku ga sãshe, dõmin kada ayyukanku su ɓãci, alhãli kuwa kũ ba ku sani ba. = --Qur'an 49:2
    Indeed, those who lower their voices before the Messenger of Allah - they are the ones whose hearts Allah has tested for righteousness. For them is forgiveness and great reward. <> Lalle waɗanda ke runtsẽwar saututtukansu a wurin Manzon Allah waɗannan ne waɗanda Allah Yã, jarrabi zukãtansu ga taƙawa. Sunã da wata irin gãfara da ijãra mai girma. = --Qur'an 49:3
    Indeed, those who call you, [O Muhammad], from behind the chambers - most of them do not use reason. <> Lalle waɗanda ke kiranka daga bãyan ɗakuna, mafi Yawansu bã su aiki da hankali. = --Qur'an 49:4
    And if they had been patient until you [could] come out to them, it would have been better for them. But Allah is Forgiving and Merciful. <> Kuma dã lalle sũ, sun yi haƙuri har ka fita zuwa gare su, haƙĩƙa, dã yã kasance mafi alhẽri gare su, kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 49:5
    O you who have believed, if there comes to you a disobedient one with information, investigate, lest you harm a people out of ignorance and become, over what you have done, regretful. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan fãsiƙi Yã zo muku da wani babban lãbãri, to, ku nẽmi bayãni, dõmin kada ku cũci waɗansu mutãne a cikin jãhilci, sabõda haka ku wãyi gari a kan abin da kuka aikata kunã mãsu nadãma. = --Qur'an 49:6
    And know that among you is the Messenger of Allah. If he were to obey you in much of the matter, you would be in difficulty, but Allah has endeared to you the faith and has made it pleasing in your hearts and has made hateful to you disbelief, defiance and disobedience. Those are the [rightly] guided. <> Kuma ku sani (cẽwa) lalle ne, a cikinku akwai Manzon Allah. Dã Yana bin ku ga (hãlãye) mãsu Yawa na al'amarin, dã kun auku a cikin zunubi, kuma amma Allah Yã sõyar da ĩmãni a gare ku, kuma Yã ƙawãta shi a cikin zukãtanku kuma Yã ƙyãmantar da kãfirci da fãsicci da sãɓo zuwa gare ku. Waɗannan (da suka lazimci sifõfin nan) su ne shiryayyu. = --Qur'an 49:7
    [It is] as bounty from Allah and favor. And Allah is Knowing and Wise. <> Bisa ga falala daga Allah da ni'ima. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima. = --Qur'an 49:8
    And if two factions among the believers should fight, then make settlement between the two. But if one of them oppresses the other, then fight against the one that oppresses until it returns to the ordinance of Allah. And if it returns, then make settlement between them in justice and act justly. Indeed, Allah loves those who act justly. <> Kuma idan jama'a biyu ta mũminai suka yi yãki, to, kuyi sulhu, a tsakãninsu. Sai idan ɗayansu ta yi zãlunci a kan gudar, to, sai ku yãƙi wadda ke yin zãlunci har ta kõma, zuwa ga umurnin Allah. To, idan ta kõma, sai ku yi sulhu a tsakãninsu da ãdalci kuma ku daidaita. Lalle Allah na son mãsu daidaitãwa. = --Qur'an 49:9
    The believers are but brothers, so make settlement between your brothers. And fear Allah that you may receive mercy. <> Mũminai 'yan'uwan jũna kawai ne, sabõda haka ku yi sulhu a tsakãnin 'yan'uwanku biyu, kuma ku bi Allah da taƙawa tsammãninku, a yi muku rahama. = --Qur'an 49:10
    O you who have believed, let not a people ridicule [another] people; perhaps they may be better than them; nor let women ridicule [other] women; perhaps they may be better than them. And do not insult one another and do not call each other by [offensive] nicknames. Wretched is the name of disobedience after [one's] faith. And whoever does not repent - then it is those who are the wrongdoers. <> "Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada waɗansu mutãne su yi izgili game da waɗansu mutãne, mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (mãsu izgilin), kuma waɗansu mãtã kada su yi izgili game da waɗansu mãtã mai yiwuwa ne su kasancc mafĩfĩta daga gare su. Kuma kada ku aibanta kanku, kuma kada ku jẽfi jũna da miyãgun sunãye na laƙabõbĩ. Tir da sũna na fãsicci a bãyãn ĩmãni. Kuma wanda bai tũba ba, to, waɗannan sũ ne azzãlumai." = --Qur'an 49:11
    O you who have believed, avoid much [negative] assumption. Indeed, some assumption is sin. And do not spy or backbite each other. Would one of you like to eat the flesh of his brother when dead? You would detest it. And fear Allah; indeed, Allah is Accepting of repentance and Merciful. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku nĩsanci abu mai yãwa na zato. Lalle sãshen zato laifi ne. Kuma kada ku yi rahõto, kuma kada sãshenku yã yi gulmar sãshe. Shin, ɗayanku nã son yã ci naman ɗan'uwansa yanã matacce? To, kun ƙĩ shi (cin nãman). Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai karɓar tũba ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 49:12
    O mankind, indeed We have created you from male and female and made you peoples and tribes that you may know one another. Indeed, the most noble of you in the sight of Allah is the most righteous of you. Indeed, Allah is Knowing and Acquainted. <> Yã kũ mutãne! Lalle ne Mũ, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangõgi da kabĩlõli, dõmin ku san jũna. Lalle mafĩfĩcinku daraja a wurin Allah, (shĩ ne) wanda yake mafĩfĩcinku a taƙawa. Lalle nẽ Allah Masani ne, Mai ƙididdigẽwa. = --Qur'an 49:13
    The bedouins say, "We have believed." Say, "You have not [yet] believed; but say [instead], 'We have submitted,' for faith has not yet entered your hearts. And if you obey Allah and His Messenger, He will not deprive you from your deeds of anything. Indeed, Allah is Forgiving and Merciful." <> ¡auyãwa suka ce: "Mun yi ĩmãni." Ka ce: "Ba ku yi ĩmãni ba, amma dai ku ce, 'Mun mĩƙawuya, ĩmani bai gama shiga a cikinzukãtanku ba. Kuma idan kun yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, to, bã zai rage muku kõme daga ayyukanku ba. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai." = --Qur'an 49:14
    The believers are only the ones who have believed in Allah and His Messenger and then doubt not but strive with their properties and their lives in the cause of Allah. It is those who are the truthful. <> Mũminan gaskiya kawai, sũ ne waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, sa'an nan ba su yi shakka ba, kuma suka yi jihãdi da dũkiyarsu da kuma rãyukansu, cikin tafarkin Allah. Waɗannan sũ ne mãsu gaskiya. = --Qur'an 49:15
    Say, "Would you acquaint Allah with your religion while Allah knows whatever is in the heavens and whatever is on the earth, and Allah is Knowing of all things?" <> Ka ce: "Kuna sanar da Allah ne game da addininku, alhãli kuwa Allah Yã san abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa, kuma Allah Masani ne ga dukan kõme?" = --Qur'an 49:16
    They consider it a favor to you that they have accepted Islam. Say, "Do not consider your Islam a favor to me. Rather, Allah has conferred favor upon you that He has guided you to the faith, if you should be truthful." <> Suna yin gõri a kanka wai sun musulunta. Ka ce: "Kada ku yi gõrin kun musulunta a kaina. Ã'a, Allah ne ke yi muku gõri dõmin Ya shiryar da ku ga ĩmãni, idan kun kasance mãsu gaskiya." = --Qur'an 49:17
    Indeed, Allah knows the unseen [aspects] of the heavens and the earth. And Allah is Seeing of what you do. <> "Lalle Allah yanã sanin gaibin sammai da ¡asa, kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa." = --Qur'an 49:18
    Qaf. By the honored Qur'an... <> ¡̃. Inã rantsuwa da Alƙur'ãni Mai girma. = --Qur'an 50:1
    But they wonder that there has come to them a warner from among themselves, and the disbelievers say, "This is an amazing thing. <> Ã'a, sun yi mãmãki, cewa mai gargaɗi, daga gare su, yã zo musu, sai kãfirai suka ce: "Wannan wani abu ne mai ban mãmãki." = --Qur'an 50:2
    When we have died and have become dust, [we will return to life]? That is a distant return." <> "Shin idan muka mutu kuma muka kasance turɓãya (zã a kõmo da mu)? Waccan kõmowa ce mai nĩsa." = --Qur'an 50:3
    We know what the earth diminishes of them, and with Us is a retaining record. <> Lalle ne Mun san abin da ƙasã ke ragẽwo daga gare su, kuma wurinMu akwai wani littãfi mai tsarẽwa. = --Qur'an 50:4
    But they denied the truth when it came to them, so they are in a confused condition. <> Ã'a, sun ƙaryata ne game da gaskiyar a lõkacin da ta je musu, sabõda haka sunã a cikin wani al'amari mai raurawa. = --Qur'an 50:5
    Have they not looked at the heaven above them - how We structured it and adorned it and [how] it has no rifts? <> Shin, to, ba su yi dubi ba zuwa ga samã a bisa gare su, yadda Muka gĩna ta, kuma Muka ƙawãce ta, kuma bã ta da waɗansu tsãgogi? = --Qur'an 50:6
    And the earth - We spread it out and cast therein firmly set mountains and made grow therein [something] of every beautiful kind, <> Da ƙasã, Mun mĩƙe ta, kuma Mun jẽfa kafaffun duwãtsu a cikinta, kuma Mun tsirar, a cikinta daga kõwane ma'auri mai ban sha'awa? = --Qur'an 50:7
    Giving insight and a reminder for every servant who turns [to Allah]. <> Dõmin wãyar da ido da tunãtarwa ga dukan bãwa mai tawakkali? = --Qur'an 50:8
    And We have sent down blessed rain from the sky and made grow thereby gardens and grain from the harvest <> Kuma Mun sassakar, daga samã ruwa mai albarka sa'an nan Muka tsirar game da shi (itãcen) lambuna da ƙwãya abin girbẽwa. = --Qur'an 50:9
    And lofty palm trees having fruit arranged in layers - <> Da itãcen dabĩno dõgãye, sunã da'ya'yan itãce gunda mãsu hauhawar jũna. = --Qur'an 50:10
    As provision for the servants, and We have given life thereby to a dead land. Thus is the resurrection. <> Dõmin arziki ga bãyi, kuma Muka rãyar da ƙasa matacciya game da shi. Kamar wannan ne fitar daga kabari kake. = --Qur'an 50:11
    The people of Noah denied before them, and the companions of the well and Thamud <> Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu (mutãnen yanzu) da ma'abũta Rassi, da Samũdãwa. = --Qur'an 50:12
    And 'Aad and Pharaoh and the brothers of Lot <> Da Ãdãwa da Fir'auna da 'yan'uwan Lũɗu. = --Qur'an 50:13
    And the companions of the thicket and the people of Tubba'. All denied the messengers, so My threat was justly fulfilled. <> Da ma'abũta ƙunci da mutãnen Tubba'u, kõwanensu ya ƙaryata Manzanni, sai ƙyacẽwaTa ta tabbata. = --Qur'an 50:14
    Did We fail in the first creation? But they are in confusion over a new creation. <> Shin, to, Mun kãsa ne game da halittar farko? Ã'a, su sunã a cikin rikici daga halitta sãbuwa. = --Qur'an 50:15
    And We have already created man and know what his soul whispers to him, and We are closer to him than [his] jugular vein <> Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta mutum kuma Mun san abin da ransa ke yin waswãsi da shi, kuma Mũ ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar jannayẽnsa. = --Qur'an 50:16
    When the two receivers receive, seated on the right and on the left. <> A lõkacin da mãsu haɗuwa biyu suke haɗuwa daga dãma, kuma daga hagu akwai wani (malã'ika) zaunanne. = --Qur'an 50:17
    Man does not utter any word except that with him is an observer prepared [to record]. <> Bã ya lafazi da wata magana fãce a lĩƙe da shi akwai mai tsaro halartacce. = --Qur'an 50:18
    And the intoxication of death will bring the truth; that is what you were trying to avoid. <> Kuma mãyen mutuwa ya jẽ da gaskiya. Wannan shĩ ne abin da ka kasance daga gare shi kanã bijirẽwa. = --Qur'an 50:19
    And the Horn will be blown. That is the Day of [carrying out] the threat. <> Kuma aka hũra a cikin ƙaho. Wancan yinin ƙyacẽwar ne fa. = --Qur'an 50:20
    And every soul will come, with it a driver and a witness. <> Kuma kõwane rai ya zo, tãre da shi akwai mai kõra da mai shaida. = --Qur'an 50:21
    [It will be said], "You were certainly in unmindfulness of this, and We have removed from you your cover, so your sight, this Day, is sharp." <> (Sai a ce masa): "Lalle ne, haƙĩƙa, ka kasance a cikin gafala daga wannan. To, Mun kuranye maka rufinka, sabõda haka ganinka a yau, mai kaifi ne." = --Qur'an 50:22
    And his companion, [the angel], will say, "This [record] is what is with me, prepared." <> Kuma abõkin haɗinsa ya ce: "Wannan shi ne abin da ke tãre da ni halarce." = --Qur'an 50:23
    [Allah will say], "Throw into Hell every obstinate disbeliever, <> (A ce wa Malã'iku), "Ku jẽfa, a cikin Jahannama, dukan mai yawan kãfirci, mai tsaurin rai." = --Qur'an 50:24
    Preventer of good, aggressor, and doubter, <> "Mai yawan hanãwa ga alhẽri, mai zãlunci, mai shakka." = --Qur'an 50:25
    Who made [as equal] with Allah another deity; then throw him into the severe punishment." <> "Wanda ya sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, sabõda haka kujẽfa shi a cikin azãba mai tsanani." = --Qur'an 50:26
    His [devil] companion will say, "Our Lord, I did not make him transgress, but he [himself] was in extreme error." <> Abõkin haɗinsa ya ce: "Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya kasance a cikin ɓata mai nĩsa." = --Qur'an 50:27
    [Allah] will say, "Do not dispute before Me, while I had already presented to you the warning. <> Ya ce: "Kada ku yi husũma a wuriNa, alhãli Na gabãtar da ƙyacewa zuwa gare ku." = --Qur'an 50:28
    The word will not be changed with Me, and never will I be unjust to the servants." <> "Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zãlunci ba ga bãyiNa." = --Qur'an 50:29
    On the Day We will say to Hell, "Have you been filled?" and it will say, "Are there some more," <> Rãnar da Muke cẽwa ga Jahannama "Shin, kin cika?" Kuma ta ce: "Ashe, akwai wani ƙãri?" = --Qur'an 50:30
    And Paradise will be brought near to the righteous, not far, <> Kuma a kusantar dã Aljanna ga mãsu taƙawa, ba da nĩsa ba. = --Qur'an 50:31
    [It will be said], "This is what you were promised - for every returner [to Allah] and keeper [of His covenant] <> "Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi da shi ga dukan mai yawan kõmawa ga Allah, mai tsarewar (umurninSa). = --Qur'an 50:32
    Who feared the Most Merciful unseen and came with a heart returning [in repentance]. <> "Wanda ya ji tsõron Mai rahama a fake, kuma ya zo da wata irin zũciya mai tawakkali." = --Qur'an 50:33
    Enter it in peace. This is the Day of Eternity." <> (A ce musu) "Ku shige ta da aminci, waccan ita ce rãnar dawwama." = --Qur'an 50:34
    They will have whatever they wish therein, and with Us is more. <> Sunã da abin da suke so a cikinta, kuma tãre da Mũ akwai ƙãrin ni'ima, = --Qur'an 50:35
    And how many a generation before them did We destroy who were greater than them in [striking] power and had explored throughout the lands. Is there any place of escape? <> Kuma da yawa Muka halakar, a gabãninsu, (mutãnen yanzu) ɗaga waɗansu al'ummomi, (waɗanda suke) sũ ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa'an nan suka yi bincike a cikin ƙasãshe: 'Kõ akwai wurin tsĩra'? (Babu). = --Qur'an 50:36
    Indeed in that is a reminder for whoever has a heart or who listens while he is present [in mind]. <> Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare shi, kõ kuwa ya jẽfa saurãro, alhãli kuwa yanã halarce (da hankalinsa). = --Qur'an 50:37
    And We did certainly create the heavens and earth and what is between them in six days, and there touched Us no weariness. <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu, a cikin kwãnaki shida, alhãli wata'yar wahala ba ta shãfe Mu ba. = --Qur'an 50:38
    So be patient, [O Muhammad], over what they say and exalt [Allah] with praise of your Lord before the rising of the sun and before its setting, <> Sabõda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadã, kuma ka yi tasĩhi game da gõdẽ wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta. = --Qur'an 50:39
    And [in part] of the night exalt Him and after prostration. <> Kuma daga dare, sai ka yi tasbĩhi a gare Shi da bãyan sujada. = --Qur'an 50:40
    And listen on the Day when the Caller will call out from a place that is near - <> Kuma ka saurãra a rãnar da mai kira ke yin kira daga wuri makusanci. = --Qur'an 50:41
    The Day they will hear the blast [of the Horn] in truth. That is the Day of Emergence [from the graves]. <> Rãnar da suke saurãron tsãwa da gaskiya. Wancan shĩ ne yinin fita (daga kabari). = --Qur'an 50:42
    Indeed, it is We who give life and cause death, and to Us is the destination <> Lalle Mũ ne haƙĩƙa, Mu ne ke rãyarwa, kuma Mũ ne ke kashẽwa, kuma zuwa gare Mu kawai ne makõmar take. = --Qur'an 50:43
    On the Day the earth breaks away from them [and they emerge] rapidly; that is a gathering easy for Us. <> Rãnar da ƙasã ke tsattsãgẽwa daga gare su, sunã mãsu gaggãwa. Wancan tãrãwar mutãne ne, mai sauƙi a gare Mu. = --Qur'an 50:44
    We are most knowing of what they say, and you are not over them a tyrant. But remind by the Qur'an whoever fears My threat. <> Mũ ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma bã zã ka zama mai tĩlasta su ba. Sabõda haka ka tunatar game da Alƙur'ani, ga wanda ke tsõron ƙyacewaTa. = --Qur'an 50:45
    By those [winds] scattering [dust] dispersing <> Inã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa. = [51:1] Da iskoki masu naushi. --Qur'an 51:1
    And those [clouds] carrying a load [of water] <> Sa'an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa). = [51:2] Sa'an nan da giragizai masu daukan ruwa. --Qur'an 51:2
    And those [ships] sailing with ease <> Sa'an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi. = [51:3] Masu gudanar da tanadi. --Qur'an 51:3
    And those [angels] apportioning [each] matter, <> Sa'an nan da Malã'iku mãsu rabon al'amari (bisa umurnin Allah). = [51:4] Suna masu rabonsu a bisa umurni. --Qur'an 51:4
    Indeed, what you are promised is true. <> Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne. = [51:5] Lalle abin da aka yi maku alkawari da zuwansa, gaskiya ne. --Qur'an 51:5
    And indeed, the recompense is to occur. <> Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne = [51:6] Haqiqa ranaran sakamako mai aukuwa ne --Qur'an 51:6
    By the heaven containing pathways, <> Inã rantsuwa da samã ma'abũciyar hanyõyi (na tafiyar taurãri da sautin rediyo). = [51:7] Duk da cewan an halitta sama babu aibi. --Qur'an 51:7
    Indeed, you are in differing speech. <> Lalle kũ, haƙĩƙa, kunã cikin magana mai sãɓa wa juna (game da Alƙur'ani). = [51:8] Kuna ta husuma game da gaskiya. --Qur'an 51:8
    Deluded away from the Qur'an is he who is deluded. <> Anã karkatar da wanda aka jũyar (daga gaskiya). = [51:9] Masu karkatawa daga gaskiya su ne masu karkatawa. --Qur'an 51:9
    Destroyed are the falsifiers <> An la'ani mãsu ƙiri-faɗi. = [51:10] An la'ani ma-qaryata. --Qur'an 51:10
    Who are within a flood [of confusion] and heedless. <> Waɗanda suke shagala a cikin zurfin jãhilci. = [51:11] Wadanda suka shagala a cikin zurfin jahilci. --Qur'an 51:11
    They ask, "When is the Day of Recompense?" <> Sunã tambaya: "Yaushe ne rãnar sakamako zã ta auku?" = [51:12] Suna qalubalantar tsayiwar ranar sakamako. --Qur'an 51:12
    [It is] the Day they will be tormented over the Fire <> Ranar da suke a kan wuta anã fitinar su. = [51:13] Ranar da za gabatar da su ga wuta. --Qur'an 51:13
    [And will be told], "Taste your torment. This is that for which you were impatient." <> (A ce musu): "Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shĩ ne abin da kuka kasance kunã nẽman zuwansa da gaggãwa." = [51:14] (A ce masu): "Ku dandani azaba; wannan shi ne abin da, da kuke qalubalanta. --Qur'an 51:14
    Indeed, the righteous will be among gardens and springs, <> Lalle mãsu taƙawa, sunã a cikin lambunan itãce da marẽmari. = [51:15] Masu taqawa su ne suka cancanci lambuna da maremari. --Qur'an 51:15
    Accepting what their Lord has given them. Indeed, they were before that doers of good. <> Sunã mãsu dĩbar abin da Ubangijinsu Ya bã su. Lalle sũ, sun kasance mãsu kyautatãwa a gabãnin haka (a dũniya). = [51:16] Za su debi ladar Ubangijinsu, saboda da sun kasance masu kyautatawa a gabanin haka. --Qur'an 51:16
    They used to sleep but little of the night, <> Sun kasance a lõkaci kaɗan na dare suke yin barci. = [51:17] Ba safai ba suke yin barcin dare dukanta ba. --Qur'an 51:17
    And in the hours before dawn they would ask forgiveness, <> Kuma a lõkutan asuba sunã ta yin istigfãri. = [51:18] Kuma a lokutan asuba suna yin istigfari. --Qur'an 51:18
    And from their properties was [given] the right of the [needy] petitioner and the deprived. <> Kuma a cikin dũkiyarsu akwai hakki ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hana wa rõƙo. = [51:19] Kaso a cikin dukiyarsu akwai hakki da suka ajiye saboda masu roqo da matalauta. --Qur'an 51:19
    And on the earth are signs for the certain [in faith] <> Kuma a cikin ƙasã akwai ãyõyi ga mãsu yaƙĩni. = [51:20] Kuma a cikin qasa akwai ayõyi ga masu yaqini. --Qur'an 51:20
    And in yourselves. Then will you not see? <> Kuma a cikin rãyukanku (akwai ãyõyi). To, bã zã ku dũbã ba? = [51:21] Da a cikin rayukanku; za ku iya gani? --Qur'an 51:21
    And in the heaven is your provision and whatever you are promised. <> Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari. = [51:22] A cikin sama arzikinku ke fitowa, da duk abin da ake yi maku alkawari. --Qur'an 51:22
    Then by the Lord of the heaven and earth, indeed, it is truth - just as [sure as] it is that you are speaking. <> To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da ƙasã, lalle shĩ (abin da ake yi muku alkawari), haƙĩƙa gaskiya ne, kamar abin da kuka zamo kunã karantãwa na magana, = [51:23] To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da qasa, wannan gaskiya ne, kamar tabbacin gaskiya cewa kuna magana. --Qur'an 51:23
    Has there reached you the story of the honored guests of Abraham? - <> Shin, lãbãrin Bãƙin Ibrãhĩm, waɗanda aka girmama, ya zo maka? = [51:24] Shin, labarin baqinIbrahim, wadanda aka girmama, ya zo maka? --Qur'an 51:24
    When they entered upon him and said, "[We greet you with] peace." He answered, "[And upon you] peace, [you are] a people unknown. <> A lõkacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce "Aminci ya tabbata a gare ku, mutãne bãƙi!" = [51:25] Sa’ad da suka ziyarce shi, suka yi “sallama” ya ce "Salam gare ku mutane baqi!" --Qur'an 51:25
    Then he went to his family and came with a fat [roasted] calf <> Sai ya jũya zuwa ga iyãlinsa, sa'an nan ya zo da maraƙi tutturna, = [51:26] Sai ya sa iyalinsa ta shirya wata maraqi tutturna. --Qur'an 51:26
    And placed it near them; he said, "Will you not eat?" <> Sai ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce: "Bã zã ku ci ba?" = [51:27] Sa’ad day ya basu, ya ce, "Ba za ku ci ba?" --Qur'an 51:27
    And he felt from them apprehension. They said, "Fear not," and gave him good tidings of a learned boy. <> Sai ya ji tsõro daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro." Kuma suka yi masa bushãra da (haihuwar) wani yaro mai ilmi. = [51:28] Sai tsoro ya kama shi game da su. Suka ce, "Kada kaji tsoro," sai suka yi masa bishara da (haihuwar) yaro mai ilmi. --Qur'an 51:28
    And his wife approached with a cry [of alarm] and struck her face and said, "[I am] a barren old woman!" <> Sai matarsa ta fuskanta cikin ƙyallõwa, har ta mari fuskarta kuma ta ce: "Tsõhuwa bakarãriya (zã ta haihu)!" = [51:29] Sai matarsa ta yi mamaki. Tana kallon takureren fuskarta: ta ce, "Ni tsohuwa ce bakarariya." --Qur'an 51:29
    They said, "Thus has said your Lord; indeed, He is the Wise, the Knowing." <> Suka ce: "Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai hikima, Mai ilmi." = [51:30] Suka ce, "Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Shi ne Mafi hikimah, Mai ilmi." --Qur'an 51:30
    [Abraham] said, "Then what is your business [here], O messengers?" <> (Ibrãĩm) ya ce: "To mẽne ne babban al'almarinku, yã kũ Manzanni!" = [51:31] (Ibrahim) ya ce, "To ina kuka nufa, ya ku manzanni?" --Qur'an 51:31
    They said, "Indeed, we have been sent to a people of criminals <> Suka ce: "Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutãne, mãsu laifi. = [51:32] Suka ce, "An aike mu ne zuwa ga mujirimai. --Qur'an 51:32
    To send down upon them stones of clay, <> "Dõmin mu saka musu waɗansu duwãtsu na wani yumɓu (bom). = [51:33] "Domin mu yi masu ruwan duwatsun yumbu. --Qur'an 51:33
    Marked in the presence of your Lord for the transgressors." <> "Waɗanda aka yi wa alãma daga wajen Ubangijinka, dõmin mãsu ɓarna." = [51:34] "Wadanda aka yi wa alama daga wajen Ubangijinka, domin masu qetare iyaka." --Qur'an 51:34
    So We brought out whoever was in the cities of the believers. <> Sa'an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai. = [51:35] Sa'an, nan Muka fitar da dukan wadanda suke muminai. --Qur'an 51:35
    And We found not within them other than a [single] house of Muslims. <> Sai dai ba mu sãmu ba, a cikinta, fãce gida guda na Musulmi. = [51:36] Sai dai ba mu samu a cikinta ba, sai gida guda na Musulmai. --Qur'an 51:36
    And We left therein a sign for those who fear the painful punishment. <> Kuma Muka bar wata ãyã, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsõron azãba, mai raɗaɗi. = [51:37] Muka sa ta zama ayah, ga wadanda ke jin tsoron azaba, mai zafi. --Qur'an 51:37
    And in Moses [was a sign], when We sent him to Pharaoh with clear authority. <> Kuma ga Mũsã, a lõkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli bayyananne. = [51:38] Kuma ga Musa ma (akwai ayah). Sa’ad da Muka aika shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli bayyananne. --Qur'an 51:38
    But he turned away with his supporters and said," A magician or a madman." <> Sai ya jũya bãya tãre da ƙarfinsa, kuma ya ce: "Mai sihiri ne kõ kuwa mahaukaci!" = [51:39] Amma sai ya juya baya, a cikin girman kansa, ya ce, "Mai sihiri ne ko kuwa mahaukaci." --Qur'an 51:39
    So We took him and his soldiers and cast them into the sea, and he was blameworthy. <> Sabõda haka, Muka kama shi tãre da rundunarsa, sa'an nan Muka jẽfa su a cikin tẽku, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi. = [51:40] Saboda haka, Muka azabta shi tare da rundunarsa. Muka jefa su a cikin teku, alhali kuwa shi ne wanda za zarga. --Qur'an 51:40
    And in 'Aad [was a sign], when We sent against them the barren wind. <> Kuma ga Ãdãwa, a lõkacin da Muka aika iska ƙẽƙasasshiya a kansu. = [51:41] Kuma ga Adawa ma (akawai ayah). Sa’ad da Muka aika iskar bala’i a kansu. --Qur'an 51:41
    It left nothing of what it came upon but that it made it like disintegrated ruins. <> Bã ta barin kõme da ta jẽ a kansa, fãce ta mayar da shi kamar rududdugaggun ƙasũsuwa. = [51:42] Ba ta bari kome ba, da ta zo a kanta sai da ta mayar da shi kamar rududdugaggun qasusuwa. --Qur'an 51:42
    And in Thamud, when it was said to them, "Enjoy yourselves for a time." <> Kuma ga Samũdãwa, a lõkacin da aka ce musu: "Ku ji ɗan dãɗi har wani ɗan lõkaci," = [51:43] Kuma ga Samudawa ma (akwai ayah). Sa’ad da aka ce masu, "Ku dan more na dan lokaci." --Qur'an 51:43
    But they were insolent toward the command of their Lord, so the thunderbolt seized them while they were looking on. <> Sai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, sabõda haka tsãwa ta kãma su, alhãli kuwa sunã kallo. = [51:44] Sai suka yi tawaye ga umurnin Ubangijinsu. saboda haka, walqiyan aradu nausa su, sa’ad da suna kallo. --Qur'an 51:44
    And they were unable to arise, nor could they defend themselves. <> Ba su kõ sãmu dãmar tsayãwa ba, kuma ba su kasance mãsu nẽman ãgaji ba. = [51:45] Ba su ko samu damar tashiwa ba, kuma ba agaza masu ba. --Qur'an 51:45
    And [We destroyed] the people of Noah before; indeed, they were a people defiantly disobedient. <> Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai. = [51:46] Da mutanen Nuhu a gabanin haka; su ma mugayen mutane ne. --Qur'an 51:46
    And the heaven We constructed with strength, and indeed, We are [its] expander. <> Kuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhãli kuwa lalle Mũ ne Mãsu yalwatãwa. = [51:47] Mun gina sama da hannunMu, kuma Mu ne za mu ci gaba da yalwatata. --Qur'an 51:47
    And the earth We have spread out, and excellent is the preparer. <> Kuma ƙasã Mun shimfiɗa ta, To, madalla da mãsu shimfiɗãwa, Mũ, = [51:48] Kuma Muka sanya qasa ta zama wurin rayuwa; madaidaicin fasali. --Qur'an 51:48
    And of all things We created two mates; perhaps you will remember. <> Kuma daga kõme Mun halitta nau'i biyu, watakila zã ku yi tunãni. = [51:49] Kuma muka halitta kome nau'i biyu (na miji da mace), la’alla ku yi tunani. --Qur'an 51:49
    So flee to Allah. Indeed, I am to you from Him a clear warner. <> Sabõda haka ku gudu zuwa ga Allah, lalle nĩ mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi. = [51:50] Saboda haka, ku gudu zuwa ga ALLAH. Shi ne Ya aiko ni zuwa gare ku, a matsayin mai gargadi bayyananne. --Qur'an 51:50
    And do not make [as equal] with Allah another deity. Indeed, I am to you from Him a clear warner. <> Kuma kada ku sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, lalle nĩ, mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi. = [51:51] Kada ku sanya tare da ALLAH wani abin bautawa na dabam. Shi ne ya aiko ni zuwa gare ku, a matsayin mai gargadi bayyananne. --Qur'an 51:51
    Similarly, there came not to those before them any messenger except that they said, "A magician or a madman." <> Kamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabãninsu ba fãce sun ce: "Mai sihiri ne kõ mahaukaci." = [51:52] Kamar haka, sa’ad da wani manzo ya je zuwa ga mutanen zamanin da, suka ce, “Masihirci ne,” ko kuwa “Mahaukaci.” --Qur'an 51:52
    Did they suggest it to them? Rather, they [themselves] are a transgressing people. <> shin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã'a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai. = [51:53] Shin, ba sun qulla yarjejeniya wa juna ba? Lalle, su masu girman kai ne. --Qur'an 51:53
    So leave them, [O Muhammad], for you are not to be blamed. <> Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne. = [51:54] To, ka qyale su; ba za zarge ka ba. --Qur'an 51:54
    And remind, for indeed, the reminder benefits the believers. <> Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai. = [51:55] Kuma ka tunatar, domin tunatarwa tana amfanin muminai. (Dalilin Rayuwarmu) --Qur'an 51:55
    And I did not create the jinn and mankind except to worship Me. <> Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini. = [51:56] Ban halitta aljannu da mutane domin kome ba sai dai su bauta Mini Ni kadai. --Qur'an 51:56
    I do not want from them any provision, nor do I want them to feed Me. <> Bã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni. = [51:57] Ba Na bukatan wani arziqi daga gare su, Ba Na kuma bukatan su ciyar da Ni. --Qur'an 51:57
    Indeed, it is Allah who is the [continual] Provider, the firm possessor of strength. <> Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi. = [51:58] ALLAH, Shi ne Mai azurtawa, Mai ikon yi, Mai cikakken qarfi. --Qur'an 51:58
    And indeed, for those who have wronged is a portion [of punishment] like the portion of their predecessors, so let them not impatiently urge Me. <> To, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggãwa. = [51:59] Wadanda suka qetare iyaka sun jawo wa kansu irin masakin abokansu; saboda haka kada su qalubalanta. --Qur'an 51:59
    And woe to those who have disbelieved from their Day which they are promised. <> Sabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari. = [51:60] Bone ya tabbata ga wadanda suka kafirta, daga ranar da ke jiransu. --Qur'an 51:60
    By the mount <> Inã rantsuwa da ¦ũr (Dũtsen Mũsã). = --Qur'an 52:1
    And [by] a Book inscribed <> Da wani littãfi rubũtacce. = --Qur'an 52:2
    In parchment spread open <> A cikin wata takardar fãta shimfiɗaɗɗa. = --Qur'an 52:3
    And [by] the frequented House <> Da Gidan da aka rãyar da shi (da ibãda). = --Qur'an 52:4
    And [by] the heaven raised high <> Da rufin nan da aka ɗaukaka. = --Qur'an 52:5
    And [by] the sea filled [with fire], <> Da tẽkun nan da aka cika (da ruwa). = --Qur'an 52:6
    Indeed, the punishment of your Lord will occur. <> Lalle, azãbar Ubangijinka, haƙĩƙa, mai aukuwa ce. = --Qur'an 52:7
    Of it there is no preventer. <> Bã ta da mai tunkuɗẽwa. = --Qur'an 52:8
    On the Day the heaven will sway with circular motion <> Rãnar da samã ke yin mõtsi tanã kai kãwo. = --Qur'an 52:9
    And the mountains will pass on, departing - <> Kuma duwãtsu nã tafiya sunã shũɗẽwa. = --Qur'an 52:10
    Then woe, that Day, to the deniers, <> To, bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa. = --Qur'an 52:11
    Who are in [empty] discourse amusing themselves. <> Waɗanda suke a cikin kududdufi sunã wãsã. = --Qur'an 52:12
    The Day they are thrust toward the fire of Hell with a [violent] thrust, [its angels will say], <> Rãnar da zã a tunkuɗa su zuwa wutar Jahannama, tunkuɗãwa. = --Qur'an 52:13
    "This is the Fire which you used to deny. <> (A ce musu): "Wannan ita ce wutar da kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita." = --Qur'an 52:14
    Then is this magic, or do you not see? <> "To, shin wannan sihiri ne kõ kuwa kũ ne bã ku gani?" = --Qur'an 52:15
    [Enter to] burn therein; then be patient or impatient - it is all the same for you. You are only being recompensed [for] what you used to do." <> "Ku shigẽ ta. To, ku yi haƙuri ko kuma kada ku yi haƙuri, dai dai ne a kanku, kawai anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa." = --Qur'an 52:16
    Indeed, the righteous will be in gardens and pleasure, <> Lalle, mãsu taƙawa, sunã a cikin gidãjen Aljanna da wata ni'ima. = --Qur'an 52:17
    Enjoying what their Lord has given them, and their Lord protected them from the punishment of Hellfire. <> Sunã mãsu jin dãɗi da abin da Ubangijinsu Ya ba su, kuma Ubangijinsu Ya tsãre musu azãbar Jahĩm. = --Qur'an 52:18
    [They will be told], "Eat and drink in satisfaction for what you used to do." <> (A ce musu): "Ku ci, ku sha, da ni'ima, dõmin abin da kuka kasance kunã aikatãwa." = --Qur'an 52:19
    They will be reclining on thrones lined up, and We will marry them to fair women with large, [beautiful] eyes. <> Sunã kishingiɗe a kan karagu waɗanda ke cikin sahu, kuma Muka aurar da su waɗansu mãtã mãsu farin idãnu, mãsu girmansu. = --Qur'an 52:20
    And those who believed and whose descendants followed them in faith - We will join with them their descendants, and We will not deprive them of anything of their deeds. Every person, for what he earned, is retained. <> Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma zũriyarsu suka bĩ su ga ĩmãnin, Mun riskar da zũriyarsu da su, alhãli kuwa bã da Mun rage musu kõme ba daga aikinsu, kõwane mutum jingina ne ga abin da ya sana'anta. = --Qur'an 52:21
    And We will provide them with fruit and meat from whatever they desire. <> Kuma Muka yalwata musu 'ya'yan itãce da nãma irin wanda suke marmari. = --Qur'an 52:22
    They will exchange with one another a cup [of wine] wherein [results] no ill speech or commission of sin. <> Sunã mĩƙa wa jũnansu a cikinta hinjãlan giya, wadda bãbu yãsassar magana a cikinta, kuma bãbu jin nauyin zunubi. = --Qur'an 52:23
    There will circulate among them [servant] boys [especially] for them, as if they were pearls well-protected. <> Kuma waɗansu samãri nã gẽwayãwa a kansu, kamar dai sũ lu'ulu'u ne wanda ke kulle. = --Qur'an 52:24
    And they will approach one another, inquiring of each other. <> Waɗansunsu suka fuskanta zuwa ga waɗansu, sunã tambayar jũna. = --Qur'an 52:25
    They will say, "Indeed, we were previously among our people fearful [of displeasing Allah]. <> Suka ce: "Lalle mũ mun kasance a gabãnin wannan (a dũniya) a cikin iyãlanmu munã jin tsõro." = --Qur'an 52:26
    So Allah conferred favor upon us and protected us from the punishment of the Scorching Fire. <> "To, Allah Yã yi mana kyautar falala, kuma Yã tsare mana azãbar iskar zãfi." = --Qur'an 52:27
    Indeed, we used to supplicate Him before. Indeed, it is He who is the Beneficent, the Merciful." <> "Lalle mũ mun kasance, a gãbanin haka, munã kiran sa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai kyautatãwa, Mai rahama." = --Qur'an 52:28
    So remind [O Muhammad], for you are not, by the favor of your Lord, a soothsayer or a madman. <> To, ka tunãtar kai fa sabõda ni'imar Ubangjinka, bã bõka kake ba, kuma bã mahaukaci ba. = --Qur'an 52:29
    Or do they say [of you], "A poet for whom we await a misfortune of time?" <> Shin zã su ce: "Mawãƙi ne, munã jiran, masĩfun mutuwa game da shĩ"? = --Qur'an 52:30
    Say, "Wait, for indeed I am, with you, among the waiters." <> Ka ce: "Ku yi jira, domin nĩ ma lalle inã a cikin mãsu jira tãre da ku." = --Qur'an 52:31
    Or do their minds command them to [say] this, or are they a transgressing people? <> Shin, hankulansu ne ke umarin su da wannan, kõ kuwa sũ wasu mutãne ne mãsu ƙetare haddi? = --Qur'an 52:32
    Or do they say, "He has made it up"? Rather, they do not believe. <> Shin, cẽwa suke yi: "Shi ne ke ƙãga faɗarsa"? Ã'a ba su dai yi ĩmãni ba. = --Qur'an 52:33
    Then let them produce a statement like it, if they should be truthful. <> Sai su zõ da wani lãbãri mai misãlinsa idan sun kasance sũmãsu gaskiya ne. = --Qur'an 52:34
    Or were they created by nothing, or were they the creators [of themselves]? <> Shin, an halitta su ne bã daga kõme ba, kõ kuwa sũ ne mãsu yin halitta? = --Qur'an 52:35
    Or did they create the heavens and the earth? Rather, they are not certain. <> Shin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ã'a ba su dai yi ĩmãnin yaƙĩni ba. = --Qur'an 52:36
    Or have they the depositories [containing the provision] of your Lord? Or are they the controllers [of them]? <> Shin, taskõkin Ubangijinka, sunã a wurinsu ne? Kõ kuwa sũ ne mãsu rinjãya? = --Qur'an 52:37
    Or have they a stairway [into the heaven] upon which they listen? Then let their listener produce a clear authority. <> Shin, sunã da wani tsãni ne wanda suke (hawa sunã) saurãron (lãbãrin samã) a cikinsa? Sai mai saurarõnsu ya zo da wani dalĩli bayyananne. = --Qur'an 52:38
    Or has He daughters while you have sons? <> Shin, Yanã da 'ya'ya mãtã ne kuma kũ, kunã da ɗiya maza ne? = --Qur'an 52:39
    Or do you, [O Muhammad], ask of them a payment, so they are by debt burdened down? <> Shin, kanã tambayar su wata ijãra ne, sabõda haka suka zama mãsu jin nauyin biyan tãrar? = --Qur'an 52:40
    Or have they [knowledge of] the unseen, so they write [it] down? <> Shin, a wurinsu akwai ilmin gaibi, sabõda haka sunã rubũtãwa? = --Qur'an 52:41
    Or do they intend a plan? But those who disbelieve - they are the object of a plan. <> Shin, sunã nufin wani kaidi ne? To, waɗanda suka kãfirta sũ ne waɗanda ake yi wa kaidi. = --Qur'an 52:42
    Or have they a deity other than Allah? Exalted is Allah above whatever they associate with Him. <> Shin, sunã da wani abin bautãwa ne wanda bã Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke yi na shirki! = --Qur'an 52:43
    And if they were to see a fragment from the sky falling, they would say, "[It is merely] clouds heaped up." <> Kuma idan sun ga wani ɓaɓɓake daga samã yãnã fãɗuwa, sai su ce wani girgije ne, mai hauhawar jũna. = --Qur'an 52:44
    So leave them until they meet their Day in which they will be struck insensible - <> To, ka bar su, sai sun haɗu da yinin nan da za a sũmar da su a cikinsa. = --Qur'an 52:45
    The Day their plan will not avail them at all, nor will they be helped. <> Rãnar da kaidinsu bã ya wadãtar masu da kõme, kuma bã a taimakon su. = --Qur'an 52:46
    And indeed, for those who have wronged is a punishment before that, but most of them do not know. <> Kuma lalle, waɗannan da suka yi zãluncin, sunã da azãba (a nan dũniya) banda waccan, kuma mafi yawansu ba su sani ba. = --Qur'an 52:47
