Day 10 - 2020 Ramadan Tafsir with Dr Isa Ali Pantami - May 3, 2020
Intro
Kamar yadda muka saba haɗuwa a wannan yammaci don tafsirin Ƙur'ani mai girma, bisa ga horewa da yadda da amincewa na Allahu subhanahu wata'ala, za mu cigaba da karatu yau. Za mu tashi akan darasi na goma a wata na Ramadana hijira shekara ta 1441 inshaAllah. Karatu da muke gabatarwa, daga ni sai alaramma kuma ake isar da shi ga al'umma, imma ta kafofin sadarwa na zumunci ko akwatin talabijin ko a cikin rediyo saboda hali da muka samu kanmu.