Hausa
|
English
|
Original
|
Translation
|
Steve Lucas yayi Bankwana da Muryar Amurka
|
Steve Lucas says goodbye to the Voice of America
|
By Ibrahim Alfa Ahmed
|
By Ibrahim Alfa Ahmed
|
01/08/2008
|
August 1, 2008
|
A bayan da ya shafe shekaru 24
|
After serving for 24 years
|
a nan Muryar Amurka,
|
here at the Voice of America,
|
Steve Lucas ya yi ban kwana
|
Steve Lucas bids farewell
|
da wannan gidan rediyo.
|
to the radio station.
|
Ma'aikatan Sashen Hausa
|
The Hausa Service employees
|
ba su bar shi
|
weren't letting him
|
ya tafi haka ba,
|
leave quietly,
|
domin kuwa sun shirya masa
|
as they organized
|
wata babbar liyafar
|
a send-off party for him,
|
da ta samu halartar
|
which was attended by
|
shugabannin sassa da dama,
|
heads of several departments,
|
da darektar Afirka
|
the Africa Division director,
|
da kuma darektan shirye-shirye na Afirka.
|
and the Africa Division program manager.
|
Shi dai Steve Lucas
|
Steve Lucas
|
ya fara
|
began
|
aiki da Muryar Amurka
|
working at the Voice of America
|
a matsayin mai labaran Hausa.
|
as a Hausa newscaster.
|
Daga nan ya zamo
|
Then he became
|
shugaban Sashen Hausa,
|
head of the Hausa Service
|
ya kuma zamo
|
and then
|
shugaban Sashen Afirka baki daya.
|
head of the entire Africa Division.
|
An nada Steve Lucas
|
Steve Lucas was then appointed as
|
darektan ofishin hulda da gidajen rediyon Afirka.
|
director in charge of African Affiliate Stations.
|
Kafin ritayarsa kuwa,
|
Before his retirement,
|
shi ne darektan ofishin hulda da gidajen rediyon duniya
|
he was director of the Office of Marketing and Program Placement
|
na Muryar Amurka.
|
for the Voice of America.
|
Ofishin ya shirya masa wata
|
This office threw him
|
liyafar ban kwana
|
a farewell party
|
a ranar talatar makon jiya.
|
last Tuesday.
|
A ranar larabar wannan makon kuma,
|
And this Wednesday,
|
Sashen Hausa ya karrama Steve Lucas
|
the Hausa Service honored Steve Lucas,
|
da maidakinsa Fatouma
|
his wife Fatouma
|
da sauran iyalinsa
|
and the rest of his family
|
a lokacin wata liyafar da ta hada da
|
at a party that also
|
mika masa lambar yabo
|
awarded him a plaque,
|
a zaman daya daga cikin jigogin kafawa
|
in recognition of his role in the establishment
|
da bunkasar
|
and development of
|
Sashen Hausa na Muryar Amurka.
|
Voice of America's Hausa Service.
|
Shugaban Sashen Hausa,
|
The head of the Hausa Service,
|
Sunday Dare, ya yaba ma Steve
|
Sunday Dare, praised Steve
|
a zaman mai basira
|
for his intelligence
|
da hangen nesa,
|
and foresight,
|
wanda har bayan barinsa Sashen Hausa
|
saying that even after his transfer to other departments,
|
ya ci gaba
|
he continued
|
da taimakawa da yin amfani da kwazonsa wajen ganin ci gaban Sashen.
|
to support the Hausa Service.
|
Ita ma tsohuwar fardusar Sashen hausa, Donnie Butler,
|
Donnie Butler, a former producer in the Hausa Service,
|
wadda ta yi ritaya
|
who retired
|
a 'yan shekarun baya,
|
a few years ago,
|
ta yiwo tattaki musamman
|
went on at great length
|
domin ta bayyana
|
to describe
|
irin karimcin Steve Lucas da yadda ya rike mutane hannu bibbiyu a Sashen Hausa.
|
how much she and others who worked with Steve Lucas continue to miss him.
|
Donnie Butler ta yi jawabi mai sosa zuciya kan irin kewar da ita da sauran wadanda suka yi aiki tare da Steve Lucas zasu yi na barinsa aiki.
|
Donnie Butler, a former producer in the Hausa Service, who retired a few years ago, went on at great length to describe how much she and others who worked with Steve Lucas continue to miss him.
|
Shirin "A Bari Ya Huce..." na wannan asabar,
|
Next Saturday’s edition of the "A Bari Ya Huce…" program
|
ya kunshi tattaunawa
|
will feature an interview
|
da Steve Lucas tare da maidakinsa Fatouma
|
with Steve Lucas and his wife Fatouma
|
a kan shawararsu
|
on their decision
|
ta yin ritaya
|
to retire
|
da kuma irin abubuwan da zasu yi nan gaba.
|
and their future plans.
