Suratu Al Imrana, Aya Ta 1-7 (Kashi Na 74)
Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, a cikin shirin da ya gabata an ji bayani kan aya ta karshe a cikin suratul Baqara, a yau kuma da yardarm Allah za mus higa cikin siratul Ali Imran.
Wannan sura ta safka ne a Madina, ita ce kuma sura ta uku a cikin kur'ani mai tsarki, kuma an ambaci wannan sura da wannan suna ne saboda ambaton sunan Imran da aka yi a cikin aya ta 33, wannan shi ne sunan mahaifin annabi Musa (AS), kuma sunan mahaifin Maryam mahaifiyar annabi (AS) koda yake a cikin wannan sura an ambaci kissar Maryar ne da danta Isa Almasihu (AS)
Sai mu saurari aya ta farko a cikin wannan sura ta Ali Imran:
Aya ta ( 1 ) da ( 2 ) Ali Imran:
الم{1} اللّهُ لا إِلَـهَ إِلاَّ هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ{2}
A. L̃. M̃. Allah, bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Rãyayye Mai tsayuwa da kõme.
Haruffan Alif-Lam-Mim, a cikin suratul Baqara mun yi bayani kan wadannan haruffa, cewa Allah madaukakin sarki ya bar wa kansa sanin ma'anarsu da shi da manzonsa, wanda wannan yana daya daga cikin mu'ujizoji na kur'ani mai tsarki kamar yadda bayani ya gabata a baya.
Ayar da ke bayan wannan kuwa, tana yin bayani ne kan siffofin Allah madaukakin sarki, wanda ya hada dukkanin kamala, ya tsarkaka daga duk wani aibi, ba a zatinsa ba kawai, a a hatta a cikin dukkanin siffofinsa. Allah shi kadai ne ba shi abokin tarayya, kuma dawwamamme ne har abada, sabanin mu abin halitta, a da babu mu, sannan aka samar da mu, kuma wani lokaci zai zo da babu mu, alhali Allah haka ba ta faruwa da shi, bil hasali ma shi ne mai samarwa da rasarwa, shi kadai ne ya cancanci bautar ba yi, baya ga shi babu wani mahaluki da ya cancanci a bauta masa a matsayin ubangiji.
Darasi daga wannan aya:
Allah ne kawai ake rusanawa a matsayin ubangiji, babu wani mahaluki da zaim iya maye gurbin Allah madaukakin sarki, komai ikonsa da dukiyarsa da karfin jikinsa.
Ayoyi na ( 3 ) zuwa ( 4 ) Ali Imran:
نَزَّلَ عَلَيْكَ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ مُصَدِّقاً لِّمَا بَيْنَ يَدَيْهِ وَأَنزَلَ التَّوْرَاةَ وَالإِنجِيلَ{3} مِن قَبْلُ هُدًى لِّلنَّاسِ وَأَنزَلَ الْفُرْقَانَ إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُواْ بِآيَاتِ اللّهِ لَهُمْ عَذَابٌ شَدِيدٌ وَاللّهُ عَزِيزٌ ذُو انتِقَامٍ{4}
Yã sassaukar da Littãfi a gare ka da gaskiya, yana mai gaskatãwa ga abin da ke gaba gare shi, kuma Allah Yã saukar da Attaura da Linjĩlã. A gabãni, suna shiryar da mutãne, kuma Ya saukar da littattafai mãsu rarrabẽwa. Lalle ne wadanda suka kãfirta da ãyõyin Allah, suna da azãba mai tsanani. Kuma Allah Mabuwayi ne, Ma'abucin azãbar rãmuwa.
Wasu daga cikin ahlul kitab a lokacin ma'aki (SAW) duk da masaniyar da suke da ita ta zuwan kur'ani mai tsarki daga Allah madaukin sarkin bayan littafan Attauara da Injinla, amma ba a shirye suke ba su yi imani da manzon karshe, kuma su karbi kur'ani mai tsarki a matsayin littafin da ya zo daga Allah madaukakin sarki.
Wannan aya ta ba su amsa da cewa, a tsawon tarihi Allah yana aiko annabawa domin shiryar da mutane, wasu daga cikinsu ana ba su sha'ri'a da littafi, dukaknin wadannan annabawa sun gasgata junasu, saboda dukakninsu daga Allah ubagiji daya suke, kuma sakonsa ne suke isarwa ga 'yan adam. A kan haka babu wani abun mamaki, domin kuwa ubangijin da ya safkar da Attauara ga annabi Musa (AS) ya safkar da Injila ga annabi Isa (AS), shi ne ya safkar da kur'ani ga manzon Muhammad (SAW)
Saboda haka wannan aya ta gaya musu cewa idan da gasket suna neman gaskiya ne, to wajibi ne su yi iani da annabi Muhammad da sakon da ya zo da shi daga Allah.
Darussan koyo daga wadannan ayoyi masu albarka:
1- Manufar zuwan dukaknin annabawa da safkar da littafai ita ce shiryar da mutane zuwa ga kadaita Allah madaukakin sarki.
2 – A duk lokacin da muka shiga dimuwa da fangima, to ku koma zuwa ga kur'ani mai tsarki, domin shi wasila ne na banbamce gaskiya da karya.
Ayoyi na ( 5 ) da ( 6 ) Ali Imran:
إِنَّ اللّهَ لاَ يَخْفَىَ عَلَيْهِ شَيْءٌ فِي الأَرْضِ وَلاَ فِي السَّمَاء{5} هُوَ الَّذِي يُصَوِّرُكُمْ فِي الأَرْحَامِ كَيْفَ يَشَاءُ لاَ إِلَـهَ إِلاَّ هُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ{6}
Lalle ne, Allah bãbu wani abin da ke bõyuwa gare Shi a cikin kasa, kuma bãbu a cikin sama. Shi ne wanda Yake suranta ku a cikin mahaifu yadda Yake so. Bãbu abin bautã wa fãce Shi Mabuwãyi, Mai hikima.
Daya daga manyan ayyukan zalunci shi ne rafkana daga ubangiji, alhali babu wani lokaci da mutum ba ya karkashin ikon ubangiji, kuma yana gani da sauraren dukkanin ayyukan mutum, ba ma mutum ba wanda adadinsa ko alama bai kai halittun Allah da ke cikin sammai da kassai ba, wadanda su ma Allah yana tare da su, yana da masaniya kan dukkanin abin da suke yi, bil hasali ma shi ne ke ikon tafiyar da su baki daya, babu abin da ke buya ga Allah, a cikin sammai da kassai da abin da ke tsakaninsu, hatta ma jariri da ke cikin mahaifa samuwarsa tana hannun Allah, shi ne yake tsara halittar jinjiri a cikin mahaifa har ya kai lokacin da zai gama girma a haife shi, ya raya shi ya kare shi, lallai Allah shi ne mai hikima.
Darussa daga wadannan ayoyi masu albarka:
1 – Yawan mutane da ababen halitta, da banbancin zamunansu da wurarensu, duk hakan ba ya sanya ubangiji ya rafkana da wani abu kankancinsa daga cikin halittunsa.
2 – Duk da cewa Allah mai karfin iko ne a kan komai da yin duk abin yake so, amma kuma a lokaci guda Allah ba ya yin wani abu da babu hikima a cikinsa.
Aya ta ( 7 ) Ali Imran:
هُوَ الَّذِيَ أَنزَلَ عَلَيْكَ الْكِتَابَ مِنْهُ آيَاتٌ مُّحْكَمَاتٌ هُنَّ أُمُّ الْكِتَابِ وَأُخَرُ مُتَشَابِهَاتٌ فَأَمَّا الَّذِينَ في قُلُوبِهِمْ زَيْغٌ فَيَتَّبِعُونَ مَا تَشَابَهَ مِنْهُ ابْتِغَاء الْفِتْنَةِ وَابْتِغَاء تَأْوِيلِهِ وَمَا يَعْلَمُ تَأْوِيلَهُ إِلاَّ اللّهُ وَالرَّاسِخُونَ فِي الْعِلْمِ يَقُولُونَ آمَنَّا بِهِ كُلٌّ مِّنْ عِندِ رَبِّنَا وَمَا يَذَّكَّرُ إِلاَّ أُوْلُواْ الألْبَابِ
Shi ne wanda ya saukar da littãfi a gare ka, daga cikinsa akwai ãyõyi bayyanannu, su ne mafi yawan Littãfin, da wasu mãsu kamã da jũna. To, amma wadanda a cikin zukãtansu akwai karkata sai suna bin abin da yake da kamã da jũna daga gare shi, dõmin nẽman yin fitina da tãwĩlinsa. Kuma bãbu wanda ya san tãwĩlinsa fãce Allah. Kuma matabbata a cikin ilmi sunã cẽwa: "Mun yi ĩmãni da shi; dukkansa daga wurin Ubangijinmu yake." Kuma bãbu mai tunãni fãce ma'abũta hankula.
A nan an ambaci ayoyin bayyanannu (muhkamat) da kuma masu kama da juna (mutashabihat) bayyanannu a nan su ne ayoyi kamar (kul huwallahu ahad) (ka ce Allah daya ne) wato Allah daya ne rak, ba shi da na biyu, to irin wadannan ayoyin bayyanannu ne, amma ayoyi masu kama da juna, su ne masu bukatar a yi bayanin abin da ake nufi, domin ma'anarsu ba a fili take ba, kamar ayar da ta ce: Hannun Allah yana kan hannayensu, wannan aya na bukatar karin haske daga malamai wadanda sukan hakikanin tafsirin kur'ani mai tsarki, domin kuwa Allah ba jiki ba ne balantana ya kasance da hannu, ga shi kuma zahirin ayar ta ambaci cewa hannun Allah yana kan hannayensu, yayin da malaman tafsiri bisa dogaro da sahihin nassi, sun bayyana ma'anar hakan da cewa; ma'anar hannun Allah a nan ita ce karfin ikonsa da mulkinsa yana birbishin na dukkanin talikai. Haka lamarin yake a sauran ayoyi makamantan wadannan.
Sau da yawa wasu kan gina akidunsu bisa dogaro da zahirin ayoyi masu kama da juna (mutashabihat) sai hakan ya kai su ga suranta Allah madaukakin sarki tamkar wani mutum ko wani abun halitta, alhali kuwa irin wadannan ayoyi na kur'ani suna bukatar tawili, kamar yadda wannan ayar ta ce babu wanda ya san tawilinsu sai Allah da kuma wadanda suka tsaga ilimi, wato annabawa da kuma wasiyyansu, da kuma wasu daga cikin salihan bayin Allah, a kan haka a irin wannan yanayi dole ne a koma gare su domin sanin ma'anar ayoyi masu kama da juna.
Darussan koyo daga wannan aya mai albarka:
1- Wasu daga cikin ayoyin kur'ani mai tsarki suna da ma'ana sabanin zahirin ayar, a irin wannan yanayi dole ne a koma ga masana na hakika, maimakon yin gaban kai wajen fassara kur'ani bisa fahimta ta kuskure.
2 – Wasu daga cikin mutane da sunan muslunci, da sunan riko da kur'ani da akidar musulunci suna juya sahihiyar akidar musulmi kan tauhidin Ubangiji (tsarki ya tabbata a gare shi madaukakin sarki)
3 – Ba rikici da hanayaniya ko fadace-fadace ce kawai ake nufi da fitina ba, babbar fitina ita ce a juya hakikanin akidar addini da tauhidin musulmi zuwa wani abu daban da ba haka yake a cikin addinin muslunci ba, fassara ayoyin ubangiji bisa san rai ko jahilci.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 8-13 (Kashi Na 75)
Jama'a masu saurare Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, sai mu fara da sauraren ayoyi na 8 da 9 a cikin suraul Ali Imran.
Ayoyi na ( 8 ) da ( 9) Ali Imran:
رَبَّنَا لاَ تُزِغْ قُلُوبَنَا بَعْدَ إِذْ هَدَيْتَنَا وَهَبْ لَنَا مِن لَّدُنكَ رَحْمَةً إِنَّكَ أَنتَ الْوَهَّابُ{8} رَبَّنَا إِنَّكَ جَامِعُ النَّاسِ لِيَوْمٍ لاَّ رَيْبَ فِيهِ إِنَّ اللّهَ لاَ يُخْلِفُ الْمِيعَادَ{9}
Yã Ubangijinmu! Kada ka karkatar da zukãtanmu bãyan kã shiryar da mu, kuma ka bã mu rahama daga gunka. Lalle ne, kai ne mai yawan kyauta. "Yã Ubangijimu! Lalle ne kai, Mai tãra mutãne ne dõmin wani yini wanda bãbu shakka a cikinsa, Lalle ne Allah bã ya sãbã lõkacin alkawari."
A cikin shirin da ya gabata idan masu saurarenmu suna tune, mun bayyana cewa malamai sun kasu kashi biyu kan fassara ayoyin kur'ani mai tsarki, akwai wadanda suna yin amfani da ayoyin kur'ani wajen canja tunanin mutane daga sahihiyar akida ta tauhidin Allah madaukakin sarki, ta yadda za su cusa ma mutane mahangarsu da kuma yadda su suka fahimci addidi, amma ta hanyar yin amfani da ayoyin kur'ani mai tsarki, kamar misalin da muka bayar na ayoyi bayyanannu, (muhkamat) da kuma masu kama da juna (mutashabihat) inda yi bayani kan cewa ayoyi muhkamat a manarsu haka take kamar yadda ya zo a zahirin aya, amma mutashabihat, ba zahirin ayar ne ma'anarsu ba, dole sai an yi tawili bisa dogaro da sahihin nassi da dalilan safkar aya da sauran hanyoyi da ake bi wajen gane tawilin aya.
Wasu daga cikin malami kuma ba su gona da iri, suna bin dukkanin hanyoyin da suka kamata wajen fassara kur'ani ba tare da saka san ransu wajen juya ma'anar ayoyin ba, to irin wadannan su ne malamai na Allah masu yin aiki da fadarsa, masu shiryar da bayinsa.
Duk da cewa mutum zai iya zama mumini shiryayye, mai yin aiki na kwarai, amma kuma duk da haka yana cikin hadari, domin kuwa shaidan irin su ne yake farauta, shi ya sanya Allah da kansa yake shiryar da muminai zuwa ga tafarkin addu'a, domin samun tabbata kan shiriya, tare da neman rahmarsa, tare da tunatar da mutum kiyama a cikin addu'arsa, domin ya kara zama cikin shiri da yin guzuri na tafiyar da ba a dawowa.
Darussa koyo daga wadannan ayoyi masu albarka:
1- Kada mutum ya rudu da imani da iliminsa, domin kuwa akwai daga cikin manyan malamai masu imani, wadanda maimakon yin hidima ga addini sun ha'inci addini, daga karshe sun yi hasarar duniya da ta lahira. Ma'anar hasarar duniya a nan ba sun rasa kudi ko dukiya ko abin da ya yi kama dahaka ba ne, ma'ana sun bar duniya Allah na fushi da su, hasarar lahira kuwa ita ce fadawa cikin azabarsa, maimakon samun rahamarsa.
2- Alamar ilimi na hakika ita ce, kaskantar da kai ga Allah madakakin sarki, yin tawalu'u a cikin lamurra, girmama bayin Allah muminai, da sauran siffofi kyawawa da kur'ani ya ambata, kuma aka gansu a aikace a cikin dukaknin ayyukan manzon Allah (SAW)
Ayoyi na ( 10 ) ( 11 ) ( 12 ) Ali Imran:
إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُواْ لَن تُغْنِيَ عَنْهُمْ أَمْوَالُهُمْ وَلاَ أَوْلاَدُهُم مِّنَ اللّهِ شَيْئاً وَأُولَـئِكَ هُمْ وَقُودُ النَّارِ{10} كَدَأْبِ آلِ فِرْعَوْنَ وَالَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ كَذَّبُواْ بِآيَاتِنَا فَأَخَذَهُمُ اللّهُ بِذُنُوبِهِمْ وَاللّهُ شَدِيدُ الْعِقَابِ{11} قُل لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ سَتُغْلَبُونَ وَتُحْشَرُونَ إِلَى جَهَنَّمَ وَبِئْسَ الْمِهَادُ{12}
Lalle ne wadanda suka kãfirta, dũkiyõyinsu bã su tunkude musu kõme daga Allah, kuma 'ya'yansu bã su tunkudẽwa, kuma wadannan, sũ ne makãmashin wuta.
Kamar dabi'ar mutãnen Fir'auna da wadanda ke a gabãninsu, sun karyata ãyõyinMu, sai Allah Ya kãmã su sabõda zunubansu, kuma Allah Mai tsananin ukũba ne.
Ka ce wa wadanda suka kãfirta: "Za a rinjãye ku, kuma a tãraku zuwa Jahannama, kuma shimfidar tã mũnana!
A cikin wadannan ayoyi Allah madaukakin sarki yana yin bayani ne ga manzonsa, tare da ba shi umurni da ya sheda wa wadanda ba su yi imani ba cewa, dukiyoyin da suke takama da su da tarin 'ya'ya da mulki da duk abin da suke ganin ya wadatar da su daga Allah madaukakin sarki, duk wannan ba zai amfane su ba, ba zai iya wadatar da su komai daga Allah ba, domin kuwa rashin imani da Allah ya sanya kafiri ya zama abun hura wutar jahannama, a ranar da dukiya da 'ya'ya da karfin iko, ko fada a ji ba su da amfani, sai wanda ya zo ma Allah da zuciya mai imani.
Allah madaukakin sarki yana yi ma muminai bayani cewa; kada su yi zaton cewa a lokacinsu ne kawai aka samu wadanda suka kafirce ma sakon Allah, suka juya fusakunsu daga gaskiya a lokacin da ta zo musu daga ubangijinsu, domin kuwa an yi mutane masu tsananin girman kai da kin gaskiya da zalunci, amma daga karshe suka halaka, hatta Fir'auna wanda ya shahara da karfin iko da sarauta da dukiya, daga karshe duk wannan bai amfane shi da komai ba sakamakon rashin imaninsa da sakon Allah da annabi Musa (AS) ya zo masa da shi, domin kuwa ya gaza a gaban karfi da ikon Allah madaukakin sarki. A kan haka wannan babban dalili ne da ishara ga kuraishawa kan cewa lallai su ma matukar ba su imani da sakon manzon allah ba, to daga karshe dai za a rinjaye su, kuma su mutu su tafi cikin azabar Allah.
Darussan koyo daga wadannan ayoyi:
1- Ka da mutum ya damfara ransa ga dukiya ko 'ya'ya, ta yadda za su hana shi bin gaskiya idan ya ganta, domin kuwa ba za su iya kubutar da shi daga azabar Allah ba a ranar kiyama.
2 – A koda yaushe shaidan yana kokari ya ga raba mai imani da imanisa, tare da kokarin kange kafiri daga hasken shiriya, ko da kuwa ya ganta kuru-kuru, ta yadda zai samu wadanda za su taya shi zama cikin wutar jahannama.
3 – Aikata zunubi a kansa abu ne mai muni, amma bin da yafi hakan muni shi ne, idan aikata zunubi ya zama wani bangare na rayuwar mutum, a lokacin ne idan har bai tuba ba, to kuwa zai yi mummunan karshe. Wal iyaz billah.
4 – Karshe kafirci da karya suna shan kaye, gaskiya kuma ta yi nasara a kansu.
Aya ta ( 13 ) Ali Imran:
قَدْ كَانَ لَكُمْ آيَةٌ فِي فِئَتَيْنِ الْتَقَتَا فِئَةٌ تُقَاتِلُ فِي سَبِيلِ اللّهِ وَأُخْرَى كَافِرَةٌ يَرَوْنَهُم مِّثْلَيْهِمْ رَأْيَ الْعَيْنِ وَاللّهُ يُؤَيِّدُ بِنَصْرِهِ مَن يَشَاءُ إِنَّ فِي ذَلِكَ لَعِبْرَةً لَّأُوْلِي الأَبْصَارِ{13}
"Lalle ne wata ãyã tã kasance a gare ku a cikin kungiyõyi biyu da suka hadu; kungiya guda tana yãki a cikin hanyar Allah, da wata kãfira, suna ganin su ninki biyu nãsu, a ganin ido. Kuma Allah yana karfafa wanda yake so da taimakonsa. Lalle ne a cikin wannan, hakĩka, akwai abin kula ga ma'abũta basĩra.
Manzon Allah (SAW) tare da sauran muminai da suke tare da shi a Makka, sun kwashe shekaru 13 cur suna shan azaba da kuntatawa a hannun mushrikan kuraishawa a garin na Makka, , daga karshe dai sun shirya kasha manzon Allah, daga nan ne Allah ya ba shi umurnin hijira daga Makka zuwa Madina, a shekara ta biyu bayan hijira, a yankin Badar an kafsa yaki tsakanin musulmi da kuma mushrikan kuraishawa, inda adadin musulmi baki daya 313 ne, kafirai kuwa adadinsu ya kai mutum 1000, amma musulmi sun samu gagarumar nasara a kan mushrikai da taimakon Allah.
Wannan aya mai albarka tana yin ishara da yadda Allah madaukakin sarki yake taimaka rundunar masu imani komai karancinsu, inda yakan saka tsoro a cikin zukatan mushrikai a lokacin kafsawa, matukar dai muminai suka tsarkake niyyarsu tsakaninsu da Allah
Darussan da ke cikin wannan aya mai albarka:
1 – Yaki a cikin addinin muslunci ana yin shi ne saboda Allah, domin neman yardar Allah, domin kare addinin muslunci, ba domin nuna iyawa ko burgewa ko fin karfi, ko neman iko da mulki na duniya ba.
2 – Daya daga cikin irin taimakon da Allah madaukakin sarki yake yi wa mumninai shi ne, yana saka tsoro da firgita a cikin zukatan makiya muslunci a lokacin yaki da musulmi, ta yadda suke kallon adadin musulmi nunkin ba lunki.
3 – Dukkanin abubuwan da suke faruwa wadanda muka gani da wadanda muke ji a cikin tarihi, akwai abubuwan lura a cikinsu, amma masu zurfin hankali da basira ne kawai suke gane hakan.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 14-17 (Kashi Na 76)
Jama'a masu saurare Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke kawo mukubayani kan ayoyin kur'ani mai tsarki tare da fitar da darussan da ke cikinsu, domin amfana daga koyarwar kur'ani mai tsarki. Har yanzu muna cikin suratul Ali Imran, inda za mu farad a sauraren karatun aya ta 14 daga cikin wannan sura mai albarka.
Aya ta (14 ) Ali Imran:
زُيِّنَ لِلنَّاسِ حُبُّ الشَّهَوَاتِ مِنَ النِّسَاء وَالْبَنِينَ وَالْقَنَاطِيرِ الْمُقَنطَرَةِ مِنَ الذَّهَبِ وَالْفِضَّةِ وَالْخَيْلِ الْمُسَوَّمَةِ وَالأَنْعَامِ وَالْحَرْثِ ذَلِكَ مَتَاعُ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَاللّهُ عِندَهُ حُسْنُ الْمَآبِ
An kawata wa mutãne son sha'awõyi daga mãtã da diya da dũkiyõyi abũbuwan tãrãwa daga zinariya da azurfa, da dawãki kiwãtattu da dabbõbin ci da hatsi. Wannan shi ne dãdin rãyuwar dũniya. Kuma Allah a wurinsa kyakkyãwar makõma take.
Allah madaukakin sarki ya halicci mutum, ya kuma saka shi a bayan kasa, ya sanya wasu abubuwa da dan adam yake bukata domin ci gaba da wannan rayuwa, domin wanzur irin mutum yana bukatar mata da 'ya'ya, domin jin dadin rayuwrsa da biyan bukatunsa na yau da kullum yana bukatar kudi, yana bukatar abin hawa da tufafi da dai sauran abubuwa na bukatuwar dan adam na larura. Mutum yakan so wadannan abubuwan kamar yadda Allah ya sanya sonsu a cikin zuciyarsa, wani lokaci kuma yakan so su fiye da kima, har ma mutum kan iya sanya su tamkar su ne manufar rayuwarsa, ya fifita son mata da 'ya'yansa da dukiyarsa fiye da komai na duniya, har ma da ibadar Allah madaukakin sarki, alhali kuwa ba su ne manufa ta rayur dan adam ba, domin kuwa su ma masu karewa ne a nan gidan duniya, kuma dayan biyu, kodai mutum ya barsu, ko kuma su su bar shi, domin kuwa makomar kowa da komai na wajen Allah madaukakin sarki. Idan mutum bai kyautata ayyukansa ba, babu ko daya daga ckin wadannan abubuwan da zai amfane shi a lahira.
Darusasn da ke cikin wannan aya mai albarka:
1 – Son kyalekyale daga abubuwan duniya dabi'a ce ta mutum, amma kuma abu mafi hadari shi ne, sonsu ya zama shi ne mafifici a cikin zuciyar mutum fiye da komai a rayuwarsa.
2 – Yin amfani da abubuwan da Allah ya hore a cikin duniya domin yin abin da sabon Allah ba ne, babu laifi a cikinsa, yin sabanin hakan ne laifi.
3 – Tunanin lahira da kwatanta jin dadin lahira da na duniya, yana rage tasirin son duniya a cikin zuciyar mutum.
Aya ta ( 15 ) Ali Imran:
قُلْ أَؤُنَبِّئُكُم بِخَيْرٍ مِّن ذَلِكُمْ لِلَّذِينَ اتَّقَوْا عِندَ رَبِّهِمْ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا وَأَزْوَاجٌ مُّطَهَّرَةٌ وَرِضْوَانٌ مِّنَ اللّهِ وَاللّهُ بَصِيرٌ بِالْعِبَادِ
Ka ce: Shin kuma, in gaya muku mafi alhẽri daga wannan? Akwai gidãjen Aljanna a wurin Ubangiji sabõda wadanda suka bi shi da takawa, kõguna suna gudãna daga karkashinsu, suna madawwama a cikinsu, da mãtan aure tsarkakakku, da yarda daga Allah. Kuma Allah Mai gani ne ga bãyinsa.
Kamar dai yadda aka mabata acikin ayar da tag abaci wannan, cewa wasu daga cikin abubuwa na duniya mutum yana sonsu bisa dabi'a, duk kuwa da cewa daga karshe dai masu gushewa ne, amma ita wannan ayar tana yin ishara ne da abubuwa na ni'ima da Allah madaukakin sarki ya yi tanadi ga masu tsoransa a duniya, wadannan ni'imomi masu dawwama ne na har abada, ba su gushewa saboda tsawon zamani, ko karewa saboda amfani da su, wannan tamkar zabi ne aka baiwa mutum domin ya zabi daya daga cikin wadannan nau'oi biyu na rayuwa, rayuwar duniya mai cike da wahalhalu, bakin ciki, kuma takaitatta. Akasin rayuwar aljanna a lahira, inda Allah ya tanadi dukkanin ni'ima da mutum bai taba yin tunaninta ba, sai dai kawai misali da ake ba shi a cikin kur'ani, domin hankali ya iya riskar cewa akwai ni'ima, amma hakikanin ni'imar aljanna Allah ne kawai ya san yadda take. Baya ga 'ya'yan marmari masu dadi, da manyan lambuna da koramu ke gudana a karkashinsu, sauran nau'oin abinci da sha, wadanda aka bada misali da su daga cikin ni'imar aljamma, sauran ni'imomin ba musansu, saboda hankalinmu ba zai kama ba, wannan kuma zai ci gaba da kasancewa ne har abada. Abu mafi soyowa ga 'yan aljanna wanda yafi dukannin wadannan ni'imomi, shi ne yardar Allah madaukakin sarki.
Darussan koyo daga wannan aya mai albarka:
1 – Hanyar isa zuwa ga ni'imomin aljanna ita ce tsoron Allah, nisantar abubuwan da ya hanana, aikata kyakkyawa a duniya, domin kuwa aljanna wuri ne mai tsarki.
2 – Jin dadin aljanna bai takaitu da abubuwan jin dadi da muka sani ba, babban jin dadin 'yan aljanna shi ne yardarm Allah.
3 – Tsarkaka daga duk wani aibu da nakasa, shi ne matsayi mafi girma mafi daraja a wurin mata, domin Allah ya siffanta matayen aljanna da cewa, mata ne tsarkaka. Aya ta ( 16 ) da ( 17 ):
الَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَا إِنَّنَا آمَنَّا فَاغْفِرْ لَنَا ذُنُوبَنَا وَقِنَا عَذَابَ النَّارِ{16} الصَّابِرِينَ وَالصَّادِقِينَ وَالْقَانِتِينَ وَالْمُنفِقِينَ وَالْمُسْتَغْفِرِينَ بِالأَسْحَارِ{17}
Wadanda suke cẽwa: "Ya Ubangijinmu! Lalle ne mu, mun yi ĩmãni, ka gãfarta mana zunubanmu kuma ka tsare mu daga azãbar wuta."
Mãsu hakuri, da mãsu gaskiya, da mãsu kankan da kai, da mãsu ciyarwa da mãsu neman gafara a lõkutan asuba.
Ayar da ta gabata ta yi mana bayani ne kan cewa masu taqawa, masu tsoron Allah su ne 'yan aljanna, yayin da ita kuma wannan ayar tana yi mana bayani ne kan dabi'u da halaye irin na masu tsoron Allah, wadanda su ne 'yan aljanna.
Aya ta farko dai tana yi mana bayani ne kan tuba da komawa zuwa ga Allah irn na masu tsron Allah. Ma'anar taqawa ko tsoron Allah ba yana nufin tsarki daga aikata duk wani sabo ba ne, mai tsoron Allah zai iya rafkana ko gafala a wani lokaci ya aikata wani abu wanda laifi ne, zunubi ne, amma ba al'adarsa ba ce aikata irin wannan laifi, sa'annan kuma mai tsoron Allah da aikata wani laifi da ya farga da hakan, a nan take zai koma zuwa ga Allah tare da neman gafararsa, da shiga cikin damuwa saboda ya aikata wani na sabon Allah, kuma zai kiyaye matukar iyawarsa wajen ganin bai kara aikata hakan ba.
Aya ta gaba kuma tana bayyana mana wasu siffofin na masu taqawa, hakuri, gaskiya a cikin akida da zantuka, ta yadda ba za a taba jin suna raki ba saboda wata matsala da duniya, ba za a taba jin karya a cikin zantukansu ba, su masu komawa ne zuwa ga Allah da rokonsa da kaskantar da kai gare shi, masu ciyarwa ne daga abin da suka mallaka, masu yin istigafari ne a karshen dare.
Wani lokaci shaidan yakan sanya mai aikin alhari ya rika jin lallai shi yana aikata abu, ya rika jiji da kai da kallon sauran mutane batattu, shi kuma yana daukar kansa mai tsarki saboda aikin alhairin da yake yi, to wanda ya samu kansa a cikin irin wannan hali ba ya daga cikin mutanen da wannan ayar ta ambata, domin siffar mai tsoron Allah ce ya kasance mai tawalu'u a cikin dukaknin lamurransa, kada ya yi wa mutane girman kai da izgili sai Allah ya kaskantar da shi ya wulakanta shi a duniya da kuma lahira.
Darussa daga wadannan ayoyi:
Tsoron Allah ba ya nufin yin watsi da komai na duniya, babban abin da ke kai mutum ga wannan matsayi shi ne aikata abin da Allah ya yi umurini da shi, da kuma nisantar duk wani abin da Allah ya yi hani a kansa. Babban abin da ke nisantar da mutum daga siffar taqawa shi ne aikata sabon Allah da gangan, da kuma ci gaba da aikata shi ba tare tuba ga Allah ba.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 18-22 (Kashi Na 77)
Jama'a masu saurare Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke kawo muku bayani dangane da ayoyin kur'ani mai tsarki da kuma darussan da suke dauke da su, inda har yanzu muke cikin uratul Ali Imran. Sai a fara da saurare karatun aya ta a cikin wannan sura mai albarka.
Aya ta ( 18 ) Ali Imran:
شَهِدَ اللّهُ أَنَّهُ لاَ إِلَـهَ إِلاَّ هُوَ وَالْمَلاَئِكَةُ وَأُوْلُواْ الْعِلْمِ قَآئِمَاً بِالْقِسْطِ لاَ إِلَـهَ إِلاَّ هُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
Allah Ya shaida cẽwa: Lalle ne bãbu abin bautãwa fãce shi kuma malãiku da ma'abũta ilmi sun shaida, yana tsaye da ãdalci, bãbu abin bautãwa face shi, Mabuwãyi, Mai hikima.
Wannan aya tana magana ga manzon Allah (SAW) da kuma sauran muminai, tare da tabbatar musu da kadaitar ubangiji wato (wahdaniyya) malamai ma'abuta hankali da ilimi da basira, suna bayyana cewa tsarin da Allah ya yi duniya a kansa da kuma yadda yake tafiyar da wannan tsari, ya isa ya zama babban dalili na samuwar Allah guda daya, wanda hakan kuma gasgata fadar ayar kur'ani mai tsarki ne da ke cewa; da a ce akwai wasu alloli a cikin sammai da kassai da tsarinsu ya rushe, da ya daidaice, kasantuwar tsari daya da duniya da sauran halittu suke tafiya a kansa babban dalili ne kan cewa mai tafiyar da tsarin shi ne ya samar da shi, kuma shi kadai ne ya yi abinsa ba tare da taimakon wani ba. Misali kan haka kuwa shi ne, da babu wahadaniyya (kadaitakar ubangiji) da an ga rana na fito ta yamma a wani lokaci, ko ta arewa ko kudu, domin kuwa da akwai wasu alloli ba ya ga Allah daya, da kowanensu ya aiwatar da iradarsa wadda ta sabawa sauran allolin, wanda hakan shi ne zai rushe tsari daya da duniya da sauran abin halitta suke tafiya a kansa, rashin samun wannan sabani a cikin tsarin da halitta ke tafiya a kansa, ya tabbatar da cewa wanda ya yi halittar da tsarin duk mahalicci daya rak.
Wasu abubuwan da suke tabbatar da cewa Allah shi kadai kuma shi ne yake da iko akan komai, shi ne ubangijin kowa da komai, shi ne yadda fitira ta dan adam da damfaru da hakan, domin kuwa a koda yaushe dan adam yana ji a kinsa cewa akwai wani karfi dake birbishinsa, ko da kuwa ya kasa gane cewa Allah ne, domin kuwa mai bautar gumaka ya dauka wannan karfin da ke birbishinsa shi ne gunkin, mai bautar dodanni ya dauka su ne suke da iko a birbishinsa, wanda wata kila mutumin babban farfesa ne kan ilmomi na hankali, kamar lissafi, sanin halayyar dan adam da sauransu, amma idan bai gane wane ubangiji ma takamaimai sai ya yi fangima da dirkaniya, to wanna jin da mutum yake da shi a cikin zuciyarsa, ya tabbatar da samur Allah.
Darussan da ke cikin wannan aya mai albarka:
1- Babban dalilin samuwar Ubangiji guda daya dab a shi da abokin tarayya shi ne tsarin da ke akwai a cikin halitta.
2- Ilimi na da babbar kima idan ya kai mutum zuwa ga sanin matsayin Allah, da bautarsa, kamar yadda shi ma imani babbar kimarsa ita ce idan ya ginu a kan sanin Allah na hakika. Aya ta ( 19 ) da ( 20 ):
إِنَّ الدِّينَ عِندَ اللّهِ الإِسْلاَمُ وَمَا اخْتَلَفَ الَّذِينَ أُوْتُواْ الْكِتَابَ إِلاَّ مِن بَعْدِ مَا جَاءهُمُ الْعِلْمُ بَغْياً بَيْنَهُمْ وَمَن يَكْفُرْ بِآيَاتِ اللّهِ فَإِنَّ اللّهِ سَرِيعُ الْحِسَابِ{19} فَإنْ حَآجُّوكَ فَقُلْ أَسْلَمْتُ وَجْهِيَ لِلّهِ وَمَنِ اتَّبَعَنِ وَقُل لِّلَّذِينَ أُوْتُواْ الْكِتَابَ وَالأُمِّيِّينَ أَأَسْلَمْتُمْ فَإِنْ أَسْلَمُواْ فَقَدِ اهْتَدَواْ وَّإِن تَوَلَّوْاْ فَإِنَّمَا عَلَيْكَ الْبَلاَغُ وَاللّهُ بَصِيرٌ بِالْعِبَادِ{20}
Lalle ne, addini a wurin Allah, shi ne Musulunci. Kuma wadanda aka bai wa Littafi ba su sãɓã ba, fãce a bãyan ilmi ya je musu, bisa zãlunci a tsakãninsu. Kuma wanda ya kãfirta da ãyõyin Allah, to, lalle ne Allah Mai gaugãwar sakamako ne.
To, idan sun yi musu da kai, sai ka ce: "Nã sallama fuskata ga Allah, haka nan wanda ya bi ni ." Kuma ka ce wa wadanda aka bai wa littãfi da Ummiyyai: "Shin kun sallama?" To, idan sun sallama, hakĩka, sun shiryu kuma idan sun jũya, to, kawai abinda ke kanka, shi ne isarwa. Kuma Allah Mai gani ne ga bãyinsa.
A lokacin annabawan Allah Musa da Isa da sauran zamunan annabawa, wajibi a kn mutanen wannan zamanin shi ne su yi imani da wannan annabin da abin da ya zo da shi na daga shari'a daga Allah madaukakin sarki, amma bayan aiko manzon Allh Muhammad (SAW) ya zama wajibi na shari'ar ubangiji a kan sauran dukkanin al'ummomin duniya da suke raye a lokacinsa su yi imani da shi, hatta ahlul kitabi wajibi ne aknsu su bi abin da manzon allah Muhammad ya zo shi, domin kuwa shi ne shugaban dukkanin annabawa da suka gabata, da wani annabi yana raye a lokacin bayyanar annabi Muhammadu, to da wannan annabi ya zama daya daga cikin mabiyan annabi Muhammadu (SAW) domin kuwa addininsa shi ne ya hada dukkanin addinai na sauran annabawan da suka gabace shi, domin daga lokacin bayyana r manzon Allah, duk wanda ya yi wani addini da sunan addinin to ba za akarba daga gare shi ba kamar yadda ayar ta nuna.
Wasu daga cikin malaman ma'abota littafi sun ki yi imani da manzon Allah a lokacin da ya zo da addinin muslunci daga Allah, duk kuwa da cewa an ambace shi a cikin littafan annabawa, da suka hada da zabura da attaura da injila, kuma sun karanta hakan sun sani, kuma sun gane shi ne ake nufi a lokacin da ya bayyana, saboda hassada, da neman wanzuwa kan matsayin girma da suke da shi a wajen mabiyansu.
Darussan koyo daga wadannan ayoyi biyu:
1- Addinin muslunci shi ne addinin da Allah ya aiko manzonsa da shi, duk wanda ya bi wani addini baya ga addinin Allah to ba za a karba daga gare shi ba.
2- Kauda ido daga gaskiya da hassada, suna kai dan adam ga halaka da fadawa cikin fushin ubangiji.
3- Abin da yake wajibi kan musulmi shi ne yin koyi da manzon Allah a cikin dukkanin lamurra, tare da yin aiki da umurninsa, da hanuwa daga haninsa, da yin amfani da hikima wajen yin mu'amala da mutane da ba su fahimci koyarwar addinin muslunci, kamar yadda manzon Allah ya nuna kyawawan dabi'u ga mutane har ma da masu adawa da shi, wanda hakan ne ma ya zama sanadiyar musuluntar wasu da dama daga cikinsu. Aya ta ( 21 ) da ( 22 ) Ali Imran:
إِنَّ الَّذِينَ يَكْفُرُونَ بِآيَاتِ اللّهِ وَيَقْتُلُونَ النَّبِيِّينَ بِغَيْرِ حَقٍّ وَيَقْتُلُونَ الِّذِينَ يَأْمُرُونَ بِالْقِسْطِ مِنَ النَّاسِ فَبَشِّرْهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ{21} أُولَـئِكَ الَّذِينَ حَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ وَمَا لَهُم مِّن نَّاصِرِينَ{22}
Lalle ne wadanda suke kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe Annabãwa bã da wani hakki ba, kuma suna kashe wadanda ke umurni da yin ãdalci daga mutãne, to, ka yi musu bushãra da azãba mai radadi.
Wadannan ne wadanda ayyukansu suka bãci a cikin dũniya da dãhira, kuma bã su da wasu mataimaka.
Wadannan ayoyi biyu masu albarka suna nuni da cewa, kin gaskiya da kafirce ma ubangiji na da mummunan tasiri ga mutum, domin kuwa ayyukan mutum suna bin akidarsa da tunaninsa ne, domin kuwa wanda bai yi imani da akida ba ba zai yi aiki da ita ba, ko da kuwa ya yi to aikin bai kai cikin zuciyarsa ba. Wasu suna kafirce ma ayoyin Allah, kuma har ma su yi shishigi kan annabawan Allah, to wadanan su ne kafirai na hakika, a ranar da za su shiga hannun Allah ba su da mai taimakonsu.
Darussa daga wannan ayoyi:
1- Kafirci da kin gaskiya yakan yi tsanani ta yadda har zai kai mabocinsa zuwa ga aikata mummunan aiki na kisan annabawan Allah.
2- Kira zuwa ga Allah da tabbatar da adalci lamari ne wajibi a kan muminai, ko da kuwa hakan zai kai su ga yin shahada a kan wannan tafarki. Mun gani a cikin tarihi yadda Imam Hussain (AS) ya fuskanci zalunci domin tabbatar da adalci, ya fuskanci kafirci domin tabbatar da muslunci, ya fuskanci karya domin tabbatar da gaskiya, ya fuskanci mutuwa domin rayuwa ta har abada, ya fuskanci tsanani da wahala da musiba domin samun ni'ima da rahma da jin dadi na har abada, kuma abin da ya yi ya zama darasi ga dukkanin al'ummomin duniya, masu son su rayu cikin 'yanci, musulmi ne ko ba musulmi, duk da cewa shi ya yi shahada, amma sakamakon haka akidarsa ta wanzu kuma ta daukaka.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 23-27 (Kashi Na 78)
Jama'a masu saurare Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke kawo muku bayani dangane da ayoyin kur'ani mai tsarki da kuma darussan da suke dauke da su, inda har yanzu muke cikin uratul Ali Imran. Sai a fara da saurare karatun ayoyi na 23 da 24 a cikin wannan sura mai albarka.
Aya ta ( 23 ) da ( 24 ) Ali Imran:
أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ أُوْتُواْ نَصِيباً مِّنَ الْكِتَابِ يُدْعَوْنَ إِلَى كِتَابِ اللّهِ لِيَحْكُمَ بَيْنَهُمْ ثُمَّ يَتَوَلَّى فَرِيقٌ مِّنْهُمْ وَهُم مُّعْرِضُونَ{23} ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ قَالُواْ لَن تَمَسَّنَا النَّارُ إِلاَّ أَيَّاماً مَّعْدُودَاتٍ وَغَرَّهُمْ فِي دِينِهِم مَّا كَانُواْ يَفْتَرُونَ{24}
Shin, ba ka ga wadanda aka bai wa rabo daga littãfi ba ana kiran su zuwa ga Littãfin Allah dõmin ya yi hukunci a tsakãninsu sa'an nan wata kungiya daga cikinsu ta jũya bãya, kuma sunã mãsu bijirẽwa?
Wannan kuwa, dõmin lalle ne su sun ce: "Wutã bã zã ta shãfe mu ba, fãce a 'yan kwãnaki kidãyayyu." Kuma abin da suka kasance sunã kirkirãwa na karya ya rũdẽ su a cikin addininsu.
A cikin shirin da ya gabata mun ambaci cewa wasu daga cikin yahudawa musamman ma malamansu sun ki yin imani da manzon allah Muhammad (SAW) a lokacin da ya zo da addinin muslunci daga Allah madaukakin sarki, duk kuwa da cewa sun gane cewa shi ne manzon karshe daka yi bayani a cikin attaura, amma kuma ba su yi imani da shi ba, saboda tsananin hassada da gaba. Wannan aya tana baiwa manzon Allah (SAW) hakuri kan irin wadannan muggan mutane da kuma abubuwan da suke yin a kiyayya da gaskiya kuru-kuru.
Ya zo a cikin wata ruwaya cewa, wani daga cikin yahudawa ya tafka laifin zina, saboda haka sai ya guje wa hukucin da ke cikin attaura kan wannan aiki day a aikata, ya tafi wurin manzon Allah, sai ya ga hukuncin da ke cikin attaura kan wannan laifin, irinsa ne daidai da wanda ke cikin kur'ani, sai bayahuden ya tashi yana izgili da ayoyin Allah, yana mai kafirce ma dukkanin littafan biyu, Attaura da kuma kur'ani mai tsarki.
Bisa ga dabi'ar yahudawa suna da girman kai da raina sauran mutane, bil hasali ma suna ganin cewa su sun fi sauran mutane baki daya, kuma dukkanin laifukan da suka aikata a rayuwar duniya ba za su taba shiga wuta ba a ranar kiyama, duk kuwa da cewa Allah ya tona asirinsu a cikin kur'ani mai tsarki.
Darussan koyo daga cikin wadannan ayoyi:
1- Ba a yin addini ta hanyar rayawa, yin imani da aiki da fadar Allah su ne suke tabbatar da mutum mai riko da addini.
2- Jiji da kai da raina sauaran mutane ba shi da kyau a cikin addini.
3- Dukkanin mutane daya suke a gaban dokokin Allah, babu wani wanda yake birbishin dokar Allah madaukakin sarki.
Aya ta ( 25 ) Ali Imran:
فَكَيْفَ إِذَا جَمَعْنَاهُمْ لِيَوْمٍ لاَّ رَيْبَ فِيهِ وَوُفِّيَتْ كُلُّ نَفْسٍ مَّا كَسَبَتْ وَهُمْ لاَ يُظْلَمُونَ
To, yãya idan Mun tãra su a yini wanda bãbu shakka a cikinsa, kuma aka cikã wa kõwane rai sakamakon abin da ya tsirfanta, alhãli kuwa, sũ bã zã a zãlunce su ba?
Wannan ayar tana koyar da mu cewa, Allah madaukakin sarki yana kallon dukkanin bayinsa da ido na adalci, ba tare da banbanci tsakanin bayahude ko banasare ko musulmi ko waninsu ba, kimar mutum shi ne kyautatawarsa. Ayar tana koyar da cewa sakamako mai kyau ko maras kyau, yana kasancewa ne a kan imani da aiki, ba a kan dangantaka ta dangi ko addini ko abin da ya yi kama da hakan ba.
Kasantuwar mutum a cikin wata babbar kabila, ko kuma wasu mutane masu daraja ta addini ba shi ne ma'auni na sanin matsayinsa a cikin addinin Allah ba, imaninsa da aikinsa shi ne ma'auni, domin kuwa akwai daga cikin iyalan annabawa da suka kafirce musu suka cutar da su, dangatakarsu da wadannan annabawan ba ta amfane su ba a duniya, kamar yadda ba za ta amfane su a lahira ba.
Darasi daga wannan aya:
1- Imani da aiki su ne muhimamn lamurra a cikin addini, ba dangantaka da masu matsayi a cikinsa ba kawai.