    And be patient, [O Muhammad], for the decision of your Lord, for indeed, you are in Our eyes. And exalt [Allah] with praise of your Lord when you arise. <> Sai ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kanã idãnunMu, kuma ka tsarkake Ubangijinka da (tasbĩhi) game da gõde Masa a lõkacin da kake tãshi tsaye (dõmin salla kõ wani abu). = --Qur'an 52:48
    And in a part of the night exalt Him and after [the setting of] the stars. <> Kuma daga dare, sai ka tsarkake Shi (da tasbĩhin) dalõkacin jũyãwar taurãri. = --Qur'an 52:49
    By the star when it descends, <> Inã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku. = --Qur'an 53:1
    Your companion [Muhammad] has not strayed, nor has he erred, <> Ma'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba. = --Qur'an 53:2
    Nor does he speak from [his own] inclination. <> Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa. = --Qur'an 53:3
    It is not but a revelation revealed, <> (Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa. = --Qur'an 53:4
    Taught to him by one intense in strength - <> (Malã'ika) mai tsananin ƙarfi ya sanar da shi. = --Qur'an 53:5
    One of soundness. And he rose to [his] true form <> Ma'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita. = --Qur'an 53:6
    While he was in the higher [part of the] horizon. <> Alhãli kuwa yanã a sararin samã mafi aukaka. = --Qur'an 53:7
    Then he approached and descended <> Sa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa. = --Qur'an 53:8
    And was at a distance of two bow lengths or nearer. <> Har ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa. = --Qur'an 53:9
    And he revealed to His Servant what he revealed. <> Sa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa). = --Qur'an 53:10
    The heart did not lie [about] what it saw. <> Zũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba. = --Qur'an 53:11
    So will you dispute with him over what he saw? <> Shin, zã ku yi masa musu a kan abin da yake gani? = --Qur'an 53:12
    And he certainly saw him in another descent <> Kuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa. = --Qur'an 53:13
    At the Lote Tree of the Utmost Boundary - <> A wurin da magaryar tuƙẽwa take. = --Qur'an 53:14
    Near it is the Garden of Refuge - <> A inda taken, nan Aljannar makoma take. = --Qur'an 53:15
    When there covered the Lote Tree that which covered [it]. <> Lõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta. = --Qur'an 53:16
    The sight [of the Prophet] did not swerve, nor did it transgress [its limit]. <> Ganinsa bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba. = --Qur'an 53:17
    He certainly saw of the greatest signs of his Lord. <> Lalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma daga ãyõyin Ubangijinsa. = --Qur'an 53:18
    So have you considered al-Lat and al-'Uzza? <> Shin, kun ga Lãta da uzza? = --Qur'an 53:19
    And Manat, the third - the other one? <> Da (wani gunki wai shi) Manãta, na ukunsu? = --Qur'an 53:20
    Is the male for you and for Him the female? <> Ashe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ (Allah) kuma da ɗiya mace? = --Qur'an 53:21
    That, then, is an unjust division. <> Wannan fa ya zama rabo naƙasasshe. = --Qur'an 53:22
    They are not but [mere] names you have named them - you and your forefathers - for which Allah has sent down no authority. They follow not except assumption and what [their] souls desire, and there has already come to them from their Lord guidance. <> Waɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kãfirai) bã su biyar kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kõma wa zaton). = --Qur'an 53:23
    Or is there for man whatever he wishes? <> Ko (an fai cẽwa) mutum zai sãmi abin da yake gũri? = --Qur'an 53:24
    Rather, to Allah belongs the Hereafter and the first [life]. <> To, Lãhira da dũniya na Allah kawai ne (wanda ya nẽme su daga wani, yã yi kuskure). = --Qur'an 53:25
    And how many angels there are in the heavens whose intercession will not avail at all except [only] after Allah has permitted [it] to whom He wills and approves. <> Akwai malã'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bã ya wadãtar da kõme fãce bãyan Allah Yã yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda. = --Qur'an 53:26
    Indeed, those who do not believe in the Hereafter name the angels female names, <> Lalle waɗannan da bã su yin ĩmãni da Lãhira, haƙĩƙa sunã kiran malã'iku da sũnan mace. = --Qur'an 53:27
    And they have thereof no knowledge. They follow not except assumption, and indeed, assumption avails not against the truth at all. <> Kuma bã su da wani ilmi game da shi, bã su bin kõme fãce zato alhãli kuwa lalle zato bã ya amfãnar da kõme daga gaskiya. = --Qur'an 53:28
    So turn away from whoever turns his back on Our message and desires not except the worldly life. <> Sabõda haka sai ka kau da kai daga wanda ya jũya bãya daga ambatonMu kuma bai yi nufin kõme ba fãce rãyuwar kusa (dũniya). = --Qur'an 53:29
    That is their sum of knowledge. Indeed, your Lord is most knowing of who strays from His way, and He is most knowing of who is guided. <> Wannan ita ce iyãkar abin da suke iya kai gare shi na ilmi. lalle Ubangijinka Shĩ ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga wanda ya nẽmi shiriya. = --Qur'an 53:30
    And to Allah belongs whatever is in the heavens and whatever is in the earth - that He may recompense those who do evil with [the penalty of] what they have done and recompense those who do good with the best [reward] - <> Kuma abin da ke cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã na Allah kawai ne, dõmin Yã sãka wa waɗanda suka mũnana da abin da suka aikata, kuma Ya sãka wa waɗanda suki kyautata da sakamakon da ya fi kyau. = --Qur'an 53:31
    Those who avoid the major sins and immoralities, only [committing] slight ones. Indeed, your Lord is vast in forgiveness. He was most knowing of you when He produced you from the earth and when you were fetuses in the wombs of your mothers. So do not claim yourselves to be pure; He is most knowing of who fears Him. <> Waɗanda ke nĩsantar manyan zunubai da abũbuwan alfãsha, fãce ƙanãnan laifuffuka, lalle Ubangijinka Mai yalwatattar gãfara ne, Shĩ ne Ya fi sani ga abinda ke gare ku a lõkacin da Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma a lõkacin da kuke tãyuna a cikin cikannan uwãyenku. Sabõda haka, kada ku tsarkake kanku, Shĩ ne Mafi sani ga wanda ya yi taƙawa. = --Qur'an 53:32
    Have you seen the one who turned away <> Shin, ka ga wannan da ya jũya baya? = --Qur'an 53:33
    And gave a little and [then] refrained? <> Ya yi kyauta kaɗan, kuma ya yi rowa? = --Qur'an 53:34
    Does he have knowledge of the unseen, so he sees? <> Shin, akwai ilmin gaibi a wurinsa, Sabõda haka yanã ganin gaibin? = --Qur'an 53:35
    Or has he not been informed of what was in the scriptures of Moses <> Ko kuwa ba a ba shi lãbãri ba ga abin da yake a cikin Littafan Mũsã? = --Qur'an 53:36
    And [of] Abraham, who fulfilled [his obligations] - <> Da Ibrãhĩm wanda ya cika alkawari? = --Qur'an 53:37
    That no bearer of burdens will bear the burden of another <> Cẽwa wani rai mai kãyan laifi bã ya ɗaukar kãyan laifin wani. = --Qur'an 53:38
    And that there is not for man except that [good] for which he strives <> Kuma mutum bã shi da kõme fãce abin da ya aikata. = --Qur'an 53:39
    And that his effort is going to be seen - <> Kuma lalle, aikinsa zã a gan shi. = --Qur'an 53:40
    Then he will be recompensed for it with the fullest recompense <> Sa'an nan a sãka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni? = --Qur'an 53:41
    And that to your Lord is the finality <> Kuma lalle, makõmar zuwa Ubangijinka kawai take? = --Qur'an 53:42
    And that it is He who makes [one] laugh and weep <> Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kũka. = --Qur'an 53:43
    And that it is He who causes death and gives life <> Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya kashe, kuma Ya rãyar. = --Qur'an 53:44
    And that He creates the two mates - the male and female - <> Kuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace. = --Qur'an 53:45
    From a sperm-drop when it is emitted <> Daga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa. = --Qur'an 53:46
    And that [incumbent] upon Him is the next creation <> Kuma a kansa ne ƙãga halitta ta biyu take. = --Qur'an 53:47
    And that it is He who enriches and suffices <> Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar. = --Qur'an 53:48
    And that it is He who is the Lord of Sirius <> Kuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira. = --Qur'an 53:49
    And that He destroyed the first [people of] 'Aad <> Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko. = --Qur'an 53:50
    And Thamud - and He did not spare [them] - <> Da Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba. = --Qur'an 53:51
    And the people of Noah before. Indeed, it was they who were [even] more unjust and oppressing. <> Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi girman kai. = --Qur'an 53:52
    And the overturned towns He hurled down <> Da waɗanda aka birkice ƙasarsu, Ya kãyar da su. = --Qur'an 53:53
    And covered them by that which He covered. <> Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su. = --Qur'an 53:54
    Then which of the favors of your Lord do you doubt? <> To, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake yin shakka? = --Qur'an 53:55
    This [Prophet] is a warner like the former warners. <> wannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko. = --Qur'an 53:56
    The Approaching Day has approached. <> Makusanciya fa, tã yi kusa. = --Qur'an 53:57
    Of it, [from those] besides Allah, there is no remover. <> Bãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta. = --Qur'an 53:58
    Then at this statement do you wonder? <> Shin, kuma daga wannan lãbãri kuke mãmãki? = --Qur'an 53:59
    And you laugh and do not weep <> Kuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka? = --Qur'an 53:60
    While you are proudly sporting? <> Alhãli kunã mãsu wãsã? = --Qur'an 53:61
    So prostrate to Allah and worship [Him]. <> To, ku yi tawãli'u ga Allah, kuma ku bauta (masa). = --Qur'an 53:62
    The Hour has come near, and the moon has split [in two]. <> Sã'a ta yi kusa, kuma wata ya tsãge. = --Qur'an 54:1
    And if they see a miracle, they turn away and say, "Passing magic." <> Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa!" = --Qur'an 54:2
    And they denied and followed their inclinations. But for every matter is a [time of] settlement. <> Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi. = --Qur'an 54:3
    And there has already come to them of information that in which there is deterrence - <> Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu. = --Qur'an 54:4
    Extensive wisdom - but warning does not avail [them]. <> Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni. = --Qur'an 54:5
    So leave them, [O Muhammad]. The Day the Caller calls to something forbidding, <> Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama. = --Qur'an 54:6
    Their eyes humbled, they will emerge from the graves as if they were locusts spreading, <> ¡asƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse. = --Qur'an 54:7
    Racing ahead toward the Caller. The disbelievers will say, "This is a difficult Day." <> Sunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa, "Wannan yini ne mai wuya!" = --Qur'an 54:8
    The people of Noah denied before them, and they denied Our servant and said, "A madman," and he was repelled. <> Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata BawanMu, kuma suka ce: "Shi mahaukaci ne." Kuma aka tsãwace shi. = --Qur'an 54:9
    So he invoked his Lord, "Indeed, I am overpowered, so help." <> Sabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), "Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako." = --Qur'an 54:10
    Then We opened the gates of the heaven with rain pouring down <> Sai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba. = --Qur'an 54:11
    And caused the earth to burst with springs, and the waters met for a matter already predestined. <> Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umurni da aka riga aka ƙaddara shi. = --Qur'an 54:12
    And We carried him on a [construction of] planks and nails, <> Kuma Muka ɗauke Nũhu a kan (jirgi) na alluna da ƙũsõshi. = --Qur'an 54:13
    Sailing under Our observation as reward for he who had been denied. <> Tanã gudãna, a kan idãnunMu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin. = --Qur'an 54:14
    And We left it as a sign, so is there any who will remember? <> Kuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni = --Qur'an 54:15
    And how [severe] were My punishment and warning. <> To, yãyã azãbãTa take da gargaɗiNa? = --Qur'an 54:16
    And We have certainly made the Qur'an easy for remembrance, so is there any who will remember? <> Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa? = --Qur'an 54:17
    'Aad denied; and how [severe] were My punishment and warning. <> Ãdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗiNa? = --Qur'an 54:18
    Indeed, We sent upon them a screaming wind on a day of continuous misfortune, <> Lalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgẽwa. = --Qur'an 54:19
    Extracting the people as if they were trunks of palm trees uprooted. <> Tanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne. = --Qur'an 54:20
    And how [severe] were My punishment and warning. <> To, yãya azãbãTa take da gargaɗiNa? = --Qur'an 54:21
    And We have certainly made the Qur'an easy for remembrance, so is there any who will remember? <> Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa? = --Qur'an 54:22
    Thamud denied the warning <> Samũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin. = --Qur'an 54:23
    And said, "Is it one human being among us that we should follow? Indeed, we would then be in error and madness. <> Sai suka ce: "Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã. = --Qur'an 54:24
    Has the message been sent down upon him from among us? Rather, he is an insolent liar." <> "Shin, an jẽfa masa Manzancin ne, a tsakãninmu? Ã'a, shĩ dai gawurtaccen maƙaryaci ne mai girman kai!" = --Qur'an 54:25
    They will know tomorrow who is the insolent liar. <> Zã su sani a gõbe, wãne ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan? = --Qur'an 54:26
    Indeed, We are sending the she-camel as trial for them, so watch them and be patient. <> Lalle Mũ, mãsu aikãwa da rãƙumar ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da kallo, kuma ka yi haƙuri. = --Qur'an 54:27
    And inform them that the water is shared between them, each [day of] drink attended [by turn]. <> Kuma ka bã su lãbãri cẽwa ruwa rababbe ne a tsakãninsu (da rãƙumar), kõwane sha, mai shi yanã halartar sa. = --Qur'an 54:28
    But they called their companion, and he dared and hamstrung [her]. <> Sai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa'an nan ya sõke ta, = --Qur'an 54:29
    And how [severe] were My punishment and warning. <> To, yãya azãbaTa take da gargaɗiNa? = --Qur'an 54:30
    Indeed, We sent upon them one blast from the sky, and they became like the dry twig fragments of an [animal] pen. <> Lalle Mũ, Mun aika tsãwa guda a kansu, sai suka kasance kamar yãyin mai shinge. = --Qur'an 54:31
    And We have certainly made the Qur'an easy for remembrance, so is there any who will remember? <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa? = --Qur'an 54:32
    The people of Lot denied the warning. <> Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi. = --Qur'an 54:33
    Indeed, We sent upon them a storm of stones, except the family of Lot - We saved them before dawn <> Lalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, fãce mabiyan Lũɗu, Mun tsirar da su a lõkacin asuba. = --Qur'an 54:34
    As favor from us. Thus do We reward he who is grateful. <> Sabõda wata ni'ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke sãka wa wanda ya gõde. = --Qur'an 54:35
    And he had already warned them of Our assault, but they disputed the warning. <> Kuma lalle, haƙĩƙa, ya yi musu gargaɗin damƙarMu, sai suka yi musu game da gargaɗin. = --Qur'an 54:36
    And they had demanded from him his guests, but We obliterated their eyes, [saying], "Taste My punishment and warning." <> Kuma lalle haƙĩƙa, su, sun nẽme shi ta wajen bãƙinsa, sai Muka shãfe idãnunsu. "To, ku ɗanɗani azãbaTa da gargaɗĩNa." = --Qur'an 54:37
    And there came upon them by morning an abiding punishment. <> Kuma lalle, haƙĩƙa, wata azãba matabbaciya tã wãye musu gari da yãƙi, tun da sãfe. = --Qur'an 54:38
    So taste My punishment and warning. <> To, ku ɗanɗani azãbãTa da gargaɗĩNa. = --Qur'an 54:39
    And We have certainly made the Qur'an easy for remembrance, so is there any who will remember? <> Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur, ani dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa? = --Qur'an 54:40
    And there certainly came to the people of Pharaoh warning. <> Kuma lalle, haƙĩƙa, gargaɗin ya jẽ wa mabiyan Fir'auna. = --Qur'an 54:41
    They denied Our signs, all of them, so We seized them with a seizure of one Exalted in Might and Perfect in Ability. <> Sun ƙaryata game da ãyõyinMu, dukansu sai Muka kãma su, irin kãmun Mabuwãyi, Mai ĩkon yi. = --Qur'an 54:42
    Are your disbelievers better than those [former ones], or have you immunity in the scripture? <> Shin, kãfiranku ne mafi alhẽri daga waɗancan, ko kuwa kunã da wata barã'a a cikin littattafai? = --Qur'an 54:43
    Or do they say, "We are an assembly supporting [each other]"? <> Kõ zã su ce: "Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara?" = --Qur'an 54:44
    [Their] assembly will be defeated, and they will turn their backs [in retreat]. <> Zã a karya tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu. = --Qur'an 54:45
    But the Hour is their appointment [for due punishment], and the Hour is more disastrous and more bitter. <> Ã'a, Sã'a ita cẽ lõkacin wa'adinsu, kuma Sã'ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta fiɗãci. = --Qur'an 54:46
    Indeed, the criminals are in error and madness. <> Lalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka. = --Qur'an 54:47
    The Day they are dragged into the Fire on their faces [it will be said], "Taste the touch of Saqar." <> Rãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. "Ku ɗanɗani shãfar wutar Saƙar." = --Qur'an 54:48
    Indeed, all things We created with predestination. <> Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri. = --Qur'an 54:49
    And Our command is but one, like a glance of the eye. <> Kuma umurninMu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido. = --Qur'an 54:50
    And We have already destroyed your kinds, so is there any who will remember? <> Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni? = --Qur'an 54:51
    And everything they did is in written records. <> Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai. = --Qur'an 54:52
    And every small and great [thing] is inscribed. <> Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne. = --Qur'an 54:53
    Indeed, the righteous will be among gardens and rivers, <> Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna. = --Qur'an 54:54
    In a seat of honor near a Sovereign, Perfect in Ability. <> A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa. = --Qur'an 54:55
    The Most Merciful <> (Allah) Mai rahama. = --Qur'an 55:1
    Taught the Qur'an, <> Yã sanar da Alƙur'ani. = --Qur'an 55:2
    Created man, <> Yã halitta mutum. = --Qur'an 55:3
    [And] taught him eloquence. <> Yã sanar da shi bayãni (magana). = --Qur'an 55:4
    The sun and the moon [move] by precise calculation, <> Rãnã da watã a kan lissãfi suke. = --Qur'an 55:5
    And the stars and trees prostrate. <> Kuma tsirrai mãsu yãɗo da itãce sunã tawãlu'i. = --Qur'an 55:6
    And the heaven He raised and imposed the balance <> Kuma samã Ya ɗaukaka ta, Kuma Yã aza sikẽli. = --Qur'an 55:7
    That you not transgress within the balance. <> Dõmin kada ku karkatar da sikẽlin. = --Qur'an 55:8
    And establish weight in justice and do not make deficient the balance. <> Kuma ku daidaita awo da ãdalci, kuma kada ku rage sikẽlin. = --Qur'an 55:9
    And the earth He laid [out] for the creatures. <> Kuma ƙasã Yã aza ta dõmin tãlikai. = --Qur'an 55:10
    Therein is fruit and palm trees having sheaths [of dates] <> A cikinta akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno mai kwasfa. = --Qur'an 55:11
    And grain having husks and scented plants. <> Da ƙwãya mai sõshiya da ƙamshi. = --Qur'an 55:12
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangjinku kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:13
    He created man from clay like [that of] pottery. <> Yã halitta mutum daga ƙẽkasasshen yumɓu kumar kasko. = --Qur'an 55:14
    And He created the jinn from a smokeless flame of fire. <> Kuma ya halitta aljani daga bira daga wutã. = --Qur'an 55:15
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:16
    [He is] Lord of the two sunrises and Lord of the two sunsets. <> Ubangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã. = --Qur'an 55:17
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:18
    He released the two seas, meeting [side by side]; <> Yã garwaya tẽku biyu (ruwan dãɗi da na zartsi) sunã haɗuwa. = --Qur'an 55:19
    Between them is a barrier [so] neither of them transgresses. <> A tsakãninsu akwai shãmaki, bã za su ƙetare haddi ba. = --Qur'an 55:20
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:21
    From both of them emerge pearl and coral. <> Lu'ulu'u da murjãni na fita daga gare su. = --Qur'an 55:22
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:23
    And to Him belong the ships [with sails] elevated in the sea like mountains. <> Kuma Yanã da manyan jirãge, waɗanda ake ƙãgãwa a cikin tẽku kamar manyan duwãtsu. = --Qur'an 55:24
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:25
    Everyone upon the earth will perish, <> Dukkan wanda ke kanta mai ƙãrẽwa ne. = --Qur'an 55:26
    And there will remain the Face of your Lord, Owner of Majesty and Honor. <> Kuma Fuskarar Ubangijinka, Mai girman Jalala da karimci, ita ce take wanzuwa. = --Qur'an 55:27
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:28
    Whoever is within the heavens and earth asks Him; every day He is bringing about a matter. <> wanda ke a cikin sammai da ƙasã yanã rõƙon Sa (Allah), a kullum Allah na a cikin wani sha'ani. = --Qur'an 55:29
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:30
    We will attend to you, O prominent beings. <> Zã mu ɗauki lõkaci sabõda ku, yã kũ mãsu nauyin halitta biyu! = --Qur'an 55:31
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:32
    O company of jinn and mankind, if you are able to pass beyond the regions of the heavens and the earth, then pass. You will not pass except by authority [from Allah]. <> Ya jama'ar aljannu da mutãne! Idan kunã iya zarcẽwa daga sãsannin sammai da ƙasã to ku zarce. Bã za ku iya zarcẽwaba fãce da wani dalĩli. = --Qur'an 55:33
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:34
    There will be sent upon you a flame of fire and smoke, and you will not defend yourselves. <> Anã sako wani harshe daga wata wutã a kanku, da narkakkiyar tagulla. To, bã zã ku nẽmi taimako ba? = --Qur'an 55:35
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:36
    And when the heaven is split open and becomes rose-colored like oil - <> Sa'an nan idan sama ta tsãge kuma ta zama jã kamar jar fãta. = --Qur'an 55:37
    So which of the favors of your Lord would you deny? - <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:38
    Then on that Day none will be asked about his sin among men or jinn. <> To, a ran nan bã zã a tambayi wani mutum laifinsa ba, kuma haka aljani. = --Qur'an 55:39
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:40
    The criminals will be known by their marks, and they will be seized by the forelocks and the feet. <> zã a iya sanin mãsu laifi da alãmarsu, sabõda haka sai a kãma kwarkaɗarsu da sãwãyensu. = --Qur'an 55:41
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:42
    This is Hell, which the criminals deny. <> Wannan Jahannama ce wadda mãsu laifi ke ƙaryatãwa game da ita. = --Qur'an 55:43
    They will go around between it and scalding water, heated [to the utmost degree]. <> Sunã kẽwaya a tsakaninta da ruwan ɗimi mai tsananin tafasa. = --Qur'an 55:44
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:45
    But for he who has feared the position of his Lord are two gardens - <> Kuma wanda ya ji tsõron tsayãwa a gaba ga Ubangijinsa yanã da Aljanna biyu. = --Qur'an 55:46
    So which of the favors of your Lord would you deny? - <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:47
    Having [spreading] branches. <> Mãsu rassan itãce. = --Qur'an 55:48
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:49
    In both of them are two springs, flowing. <> A cikinsu akwai marẽmari biyu sunã gudãna. = --Qur'an 55:50
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:51
    In both of them are of every fruit, two kinds. <> A cikinsu akwai nau'i biyu daga kõwane 'ya'yan itãcen marmari. = --Qur'an 55:52
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:53
    [They are] reclining on beds whose linings are of silk brocade, and the fruit of the two gardens is hanging low. <> Sunã gincire a kan waɗansu shimfiɗu cikinsu tufãfin alharĩni mai kauri ne kuma nũnannun 'yã'yan itãcen Aljannar biyu kusakusa suke. = --Qur'an 55:54
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:55
    In them are women limiting [their] glances, untouched before them by man or jinni - <> A cikinsu akwai mãtã mãsu taƙaita ganinsu, wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗebe budurcinsu ba kuma haka wani aljani. = --Qur'an 55:56
    So which of the favors of your Lord would you deny? - <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:57
    As if they were rubies and coral. <> Kamar dai su yaƙũtu ne da murjãni. = --Qur'an 55:58
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:59
    Is the reward for good [anything] but good? <> Shin, kyautatãwa nã da wani sakamako? (Ã'aha) fãce kyautatãwa. = --Qur'an 55:60
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:61
    And below them both [in excellence] are two [other] gardens - <> Kuma baicinsu akwai waɗansu gidãjen Aljanna biyu. = --Qur'an 55:62
    So which of the favors of your Lord would you deny? - <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:63
    Dark green [in color]. <> Mãsu duhun inuwa. = --Qur'an 55:64
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:65
    In both of them are two springs, spouting. <> A cikinsu akwai marẽmari biyu masu kwarãrar ruwa. = --Qur'an 55:66
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:67
    In both of them are fruit and palm trees and pomegranates. <> A cikinsu akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno darummãni. = --Qur'an 55:68
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:69
    In them are good and beautiful women - <> A cikinsu, akwai wasu mãtã mãsu kyaun hãlãye, mãsu kyaun halitta. = --Qur'an 55:70
    So which of the favors of your Lord would you deny? - <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:71
    Fair ones reserved in pavilions - <> Mãsu farin idãnu da baƙinsu waɗanda aka tsare a cikin haimõmi. = --Qur'an 55:72
    So which of the favors of your Lord would you deny? - <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:73
    Untouched before them by man or jinni - <> Wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗẽbe budurcinsu ba, kuma haka wani aljani. = --Qur'an 55:74
    So which of the favors of your Lord would you deny? - <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:75
    Reclining on green cushions and beautiful fine carpets. <> Sunã gincire a kan wasu matãsai mãsu kõren launi da katĩfun Abkara kyãwãwa. = --Qur'an 55:76
    So which of the favors of your Lord would you deny? <> To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? = --Qur'an 55:77
    Blessed is the name of your Lord, Owner of Majesty and Honor. <> Sũnan Ubangjinka, Mai girman Jalãla da Karimci, ya tsarkaka. = --Qur'an 55:78
    When the Occurrence occurs, <> Idan mai aukuwa ta auku. = --Qur'an 56:1
    There is, at its occurrence, no denial. <> Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta. = --Qur'an 56:2
    It will bring down [some] and raise up [others]. <> (Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa. = --Qur'an 56:3
    When the earth is shaken with convulsion <> Idan aka girgiza ƙasã girgizwa. = --Qur'an 56:4
    And the mountains are broken down, crumbling <> Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa. = --Qur'an 56:5
    And become dust dispersing. <> Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa. = --Qur'an 56:6
    And you become [of] three kinds: <> Kuma kun kasance nau'i uku. = --Qur'an 56:7
    Then the companions of the right - what are the companions of the right? <> Watau mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma? = --Qur'an 56:8
    And the companions of the left - what are the companions of the left? <> Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu? = --Qur'an 56:9
    And the forerunners, the forerunners - <> Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan, = --Qur'an 56:10
    Those are the ones brought near [to Allah] <> Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar. = --Qur'an 56:11
    In the Gardens of Pleasure, <> A ckin Aljannar ni'ima. = --Qur'an 56:12
    A [large] company of the former peoples <> Jama'a ne daga mutãnen farko. = --Qur'an 56:13
    And a few of the later peoples, <> Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe. = --Qur'an 56:14
    On thrones woven [with ornament], <> (Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙuu. = --Qur'an 56:15
    Reclining on them, facing each other. <> Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna. = --Qur'an 56:16
    There will circulate among them young boys made eternal <> Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu. = --Qur'an 56:17
    With vessels, pitchers and a cup [of wine] from a flowing spring - <> Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga. = --Qur'an 56:18
    No headache will they have therefrom, nor will they be intoxicated - <> Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa. = --Qur'an 56:19
    And fruit of what they select <> Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe. = --Qur'an 56:20
    And the meat of fowl, from whatever they desire. <> Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa. = --Qur'an 56:21
    And [for them are] fair women with large, [beautiful] eyes, <> Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu. = --Qur'an 56:22
    The likenesses of pearls well-protected, <> Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye. = --Qur'an 56:23
    As reward for what they used to do. <> A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa. = --Qur'an 56:24
    They will not hear therein ill speech or commission of sin - <> Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi. = --Qur'an 56:25
    Only a saying: "Peace, peace." <> Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun. = --Qur'an 56:26
    The companions of the right - what are the companions of the right? <> Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma? = --Qur'an 56:27
    [They will be] among lote trees with thorns removed <> (Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya. = --Qur'an 56:28
    And [banana] trees layered [with fruit] <> Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya. = --Qur'an 56:29
    And shade extended <> Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya. = --Qur'an 56:30
    And water poured out <> Da wani ruwa mai gudãna. = --Qur'an 56:31
    And fruit, abundant [and varied], <> Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa. = --Qur'an 56:32
    Neither limited [to season] nor forbidden, <> Bã su yankẽwa kuma bã a hana su. = --Qur'an 56:33
    And [upon] beds raised high. <> Da wasu shimfiɗu maɗaukaka. = --Qur'an 56:34
    Indeed, We have produced the women of Paradise in a [new] creation <> Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa. = --Qur'an 56:35
    And made them virgins, <> Sa'an nan Muka sanya su budurwai. = --Qur'an 56:36
    Devoted [to their husbands] and of equal age, <> Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya. = --Qur'an 56:37
    For the companions of the right [who are] <> Ga mazõwa dãma. = --Qur'an 56:38
    A company of the former peoples <> Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko. = --Qur'an 56:39
    And a company of the later peoples. <> Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe. = --Qur'an 56:40
    And the companions of the left - what are the companions of the left? <> Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu? = --Qur'an 56:41
    [They will be] in scorching fire and scalding water <> Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi. = --Qur'an 56:42
    And a shade of black smoke, <> Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi. = --Qur'an 56:43
    Neither cool nor beneficial. <> Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba. = --Qur'an 56:44
    Indeed they were, before that, indulging in affluence, <> Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi. = --Qur'an 56:45
    And they used to persist in the great violation, <> Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma. = --Qur'an 56:46
    And they used to say, "When we die and become dust and bones, are we indeed to be resurrected? <> Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?" = --Qur'an 56:47
    And our forefathers [as well]?" <> "Shin, kuma da ubanninmu na farko?" = --Qur'an 56:48
    Say, [O Muhammad], "Indeed, the former and the later peoples <> Ka ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe." = --Qur'an 56:49
    Are to be gathered together for the appointment of a known Day." <> "Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne." = --Qur'an 56:50
    Then indeed you, O those astray [who are] deniers, <> "Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!" = --Qur'an 56:51
    Will be eating from trees of zaqqum <> "Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)." = --Qur'an 56:52
    And filling with it your bellies <> "Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta." = --Qur'an 56:53
    And drinking on top of it from scalding water <> "Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi." = --Qur'an 56:54
    And will drink as the drinking of thirsty camels. <> "Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa." = --Qur'an 56:55
    That is their accommodation on the Day of Recompense. <> Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako. = --Qur'an 56:56
    We have created you, so why do you not believe? <> Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba? = --Qur'an 56:57
    Have you seen that which you emit? <> Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi? = --Qur'an 56:58
    Is it you who creates it, or are We the Creator? <> Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa? = --Qur'an 56:59
    We have decreed death among you, and We are not to be outdone <> Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa ba, = --Qur'an 56:60
    In that We will change your likenesses and produce you in that [form] which you do not know. <> A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba. = --Qur'an 56:61
    And you have already known the first creation, so will you not remember? <> Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba? = --Qur'an 56:62
    And have you seen that [seed] which you sow? <> Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa? = --Qur'an 56:63
    Is it you who makes it grow, or are We the grower? <> Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa? = --Qur'an 56:64
    If We willed, We could make it [dry] debris, and you would remain in wonder, <> Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki. = --Qur'an 56:65
    [Saying], "Indeed, we are [now] in debt; <> (Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!" = --Qur'an 56:66
    Rather, we have been deprived." <> "Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!" = --Qur'an 56:67
    And have you seen the water that you drink? <> Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha? = --Qur'an 56:68
    Is it you who brought it down from the clouds, or is it We who bring it down? <> Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa? = --Qur'an 56:69
    If We willed, We could make it bitter, so why are you not grateful? <> Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa? = --Qur'an 56:70
    And have you seen the fire that you ignite? <> Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa? = --Qur'an 56:71
    Is it you who produced its tree, or are We the producer? <> Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa? = --Qur'an 56:72
    We have made it a reminder and provision for the travelers, <> Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji. = --Qur'an 56:73
    So exalt the name of your Lord, the Most Great. <> Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma. = --Qur'an 56:74
    Then I swear by the setting of the stars, <> To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri. = --Qur'an 56:75
    And indeed, it is an oath - if you could know - [most] great. <> Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani. = --Qur'an 56:76
    Indeed, it is a noble Qur'an <> Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja. = --Qur'an 56:77
    In a Register well-protected; <> A cikin wani littafi tsararre. = --Qur'an 56:78
    None touch it except the purified. <> Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake. = --Qur'an 56:79
    [It is] a revelation from the Lord of the worlds. <> Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta. = --Qur'an 56:80
    Then is it to this statement that you are indifferent <> Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa? = --Qur'an 56:81
    And make [the thanks for] your provision that you deny [the Provider]? <> Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)? = --Qur'an 56:82
    Then why, when the soul at death reaches the throat <> To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa). = --Qur'an 56:83
    And you are at that time looking on - <> Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo. = --Qur'an 56:84
    And Our angels are nearer to him than you, but you do not see - <> Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani. = --Qur'an 56:85
    Then why do you not, if you are not to be recompensed, <> To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba? = --Qur'an 56:86
    Bring it back, if you should be truthful? <> Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya. = --Qur'an 56:87
    And if the deceased was of those brought near to Allah, <> To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta, = --Qur'an 56:88
    Then [for him is] rest and bounty and a garden of pleasure. <> Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima. = --Qur'an 56:89
