gizo (gizo, sn., nj., mc., kooki) (1) wata halitta mai wayo ta cikin tatsuniyoyin Hausa. (ii) mutum mai wayo. (iii) bakan-; watau (a) wani abu mai kama da baka mai launi-launi da yake fitowa idan an yi hadari, wanda yake ba kasafai akan yi ruwa ba idan ya fito. (b) daurin guga. (c) wata irin iska (aljan) da ake samu a cikin rijiyoyi. (iv) siddabaru.
gizo (gizoo, sn., nj.) (i) suma mai tsawo wadda take ba a gyara ta ba. (ii) gidan ~; watau gidan yari.