Ayoyi na ( 26 ) da ( 27 ) Ali Imran:
قُلِ اللَّهُمَّ مَالِكَ الْمُلْكِ تُؤْتِي الْمُلْكَ مَن تَشَاء وَتَنزِعُ الْمُلْكَ مِمَّن تَشَاء وَتُعِزُّ مَن تَشَاء وَتُذِلُّ مَن تَشَاء بِيَدِكَ الْخَيْرُ إِنَّكَ عَلَىَ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ{26} تُولِجُ اللَّيْلَ فِي الْنَّهَارِ وَتُولِجُ النَّهَارَ فِي اللَّيْلِ وَتُخْرِجُ الْحَيَّ مِنَ الْمَيِّتِ وَتُخْرِجُ الَمَيَّتَ مِنَ الْحَيِّ وَتَرْزُقُ مَن تَشَاء بِغَيْرِ حِسَابٍ{27}
Ka ce: "Yã Allah Mamallakin mulki, kanã bayar da mulki ga wanda kake so, Kanã zãre mulki daga wanda ka so, kuma kanã buwãyar da wanda kake so, kuma Kanã kaskantar da wanda ka so, ga hannunka alhẽri yake. Lalle ne kai, a kan kõwane abu, Mai ĩko ne."
"Kanã shigar da dare a cikin yini, kuma Kanã shigar da yini a cikin dare, kuma Kana fitar da mai rai daga mamaci, kuma Kanã fitar da mamaci daga mai rai, kuma Kanã azurta wanda Kake so bã da lissafi ba."
Wadannan ayoyi guda biyu masu albarka suna nuna wa manzon Allah (SAW) tare da sauran musulmi cewa, dukkan komai na ga hannun Allah madaukakin sarki, shi ne yake kwararo samuwa da taimakonsa ga dukkanin abin halitta, wadanda ke cikin sammai da kassai da kuma abin ke tsakaninsu.
Wasu daga cikin malaman tafsiri sun kawo wata kissa dangane da yakin Ahzab, wanda musulmi suka gina manyan ramuka da suka kewaye birnin Madina, tare d tara tulin kasar da aka fitar daga ramukan a gefen birnin wato (ganuwa), ta yadda mushrikai ba za su iya tsalkawa cikin birnin Madina ba. A lokacin da manzon Allah (SAW) yake haka rami tare sauran musulmi, ya sari wani dutse a cikin kasa da masassabin da ke a hannusa mai albarka, sai tartsatsin wuta ya tashi, sai manzon Allah ya yi farin ciki da hakan, inda ya sheda ma musulmi cewa da ikon Allah za a yi nasara kan Biladul faris da kuma Rom, haka lamarin ya kasance kuwa kamar yadda manzon Allah ya yi bushara.
Abun koyo daga wadannan ayoyi:
1- Tsarin na samuwar dukaknin abun halitta da tafiyar da tsari na ga hannun Allah madaukakin sarki, ikonsa ne birbishin dukkanin talikai, mu kuma abun halitta abin day a rataya kanmusu shi ne yin aiki da abin ya yi umurni da shi, da hanuwa daga abin da ya yi hani daga gare shi, kiyaye dukkanin dokokinsa da iyakokinsa, duk da cewa aikinmu ba zai iya zama daidai da sakamon aljannar ubangiji da ni'imarsa ba, amma yin kokari gwargwadon iko, saura kuma Allah ne ke cikawa da rahmarsa da tausayinsa ga bayinsa.
2- Mulki na ga Allah shi kadai, babu abokin tarayya a cikin mulkinsa, mulkinsa dawwamamme ne, yayin da duk wani mulki mai gushewa ne.
3- Dabi'ar samuwa ta abin halitta tana zagayawa ne tsakanin mutuwa da rayuwa, misali a cikin kwayar hatsi da babu rayuwa , babu motsi, sai tsiro ya fito, kuma ya zama abincin da mutum da dabbobi suke ci su rayu, daga abin da tsiron ya fitar Allah yake fitar da kwayoyin halittar jikunna, kuma su rayu da ikonsa madaukakin sarki.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 28-32 (Kashi Na 79)
Jama'a masu saurare Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke kawo muku bayani dangane da ayoyin kur'ani mai tsarki da kuma darussan da suke dauke da su, inda har yanzu muke cikin uratul Ali Imran. Sai a kasance tare da mu a cikin shirin.
Aya ta ( 28 ) da ( 29 ) Ali Imran:
لاَّ يَتَّخِذِ الْمُؤْمِنُونَ الْكَافِرِينَ أَوْلِيَاء مِن دُوْنِ الْمُؤْمِنِينَ وَمَن يَفْعَلْ ذَلِكَ فَلَيْسَ مِنَ اللّهِ فِي شَيْءٍ إِلاَّ أَن تَتَّقُواْ مِنْهُمْ تُقَاةً وَيُحَذِّرُكُمُ اللّهُ نَفْسَهُ وَإِلَى اللّهِ الْمَصِيرُ{28} قُلْ إِن تُخْفُواْ مَا فِي صُدُورِكُمْ أَوْ تُبْدُوهُ يَعْلَمْهُ اللّهُ وَيَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأرْضِ وَاللّهُ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ{29}
Kada mũminai su riki kãfirai masõya, ba ya ga mũminai. Kuma wanda ya yi wannan, to, bai zama a cikin kõme ba daga Allah, fãce fa dõmin ku yi tsaro daga gare su da 'yar kãriya. Kuma Allah yana tsõratar da ku kansa. Kuma zuwa ga Allah makõma take.
Ka ce: "Idan kun bõye abin da ke a cikin kirãzanku, kõ kuwa kun bayyana shi, Allah Yana sanin sa. Kuma Yana sanin abin da ke a cikin sammai da kasa. Kuma Allah a kan kõwane abu Mai ĩko ne."
Wadannan ayoyi masu albarka suna bayani ne dangane da irin alakar da ke akwai tsakanin muminiai da kuma wadanda ba su yi imani ba, duk wata dangantaka za ta hada munimin da wani bangare ta fuskacin jibintar lamari dole ne ta kasance bisa asasi na imani da Allah madaukakin sarki, tare da karfafa muminai kan hada kai da junansu, da zama tsintsiya daya madaurinki daya, ta yadda ba za su baiwa makiya addinin Allah damar kutsawa a tsaknainsu ba, balantana har su shimfida ikonsu kan al'ummar musulmi.
Ko da yake a wasu wurare da kafirci iko, yana da matukar wahala musulmi ya bayyana kidarsa ta imani, wanda wata kila yin hakan zai iya kai shi ga rasa ransa ko abin da ya mallaka, to a irin wannan yanayi sai musulmi ya yi taka tsan-tsan wajen bayyana matsayinsa, a lokaci guda kuma ya kiyaye abin da Allah ya haramta gwargwadon ikonsa.
Akwai lokutan da sadaukantarwa takan wajaba domin wanzur addinin Allah, akwai lokutan da kuma ake bukatar yin taka tsan-tsan, kamar dai misalin da aka bayar na kasashen da suke matukar kiyayya da addinin muslunci, inda a halin yanzu muke ganin haka a wannan zamani, inda akan kone masallatan musulmi da cin zarafinsu, lamarin har ya wuce hakan ma ya kai ga kone alkur'ani mai tsarki, saboda tsananin kiyayyar da ake yi da musulunci da musulmi a irin wadannan kasashe, to a lokacin sai musulmi ya yi hattara a lokacin da ya sami kansa a irin wadannan wurare.
Duk lokacin da mumini ya ji tsoron cewa zai cutu kuma za a iya cutar da addininsa sakamakon bayyana imaninsa, to ya halasta ya boye imaninsa a cikin zuciya.
Darussan da za mu koya daga wadannan ayoyi masu albarka:
1- Bai halasta ga muminai su amince da kafirai ba, ta yadda har za su samu damar shimfida ikonsu kan al'ummar musulmi, dole ne muminai su karfafa hadin kai tsakaninsu, domin hana makiya kutsawa a tsakaninsu.
2- Boye imani a lokacin tsoro daga cutarwar kafirai ga muminai da addinin muslunci ya halasta, matukar dai hakan ba zai kai ga share addini ba.
Aya ta ( 30 ) Ali Imran:
يَوْمَ تَجِدُ كُلُّ نَفْسٍ مَّا عَمِلَتْ مِنْ خَيْرٍ مُّحْضَراً وَمَا عَمِلَتْ مِن سُوَءٍ تَوَدُّ لَوْ أَنَّ بَيْنَهَا وَبَيْنَهُ أَمَداً بَعِيداً وَيُحَذِّرُكُمُ اللّهُ نَفْسَهُ وَاللّهُ رَؤُوفُ بِالْعِبَادِ
A Rãnar da kõwane rai yake sãmun abin da ya aikata daga alhẽri, a halarce, da kuma abin da ya aikata daga sharri, alhãli yana gũrin, dã a ce akwai fage mai nĩsa a tsakãninsa da abin da ya aikata na sharrin! Kuma Allah Yanã tsõratar da kũ kansa. Kuma Allah Mai tausayi ne ga bãyinsa.
Wannan aya mai albarka tana yin gargadi ne ga dukkanin mutane kan abin da ke jiransu bayan barin gidan duniya, domin su kwana da sanin cewa Allah madaukakin sarki yana da labarin dukkanin ayyukan da bayinsa suka yi a rayuwar duniya, kuma kowane mutum zai iske abin da ya aikata ba ragi ba kari, ta yadda wadanda suka aikata munanan ayyuka za su yi fatan a ce wadannan ba ayyukansu ba ne, a kan haka Allah yake gargadi ga dukkanin talikai da su ji tsoron saba masa a rayuwar duniya, domin shi Allah mai tausayi ne da jin kai, duk da sabonsa da bayinsa ke yi yana ba su lokaci da rata domin su tuba, kuma yana ba su dukkanin ni'imar da yake baiwa kowa a cikin rayuwar duniya, amma idan suka mutu a irin wannan hali, hujja ta riga ta yanke musu.
Darussan da suke cikin wannan aya mai albarka:
1- Da dama daga cikin ayyukan da muke so aduniya, a ranar lahira za mu guji wadannan ayyukan, kuma mu yi da na sani a kansu.
2- Gargadin da Allah yake yi wa mutane kan su guji aikata sabo da munanan ayuuka, ba komai ba ne illa tausayin ubangiji ga bayinsa, domin kada su fada cikin fushinsa da hakan zai kai su ga shiga cikin azabarsa.
Aya ta ( 31 ) da ( 32 ) Ali Imran:
قُلْ إِن كُنتُمْ تُحِبُّونَ اللّهَ فَاتَّبِعُونِي يُحْبِبْكُمُ اللّهُ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ وَاللّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ{31} قُلْ أَطِيعُواْ اللّهَ وَالرَّسُولَ فإِن تَوَلَّوْاْ فَإِنَّ اللّهَ لاَ يُحِبُّ الْكَافِرِينَ{32}
Ka ce: "Idan kun kasance kunã son Allah to, ku bĩ ni, Allah Ya sõ ku, kuma Ya gãfarta muku zunubanku. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin kai."
Ka ce: "Ku yi dã'a ga Allah da Manzo." To, amma idan sun jũya bãya, to, lalle ne Allah bã ya son kãfirai.
Addinin Allah ba cika baki ba ne, bin umurnin Allah ta hanyar bin manzon Allah (SAW) a cikin dukaknin lamurra ne, da kuma hanuwa daga hannin Allah, shi ma ta hanyar bin abin da manzon Allah ya hana, domin kuwa sai abin manzon Allah ne aka bi Allah, ba za a iya bin Allah ba tare da an bi ta hanyar manzo ba. Son Allah madaukakin sarki yana kasancewa ne kawai ta hanyar bin manzon Allah, bin manzon Allah kuma ba ya nufin duk inda ya shiga kaima ka bishi, balantana wani ya ce manzo ya kaura balanta mu yi ta binsa duk inda ya shiga, ma'ana a nan ita ce bin umurninsa da kuma hanuwa daga haninsa, domin umurnin manzo umurnin Allah ne, haninsa hanin Allah, ba ya fadin son ransa sai abin da Allah ya yi masa wahayi.
Darussan koyo daga wadanann ayoyi masu albarka:
1- Bin Allah yana kasancewa ta hanyar bin manzon Allah (SAW)
2- Nuna son Allah ba tare da yin aiki da biyayya gare shi da manzonsa ba, ba shi da ma'ana.
3- Fadar manzon Allah na misilta fadar Allah ne, fadar manzon Allah hujja ce a kanmu, yin watsi da ita na daidai yin watsi da fadar Allah madaukakin sarki. A kan haka za mu fahimci cewa yin biyayya ga umurnin Allah ta hanyar yin biyayya ga ma'aikinsa (SAW) shi ne abin da zai kai musulmi zuwa ga samun sa'ada ta duniya da lahira, domin kuwa hakan zai kai musulmi ga samun gafarar ubangiji, da samun rabo a lahira na aljanna, a daidai lokacin da saba ma Allah da manzonsa da ci gaba da aikata sabo ba tare da tuba ba, zai kai ma'abucinsa zuwa ga tabewa ta duniya da lahira wa iyazu billah.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 33-37 (Kashi Na 80)
Jama'a masu saurare Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke kawo muku bayani dangane da ayoyin kur'ani mai tsarki da kuma darussan da suke dauke da su, domin yin fadakarwa ga kawukanmu da kuma masu saurarenmu, inda har yanzu muke cikin suratul Ali Imran. Sai a kasance tare da mu a cikin shirin.
Aya ta ( 33 ) da ( 34 ) Ali Imran:
إِنَّ اللّهَ اصْطَفَى آدَمَ وَنُوحاً وَآلَ إِبْرَاهِيمَ وَآلَ عِمْرَانَ عَلَى الْعَالَمِينَ{33} ذُرِّيَّةً بَعْضُهَا مِن بَعْضٍ وَاللّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ{34}
Lalle ne Allah Yã zãbi Ãdam da Nũhu da gidan Ibrãhĩma da gidan Imrãna a kan tãlikai.
Zuriyya ce sãshensu daga sãshe, kuma Allah Mai ji ne, Masani.
Allah madaukakin sarki ya zabi wasu daga cikin bayinsa domin shiryar da sauran bayinsa kan sahihin tafarkin da yake bukatar su kasance a kansa. Domin isar da wannan sako kamar yadda Allah yake son a isar da shi, kasantuwarsa sako ne mai tsarki, hakan na bukatr tsarkakan mutane da suka da cewa da isar da wannan sako na ubangiji madaukakin sarki.
Duk da cewa Allah madaukakin sarki ya sanya zabi a cikin lamarin addininsa, babu wani annabi da ya zo ya tilasta kowa a kan bin addininsa, domin kuwa dukaknin annabawa suna yin kira ne zuwa ga kadaita Allah madaukakin sarki (tauhidi) amma za mu ga cewa dukkanin annabawan Allah da wasiyyansu mutane ne na gari a tarihin rayuwarsu baki daya, tun daga rayuwarsu ta kuruciya har zuwa lokacin da suka samu annabci daga Allah madaukakin sarki, haka nan kuma wadanda annabawa suke yin wasici da su, suma tsarkakan mutane ne da suka tashi a cikin kyakyawar dabi'a, kuma aka sansu a matsayin salihai a baki dayan rayuwarsu.
Wannan na daga cikin hikimar Allah madaukakin sarki, da ya tayar da manzonsa Muhammad (SAW) a cikin zuriya wadda ta kadaita Allah, domin kuwa zuriyar Bani Hashim zuriya ce wadda take a kan tafarki na tauhidi na kadaita Allah, akmar yadda tarihi ya tabbatar da cewa kabilar Bani hashim wadda ita ce kabilar da aka haifi manzon allah a cikinta tana kan addinin Ibrahim (AS) ne da ake kira din Hanif, wato addinin kadaita Allah, addinin da bai yarda da bautar gumaka ko wasunsu ba, sai Allah shi kadai, wannan na daga cikin dalilan da ke tabbatar da cewa mahaifan manzon Allah ba mushrikai ba ne, kamar yadda kakansa Abu Abdulmuttalib da amminsa Abu Talib su kasance a kan wannan tafarki na din hanif, wato addinin kadaita Allah da annabi Ibrahim (AS) ya zo da shi, wanda kuma addinin muslunci ci gaban wancan kira ne na annabi Ibrahim, da ke kira zuwa kadaita Allah a cikin kudiri da bauta, da kuma yin imani da manzonsa da sakon da ya zo da shi ga talikai, domin shiryar da su zuwa ga sahihin tafarki.
Darussan da za mu dauka daga wadanna ayoyi masu albarka:
1- Akwai banbanci ta fuskacin fifikon daraja da daukaka a tsakanin mutane, Allah yana zabar mafifita ta fuskacin daraja daga cikin mutane sai ya dora musu alhakin shiryar da bayinsa zuwa ga tafarkinsa.
2- Gado yana da tasiri mai matukar muhimmanci wajen ciratar kyawawan dabi'u da kamala irin ta mutum. Aya ta (35 ) da ( 36 ) Ali Imran:
إِذْ قَالَتِ امْرَأَةُ عِمْرَانَ رَبِّ إِنِّي نَذَرْتُ لَكَ مَا فِي بَطْنِي مُحَرَّراً فَتَقَبَّلْ مِنِّي إِنَّكَ أَنتَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ{35} فَلَمَّا وَضَعَتْهَا قَالَتْ رَبِّ إِنِّي وَضَعْتُهَا أُنثَى وَاللّهُ أَعْلَمُ بِمَا وَضَعَتْ وَلَيْسَ الذَّكَرُ كَالأُنثَى وَإِنِّي سَمَّيْتُهَا مَرْيَمَ وِإِنِّي أُعِيذُهَا بِكَ وَذُرِّيَّتَهَا مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ{36}
A lõkacin da mãtar Imrãna ta ce: "Ya Ubangijina! Lalle ni, nã yi bãkancen abin da ke cikin cikĩna gare ka; ya zama 'yantacce, ka karba daga gare ni. Lalle ne Kai, Kai ne Mai ji, Masani."
To, a lõkacin da ta haife ta sai ta ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne nĩ, nã haife ta mace!"KumaAllah ne Mafi sanin abin da ta haifa." Kuma namiji bai zama kamar mace ba. Kuma nĩ nã yi mata suna Maryamu kuma lalle ne ni, ina nẽma mata tsari gare Ka, ita da zũriyarta daga Shaidan jẽfaffe."
Wannan aya mai tsaki tana yin bayani ne kan haihuwar Maryam mahafiyar annabi Isa Almasih (AS) wanda ambaton sunan Imran mahaifin Maryam (AS) shi ne dalilin ambaton surar da suna Ali Imran kamar dai yadda muka bayani a baya.
Ya zo a cikin littafa tarihi cewa, Annabi Zakari da Imran suna cikin salihan mutane a cikin al'ummar Bani Isra'ila, kuma sun auri mata biyu 'yan uwan juna, amma babu ko daya daga cikinsu da ta samu haihuwa, sai mahaifiyar Maryam (AS) wadda ita ce ta auri Imran, a lokacin da ta yi bakancen cewa idan Allah ya bata haihuwa, to za ta sanya abin da ta Haifa ya zama mai hidima a masallacin Qods, sai Allah madaukakin sarki ya bata diya mace mai albarka Maryam (AS) duk kuwa da cewa ita a cikin ranta ta so ta sami da namiji ne domin cika bakancen da ta yi, na sanya abin da ta haifa ya yi hidima a masallaci, duk kuwa da cewa Allah shi ne ya fi sani hikimar da ke tattare da haihuwardiya mace da ta yi.
Mahaifiyarta san mata suna Maryam, kuma ta roki Allah da ya kare mata ita daga sharrin shaidanu, domin ta cika bakancen da ta yi. Hikimar Allah ta haihuwar Maryam wadda ta kasance mace mafi daraja a lokacinta, ita ce Allah madaukakin sarki ya zabar ma annabinsa Isa Almasih (AS) Mahifiya ne, wadda ta fi dukaknin mata daraja da albarka a duniya baki daya a lokacin.
Darussan koyo daga wadannan ayoyi masu albarka:
1- Salihan mutane kafin haihuwar 'ya'yansu suna tunanin yadda za su saka su hanya mai kyau domin yin hidima ga addinin Allah.
2- Yin hidima a masallaci na daga cikin ayyuka masu daraja da albarka, ta yadda salihan bayi suke rokon Allah ya ba su 'ya'yan da za su yi hidima ga masallata.
3- Zabar suna mai kyau ga yaro ko yarinya yana da kyau, domin kuwa matar Imran ta zabi suna Maryam, wanda ke nufin mace mai yawan ibada da hidima a tafarkin Allah.
4- A lokacin tarbiyar yaro a mayar da lamari ga Allah domin neman shiriyarsa da kariya daga sharrin shaidanu.
Aya ta ( 37 ) Imran:
فَتَقَبَّلَهَا رَبُّهَا بِقَبُولٍ حَسَنٍ وَأَنبَتَهَا نَبَاتاً حَسَناً وَكَفَّلَهَا زَكَرِيَّا كُلَّمَا دَخَلَ عَلَيْهَا زَكَرِيَّا الْمِحْرَابَ وَجَدَ عِندَهَا رِزْقاً قَالَ يَا مَرْيَمُ أَنَّى لَكِ هَـذَا قَالَتْ هُوَ مِنْ عِندِ اللّهِ إنَّ اللّهَ يَرْزُقُ مَن يَشَاءُ بِغَيْرِ حِسَابٍ
Sai Ubangijinta Ya karbe ta karba mai kyau. Kuma Ya yabanyartar da ita yabanyartarwa mai kyau, kuma Ya sanya rẽnonta ga Zakariyya. Ko da yaushe Zakariyya ya shiga a gare ta a, sai ya sãmi abinci a wurinta. ya ce: "Yã Maryamu! Daga ina wannan yake zuwa gare ki?" ta ce: "Daga wurin Allah yake. Lalle ne Allah yana azurta wanda Ya so ba da lissafi ba."
Kamar yadda aka mabata a cikin ayar da ta gabata cewa, mahaifiyar Maryam ta yi bakance ne kan za ta sanya duk abin da ta Haifa ya zama mai hidima a masallacin Qudus, amma sai Allah ya bata mace, domin ta cika wannan bakance da ta yi wa Allah madaukakin sarki, sai ta sanya Maryam ta zama mai hidima a wannan masallaci mai daraja, Annabi Zakariyya (AS) ya dauki nauyin rainonta.
Maryam (AS) ta girma a karkashin kulawar Annabi Zakariya (AS) a duk lokacin day a shiga wurin day a ajiye ta domin kai mata abinci, sai ya ga nau'in abinci iri-iri da kayan marmari wadanda ba a san irinsu ba, bayan annabi Zakariyya (AS) ya tambaye ta daga ina take samun wannan abinci sai ta gaya masa cewa daga wurin Allah ne abincin yake zuwa, kasantuwarsa annabin Allah, ya gane cewa lallai wannan abincin daga aljanna ne mala'iku suke kawo ma Maryam shi.
Darussan da ke cikin wannan aya mai albarka:
1- Duk aikin da ake yi saboda Allah to zai ta kara samun ci gaba da bunkasa.
2- Mace za ta iya kaiwa ga wani matsayi a wurin Allah ta yadda har annabin Allah zai yi mamakin matsayinta a wurin Allah.
3 – Idan bawan Allah ya aikata abin da ya rataya kansa, to Allah zai isar masa daga sauran duk abin da shafi rayuwarsa.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 38-43 (Kashi Na 81)
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wani sabon shirin Hannunka Mai Sanda da ke mana dubi da kuma sharhi cikin wasu ayoyi na Alkur’ani mai girma. Da fatan za ku kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.
Za mu fara shirin na mu ne da sauran ayoyi na 38 da 39 na Suratu Al Imrana kana daga baya kuma mu yi sharhi kanta: Yanzu bari mu saurari wadannan ayoyin:
هُنَالِكَ دَعَا زَكَرِيَّا رَبَّهُ قَالَ رَبِّ هَبْ لِي مِن لَّدُنْكَ ذُرِّيَّةً طَيِّبَةً إِنَّكَ سَمِيعُ الدُّعَاء{38} فَنَادَتْهُ الْمَلآئِكَةُ وَهُوَ قَائِمٌ يُصَلِّي فِي الْمِحْرَابِ أَنَّ اللّهَ يُبَشِّرُكَ بِيَحْيَـى مُصَدِّقاً بِكَلِمَةٍ مِّنَ اللّهِ وَسَيِّداً وَحَصُوراً وَنَبِيّاً مِّنَ الصَّالِحِينَ{39}
"A can ne Zakariyya ya roki Ubangijinsa, ya ce, Ya Ubangijina! Ka ba ni zuriya mai kyau daga gunKa. Lalle ne Kai Mai jin addu'a Kake. Sai mala'iku suka kiraye shi, alhali kuwa shi yana tsaye yana salla a cikin masallaci. (Suka ce), Lalle ne, Allah Yana ma ka bushara da Yahaya, alhali yana mai gaskatarwar wata kalma daga allah, kuma shugaba, kuma tsarkakke, kuma annabi daga salihai".
Kamar yadda mu ka fadi a shirin da ya gabata cewa Maryam wacce take hidima a Baitul Mukaddas sakamakon bakance da mahaifiyarta ta yi, tana gudanar da lokacinta wajen bautar Allah da mancewa da dukkan komai in ba bautan Ubangiji da neman taimakonsa ba. To sai dai a duk lokacin annabi Zakariya wanda shi ne mai kula da ita ya zo wajenta don ganin halin da take ciki, sai ya dinga ganin abinci da 'ya'yan itatuwa wadanda ba lokacinsu ba ne. A wata rana da ya zo wajenta ya ga irin wadannan abincin ne don haka sai ya daga hannayensa sama yana rokon Ubangiji da cewa Ya Allah kamar yadda ka ba wa mahaifiyar Maryam irin wannan diyar tsarkakka ma'abociyar imani, to ni ma Ya allah ka ba wa matata wani da tamkar Maryam.
Allah dai ya karbi wannan addu'a ta Zakariyya. A lokacin da ya kasance a wajen ibadarsa yana ta bautar Ubangiji, sai Mala'ikun Ubangiji suka sauka masa suna masu masa bisharar cewa nan ba da jimawa ba za a ba shi da mai suna Yahya, wannan yaron kuwa yana da siffofi kamar haka: na farko zai yi imani da annabin lokacinsa wato annabi Isa (a.s), wanda hakan zai sanya mutane yin imani da annabi Isan.
Na biyu shi ne cewa mutane za su dauke shi a matsayin shugabansu kuma abin koyinsu a bangaren kyawawan halaye da ayyuka na kwarai. Na uku shi ne cewa shi mutum ne mai nesantar soyace-soyacen zuciya da abubuwa na duniya. Sannan kuma siffa mafi muhimmanci cikin hakan shi ne cewa Allah Madaukakin Sarki zai aiko shi a matsayin annabi sannan kuma zai zamanto daga cikin salihai.
Yanzu kuma bari mu yi dubi cikin darussan da za mu iya dauka daga cikin wadannan ayoyi:
Kimar da 'ya'ya yana cikin tsarki da imaninsu ne ba wai batun jinsinsu (wato namiji ne ko mace ba. A cikin wannan kissar za mu ga cewa Allah Madaukakin Sarki ya ba wa Imrana diya mace ce, wacce ita ce Maryam sannan wa Zakariya kuma ya ba shi da namiji wato Yahya, to amma dukkaninsu sun kasance masu imani da kuma tsarkin zuciya.
To yanzu kuma bari mu saurari ayoyi na 40 da 41 na wannan Sura ta Al Imrana:
قَالَ رَبِّ أَنَّىَ يَكُونُ لِي غُلاَمٌ وَقَدْ بَلَغَنِيَ الْكِبَرُ وَامْرَأَتِي عَاقِرٌ قَالَ كَذَلِكَ اللّهُ يَفْعَلُ مَا يَشَاءُ{40} قَالَ رَبِّ اجْعَل لِّيَ آيَةً قَالَ آيَتُكَ أَلاَّ تُكَلِّمَ النَّاسَ ثَلاَثَةَ أَيَّامٍ إِلاَّ رَمْزاً وَاذْكُر رَّبَّكَ كَثِيراً وَسَبِّحْ بِالْعَشِيِّ وَالإِبْكَارِ{41}
"Ya ce: Ya Ubangijina! Ya ya yaro zai samu a gare ni, alhali kuwa, lalle tsufa ya same ni, kuma matata bakarariya ce? Allah ya ce, Kamar hakan ne, Allah yana aikata abin da yake so. Ya ce: Ya Ubangijina! Ka sanya mini wata alama! Allah ya ce: Alamarka it ace ba za ka iya yi wa mutane magana ba har yini uku face ishara. Sai ka ambaci Ubangijinka da yawa. Kuma ka yi tasbihi da marece da safe".
To duk da yake Zakariya shi da kansa ne ya bukaci Allah Madaukakin Sarki da ya ba shi da namiji, to amma a lokacin da ya yi masa bishara da wannan dan lamarin ya ba shi mamaki don kuwa matarsa ta tsufa bat a haihuwa sannan ga shi kuma shi ma kansa ya tsufa, don haka ba ya ma tunanin samun da.
Lalle a fili yake cewa duk wani mutum da ya fuskanci wani lamari wanda ya saba wa dabi'a da kuma yadda ake tafiya a kai, to kuwa hakan zai ba shi mamaki da kuma neman karin bayani duk kuwa da cewa ya yi imani da faruwar hakan amma kuma zai so ya ga lamarin a fili da idanuwansa. A saboda haka ne Zakariyya ya bukaci Allah Madaukakin Sarki da ya nuna masa wannan lamari da daya ne daga cikin irin kudurarsa. Don haka sai Allah ya bayyana masa wasu alamomi da za su tababtar masa da yiyuwar wannan lamari.
Cikin ikon Allah kuwa, Zakariyya wanda ba shi da wata matsala wajen magana, sai ga shi ya rasa wannan karfi na magana da ya ke da shi na tsawon wadannan kwanaki ukun, ta yadda in dai ba ta hanyar ishara ba, ba shi da wata hanya da zai bayyanar da abin da ya ke so har sauran mutane su fahimci abin da ya ke nufi, sai dai kawai a duk lokacin da ya ke son yin zikiri ne bakin nasa yake buduwa.
Darasin da za mu dauka daga cikin wadannan ayoyi sun hada da:
1- Iradar Ubangiji tana sama da dukkan komai, a duk lokacin da ya so ba wa wani tsoho da ko kuma wata mace wacce ba ta haihuwa diya, to babu wani abin da zai hana faruwar hakan. 2- Allah Madaukakin Sarki yana karfin aikata komai. Idan har ya so sai ya sanya harshe ya zamanto hanyar magana idan kuma ya so sai ya hana shi maganar.
Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 42 da 43 na cikin Suratu Al Imranan:
وَإِذْ قَالَتِ الْمَلاَئِكَةُ يَا مَرْيَمُ إِنَّ اللّهَ اصْطَفَاكِ وَطَهَّرَكِ وَاصْطَفَاكِ عَلَى نِسَاء الْعَالَمِينَ{42} يَا مَرْيَمُ اقْنُتِي لِرَبِّكِ وَاسْجُدِي وَارْكَعِي مَعَ الرَّاكِعِينَ{43}
"Kuma a lokacin da mala'iku suka ce: Ya Maryamu! Lalle ne, Allah Ya zabe ku, kuma Ya tsarkake ki, kuma Ya zabe ki a kan matan talikai. Ya Maryamu! Ki yi kankan da kai ga Ubangijinki, kuma ki yi sujada, kuma ki yi ruku'i tare da masu ruku'i.
Irin tsarki, salla da ibada saboda da Allah na Maryam (a.s) shi ne ya sanya Allah Madaukakin Sarki ya zabe da kuma sanya ta sama da sauran mata sannan kuma matsayin da ta ke da shi ya kai ta yadda har Mala'iku sukan zo wajenta suna magana da ita, suna mata bishara da kuma isar mata da umurnin Ubangiji kai tsaye, sannan kuma ta haifi daya daga cikin annabawan Allah masu girma wato annabi Isa (a.s) sannan kuma ya tashi karkashin kulawarta har ma mala'ikun Allah suna gaya mata cewa ta ci gaba da kiyaye wannan kankan da kai da take shi saboda wannan ni'ima da Allah ya yi mata sannan kuma ta ci gaba da gode masa, ta yi masa ruku'i da sujada tare da sauran masu salla.
Daga cikin darussan da za mu iya dauka daga cikin wadannan ayoyi guda biyu akwai cewa:
1- Ba haka kawai Allah Madaukakin Sarki ya ke zaban kowane mutum ba, face dai Allah Madaukakin Sarki yana zaban mutum ne bisa asasi na dacewa da kuma irin karfin da ya ke da shi. Allah Madaukakin Sarki ya zabi Maryam da ba ta irin wannan matsayi da take da shi ne saboda tsarkin zuciyar da take da shi ne. 2- Mala'ikun Allah suna magana ma da wadanda ba annabawa ba, amma dai da sharadin cewa suna da irin wannan matsayi. 3- Halartar sallar jam'i ga mata wani lamari ne abin so, to amma da sharadin cewa su din nan suna da irin matsayi na Maryam.
Masu saurare da haka ne muka kawo karshen shirin na mu na yau, sai kuma a saduwa ta gaba inda za mu dora daga inda muka tsara. Kafin nan na ke cewa ku zama lafiya. Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 44-47 (Kashi Na 82)
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wani sabon shirin Hannunka Mai Sanda da ke mana dubi da kuma sharhi cikin wasu ayoyi na Alkur’ani mai girma. Da fatan za ku kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.
Za mu fara shirin na mu ne da sauran ayoyi na 44 na Suratu Al Imrana kana daga baya kuma mu yi sharhi kanta: Yanzu bari mu saurari wannan ayar:
ذَلِكَ مِنْ أَنبَاء الْغَيْبِ نُوحِيهِ إِلَيكَ وَمَا كُنتَ لَدَيْهِمْ إِذْ يُلْقُون أَقْلاَمَهُمْ أَيُّهُمْ يَكْفُلُ مَرْيَمَ وَمَا كُنتَ لَدَيْهِمْ إِذْ يَخْتَصِمُونَ{44}
"Wannan yana daga labarum gaibi, Muna yin wahayinsa zuwa gare ka (Ya Muhammadu). Ba ka kasance ba a wurinsu, a lokacin da suke jefa alkalumansu (domin kuri'a) wane ne zai yi renon Maryam. Kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lokacin da suke ta yin husuma".
A kokarin da suke yi na inkarin matsayin Alkur'ani da kuma nuna cewa shi din nan ba wahayi ne na Ubangiji ba, mushirikan Makka sun kasance suna cewa Alkur'ani dai bai wuce wani littafi na labarai ba, sannan kuma Muhammadu ya koyi wadannan labarai ne daga littafan yahudawa da suka gabata sannan ya zo yana karanta su.
A lokacin da ya ke amsa musu wannan tambaya ta su, Allah Madaukakin Sarki yana fadin cewa: da dama daga cikin kissosin da suka zo cikin Alkur'ani lamurra ne na gaibi wanda babu wani da ya sansu, shi kansa annabi a kan sanar da shi su ne ta hanyar wahayi. A matsayin misali wannan lamari na bakance mahaifiyar Maryam ba kowa ne ya san shi in ba Allah ba, haka nan batun kuri'ar daukan nauyin kula da Maryam, dukkanin wadannan labarai ne na gaibi wanda aka gaya wa Annabi ta hanyar wahayi.
Dangane da batun daukan nauyin kula da Maryam, a shirye-shiryen da suka gabata mun bayyana cewar mahaifiyar Maryam ta yi bakancen cewa za ta sanya dan da za ta haifa ya zamanto mai yin hidima ga Baitul Mukaddas. Don haka ne ta zo da ita zuwa ga masu kula da wannan masallaci don su gudanar da kuri'a a tsakaninsu dangane da wanda zai dauki wannan nauyin saboda iyayen Maryam sun kasance mutane ne masu mutumci wadanda ake girmama su cikin Bani Isra'ila, don haka kowa yana son ya sami wannan damar.
Daga wannan ayar za mu iya daukan darussa kamar haka:
1- Alkur'ani wahayi ne na Ubangiji, ba wai rubutu ne na wadansu mutane ba wanda aka samo shi daga wasu littafa na daban ba ko kuma abu ne da aka ruwaito shi daga abubuwan da wasu suka haddace ba. 2- Kamata ya yi gasa ta zamanto kan daukan wani nauyi na Ubangiji kuma mai sarki, ba wai saboda neman matsayi da mukami ba.
Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 45 ta cikin Suratu Al Imrana:
إِذْ قَالَتِ الْمَلآئِكَةُ يَا مَرْيَمُ إِنَّ اللّهَ يُبَشِّرُكِ بِكَلِمَةٍ مِّنْهُ اسْمُهُ الْمَسِيحُ عِيسَى ابْنُ مَرْيَمَ وَجِيهاً فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ وَمِنَ الْمُقَرَّبِينَ{45}
"A lokacin da mala'iku suka ce: "Ya Maryamu! Lalle ne Allah Yana ba ki bushara da wata kalma daga gare Shi; sunansa Masihu Isa dan Maryama, yana mai daraja a duniya da Lahira kuma daga Makusanta".
Maryam dai ta zamanto mai hidima ga masallaci ne saboda bakancen da mahaifiyarta ta yin e, haka nan kuma ta ci gaba da bautar Allah sannan mala'iku kuma suna kawo mata abincin da take ci daga sama. Hakan ya sanya ta samun damar da Allah Madaukakin Sarki ya arzurta tad a wani da wanda a wajen mutane ma ya zamanto mai matsayi mai girma haka nan kuma a wajen Ubangiji ma ya zamanto daga cikin na kurkusa. To sai dai sabanin abin da mabiya addinin kirista suka yi imani da shi, Isa dai ba Allah ba ne sannan kuma ba dan Allah ba ne, shi din nan dan Maryam ne sannan kuma bawan Allah kuma halittansa.
Shi halitta ne wanda samuwarsa take nuni da karfi da kuma daukaka ta Ubangiji don haka ne Allah ya kira shi da sunan kalma, kamar yadda a cikin aya ta 109 ta cikin Suratul Kahf ya bayyana dukkanin halittun Ubangiji da sunan kalmominsa.
Daga cikin wannan ayar za mu iya fahimtar darussa kamar haka:
1- Mala'ikun Allah, baya ga annabawan Allah, har ila yau suna magana da sauran bayin Allah salihai, shin maza ne ko kuma mata. 2- Duk kuwa da cewa annabi Isa (a.s) dai an haife shi neb a tare da yana da mahaifi ba, to amma duk da haka shi dai ba dan Allah ba ne, face dai shi dan Maryam.
To yanzu kuma bari mu saurari aya ta 46 ta cikin Suratu Al Imrana:
وَيُكَلِّمُ النَّاسَ فِي الْمَهْدِ وَكَهْلاً وَمِنَ الصَّالِحِينَ{46}
"Kuma yana yi wa mutane magana a cikin shimfidar jariri, da kuma lokacin da yana dattijo, kuma yana daga salihai".
Wato Ya Maryam wannan yaro da za muka yi miki bisharar cewa za mu ba ki shi zai yi magana da mutane tun lokacin yana jariri ne haka nan kuma a lokacin da ya girma, sannan kuma zai kasance daga cikin salihan bayi.
A lokacin da Maryam ta ji wannan bishara ta da, ta damu sosai saboda mutane za su zarge ta da kuma tuhumarta da mummunan aiki, don kuwa ba ta da miji. A saboda haka ne mala'iku suka ce mata: don ba ki kariya da kuma tabbatar da wannan tsarki na ki, lalle za mu bude bakin wannan jariri na ki yayi magana da kuma kore duk wata tuhuma da za a yi miki.
Shi din nan tamkar sauran manyan salihan bayi, zai yi magana cikin fasaha da kuma dukkan karfi ta yadda kowa zai yi mamaki sannan kuma za a ga mu'ujizar Ubangiji cikin halittars.
Yanzu kuma bari mu yi dubi cikin darussan da suke cikin wannan ayar:
1- Bai kamata mu yi shakka cikin kudura ta Ubangiji ba, don kuwa wanda zai iya ba wa Maryam da ba tare da miji ba, lalle zai iya bude bakin jariri da ke cikin zanin goyo ya yi magana. 2- Idan har mahaifiya ta zamanto mai kyawawan halaye da dabi'u na kwarai, to kuwa irin wannan yanayi zai iya komawa ga 'ya'yanta.
Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 47 ta cikin Suratu Al Imranan:
قَالَتْ رَبِّ أَنَّى يَكُونُ لِي وَلَدٌ وَلَمْ يَمْسَسْنِي بَشَرٌ قَالَ كَذَلِكِ اللّهُ يَخْلُقُ مَا يَشَاءُ إِذَا قَضَى أَمْراً فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُ كُن فَيَكُونُ{47}
"Ta ce: Ya Ubangiji! Yaya yaro zai kasance a gare ni, alhali kuwa wani mutum bai shafe ni ba? (Allah) Ya ce: "Kamar wannan ne, Allah Yana halittar abin da Yake so. Idan ya hukumta wani al'amari, sai ya ce masa, 'Ka kasance! Sai ya kasance".
To a dabi'ance dai bishara ga Maryam na cewa za a bata da, sannan da kuma irin wannan, lalle wani tunani da kuma tambaya za ta zo wa Maryam cewa ta ya ya hakan za ta faru alhali kuwa ba ta da miji, don kuwa samun uwa da uba wasu abubuwa ne guda biyu da a dabi'ance ake bukatarsu kafin a sami zuriya.
To don amsa mata wannan tambayar ce Allah Madaukakin Sarki ya aiko da mala'iku zuwa wajenta suka sanar da ita cewa tsari na dabi'a dai wani lamari ne da ke hannun Ubangiji, ta yadda a duk lokacin da ya so ya kan iya sauya wannan tsari, wato ya samar da dan'adam ba ta wannan hanya da aka saba da ita ba.
A karshen ayar dai ta yi ishara da wani tushe da tsari na asasi dangane da halitta inda Allah Madaukakin Sarki ya ke cewa daga lokacin da ya so faruwa ko kuma samuwar wani abu nan take abin ya kan faru ko kuma ya samu ba tare da wani bata lokaci ko kuma samar da yanayin da aka saba da shi ba.
Daga wannan ayar za mu iya fahimtar cewa:
Hannun Allah Madaukakin Sarki a bude yake dangane da dukkanin halittunsa. A wajen Allah hanya ta dabi'a wacce aka saba da ita da ma wacce ba ta dabi'a ba babu wani bambanci a wajensa, a duk lokacin da ya so samar da wani abu zai samar da shi ne.
Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 48-53 (Kashi Na 83)
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wani sabon shirin Hannunka Mai Sanda da ke mana dubi da kuma sharhi cikin wasu ayoyi na Alkur’ani mai girma. Da fatan za ku kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.
Za mu fara shirin na mu ne da sauran ayoyi na 48 da 49 na Suratu Al Imrana kana daga baya kuma mu yi sharhi kanta: Yanzu bari mu saurari wannan ayar:
وَيُعَلِّمُهُ الْكِتَابَ وَالْحِكْمَةَ وَالتَّوْرَاةَ وَالإِنجِيلَ{48} وَرَسُولاً إِلَى بَنِي إِسْرَائِيلَ أَنِّي قَدْ جِئْتُكُم بِآيَةٍ مِّن رَّبِّكُمْ أَنِّي أَخْلُقُ لَكُم مِّنَ الطِّينِ كَهَيْئَةِ الطَّيْرِ فَأَنفُخُ فِيهِ فَيَكُونُ طَيْراً بِإِذْنِ اللّهِ وَأُبْرِئُ الأكْمَهَ والأَبْرَصَ وَأُحْيِـي الْمَوْتَى بِإِذْنِ اللّهِ وَأُنَبِّئُكُم بِمَا تَأْكُلُونَ وَمَا تَدَّخِرُونَ فِي بُيُوتِكُمْ إِنَّ فِي ذَلِكَ لآيَةً لَّكُمْ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ{49}
“Kuma Ya sanar da shi rubutu da hikima da Taurata da Injila. Kuma (Ya sanya shi) manzo zuwa ga Bani Isra’ila (da sako, cewa), Lalle ne, ni hakika, na zo muku da wata aya daga Ubangijinku. Lalle ne, ni, ina halitta muku daga laka, kamar siffar tsuntsu, sa’an nan in hura a cikinsa, sai ya kasance tsuntsu, da izinin Allah. Kuma ina warkar da wanda aka Haifa makaho da kuturu kuma ina rayar da matattu, da izinin Allah. Kuma ina gaya muku abin da kuke ci da abin da kuke ajiyewa a cikin gidajenku. Lalle ne, a cikin wannan akwai aya a gare ku, inda kun kasance masu yin imani”.
A shirye shiryen da suka gabata mun bayyana cewa Annabi Isa (a.s) ya yi magana da mutane tun yana cikin majanyin goyo na mahaifiyarsa sannan kuma ya kare mahaifiyarsa dangane da tuhumar da ake mata. To a cikin wannan ayar kuma an yi bayanin wasu siffofin ne da Annabi Isa (a.s) ya kebanta das u.
A fili yake cewa duk wani annabin da ya ke son ya jagoranci al’ummarsa wajibi ne ya zamanto yana da wasu siffofi na musamman wanda daya daga cikin su shi ne ilimi da masaniya. A saboda haka ne koyarwa da kuma tarbiyyar annabawa suke hannun Allah Madaukakin Sarki don wadannan masaniya da ilmi na su su zamanto sun tsira daga dukkanin kuskure. Na biyu kuma baya ga ilimi na zahiri wanda yake tattare da dukknain mutane, wajibi ne kuma su zamanto suna da ilimi na gaibi da labarurrukan al’ummomin da suka gabata.
To sai dai samun ilimi da masaniya su kadai ba sa wadatarwa, wajibi ne kowane Annabi ya gabatar da wata mu’ujiza wajen tabbatar da annabci da kuma sakon da Allah ya aiko da shi don mutane su yarda da abubuwan da yake fadi sannan kuma su yi aiki da su. Duk da cewa ita kanta samuwar Annabi Isa, ita kanta mu’ujiza ce, don kuwa mahaifiyarsa Maryam ta haife shi ne ba tare da tana da miji ba sannan shi ma bayan haihuwarsa ya yi magana da mutane, to amma duk da haka Annabi Isa ya gabatar wa Bani Isra’ila wadanda zuwa gare su ne Allah ya aiko shi da wasu mu’ujizozin don dai su yarda da abin da ya ke fadi. Daga cikin wadannan mu’ujizozin shi ne yana halittar tsuntsu daga laka, yana warkar da marasa lafiya, yana rayar da matattu sannan yana bas u labarin abubuwan da ke gudana a cikin gidajensu, duk kuwa da cewa dukkanin wadannan abubuwa yana yin su ne bisa izini da kuma umurnin Ubangiji, don kuwa halitta da kuma bayanin gaibi abubuwa ne da suka kebanta Ubangiji Madaukakin Sarki, to amma yana ba da wannan karfin ga duk wanda ya so.
To sai dai kuma wasu daga cikin wadanda suka yi imani da shi din, sakamakon wadannan abubuwan da ya yi da kuma irin yanayin da aka haife shi wanda ya saba wa yadda dan’adam ya sani don haka sai suka dauke shi a matsayin dan Allah (wal iyazu billah) alhali shi dan Maryam ne ba wai dan Ubangiji ba, sannan kuma dukkanin abin da ya faru da shi da kuma abubuwan da ya aikata duk sun faru ne bisa umurni da kuma kudura ta Ubangiji.