    And if he was of the companions of the right, <> Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma, = --Qur'an 56:90
    Then [the angels will say], "Peace for you; [you are] from the companions of the right." <> Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma. = --Qur'an 56:91
    But if he was of the deniers [who were] astray, <> Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun, = --Qur'an 56:92
    Then [for him is] accommodation of scalding water <> Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi. = --Qur'an 56:93
    And burning in Hellfire <> Da ƙõnuwa da Jahĩm, = --Qur'an 56:94
    Indeed, this is the true certainty, <> Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni. = --Qur'an 56:95
    So exalt the name of your Lord, the Most Great. <> Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangijinka, Mai karimci. = --Qur'an 56:96
    Whatever is in the heavens and earth exalts Allah, and He is the Exalted in Might, the Wise. <> Abin da ke cikin sammai da ƙasa yã yi tasbĩhi ga Allah. Kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima. = --Qur'an 57:1
    His is the dominion of the heavens and earth. He gives life and causes death, and He is over all things competent. <> Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa: Yanã rãyarwa kuma Yanã kashẽwa, kuma Shĩ Mai ikon yi ne a kan kõme. = --Qur'an 57:2
    He is the First and the Last, the Ascendant and the Intimate, and He is, of all things, Knowing. <> Shĩ ne Na farko, Na ƙarshe, Bayyananne, Bõyayye, kuma Shĩ Masani ne ga dukkan kõme. = --Qur'an 57:3
    It is He who created the heavens and earth in six days and then established Himself above the Throne. He knows what penetrates into the earth and what emerges from it and what descends from the heaven and what ascends therein; and He is with you wherever you are. And Allah, of what you do, is Seeing. <> Shĩ ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin wasu kwãnuka shida, sa'an nan Ya daidaitu a kan Al'arshi, Yanã sanin abin da ke shiga cikin ƙasa da abin da ke fita daga gare ta, da abin da ke sauka daga sama da abin da ke hawa cikinta, kuma Shĩ yanã tareda ku duk inda kuka kasance. Kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa. = --Qur'an 57:4
    His is the dominion of the heavens and earth. And to Allah are returned [all] matters. <> Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma zuwa gare Shĩ (Allah) kawai ake mayar da al'amura. = --Qur'an 57:5
    He causes the night to enter the day and causes the day to enter the night, and he is Knowing of that within the breasts. <> Yanã shigar da dare a cikin yini, kuma Yanã shigar da yini a cikin dare, kuma Shi Masani ne ga abin da yake a cikin ƙirãza. = --Qur'an 57:6
    Believe in Allah and His Messenger and spend out of that in which He has made you successors. For those who have believed among you and spent, there will be a great reward. <> Ku yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, kuma ku ciyar daga abin da Allah Ya wakilta ku a cikinsa (na dũkiya). To, waɗannan da suka yi ĩmãni daga cikinku, kuma suka ciyar, sunã da wani sakamako mai girma. = --Qur'an 57:7
    And why do you not believe in Allah while the Messenger invites you to believe in your Lord and He has taken your covenant, if you should [truly] be believers? <> kuma me ya same ku, bã zã ku yi ĩmãni ba da Allah, alhãli kuwa manzonSa na kiran ku dõmin ku yi ĩmãni da Ubangijinku, kuma lalle Allah Ya karɓi alkawarinku (cẽwa zã ku bauta Masa)? (Ku bauta Masa) idan kun kasance mãsu ĩmãni. = --Qur'an 57:8
    It is He who sends down upon His Servant [Muhammad] verses of clear evidence that He may bring you out from darknesses into the light. And indeed, Allah is to you Kind and Merciful. <> Shĩ ne wanda ke sassaukar da ãyõyi bayyanannu ga BãwanSa, dõmin Ya fitar da ku daga duffai zuwa ga haske, kuma lalle Allah haƙĩƙa Mai tausayi ne gare ku, Mai jin ƙai. = --Qur'an 57:9
    And why do you not spend in the cause of Allah while to Allah belongs the heritage of the heavens and the earth? Not equal among you are those who spent before the conquest [of Makkah] and fought [and those who did so after it]. Those are greater in degree than they who spent afterwards and fought. But to all Allah has promised the best [reward]. And Allah, with what you do, is Acquainted. <> Kuma me ya sãme ku, bã zã ku ciyar ba dõmin ɗaukaka kalmar Allah, alhãli kuwa gãdon sammai da ƙasã na Allah ne? Wanda ya ciyar a gabãnin cin nasara, kuma ya yi yãƙi daga cikinku, bã ya zama daidai (da wanda bai yi haka ba). waɗancan ne mafĩfĩta girman daraja bisa ga waɗanda suka ciyar daga bãya kuma suka yi yãƙi. Kuma dukansu Allah Ya yi musu wa'adi da (sakamako) mai kyau, kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa. = --Qur'an 57:10
    Who is it that would loan Allah a goodly loan so He will multiply it for him and he will have a noble reward? <> Wãne ne wanda zai ranta wa Allah rance mai kyau dõmin Allah Ya ninka masa shi (a dũniya) kuma Yanã da wani sakamako na karimci (a Lãhira)? = --Qur'an 57:11
    On the Day you see the believing men and believing women, their light proceeding before them and on their right, [it will be said], "Your good tidings today are [of] gardens beneath which rivers flow, wherein you will abide eternally." That is what is the great attainment. <> Rãnar da zã ka ga mũminai maza da mũminai mãtã haskensu nã tafiya a gaba gare su, da kuma dãma gare su. (Anã ce musu) "Bushãrarku a yau, ita ce gidajen Aljanna." Ruwa na gudãna daga ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu. Wannan, shĩ ne babban rabo mai girma. = --Qur'an 57:12
    On the [same] Day the hypocrite men and hypocrite women will say to those who believed, "Wait for us that we may acquire some of your light." It will be said, "Go back behind you and seek light." And a wall will be placed between them with a door, its interior containing mercy, but on the outside of it is torment. <> Rãnar da munafikai maza da munãfikai mãtã ke cẽwa waɗanda suka yi ĩmãni: "Ku dũbẽ mu, mu yi makãmashi daga haskenku!" A ce (musu): "Ku kõma a bãyanku, dõmin ku nẽmo wani haske." Sai a danne a tsakãninsu da wani gãru yanã da wani ƙyaure, a cikinsa nan rahama take, kuma a bãyansa daga wajensa azaba take. = --Qur'an 57:13
    The hypocrites will call to the believers, "Were we not with you?" They will say, "Yes, but you afflicted yourselves and awaited [misfortune for us] and doubted, and wishful thinking deluded you until there came the command of Allah. And the Deceiver deceived you concerning Allah. <> Sunã kiran su, "Ashe, bã tãre muke da ku ba?" Su ce: "Ĩ, amma kũ, kun fitini kanku, kuma kun yi jiran wata masĩfa, kuma kunyi shakka, kuma waɗansu gũrace-gũrace sun rũɗe ku, har umurnin Allah ya jẽ muku, kumamarũɗi ya rũɗe ku game da Allah." = --Qur'an 57:14
    So today no ransom will be taken from you or from those who disbelieved. Your refuge is the Fire. It is most worthy of you, and wretched is the destination. <> "To, a yau bã zã a karɓi fansa daga gare ku ba. Kuma bã zã a karɓa daga waɗanda suka kãfirta ba. Makõmarku wutã ce, ita ce mai dacẽwa da ku, kuma makõmarku ɗin nan tã mũnana." = --Qur'an 57:15
    Has the time not come for those who have believed that their hearts should become humbly submissive at the remembrance of Allah and what has come down of the truth? And let them not be like those who were given the Scripture before, and a long period passed over them, so their hearts hardened; and many of them are defiantly disobedient. <> Shin, lõkaci bai yi ba ga wa ɗanda suka yi ĩmãnĩ zukãtansu su yi tawãlu'i ga ambaton Allah da abin da ya sauka daga gaskiya? Kada su kasance kamar waɗanda aka bai wa littãfi a gabãnin haka, sai zãmani ya yi tsawo a kansu, sabõda haka zukãtansu suka ƙẽƙashe, kuma masu yawa daga cikinsu fãsiƙai ne. = --Qur'an 57:16
    Know that Allah gives life to the earth after its lifelessness. We have made clear to you the signs; perhaps you will understand. <> Ku sani cẽwa Allah Yanã rãyar da ƙasã a bãyan mutuwarta. Lalle Mun bayyanamuku ãyõyi da fatan zã ku yi hankali. = --Qur'an 57:17
    Indeed, the men who practice charity and the women who practice charity and [they who] have loaned Allah a goodly loan - it will be multiplied for them, and they will have a noble reward. <> Lalle mãsu gaskatãwa maza da mãsu gaskatãwa mãtã, kuma suka ranta wa Allah rance mai kyau, anã riɓanya musu, kuma suna da wani sakamako na karimci. = --Qur'an 57:18
    And those who have believed in Allah and His messengers - those are [in the ranks of] the supporters of truth and the martyrs, with their Lord. For them is their reward and their light. But those who have disbelieved and denied Our verses - those are the companions of Hellfire. <> Kuma waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da MazanninSa waɗannan sũ ne kamãlar gaskatãwa kuma su ne mãsu shahãda awurin Ubangjinsu. sunã da sakamakonsu da haskensu. waɗanda suka kafirta kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu, waɗannan su ne'yan Jahĩm. = --Qur'an 57:19
    Know that the life of this world is but amusement and diversion and adornment and boasting to one another and competition in increase of wealth and children - like the example of a rain whose [resulting] plant growth pleases the tillers; then it dries and you see it turned yellow; then it becomes [scattered] debris. And in the Hereafter is severe punishment and forgiveness from Allah and approval. And what is the worldly life except the enjoyment of delusion. <> Ku sani cẽwa rãyuwar dũniya wãsã ɗai ce da shagala da ƙawa da alafahri a tsakãninku da gãsar wadãta ta dũkiya da ɗiya, kamar misãlin shũka wadda yabanyarta ta bãyar da sha'awa ga manõma, sa'an nan ta ƙẽƙashe, har ka ganta tã zama rawaya sa'an nan ta kõma rauno. Kuma, alãmra akwai azãba mai tsanani da gãfara daga Allah da yarda. Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba fãce ɗan jin dãɗin rũɗi kawai. = --Qur'an 57:20
    Race toward forgiveness from your Lord and a Garden whose width is like the width of the heavens and earth, prepared for those who believed in Allah and His messengers. That is the bounty of Allah which He gives to whom He wills, and Allah is the possessor of great bounty. <> Ku yi tsẽre zuwa ga (nẽman) gãfara daga Ubangjinku, da Aljanna fãɗinta kamar fãɗin samã da ƙasã ne, an yi tattalinta dõmin waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzanninSa. Wannan falalar Allah ce, Yanã bãyar da ita ga wanda Ya so. Kuma Allah Mai falala ne Mai girma. = --Qur'an 57:21
    No disaster strikes upon the earth or among yourselves except that it is in a register before We bring it into being - indeed that, for Allah, is easy - <> Wata masifa bã zã ta auku ba a cikin ƙasã kõ a cikin rayukanku fãce tanã a cikin littãfi a gabãnin Mu halitta ta. Lalle wannan, ga Allah, mai sauƙi ne. = --Qur'an 57:22
    In order that you not despair over what has eluded you and not exult [in pride] over what He has given you. And Allah does not like everyone self-deluded and boastful - <> Dõmin kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, kuma kada ku yi mumar alfahari da abin da Ya bã ku. Kuma Allah bã Ya son dukkan mai tãƙama, mai alfahari. = --Qur'an 57:23
    [Those] who are stingy and enjoin upon people stinginess. And whoever turns away - then indeed, Allah is the Free of need, the Praiseworthy. <> Watau, waɗanda ke yin rõwa, kuma sunã umumin mutãne da yin rõwa. Kuma wanda ya jũya bãya, to, lalle Allah, Shĩ ne kaɗai Mawadãci, Gõdadde. = --Qur'an 57:24
    We have already sent Our messengers with clear evidences and sent down with them the Scripture and the balance that the people may maintain [their affairs] in justice. And We sent down iron, wherein is great military might and benefits for the people, and so that Allah may make evident those who support Him and His messengers unseen. Indeed, Allah is Powerful and Exalted in Might. <> Haƙĩƙa, lalle Mun aiko ManzanninMu da hujjõji bayyanannu, kuma Muka saukar da Littãfi da sikẽli tãre da su dõmin mutãne su tsayu da ãdalci, kuma Mun saukar da baƙin ƙarfe, a cikinsa akwai cutarwa mai tsanani da amfãni ga mutãne, kuma dõmin Allah Ya san mai taimakonSa da ManzanninSa a fake. Lalle ne Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi. = --Qur'an 57:25
    And We have already sent Noah and Abraham and placed in their descendants prophethood and scripture; and among them is he who is guided, but many of them are defiantly disobedient. <> Kuma haƙĩƙa, lalle, Mun aiki Nũhu da Ibrahĩm, kuma Muka sanya Annabci da Littĩfi a cikin zuriyarsu; daga cikinsu akwai mai nẽman shiryuwa, kuma mãsu yawa daga cikinsu fasiƙai ne. = --Qur'an 57:26
    Then We sent following their footsteps Our messengers and followed [them] with Jesus, the son of Mary, and gave him the Gospel. And We placed in the hearts of those who followed him compassion and mercy and monasticism, which they innovated; We did not prescribe it for them except [that they did so] seeking the approval of Allah. But they did not observe it with due observance. So We gave the ones who believed among them their reward, but many of them are defiantly disobedient. <> Sa'an nan Muka biyar a bãyansu da ManzanninMu; kuma Muka biyar da ĩsã ɗan Maryama, kuma Muka ba shi Linjila kuma Muka sanya tausayi da rahama a cikin zukãtan waɗanda suka bĩ shi, da ruhbãnanci wanda suka ƙãga, shi, ba Mu rubũta shi ba a kansu, fãce dai (Mun rubũta musu nẽman yardar Allah, sa'an nan ba su tsare shi haƙƙin tsarẽwarsa ba, sabõda haka Muka bai wa waɗanda suka yi ĩmãni daga cikinsu sakamakonsu kuma mãsu yawa daga cikinsu fãsiƙai ne. = --Qur'an 57:27
    O you who have believed, fear Allah and believe in His Messenger; He will [then] give you a double portion of His mercy and make for you a light by which you will walk and forgive you; and Allah is Forgiving and Merciful. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, ku yi ĩmãni da ManzonSa Ya bã ku rabo biyu daga rahamarSa, kuma Ya sanya muku wani haske wanda kuke yin tafiya da shi, kuma Ya gãfarta muku. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai rahama. = --Qur'an 57:28
    [This is] so that the People of the Scripture may know that they are not able [to obtain] anything from the bounty of Allah and that [all] bounty is in the hand of Allah; He gives it to whom He wills. And Allah is the possessor of great bounty. <> Dõmin kada mutãnen Littãfi su san cẽwa lalle bã su da ikon yi ga kõme na falalar Allah, kuma ita falalar ga hannun Allah kawai take, Yanã bãyar da ita ga wanda Ya so (wannan jãhilci yã hana su ĩmani). Kuma Al1ah Mai falala ne mai girma. = --Qur'an 57:29
    Certainly has Allah heard the speech of the one who argues with you, [O Muhammad], concerning her husband and directs her complaint to Allah. And Allah hears your dialogue; indeed, Allah is Hearing and Seeing. <> Lalle Alla Ya ji maganar wadda ke yi maka jãyayya game da mijinta, tanã kai ƙãra ga Allah, kuma Allah nã jin muhawararku. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani. = --Qur'an 58:1
    Those who pronounce thihar among you [to separate] from their wives - they are not [consequently] their mothers. Their mothers are none but those who gave birth to them. And indeed, they are saying an objectionable statement and a falsehood. But indeed, Allah is Pardoning and Forgiving. <> Waɗanda ke yin zihãri daga cikinku game da mãtansu, sũmãtan nan bã uwãyensu ba ne, bãbu uwayensu fãce waɗanda suka haife su. Lalle sũ, sunã faɗar abin ƙyãmã na magana da ƙarya, kuma lalle Allah haƙĩƙa Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara. = --Qur'an 58:2
    And those who pronounce thihar from their wives and then [wish to] go back on what they said - then [there must be] the freeing of a slave before they touch one another. That is what you are admonished thereby; and Allah is Acquainted with what you do. <> Waɗanda ke yin zihãri game da mãtansu, sa'an nan su kõma wa abin da suka faɗa, to, akwai 'yanta wuya a gabãnin su shãfi jũna. Wannan anã yi muku wa'azi da shi. Kuma Allah Mai ƙididdigewa ne ga abin da kuke aikatãwa. = --Qur'an 58:3
    And he who does not find [a slave] - then a fast for two months consecutively before they touch one another; and he who is unable - then the feeding of sixty poor persons. That is for you to believe [completely] in Allah and His Messenger; and those are the limits [set by] Allah. And for the disbelievers is a painful punishment. <> To, wanda bai sãmu ba, sai azumin wata biyu jẽre a gabãnin su shãfi jũna, sa'an nan wanda bai sãmi ĩkon yi ba, to, sai ciyar da miskĩnai sittin. Wannan dõmin ku yĩ ĩmãni da Allah da Manzonsa. Kuma waɗannan hukunce-hukunce haddõdin Allah ne. Kuma kãfirai, sunã da azãba mai raɗadi. = --Qur'an 58:4
    Indeed, those who oppose Allah and His Messenger are abased as those before them were abased. And We have certainly sent down verses of clear evidence. And for the disbelievers is a humiliating punishment. <> Lalle waɗanda ke sãɓã wa Allah da ManzonSa, an wulãkanta su kamar yadda aka wulãkantar da waɗanda ke a gabãninsu, kuma lalle Mun saukar da ãyõyi bayyanannu, kuma kãfirai nã da azãba mai wulãkantãwa. = --Qur'an 58:5
    On the Day when Allah will resurrect them all and inform them of what they did. Allah had enumerated it, while they forgot it; and Allah is, over all things, Witness. <> Rãnar da Allah zai tãyar da su gabã ɗaya, sa'an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka aikata, Allah Yã lissafa shi, alhãli kuwa sũ, sun manta da shi, kuma a kan kõme Allah Halartacce ne. = --Qur'an 58:6
    Have you not considered that Allah knows what is in the heavens and what is on the earth? There is in no private conversation three but that He is the fourth of them, nor are there five but that He is the sixth of them - and no less than that and no more except that He is with them [in knowledge] wherever they are. Then He will inform them of what they did, on the Day of Resurrection. Indeed Allah is, of all things, Knowing. <> Ashe, ba ka ga cẽwa lalle Allah Yanã sane da abin da yake a cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa ba? Wata gãnãwa ta mutum uku bã zã ta kasance ba fãce Allah Shĩ ne na huɗu ɗinta, kuma bãbu ta mutum biyar fãce Shĩ ne na shida ɗinta, kuma babu abin da ya kãsa wannan kuma babu abin da yake mafi yawa fãce Shĩ Yanã tãre da su duk inda suka kasance, sa'an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka aikata a Rãnar ¡iyãma. Lalle Allah Masani ne ga dukkan kõme. = --Qur'an 58:7
    Have you not considered those who were forbidden from private conversation, then they return to that which they were forbidden and converse among themselves about sin and aggression and disobedience to the Messenger? And when they come to you, they greet you with that [word] by which Allah does not greet you and say among themselves, "Why does Allah not punish us for what we say?" Sufficient for them is Hell, which they will [enter to] burn, and wretched is the destination. <> Ashe, ba ka ga waɗanda aka hane su ba daga ganãwar, sa'an nan sunã kõmã wa abin da aka hane su daga gare shi, kuma sunã gãnãwa game da zunubi da zãlunci da sãɓã wa Manzon Allah, kuma idan sun zo maka sai su gasihe ka da abin da Allah bai gaishe ka da shi ba, kuma sunã cẽwa a cikin zukatansu: "Don me Allah ba Ya yi mana azãba sabõda abin da muke faɗi?" Jahannama ita ce mai isarsu, zã su shigeta. Sabõda haka makõmarsu ta mũnana. = --Qur'an 58:8
    O you who have believed, when you converse privately, do not converse about sin and aggression and disobedience to the Messenger but converse about righteousness and piety. And fear Allah, to whom you will be gathered. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan za ku yi gãnãwa, to, kada ku gãna game da zunubi da zãlunci da sãɓã wa Manzon Allah, kuma ku yi gãnãwa game da alhẽri da taƙawa. Ku bi Allah da taƙawa wanda zã a tattara ku zuwa gare, shi. = --Qur'an 58:9
    Private conversation is only from Satan that he may grieve those who have believed, but he will not harm them at all except by permission of Allah. And upon Allah let the believers rely. <> Gãnãwar daga Shaiɗan take kawai dõmin ya mũnanã wa waɗanda suka yi ĩmãni, alhãli kuwa bã zai iya cũtar su da kõme ba fãce da iznin Allah. Kuma sai mũminai su dogara ga Allah. = --Qur'an 58:10
    O you who have believed, when you are told, "Space yourselves" in assemblies, then make space; Allah will make space for you. And when you are told, "Arise," then arise; Allah will raise those who have believed among you and those who were given knowledge, by degrees. And Allah is Acquainted with what you do. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan an ce muka, "Ku yalwatã a cikin majalisai," to, ku yalwatã, sai Allah Ya yalwatã muku, kuma idan an ce muku, "Ku tãshi" to, ku tãshi. Allah nã ɗaukaka waɗanda suka yi ĩmãni daga cikinku da waɗanda aka bai wa ilim wasu darajõji mãsu yawa, kuma, Allah Mai ƙididdigewa ne ga dukan kõme. = --Qur'an 58:11
    O you who have believed, when you [wish to] privately consult the Messenger, present before your consultation a charity. That is better for you and purer. But if you find not [the means] - then indeed, Allah is Forgiving and Merciful. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan zã ku gãnãwa da Manzon Allah, to, ku gabãtar da 'yar sadaka a gabãnin gãnãwarku, wannan ne mafi alhẽri a gare ku, kuma mafi tsarki. Sai idan ba ku sãmi (abin sadakar ba), to, lalle, Allah, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 58:12
    Have you feared to present before your consultation charities? Then when you do not and Allah has forgiven you, then [at least] establish prayer and give zakah and obey Allah and His Messenger. And Allah is Acquainted with what you do. <> Ashe, kun ji tsõron ku gabãtar da sadakõki a gabãnin gãnãwarku? To, idan ba ku aikata ba, kuma Allah Ya kõmo da ku zuwa ga sauƙi, sai ku tsai da salla, kuma ku bãyar da zakka, kuma ku yi ɗã'ã ga Allah da ManzonSa. Kuma Allah ne Mai ƙididdigewa ga abin da kuke aikatãwa. = --Qur'an 58:13
    Have you not considered those who make allies of a people with whom Allah has become angry? They are neither of you nor of them, and they swear to untruth while they know [they are lying]. <> Ashe, baka ga waɗanda suka jiɓinci waɗansu mutãne da Allah Ya yi hushi a kansu ba, bã su cikinku, kuma bã su a cikinsu kuma sunã rantsuwa a kan ƙarya, alhãli kuwa sunã sane? = --Qur'an 58:14
    Allah has prepared for them a severe punishment. Indeed, it was evil that they were doing. <> Allah Ya yi musu tattalin azãba mai tsanani. Lalle sũ abin da suka kasance sunã aikatãwa ya mũnana. = --Qur'an 58:15
    They took their [false] oaths as a cover, so they averted [people] from the way of Allah, and for them is a humiliating punishment. <> Sun riƙi rantsuwõwinsu garkuwa, sabõda haka suka kange (mũminai) daga jihãdin ɗaukaka tafarkin Allah. To, sunã da azãba mai wulãkantãwa. = --Qur'an 58:16
    Never will their wealth or their children avail them against Allah at all. Those are the companions of the Fire; they will abide therein eternally <> Dũkiyõyinsu ba su wadãtar musu kõme ba daga Allah, haka kuma ɗiyansu. Waɗannan 'yan wutã ne. Sũ, mãsu dawwama ne a cikinta. = --Qur'an 58:17
    On the Day Allah will resurrect them all, and they will swear to Him as they swear to you and think that they are [standing] on something. Unquestionably, it is they who are the liars. <> Rãnar da Allah ke tãyar da su gabã ɗaya, sai su yi Masa rantsuwa kamar yadda suke yi muku rantsuwa (a nan dũniya) kuma sunã zaton cẽwa sũ a kan wani abu suke! To, lalle sũ, sũ ne maƙaryata. = --Qur'an 58:18
    Satan has overcome them and made them forget the remembrance of Allah. Those are the party of Satan. Unquestionably, the party of Satan - they will be the losers. <> Shaiɗan ya rinjaya a kansu, sai ya mantar da su ambaton Allah, waɗannan ƙungiyar Shaiɗan ne. To, lalle ƙungiyar Shaiɗan, sũ ne mãsu hasãra. = --Qur'an 58:19
    Indeed, the ones who oppose Allah and His Messenger - those will be among the most humbled. <> Lalle, waɗanda ke sãɓã wa Allah da ManzonSa waɗannan sunã a cikin (mutãne) mafi ƙasƙanci. = --Qur'an 58:20
    Allah has written, "I will surely overcome, I and My messengers." Indeed, Allah is Powerful and Exalted in Might. <> Allah Ya rubũta cẽwa," Lalle zan rinjãya, Nĩ da ManzanniNa." Lalle Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi. = --Qur'an 58:21
    You will not find a people who believe in Allah and the Last Day having affection for those who oppose Allah and His Messenger, even if they were their fathers or their sons or their brothers or their kindred. Those - He has decreed within their hearts faith and supported them with spirit from Him. And We will admit them to gardens beneath which rivers flow, wherein they abide eternally. Allah is pleased with them, and they are pleased with Him - those are the party of Allah. Unquestionably, the party of Allah - they are the successful. <> Bã zã ka sãmi mutãne mãsu yin ĩmãni da Allah da RãnarLãhira sunã sõyayya da wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa ba, kõ dã sun kasance ubanninsu ne, kõ ɗiyansu kõ 'yan'uwansu, ko danginsu. waɗannan Allah Yã rubuta ĩmãni a cikin zukãtansu, kuma Yã ƙarfafa su da wani rũhi daga gare Shi, kuma zai shigar da su a gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu. Allah Yã yarda da su, kuma sun yarda da Shi. Waɗannan ƙungiyar Allah ne. To, lalle ƙungiyar Allah sũ ne mãsu babban rabo. = --Qur'an 58:22
    Whatever is in the heavens and whatever is on the earth exalts Allah, and He is the Exalted in Might, the Wise. <> Abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasã ya yi tasbihi ga Allah, alhãli kuwa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima. = [59:1] Masu tasbihi ga ALLAH su ne kome da ke cikin sammai da abin da ke cikin qasa, kuma Shi ne Mabuwayi, Mai hikimah. --Qur'an 59:1
    It is He who expelled the ones who disbelieved among the People of the Scripture from their homes at the first gathering. You did not think they would leave, and they thought that their fortresses would protect them from Allah; but [the decree of] Allah came upon them from where they had not expected, and He cast terror into their hearts [so] they destroyed their houses by their [own] hands and the hands of the believers. So take warning, O people of vision. <> Shĩ ne wanda Ya fitar da waɗanda suka kãfirta daga Mazõwa Littãfi, daga gidãjẽnsu da kõra ta farko. Ba ku yi zaton sunã fita ba, kuma sun tabbata cẽwa gãnuwõwinsu mãsu tsare su ne daga Allah, sai Allah Ya jẽ musu daga wajen da ba su yi zato ba, kuma Ya jẽfa tsõro a cikin zukãtansu, sunã rushe gidãjensu da hannãyensu da kuma hannãyen mũminai. To, ku lũra fa, ya mãsu basĩrõri. = [59:2] Shi ne wanda Ya fitar da wadanda suka kafirta daga mazowa Littafi, da tashiwa na kora daga gidajensu. Ba ku yi zaton za su fita ba, kuma sun yi zaton cewa shirin da suka yi zai tsare su ne daga ALLAH. Amma sai ALLAH Ya je masu daga inda ba su yi zato ba, kuma Ya jefa tsoro a cikin zukatansu. Ta haka ne, su da kansu suka bar gidajensu, da kuma qarin matsi daga muminai. To, ya kamata ku koyi darasi daga wannan, ya ku masu basira. --Qur'an 59:2
    And if not that Allah had decreed for them evacuation, He would have punished them in [this] world, and for them in the Hereafter is the punishment of the Fire. <> Kuma ba dõmin Allah Ya rubuta musu kõrar ba, dã Ya azabta su a cikin dũniya, kuma a Lãhira sunã da azãbar wutã. = [59:3] Kuma idan da ALLAH bai rubuta masu kara ba, da Ya azabta su a cikin duniya (wanda ma ya fi muni da tilasta su fita). Kuma a Lahira zai sanya su cikin azabar wuta. --Qur'an 59:3
    That is because they opposed Allah and His Messenger. And whoever opposes Allah - then indeed, Allah is severe in penalty. <> Wannan dõmin lalle su, sun sãɓa wa Allah, da ManzonSa alhãli kuwa wanda ya sãɓa wa Allah, to, lalle Allah, Mai tsananin uƙũba ne. = [59:4] Wannan domin sun saba wa ALLAH, da manzonSa. Saboda wadanda suka saba wa ALLAH da manzonSa, to, ALLAH Mai tsananin uquba ne. --Qur'an 59:4
    Whatever you have cut down of [their] palm trees or left standing on their trunks - it was by permission of Allah and so He would disgrace the defiantly disobedient. <> Abin da kuka sãre na dabĩniya, kõ kuka bar ta tsaye a kan asallanta, to da iznin Allah ne, kuma dõmin Ya wulãkanta fasiƙai, = [59:5] Ko kun sare itaciya, ko ku bar ta a tsaye a kan asallanta, to da iznin ALLAH ne. Domin lalle ne sai Ya wulakanta fasiqai. --Qur'an 59:5
    And what Allah restored [of property] to His Messenger from them - you did not spur for it [in an expedition] any horses or camels, but Allah gives His messengers power over whom He wills, and Allah is over all things competent. <> Kuma abin da Allah Ya sanya ya zama ganĩma ga ManzonSa, daga gare su, to, ba ku yi hari a kansa da dawãki ko rãƙuma ba amma Allah ne Ya rinjãyar da ManzanninSa a kan wanda Yake so, kuma Allah Mai ĩkon yi ne a kan kõme. = [59:6] Duk abin da ALLAH Ya mayar ga manzonSa na ganima, ba domin sakamakon qoqarin yaqinku ba ne, ko da kun yi yaqi a kan dawaki ne ko qafa. ALLAH Shi ne Mai aike wa da ManzanninSa a kan wanda Yake so, ALLAH Mai ikon yi ne a kan kome. --Qur'an 59:6
    And what Allah restored to His Messenger from the people of the towns - it is for Allah and for the Messenger and for [his] near relatives and orphans and the [stranded] traveler - so that it will not be a perpetual distribution among the rich from among you. And whatever the Messenger has given you - take; and what he has forbidden you - refrain from. And fear Allah; indeed, Allah is severe in penalty. <> Abin da Allah Ya sanya shi ganĩma ga ManzonSa dagamutãnen ƙauyukan nan, to, na Allah ne, kuma na ManzonSa ne kuma na mãsu dangantaka da mãrayu da miskĩnai da ɗan hanya (matafiyi) ne dõmin kada ya kasance abin shãwãgi a tsakãnin mawadãta daga cikinku kuma abin da Manzo ya bã ku, to, ku kama shi, kuma abin da ya hane ku, to, ku bar shi. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle, Allah, Mai tsananin uƙũba ne. = [59:7] Duk abin da ALLAH Ya mayar da wa manzonSa na ganima daga mutanen Alqaryan nan, to, na ALLAH ne, kuma na manzonSa ne (wanda za bayar da shi ta hanyan sadaqa). Ku kuma ba shi ga dangi, da marayu, da miskinai, da dan hanya. Domin kada ya kasance ba sai masu qarfi ne a cikin ku kawai za su amfana ba. Kuma abin da manzo ya ba ku to, sai ku karba, amma kada ku dauki abin da ya hane ku da shi. Ku bi ALLAH da taqawa. ALLAH Mai tsananin uquba ne. --Qur'an 59:7
    For the poor emigrants who were expelled from their homes and their properties, seeking bounty from Allah and [His] approval and supporting Allah and His Messenger, [there is also a share]. Those are the truthful. <> (Ku yi mãmãki) Ga matalauta mãsu hijira waɗanda aka fitar daga gidãjẽnsu da dũkiyõyinsu, sunã nẽman falala daga Allah da kuma yarda, kuma sunã taimakon Allah da ManzonSa! Waɗannan sũ ne mãsu gaskiya. = [59:8] (Ku baiwa) matalauta wadanda suka yi hijira. Wadanda aka fitar daga gidajensu da dukiyoyinsu, domin sun nemi falala daga ALLAH da kuma yarda, kuma domin taimakon ALLAH da manzonSa. Wadannan su ne masu gaskiya. --Qur'an 59:8
    And [also for] those who were settled in al-Madinah and [adopted] the faith before them. They love those who emigrated to them and find not any want in their breasts of what the emigrants were given but give [them] preference over themselves, even though they are in privation. And whoever is protected from the stinginess of his soul - it is those who will be the successful. <> Da waɗanda suka zaunar da gidãjensu (ga Musulunci) kuma (suka zãɓi) ĩmãni, a gabãnin zuwansu, sunã son wanda ya yi hijira zuwa gare su, kuma bã su tunãnin wata bukãta a cikin ƙirãzansu daga abin da aka bai wa muhãjirĩna, kuma sunã fĩfĩta waɗansu a kan kãwunansu, kuma ko dã sunã da wata larũra. Wanda ya sãɓã wa rõwar ransa, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo. = [59:9] Wadanda kuma suka ba su gidajen zama da wuraren fakewa, kuma suka kasance muminai, a gabanin zuwansu, suna son wadanda suka yi hijira zuwa gare su, kuma ba su yi tunanin wata bukata a cikin zukatansu ba na taimakon su. Ba shakka, da yardan zukatansu, sun fi ba su hankali a kan kawunansu, ko da yake su ma suna bukatan abin da suka kasance suna bayarwa. Lalle, wadanda suka fi qarfin zukatansu na rowa, to, wadannan su ne masu babban rabo. --Qur'an 59:9
    And [there is a share for] those who came after them, saying, "Our Lord, forgive us and our brothers who preceded us in faith and put not in our hearts [any] resentment toward those who have believed. Our Lord, indeed You are Kind and Merciful." <> Kuma waɗanda suka zõ daga bãyansu, sunã cẽwa, "Yã Ubangijinmu! Ka yi gãfara a gare mu, kuma ga 'yan'uwanmu, waɗanda da suka riga mu yin ĩmãni, kada Ka sanya wani ƙulli a cikin zukãtanmu ga waɗanda suka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu! Lalle Kai ne Mai tausayi, Mai jin ƙai. = [59:10] Kuma wadanda suka zo daga bayansu, suka ce, "Ubangijinmu, Ka yi gafara a gare mu, kuma ga 'yan'uwanmu, wadanda da suka riga mu yin imani, kada Ka sanya wani qiyayya a cikin zukatanmu ga wadanda suka yi imani. Ubangijinmu, Kai ne Mai tausayi, Mafi jin qai. --Qur'an 59:10
    Have you not considered those who practice hypocrisy, saying to their brothers who have disbelieved among the People of the Scripture, "If you are expelled, we will surely leave with you, and we will not obey, in regard to you, anyone - ever; and if you are fought, we will surely aid you." But Allah testifies that they are liars. <> Ashe, ba ka ga waɗanda suka yi munãfinci ba, sunã cẽwa ga 'yan'uwansu, waɗanda suka kãfirta daga Mazõwa Littafi, "Lalle idan an fitar da ku, lalle zã mu fita tãre da ku, kuma bã zã mu yi ɗã'a ga kõwa ba game da ku, har abada, kuma lalle idan an yãƙe ku, lalle zã mu taimake ku haƙĩƙatan?" Alhãli kuwa Allah na shaidar cẽwa lalle sũ tabbas, maƙaryata ne. = [59:11] Shin, ko ka ga wadanda suka iya halin munafinci, kuma yadda suke cewa ga 'yan'uwansu, wadanda suka kafirta daga mazowa Littafi, "Idan aka fitar da ku za mu fita tare da ku, kuma ba za mu yi biyayya ga wanda duk ya saba maku ba, har abada. Kuma idan wani ya yaqe ku, za mu yi yaqi da ku." Alhali kuwa ALLAH Yana shaidar cewa su maqaryata ne. --Qur'an 59:11
    If they are expelled, they will not leave with them, and if they are fought, they will not aid them. And [even] if they should aid them, they will surely turn their backs; then [thereafter] they will not be aided. <> Lalle idan an fitar da su, bã zã su fita tãre da su ba kuma lalle idan an yãƙe su bã zã su taimake su ba, kuma lalle idan sun taimake su lalle ne, haƙĩƙatan, zã su jũyar da bãyansu dõmin gudu, sa'an nan kuma bã zã a taimake su ba. = [59:12] Lalle, idan aka fitar da su, ba za su fita tare da su ba, kuma da an yaqe su, da ba za su taimake su ba, ko da ma sun taimaka masu, da za su juya baya su gudu, sa'an nan kuma ba za a taimake su ba. --Qur'an 59:12
    You [believers] are more fearful within their breasts than Allah. That is because they are a people who do not understand. <> Lalle kũ ne kuka fi bãyar da firgita a cikin zukãtansu bisa ga Allah, wannan kuwa dõmin sũ lalle waɗansu irin mutãne ne da bã su gãnẽwa. = [59:13] Lalle, ku ne kuka fi firgitad da su a cikin zukatansu bisa ga tsoronsu na ALLAH. Wannan kuwa domin su wadansu irin mutane ne da ba su ganewa. --Qur'an 59:13
    They will not fight you all except within fortified cities or from behind walls. Their violence among themselves is severe. You think they are together, but their hearts are diverse. That is because they are a people who do not reason. <> Bã su iya yãƙar ku gabã ɗaya, fãce a cikin garũruwa mãsu gãnuwa da gãruna, kõ kuma daga bãyan katangu. Yãkinsu a tsãkaninsu mai tsanani ne, kanã zaton su a haɗe, alhãli kuwa zukãtansu dabam- dabam suke. Wannan kuwa dõmin sũ, lalle wasu irin mutane ne da bã su hankalta. = [59:14] Ba su iya gamewa su yaqe ku, sai idan suna a cikin dakuna masu kariya sosai, ko kuma daga bayan katanga. Yaqinsu ya kan kasance abu ne mai wuya a tsakaninsu. Za ka zaton su masu hadin kai ne, alhali kuwa zukatansu dabam- dabam suke. Wannan kuwa domin su mutane ne da ba su ganewa. --Qur'an 59:14
    [Theirs is] like the example of those shortly before them: they tasted the bad consequence of their affair, and they will have a painful punishment. <> Kamar misãlin waɗanda ke a gabãninsu, bã da daɗẽwa ba, sun ɗanɗani kũɗar al'amarinsu, kuma sunã da wata azãba mai raRaɗi. = [59:15] Qaddaransu kamar misalin wadanda suke a gabaninsu ne. suna dandana irin sakamakon shawaran da suka yanke ne. suna da azaba mai radadi. --Qur'an 59:15
    [The hypocrites are] like the example of Satan when he says to man, "Disbelieve." But when he disbelieves, he says, "Indeed, I am disassociated from you. Indeed, I fear Allah, Lord of the worlds." <> Kamar misãlin Shaiɗan a lõkacin da yake cẽ wa mutum, "Ka kãfirta," To, a lõkacin da ya kãfirta ɗin, ya ce (masa): "Lalle bãbu ruwãna da kai. Lalle ni inã tsõron Allah Ubangijin halitta!" = [59:16] Misalinsu kamar na Shaidan ne: sa’ad da zai ce wa mutum, "Ka kafirta," sa’annan da zaran ya kafirta, sai ya ce, "Na shika ka. Ni ina tsoron ALLAH Ubangijin halitta." --Qur'an 59:16
    So the outcome for both of them is that they will be in the Fire, abiding eternally therein. And that is the recompense of the wrong-doers. <> Sai ãƙibarsu ta kasance cẽwa su biyun duka sunã a cikin wutã, sunã mãsu dawwama a cikinta. "Kuma wannan shĩ ne sakamakon mãsu zãlunci." = [59:17] Sai aqibar dukansu biyu ta kasance suna cikin wuta, wurin da a cikinta za su yi zama na dauwama. Wannan shi ne sakamakon azzalumai. --Qur'an 59:17
    O you who have believed, fear Allah. And let every soul look to what it has put forth for tomorrow - and fear Allah. Indeed, Allah is Acquainted with what you do. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma rai ya dũbi abin da ya gabãtar dõmin gõbe, kuma ku bi Allah da taƙawa. lalle Allah, Mai ƙididdigewa ne ga abin da kuke aikatãwa. = [59:18] Ya ku wadanda kuka yi imani, ku bi ALLAH da taqawa, kowace rai ta dubi abin da ta gabatar domin gobe. Ku bi ALLAH da taqawa. ALLAH Mai kididdigewa ne ga abin da kuke aikatawa. --Qur'an 59:18
    And be not like those who forgot Allah, so He made them forget themselves. Those are the defiantly disobedient. <> Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka manta Allah shi kuma Ya mantar da su rãyu, kansu. Waɗannan sũ ne fãsiƙai. = [59:19] Kada ku kasance kamar wadanda suka manta ALLAH, Shi kuma Ya sa suka manta da kawunansu. Wadannan su ne fasiqai. --Qur'an 59:19
    Not equal are the companions of the Fire and the companions of Paradise. The companions of Paradise - they are the attainers [of success]. <> 'Yan Wutã da 'yan Aljanna bã su daidaita. 'Yan Aljanna, sũ ne mãsu babban rabo. = [59:20] Ba daya bane mazaunan wuta, da mazaunan Aljannah; mazaunan Aljannah, su ne masu babban rabo. --Qur'an 59:20
    If We had sent down this Qur'an upon a mountain, you would have seen it humbled and coming apart from fear of Allah. And these examples We present to the people that perhaps they will give thought. <> Dã Mun saukar da wannan Alƙur'ani a kan dũtse, dã lalle kã ga dũtsen yanã mai tawãli'u, mai tsattsãgẽwa sabõda tsõron Allah, kuma waɗancan misãlai Munã bayyana su ne ga mutãne, da fatan za su yi tunãni. = [59:21] Idan da Mun saukar da wannan Alqur’ani a kan tsauni, da za ka ga tsaunin yana makyarkyata yana marmashewa, saboda tsoron ALLAH. Muna buga wadannan misalai ga mutane, da fatan za su yi tunani. --Qur'an 59:21
