Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

GLOSS/409 Tattaunawa domin Kidayar Jama'a (A Census Interview)

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
  1. https://gloss.dliflc.edu/products/gloss/hua_soc409/hua_soc409_source.html
  2. https://gloss.dliflc.edu/LessonViewer.aspx?lessonId=35683&lessonName=hua_soc409&linkTypeId=0
Tattaunawa domin Kidayar Jama'a A Census Interview
Namiji: To, da farko, su wane ne cikin gidan, kuma shekarunsu nawa? Man: Okay, so first of all, who lives in the home, and what are their ages?
Mace: To, sunana Fatima Iliya. Ina da shekara ashirin da shidda da haifuwa. Ni mutuniyar ƙasar Nijar ce. Ina zaune a garin Kore, a jihar Damagaram. Ina da miji da kuma yara biyu. Mijina, sunansa Lawali. Yana da shekara arba’in ko arba’in da daya. Dana, sunansa Sa’idu. Yana da shekara 12 da haifuwa. Diyata kuma, sunanta Zara. Tana da shekara 9 da haifuwa. Woman: Okay, my name is Fatima Iliya. I am 26 years old. I am a citizen of Niger. I live in the town of Kore, in the Zinder Department. I have a husband and two children. My husband’s name is Lawali. He is 40 or 41 years old. My son is named Sa’idu. He is 12 years old. My daughter’s name is Zara. She is nine years old.
Namiji: To, wane irin aiki ne kuke yi? Man: Okay, what kind of work do you (all) do?
Mace: To, mijina manomi ne da kuma ɗan kasuwa. Muna da gona kusa da gari. A lokacin damina yana shuka hatsi da wake da kuma gurjiya. A ranar Talata yana tafiyan kasuwa. A kasuwa yana saida kaya kamar taliya da filawa. Ni kuma, malamar makaranta ce. Ina aiki a makarantar firamare ta Kore. Ina koyar da harshen Faransanci. Yaranmu suna tafiya makaranta. Ba su aiki. Woman: Well, my husband is a farmer and a merchant. We have a farm close to town. During the rainy season, he plants millet, beans, and peanuts. On Tuesdays, he goes to the market. At the market, he sells things like pasta noodles and flour. As for me, I am a teacher at the primary school in Kore. I teach French. Our children go to school. They don’t work.
Namiji: Uwayenki kuma? Man: And your parents?
Mace: To, ni ‘yar Kore ce. Uwayena suna zauna cikin Kore kusa da gidanmu. Ubana limami ne a babban massalacin gari. Woman: I am from Kore. My parents live in Kore, near our house. My father is the imam at the main mosque in town.
Namiji: Kina da ‘yan’uwa kuma? Man: And, do you have siblings?
Mace: I. Ina da ya da ƙane. Yata tana da shekara talatin da haifuwa. Ta yi aure da wani namiji a Zinder. Tana zaune a Zinder. Tana saida tomatir a kasuwa. Ƙanena yana da shekara ashirin da huɗu da haifuwa. Shi ɗalibi ne a jami’ar ‘Yamai. Yana karatun ilimin kimiyya. Woman: Yes, I have an older sister and a little brother. My sister is 30 years old. She is married to a man in Zinder. She lives in Zinder. She sells tomatoes at the market. My little brother is 24 years old. He is a student at the University of Niamey. He studies science.
Namiji: To na gode malama. Man: Thank you, ma’am.