|
Wakilin Sashen hausa na farko,
|
The first Hausa Service stringer,
|
Sani Abdullahi Tsafe,
|
Sani Abdullahi Tsafe,
|
shi ma ya tofa albarkacin bakinsa cikin shirin
|
will also participate in the program,
|
a kan halayyan dattaku na Steve Lucas.
|
where he comments on for Steve Lucas' gentlemanly character.
|
n/a
|
[Translator’s note: The program title "A Bari Ya Huce…" is derived from a Hausa proverb ("A bari ya huce shi ke kawo rabon wani"), which translates as "Seize the moment."]
|
Babu shakka,
|
Without a doubt,
|
dukkanmu
|
all of us
|
a nan
|
here
|
Sashen Hausa
|
at the Hausa Service
|
za mu yi kewar Steve Lucas,
|
will miss Steve Lucas;
|
amma da yake Nijar zai koma ya zauna,
|
But since he is moving to Niger Republic;
|
mun san cewa
|
we know that,
|
in sha Allahu
|
God willing,
|
ba ganin karshe ba ke nan da shi.
|
we have not seen the last of him.
|
Hausa
|
English
|
Original
|
Translation
|
Steve Lucas yayi Bankwana da Muryar Amurka
|
Steve Lucas says goodbye to the Voice of America
|
By Ibrahim Alfa Ahmed
|
By Ibrahim Alfa Ahmed
|
01/08/2008
|
August 1, 2008
|
A bayan da ya shafe shekaru 24
|
After serving for 24 years
|
a nan Muryar Amurka,
|
here at the Voice of America,
|
Steve Lucas ya yi ban kwana
|
Steve Lucas bids farewell
|
da wannan gidan rediyo.
|
to the radio station.
|
Ma'aikatan Sashen Hausa
|
The Hausa Service employees
|
ba su bar shi
|
weren't letting him
|
ya tafi haka ba,
|
leave quietly,
|
domin kuwa sun shirya masa
|
as they organized
|
wata babbar liyafar
|
a send-off party for him,
|
da ta samu halartar
|
which was attended by
|
shugabannin sassa da dama,
|
heads of several departments,
|
da darektar Afirka
|
the Africa Division director,
|
da kuma darektan shirye-shirye na Afirka.
|
and the Africa Division program manager.
|
Shi dai Steve Lucas
|
Steve Lucas
|
ya fara
|
began
|
aiki da Muryar Amurka
|
working at the Voice of America
|
a matsayin mai labaran Hausa.
|
as a Hausa newscaster.
|
Daga nan ya zamo
|
Then he became
|
shugaban Sashen Hausa,
|
head of the Hausa Service
|
ya kuma zamo
|
and then
|
shugaban Sashen Afirka baki daya.
|
head of the entire Africa Division.
|
An nada Steve Lucas
|
Steve Lucas was then appointed as
|
darektan ofishin hulda da gidajen rediyon Afirka.
|
director in charge of African Affiliate Stations.
|
Kafin ritayarsa kuwa,
|
Before his retirement,
|
shi ne darektan ofishin hulda da gidajen rediyon duniya
|
he was director of the Office of Marketing and Program Placement
|
na Muryar Amurka.
|
for the Voice of America.
|
Ofishin ya shirya masa wata
|
This office threw him
|
liyafar ban kwana
|
a farewell party
|
a ranar talatar makon jiya.
|
last Tuesday.
|
A ranar larabar wannan makon kuma,
|
And this Wednesday,
|
Sashen Hausa ya karrama Steve Lucas
|
the Hausa Service honored Steve Lucas,
|
da maidakinsa Fatouma
|
his wife Fatouma
|
da sauran iyalinsa
|
and the rest of his family
|
a lokacin wata liyafar da ta hada da
|
at a party that also
|
mika masa lambar yabo
|
awarded him a plaque,
|
a zaman daya daga cikin jigogin kafawa
|
in recognition of his role in the establishment
|
da bunkasar
|
and development of
|
Sashen Hausa na Muryar Amurka.
|
Voice of America's Hausa Service.
|
Shugaban Sashen Hausa,
|
The head of the Hausa Service,
|
Sunday Dare, ya yaba ma Steve
|
Sunday Dare, praised Steve
|
a zaman mai basira
|
for his intelligence
|
da hangen nesa,
|
and foresight,
|
wanda har bayan barinsa Sashen Hausa
|
saying that even after his transfer to other departments,
|
ya ci gaba
|
he continued
|
da taimakawa da yin amfani da kwazonsa wajen ganin ci gaban Sashen.
|
to support the Hausa Service.
|
Ita ma tsohuwar fardusar Sashen hausa, Donnie Butler,
|
Donnie Butler, a former producer in the Hausa Service,
|
wadda ta yi ritaya
|
who retired
|
a 'yan shekarun baya,
|
a few years ago,
|
ta yiwo tattaki musamman
|
went on at great length
|
domin ta bayyana
|
to describe
|
irin karimcin Steve Lucas da yadda ya rike mutane hannu bibbiyu a Sashen Hausa.