    He is Allah, other than whom there is no deity, Knower of the unseen and the witnessed. He is the Entirely Merciful, the Especially Merciful. <> (Wanda Ya saukar da Alƙur'ani) Shi ne Allah, wanda bãbu wani abin bautãwa fãce Shi Masanin fake da bayyane, Shĩ ne Mai rahama, Mai jin ƙai. = [59:22] Shi ne ALLAH, wanda babu wani abin bautawa sai Shi. Masanin fake da bayyane, Shi ne Mafi rahamah, Mafi jin qai. --Qur'an 59:22
    He is Allah, other than whom there is no deity, the Sovereign, the Pure, the Perfection, the Bestower of Faith, the Overseer, the Exalted in Might, the Compeller, the Superior. Exalted is Allah above whatever they associate with Him. <> Shĩ ne Allah, wanda bãbu abin bautãwa fãce shi, Mai mulki, Mai tsarki, Aminci, Mai amintarwa, Mai Tsarẽwa, Mabuwãyi, Mai t஛astãwa Mai nuna isa, tsarki ya tabbata a gare Shi daga abin da suke yi na shirki da Shi. = [59:23] Shi ne ALLAH; wanda babu abin bautawa sai Shi. Almaliku, Alquddusu, Alsalamu, Almu’minu, Almuhaiminu, Al’azizu, Aljabbaru, Almutakabbiru, Subhana ALLAH, daga abin da suke yi na shirka da Shi. --Qur'an 59:23
    He is Allah, the Creator, the Inventor, the Fashioner; to Him belong the best names. Whatever is in the heavens and earth is exalting Him. And He is the Exalted in Might, the Wise. <> Shĩ ne Allah, Mai halitta, Mai ginãwa, Mai sũrantãwa. Yanã da sũnãye mãsu kyau, abin da ke a cikin sammai da ƙasa sunã tsarkake Shi, kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima. = [59:24] Shi ne ALLAH; Mai halitta, Mai ginawa, Mai surantawa. Shi ne ke da sunaye mafi kyau. Masu tsarkake Shi, su ne abin da ke a cikin sammai da qasa, kuma Shi ne Mabuwayi,Mafi hikimah. --Qur'an 59:24
    O you who have believed, do not take My enemies and your enemies as allies, extending to them affection while they have disbelieved in what came to you of the truth, having driven out the Prophet and yourselves [only] because you believe in Allah, your Lord. If you have come out for jihad in My cause and seeking means to My approval, [take them not as friends]. You confide to them affection, but I am most knowing of what you have concealed and what you have declared. And whoever does it among you has certainly strayed from the soundness of the way. <> Ya kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku riƙi maƙiyĩNa kuma maƙiyinku masõyi, 845. Kuna jẽfa sõyayya zuwa gare su, alhãli kuwa haƙĩƙa sun kãfirta da abin da ya zo muku, na gaskiya, sunã fitar da Manzon Allah tãre da ku (daga gidãjenku) dõmin kun yi ĩmãni da Allah, Ubangijinku, idan kun fito dõmin jihãdi sabõda ɗaukaka kalmaTa da nẽman yardaTa, kunã asirta sõyayya zuwa gare su alhãli kuwa Nĩ ne Mafi sani ga abin da kuka ɓõye da abin da kuka bayyana, kuma duk wanda ya aikata shi daga cikinku, to, lalle ya ɓace daga tsakar hanya. = [60:1] Ya ku wadanda kuka yi imani, kada ku riqi maqiyaNa kuma maqiyanku masoyi, kuna nuna masu qauna, alhali kuwa sun kafirta da gaskiyan da ya zo maku, na gaskiya. Suna tsananta wa aanzo, tare da ku, domin kawai kun yi imani da ALLAH, Ubangijinku. Idan kun shirya domin jihadi saboda daukakaNa, da neman yardaTa, ta yaya za ku so su a boye? Ni ne Mafi sani ga abin da kuka boye da abin da kuka bayyana. Wadanda a cikinku suke aikata irin wannan, to, sun bata daga tsakar hanya. --Qur'an 60:1
    If they gain dominance over you, they would be to you as enemies and extend against you their hands and their tongues with evil, and they wish you would disbelieve. <> Idan sun kãma ku, zã su kasance maƙiya a gare ku, kuma su shimfiɗa hannuwansu da harsunan gũrin ku kãfirta. = [60:2] Idan suka gamu da ku, sai su yi da ku kamar maqiya, kuma su cutar da ku da hannuwansu da harsunansu. Suna gurin ku ma ku kafirta. --Qur'an 60:2
    Never will your relatives or your children benefit you; the Day of Resurrection He will judge between you. And Allah, of what you do, is Seeing. <> Zumuntarku bã zã ta amfãne ku ba, haka kuma ɗiyanku, a Rãnar Kiyãma. (Allah) zai rarrabe tsakãninku, kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa. = [60:3] Danginku da dukiyoyinku ba za su amfane ku ba. A Ranar Alqiyamah zai yi hukunci tsakaninku. ALLAH Mai gani ne ga abin da kuke aikatawa. --Qur'an 60:3
    There has already been for you an excellent pattern in Abraham and those with him, when they said to their people, "Indeed, we are disassociated from you and from whatever you worship other than Allah. We have denied you, and there has appeared between us and you animosity and hatred forever until you believe in Allah alone" except for the saying of Abraham to his father, "I will surely ask forgiveness for you, but I have not [power to do] for you anything against Allah. Our Lord, upon You we have relied, and to You we have returned, and to You is the destination. <> Lalle abin kõyi mai kyau ya kasance a gare ku game da Ibrãhĩm da waɗanda ke tãre da shi a lõkacin da suka ce wa mutnensu, "Lalle mũ bãbu ruwanmu daku, kuma da abin da kuke bautãwa, baicin Allah, mun fita batunku, kuma ƙiyayya da jiyẽwa jũna sun bayyana a tsakãninmu, sai kun yi ĩmãni da Allah Shi kaɗai." Fãce maganar Ibrãhĩm ga ubansa (da yace), "Lalle za ni nẽma maka gãfara kuma ban mallaki kõme ba daga Allah sabõda kai." "Yã Ubangijinmu! A gare Ka muka dõgara, kuma gare Ka muka mayar da al' amuranmu, kuma zuwa gare Ka makõma take." = [60:4] Wani abin koyi mai kyau ya kasance a gare ku game da Ibraham da wadanda ke tare da shi. Sa’ad da suka ce wa mutnensu, "Mun shika ku da abubuwan da kuke bautawa baicin ALLAH. Mun fita harqanku, kuma ba za ku ga kome ba daga gare mu sai qiyayya da adawa, har sai kun yi imani da ALLAH Shi KADAI.”* Amma dai furcin Ibrahim sa’ad da ya ce wa babansa, "Zan nema maka gafara,** amma ban mallaki kowane iko ba da zan kare ka daga ALLAH." "Ubangijinmu, a gare Ka muka dogara, kuma gare Ka muka mayar da al' amuranmu; kuma zuwa gare Ka makoma take. --Qur'an 60:4
    Our Lord, make us not [objects of] torment for the disbelievers and forgive us, our Lord. Indeed, it is You who is the Exalted in Might, the Wise." <> "Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanya mu fitina ga waɗanda suka kãfirta, kuma Ka yi gãfara gare Mu. Ya Ubangijinmu! Kai ne Mabuwãyi, Mai hikima! = [60:5] "Ubangijinmu, kada Ka sanya mu fitina ga wadanda suka kafirta, kuma Ka yi gafara gare mu. Ubangijinmu, Kai ne Mabuwayi, Mafi hikimah.” --Qur'an 60:5
    There has certainly been for you in them an excellent pattern for anyone whose hope is in Allah and the Last Day. And whoever turns away - then indeed, Allah is the Free of need, the Praiseworthy. <> Lalle, haƙĩƙa, abin kõyi mai kyau ya kasance a gare ku daga cikinsu, ga wanda ya kasance yanã fãtan (rahamar) Allah da Rãnar Lãhira, kuma wanda ya jũya bãya, to, lalle Allah, Shĩ ne wadãtacce, Gõdadde. = [60:6] Akwai abin koyi mai kyau gare ku daga cikinsu, ga wadanda suke neman ALLAH da Ranar Lahira. Amma kuma wadanda suka juya baya, to, ALLAH Shi ne wadatacce, godadde. --Qur'an 60:6
    Perhaps Allah will put, between you and those to whom you have been enemies among them, affection. And Allah is competent, and Allah is Forgiving and Merciful. <> Anã tsammãnin Allah Ya sanya, a tsakãninku da tsakãnin waɗanda kuka yi ƙiyayya da su, wata sõyaya daga gare su, kuma Allah Mai ĩkon yi ne, kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = [60:7] ALLAH sai Ya canza qiyayya a tsakaninku da su zuwa soyayya. ALLAH Mai ikon yi ne. Kuma ALLAH Mai gafara ne, Mafi jin qai. --Qur'an 60:7
    Allah does not forbid you from those who do not fight you because of religion and do not expel you from your homes - from being righteous toward them and acting justly toward them. Indeed, Allah loves those who act justly. <> Allah bã Ya hana ku, daga waɗanda ba su yãƙe ku ba sabõda addini kuma ba su fitar da ku ba daga gidãjenku, ga ku kyautata musu kuma ku yi musu ãdalci. Lalle Allah Yanã son mãsu ãdalci. = [60:8] ALLAH ba Ya hana ku, dakantaka da wadanda ba su yaqar ku sabada addini, kuma ba su fitar da ku daga gidajenku. Za ku iya abokantaka da su kuma ku yi masu adalci. ALLAH Yana son masu adalci. --Qur'an 60:8
    Allah only forbids you from those who fight you because of religion and expel you from your homes and aid in your expulsion - [forbids] that you make allies of them. And whoever makes allies of them, then it is those who are the wrongdoers. <> Allah Yanã hana ku kawai daga waɗanda suka yãke ku sabõda addini kuma suka fitar da ku daga gidãjenku, kuma suka taimaki jũna ga fitar da ku, karku jiɓince su, kuma wanda ya jiɓince su, to waɗannan sũ ne azzãlumai. = [60:9] ALLAH Ya hana ku kawai daga yin abokantaka da wadanda suke yaqar ku saboda addini, kuma suka fitar da ku daga gidajenku, kuma suka hada kai da juna domin su kore ku. Kada ku jibince su. Wadanda suka jibince su, to wadannan su ne azzalumai. --Qur'an 60:9
    O you who have believed, when the believing women come to you as emigrants, examine them. Allah is most knowing as to their faith. And if you know them to be believers, then do not return them to the disbelievers; they are not lawful [wives] for them, nor are they lawful [husbands] for them. But give the disbelievers what they have spent. And there is no blame upon you if you marry them when you have given them their due compensation. And hold not to marriage bonds with disbelieving women, but ask for what you have spent and let them ask for what they have spent. That is the judgement of Allah; He judges between you. And Allah is Knowing and Wise. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan mãtã mũminai suka zo muku, sunã mãsu hijira, to, ku jarraba su. Allah Shĩ ne mafi sani ga ĩmãninsu. To, idan kun san sũ mũminai ne, kada ku mayar da su zuwa ga kãfirai. Sũ mãtan bã su halatta ga aurensu, sũ kuma kãfiran bã su halatta ga auren mãtan. Ku bã su abin da suka ɓatar na dũkiya. Kuma bãbu laifi a kanku ga ku aure su idan kun bã su sadãkõkinsu. Kuma kada ku riƙe auren mãtã kãfirai, kuma ku tambayi abin da kuka ɓatar daga dũkiya, su kuma kãfirai su tambayi abin da suka ɓatar na dũkiya. Wannan hukuncin Allah ne Yanã hukunci a tsakãninku. kuma Allah, Masani ne, Mai hikima = [60:10] Ya ku wadanda kuka yi imani, idan mata muminai (suka bar abokan gaba) sai suka nemi mafaka a gare ku, to, ku jarraba su. ALLAH Shi ne mafi sani ga imaninsu. To, idan kuka tabbatar cewa su muminai ne, kada ku mayar da su zuwa ga kafirai. Su matan ba su halatta ga aurensu ba, kuma su kafiran ba su halatta ga auren matan ba. Ku mayar masu da abin da suka biya na sadaqi. Kuma babu laifi a kanku idan kuka aure su, mudun kun biya su sadaqokinsu. Kada ku riqi mata kafirai (idan suna son su zama da abokan gaba). Za ku iya ku tambaye su abin da kuka biya na sadaqi, su kuma kafirai su tambayi abin da suka biya na dukiya. Wannan hukuncin ALLAH ne; Yana hukunci a tsakaninku. ALLAH Masani ne, Mafi hikimah. --Qur'an 60:10
    And if you have lost any of your wives to the disbelievers and you subsequently obtain [something], then give those whose wives have gone the equivalent of what they had spent. And fear Allah, in whom you are believers. <> Kuma idan wani abu ya kuɓuce muku daga mãtanku zuwa ga kãfirai sa'an nan kuma kuka ɗauki fansa, to, sai ku bai wa waɗanda matansu suka tafi kwatankwacin abin da suka ɓatar na dũkiya. Kuma ku yi biyayya da taƙawa ga Allah wanda kuke mãsu ĩmãni da Shi, Shi Kaɗai. = [60:11] Kuma idan kowane daga cikin matan aurenku ta shiga qungiyar maqiya, sa’annan aka tilasta maku yaqi, to, sai ku tilasta wa maqiya su ba da fansa ga mutanen da suka rasa matan aurensu. Ku yi biyayya da taqawa ga ALLAH, wanda kuke imani da Shi. --Qur'an 60:11
    O Prophet, when the believing women come to you pledging to you that they will not associate anything with Allah, nor will they steal, nor will they commit unlawful sexual intercourse, nor will they kill their children, nor will they bring forth a slander they have invented between their arms and legs, nor will they disobey you in what is right - then accept their pledge and ask forgiveness for them of Allah. Indeed, Allah is Forgiving and Merciful. <> Yã kai Annabi! Idan mãtã mũminai suka zo maka sunã yi maka mubãya'a a kan bã zã su yi shirki da Allah ba ga kõme, kuma bã su yin sãtã, kuma bã su yin zina, kuma bã su kashe, ya'yansu, kuma bã su zuwa da ƙarya da suke ƙirƙirãwa a tsãkanin hannuwansu da ƙafãfunsu kuma bã su sãɓa maka ga wani abu da aka sani na sharĩ'a, to, ka karɓi mubãya'arsu, kuma ka nẽmi Allah Ya gãfarta musu. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = [60:12] Ya kai Annabi, idan mata muminai (wadanda suka bar kafirai) suka zo maka domin su nemi mafaka da kai, suka yi maka mubaya'a a kan ba za su yi shirki da ALLAH ba, kuma ba za su yi sata ba, kuma ba za su yi zina ba, kuma ba za su kashe ya'yansu ba, kuma ba za su yi qarya ba, kuma ba za su saba maka ga wani abu na shari'a, to, ka karbi mubaya'arsu, kuma ka roqi ALLAH Ya gafarta masu. ALLAH Mai gafara ne, Mafi jin qai. --Qur'an 60:12
    O you who have believed, do not make allies of a people with whom Allah has become angry. They have despaired of [reward in] the Hereafter just as the disbelievers have despaired of [meeting] the inhabitants of the graves. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku jiɓinci waɗansu mutãne da Allah Ya yi hushi a kansu. Lalle sun yanke tsammãni daga (rahamar) Lãhira, kamar yadda kãfirai suka yanke tsammãni daga mazõwa kaburbura. = [60:13] Ya ku wadanda kuka yi imani, kada ku jibinci wadanda ALLAH Ya yi fushi a kansu, kuma wadanda suka dauwama a cikin kafirci; su kamar kafiran da suka fid da rai a cikin kaburbura. --Qur'an 60:13
    Whatever is in the heavens and whatever is on the earth exalts Allah, and He is the Exalted in Might, the Wise. <> Abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasã ya yi tasbihi ga Allah alhãli kuwa, Shi ne Mabuwayi, Mai hikima. = [61:1] Masu tasbihi ga ALLAH shi ne abin da ke cikin sammai da abin da ke qasa. Shi ne Mabuwayi, Mafi hikimah. --Qur'an 61:1
    O you who have believed, why do you say what you do not do? <> Ya kũ waɗanda suka yi ĩmani! Don me kuke faɗin abin dã ba ku aikatãwa? = [61:2] Ya ku wadanda kuka yi imani, oon me kuke fadin abin da ba ku aikatawa? --Qur'an 61:2
    Great is hatred in the sight of Allah that you say what you do not do. <> Ya girma ga zama abin ƙyãma awurin Allah, ku faɗi abin da bã ku aikatãwa. = [61:3] Abu mafi qyama a wurin ALLAH shi ne ku fadi abin da ba ku aikatawa. --Qur'an 61:3
    Indeed, Allah loves those who fight in His cause in a row as though they are a [single] structure joined firmly. <> Lalle Allah Yanã son waɗanda ke yin yãƙi dõmin ɗaukaka KalmarSa, a cikin safu kamar sũ gini ne mai ɗamfarar jũna. = [61:4] ALLAH Yana son wadanda suke yin yaqi domin daukaka KalmarSa, a cikin safu kamar su burki a cikin bango. --Qur'an 61:4
    And [mention, O Muhammad], when Moses said to his people, "O my people, why do you harm me while you certainly know that I am the messenger of Allah to you?" And when they deviated, Allah caused their hearts to deviate. And Allah does not guide the defiantly disobedient people. <> Kuma a lõkacin da Mũsã ya ce wa mutãnensa: "Yã mutãnena! sabõda me kuke cũtar da ni, alhãli kuwa lalle kun sani cẽwa lalle nĩ Manzon Al1ah ne zuwa gare ku?" To, a lõkacin da suka karkace, Allah Ya karkatar da zukãtansu. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fasiƙai. = [61:5] Sa’ad da Musa ya ce wa mutanensa, "Ya mutanena sabõda me kuke cutar da ni, alhali kuwa kun san cewa ni manzon ALLAH ne zuwa gare ku?" Da suka karkace sai ALLAH Ya karkatar da zukatansu. Saboda ALLAH ba Ya shiryar da fasiqan mutane. --Qur'an 61:5
    And [mention] when Jesus, the son of Mary, said, "O children of Israel, indeed I am the messenger of Allah to you confirming what came before me of the Torah and bringing good tidings of a messenger to come after me, whose name is Ahmad." But when he came to them with clear evidences, they said, "This is obvious magic." <> Kuma a lõkacin da Ĩsã ɗan Maryayama ya ce: "Yã BanĩIsrã'ĩla! Lalle nĩ Manzon Allah ne zuwa gare ku, mai gaskata abin da ke gaba gare ni na Attaura, kuma mai bãyar da bushãra da wani Manzo da ke zuwa a bãyãna, SũnasaAhmad (Mashãyabo)." To, a lõkacin da ya jẽ musu da hujjõji, suka ce: "Wannan sihiri ne, bayyananne." = [61:6] Sa’ad da kuma Isah, dan Maryam, ya ce, "Ya Bani Isra’ila, ni manzon ALLAH ne zuwa gare ku, mai gaskatad da abin da ke gaba gare ni na Attaurah, kuma mai bayar da bishara da wani manzo da ke zuwa a bayana, sunasa Ahmad (mashayabo)." To, sa’ad da ya nuna masu hujjoji, suka ce, "Wannan sihiri ne, bayyananne." --Qur'an 61:6
    And who is more unjust than one who invents about Allah untruth while he is being invited to Islam. And Allah does not guide the wrongdoing people. <> Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ya Jingina ta ga Allah, alhãli kuwa shĩ, anã kiran sa zuwa ga Musulunci? Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai. = [61:7] Wane ne mafi zalunci sama da wanda ya qirqira qarya ya Jingina ta ga ALLAH, alhali kuwa ana kiran sa zuwa ga Musulunci? ALLAH ba Ya shiryar da azzaluman mutane. --Qur'an 61:7
    They want to extinguish the light of Allah with their mouths, but Allah will perfect His light, although the disbelievers dislike it. <> Sunã nufin su bice hasken Allah da bãkunansu alhãli kuwa Allah Mai kammala haskenSa ne, kuma kõ da kãfirai sun ƙi. = [61:8] Suna fatan su kashe hasken ALLAH da bakunansu. Amma kuwa ALLAH Mai kammala haskenSa ne, ko da kafirai ba su so. --Qur'an 61:8
    It is He who sent His Messenger with guidance and the religion of truth to manifest it over all religion, although those who associate others with Allah dislike it. <> Shi ne wanda Ya aiko ManzonSa da shiriya da addĩnin gakiya, dõmin Ya ɗaukaka shi a kan wani addĩni dukansa kuma kõ dã mushirikai sun ƙi. = [61:9] Shi ne wanda Ya aiko manzonSa* da shiriya da addinin gakiya, kuma zai daukaka shi a kan dukkan addinai, ko da mushirikai ba su so. --Qur'an 61:9
    O you who have believed, shall I guide you to a transaction that will save you from a painful punishment? <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Shin, in nũna muku wani fatauci wanda zai tsarshe ku daga wata azãba mai raɗaɗi? = [61:10] Ya ku wadanda kuka yi imani, bari sanar da ku wata sana’a wanda za ta kubutad da ku daga azaba mai radadi. --Qur'an 61:10
    [It is that] you believe in Allah and His Messenger and strive in the cause of Allah with your wealth and your lives. That is best for you, if you should know. <> Ku yi ĩmani da Allah da ManzonSa, kuma ku yi jihãdi ga ɗaukaka kalmar Allah game da dũkiyõyinku da rãyukanku. Wannan shĩ ne alhẽri a gare ku idan kun kasance kuna da sani. = [61:11] Ku yi imani da ALLAH da manzonSa, kuma ku yi jihadi fisabili ALLAH da dukiyoyinku da rayukanku. Wannan ita ce sana’a mafi kyau a gare ku, idan kun kasance kuna da sani. --Qur'an 61:11
    He will forgive for you your sins and admit you to gardens beneath which rivers flow and pleasant dwellings in gardens of perpetual residence. That is the great attainment. <> Sai Allah Ya gãfarta muku zunubbanku, kuma Ya shigar da ku gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, da waɗansu ɗãkuna mãsu dãɗi a cikin gidãjen Aljannar zama. Wannan shĩ ne babban rabo, mai girma. = [61:12] Sakamakon haka, sai ALLAH Ya gafarta maku zunubanku, kuma Ya shigar da ku gidajen Aljannah, wanda qoramu na gudana a qarqashinsu, kuma da kyawawan gidaje masu qasaita a cikin gidajen Aljannar zama. Wannan shi ne babban rabo, mai girma. --Qur'an 61:12
    And [you will obtain] another [favor] that you love - victory from Allah and an imminent conquest; and give good tidings to the believers. <> Da wata (falala) da yake kunã son ta; taimako daga Allah da cin nasara wanda yake kusa. Kuma ka yi bushãra ga mũminai. = [61:13] Bugu da qari, za ku sami abin da ranku ke so na ainihi: taimako daga ALLAH da tabbacin cin nasara. Ka yi bishara ga muminai. --Qur'an 61:13
    O you who have believed, be supporters of Allah, as when Jesus, the son of Mary, said to the disciples, "Who are my supporters for Allah?" The disciples said, "We are supporters of Allah." And a faction of the Children of Israel believed and a faction disbelieved. So We supported those who believed against their enemy, and they became dominant. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Ku kasance mataimakan Allah kamar abin da Ĩsã ɗanMaryama ya ce ga Hawãriyãwa, "Waɗanne ne mataimakãna zuwa ga (aikin) Allah?" Sai wata ƙungiya daga Banĩ Isrã'ĩla ta yi ĩmãni, kuma wata ƙungiya ta kãfirta. Sai muka ƙarfafa waɗanda suka yi ĩmãni a kan maƙiyansu, sabõda haka suka wãyi gari marinjãya. = [61:14] Ya ku wadanda suka yi imani, uu kasance mataimakan ALLAH, kamar Hawariyawan Isah, dan Maryamu. Sa’ad da ya ce masu, "Wanne ne mataimakana zuwa ga ALLAH?" Sai Hawariyawa suka ce, “Mu mataimakan ALLAH ne.” Ta haka ne, wata qungiya daga Bani Isra’ila suka yi imani, kuma wata qungiya ta kafirta. Sai muka qarfa wadanda suka yi imani a kan maqiyansu, har sai da suka rinjaya. --Qur'an 61:14
    Whatever is in the heavens and whatever is on the earth is exalting Allah, the Sovereign, the Pure, the Exalted in Might, the Wise. <> Abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin kasã sunã tasbĩhi ga Allah, Mamallaki, Mai tsarki' Mabuwãyi, Mai hikima. = [62:1] Masu tasbihi ga ALLAH shi ne duk abin da ke cikin sammai da abin da ke a cikin qasa; Al-maliki, Al-quddusi, Al-‘azizi, Al-hakim. --Qur'an 62:1
    It is He who has sent among the unlettered a Messenger from themselves reciting to them His verses and purifying them and teaching them the Book and wisdom - although they were before in clear error - <> Shĩ ne wanda Ya aika, a cikin mabiya al'ãdu, wani Manzo daga gare su yanã karanta ãyõyinSa a kansu, kuma yanã tsarkake su, kuma yanã sanar da su littafin da hikimarsa kõ da yake sun kasance daga gabãninsa lalle sunã a cikin ɓata bayyanãnna. = [62:2] Shi ne wanda Ya aika, a cikin mabiya al'adu, wani manzo daga gare su, yana karanta ayoyinSa a gare su, yana tsarkake su, kuma yana mai sanar da su littafi da hikimah. Kafin wannan, da sun kasance a cikin bata bayyanãnna. --Qur'an 62:2
    And [to] others of them who have not yet joined them. And He is the Exalted in Might, the Wise. <> Da waɗansu mutãne daga gare su, ba su i da riskuwa da sũ ba, alhãli kuwa shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima. = [62:3] Da zamanin wadansu mutane masu zuwa daga gare su masu yawa, Shi ne Mabuwayi, Mafi hikimah. --Qur'an 62:3
    That is the bounty of Allah, which He gives to whom He wills, and Allah is the possessor of great bounty. <> Waccan wata falalar Allah ce Yanã bãyar da ita ga wanda Yake so. Kuma Allah ne Ma'abũcin dukan falala mai girma. = [62:4] Wannan ita ce falalar ALLAH wanda Yake bayar da ita ga wanda Yake so. Kuma ALLAH ne Ma'abucin dukan falalan da babu iyaka. --Qur'an 62:4
    The example of those who were entrusted with the Torah and then did not take it on is like that of a donkey who carries volumes [of books]. Wretched is the example of the people who deny the signs of Allah. And Allah does not guide the wrongdoing people. <> Misãlin waɗanda aka ɗõra wa ɗaukar Attaura sa'an nan ba su ɗauke ta ba, kamar misãlin jãki ne Yanã ɗaukar littattafai. Tir da misãlin mutãnen nan da suka ƙaryatã game da ãyõyin Allah! Kuma Allah bã Yã shiryar da mutãnẽ azzãlumai. = [62:5] Misalin wadanda aka ba su Attaurah sa’annan suka gaza riqonta, kamar misalin jaki ne dauke da kayan litattafai na qwarai. Tir da misalin mutanen nan da suka qaryatad da ayoyin ALLAH. Kuma ALLAH ba Ya shiryar da azzaluman mutane. --Qur'an 62:5
    Say, "O you who are Jews, if you claim that you are allies of Allah, excluding the [other] people, then wish for death, if you should be truthful." <> Ka ce: "Yã kũ waɗandasuka tũba (Yahũdu)! Idan kun riya cẽwa kũ ne zãɓaɓɓun Allah bã sauran mutanẽ ba, sai ku yi gũrin mutuwa idan kun kasance mãsu gaskiya." = [62:6] Ka ce, "Ya ku wadanda suke Yahudu, idan kun riya cewa ku ne zababbu na ALLAH, kebe da sauran mutane ba, to, ku yi gurin mutuwa idan kun kasance masu gaskiya!" --Qur'an 62:6
    But they will not wish for it, ever, because of what their hands have put forth. And Allah is Knowing of the wrongdoers. <> Kuma bã zã su yi gũrinta ba har abadã sabõda abin da hannãyen su suka gabãtar. Kuma Allah ne masani ga azzãlumai = [62:7] Ba za su yi gurinta ba har abada, saboda abin da hannayen su suka gabatar. ALLAH ne masanin azzalumai. --Qur'an 62:7
    Say, "Indeed, the death from which you flee - indeed, it will meet you. Then you will be returned to the Knower of the unseen and the witnessed, and He will inform you about what you used to do." <> Ka ce "Lalle mutuwar nan da kuke gudũ daga gareta, to, lalle ita mai haɗuwa da ku ce sa'an nan kuma anã mayar da kũ zuwa ga masanin fake da bayyane, dõmin Ya bãku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa." = [62:8] Ka ce "Mutuwar nan da kuke neman ku kubuce wa, za ta hadu da ku, ba jima ko ba dade. Sa’annan a mayar da ku zuwa ga masanin fake da bayyane, sa’anna Ya baku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa." --Qur'an 62:8
    O you who have believed, when [the adhan] is called for the prayer on the day of Jumu'ah [Friday], then proceed to the remembrance of Allah and leave trade. That is better for you, if you only knew. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan anyi kirã zuwã ga salla a rãnar Jumu'a, sai ku yi aiki zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar ciniki. Wancan ɗinku ne mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance kunã sani. = [62:9] Ya ku wadanda suka yi imani, idan anyi kira zuwa ga Sallah a ranar Jumu'ah, sai ku yi sauri zuwa ga ambaton ALLAH, ku bar dukkan harkokin kasuwanci. Wannan ita ce mafi alheri a gare ku idan da kun sani. --Qur'an 62:9
    And when the prayer has been concluded, disperse within the land and seek from the bounty of Allah, and remember Allah often that you may succeed. <> Sa'an nan idan an ƙarẽ salla, Sai ku wãtsu a cikin ƙasã kuma ku nẽma daga falalar Allah, kuma ku ambaci sũnan Allah da yawa ɗammãninku, ku sãmi babban rabo. = [62:10] Sa'an nan idan an idar da Sallah, sai ku watsu a cikin qasa domin nemi daga falalar ALLAH, kuma ku ci gaba da ambatar sunan ALLAH a kullum, la’alla ku sami babban rabo. --Qur'an 62:10
    But when they saw a transaction or a diversion, [O Muhammad], they rushed to it and left you standing. Say, "What is with Allah is better than diversion and than a transaction, and Allah is the best of providers." <> Kuma idan suka ga wani fatauci kõ kuma wani wasan shagala, sai su yi rũgũguwar fita zuwa gare su, kuma su bar ka kanã tsaye. Ka ce: "Abin da yake a wurin Allah ne mafi alhẽri daga fataucin, alhãli kuwa Allah ne Mafi alhẽrinmãsu arzũtãwa." = [62:11] Kuma idan wasun su suka ga gamu da wani dillanci na kasuwanci, ko kuma wani wasan shagala, sai su rigenta fita zuwa gare shi kuma su bar ka a tsaye! Ka ce, "Abin da yake a wurin ALLAH shi ne mafi alheri da nishadi ko tijarah. ALLAH ne Mafi alherin masu arzutawa." --Qur'an 62:11
    When the hypocrites come to you, [O Muhammad], they say, "We testify that you are the Messenger of Allah." And Allah knows that you are His Messenger, and Allah testifies that the hypocrites are liars. <> Idan munãfukai suka jẽ maka suka ce: "Munẽ shaidar lalle kai haƙĩƙa Manzon Allah ne," Kuma Allah Yanã sane da lalle Kai, haƙĩƙa ManzonSa ne, kuma Allah Yanã shaida lalle munafukan haƙĩƙa, maƙaryata ne. = --Qur'an 63:1
    They have taken their oaths as a cover, so they averted [people] from the way of Allah. Indeed, it was evil that they were doing. <> Sun riƙi rantsuwõwinsu garkuwa, sai suka taushe daga tafarkin Allah. Lalle sũ abin da suka kasance sunã aikatãwa ya mũnana. = --Qur'an 63:2
    That is because they believed, and then they disbelieved; so their hearts were sealed over, and they do not understand. <> Wancan, dõmin lalle sũ, sun yi ĩmãni, sa'an nan kuma suka kãfirta, sai aka yunƙe a kan zukãtansu. Sabõda sũ, bã su fahimta. = --Qur'an 63:3
    And when you see them, their forms please you, and if they speak, you listen to their speech. [They are] as if they were pieces of wood propped up - they think that every shout is against them. They are the enemy, so beware of them. May Allah destroy them; how are they deluded? <> Kuma idan kã gan su, sai jikunansu su bã ka sha'awa kuma idan sun faɗa, zã ka saurãra ga maganarsu. Kamar dai sũ ƙyami ne wanda aka jingine. Sunã zaton kõwace tsãwa a kansu take. Sũ ne maƙiyan, sai ka yi saunarsu. Allah Yã la'ane su. Yãya ake karkatar da su? = --Qur'an 63:4
    And when it is said to them, "Come, the Messenger of Allah will ask forgiveness for you," they turn their heads aside and you see them evading while they are arrogant. <> Kuma idan aka ce musu "Ku zo Manzon Allah ya nẽma maku gãfara," Sai su gyãɗa kãwunansu, kuma ka gan su sunã kangẽwa, alhãli kuwa sunã mãsu girman kai. = --Qur'an 63:5
    It is all the same for them whether you ask forgiveness for them or do not ask forgiveness for them; never will Allah forgive them. Indeed, Allah does not guide the defiantly disobedient people. <> Daidai ne a kansu, kã nẽma musu gãfara kõ ba ka nẽmamusu ba. faufau Allah bã zai gãfarta musu ba. Lalle Allah, bã zai shiryar da mutãne fãsiƙai ba. = --Qur'an 63:6
    They are the ones who say, "Do not spend on those who are with the Messenger of Allah until they disband." And to Allah belongs the depositories of the heavens and the earth, but the hypocrites do not understand. <> Sũ ne waɗanda ke cẽwa "Kada ku ciyar a kan wanda ke wurin Manzon Allah har su wãtse," alhali kuwa taskõkin sammai da ƙasa ga Allah suke kuma amma munãfukai bã su fahimta. = --Qur'an 63:7
    They say, "If we return to al-Madinah, the more honored [for power] will surely expel therefrom the more humble." And to Allah belongs [all] honor, and to His Messenger, and to the believers, but the hypocrites do not know. <> Sunã cẽwa "Lalle ne idan mun kõma zuwa Madĩnar, haƙĩƙa mafi rinjaya zai fitar da mafi ƙasƙanta daga gare ta, alhãli kuwa rinjãyar ga Allah take kuma da ManzonSa, kuma da mũminai, kuma amma munãfikai ba su sani ba." = --Qur'an 63:8
    O you who have believed, let not your wealth and your children divert you from remembrance of Allah. And whoever does that - then those are the losers. <> Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada dũkiyõyinku da ɗiyanku su shagaltar da ku daga ambaton Allah. Kuma wanda ya yi haka, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra. = --Qur'an 63:9
    And spend [in the way of Allah] from what We have provided you before death approaches one of you and he says, "My Lord, if only You would delay me for a brief term so I would give charity and be among the righteous." <> Kuma ku ciyar daga abin da Muka azurta ku daga gãbanin mutuwa ta je wa ɗayanku har ya ce: "Yã Ubangijina! Don me ba Ka yi mini jinkiri ba zuwa ga wani ajali makusanci dõmin in gaskata kuma in kasance daga sãlihai?" = --Qur'an 63:10
    But never will Allah delay a soul when its time has come. And Allah is Acquainted with what you do. <> Kuma Allah bã zai jinkirta wa wani rai ba idan ajalinsa ya je. Kuma Allah Masani ne ga abin da suke aikatãwa. = --Qur'an 63:11
    Whatever is in the heavens and whatever is on the earth is exalting Allah. To Him belongs dominion, and to Him belongs [all] praise, and He is over all things competent. <> Abin da yake a cikin sammai da wanda yake a cikin ƙasã sunã tasbĩhi ga Allah. Gare Shi mulki yake, kuma gare Shi gõdiya take. Kuma Shi, a kan kõme, Mai ikon yi ne. = --Qur'an 64:1
    It is He who created you, and among you is the disbeliever, and among you is the believer. And Allah, of what you do, is Seeing. <> Shĩ ne wanda Ya halitta ku. Sa'an nan daga gare ku akwai kãfiri kuma daga gare ku akwai mũmini. Kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa. = --Qur'an 64:2
    He created the heavens and earth in truth and formed you and perfected your forms; and to Him is the [final] destination. <> Ya halitta sammai da ƙasã da abin da yake hakkinSa. Kuma Ya sũranta ku, sa'an nan Ya kyautata sũrõrinku. Kuma zuwa gare Shi makõma take. = --Qur'an 64:3
    He knows what is within the heavens and earth and knows what you conceal and what you declare. And Allah is Knowing of that within the breasts. <> Yanã sanin abin da ke a cikin sammai da ƙasã. Kuma Yanã sanin abin da kuke bõyẽwa da abin da kuke bayyanãwa. Kuma Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza. = --Qur'an 64:4
    Has there not come to you the news of those who disbelieved before? So they tasted the bad consequence of their affair, and they will have a painful punishment. <> Shin, babban lãbãri bai je muku ba na waɗanda suka kãfirta daga gabãni, sai suka ɗanɗani uƙũbar al'amarinsu kuma sunã da wata azãba mai raɗaɗi? = --Qur'an 64:5
    That is because their messengers used to come to them with clear evidences, but they said, "Shall human beings guide us?" and disbelieved and turned away. And Allah dispensed [with them]; and Allah is Free of need and Praiseworthy. <> Wancan sabõda lalle su Manzanninsu sun kasance sunã jẽ musu da hujjõji bayyanannu, sai suka ce: "Ashe, wasu mutane za su shiryar da mũ?" Sai suka kãfirta kuma suka jũya bãya, kuma Allah Ya wadãtu (daga gare su). Kuma Allah wadãtacce ne, Gõdadde. = --Qur'an 64:6
    Those who disbelieve have claimed that they will never be resurrected. Say, "Yes, by my Lord, you will surely be resurrected; then you will surely be informed of what you did. And that, for Allah, is easy." <> Waɗanda suka kãfirta sun riya cẽwa bã zã a tãyar da su ba. Ka ce: "Ni, inã rantsuwa da Ubangijĩna. Lalle zã a tãyar da ku haƙĩƙatan, sa'an nan kuma lalle anã bã ku lãbãri game da abin da kuka aikata. Kuma wannan ga Allah mai sauƙi ne." = --Qur'an 64:7
    So believe in Allah and His Messenger and the Qur'an which We have sent down. And Allah is Acquainted with what you do. <> Sabõda haka ku yi ĩmani da Allah da ManzonSa da hasken nan da Muka saukar. Kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Mai labartawa ne. = --Qur'an 64:8
    The Day He will assemble you for the Day of Assembly - that is the Day of Deprivation. And whoever believes in Allah and does righteousness - He will remove from him his misdeeds and admit him to gardens beneath which rivers flow, wherein they will abide forever. That is the great attainment. <> A rãnar da Yake tattara ku dõmin rãnar tãruwa. Wancan ne rãnar kãmunga. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah, kuma ya aikata aikin ƙwarai, zai kankare masa mũnãnan ayyukansa, kuma Yashigar da shi gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu har abada. Wannan ne babban rabo mai girma. = --Qur'an 64:9
    But the ones who disbelieved and denied Our verses - those are the companions of the Fire, abiding eternally therein; and wretched is the destination. <> Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata game da ayõyinMu, waɗannan sũne'yan wuta, sunã madawwama a cikinta. Kuma tir da makõma, ita. = --Qur'an 64:10
    No disaster strikes except by permission of Allah. And whoever believes in Allah - He will guide his heart. And Allah is Knowing of all things. <> Wata masĩfa bã zã ta sãmu ba fãce da iznin Allah. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah, Allah zai shiryar da zuciyarsa. Kuma Allah, ga dukan kõme, Masani ne. = --Qur'an 64:11
    And obey Allah and obey the Messenger; but if you turn away - then upon Our Messenger is only [the duty of] clear notification. <> Kuma ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga Manzo. Sa'an nan idan kun jũya bãya, to, abin sani kawai, akwai iyarwa bayyananna a kan ManzonMu. = --Qur'an 64:12
    Allah - there is no deity except Him. And upon Allah let the believers rely. <> Allah bãbu wani abin bauta wa fãce Shi. Kuma ga Allah, sai mũminai su dõgara. = --Qur'an 64:13
    O you who have believed, indeed, among your wives and your children are enemies to you, so beware of them. But if you pardon and overlook and forgive - then indeed, Allah is Forgiving and Merciful. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Lalle ne daga mãtanku da ɗiyanku akwai wani maƙiyi a gare ku, sai ku yi saunarsu. Kuma idan kuka yãfe, kuma kuka kau da kai, kuma kuka gãfarta, to, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 64:14
    Your wealth and your children are but a trial, and Allah has with Him a great reward. <> Dũkiyõyinku da ɗiyanku fitina ɗai ne. Kuma Allah, a wurinSa akwai wani sakamako mai girma. = --Qur'an 64:15
    So fear Allah as much as you are able and listen and obey and spend [in the way of Allah]; it is better for your selves. And whoever is protected from the stinginess of his soul - it is those who will be the successful. <> Sai ku bi Allah da taƙawa gwargwadon abin da kuka sãmi ĩko. Kuma ku saurãra kuma ku yi ɗã'ã, kuma ku ciyar, ya fi zama alhẽri gare ku. Kuma wandaya sãɓã wa rõwar ransa, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo. = --Qur'an 64:16
    If you loan Allah a goodly loan, He will multiply it for you and forgive you. And Allah is Most Appreciative and Forbearing. <> Idan kun bai wa Allah rance, rance mai kyau, (Allah) zai ninka shi a gare ku kuma Ya gãfarta muku. Kuma Allah Mai yawan gõdiya ne, Mai haƙuri. = --Qur'an 64:17
    Knower of the unseen and the witnessed, the Exalted in Might, the Wise. <> Shĩ ne Masanin fake da bayyane, Mabuwayi, Mai hikima. = --Qur'an 64:18
    O Prophet, when you [Muslims] divorce women, divorce them for [the commencement of] their waiting period and keep count of the waiting period, and fear Allah, your Lord. Do not turn them out of their [husbands'] houses, nor should they [themselves] leave [during that period] unless they are committing a clear immorality. And those are the limits [set by] Allah. And whoever transgresses the limits of Allah has certainly wronged himself. You know not; perhaps Allah will bring about after that a [different] matter. <> Ya kai Annabi! Idan kun saki mãtã, sai ku sake su ga iddarsu, kuma ku ƙididdige iddar. Kuma ku bi Allah Ubangijinku da taƙawa. Kada ku fitar da su daga gidãjensu, kuma kada su fita fãce idan sunã zuwa da wata alfãshã bayyananna. Kuma waɗancan iyakõkin Allah ne. Kuma wanda ya ƙẽtare iyãkõkin Allah, to, lalle ya zãlunci kansa. Ba ka sani ba ɗammãnin Allah zai fitar da wani al'amari a bãyan haka. = --Qur'an 65:1
    And when they have [nearly] fulfilled their term, either retain them according to acceptable terms or part with them according to acceptable terms. And bring to witness two just men from among you and establish the testimony for [the acceptance of] Allah. That is instructed to whoever should believe in Allah and the Last day. And whoever fears Allah - He will make for him a way out <> Sa'an nan idan sun isa ga ajalinsu (na idda) sai ku riƙe su da abin da aka sani kõ ku rabu da su da abin da aka sani kuma ku shaidar da mãsu adalci biyu daga gare ku. Kuma ku tsayar da shaidar dõmin Allah. Wancan ɗinku anã yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance yanã yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, Allah zai sanya masa mafita. = --Qur'an 65:2
    And will provide for him from where he does not expect. And whoever relies upon Allah - then He is sufficient for him. Indeed, Allah will accomplish His purpose. Allah has already set for everything a [decreed] extent. <> Kuma Ya arzũta shi daga inda bã ya zato. Kuma wanda ya dõgara ga Allah, to, Allah ne Ma'ishinsa. Lalle Allah Mai iyar da umurninSa ne. Haƙĩƙa Allah Ya sanyama'auni ga dukan kõme. = --Qur'an 65:3