Daga wadannan ayoyi mun koyi cewa:
1- Waliyan Allah za su iya kutsawsa cikin tsarin halitta da dabi’a da kuma haifar da sauyi cikin hakan sai dai kuma za su iya yin hakan ne bisa yarda da kuma izinin Ubangiji. 2- Idan har bayin Allah salihai za su iya tayar da matattau a duniya, to kuwa tayar da matattu a ranar tashin alkiyama a wajen Allah ba wani lamari ne mai girma ko kuma abin da ba zai yiyu ba. 3- Bai kamata mu wuce gona da iri cikin bayin Allah da daukansu a matsayin Ubangiji ba saboda wani abin da suka aikata ba.
To yanzu kuma bari mu saurari ayoyi na 50 zuwa 51 na cikin Suratu Al Imranan:
وَمُصَدِّقاً لِّمَا بَيْنَ يَدَيَّ مِنَ التَّوْرَاةِ وَلِأُحِلَّ لَكُم بَعْضَ الَّذِي حُرِّمَ عَلَيْكُمْ وَجِئْتُكُم بِآيَةٍ مِّن رَّبِّكُمْ فَاتَّقُواْ اللّهَ وَأَطِيعُونِ{50} إِنَّ اللّهَ رَبِّي وَرَبُّكُمْ فَاعْبُدُوهُ هَـذَا صِرَاطٌ مُّسْتَقِيمٌ{51}
“Kuma ina mai gaskatawa ga abin da yake a gabanina daga Taurata. Kuma (na zo) domin in halatta musu sashen abin da aka haramta muku. Kuma na tafo muku da wata aya daga Ubangijinku. Sai ku bi Allah da takawa, kuma ku yi mini da’a. Lalle Allah Shi ne Ubangijina, kuma Ubangijinku, sai ku bauta masa. Wannan ce hanya madaidaiciya.
Bisa la’akari da cewa Annabi Musa (a.s) a matsayinsa na manzon da aka aiko wa Bani Isra’ila ya zo musu da Attaura a matsayin littafi daga wajen Ubangiji. To a cikin wannan ayar Annabi Isa (a.s) yana gaya wa mutane ne cewa nid in nan ma kamar Annabi Musa daga wajen Allah Madaukakin Sarki na ke sannan kuma na gaskata littafinsa, sannan kuma ina dage muku wasu abubuwan da aka haramta muku su da kuma dankara muku su a cikin Attaura sakamakon zunubin da kuka aikata, to amma da sharadin fa za ku yi imani da kuma ci gaba da tsayawa kan wannan imani na ku, wato ku ci gaba da bin wannan addini da Allah ya aiko muku da shi.
To a nan ma Annabi Isa ya bayyana kansa a matsayin bawan Allah yana mai cewa: Allah dais hi ne Ubangijina kuma Ubangijinku don haka mu bauta masa shi kadai sannan kuma mu tsaya kyam a bisa tafarkinsa wanda shi ne madaidaicin tafarki.
Daga cikin wadannan ayoyi za mu iya fahimtar darussa kamar haka:
1- Annabawan Allah sun yi imani da junansu, sannan kuma kowane annabin da ya zo daga baya ya yi imani da littafan annabawan da suka gabace shi. 2- Aiko annabawa wani lamari ne na Ubangiji da ya kasance tsawon tarihi, bawai wani lamari ne da ya kebanci wani waje ko kuma wani lokaci ba ne. 3- Annabawan Allah dai, kamar yadda suke da wilaya ta kutsawa cikin yanayin halitta, haka nan kuma suke da wilaya ta kafa dokoki da hukumce-hukumce, ko da yake dukkanin wadannan abubuwa biyu bisa umurni da kuma izinin Allah Madaukakin Sarki ne.
To yanzu kuma bari mu saurari ayoyi na 52 zuwa 53 na cikin Suratu Al Imranan:
فَلَمَّا أَحَسَّ عِيسَى مِنْهُمُ الْكُفْرَ قَالَ مَنْ أَنصَارِي إِلَى اللّهِ قَالَ الْحَوَارِيُّونَ نَحْنُ أَنصَارُ اللّهِ آمَنَّا بِاللّهِ وَاشْهَدْ بِأَنَّا مُسْلِمُونَ{52} رَبَّنَا آمَنَّا بِمَا أََََََََََََََََنزَلْتَ وَاتَّبَعْنَا الرَّسُولَ فَاكْتُبْنَا مَعَ الشَّاهِدِينَ{53}
“To a lokacin da Isa ya gane kafirci daga gare su, sai y ace: “Su wane ne mataimakana zuwa ga Allah? Hawariyawa suka ce: “Mu ne mataimakan Allah. Mun yi imani da Allah. Kuma ka shaida cewa, lalle ne mu, masu sallamawa ne. Ya Ubangijinmu! Mun yi imani da abin da ka saukar, kuma mun bi Manzonka, sai ka rubuta mu tare da masu shaida”.
Duk da alamu da mu’ujizozin da Bani Isra’ila suka gani dangane da Annabi Isa (a.s), to amma da dama daga cikinsu ba su yi imani da shi ba sun ci gaba da zama cikin kafircinsu, wasu ‘yan kadan ne kawai suka yi imani da shi da kuma goyon bayansa, wadanda su ne Alkur’ani mai girma ya ke kiransu da Hawariyawa, wato mutanen da suka yi watsi da tafarkin bata da sauran mutane suka kama sannan kuma suka riki gaskiya.
Daga cikin darussan da za mu iya dauka daga cikin wadannan ayoyi sun hada da:
1- Fahimtar muminai masu riko da kuma sadaukarwa saboda addini daya ne daga cikin ayyukan shugabanni na addini. 2- Annabawan Allah dai suna kiran mutane ne zuwa ga Allah ba wai zuwa ga kansu ba, kamar yadda shi kansa Annabi Isa ya fadi cewa su wane ne za su taimaka wa addinin Allah. 3- Imani yana nufin mika wuya ga Allah, wato duk wanda ya yi imani da Allah, wajibi ne ya zamanto mai biyayya ga umurnin Allah da annabinsa.
Da haka ne muka kawo karshen shirin na mu na yau, sai kuma a saduwa ta gaba. Kafin nan na ke cewa wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 54-60 (Kashi Na 84)
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wani sabon shirin Hannunka Mai Sanda da ke mana dubi da kuma sharhi cikin wasu ayoyi na Alkur’ani mai girma. Da fatan za ku kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.
Za mu fara shirin na mu ne da sauran ayoyi na 54-55 na Suratu Al Imrana kana daga baya kuma mu yi sharhi kanta: Yanzu bari mu saurari wannan ayar:
وَمَكَرُواْ وَمَكَرَ اللّهُ وَاللّهُ خَيْرُ الْمَاكِرِينَ{54} إِذْ قَالَ اللّهُ يَا عِيسَى إِنِّي مُتَوَفِّيكَ وَرَافِعُكَ إِلَيَّ وَمُطَهِّرُكَ مِنَ الَّذِينَ كَفَرُواْ وَجَاعِلُ الَّذِينَ اتَّبَعُوكَ فَوْقَ الَّذِينَ كَفَرُواْ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ ثُمَّ إِلَيَّ مَرْجِعُكُمْ فَأَحْكُمُ بَيْنَكُمْ فِيمَا كُنتُمْ فِيهِ تَخْتَلِفُونَ{55}
“Kuma (kafirai) suka yi makirci, Allah kuma ya yi musu (sakamakon) makircin, kuma Allah ne Mafi alherin masu saka wa makirci. A lokacin da Ubangiji y ace: Ya Isa! Lalle Ni Mai karbar ranka ne, kuma Mai dauke ka ne zuwa gare Ni, kuma Mai tsarkake ka daga wadanda suka kafirta, kuma Mai sanya wadanda suka bi ka a bisa wadanda suka kafirta, har Ranar Kiyama. Sa’an nan kuma zuwa gare Ni makomarku take, sa’an nan In yi hukumci a tsakaninku, a cikin abin da kuka kasance kuna saba wa jina”.
A shirin da ya gabata mun bayyana cewar duk da irin mu’ujizozi masu yawa da Annabi Isa (a.s) ya nuna, amma wasu sun ki yin imani da shi, don haka ne wadannan ayoyi suke magana dangane da makircin da suke kullawa na kashe shi da bayyana cewar shugabannin wancan lokacin sun tsara wani mummunan shiri duk dai da nufin kashe wannan haske da ya zo da shi.
Sun saka wata lada mai yawan gaske ga duk wanda ya kamo musu Annabi Isa da mabiyansa da kuma share fagen kashe shi, to sai dai kuma Allah Madaukakin Sarki ya mai da wannan makirci na su ya zamanto aikin banza ya kuma tseratar da Annabi Isa, kamar yadda mabiya addinin Kirista suka yi imani da cewa yahudawa sun daure Annabi Isan da nufin giciye shi, har ma sun kashe shi da kuma bisne shi amma daga baya Allah ya tayar da shi a tsakankanin matattu da kuma tafiya da shi sama. To sai dai kamar yadda ayoyin Alkur’ani suka nuna musamman ma aya ta 157 ta cikin Suratun Nisa'i ta nuna yahudawan wani mutum na daban wanda aka mai dai kamananninsa ya yi kama da na Annabi Isan ne suka kama da kuma kashe shi. To amma Annabi Isa kan Allah cikin ikonsa ya tseratar da shi da kuma dauke shi zuwa sama, kamar yadda annabin mu Muhammad (s.a.w.a.) ma aka tafi da shi na wani lokaci zuwa sama don yin mi’iraji da samun ilmummuka daban-daban.
Wannan ayar ta ci gaba da yin bishara ga mabiya addinin kirista cewa za su yi nasara da samun daukaka a kan kafirai, wadanda a wancan lokacin su ne yahudawan. Hakan daya ne daga cikin bisharorin da Alkur’ani mai girma ya yi kimanin shekaru dubu da dari hudun da suka gabata wanda kuma ya zuwa yanzu ya tabbata.
Daga cikin wannan ayar za mu iya daukan darussa kamar haka:
1- Irada da bukatar Ubangiji suna sama da dukkanin kokari da tunani na dan’adam, don haka bai kamata mu kulla wani makirci a kan iradar Ubangiji ba. 2- Biyayya ga annabawa lamari ne da ke tabbatar da daukaka da kuma nasara, sabanin kafirci wanda babu wani abin da yake haifarwa in banda halaka.
Yanzu kuma bari mu saurari ayoyi na 56, 57 da 58 na Suratu Al Imranan:
فَأَمَّا الَّذِينَ كَفَرُواْ فَأُعَذِّبُهُمْ عَذَاباً شَدِيداً فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ وَمَا لَهُم مِّن نَّاصِرِينَ{56} وَأَمَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُواْ الصَّالِحَاتِ فَيُوَفِّيهِمْ أُجُورَهُمْ وَاللّهُ لاَ يُحِبُّ الظَّالِمِينَ{57} ذَلِكَ نَتْلُوهُ عَلَيْكَ مِنَ الآيَاتِ وَالذِّكْرِ الْحَكِيمِ{58}
“To, amma wadanda suka kafirta, sai In azabta su da azaba mai tsanani, a cikin duniya da Lahira, kuma ba su da wasu masu taimako. Kuma amma wadanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan kwarai, sai (Allah) Ya cika musu ladansu. Kuma Allah ba ya son azzalumai. Wannan muna karanta shi a gare ka (Ya Muhammadu) daga ayoyi, da Tunatarwa mai hikima (wato Alkur’ani)”.
Wannan makirci na Bani Isra’ila na kashe Annabi Isa (a.s) ya bayyana a hali don haka Allah Madaukakin Sarki ya sanya su karkashin azaba mai tsananin gaske. A bisa riwaya ta tarihi, daya daga cikin sarakunan Rum ya yi kimanin shekaru arba’in yana mulkansu, ya kashe dubban mutane daga cikinsu ko kuma ya kama su a matsayin fursunonin yaki. Tabbas Allah Madaukakin Sarki ba ya zaluntar wani, hukumcin da ya ke yankewa a kan mutane yana da alaka ne da abubuwan da suka aikata, don kuwa kafirci da taurin kai ba shi da wani sakamakon da ya wuce fada karkashin iko da zaluncin azzalumai, kamar yadda imani da kuma ayyuka na kwarai ba shi da wani sakamakon da ya wuce ni’imomi na duniya da lahira.
Daga wadannan ayoyi za mu iya daukan darussa kamar haka:
1- Duk kuwa da cewa sunnar Ubangiji ta ginu ne bisa jinkirta azaba ko kuma lada har zuwa ranar tashin kiyama, to amma duk da haka a wasu lokuta mutum ya kan fara ganin sakamakon abubuwan da ya aikata. 2- Babu wani karfin da ya isa ya tsaya a gaban karfi na Ubangiji da hana faruwar abin da Allah ya so faruwarsa. Don haka wajibi ne mu yi tunani kan ayyukan da muke aikatawa.
To yanzu kuma bari mu saurari ayoyi na 59 da 60 na cikin Suratu Al Imranan:
إِنَّ مَثَلَ عِيسَى عِندَ اللّهِ كَمَثَلِ آدَمَ خَلَقَهُ مِن تُرَابٍ ثِمَّ قَالَ لَهُ كُن فَيَكُونُ{59} الْحَقُّ مِن رَّبِّكَ فَلاَ تَكُن مِّن الْمُمْتَرِينَ{60}
“Lalle, ne misalin Isa a wurin Allah kamar misalin Adama ne, (Allah) Ya halitta shi daga turbaya, sa’an nan kuma ya ce masa: “Ka kasance”. Sai yana kasancewa. Gaskiya daga Ubangijinka take, saboda haka kada ka kasance daga masu shakka”.
Wasu daga cikin kiristocin garin Madina sun tafi wajen Manzon Allah (s.a.w.a.) don tattaunawa da shi. A cikin tattaunawar ta su sai suka gabatar da batun haihuwar Annabi Isa (a.s) ba tare da uba ma a matsayin dalilin da ke tabbatar da cewa shi Ubangiji ne, don haka sai aka saukar da wannan ayar a matsayin amsa ga abin da suka gabatar inda take cewa: Idan har haihuwar wani mutum ba tare da uba ba yana tabbatar da ubangijintakan mutumin ne, to me ya sa ba ku ambaci Annabi Adamu wanda haihuwarsa ma ta fi ta Annabi Isa din ban mamaki saboda shi ba shi da uwa da uba din ma ba, ba ku ambace shi a matsayin Allah ko kuma dan Allah din ba.
Daga nan sai Allah Madaukakin Sarki ya gaya wa Annabi (s.a.w.a.) da sauran musulmi cewa: maganar gaskiya dai ita ce maganar Allah wacce ta hada dukkanin komai sabanin maganganun sauran mutane wadanda imma dai sun ginu ne bisa jahilci da kuskure ko kuma bisa son zuciya. A saboda haka maganar Allah, magana ce ta gaskiya kada mu bari wasu su sanya mana shakku cikin zuciyarmu dangane da maganar Ubangiji.
Bari mu karkare shirin na mu da darussan da za mu iya dauka daga cikin wadannan ayoyi:
1- Mu’ujizar Ubangiji da ta bayyana cikin halittar wasu daga cikin annabawan Allah, wani lamari ne da ke nuni da irin karfi na Ubangiji ba wai cewa su din nan Alloli ba ne. 2- Ana iya fahimtar gaskiya ne cikin maganganun Ubangiji, matukar dai muna son gaskiya to mu nema ta cikin maganganun Ubangiji.
A nan muka kawo karshen shirin na mu na yau, sai a kasance tare da mu a cikin shiri na gaba. Kafin nan na ke cewa wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 61-64 (Kashi Na 85)
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa cikin wani sabon shirin Hannunka Mai Sanda da ke mana dubi da kuma sharhi cikin wasu ayoyi na Alkur’ani mai girma. Da fatan za ku kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.
Za mu fara shirin na mu ne da sauran aya ta 61 na Suratu Al Imrana kana daga baya kuma mu yi sharhi kanta: Yanzu bari mu saurari wannan ayar:
فَمَنْ حَآجَّكَ فِيهِ مِن بَعْدِ مَا جَاءكَ مِنَ الْعِلْمِ فَقُلْ تَعَالَوْاْ نَدْعُ أَبْنَاءنَا وَأَبْنَاءكُمْ وَنِسَاءنَا وَنِسَاءكُمْ وَأَنفُسَنَا وأَنفُسَكُمْ ثُمَّ نَبْتَهِلْ فَنَجْعَل لَّعْنَةَ اللّهِ عَلَى الْكَاذِبِينَ{61}
“To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bayan abin da ya zo maka daga ilimi, to ka ce: “Ku zo mu kirayi ‘ya’yanmu da ‘ya’yanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku, sa’an nan kuma mu kankantar da kai, sa’an nan kuma mu sanya la’anar Allah a kan makaryata”.
Dalilin saukar wannan ayar kamar yadda ya zo cikin tarihi shi ne cewa: a shekara ta goma ta hijira, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya aike da wasu sahabbansa zuwa yankin Najran da ke kasar Yemen don isar da sakon Musulunci, a saboda haka kiristocin wannan gari na Najran sai suka aike da wata tawaga wajen Manzon Allah (s.a.w.a.) don tattaunawa da shi, bayan tattaunawa da shi kan Annabi Isa da sauransu da kuma karfafan hujjojin da Annabi ya gabatar musu sun ki su amince da gaskiya, don haka Allah Madaukakin Sarki ya umurci Manzonsa da ya yi mubahala da su. Don haka sai ya ce musu: ku zo da ‘ya’yanku da matanku da kuma ku kanku, mu ma za mu zo da ‘ya’yanmu da matanmu da kuma kanmu, sannan mu hadu a wani waje, mu kaskantar da kanmu a gaban Allah sannan kuma mu bukaci Ubangiji da ya sauke azaba da bala’insa a kan duk wata kungiyar da take kan karya. Kiristocin Najran din dai sun bukaci da a ba su lokaci don yin shawara. Bayan shawartar manyansu sun gaya musu cewa: Kuna iya amincewa da wannan shawarar amma idan har kuka gaa Annabi Musulunci ya zo da wasu ‘yan kadan daga cikin iyalan gidansa maimakon sauran sahabbansa don yin wannan mubahalar, to lalle kada ku taba yarda ku yi wannan mubahalar ku yi sulhu da shi, don kuwa idan har kuka yarda kuka yi mubahala da shi da wadannan iyalan gidan nasa to kuwa za ku halaka.
Lokacin da ranar mubahalar ta zo sai suka ga Manzon Allah (s.a.w.a.) ya zo da mutane hudu kawai, wato ‘yarsa Fatima, sirikinsa Ali bn Abi Talib da ‘ya’yansu biyu Hasan da Husain, sai daya daga manyan kiristocin ya ce musu: Lalle ni dai ina ganin wadansu fuskoki wadanda idan har suka yi addu’a to kuwa za a iya matsawa da wannan dutsen daga inda ya ke, idan kuwa har suka yi fushi da mu to kuwa babu wani guda daga cikin mu da zai saura a bayan kasa. A saboda haka kada ku kuskura ku yi mubahala da su.
Daga wannan ayar za mu iya daukan darussa kamar haka:
1- Wajibi ne a amsa tambayoyin da aka gabatar da amsar da take cike da karfaffiyar hujja, to amma taurin kai da rashin karbar gaskiya ba shi da wani sakamakon da ya wuce halaka da kuma la’ana ta Ubangiji. 2- Matukar dai mun yi imani da addinin Ubangiji, to mu tsaya kyam a kansa da kuma yarda da cewa babu wani abin da makiya za su iya yi mana. 3- Ahlulbaitin Ma’aiki (s.a.w.a.) suna da wani matsayi mai girma a wajen Allah da nan take Allah ya ke karbar addu’oinsu, sannan kuma Manzon Allah (s.a.w.a.) ya bayyanar da Hasan da Husaini (a.s) a matsayin ‘ya’yansa sannan Imam Ali bn Abi Talib (a.s) kuma a matsayin kansa. 4- Annabawan Allah suna neman taimakon Ubangiji ne bayan sun sauke nauyi na aikin da ke wuyansu kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi a wannan yanayi inda sai da ya isar da sako da ayyuka na zahiri da ya kamata ya yi kafin ya nemi daukin Ubangiji a kan wadannan kiristoci.
Yanzu kuma bari mu saurari ayoyi na 62 da 63 na cikin Suratu Al Imranan:
إِنَّ هَـذَا لَهُوَ الْقَصَصُ الْحَقُّ وَمَا مِنْ إِلَـهٍ إِلاَّ اللّهُ وَإِنَّ اللّهَ لَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ{62} فَإِن تَوَلَّوْاْ فَإِنَّ اللّهَ عَلِيمٌ بِالْمُفْسِدِينَ{63}
“Lalle ne wannan, hakika, shi ne labari tabbatacce, kuma babu wani abin bautawa face Allah, kuma lalle ne, Allah, hakika, Shi ne Mabuwayi Mai hikima”.
A ci gaba da magana kan wannan lamari na mubahala, Allah Madaukakin Sarki yana gaya wa manzonsa cewa: Abin da muka saukar maka dangane da lamarin Annabi Isa al-Masihu, shi ne hakikanin labarin rayuwarsa wanda idan ba Allah ba babu wani da ya ke da cikakken labarin hakan. Abin da wasu mutane suke fadi dangane da Annabi Isa na cewa shi dan Allah ne ko kuma ma Allah din ne ba wani abu ba ne face karya, don kuwa Mahalicci dai guda ne sannan kuma babu wani abin bautawa in ba shi ba. A saboda haka mutanen da suka yi tawaye wa gaskiya su san cewa Allah yana sane da abubuwan da suke aikatawa, sannan kuma zai hukumta su.
A hakikanin gaskiya labaran da suke yawo a tsakanin mutane suna karkashin yanayi biyu ne, ko dai kagaggun labarai ne wadanda babu gaskiya cikinsu wani tsari ne kawai na marubuta, ko kuma an samo su ne daga tarihin magabatan da suka gabata, sai dai kawai an shigo da wasu karya cikinsu ne.
To amma labarurrukan da suka zo cikin Alkur’ani, da farko dai labarurruka ne na gaskiya ba wai na karya ko zato ba ne. na biyu kuma shi ne cewa gaskiya ne sannan kuma suna bayanin abin da ya ke gaskiya ne. A saboda haka babu wani ragi ko kari a cikinsu.
Daga wadannan ayoyi za mu iya fahimtar wasu darussa kamar haka:
1- Idan har da ba don Alkur’ani ba, da hakikanin labarin Annabi Isa da sauran annabawa da dama da al’ummun da suka gabata sun buya mana. 2- Kin yarda da gaskiya da kuma taurin kai daya ne daga cikin alamu na lalata da bata wanda ya ke jan al’umma zuwa ga bata da kauce wa hanya. 3- Idan har muka dauka cewa dukkanin ayyukan da muke aikatawa suna karkashin sanya idanuwan Ubangiji ne, to kuwa za mu yi taka tsantsan sosai cikin ayyukan da muke aikatawa.
Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 64 ta cikin Suratu Al Imranan:
قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ تَعَالَوْاْ إِلَى كَلَمَةٍ سَوَاء بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمْ أَلاَّ نَعْبُدَ إِلاَّ اللّهَ وَلاَ نُشْرِكَ بِهِ شَيْئاً وَلاَ يَتَّخِذَ بَعْضُنَا بَعْضاً أَرْبَاباً مِّن دُونِ اللّهِ فَإِن تَوَلَّوْاْ فَقُولُواْ اشْهَدُواْ بِأَنَّا مُسْلِمُونَ{64}
“Ka ce: Ya ku Mutanen Littafi! Ku tafo zuwa ga kalma mai daidaitawa a tsakaninmu da ku; kada mu bauta wa kowa face Allah. Kuma kada mu hada kome da shi, kuma kada sashenmu ya riko sashe Ubangiji, baicin Allah.” To, idan sun juya baya sai ku ce: Ku yi shaida cewa lalle ne mu masu sallamawa ne”.
A cikin ayoyin da suka gabata, da farko dai Alkur’ani mai girma ya kirayi kiristoci ne zuwa ga karbar addinin Musulunci bisa asasi na hujjoji da hankali, to amma da ya ke sun ki amincewa sai ya kiraye su zuwa ga mubahala, to a nan ma dai bas u yarda su yi hakan ba. Don haka a cikin wannan ayar sai Allah Madaukakin Sarki ya gaya wa manzonsa cewa: ka gaya musu cewa matukar dai ba a shirye suke su karbi Musulunci ba, to alal akalla su amince da tafiya da haduwa kan akidoji da tunanin da suka yi tarayya kansu sannan kuma su tsaya kyam wajen tinkarar shirka da kafirci.
A matsayin misali akwai wadansu daga cikin masanan kiristocin da suka sauya halal da haramun din Ubangiji alhali kuwa hakan wani hakki ne na Ubangiji. A saboda haka ne Alkur’ani yake cewa: ku zo mu yi watsi da wadannan mutane kada mu yi musu biyayya don kuwa su kansu suna ganin kansu ne a matsayin kishiyoyin Ubangiji wajen kafa dokoki. Daga karshe ayar tana magana da musulmi tana gaya musu cewa: Idan har kun kirayi ma’aboya littafi zuwa ga hadin kai da aiki tare amma suka ki amincewa, to kada ku yi sako-sako da tafarkin da kuke kai, ku fito fili ku fadi cewa mu dai Allah shi kadai za mu mika wa kai, sannan kuma ku din nan da abubuwan da kuke bauta wa ba za ku yi wani tasiri a kan mu ba.
Daga wannan ayar za mu iya fahimtar wasu darussa kamar haka:
1- Alkur’ani mai girma ya kiraye mu zuwa ga hadin kai da Ahlul kitabi bisa abubuwan da muka yi tarayya da su a kansu. A saboda haka gabatar da duk wani abin da ake da sabani kansa a tsakanin musulmi wani lamari ne abin ki sannan kuma wanda ya saba wa koyarwar Alkur’abi da kuma Musulunci. 2- Dukkanin mutane daidai suke, babu wani da ya ke da iko a kan dan’uwansa, in ba bisa umurnin Ubangiji ba. 3- Ya kamata musulmi su ba da himma wajen kiran Ahlul Kitabi zuwa ga Musulunci, idan ma har ba su cimma dukkanin manufofin da suke son cimmawa ba, to su yi kokari wajen cimma wasu daga cikinsu.
Da haka ne muka kawo karshen shirin na mu na yau sai kuma a shiri na gaba inda za mu dora daga inda muka tsara. Kafin nan nake cewa ku zama lafiya.
Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 65-71 (Kashi Na 86)
Da sunan Allah mai Rahama Mai Jin Kai. Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku acikin wannan shirin. A wannan ranar ma dai muna tare da ku ne acikin wannan shirin kaso na 74 da mu ke gabatar musu da tafsirin ayoyin kur’ani mai girma. Da fatan za ku kasance tare da mu domin jin yadda shirin zai kasance.
Yanzu za mu karanta ayoyi na 65 da kuma na 66 a cikin suratu Ali-Imran.:
يَا أَهْلَ الْكِتَابِ لِمَ تُحَآجُّونَ فِي إِبْرَاهِيمَ وَمَا أُنزِلَتِ التَّورَاةُ وَالإنجِيلُ إِلاَّ مِن بَعْدِهِ أَفَلاَ تَعْقِلُونَ{65} هَاأَنتُمْ هَؤُلاء حَاجَجْتُمْ فِيمَا لَكُم بِهِ عِلمٌ فَلِمَ تُحَآجُّونَ فِيمَا لَيْسَ لَكُم بِهِ عِلْمٌ وَاللّهُ يَعْلَمُ وَأَنتُمْ لاَ تَعْلَمُونَ{66}
“Ya ku ma’abota littafi me ya sa ku ke yin jayayya akan Ibrahim, alhali ba a saukar da attaura da linjila sai bayansa ba, shin ba za ku hankalta ba. Ga ku nan ku wadannan mutanen kun yi husuma acikin abinda ku ke da sani da shi, to don me ku ke jayayya akan abinda ba ku da sani das hi. Allah yana da masaniya ku kuwa ba ku da masaniya.”
A kodayaushe a tsawon tarihi da akwai jayayya akan kowanene mai gaskiya a tsakanin mabiya annabawa, kowane yana baiwa kansa gaskiya, tare da cewa dukkanin annabawa sun zo ne daga Ubangiji daya, kuma littatafan da su ka zo da su basu cin karo da juna. Sai dai abin takaici ne cewa bangaranci na ido rufe shi ne abinda ya sa, wasu ma’abota addini su ke bude yaki da waninsu ba tare da sun kiraye su zuwa ga gaskiya ba bisa kwararan dalilai. Har zuwa lokacin annabi Isa (a.s) mabiya annabi Musa (a.s) suna da wajabcin biyayya gare shi, sai dai saboda bangaranci na ido rufe ba su zama cikin shiri na yin biyayya a gare shi ba. Sun kuma rika daukar kansu a matsayin annabi Ibrahim alhali ya zo ne kafin annabi Musa (a.s)! Saboda wannan bashi da wani tushe ta fuskar tarihi, Allah madaukakin sarki ya ke yin Magana da nasara da yahudawa da cewa: Ku ne tushen wannan sabanin na addini da bangaranci na ido rufe domin kuna yin jayayya ne akan annabi Isa wanda kun ga haihuwarsa da kuma rayuwarsa, amma kuma kun koma kuna yin jayayya akan annabi Ibrahim wanda ba ku da wata masaniya akan addininsa, kuna bayyana cewa ku mabiyansa ne. Idan kun kasa cimma matsaya akan abinda ku ke da masaniya akansa me kuma zai kai ku yin jayayya akan abinda ba ku da masaniya akansa. Abinda za mu koya daga wadannan ayoyin. 1-Wajibi gaskiyar addini ta ginu bisa kwararan dalilai, ba saboda jinginuwa da wani mutum ko kuma tarihin wani addini ba. 2-Tattaunawa da yin nazari suna da kima domin kaiwa ga gaskiya, idan kuma ba za ta kai ga haddasa sabani da jayayya ba.
Yanzu kuma sai ayoyi na 67 da a 68 a cikin suratu Ali-Imran.
مَا كَانَ إِبْرَاهِيمُ يَهُودِيّاً وَلاَ نَصْرَانِيّاً وَلَكِن كَانَ حَنِيفاً مُّسْلِماً وَمَا كَانَ مِنَ الْمُشْرِكِينَ{67} إِنَّ أَوْلَى النَّاسِ بِإِبْرَاهِيمَ لَلَّذِينَ اتَّبَعُوهُ وَهَـذَا النَّبِيُّ وَالَّذِينَ آمَنُواْ وَاللّهُ وَلِيُّ الْمُؤْمِنِينَ{68}
“Ibrahim bai kasance bayahude ba kuma ba banasare ba ne, sai dais hi ya kasance ne akan addini mikakke mai mika kai, baki kuma kasance a cikin mushrikai ba. Mafi cancantar mutane da annabi Ibrahim su ne wadanda su ka bi shi da kuma wannan annabin da wadanda su ka yi imani a tare da shi. Allah shi ne majibincin lamarin muminai.”
A ci gaban ayar da ta gabata, wannan ayar tana bayyana annabi Ibrahim a matsayin mutum mai neman gaskiya da kuma mika kai gare ta. Tushen sabaninku shi ne son kai da ku ke da shi wanda kuma shi ne darajar koli ta shirka. Idan kuma son ta hanyar danganta kawunanku da annabi Ibrahim ne za ku jawo wa kanku farin jini, to ku sani cewa ba ta hanyar dadin baki ne ake zama mai addini ba. Wanda ya fi kusanci da annabi Ibrahim shi ne wanda ya ke yin biyayya a gare shi a aiki. Ya tabbatar da cewa shi mai binsa ne a aikace kamar yadda annabin musulunci da sahabbansa su ka kasance, kuma suna bayyana kansu a matsayin masu bin addinin Ibrahim ba cewa su ke yi annabi Ibrahim ne mai biyayya a gare su. Abubuwand a za mu koya daga wadannan ayoyin. 1-Alaka ta tunani da addini ita ce sama da alaka ta jini da dangantaka.Mutanen da su ka yi tarayya ta fuskar tunani da akida su ne mafi kusanci da juna. 2-Ba dole ne mabiya wata akida su zama daga kabila guda ba, muhimmin abu shi ne biyayya ga akida da yin imani da ita. Ba harshe ne ko kabila ba, kamar yadda annabin musulunci ya ke fadawa Salman Farisi cewa: Salmanu namu ne” alhali ta fsukar kabila shi ba balara be ba ne.
Yanzu kuma sai ayoyi na 69 da 71 na suratu Ali-Imran.
وَدَّت طَّآئِفَةٌ مِّنْ أَهْلِ الْكِتَابِ لَوْ يُضِلُّونَكُمْ وَمَا يُضِلُّونَ إِلاَّ أَنفُسَهُمْ وَمَا يَشْعُرُونَ{69} يَا أَهْلَ الْكِتَابِ لِمَ تَكْفُرُونَ بِآيَاتِ اللّهِ وَأَنتُمْ تَشْهَدُونَ{70} يَا أَهْلَ الْكِتَابِ لِمَ تَلْبِسُونَ الْحَقَّ بِالْبَاطِلِ وَتَكْتُمُونَ الْحَقَّ وَأَنتُمْ تَعْلَمُونَ{71}
“Wadansu mutane na ma’abota littafi sun guraci batar da ku, ba sa batar da kowa sai kawunansu ba tare da hasashensu ba.” “Ya ku ma’abota littafi don me ku ke kafirta da ayoyin Allah, alhali ku, shaidu ne.” “Ya ku ma’abota littafi don me ku ke cudanya karya da gaskiya, kuma ku ke boye gskiya alhali kuna sane.”
Wadannan ayoyin sun fito da abinda ya ke a boye dangane da makiya addini da hanyar gaskiya ta fadin cewa: Wani sashe na masu daukar kansu a matsayin masu bautar Allah kuma ma’abota littafi, suna fatan ganin cewa ku musulmi kun zama batattu daidai da su, tare da cewa suna sane da alamun da su ka zo a cikin Attaura da Linjila dangane da annabin musulunci, da kuma cewa wajibi ne a yi imani da shi, sai dai duk da haka jahilci da kuma bangaranci sun ingiza su zuwa boye gaskiyar da su ke da masaniya akanta. Ko kuma su riga bayyanata ta hanyar bata. A dailin haka wadannan ayoyin suna a matsayin gargadi ne ga musulmi akan yadda alakarsu ta ke da mabiya wasu addinai, kada ya zamana sun fisgu zuwa gare su. Su kuma zama cikin sani da fahimtar tanadi da shirin da su ke da shi na batar da musulmi. Abubuwan da za mu koya daga wadannan ayoyin. 1-Sanin makiya da fahimtar makirce-makircen da su ke kitsawa, wajibi ne domin a samu a tsira daga sharrinsu. Dole ne a kasance a cikin lura kada a bada dama ta yadda samarin musulmi za su karkata gare su. 2-Wanda duk ya ke son karkatar da wasu to a matsayin farko yana karkatar da kansa ne, domin kuwa babu wani abu da batacce ya ke da shi da ya wuce munafinci da kiyayya. 3-wajibi ne ga mumini ya kasance mai neman sanin yadda zai tantance gaskiya daga bata a kodayaushe, saboda kada makiya su sami dammar hargitsa masa lamurra su kuma cimma manufarsu. A karshen wannan shirin muna rokon Allah madaukakin sarki da ya nesantamu daga girman kai dab akin kishi na bangaranci da kabilanci. Ya kuma cusa masa kyawawan halaye na neman gaskiya. Sai kuma wani shirin.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 72-76 (Kashi Na 87)
Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku acikin kaso na 75 na wannan shirin da mu ke kawo muku fassarar ayoyin kur’ani mai girma. Da fatan za a kasance a tare da mu domin a ji ci gaban shirin.
Yanzu zamu karanta aya ta 72 a cikin suratu Ali-Imran.
وَقَالَت طَّآئِفَةٌ مِّنْ أَهْلِ الْكِتَابِ آمِنُواْ بِالَّذِيَ أُنزِلَ عَلَى الَّذِينَ آمَنُواْ وَجْهَ النَّهَارِ وَاكْفُرُواْ آخِرَهُ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ
“Wadansu mutane daga ma’abota littafi su ka ce ku bada gaskiya ga abinda aka saukar ga wadanda su ka bada gaskiya, farkon rana, ku kafirce da shi karshenta, watakila sa komo ga barin addini.”
A shirin da ya gabata mun bayyana cewa kafirai suna da tanadi mai yawa akan yadda za su raunan imanin musulmi, wanda daya daga cikinsu shi ne cakuda gaskiya da karya. To wannan ayar tana yin Magana ne akan wani salon na makircin makiya: jagororin kafirci suna bada umarni ga wasu mabiyansu da su bayyana cewa sun yi imani da kur’ani da annabin musulunci, su kuma kutsa su shiga cikin musulmi, amma bayan wani lokaci kadan sai su ce sun fice daga musulunci, su fadawa musulmi cewa mun yi kuskure domin kuwa addininmu ya fi addininku, saboda haka za mu koma addininmu na baya. A fili ya ke cewa wannan irin yaudarar za ta yi tasiri ga wasu, ya kuma jefa wasu cikin shakku akan addininsu na musulunci. Haka nan kuma zai yi tasiri wajen hana wasu kafiran shiga musulunci. Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-Bai kamata ace musulmi suna da saukin kai ba wajen fahimtar abinda ke faruwa, ya zama suna gaskata duk abinda su ka gani cikin sauki. Wajibi ne su zama masu fadaka da lura saboda kada su fada cikin tarkon munafikai da kafirai. 2-Fatan makiya bai tsaya a cikin son ganin sun kafirtar da musulmi ba, suna da tsari da tanadi saboda haka wajibi ne ga musulmi su kasance cikin shiri da tanadi domin kalubalantar yakin al’adu daga makiya.
Yanzu kuma za mu karanta ayoyi na 73 da 74 a cikin suratu Ali Imrana.
وَلاَ تُؤْمِنُواْ إِلاَّ لِمَن تَبِعَ دِينَكُمْ قُلْ إِنَّ الْهُدَى هُدَى اللّهِ أَن يُؤْتَى أَحَدٌ مِّثْلَ مَا أُوتِيتُمْ أَوْ يُحَآجُّوكُمْ عِندَ رَبِّكُمْ قُلْ إِنَّ الْفَضْلَ بِيَدِ اللّهِ يُؤْتِيهِ مَن يَشَاءُ وَاللّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ{73} يَخْتَصُّ بِرَحْمَتِهِ مَن يَشَاءُ وَاللّهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيمِ{74}
“Kada ku gaskata wani sai wanda ya bi addininku, kace shiriya ta Allah ce, akan bada kwatankwacin abinda aka baku, kuma ya kafa muku hujja a wurin Ubangijinku. Ka ce falala tana hannun Allah yana bada ita ga wanda ya so. Allah mai yalwar falala ne kuma masani. Yana kebantar wanda ya ga dama da falalarsa. Allah ma’abocin falala ne mai girma.”
A cikin ayoyin da su ka gabata mun fahimci cewa jagororin yahudawa suna da shiri da tanadi na raunana imanin musulmi. Shi ne cewa su nuna cewa sun yi imani da annabin musulunci sannan sai su kafirce. To wannan ayar tana ci gaba da yin bayani ne akan makircinsu, suna fadawa junansu cewa wannan shirin namu dole ne ya kasance cikin sirri. Kada mu yi imani da wani idan ba mu kanmu hatta mushrikai. Sai dai acikin wannan ayar Allah ya tona musu asiri, ya bada umarni ga manzonsa da ya fada musu cewa: Shiriya daga Allah kadai take, ba ta da alaka da wata kabila ta musamman. Kuma wannan makircin naku ba zai yi tasiri akan wadanda Allah ya shiryar da su ba saboda haka kada ma ku bata lokacinku. Ayar ta ci gaba da yin bayani akan abinda manyan yahudawa su ke fada suna cewa: Kada ku yi tsammanin cewa wani mutum zai iya samun matsayi irin wanda ku ke da shi acikin saukakken littafi sannan kuma ya iya yin galaba akanku a ranar kiyama ta hanyar kafa hujjoji a gaban Ubangiji. Kune mafifitan mutane a duniya annabta da hankali suna a wurinku ne. Ubangiji ya maida martani akan wannan zance mara tushe da cewa: Dukkanin abubuwan da su ke jawo ni’imomi, matsayin annabci da kuma karfin kafa dalili, daga Allah su ke baki daya, yana kuma bada su ne ga wanda ya dace. Kuma falala da baiwarsa suna da yalwa. Abubuwan da za mu koya daga cikin wadannan ayoyi. 1-Falalar Allah ba ta takaita ga wata al’umma guda daya ba, yana bada ita ga wanda ya so bisa cancanta. 2-jagororin ma’abota littafi suna shiri da tanadi, na hana mabiyansu shiga musulunci.
Yanzu kuma sai ayoyi na 75 da 76 na suratu Ali-imran.
وَمِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ مَنْ إِن تَأْمَنْهُ بِقِنطَارٍ يُؤَدِّهِ إِلَيْكَ وَمِنْهُم مَّنْ إِن تَأْمَنْهُ بِدِينَارٍ لاَّ يُؤَدِّهِ إِلَيْكَ إِلاَّ مَا دُمْتَ عَلَيْهِ قَآئِماً ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ قَالُواْ لَيْسَ عَلَيْنَا فِي الأُمِّيِّينَ سَبِيلٌ وَيَقُولُونَ عَلَى اللّهِ الْكَذِبَ وَهُمْ يَعْلَمُونَ{75} بَلَى مَنْ أَوْفَى بِعَهْدِهِ وَاتَّقَى فَإِنَّ اللّهَ يُحِبُّ الْمُتَّقِينَ{76}
“Daga cikin ma’abota littafi da akwai wanda idan ka amince masa da dukiya mai dimbin yawa, zai bada shi shi ya zuwa gare ka, akwai daga cikinsu wanda idan ka amince masa da zinari daya ba zai bada shi ba gare ka, sai muddin kana kansa a tsaye. Wadancanenka saboda suna cewa ukuba ba ta kasancewa akanmu acikin wadanda ba ma’abota littafi ba. Suna girba karya akan Ubangiji, cikin saninsu.” “Na’am wanda ya cika alkawalinsa, ya kuma ji tsoron Ubangiji, to Allah yana son masu takawa.”
Wannan ayar, tamkar sauran ayoyin da su ka gabata tana koyawa musulmi yin adalci ne a wajen hulda da masu sabani da su. Tana fadin cewa: A tsakanin ma’abota littafi da akwai mutanen kirki amintattu wadanda duk girman amanar da ka basu ajiya za su dawo maka da ita kamar yadda ta ke. Sai dai bangarancin da wani sashe nasu ya ke da shi, ya sa suna jin cewa dukiyar duk wanda ba bayahude ba halaliya ce a gare su su ci. Abin mamaki shi ne cewa sun baiwa wannan mahangar mara tushe siffar addini. Suna fadin cewa Allah ne ya halarta musu su kwaci dukiyar duk wanda ba bayahude ba. Kur’ani ya ci gaba da yin bayanin cewa: Bai kamata musulmi su yi kasa aguiwa wajen karbar hakkinsu ba da aka kwace, su kwaci hakkinsu da karfi. A wannan lokacin ma da yahudawa su ka kafa Isra’ila akan kasar Palasdinu da su ka kwace, basu girmama dokokin bil’adama ko dokokin duniya. Kuma a kowace rana ta Allah suna kokarin kwace wata kasar ne ta musulmi, saboda haka wajibi ne ga musulmi da su kwaci hakkinsu. Abubuwan da za mu koya daga wadannan ayoyin. 1-Wajibi a yi adalci hatta akan makiyi, kada mu dauke su cewa baki dayansu maha’inta ne kuma gurbatattu. 2-Rikon amana abin kwarai ne kowanene mai yinsa, koda kuwa makiyi ne. Cin amana mummunan aiki ne koda kuwa koda daga makiyi ne. 3-Abin ya fi sabo muni shi ne halarta aikata sabon. Yahudawa suna cin dukiyar mutane ba bisa hakki ba sannan kuma su ke halarta wannan mummunan aikin nasu da kuma danganta shi ga Ubangiji. 4-Rikon amana da girmama yarjejeniya da daidaikun mutane ko kuma al’umma yana daga cikin alamar tsoron Allah, wanda ya ke jawo wa mutum kauna a wurin Ubangiji. Muna kare wannan shirin da yin roko ga Allah akan ya cusa mana ruhin yin adalci da rikon amana, saboda mu zama masu yin adalci akan kowane mutum. Sai kuma mun sake haduwa acikin wani shirin.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 77-82 (Kashi Na 88)
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai. Masu sauraro muna yi muku maraba da sake saduwa da ku acikin wannan shirin na hannunka mai sanda. Muna kuma tare da ku ne a cikin karo na 76 na wannan shirin da mu ke kawo muku. Sai kuma mu kasha kunnuwa domin ci gaba da sauraron ayoyin da mu ke karantowa daga cikin suratu Ali-imrana tare da fassara.
Yanzu za mu karanto aya ta 77 a cikin suratu Ali-imrana.
إِنَّ الَّذِينَ يَشْتَرُونَ بِعَهْدِ اللّهِ وَأَيْمَانِهِمْ ثَمَناً قَلِيلاً أُوْلَـئِكَ لاَ خَلاَقَ لَهُمْ فِي الآخِرَةِ وَلاَ يُكَلِّمُهُمُ اللّهُ وَلاَ يَنظُرُ إِلَيْهِمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَلاَ يُزَكِّيهِمْ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
“Hakika wadanda su ke musanyo dan tamani kankani mai makon alkawalin Allah, da rantse-rantsensu, wadancanenka babu rabo a gare su a lahira, Allah ba zai yi Magana da su ba, ba kuma zai dube su (da rahama ba) a ranar kiyama ba kuma zai tsarkake su ba. A zaba mai radadi ta tabbata a gare su.”
Ubangiji madaukaki ya shiryar da mutum zuwa ga sa’ada ta hanyoyi guda biyu. Na farko shi ne fitra, wacce ta ke nufin lamirin da ya ke tattare da mutum ya ke kuma kokarin sanar da shi ayyukan kwarai, na biyu kuwa shi ne wahayi, wanda tushensa shi ne ilimin Allah mara iyaka, ya isowa mutane a cikin addini, ya ke kuma yi wa mutum jagora zuwa ga kamala. Alkawullan Allah sun a kunshe cikin lamiri da kuma addini, kuma hankalin mutum ya sanya hannu akansu ya amince da su, saboda haka mutum ya zama mai dauke da nauyin aiwatar da su. Sai dai abin takaici ne cewa wani gungu na mutane sun take wannan alkawalin, kuma saboda su kai ga cimma manufofinsu na duniya sun fifita sha’awace-sha’awacen zuciyarsu akan komai. A fili ya ke cewa wannan irin hali yana da sakamakon da mai shi zai gani, wanda shi ne haramta masa shiga karkashin jin kan Allah a ranar kiyama, wanda a wannan lokacin dukkanin halittu su ke da bukatuwa da jin kai daga mahaliccinsu. Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-Karya alkawali da kuma karya rantsuwa yana iya kai mutum ga fita daga addini da kuma jefa shi cikin wutar jahannama. 2-Rikon amana yana daga cikin alkawalin Allah kamar yadda ya zo a cikin ayoyin baya akan rikon amana ta mutane. Wannan ayar kuwa tana Magana ne akan alkawalin Allah wanda ya zama wajibi a cika shi.
