Toggle menu
24K
665
183
158.3K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

UMD NFLC Hausa Lessons/59 Sudanese Politics

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

Overview

  1. Lesson Title: Sudanese Politics-This is a report about the International Criminal Court's decision regarding the Sudanese president.
  2. Language: Hausa
  3. Topic: Defense/Security
  4. ILR Level: 1+/2
  5. ACTFL Proficiency: Advanced-Mid, Advanced-Low, Intermediate-High; This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
  6. Modality: Reading
  7. Learning Objective: Maintenance & Improvement
  8. Subject Area: Language
  9. Material Type: LLO
  10. Publication Year: 2009
  11. ObjectID: T8RHA14

Transcript Audio


Transcript

Original Translation

Kasashen duniya sun nuna damuwa kan bayar da sammacin kame shugaban kasar Sudan da kotun kasa da kasa ta yi

A ranar 4 ga wata, kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa ta bayar da sammaci domin tsare shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir, akan tuhumarsa da take yi da aikata laifuffukan yaki da take hakkin bil'adama. Wannan dai shi ne karo na farko da wannan kotu ta yanke irin wannan hukunci akan wani shugaba dake kan karagar mulki. Ko bayar da umurnin cafke Omar Al-Bashir da kotun kasa da kasa ta yi zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a Sudan, yana jawo hankalin kasa da kasa da damuwarsu. A wanann rana, kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa ta sanar da cewa, Al-Bashir yana da hannu a aikata laifuffukan keta hakkin bil'adama guda 5 da na yaki guda 2 a yankin Darfur, amma mashawarcin shugaba Al-Bashir na Sudan ya ki amincewa da wannan sammaci. A ranar 3 ga wata kuma, Al-Bashir ya nuna cewa, kamata ya yi kasar Sudan ta dukufa kan kiyaye zaman lafiya da neman bunkasuwa a kasar, amma ba za ta maida hankalinta kan kowane kuduri da kotun kasa da kasa ta tsayar a kanta ba. Bayan da kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa ta bayyana sanarwar bada sammacin kame Omar Al-Bashir, darurruwan mutane sun yi dandazo a titunan Khartoum, babban birnin kasar Sudan, don nuna adawa da hukuncin da kotun ta yanke. Masu zanga-zanga sun yi gangami a gaban kofar majalisar ministoci ta kasar, inda suka nuna tsayayyen goyon-baya ga Omar Al-Bashir, da zargi kotun kasa da kasa da ta yi shiga-sharo-ba-shanu cikin harkokin cikin gida na kasar Sudan. A watan Yuli na shekara ta 2008, kotun laifuffuka ta kasa da kasa ta zargi Al-Bashir da aikata laifuffuka guda 10 masu alaka da laifuffukan kisan kare dangi a Darfur, da rokon kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa da ta bada sammaci don tsare Al-Bashir. Game da wannan batu, kasashen duniya suna fatan hukuncin da wannan kotu ta yanke zai amfana wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a Sudan. Sakamakon shiga-tsakanin da Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyar tarayyar Afirka, gami da kasashe makwabtan Sudan suka yi, gwamnatin Sudan ta bayyana fatanta na yin shawarwari tare da kungiyoyin 'yan adawa, don cimma kulla yarjejeniyar shimfida zaman lafiya mai dorewa a yankin Darfur. Amma akwai wasu kungiyoyin 'yan adawa wadanda suka ki sanya hannu kan wannan yarjejeniya, inda suka bukaci da a kara samun moriya, da raba iko da dukiyoyi a wannan yanki na Darfur. Bayan da kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa ta bayar da sammacin cafke Omar Al-Bashir, kasashen duniya sun bayyana damuwarsu sosai. Kwanan baya, sakatare-janar na MDD Mista Ban Ki-Moon ya nuna cewa, tuhumar da kotun kasa da kasa ta yiwa Omar Al-Bashir, ba za ta taimaka ba wajen gudanar da yarjejeniyar shimfida zaman lafiya daga dukkan fannoni a kasar Sudan. A waje guda kuma, shugaba kwamitin kungiyar tarayyar Afirka Mista Jean Ping ya bayar da wata sanarwa a ranar 4 ga wata, inda ya jaddada cewa, bai kamata ba yanke hukunci ta hanyar shari'a ya jawo tsaiko ga yunkurin kiyaye zaman lafiya a Sudan. Akwai wasu kasashen Afirka kuma wadanda suka yi barazanar yin watsi da kujerun membobin kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa, don nuna matukar bacin-rai game da umurnin kama Omar Al-Bashir. Ministan harkokin wajen kasar Masar Ahmed Abul Gheit ya nuna cewa, abun da kotun kasa da kasa ta yi, zai lahanta yanayin tsaro da kwanciyar hankali a kasar Sudan, ya kuma yi kira ga kwamitin sulhun MDD da ya kira taron gaggawa, don tattaunawa kan jingine batun kama shugaba Omar Al-Bashir na Sudan.

Concern Over the International Court's Decision About the President of Sudan

On the fourth of this month [March 2009], the International Criminal Court [ICC] issued a warrant for the arrest of Sudanese President Omar al-Bashir based on charges that he had committed war crimes and crimes against humanity. This is the first time the court has handed down this type of judgment against a sitting head of state. Whether or not the International Court’s order to detain Omar al-Bashir will help lead to peace in Sudan, it has attracted the attention and concern of the international community.