    And those who no longer expect menstruation among your women - if you doubt, then their period is three months, and [also for] those who have not menstruated. And for those who are pregnant, their term is until they give birth. And whoever fears Allah - He will make for him of his matter ease. <> Kuma waɗanda suka yanke ɗammãni daga haila daga mãtanku, idan kun yi shakka, to, iddarsu watã uku ce da waɗanda ba su yi haila ba. Kuma ma'abũta cikinna ajalinsu, (shi ne) cewa su haifi cikinnansu. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, (Allah) zai sanya masa wani sauƙi daga al'amarinsa. = --Qur'an 65:4
    That is the command of Allah, which He has sent down to you; and whoever fears Allah - He will remove for him his misdeeds and make great for him his reward. <> Wancan umurnin Allah ne, Ya saukar da shi zuwa gare ku. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, Allah zai kankare masa mũnãnan ayyukansa, kuma Ya girmama masa sãkamako. = --Qur'an 65:5
    Lodge them [in a section] of where you dwell out of your means and do not harm them in order to oppress them. And if they should be pregnant, then spend on them until they give birth. And if they breastfeed for you, then give them their payment and confer among yourselves in the acceptable way; but if you are in discord, then there may breastfeed for the father another woman. <> Ku zaunar da su daga inda kuka zaunar daga gwargwadon sãmunku. Kuma kada ku cũce su dõmin ku ƙuntata a kansu. Kuma idan sun kasance ma'abũta ciki, sai ku ciyar da su har su haifi cikinsu. Sa'an nan idan sun shãyar da mãma sabõda ku, sai ku bã su tsãdõdinsu. Kuma ku yi shãwara a tsakãninku bisa abin da aka sani. Kuma idan kun nũna talauci to wata mace zã ta shãyar da mãma sabõda shi (mijin). = --Qur'an 65:6
    Let a man of wealth spend from his wealth, and he whose provision is restricted - let him spend from what Allah has given him. Allah does not charge a soul except [according to] what He has given it. Allah will bring about, after hardship, ease. <> Sai mawadãci ya ciyar daga wadãtarsa kuma wanda aka ƙuntata masa arzikinsa, to, sai ya ciyar daga abin da Allah Ya bã shi. Allah bã Ya kallafa wa wani rai fãce abin da Ya bã shi. Allah zai sanya sauƙi a bãyan tsanani. = --Qur'an 65:7
    And how many a city was insolent toward the command of its Lord and His messengers, so We took it to severe account and punished it with a terrible punishment. <> Kuma da yawa daga alƙarya wadda ta yi tsaurin kai daga barin umurnin Ubangijinta da ManzanninSa, sai Muka yi mata hisãbi, hisãbi mai tsanani, kuma Muka, azabtar da ita azãba abar ƙyãma. = --Qur'an 65:8
    And it tasted the bad consequence of its affair, and the outcome of its affair was loss. <> Sa'an nan ta ɗanɗana masĩfar al'amarinta. kuma ƙarshen al'amarinta ya kasance hasãra, = --Qur'an 65:9
    Allah has prepared for them a severe punishment; so fear Allah, O you of understanding who have believed. Allah has sent down to you the Qur'an. <> Allah Ya yi musu tattalin wata azãba mai tsanani. Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, yã ma'abũta hankula, waɗanda suka yi ĩmãni! Haƙĩƙa Allah Ya saukar da wata tunãtarwa zuwa gare ku. = --Qur'an 65:10
    [He sent] a Messenger [Muhammad] reciting to you the distinct verses of Allah that He may bring out those who believe and do righteous deeds from darknesses into the light. And whoever believes in Allah and does righteousness - He will admit him into gardens beneath which rivers flow to abide therein forever. Allah will have perfected for him a provision. <> Manzo, yanã karãtun ãyõyin Allah bayyananu a kanku dõmin Ya fitar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai daga duffai zuwa ga haske. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah ya aikata aikin ƙwarai Allah zai shigar da shi gidãjen Aljanna ƙoramu nã gudãna daga ƙarƙashnsu sunã mãsu dawwama a cikinsu har abada. Haƙĩƙa Allah Yã kyautata masa arziki. = --Qur'an 65:11
    It is Allah who has created seven heavens and of the earth, the like of them. [His] command descends among them so you may know that Allah is over all things competent and that Allah has encompassed all things in knowledge. <> Allah, wanda Ya halitta bakwai ɗin sammai kuma daga ƙasã kwatankwacinsu, umuruinSa yanã ta sauka a tsakaninsu dõmin ku san lalle Allah Mai ĩkon yi ne akan dukan kõme, kuma lalle Allah, haƙĩƙa Ya kẽwaye ga dukan kõme da sani. = --Qur'an 65:12
    O Prophet, why do you prohibit [yourself from] what Allah has made lawful for you, seeking the approval of your wives? And Allah is Forgiving and Merciful. <> Yã kai Annabi! Don me kake haramta abin da Allah Ya halatta maka, kanã nẽman yardar mãtanka, alhãli kuwa Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 66:1
    Allah has already ordained for you [Muslims] the dissolution of your oaths. And Allah is your protector, and He is the Knowing, the Wise. <> Haƙĩƙa Allah ya faralta muku warware rantsuwõyinku, kuma Allah ne Mataimakinku kuma shĩ ne Masani, Mai hikima. = --Qur'an 66:2
    And [remember] when the Prophet confided to one of his wives a statement; and when she informed [another] of it and Allah showed it to him, he made known part of it and ignored a part. And when he informed her about it, she said, "Who told you this?" He said, "I was informed by the Knowing, the Acquainted." <> Kuma a sã'ilin da Annabi ya asirta wani lãbãri zuwa ga sãshen mãtansa, to, a lõkacin da ta bã da lãbari da shi. Kuma Allah Ya bayyana shi a gare shi, ya sanar da sãshensa kuma ya kau da kai daga wani sãshe. To, a lõkacin da ya bã ta lãbãri da shi, ta ce: "Wãne ne ya gaya maka wannan?" Ya ce: "Masani, Mai labartãwa, Ya gaya mini." = --Qur'an 66:3
    If you two [wives] repent to Allah, [it is best], for your hearts have deviated. But if you cooperate against him - then indeed Allah is his protector, and Gabriel and the righteous of the believers and the angels, moreover, are [his] assistants. <> Idan kũ biyu kuka tũba zuwa ga Allah, to, haƙĩƙa zukãtanku sun karkata. Kuma idan kun taimaki jũna a kansa to, lalle Allah Shĩ ne Mataimakinsa, da Jibrĩlu da sãlihan mũminai. Kuma malã'iku a bãyan wancan, mataimaka ne. = --Qur'an 66:4
    Perhaps his Lord, if he divorced you [all], would substitute for him wives better than you - submitting [to Allah], believing, devoutly obedient, repentant, worshipping, and traveling - [ones] previously married and virgins. <> Mai yiwuwa ne Ubangijinsa, idan ya sake ku, Ya musanya masa waɗansu mãtan aure mafiya alhẽri daga gare ku, Musulmai mũminai mãsu tawãli'u, mãsu tũba, mãsu ibãda, mãsu, azumi, zawarõri da 'yammãta. = --Qur'an 66:5
    O you who have believed, protect yourselves and your families from a Fire whose fuel is people and stones, over which are [appointed] angels, harsh and severe; they do not disobey Allah in what He commands them but do what they are commanded. <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kãre wa kanku (da iyãlinku wata wuta makãmashinta mutãne da duwãtsu ne. A kanta akwai waɗansu malã'iku mãsu kauri, mãsu ƙarfi. Bã su sãɓã wa Allah ga abin da Ya umurce su, kuma sunã aikata abin da ake umunin su. = --Qur'an 66:6
    O you who have disbelieved, make no excuses that Day. You will only be recompensed for what you used to do. <> Yã kũ waɗanda suka kãfirta! Kada ku kãwo wani uzuri a yau. Anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa kawai ne. = --Qur'an 66:7
    O you who have believed, repent to Allah with sincere repentance. Perhaps your Lord will remove from you your misdeeds and admit you into gardens beneath which rivers flow [on] the Day when Allah will not disgrace the Prophet and those who believed with him. Their light will proceed before them and on their right; they will say, "Our Lord, perfect for us our light and forgive us. Indeed, You are over all things competent." <> Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kõma zuwa ga Allah kõmawar gaskiya. Mai yiwuwa Ubangjinku Ya kankare muku miyãgun ayyukanku kuma Ya shigar da ku a gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu a rãnar da Allah bã Ya kunyatar da Annabi da wadanda suka yi ĩmãni tãre da shi. Haskensu yanã tafiya a gaba gare su da jihõhin dãmansu, sunã cẽwa, "Yã Ubangijiumu! Ka cika mana haskenmu, kuma Ka yi mana gãfara. Lalle Kai, a kan dukkan kõme, Yã kai Mai ikon yi ne." = --Qur'an 66:8
    O Prophet, strive against the disbelievers and the hypocrites and be harsh upon them. And their refuge is Hell, and wretched is the destination. <> Yã kai Annabi! Ka yãki kãfirai da munãfwkai. Kuma ka tsananta a kansu. Kuma matattararsu Jahannama ce, kuma tir da makoma, ita. = --Qur'an 66:9
    Allah presents an example of those who disbelieved: the wife of Noah and the wife of Lot. They were under two of Our righteous servants but betrayed them, so those prophets did not avail them from Allah at all, and it was said, "Enter the Fire with those who enter." <> Allah Ya buga wani misãli dõmin waɗanda suka kãfirta: mãtar Nũhu da mãtar Lũɗu, sun kasance a ƙarƙashin wasu bãyi biyu daga bãyinMu sãlihai, saisuka yaudare su, sabõda haka ba su wadãtar musu da kõme daga Allah ba. Kuma aka ce: "Ku shiga, kũ biyu, wutã tãre da mãsu shiga." = --Qur'an 66:10
    And Allah presents an example of those who believed: the wife of Pharaoh, when she said, "My Lord, build for me near You a house in Paradise and save me from Pharaoh and his deeds and save me from the wrongdoing people." <> Kuma Allah Ya buga wani misãli dõmin waɗanda suka yi ĩmãni; matar Fir'auna, sa'ad da ta ce "Ya Ubangiji! Ka gina mini wani gida a wurinKa a cikin Aljanna. Kuma Ka tsĩrar da ni daga Fir'auna da aikinsa. Kuma Ka tsĩrar da ni daga mutãnen nan azzãlumai." = --Qur'an 66:11
    And [the example of] Mary, the daughter of 'Imran, who guarded her chastity, so We blew into [her garment] through Our angel, and she believed in the words of her Lord and His scriptures and was of the devoutly obedient. <> Da Maryama ɗiyar Imrãna wadda ta tsare farjinta, sai Muka hũra a cikinsa daga rũhinMu. Kuma ta gaskata game da ãyõyin Ubangijinta da LittattafanSa alhãli kuwa ta kasance daga mãsu tawãli'u. = --Qur'an 66:12
    Blessed is He in whose hand is dominion, and He is over all things competent - <> (Allah), Wanda gudãnar da mulki yake ga hannunSa, Ya tsarkaka, kuma Shi Mai ĩko ne a kan kome. = [67:1] Mafi girma Shi ne wanda a hannunSa ne mulki yake, kuma Shi ne Mai iko bisa kan kome. --Qur'an 67:1
    [He] who created death and life to test you [as to] which of you is best in deed - and He is the Exalted in Might, the Forgiving - <> Shi ne Wanda Ya halitta mutuwa da rãyuwa domin Ya jarraba ku, Ya nũna wãye daga cikinku ya fi kyãwon aiki, Shi ne Mabuwãyi, Mai gafara. = [67:2] Shi ne Wanda Ya halitta mutuwa da rayuwa domin Ya jarraba wadanda za su fi kyawon aiki.* Shi ne Mabuwayi, Mai gafara. --Qur'an 67:2
    [And] who created seven heavens in layers. You do not see in the creation of the Most Merciful any inconsistency. So return [your] vision [to the sky]; do you see any breaks? <> Shi ne wanda Ya halitta sammai bakawi, ɗabaƙõƙi a kan jũna, bã za ka ga goggociya ba a cikin halittar (Allah) Mai rahama. Ka sãke dũbawa, ko za ka ga wata ɓaraka? = [67:3] Shi ne wanda Ya halitta sammai bakawi, da shinfidodi a kan juna. Ba za ka ganin aibi a cikin halittar Mafi rahamah. Ka sake dubawa; ko za ka ga wata aibi? --Qur'an 67:3
    Then return [your] vision twice again. [Your] vision will return to you humbled while it is fatigued. <> Sa'an nan ka sake maimaita, dũbãwa, ganinka zai komo maka, gajiyayye, ba da ganin wata naƙasa bã. = [67:4] Ka sake maimaita dubawa; ganinka zai komo maka batir da kadawa. --Qur'an 67:4
    And We have certainly beautified the nearest heaven with stars and have made [from] them what is thrown at the devils and have prepared for them the punishment of the Blaze. <> Kuma lalle Mun ƙawãta samar farko da fitillu, kuma Muka sanya su abin jifa ga shaiɗanu, kuma Muka yi musu tattalin azãbar Sa'ĩr. = [67:5] Kuma Mun qawata samar duniya da fitillu, kuma Muka tsare iyakanta da abin jifa ga shaidanu; kuma Muka yi masu shirin azabar Sa’ir. --Qur'an 67:5
    And for those who disbelieved in their Lord is the punishment of Hell, and wretched is the destination. <> Kuma waɗanda suka kafirce wa Ubangjinsu na da azãbar Jahannama, tã munana ga zamanta makõmarsu. = [67:6] Kuma wadanda suka kafirce wa Ubangjinsu, suna da azabar Jahannama. Wannan ita ce makoma ta zullumi. --Qur'an 67:6
    When they are thrown into it, they hear from it a [dreadful] inhaling while it boils up. <> Idan an jẽfa su a cikinta, sai su ji daga gare ta wata ƙãra, tana tafasa. = [67:7] Idan aka jefa su a cikinta, sai su ji daga gare ta wata qara, sa’ad da take hamami. --Qur'an 67:7
    It almost bursts with rage. Every time a company is thrown into it, its keepers ask them, "Did there not come to you a warner?" <> Tana kusa ta tsãge domin hushi, ko da yaushe aka jẽfa wani ɓangaren jama'a a cikinta, matsaranta na tambayar su da cewa, "Wani mai gargaɗi bai je muku ba?" = [67:8] Tana kusa ta fashe domin hushi. A ko da yaushe aka jefa wani bagaren jama'a a cikinta, masu gadinta za su tambaye su da cewa, " Shin wani mai gargadi bai je maku ba ne?" --Qur'an 67:8
    They will say," Yes, a warner had come to us, but we denied and said, 'Allah has not sent down anything. You are not but in great error.'" <> Sai su ce: "I, lalle wani mai gargaɗi ya je mana, sai muka ƙaryata shi, muka ce, 'Allah bai saukar da kome ba, bã ku cikin kõme sai ɓata babba.'" = [67:9] Za su amsa cewa, "Na’am, lalle wani mai gargadi ya je mana, amma sai muka qaryata shi muka ce, 'ALLAH bai saukar da kome ba. Ba ku cikin kome sai babban bata.'" --Qur'an 67:9
    And they will say, "If only we had been listening or reasoning, we would not be among the companions of the Blaze." <> Kuma suka ce: "Dã mun zamo muna saurãre, kõ muna da hankali, dã ba mu kasance a cikin 'yan sa'ĩr ba." = [67:10] Kuma suka ce, "Da mun ji, ko muka kane, da ba mu kasance a cikin 'yan sa’ir ba." --Qur'an 67:10
    And they will admit their sin, so [it is] alienation for the companions of the Blaze. <> Wato su yi iƙrãri da laifinsu. Allah Ya la'ani'yan sa'ĩr! = [67:11] Wato sun yi iqrari da laifinsu. La'ana ya tabbata ga 'yan sa'ir. --Qur'an 67:11
    Indeed, those who fear their Lord unseen will have forgiveness and great reward. <> Lalle waɗanda ke tsõron Ubangjinsu, a ɓoye, suna da wata gãfara da wani sakamako mai girma. = [67:12] Amma wadanda suke gurmama Ubangjinsu, su kadai a fake, sun kai ga wata gafara da sakamako mai girma. --Qur'an 67:12
    And conceal your speech or publicize it; indeed, He is Knowing of that within the breasts. <> Kuma ku asirta maganarku ko ku bayyana ta, lalle shi, (Allah), Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza. = [67:13] Kuma ok da ku asirta furcinku, ko ku bayyana ta, Shi Masani ne ga abin da ke cikin zukata. --Qur'an 67:13
    Does He who created not know, while He is the Subtle, the Acquainted? <> Ashe, wanda Ya yi halitta bã zai iya saninta ba, alhãli kuwa shi Mai tausasãwa ne, kuma Mai labartawa? = [67:14] Shin, wanda Ya yi halitta ba zai iya saninta ba? Shi ne Mai tausasawa, kuma Mai labartawa. --Qur'an 67:14
    It is He who made the earth tame for you - so walk among its slopes and eat of His provision - and to Him is the resurrection. <> Shi, (Allah), Yã sanya muku ƙasa hõrarriya, sai ku tafi cikin sãsanninta, kuma ku ci daga arzikinSa, kuma zuwa gare shi ne tãshin yake. = [67:15] Shi ne wanda Ya sanya maku qasa horarriya domin yi maku hidima. Ku yi yawo cikin sasanninta, kuma ku ci daga arzikinSa. Zuwa gare Shi ne za tarinku yake. --Qur'an 67:15
    Do you feel secure that He who [holds authority] in the heaven would not cause the earth to swallow you and suddenly it would sway? <> Shin kõ kun amince cewa wanda ke cikin sama, bã zai iya shãfe ƙasa tãre da ku ba, sai ga ta tana mai girgiza? = [67:16] Shin, ko kun tabbatar cewa wanda ke cikin sama, ba zai iya shafe qasa tare da ku ba, Ya sa ta birkida? --Qur'an 67:16
    Or do you feel secure that He who [holds authority] in the heaven would not send against you a storm of stones? Then you would know how [severe] was My warning. <> Kõ kun amincẽ cewa wanda ke cikin sama bã zai iya sako muku iskar gũguwa ba? To, zã ku san yadda (ãƙibar) gargaɗiNa take. = [67:17] Ko kun tabbatar cewa wanda ke cikin sama ba zai iya sako maku bala’in iskar goguwa ba? To, za ku iya sanin yadda gargadiNa take? --Qur'an 67:17
    And already had those before them denied, and how [terrible] was My reproach. <> Lalle, waɗanda ke gabansu sun ƙaryata (manzanni). To, yãya (ãƙibar) gargaɗiNa ta kasance? = [67:18] Wadansu a gabansu sun qaryata; (manzanni) to, yaya aqibar gargadiNa ta kasance! --Qur'an 67:18
    Do they not see the birds above them with wings outspread and [sometimes] folded in? None holds them [aloft] except the Most Merciful. Indeed He is, of all things, Seeing. <> Bã zã su yi dũbi ba zuwa ga tsuntsãye a kansu, mãsu sanwã, kuma suna fiffikãwa, bãbu mai riƙe da su sai (Allah), Mairahama? Lalle shi Mai gani ne ga dukan kõme. = [67:19] Ba su ga tsuntsaye ba ne a bisansu, da suka yi ginshiqin layin sahu, kuma suka baje fikafikinsu? Mafi rahamah Shi ne Ya riqe su a cikin iska. Shi ne Mai gani ga dukan kome. --Qur'an 67:19
    Or who is it that could be an army for you to aid you other than the Most Merciful? The disbelievers are not but in delusion. <> Wãne ne wanda zai zame muku mayãƙin da zai taimake ku, wanda bã (Allah) ba, Mai rahama? Kãfirai ba su a cikin kõme fãce rũɗu. = [67:20] Ina mayaqan da za su taimake ku ga Mafi rahamah? Lalle, kafirai rudadu ne. --Qur'an 67:20
    Or who is it that could provide for you if He withheld His provision? But they have persisted in insolence and aversion. <> Wãne ne wanda zai ciyar da ku, idan (Allah) Ya riƙe arzikinSa? A'aha, sun yi zurfi cikin girman kai da tãshin hankali. = [67:21] Wane ne wanda zai ciyar da ku, idan Ya riqe arzikinSa? Lalle, sun yi zurfi cikin girman kai da qyama. --Qur'an 67:21
    Then is one who walks fallen on his face better guided or one who walks erect on a straight path? <> Shin, wanda ke tafiya a kife a kan fuskarsa yã fi zama a kan shiryuwa, ko kuwa wanda ke tafiya miƙe a kan hanya madaidaiciya? = [67:22] Shin, wanda ke tafiya yana kifewa a kan fuskarsa ya fi zama a kan shiryuwa, ko kuwa wanda ke tafiya a miqe a kan hanya madaidaiciya? --Qur'an 67:22
    Say, "It is He who has produced you and made for you hearing and vision and hearts; little are you grateful." <> Ka ce: "(Allah) Shine Wanda Ya ƙaga halittarku, Ya sanya muku ji da gani da tunãni, amman kaɗan ce ƙwarai godiyarku!" = [67:23] Ka ce, "Shi ne Wanda Ya qaga halittarku, Ya sanya maku ji da gani da tunani, amman qalilan ne kawai kuke godewa." --Qur'an 67:23
    Say, "It is He who has multiplied you throughout the earth, and to Him you will be gathered." <> Kuma kace "Shi ne Ya halitta ku daga ƙasã, kuma zuwa gareShi ne ake tãshin ku." = [67:24] Kuma kace "Shi ne Ya sanya ku a qasa, kuma zuwa gare Shi ne za tara ku." --Qur'an 67:24
    And they say, "When is this promise, if you should be truthful?" <> Kuma sunã cewa, "Yaushe ne wannan alkawarin zai tabbata in dai kun kasance mãsu gaskiya ne kũ?" = [67:25] Kuma suna qalubalanta, "Yaushe ne wannan alkawarin zai tabbata in dai kun kasance masu gaskiya ne ku?" --Qur'an 67:25
    Say, "The knowledge is only with Allah, and I am only a clear warner." <> Ka ce: "Ilmin a wurin Allah kawai yake, kuma ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyana (gargaɗin)." = [67:26] Ka ce, "Wannan ilmin a wurin ALLAH kawai yake; kuma ni mai bayyana gargadi ne kawai." --Qur'an 67:26
    But when they see it approaching, the faces of those who disbelieve will be distressed, and it will be said, "This is that for which you used to call." <> To, lokacin da suka gan ta (azãbar) a kusa, fuskokin waɗanda suka kãfirta suka mũnana, kuma aka ce (musu) wannan shi ne abin da kuka zamo kuna ƙaryatãwa. = [67:27] To, lokacin da suka gan ta tana aukuwa, fuskokin wadanda suka kafirta za su munana, kuma za zayyana: “Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna qaryatawa. --Qur'an 67:27
    Say, [O Muhammad], "Have you considered: whether Allah should cause my death and those with me or have mercy upon us, who can protect the disbelievers from a painful punishment?" <> Ka ce musu "Idan Allah Ya halaka ni nĩ da wanda ke tãre da ni, ko kuma, Yã yi mana rahama, to, wãne ne zai tserar da kafirai daga wata azãba mai raɗaɗi?" = [67:28] Ka ce, "Idan ALLAH Ya ga dama Ya halaka ni, ni da wanda suke tare da ni, ko kuma Ya yi mana rahamah, to, wane ne zai iya tserar da kafirai daga wata azaba mai radadi?" --Qur'an 67:28
    Say, "He is the Most Merciful; we have believed in Him, and upon Him we have relied. And you will [come to] know who it is that is in clear error." <> Ka ce: "Shĩ ne Mai rahama mun yi ĩmãni da Shi, gare Shi muka dogara, saboda haka zã ku san wanda yake a cikin ɓata bayyananniya." = [67:29] Ka ce: "Shi ne Mafi rahamah; mun yi imani da Shi, gare Shi muka dogara. Saboda haka, za ku san wanda yake a cikin bata bayyananniya." --Qur'an 67:29
    Say, "Have you considered: if your water was to become sunken [into the earth], then who could bring you flowing water?" <> Ka ce: "Ko kun gani, idan ruwanku ya wãyi gari faƙaƙƙe, to, wãne ne zai zo muku da ruwa wani mai ɓuɓɓuga?" = [67:30] Ka ce, "Ko kun gani, idan ruwan shanku ya nutse fa, to, wane ne zai zo maku da ruwan sha?" --Qur'an 67:30
    Nun. By the pen and what they inscribe, <> Ñ. Na rantse da alƙalami da abin da (marubũta) suke rubũtãwa. = --Qur'an 68:1
    You are not, [O Muhammad], by the favor of your Lord, a madman. <> Kai, sabõda ni'imar Ubangijinka, bã mahaukaci kake ba. = --Qur'an 68:2
    And indeed, for you is a reward uninterrupted. <> Kuma, lalle, haƙĩƙa kanã da lãdar da bã ta yankewa. = --Qur'an 68:3
    And indeed, you are of a great moral character. <> Kuma, lalle haƙiƙa kana a kan hãlãyen kirki, manya. = --Qur'an 68:4
    So you will see and they will see <> Don haka, zã ka gani, sũ kuma zã su gani. = --Qur'an 68:5
    Which of you is the afflicted [by a devil]. <> Ga wanenku haukã take. = --Qur'an 68:6
    Indeed, your Lord is most knowing of who has gone astray from His way, and He is most knowing of the [rightly] guided. <> Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkinSa. Kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa. = --Qur'an 68:7
    Then do not obey the deniers. <> Saboda haka kada ka bi mãsu ƙaryatãwa. = --Qur'an 68:8
    They wish that you would soften [in your position], so they would soften [toward you]. <> Sunã fatar ka sassauta, su kuma sũ sassauta. = --Qur'an 68:9
    And do not obey every worthless habitual swearer <> Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce. = --Qur'an 68:10
    [And] scorner, going about with malicious gossip - <> Mai zunɗe, mai yãwo da gulma. = --Qur'an 68:11
    A preventer of good, transgressing and sinful, <> Mai hana alhẽri mai zãlunci, mai zunubi. = --Qur'an 68:12
    Cruel, moreover, and an illegitimate pretender. <> Mai girman kai, bãyan haka kuma la'ĩmi (bã ya son alhẽri). = --Qur'an 68:13
    Because he is a possessor of wealth and children, <> Sabõda yã kasance mai dũkiya da ɗiya. = --Qur'an 68:14
    When Our verses are recited to him, he says, "Legends of the former peoples." <> Idan ana karanta masa ãyõyinMu, sai ya ce: "Tatsũniyõyin mutãnen farko ne." = --Qur'an 68:15
    We will brand him upon the snout. <> Zã Mu yi masa alãma a kan hanci. = --Qur'an 68:16
    Indeed, We have tried them as We tried the companions of the garden, when they swore to cut its fruit in the [early] morning <> Lalle Mun jarrabe su kamar yadda Muka jarrabi mãsu gonar lambu, a lokacin da suka yi rantsuwa, wai lalle zã su girbe amfãninta, suna mãsu asubanci. = --Qur'an 68:17
    Without making exception. <> Kuma (suka yi niyya), bã su kõ tõgẽwa. = --Qur'an 68:18
    So there came upon the garden an affliction from your Lord while they were asleep. <> Wani mai kẽwayãwa daga Ubangijinka ya kẽwayã a kanta, (ya ƙone ta,) alhãli sunã barci. = --Qur'an 68:19
    And it became as though reaped. <> Sai ta wãyi gari (baƙa ƙirin) kamar dare. = --Qur'an 68:20
    And they called one another at morning, <> Sai suka kirãyi jũna, sunã mãsu yin asubanci. = --Qur'an 68:21
    [Saying], "Go early to your crop if you would cut the fruit." <> Cẽwa ku yi sammakõ ga amfãnin gõnarku, idan kun kasance mãsu girbewa. = --Qur'an 68:22
    So they set out, while lowering their voices, <> Sai suka tafi sunã shãwara a ɓõye (sunã cẽwa). = --Qur'an 68:23
    [Saying], "There will surely not enter it today upon you [any] poor person." <> "Lalle kada wani miskĩni ya shigar muku ita a yau!" = --Qur'an 68:24
    And they went early in determination, [assuming themselves] able. <> Kuma suka yi sammako akan (niyyar) rõwa, matuƙar iyãwarsu. = --Qur'an 68:25
    But when they saw it, they said, "Indeed, we are lost; <> Lõkacin da suka gan ta, sai suka ce: "Lalle, mun saki hanya (mun ɓace)!" = --Qur'an 68:26
    Rather, we have been deprived." <> "Ba haka ba, mũ dai, an hana mu ne." = --Qur'an 68:27
    The most moderate of them said, "Did I not say to you, 'Why do you not exalt [Allah]?' " <> Mafificinsu (hankali) ya ce: "Ban gaya muku ba, yã kamata ku tsarkake Allah?" = --Qur'an 68:28
    They said, "Exalted is our Lord! Indeed, we were wrongdoers." <> Suka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle, mu mun kasance azzãlumai." = --Qur'an 68:29
    Then they approached one another, blaming each other. <> Sai suka fuskanci jũna, sunã zargin kansu. = --Qur'an 68:30
    They said, "O woe to us; indeed we were transgressors. <> Suka ce: "Kaitonmu! Lalle, mũ ne muka kasance mãsu ƙẽtare iyãka." = --Qur'an 68:31
    Perhaps our Lord will substitute for us [one] better than it. Indeed, we are toward our Lord desirous." <> "Mai yiwuwa ne Ubangijinmu Ya musanya mana da wani abu da yã fi ta. Lalle, mũ (ba mu yanke ƙauna ba) zuwa ga Ubangijinmu, mãsu kwaɗayi ne." = --Qur'an 68:32
    Such is the punishment [of this world]. And the punishment of the Hereafter is greater, if they only knew. <> Haka dai azãbar take, kuma lalle ne azãbar Lãhira ta fi girma, in da sun kasance zã su iya gãnẽwã. = --Qur'an 68:33
    Indeed, for the righteous with their Lord are the Gardens of Pleasure. <> Lalle ne mãsu taƙawa nã da a wurin Ubangijinsu, gidãjen Aljanna na ni'ima. = --Qur'an 68:34
    Then will We treat the Muslims like the criminals? <> Shin ko zã Mu sanya waɗanda ke bi da ɗa'a kamar mãsu laifi? = --Qur'an 68:35
    What is [the matter] with you? How do you judge? <> Me ya sãme ku, yãya kuke yin hukunci (da haka)? = --Qur'an 68:36
    Or do you have a scripture in which you learn <> Ko kuna da wani littafi, wanda a cikinsa, kuke karantãwa? = --Qur'an 68:37
    That indeed for you is whatever you choose? <> Cẽwã kunã da, a cikinsa lalle (duk) abin da rãyukanku suka zãɓa? = --Qur'an 68:38
    Or do you have oaths [binding] upon Us, extending until the Day of Resurrection, that indeed for you is whatever you judge? <> Kõ kunã (riƙe) da wasu rantsuwõyin alkawari a kanMu, har ya zuwa Rãnar ¡iyãma, cẽwa lalle ne kunã da abin da kuke hukuntã wa kanku? = --Qur'an 68:39
    Ask them which of them, for that [claim], is responsible. <> Ka tambaye su, wãne, a cikinsu, ke lãmuncewã ga sãmun wannan (hukuncin)? = --Qur'an 68:40
    Or do they have partners? Then let them bring their partners, if they should be truthful. <> Kõ sunã da abõkan tãrẽwa (ga wannan ra'ayi)? To, sai su kãwo abõkan tãrayyarsu, idan sun kasance mãsu gaskiya. = --Qur'an 68:41
    The Day the shin will be uncovered and they are invited to prostration but the disbelievers will not be able, <> Ranar da zã a kuranye ƙwabri, kuma a kira su zuwa ga yin sujũda, sai bã zã su iyãwa ba. = --Qur'an 68:42
    Their eyes humbled, humiliation will cover them. And they used to be invited to prostration while they were sound. <> Su fito da idãnu ƙasƙantattu, wulãkanci yana rufe su. Lalle ne a dã sun kasance anã kiran su zuwa, yin sujũdar, alhãli kuwa sunã lãfiya lau, (suka ƙi yi). = --Qur'an 68:43
    So leave Me, [O Muhammad], with [the matter of] whoever denies the Qur'an. We will progressively lead them [to punishment] from where they do not know. <> Sabõda haka ka bar Ni da mai ƙaryata wanna lãbãri (Alƙur'ãni). Zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba. = --Qur'an 68:44
    And I will give them time. Indeed, My plan is firm. <> Ina jinkirtã musu, lalle kaidiNa mai ƙarfi ne. = --Qur'an 68:45
    Or do you ask of them a payment, so they are by debt burdened down? <> Kõ kana tambayar su wata la'ada ne, sabõda haka sũ, daga wannan tãrar, suke jin an nauyaya musu? = --Qur'an 68:46
    Or have they [knowledge of] the unseen, so they write [it] down? <> Ko kuma sunã da ilmin gaibu ne, wãto sunã yin rubũtun (abin da suke faɗã daga gare shi) ne? = --Qur'an 68:47
    Then be patient for the decision of your Lord, [O Muhammad], and be not like the companion of the fish when he called out while he was distressed. <> Sabõda haka, ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar Ma'abũcin kĩfi, alõkacin da ya yi kira, alhãli yana cike da hushi. = --Qur'an 68:48
    If not that a favor from his Lord overtook him, he would have been thrown onto the naked shore while he was censured. <> Ba dõmin ni'ima daga wajen Ubangijinsa tã riske shi ba, lalle ne da an jẽfa shi a cikin wõfintacciyar ƙasa, alhãli yanã abin zargi. = --Qur'an 68:49
    And his Lord chose him and made him of the righteous. <> Sai Ubangijinsa Ya zãɓe shi, sa'an nan Ya sanya shi a cikin mutãnen kirki. = --Qur'an 68:50
    And indeed, those who disbelieve would almost make you slip with their eyes when they hear the message, and they say, "Indeed, he is mad." <> Kuma lalle, ne waɗanda suka kãfirta sunã yin kamar su kãyar da kai sabõ da kallonsu (kallon mãmãki), a lokacin da suke jin karãtun Alƙur'ãni, kuma sunã cẽwa, "Lalle ne shi mahaukaci ne!" = --Qur'an 68:51
    But it is not except a reminder to the worlds. <> Shi (Alƙur'ãni) bai kasance ba, fãce abin tunãtarwa ne ga duka dũniya. = --Qur'an 68:52
    The Inevitable Reality - <> Kiran gaskiya! = --Qur'an 69:1
    What is the Inevitable Reality? <> Mẽne ne kiran gaskiya? = --Qur'an 69:2
    And what can make you know what is the Inevitable Reality? <> Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya? = --Qur'an 69:3
    Thamud and 'Aad denied the Striking Calamity. <> Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya! = --Qur'an 69:4
    So as for Thamud, they were destroyed by the overpowering [blast]. <> To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani. = --Qur'an 69:5
    And as for 'Aad, they were destroyed by a screaming, violent wind <> Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi. = --Qur'an 69:6
    Which Allah imposed upon them for seven nights and eight days in succession, so you would see the people therein fallen as if they were hollow trunks of palm trees. <> (Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi. = --Qur'an 69:7
    Then do you see of them any remains? <> To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu? = --Qur'an 69:8
    And there came Pharaoh and those before him and the overturned cities with sin. <> Kuma Fir'auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi. = --Qur'an 69:9
    And they disobeyed the messenger of their Lord, so He seized them with a seizure exceeding [in severity]. <> Dõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu mai ƙãruwar (tsanani). = --Qur'an 69:10
    Indeed, when the water overflowed, We carried your ancestors in the sailing ship <> Lalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙẽtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan. = --Qur'an 69:11
    That We might make it for you a reminder and [that] a conscious ear would be conscious of it. <> Dõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi). = --Qur'an 69:12
    Then when the Horn is blown with one blast <> To, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya. = --Qur'an 69:13
    And the earth and the mountains are lifted and leveled with one blow - <> Kuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya. = --Qur'an 69:14
    Then on that Day, the Resurrection will occur, <> A ran nan, mai aukuwa zã ta auku. = --Qur'an 69:15
    And the heaven will split [open], for that Day it is infirm. <> Kuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce. = --Qur'an 69:16
    And the angels are at its edges. And there will bear the Throne of your Lord above them, that Day, eight [of them]. <> Kuma malã'iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã'iku) takwas na ɗauke da Al'arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar. = --Qur'an 69:17
    That Day, you will be exhibited [for judgement]; not hidden among you is anything concealed. <> A rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓõyẽwa. = --Qur'an 69:18
    So as for he who is given his record in his right hand, he will say, "Here, read my record! <> To, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa), "Ku karɓa, ku karanta littafina." = --Qur'an 69:19
    Indeed, I was certain that I would be meeting my account." <> "Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne." = --Qur'an 69:20
    So he will be in a pleasant life - <> Sabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda. = --Qur'an 69:21
    In an elevated garden, <> A cikin Aljanna maɗaukakiya. = --Qur'an 69:22
    Its [fruit] to be picked hanging near. <> Nunannun 'yã'yan itãcenta makusantã ne (ga mai son ɗĩba), = --Qur'an 69:23
    [They will be told], "Eat and drink in satisfaction for what you put forth in the days past." <> (Ana ce musu) "Ku ci, kuma ku sha a cikin ni'ima, sabõda abin da kuka gabãtar a cikin kwãnukan da suka shige." = --Qur'an 69:24
    But as for he who is given his record in his left hand, he will say, "Oh, I wish I had not been given my record <> Kuma wanda aka bai wa littãfinsa ga hagunsa, sai ya ce: "Kaitona, ba a kãwo mini littãfina ba!" = --Qur'an 69:25
    And had not known what is my account. <> "Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisãbina ba!" = --Qur'an 69:26
    I wish my death had been the decisive one. <> "In dã dai ita, tã kasance mai halakã ni gabã ɗaya ce! = --Qur'an 69:27
    My wealth has not availed me. <> "Dukiyãta ba ta wadatar da ni ba!" = --Qur'an 69:28
    Gone from me is my authority." <> "Ĩkona ya ɓace mini!" = --Qur'an 69:29
    [Allah will say], "Seize him and shackle him. <> (Sai a ce wa malã'iku) "Ku kãmã shi, sa'an nan ku sanyã shi a cikin ƙuƙumi." = --Qur'an 69:30
    Then into Hellfire drive him. <> "Sa'an nan, a cikin Jahĩm, ku ƙõna shi." = --Qur'an 69:31
    Then into a chain whose length is seventy cubits insert him." <> "Sa'an nan, acikin sarƙa, tsawonta zirã'i saba'in, sai ku sanya shi." = --Qur'an 69:32
    Indeed, he did not used to believe in Allah, the Most Great, <> "Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin ĩmãni da Allah, Mai girma!" = --Qur'an 69:33
    Nor did he encourage the feeding of the poor. <> "Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci!" = --Qur'an 69:34
    So there is not for him here this Day any devoted friend <> "Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi." = --Qur'an 69:35
    Nor any food except from the discharge of wounds; <> "Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn." = --Qur'an 69:36
    None will eat it except the sinners. <> "Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci." = --Qur'an 69:37
    So I swear by what you see <> To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba, = --Qur'an 69:38
    And what you do not see <> Da abin da bã ku iya gani. = --Qur'an 69:39
    [That] indeed, the Qur'an is the word of a noble Messenger. <> Lalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne. = --Qur'an 69:40
    And it is not the word of a poet; little do you believe. <> Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata. = --Qur'an 69:41
    Nor the word of a soothsayer; little do you remember. <> Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa. = --Qur'an 69:42
    [It is] a revelation from the Lord of the worlds. <> Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka. = --Qur'an 69:43
    And if Muhammad had made up about Us some [false] sayings, <> Kuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu. = --Qur'an 69:44
    We would have seized him by the right hand; <> Dã Mun kãma shi da dãma. = --Qur'an 69:45
    Then We would have cut from him the aorta. <> sa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã. = --Qur'an 69:46
    And there is no one of you who could prevent [Us] from him. <> Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbarMu) daga gare shi. = --Qur'an 69:47
    And indeed, the Qur'an is a reminder for the righteous. <> Kuma lalle ne shi (Alƙur'ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa. = --Qur'an 69:48
    And indeed, We know that among you are deniers. <> Kuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa. = --Qur'an 69:49
    And indeed, it will be [a cause of] regret upon the disbelievers. <> Kuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai. = --Qur'an 69:50
    And indeed, it is the truth of certainty. <> Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙshẽni. = --Qur'an 69:51
    So exalt the name of your Lord, the Most Great. <> Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma. = --Qur'an 69:52
    A supplicant asked for a punishment bound to happen <> Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa. = --Qur'an 70:1
    To the disbelievers; of it there is no preventer. <> Ga kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa. = --Qur'an 70:2
    [It is] from Allah, owner of the ways of ascent. <> Daga Allah Mai matãkala. = --Qur'an 70:3
    The angels and the Spirit will ascend to Him during a Day the extent of which is fifty thousand years. <> Malã'iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne. = --Qur'an 70:4
    So be patient with gracious patience. <> Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo. = --Qur'an 70:5
    Indeed, they see it [as] distant, <> Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa. = --Qur'an 70:6
    But We see it [as] near. <> Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa. = --Qur'an 70:7
    On the Day the sky will be like murky oil, <> Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa. = --Qur'an 70:8
    And the mountains will be like wool, <> Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi. = --Qur'an 70:9
    And no friend will ask [anything of] a friend, <> Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake. = --Qur'an 70:10
    They will be shown each other. The criminal will wish that he could be ransomed from the punishment of that Day by his children <> Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa, = --Qur'an 70:11
    And his wife and his brother <> Da matarsa da ɗan'uwansa. = --Qur'an 70:12
    And his nearest kindred who shelter him <> Da danginsa, mãsu tattarã shi. = --Qur'an 70:13
    And whoever is on earth entirely [so] then it could save him. <> Da wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa'an nan fansar, ta tsĩrar da shi. = --Qur'an 70:14
    No! Indeed, it is the Flame [of Hell], <> A'aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã, = --Qur'an 70:15
    A remover of exteriors. <> Mai twãle fãtar goshi. = --Qur'an 70:16
    It invites he who turned his back [on truth] and went away [from obedience] <> Tanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai. = --Qur'an 70:17
    And collected [wealth] and hoarded. <> Ya tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka. = --Qur'an 70:18