Yanzu kuma sai aya ta 78 a cikin suratu Ali-imran.
وَإِنَّ مِنْهُمْ لَفَرِيقاً يَلْوُونَ أَلْسِنَتَهُم بِالْكِتَابِ لِتَحْسَبُوهُ مِنَ الْكِتَابِ وَمَا هُوَ مِنَ الْكِتَابِ وَيَقُولُونَ هُوَ مِنْ عِندِ اللّهِ وَمَا هُوَ مِنْ عِندِ اللّهِ وَيَقُولُونَ عَلَى اللّهِ الْكَذِبَ وَهُمْ يَعْلَمُونَ
“Daga cikinsu da akwai jama’a da su ke karkatar da harshensu da karatun littafi domin ku zaci cewa daga littafi ne( wanda Allah ya saukar.) alhali shi baya daga cikin littafi. Suna fadin cewa shi daga Allah ya ke alhali ba daga Allah ya ke ba. Suna girba karya ga Allah alhali suna cikin sani.”
Kamar yadda mu ka fada a cikin shirin baya cewa daya daga cikin dalilan da su ke karkatar da mutane da batar da su shi ne malaman addini wadanda ba a shirye su ke su fadawa mutane gaskiya ba, kodai saboda kare matsayin da su ke da shi a tsakanin al’umma ko kuma saboda ci gaba da rike shugabancinsu na addini ko kuma saboda hassada. Kuma baya ga boye gaskiya da su ke yi suna karkatar da abinda ya ke gaskiya da maida shi karya, su kuma rika bayyana ra’ayinsu a matsayin cewa addini ne. Alkur’ani ya yi wa musulmi bayani akan hatsarin mutane irin wadannan, saboda kada su fada cikin tarkon kamanninsu na zahiri da kuma dadin bakinsu. Su kuma san cewa mutane irin wadannan su ne wadanda su ke fakewa da addini suna dibga karya mafi grima ga Allah. Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-Ba kowane zance ne za mu kashe kunnuwa mu saurare shi ba komai dadinsa, domin kuwa da akwai wani zancen na mutane wanda saboda dadinsa sai kace kur’ani amma a hakikanin gaskiya yana fada ne da kur’ani. 2-Kada mu gafala daga hatsarin makiya wadanda ba su tsoron Allah, su ne wadanda su ke batar da mutane cikin ganganci, su ke kuma yi wa Allah karya, su ke bayyana maganganunsu a matsayin na Ubangiji.
Yanzu kuma sai aya ta 79-80 a cikin suratu Ali-imrana.
مَا كَانَ لِبَشَرٍ أَن يُؤْتِيَهُ اللّهُ الْكِتَابَ وَالْحُكْمَ وَالنُّبُوَّةَ ثُمَّ يَقُولَ لِلنَّاسِ كُونُواْ عِبَاداً لِّي مِن دُونِ اللّهِ وَلَـكِن كُونُواْ رَبَّانِيِّينَ بِمَا كُنتُمْ تُعَلِّمُونَ الْكِتَابَ وَبِمَا كُنتُمْ تَدْرُسُونَ{79} وَلاَ يَأْمُرَكُمْ أَن تَتَّخِذُواْ الْمَلاَئِكَةَ وَالنِّبِيِّيْنَ أَرْبَاباً أَيَأْمُرُكُم بِالْكُفْرِ بَعْدَ إِذْ أَنتُم مُّسْلِمُونَ{80}
“Ba zai yiyu ba ga bil’adama, Allah ya ba shi littafi da hikima da annabci sannan ya fadawa mutane cewa: Ku zama bayina ba Allah ba, sai dai zai ce: Ku zama na Allah masu takawa saboda iliminku da littafi da kuma abinda ku ke karantawa.” “Ba zai umarce ku ba ku riki mala’iku da annabawa a matsayin iyayengiji. Shin zai umarce ku da kafirci bayan ku musulmi ne?”
A ci gaba da bayani akan hatsarin da ya ke tattare malaman addini masu karkataccen tunani, wadannan ayoyin guda biyu tana yin Magana da su tana cewa: Hatta annabawa wadanda Allah ne ya aiko su, ba su da hakkin su kirayi mutane da yin biyayya gare su, wajibi ne a gare su su kirayi mutane zuwa ga bin Allah da yi masa bauta, saboda haka me zai su ku da ku ke mabiya annabawa da aikinku shi ne koyar da littafi, za ku rika kiran mutane zuwa ga yi mu ku biyayya? Abinda ake tsammani daga gare ku malamai wadanda su ke da masaniya akan littafin Allah kuma a kodayaushe ku ke koyar da shi, shi ne ku zama masu biyayya ga hukunce-hukuncen Allah fiye da kowa, ku zama malamai na Allah. Bugu da kari, karbar wani mutum a matsayin Ubangiji da kuma tsoma baki acikin harkar dokoki ko kuma kokarin sauya su, to yana nufin kafirci. Babu kuma wanda ya ke da wannan hakkin koda kuwa annabawa ne ko mala’iku, saboda haka a wanene dalili ne ku malaman addini ma’abota littafi ku ke baiwa kanku hakkin Ubagijintaka, ku ke baiwa kanku hakkin yin doka da danganta ta ga addini, ku ke kuma sauya dokokin addini? Abinda za mu koya daga wannan aya. 1-Yin amfani da matsayi da mukami domin kare manufa ta kashin kai, abu ne da aka haramta, hatta annabawa ba su da hakkin yin amfani da matsayarsu domin daukaka kawunansu. 2-Malamai na Allah ne kadai su ke da hakkin fassara kur’ani, kuma hanyar zama malamai na shi ne ita ce dauke kewa da kur’ani da kuma koyansa da koyar da shi. 3-An hana wuce gona da iri wajen daukaka matsayin annabawa da waliyan Allah, so bayin Allah ne sun kuma samu matsayi da daukakar da su ke da su ne ta hanyar bautar Allah, amma su ba iyayengiji ba ne. 4-Ba karyata samuwar Ubangiji ba ne kadai kafirci, amincewa da cewa mutum yana da hakkin sauya dokoki saboda su ci karo da dokokin Allah, yana nufin inkarin Ubangiji kuma kafirci ne. Yanzu kuma sai aya ta 81-82 acikin suratu Ali-Imrana.
وَإِذْ أَخَذَ اللّهُ مِيثَاقَ النَّبِيِّيْنَ لَمَا آتَيْتُكُم مِّن كِتَابٍ وَحِكْمَةٍ ثُمَّ جَاءكُمْ رَسُولٌ مُّصَدِّقٌ لِّمَا مَعَكُمْ لَتُؤْمِنُنَّ بِهِ وَلَتَنصُرُنَّهُ قَالَ أَأَقْرَرْتُمْ وَأَخَذْتُمْ عَلَى ذَلِكُمْ إِصْرِي قَالُواْ أَقْرَرْنَا قَالَ فَاشْهَدُواْ وَأَنَاْ مَعَكُم مِّنَ الشَّاهِدِينَ{81} فَمَن تَوَلَّى بَعْدَ ذَلِكَ فَأُوْلَـئِكَ هُمُ الْفَاسِقُونَ{82}
“Yayin da Allah ya karbi alkawalin annabawa, a lokacin da na ba ku littafi da hikima sai manzo ya zo mu ku wanda ya ke gaskata abinda ya ke tare da ku , shin za ku yi imani da shi, kuma za ku taimaka masa? Ubangiji ya ce kun yi furuci da wannan? Sai su ka ce mun yi furuci. Sai (ubangiji) ya ce: To ku shaida ni ma ina tare da ku daga cikin masu shaida.” (To wanda duk ya juya bayan wannan alkawalin to wadancanenka su ne fasikai.”
Kamar yadda ya zo acikin tafsirai da riwayoyi, Ubangiji ya karbi alkawali daga annabawan da su ka gabata kamar Musa da isa, da su yi wa mutanensu bushara da zuwan annabin musuluci ta hanyar yin bayani akan siffofinsa na musamman domin su share fagen yi imani da shi idan ya bayyana. Domin kuwa dukkanin annabawa daga Unagiji guda su ka zo kuma littatafan da su ka zo da su suna gaskata juna. Saboda haka wajibi ne akan masu biyayya ga annabawan da su gabata da su sallamawa annabin Musulunci a lokacin bayyanarsa. Abubuwan da za mu koya daga wadannan ayoyin. 1-Banbancin da ya ke tsakanin annabawa wajen isar da sako, kamar banbancin da malamai su ke da shi ne a cikin makaranta wajen koyawa, dukkaninsu manufa guda daya su ke da ita, kuma kowane malami yana kiran dalibansa da sauraron darasin da malami na gaba zai koya masa. 2-Imani kadai baya wadatarwa, wajibi ne a kare addini da taimakonsa da kuma masu biyayya gare shi. 3-Kasantuwar dukkanin annabawa masu gaskata junansu, babu wani dalili da zai sa mabiya annabawan za su zama masu bakin kishi da gaba da juna. A karshen wannan shirin muna rokon Allah da ya kiyaye mu daga murguda da sauya hukunce-hukuncen Allah.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 83-89 (Kashi Na 89)
Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin kaso na 77 wanda mu ke kawo muku fassarar ayoyin kur’ani mai girma.Da fatan za a kasance tare da mu domin jin yadda shirin zai kasance.
Yanzu za mu karanta aya ta 83 da acikin suratu Ali-Imran.
أَفَغَيْرَ دِينِ اللّهِ يَبْغُونَ وَلَهُ أَسْلَمَ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ طَوْعاً وَكَرْهاً وَإِلَيْهِ يُرْجَعُونَ
“Shin wanin addinin Allah su ke so, alhali dukkan abinda ya ke sammai da kasa ya mika wuya gare shi, cikin so ko tilas, kuma zuwa gare shi za ku koma.”
Halittun da Allah ya halitta nau’i biyu ne, masu ‘yancin zabin hanyar da za su bi, kamar mutum da muka wadanda bisa dabi’ar halittarsu basu da zabi, sai dai hankali ba tare da sha’awace-sha’awacen zuciya ba, kamar mala’iku. Wannan ayar tana cewa dukkanin halittu sun mika wuya ga dokokin Allah a cikin tsarin halitta- wadanda su ke zabi ne ko wadanda ba su da zabi, to me ya sa ko ke komawa zuwa ga mutane domin su yi mu ku dokoki, ku gafala daga dokokin Allah? Shin wani mutum wanda ba mahalicci ba yana da hakkin yi wa mutum doka? Shin ya dace wani mahaluki ya yi watsi da addinin mahalicci ya yi riko da waninsa? Abinda mu ke koya daga wannan aya. 1-Duniya da dukkanin girman da ta ke da shi ta mika kai ga Ubangiji, saboda haka idan ba mu mika wuya ba za mu zama saniyar ware a cikin tsarin halitta. 2-Kawo karshen duniya da kuma mu kanmu a hannun Ubangiji ya ke, me zai hana mu mika kai gare shi cikin zabinmu? 3-Hakikanin addini shi ne mika kai ga Ubangiji, mumini bashi da wata manufa ta kashin kanshi da ta ke cikin karo da abinda Allah ya ke so.
Yanzu kuma za mu karanta ayoyi na 84 da 85 a cikin suratu Ali-imran.
قُلْ آمَنَّا بِاللّهِ وَمَا أُنزِلَ عَلَيْنَا وَمَا أُنزِلَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَإِسْمَاعِيلَ وَإِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ وَالأَسْبَاطِ وَمَا أُوتِيَ مُوسَى وَعِيسَى وَالنَّبِيُّونَ مِن رَّبِّهِمْ لاَ نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِّنْهُمْ وَنَحْنُ لَهُ مُسْلِمُونَ{84} وَمَن يَبْتَغِ غَيْرَ الإِسْلاَمِ دِيناً فَلَن يُقْبَلَ مِنْهُ وَهُوَ فِي الآخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ{85}
“Ku ce mun yi imani da Allah da abinda aka saukar a gare mu da abinda aka saukar ga Ibrahim da Isma’ila da Ishaka da ya’akub da ‘ya’yansa annabawa da abinda aka baiwa musa da Isa da annabawa, daga Ubangijinsu. Ba mu sanya banbanci a tsakanin daya daga cikinsu, mu masu mika wuya ne a gare shi.” “Wanda duk ya nemi wani addini ba musulunci ba to har abada ba za a karba daga gare shi ba, kuma a lahira shi yana daga cikin tababbu.”
A cikin wannan ayar Allah yana yin kira ne ga annabin musulunci da kuma muminai da su shelanta bada gaskiyarsu ga annabawan da su ka gabata da kuma littatafan da Allah ya saukar a gare su. Haka nan kuma su jaddada mika wuyansu ga dokokin Allah, domin kuwa dukkaninsu suna yin kira ne zuwa ga samarwa mutum sa’ada. Abu ne da ya ke afili cewa duk wani manzo da ya zo yana dora koyarwarsa ne akan ta sauran annabawan da su ka gabace shi. Mabiya annabawan da su ka gabaci annabin musulunci, wajibi ne akansu da su yi biyayya ga annabi Muhammad (s.a.w) a lokacin da ya bayyana, wanda duk ya tsaya akan koyarwar annabin da ya gabata to aikinsa ba karbabbe ba ne. Abubuwan da za mu koya daga wadannan ayoyin. 1-Dukkanin annabawa manufa guda su ke da ita duk da cewa salon koyarwarsu ya banbanta saboda banbancin zamanin da su ka rayu a cikinsa. 2-Rashin yin biyayya ga addinin musulunci bayan bayyanarsa, yana a matsayin yin asara. 3-Karbar musulunci da gaskata shi baya nufin kore gaskiyar addinan da annabawan baya su ka zo da su, yin imani da su yana a matsayin wani sashe ne na imanin musulmi.
Yanzu kuma za mu saurari ayoyi na 86 da 87 acikin wannan sura.
كَيْفَ يَهْدِي اللّهُ قَوْماً كَفَرُواْ بَعْدَ إِيمَانِهِمْ وَشَهِدُواْ أَنَّ الرَّسُولَ حَقٌّ وَجَاءهُمُ الْبَيِّنَاتُ وَاللّهُ لاَ يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ{86} أُوْلَـئِكَ جَزَآؤُهُمْ أَنَّ عَلَيْهِمْ لَعْنَةَ اللّهِ وَالْمَلآئِكَةِ وَالنَّاسِ أَجْمَعِينَ{87}
“Allah ba zai shiryar da mutanen da su ka kafirta bayan imaninsu ba, bayan shaidawarsu akan cewa manzon Allah gaskiya ne,alhali hujjoji mabayyana sun zo musu. Allah baya shiryar da mutanen da su ke azzalumai. Wadancanenka sakamakonsu shi ne la’anar Allah da ta mala’ikunsa da dukkanin mutane.”
Daya daga cikin hatsarin da ya ke fuskantar muminai shi ne yin ridda. Tarihi yana dauke da labarin mutanen da su ka bada gasiya da Allah da kuma manzonsa kuma sun yi imani da cewa Allah gaskiya ne sun kuma san hakikanin musulunci, amma kuma su ka juya baya su ka karkace sannan su ka kafrita. A fili ya ke cewa da akwai banbanci a tsaknin mutumin da bai san gaskiya ba da kuma wanda ya santa sannan ya kafirce da ita cikin sani. Mutum mai hali na biyu ya haramtawa kansa samun rahamar Ubangiji wacce ta kebanata da muminai. Saboda haka Allah da manzonsa da mala’iku da dukkanin mutane masu son gaskiya suna la’antar wannan irin mutumin. Abubuwan da za mu koya daga wadannan ayoyin. 1-Farkon yin imani bai isa ba, yana bukatar ya ci gaba har zuwa karshen rayuwa, domin kuwa a kodayaushe mutum yana fuskantar hatsarin yin ridda. 2-Mu ne ke da alhakin share fagen da Allah zai shiryar da mu, haka nan a hannunmu ne ikon haramtawa kawunanmu samun rahamarsa ta ke. Ubangiji baya zaluntar kowane mahaluki, mu ne mu ke zaluntar kawunanmu ta hanyar juyawa gaskiya baya. 3-Wajibi ne ga mutane su nuna kubutarsu ga daidaikun mutanen da su ka yi ridda.
Yanzu kuma za mu saurari ayoyi na 88 da 89 na suratu Ali-Imran.
خَالِدِينَ فِيهَا لاَ يُخَفَّفُ عَنْهُمُ الْعَذَابُ وَلاَ هُمْ يُنظَرُونَ{88} إِلاَّ الَّذِينَ تَابُواْ مِن بَعْدِ ذَلِكَ وَأَصْلَحُواْ فَإِنَّ الله غَفُورٌ رَّحِيمٌ{89}
“ Madawwama ne a cikinta( la’ana) ba kuma za a saukake musu azaba ba ba kuma za a saurara musu ba.” “Sai wadanda su ka tuba bayan haka sannan su ka kyautata, to Allah mai gafara ne kuma mai rahama.”
Akodayaushe su suna cikin la’anta, kuma azaba ba za ta yi sauki a gare su ba kuma ba za a yi musu rangwame ba. Sai dai wadanda bayan riddarsu su ka tuba sannan su ka sake gyara tunaninsu da akidunsu, domin kuwa Allah mai rahama ne da jin kai. Wanda duk ya ja da baya ya yi watsi da bada gaskiya alhali yana da sani da fahimtar gaskiya, to sakamakonsa yana da nauyi. A duniya mutane ma’abota gaskiya za su rika la’antarsa a lahira kuma zai kasance cikin azabar Allah mai tsanani. Wannan ajin na mutane basu cancanci samun sauki ba ko kuma jinkirin azabtarwa ta kowace fuska. Sun yi nisa daga rahamar Allah, sai dai duk da haka kofar tuba a bude ta ke ba a rufe ba. Hatta mutane irin wadannan matukar da gaske su ke yi, idan su ka yi nadama da gaske su ka sauya tunani da ayyukansu, to gafarar Allah za ta shafe su. Abubuwan da za mu koya daga wadannan ayoyi. 1-Tuba ba a fatar baki kadai ya ke ba, tuba na gaskiya ya shafi sauya tunani da gyara shi da kuma ayyukan kwarai maimakon munana. 2-Baya ga karbar tuban masu laifi da Ubangiji ya ke yi, yana kuma son masu tuba. A karshen wannan shirin muna rokon Allah da ya tabbatar da duga-duganmu akan imani da shi da kuma annabawansa, ya kuma karshensu ya yi kyau. Sai kuma mun sake hadewa a cikin wani shirin.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 90-94 (Kashi Na 90)
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai. Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin kaso na 78. Muna kuma kawo muku fassarar ayoyin kur’ani mai girma ne acikinsa. Da fatan za a kasance a tare da mu domin a ji ci gaban shirin daga inda mu ka tsaya a baya.
Yanzu za mu karanta ayoyi na 90 da 91 na suratu Ali-imran.
إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُواْ بَعْدَ إِيمَانِهِمْ ثُمَّ ازْدَادُواْ كُفْراً لَّن تُقْبَلَ تَوْبَتُهُمْ وَأُوْلَـئِكَ هُمُ الضَّآلُّونَ{90} إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُواْ وَمَاتُواْ وَهُمْ كُفَّارٌ فَلَن يُقْبَلَ مِنْ أَحَدِهِم مِّلْءُ الأرْضِ ذَهَباً وَلَوِ افْتَدَى بِهِ أُوْلَـئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ وَمَا لَهُم مِّن نَّاصِرِينَ{91}
“Wadanda su ka kafirta bayan sun bada gaskiya sannan su ka kara kafirci, to ba za a karbi tubansu ba, wadancanenka su ne batattu.” “Wadanda su ka kafirta sannan su ka mutu suna kafirai to har abada ba za a karbi cikin kasa na zinare ba daga dayansu, koda zai yi fansa das hi. Wadancanenka suna da azaba mai radadi, ba su da mataimaki.”
Mutum yana da ‘yancin zabawa kansa hanyar da zai bi. Zai kuma iya zabar wacce zai bi tsakanin imani da kafirci. Wasu mutane suna karbar imani saboda biyayya ga magabatansu ko kuma saboda wasu dalilai na kashin kansu bisa la’akari da yanayin zamani, amma saboda imanin mutane irin wadannan bai ginu bisa ginshiki mai karfi ba, sai su yi watsi da shi cikin sauki. Su rungumi kafirci. Mutane irin wadannan suna nutsewa cikin kafirci da kuma yin kurmuwa acikinsa ta yadda duk wata kafar komawa da baya da gyara kawukansu za ta rufe. Kuma babu wani abu wanda ya ke sa su farka sai dai mutuwa ko kuma nasarar da musulmi za su samu. A fili ya ke cewa idan har wadannan mutanen sun mika wuya ga musulmi to saboda tsoro ne ba saboda tuba na gaskiya ba. Domin kuwa tuban gaskiya ba ya kasancewa da tsoro. Babu wani abu wanda zai iya tseratar da mutane irin wadannan daga azabar Allah a lahira ko mai yawan dukiyarsu. Abubuwan da za mu koya daga wadannan ayoyin. 1-Kare imani shi ne mafi muhimmanci daga shi kanshi imanin domin kuwa mutane da dama sun yi imani amma su ka kafirce. 2-Ubangiji mai karbar tuba ne, amma wasu mutane da su ke nacewa akan kafirci suna rufewa kansu kofar tuba. 3-Kada mu sakankance da halin da mu ke ciki a wannan lokacin, domin kuwa kowane mumini yana fuskantar hatsarin kafircewa.
Yanzu kuma za mu saurari aya ta 92 a cikin suratu Ali-Imran.
لَن تَنَالُواْ الْبِرَّ حَتَّى تُنفِقُواْ مِمَّا تُحِبُّونَ وَمَا تُنفِقُواْ مِن شَيْءٍ فَإِنَّ اللّهَ بِهِ عَلِيمٌ
“Ba za ku sami sakamakon da’a( biyayya) ba har sai kun ciyar daga abinda ku ke so. Abinda ku ka ciyar na kyawawa, to Allah yana sane da shi.”
A cikin harshen larabci Kalmar “Bir” tana da ma’anoni masu fadi wacce ta kunshi duk wani abu mai kyau na tunani da kuma aiki. A cikin kur’ani an lissafa ayyuka irin su salla da jihadi da cika alkawali a matsayin “Bir” Wani daga ma’anar wannan Kalmar ta “Bir” shi ne ciyarwa akan tafarkin Allah, wato mutum ya bayar da abinda ya ke kauna wanda kuma zuciyarsa ta damfaru da shi. Ba wai ciyar da abubuwan da an riga an gama amfani da na, an kuma ci moriyarsu ba. An rawaito cewa a daren amarcin Fatima diyar ma’aiki wani almajiri ya zo yana barar tufafin da ya tsufa saboda diyarsa. Fatima ta bashi tufafinta na amarci wanda shi ne ya ke nuni da ma’anar wannan ayar. Wato abinda ku ke kauna da so, ku bayar da shi sadaka. Shakka babu ciyarwa tana da ma’ana mai fadi, wanda ya shafi duk wani taimako ga wasu, ya hada da kyauta da yin sadaka da kuma bada bashi da rance da kuma waqafi da bakance. Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-A bisa mahanga ta addini ayyukan kwarai ba su takaita acikin salla da ibada ba, sun shafi taimakawa marasa-shi kuma cike gurbin da ake da shi ta fuskar tattalin arziki nauyi ne da ya rataya a wuyan mumini. 2-Saboda Allah yana ganin ciyarwar da mu ke yi, ya zama wajibi a gare mu mu bayar da abu mafi kyawu ta fuskar inganci da kuma yawa. 3-Shahidai suna samun daraja ta koli domin kuwa sun sadaukar da abu mafi darja da su ke da shi wato rayukansu. 4-Kimar abinda za a ciyar shi ne mai muhimmanci ba yawansa ba, wato ya zamana mai kyawu koda kuwa kadan ne. 5-Manufar ciyarwa a musulunci ba ta takaita acikin kosar da masu jin yunwa ba kadai, ta shafi cire zuciyar mai ciyarwar daga damfaruwa da abin duniya, abinda ya ke sa ruhinsa ya daukaka.
Yanzu kuma sai ayoyi na 93 da 94 a cikin suratu Ali-Imrana.
كُلُّ الطَّعَامِ كَانَ حِـلاًّ لِّبَنِي إِسْرَائِيلَ إِلاَّ مَا حَرَّمَ إِسْرَائِيلُ عَلَى نَفْسِهِ مِن قَبْلِ أَن تُنَزَّلَ التَّوْرَاةُ قُلْ فَأْتُواْ بِالتَّوْرَاةِ فَاتْلُوهَا إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ{93} فَمَنِ افْتَرَىَ عَلَى اللّهِ الْكَذِبَ مِن بَعْدِ ذَلِكَ فَأُوْلَـئِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ{94}
“Dukkanin abinci ya kasance halaliya ga Bani-Isra’ila sai wanda ya’kub ya haramtawa kansa, shi ma gabanin asaukar da attaura. Ka ce ku zo da attaura ku karanta ta idan kun kasance masu gaskiya. Wanda duk ya kirkri karya ga Allah bayan wannan to wancanenka su ne azzalumai.”
Daya daga cikin abinda yahudawan madina su ke zargin annabin musulunci da shi, shi ne cewa da akwai banbancin a tsakanin shari’ar da musulunci ya zo da ita da kuma shari’ar annabi Musa da Isa. Suna kuma kafa misali da cewa awurin annabawan da su ka gabata cin naman rakumi da kuma shan nononsa haramun ne, amma a musulunci halaliya ce. Allah yana maida musu martani da cewa: A cikin shari’ar Musa da Isa ma cin naman rakumi da shan nononsa halaliya ce, annabi ya’kub ne kadai ya haramtawa kansa domin kuwa yana yi masa illa, saboda haka ya daina amfani da shi a matsayin abinci. Sai Bani Isra’ila su ka dauka cewa ya yi haka ne saboda shari’a ce ta haramta masa, alhali wata matsala ce da ta shafe shi shi kadai. A ci gaban wannan ayar yana cewa: Attaura ita ce mizanin shari’ar da annabi Musa ya zo da ita, ba abinda ku ka ji da fatar baki ba ko jita-jita, abinda ya zo a cikinta na haramci to shi ne haramun, ba ku dangantawa Ubangiji wani hukunci ba tare da dalili ba. Abubuwan da zamu koya daga cikin wadannan ayoyin. 1-Kada mu haramta abinda Allah ya halarta, kuma kada halarta abinda Allah ya haramta, kada kuma mu dauki abinda al’ada ta yi hukunci akansa mu bashi hukuncin addini. 2-Ka’ida ta bai daya ita ce kowane abinci halal ne, sai wanda shari’a ta haramta da dalili. 3-Kada mu rika baiwa rayinmu na kashin kanmu siffa ta addini, wanda shi ne zalunci mafi girma ga addini. Muna kawo karshen wannan shirin cikin fatan Allah ya sa mu zama masu rigegeniya wajen ciyar da marasa-shi da kuma aiki da hukunce-hukuncen addini, da yin biyayya ga littafin Allah, ba biyayya ga al’adu ba. Sai kuma wani shirin anan gaba.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 95-99 (Kashi Na 91)
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na hannunka mai sanda. Shirin wanda yake dubi cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma don su zama darasi a cikin rayuwar ma. Da fatan masu saurare zasu kasance tare da kuma.
- .
A cikin shirimmu na yau zamu dabu wasu ayoyi a cikin sarar Ali-imran. Kuma zamu fara da sauraron aya ta 95 daga cikin surar kamar haka.
قُلْ صَدَقَ اللّهُ فَاتَّبِعُواْ مِلَّةَ إِبْرَاهِيمَ حَنِيفاً وَمَا كَانَ مِنَ الْمُشْرِكِينَ
95-Ka ce: "Allah Ya yi gaskiya, sabõda haka ku bi akĩdar Ibrãhĩma mai karkata zuwa ga gaskiya; kuma bai kasance daga mãsu shirki ba."
A cikin shirimmu da ya gabata mun bayyana cewa kabilar Bani Isra'ila sun haramtawa kansu cin wasu nau'o'in a binci, amma sai suka dangata haramcin ga Allah. Don haka sai manzon Allah (s) ya ce da su: Idan gaskiya kuke fada to ku kawo dalili na haramcin wadan nan abincin a cikin littafin Attaura. Wanna ayar tana bayyanawa bani, isra'ila cewa, tunda ku kuna riya cewa ku masu bin annabi Ibrahim (a) ne. To ku kasance kamarsa, don shi baya bin son zuciyarsa yana biyayya ga umurnin Ubangijinsa baya bin son zuciyarsa, me yasa bazaku zama kamar shi ba?. Me yasa kuke bin al-adun da kuka kirkirowa kanku, kuka dorawa kanku? Muna iya daukar darussa daga cikin wannan ayar kamara haka. 1. Fadin gaskiya da binsa na daga cikin abinda mafifitan bayin Allah suke kai a duk tsawon zamani. Don haka mu yi kokari muma mu zama kamarsu, mu dauki misali daga rayuwarsu. 2. Karban dokoki ko tsarin rayuwa wanda ya sabawa na Ubangiji yana matsayin shirka da shi ne a cikin hakkinsa da ya kebantu da shi. Wato na kafa dokoki wa bayinsa.
Yanzu kuma bari mu saurari ayoyi na 96 da kuma 97 a cikin surar ta Ali-Imran kamar haka.
إِنَّ أَوَّلَ بَيْتٍ وُضِعَ لِلنَّاسِ لَلَّذِي بِبَكَّةَ مُبَارَكاً وَهُدًى لِّلْعَالَمِينَ{96} فِيهِ آيَاتٌ بَيِّـنَاتٌ مَّقَامُ إِبْرَاهِيمَ وَمَن دَخَلَهُ كَانَ آمِناً وَلِلّهِ عَلَى النَّاسِ حِجُّ الْبَيْتِ مَنِ اسْتَطَاعَ إِلَيْهِ سَبِيلاً وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ الله غَنِيٌّ عَنِ الْعَالَمِينَ{97}
96-Kuma lalle ne, ¦aki na farko da aka aza dõmin mutãne, hakĩka, shi ne wanda ke Bakka mai albarka kuma shiriya ga tãlikai.
97-A cikinsa akwai ãyõyi bayyanannu; (ga misãli) matsayin Ibrãhĩma. Kuma wanda ya shige shi yã kasance amintacce. Kuma akwai hajjin ¦ãkin dõmin Allah a kan mutãne, ga wanda ya sãmi ĩkon zuwa gare shi, kuma wanda ya kafirta to lalle Allah Mawadãci ne daga barin tãlikai.
A cikin abin da yahudawa suke zargin musulmi na farko da shi, shi ne cewa, Baitil muqaddasi, masallaci ne wanda annabi Sulaiman (a) ya gina tun kimani shekaru 1000 kafin haihuwar annabi Isa (a), ma ya sa kuke fuskantar dakin ka'aba a cikin sallolinku al-hali bata da jimawa irin na baitul mukaddasi?. Alkur'ani mai girma ya basu amsa da cewa. Ai dakin ka'aba shi ne dakin da aka fara bautar Allah a cikinsa. Kuma yana da dadewa wanda babu wani wuri ko masallaci a bayan kasa yake da shi. A cikin ruwayoyi an bayyana cewa, annabi Adam (a) ne ya fara aje asasin dakin ka'aba, sannan annabi Ibrahim da dansa Isma'ila suka kammala aikin tada ginin dakin. Kuma dukkan annabawan Allah sun ziyarci wannan dakin suna bautawa Allah a lokuta daban daban. San dakin ka'aba ba kawai daki ne wanda musulmi suke fuskanta a lokutan sallarsu har sau biyar a yini kasai ba. Harma a ko wace shekara wadanda suke da hali daga cikinsu suna taruwa don gabatar da wani irin ibada ta musamman a wajen. Kuma wajibe da wanda yake da iko akalla sau daya a rayuawarsa ya halarci wannan ibada ta aikin hajji. Banda haka, akwai wani dutse wanda annabi Ibrahim (a) yake hawa kansa a lokacinda yake daga bongon dakin ka'aba. Wannan duntsen har yanzu yana nan an kiyaye shi kusa da shi dakin ka'aban. Wato makama Ibrahim. Har'ila kiayae wannan dutsen a inda yake wata alamace wacce duk wannan ya je wurin yakamata ace wannan dutsen ya zama abin tunani da kula a wajensa. Chanjin yanayi ambaliyan ruwa, da wasu sauye sauyen da aka samu a duniya na daruruwan shekaru bai sauya halin da wannan wurin yake ba. Sannan dakin Ka'aba da kuma garin Makka wurin na mai aminci a wajen Allah. An hana yankar itaciya ko farautar tsuntsayi a garin. Hakama idan wani mai lafi ma ya fake da dakin ka'aba ba za'a yake shi a ca ba, sai dai ayi masa wasu dabarbaru ko a takura masa don ya bar wurin. Amma baya halatta a zubar da jinisa a cikinsa. Acikin wadannan ayoyi biyu muna iya daukar darussa kamar haka. 1. Idan a yau a duniya muna da wani wuri da wakilan kasashen duniya gaba daya suke taruwa. To Allah tun farkon samuwar mutum a bayan kasa ya rika ya samar masu dakin ka'aba a matsayin wurin bauta sannan wajen taruwansu don su tattauna matsalolinsu da kuma ci gabansu. 2. Allah baya kallafawa bayinsa abinda ba za su iya ba. Don haka kowa zai yi aiki gwargwadon karfinsa na dukiya da kuma lafiyan jikinsa. 3. Amfanin biyayya ga dokokin Allah suna komowa ne a garemu. Allah baya amfanuwa da biyayyarmu kamar baya amnafanuwa da hatta halittarmu.
Yanzun kuma mu saurari ayoyi na 98 da kuma 99 cikin surar ta Ali-Imran kamar haka.
قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ لِمَ تَكْفُرُونَ بِآيَاتِ اللّهِ وَاللّهُ شَهِيدٌ عَلَى مَا تَعْمَلُونَ{98} قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ لِمَ تَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ اللّهِ مَنْ آمَنَ تَبْغُونَهَا عِوَجاً وَأَنتُمْ شُهَدَاء وَمَا اللّهُ بِغَافِلٍ عَمَّا تَعْمَلُونَ{99}
98-Ka ce: "Ya kũ Mutãnen Littãfi! Don me kuke kãfirta da ãyõyin Allah, alhãli kuwa Allah Mai shaida ne a kan abin da kuke aikatãwa?"
99-Ka ce: "Ya ku Mutãnen Littãfi! Don me kuke taushe wanda ya yi ĩmani, daga hanyar Allah, kuma kunã nẽman ta zama karkatacciya, alhãli kuwa kunã mãsu shaida? Kuma Allah bai gushe daga abin da kuke aikatãwa ba yana Masani."
Duk da cewa a lokacinda addinin Musulunci ya bayyana a kasashen larabaw, yahudawa sune mafi yawa daga cikin ma'abota littafi a yankin. Kuma dalilin yawansu zuwansu da kuma cicirindonsu a yankin shi ne dakon bayyana annabin karshe wanda zai zo da sakon Allah na karshe ga bayinsa. Sai dai abin bakin ciki shi ne cewa, bayan hijirar manzon Allah (s) zuwa Madina maimakon su yi imani da shi, da kuma littafin alkur'ani da ya zo da shi, sai suka kafirce masa suka kafircewa littafin da ya zo da shi. Banda hakama sun hada kai da sauran mushrikan larabawa don ganin bayan manzon Allah (s) da kuma addininsa. Sun tsaya kai da fata suna hana mutane shigar addinin Musulunci da kuma imani da manzancin manzon Allah (s). A cikin wadannan ayoyi Allah yana fadawa masu cewa: Shin baku san cewa Allah yana ganin abinda kukeyi ba ? A bayyane da kuma boye? Shin me yasa kuke hana mutane shiga addinin Allah bayan kun san gaskiya ?. Muna iya daukar darussa a cikin wadannan ayoyi kamar haka. 1. Idon mun yi iamanin cewa Allah yana kallon duk abinda muke yi- wannan zai hana mu aikata mafi yawan laifuffuka da da muke yi. Hanya mafi inganci na kaucewa sabon Allah shi ne sani da kuma imani da cewa ubangiji yana kallommu. 2. Mafi yawan mutane wadanda suke adawa da addinin Musulunci sun san cewa su ne suke kan bata- amma duk da haka sai suna bin hanyar bata. Daga karshe masu sauraro muna rokon Allah da ya sanya rabommu cikin ziyarar dakinsa kuma ya gabafar ta mana zunubbammu. Da fatan an amfana da shirin. Wassalamu alaikum warahmatullahi…
Suratu Al Imrana, Aya Ta 100-104 (Kashi Na 92)
Assalamu alaikum masu saurare barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na hannunka mai sanda cikin wanda yake dubi cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma don su zama darasi a cikin rayuwarma. Da fatan masu saurare zasu kasanci tare da mu kamar yadda aka saba.
- .
A yau shirimmu zai fara da ayoyi 100 da kuma 101 cikin surara Ali Imrana. Kamar haka:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوَاْ إِن تُطِيعُواْ فَرِيقاً مِّنَ الَّذِينَ أُوتُواْ الْكِتَابَ يَرُدُّوكُم بَعْدَ إِيمَانِكُمْ كَافِرِينَ{100} وَكَيْفَ تَكْفُرُونَ وَأَنتُمْ تُتْلَى عَلَيْكُمْ آيَاتُ اللّهِ وَفِيكُمْ رَسُولُهُ وَمَن يَعْتَصِم بِاللّهِ فَقَدْ هُدِيَ إِلَى صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ{101}
Ya ku wadanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi dã'aga wani bangare daga wadanda aka bai wa Littãfi, zã su mayar da ku kãfirai a bãyan ĩmãninku! Kuma yãyã kuke kãfircẽwa alhãli kuwa anã karanta ãyõyin Allah a gare ku, kuma a cikinku akwai manzonSa? Kuma wanda ya nẽmi tsari da Allah, to, an shiryar da shi zuwa ga hanya mikakkiya.
Kafin hijirar manzon Allah (s) zuwa madani, kabilun Hazraj da sun dau shekaru suna yake yake a tsakaninsu, amma bayan shigorsu musulunci, kuma bayan hijirar manzon Allah (s) daga makka zuwa madina sun daina yakar juna, zaman lafiya da aminci ya wanzu a tsakaninsu albarkacin jagorancin manzona Allah (s) Amma wasu daga cikin shuwagabannin yahudawa wadanda wannan zaman lafiya da aka samu a tsakanin kabilun larabawa a madina bai yi masu dadi ba, sun fara kulle kulle na sake tada yaki a tsakanin wadannan kabili. Inda suka ingiza wani daga cikin musulmi wanda ya fara data tsohuwar gaba da ke tsakanin wadananan kabilu. Wannan makircin ya kusan kai ga nasar, don saura kadan su kai ga yaki sai wadan nan ayoyi suka sauka. Tana gargadi ga musulmi da su yi hankali da makircin makiya kafirai. Ta nuna masu cewa manufarsu shi ne nisanta tsakaninsu da kuma kaudasu daga tafarkin Ubangiji ne. Banda haka samuwar manzon Allah (s) da kuma littafin Allah a tsakaninsu wata igiya ce da ta daure tsakaninsu ta samar da hadin kai da fahintar juna. Don haka ta gargadesu da su yi biyayya ga umurnin Allah su kaucewa makirce makircen makiya. Muna iya daukan darussa da cikin wadannan ayoyi kamar haka. 1. Fatar makiya shi ne ganin imanimmu da manzon Allah (s) da kuma littafinsa ya yi rauni. Don haka kada mu bada kofa garesu wajen cimma wannan manufar tasu. 2. Kada mu rudu da karfin imanimmu da tsoron Allah wadanda muke tare da su a yanzun, da dama daga cikin muminai sun yi mummunan karshe sun mutu kafirai bayan imani. 3. Samuwar littafin Allah a tsakanin musulmi bai wadatar wajen tabbatra da su kan shiriya ba, kasantuwar zubabbun shuwagabanni daga Ubangiji a tsakanin musulmi da kuma biyayya a garesu lazimi ne. 4. Duk abinda musulmi zai yi ya tabbatar wanda zai kai shi ga tafarki madaidaici ne, ba hanyar bata da kaucewa gaskiya ba.
Yanzu kuma sai mu saurari ayayo na 102 da kuma 103 a cikin surar Ali Imran kamar haka:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ اتَّقُواْ اللّهَ حَقَّ تُقَاتِهِ وَلاَ تَمُوتُنَّ إِلاَّ وَأَنتُم مُّسْلِمُونَ{102} وَاعْتَصِمُواْ بِحَبْلِ اللّهِ جَمِيعاً وَلاَ تَفَرَّقُواْ وَاذْكُرُواْ نِعْمَتَ اللّهِ عَلَيْكُمْ إِذْ كُنتُمْ أَعْدَاء فَأَلَّفَ بَيْنَ قُلُوبِكُمْ فَأَصْبَحْتُم بِنِعْمَتِهِ إِخْوَاناً وَكُنتُمْ عَلَىَ شَفَا حُفْرَةٍ مِّنَ النَّارِ فَأَنقَذَكُم مِّنْهَا كَذَلِكَ يُبَيِّنُ اللّهُ لَكُمْ آيَاتِهِ لَعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ{103}
Ya ku wadanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da takawa, a kan hakkin binsa da takawa, kuma kada ku mutu fãce kuna mãsu sallamawa (Musulmi). Kuma ku yi daidami da igiyar Allah gabã daya, kuma kada ku rarraba. Kuma ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da kuka kasance makiya sai Ya sanya sõyayya a tsakãnin zukãtanku sabõda haka kuka wãyi gari, da ni'imarSa, 'yan'uwa. Kuma kun kasance a kan gãbar rãmi na wutã sai Ya tsãmar da ku daga gare ta, Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ayõyinSa, tsammãninku, zã ku shiryu.
Akwai manya manyan azuzuwa a cikin makarantu irin na annabawan Allah inda suka bada tarbiya ga mabiyansu gwargwadon abinda kowannensu zai iya dauka. Imani da takwa ma suna nan marhala marhala. Duk wata kamala ko aiki na alkhairi yana da matakai daya bayan daya. Don haka ne Allah ta'ala ya umurci manzon Allah (s) da ya ce – رب زدنی علما - wato –Ubangiji ka kara mani sani-. Don haka wannan ayar tana kodaitar da muminai das u nemi Karin takwa ko kuma tsoron Allah a wajensa, tsoro wanda zai kare ku daga mummunan ayyuka kuma ya kai ku ga aikata kyawawa. Aya ta 203 tana kira ga musulmi da su hada kansu karkashin inuwar addinin Allah. Kuma tana tunatar dasu cewa, kafin su zama masu imani, suna cikin wani mummunan yanayi na rashin zaman lafiya da gaba a tsakaninsu. Suna cikin hatsari wanda a ko yauce suna iya halaka, amma sai Allah ya tsamosu ya shiryatar da su ya kyautata zamantakewa a tsakaninsu ya samar da aminci da zaman lafiya a tsakaninsu. Don haka godewa Allah da wannan ni'amar. Daga cikin wadannan ayoyi muna iya fahintar abubuwa kamar haka. 1. Kekyawan karshe, mutuwa cikin imani su ne suke bayyana makomar mutum. Yadda mutum zai mutu yana da dangataka da yadda ya rayu a nan duniya. 2. Hadin kai tsakanin musulmi yana samuwa ne kadai karkashin tutar addini. Hadin kai bias asasin kabilanci, yan kasanci ko harshe bay a tabbata kuma baya dawwama. 3. Har'ila yau hadin kai bisa asasin alkawula da kasa da kasa, ko siyasa ko ta tsaro da soje ba masu tabbata bane. Haduwar zukata shi ne kadai tafarkin samun hadin kai, kuma wannan yana hannun ubanjini. Shi kadai ne yake iya hada zukatan mutane. 4. Tunawa da ni'imomin Ubangiji yana sanya mutum biyayya da kuma shauki a gareshi. Kamar yadda gafala da kuma mancewa daga wadannan ni'imomin yakan jawo rasa su.
Yanzu kuma mu saurari aya ta 104 cikin surar ta Ali Imran kamar haka:
وَلْتَكُن مِّنكُمْ أُمَّةٌ يَدْعُونَ إِلَى الْخَيْرِ وَيَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنكَرِ وَأُوْلَـئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ{104}
Kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alhẽri, kuma suna umurnida alhẽri, kuma suna hani dagaabin da ake ki. Kuma wadannan, sũ ne mãsu cin nasara.
Mutane suna cikin tare ne. Rayuwar daddaikun mutane ko yana so ko baya so ko ya sani ko bai sani ba, halayensu suna tasiri ga sauran mutanen da suke rayuwa tare. Rayuwa tare kamar tafiya ce a cikin jirgin ruwa, wanda idan wani daga cikinsu ya huda wani bangare da jirgin ruwa zai shigo ya halakasu gaba daya. Don haka a bisa yardar kowa, ya zama wajibi a taru a rike hannun duk wanda zai yi kokarin huda wani sashin jirgin don a tsira tare. Addinin musulunci ya dauki wannan ka'ida ta hankali, sai ya samar da wani taklifi mai sun – امر بالمعروف ونهی عن المنکر - a cikin wannan taklifin Allah ya bukaci daddaikun musulmi a ko ina yake idan ya ga inda ake sabawa Allah ko kuma aka bar amfani da umurninsa to ya yi gargadi ya tunatar da masu sabon su dawa kan tafarki. Shi wannan taklifin yana kan ko wani musulmi gorgodon ikonsa. Amma duk da haka, wannan ayar ta bukaci a samar da wata jama'a ko ma'aikata wacce dace da yin wannan aikin da umurni da hani a inda ya dace. Kamar dai misali idan wani ya tuka motarsa ta hanyar da bai dace ba, zaka ga sauran direbobi suka ta dannan hon suna haska fitillu don su fahintar da shi baya tafiya yadda ya dace, sannan dansanda kuma zai yi aikinsa na ganin kowa ya kiyaye dokokin tuki da tafiya kan tituna. Wani abin lura anan shi ne cewa ayar ta - امر بالمعروف ونهی عن المنکر - ta zo bayan aya wacce take kira zuwa ga hadin kai tsakanin musulmi. Wanda yake nuna cewa kiyaye tsare da dokoki a cikin al-umma ba zai samu ba said a hadin kai a tsakanin daddaikun al-ummar. Daga karshe muna iya daukar darussa a cikin wadan nan ayoyi kamar haka. 1. A cikin al-ummar musulmi dole ne a samar da wata jama'a wacce take kula kai kawo da kuma halayen mutane. Wacce zata hana aikata laifi kuma ta yi umurni da abinda ya dace. 2. Ana samun rayuwa mai inganci ne karkashin inuwar tausayawa juna da kuma kokari wajen warware matsalolin al-umma. 3. Mumini baya tunani kan tsamar da kansa kadai daga matsalolin rayuwa ba. Yana ta kansa kuma yana tunanin sauran alummar gaba dayanta. 4. Ana gabatar da kira zuwa ga ayyukan alkhairi kafin a toshe hanyar barna. Don idon ayyukan alkhairi sun yawaita a cikin al-umma, hanyoyin barna zasu yi karanci sosai. Masu sauraro anan kuma zamu dasa aya sai kuma a wani shirin idan Allah ya akimu wassalamu alaikuma warahmatullahi wabarakatu.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 105-109 (Kashi Na 93)
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na hannunka mai sanda. Shiri wanda yake dubi cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma do su zama fitilla a garemu a cikin rayuwarmu. Da fatan masu saurare zasu kasance tare da mu.