|
how much she and others who worked with Steve Lucas continue to miss him.
|
Donnie Butler ta yi jawabi mai sosa zuciya kan irin kewar da ita da sauran wadanda suka yi aiki tare da Steve Lucas zasu yi na barinsa aiki.
|
Donnie Butler, a former producer in the Hausa Service, who retired a few years ago, went on at great length to describe how much she and others who worked with Steve Lucas continue to miss him.
|
Shirin "A Bari Ya Huce..." na wannan asabar,
|
Next Saturday’s edition of the "A Bari Ya Huce…" program
|
ya kunshi tattaunawa
|
will feature an interview
|
da Steve Lucas tare da maidakinsa Fatouma
|
with Steve Lucas and his wife Fatouma
|
a kan shawararsu
|
on their decision
|
ta yin ritaya
|
to retire
|
da kuma irin abubuwan da zasu yi nan gaba.
|
and their future plans.
|
Wakilin Sashen hausa na farko,
|
The first Hausa Service stringer,
|
Sani Abdullahi Tsafe,
|
Sani Abdullahi Tsafe,
|
shi ma ya tofa albarkacin bakinsa cikin shirin
|
will also participate in the program,
|
a kan halayyan dattaku na Steve Lucas.
|
where he comments on for Steve Lucas' gentlemanly character.
|
n/a
|
[Translator’s note: The program title "A Bari Ya Huce…" is derived from a Hausa proverb ("A bari ya huce shi ke kawo rabon wani"), which translates as "Seize the moment."]
|
Babu shakka,
|
Without a doubt,
|
dukkanmu
|
all of us
|
a nan
|
here
|
Sashen Hausa
|
at the Hausa Service
|
za mu yi kewar Steve Lucas,
|
will miss Steve Lucas;
|
amma da yake Nijar zai koma ya zauna,
|
But since he is moving to Niger Republic;
|
mun san cewa
|
we know that,
|
in sha Allahu
|
God willing,
|
ba ganin karshe ba ke nan da shi.
|
we have not seen the last of him.
|
A bayan da ya shafe shekaru 24 a nan Muryar Amurka, Steve Lucas yayi ban kwana da wannan gidan rediyo. Ma'aikatan Sashen Hausa ba su bar shi ya tafi haka ba, domin kuwa sun shirya masa wata babbar liyafar da ta samu halartar shugabannin sassa da dama, da darektar Afirka da kuma darektan shirye-shirye na Afirka.
Shi dai Steve Lucas ya fara aiki da Muryar Amurka a matsayin mai labaran Hausa. Daga nan ya zamo shugaban Sashen Hausa, ya kuma zamo shugaban Sashen Afirka baki daya. An nada Steve Lucas darektan ofishin hulda da gidajen rediyon Afirka.
Kafin ritayarsa kuwa, shi ne darektan ofishin hulda da gidajen rediyon duniya na Muryar Amurka. Ofishin ya shirya masa wata liyafar ban kwana a ranar talatar makon jiya. A ranar larabar wannan makon kuma, Sashen Hausa ya karrama Steve Lucas da maidakinsa Fatouma da sauran iyalinsa a lokacin wata liyafar da ta hada da mika masa lambar yabo a zaman daya daga cikin jigogin kafawa da bunkasar Sashen Hausa na Muryar Amurka.
Shugaban Sashen Hausa, Sunday Dare, ya yaba ma Steve a zaman mai basira da hangen nesa, wanda har bayan barinsa Sashen Hausa ya ci gaba da taimakawa da yin amfani da kwazonsa wajen ganin ci gaban Sashen.
Ita ma tsohuwar fardusar Sashen hausa, Donnie Butler, wadda ta yi ritaya a 'yan shekarun baya, ta yiwo tattaki musamman domin ta bayyana irin karimcin Steve Lucas da yadda ya rike mutane hannu bibbiyu a Sashen Hausa. Donnie Butler ta yi jawabi mai sosa zuciya kan irin kewar da ita da sauran wadanda suka yi aiki tare da Steve Lucas zasu yi na barinsa aiki.
Shirin "A Bari Ya Huce..." na wannan asabar, ya kunshi tattaunawa da Steve Lucas tare da maidakinsa Fatouma a kan shawararsu ta yin ritaya da kuma irin abubuwan da zasu yi nan gaba. Wakilin Sashen hausa na farko, Sani Abdullahi Tsafe, shi ma ya tofa albarkacin bakinsa cikin shirin a kan halayyan dattaku na Steve Lucas.
Babu shakka, dukkanmu a nan Sashen Hausa za mu yi kewar Steve Lucas, amma da yake Nijar zai koma ya zauna, mun san cewa in sha Allahu ba ganin karshe ba ke nan da shi.
|