    Indeed, mankind was created anxious: <> Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi. = --Qur'an 70:19
    When evil touches him, impatient, <> Idan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri. = --Qur'an 70:20
    And when good touches him, withholding [of it], <> Kuma idan alhẽri ya shãfe shi, ya yi rõwa. = --Qur'an 70:21
    Except the observers of prayer - <> Sai mãsu yin salla, = --Qur'an 70:22
    Those who are constant in their prayer <> Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne. = --Qur'an 70:23
    And those within whose wealth is a known right <> Kuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne. = --Qur'an 70:24
    For the petitioner and the deprived - <> Ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon. = --Qur'an 70:25
    And those who believe in the Day of Recompense <> Da waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako. = --Qur'an 70:26
    And those who are fearful of the punishment of their Lord - <> Da waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro. = --Qur'an 70:27
    Indeed, the punishment of their Lord is not that from which one is safe - <> Lalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincẽwaba ce. = --Qur'an 70:28
    And those who guard their private parts <> Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne. = --Qur'an 70:29
    Except from their wives or those their right hands possess, for indeed, they are not to be blamed - <> Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne. = --Qur'an 70:30
    But whoever seeks beyond that, then they are the transgressors - <> To, duk wanda ya nẽmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka. = --Qur'an 70:31
    And those who are to their trusts and promises attentive <> Kuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne. = --Qur'an 70:32
    And those who are in their testimonies upright <> Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgẽwa ne. = --Qur'an 70:33
    And those who [carefully] maintain their prayer: <> Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarẽwa ne. = --Qur'an 70:34
    They will be in gardens, honored. <> Waɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne = --Qur'an 70:35
    So what is [the matter] with those who disbelieve, hastening [from] before you, [O Muhammad], <> Mẽ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar (gudu). = --Qur'an 70:36
    [To sit] on [your] right and [your] left in separate groups? <> Daga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama'a-jama'a! = --Qur'an 70:37
    Does every person among them aspire to enter a garden of pleasure? <> Shin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne (ba da wani aiki ba)? = --Qur'an 70:38
    No! Indeed, We have created them from that which they know. <> A'aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani. = --Qur'an 70:39
    So I swear by the Lord of [all] risings and settings that indeed We are able <> Sabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne. = --Qur'an 70:40
    To replace them with better than them; and We are not to be outdone. <> Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba. = --Qur'an 70:41
    So leave them to converse vainly and amuse themselves until they meet their Day which they are promised - <> Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita). = --Qur'an 70:42
    The Day they will emerge from the graves rapidly as if they were, toward an erected idol, hastening. <> Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa. = --Qur'an 70:43
    Their eyes humbled, humiliation will cover them. That is the Day which they had been promised. <> Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa.) = --Qur'an 70:44
    Indeed, We sent Noah to his people, [saying], "Warn your people before there comes to them a painful punishment." <> Lalle ne Mun aiki Nũhu zuwa ga mutãnensa, cẽwa ka yi gargaɗi ga mutãnenka gabãnin wata azãba mai raɗaɗi ta zo musu. = --Qur'an 71:1
    He said, "O my people, indeed I am to you a clear warner, <> Ya ce: "Ya mutãnena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanãwa." = --Qur'an 71:2
    [Saying], 'Worship Allah, fear Him and obey me. <> "Cewa ku bauta wa Allah, ku ji tsõronSa, kuma ku bĩ ni." = --Qur'an 71:3
    Allah will forgive you of your sins and delay you for a specified term. Indeed, the time [set by] Allah, when it comes, will not be delayed, if you only knew.' " <> "Allah zai gãfarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, dã kun kasance masana (ga abin da nake faɗã dã, kun bar kãfirci)." = --Qur'an 71:4
    He said, "My Lord, indeed I invited my people [to truth] night and day. <> Nũhu) ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirãyi mutãnena, a cikin dare da yini." = --Qur'an 71:5
    But my invitation increased them not except in flight. <> "To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu (daga gare ni)." = --Qur'an 71:6
    And indeed, every time I invited them that You may forgive them, they put their fingers in their ears, covered themselves with their garments, persisted, and were arrogant with [great] arrogance. <> "Kuma lalle ne ni, kõ da yaushe na kirãye su dõmin Ka gãfarta musu, sai su sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufãfinsu, su dõge ga yin laifi. Sun yi girman kai iyãkar girman kai." = --Qur'an 71:7
    Then I invited them publicly. <> "Sa'an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane." = --Qur'an 71:8
    Then I announced to them and [also] confided to them secretly <> "Sa'an nan lalle ne, na yi yẽkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri." = --Qur'an 71:9
    And said, 'Ask forgiveness of your Lord. Indeed, He is ever a Perpetual Forgiver. <> "Shi na ce, 'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne." = --Qur'an 71:10
    He will send [rain from] the sky upon you in [continuing] showers <> "Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga." = --Qur'an 71:11
    And give you increase in wealth and children and provide for you gardens and provide for you rivers. <> "Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya, Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna." = --Qur'an 71:12
    What is [the matter] with you that you do not attribute to Allah [due] grandeur <> "Me ya sãme ku, bã ku fãtar sãmun natsuwa daga Allah," = --Qur'an 71:13
    While He has created you in stages? <> "Alhãli kuwa, lalle ne, Ya halitta. ku, a cikin hãlãye?" = --Qur'an 71:14
    Do you not consider how Allah has created seven heavens in layers <> "Ba ku ga yadda Allah Ya halitta wasu sammai bakwai ɗabaƙõƙĩ a kan jũna ba?" = --Qur'an 71:15
    And made the moon therein a [reflected] light and made the sun a burning lamp? <> "Ya sanya watã a cikinsu, yana mai haske, Ya sanya rãnã babbar fitila?" = --Qur'an 71:16
    And Allah has caused you to grow from the earth a [progressive] growth. <> "Kuma Allah Ya tsirar da ku daga ƙasa (kamar ganye) tsirarwa." = --Qur'an 71:17
    Then He will return you into it and extract you [another] extraction. <> "Sa'an nan Ya mayar da ku a cikinta, kuma Ya fitar da ku fitarwa." = --Qur'an 71:18
    And Allah has made for you the earth an expanse <> "Kuma Allah Ya sanya muku ƙasa shimfidaɗɗiya." = --Qur'an 71:19
    That you may follow therein roads of passage.' " <> "Dõmin ku shiga a cikinta, hanyõyi mãsu fãɗi." = --Qur'an 71:20
    Noah said, "My Lord, indeed they have disobeyed me and followed him whose wealth and children will not increase him except in loss. <> Nũhu ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne sũ sun saɓa mini sun bi wanda dukiyarsa da ɗiyansa ba su ƙãre shi da kõme ba sai da hasãra." = --Qur'an 71:21
    And they conspired an immense conspiracy. <> "Kuma sun yi wani mãkirci, mãkirci babba." = --Qur'an 71:22
    And said, 'Never leave your gods and never leave Wadd or Suwa' or Yaghuth and Ya'uq and Nasr. <> "Kuma suka ce: Faufau kada ku bar gumãkanku, kuma faufau, kada ku bar wadda, kuma kada ku bar suwã kuma kada ku bar Yagũsa da Ya'ũƙa da Nasra." = --Qur'an 71:23
    And already they have misled many. And, [my Lord], do not increase the wrongdoers except in error." <> "Kuma lalle ne sun ɓatar da (mutãne) mãsu yawa, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai (kõme) sai ɓata." = --Qur'an 71:24
    Because of their sins they were drowned and put into the Fire, and they found not for themselves besides Allah [any] helpers. <> Sabõda laifukansu na ganganci aka nutsar da su, sa'an nan aka sanya su a wuta. Saboda haka ba su sãmã wa kansu wani mataimaki wanin Allah ba. = --Qur'an 71:25
    And Noah said, "My Lord, do not leave upon the earth from among the disbelievers an inhabitant. <> Kuma Nũhu ya ce: "Ya Ublngijina! Kada Ka bari, a kan ƙasa, daga cikin kãfirai, wanda ke zama a cikin gida." = --Qur'an 71:26
    Indeed, if You leave them, they will mislead Your servants and not beget except [every] wicked one and [confirmed] disbeliever. <> "Lalle ne, Kai idan Ka bar su, zã su ɓatar da bãyinKa, kuma bã zã su haifi kowa ba fãce fãjiri mai yawan kãfirci" = --Qur'an 71:27
    My Lord, forgive me and my parents and whoever enters my house a believer and the believing men and believing women. And do not increase the wrongdoers except in destruction." <> "Ya Ubanginjina! Ka yi mini gãfara (ni) da mahaifana biyu, da wanda ya shiga gidana, yana mai ĩmãni, da mũminai maza da mũminai mãtã, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai kõme sai halaka." = --Qur'an 71:28
    Say, [O Muhammad], "It has been revealed to me that a group of the jinn listened and said, 'Indeed, we have heard an amazing Qur'an. <> Ka ce: "An yi wahayi zuwa gare ni cewa wasu jama'a na aljannu sun saurũri (karatuna), sai suka ce: Lalle ne mũ mun ji wani abin karantãwa (Alƙui'ãni), mai ban mãmãki." = --Qur'an 72:1
    It guides to the right course, and we have believed in it. And we will never associate with our Lord anyone. <> "Yana nũni zuwa ga hanyar ƙwarai, sabõda haka mun yi ĩmãni da shi bã zã mu kõma bautã wa Ubangijinmu tãre da kõwa ba." = --Qur'an 72:2
    And [it teaches] that exalted is the nobleness of our Lord; He has not taken a wife or a son <> "Kuma lalle ne shĩ girman Ubangijinmu, Ya ɗaukaka, bai riƙi mãta ba, kuma bai riƙi ɗã ba." = --Qur'an 72:3
    And that our foolish one has been saying about Allah an excessive transgression. <> "Kuma lalle ne shi, wãwanmu ya kasance yana faɗar abin da ya ƙetare haddi ga Allah." = --Qur'an 72:4
    And we had thought that mankind and the jinn would never speak about Allah a lie. <> "Kuma lalle ne mũ, mun yi zaton mutum da aljani bã zã su iya faɗar ƙarya ba ga Allah." = --Qur'an 72:5
    And there were men from mankind who sought refuge in men from the jinn, so they [only] increased them in burden. <> "Kuma lalle ne shi wasu maza daga cikin mutãne, sun kasance sunã nẽman tsari da wasu maza daga cikin aljannu, sabõda haka suka ƙara musu girman kai." = --Qur'an 72:6
    And they had thought, as you thought, that Allah would never send anyone [as a messenger]. <> "Kuma lalle ne sũ, sun yi zato, kamar yadda kuka yi zato, cewa Allah bã zai aiko kowa ba." = --Qur'an 72:7
    And we have sought [to reach] the heaven but found it filled with powerful guards and burning flames. <> "Kuma lalle ne mũ mun nẽmi (hawan) sama, sai muka, sãme ta an cika ta da tsaro mai tsanani da kuma yũlãye." = --Qur'an 72:8
    And we used to sit therein in positions for hearing, but whoever listens now will find a burning flame lying in wait for him. <> "Kuma lalle ne mũ, mun kasance muna zama daga garẽta, a wurãren zama dõmin saurare. To wanda ya yi saurãre a yanzu, zai sãmi yũla, mai dãko dõminsa." = --Qur'an 72:9
    And we do not know [therefore] whether evil is intended for those on earth or whether their Lord intends for them a right course. <> "Kuma lalle ne mũ ba mu sani ba, shin, sharri ne aka yi nufi ga waɗanda ke cikin ƙasa, ko Ubangijinsu Yã yi nufin shiriya a gare su ne?" = --Qur'an 72:10
    And among us are the righteous, and among us are [others] not so; we were [of] divided ways. <> "Kuma lalle ne mũ, akwai sãlaihai a cikinmu, kuma akwai a cikinmu waɗanda ba haka bã mun kasance ƙungiyõyi dabam-dabam." = --Qur'an 72:11
    And we have become certain that we will never cause failure to Allah upon earth, nor can we escape Him by flight. <> "Kuma lalle ne mũ mun tabbatã bã zã mu buwãyi Allah ba, a cikin ƙasa, kuma bã zã mu buwãye Shi da gudu ba." = --Qur'an 72:12
    And when we heard the guidance, we believed in it. And whoever believes in his Lord will not fear deprivation or burden. <> "Kuma lalle ne mũ, a lõkacin da muka ji shiriya, mun yi ĩmãni da ita. To wanda ya yi ĩimãni da Uhangijinsa, bã zai ji tsõron nakkasa ba, kuma bã zai ji tsõron zãlunci ba." = --Qur'an 72:13
    And among us are Muslims [in submission to Allah], and among us are the unjust. And whoever has become Muslim - those have sought out the right course. <> "Kuma lalle ne mũ akwai a cikinmu, waɗanda suka mĩƙa wuya, kuma akwai a cikinmu karkatattu. to, wanda ya mĩƙa wuya waɗancan kam sun nufi shiryuwa." = --Qur'an 72:14
    But as for the unjust, they will be, for Hell, firewood.' <> "Kuma amma karkatattu sai suka kasance makãmashi ga Jahannama." = --Qur'an 72:15
    And [Allah revealed] that if they had remained straight on the way, We would have given them abundant provision <> "Kuma dã sun tsayu sõsai a kan hanya, dã lalle Mun shãyar da su ruwa mai yawa." = --Qur'an 72:16
    So We might test them therein. And whoever turns away from the remembrance of his Lord He will put into arduous punishment. <> "Domin Mu jarraba su a ciki, kuma wanda ya kau da kai daga tuna Ubangijinsa, Ubangijinsa zai shigar da shi azãba mai hauhawa." = --Qur'an 72:17
    And [He revealed] that the masjids are for Allah, so do not invoke with Allah anyone. <> "Kuma lalle ne wurãren sujada na Allah ne, saboda haka kada ku kira kõwa tãre da Allah (da su, a cikinsu)." = --Qur'an 72:18
    And that when the Servant of Allah stood up supplicating Him, they almost became about him a compacted mass." <> "Kuma, lalle ne shi, a lõkacin da bãwan Allah ke kiran Sa sun yi kusa su zama kamar shirgi a kansa." = --Qur'an 72:19
    Say, [O Muhammad], "I only invoke my Lord and do not associate with Him anyone." <> Ka ce: "lna kiran Ubangijina ne kawai, kuma bã zan tãra kowa da Shi ba." = --Qur'an 72:20
    Say, "Indeed, I do not possess for you [the power of] harm or right direction." <> Ka ce: "Lalle ne, nĩ bã ni mallakar wata cũta gare ku, kuma bã ni mallakar wani alhẽri." = --Qur'an 72:21
    Say, "Indeed, there will never protect me from Allah anyone [if I should disobey], nor will I find in other than Him a refuge. <> Ka ce: "Lalle ne, nĩ kõwa bã ya iya cẽtona daga Allah, kuma bã zan iya sãmun mafaka ba daga gare Shi." = --Qur'an 72:22
    But [I have for you] only notification from Allah, and His messages." And whoever disobeys Allah and His Messenger - then indeed, for him is the fire of Hell; they will abide therein forever. <> "Fãce iyarwa, daga Allah, da manzancinsa. To, wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, to, lalle yana da wutar Jahannama suna mãsu dawwama a cikinta, har abada." = --Qur'an 72:23
    [The disbelievers continue] until, when they see that which they are promised, then they will know who is weaker in helpers and less in number. <> Har idan sun ga abin da ake yi musu gargaɗi da shi, to, zã su san wanda ya zama mafi raunin mataimaki da mafi ƙarancin adadi. = --Qur'an 72:24
    Say, "I do not know if what you are promised is near or if my Lord will grant for it a [long] period." <> Ka ce: "Ban sani ba a kusa ne abin da ake yi muku gargaɗi da shi, ko Ubangijina Ya sanya maSa dõgon ajali!" = --Qur'an 72:25
    [He is] Knower of the unseen, and He does not disclose His [knowledge of the] unseen to anyone <> "Shi ɗai ne Masanin fake sabõda haka, bã Ya bayyana gaibinSa ga kowa." = --Qur'an 72:26
    Except whom He has approved of messengers, and indeed, He sends before each messenger and behind him observers <> "Fãce ga wanda Yã yarda da shi, wato wani manzo sa'an nan lalle ne, zai sanya gãdi a gaba gare shi da bãya gare shi." = --Qur'an 72:27
    That he may know that they have conveyed the messages of their Lord; and He has encompassed whatever is with them and has enumerated all things in number. <> "Dõmin Ya san lalle, sun iyar da sãƙonnin Ubangijinsu, kuma (Shi Ubangijin) Yã kẽwaye su da sani, kuma Yã lissafe dukan kõme da ƙididdiga." = --Qur'an 72:28
    O you who wraps himself [in clothing], <> Yã wanda ya lulluɓe! = --Qur'an 73:1
    Arise [to pray] the night, except for a little - <> Ka tsayu domin yin salla a cikin dare (duka) fãce kaɗan. = --Qur'an 73:2
    Half of it - or subtract from it a little <> Rabinsa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi. = --Qur'an 73:3
    Or add to it, and recite the Qur'an with measured recitation. <> Ko ka ƙara kansa kuma ka kyautata karanta Alƙu'ãni, daki daki. = --Qur'an 73:4
    Indeed, We will cast upon you a heavy word. <> Lalle ne, Mũ, zã Mu jẽfa maka magana mai nauyi. = --Qur'an 73:5
    Indeed, the hours of the night are more effective for concurrence [of heart and tongue] and more suitable for words. <> Lalle ne, tashin dare shi ne mafi tsananin natsuwa, kuma mafi daidaituwa ga magana. = --Qur'an 73:6
    Indeed, for you by day is prolonged occupation. <> Lalle ne, kanã da, a cikin yini, wani tasĩhi mai tsawo. = --Qur'an 73:7
    And remember the name of your Lord and devote yourself to Him with [complete] devotion. <> Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, kuma ka yanke (ƙauna daga kowa ka koma) zuwa gare Shi, yankewa. = --Qur'an 73:8
    [He is] the Lord of the East and the West; there is no deity except Him, so take Him as Disposer of [your] affairs. <> Shi ne Ubangijin mafitar rãnã da mafãɗarta, bãbu abin bautawa fãce Shi. Sabõda haka ka riƙe Shi wakili. = --Qur'an 73:9
    And be patient over what they say and avoid them with gracious avoidance. <> Kuma ka yi haƙuri ga abin da suke faɗã, kuma ka ƙaurace musu, ƙauracẽwa mai kyãwo. = --Qur'an 73:10
    And leave Me with [the matter of] the deniers, those of ease [in life], and allow them respite a little. <> Kuma ka bar Ni da mãsu ƙaryatãwa, mawadãta, kuma ka jinkirta musu kaɗan. = --Qur'an 73:11
    Indeed, with Us [for them] are shackles and burning fire <> Lalle ne, a wurinMu, akwai wasu marũruwa mãsu nauyi da Jahĩm. = --Qur'an 73:12
    And food that chokes and a painful punishment - <> Da wani abinci mai mãƙara da azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 73:13
    On the Day the earth and the mountains will convulse and the mountains will become a heap of sand pouring down. <> Rãnar da ƙasa ke raurawa, da duwãtsu kuma duwãtsu su kasance tudun rairayi mai malãlã. = --Qur'an 73:14
    Indeed, We have sent to you a Messenger as a witness upon you just as We sent to Pharaoh a messenger. <> Lalle ne, Mũ. Mun aika zuwa gare ku, wani Manzo mai shaida a kanku, kamar yadda Muka aika wani Manzo zuwaga Fir'auna, = --Qur'an 73:15
    But Pharaoh disobeyed the messenger, so We seized him with a ruinous seizure. <> Sai Fir'auna ya saɓa wa Manzon, saboda haka Muka kãma shi kãmu mai tsanani. = --Qur'an 73:16
    Then how can you fear, if you disbelieve, a Day that will make the children white- haired? <> To, yãya, idan kun kãfirta, zã ku kãre (azabar) wani yini mai mayar da yãra (tsofaffi) mãsu hurhura. = --Qur'an 73:17
    The heaven will break apart therefrom; ever is His promise fulfilled. <> Sama za ta tsãge a cikinsa, wa'adinsa yã kasance mai aukuwa. = --Qur'an 73:18
    Indeed, this is a reminder, so whoever wills may take to his Lord a way. <> Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, sai dai wanda ya so, ya kãma hanyar ƙwarai zuwa ga Ubangijinsa. = --Qur'an 73:19
    Indeed, your Lord knows, [O Muhammad], that you stand [in prayer] almost two thirds of the night or half of it or a third of it, and [so do] a group of those with you. And Allah determines [the extent of] the night and the day. He has known that you [Muslims] will not be able to do it and has turned to you in forgiveness, so recite what is easy [for you] of the Qur'an. He has known that there will be among you those who are ill and others traveling throughout the land seeking [something] of the bounty of Allah and others fighting for the cause of Allah. So recite what is easy from it and establish prayer and give zakah and loan Allah a goodly loan. And whatever good you put forward for yourselves - you will find it with Allah. It is better and greater in reward. And seek forgiveness of Allah. Indeed, Allah is Forgiving and Merciful. <> Lalle ne, Ubangijinka Yã sani cẽwa, kai kana tsayuwa a kusan kashi biyu daga uku na dare, da rabinsa, da sulusinsa, tãre da wani ɓangare na waɗanda ke tãre da kai. Allah Yake iya ƙaddara dare da yini, Ya san bã zã ku iya lissafa shi ba, sabõda haka Ya karɓi tubarku sai, ku karanta abin da ya sauƙaƙa na Alƙur'ãni. Ya san wasu daga cikinku, zã su yi cĩwo, kuma wasu zã su yi tafiya cikin ƙasa suna nẽman falalar Allah da fatauci, kuma wasu zã su yi yãƙi a cikin banyar Allah. Sabõda haka ku karanta abin da ya sauƙaƙa daga gare shi, kuma ku tsai da salla kuma ku bãyar da zakka, kumaa ku bai wa Allah rance, rance mai kyãwo. Kuma abin da kuka gabatar dõmin kanku, na alhẽri, zã ku sãme shi a wurin Allah zai kasance mafifici (daga wanda kuka ajiye) kuma zai fi girma ga sakamako, kuma ku rõƙi Allah gãfara; lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. = --Qur'an 73:20
    O you who covers himself [with a garment], <> Yã wanda ya lulluɓa da mayãfi. = --Qur'an 74:1
    Arise and warn <> Ka tãshi dõmin ka yi gargaɗi = --Qur'an 74:2
    And your Lord glorify <> Kuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi, = --Qur'an 74:3
    And your clothing purify <> Kuma tutãfinka, sai ka tsarkake su, = --Qur'an 74:4
    And uncleanliness avoid <> Kuma gumãka, sai ka ƙaurace musu. = --Qur'an 74:5
    And do not confer favor to acquire more <> Kada ka yi kyauta kana nẽman ƙãri = --Qur'an 74:6
    But for your Lord be patient. <> Kuma sabõda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure = --Qur'an 74:7
    And when the trumpet is blown, <> To, idan aka yi bũsa a cikin ƙaho. = --Qur'an 74:8
    That Day will be a difficult day <> To, wannan, a rãnar nan, yini ne mai wuya = --Qur'an 74:9
    For the disbelievers - not easy. <> A kan kãfirai, bã mai sauƙi ba ne. = --Qur'an 74:10
    Leave Me with the one I created alone <> Ka bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai, = --Qur'an 74:11
    And to whom I granted extensive wealth <> Kuma Na sanya masa dũkiya shimfiɗaɗɗiya = --Qur'an 74:12
    And children present [with him] <> Da ɗiyã halartattu, = --Qur'an 74:13
    And spread [everything] before him, easing [his life]. <> Kuma Na shimfiɗa? masa kõme shimfiɗãwa. = --Qur'an 74:14
    Then he desires that I should add more. <> Sa'an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri! = --Qur'an 74:15
    No! Indeed, he has been toward Our verses obstinate. <> Faufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyinMu, mai tsaurin kai. = --Qur'an 74:16
    I will cover him with arduous torment. <> Zã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa. = --Qur'an 74:17
    Indeed, he thought and deliberated. <> Lalle ne, Shi, yã yi tunãni, kuma yã ƙaddara (abin da zai faɗã game da Alƙur'ãni) = --Qur'an 74:18
    So may he be destroyed [for] how he deliberated. <> Sabõda haka, aka la'ane shi, kamar yadda ya ƙaddara. = --Qur'an 74:19
    Then may he be destroyed [for] how he deliberated. <> Sa'an nan, aka la'ane shi kamar yadda ya ƙaddara. = --Qur'an 74:20
    Then he considered [again]; <> Sa'an nan, ya yi tunãni = --Qur'an 74:21
    Then he frowned and scowled; <> Sa'an nan, ya gintse huska? kuma ya yi murtuk. = --Qur'an 74:22
    Then he turned back and was arrogant <> Sa'an nan, ya jũya bãya, kuma ya bunƙãsa, = --Qur'an 74:23
    And said, "This is not but magic imitated [from others]. <> Sai ya ce: "Wannan abu dai bã kõme ba ne fãce wani sihiri, wanda aka ruwaito." = --Qur'an 74:24
    This is not but the word of a human being." <> "Wannan maganar mutum dai ce." = --Qur'an 74:25
    I will drive him into Saqar. <> Zã Ni ƙõna shi da Saƙar. = --Qur'an 74:26
    And what can make you know what is Saqar? <> Kuma mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽwa Saƙar! = --Qur'an 74:27
    It lets nothing remain and leaves nothing [unburned], <> Bã ta ragẽwa, kuma bã ta bari. = --Qur'an 74:28
    Blackening the skins. <> Mai nãcẽwa ga jiki ce (da (ƙũna). = --Qur'an 74:29
    Over it are nineteen [angels]. <> A kanta akwai (matsara) gõma shã tara. = --Qur'an 74:30
    And We have not made the keepers of the Fire except angels. And We have not made their number except as a trial for those who disbelieve - that those who were given the Scripture will be convinced and those who have believed will increase in faith and those who were given the Scripture and the believers will not doubt and that those in whose hearts is hypocrisy and the disbelievers will say, "What does Allah intend by this as an example?" Thus does Allah leave astray whom He wills and guides whom He wills. And none knows the soldiers of your Lord except Him. And mention of the Fire is not but a reminder to humanity. <> Kuma ba Mu sanya ma'abũta wutã (wãto matsaranta) ba, fãce malã'iku, kuma ba Mu sanya adadinsu (gõma sha tara) ba, fãce dõmin fitina ga waɗanda suka kãfirta domin waɗanda aka bai wa littãfi su sãmi yaƙĩni kuma waɗanda suka yi ĩmãni su ƙãra ĩmãni, kuma waɗanda aka bai wa littãfi da mũminai bã zã su yi shakka ba, kuma domin wa ɗanda a cikin zukatansu akwai wata cuta da kãfirai su ce: "Mẽ Allah Yake nufi da wannan, ya kasance misãli?" Haka dai Allah ke ɓatar da wanda Ya so, kuma Ya shiryar da wanda ya so. Kuma bãbu wanda ya san mayãƙan Ubangijinka fãce Shi, kuma ita (wutar) ba ta kasance ba fãce wata tunãtarwa ce ga mutum. = --Qur'an 74:31
    No! By the moon <> A'aha! Ina rantsuwa da watã. = --Qur'an 74:32
    And [by] the night when it departs <> Da dare a lõkacin da ya jũyar da baya. = --Qur'an 74:33
    And [by] the morning when it brightens, <> Da sãfiya idan ta wãye. = --Qur'an 74:34
    Indeed, the Fire is of the greatest [afflictions] <> Ita (wutar) ɗayan manyan masĩfũ? ce. = --Qur'an 74:35
    As a warning to humanity - <> Mai gargaɗĩ ce ga mutum. = --Qur'an 74:36
    To whoever wills among you to proceed or stay behind. <> Ga wanda ya so, daga cikinku, ya gabãta ko ya jinkirta. = --Qur'an 74:37
    Every soul, for what it has earned, will be retained <> Kõwane rai ga abin da ya aikata jingina ce. = --Qur'an 74:38
    Except the companions of the right, <> Fãce mutãnen dãma. = --Qur'an 74:39
    [Who will be] in gardens, questioning each other <> A cikin Aljanna suna tambayar jũna. = --Qur'an 74:40
    About the criminals, <> Game da mãsu laifi. = --Qur'an 74:41
    [And asking them], "What put you into Saqar?" <> (Su ce musu) "Me ya shigar da ku a cikin Saƙar?" = --Qur'an 74:42
    They will say, "We were not of those who prayed, <> Suka ce: "Ba mu kasance munã a cikin mãsu salla ba." = --Qur'an 74:43
    Nor did we used to feed the poor. <> "Kuma ba mu kasance muna ciyar da matalautã ba." = --Qur'an 74:44
    And we used to enter into vain discourse with those who engaged [in it], <> "Kuma mun kasance muna kũtsãwa tãre da mãsu kũtsãwa." = --Qur'an 74:45
    And we used to deny the Day of Recompense <> "Mun kasance munã ƙaryata rãnar sãkamako." = --Qur'an 74:46
    Until there came to us the certainty." <> "Har gaskiya (wãto mutuwa) ta zo mana." = --Qur'an 74:47
    So there will not benefit them the intercession of [any] intercessors. <> Sabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba. = --Qur'an 74:48
    Then what is [the matter] with them that they are, from the reminder, turning away <> Haba! Me ya same su, suka zama mãsu bijirewa daga wa'azin gaskiya. = --Qur'an 74:49
    As if they were alarmed donkeys <> Kamar dai sũ, jãkuna firgitattu ne. = --Qur'an 74:50
    Fleeing from a lion? <> Sun gudu daga zãki. = --Qur'an 74:51
    Rather, every person among them desires that he would be given scriptures spread about. <> A'aha! Kõwãne mutum daga cikinsu yanã son a zo masa da takardu (da sũnansa) ana wãtsãwa = --Qur'an 74:52
    No! But they do not fear the Hereafter. <> A'aha! Kai dai, bã su jin tsõron Lãhira. = --Qur'an 74:53
    No! Indeed, the Qur'an is a reminder <> A'aha! Lalle ne, shi (Alƙur'ãni) tunãtarwa ce. = --Qur'an 74:54
    Then whoever wills will remember it. <> Dõmin wanda ya so, ya tuna. = --Qur'an 74:55
    And they will not remember except that Allah wills. He is worthy of fear and adequate for [granting] forgiveness. <> Kuma bã zã su tuna ba fãce idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gãfara. = --Qur'an 74:56
    I swear by the Day of Resurrection <> Bã sai Nã yi rantsuwa da Rãnar ¡iyãma ba. = --Qur'an 75:1
    And I swear by the reproaching soul [to the certainty of resurrection]. <> Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin kansa ba. = --Qur'an 75:2
    Does man think that We will not assemble his bones? <> Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba? = --Qur'an 75:3
    Yes. [We are] Able [even] to proportion his fingertips. <> Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa. = --Qur'an 75:4
    But man desires to continue in sin. <> Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa. = --Qur'an 75:5
    He asks, "When is the Day of Resurrection?" <> Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?" = --Qur'an 75:6
    So when vision is dazzled <> To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli). = --Qur'an 75:7
    And the moon darkens <> Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe). = --Qur'an 75:8
    And the sun and the moon are joined, <> Aka tãra rãnã da watã = --Qur'an 75:9
    Man will say on that Day, "Where is the [place of] escape?" <> Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu?" = --Qur'an 75:10
    No! There is no refuge. <> A'aha! bãbu mafaka. = --Qur'an 75:11
    To your Lord, that Day, is the [place of] permanence. <> zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake. = --Qur'an 75:12
    Man will be informed that Day of what he sent ahead and kept back. <> Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar. = --Qur'an 75:13
    Rather, man, against himself, will be a witness, <> Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne. = --Qur'an 75:14
    Even if he presents his excuses. <> Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba). = --Qur'an 75:15
    Move not your tongue with it, [O Muhammad], to hasten with recitation of the Qur'an. <> Kada ka mõtsar da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni). = --Qur'an 75:16
    Indeed, upon Us is its collection [in your heart] and [to make possible] its recitation. <> Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa. = --Qur'an 75:17
    So when We have recited it [through Gabriel], then follow its recitation. <> To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa. = --Qur'an 75:18
    Then upon Us is its clarification [to you]. <> sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa. = --Qur'an 75:19
    No! But you love the immediate <> A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne. = --Qur'an 75:20
    And leave the Hereafter. <> Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira). = --Qur'an 75:21
    [Some] faces, that Day, will be radiant, <> Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne. = --Qur'an 75:22
    Looking at their Lord. <> Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne. = --Qur'an 75:23
    And [some] faces, that Day, will be contorted, <> Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne. = --Qur'an 75:24
    Expecting that there will be done to them [something] backbreaking. <> Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso. = --Qur'an 75:25
    No! When the soul has reached the collar bones <> A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai. = --Qur'an 75:26
    And it is said, "Who will cure [him]?" <> kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada?" = --Qur'an 75:27
    And the dying one is certain that it is the [time of] separation <> Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce. = --Qur'an 75:28
    And the leg is wound about the leg, <> Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri. = --Qur'an 75:29
    To your Lord, that Day, will be the procession. <> Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa take. = --Qur'an 75:30
    And the disbeliever had not believed, nor had he prayed. <> To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba! = --Qur'an 75:31
    But [instead], he denied and turned away. <> Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya! = --Qur'an 75:32
    And then he went to his people, swaggering [in pride]. <> Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama. = --Qur'an 75:33
    Woe to you, and woe! <> Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa. = --Qur'an 75:34
    Then woe to you, and woe! <> Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa. = --Qur'an 75:35
    Does man think that he will be left neglected? <> Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)? = --Qur'an 75:36
    Had he not been a sperm from semen emitted? <> Bai kasance iɗgo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa) = --Qur'an 75:37
    Then he was a clinging clot, and [Allah] created [his form] and proportioned [him] <> Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa; = --Qur'an 75:38
    And made of him two mates, the male and the female. <> Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace? = --Qur'an 75:39
    Is not that [Creator] Able to give life to the dead? <> Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu? = --Qur'an 75:40
    Has there [not] come upon man a period of time when he was not a thing [even] mentioned? <> Lalle ne, wata mudda ta zamani tã zo a kan mutum, bai kasance kõme ba wanda ake ambata. = --Qur'an 76:1
    Indeed, We created man from a sperm-drop mixture that We may try him; and We made him hearing and seeing. <> Lalle ne, Mũ Mun halitta mutum daga ɗigon ruwa garwayayye, Muna jarraba shi, sabõda haka Muka sanya shi mai ji mai gani, = --Qur'an 76:2
    Indeed, We guided him to the way, be he grateful or be he ungrateful. <> Lalle ne, Mũ, Mun shiryar da shi ga hanyar ƙwarai, ko ya zama mai gõdiya, kuma ko ya zama mai kãfirci. = --Qur'an 76:3
    Indeed, We have prepared for the disbelievers chains and shackles and a blaze. <> Lalle ne, Mũ, Mun yi tattali, dõmin kãfirai, sarƙoƙi da ƙuƙumma da sa'ĩr. = --Qur'an 76:4
    Indeed, the righteous will drink from a cup [of wine] whose mixture is of Kafur, <> Lalle ne, mutãnen kirki zã su sha daga finjãlin giya abin gaurayarta yã kãsance kãfur ne. = --Qur'an 76:5
    A spring of which the [righteous] servants of Allah will drink; they will make it gush forth in force [and abundance]. <> Wani marmaro ne, daga gare shi bayin Allah suke sha, suna ɓuɓɓugar da shi ɓuɓɓugarwa. = --Qur'an 76:6
    They [are those who] fulfill [their] vows and fear a Day whose evil will be widespread. <> Suna cikãwa da alwãshin (da suka bãkanta), kuma suna tsõron wani yini wanda sharrinsa ya kasance mai tartsatsi ne. = --Qur'an 76:7
    And they give food in spite of love for it to the needy, the orphan, and the captive, <> Kuma suna ciyar da abinci, a kan suna bukãtarsa, ga matalauci da marãya da kãmamme. = --Qur'an 76:8
    [Saying], "We feed you only for the countenance of Allah. We wish not from you reward or gratitude. <> (Suna cẽwa): "Munã ciyar da ku ne dõmin nẽman yardar Allah kawai, bã mu nufin sãmun wani sakamako daga gare ku, kuma bã mu nufin gõdiya. = --Qur'an 76:9
    Indeed, We fear from our Lord a Day austere and distressful." <> "Lalle ne, mũ muna tsõro daga Ubangijinmu, wani yini mai gintsẽwa, mai murtukẽwa." = --Qur'an 76:10
    So Allah will protect them from the evil of that Day and give them radiance and happiness <> Sabõda haka Allah Ya tsare musu sharrin wannan yini, kuma Ya hlɗa su da annũrin huska da farin ciki, = --Qur'an 76:11
    And will reward them for what they patiently endured [with] a garden [in Paradise] and silk [garments]. <> Kuma Ya sãka musu sabõda haƙurin da suka yi, da Aljanna da tufãfin alharini. = --Qur'an 76:12
    [They will be] reclining therein on adorned couches. They will not see therein any [burning] sun or [freezing] cold. <> Sunã mãsu zaman ginciri, a cikinta, a kan karagu, bã su ganin rãnã a cikinta, kuma bã su ganin jaura. = --Qur'an 76:13
    And near above them are its shades, and its [fruit] to be picked will be lowered in compliance. <> Kuma, inuwõyinta suna kusa, a kansu, an hõre nunannun 'yã'yan itãcenta, hõrẽwa. = --Qur'an 76:14
    And there will be circulated among them vessels of silver and cups having been [created] clear [as glass], <> Kuma ana kẽwayãwa a kansu da finjãlai na azurfa da kofuna waɗanda suka kasance na ƙarau. = --Qur'an 76:15
    Clear glasses [made] from silver of which they have determined the measure. <> ¡arau na azurfa, sun ƙaddara su ƙaddarawa, daidai bukãta. = --Qur'an 76:16
    And they will be given to drink a cup [of wine] whose mixture is of ginger <> Ana shayarwa da su, a cikinta, finjalan giya, wadda abin gaurayarta ya kasance zanjabil ne. = --Qur'an 76:17
    [From] a fountain within Paradise named Salsabeel. <> Wani marmaro ne, a cikinta, ana kiran sa salsabil. = --Qur'an 76:18
    There will circulate among them young boys made eternal. When you see them, you would think them [as beautiful as] scattered pearls. <> Kuma wasu yara samãrin dindindin na kẽwayãwa, a kansu, idan ka gan su, zã ka zaci sũ lu'ulu'u ne wanda aka wãtsa. = --Qur'an 76:19
    And when you look there [in Paradise], you will see pleasure and great dominion. <> Kuma idan kã ga wannan wurin, to, kã ga wata irin ni'ima da mulki babba. = --Qur'an 76:20
    Upon the inhabitants will be green garments of fine silk and brocade. And they will be adorned with bracelets of silver, and their Lord will give them a purifying drink. <> Tufãfinsu na sama na alharĩ ni ne, kõre da mai walƙiya, kuma an ƙawãce su da mundãye na wata curin azurfa kuma Ubangijinsu, Ya shãyar da su abin sha mai tsarkakẽwar (ciki). = --Qur'an 76:21
    [And it will be said], "Indeed, this is for you a reward, and your effort has been appreciated." <> (A ce musu) "Lalle ne, wannan ya kasance, a gare ku sakamako, kuma aikink. ya kasance abin gõdewa." = --Qur'an 76:22
    Indeed, it is We who have sent down to you, [O Muhammad], the Qur'an progressively. <> Lalle, Mũ ne Muka saukar da Alƙur'ãni a gare ka, saukarwa. = --Qur'an 76:23
    So be patient for the decision of your Lord and do not obey from among them a sinner or ungrateful [disbeliever]. <> Sabõda haka ka yi haƙuri ga hukuncin Ubangijinka, kuma kada ka bi, daga cikinsu, mai zunubi ko mai kãfirci. = --Qur'an 76:24
    And mention the name of your Lord [in prayer] morning and evening <> Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, sãfe da maraice. = --Qur'an 76:25
    And during the night prostrate to Him and exalt Him a long [part of the] night. <> Daga dare, sai ka yi sujũda gare Shi, kuma ka tsarkake Shi darẽ mai tsawo. = --Qur'an 76:26
    Indeed, these [disbelievers] love the immediate and leave behind them a grave Day. <> Lalle ne, waɗannan suna son mai gaugãwa (dũniya) kuma suna bari, a bãyansu, wani yini mai nauyi. = --Qur'an 76:27