To bara mu fara shirimmu da karatun aya ta 105 daga cikin surar Ali-imrana kamar haka.
وَلاَ تَكُونُواْ كَالَّذِينَ تَفَرَّقُواْ وَاخْتَلَفُواْ مِن بَعْدِ مَا جَاءهُمُ الْبَيِّنَاتُ وَأُوْلَـئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ عَظِيم
105-Kuma kada ku kasance kamar wadanda suka rarrabu kuma suka sãbã wa jũna, bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu kuma wadannan sunã da azãba mai girma.
A cikin shirimmu da ya gabata mun ji yadda Ubangiji ya kira a matsayin musulmi yan uwan juna. Bambancin kabila, launin fata, kasa da sauransu basa da tasiri wajen tabbatar da yanuwantaka tsakanin masu imani da addinin guda. Don haka mumini a ko ina yake a duniya kuma a ko wani zamani ya yake Allah ya kulla yanuwantaka a tsakaninsu. A wani hadisi manzon Allah (s) yana cewa "Yan uwana sune wadanda zasu zo nan gaba, basu taba ganina ba, amma kuma suka yi imani da ni, wadan nan sune yan uwana na gaskiya. Daya daga cikin lamuran da suke barazana ga mabiya addinan sama a ko yauce a tsawon tahiri shi ne, matsalar sabani da rarrabuwa tsakanin mabiya addini guda, wani lokacin suna samun sabani bisa kabilanci, ko shugabanci da sauransu. Wannan aya tana kashedi wa muminai kan cewa kada su rarraba su kawo sabani a tsakaninsu, wadanda suke kokarin cusa sabani a cikin muminai Allah ya yi masu alkawarin azaba mai tsanani. Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka. 1. Ba a ko yauce bane jahilci da rashin sani suke jefa muminai cikin sabani da rarrabuwar kawuna. Wasu lokacinda mutum yana sane da gaskiya, amma don wata bukata tasa sai ya jafe sabani tsakanin muminai don ya rarraba kansu wanda hakan zai bashi dammar kaiwa ga burinsa. 2. Yakamata mu dauki darasi daga cikin al-ummu da suka gabace mu shin sun kai ga nasara ne ta hanyar sabani da rarrabuwar kawuna ? ko kuma ta hanyar hadin kai da zama tsuntsiya madaurinki daya.?
A halin yanzu bari mu saurari karatun aya ta 106 a cikin sura ta Ali-Imran kamar haka.
يَوْمَ تَبْيَضُّ وُجُوهٌ وَتَسْوَدُّ وُجُوهٌ فَأَمَّا الَّذِينَ اسْوَدَّتْ وُجُوهُهُمْ أَكْفَرْتُم بَعْدَ إِيمَانِكُمْ فَذُوقُواْ الْعَذَابَ بِمَا كُنْتُمْ تَكْفُرُونَ{106} وَأَمَّا الَّذِينَ ابْيَضَّتْ وُجُوهُهُمْ فَفِي رَحْمَةِ اللّهِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ{107}
106-A rãnar da wasu fuskõki suke yin fari kuma wasu fuskõki suke yin baki (zã a ce wa wadanda fuskokinsu suke yin bakin): "Shin kun kãfirta a bayan ĩmãninku? Don haka sai ku dandani azãba sabõda abin da kuka kasance kuna yi na kãfirci." 107-Kuma amma wadanda fuskõkinsu suka yi fari, to sũ suna cikin rahamar Allah kuma, su a cikinta, madawwama, ne.
A ranar kiyama mutane zasu kasu kashi biyu, akwai wadanda zasu zo fuskokinsu na haske, wasu kuma fuskokinsu sun yi baki da duhu. Sai a fadawa wadanda suka zo da bakaken fuskoki ku shiga cikin azaba sanadiyyar kaficinku. Wadanda suka zo da fuskoki masu haske kuma zasu shiga aljanna suna masu dawwama a cikinta.
A rayuwarmu ta duniya ayyukammu suna da tasiri a bayyana ne ko zahira da kuma a boye ko kuma badini. Tasirinsu na badini zasu bayyana a lahira wanda da su ne ake rarraba makoman mutane aljanna ko wuta. Fuskoki masu haske da fuskokin masu duhu suna kwatanta irin ayyukammu mutum a rayuwar duniya ne. Inda haske yana zama alamar ayyuka masu kyau a yayinda duhu da baki suke nuna munanan ayyuka.
Don haka muna iya daukar darussa a cikin wadan nan ayoyi kamar haka.
1. Idan a cikin rayuwarmu ta duniya mun kasance tare da gaskiya, mun zama masu kyautata ayyukan, to a lahira zamu tashi fuskokimmu suna haske. Sabanin idon rayuwarmu bata kasance haka a duniya ba. 2. Kada mu rudu da imanin da muke da shi a halin yanzu, shi kafirci yana barazana ga muminai ma. Shi yasa muke addu'a Allah ya kyautata karhsemmu.
Yanzun kuma bara mu saurari karatun ayoyi na 108 da kuma 109 na cikin surar Ali-Imran kamar haka.
تِلْكَ آيَاتُ اللّهِ نَتْلُوهَا عَلَيْكَ بِالْحَقِّ وَمَا اللّهُ يُرِيدُ ظُلْماً لِّلْعَالَمِينَ{108} وَلِلّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ وَإِلَى اللّهِ تُرْجَعُ الأُمُورُ{109}
108-Wadannan ãyõyin Allah ne, muna karanta su a gare ka da gaskiya, kuma Allah bã Ya nufin wani zãlunci ga tãlikai.
109-Kuma abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin kasa na Allah ne, kuma zuwa gare Shi ake mayar da al'amurra.
Wadanan ayoyi suna Magana ne da manzon Allah(s) da kuma musulmi gabata daya kan abu guda wato adalcin ubangiji. Allah ba zai taba dorawa mutane abinda bazasu iya ba. Sannan ba zai azabtar da su fiye da abinda suka cancanta na azaba ba. Don haka idan wasu sun tashi fuskokinsu suna haske a ranar kiyama, wasu kuma fuskokinsu sun yi duhu to bisa abinda suka zabarwa kansu ne. Ba Allah ne ya zabar masu ba. Hakama wanda ya shiga jahannama (Allah ya kiyaye mu) ayyukansa a duniya suka jefa shi cikinta ba kaddarar Allah ba ne. Sannan ka'ida ta zaluntar wani shi ne ya kasance azzalumin jahili ne, aajizi mabukaci ko kuma mai sun daukar fansa. Wadannan sifofi duk sun koru daga barin Ubangiji. Don Allah baya zaluntar bayinsa. Shi ne ya halicci sammai da kassai mafi girma da fadi, ta yaya zai bukaci wani abu daga bayinsa? Shi ne ya halicci mutane da rahamarsa ta yaya zai zaluncesu? Shi ya umurcemu da barin zalunci ta yaya zai zalunce mu? Don haka muna iya daukar darussa a cikin wadannan ayoyi kamar haka. 1. Ubangiji wanda mukayi imani da shi, mahaliccin sammai da kassai, ya sanya dokoki da kuma sakamakon ayyukamma bisa adalci. Baya bukatar zaluntar wani daga cikin bayinsa. 2. Allah ne ya fara kome kuma gareshi ne makomar kome da kome, duk abinda mutum ya aikata na alkhaida da sharri suna tabbata basa bacewa bayan mutuwarsa.
Daga karshe masu sauraro a nan zamu dasa aya sai shirimmu na gaba, muna rakon Allah ya kiyayemu daga sharrin ayyukammu, ya tada mu tare da salihan bayinsa a ranar kiyama fuskokimmu suna haske da ayyukammu na alkhairi. Wassalamu alaikum warahmatullah.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 110-115 (Kashi Na 94)
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na hannunka mai sanda shiri wanda yake dubi cikin ayoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila mai haskake rayuwarmu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.
- .
A halin yanzu bari mu bude shirimmu da sauraron karatun aya ta 110 daga cikin surar Ali-Imran kamar haka.
كُنتُمْ خَيْرَ أُمَّةٍ أُخْرِجَتْ لِلنَّاسِ تَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَتَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنكَرِ وَتُؤْمِنُونَ بِاللّهِ وَلَوْ آمَنَ أَهْلُ الْكِتَابِ لَكَانَ خَيْراً لَّهُم مِّنْهُمُ الْمُؤْمِنُونَ وَأَكْثَرُهُمُ الْفَاسِقُون
110-Kun kasance mafi alhẽrin al'umma wadda aka fitar ga mutãne kuna umurni da alhẽri kuma kunã hani daga abin da ake ki, kuma kunã ĩmãni da Allah. Kuma dã Mutãnen Littãfi sun yi ĩmãni, lalle ne, dã (haka) yã kasance mafi alhẽri a gare su. Daga cikinsu akwai mũminai, kuma mafi yawansu fãsikai ne.
Mutane da dama suna zaton cewa addini wasu dokoki ne na ibadu da suke kebanci mutane daddaiku da ubangijinsu. Don haka a tunaninsu addini kawai shi ne sallah, azumi, karatun alqur'ani addu'a da sauransu. Amma gaskiyan lamarin shi ne addinin ya tattara kome da kome, addinin tarin dokoki ne wadanda suke iyakance dangantakar daddaikun mutane da ubangijinsu, da kuma sauran mutane da halittunsa. Har'ila yau saddini ya kunshi dukkan bangarorin rayuwa mutane. Hatta shi sallar, musulmi ya yi ta cikin jama'a yafi wanda zai yi shi kadai a gida. Horo da kekkewan ayyuka da kuma hani daga miyagun ayyuka, shi ne abu mafi muhimmanci da ke kare al-ummar musulmi daga fadawa cikin bata da kuma lalacewa. A cikin shirimmu da ya gabata mun bayyana cewa aikin-Amru bil-maruf da nahyi anil munkari – yana tabbata net a hanyoyi biyu, na farko shi net a hanyar hukuma ko jama'a masu kula da harkokin jama'a a cikin al-umma suna sanya ido a kan dukkan lamuran da ke faruwa a cikin al-umma kamar dai aikin jami'an tsaro na yansanda ko makamancinsu. Da biyu kuma aiki ne da ya hau kan dukkan mutane, a duk sanda suka sami kansu inda yakamata su yi gargadi ko su yi hani suna yi don kare tsarin da harkoki suke tafiya a cikin al-ummar. Kamr yadda aya ta 104 a cikin wannan surar ta ambata a bayan. Amma wannan ayar tana magana ne kan cewa mutum musulmi, ba wai kawai an umurce shi da ya kula da kansa shi kadai ba. Banda kula da kansa dole ne ya kasance yana tunanin sauran al-ummar. Yan tunanin yadda zai yada ayyuka masu kyau da kuma nisantar da ita al-ummar daga munanan ayyuka, wanda zai sa a sami al-umma mafi alkhairi, wacce zata zama abin misali ga wasu. Don haka muna iya daukar darussa kamar haka a cikin wannan ayar kamar haka. 1) umurni da kyawawan ayyuka ba tare da hana munanan ayyuka ba, bai wadatar ba. Dole ne ayyukan biyu su tafi tare kafin a sami natija mai kyau. 2) Umurni da ayyuka masu kyau da kuma hana munanan ayyuka, ya shafi kowa da kowa, babu bambanci cikin shekaru, kabila, launin fata, arziki da taulanci ko matsayi a cikin mutane. Musulmi yana da damar yiwa kowa nasiha da gargadi a ko ina yake kuma ko menene matsayinsa a cikin mutane. 3) Fifiko da daukaka a cikin al-ummar musulmi yana tattare da irin tasirin da ayyukansa na umurni da kyawawan ayyuka da kuma hana munanan suke yi a cikin al-umma. 4) Zama mafificin al-umma dole ne ya kasance al-ummar ta yi imani kuma ta hada da ayyuka masu kyau, wadanda suke kyautata lamuran ita al-ummar.
Yanzu kuma bari mu saurari karatun ayoyi na 111 da kuma 112 a cikin surar ta Ali-imran kamar haka.
لَن يَضُرُّوكُمْ إِلاَّ أَذًى وَإِن يُقَاتِلُوكُمْ يُوَلُّوكُمُ الأَدُبَارَ ثُمَّ لاَ يُنصَرُونَ{111} ضُرِبَتْ عَلَيْهِمُ الذِّلَّةُ أَيْنَ مَا ثُقِفُواْ إِلاَّ بِحَبْلٍ مِّنْ اللّهِ وَحَبْلٍ مِّنَ النَّاسِ وَبَآؤُوا بِغَضَبٍ مِّنَ اللّهِ وَضُرِبَتْ عَلَيْهِمُ الْمَسْكَنَةُ ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ كَانُواْ يَكْفُرُونَ بِآيَاتِ اللّهِ وَيَقْتُلُونَ الأَنبِيَاءَ بِغَيْرِ حَقٍّ ذَلِكَ بِمَا عَصَوا وَّكَانُواْ يَعْتَدُونَ{112}
111-Bã zã su cũce ku ba, fãce dai tsangwama. Kuma idan sun yãke ku zã su jũya muku bãya, sa'an nan kuma bã zã a taimake su ba.
112-An dõra kaskanci a kansu a inda duk aka sãme su fãce da wani alkawari daga Allah, da alkawari daga mutãne. Kuma sun kõma da fushi daga Allah, kuma aka dõra talauci a kansu. Wannan kuwa dõmin sũ, lalle sun kasance suna kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe annabãwa, bã da wani hakki ba. Wannan kuwa dõmin sãbãwar da suka yi ne, kuma sun kasance suna yin ta'adi.
Wadannan ayoyi suna bishara ne ga musulmi, na cewa fa idan sun yi umurni da kyawawan ayyuka suka kuma hana munana a cikin al-umma. To an lamunce masu cewa babu wani hatsari daga bangaren makiya da zai yi masu barazana ko zai fada masu. Makiyansu ba zasu jure yaki da ku ba fashe sun juya baya, suna kaskantattu. Wannan ayar tana maganar yahudawa ne. Kuma tana daga cikin ayayin da suka bayyana irin halin da yahudawa zasu kasance a rayuwar duniya tun bayan bayyanar musulunci da kuma kafircewarsu da shi. Alkur'ani yana nuna cewa a duk tsawon tarihi zasu kasasnce kaskantattu. A halin yanzu babu kasa a duniya ko da guda wacce take bin addinin da tsarin yahudanci, sannan hatta kasar Palasdinu da suka kwace da sunan kafa kasar yahudawa sun zama abin ki a dukkan kasashen duniya. Duk da irin dukiyoyi da karfin fada a ji da yahudawa suke da shi a wasu kasashen yamma, sai dai wannan bai sa suka sami yardarm mutanen duniya ba. Don haka sun kasance kaskantattu kamar yadda alkur'ani mai girma ya bayyana. A cikin wadannan ayoyi muna iya daukar darussa kamar haka. 1) Imani da Allah yana zama kariyar mumini daga makiyansa, kuma ya zama sababin faduwarsa da kuma rushewarsa. 2) Daukaka tana samuwa ne kadai ta hanyoyi guda biyu. Dangantaka mai kyau da Allah, da kuma dangantaka mai kyau da mutane. Idan wadannan abubuwa biyu suka hada babu wani abu da zai iya cutar da mumini a duniya. 3) Sabon Allah da shishigi sune musabbabin kaskanci da waulakanci a duniya kafin lahira.
Yanzun kuma mu saurari karatun ayoyi na 113, 114 da kuma 115 kamar haka
لَيْسُواْ سَوَاء مِّنْ أَهْلِ الْكِتَابِ أُمَّةٌ قَآئِمَةٌ يَتْلُونَ آيَاتِ اللّهِ آنَاء اللَّيْلِ وَهُمْ يَسْجُدُونَ{113} يُؤْمِنُونَ بِاللّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ وَيَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنكَرِ وَيُسَارِعُونَ فِي الْخَيْرَاتِ وَأُوْلَـئِكَ مِنَ الصَّالِحِينَ{114} وَمَا يَفْعَلُواْ مِنْ خَيْرٍ فَلَن يُكْفَرُوْهُ وَاللّهُ عَلِيمٌ بِالْمُتَّقِينَ{115}.
113- Ba su zama daidai ba; daga cikin Mutãnen Littafi akwai wata al'umma wadda take tsaye, suna karãtun ayõyin Allah a cikin sã'õ'in dare, alhãli kuwa sunã yin sujada.
114-Suna ĩmãni da Allah da Yinin Lãhira, kuma suna umurni da abin da kyawawan ayyuka kuma suna hani daga munanan ayyuka, kuma sunã gaugãwa a cikin aikata alhẽrai. Kuma wadannan suna cikin sãlihai.
115-Kuma abin da suka aikata daga alhẽri, to, bã zã a yi musu musunsa ba. Kuma Allah Masani ne ga mãsu takawa.
Bayan da ayoyin da suka gabata suka bayyana makirce makirncen yahudawa da kuma yadda suke kokarin batar da mutane daga bin hanyar gaskiya. Wadannan ayoyi suna maganar bangaren yahudawa masu kyawawan ayyuka kuma salihan bayin Allah. Ayoyin suka kira ga musulmi su gane cewa ma'abuta littafi ba dukkansu ne haka ba. Akwai masu abida daga cikinsu, suna sujada a cikin dare, sun yi imani da Allah da kuma ranar lahira. Sanna suna yada ayyuka na alkhairi cikin mutane. Suna hana yaduwar fasadi a cikin mutane. Allah ba zai yi watsi da ayyukansu ba kuma zai karbi ayyukan alkhairi daga duk wanda ya aikta su. Wannan shi ne yadda alkur'ani mai girma yake kallon ma'abuta littafi wato ahlulkiba, da kuma yadda yake nuna adalci a cikin lamarinsu. Sannan ayoyin suna ishara ga musulmi su kasance kamar mutanen kirki daga cikin su ma'abuta littafi. Har'ila ya yakamata musulmi su kula da yadda yakamata su yi mu'amala da wadanda ba musulmi ba. Don akwai matanen kirki daga cikinsu, halayemmu masu kyau suna iya jawosu zuwa ga shiga addinin musulunci. Muna iya daukan darussa cikin wadannan ayoyi kamar haka. 1) Gaskiya daga ko waye ya fito mu karbe shi, sannan a dai dai lokacinda muke sukan mabiyan wasu addinai kada mu rufe idanummu daga kyawawan ayyukansu. 2) Tsakiyan dare shi ne lokacinda yafi dacewa don munajati da kuma samun kusanci da Ubanjiki. 3) Bukata ta umurni da ayyuka masu kyawu da kuma hani daga munanan ayyukan bai kebantu da addinin musulunci ba, sun zo a cikin sauran addinan sama ma. 4) An gabatar da umurni da kyawawan ayyukan kan hani daga munanan ayyuka. Don idan ayyuka masu kyau sun yawaita a cikin al-umma munana ayyuka zasu yi karanci. Kamar a ce idan aure ya yawaita a cikin al-umma ayyukan alfasha zasu yi karanci. 5) Yin sauri wajen aikata alkhairi yana da muhimmanci a wajen ubangiji. Da wanna kuma masu saurare muka kawo karshen shirimmu nay au sai kuma wani lokaci idan Allah ya kaimu a huta lafiya wasalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 116-120 (Kashi Na 95)
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na hannunka mai sanda shiri wanda yake dubi cikin wasu ayoyin alqu'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwarmu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.
- .
Da farko bari mu saurari karatun ayoyi 116 da ta 117 daga cikin surar Aali-Imran kamar haka.
إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُواْ لَن تُغْنِيَ عَنْهُمْ أَمْوَالُهُمْ وَلاَ أَوْلاَدُهُم مِّنَ اللّهِ شَيْئاً وَأُوْلَـئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ{116} مَثَلُ مَا يُنفِقُونَ فِي هِـذِهِ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا كَمَثَلِ رِيحٍ فِيهَا صِرٌّ أَصَابَتْ حَرْثَ قَوْمٍ ظَلَمُواْ أَنفُسَهُمْ فَأَهْلَكَتْهُ وَمَا ظَلَمَهُمُ اللّهُ وَلَـكِنْ أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ{117}
116 - Lalle ne wadanda suka kãfirta, dũkiyõyinsu kõ yayansu bã zã su wadatar musu da kõme ba daga Allah, kuma wadannan abõkan wuta ne, sũ, acikinta, madawwama ne. 117- Misãlin abin da suke ciyarwa, a cikin wannan rãyuwar dũniya, kamar misãlin iska ce (wadda) a cikinta akwai tsananin sanyi, ta sãmi shukar wasu mutãne wadanda suka zãlunci kansu, sai ta halakar da ita. Allah bai zãlunce su ba, amma kansu suka kasance sunã zãlunta.
Daya daga cikin lamuran da suke kai wasu mutane ga kafirci shi ne jin cewa basa bukatar taimakon Allah, sun wadatu basa bukatan taimakonsa. Wannan mafi yawa yana faruwane a dai dai lokacinda wani yana ganin ya tara dukiya mai yawa ga kuma yaya su ma masu yawa. Yana ganin duk a binda yake bukata wadannan sun wadatar da shi. Wannan sai ya kaisu ga kafircewa Allah. Sai suna ganin cewa idan akwai Allah ma, to dukiya da yaya sun wadatar da shi. baya bukatar taimakon Allah. Don haka wadannan ayoyi sun yi radda wannan tunanin kuma sun tunatar da irin wadan nan kafiran cewa, idan dukiya da yaya sun wadatar da kai a rayuwar duniya shin ranar kiyama kuma wa zai kare ka daga azabar Allah?. Sai kuma aya ta 117 ta kara bayani kan ayyuka na alkhairi wanda wasu kafirai suke yi, kamar dukiyoyin da suke kashewa. Ayara ta bayyan abinda suke kashewa kamar wanda ya yi shuka ne a wurin bai dace ba, wurin da ko da shuka ta fita, to ba zai yi wani amfani ba, don rashin dacewar wurin shukar. Kafirci yana nan kamar yadda guguwa da iska mai karfi yake lalata gonaki, don haka duk abinda suka aikata na alkhairi kafirci yana lalata su. Sannan banda haka, ayyuka suna tafiya tare da niyya ne. Shi kafiri wanda bai yi imani da Allah ba, ayyukansa masu kyau ba abin karba bane a wajen Allah. Sannan rashin karban ba wai ubangiji ya zalunce shi ba, aa shi ya zalunci kansa. Don haka a cikin wadannan ayoyi muna iya daukar darussa kamar haka. 1. Jiji da kai da alfahari da dukiya da kuma yaya, da kuma jin cewa mutum baya bukatar taimakon Allah, wasu alamu ne na kafirci da kuma rashin godiya. 2. Manufar ciyarwa a musulnci ba wai kawai kosar da mayunwaci kadai bane. Idan haka ne babu bambanci tsakanin musulmi da kafiri. Amma abin lura shi ne cewa duk abinda kafiri ya ciyar bai da ladarsa a ranar kiyama. 3. Fushin Allah da azabarsa kan kafirai sakamakon ayyukansu ne ba zaluntansu ne ya yi ba.
Yanzu kuma mu saurari aya ta 118 cikin surar Aali-Imran kamar haka.
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ لاَ تَتَّخِذُواْ بِطَانَةً مِّن دُونِكُمْ لاَ يَأْلُونَكُمْ خَبَالاً وَدُّواْ مَا عَنِتُّمْ قَدْ بَدَتِ الْبَغْضَاء مِنْ أَفْوَاهِهِمْ وَمَا تُخْفِي صُدُورُهُمْ أَكْبَرُ قَدْ بَيَّنَّا لَكُمُ الآيَاتِ إِن كُنتُمْ تَعْقِلُونَ{118}
118 - Yã ku wadanda suka yi ĩmãni! Kada ku riki abõkan asĩri daga waninku, ba su takaita muku barna. Kuma sun yi gũrin abin da zã ku cũtu da shi. Hakĩka, kiyayya tã bayyana daga bãkunansu, kuma abin da zukãtansu ke bõyẽwa shi ne mafi girma. Kuma lalle ne, Mun bayyana muku ãyõyi, idan kun kasance kunã hankalta.
Daya daga cikin abubuwan da suke barazana ga al-ummar musulmi shi ne samuwar bakin mutane a cikin harkokin siyasa da jagoranci, wanda zai basu damar sanin asiran musulmi. Duk da cewa wani lokaci a zahira zasu bayyana cewa su masoya ne. Amma bisa hakika basa son musulunci kuma basa son ganin ci gaban addinin musulunci da musulmi. Banda haka suna kokarin ganin bayan addinin musulunci da musulmi ko ta wace hanya zasu samu. Kai wasunsu ma basa boye kiyayya da sukewa musulmi da musulunci. Don haka cikin wannan ayar muna iya daukan darussa kamar haka. 1) - Mumini dole ne ya kasance mai tunani da kuma kula da addininsa, kada ya yi sake ya bada dama wa makiya su san asiransa. Dole ne ya yi mu'amala da su tare da taka tsantsan. 2) - Samuwar sojojin ko jami'an tsaron kafirai a cikin kasashen musulmi haramun ne, don hakan yana nuna rauni da gazawar musulmi wajen tafiyar da lamuransu. 3)- Duk da cewa ya halatta a yi mu'amala da kafirai, amma dole ne a ko yauce mu san cewa musulunci da kafirci ba daya suke ba.
Yanzu kuma mu saurari karatun aya ta 119 da 120 a cikin surar ta Ali-Imran kamar haka.
هَاأَنتُمْ أُوْلاء تُحِبُّونَهُمْ وَلاَ يُحِبُّونَكُمْ وَتُؤْمِنُونَ بِالْكِتَابِ كُلِّهِ وَإِذَا لَقُوكُمْ قَالُواْ آمَنَّا وَإِذَا خَلَوْاْ عَضُّواْ عَلَيْكُمُ الأَنَامِلَ مِنَ الْغَيْظِ قُلْ مُوتُواْ بِغَيْظِكُمْ إِنَّ اللّهَ عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ{119} إِن تَمْسَسْكُمْ حَسَنَةٌ تَسُؤْهُمْ وَإِن تُصِبْكُمْ سَيِّئَةٌ يَفْرَحُواْ بِهَا وَإِن تَصْبِرُواْ وَتَتَّقُواْ لاَ يَضُرُّكُمْ كَيْدُهُمْ شَيْئاً إِنَّ اللّهَ بِمَا يَعْمَلُونَ مُحِيطٌ{120}
119 - Gã ku nan! Kunã son su bã sa son ku, kuma kuna ĩmãni da Littãfi dukaninsa. Kuma idan sun hadu da ku sukan ce "Mun yi ĩmani". Kuma idan sun kadaita sai su cizi yãtsu a kanku don takaici. Ka ce "Ku mutu da takaicinku. Lalle ne, Allah Masani ne ga abin da ke cikin kirãza." 120 - Idan wani alhẽri ya shãfe ku sai ya bakanta musu rai, kuma idan wata cũtar ta shãfe ku sai su yi farin ciki da ita. Kuma idan kun yi hakuri kuma kuka yi takawa, kullinsu bã zai cũtar da ku da kõme ba. Lalle ne, Allah ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa ne.
Wadannan ayoyi suna bayyana tunanin kafirai dangane da musulmine, suna bayyana abinda yake boye a cikin zukatan makiya musulmi na gaba da rashin yarda. Don haka ayoyin suna kashedi wa musulmi da su san cewa kada su zaci cewa don suna kusantan makiya musulunci suna bayyana na masu so, su ma kamar yadda kuke suke ba. Hatta idon a bayyana sun nuna cewa sun amince da addininku, amma a boye suna matukar gaba da ku. Duk lokacinda kuka sami wani ci gaba wannan yana bakanta masu rai. Idan musiba ta same ku kuma su kanyi farin ciki da hakan. Don haka babu mafita sai yin hankali da su, da kuma tsayin daka wajen mu'amala da su. Sanna da kiyaye dokokin Allah, wannan ne zai sa ba zasu iya cutar da ku ba. Daga karshe muna iya daukan darussa daga cikin wadannan ayoyi kamar haka. 1) - Dangantaka tsakanin kasashen musulmi dole ne ta kasance ta mutunta juna, idan ba haka ba to zai zama sanadiyyar kaskanci da wulakanci ga musulmi. 2) - Bai kamata musulmi ya kasance mai saurin yarda da abinda makiyi yake bayyanawa na so da amincewa da shi ba. Dole ne yayi taka tsantsan da su. 3) - A lokacinda makiya suka bayyana kiyayyansu a fili ga musulmi to ya zama dole su ma su bayyana matsayinsu a fili da kuma nuna masu adawa a fili. 4) - Hanyar da makiya suke bi don shiga lamuran musulmi su ne ta kodaitarwa da kuma tsoratarwa, idan musulmi ya ji tsoron Allah kuma ya yi dauriya babu abinda zai same shi daga bangaren makiya. Daga karshe masu sauraro anan ne zamu dasa aya cikin shirimmu na yau, don kurewar lokaci, sai kuma shiri na gaba idan Allah ya kaimu.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 121-125 (Kashi Na 96)
Bismillahir Rahmanir Rahim Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. A yau sharhin namu zai fara ne daga aya ta 121 ta surar Ali Imrana da fatar zaku kasance tare da mu.
To madalla. Da farko bari mu ji wannan aya ta 121 daga surar ta Ali Imarana:
وَإِذْ غَدَوْتَ مِنْ أَهْلِكَ تُبَوِّئُ الْمُؤْمِنِينَ مَقَاعِدَ لِلْقِتَالِ وَاللّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ
“Kuma a lõkacin da ka yi sauko daga iyãlanka kana zaunar da mũminai a wurãren zamadõmin yãki, kuma Allah Mai ji ne, Masani.”
Wannan aya tana bayani ne akan yakin Uhudu da kuma matsalolin da Musulmi suka samu a lokacinsa. Yakin Uhudu dai ya biyo bayan yakin Badar ne wanda aka yi a shekara ta biyu bayan hijirar Maaiki a wani wuri kusa da garin Makka. A yakin Badar mushrikai sun sha kaye kuma Musulmi sun kasha musu mutane da yawa sun kuma kama wasu da dama. A wancan lokaci Abu Sufyan daya daga cikin dattawan Makka ya yi sha alwashin sai ya dauki fansa daga Musulmi saboda haka ne kafiran Makka suka shirya gagarumin yaki mai mahaya dawaki da masu yaki a kasa tare da cikakken shirin kayan yaki da guzuri, suka nufi nbbirnin Madina. Da maaikin Allah ya ji wannan labara sai ya kira taro a masallacinsa don jamaa su yi shawara a kn yanda zasu fuskanci wannan lamari. Dattawa da tsofaffin Madina sai suka ce ya kamata Musulmi su tsaya daga cikin gari su kare gari ga gidajensu, amma matasa majiya karfi da kumaji sai suka ce ya kamata a fita a tinkari maharani a waje da gari. Manzon Allah sai ya tambayi jamaa da suke tare da shi don su bayyana raayinsu a kan wannna lamari sai akasarin suka ce ya kamata a dauki maganar matasan. Ko da yake shi kansa Maaiki ya fi son a tsaya a Madina kada a bar gari don a tari abokan gaba daga waje, amma saboda karfafa wa matasan nan guiwa sai ya yarda a fita kamar yanda mutane suka zaba. Ranar Jumaa da ta zagayo sai Maaiki ya sanar da jamaa baki daya da abin da ake ciki da shawarar da aka yanke. Bayan salla mutane 1000 daga Muhajirun da Ansar suka fita tare da Annabi suka nufi dutsen Uhudu inda suka ja daga. Amma kafin su isa mutane 300 sun ja da baya sun koma gida saboda haka da mutane 700 manzon Allah ya isa wurin yaki. Abokan gaba sun doso Madina sai runduna biyu suka fuskanci juna a bakin dutsen Uhudu kuma ba jima ba yaki ya fara, Musulmki suna kabbara: Allahu akbar, Allahu akbar, kafirai kuma suna kada ganguna suna busa. Sojojin Musulmi sai suka afka wa sojojin Kuraishawan kuma nan da nan sai kafirai suka rikice wasu suka arce. Wasu Musulmi sun dauka da wannan fatattakar farko da suka yi wa kafirai nasara ta kamala saboda haka sai suka bar wuarren da Annabi ya tsai das u a filin yaki, suka kama dibar ganima suna farin ciki. Ba zato ba tsammani sai wasu sojojin Kuraishawa suka lababa suka fito wa Musulmi ta baya. Wannan gafala da rashin bin umarnin Annabi da wasu Musulmi suka yi ya jawo kasha sojojin Musulmi da raunata wasu, wasu kuma suka gudu daga bakin daga. A wannan lokaci kuma sai aka yada jita-jitar cewa an kashe Annabi wanda kuma hakan sai ya kara wa wasu daga mayakan Musulmi tsoro a zukata kuma hakan ya sa suka tsere daga fagen fama. Saboda haka yakin da ya faro da nasarar rundunar Musulmi, ya baci musu daga karshe. Wannan aya tana koyar da darusa kamar haka: 1-Aikin da Allah ya dora wa Annabi (Ts.) bai takaita da isar da sakon Ubangiji kadai da, ya ma hada da kafa tsarin gudanar da wannan sako da tinkarar makiya addini, kuma sauran Musulmi su ma ba ayuyukan da aka dora musu da daidaku kamar salla da azumi kadai ne ya wajaba a kansu, aikinsu ne su kare wannan addini da alummar Musulunci. 2-Duk da muhimmancin kula da iyali da biyan bukatun matar mutum da yayansa, amma fafutukar kare addini ya fi muhimmanci, saboda mai zuwa fagen yaki zai baro iyalansa ne a gida, kuma hala ya yi shahada kamar yanda wasu sahabban Annabi suka yi shahada a Uhudu.
Yanzu kuma bari muji ji aya ta 122 da ta 123 na wannan sura ta Ali Imran:
إِذْ هَمَّت طَّآئِفَتَانِ مِنكُمْ أَن تَفْشَلاَ وَاللّهُ وَلِيُّهُمَا وَعَلَى اللّهِ فَلْيَتَوَكَّلِ الْمُؤْمِنُونَ{122} وَلَقَدْ نَصَرَكُمُ اللّهُ بِبَدْرٍ وَأَنتُمْ أَذِلَّةٌ فَاتَّقُواْ اللّهَ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ{123}
“A lõkacin da kungiyõyi biyu daga gare ku suka yi niyyar su karye, kuma Allah ne Majibincinsu, don haka, ga Allah mũminai sai su dogara. Kuma lalle ne, hakĩka, Allah Yã taimake ku a Badar, alhãli kuwa kunã mafiya rauni, sabõda haka ku bi Allah da takawa tsammãninku, kuna gõdewa.”
Wasu jamaa daga cikin kabilun Aws da Khazraj wadanda sun tafo yaki tare da Annabi, da suka ga yawan rundunar abokan gaba sai tsoro ya kama su har ma su ka yanke shawaarr zasu koma gida amma da taimakon ALLAHda kuma bayanan Maaiki sai suka sake daura niyar yaki kuma Allah ya kwace su daga yaudarar Shedan. Wadannan ayoyi suna ajwo hankalin sahabbai da sauran Musulmi cewa, ‘Ku da ku kuka sami taimakon Ubangiji a yakin Badar duk da cewa mayakan ku basu da yawa, to me ya sa a wannan yaki kuke kashe jiki ba ku tsayawa kyam domin kare addini. Kada ku ji tsoron abokan gaba, ku ji tsaoron saba wa umarnin Allah Kada ku dogara ga yawanku ko karfinku, ku dogara ga Allah ku yi tawakkali gare shi, kuma idan kuka yi haka zaku samu rahamar Allah da niimominsa.’ Wadannan ayoyi suna dauke da darussa kamar haka: 1-ALLAH ba ya kyale muminai ba tare da taimako ba, ya na jibintar lamarinsu da kare su daga sharrin abokan gaba. 2-Tsoron yaki shi yake kasha jikin mutane har ma ya sa su gudu daga fagen fama, kuma ba maganin wannan sai karfafa imani da tawakkali ga Ubangiji. 3-ALLAH madaukakin sarki ya san ayyukanmu da ma da abinda zukatanmu suka kulla. A cikin wadannan ayoyi mun ji yanda Allah ya sanar da manzonsa niyar da wasu jamaa su ka yi cewa zasu fasa yakin su koma gida. 4-Wajibi ne a gode wa niimomin Allah da hanayar yin takawa da kiyaye dokokinsa, idan ko ba haka ba niimomin zasu jawo wa mutum girman kai da jiji-da-kai da kuma sa abokin gaba ya galaba a kan mutum.
Yanzu kuma bari mu ji aya ta 124 da 125.
إِذْ تَقُولُ لِلْمُؤْمِنِينَ أَلَن يَكْفِيكُمْ أَن يُمِدَّكُمْ رَبُّكُم بِثَلاَثَةِ آلاَفٍ مِّنَ الْمَلآئِكَةِ مُنزَلِينَ{124} بَلَى إِن تَصْبِرُواْ وَتَتَّقُواْ وَيَأْتُوكُم مِّن فَوْرِهِمْ هَـذَا يُمْدِدْكُمْ رَبُّكُم بِخَمْسَةِ آلافٍ مِّنَ الْمَلآئِكَةِ مُسَوِّمِينَ{125}
“A lõkacin da kake cewa ga mũminai, "Shin bai ishe ku ba, Ubangijinku Ya taimake ku da dubu uku daga malã'iku saukakku?" "Na'am! Idan kuka yi hakuri, kuma kuka yi takawa, kuma suka zo muku da gaugawarsu, irin wannan, Ubangijinku zai kãre ku da dubu biyar daga malãiku mãsu alãma.”
Wadannan ayoyi suna bayyana alkawarin Allah na bai wa muminai nasara da aiko da malaiku a fagagen da ake yakin jihadi domin kare addinin Ubangiji da daukaka kalmarsa. Bisa hakika mu mutane masu halittar jiki ba zamu iya sanin amlaiku wadanda sub a jiki ne das u ba, amma imanin da muka yi da Alkurani shi ya sa muka yi imani da samuwarsu. Malaiku sun halarci yakin Uhudu domin bai wa sojojin Musulunci karfin zuciya da kuma halartar tasu ta sa ana ganin rundunar Musulunci ta kara yawa, a gefe guda kuma ta jefa tsoro a zukatan abokan gaba. Za mu iya famintar abubuwa muhimmai daga wadannan ayoyi guda biyu: 1-Shi mumini wajibi ne ya dogara ga Allah saboda dukkanin halittu cikin su har da malaiku, mayakan Allah ne saboda haka tilas abokan gaba su ji tsoron yin gaba-da-gaba da rundunar Musulunci domin kuwa bad a Musulmin ne yake fito-na-fito ba, da Allah ne suke yaki. 2-A mahangar addini ga rayuwa, rayuwar mutune tana da alaka da malaiku. 3- A lokacin da mayakan Musulunci suka yi tsayin daka Allah ya aiko musu da taimako na gaibi wato na boye. 4-Ana bukatar Musulmi su kiyaye dokokin Allah wato sui yi takawa, har a wajen yaki, saboda haka wajibi ne sojojin Musulunci su zama masu takawa a ko da yaushe. 5-Malaikun Allah suna aiki a dukkan sassan talikai kuma ko wace jamaa ta malaiku tana gudanar da wani aiki na musamman, kuma wasu daga cikinsu shi ne kare sojojin Musulunci.
To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shrii na gaba da yardar Allah. zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar Al Imran. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 126-131 (Kashi Na 97)
Bismillahir Rahmanir Rahim Assalamum alaikum jamaa. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannun ka mai Sanda, Shirin da uya ke kawo muku bayanai a kan wasu ayoyi daga Alkurani mai girma. A shirin da ya gabata mun ji bayanai ne akan ayoyin Surar Al Imrana daga aya ta 121 zuwa ta 125, yanzu kuma zamu dora daga aya ta 126, sai ku biyo mu sannu a hankali.
To madalla. Bari mu fara da sauraron aya ta 126 da ta 127.
وَمَا جَعَلَهُ اللّهُ إِلاَّ بُشْرَى لَكُمْ وَلِتَطْمَئِنَّ قُلُوبُكُم بِهِ وَمَا النَّصْرُ إِلاَّ مِنْ عِندِ اللّهِ الْعَزِيزِ الْحَكِيمِ{126} لِيَقْطَعَ طَرَفاً مِّنَ الَّذِينَ كَفَرُواْ أَوْ يَكْبِتَهُمْ فَيَنقَلِبُواْ خَآئِبِينَ{127}
"Allah kuwa bai sanya shi taimako ba sai don albishir a gare ku, kuma don zukatanku su kwanta da shi. Amma fa ba wata nasara sai daga Allah Mabuwayi, Gwani. (Wannan taimako) don ya karya lagon wani bangare ne daga wadanda suka kafirta, ko kuma ya wulakanta su, har su juya da baya suna tababbu."
Kamar yanda muka fadi a shirin da ya gabata, daya daga cikin taimakon Allah da ake samu a fagen fama shi ne sauko da malaiku. Su malaiku ba ga annabawa kadai suke sauka ba, har ma da muminai masu tsayin daka, domin tabbatar da zukatansu da karfafa musu fatar samun nasara da kara musu himma da karfin guiwa. Sabanin yanda Shedan yake kokarin kashe guiwar muminai a lokacin da suke yaki da kafirci da bata, su kuma malaiku suna sanyaya zukatan masu imani suna kuma kwantar musu da hankali da basu natsuwa, har ma suna cusa musu kumajin murkushe abokan gaba ko kuma alal akalla su dandana musu dacin faduwa da rashin galaba ta yadda zasu fasa kawo wani farmaki a nan gaba. Wadannan ayoyi suna kunshe da darusa kamar haka: 1-Duk wata magana ko rubutu wadanda zasu karayar da zukatan mayakan Musulunci tamkar kira daga Shedan, haka nan duk magana ko aiki da zasu tabbatar da natsuwa da albishirin nasara da sojoji kamar daga wahayin Ubangiji suka. 2-Duk da cewa Allah madaukakin Sarki yana da ikon bai wa Musulmi nasara a kowane yaki amma bisa tsarin hikima ya ke aiki saboda haka idan Miusulmi suka yi kasala ba makawa zasu sha kaye. 3-Hadin kai da karfi da jaruntaka dole ne su kasance ta yadda abokan gaba kada su sa ran kutsawa da samun galaba a kansu, kuma duk lokacin da suka nemi yi wa Musulmi hawan kawara su gane cewa su ne da kaskanci da kasawa.
Yanzu kuma sai aya ta 128 da ta 129 daga surar Al-Imrana.
لَيْسَ لَكَ مِنَ الأَمْرِ شَيْءٌ أَوْ يَتُوبَ عَلَيْهِمْ أَوْ يُعَذَّبَهُمْ فَإِنَّهُمْ ظَالِمُونَ{128} وَلِلّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الأَرْضِ يَغْفِرُ لِمَن يَشَاءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَاءُ وَاللّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ{129}
"Ba ka da ikon wani abu game da alamarin. Ko Allah ya yafe musu, ko ya yi musu azaba, hakika su dai azzalumai ne. Kuma abin da yake cikin sammai da abin da ya ke cikin kasa na Allah ne.Yana yin gafara ga wanda ya so. Ya kuma yi azaba ga wanda ya so. Allah kuma mai gafara ne mai jin kai."
Littafin tafsiri sun yi bayanin cewa a lokacin yakin Uhudu, duwatsun da mayakan kafirai suke jefawa suka sami Manzon Allah suka karya masa hakorinsa mai albarka har jini ya yi ta zuwa. Da haka ya faru sai Maaiki (s.) ya ce: 'Ya ku jamaa, ta yaya zaku sami rabauta?' Da ya fadi haka sai wannan aya ta sauka tana tuna mas ada cewa: Ya kai Annabi ba a dora maka nauyin rabautar mutane ba, aikin ka shi ne isar da sako gare su, wanda ya so ya karbe shi ya rabauta, wanda kuma ya so ya ki karba kuma Allah ga wadanda suka juya wa sakonsa baya, ko dai ya yi musu ludufi ya gafarta musu ko kuma azabta su. Wannan aya tana cikin alamun masu tabbatar da cewa Annabi da Alkurani suna bisa gaskiya, wato babu wani nauyin da aka dora wa Annabi dangane da bai wa jamaa lada ko horo. Idan da Annabi ba maaikin Allah ba ne da ba zai bayyana wannan magana ta Allah kuma da shi ba mai gaskiya ba ne dab a zai isar da irin wadannan ayoyi masu hana shi fada ko yin wani abu ba, saboda wadannan ayoyi suna nuna iyakar ikonsa na manzanci wanda ya nuna cewa ba shi da hakkin gafarta wa mutane ko azzabtasu. Wadannan ayoyi suna koya mana darusa: 1-Annabi da kuma jagororin addini da suka zo a bayansa an umarce su ne da aikata nauyin da aka dora musu ba sakamakon da aikin zai kawo ba, wato nasara bata hannunsu. Wajibi ne su fadi kalmar gaskiya jamaa su ji, amma ba aikinsu ne su su sa mutane su karbi maganarsu ba kuma sakamakon da Allah zai yi wa mutane bay a wuyansu. 2-Hanyar tuba bata dogara da wani mutum ko yanayi ba, hatta masu gudu daga fagen daga ko ma kafiran yaki idan suka tuba suka nemi gafara Ubangiji zai karbe su ya gafarta musu. 3-Yin gafara ko yin azaba ya takaita ne ga Allah, kuma ko ceton da waliyansa suke yi ma sai da izininsa za su yi shi. 4-Musabbin azaba da Allah zai yi wa bayinsa shi ne zalunci da kafirci da butulcin niimomin Allah da suke yi.
Yanzu kuma bari mu saurarai aya ta 130 da 131.
