Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

GLOSS/423

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

https://gloss.dliflc.edu/products/gloss/hua_soc423/hua_soc423_source.html

Tarihin Rayuwa A Life Story
To, tarihina, shi ne. An haifeni a birnin Zaria, inda na yi makarantar firamare. A lokacin da nike da shekara 12 da haifuwa, babana ya samu aiki a wani masana’anta a Abuja. Saboda haka mun tashi daga Zaria mun koma Abuja da zama. Okay, this is my life story. I was born in the city of Zaria, which is where I went to primary school. When I was 12 years old, my father got a job in a factory in Abuja. Because of that, we left Zaria and moved to Abuja.
Da muka koma Abuja, na fara sakandare a makarantar gwamnati da ke unguwar Garki. Na kuma samu takardar kammala sakandare a can. Daga nan sai na samu damar yin karatu a jami’ar New York. Na yi shekara huɗu ina karatu a Amurka, kuma na samu digiri a fannin aikin jarida. When we moved to Abuja, I began secondary school at the government school in the Garki neighborhood. I received my secondary school diploma there. At that point, I received an opportunity to study at New York University. I spent four years studying in America, and I received my degree in journalism.
Bayan na samu digirin, sai na koma Kano a nan Nijeriya inda na kama aiki a wani gidan rediyo. Bayan shekara biyu a nan, sai na yi aure. Bayan na yi aure, na bar aiki a gidan rediyon. Mun yi shekara uku haka, sai Allah ya yi wa maigidana rasuwa. Bayan mutuwarsa sai na koma Kaduna inda na kama aiki a wani gidan rediyo daban. After receiving my degree, I returned to Kano, here in Nigeria, where I took a job at a radio station. After two years there, I got married. After I got married, I left work at the radio station. We spent three years like that, and then my husband passed away. After his death, I moved to Kaduna, where I took a job at a different radio station.
Na yi shekara biyar a can. Sai an gaya mini cewa akwai gurbin aiki a sashen Hausa na gidan rediyon Jamus. Na aika musu takardar neman aiki. Bayan wajen sati biyar sai na samu labarin cewa na samu aikin. Nan da nan na koma garin Bonn a ƙasar Jamus. Bayan na yi shekara uku a nan, sai na yi aure da wani namiji. Bayan ‘yan shekaru kaɗan sai Allah ya sa na haifi ɗa namiji. Kowace shekara muna zuwa Nijeriya don mu ziyarci ‘yan’uwa. Wata rana kuma muna so mu koma Nijeriya da zama. I spent five years there. Then, I was told that there was a job opening at the Hausa section of Germany’s radio service. I sent them my application. After about five weeks, I got news that I had gotten the job. Right away, I moved to Bonn, Germany. After three years here, I married a man. After a few years, I gave birth to a boy. Every year, we go to Nigeria to visit family. Someday, we want to move back to Nigeria.
Aiki Na Shidda Activity Six
Mijina, mutumin Nijar ne. Yana da digiri a fannin aikin noma daga jami’ar Paris a ƙasar Faransa. Bayan ya samu digirinsa, ya koma ƙasar Amurka da zama. A can ya yi aiki a wani babban kamfanin abinci. Yanzu yana aiki a wata ƙungiya a Jamus. Ƙungiyar tana yin aikin noma a ƙasashen Afirka daban-daban. My husband is a Nigerien. He has a degree in agriculture from the University of Paris in France. After he got his degree, he moved to America. There, he worked for a large food company. Now, he works at an organization in Germany. The organization works in agriculture in various African countries.