Africa's week in pictures: 5-11 November 2021 Published 12 November 2021 [1] <> Hotunan Afrika na mako: Daga ranar 5 zuwa ranar 11 ga watan Nuwambar 2021 (13 Nuwamba 2021) [2]
Fisherman Osman Abdulahi carries a hammerhead shark onto shore in Somalia's capital Mogadishu on Friday. Wani masunci mai suna Osman Abdulahi dauke da babban kifi da ya kamo a wani kogin da ke Mogadishu, babban birnin Somalia ranar Juma'a. --bbchausa verticals/pics/2021-11-05
On Wednesday people line the streets in Benin's capital, Cotonou, as sacred artefacts looted 130 years ago during French colonial rule are finally returned. Ranar Laraba mutane sun yi layi a kan titunan Cotonou, babban birnin Benin, a yayin da aka komawa da kasar wasu kayayykin tarihi da aka sace shekaru 130 da suka wuce lokacin mulkin mallakar Faransa. --bbchausa verticals/pics/2021-11-05
The next day in Senegal, members of the Mouride Islamic brotherhood commemorate their late founder Amadou Bamba. Washegari a Senegal, mambobin kungiyar Morudai ta mabiya addinin Musulunci, sun yi bikin tunawa da mutuwar mutumin da ya kafa kungiyar Amadou Bamba. --bbchausa verticals/pics/2021-11-05
Nigerian artist Alduphina Imuede poses with one of her pieces at the annual Art X Lagos fair on Friday... 'Yar Najeriya mai zane-zane Alduphina Imuede a tsaye a kusa da wadansu zane-zane da ta yi a wajen bikin nunin zane-zane na shekara mai taken Art X da aka yi a birnin Lagos ranar Juma'a... --bbchausa verticals/pics/2021-11-05
West Africa's biggest annual art fair once again opened its doors to visitors, having made last year's event online-only to prevent the spread of coronavirus... An sake bude babban taro kan zane-zane na Afirka ta Yamma, bayan da aka gudanar da shi ta intanet a shekarar da ta wuce saboda annobar korona... --bbchausa verticals/pics/2021-11-05
Painter and sculptor Ayoola Gbolahan also had his work on show at the event in Nigeria. Mai zayyana Ayoola Gbolahan shi ma ya nuna kayan da ya zana a wurin taron nan Najeriya. --bbchausa verticals/pics/2021-11-05
UFC fighter Kamaru Usman, nicknamed "the Nigerian Nightmare", psychs up before successfully defending his welterweight title against Colby Covington in New York City on Saturday. Dan damben nan Kamaru Usman, wanda ake wa lakabi da "the Nigerian Nightmare", yana shiri inda daga bisani ya kare kambunsa a fafatawar da suka yi da Colby Covington a birnin New York City ranar Asabar. --bbchausa verticals/pics/2021-11-05
Following the death of Abdul Razzaq Lachhab from inhaling tear gas fired by police during protests over rubbish collection in Tunisia, demonstrators against state violence wave banners on Saturday bearing his name. Bayan mutuwar Abdul Razzaq Lachhab sakamakon shakar barkonon-tsohuwar da 'yan sanda suka watsa masa lokacin zanga-zanga kan kwashe shara a Tunisia, masu zanga-zangar kyamar rikici sun rika kwalaye masu dauke da sunansa ranar Asabar. --bbchausa verticals/pics/2021-11-05
In recent days more than 5,000 people have fled across the border to Uganda after attacks by rebels in Chanzu and Runyonyi, in the eastern Democratic Republic of Congo. A kwanakin baya-bayan nan kusan mutum 5,000 suka tsere suka tsallaka iyaka zuwa Uganda bayan hare-haren da 'yan tawayen da ke Chanzu da Runyonyi, suke kai musu a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo. --bbchausa verticals/pics/2021-11-05
Kenya's Albert Korir races to victory in the New York City marathon on Sunday, having come second in 2019. Dan tseren Kenya Albert Korir ya yi nasara a gasar tsere da aka gudanar a birnin New York City ranar Lahadi, bayan da ya zo matsayi na biyu a shekarar 2019. --bbchausa verticals/pics/2021-11-05
Cabbage vendors take a nap while waiting for customers at the Lafto fruit and vegetable market in Ethiopia's capital, Addis Ababa, on Friday. Masu tallan kabeji suna yin bacci a yayin da suke jiran kwastomomi a kasuwar kayan marmari da ke Addis Ababa, babban birnin Ethiopia, ranar Juma'a. --bbchausa verticals/pics/2021-11-05
It's dinner time at a monkey refuge on Santiago Island, in Cape Verde, on Saturday. Lokacin cin abincin wannan birin da ke Tsibirin Santiago da ke Cape Verde, ya yi a ranar Asabar. --bbchausa verticals/pics/2021-11-05
On Tuesday, Kevin Ochieng Onyango wins the 2021 Environmental Photographer of the Year award in the Climate Action category, for this shot called The Last Breath. "A boy takes in air from the plant, with a sand storm brewing in the background, in an artistic impression of the changes to come," says the photographer. Ranar Talata, Kevin Ochieng Onyango ya lashe gasar Hotuna kan Muhalli ta 2021 a bangaren Sauyin Yanayi saboda hoton da ya dauka mai take The Last Breath. "Wani yaro ya shaki iska daga tsirrai a yayin da gugwa take hadawa a bayansa, a wata alama ta sauyin da ke tafe," a cewar mai daukar hoton. --bbchausa verticals/pics/2021-11-05
Gifts for children go on sale at the Lagos International Trade Fair in Nigeria on Wednesday. Ana sayar da katunan da ake bai wa yara kyautarsu a wurin bajekoli da aka gudanar a Lagos ranar Juma'a. --bbchausa verticals/pics/2021-11-05
And South African golfer Jacques Blaauw competes in the Rolex Challenge Tour Grand Final in Spain on Sunday. 'Yar kwallon golf ta Afrika Ta Kudu Jacques Blaauw ta kammala zagayenta a gasar Rolex Challenge Tour Grand Final da aka yi a Sifaniya ranar Lahadi. --bbchausa verticals/pics/2021-11-05