    We have created them and strengthened their forms, and when We will, We can change their likenesses with [complete] alteration. <> Mũ ne Muka halitta su kuma Muka, ƙarfafa halittarsu, kuma idan Mun so, za Mu musanyâ su da wasu mutane kwatankwacinsu, musanyawa. = --Qur'an 76:28
    Indeed, this is a reminder, so he who wills may take to his Lord a way. <> Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, saboda wanda ya so ya riƙa hanyar kirki zuwa ga Ubangijinsa. = --Qur'an 76:29
    And you do not will except that Allah wills. Indeed, Allah is ever Knowing and Wise. <> Kuma, bã zã ku so ba, sai Allah Ya so, lalle ne Allah Yã kasance Masani' Mai hikima. = --Qur'an 76:30
    He admits whom He wills into His mercy; but the wrongdoers - He has prepared for them a painful punishment. <> Yana shigar da wanda Ya so a cikin rahamarsa, kuma azzãlumai, Yã yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 76:31
    By those [winds] sent forth in gusts <> Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna. = --Qur'an 77:1
    And the winds that blow violently <> Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi. = --Qur'an 77:2
    And [by] the winds that spread [clouds] <> Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa. = --Qur'an 77:3
    And those [angels] who bring criterion <> sa'an nan, da ãyõyi mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa. = --Qur'an 77:4
    And those [angels] who deliver a message <> Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni. = --Qur'an 77:5
    As justification or warning, <> Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi. = --Qur'an 77:6
    Indeed, what you are promised is to occur. <> Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne = --Qur'an 77:7
    So when the stars are obliterated <> To, idan taurãri aka shãfe haskensu. = --Qur'an 77:8
    And when the heaven is opened <> Kuma, idan sama aka tsãge ta. = --Qur'an 77:9
    And when the mountains are blown away <> Kuma, idan duwãtsu aka nike su. = --Qur'an 77:10
    And when the messengers' time has come... <> Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su. = --Qur'an 77:11
    For what Day was it postponed? <> Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali. = --Qur'an 77:12
    For the Day of Judgement. <> Domin rãnar rarrabẽwa. = --Qur'an 77:13
    And what can make you know what is the Day of Judgement? <> Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa? = --Qur'an 77:14
    Woe, that Day, to the deniers. <> Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! = --Qur'an 77:15
    Did We not destroy the former peoples? <> Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba. = --Qur'an 77:16
    Then We will follow them with the later ones. <> Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe? = --Qur'an 77:17
    Thus do We deal with the criminals. <> Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi. = --Qur'an 77:18
    Woe, that Day, to the deniers. <> Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa! = --Qur'an 77:19
    Did We not create you from a liquid disdained? <> Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba. = --Qur'an 77:20
    And We placed it in a firm lodging <> Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce. = --Qur'an 77:21
    For a known extent. <> Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna. = --Qur'an 77:22
    And We determined [it], and excellent [are We] to determine. <> Sa'an nan, Muka nũna iyãwarMu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa. = --Qur'an 77:23
    Woe, that Day, to the deniers. <> Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa! = --Qur'an 77:24
    Have We not made the earth a container <> Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba. = --Qur'an 77:25
    Of the living and the dead? <> Ga rãyayyu da matattu, = --Qur'an 77:26
    And We placed therein lofty, firmly set mountains and have given you to drink sweet water. <> Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi? = --Qur'an 77:27
    Woe, that Day, to the deniers. <> Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! = --Qur'an 77:28
    [They will be told], "Proceed to that which you used to deny. <> Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi! = --Qur'an 77:29
    Proceed to a shadow [of smoke] having three columns <> Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku. = --Qur'an 77:30
    [But having] no cool shade and availing not against the flame." <> Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta. = --Qur'an 77:31
    Indeed, it throws sparks [as huge] as a fortress, <> Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye. = --Qur'an 77:32
    As if they were yellowish [black] camels. <> Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe. = --Qur'an 77:33
    Woe, that Day, to the deniers. <> Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! = --Qur'an 77:34
    This is a Day they will not speak, <> Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba. = --Qur'an 77:35
    Nor will it be permitted for them to make an excuse. <> Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari. = --Qur'an 77:36
    Woe, that Day, to the deniers. <> Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! = --Qur'an 77:37
    This is the Day of Judgement; We will have assembled you and the former peoples. <> Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko. = --Qur'an 77:38
    So if you have a plan, then plan against Me. <> To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita. = --Qur'an 77:39
    Woe, that Day, to the deniers. <> Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! = --Qur'an 77:40
    Indeed, the righteous will be among shades and springs <> Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari. = --Qur'an 77:41
    And fruits from whatever they desire, <> Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari. = --Qur'an 77:42
    [Being told], "Eat and drink in satisfaction for what you used to do." <> (A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa." = --Qur'an 77:43
    Indeed, We thus reward the doers of good. <> Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. = --Qur'an 77:44
    Woe, that Day, to the deniers. <> Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! = --Qur'an 77:45
    [O disbelievers], eat and enjoy yourselves a little; indeed, you are criminals. <> (Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne." = --Qur'an 77:46
    Woe, that Day, to the deniers. <> Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! = --Qur'an 77:47
    And when it is said to them, "Bow [in prayer]," they do not bow. <> Kuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba." = --Qur'an 77:48
    Woe, that Day, to the deniers. <> Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! = --Qur'an 77:49
    Then in what statement after the Qur'an will they believe? <> To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni = --Qur'an 77:50
    About what are they asking one another? <> A kan mẽ suke tambayar jũna? = --Qur'an 78:1
    About the great news - <> A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni)? = --Qur'an 78:2
    That over which they are in disagreement. <> Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa? = --Qur'an 78:3
    No! They are going to know. <> A'aha! Zã su sani. = --Qur'an 78:4
    Then, no! They are going to know. <> Kuma, a'aha! Zã su sani. = --Qur'an 78:5
    Have We not made the earth a resting place? <> Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba? = --Qur'an 78:6
    And the mountains as stakes? <> Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)? = --Qur'an 78:7
    And We created you in pairs <> Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã? = --Qur'an 78:8
    And made your sleep [a means for] rest <> Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa? = --Qur'an 78:9
    And made the night as clothing <> Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura? = --Qur'an 78:10
    And made the day for livelihood <> Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci? = --Qur'an 78:11
    And constructed above you seven strong [heavens] <> Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi? = --Qur'an 78:12
    And made [therein] a burning lamp <> Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)? = --Qur'an 78:13
    And sent down, from the rain clouds, pouring water <> Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba? = --Qur'an 78:14
    That We may bring forth thereby grain and vegetation <> Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi? = --Qur'an 78:15
    And gardens of entwined growth. <> Da itãcen lambuna mãsu lillibniya? = --Qur'an 78:16
    Indeed, the Day of Judgement is an appointed time - <> Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci. = --Qur'an 78:17
    The Day the Horn is blown and you will come forth in multitudes <> Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a. = --Qur'an 78:18
    And the heaven is opened and will become gateways <> Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi. = --Qur'an 78:19
    And the mountains are removed and will be [but] a mirage. <> Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra. = --Qur'an 78:20
    Indeed, Hell has been lying in wait <> Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata. = --Qur'an 78:21
    For the transgressors, a place of return, <> Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma. = --Qur'an 78:22
    In which they will remain for ages [unending]. <> Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna. = --Qur'an 78:23
    They will not taste therein [any] coolness or drink <> Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha. = --Qur'an 78:24
    Except scalding water and [foul] purulence - <> Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini. = --Qur'an 78:25
    An appropriate recompense. <> Sakamako mai dãcẽwa. = --Qur'an 78:26
    Indeed, they were not expecting an account <> Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi. = --Qur'an 78:27
    And denied Our verses with [emphatic] denial. <> Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyinMu, ƙaryatãwa! = --Qur'an 78:28
    But all things We have enumerated in writing. <> Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce. = --Qur'an 78:29
    "So taste [the penalty], and never will We increase you except in torment." <> Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba. = --Qur'an 78:30
    Indeed, for the righteous is attainment - <> Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo. = --Qur'an 78:31
    Gardens and grapevines <> Lambuna da inabõbi. = --Qur'an 78:32
    And full-breasted [companions] of equal age <> Da cikakkun 'yammata, tsãrar jũna. = --Qur'an 78:33
    And a full cup. <> Da hinjãlan giya cikakku. = --Qur'an 78:34
    No ill speech will they hear therein or any falsehood - <> Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa. = --Qur'an 78:35
    [As] reward from your Lord, [a generous] gift [made due by] account, <> Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa. = --Qur'an 78:36
    [From] the Lord of the heavens and the earth and whatever is between them, the Most Merciful. They possess not from Him [authority for] speech. <> Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi. = --Qur'an 78:37
    The Day that the Spirit and the angels will stand in rows, they will not speak except for one whom the Most Merciful permits, and he will say what is correct. <> Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai. = --Qur'an 78:38
    That is the True Day; so he who wills may take to his Lord a [way of] return. <> Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa. = --Qur'an 78:39
    Indeed, We have warned you of a near punishment on the Day when a man will observe what his hands have put forth and the disbeliever will say, "Oh, I wish that I were dust!" <> Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!" = --Qur'an 78:40
    By those [angels] who extract with violence <> Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi. = --Qur'an 79:1
    And [by] those who remove with ease <> Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi. = --Qur'an 79:2
    And [by] those who glide [as if] swimming <> Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo. = --Qur'an 79:3
    And those who race each other in a race <> Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umurnin Allah) kamar suna tsẽre. = --Qur'an 79:4
    And those who arrange [each] matter, <> Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni. = --Qur'an 79:5
    On the Day the blast [of the Horn] will convulse [creation], <> Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa. = --Qur'an 79:6
    There will follow it the subsequent [one]. <> Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye. = --Qur'an 79:7
    Hearts, that Day, will tremble, <> Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne. = --Qur'an 79:8
    Their eyes humbled. <> Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu. = --Qur'an 79:9
    They are [presently] saying, "Will we indeed be returned to [our] former state [of life]? <> Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu? = --Qur'an 79:10
    Even if we should be decayed bones? <> "Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?" = --Qur'an 79:11
    They say, "That, then, would be a losing return." <> Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!" = --Qur'an 79:12
    Indeed, it will be but one shout, <> To, ita kam, tsãwa guda kawai ce. = --Qur'an 79:13
    And suddenly they will be [alert] upon the earth's surface. <> Sai kawai gã su a bãyan ƙasa. = --Qur'an 79:14
    Has there reached you the story of Moses? - <> Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka? = --Qur'an 79:15
    When his Lord called to him in the sacred valley of Tuwa, <> A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã? = --Qur'an 79:16
    "Go to Pharaoh. Indeed, he has transgressed. <> Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi. = --Qur'an 79:17
    And say to him, 'Would you [be willing to] purify yourself <> "Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka. = --Qur'an 79:18
    And let me guide you to your Lord so you would fear [Him]?'" <> "Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa?" = --Qur'an 79:19
    And he showed him the greatest sign, <> Sai ya nũna masa ãyar nan mafi girma. = --Qur'an 79:20
    But Pharaoh denied and disobeyed. <> Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni), = --Qur'an 79:21
    Then he turned his back, striving. <> Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri. = --Qur'an 79:22
    And he gathered [his people] and called out <> Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira. = --Qur'an 79:23
    And said, "I am your most exalted lord." <> Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka." = --Qur'an 79:24
    So Allah seized him in exemplary punishment for the last and the first [transgression]. <> Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko. = --Qur'an 79:25
    Indeed in that is a warning for whoever would fear [Allah]. <> Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah. = --Qur'an 79:26
    Are you a more difficult creation or is the heaven? Allah constructed it. <> Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta. = --Qur'an 79:27
    He raised its ceiling and proportioned it. <> Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta. = --Qur'an 79:28
    And He darkened its night and extracted its brightness. <> Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta. = --Qur'an 79:29
    And after that He spread the earth. <> Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta. = --Qur'an 79:30
    He extracted from it its water and its pasture, <> Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta. = --Qur'an 79:31
    And the mountains He set firmly <> Da duwatsu, Yã kafe ta. = --Qur'an 79:32
    As provision for you and your grazing livestock. <> Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku. = --Qur'an 79:33
    But when there comes the greatest Overwhelming Calamity - <> To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo. = --Qur'an 79:34
    The Day when man will remember that for which he strove, <> Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata. = --Qur'an 79:35
    And Hellfire will be exposed for [all] those who see - <> Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani. = --Qur'an 79:36
    So as for he who transgressed <> To, amma wanda ya yi girman kai. = --Qur'an 79:37
    And preferred the life of the world, <> Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya). = --Qur'an 79:38
    Then indeed, Hellfire will be [his] refuge. <> To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma. = --Qur'an 79:39
    But as for he who feared the position of his Lord and prevented the soul from [unlawful] inclination, <> Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai. = --Qur'an 79:40
    Then indeed, Paradise will be [his] refuge. <> To, lalle ne Aljanna ita ce makõma. = --Qur'an 79:41
    They ask you, [O Muhammad], about the Hour: when is its arrival? <> Sunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta? = --Qur'an 79:42
    In what [position] are you that you should mention it? <> Me ya haɗã ka da ambatonta? = --Qur'an 79:43
    To your Lord is its finality. <> Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake. = --Qur'an 79:44
    You are only a warner for those who fear it. <> Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta. = --Qur'an 79:45
    It will be, on the Day they see it, as though they had not remained [in the world] except for an afternoon or a morning thereof. <> Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa. = --Qur'an 79:46
    The Prophet frowned and turned away <> Yã game huska kuma ya jũya bãya. = --Qur'an 80:1
    Because there came to him the blind man, [interrupting]. <> Sabõda makãho yã je masa. = --Qur'an 80:2
    But what would make you perceive, [O Muhammad], that perhaps he might be purified <> To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka. = --Qur'an 80:3
    Or be reminded and the remembrance would benefit him? <> Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi? = --Qur'an 80:4
    As for he who thinks himself without need, <> Amma wanda ya wadãtu da dũkiya. = --Qur'an 80:5
    To him you give attention. <> Sa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi! = --Qur'an 80:6
    And not upon you [is any blame] if he will not be purified. <> To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba? = --Qur'an 80:7
    But as for he who came to you striving [for knowledge] <> Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa. = --Qur'an 80:8
    While he fears [Allah], <> Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah. = --Qur'an 80:9
    From him you are distracted. <> Kai kuma kã shagala ga barinsa! = --Qur'an 80:10
    No! Indeed, these verses are a reminder; <> A'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce. = --Qur'an 80:11
    So whoever wills may remember it. <> Sabõda wanda ya so ya tunaShi (Allah). = --Qur'an 80:12
    [It is recorded] in honored sheets, <> (Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa, = --Qur'an 80:13
    Exalted and purified, <> Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa. = --Qur'an 80:14
    [Carried] by the hands of messenger-angels, <> A cikin hannãyen mala'iku marubũta. = --Qur'an 80:15
    Noble and dutiful. <> Mãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah. = --Qur'an 80:16
    Cursed is man; how disbelieving is he. <> An la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa! = --Qur'an 80:17
    From what substance did He create him? <> Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi? = --Qur'an 80:18
    From a sperm-drop He created him and destined for him; <> Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye). = --Qur'an 80:19
    Then He eased the way for him; <> Sa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa. = --Qur'an 80:20
    Then He causes his death and provides a grave for him. <> Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari. = --Qur'an 80:21
    Then when He wills, He will resurrect him. <> Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi. = --Qur'an 80:22
    No! Man has not yet accomplished what He commanded him. <> Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari). = --Qur'an 80:23
    Then let mankind look at his food - <> To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa. = --Qur'an 80:24
    How We poured down water in torrents, <> Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa. = --Qur'an 80:25
    Then We broke open the earth, splitting [it with sprouts], <> Sa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa. = --Qur'an 80:26
    And caused to grow within it grain <> Sa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya, a cikinta. = --Qur'an 80:27
    And grapes and herbage <> Da inabi da ciyãwa. = --Qur'an 80:28
    And olive and palm trees <> Da zaitũni da itãcen dabĩno. = --Qur'an 80:29
    And gardens of dense shrubbery <> Da lambuna, mãsu yawan itãce. = --Qur'an 80:30
    And fruit and grass - <> Da 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi. = --Qur'an 80:31
    [As] enjoyment for you and your grazing livestock. <> Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku. = --Qur'an 80:32
    But when there comes the Deafening Blast <> To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo. = --Qur'an 80:33
    On the Day a man will flee from his brother <> Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa. = --Qur'an 80:34
    And his mother and his father <> Da uwarsa da ubansa. = --Qur'an 80:35
    And his wife and his children, <> Da mãtarsa da ɗiyansa. = --Qur'an 80:36
    For every man, that Day, will be a matter adequate for him. <> Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi. = --Qur'an 80:37
    [Some] faces, that Day, will be bright - <> Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne. = --Qur'an 80:38
    Laughing, rejoicing at good news. <> Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra. = --Qur'an 80:39
    And [other] faces, that Day, will have upon them dust. <> Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu. = --Qur'an 80:40
    Blackness will cover them. <> Baƙi zai rufe su. = --Qur'an 80:41
    Those are the disbelievers, the wicked ones. <> Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu). = --Qur'an 80:42
    When the sun is wrapped up [in darkness] <> Idan rãna aka shafe haskenta = --Qur'an 81:1
    And when the stars fall, dispersing, <> Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani). = --Qur'an 81:2
    And when the mountains are removed <> Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su. = --Qur'an 81:3
    And when full-term she-camels are neglected <> Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba. = --Qur'an 81:4
    And when the wild beasts are gathered <> Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su. = --Qur'an 81:5
    And when the seas are filled with flame <> Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta. = --Qur'an 81:6
    And when the souls are paired <> Kuma idan rãyuka aka haɗa su da jikunkunansu. = --Qur'an 81:7
    And when the girl [who was] buried alive is asked <> Kuma idan wadda aka turbuɗe ta da rai aka tambaye ta. = --Qur'an 81:8
    For what sin she was killed <> "Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?" = --Qur'an 81:9
    And when the pages are made public <> Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su). = --Qur'an 81:10
    And when the sky is stripped away <> Kuma idan sama aka fẽɗe ta. = --Qur'an 81:11
    And when Hellfire is set ablaze <> Kuma idan Jahĩm aka hũra ta = --Qur'an 81:12
    And when Paradise is brought near, <> Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita. = --Qur'an 81:13
    A soul will [then] know what it has brought [with it]. <> Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan). = --Qur'an 81:14
    So I swear by the retreating stars - <> To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã ba. = --Qur'an 81:15
    Those that run [their courses] and disappear - <> Mãsu gudu suna ɓũya. = --Qur'an 81:16
    And by the night as it closes in <> Da dare idan ya bãyar da bãya. = --Qur'an 81:17
    And by the dawn when it breathes <> Da sãfiya idan ta yi lumfashi. = --Qur'an 81:18
    [That] indeed, the Qur'an is a word [conveyed by] a noble messenger <> Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah. = --Qur'an 81:19
    [Who is] possessed of power and with the Owner of the Throne, secure [in position], <> Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi. = --Qur'an 81:20
    Obeyed there [in the heavens] and trustworthy. <> Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce. = --Qur'an 81:21
    And your companion is not [at all] mad. <> Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne. = --Qur'an 81:22
    And he has already seen Gabriel in the clear horizon. <> Kuma lalle ne, yã gan shi a cikin sararin sama mabayyani. = --Qur'an 81:23
    And Muhammad is not a withholder of [knowledge of] the unseen. <> Kuma shi, ga gaibi bã mai rowa ba ne. = --Qur'an 81:24
    And the Qur'an is not the word of a devil, expelled [from the heavens]. <> Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce. = --Qur'an 81:25
    So where are you going? <> Shin, a inã zã ku tafi? = --Qur'an 81:26
    It is not except a reminder to the worlds <> Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai. = --Qur'an 81:27
    For whoever wills among you to take a right course. <> Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu. = --Qur'an 81:28
    And you do not will except that Allah wills - Lord of the worlds. <> Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda. = --Qur'an 81:29
    When the sky breaks apart <> Idan sama ta tsãge. = --Qur'an 82:1
    And when the stars fall, scattering, <> Kuma idan taurãri suka wãtse. = --Qur'an 82:2
    And when the seas are erupted <> Kuma idan tẽkuna aka facce su. = --Qur'an 82:3
    And when the [contents of] graves are scattered, <> Kuma idan kaburbura aka tõne su. = --Qur'an 82:4
    A soul will [then] know what it has put forth and kept back. <> Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar. = --Qur'an 82:5
    O mankind, what has deceived you concerning your Lord, the Generous, <> Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karimci. = --Qur'an 82:6
    Who created you, proportioned you, and balanced you? <> Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka. = --Qur'an 82:7
    In whatever form He willed has He assembled you. <> A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta. = --Qur'an 82:8
    No! But you deny the Recompense. <> A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako! = --Qur'an 82:9
    And indeed, [appointed] over you are keepers, <> Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara. = --Qur'an 82:10
    Noble and recording; <> Mãsu daraja, marubũta. = --Qur'an 82:11
    They know whatever you do. <> Sunã sanin abin da kuke aikatãwa. = --Qur'an 82:12
    Indeed, the righteous will be in pleasure, <> Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima. = --Qur'an 82:13
    And indeed, the wicked will be in Hellfire. <> Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm. = --Qur'an 82:14
    They will [enter to] burn therein on the Day of Recompense, <> Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako. = --Qur'an 82:15
    And never therefrom will they be absent. <> Bã zã su faku daga gare ta ba. = --Qur'an 82:16
    And what can make you know what is the Day of Recompense? <> Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rẽnar sakamako? = --Qur'an 82:17
    Then, what can make you know what is the Day of Recompense? <> Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako? = --Qur'an 82:18
    It is the Day when a soul will not possess for another soul [power to do] a thing; and the command, that Day, is [entirely] with Allah. <> Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake. = --Qur'an 82:19
    Woe to those who give less [than due], <> Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa. = --Qur'an 83:1
    Who, when they take a measure from people, take in full. <> Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu. = --Qur'an 83:2
    But if they give by measure or by weight to them, they cause loss. <> Kuma idan sun auna musu da zakka ko da sikẽli, suna ragẽwa = --Qur'an 83:3
    Do they not think that they will be resurrected <> Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba? = --Qur'an 83:4
    For a tremendous Day - <> Domin yini mai girma. = --Qur'an 83:5
    The Day when mankind will stand before the Lord of the worlds? <> Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta? = --Qur'an 83:6
    No! Indeed, the record of the wicked is in sijjeen. <> Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn. = --Qur'an 83:7
    And what can make you know what is sijjeen? <> Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn? = --Qur'an 83:8
    It is [their destination recorded in] a register inscribed. <> Wani 1ittãfi ne rubũtacce. = --Qur'an 83:9
    Woe, that Day, to the deniers, <> Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa. = --Qur'an 83:10
    Who deny the Day of Recompense. <> Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako. = --Qur'an 83:11
    And none deny it except every sinful transgressor. <> Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi. = --Qur'an 83:12
    When Our verses are recited to him, he says, "Legends of the former peoples." <> Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne. = --Qur'an 83:13
    No! Rather, the stain has covered their hearts of that which they were earning. <> A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu. = --Qur'an 83:14
    No! Indeed, from their Lord, that Day, they will be partitioned. <> A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne. = --Qur'an 83:15
    Then indeed, they will [enter and] burn in Hellfire. <> Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne. = --Qur'an 83:16
    Then it will be said [to them], "This is what you used to deny." <> Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi." = --Qur'an 83:17
    No! Indeed, the record of the righteous is in 'illiyyun. <> A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna? = --Qur'an 83:18
    And what can make you know what is 'illiyyun? <> Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna? = --Qur'an 83:19
    It is [their destination recorded in] a register inscribed <> Wani littãfi ne rubũtacce. = --Qur'an 83:20
    Which is witnessed by those brought near [to Allah]. <> Muƙarrabai suke halarta shi. = --Qur'an 83:21
    Indeed, the righteous will be in pleasure <> Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima. = --Qur'an 83:22
    On adorned couches, observing. <> A kan karagu, suna ta kallo. = --Qur'an 83:23
    You will recognize in their faces the radiance of pleasure. <> Kana sani a cikin huskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima. = --Qur'an 83:24
    They will be given to drink [pure] wine [which was] sealed. <> Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta. = --Qur'an 83:25
    The last of it is musk. So for this let the competitors compete. <> ¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma. = --Qur'an 83:26
    And its mixture is of Tasneem, <> Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake. = --Qur'an 83:27
    A spring from which those near [to Allah] drink. <> (Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi. = --Qur'an 83:28
    Indeed, those who committed crimes used to laugh at those who believed. <> Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya. = --Qur'an 83:29
    And when they passed by them, they would exchange derisive glances. <> Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe. = --Qur'an 83:30
    And when they returned to their people, they would return jesting. <> Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci. = --Qur'an 83:31
    And when they saw them, they would say, "Indeed, those are truly lost." <> Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne." = --Qur'an 83:32
    But they had not been sent as guardians over them. <> Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu. = --Qur'an 83:33
    So Today those who believed are laughing at the disbelievers, <> To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya. = --Qur'an 83:34
    On adorned couches, observing. <> A kan karagu, suna ta kallo. = --Qur'an 83:35
    Have the disbelievers [not] been rewarded [this Day] for what they used to do? <> Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa? = --Qur'an 83:36
    When the sky has split [open] <> Idan sama ta kẽce, = --Qur'an 84:1
    And has responded to its Lord and was obligated [to do so] <> Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin saurãron, = --Qur'an 84:2
    And when the earth has been extended <> Kuma idan ƙasã aka mĩƙe ta, = --Qur'an 84:3
    And has cast out that within it and relinquished [it] <> Kuma ta jẽfar da abin da yake a cikinta, tã wõfinta daga kõme. = --Qur'an 84:4
    And has responded to its Lord and was obligated [to do so] - <> Kuma ta saurãri Ubangijinta, aka wajabta mata yin saurãren, = --Qur'an 84:5
    O mankind, indeed you are laboring toward your Lord with [great] exertion and will meet it. <> Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, To, kai mai haɗuwa da Shi ne. = --Qur'an 84:6
    Then as for he who is given his record in his right hand, <> To, amma wanda aka bai wa littãfinsa da damansa. = --Qur'an 84:7
    He will be judged with an easy account <> To, za a yi masa hisãbi, hisãbi mai sauƙi. = --Qur'an 84:8
    And return to his people in happiness. <> Kuma ya jũya zuwa ga iyãlinsa (a cikin Aljanna), yanã mai raha. = --Qur'an 84:9
    But as for he who is given his record behind his back, <> Kuma amma wanda aka bai wa littãfinsa, daga wajen bãyansa. = --Qur'an 84:10
    He will cry out for destruction <> To, zã shi dinga kiran halaka! = --Qur'an 84:11
    And [enter to] burn in a Blaze. <> Kuma ya shiga sa'ĩr. = --Qur'an 84:12
    Indeed, he had [once] been among his people in happiness; <> Lal1e ne shi, yã kasance (a dũniya) cikin iyãlinsa yanã mai raha. = --Qur'an 84:13
    Indeed, he had thought he would never return [to Allah]. <> Lalle ne yã yi zaton bã zai kõmo ba. = --Qur'an 84:14
    But yes! Indeed, his Lord was ever of him, Seeing. <> Na'am! Lalle ne, Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi. = --Qur'an 84:15
    So I swear by the twilight glow <> To, ba sai Nã rantse da shafaƙi ba. = --Qur'an 84:16
    And [by] the night and what it envelops <> Da dare, da abin da ya ƙunsa. = --Qur'an 84:17
    And [by] the moon when it becomes full <> Da watã idan (haskensa) ya cika. = --Qur'an 84:18
    [That] you will surely experience state after state. <> Lalle ne kunã hawan wani hãli daga wani hãli. = --Qur'an 84:19
    So what is [the matter] with them [that] they do not believe, <> To, mẽ ya sãme su, ba su yin ĩmãni? = --Qur'an 84:20
    And when the Qur'an is recited to them, they do not prostrate [to Allah]? <> Kuma idan an karanta Alkur'ãni a kansu, bã su yin tawãli'u? = --Qur'an 84:21
    But those who have disbelieved deny, <> Ba haka ba! waɗanda suka kãfirta, sai ƙaryatãwa suke yi. = --Qur'an 84:22
    And Allah is most knowing of what they keep within themselves. <> Alhãli Allah Shĩ ne Mafi sani ga abin a suke tãrãwa. = --Qur'an 84:23
    So give them tidings of a painful punishment, <> Saboda haka, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi. = --Qur'an 84:24
    Except for those who believe and do righteous deeds. For them is a reward uninterrupted. <> Fãce waɗanda suka yi ĩmãni, suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bã ya yankẽwa. = --Qur'an 84:25
    By the sky containing great stars <> Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara. = --Qur'an 85:1
    And [by] the promised Day <> Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa, = --Qur'an 85:2
    And [by] the witness and what is witnessed, <> Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta a cikinsa = --Qur'an 85:3
    Cursed were the companions of the trench <> An la'ani mutãnen rãmi. = --Qur'an 85:4
    [Containing] the fire full of fuel, <> Wato wuta wadda aka hura. = --Qur'an 85:5
    When they were sitting near it <> A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune. = --Qur'an 85:6
    And they, to what they were doing against the believers, were witnesses. <> Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce. = --Qur'an 85:7
    And they resented them not except because they believed in Allah, the Exalted in Might, the Praiseworthy, <> Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa. = --Qur'an 85:8
    To whom belongs the dominion of the heavens and the earth. And Allah, over all things, is Witness. <> Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake. = --Qur'an 85:9
    Indeed, those who have tortured the believing men and believing women and then have not repented will have the punishment of Hell, and they will have the punishment of the Burning Fire. <> Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara. = --Qur'an 85:10
    Indeed, those who have believed and done righteous deeds will have gardens beneath which rivers flow. That is the great attainment. <> Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba. = --Qur'an 85:11
    Indeed, the vengeance of your Lord is severe. <> Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai. = --Qur'an 85:12
    Indeed, it is He who originates [creation] and repeats. <> Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa). = --Qur'an 85:13
    And He is the Forgiving, the Affectionate, <> Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya. = --Qur'an 85:14
    Honorable Owner of the Throne, <> Mai Al'arshi mai girma = --Qur'an 85:15
    Effecter of what He intends. <> Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi. = --Qur'an 85:16
    Has there reached you the story of the soldiers - <> Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka. = --Qur'an 85:17
    [Those of] Pharaoh and Thamud? <> Fir'auna da samũdãwa? = --Qur'an 85:18
    But they who disbelieve are in [persistent] denial, <> Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa. = --Qur'an 85:19
    While Allah encompasses them from behind. <> Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da saninSa). = --Qur'an 85:20
    But this is an honored Qur'an <> Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma. = --Qur'an 85:21
    [Inscribed] in a Preserved Slate. <> A cikin Allo tsararre. = --Qur'an 85:22
    By the sky and the night comer - <> Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare. = --Qur'an 86:1
    And what can make you know what is the night comer? <> To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare? = --Qur'an 86:2
    It is the piercing star - <> Shi ne taurãron nan mai tsananin haske. = --Qur'an 86:3
    There is no soul but that it has over it a protector. <> Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro. = --Qur'an 86:4
    So let man observe from what he was created. <> To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi? = --Qur'an 86:5
    He was created from a fluid, ejected, <> An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna. = --Qur'an 86:6
