babban birnin tarayyan Naijeriya kuma fadan gwamnatin tarayyar Naijeriya wanda ake yiwa lak'abi da centre of unity. wato 'cibiyar had'in kai'
Kalmar ta samo asali ne daga sunan wad'ansu 'Yan uwan juna masu jan fata, wato 'Habu ja' da kuma 'Sule ja', inda sunan 'Sule ja' shine aka sanyawa wani birni dake Jihar Niger, a yayin da 'Habu ja' kuma aka sanya wa Babban birnin tarayya, to amma daga baya sunan ya rikid'e zuwa 'Abuja' saboda galibi mutanen kudu basa iya furta harafin 'ha'
Birnin Abuja yana tsakiyan Naijeriya ne tsakanin kuda da arewa, wanda kuma yake da Yawan jama'an da suka kai dubu d'ari bakwai da dubu saba'in da shida da d'ari biyu da casa'in da takwas (a bisa k'idayan shekara ta dubu biyu da shida), shine birni na goma mafi yawan jama'a a Naijeria, kuma an fara gina birnin Abuja ne a shekara ta alif d'ari tara da tamanin (1980), kuma sannan aka ayyana shi a matsayin babban birnin tarayyan Naijeriya a ranar sha biyu ga watan sha biyu ta shekara ta alif d'ari tara da casa'in da d'aya (12-12-1991) a lokacin shugabancin mulkin soji na Ibrahim Badamasi Babangida.