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ لاَ تَأْكُلُواْ الرِّبَا أَضْعَافاً مُّضَاعَفَةً وَاتَّقُواْ اللّهَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ{130} وَاتَّقُواْ النَّارَ الَّتِي أُعِدَّتْ لِلْكَافِرِينَ{131}
"Ya ku wadanda kuka ba da gaskiya, kada ku ci riba ninkin ba ninkin. Kuma ku ji tsoron Allah don ku rabauta. Kuma ku ji tsoron wuta wadda aka tanada don kafirai"
A addinin Musulunci yakin jihadi da kokari a kan tafarkin Allah ba a raba shi da alamura na tattalin arzkiki da zamantakewa. Saboda haka ne a tsakiyar ayoyin da suka maganna akan yakin Uhudu sai aka shigar da batun cin riba wanda yana cikin matsalolin alummar bilAdam take fama da su. An bayyana haramcin riba ta hanyoyi daban daban: da farko an ambaci muminai sanna ana yi hani a kan cin riba domin a nuna cewa imani ba ya tafiya tare da cin riba; a gaba kuma Allah Madaukakin sarki ya hori muminai da su ji tsoron Allah su nisanci riba, wato tsoron Allah ya yi hannun riga da cin kudin ruwa; a wani wuri kuma ya umarci mutane da su nisanci riba saboda su sami rabauta, wato dai ana samun rabauta ne a duniya da lahira idan ba a cin riba. Malaman addini sun bayyana nauoin riba filla-filla a littfansu na fikihu, amma abin da wannnan aya taakidi a kansa shi ne hani nda haramcin dukkan nauoin riba wanda yake sa dukiya ta taru a ahnnayen mutane kalilan saura kuma suna nan cikin talauci da wahala. Alummar da take yakin abokin gaba zata iya cin nasara ne kawai idan mutanenta suna kauta da tallafawa da ihlasi, ba masu bauta wa dukiya ba. A wannan aya muna iya koyon darussa kamar haka: 1-Takawa ko tsoron Allah ba a cikin ayyukan ibada kadai ake yinta ba, har ma a harkokin kudi da tattalin arziki dole ne a kiyaye takawa. 2-Lafiyayyen tsarin tattalin arziki yana samuwa ne cikin jamaa masu imani da takawa da kiyaye dokokin Ubangiji. 3-Ba dukiya da abin duniya ne suke kawo rabauta da kyakkyawar rayuwa ba, mutum yana rabauta ne idan ya kare hakkokin jamaa. 4-Cin riba wani nau'i ne kafircewa niimomin Allah wato yin butulci kuma Musulmi mai cin riba shi ma a a yi masa azabar wuta.
Jamaa masu sauarre a na zamu dakata sai shiri na gaba zaku ji mu da ci gaba shirin Hannunka mai sanda. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 132-136 (Kashi Na 98)
Bismillahir Rahmanir Rahim Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. A yau sharhin namu zai fara ne daga aya ta 132 ta surar Ali Imrana da fatar zaku kasance tare da mu.
To madalla. Da farko bari mu ji wannan aya ta 132 da ta 133 na wannan sura ta Ali Imaran:
وَأَطِيعُواْ اللّهَ وَالرَّسُولَ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ{132} وَسَارِعُواْ إِلَى مَغْفِرَةٍ مِّن رَّبِّكُمْ وَجَنَّةٍ عَرْضُهَا السَّمَاوَاتُ وَالأَرْضُ أُعِدَّتْ لِلْمُتَّقِينَ{133}
“Kuma ku bi Allah da Manzo don a yi muku rahama. Kuma ku yi gaggawa zuwa neman gafara daga Ubangijinku da kuma zuwa aljanna wadda fadinta yake daidain da sammai da kasa, an tanade ta don masu tsoron Allah.”
Bayan Ubangiji ya yi magana a kan yakin Uhudu da haramcin riba ko kudin ruwa a ayoyin dfa suka gabata, a wadasnnan kuma ya na horon Musulmi da aikata abubuwa biyu. Na farko shi ne cikakkiyar biyayya ga umarnin Allah da Maaikinsa wanda shi ne sharadin samun rahama da taimakon Ubangiji kuma rashin biyayya shi ne ya jawo faduwa kamar yadda mayakan Musulunci suka yi rashin nasara a yakin Uhudu. Na biyu kuma shi ne yin gaggawa wajen aikata alheri wa wasu wanda kum ahakan yake kawo gafarta zunnubai da samun aljanna. Abin day a janyo wa mayaka a Uhudu shi gaggawar tara ganima, gay an kasuwa kuma abin da yake jawo cin riba shi ne kwadayin tara dukiya, amma Alkurani yana kiran muminai da su yi gaggawar neman gafarar Ubangiji da da rahamarsa wanda yin haka zai sharefagen shiga aljanna wacce fadinta kamar fadin sammai da kasa, wacce kuma tsoron Allah shi ne sharadin shigarta. Wadannan ayoyi suna koyar da mu wadannan darusa: 1-Mutum yana shiga fagen rahamar Allah jinkansa ne yayin da shi ma yake jinkan marasa karfi kuma bay a karbar kudin ruwa idan ya bada bashi. 2-Bai kamata muminai su tsaya wuri guda ba bu ci gaba ba, kamata ya yi a kullum suna cikin himma da neman karuwa da yin gasar aikata ayyukan alheri masu anfani ga alumma.
Sai aya ta 134:
الَّذِينَ يُنفِقُونَ فِي السَّرَّاء وَالضَّرَّاء وَالْكَاظِمِينَ الْغَيْظَ وَالْعَافِينَ عَنِ النَّاسِ وَاللّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ{134}
“Su ne wadanda suke ciyarwa cikin halin yalwa da matsi da masu hadiye fushi da masu yafe wa mutan. Allah kuwa yana son masu kyautatawa..”
Wannan aya kuma tana bayani kan hanyoyin samun gafara. Yafe wa mutane idan sun yi wa mutum laifi da kuma nisantar fushi da gaba muhimman hanyoyi ne na samun gafarar Allah amma kafin Allah ya ambaci gafara sai da ya ambaci yafe wa mutane bashi da taimaka wa marasa karfi a cikin alumma a matsayin abubuyw ada suke buda wa mutum kofar samun gafarar Ubangiji. Akasarin mutane suka tsammanin cewa masu hali ne kawai suke iya kauta da taimako, amma ba haka abin ya ke ba. Yawayawan masu hali wadanda suke kyauta zaka samu cewa kafin su sami dukiyar ma suna damuwa da mabukata kuma yana taimaka musu gwargwadon hali. Saboda haka ne wannan aya take cewa muminai ko suna da walwala ko kuma basu da ita suna kyauta da ciyarwa. Wannan aya tana koyar da mu wadannan darusa: 1-Ciyar da dukiya yana bukatar mutun ya zama mai zuciyar kyauta ne ba mallakar tarun dukiya ba. Da yawa ana samun masu kudi amma marowata, da marasa walwala amma masu kayuta. 2-Mai tsoron Allah ko takawa ba wai zai kaurace wa jamaa ba ne, zai rayau tare da su ne, yana hulda da taimakawa da dukiya da kyawawan halayensa. 3-Wanda yake son ya zama abin kaunar Allah dole ne ya bada dukiyarsa ya kuma nisanci nuna wa jama kiyayya da mugun hali.
Sai mu saurari aya ta 135:
وَالَّذِينَ إِذَا فَعَلُواْ فَاحِشَةً أَوْ ظَلَمُواْ أَنْفُسَهُمْ ذَكَرُواْ اللّهَ فَاسْتَغْفَرُواْ لِذُنُوبِهِمْ وَمَن يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلاَّ اللّهُ وَلَمْ يُصِرُّواْ عَلَى مَا فَعَلُواْ وَهُمْ يَعْلَمُونَ{135}
"Da kuma wadanda suka aikata mummunan aiki ko suka cuci kansu su kan tuna da Allah sannan su nemi gafara game da laifukansu, ba kuwa mai gafarta laifuka sai Allah, ba kuma za su ci gaba bisa abin da suka aikata ba, alhali suna sane."
Wasu sun dauka mumini shi ne wanda sam-sam baya zunubi ko kuskure amma ko masu takawa ma sukan yi wadannan kurakurai sai dai bambamcinsi da sauran mutane shi ne su da wuri suke tuba su bar mummunan aiki, saboida sun san cewa Ubangiji mai gafara ne da karbar tuba. Banbanci tsakanin masu mike kafa cikin sabo da su muminai da suke kuskure shi ne na farkon suna sabo a shirye ammma muminai dabaiar danAdamtaka ta fizgarsu ba tare da zato ba kuma nan take sai su koma ga Allah su tuba. Darussa: 1-Takawa ba tana nufin dawwamammiyar kariya daga zunibi ba, abinda take nufi shi ne gaggauta yin tuba da rashin dogewa cikin sabo. 2-Abin da ya fi sabo hadari shi ne gafala daga munin sabo da rashin tunawa da tuba balle ma mutum ya yi. 3-Zunubi shi ne zalunci mafi muni da mutum zai yi wa ruhin da Allah ya sanya a cikin jikin mutum.
Yanzu kuma sai aya ta 136:
أُوْلَـئِكَ جَزَآؤُهُم مَّغْفِرَةٌ مِّن رَّبِّهِمْ وَجَنَّاتٌ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا وَنِعْمَ أَجْرُ الْعَامِلِينَ{136}
"Wadancan sakamakonsu shi ne gafara dafga Ubangijinsu da aljannoni (wadanda) koramu suke gudana ta karkashiunsu, sun madawwama a cikinsu. madalla da ladar masu aiki (na gari)."
Aya ta 133 ta hori muminai da su yi gaggawar neman gafarar Allah da kuma aljanna. Ayoyi na 134 da 135 kuma sun bayyana hanyoyin samun gafarar, wato ciyar da dukiya ga masu bukata, da yin alheri da kuma yafe wa mutane da tuba daga zunubbai. Mutanmen da zasu sami rahamar Ubangiji da gafararsa su ne masu takawa, wato bayan an jarrabesu da yin zunubi sun tuba sun tsarkaka daga zaunubi, kum sakamakonsu shi ne aljanna wadda fadinta baya misaltuwa. Wani abin lura a nan shi ne wadannan ayoyin suna karewa ne da kalmomin 'masu takawa', 'masu kautatawa' da 'masu aiki' kuma wannan ya nuna cewa takawa ko tsoron Allah ba yana nufin mutum ya kauracewa jamaa ya ce ya dukufa da ibada kadai ba, a a mai takawa yana cudanya da jamaa, yana aikata alheri. Darussa: 1-Fata da tsammani kadai ba zasu kai mutum ga ludufin Ubangiji ba, dole ne sai an aikata kyakkyawan aiki tare da kyakkyawar niya. 2-Idan dai mutum bai tsarkaka daga zunubbai ba ba zai cancanci shiga jamaar salihan mutane masu tsarki kuma mutanen aljanna ba.
To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar Al Imran. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 137-142 (Kashi Na 99)
Bismillahir Rahmanir Rahim Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. A yau sharhin namu zai fara ne daga aya ta 137 ta surar Ali Imrana.
To madalla. Da farko bari mu ji wannan aya ta 137 da ta 138 na wannan sura ta Ali Imaran:
قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِكُمْ سُنَنٌ فَسِيرُواْ فِي الأَرْضِ فَانْظُرُواْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُكَذَّبِينَ{137} هَـذَا بَيَانٌ لِّلنَّاسِ وَهُدًى وَمَوْعِظَةٌ لِّلْمُتَّقِينَ{138}
"Lalle ne misãlai sun shũde a gabãninku, sai ku yi tafiya a cikin kasa sa'an nan ku dũba, yãyã karshen mãsu karyatãwa ya kasance. Wannan bayãni ne ga mutãne, kuma shiriya ce da wa'azi ga mãsu takawa (wato tsoron Allah).”
Daya daga salon da Alkurani ya ke bi wajen shiriyarwa da yi wa mutane tarbiya shi ne yin ishara ga tarihin wanadanda alummomin da suka gabata. Kafin wanna zamani namu alummomin da yawa sun rayu sunn shude kuma sanin tarihinsu da yanda suka kare da rayuwar duniya babban darasi ne a garemu masu rayuwa a yanzu. Dalili kuwa shi ne rayuwar duniya tana tafe ne bisa wasu tabbatattun kaidoji ko sunnonin da Allah ya tsara kuma sanin wadannan kaidoji ba ya yiwuwa ba tareda sanin tarihin dan Adam ba. Saboda haka ner Alkurani mai girma ya ke umurtan mu da yin tafiya a cikin kasa da kuma yin nazari gandane da tarihin magabata ta yadda idan mun yi dubi da idon basira zamu gane ayyuakan alheri ko na sharri da suka aikata da kuma sakamakon wadannan ayyuka, domin mu yi koyi da ayyukansu na kwarai kuma kada mu maiamita mugayen ayyuakan wadanmda suka gabata. Wadannan ayoyi suna koyar da mu wadannan darusa: 1-Musulunci ya na umurni da tafiya cikin kasashe musamman wuraren tarihi inda tsofaffin dauloli suka yi zamani, kuma a dubi wuraren tare da yin tunani da daukan darasi. 2-Abubuwan da suke kawo daukaka ko kaskanci basu sauya wa a duk tsawon tarihi kuma muna bukatar sanin wadannan abubuwa a rayuwarmu ta yau. 3-Ko da yake an sauko da Alkurani ne don shiryar da dukkan mutane amma masu tsarki ne kawai zasu amsa kiransa su sami shiriya.
Sai mu saurari aya ta 139:
وَلاَ تَهِنُوا وَلاَ تَحْزَنُوا وَأَنتُمُ الأَعْلَوْنَ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ{139}
" Kuma kada ku yi rauni, kuma kada ku yi bakin ciki, alhãli kuwa kũ ne mafiya daukaka, idan kun kasance mãsu ĩmãni."
Faduwar da rundunar Musulmi ta samu a yakin Uhudu ta sa su karaya sai aka saukar da wanna aya domin karfafa musu guiwa don kada su yanke kauna saboda kawai rashin nasara a lokaci guda wanda shi din ma ya faru ne saboda sun saba umarnin da akja basu. A maimaon haka ya kamata su karfafa imaninsu su dane cewa su ne zasu sami nasara daga karshe. A cikin ayoyin da suka gabata an batun muhimmancin lura da sunnar Allah wato kaidojin rayuwar alummu da Allah ya sanya da yanda suka gudana a alummomin baya. Wannan aya ta bayyana daya daga cikin wadannan kaidoji wanda kuma mayakan Musulmi sun ga aikinta kiri-kiri. Wannan kaida kuwa it ace: Abu mafi muhimmanci da zai bai wa wata alumma daukaka shi ne imani da A.. da yin biyayya ga manzanninsa, saba wa umarnin Allah da na Maaikinsa suna jawo faduwa da kaskanta, kuma wannan ya bayyana a filki a yakin Uhudu. A wannan aya muna iya koyon darussa kamar haka: 1-Imani da Allah dalili ne na daukaka, ba a lahira kadai ba, har ma a nan duniya alummomin da suke da imani da dogaro da Allah suna samun daukaka a kan saura. 2-Bai kamata faduwa ko rashin nasara ya sa karaya da ja da baya ba, ya kamata hakan ya zama abin izna da daukar darasi da shirya wa gaba.
Yanzu kuma sai aya ta 140 da ta 141:
إِن يَمْسَسْكُمْ قَرْحٌ فَقَدْ مَسَّ الْقَوْمَ قَرْحٌ مِّثْلُهُ وَتِلْكَ الأيَّامُ نُدَاوِلُهَا بَيْنَ النَّاسِ وَلِيَعْلَمَ اللّهُ الَّذِينَ آمَنُواْ وَيَتَّخِذَ مِنكُمْ شُهَدَاء وَاللّهُ لاَ يُحِبُّ الظَّالِمِينَ{140} وَلِيُمَحِّصَ اللّهُ الَّذِينَ آمَنُواْ وَيَمْحَقَ الْكَافِرِينَ{141}
" Idan wani mĩki ya shãfe ku, to, lalle ne, wani mĩki kamarsa ya shãfi mutãnen, kuma wadancan kwãnaki Muna jujjuya su a tsakãnin mutãne dõmin Allah Ya san wadanda suka yi ĩmãni kuma Ya sãmi mãsu shahãda daga gare ku. Kuma Allah ba Ya son azzãlumai. Kuma dõmin Allah Ya tsarkake wadanda suka yi ĩmãni,kuma Ya hallakar da kãfirai."
Wadannan ayoyi suna koyar da wat sunnar Allah ko kuma kaidar tsrain rayuwa da Allah ya kafa wannan kaida kuwa it ace: Ba wanda yayanin rayuwa zai tabbata masa har abada ba sauyi domin kuwa baki-dayan rayuwa tan an duniya kewayawa take yi, dadi yana maye gurbin rashin dadi, kuma ana cikin samun nasara sai ka ga faduwa ta shigo. Kuma Allah ya tanadi wannan sauyi da samu da rashi ne domin fito da hakikanin halayen mutane kuma domin a tace a ga mumini na kwarai, a kuma bayyana munafukai ko masu raunin imani. Hakan kuma yana nuna wa wadanda basu da tsarkin zuciya cewa yana yiwuwa mutum ya tsakake zuciya ya yi aiki saboda Allah. Wadannan ayoyi suna rarrashin Musulmi tare da karfafa musu guiwa cewa: Ko da yake kun sami koma baya ayakin Uhudu amma ai kun sami nasara a yakin Badar, idan kun sami raunuka a wannan yakin ai abokan gabanku ma sun sami raunuka saboda haka ku sani cewa abin dab a dadi ba ku kadai yakie samu ba kuma ba kullum a ke kan abu daya, sai dai ku ke da nasara da kyakkayawan karshe alhali kafirai sun kama hanyar gushewa ne. Akwai darusan a wadanna ayoyi: 1-Jarrabawa tana zuwa ta hanyar abubuwa marasa dadi kamar yaki da sauransu kuma wannan yana faruwa a tsawon tarihi domin sunna c eta Allah. 2-Nasarar da kafirai suka samu jarrabawa ce ga muminai ba wai alama ce ta cewa Allah yana kaunar kafiran ba. 3-Yakin jihadi maauni ne mai nuna mutane masu tsakin zuciya da imani. Ko kusa mumini baya karaya a fagen yaki domin kuwa idan ma an kasha shi ne to shahada zai yi kuma ita kanta shahada wata rabauta ce a gareshi.
Sai mu saurari aya ta 142:
أَمْ حَسِبْتُمْ أَن تَدْخُلُواْ الْجَنَّةَ وَلَمَّا يَعْلَمِ اللّهُ الَّذِينَ جَاهَدُواْ مِنكُمْ وَيَعْلَمَ الصَّابِرِينَ{142}
"Ko kun yi zaton za ku shiga Aljanna ne alhãli har yanzu Allah bai bãda sanin wadanda suka yĩ jihãdi daga gare ku ba, kuma Ya san mãsu hakuri? "
Wannan aya ma kamar ayoyin da suka gabace ta, tana bayyana cewa imani yana sa mutane su tafi fagen yaki da karfin jikinsu domin kare addini da kasar Musulun ci, saboda haka kada Musulmi su dauka da zara mutum ya bayyana imani a zahiri, ko m ahar da aikata ayyukan ibada kamar salla da azumi, shi ke nan sai aljanna. A fagen fama ne ake tantancewa a ware masu imanin gaskiya kuma suke shirye su kare addini daga wadanda imaninsu a baki ne kawai bai kafu a zukatansu ba. Akwai abin koyo a wadannan ayoyi: 1-A nisanci burace-buracen masu yawa wadanda kuma suke jawo jin isa kuma da karshe a gamu da karaya. 2-Da aiki ne ana samun aljannna bad a daawar imani ba. 3-Ba fagen yaki ne kadai ake bukatar hakuri da jihadi ba; a kullum mumini yan acikin yaki da Shedan da shaawace-shaawacen zuciya da kuma hakuri wajen aikata umurninn Ubangiji.
To jamaa da haka ne zamu dakata a shirin Hannunka Mai Sanda. Sai shiri na gaba. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 143-148 (Kashi Na 100)
Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. A yau sharhin namu zai fara ne daga aya ta 143 ta surar Ali Imrana da fatar zaku kasance tare da mu.
To madalla. Da farko bari mu ji wannan aya ta 143 na wannan sura ta Ali Imaran:
وَلَقَدْ كُنتُمْ تَمَنَّوْنَ الْمَوْتَ مِن قَبْلِ أَن تَلْقَوْهُ فَقَدْ رَأَيْتُمُوهُ وَأَنتُمْ تَنظُرُونَ{143}
“Hakĩka kun kasance kuna bũrin mutuwa tun a gabãnin ku hadu da ita, to lalle ne kun gan ta, alhãli kuwa kuna kallo.”
A yakin Badar Musulmi sun sami cikakkiyar nasara wasu mayansu kuma sun yi shahada. Wasu Muslmi suka ce: ina ma da mu ma mun yi shahada a Badar, amma a yakin Uhudu da suka mga alamun rashin nasara sai suka tsere suka bar maaikin Allah fagen yaki. Wannan aya tana laifanta irin wadannan mutanbe, da cewa: saboda me a lokacin da ake bukatar aiki da turjiya har ma da bad a rayuka domin kare addini suka gudu suka gaza wajen kare addinin Allah da Maikinsa? Wannan aya tana koya mana: 1-Kada buri ya yaudare mu saboda bamu san me zai faru ba idan aka je ga aiki, ba mu san abin da zamu yi ba idan mun fuskanci jarrabawar Ubangiji. 2-Masu daawar imani suna da yawa amma wadanda suke a shirye su kare addini ko da zasu rasa rayukansu kalilan ne.
Sai mu saurari aya ta 144:
وَمَا مُحَمَّدٌ إِلاَّ رَسُولٌ قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِهِ الرُّسُلُ أَفَإِن مَّاتَ أَوْ قُتِلَ انقَلَبْتُمْ عَلَى أَعْقَابِكُمْ وَمَن يَنقَلِبْ عَلَىَ عَقِبَيْهِ فَلَن يَضُرَّ اللّهَ شَيْئاً وَسَيَجْزِي اللّهُ الشَّاكِرِينَ{144}
" Kuma Muhammadu bai zamo ba face manzo, kuma lalle ne manzanni sun shũde a gabãninsa. Ashe idan ya mutu ko kuwa aka kashe shi, zã ku jũya baya ku koma kafirci? To, wanda ya jũya baya ya koma kafirci, bã zai cũci Allah da kõme ba. Kuma Allah zai sãka wa mãsu gõdiya”
Daga cikin abubuwa da suka faru a lokacin yakin Uhudu akwai batun jita jita da ak yada cewa Annabin rahama (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da alayensa) ya yi shahada. Raunin da ji a lokacin da abokan gaba suka jefo dutse ya same shi ya sa jinni ya yi ta zuba a fuskarsa mai albarka. Nan take wani makiyi sai ya daga murya ya ce: ‘An kashe Muhammadu!’ Wannan jita jita ta dadada rayukan kafirai ta kuma kara musu karfin guiwa, a gefe guda kuma ta jawo wa wasu daga cikin mayakan Musulmi sun karaya har ma sun gudu daga filin daga. Amma wasu sahabbai kuma sai suka daga murya suka ce: ‘To idan ba Muhammadu ai hanyar Muhammadu da Ubangijisa tana nan, don me ku ke guduwa?’ Wannan aya tana cewa muminai, ai kafin wannan annabinku annabawa da yawa sun zo, to bayan mutuwarsu mabiyansu sun bar addini ne, balle ku ce idan Annabi Muhammadu ya mutu sai nan take ku rikice ku fara tunanin guduwa? Darussa: 1-Kamar vsauran mutane annabawa su ma suna rayuwa ne karkashin kaidar dabi’a mai iko da rayuwa da mutuwa kuma ba zasu tabbata har abada ba. 2-Rayuwar annabi ta ke da iyaka, ba tafarkinsa ba, kuma mu Allah muke bautawa ba mutum ba saboda haka ba zamu bar addini domin Annabi ya mutu ko ya yi shahada ba. 3-Barin mutane addini ba zai cutar da Allah ba domin kuwa bas hi da bukutar su balle ayyukan Ibadan da suke yi. 4-Mu karfafa imaninmu ta yadda ko da mun rasa Annabi ko wasu jagororin addini imaninmu ba zai girgiza ba.
Yanzu kuma sai aya ta 145:
وَمَا كَانَ لِنَفْسٍ أَنْ تَمُوتَ إِلاَّ بِإِذْنِ الله كِتَاباً مُّؤَجَّلاً وَمَن يُرِدْ ثَوَابَ الدُّنْيَا نُؤْتِهِ مِنْهَا وَمَن يُرِدْ ثَوَابَ الآخِرَةِ نُؤْتِهِ مِنْهَا وَسَنَجْزِي الشَّاكِرِينَ{145}
" Kuma bãbu wani rai da zai mutu fãce da iznin Allah, wa'adi ne mai kayyadadden lokaci. Kuma wanda yake nufin sakamakon dũniya za Mu bã shi daga gare ta, wanda kuwa ya ke nufin samakon lãhira za Mu bã shi daga gare ta. Kuma zã Mu sãka wa mãsu godiya.”
Babban dalilin da yake sa mutaen su gudu daga fagen yaki shi ne tsoron mutuwa saboda haka ne wanbnan aya take cewa mutuwa a hannun Allah take kuma zata sami mutum nre a lokaci ayyananne. Da yawa ana samun tsofaffi su je yaki su dawo lafiya, kuma da yawa ana samun matasa masu gudu su bar fagen yaki amma sai ya fada wani hadari har ya rasa ransa. Saboda haka ne Alkurani yajke bayyana aniya daban daban da mutane suke tafiya yaki da su: wasu suna neman ganima ne wasu kuma suna neman yardarm Ubangiji da ladarsa. A cikin wannan aya akwai darussa da ya kamata mu yi lura da su: 1-Guduwa daga fagen yaki ba shi ne kariya daga mutuwa ba, kuma tabbata da jajircewa a yaki ba dole ne ya zama musabbabin mutuwar mutum ba. 2-Mutuwa bata hannun dan Adam amma mu muke zabar niyar da muke aikata ayyuka saboda ita, don haka ya kamata mu zabi yin aiki saboda lahira mai tabbata a mamaikon yinsa saboda da duniya mai karewa, wanda kuma mutuwa ita mafarin rayuwar lahira.
Sai mu saurari aya ta 146, da ta 147 da ta 148:
وَكَأَيِّن مِّن نَّبِيٍّ قَاتَلَ مَعَهُ رِبِّيُّونَ كَثِيرٌ فَمَا وَهَنُواْ لِمَا أَصَابَهُمْ فِي سَبِيلِ اللّهِ وَمَا ضَعُفُواْ وَمَا اسْتَكَانُواْ وَاللّهُ يُحِبُّ الصَّابِرِينَ{146} وَمَا كَانَ قَوْلَهُمْ إِلاَّ أَن قَالُواْ ربَّنَا اغْفِرْ لَنَا ذُنُوبَنَا وَإِسْرَافَنَا فِي أَمْرِنَا وَثَبِّتْ أَقْدَامَنَا وانصُرْنَا عَلَى الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ{147} فَآتَاهُمُ اللّهُ ثَوَابَ الدُّنْيَا وَحُسْنَ ثَوَابِ الآخِرَةِ وَاللّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ{148}
"Kuma da akwai wasu annabawa da yawa wadanda jama'a mãsu yawa suka yi yãki tãre da su, kuma basu karaya ba game da abin da ya same su saboda Allah, kuma ba su yi rauni ba kuma ba su wulakantan ba. Kuma Allah yana son mãsu hakuri. Bãbu abin da ya yake fitowa daga bakinsu fãce faɗarsu: 'Ya Ubangijinmu! Ka gãfarta mana zunubanmu da zarmewarmu a cikin al'amarinmu, kuma Ka tabbatar da dugaduganmu, kuma Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai.' Allah Yã sãka musu da sakamakon dũniya da kuma kyakkyawan sakamakon Lãhira. Kuma Allah yana son mãsu kyautatãwa.”
Bayan da a ayoyin da suka gabata A.. Madaukakin sarki ya yi suka wa masu karaya da saba umarni da kuma guduwa dfaga yaki, a wannan ayoyi kuma ya yi bayyani ne dandane da wasu annabawan da suka gabaci Maaikin Allah, wadanda kuma suka yi yaki a tafarkin Ubangiji tare da mabiyansu masu ihlasi da dagewa kuma sun sha wahalhalu, sun sami raunuka a yaki. Ayoyin suna cewa wadancan mabiya annabawan farko basu yi kasala ko kjaraya ba to me ya sa ba zaku yi koyi da ba, me yya sa zaku kyale Annabi a filin yaki a tsakiyar abokan gaba? A wadannan ayoyi da akwai darusa da dama, ga wasu daga cikinsu: 1-Mu yi izna mu dauki darasai daga rayuwar maganata wadanda suka yi tsayin daka a kan tafarkin Ubangiji domin mu ma mu nisanci rauni dacgazawa da karaya. 2-Imani da Allah shi ne ginshiki mai bai wa mutane karfin zuciya da tsayuiwar daka a fagen taki. 3-Rayuwar annabawa ta hade da jihadi da fafutukar tabbatar da gaskiya ne ba jin dadi da hutu ba. 4-Sauke nauyi da tsayuwar daka wajen aikata wajibai yana da muhimmanci, ko mutum ya yi nasara ko kada ya sami nasara. 5-Laifuka da sabo suna cikin abubuwan da suke jawo faduwa a fagen fama, saboda haka mayakan Musulunci masu ihlasi suna iya magance abubuwan da suke hana samun nasara idan suka yi riko da istigfari da tuba wa Allah.
- To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shrii na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar Al Imran. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 149-153 (Kashi Na 101)
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.
A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 149-150 da ke cikin suratu-Ali Imrana:-.
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوَاْ إِن تُطِيعُواْ الَّذِينَ كَفَرُواْ يَرُدُّوكُمْ عَلَى أَعْقَابِكُمْ فَتَنقَلِبُواْ خَاسِرِينَ{149} بَلِ اللّهُ مَوْلاَكُمْ وَهُوَ خَيْرُ النَّاصِرِينَ{150}
" Ya ku wadanda kuka yi imani, idan kuka biye wa wadanda suka kafirce, to za su mai da ku baya, {wato kafirci} sai ku koma kuna masu hasara. A'a Allah ne majibincinku kuma shi ne fiyayyen masu taimako".
Hakika daya daga cikin hatsarorin da ke barazana ga daidaikun mutane da suka rungumi Musulunci a matsayin addini da ma al'ummar musulmi baki daya shi ne yadda ake samun koma baya a riko da koyarwar asalin addini na Musulunci da abubuwa masu kima da ke cikinsa saboda cimma wasu manufofi na duniya, inda a farkon al'amari zaka tarar da daidaikun mutane da ma jama'a masu yawa sun fi goyon bayan tafarkin imani tare da fifita shi a kan hanyar kafirci, amma bayan wani lokaci ganin yadda batun 'yanci da sharholiyar duniya ke gudana a tsakanin al'ummomin da ba musulmi ba ne, sai imaninsu da ayyukansu su yi rauni kuma su kasance cikin rudu a rayuwarsu.
Hakika alkur'ani mai girma ya yi gargadi ga irin wadannan jama'a inda yake nusar da muminai cewa; idan suka goyi bayan kafirci a maimakon umurnin Allah Madaukaki, to tabbas kafirai zasu janyo musu koma baya a maimakon ci gaba, domin kafirai ba su burin ganin muminai sun samu ci gaba ta kowace bangare sakamakon haka sai muminan sun zame sun yi hasara mai girma saboda da sun yi hasarar duniya da lahira. Kamar haka ne Allah Madaukaki ke magana da muminai da cewa: "Shin suna neman wata daukaka ne a wurinsu {wato kafirai} To hakika daukaka dukkaninta ta Allah ce". Lalle Allah ya hana muminai komawa ga kafirai domin neman daukaka da matsayi, saboda dukkanin daukaka da matsayi suna wajensa ne madaukaki.
Don haka a cikin ayar da muka saurara zamu iya fahimtar abubuwa kamar haka:-
{1} Hakika dabi'ar barin tafarkin imani wato ridda da kaucewa hanya madaidaiciya wata babbar barazana ce ga duk wani mumini. Don haka akwai bukatar mu kiyaye kanmu daga yaudara da waswasin shaidan makiyi.
{2} Rashin samun nasara a filin yaki baya nufin yin hasara ce, iyaka dai babbar hasara ita ce rashin samun nasara a fagen yaki tsakanin imani da kafirci, inda kafirci zai yi galaba a kan imani.
{3} Matukar muna neman daukaka da matsayi a rayuwarmu, to ta hanyar biyayya ga Allah Madaukaki ne kadai zamu kai ga samun wannan daukaka da matsayin.
Yanzu kuma shirinmu zai ci gaba ta hanyar sauraren aya ta 151 da ke cikin suratu-Ali Imrana:-
سَنُلْقِي فِي قُلُوبِ الَّذِينَ كَفَرُواْ الرُّعْبَ بِمَا أَشْرَكُواْ بِاللّهِ مَا لَمْ يُنَزِّلْ بِهِ سُلْطَاناً وَمَأْوَاهُمُ النَّارُ وَبِئْسَ مَثْوَى الظَّالِمِينَ{151}
"Zamu jefa tsoro a cikin zukatan wadanda suka kafirta saboda shirkar da suka yi da Allah game da abin da bai saukar da wata hujja a kansa ba, kuma makomarsu wuta ce, kuma makomar azzalumai ta munana".
Ayar da ta gabata tana suka ne dangane da yadda zukatan wasu musulmi suka yaudaru da halin sharholiyar duniya da kafirai suke ciki, amma a wannan ayar ana tunasar da musulmi ne cewa kada su yi tsammanin dogaro da kafirai zai sanya su samu kwanciyar hankali da nutsuwa, iyaka dai su sani duk wani dogaro da wani abu ba Allah ba ko neman taimako daga wani, karkata ne zuwa ga shirka kuma kafirci ne. Sakamakon haka irin mutanen da suke kaurace wa Allah ta hanyar dogaro da wasu abubuwa na daban, a kullum suna cikin rayuwar rudu ce da rashin takamammen matsayi, kuma tsoro da kaduwa sukan mamaye musu zukata a rayuwar duniya, sannan a ranar kiyama su kasance tare da kafirai da azzalumai a cikin wutan jahannama. Don haka kasancewa tare da kafirai ba lamari ne da zai kwantar da hankali da wanzar da jin dadin duniya ba, kamar yadda ba zai taba kai mutum ga samun tsira a ranar lahira ba.
Hakika a cikin wannan aya zamu iya fahimtar al'amura kamar haka:-
{1} Dogaro da wani ba Allah ba, shirka ne kuma yana gadar da tsoro, yayin da imani da Allah tare da tuna shi a kowane hali ke gadar da kwanciyar hankali da nutsuwa.
{2} Mafi girman kunci da ke lullube zukatan kafirai shi ne tsananin tsoron mutuwa da rayuwa maras alkibla, kuma a duk lokacin da adadin yawan muminai ya karu hakan yana kara firgita kafirai.
Shirin namu zai ci gaba ta hanyar sauraren aya ta 152 da ke cikin suratu Ali Imrana kamar haka:-
وَلَقَدْ صَدَقَكُمُ اللّهُ وَعْدَهُ إِذْ تَحُسُّونَهُم بِإِذْنِهِ حَتَّى إِذَا فَشِلْتُمْ وَتَنَازَعْتُمْ فِي الأَمْرِ وَعَصَيْتُم مِّن بَعْدِ مَا أَرَاكُم مَّا تُحِبُّونَ مِنكُم مَّن يُرِيدُ الدُّنْيَا وَمِنكُم مَّن يُرِيدُ الآخِرَةَ ثُمَّ صَرَفَكُمْ عَنْهُمْ لِيَبْتَلِيَكُمْ وَلَقَدْ عَفَا عَنكُمْ وَاللّهُ ذُو فَضْلٍ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ{152}
"Kuma hakika Allah ya cika muku alkawarinsa a lokacin da kuke karkashe su da izininsa, har zuwa lokacin da kuka karaya kuma kuka yi jayayya {a tsakaninku} kan umurnin {annabi}, kuma kuka saba, bayan {Allah} ya nuna muku abin da kuke so. Daga cikinku akwai wadanda suke nufin duniya, akwai kuma daga cikinku wadanda suke nufin lahira, sannan kuma ya dora su a kanku don ya jarrabe ku. Kuma hakika ya yafe muku laifinku. Kuma Allah ma'abucin falala ne ga muminai".
Sakamakon galaba da kafirai suka yi a kan musulmi a lokacin yakin Uhdu wasu musulmi sun yi suka kan manzon Allah; suna cewa ashe Allah bai yi alkawarin cewa zamu yi nasara a kan kafirai ba? to don menene a wannan yaki kafirai suka yi galaba a kanmu?. To lalle a wannan aya ana mayar musu da martani ne da cewa: Hakika alkawarin Allah gaskiya ne kuma tabbas ya Allah ya cika alkawarinsa, saboda a farkon yaki musulmi sun yi galaba a kan makiyansu ta hanyar karkashe su da taimakon Allah, amma wasu dalilai suka sanya kafirai suka yi galaba a kan musulmi, dalilan kuwa su hada da:-
Na farko a lokacin da musulmi suka ga makiya suna tserewa suna barin tarin dukiyarsu saboda karaya da suka yi, sai musulmi dukufa wajen kwasar ganimar dukiyar suka sha'afa da batun yaki.
Na biyu rashin bin umurnin manzon Allah {s.a.w} da ya bayyana musu cewa a kowane irin hali kada mayakan musulmi da suke kan dutsen Uhudu su kuskura su bar wannan tungar, amma sai suka yi sabani a tsakaninsu, inda daga karshe suka saba umurnin manzon Allah suka sauka daga kan dutse domin kwasan ganima lamarin da bai wa makiya damar yi musu kofar rago.
Na uku baya ga wadancan dalilai da muka ambata, a farkon yakin Allah Madaukaki ya bai mayakan musulmi gagarumar nasara, sai a karshe ne suka dandana kudarsu domin hakan ya zame musu darasi tare da sanin cewa taimakon Allah yana tare da jama'ar da suka mika al'amarinsu gare shi da yin riko da hadin kai, don haka galabar da kafirai suka samu a kan musulmi wani babban darasi ne ga al'umma.
A wannan aya zamu fahimci abubuwa kamar haka:-
{1} Alkawarin Allah na taimakawa muminai yana gudana ne matukar muminai suka aiki da hakkin da ya rataya a kansu.
{2} Rauni da rabuwar kai gami da sabawa umurnin jagora suna daga cikin muhimman dalilan da suka janyo yin galaba a kan musulmi, kuma a wannan bangaren babu bambanci tsakanin mumini da kafiri duk wanda ya sabawa wadannan ginshikai babu makawa zai fuskanci mummunar sakamako.
{3} Wasu daga cikin mayakan musulmi sun tafi yaki ne domin neman ganima saboda son duniya wanda babu batun lahira a gabansu.
{4} Rashin samun nasara hanya ce da Allah yake jaraba bayinsa da shi wanda maimakon muminai su yanke tsammani sai hakan ya zame musu wata babbar darasi da zata kai su ga samun nasara a gaba.
Har ila yau shirinmu zai ci gaba ta hanyar ambato aya ta 153 daga cikin suratu- Ali Imrana kamar haka:
إِذْ تُصْعِدُونَ وَلاَ تَلْوُونَ عَلَى أحَدٍ وَالرَّسُولُ يَدْعُوكُمْ فِي أُخْرَاكُمْ فَأَثَابَكُمْ غُمَّاً بِغَمٍّ لِّكَيْلاَ تَحْزَنُواْ عَلَى مَا فَاتَكُمْ وَلاَ مَا أَصَابَكُمْ وَاللّهُ خَبِيرٌ بِمَا تَعْمَلُونَ{153}
"{Ku tuna} A lõkacin da kuka gudu {daga fagen yaki} kuma ba ku karkata gurin kowa ba, alhãli kuwa Manzon Allah nã kiran ku ta bayanku saboda haka ya sãkã muku da bakin cikin {gudunku} saboda bakin cikin {saba wa umurnin Manzo}. Domin kada ku yi bakin ciki a kan abin da ya kubuce muku, kuma kada ku yi bakin cikin a kan abin da ya sãme ku. Kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa".
Daya daga cikin munanan abin da ya faru a lokacin yakin Uhudu shi ne kofar rago da makiya suka yi wa musulmi da hakan ya sanya musulmi suka tsere daga filin yaki suka bar Manzon Allah {s.a.w} da wasu sahabbai 'yan kadan, kuma duk kiran da Manzon Allah {s.a.w} ya yi ga musulmi kan su tsaya a wajen da ya umurce su, ba su kiyaye umurnin na shi ba.
Alkur'ani mai girma yana bayyana cewa; rashin bin umurni da tserewar da musulmi suka yi daga filin yaki sune dalilan da suka sanya rundunar makiya kafirai suka yi galaba a kansu, kuma bakin cikin da musulmi suka yi dangane da galabar da kafirai suka yi a kansu ya yi sanadiyyar mantar da su batun ganimar yaki, wahala da suka fuskanta da raunukan da suka samu, tabbas bakin cikin da musulmi suka janyo wa Manzon Allah {s.a.w} shi ya janyon musu afkawa cikin tsananin bakin ciki da suka shiga ciki.
Hakika a cikin wannan aya zamu fahimci abubuwa kamar haka:-
{1} Rashin bin umurnin jagoran addini yana haifar da tsoro da ke kai ga gudu a filin yaki tare da bai makiya damar samun galaba.
{2} Filin yaki fage ne na jarabawa ga masu ikrarin imani, saboda duk wanda ya fita yaki ana daukansa a matsayin mumini, amma lokacin da aka shiga cikin halin tsanani da wahala a nan ne ake gane muminai na gaskiya.
{3} Daukan darasi daga mummanan halin da al'ummar musulmi suka shiga a baya da rashin nuna bakin ciki kan rashin wani abu na daga dukiya a rayuwar duniya ko masifa da ta afka mana.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 154-158 (Kashi Na 102)
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.
A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 154 da ke cikin suratu-Ali Imrana kamar haka:-
ثُمَّ أَنزَلَ عَلَيْكُم مِّن بَعْدِ الْغَمِّ أَمَنَةً نُّعَاساً يَغْشَى طَآئِفَةً مِّنكُمْ وَطَآئِفَةٌ قَدْ أَهَمَّتْهُمْ أَنفُسُهُمْ يَظُنُّونَ بِاللّهِ غَيْرَ الْحَقِّ ظَنَّ الْجَاهِلِيَّةِ يَقُولُونَ هَل لَّنَا مِنَ الأَمْرِ مِن شَيْءٍ قُلْ إِنَّ الأَمْرَ كُلَّهُ لِلَّهِ يُخْفُونَ فِي أَنفُسِهِم مَّا لاَ يُبْدُونَ لَكَ يَقُولُونَ لَوْ كَانَ لَنَا مِنَ الأَمْرِ شَيْءٌ مَّا قُتِلْنَا هَاهُنَا قُل لَّوْ كُنتُمْ فِي بُيُوتِكُمْ لَبَرَزَ الَّذِينَ كُتِبَ عَلَيْهِمُ الْقَتْلُ إِلَى مَضَاجِعِهِمْ وَلِيَبْتَلِيَ اللّهُ مَا فِي صُدُورِكُمْ وَلِيُمَحَّصَ مَا فِي قُلُوبِكُمْ وَاللّهُ عَلِيمٌ بِذَاتِ الصُّدُورِ{154}
"Sannan kuma {Allah} Ya saukar muku da aminci bãyan {wancan} bakin cikin; gyangyadi yanã daukar wata kungiya daga cikinku, kuma wata kungiya zukatansu sun shiga cikin damuwa suna zaton abin da bã shi ne gaskiya ba a game da Allah, irin zaton jahiliyya, suna cẽwa: "Shin za mu sami wani abu daga nasara kuwa?" Ka ce, "Lalle ne al'amari dukkaninsa na Allah ne." Suna bõyẽwa a cikin zukatansu, abin da bã su bayyana shi a gare ka. Suna cẽwa: "Da munã da wani abu {na nasara} daga al'amarin dã ba a kashe mu ba a nan."Ka ce: "Kõ dã kun kasance a cikin gidãjenku, dã wadanda aka rubũta musu mutuwar sun fito zuwa makwantarsu;" kuma {dalilin rashin nasararku a yaki shi ne} dõmin Allah Ya jarrabi abin da ke cikin kirãzanku. Kuma dõmin Ya tsarkake abin da ke cikin zukãtanku. Allah Masani ne ga abin da ke cikin kirãza".
Kamar yadda muka bayyana a shirinmu da ya gabata: Yin galaba a kan musulmi a lokacin yakin Uhudu ya samu asali ne daga rauni da rashin biyayya ga umurnin Manzon Allah {s.a.w} wanda har ta kai tserewar wasu musulmi daga filin yaki, lamarin da ya yi sanadiyyar hasarar rayuka da haifar da tsananin bakin ciki a zukatan musulmi. Baya faruwar wannan lamari musulmi sun zo wajen Manzon Allah {s.a.w} suna neman uzuri kan kuskuren da suka aikata, don haka Manzon Allah {s.a.w} ya yafe musu kuma Allah Madaukaki ya karbi tubarsu kuma ya saukar da nutsuwa a cikin zukatansu. Sai dai wasu gungun jama'a da ba su son daura alhakin rashin nasarar da ya faru a kan sakacinsu, sun dauki matakin daura rashin nasarar kan Allah da Manzonsa, inda suke cewa: Ashe Allah ba ya yi alkawarin taimaka mana ba, to don mene ne bai taimaka ba har makiya suka samu nasara a kanmu? Har ila yau wadannan gungun jama'a sun tunkari manzon Allah {s.a.w} suna cewa: Tun farkon yakin ai mun bada shawarin cewa kada a fice zuwa yaki a zauna a cikin birnin Madinah domin kare kai daga cikin birnin, amma Manzon Allah yaki aiki da shawarinmu, don haka ne aka yi nasara a kanmu.
Hakika Allah ya mai da martani ga wadannan gungun jama'a da cewar abi na farko shi ne: Alkawarin taimako ya dogara ne kan tsayin daka da gudanar da gwagwarmaya, ba wai don tsira da kanku ku tsere ku bar Manzon Allah ba kuma duk da haka kuna kuna tsammanin samun nasara, lalle wannan munanta zato ne ga Allah kuma mummunan zato ne da kuke dauke da ita tun zamanin jahiliyya, inda kuke jiran nasarar da ba ku cancanceta ba.
Abi na biyu shi ne mutuwa da shahada ba a hannunku suke ba, da har zaku ce idan da muna gida ba za a kashe mu ba, lalle duk wadanda lokacin mutuwarsu ya yi koda sun fake a cikin gida ne za a kashe su. Baya ga haka wannan abin da ya faru; shin mai kyau ne ko maras kyau ne wata jarabawa ce gare ku da zata fayyace abin da kuka boye tare sanin hakikaninku na bayyane.
Hakika a wannan aya zamu fahimci abubuwa kamar haka:-
{1} Wadannan gungun jama'a suna cikin kangin tunani mai kunci da suke munanta zato ga Allah, kuma lalle ba su dauke da cikekken imani na gaskiya.
{2} A duk lokacin da muka samu rashin nasara a kan wani lamari, to abin da zamu yi shi ne mu yi kokarin gano inda matsalar da ke domin mu gyara ta, ba wai mu munanta zato ga Allah ba ko daura alhakin rauninmu a kansa.
{3} Allah Madaukaki yana sane da duk wani abin da ke cikin zukata da tunanin kowa, kuma bayan da wani abu maras dadi ya faru ne zamu fahimci kanmu tare da sanin irin matsayin imaninmu, kuma a wannan lokacin ne zamu kai ga sanin sauran mutane, sannan hakan zai ba mu damar fahimtar shin zamu iya daukan hakkin da ya rataya a kanmu ko ba zamu iya ba.