On the day [the warrant was issued], the ICC announced that al-Bashir was complicit in committing five crimes against humanity and two war crimes in the Darfur region, but an advisor to President al-Bashir rejected the warrant. On March 3, al-Bashir had indicated that Sudan must devote its efforts to promoting peace and seeking development, and that [the country] would not concern itself with any resolution that might be issued against it by the ICC.

After the ICC announced it was issuing a warrant for Omar al-Bashir’s arrest, concerned individuals gathered in the streets of Khartoum, the capital of Sudan, to demonstrate their opposition to the court’s decision. Demonstrators sounded the alarm in front of the National Legislature, where they showed their steadfast support for Omar al-Bashir and accused the ICC of meddling in Sudan’s domestic affairs.

In July of 2008, the ICC [actually, the ICC’s Chief Prosecutor] had accused al-Bashir of committing ten crimes related to genocide in Darfur and had asked the ICC to issue a warrant for al-Bashir’s arrest. The international community was hoping that the court’s verdict in this matter would promote peace and stability in Sudan. Following the intervention of the United Nations, the African Union, and Sudan’s neighbors, the Sudanese government expressed its willingness to consult with opposition groups in order to achieve a binding agreement to establish lasting peace in Darfur. But there were some opposition groups that refused to sign the agreement because they wanted to be granted additional benefits in addition to sharing power and resources in this region of Darfur.

The international community expressed grave concern when the ICC issued the warrant to detain Omar al-Bashir. UN Secretary-General Ban Ki-Moon recently pointed out that the ICC’s accusations against Omar al-Bashir would hinder administration of the peace treaty in all regions of Sudan. Likewise, the chairman of the Commission of the African Union, Mr. Jean Ping, made an announcement on the fourth of this month in which he affirmed that the search for justice must not jeopardize the effort to promote peace in Sudan. Demonstrating their extreme disappointment with the order to arrest Omar al-Bashir, some African countries threatened to unseat members of the ICC. Egyptian Foreign Minister Ahmed Aboul Gheit stated that the action by the ICC would compromise security and stability in Sudan, and he called on the UN Security Council to convene an emergency meeting to discuss deferring the matter of Sudanese President Omar al-Bashir’s arrest.

Glossary

Hausa English Meaning
yaki da hakin bil'adama (lit: fight for human rights) to fight for people's rights, to fight on behalf of people
yana da hannu (lit: he has a hand) taking part in an action, being guilty of doing something
zanga-zanga to protest, to strike, demonstrations
shiga sharo ba shanu (lit: participating in sharo without cattle) to meddle, to involve oneself in a situation/action without having the appropriate tools 

Sharo is a reference to the traditional male rite of passage among the pastoralist Fulani, whose cattle are a key component of their cultural identity.

kisan kare dangi (lit: to end relatives) massacre, mass murder
Majalisar dinkin duniya (lit: council/legislature that sows the world) the United Nations
shimfida zaman lafiya mai dorewa laying a strong foundation for peace
cafke to catch, to arrest
jingine to lay something to rest, to hang

Notes

1. Sudan

Like many African countries, Sudan has experienced political instability since gaining its independence in 1956. Military coups and religious and ethnic conflicts have killed or displaced many innocent citizens. Most recently, the civil war in Darfur between northern Afro-Arab tribes and southern non-Arab ethnic groups has gained the attention of the international community because of reports of genocide. Much of the conflict in Sudan centers on religious and ethnic difference between its northern and southern regions. According to the 2008 article “Sudan: Politics, Government, and Taxation,” the political scene in Sudan has been dominated by northerners; and southerners, “upset by the strict Islamic penal code” as well as “the deterioration of the economy” have sought to secede from Sudan.

Sudan: Politics, government, and taxation. (2008). Encyclopedia of the Nations. Retrieved May 28, 2009, from http://www.nationsencyclopedia.com/economies/Africa/Sudan-POLITICS-GOVERNMENT-AND-TAXATION.html

2. Omar al-Bashir

Omar al-Bashir, the current president of Sudan, came to power in a bloodless military coup in 1989. One of his first acts was the suspension of all political parties and the nationalization of an Islamic legal code. The Wikipedia article “Omar Hassan Ahmad al-Bashir” states that al-Bashir also “issued purges and executions in the upper ranks of the army, the banning of associations, political parties, and independent newspapers and the imprisonment of leading political figures and journalists.” The civil war that has raged for nearly 20 years in Sudan has involved the Sudan People’s Liberation Army of southern Sudan and al-Bashir’s government. The charges of genocide against al-Bashir include accusations that his government has suppressed evidence of ethnic cleansing and mass graves.

Omar Hassan Ahmad al-Bashir. (2009, May 27). Wikipedia. Retrieved May 28, 2009, from http://en.wikipedia.org/wiki/Omar_Al-Bashir

3. More Information

To read more about the coup which brought al-Bashir to power, read Alan Cowell’s article “Military Coup in Sudan Ousts Civilian Regime” from the New York Times, available online at the following link:

http://query.nytimes.com/gst/fullpage.html?res=950DE4DA103DF932A35754C0A96F948260