    Emerging from between the backbone and the ribs. <> Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji. = --Qur'an 86:7
    Indeed, Allah, to return him [to life], is Able. <> Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne. = --Qur'an 86:8
    The Day when secrets will be put on trial, <> Rãnar da ake jarrabawar asirai. = --Qur'an 86:9
    Then man will have no power or any helper. <> Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah). = --Qur'an 86:10
    By the sky which returns [rain] <> Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa. = --Qur'an 86:11
    And [by] the earth which cracks open, <> Da ƙasa ma'abũciyar tsãgẽwa, = --Qur'an 86:12
    Indeed, the Qur'an is a decisive statement, <> Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki = --Qur'an 86:13
    And it is not amusement. <> Kuma shĩ bã bananci bane = --Qur'an 86:14
    Indeed, they are planning a plan, <> Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai. = --Qur'an 86:15
    But I am planning a plan. <> Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi. = --Qur'an 86:16
    So allow time for the disbelievers. Leave them awhile. <> Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu. = --Qur'an 86:17
    Exalt the name of your Lord, the Most High, <> Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka. = --Qur'an 87:1
    Who created and proportioned <> Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar. = --Qur'an 87:2
    And who destined and [then] guided <> Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri). = --Qur'an 87:3
    And who brings out the pasture <> Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã. = --Qur'an 87:4
    And [then] makes it black stubble. <> Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa. = --Qur'an 87:5
    We will make you recite, [O Muhammad], and you will not forget, <> Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba. = --Qur'an 87:6
    Except what Allah should will. Indeed, He knows what is declared and what is hidden. <> Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye. = --Qur'an 87:7
    And We will ease you toward ease. <> Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi. = --Qur'an 87:8
    So remind, if the reminder should benefit; <> Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni. = --Qur'an 87:9
    He who fears [Allah] will be reminded. <> Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna. = --Qur'an 87:10
    But the wretched one will avoid it - <> Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta, = --Qur'an 87:11
    [He] who will [enter and] burn in the greatest Fire, <> Wanda zai shiga wutar da tã fi girma. = --Qur'an 87:12
    Neither dying therein nor living. <> Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba. = --Qur'an 87:13
    He has certainly succeeded who purifies himself <> Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo. = --Qur'an 87:14
    And mentions the name of his Lord and prays. <> Kuma ya ambaci sũnan Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla. = --Qur'an 87:15
    But you prefer the worldly life, <> Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya. = --Qur'an 87:16
    While the Hereafter is better and more enduring. <> Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa. = --Qur'an 87:17
    Indeed, this is in the former scriptures, <> Lalle ne, wannan yanã a cikin littafan farko. = --Qur'an 87:18
    The scriptures of Abraham and Moses. <> Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã. = --Qur'an 87:19
    Has there reached you the report of the Overwhelming [event]? <> Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka? = --Qur'an 88:1
    [Some] faces, that Day, will be humbled, <> Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne. = --Qur'an 88:2
    Working [hard] and exhausted. <> Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya. = --Qur'an 88:3
    They will [enter to] burn in an intensely hot Fire. <> Zã su shiga wata wuta mai zãfi. = --Qur'an 88:4
    They will be given drink from a boiling spring. <> Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa. = --Qur'an 88:5
    For them there will be no food except from a poisonous, thorny plant <> Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi. = --Qur'an 88:6
    Which neither nourishes nor avails against hunger. <> Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba. = --Qur'an 88:7
    [Other] faces, that Day, will show pleasure. <> Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne. = --Qur'an 88:8
    With their effort [they are] satisfied <> Game da aikinsu, masu yarda ne. = --Qur'an 88:9
    In an elevated garden, <> (Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya. = --Qur'an 88:10
    Wherein they will hear no unsuitable speech. <> Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta. = --Qur'an 88:11
    Within it is a flowing spring. <> A cikinta akwai marmaro mai gudãna. = --Qur'an 88:12
    Within it are couches raised high <> A cikinta akwai gadãje maɗaukaka. = --Qur'an 88:13
    And cups put in place <> Da kõfuna ar'aje. = --Qur'an 88:14
    And cushions lined up <> Da filõli jẽre, = --Qur'an 88:15
    And carpets spread around. <> Da katifu shimfiɗe. = --Qur'an 88:16
    Then do they not look at the camels - how they are created? <> Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su? = --Qur'an 88:17
    And at the sky - how it is raised? <> Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta? = --Qur'an 88:18
    And at the mountains - how they are erected? <> Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su? = --Qur'an 88:19
    And at the earth - how it is spread out? <> Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta? = --Qur'an 88:20
    So remind, [O Muhammad]; you are only a reminder. <> sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai. = --Qur'an 88:21
    You are not over them a controller. <> Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba. = --Qur'an 88:22
    However, he who turns away and disbelieves - <> Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta. = --Qur'an 88:23
    Then Allah will punish him with the greatest punishment. <> To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma. = --Qur'an 88:24
    Indeed, to Us is their return. <> Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take. = --Qur'an 88:25
    Then indeed, upon Us is their account. <> Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi. = --Qur'an 88:26
    By the dawn <> Inã rantsuwa da alfijiri. = --Qur'an 89:1
    And [by] ten nights <> Da darũruwa gõma. = --Qur'an 89:2
    And [by] the even [number] and the odd <> Da (adadi na) cikã da (na) mãrã. = --Qur'an 89:3
    And [by] the night when it passes, <> Da dare idan yana shũɗewa. = --Qur'an 89:4
    Is there [not] in [all] that an oath [sufficient] for one of perception? <> Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)? = --Qur'an 89:5
    Have you not considered how your Lord dealt with 'Aad - <> Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba? = --Qur'an 89:6
    [With] Iram - who had lofty pillars, <> Iramawa mãsu sakon ƙĩrar jiki. = --Qur'an 89:7
    The likes of whom had never been created in the land? <> Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya). = --Qur'an 89:8
    And [with] Thamud, who carved out the rocks in the valley? <> Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi suka yi gidãje)? = --Qur'an 89:9
    And [with] Pharaoh, owner of the stakes? - <> Da Fir'auna mai turãku. = --Qur'an 89:10
    [All of] whom oppressed within the lands <> Waɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa? = --Qur'an 89:11
    And increased therein the corruption. <> Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu. = --Qur'an 89:12
    So your Lord poured upon them a scourge of punishment. <> Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba. = --Qur'an 89:13
    Indeed, your Lord is in observation. <> Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka. = --Qur'an 89:14
    And as for man, when his Lord tries him and [thus] is generous to him and favors him, he says, "My Lord has honored me." <> To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni." = --Qur'an 89:15
    But when He tries him and restricts his provision, he says, "My Lord has humiliated me." <> Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni." = --Qur'an 89:16
    No! But you do not honor the orphan <> A'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya! = --Qur'an 89:17
    And you do not encourage one another to feed the poor. <> Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci! = --Qur'an 89:18
    And you consume inheritance, devouring [it] altogether, <> Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa. = --Qur'an 89:19
    And you love wealth with immense love. <> Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa. = --Qur'an 89:20
    No! When the earth has been leveled - pounded and crushed - <> A'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai. = --Qur'an 89:21
    And your Lord has come and the angels, rank upon rank, <> Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, safũ- safu. = --Qur'an 89:22
    And brought [within view], that Day, is Hell - that Day, man will remember, but what good to him will be the remembrance? <> Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi! = --Qur'an 89:23
    He will say, "Oh, I wish I had sent ahead [some good] for my life." <> Yana dinga cẽwa, "Kaitona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata!" = --Qur'an 89:24
    So on that Day, none will punish [as severely] as His punishment, <> To, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah. = --Qur'an 89:25
    And none will bind [as severely] as His binding [of the evildoers]. <> Kuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurinSa. = --Qur'an 89:26
    [To the righteous it will be said], "O reassured soul, <> Yã kai rai mai natsuwa! = --Qur'an 89:27
    Return to your Lord, well-pleased and pleasing [to Him], <> Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya) abar yardarwa (da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira). = --Qur'an 89:28
    And enter among My [righteous] servants <> Sabõbda haka, ka shiga cikin bãyiNa (mãsu bin umurui a dũniya). = --Qur'an 89:29
    And enter My Paradise." <> Kuma ka shiga AljannaTa (a Lãhira). = --Qur'an 89:30
    I swear by this city, Makkah - <> Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari ba. = --Qur'an 90:1
    And you, [O Muhammad], are free of restriction in this city - <> Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari. = --Qur'an 90:2
    And [by] the father and that which was born [of him], <> Da mahaifi da abin da ya haifa. = --Qur'an 90:3
    We have certainly created man into hardship. <> Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala. = --Qur'an 90:4
    Does he think that never will anyone overcome him? <> Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa? = --Qur'an 90:5
    He says, "I have spent wealth in abundance." <> Yana cẽwa "Na halakarda dũkiya mai yawa," = --Qur'an 90:6
    Does he think that no one has seen him? <> Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba? = --Qur'an 90:7
    Have We not made for him two eyes? <> Shin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba? = --Qur'an 90:8
    And a tongue and two lips? <> Da harshe, da leɓɓa biyu. = --Qur'an 90:9
    And have shown him the two ways? <> Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi biyu ba? = --Qur'an 90:10
    But he has not broken through the difficult pass. <> To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba? = --Qur'an 90:11
    And what can make you know what is [breaking through] the difficult pass? <> Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã? = --Qur'an 90:12
    It is the freeing of a slave <> Ita ce fansar wuyan bãwa. = --Qur'an 90:13
    Or feeding on a day of severe hunger <> Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abũcin yunwa. = --Qur'an 90:14
    An orphan of near relationship <> Ga marãya ma'abũcin zumunta. = --Qur'an 90:15
    Or a needy person in misery <> Ko kuwa wani matalauci ma'abũcin turɓãya. = --Qur'an 90:16
    And then being among those who believed and advised one another to patience and advised one another to compassion. <> Sa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi. = --Qur'an 90:17
    Those are the companions of the right. <> Waɗannan ne ma'abũta albarka = --Qur'an 90:18
    But they who disbelieved in Our signs - those are the companions of the left. <> Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyinMu, sũ ne ma'abũta shu'umci = --Qur'an 90:19
    Over them will be fire closed in. <> A kansu akwai wata wuta abar kullewa. = --Qur'an 90:20
    By the sun and its brightness <> Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta. = --Qur'an 91:1
    And [by] the moon when it follows it <> Kuma da wata idan ya bi ta. = --Qur'an 91:2
    And [by] the day when it displays it <> Da yini a lõkacin da ya bayyana ta. = --Qur'an 91:3
    And [by] the night when it covers it <> Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta. = --Qur'an 91:4
    And [by] the sky and He who constructed it <> Da sama da abin da ya gina ta. = --Qur'an 91:5
    And [by] the earth and He who spread it <> Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta. = --Qur'an 91:6
    And [by] the soul and He who proportioned it <> Da rai da abin da ya daidaita shi. = --Qur'an 91:7
    And inspired it [with discernment of] its wickedness and its righteousness, <> Sa'an nan ya sanar da shi fãjircinsa da shiryuwarsa. = --Qur'an 91:8
    He has succeeded who purifies it, <> Lalle ne wanda ya tsarkake shi (rai) ya sãmi babban rabo. = --Qur'an 91:9
    And he has failed who instills it [with corruption]. <> Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe shi (da laifi) ya tãɓe. = --Qur'an 91:10
    Thamud denied [their prophet] by reason of their transgression, <> Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu. = --Qur'an 91:11
    When the most wretched of them was sent forth. <> A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu). = --Qur'an 91:12
    And the messenger of Allah [Salih] said to them, "[Do not harm] the she-camel of Allah or [prevent her from] her drink." <> Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!" = --Qur'an 91:13
    But they denied him and hamstrung her. So their Lord brought down upon them destruction for their sin and made it equal [upon all of them]. <> Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi). = --Qur'an 91:14
    And He does not fear the consequence thereof. <> Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar). = --Qur'an 91:15
    By the night when it covers <> Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa. = --Qur'an 92:1
    And [by] the day when it appears <> Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa. = --Qur'an 92:2
    And [by] He who created the male and female, <> Da abin da ya halitta namiji da mace. = --Qur'an 92:3
    Indeed, your efforts are diverse. <> Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke. = --Qur'an 92:4
    As for he who gives and fears Allah <> To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa. = --Qur'an 92:5
    And believes in the best [reward], <> Kuma ya gaskata kalma mai kyãwo. = --Qur'an 92:6
    We will ease him toward ease. <> To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi. = --Qur'an 92:7
    But as for he who withholds and considers himself free of need <> Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa. = --Qur'an 92:8
    And denies the best [reward], <> Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo. = --Qur'an 92:9
    We will ease him toward difficulty. <> To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani. = --Qur'an 92:10
    And what will his wealth avail him when he falls? <> Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta). = --Qur'an 92:11
    Indeed, [incumbent] upon Us is guidance. <> Lãlle aikinMu ne, Mu bayyana shiriya. = --Qur'an 92:12
    And indeed, to Us belongs the Hereafter and the first [life]. <> Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne. = --Qur'an 92:13
    So I have warned you of a Fire which is blazing. <> Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka. = --Qur'an 92:14
    None will [enter to] burn therein except the most wretched one. <> Bãbu mai shigarta sai mafi shaƙãwa. = --Qur'an 92:15
    Who had denied and turned away. <> Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya. = --Qur'an 92:16
    But the righteous one will avoid it - <> Kuma mafi taƙawa zai nisance ta. = --Qur'an 92:17
    [He] who gives [from] his wealth to purify himself <> Wanda yake bãyar da dũkiyarsa, alhãli yana tsarkaka. = --Qur'an 92:18
    And not [giving] for anyone who has [done him] a favor to be rewarded <> Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta. = --Qur'an 92:19
    But only seeking the countenance of his Lord, Most High. <> Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka. = --Qur'an 92:20
    And he is going to be satisfied. <> To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi). = --Qur'an 92:21
    By the morning brightness <> Inã rantsuwa da hantsi. = --Qur'an 93:1
    And [by] the night when it covers with darkness, <> Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa). = --Qur'an 93:2
    Your Lord has not taken leave of you, [O Muhammad], nor has He detested [you]. <> Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba. = --Qur'an 93:3
    And the Hereafter is better for you than the first [life]. <> Kuma lalle ta ƙarshe ce mafi alheri a gare ka daga ta farko. = --Qur'an 93:4
    And your Lord is going to give you, and you will be satisfied. <> Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda. = --Qur'an 93:5
    Did He not find you an orphan and give [you] refuge? <> Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma? = --Qur'an 93:6
    And He found you lost and guided [you], <> Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai? = --Qur'an 93:7
    And He found you poor and made [you] self-sufficient. <> Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka? = --Qur'an 93:8
    So as for the orphan, do not oppress [him]. <> Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi. = --Qur'an 93:9
    And as for the petitioner, do not repel [him]. <> Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa. = --Qur'an 93:10
    But as for the favor of your Lord, report [it]. <> Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya). = --Qur'an 93:11
    Did We not expand for you, [O Muhammad], your breast? <> Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta)? = --Qur'an 94:1
    And We removed from you your burden <> Kuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe. = --Qur'an 94:2
    Which had weighed upon your back <> Wanda ya nauyayi bãyanka? = --Qur'an 94:3
    And raised high for you your repute. <> Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka? = --Qur'an 94:4
    For indeed, with hardship [will be] ease. <> To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi. = --Qur'an 94:5
    Indeed, with hardship [will be] ease. <> Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi. = --Qur'an 94:6
    So when you have finished [your duties], then stand up [for worship]. <> Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah). = --Qur'an 94:7
    And to your Lord direct [your] longing. <> Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi. = --Qur'an 94:8
    By the fig and the olive <> Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn. = --Qur'an 95:1
    And [by] Mount Sinai <> Da Dũr Sĩnĩna. = --Qur'an 95:2
    And [by] this secure city [Makkah], <> Da wannan gari amintacce. = --Qur'an 95:3
    We have certainly created man in the best of stature; <> Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa. = --Qur'an 95:4
    Then We return him to the lowest of the low, <> Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni = --Qur'an 95:5
    Except for those who believe and do righteous deeds, for they will have a reward uninterrupted. <> Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa. = --Qur'an 95:6
    So what yet causes you to deny the Recompense? <> To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)? = --Qur'an 95:7
    Is not Allah the most just of judges? <> Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba? = --Qur'an 95:8
    Recite in the name of your Lord who created - <> Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta. = --Qur'an 96:1
    Created man from a clinging substance. <> Ya hahitta mutum daga gudan jini. = --Qur'an 96:2
    Recite, and your Lord is the most Generous - <> Ka yi karatu, kuma UbangiJinka shi ne Mafi karimci. = --Qur'an 96:3
    Who taught by the pen - <> Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami. = --Qur'an 96:4
    Taught man that which he knew not. <> Ya sanar da mutum abin da bai sani ba. = --Qur'an 96:5
    No! [But] indeed, man transgresses <> A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu). = --Qur'an 96:6
    Because he sees himself self-sufficient. <> Dõmin yã ga kansa, yã wadãta. = --Qur'an 96:7
    Indeed, to your Lord is the return. <> Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take. = --Qur'an 96:8
    Have you seen the one who forbids <> Shin, kã ga wanda ke hana. = --Qur'an 96:9
    A servant when he prays? <> Bãwã idan yã yi salla? = --Qur'an 96:10
    Have you seen if he is upon guidance <> Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya? = --Qur'an 96:11
    Or enjoins righteousness? <> Ko ya yi umurni da taƙawa? = --Qur'an 96:12
    Have you seen if he denies and turns away - <> Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya? = --Qur'an 96:13
    Does he not know that Allah sees? <> Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani? = --Qur'an 96:14
    No! If he does not desist, We will surely drag him by the forelock - <> A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa. = --Qur'an 96:15
    A lying, sinning forelock. <> Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi. = --Qur'an 96:16
    Then let him call his associates; <> Sai ya kirayi ƙungiyarsa. = --Qur'an 96:17
    We will call the angels of Hell. <> Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma). = --Qur'an 96:18
    No! Do not obey him. But prostrate and draw near [to Allah]. <> A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u, kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka). = --Qur'an 96:19
    Indeed, We sent the Qur'an down during the Night of Decree. <> Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi (Alƙur'ãni) a cikin Lailatul ƙadari (daren daraja) = --Qur'an 97:1
    And what can make you know what is the Night of Decree? <> To, me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul ¡adari? = --Qur'an 97:2
    The Night of Decree is better than a thousand months. <> Lailatul ¡adari mafi alheri ne daga wasu watanni dubu. = --Qur'an 97:3
    The angels and the Spirit descend therein by permission of their Lord for every matter. <> Mala'iku da Rũhi suna sauka a cikinsa da iznin Ubangijinsu sabõda kowane umurni. = --Qur'an 97:4
    Peace it is until the emergence of dawn. <> Sallama ne shi daren, har fitar alfijiri. = --Qur'an 97:5
    Those who disbelieved among the People of the Scripture and the polytheists were not to be parted [from misbelief] until there came to them clear evidence - <> Waɗanda suka kãfirta daga mũtanen Littafi, da mushirikai, ba su kasance masu gushewa daga gaskiya ba har hujja ta je musu. = --Qur'an 98:1
    A Messenger from Allah, reciting purified scriptures <> Wani Manzo daga Allah, yana karatun wasu takardu masu tsarki. = --Qur'an 98:2
    Within which are correct writings. <> A cikinsu akwai wasu littafai mãsu ƙĩma da daraja. = --Qur'an 98:3
    Nor did those who were given the Scripture become divided until after there had come to them clear evidence. <> Kuma waɗanda aka bai wa Littafi ba su sãɓa wa juna ba face bayan hujjar ta je musu. = --Qur'an 98:4
    And they were not commanded except to worship Allah, [being] sincere to Him in religion, inclining to truth, and to establish prayer and to give zakah. And that is the correct religion. <> Kuma ba a umarce su da kome ba fãce bauta wa Allah suna mãsu tsarkake addinin gare Shi, mãsu karkata zuwa ga addinin gaskiya, kuma su tsai da salla kuma su bãyar da zakka, kuma wannan shi ne addinin waɗanda suke a kan hanyar ƙwarai. = --Qur'an 98:5
    Indeed, they who disbelieved among the People of the Scripture and the polytheists will be in the fire of Hell, abiding eternally therein. Those are the worst of creatures. <> Lalle ne waɗanda suka kafirta daga mutanen Littafi da mushirikai sana cikin wutar Jahannama suna madawwama a cikinta. Waɗannan su ne mafi ashararancin tãlikai. = --Qur'an 98:6
    Indeed, they who have believed and done righteous deeds - those are the best of creatures. <> Lalle ne waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, waɗannan su ne mafifita alherin halitta. = --Qur'an 98:7
    Their reward with Allah will be gardens of perpetual residence beneath which rivers flow, wherein they will abide forever, Allah being pleased with them and they with Him. That is for whoever has feared his Lord. <> Sakamakonsu, a wurin Ubangijinsu, shi ne gidajen Aljannar zama, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu sunã madawwama a cikinta har abada. Allah Ya yarda da su, kuma su, sun yarda da Shi. wannan sakamako ne ga wanda ya ji tsõron Ubangijinsa. = --Qur'an 98:8
    When the earth is shaken with its [final] earthquake <> Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta. = --Qur'an 99:1
    And the earth discharges its burdens <> Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi. = --Qur'an 99:2
    And man says, "What is [wrong] with it?" - <> Kuma mutum ya ce "Mẽ neya same ta?" = --Qur'an 99:3
    That Day, it will report its news <> A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta. = --Qur'an 99:4
    Because your Lord has commanded it. <> cewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta. = --Qur'an 99:5
    That Day, the people will depart separated [into categories] to be shown [the result of] their deeds. <> A rãnar nan mutane za su fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu. = --Qur'an 99:6
    So whoever does an atom's weight of good will see it, <> To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi. = --Qur'an 99:7
    And whoever does an atom's weight of evil will see it. <> Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi. = --Qur'an 99:8
    By the racers, panting, <> Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki. = --Qur'an 100:1
    And the producers of sparks [when] striking <> Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa. = --Qur'an 100:2
    And the chargers at dawn, <> Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba. = --Qur'an 100:3
    Stirring up thereby [clouds of] dust, <> Sai su motsar da ƙũra game da shi. = --Qur'an 100:4
    Arriving thereby in the center collectively, <> Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya. = --Qur'an 100:5
    Indeed mankind, to his Lord, is ungrateful. <> Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa. = --Qur'an 100:6
    And indeed, he is to that a witness. <> Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa dl haka. = --Qur'an 100:7
    And indeed he is, in love of wealth, intense. <> Kuma 1alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne. = --Qur'an 100:8
    But does he not know that when the contents of the graves are scattered <> Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura. = --Qur'an 100:9
    And that within the breasts is obtained, <> Aka bayyana abin da ke cikin zukata. = --Qur'an 100:10
    Indeed, their Lord with them, that Day, is [fully] Acquainted. <> Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne? = --Qur'an 100:11
    The Striking Calamity - <> Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)! = --Qur'an 101:1
    What is the Striking Calamity? <> Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa? = --Qur'an 101:2
    And what can make you know what is the Striking Calamity? <> Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa? = --Qur'an 101:3
    It is the Day when people will be like moths, dispersed, <> Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa. = --Qur'an 101:4
    And the mountains will be like wool, fluffed up. <> Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe. = --Qur'an 101:5
    Then as for one whose scales are heavy [with good deeds], <> To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi. = --Qur'an 101:6
    He will be in a pleasant life. <> To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda. = --Qur'an 101:7
    But as for one whose scales are light, <> Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi). = --Qur'an 101:8
    His refuge will be an abyss. <> To, uwarsa Hãwiya ce. = --Qur'an 101:9
    And what can make you know what that is? <> Kuma me ya sanar da kai mece ce ita? = --Qur'an 101:10
    It is a Fire, intensely hot. <> Wata wuta ce mai zafi. = --Qur'an 101:11
    Competition in [worldly] increase diverts you <> Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (dagaibada mai amfaninku). = --Qur'an 102:1
    Until you visit the graveyards. <> Har kuka ziyarci kaburbura. = --Qur'an 102:2
    No! You are going to know. <> A'aha! (Nan gaba) zã ku sani. = --Qur'an 102:3
    Then no! You are going to know. <> Sa'an nan, tabbas, zã ku sani. = --Qur'an 102:4
    No! If you only knew with knowledge of certainty... <> Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni. = --Qur'an 102:5
    You will surely see the Hellfire. <> Lalle ne da kuna ganin Jahĩm. = --Qur'an 102:6
    Then you will surely see it with the eye of certainty. <> Sa'an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane. = --Qur'an 102:7
    Then you will surely be asked that Day about pleasure. <> Sa'an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku). = --Qur'an 102:8
    By time, <> Ina rantsuwa da zãmani. = --Qur'an 103:1
    Indeed, mankind is in loss, <> Lalle ne mutum yana a cikin hasara. = --Qur'an 103:2
    Except for those who have believed and done righteous deeds and advised each other to truth and advised each other to patience. <> Fãce waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi wa juna wasiyya da bin gaskiya, kuma suka yi wa juna wasiyya da yin haƙuri (su kam, basu cikin hasara). = --Qur'an 103:3
    Woe to every scorner and mocker <> Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa). = --Qur'an 104:1
    Who collects wealth and [continuously] counts it. <> Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa. = --Qur'an 104:2
    He thinks that his wealth will make him immortal. <> Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi. = --Qur'an 104:3
    No! He will surely be thrown into the Crusher. <> A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama. = --Qur'an 104:4
    And what can make you know what is the Crusher? <> Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama? = --Qur'an 104:5
    It is the fire of Allah, [eternally] fueled, <> Wutar Allah ce wadda ake hurawa. = --Qur'an 104:6
    Which mounts directed at the hearts. <> Wadda take lẽƙãwa a kan zukata. = --Qur'an 104:7
    Indeed, Hellfire will be closed down upon them <> Lalle ne ita abar kullẽwa cea kansu. = --Qur'an 104:8
    In extended columns. <> A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu. = --Qur'an 104:9
    Have you not considered, [O Muhammad], how your Lord dealt with the companions of the elephant? <> Ashe, ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata ga mutanen giwa ba? = --Qur'an 105:1
    Did He not make their plan into misguidance? <> Ashe, bai sanya kaidinsu a cikin ɓata ba? = --Qur'an 105:2
    And He sent against them birds in flocks, <> Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a-jama'a. = --Qur'an 105:3
    Striking them with stones of hard clay, <> Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta. = --Qur'an 105:4
    And He made them like eaten straw. <> Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye? = --Qur'an 105:5
    For the accustomed security of the Quraysh - <> Sabõda sãbon ¡uraishawa. = --Qur'an 106:1
    Their accustomed security [in] the caravan of winter and summer - <> Sãbonsu na tafiyar hunturu da ta bazara. = --Qur'an 106:2
    Let them worship the Lord of this House, <> Sabõda haka sai su bauta wa Ubangijin wannan Gida (Ka'abah). = --Qur'an 106:3
    Who has fed them, [saving them] from hunger and made them safe, [saving them] from fear. <> wanda Ya ciyar da su (Ya hana su) daga yunwa, kuma Ya amintar da su daga wani tsõro. = --Qur'an 106:4
    Have you seen the one who denies the Recompense? <> Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako? = [107:1] Shin, ka san wanda ke qaryata addini? --Qur'an 107:1
    For that is the one who drives away the orphan <> To, wannan shi ne ke tunkue marãya (daga haƙƙinsa). = [107:2] To, wannan shi ne wanda wulakanta marayu. --Qur'an 107:2
    And does not encourage the feeding of the poor. <> Kuma bã ya kwaaitarwa bisa bãyar da abinci ga matalauci. = [107:3] Kuma ba ya qawaitad da bayar da abinci ga matalauci. --Qur'an 107:3
    So woe to those who pray <> To, bone yã tabbata ga masallata. = [107:4] Bone ya tabbata ga masallata. --Qur'an 107:4
    [But] who are heedless of their prayer - <> Waɗanda suke masu shagala daga sallarsu. = [107:5] Wadanda ba su kulawa daga sallarsu. --Qur'an 107:5
    Those who make show [of their deeds] <> Waɗanda suke yin riya (ga ayyukansu) = [107:6] Wadanda suke yin riya ne kawai --Qur'an 107:6
    And withhold [simple] assistance. <> Kuma suna hana taimako. = [107:7] Kuma suna hana taimako. --Qur'an 107:7
    Indeed, We have granted you, [O Muhammad], al-Kawthar. <> Lalle ne Mu, Mun yi maka kyauta mai yawa. = [108:1] Mun yi maka kyauta mai yawa. --Qur'an 108:1
    So pray to your Lord and sacrifice [to Him alone]. <> Saboda haka, ka yi salla dõmin Ubangijinka, kuma ka sõke (baiko, wato sukar raƙumi). = [108:2] Saboda haka, ka yi sallah domin Ubangijinka, kuma ka yi sadaqa. --Qur'an 108:2
    Indeed, your enemy is the one cut off. <> Lalle mai aibanta ka shi ne mai yankakkiyar albarka. = [108:3] Mai adawa da kai, shi ne zai yi hasara. --Qur'an 108:3
    Say, "O disbelievers, <> Ka ce: "Ya kũ kãfirai!" = [109:1] Ka ce, "Ya ku kafirai. --Qur'an 109:1
    I do not worship what you worship. <> "Bã zan bautã wa abin da kuke bautã wa ba." = [109:2] "Ba na bauta wa abin da kuke bauta wa." --Qur'an 109:2
    Nor are you worshippers of what I worship. <> "Kuma kũ, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bautã wa ba." = [109:3] "Kuma ku, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bauta wa ba." --Qur'an 109:3
    Nor will I be a worshipper of what you worship. <> "Kuma nĩ ban zama mai bautã wa abin da kuka bautã wa ba." = [109:4] "Kuma ni ba zan taba zama mai bauta wa abin da kuke bauta wa ba. --Qur'an 109:4
    Nor will you be worshippers of what I worship. <> "Kuma kũ, ba ku zama mãsu bautã wa abin da nake bautã wa ba." = [109:5] "Kuma ku, ba za ku taba zama masu bauta wa abin da nike bauta wa ba." --Qur'an 109:5
    For you is your religion, and for me is my religion." <> "Addininku na garẽ ku, kuma addinina yanã gare ni." = Addininku na gare ku, kuma addinina na gare ni. --Qur'an 109:6
    When the victory of Allah has come and the conquest, <> Idan taimakon Allah ya zo da cin nasara. = [110:1] Idan taimakon ALLAH ya zo da cin nasara. --Qur'an 110:1
    And you see the people entering into the religion of Allah in multitudes, <> Kuma ka ga mutane suna shiga addinin Allah, ƙungiya-ƙungiya. = [110:2] Kuma ka ga mutane suna shiga addinin ALLAH, qungiya-qungiya. --Qur'an 110:2
    Then exalt [Him] with praise of your Lord and ask forgiveness of Him. Indeed, He is ever Accepting of repentance. <> To, ka yi tasbihi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka nẽme Shi gafara, lalle Shi (Ubangijinka) Ya kasance Mai karɓar tũba ne. = [110:3] To, ka yi tasbihi game da gode wa Ubangijinka, kuma ka neme Shi gafara, Shi ne Mai karbar tuba. --Qur'an 110:3
    May the hands of Abu Lahab be ruined, and ruined is he. <> Hannãye biyu na Abũlahabi sun halaka, kuma ya halaka. = [111:1] Hannaye biyu na Abulahabi sun halaka, kuma ya halaka. --Qur'an 111:1
    His wealth will not avail him or that which he gained. <> Dũkiyarsa ba ta tsare masa kõme ba, da abin da ya tãra. = [111:2] Dukiyarsa da duk abin da ya tara, ba za su taimaka masa ba. --Qur'an 111:2
    He will [enter to] burn in a Fire of [blazing] flame <> Zã ya shiga wuta mai hũruwa. = [111:3] Ya jawo wa kansa wuta mai huruwa. --Qur'an 111:3
    And his wife [as well] - the carrier of firewood. <> Tãre da matarsa mai ɗaukar itacen (wuta). = [111:4] Tare da matarsa wanda ta yi jagorar gallazawa. --Qur'an 111:4
    Around her neck is a rope of [twisted] fiber. <> A cikin kyakkyãwan wuyanta akwai igiya ta kaba (Rãnar ¡iyãma). = [111:5] Za tayar da ita (Alqiyamah) da igiyar qaya a wuyanta. --Qur'an 111:5
    Say, "He is Allah, [who is] One, <> Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci." = [112:1] Ka ce, "Shi ne ALLAH Makadaci." --Qur'an 112:1
    Allah, the Eternal Refuge. <> "Allah wanda ake nufin Sa da buƙata." = [112:2] "]ALLAH wanda Shi ne cikakke." --Qur'an 112:2
    He neither begets nor is born, <> "Bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba." = [112:3] "Bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba." --Qur'an 112:3
    Nor is there to Him any equivalent." <> "Kuma babu ɗaya da ya kasance tamka a gare Shi." = [112:4] "Kuma babu daya da ya kasance tamka a gare Shi." --Qur'an 112:4
    Say, "I seek refuge in the Lord of daybreak <> Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin safiya" = [113:1] Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin safiya" --Qur'an 113:1
    From the evil of that which He created <> "Daga sharrin abin da Ya halitta." = [113:2] "Daga sharrin abin da Ya halitta." --Qur'an 113:2
    And from the evil of darkness when it settles <> "Da sharrin dare, idan ya yi duhu." = [113:3] "Da sharrin dare, idan ya yi duhu." --Qur'an 113:3
    And from the evil of the blowers in knots <> "Da sharrin mãtã mãsu tõfi a cikin ƙulle-ƙulle." = [113:4] "Da sharrin mata masu tofi a cikin qulle-qulle." --Qur'an 113:4
    And from the evil of an envier when he envies." <> "Da sharrin mai hãsada idan ya yi hasada." = [113:5] "Da sharrin mai hasada idan ya yi hasada." --Qur'an 113:5
    Say, "I seek refuge in the Lord of mankind, <> Ka ce "Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne." = [114:1] Ka ce, "Ina neman tsari ga Ubangijin mutane." --Qur'an 114:1
    The Sovereign of mankind. <> "Mamallakin mutane." = [114:2] "Mamallakin mutane." --Qur'an 114:2
    The God of mankind, <> "Abin bautãwar mutãne." = [114:3] "Abin bautawar mutane." --Qur'an 114:3
    From the evil of the retreating whisperer - <> "Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa." = [114:4] "Daga sharrin mai sanya wasuwasi, mai silalewa." --Qur'an 114:4
    Who whispers [evil] into the breasts of mankind - <> "Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane." = [114:5] "Wanda ke sanya wasuwasi a cikin sadarin mutane." --Qur'an 114:5
    From among the jinn and mankind." <> "Daga aljannu da mutane." = [114:6] "Daga aljannu da mutane." --Qur'an 114:6