Shirinmu zai ci gaba net a hanyar ambaton aya ta 155 da ke cikin suratu-Ali Imrana kamar haka:-
إِنَّ الَّذِينَ تَوَلَّوْاْ مِنكُمْ يَوْمَ الْتَقَى الْجَمْعَانِ إِنَّمَا اسْتَزَلَّهُمُ الشَّيْطَانُ بِبَعْضِ مَا كَسَبُواْ وَلَقَدْ عَفَا اللّهُ عَنْهُمْ إِنَّ اللّهَ غَفُورٌ حَلِيمٌ{155}
"Hakika wadanda suka gudu daga cikinku a ranar da runduna biyu suka hadu, shaidan ne kawai ya yi talãlãbantar da su, sabõda sãshin abin da suka aikata na laifi. Kuma hakĩka, Allah ya yi afuwa a gare su. Kuma lalle Allah Mai gãfara ne Mai hakuri".
A cikin wannan aya bayan nuni ga matakin da musulmi suka dauka na tserewa daga filin yaki a lokacin Uhudu, ayar ta kuma yi nuni kan dalilin gudun daga fagen yakin da cewa: ayyukan laifuffuka da suka aikata a baya shi ne dalilin raunin imaninsu ta yadda suke saurin mika wuya ga wasiwasin shaidan, don haka a lokacin da suka ga rayuwarsu tana cikin hatsari ba a shirye suke su sadaukar da rayuwarsu ta hanyar addini ba.
A cikin wannan aya zamu fahimci abubuwa kamar haka:-
{1} Aikata kananan laifuffuka suka bude hanyar da shaidan zai samu damar sanya wasiwasi mai girma a cikin zukata ta yadda mutum zai kai ga matakin juya baya ga Allah da manzonsa domin neman tsira da rayuwarsa.
{2} Laifi yana janyo raunana zukatan mayaka tare da bude wa shaidan hanyar yin kutse a zukata, don haka kafin tafiya filin yaki wajibi ne musulmi su dauki matakin tsarkake zukatansu ta hanyar tuba da neman gafarar Allah don samun karfin imanin tunkarar makiya.
{3} Allah baya nisantar da masu kuskure daga gare shi matukar suka yi nadama kan abin da suka aikata, domin Allah mai gafara ne.
Yanzu kuma zamu saurari aya ta 156 a cikin suratu- Ali Imrana kamar haka:-
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ لاَ تَكُونُواْ كَالَّذِينَ كَفَرُواْ وَقَالُواْ لإِخْوَانِهِمْ إِذَا ضَرَبُواْ فِي الأَرْضِ أَوْ كَانُواْ غُزًّى لَّوْ كَانُواْ عِندَنَا مَا مَاتُواْ وَمَا قُتِلُواْ لِيَجْعَلَ اللّهُ ذَلِكَ حَسْرَةً فِي قُلُوبِهِمْ وَاللّهُ يُحْيِـي وَيُمِيتُ وَاللّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ{156}
Yã ku wadanda kuka yi ĩmani, kada ku kasance kamar wadanda suka kãfirta kuma suka ce wa'yan'uwansu idan sun yi tafiya a bayan kasa kõ suka kasance a wurin yãki suka mutu: "Dã sun kasance a tare da mu ai da ba su mutu ba, kuma dã ba a kashe su ba." Dõmin Allah Ya sanya waccan magana ta zama nadãma a cikin zukãtansu. Kuma Allah ne yake rãyarwa kuma yake kashewa. Kuma Allah yana ganin {duk} abin da kuke aikatawa.
Ayar da ta gabata tana bayanin irin uzurin da munafukai suka gabatar ne domin kin fita zuwa yakin Uhudu, amma a wannan aya ana bayyana wannan uzurin ne a matsayin kafirce wa Allah; inda ake bayyana cewar: Ya ku muminai don mene ne kuke maimaita furucin da munafukai ke yi, inda suke cewa; da sun kasance tare da mu, ba su fice daga cikin gari ba kuma ba su tafi yaki ba da wannan abin da ya faru da su bai wakana ba: Ka ce ba su da masaniyar mutuwa da rayuwa suna hannun Allah ne, shi ke rayar da wanda ya ga dama kuma ya kashe wanda ya ga dama, iyaka dai a ranar kiyama ce zasu fahimci hakikanin gaskiya, inda wadannan ayyuka da maganganun da suke yi zasu zame musu hasara kuma babban nadama.
Hakika a cikin wannan aya zamu fahimci abubuwa kamar haka:-
{1} Wasu maganganun da suke fitowa daga bakuna maganganu ne na kafirci da suka yi hannun riga da koyarwar addini, kuma mutum da yake munafiki ya fi kusa da kafirci.
{2} Mu kasance cikin kula da kiyayewa dangane da irin furucin da yake fitowa daga wasu masoyanmu marassa zurfin tunani saboda makiya zasu iya amfani da su wajen cusa maganganu da zata kashe gwiwa da yanke kauna a tsakanin al'umma.
{3} Kada mu sake son tsawon rayuwa a duniya ya hana mu fita zuwa yaki domin jihadi, hakika akwai da dama daga cikin tsoffi da suka fita yaki kuma suka dawo da ransu, wasu da dama daga cikin samari kuma suka ki fita yaki amma suka yi gajeren rayuwa a duniya.
Yanzu kuma zamu saurari aya ta 157-158 da ke cikin suratu Ali-Imrana kamar haka:-
وَلَئِن قُتِلْتُمْ فِي سَبِيلِ اللّهِ أَوْ مُتُّمْ لَمَغْفِرَةٌ مِّنَ اللّهِ وَرَحْمَةٌ خَيْرٌ مِّمَّا يَجْمَعُونَ{157} وَلَئِن مُّتُّمْ أَوْ قُتِلْتُمْ لإِلَى الله تُحْشَرُونَ{158}
Kuma lalle ne idan aka kashe ku a cikin hanyar Allah, ko kuka mutu, to hakĩka gãfara daga Allah da rahama ne mafi alhẽri daga abin da suke tãrãwa. Kuma lalle ne idan kun mutu ko kuwa aka kashe ku, to hakĩka zuwa ga Allah ake tãra ku.
Wadannan ayoyi suna karfafa zukatan muminai ne a lokacin yakin Uhudu, inda ake fadakar da su kan kada su saurari maganganun munafukai marassa tushe, kuma su sani cewa idan har suka mutu ta hanyar Allah ko aka kashe su a filin yaki, to babu wani hasara da suka yi, iyaka dai sun samu babban rabo ne saboda rahamar Allah da gafararsa za su yi sanadiyar kai ku ga samun gidan aljanna da zaku dauwama a ciki, wanda ya fi daraja da kima kan duk wani abin da munafukai da kafirai da sauran mutane zasu tara a tsawon rayuwarsu ta duniya.
A cikin wadannan ayoyi zamu fahimci cewa:-
{1} Abu mafi muhimmanci duk wata mutuwa a kan tafarkin Allah tana kai mutum ga samun babban rabo na rahama da gafarar Allah, misali idan mutum ya fice zuwa neman ilimi saboda Allah, sai mutuwa ta riske shi, to zai kasance daga cikin wadanda rahama da gafarar Allah zasu lulube shi.
{2} Hakika babu makawa ga mutuwa, dole ne kowane mahaluki ya mutu, to don mene ne ba zamu zabawa kanmu mafi kyauwun nau'in mutuwa ba? Imam Husaini jikan Manzon Allah {s.a.w} yana cewa: "Idan dai har wannan jiki an shirya mata mutuwa, to lalle shahada a kan tafarki Allah ita ce mafi daukakar mutuwa".
Suratu Al Imrana, Aya Ta 159-163 (Kashi Na 103)
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da saduwa da ku a cikin shirin hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, inda a yau Sunusi Wunti zai kasance tare da ku, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa.
A shirinmu na yau zamu fara ne da sauraren aya ta 159 da ke cikin suratu Ali-Imrana kamar haka:-
فَبِمَا رَحْمَةٍ مِّنَ اللّهِ لِنتَ لَهُمْ وَلَوْ كُنتَ فَظّاً غَلِيظَ الْقَلْبِ لاَنفَضُّواْ مِنْ حَوْلِكَ فَاعْفُ عَنْهُمْ وَاسْتَغْفِرْ لَهُمْ وَشَاوِرْهُمْ فِي الأَمْرِ فَإِذَا عَزَمْتَ فَتَوَكَّلْ عَلَى اللّهِ إِنَّ اللّهَ يُحِبُّ الْمُتَوَكِّلِينَ{159}
"Sabõda wata rahama ce daga Allah ka yi sanyin hali a gare su. Kuma dã kã kasance mai fushi mai kaushin hali, dã sun wãtse daga gere ka. Sai ka yãfe musu laifinsu, kuma ka nẽma musu gãfara, kuma ka yi shãwara da su a cikin al'amura. Sannan kuma idan ka yi niyyar zartarwa, to, sai ka dõgara ga Allah, hakika Allah Yana son mãsu tawakkali".
Wannan aya tana nuni ne kan wasu daga cikin kyawawan dabi'un Manzon Allah {s.a.w}, inda take bayyana cewar hakika dalilan da suka sanya mutanen da suke da kaushin hali tare da son gudanar da yake-yake daga kabilar larabawa suka mika wuya gare ka Ya kai Manzon Allah {s.a.w} ta hanyar yin imani da goya maka baya, sune taushin halinka da kyawawan dabi'unka na jin kai da rahama, don haka ayar ke bayyana cewar idan da ace zaka kasance kamarsu, mai dauke da kaushin hali da saurin tunzura da babu wanda zai kusance ka, kuma da tuni sun yi watsi da imanin da suka yi da sakon Musulunci. Don haka sabawa umurnin da suka yi a lokacin yakin Uhudu lamari ne da ya riga ya shige, saboda haka ka koma ga Allah Madaukaki domin nema musu gafara kan wannan laifin. Sannan kafin yakin Uhudu ka kasance kana gudanar da shawara da su, duk da cewa shawararsu a yakin Uhudu ba ta yi amfani ba, amma duk da haka; ka ci gaba da gudanar da shawara da su kan al'amurar da suka shafe su, domin kai ne babban abin koyi gare su.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Dabi'ar taushin zuciya da nuna jin kai wata babbar kyauta ce daga Allah Madaukaki da ke gadar da ita ga jagororin addini, don haka duk wanda yake matsayin mai shiryarwa da gudanar da fadakarwa ga jama'a, to dole ne ya siffantu da wadannan kyawawan dabi'u.
{2} Duk wani mutum da ya munanta mana, sannan ya yi nadama kan kan abin da ya aikata, to sai mu dauki matakin yi masa uzuri tare da yafe masa kuskuren da ya aikata.
Yanzu kuma shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar sauraren aya ta 160 da ke cikin suratu-Ali Imrana:-
إِن يَنصُرْكُمُ اللّهُ فَلاَ غَالِبَ لَكُمْ وَإِن يَخْذُلْكُمْ فَمَن ذَا الَّذِي يَنصُرُكُم مِّن بَعْدِهِ وَعَلَى اللّهِ فَلْيَتَوَكِّلِ الْمُؤْمِنُونَ{160}
"Idan Allah Ya taimake ku, to, bãbu mai rinjayarku. Kuma idan Ya tabar da ku, to, wãnẽ ne zai taimake ku bãyanSa? Saboda haka sai mũminai su dõgara ga Allah".
A cikin ayar da ta gabata an yi umurni ga Manzon Allah {s.a.w} kan ya kasance mai dogaro da Allah, to a wannan ayar ana umurni ga muminai ne kan su kasance masu dogaro da Allah, kuma saboda haka ne ake bayanin cewar duk wata daukaka da kaskanci suna hannun Allah ne, don haka babu wata daukaka ko kaskanci da zasu riski mutum sai da yardan Allah, idan kuma Allah ya so mutum da alheri, to babu wanda zai iya hanawa, kamar yadda idan ya saukar da ukuba da kaskanci kan mutum, to babu wani karfi da zai kare shi, don haka idan mutum ya fahimci hakikanin wannan lamari, to zai yanke kauna daga duk wani abu da ba Allah ba, kuma ba zai gudanar da wani aiki ba sai domin Allah, sannan zai kasance baya tsoron kowa sai Allah, tare da yanke fatarsa ga sauran mutune sai Allah shi kadai, to wannan shi ne ma'anar dogaro da Allah.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} A al'amuran da suka shafi mutum shi kadai da na zamantakewarsa da sauran jama'a maimakon ya dogara da wani ko wasu, kamata ya yi ya dogara ga Allah, saboda dukkanin halittu muna karkashin kulawar Allah ne.
{2} Sau nawa nasarori da suka samo asali daga sanadi na zahiri da na dabi'a suka gushe tare da rushewa, amma nasarar Allah da tallafinsa suka tabbata.
Yanzu kuma zamu saurari aya ta 161 ne da ke cikin suratuAli-Imrana kamar haka:-
وَمَا كَانَ لِنَبِيٍّ أَن يَغُلَّ وَمَن يَغْلُلْ يَأْتِ بِمَا غَلَّ يَوْمَ الْقِيَامَةِ ثُمَّ تُوَفَّى كُلُّ نَفْسٍ مَّا كَسَبَتْ وَهُمْ لاَ يُظْلَمُونَ{161}
"Kuma bãi kamata ga wani annabi ya yi ha'inci ba {wato ya danne hakki}. Wanda ya yi ha'inci, to zai zo da abin da ya yi ha'inci a kai a rãnar kiyama. Sannan a saka wa kõwane rai da abin da ta aikata. Kuma bã zã a zãlunce su ba".
Hakika ba abu ne mai yiyuwa ba a samu wani annabi ya aikata ha'inci, kuma duk wanda ya yi ha'inci, to a ranar kiyama zai zo da wannan abin ya yi ha'inci a kansa, a wannan rana ta kiyama kowane mutum zai tarad da sakamakon duk wani abin da ya aikata kuma babu wanda za a zalunce shi a wannan ranar.
A lokacin yakin Uhudu Manzon Allah {s.a.w} ya bada umurnin gudanar da tsaron wata mashiga da ke gefen dutsen Uhudu ga wasu jama'a, inda yake bayyana musu cewar duk irin nasarar da muka samu ko galabar da aka yi a kanmu, kada ku kuskura ku bar wannan wajen, kuma zaku samu duk wani rabo na daga ganimar da aka samu, amma a lokacin da musulmi suka samu nasara a kan kafirai, sai mafi yawan wadannan jama'a suka bar wajen da aka musu umurni da su tsare, suka shiga cikin ayarin da ke kwasar ganima; wannan ayar tana magana da su da cewa; shin kuna tsammanin Manzon Allah zai ha'ince ku ne dangane da ganimar da aka samu, don haka kuka bar wajen da aka muku umurni da tsarewa, alhalin matsayin annabci ya yi hannun riga da duk wani nau'in ha'inci? Hakika dukkanin annabawan Allah amintattu ne da suke kare hakkokin mutane.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Wasu daga cikin sahabban Manzon Allah {s.a.w} duk da cewar sun fahimci hakikaninsa da tsarkinsa gami da rikon amanarsa amma duk da haka ba su da cikekken imani, saboda haka suke tsammanin zai iya aikata ha'inci. Don haka mu dauki matakin kare kanmu daga irin wannan mummunar zato na shaidanci.
{2} A daidai lokacin da ake samun wasu mutane suna munanta zato ga Manzon Allah {s.a.w}, shin muna tsammanin dukkanin mutane zasu kyautata mana zato kan ayyukan da muke aikatawa? Lalle wannan lamari ba mai yiyuwa ba ne, don haka sai mu dauki matakin samun 'yardan Allah da amincewarsa.
{3} Azaba ukubar lahira zasu kasance sakamakon ayyukanmu ne kawai domin Allah baya zaluntan bayinsa.
Yanzu kuma zamu saurari aya ta 162-163 ne daga cikin suratu Ali-Imrana kamar haka:-
أَفَمَنِ اتَّبَعَ رِضْوَانَ اللّهِ كَمَن بَاء بِسَخْطٍ مِّنَ اللّهِ وَمَأْوَاهُ جَهَنَّمُ وَبِئْسَ الْمَصِيرُ{162} هُمْ دَرَجَاتٌ عِندَ اللّهِ واللّهُ بَصِيرٌ بِمَا يَعْمَلُونَ{163}
"Shin wanda ya bi yardar Allah yana zama kamar wanda ya kõma da fushi daga Allah, kuma makomarsa Jahannama ce? Kuma tir da makõma. Sũ {wadancan da aka bayyana suna da} darajõji a wurin Allah, kuma Allah Mai gani ne ga abin da suke aikatawa".
A cikin wadannan ayoyi biyu a takaice zamu fahimci yadda aka kwatanta tsakanin sakamakon muminai da na munafukai da cewa; wadanda manufar ayyukansu ita ce neman 'yardan Allah, to zasu samu matsayi da daraja mai girma a wajensa kuma zasu kasance abin kyakkyawan abin koyi, sabanin wadanda koda sun so Allah sun so shi ne domin cimma bukatun kansu, irin wadannan mutane sun riki addini ne a matsayin hanyar kai wa ga bukatunsu na duniya, don haka suna cikin fushin Allah kuma karshen ayyukansu hasara ce da halaka duniya da lahira.
Ya zo cikin ruwaya cewar a lokacin da Manzon Allah {s.a.w} ya bada umurnin tafiya yakin Uhudu wasu gungun munafukai sun dauki matakin gabatar da uzurorin marassa tushe domin kada su fita zuwa yakin, kuma wasu gungun musulmai da suke da raunin imani sun bi sahunsu na rashin tafiya zuwa yakin, don haka a wannan aya aka ambaci alamar wadannan mutane kuma aka tanada musu wutan jahanna domin ta kasance makoma gare su, wasu daga cikin wadanda suka fita zuwa yakin kuma amma cikin rashin karfin gwiwa saboda nadamar da suka yi kana bin da suka aikata, sai aka gafarta musu.
A cikin wadannan ayoyi zasu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Babbar manufa mai kima ita ce samun 'yardan Allah wadda ita ce sama da duk wata manufa kuma tana kai mutum ga samun babban matsayin a wajen Allah Madaukaki.
{2} Kada a tsakanin al'ummar musulmi ya kasance ana daidaita tsakanin masu jihadi da gwagwarmaya da wadanda ba su jihadi da yaki ta farkin Allah a matsayin daya saboda kin gudanar da jihadi yana janyo saukan fushin Allah.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 164-168 (Kashi Na 104)
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da saduwa da ku a cikin shirin hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, inda a yau Sunusi Wunti zai kasance tare da ku, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa.
A shirinmu na yau zamu fara ne da sauraren aya ta 164 da ke cikin suratu Ali-Imrana kamar haka:-
لَقَدْ مَنَّ اللّهُ عَلَى الْمُؤمِنِينَ إِذْ بَعَثَ فِيهِمْ رَسُولاً مِّنْ أَنفُسِهِمْ يَتْلُو عَلَيْهِمْ آيَاتِهِ وَيُزَكِّيهِمْ وَيُعَلِّمُهُمُ الْكِتَابَ وَالْحِكْمَةَ وَإِن كَانُواْ مِن قَبْلُ لَفِي ضَلالٍ مُّبِينٍ{164}
Hakĩka Allah Yã yi babbar falala a kan mũminai, dõmin Yã aiko musu Manzo daga cikinsu, yana karanta musu ãyõyinSa, kuma yana tsarkake su, kuma yana karantar da su Littãfi da hikima, kuma lalle sun kasance daga gabãni haka suna cikin bata bayyananniya".
Hakika Allah Madaukaki cikin rahamarsa da jin kansa ga dukkanin halittu ya ni'imta su da shiriya musamman dan Adam, saboda shiriya daya ce daga cikin manyan ni'imomi da Allah ya azurta mutum da shi, domin idan a asalin halittar mutum babu shiriya tare da shi, to hakan zai yi sanadiyyar salwantar duk wani karfi da shirin da yake da shi a rayuwa, ko kuma afkawa cikin gurbataccen tunani da mummunar dabi'a, kamar haka ne a yau muke ganin mutanen da suka yi watsi da shiriyar da Allah ya azurta dan Adam da ita, ta hanyar hankali da wahayi musamman ma shiriyar da ke zuwa ga dan Adam ta hanyar wahayi, hakika duk da tarin ilimin da irin wadannan mutane suke dauke da shi, amma maimakon sun kasance cikin saukin rayuwa da kwanciyar hankali, sun kasance suna rayuwa cikin tashin hankali, bakin ciki, kiyayya da juna da rikici a kasashen da suke riya ci gaba da wayewa.
Hakika saboda tsarkake mutane daga dauda da kazantar rayuwa domin dora su a kan hanyar shiriya da kamala ne, Allah Madaukaki ya aiko Annabawa suna fayyace musu maganarsa da koyar da su da hikima, inda Annabawan suka tarbiyantar da hankali da tunanin mutane, tare da tseratar da su daga afkawa cikin halaka da bata.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Aiko Annabawa wata babbar kyauta ce daga Allah zuwa ga mutane, don haka dole ne mu fahimci irin wannan babbar ni'ima.
{2} Tsarkin zuciya shi ne gaba a kan neman sani, sannan ilimi shi ne hasken rayuwa da ke tseratar da mutum daga afkawa cikin halaka.
{3} Dole ne gina kai da tsarkake zuciya su kasance karkashin inuwar makarantar Annabawa da ayoyin Allah, domin tarbiyyantar da kai da neman zama mutum na kwarai ta hanyar da bashi da wata alaka da maganar Allah ko koyarwar Annabawa, to shakka babu lamari ne da zai kai mutum ga halaka.
Yanzu kuma shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar sauraren aya ta 165 da ke cikin suratu-Ali Imrana:-
أَوَلَمَّا أَصَابَتْكُم مُّصِيبَةٌ قَدْ أَصَبْتُم مِّثْلَيْهَا قُلْتُمْ أَنَّى هَـذَا قُلْ هُوَ مِنْ عِندِ أَنْفُسِكُمْ إِنَّ اللّهَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ{165}
"Shin kuma a lõkacin da wata masĩfa ta sãme ku {a yakin Uhudu} alhãli kuwa kun sãmar da irin ninkinta {a kan abokan gaba a lokacin yakin Badar}, sai kuka ce: "Ta yaya wannan ya faru?" Ka ce: "Shi {wannan} daga wurinku ne {saboda saba umurnin Annabi da kuka yi}. Hakika Allah mai iko ne a kan dukkan kõmai".
A yakin Uhudu a lokacin da aka yi galaba a kan musulmai an kashe musu mutane saba'in, sai suke tambayar Manzon Allah cewa; don mene ne dalilin da ya sanya aka yi galaba a kanmu? Sai Allah ke mayar musu da martani da cewa: A shekarar da ta gabata a lokacin yakin Badar kun janyo mummunar hasara ga kafirai ninkin hasarar da suka janyo muku, inda kuka kashe musu mutane saba'in, tare da kame fursunonin yaki saba'in, baya ga haka kuma; galabar da aka yi a kanku a wannan shekara a yakin Uhudu ya samo asali ne daga rauninku da rashin bin umurni gami da sabanin da ku yi a tsakaninku, don haka kada ku yi tsammanin Allah Madaukaki baya da ikon taimaka muku ne da gadar muku da nasara, lalle Allah mai iko ne a kan komai, amma sharadin samun taimakonsa ya dogara ne kan biyayyarku ga Annabi, ba wai ku saba wa umurnin Annabi sannan kuma ku yi zaton samun nasara daga wajen Allah Madaukaki ba.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} A lokacin da muke ganin wahala da rashin samun nasara a yakin Uhudu, kamata ya yi mu tuna nasarar yakin Badar.
{2} A lokacin da muke binciken dalilin rashin nasara, kamata ya yi mu fara da kanmu ta hanyar tunanin sanin inda rauninmu yake da kokarin magance shi, ba wai mu dora alhakin raunin kan wasu ba.
Yanzu kuma zamu saurari aya ta 166 zuwa 167 ne da suke cikin suratuAli-Imrana kamar haka:-
وَمَا أَصَابَكُمْ يَوْمَ الْتَقَى الْجَمْعَانِ فَبِإِذْنِ اللّهِ وَلِيَعْلَمَ الْمُؤْمِنِينَ{166} وَلْيَعْلَمَ الَّذِينَ نَافَقُواْ وَقِيلَ لَهُمْ تَعَالَوْاْ قَاتِلُواْ فِي سَبِيلِ اللّهِ أَوِ ادْفَعُواْ قَالُواْ لَوْ نَعْلَمُ قِتَالاً لاَّتَّبَعْنَاكُمْ هُمْ لِلْكُفْرِ يَوْمَئِذٍ أَقْرَبُ مِنْهُمْ لِلإِيمَانِ يَقُولُونَ بِأَفْوَاهِهِم مَّا لَيْسَ فِي قُلُوبِهِمْ وَاللّهُ أَعْلَمُ بِمَا يَكْتُمُونَ{167}
"Kuma abin da ya sãme ku a rãnar da kungiyoyin nan biyu suka hadu, to, {ya same ku ne} da izinin Allah, kuma {Ya jarrabe ku ne} dõmin Ya san mũminai {na gaskiya}. Kuma dõmin Ya san wadanda suka yi munãfunci, kuma an ce musu: "Ku zo ku yi yãki saboda Allah kõ ku gudanar da kariya. Sai suka ce: "Dã mun san (yadda ake) yãki dã mun bĩ ku." Sũ {wadannan munafukan} a wannan ranar sun fi kusa da kafirci a kan imani. Sunã cẽwa da bãkunansu abin da bã shi ne a cikin zukãtansu ba. Allah ne Mafi sani ga abin da suke bõyewa".
Kamar yadda a cikin shirinmu da ya gabata muka bayyana cewar a lokacin da aka samu labarin harin da mushirikai suka kai kan birnin Madinah daga Makkah, Manzon Allah {s.a.w} ya kira taro a Masallaci domin gudanar da shawari da jama'a, inda mafiya yawa suka bada shawarar cewa musulmai su fice zuwa yaki, kuma su ja daga a gefen dutsen Uhudu, amma wasu manyan Madinah suka nuna rashin amincewar da wannan shawarar, inda suke ganin musulmai su ci gaba da zama a cikin Madinah da cikin gidajensu a matsayin jan daga domin kare mushirikai daga kaddamar da hari kan musulmi, amma sai Manzon Allah {s.a.w} ya fifita ra'ayin samari da shi ne ra'ayin mafi rinjaye, wannan mataki da Manzon Allah ya dauka ya fusata manyan Madinah, don haka a lokacin da aka shirya fita yakin Uhudu sai suka dinga zuwa suna gabatar da wasu uzurori marassa tushe domin kada su fice zuwa yakin, kuma da nufin raunana zukatan sauran musulmai saboda suma su dauki matakin janyewa daga zuwa yakin.
Alkur'ani yana magana da muminai cewa; idan yakin Uhudu ya kasance yaki mai daci gare ku, amma hakan mataki ne na tantance tsakanin muminai na gaskiya da masu da'awar imani, kuma jarabawa ce ta bambance tsakanin masu mika kai ga umurnin Manzon Allah da wadanda suke tare da Manzon Allah domin cimma manufofinsu.
A wadannan ayoyi zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Abubuwan da suke faruwa masu muni da na dadi a rayuwa wata jarabawa ce na Allah domin bambance mutanen kirki, don haka mu kiyaye kada mu fadi a irin wannan jarabawar.
{2} Munafunci da nuna fuska biyu yana kai mutum ga musun gaskiya da kafirce wa Allah, kuma kada mu taba tsammanin wayo da dabarar zama da kowace jama'a ita ce mafita, lalle daukan matsayi da gudanar da dabi'ar gaskiya sune mafi dacewar hanyar samun nasarar rayuwa.
{3} Daukan matakin kare kai da mutunci da kuma kasa suna daga cikin ayyuka masu kima a Musulunci, don haka duk wanda ya rasa ransa wajen kare wadannan abubuwa yana daga cikin jerin shahidai.
Yanzu kuma zamu saurari aya ta 168 ne da ke cikin suratuAli-Imrana kamar haka:-
الَّذِينَ قَالُواْ لإِخْوَانِهِمْ وَقَعَدُواْ لَوْ أَطَاعُونَا مَا قُتِلُوا قُلْ فَادْرَؤُوا عَنْ أَنفُسِكُمُ الْمَوْتَ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ{168}
"Wadanda suka ce wa 'yan'uwansu, alhalin kuwa sun yi zamansu {sun ki fita zuwa yaki} "Dã sun bi shawararmu ai dã ba a kashe su ba." Ka ce: "To, ku kare kanku daga mutuwar idan kun kasance mãsu gaskiya."
Wadanda suke furta maganganu marassa tushe na barna kafin fita zuwa yaki, kuma hakan ya yi sanadiyyar raba kan al'ummar musulmi, tare da karya musu zuciya, a bayan gudanar da yakin ma ba su janye daga yada mummunar farafagandarsu ba, a maimakon su zargi kansu dangane da mummunar matakin da suka dauka na rashin kare mutunci da kimarsu a rayuwa da kuma kare garinsu, sun koma suna zargin mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu a fagen yaki domin kare addini da mutuncinsu, alhali kuwa mutuwa ba ta takaita a filin yaki ba, kuma babu mahalukin da zai iya gujewa mutuwar, don haka Allah Madaukaki yake magana da su da cewa: kada ku taba tsammanin gujewa yaki da kuka yi, zai sanya ku iya gujewa mutuwa, domin mutuwa tana kan duk wani mahaluki. Don haka madalla da halin mutanen da suka gabatar da rayuwarsu ta hanyar biyayya ga umurnin Ubangijinsu, su kuwa wadanda suka gujewa yaki tir da mummunar halin da zasu shiga a yayin mutuwa.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Hakika zama a gida domin kin yi yaki a lokacin da makiya suka kawo hari da lokacin da al'ummar musulmi ke fuskantar hatsari alama ce ta munafunci da rashin imani.
{2} Raunana zukatan iyalan shahidai da jarumai da suka samu raunuka a fagen yaki, daya ne daga cikin ayyukan da munafukai da masu nuna fuska biyu ke gudanarwa.
{3} Munafiki yana ganin kansa a matsayin madaukaki a kan sauran mutane, kuma har ma yana zaton sauran mutane zasu bi ra'ayinsa tare da yin koyi da shi.
To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 169-173 (Kashi Na 105)
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da saduwa da ku a cikin shirin hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, inda a yau Sunusi Wunti zai kasance tare da ku, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa.
A shirinmu na yau zamu fara ne da sauraren aya ta 169 da ke cikin suratu Ali-Imrana kamar haka:-
وَلاَ تَحْسَبَنَّ الَّذِينَ قُتِلُواْ فِي سَبِيلِ اللّهِ أَمْوَاتاً بَلْ أَحْيَاء عِندَ رَبِّهِمْ يُرْزَقُونَ{169}
"Kuma Kada ka yi zaton wadanda aka kashe a kan hanyar Allah matattu ne. A'a, rãyayyu ne su a wajen Ubangijinsu ana azurta su".
A bayan kashe mutane saba'in daga cikin musulmi a yakin Uhudu, munafukai sun mayar da Madinah fagen juyayi da nuna jin kai ga iyalan wadanda aka kashe, kuma suka daura alhakin kashe su a kan Manzon Allah {s.a.w} da sahabbansa wanda hakan ma ya kara raunana zukatan musulmi.
A gefe guda kuma shugaban mushirikai a Makkah Abu-Sufyan dangane da yakin Uhudu yana cewa; musulmai saba'in da muka kashe a Uhudu sune maimakon mutanenmu saba'in da suka kashe a lokacin yakin Badar; dangane da wannan farafaganda da mushirikai da munafukai ke yadawa Allah Madaukaki ya saukar da wannan aya a matsayin mai da martani gare su; inda ke bayyana cewa; kada mutane su dauka babu bambanci tsakanin kisan da aka yi musulmi da wanda aka yi ga mushirikai, tabbas dukkaninsu sun bar duniya, amma musulmi da ya mutu ta hanyar shahada yana cikin wata ni'ima da Allah ya kebance da ita. Don haka Manzon Allah {s.a.w} yake mai da martani ga Abu-Sufyan da cewar mutanenmu da aka kashe suna cikin aljanna, amma mutanenku da aka kashe suna cikin wutan jahannama. Kamar yadda ya zo cikin ruwaya cewa; "duk wata kyakkyawar dabi'a, akwai kyakkyawar dabi'ar da ta darata, sai dai matsayin shahada a duk lokacin da mutum ya yi shahada ya kai kolin matsayi, kuma baya yiyuwa a iya kwatanta irin alherinsa, don haka ne Annabawa da waliyan Allah a cikin addu'o'insu suke rokon Allah ya azurta su da shahada".
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Daukan shahada a matsayin halaka ko hasara gurbataccen tunani ne. Lalle shahada ba faduwa ba ce ko hasarar rayuwa, amma riba ce da karuwa.
{2} Shahada ba yana nufin karshen rayuwar shahidi ba ne, wata sabuwar rayuwa ce zai fara cikin kulawar Allah, sau nawa ake samun mafi yawan rayayyu amma a hakika matattu ne, kuma sau nawa mafi yawan wadanda aka kashe, suke matsayin rayayyu, kamar haka ne makaho baya fahimtar ma'anar gani, domin mu makafi ne ba mu da masaniya kan al'amarin lahira, ba zamu fahimci hakikanin rayuwar lahira ba.
Yanzu kuma shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar sauraren aya ta 170 zuwa 171 da ke cikin suratu-Ali Imrana:
َرِحِينَ بِمَا آتَاهُمُ اللّهُ مِن فَضْلِهِ وَيَسْتَبْشِرُونَ بِالَّذِينَ لَمْ يَلْحَقُواْ بِهِم مِّنْ خَلْفِهِمْ أَلاَّ خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلاَ هُمْ يَحْزَنُونَ{170} يَسْتَبْشِرُونَ بِنِعْمَةٍ مِّنَ اللّهِ وَفَضْلٍ وَأَنَّ اللّهَ لاَ يُضِيعُ أَجْرَ الْمُؤْمِنِينَ{171}
"Suna mãsu farin ciki sabõda abin da Allah Ya bã su daga falalarSa, kuma suna yin bushãra ga wadanda ba su riske su ba, cewa: Bãbu wani abin tsõro a kansu kuma ba su zama suna yin bakin ciki ba." Suna yin bushãra sabõda wata ni'ima daga Allah da wata falala. Kuma lalle ne Allah bã ya tozartar da ladan mũminai".
A cikin wadannan ayoyi alkur'ani yana bayanin irin halin jin dadi da shahidai suka riska ne bayan samun matsayin shahada; inda kur'anin ke bayyana cewar baya ga nuna amincewa da shahadar da suka yi ta hanyar sadaukar da rayuwarsu domin Allah, suna kuma kiran sauran muminai da 'yan uwansu zuwa ga wannan matsayin madaukaki, suna ce musu kada su ji wani tsoro, kuma babu wani bakin cikin da zasu tarar ta hanyar shahada, iyaka dai jin kai da fafalar Allah ne zasu lullube su.
A karkashin wadannan ayoyi zamu fahimci cewa rayuwar shahidai a lokacin zaman kabari, rayuwa ce ta hakika da take kunshe da rayuwar jin dadi, wadata da busharar sakamako mai girma, don haka rayuwar shahidi ba yana nufin ci gaba da wanzuwar yabonsa a tsawon tarihi ba ne kawai.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Sakon shahidai shi ne zaburar da mutane zuwa ga hanyar Allah har su kai ga samun matsayin shahada, shahadar da take kawar da duk wani tsaro da bakin ciki a rayuwar duniya da lahira.
{2} Babban abin da shahidai suke buri shi ne samun jin kai da falalar Allah Madaukaki, ba wai yabon aikinsu da rubuta su cikin wadanda suka yi shahada ba.
Yanzu kuma zamu saurari aya ta 172 ne da ke cikin suratuAli-Imrana kamar haka:-
الَّذِينَ اسْتَجَابُواْ لِلّهِ وَالرَّسُولِ مِن بَعْدِ مَا أَصَابَهُمُ الْقَرْحُ لِلَّذِينَ أَحْسَنُواْ مِنْهُمْ وَاتَّقَواْ أَجْرٌ عَظِيمٌ{172}
"Wadanda suka amsa kira zuwa ga Allah da ManzonSa bãyan mĩki ya sãme su {a yakin Uhudu} To wadanda suka kyautata a cikinsu, kuma suka ji tsoron {Allah} suna da wata lada mai girma".
Dangane da wannan aya, ya zo cikin tarihi cewar bayan da kafiran Kuraishawa suka yi nasara a yakin Uhudu a kan hanyarsu ta komawa birnin Makkah, sai suka yi tunanin cewa abin da yafi dacewa tun da sun yi galaba a kan musulmai kuma mun karya karfin zuciyar mayakansu, kai wa su kaddamar da wani sabon hari kan birnin Madinah domin su kara sa murkushe sauran musulman da suka rage don kawo karshen addinin Musulunci. Labarin shirin makiya na sake kaddamar da hari kan musulmi ya kai ga Manzon Allah, don haka ya bada umurnin shirya rundunar yaki domin tunkarar makiya, ciki har da mayakan musulmi da suka samu raunuka a yakin Uhudu.
Shugaban mushirikan Makkah Abu-Sufyan ya samu labarin shirin da musulmai suka yi na hada ayarin yaki, sai ya yi tsammanin wata sabuwar runduna musulmai suka shirya domin sake tunkarar wani sabon yaki don daukan fansar hasarar da aka musu, saboda haka sai Abu-Sufyan ya janye aniyarsu na kai hari kan birnin Madinah, amma duk da cewar makiya ba su kai wani sabon hari kan Madinah ba, alkur'ani ya jinjinawa mayakan musulmi da suka samu raunuka a yakin Uhudu kuma suka sake shirin tunkarar wani sabon yaki tare da musu babban bushara.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
Abu mafi muhimmanci shi ne gudanar da shiri domin tunkarar duk wani aiki da mutum ya sanya a gaba musamman hakkin da ya rataya a wuyansa, shin ya samu damar aiwatar da aikin ko kuma bai samu sukunin gudanar da aikin ba, saboda duk aikin da aka gudanar da shi ba tare da gudanar da shiri ba ko aka gudanar da aikin ba a bisa son rai ba, to wannan aikin baya zama mai kima.
Halattar filin yaki ba tare da guzurin tsoron Allah da kyawawan ayyuka ba, to wannan azamar ba ta zama mai kima.
Yanzu kuma zamu saurari aya ta 173 ne da ke cikin suratuAli-Imrana kamar haka:-
الَّذِينَ قَالَ لَهُمُ النَّاسُ إِنَّ النَّاسَ قَدْ جَمَعُواْ لَكُمْ فَاخْشَوْهُمْ فَزَادَهُمْ إِيمَاناً وَقَالُواْ حَسْبُنَا اللّهُ وَنِعْمَ الْوَكِيلُ{173}
"Wadanda mutãne suka ce musu: "Lalle ne mutãne sun tãra (rundunõni) sabõda ku, don haka ku ji tsõronsu. Sai (wannan magana) ta kara musu ĩmãni, kuma suka ce: "Allah ya isar mana kuma mãdalla da madogara."
Daga cikin manyan hatsarori da suke barazana ga al'ummar musulmi musamman jama'ar da suke marassa zurfin tunani sune ganin girman makiya da raina matsayin addininsu, irin wannan tsoro da raina kai a gaban makiya a mafi yawan lokaci shi ke janyo kashe gwiwa wajen fuskantar makircin makiya, kuma hakan ba yana hana mutum ficewa zuwa yaki ba ne kawai, har ma yana gadar da tsoro da firgita da ke sanadiyyar hana sauran musulmi zuwa fagen yaki. Don haka maimakon tsoron makiya wajibi ne mutane su dogara ga Allah shi kadai, wanda dukkanin karfi da iko ke hannunsa kuma shi ne kadai ya wadata daga dukkan komai.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} A lokacin yaki mu kiyaye tare da sanya ido kan mutanen da makiya suka turo cikinmu da nufin cusa muggan tunani na tsoratarwa a tsakanin mutane.
{2} Duk wani karfi da matsayi na girma da makiyi ke da shi, lalle karfin Allah yana sama da duk wani karfi, don haka wajibi ne maimakon tsoron makiyi mu ji tsoron Allah tare da dogaro gare shi.
{3} Duk wani tsanani da wahala da ke cikin yaki, hakan yana da babban tasiri mai albarka, cikin albarkansa kuwa har da karfafa imanin mayaka da sauran musulmi.
To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 174-178 (Kashi Na 106)
Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannuka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Ali Imran, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.
Aya ta (174) Ali Imran:
فَانقَلَبُواْ بِنِعْمَةٍ مِّنَ اللّهِ وَفَضْلٍ لَّمْ يَمْسَسْهُمْ سُوءٌ وَاتَّبَعُواْ رِضْوَانَ اللّهِ وَاللّهُ ذُو فَضْلٍ عَظِيمٍ{174}
Sa'an nan suka jũya da wata ni'ima daga Allah da wata falala, wata cũta ba ta shãfe su ba, kuma suka bi yardar Allah. Kuma Allah ne Ma'abucin falala Mai girma.
Kamar yadda muka fada a cikin bayanin ayar da ta gabata, manzon Allah (SAW) ya umurci dukkanin musulmi da suka halarci yakin Uhud da su kara daura damara domin tunkarar rundunar mushrikai da suke nufin afkawa birnin madina, hakan ya sanya hatta wadanda suka ji raunuka ba a bar su a baya ba wajen aiwatar da wannan umurni na manzo, hakan ya jefa tsoro mai tsanani a cikin zukatan kafirai, inda suka ja baya, bayan sun kudiri aniyar yin kisan gilla a kan muslmi a cikin birnin Madina. Sai wannan ayar ta safka, domin yaba wa musulmi da kuma jaruntar da suka nuna.
Wannan ayar tana koyar da mu wani babba darasi, shi ne cewa idan musulmi suka san abin da ya rataya kansu kuma suka yi aiki da umurnin Allah, to za su samu taimakon ubangiji a cikin dukkanin halin da suka samu kansu na tsanani.
Aya ta (175) Ali Imran:
إِنَّمَا ذَلِكُمُ الشَّيْطَانُ يُخَوِّفُ أَوْلِيَاءهُ فَلاَ تَخَافُوهُمْ وَخَافُونِ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ{175}
Wancan, Shaidan ne kawai yake tsõratar da masõyansa. To, kada ku ji tsõronsu ku ji tsõrona idãn kun kasance mãsu ĩmãni.
Kamar yadda ya zo a cikin ayar da ta gabata, duk wanda ya nemi yardar Allah a cikin aikinsa, wani adadi na makiya Allah ba zai tsorata shi, koda kuwa yana cikin wani mawuyacin hali, kamar yadda muka ambata dangane da musulmi da suka samu raunuka a yakin Uhud, amma wannan ayar mai albarka tana yin Magana ne ga masu raunin imani, inda take jan hankalinsu da kada su ba shaidan kafa a cikin zukatansu, har ya samu damar kautar daga tafarkin Allah, idan mutum ya kama wata hanya da ba ta ubangiji ba, to hakika shaidan zai samu wurin zama a cikin zuciyarsa, zai hadu da kaskanci a cikin lamurransa, alhali ko daukaka tana ga Allah da manzonsa da kuma muminai.
Alkur'ani mai tsarki yana magana da musulmi yana cewa; idan kun kasance masu gaskiya a cikin imaninku, to kada ku karkata ga abin da shedan ke raya ma abokansa na daga tsoro, ku ji tsoron Allah shi kadai, kada ku bari karfin makiya ko yawansu ya tsorata ku ya firgita ku, domin kuwa duk yawansu da karfinsu ba su kai karfin Allah madaukakin sarki ba, kuma shi ne mai iko a kan komai.
Abubuwan da za mu koya na darasi daga wannan aya mai albarka:
1- Duk wata farfaganda da za a yada da nufin haifar da tsoro a cikin musulmi, tare da firgita su, wannan farfaganda ce ta shaidan.
2- Jin tsoro a filin yaki da makiya musulunci, dalili ne na raunin imani, da kuma yin biyayya ga rudun shaidan.
3- Tsoratarwa da yin barazana, daya ce daga cikin hanyoyin siyasar shaidanci, wadda irinta ce manyan kasashe da al'ummomi masu girman kai suke bi, da nufin gamawa da raunana a duniya.
Aya ta (176) da (177) Ali Imran:
وَلاَ يَحْزُنكَ الَّذِينَ يُسَارِعُونَ فِي الْكُفْرِ إِنَّهُمْ لَن يَضُرُّواْ اللّهَ شَيْئاً يُرِيدُ اللّهُ أَلاَّ يَجْعَلَ لَهُمْ حَظّاً فِي الآخِرَةِ وَلَهُمْ عَذَابٌ عَظِيمٌ{176} إِنَّ الَّذِينَ اشْتَرَوُاْ الْكُفْرَ بِالإِيمَانِ لَن يَضُرُّواْ اللّهَ شَيْئاً وَلهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ{177}
Kuma wadannan da suke gaugãwa a cikin kãfirci kada su bãta maka rai. Lalle ne su, bã zã su cũtar da Allah da kõmai ba. Allah yanã nufin bã zai sanya musu wani rabo a lahira ba, kuma suna da wata azãba mai girma.
Lalle ne, wadanda suka sayi kãfirci da ĩmani, ba zã su cũtar da Allah da kõmai ba. Kuma sunã da azãba mai radadi.
Bayan da wasu daga cikin musulmi suka saba umurnin manzon Allah a lokacin yakin Uhud, wasu daga cikinsu zuciyarsu ta raunana, sai suka fara jin tsoro, suka fara nuna damursu da kaduwarsu a fili, suna tambayar cewa yaya makomarsu za ta kasance idan kafirai suka yi nasara a kansu, kenan za su kaskanta. A cikin nassin wannan aya mai albarka Allah madaukakin sarki yana sheda ma manzonsa (SWA) cewa nasarar da kafirai suka samu a Uhud bayan da wasu daga cikin musulmi suka saba umurninsa, ba nasara ce ba ga kafirai, haka nan kuma ba wata daukaka ba ce balantana su daga ma musulmi kai, hakan lamari ne kawai da zai kara saka su cikin halakar kafirci da shirka, suna cikin hasarar duniya da kuma hasarar lahira. Haka nan kuma kafircin wadannan mushrikai ba zai cutar da Allah madaukakin sarki da komai ba. Maimakon haka ma su ne suke cutuwa da kafirci da shirkarsu, kuma su koma zuwa ga Allah su shiga azaba mai radadi.
Aya ta (178) Ali Imran:
وَلاَ يَحْسَبَنَّ الَّذِينَ كَفَرُواْ أَنَّمَا نُمْلِي لَهُمْ خَيْرٌ لِّأَنفُسِهِمْ إِنَّمَا نُمْلِي لَهُمْ لِيَزْدَادُواْ إِثْماً وَلَهْمُ عَذَابٌ مُّهِينٌ{178}
Kuma kada wadanda suka kãfirta su yi zaton cẽwa, lalle ne jinkirin da muke yi musu alhẽri ne ga rãyukansu. Munã yi musu jinkirin ne dõmin su kãra laifi kawai, kuma suna da azãba mai wulãkantarwa.
