Toggle menu
24.1K
670
183
158.6K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:beyond

Discussion page of beyond

Glosbe's example sentences of beyond [1]

  1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar beyond:
    1. More than that, Jehovah wants your joy to last beyond the time of youth.
      Ban da haka, Jehobah yana son ku ci gaba da farin ciki har sa’ad da kuka tsufa. [2]

    2. Never should we assume that we are beyond the reach of divine forgiveness.
      Kada mu taɓa tunani cewa mun wuce Allah ya gafarta mana. [3]

    3. The more time that went by, the more I thought I was beyond Jehovah’s forgiveness.
      Yayin da lokaci yake wucewa, sai na soma gani kamar Jehobah ba zai gafarta min zunubaina ba. [4]

    4. Such a notion would be beyond belief.
      Wannan ra’ayin ba zai taɓa kasancewa gaskiya ba. [5]

    5. However, the work on the temple complex continued down to and beyond the Passover of 30 C.E., when the Jews said that it took 46 years to build it.
      Amma, an ci gaba da gini a haikalin har bayan Idin Ƙetarewa na shekara 30 A.Z. shi ya sa Yahudawa suka ce ginin ya kai har shekaru 46. [6]

    6. 1:16) Beyond our being thus rewarded, we will see others agree with the sentiment that Paul quoted at Romans 10:15: “How comely are the feet of those who declare good news of good things!” —Isa.
      1:16) Fiye da albarkar da za mu samu, za mu ga mutane suna amincewa da kalaman da Bulus ya yi ƙaulinsa a Romawa 10:15: “Ina misalin darajan ƙafafu na masu-kawo bishara ta alheri!”—Isha. [7]

    7. Referring to the ministry, Paul wrote fellow anointed Christians: “We have this treasure in earthen vessels, that the power beyond what is normal may be God’s and not that out of ourselves.” —2 Corinthians 4:7.
      Da yake maganar hidima, Bulus ya rubuta wa ’yan’uwa Kiristoci shafaffu: “Muna da wannan kaya mai-daraja cikin tukwane na ƙasa, domin mafificin girman iko ya kasance na Allah, ba daga wurin mu da kanmu ba.”—2 Korinthiyawa 4:7. [8]

    8. Satan would like to have us conclude that we are beyond the reach of Jehovah’s mercy and are incapable of meeting His requirements.
      Shaiɗan yana son mu ji cewa zunubinmu ya yi yawa ainun kuma Jehobah ba zai yafe mana ba kuma ba za mu iya bin ƙa’idojinsa ba. [9]

    9. Powerful forces completely beyond our control also dominate our lives and dictate what happens to us.
      Yanayi kuma da suka fi ƙarfinmu su ma suna mamaye rayuwarmu suna sarrafa abin da yake faruwa da mu. [10]

    10. 1:3, 4) Nehemiah’s prayers were answered beyond his expectations when King Artaxerxes allowed him to go to Jerusalem to rebuild its wall.
      1:3, 4) An amsa addu’o’in Nehemiya fiye da yadda yake tsammani sa’ad da Sarki Artaxerxes ya ƙyale shi ya tafi Urushalima don ya sake gina ganuwarta. [11]

    11. 2:7) He can fortify you, giving you “the power beyond what is normal.” —2 Cor.
      2:7) Zai iya ƙarfafa ka, kuma ya ba ka “mafificin girman iko.”—2 Kor. [12]

    12. In some cases, the roots may penetrate deeper into the ground than the height of the tree, or the roots may extend horizontally well beyond the spread of the tree’s foliage.
      A wani lokaci, saiwar na iya zurfi sosai fiye da tsawon itacen, ko kuma saiwoyi za su iya faɗaɗa sosai fiye da ganyen itacen. [13]

    13. 8 One important factor that can help us cope with life’s problems is to recognize that certain things are simply beyond our control.
      8 Wani abu mai muhimmanci da zai taimaka mana mu bi da matsaloli na rayuwa shi ne fahimtar cewa akwai wasu abubuwa da suka fi ƙarfinmu. [14]

    14. 14 Keep in mind, too, that we have the powerful backing of Shiloh, who along with his Father will let no enemy —demon or human— test our obedience beyond what we can bear.
      14 Ka tuna cewa, muna da goyon bayan Shiloh, wanda tare da Ubansa ba za su bar magabta—aljanu ko ’yan Adam—su gwada biyayyarmu fiye da yadda za mu jimre ba. [15]

    15. He can “do more than superabundantly beyond all the things we ask or conceive.”
      Zai iya “aikata ƙwarai da gaske gaba da dukan abin da muke roƙo ko tsammani.” [16]

    16. He knew that no obstacles, no human frailties, could prevent Jehovah from imparting “power beyond what is normal” to any Christian endeavoring to serve Him faithfully.
      Ya sani cewa babu wasu hani, ba kumamanci na ’yan Adam, da zai iya hana Jehovah daga bada “mafificin girman iko” ga kowane Kirista da yake ƙoƙarin ya bauta Masa da aminci. [17]

    17. (Matthew 24:14) Although we are imperfect, we can take heart from Paul’s words: “We have this treasure [of the ministry] in earthen vessels, that the power beyond what is normal may be God’s and not that out of ourselves.”
      (Matta 24:14) Ko da mu ajizai ne, kalmomin Bulus zai ƙarfafa mu: “Muna da wannan kaya mai-daraja [na hidima] cikin tukwane na ƙasa, domin mafificin girman iko ya kasance na Allah, ba daga wurin mu da kanmu ba.” [18]

    18. We have this assurance: “God is faithful, and he will not let you be tempted beyond what you can bear, but along with the temptation he will also make the way out in order for you to be able to endure it.”
      Muna da wannan tabbacin: “Allah mai-aminci ne, da ba za ya bari a yi muku jaraba wadda ta fi ƙarfinku ba; amma tare da jaraba za ya yi muku hanyar tsira, da za ku iya jimrewa.” [19]

    19. Study will fortify us so that “the power beyond what is normal may be God’s and not that out of ourselves.”
      Yin nazari zai ƙarfafa mu saboda “mafificin girman iko ya kasance na Allah, ba daga wurin mu da kanmu ba.” [20]

    20. The benefits of obedience go far beyond the parent-child relationship.
      Fa’idojin biyayya ya ɗara dangantakar yara da iyaye kawai. [21]

    21. Mention some circumstances where “power beyond what is normal” is particularly needed.
      Ka ambata wasu yanayi inda musamman ake bukatar “mafificin girman iko.” [22]

    22. Or do I dismiss these people as being beyond hope?’
      Ko kuma ina ƙin waɗannan mutane cewa ba za su taɓa canjawa ba?’ [23]

    23. Because Jehovah grants us “power beyond what is normal.”
      Domin Jehovah yana ba mu “mafificin girman iko.” [24]

    24. Asserting that such calamitous events were beyond human understanding or explanation, Voltaire wrote:
      Yana cewa ’yan Adam ba za su iya fahimta ko kuma bayyana irin wannan aukuwa ta bala’i ba, Voltaire ya rera: [25]

    25. “Although beyond hope, yet based on hope he had faith, that he might become the father of many nations.”
      ‘Shi wannan bisa ga kafa bege ya bada gaskiya saɓanin tsammani, da za ya zama uban al’ummai dayawa.’ [26]


Retrieved July 6, 2019, 8:59 pm via glosbe (pid: 9153)