Allah Madaukakin sarki yana ba kafirai rata a cikin abin da suke yi na kafrci, wannan kuma sunna ce ta Allah, wannan kuwa ba gazawa ce daga Allah ba, a'a yana ba su dama ne domin su yi abin da suke so, su yi girman kai su yi jiji da kai, su yi kafirci da fitsara a bayan kasa, ta yadda Allah zai kama su da hujja, wanda hakan ke tabbatar da adalci irin na Allah. Domin kuwa da a ce lokacin da suke cikin kafircinsu za su dawo su tuba su kadaita Allah, su bi manzonsa, to da Allah ya gabatar musu dukkanin abin da suka yi masa na manyan laifuka.
To amma kafirai da suke cikin duhun dimuwa, suka yi nisa da hasken shiriya, suna ganin hakan tamkar gazawa ce daga Allah, domin kuwa ya ce kada a yi kaza, su kuma sun yi wannan abun ba tare da wani abu ya same su ba, wannan sai ya kara nisantar da su hasken imani, tare da kara nutsewa a cikin bata da duhun kafirci da shirka.
A cikin wannan aya za mu darussa kaamar haka:
1- Ratar da Allah yake baiwa masu saba masa ba gazawa ba ce, Allah yanayin hakan ne saboda dalilai guda biyu. Na daya: saboda ya ba su lokaci ko wata kila daga baya su hankalta su dawo ya tuba su koma zuwa ga Allah. Na biyu: Idan har mutum ya bar gidan duniya a kana bin da yake yi ba tare da ya tuba, to Allah zai kama shi da hujja.
2- Tsawon rayuwa ba shi ne muhimmi ba, yin amfani da ita wajen biyayya ga Allah shi ne muhimmi. Imam Sajjad (AS) yana rokon Allah da cewa; idan rayuwarsa za ta zama abin wasa a hannun shaidan, to Allah ya taikaita rayuwarsa a kan imani da biyayya gare shi.
3- Kada a yanke hukunci kai tsaye da ayyukan kafirai da azzalumai, karshensu shi ne abin yanke hukunci da shi.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 179-182 (Kashi Na 107)
Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannuka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Ali Imran, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.
Aya ta (179) Ali Imran:
مَّا كَانَ اللّهُ لِيَذَرَ الْمُؤْمِنِينَ عَلَى مَا أَنتُمْ عَلَيْهِ حَتَّىَ يَمِيزَ الْخَبِيثَ مِنَ الطَّيِّبِ وَمَا كَانَ اللّهُ لِيُطْلِعَكُمْ عَلَى الْغَيْبِ وَلَكِنَّ اللّهَ يَجْتَبِي مِن رُّسُلِهِ مَن يَشَاءُ فَآمِنُواْ بِاللّهِ وَرُسُلِهِ وَإِن تُؤْمِنُواْ وَتَتَّقُواْ فَلَكُمْ أَجْرٌ عَظِيمٌ{179}
Allah bai kasance yana barin mũminai a kan abin da kuke kansa ba, sai ya rarrabe mummũna daga mai kyau. Kuma Al lah bai kasance yanã sanar da ku gaibi ba. Kuma amma Allah yana zãben wanda ya so daga manzanninsa. Sabõda haka ku yi ĩmãni da Allah da manzanninsa Kuma idan kun yi ĩmãni kuma kuka yi takawa, to kunã da lãdã mai girma.
Wannan ayar ita ce ayar karshe da ke yin magana kan yakin Uhud a cikin wannan sura, inda take yin hannuka mai sanda ga muminai da suka halarci wannan yaki, da cewa kada su yi zaton Allah madaukakin sarki zai bar muminai haka nan sake, Allah yana kawo jarabawa a cikin mumunai domin ya banbamce masu imani na gaske da kuma bare gurbi, domin kuwa ba dukkanin mutanen da suke shiga cikin muminai ne suke da imani irin na muminai ba, a kan haka sai Allah ya sanya tsanani da wahala a wasu lokuta a tafarkinsa, domin hakan ya zama hanyar tantance imani na gaskiya da kuma bare gurbi.
Allah madaukakin sarki ba ya yin hakan saboda rashin masaniya dangane da imanin bayinsa, yana yin hakan hakan ne domin komai ya zama zahiri ga muminai na gaskiya, su san wane ne ke tare da manzonsa da gasket, wane ne kuma yake tare da shi saboda wata maslaha ta kashin kansa kawai, ta yadda a ranar Uhud hakan ta faru, inda Allah ya jarraba muminai, kuma masu imani na gaskiya daga cikinsu suka ci wannan jarabawa, yayin munafukai suka saba umurnin manzon Allah kuma suka fadi jarabawa.
Darussan koyo daga wannan aya mai albarka:
1- Allah madaukakin sarki yakan kyale kafirai su yi ta kafircinsu har sai ranar da zai kama su bisa hujja, amma kuma bisa sunna ta Allah ba ya barin muminai haka nan kara zube har sai ya yi ta jaraba imaninsu, domin tabbatar da cewa da gasket suke yi.
2- Kada mu yi ta bin diddigin sirrin mutane domin kuwa Allah bai yi umurni da hakan ba, shi ne ya san sirrin kowa daga cikin bayinsa.
3- Allah madaukakin sarki shi kadai ne wanda ke da ilimin gaibi, sai kuma wasu daga cikin bayinsa da ya sanar da su wasu abubuwan na gaibu saboda matsayinsu a wurinsa.
4- Abin da ya rataya kanmu shi ne yin imani da Allah da kuma jin tsoronsa, da aikata umurninsa gami da hanuwa daga haninsa.
Aya ta (180) Ali Imran:
وَلاَ يَحْسَبَنَّ الَّذِينَ يَبْخَلُونَ بِمَا آتَاهُمُ اللّهُ مِن فَضْلِهِ هُوَ خَيْراً لَّهُمْ بَلْ هُوَ شَرٌّ لَّهُمْ سَيُطَوَّقُونَ مَا بَخِلُواْ بِهِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَلِلّهِ مِيرَاثُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَاللّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ{180}
Kuma kada wadannan da suke yin rõwa da abin da Allah ya bã su daga falalarsa su yi zaton shĩ ne mafi alhẽri a gare su, A'a, shĩ mafi sharri ne a gare su. Zã a yi musu sakandami da abin da suka yi rõwa da shi a rãnar kiyãma, kuma ga Allah gãdon sammai da kasa yake, kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Masani ne.
Ayoyin da suka gabata sun yi mana hannunka mai sanda ne lan matsayin yaki ko jihadi a addinin muslunci, da yadda mumunai suke sadaukantar da rayukansu saboda daukakar addini, yayin da wannan aya take yi mana hannuka mai sanda kan muhimamncin ciyarwa, fitar da hakkin Allah, taimaka ma mai rauni da mabukaci, domin mumini mai imani na gaskiya ba zai iya hana mabukaci ba, bil hasali ma tausayi da son taimako na daga cikin alamomi na mumini, domin kuwa mumini yana so ma dan uwansa abin da yake so ga kansa. Hakika lamarin ciyarwa da taimakon raunana a cikin al'umma, yana daya daga cikin hanyoyi na jarabawar ubangiji ga muminai, a lokacin da Allah ya ba wani dukiya, kuma bai aiwatar da abin da ya kamata ya yi da ita ba ta hanyar fitar hakkin Allah, wato fitar da zakka da khumusi da kuma taimakon mabukata, to hakika ya fadi jawabawa.
Daga wannan aya mai albarka za mu koyi darussa kamar haka:
1- Yin tunanin cewa, fitar da dukiya domin taimakon maras karfi ko mabukaci zai yi sanadiyar raguwar dukiyar, hakan babbar tawaya ce ga ma'abucin wannan tunani, domin kuwa dukiya na daga cikin falaloli na Allah da yake baiwa bayinsa gwargwadon yadda ya so da kuma hikimarsa, domin kuwa wanda Allah ya ba shi dukiya a cikin mutane hakan ba ya nufin shi ya fi sauran mutanen matsayi a wurin Allah ba ne, bil hasali ma ta hanyar yin amfani da dukiyarsa kamar yadda Allah ya yi umurni ne hakan zai sama masa matsayin a wurin Allah, kuma ciyar da dukiyar da yin taimako shi ne zai jawo albarka a cikinta tare da karin bunkasarta, sabanin taskace ta da haramta ta ga mabukata.
2- Dukkanin dukiyar da ba a yi amfani da ita kamar yadda Allah ya yi umurni ba, babu alkhairi a cikinta, maimakon hakan ma za ta bude kofofin sharri ga ma'abucinta.
3- Dukkanin abin da ke cikin duniya na ubangiji ne, mun zo duniya hannu biyu, kuma hannu biyu za mu koma.
4- Lahira wuri ne da aiki na gari ke amfanar da m'abucinsa, yayin da tarin dukiya a gidan duniya ba zai yi amfani a lahira ba.
Aya ta (181) da (182) Ali Imran:
لَّقَدْ سَمِعَ اللّهُ قَوْلَ الَّذِينَ قَالُواْ إِنَّ اللّهَ فَقِيرٌ وَنَحْنُ أَغْنِيَاء سَنَكْتُبُ مَا قَالُواْ وَقَتْلَهُمُ الأَنبِيَاءَ بِغَيْرِ حَقٍّ وَنَقُولُ ذُوقُواْ عَذَابَ الْحَرِيقِ{181} ذَلِكَ بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيكُمْ وَأَنَّ اللّهَ لَيْسَ بِظَلاَّمٍ لِّلْعَبِيدِ{182}
Lalle ne, Allah yã ji maganar wadanda suka ce: " Allah fakĩri ne, mũ ne wadãtattu." za mu rubũta abin da suka fada, da kisan da suka yi wa Annabãwa bã da wani hakki ba kuma mu ce: "Ku dandani azãba mai kuna!
"Wannan (azãbar) kuwa sabõda abin da hannuwanku suka gabãtar ne. Kuma lalle ne Allah bai zama mai zãlunci ga bãyinsa ba."
Ya zo a cikin littafai da dama na tafsirin kur'ani mai tsarki cewa, manzon Allah (SAW) ya aike da wata wasika zuwa ga kabilar yahudawa da ke gefen birnin Madina, yana kiransu zuwa ga musulunci, da yin sallah da kuma bayar da zakka da ciyar da dukiyoyinsu domin Allah, sai shugaban kabilar yahuwan yake yin izgili da wannan wasika, har ma yana cewa: Allah shi ne mabukaci a wurinmu, mu ba mu ne mabukata ba, ya roke mu da mu ba shi kudi, ya yi mana alkawarin cewa a ranar kiyama zai mayar mana da yawa.
Bayan wannan furuci na shugaban yahudawan ne sai wannan aya mai albarka ta safka, inda Allah ya sheda ma manzonsa cewa wadanda suka yi wannan furuci za su shiga cikin azabar jahammana a ranar kiyama.
Darussan koyo daga wadannan ayoyi:
1- Kiran da Allah ya yi mana na ciyar da dukiyarmu, mu taimaka ma marassa galihu, hakan ba ya nufin Allah na da bukata zuwa ga dukiyarmu, domin kuwa hakikanin lamarin ma shi ne dukiyar ta Allah ce, ta zo hannunmu ne kawai ta wasu hanyoyi.
2- Dole ne a kiyaye abubuwan da ake tsarkakewa a addini, keta alfarmar ababe masu tsarki na addini, yana tattare da bala'oi a cikin al'umma.
3- Yin izgili ga manzon Allah (SAW) yana gadar da fushin Allah mai tsanani, a duk lokacin da aka yi wa manzon Allah izgili, to Allah ne da kansa ke rama masa.
4- Allah yakan bar masu kafirce ma ayoyinsa su ci karensu babu babbaka a gidan duniya, a ranar kiyama kuma ya saka su cikin azaba sakamakon abin da suka aikata a bisa hujja.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 183-186 (Kashi Na 108)
Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannuka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Ali Imran, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.
Aya ta (183) Ali Imran:
الَّذِينَ قَالُواْ إِنَّ اللّهَ عَهِدَ إِلَيْنَا أَلاَّ نُؤْمِنَ لِرَسُولٍ حَتَّىَ يَأْتِيَنَا بِقُرْبَانٍ تَأْكُلُهُ النَّارُ قُلْ قَدْ جَاءكُمْ رُسُلٌ مِّن قَبْلِي بِالْبَيِّنَاتِ وَبِالَّذِي قُلْتُمْ فَلِمَ قَتَلْتُمُوهُمْ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ{183}
Wadanda suka ce: "Lalle ne Allah yã yi alkawari gare mu, kada mu yi ĩmãni da wani manzo, sai yã zo mana da baiko da wuta za ta ci." Ka ce: "Lalle ne wasu manzanni sun je muku, a gabãnĩna da hujjõji bayyanannu, kuma da abin da kuka fada, to, don me kuka kashe su, idan kun kasance mãsu gaskiya?" Wasu daga cikin yahudawa suna kokarin kare kansu da kawo hujjoji marassa tushe kan rashin yin imani da manzon Allah (SAW) , wannan aya mai albarka tana yin ishara da wasu daga cikin irin waddannan yahudawa, da suke cewa ba za su yi iamni da wani manzo ba har sai ya zo musu da wata dabba ya yi layya da ita, kuma tsawa ta zo daga sama ta kone wannan yankakkiyar dabbar a gaban mutane, wanda hakan ke nuna an karbi layyarsa, akmar dai yadda ya faru tsakanin Habila da Kabila 'ya'yan annabi Adamu (AS) inda Allah ya karbi layyar Habila ta hanyar safkar da tsawa ta kone abin layyar, shi kuma kabila ba a karba daga gare shi ba.
Kur'ani mai tsarki ya mayar damartani ga irin wadannan yahudawa da cewa, ba dole ne mu'ujizar dukaknin annabawa ta yi daidai da ta juna ba, kowane annabi yana da mu'ujizarsa, na biyu kuma, annabawan da suka zo ma yahudawa da mu'jizozi ba su karbe sub a, har ma sun kasha wasu daga cikin annabawan Allah da dama da suka zo mus da mu'ujiza, kuma hatta ma a cikin littafin Attaura an ambaci hakan.
Darussan koyo daga wannan aya mai albarka:
1- Baya kamata a danganta karya ga Allah domin gudu daga karbar gaskiya.
2- Yin layyar dabbobi saboda Allah ya samo asali tun daga lokacin annabawan da suka gabata, har ma yazo a matsayin mu'ajiza ga wasu daga cikin annabawan Allah.
Aya ta (184) Ali Imran:
فَإِن كَذَّبُوكَ فَقَدْ كُذِّبَ رُسُلٌ مِّن قَبْلِكَ جَآؤُوا بِالْبَيِّنَاتِ وَالزُّبُرِ وَالْكِتَابِ الْمُنِيرِ{184}
To, idan sun karyata ka, to lalle ne, an karyata wasu manzanni a gabãninka, sun je musu da hujjõji bayyanannu da littattafai, da kuma Littafi mai haske.
Wannan aya mai alabarka tana yin Magana da manzon allah kai tsaye, inda take sheda masa cewa idan mushrikai da yahudawa sun karta sakon da ya zo da shi daga Allah, to da ma wannan sunna ce ta masu karyata manzannin Allah, domin kuwa annabawan da suka gabace shi sun fuskanci haka daga masu jayayya da ayoyin Allah, duk kuwa da cewa sun zo musu da dalilai dake tabbatar da annabcinsu, wadanda suke yanke duk wata hujja, to amma haka sunnar Allah ta gabata. Wasu daga cikin annabawa sun samu mabiya da suka yi mani da su, wasu kuma an kashe su a lokacin da suka fara kira, wasu kuma sun dauki dogon lukaci suna kira, amma kadan ne daga cikin mutanensu suka yi imani.
Darussan koyo daga wannan aya mai albarka:
1- Sanin abin da ya faru a cikin tarih, da yadda annabawan Allah suka sha wahala wajen isar da sakon ubangiji, na tabbatar wa 'yan baya cewa bin tafarkin ubangiji na tattare wahalhalu da kuma bukatar hakuri.
2- Kiran manzon Allah bai takaitu da lokacin da ya rayuwa ba, kasantuwar shi ne manzon karshe, babu wani manzo a bayansa, kiransa da sakon day a zo da shi daga Allah, shi ne wanzajje har zuwa ranar tashin kiyama.
Aya ta (185) Ali Imran:
كُلُّ نَفْسٍ ذَآئِقَةُ الْمَوْتِ وَإِنَّمَا تُوَفَّوْنَ أُجُورَكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فَمَن زُحْزِحَ عَنِ النَّارِ وَأُدْخِلَ الْجَنَّةَ فَقَدْ فَازَ وَما الْحَيَاةُ الدُّنْيَا إِلاَّ مَتَاعُ الْغُرُورِ{185}
Kõwane rai mai dandanar mutuwa ne. Kuma ana cika muku ladarku ne a rãnar kiyãma. To, wanda aka nĩsantar daga barin wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to lalle ne yã tsĩra. Kuma rãyuwar dũniya ba ta kasance ba fãce jin dãdi na rũdi.
Wannan aya mai albarka tana yin hannunka mai sanda ga masu imani , amsu biyayya ga annabawan Allah, da su san cewa duk abin da zai same su a tafarkin ubangiji iyakar shi gidan duniya, kuma kowa zai bar gidan duniya, da wanda ya kyautata da kuma wanda ya munana, banbamci dai shi ne, su wadanda suka kyautata suka yi iamani da aiki na gari, Allah zai cika msuu ladarsu, domin babban rabo a ranar kiyama shi ne mutum ya kubuta daga fushin Allah ya shiga cikin rahamarsa. Wadanda suka kafirce ma Allah ba komai ba ne ya rude illa duniya da kyale-kyalenta mai karewa. A kan haka wannan wannan aya take fadakar da muminai kan wajabcin yin hakuri da yin juriya kan duk wasu musibu a tafarkin ubangiji, domin samun babban rabo a ranar kiyama.
Darussan koyo daga wannan aya:
1- Mutuwa tana kan kowa, hatta annabawan Allah ba za su dawwama agidan duniya ba, balantana sauran mutane, muminai da wadanda ba muminai ba.
2- Mutuwa ba karshen rayuwa ba ce, a 'a cirata ce daga rayuwa zuwa wata rayuwar ta daban, wasu za su farin ciki da wannan sabuwar rauwa bayan mutuwa, wasu kuma za su yi bakin ciki da nadama.
3- Kada dukiyoyi da mulki da jin dadin duniya su rude mu, domin kuwa ba masu dawwama ba ne, ni'ima da jin dadin lahira shi ne madawwami.
Aya ta (186) Ali Imran:
لَتُبْلَوُنَّ فِي أَمْوَالِكُمْ وَأَنفُسِكُمْ وَلَتَسْمَعُنَّ مِنَ الَّذِينَ أُوتُواْ الْكِتَابَ مِن قَبْلِكُمْ وَمِنَ الَّذِينَ أَشْرَكُواْ أَذًى كَثِيراً وَإِن تَصْبِرُواْ وَتَتَّقُواْ فَإِنَّ ذَلِكَ مِنْ عَزْمِ الأُمُورِ{186}
Lalle ne zã a jarraba ku a cikin dũkiyarku da rãyukanku, kuma lalle ne kuna jin cũtarwa mai yawa daga wadanda aka bai wa littãfi a gabãninku da kuma wadanda suka yi shirki. Kuma idan kun yi hakuri, kuma kuka yi takawa, to lalle ne wannan yana daga manyan al'amurra.
Kamar yadda ya zo a cikin tarihi cewa, a lokacin da musulmi suka yi hijira daga Makka zuwa Madina, mushrikan Makka sun kai hari kan musulmi da dukiyoyinsu, sun cutar da su matuka. Haka nan kuma bayan da suka zo birnin Madina, yahudawa sun cutar da su, musamman ma matan musulmi, inda suka yi musu wulakanci saboda tsananin kiyayya da addinin muslunci. Wannan lamari ya ci gaba da faruwa, har zuwa lokacin da manzon allah (SAW) ya bayar da umurni kan cewa, duk bayahuden da ya kara wulakanta matan musulmi a Madina jininsa ya halitta, to daga lokacin sai yahudawa suka ji tsoro, domin kuwa sun san san matsayin umurnin manzon Allah a wajen musulmi. Saboda haka wannan aya tana kara karfafa gwiwar musulmi ne wajen yinhakuri bisa cutarwar mushrikai da makiya addini musulunci yahudawa da sauransu, domin kuwa idan musulmi suka yi hakuri , to hakan zai zama labari a wata rana.
Darussan koyo daga wannan aya mai albarka:
1- Rayuwa baki dayanta jarabawa ce, abin da mutum ya mallaka ma a cikinta shi ma jarabawa ce, domin Allah ya ga yada bayinsa za su yi aiki da umurninsa, da kuma hanuwa daga hanninsa.
2- Masu kiyayya da addinin musulunci a koda yaushe za su iya hada kai domin ganin bayan wannan addini, ko da kuwa akwai sabani a tsakaninsu kan wasu abubuwa, ko da kuwa akwai banbanci addini a tsakaninsu, amma in dai sun hadu kan kiyayya da musulunci to za su iya hada kai domin cutar da musulmi, kamar yadda mushrikai suka hada kai da yahudawa domin cutar da manzon Allah da sauran muminai a Madina.
Da wannan muka kawo karshen shirin na yau, sai a kasance tare da mu a shiri na gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 187-190 (Kashi Na 109)
Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannuka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Ali Imran, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.
Aya ta (187) Ali Imran:
وَإِذَ أَخَذَ اللّهُ مِيثَاقَ الَّذِينَ أُوتُواْ الْكِتَابَ لَتُبَيِّنُنَّهُ لِلنَّاسِ وَلاَ تَكْتُمُونَهُ فَنَبَذُوهُ وَرَاء ظُهُورِهِمْ وَاشْتَرَوْاْ بِهِ ثَمَناً قَلِيلاً فَبِئْسَ مَا يَشْتَرُونَ{187}
Kuma a lõkacin da Allah Ya riki alkawarin wadanda aka bai wa Littãfi, "Lalle ne za bayyana shi ga mutãne, kuma bã zã ku bõye shi ba." Sai suka jẽfar da shi a bãyan bãyansu, kuma suka sayi 'yan kudi kadan da shi. To, tir da abin da suke saye.
A koda yaushe a cikin al'ummomi, mutanen da suke su ne a matsayi tsaka tsaki, suna yin biyayya ne ga manya daga cikin al'umma, wannan ne ya sanya idan manya suka gyaru sai al'umma ta gyaru, idan kuma suka lalace hakan zai yi tasiri wajen lalacewar al'ummar.
Daya daga cikin abubuwan da Allah ya dora ma masana ma'abuta ilimi daga cikin al'umma shi ne, su bayyana ma mutane abin da yake daidai da wanda ba daidai ba, su gayama mutane abin da yake gaskiya, kada su boye ayoyin Allah, domin boye gaskiya da kange mutane daga fahimtar abin da ya zo a cikin umurnin babban laifi ne.
Kamar yadda ya tabbata a cikin tarihi cewa, masana daga cikin wadanda aka baiwa littafi sun yi shir da bakunansu dangane da busharar da ta zo a cikin littafan attauara da linjila, kan bayyanar manzon karshe Muhammad (SAW) ta yadda suka bar mutanensu cikin duhun jahilci, maimakon haka ma a hankali-a hakali sun yi ta cire duk wata bushara kan bayyanar manzon Allah na karshe a cikin littafan na su, domin kada su rasa mabiya.
Darussan da ke cikin wannan aya:
1 – Ba wai kawai fadar abin da gaskiya ne laifi ba, a'a shi kansa yin shiru kana bin da yake gaskiya laifi ne.
2 – Masana daga cikin al'umma abin tamabaya ne kan shiriya ko batar al'umma.
Aya ta (188) Ali Imran:
لاَ تَحْسَبَنَّ الَّذِينَ يَفْرَحُونَ بِمَا أَتَواْ وَّيُحِبُّونَ أَن يُحْمَدُواْ بِمَا لَمْ يَفْعَلُواْ فَلاَ تَحْسَبَنَّهُمْ بِمَفَازَةٍ مِّنَ الْعَذَابِ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ{188}
Kada ka yi zaton wadanda suke yin farin ciki da abin da suka bãyar, kuma suna son a yabe su da abin da ba su aikatã ba. To, kada ka yi zaton su da tsĩra daga azãba. Kuma suna da azãba mai radadi.
Mutane sun kasu kashi uku ta fuskar aiki da manufar aikin nasu, kashi na farko su ne masu yin aiki saboda Allah, ba son wani yasan abin da suka yin a alkhairi in ba Allah, domin kuwa saboda shi suka yi. Kashi na biyu kuma su ne wadanda suke yin aikin alhairin, amma kuma a lokaci guda suna mutane su san sun yi domin a yaba musu, su ne ake kira masu aikin riya. Kashi na uku kuma su ne wadanda ba sa yin aikin alkhairi, amma kum suna son yabo daga mutane, wannan aya ta zargi kashi na biyu da na uku, tare da bayyana su a matsayin wadanda za su tashia tutar babu, maimakon haka ma za su hadu da fushin ubangiji a ranar kiyama.
Darussan koyo daga wannan aya:
1 – Daya daga cikin abubuwan da ke nisantar da mutum daga sahihiyar turba ta ubangiji shi ne jiran yabo ba tare da aiki ba.
2 – Duk aikin da aka yi shi ba domin neman yardarm Allah ba shi kadai, ba zai amfani ma'abucinsa a wurin ubangiji ba.
3 – Son yabo da neman matsayi hanya ce da shaidan kan yi amfani da ita domin halakar da 'yan adam.
4 – Mai aikata wani laifi na sabo mai yiwuya ya fadaka ya daina ya tuba, amma mutane masu jin kansu da meman matsayi sukan yi nisa a cikin irin wannan tabi'a, ta yadda sukan kai matsayin da shaidan kan zama majibincin lamarinsu, wa iyazul billah.
Aya ta (189) da (190) Ali Imran:
وَلِلّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَاللّهُ عَلَىَ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ{189} إِنَّ فِي خَلْقِ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَاخْتِلاَفِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ لآيَاتٍ لِّأُوْلِي الألْبَابِ{190}
Kuma ga Allah mulkin sammai da kasa yake. Kuma Allah, a kan kõmai mai ĩkon yi ne. Lalle ne, a cikin halittar sammai da kasa da sãbãwar dare da yini akwai ãyõyi ga ma'abũta hankali.
Daya daga cikin abubuwan da kur'ani mai tsarki ya kebanta da su shi ne, kiran musulmi zuwa ga tunani a cikin ayoyin Allah da ke cikin halittunsa, domin kara samun sakankancewa da ubangiji. Imani yana da abubuwan da suke kara karfafa shi tare da kai shi zuwa ga babban matsayi, baya ga sauran ayyuka na ibada da Allah ya farlanta, da kuma wadanda aka so yi na mustahabbi, tare da aikata umurnin Allah da hanuwa da haninsa a cikin dukaknin lamurra, yin tunani kan halittar sammai da kassai da abin da ke tsakaninsu, da kuma yadda Allah yake sarrafa dare da rana sauran ayoyin ubangiji, hakan yana matsayin ibada ne, kuma yana kara karfafa imanin musulmi.
An bayyana wadannan ayoyin biyu daga cikin ayoyin da ake son mutum ya karanta kafin ya fara sallar dare (kiyamullail) domin kuwa suna tuna mutum mutum da kudirar Allah, da kara sanin matsayin girmansa.
Darussan koyo daga wadannan ayoyi masu albarka:
1 – Duk da irin girman da kasa take da shi, idan aka hada girmanta da girman sama da fadinta, za a ga kasa ba komai ba ce, to ina ga girman kudira ta Allah wanda ya halicci sama da kasa da dukkanin abin da ke tsakaninsu, kuma yake da iko a kansu?
2 – Sanin yanayin halittar duniya da sirrin da ke cikinta, wata shimfida ce ta sanin ubangiji, kamar yadda sanin ilimi na dabi’a zai iya taimaka mutum wajen sanin Allah da karfin ikonsa da kuma hikimarsa.
3 – Yin tunani kan halittar duniya da abin da ke cikinta d akuma sama da yadda take birbishin kasa domin sanin kudirar Allah, wannan shi ne ilimi, amma tunani ko samun masaniya kan halittar duniya da ba zai kai ma’abucinsa zuwa ga sanin kudirar Allah ba, hakan ya zama jahilci na hakika.
Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na yau, sai idan Allah ya kai mu shiri nagaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya. Wassalamu alaikum wa rahmatullah.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 191-195 (Kashi Na 110)
Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannuka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Ali Imran, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.
Aya ta (191) Ali Imran:
الَّذِينَ يَذْكُرُونَ اللّهَ قِيَاماً وَقُعُوداً وَعَلَىَ جُنُوبِهِمْ وَيَتَفَكَّرُونَ فِي خَلْقِ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ رَبَّنَا مَا خَلَقْتَ هَذا بَاطِلاً سُبْحَانَكَ فَقِنَا عَذَابَ النَّارِ{191}
Wadanda suke ambatar Allah a tsaye da zaune da a kan sãsanninsu, kuma suna tunãni a kan halittar sammai da kasa: "Yã Ubangijinmu! Ba ka halicci wannan a kan banza ba. Tsarki ya tabbata gare ka! Ka tsare mu daga azãbar wuta.
Wannan aya mai albarka tana yin nuni ne da cewa ma'abota hankali su ne wadanda suke tuna Allah da ambatonsa tare da yin tunani a cikin halittar sammai da kassai, domin kuwa sun san wannan duniya da abin da ke cikinta ba wai kawai tana da mahalicci ban e, a'a shi mahaliccin ya yi ta ne da wata manufa, ya kuma yana tafiyar da ita kan tsari na musamman, kamar yadda mutum kan gina gida, yana yin hakan ne da manufa ta musamman, da kuma tsarin da yake son gidan ya kasance.
Idan mutum ya fahimci cewa lallai Allah madaukakin sarki mahaliccin kowa da komai ya halicci duniya ne da wata manufa ta musamman, to a nan kuma mutum zai riski cewa to mu kanmu da muke a cikin duniyar Allah bai halicci mu kawai domin cike wuri ba, kuma bai bar rayuwarmu kara zube ba, yana da manufar halittarmu, da kuma tsari day a dora rayuwarmu a kai na dabi'a, da kuma tsari na dokoki da yake son rayuwarmu ta tafi a kansa.
Darussan koyo daga wannan aya mai albarka:
1 – Tuna Allah da ambatonsa ya dace da kowane wuri da a lokaci a cikin duniya, ma'abota hankali da tunani na gaskiya su ne masu tuna Allah da ambatonsa a cikin wane yanayi.
2 – Imanin mutu yanasamun kima da matsayi ne idan ya ginu kan sani, tunani kan kudirar Allah da zikiri na ambato, gishikai ne da suke karfafa imanin mumini.
3 – Babbar manufar halittarmu a cikin wannan dunya ita ce sanin Allah da bauta masa, da samun kusanci zuwa gare shi ta hanyar bin umurinsa, da nisantar haninsa.
Aya ta (192) Ali Imran:
رَبَّنَا إِنَّكَ مَن تُدْخِلِ النَّارَ فَقَدْ أَخْزَيْتَهُ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنصَارٍ{192}
"Ya Ubangijinmu! Lalle ne wanda ka shigar a cikin wuta, to hakĩka ka tozarta shi kuma bãbu wasu mataimaka ga azzãlumai. Wannan aya tana yin nuni da yadda sakamakon ubangiji yake kasancewa kan wadanda suka yi watsi da umurnin Allah a rayuwar duniya. Masu hankali wadanda wannan ayar ke nuni da su wato muminai na gaskiya, suna cewa duk wanda Allah ya sanya a cikin wutarsa hakika ya tabar da shi , ya wulakantar da shi. Duk kuwa da cewa su muminai masu ambaton Allah ba suna bauta ma Allah domin ya cancanci hakan, hakika suna tsoron fushin Allah da azabarsa, kuma lallai suna son rahamarsa da ni'imar da ya yi alkawali ga bayinsa na gari a ranar kimayama, to amma wadanda suka yi nisa cikin sanin Allah koda babu wadannan abubuwan za su bauta masa saboda sanin girmansa da cancantar da hakan.
1 – Rashin yin tunani kan halittar ubangiji, yana cutar da ran mutum, kuma babban zalunci ne ga ruhi.
2 – Azzalumai da suka yi watsi umurnin Allah a rayuwar duniya, a ranar kiyama za a haramta musu ceton wadanda Allah ya ba su izinin yin ceto ga wanda suke so.
Aya (193) da (194) Ali Imran:
رَّبَّنَا إِنَّنَا سَمِعْنَا مُنَادِياً يُنَادِي لِلإِيمَانِ أَنْ آمِنُواْ بِرَبِّكُمْ فَآمَنَّا رَبَّنَا فَاغْفِرْ لَنَا ذُنُوبَنَا وَكَفِّرْ عَنَّا سَيِّئَاتِنَا وَتَوَفَّنَا مَعَ الأبْرَارِ{193} رَبَّنَا وَآتِنَا مَا وَعَدتَّنَا عَلَى رُسُلِكَ وَلاَ تُخْزِنَا يَوْمَ الْقِيَامَةِ إِنَّكَ لاَ تُخْلِفُ الْمِيعَادَ{194}
Yã Ubangijinmu! Lalle ne mũ mun ji Mai kira yanã yin kira zuwa ga ĩmãni cẽwa, 'Ku yi ĩmãni da Ubangijinku.' Sai muka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu Ka gãfarta mana zunubanmu, kuma Ka kankare miyãgun ayyukanmu daga gare mu. Kuma ka karbi rãyukanmu tãre da mutãne na gari.
"Yã Ubangijinmu! Ka bã mu abin da ka yi mana alkawari a kan manzanninka, kuma kada ka tozarta mu a rãnar ¡iyãma. Lalle ne kai bã ka sãbãwa alkawari."
Ma'abota hankali ba wai waia suna bin abin da suka fahimta ba ne danganae da ubangiji ta hanyar tunaninsu, a a stunaninsu yana taimaka musu ne wajen gano ubangiji, a lokacin da mazannin Allah suka zo da sako sukan bi annabawan Allah ba tare da wata jayayya ba, domin kuwa sun san cewa lallai wannan sakon yana tabbatar da abin da suka fahimta ne, da ke tabbatar da cewa wanda ya halicci duniya da abin da ke cikinta mahalicci daya ne, kuma shi ne ya cancanci bautar dukkanin talikai.
Ta hanyar sakon da annabawan Allah suka zo da shi suke fahimtar cewa bayan rayuwar duniya akawai sakamako na azaba ga wadanda ba su bi Allah ba, kamar yadda akwai sakamako na ni'ima da lada mai yawa ga wadanda suka kiyaye dokoki na Allah a rayuwar duniya.
Saboda haka ne suke neman gafar ubangiji da rahamarsa kan kurakuran da suka aikata.
Darussan koyo daga wadannan ayoyi masu albarka:
1 – Karbar gaskiya da yin aiki da ita hakan na daga cikin alamu na cikar hankali.
2 – Yin Istigfari da tuba daga ayyukan zunubi, na tafiya ne tare da imani a kowane lokaci, barin istigfari na kawo raunin imani da kawar da natsuwar ruhi.
3 – Zurfin tunani kafin aikata duk wani aiki, na daga cikin alamun masu imani na gaskiya.
Aya ta (195) Ali Imran:
فَاسْتَجَابَ لَهُمْ رَبُّهُمْ أَنِّي لاَ أُضِيعُ عَمَلَ عَامِلٍ مِّنكُم مِّن ذَكَرٍ أَوْ أُنثَى بَعْضُكُم مِّن بَعْضٍ فَالَّذِينَ هَاجَرُواْ وَأُخْرِجُواْ مِن دِيَارِهِمْ وَأُوذُواْ فِي سَبِيلِي وَقَاتَلُواْ وَقُتِلُواْ لأُكَفِّرَنَّ عَنْهُمْ سَيِّئَاتِهِمْ وَلأُدْخِلَنَّهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الأَنْهَارُ ثَوَاباً مِّن عِندِ اللّهِ وَاللّهُ عِندَهُ حُسْنُ الثَّوَابِ{195}
Sabõda haka Ubangijinsu Ya karba musu cẽwa, "Lallene Nĩ bã zan tozartar da aikin wani mai aiki ba daga gare ku, namiji ne ko kuwa mace, sãshenku daga sãshe. To, wadanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidãjensu, kuma aka cũtar da su a cikin tafarkina, kuma suka yi yãki, kuma aka kashe su, lalle ne zan kankare musu munanan ayyukansu, kuma lalle ne zan shigar da su gidãjen Aljanna (wadanda) koramu ke gudãna daga karkashinsu, hakan sakamako daga wurin Allah. Kuma a wurinsa akwai kyakkyawan sakamako.
A cikin ayoyin da suka gabata mun ga yadda aka bayyana alamomin muminai na hakika, inda muka fahimci cewa imanin yana samun kafuwa ne idan ya ginu kan sani, wanda hakan ke ma'abucinsa zuwa ga mika wuwa ga Allah mikawa, suna rokon gafar ubangiji daga zunubbansu, sai Allah madaukakin sarki ya karba musu da cewa ya karbi addu'arsu da istigfarinsu. A koda yaushe Allah mai rahama ne da tausayi ga bayinsa, domin kuwa mutum zai saba masa, sa'annan ya nemi gafararsa kuma ya gafarta masa, kuma ya ba shi ladar istigfarin da ya yi, haka nan kuma ayyuka na gari da mutum mumimini ya aikata ba za a tozarta sub a, daga namiji ne ko mace babu banbanci. Duk da cewa hatta wanda ba mumini ba idan ya aikata wani abu na alkhairi Allah zai saka masa da alkhairi a gidan duniya, wannan na daga cikin adalci irin na ubangiji madaukakin sarki. Dukkanin wahalhalun da muminai suka sha domin daukaka kalmar Allah, hijira, da jihadi, da cutarwar da suke sha a hannun mushrikai da kafirai, a lokacin manzon Allah ne ko bayan wafatinsa, duk wannan na daga cikin abin da Allah zai yi wa muminai sakamako na allhairi a kansa.
Darussan koyo daga wanna aya mai albarka:
1 – Babu wani aiki da ba shi da sakamako, na alkhairi ko na sharri, amma Allah yana saka wa babban alkairi ne a ranar kiyama ga wadanda suka yi ayyuka na gari.
2 – Mace da namiji duk matsayinsu daya wajen neman yardar Allah.
3 – Allah yana sanya muminai a cikin aljanna ne da rahmarasa, amma kuma ayoyi da daman a kur'ani sun yi mana hannunka mai sanda kan matsayin da aiki na gari yake da shi wajen kai mutum zuwa ga samun wannan rahama ta ubangiji a ranar kiyama.
Da wannan muka mkawo karshen shirin, sai haduwa ta gabata za mu ci gaba daga inda muka tsaya, kafin na ke yi muku fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullah.
Suratu Al Imrana, Aya Ta 196-200 (Kashi Na 111)
Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannuka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Ali Imran, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.
Aya ta (196) da (197) Ali Imran:
لاَ يَغُرَّنَّكَ تَقَلُّبُ الَّذِينَ كَفَرُواْ فِي الْبِلاَدِ{196} مَتَاعٌ قَلِيلٌ ثُمَّ مَأْوَاهُمْ جَهَنَّمُ وَبِئْسَ الْمِهَادُ{197}
Kada jujjuyawar wadanda suka kãfirta a cikin garũruwa ta rũde ka.
Jin dãdi ne kadan sa'an nan makõmarsu Jahannama ce, kuma tir da shimfida ita!
A lokacin da muminai suke cikin wahala ta rayuwa a farkon bayyanar musulunci, kafirai mushrikan Makka da yahudawan Madina suna cikin jin dadi da walwala, wannan yasa wasu daga cikin muminai suna dasa alamar tamabaya cewa, mene yasa suke cikin wahala da kuncin rayuwa, alhali su ne suka yi imani da Allah da manzonsa, yayin da mushrikai da ba su imani ba suke jin dadi suna ta facaka yadda ransu ke so?
Wannan aya mai albarka ta safka domin ta natsar ma muminai da rayukansu, inda take nuni da cewa kada yanayin jin dadi da sheke aya da kafirai suke yi ya rudi muminai, domin kuwa wannan jin dadin nasu dan takaitacce ne, yayin da wahala da kuncin da muminai suke ciki shi ma takaitacce ne, kuma dukakninsu za su koma ga Allah ne, a lokacin ne kafirai za su ga cewa jin dadinsu a rayuwar duniya na dan lokaci ne kawai, kuma za su shiga azabar Allah ta har abada, yayin da muminai za su manata da dukaknin wahalhalu da kuncin da suka shiga, sakamakon imani da Allah, domin kuwa a ranar Allah zai saka musu da aljannarsa, inda za su rayu cikin ni'ima da jin dadi da walwala ta har abada.
Wadannan ayoyi suna magana ne kai tsaye da musulmi a lokacin manzon Allah, amma kuma tana magana da dukkanin muminai da suka zo bayan ma'aiki har zuwa tashin kiyama.
Darussan koyo daga wadannan ayoyi masu albarka:
1 – Dukiya da jin dadin rayuwar duniya masu rudi ne, kada mai imani ya bari dukiya ta rude shi, har ya rasa imaninsa, ko kuma hankoron neman dukiyar ya kai shi ga rabuwa da imaninsa.
2 – Idan muka duba mutanen da suka zama bayin duniya da tarkacenta, sau da yawa karshesu yana zama mai ban tausayi, wasu lokuta kafin su bar gida duniya suka rasa abin da suka tara na dimbin dukiya, wanda kan sanya su yin izgili da wulakanci ga mutane. Ko kuma ga dukiyar amma babu jin dadin balantana natsuwa ta ruhi.
3 – Duniya da dukaknin tarkacen da ke cikinta masu karewa ne, saboda haka mumini yana neman halas dinsa a duniya ne domin neman lahira.
Aya ta (198) Ali Imran:
لَكِنِ الَّذِينَ اتَّقَوْاْ رَبَّهُمْ لَهُمْ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا نُزُلاً مِّنْ عِندِ اللّهِ وَمَا عِندَ اللّهِ خَيْرٌ لِّلأَبْرَارِ{198}
Amma wadanda suka bi Ubangijinsu da takawa sunã da Gidãjen Aljanna (wadabda) koramu ke gudãna a karkashinsu suna madawwama a cikinsu, a kan, liyãfa daga wurin Allah, kuma abin da ke wurin Allah ne mafi alhẽri ga barrantattu.
Ayoyin da suka gabata sun yi mana ishara da cewa wadanda suka kafirka, kuma suka rika yi wa muminai izgili da dukiyar da suka mallaka a gidan duniya, a ranar kiyama ba su da rabo a cikin rahamar Allah, yayin da muminai da suka sha wahala suka rasa abin da suka mallaka na dukiya sakamakon imaninsu da Allah da manzonsa, a ranar kiyama suna tare da rahamar Allah.
Wannan aya tana tabbata mana da cewa hakika wadanda suka ji tsoron ubangijinsu a gidan duniya, ta hanyar yi imani da Allah da manzonsa, da yin aiki da umurnin Allah, to a ranar kiyama su ne suke da manyan gidaje na aljanna, duk kuwa da cewa bin dokokin Allah na tattare da jarabawa ga mumini, domin kuwa wadannan dokoki suna hana shi abubuwa da dama da ransa kan raya masa, amma saboda Allah ya hana ya kan bari domin kada ya saba ma Allah, saboda wannan juriya da tsentseni sai Allah ya saka musu da aljanna da rahamarsa.
Darussan koyo daga wannan aya:
1 – Saharadin karbar imani da aiki shi ne taqawa (tsoron Allah)
2 – Muminai a ranar kiyama tamkar baki ne, Allah kuma shi mai masafkin baki, Aljanna kuma tamkar wani wurin karbar bakin ne, amma akwai ni'imomin da Allah zai yi wa muminai da shi kadai ne ya sansu.
Aya ta (199) Ali Imran:
وَإِنَّ مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ لَمَن يُؤْمِنُ بِاللّهِ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْكُمْ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْهِمْ خَاشِعِينَ لِلّهِ لاَ يَشْتَرُونَ بِآيَاتِ اللّهِ ثَمَناً قَلِيلاً أُوْلَـئِكَ لَهُمْ أَجْرُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ إِنَّ اللّهَ سَرِيعُ الْحِسَابِ{199}
Kuma lalle ne daga Mutãnen Littãfi hakĩka akwai wanda yake yin ĩmãnĩ da Allah da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar zuwa gare su, sunã mãsu tawãlu'i ga Allah, bã su sayen tamani kadan da ãyõyin Allah. Wadannan suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu. Lalle ne Allah Mai gaugãwar sakamako da yawa ne.
Bayan hijirar muminai daga Makkka zuwa Madina, wasu daga cikin yahudawa da kiristocin Madina sun fahimci addinin muslunci, kuma sun yi imani da sakon ma'aiki. Ya zo a cikin ruwayoyin cewa Najjashi sarkin Habasha na wancan lokacin ya yi imani da sakon ma'aiki, saboda haka ne ma a lokacin da ya rasu manzon allah tare da musulmi suka yi masa sallar mamaci daga nesa, sai wasu munafukai daga cikin wadanda suke tare da manzon Allah suka koma bayan idonsa suna surutai, suna cewa manzon Allah ya ja mutane suna yi wani mutum kafiri salla, alhali ma bai taba ganinsa ba, sai wannan aya ta safka kuma ta ba su amasa.
Darussan koyo daga wannan aya mai albarka:
1 – A lokacin da musulmi yake mu'amala da musulmi da ma wanda ba musulmi ba, dole ne ya kiyaye adalci, ba ya kamata a kawar da kai daga kyautatawar mutum, musulmi ne ko ba musulmi ba.
2 – Iamni da Allah yana gadar da tawalu'u da yin watsi da rudun shaidan da girman kai.
Aya ta (200) Ali Imran:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ اصْبِرُواْ وَصَابِرُواْ وَرَابِطُواْ وَاتَّقُواْ اللّهَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ{200}
Yã ku wadanda suka yi ĩmani! Ku yi hakuri kuma ku yi dauriya, kuma ku yi zaman dãko, kuma ku yi takawa, tsammãninku zã ku ci nasara.
Wannan aya mai labarka ita ce aya ta karshe a cikin surat Ali Imran, wadda ta kunshi umurni hudu daga Allah kai tsaye zuwa ga muminai., wato tabbata da yin hakuri a kan imani da da lamurran na daidaiku da kuma na jama'a, yin tsayin daka wajen kare martabar addini da akidar musulunci, haka nan kuma da yin tsayin daka wajen kare al'ummar musulmi da rayukansu da dukiyoyinsu daga shishigin makiya, wanda kuma samun hakan yana dogara da imani da kuma tsaron Allah da muminai suke da shi(taqawa)
Darussan koyo daga wannan aya mai albarka:
1 – Idan makiya addinin Allah za su samu dauriya da dakewa kana bin da suke yin a yin zagon kasa ga hanyar Allah, to mumini shi ne yafi dacewa da ya yi tsayin daka wajen kare addini ubangiji.
2 – Yin tsayin daka kan lamarin addini na bukatar hakuri da juriya da tsoron Allah.
Da wanan muka kawo karshen wannan sura ta Ali Imran, sai a kasance tare da mu a cikin shiri na gaba, kafin nan na ke yi muku fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullah.