Toggle menu
24.1K
670
183
158.5K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

GLOSS/hua sec302

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

https://gloss.dliflc.edu/products/gloss/hua_sec302/default.html [1]

Tawagar ECOWAS a Ivory Coast
ECOWAS Delegation in Ivory Coast
Jami'an yankin Afirka ta Yamma za su yi tattaki zuwa Ivory Coast domin shiga tsakanin gwamnati da sojojin ƙasar da ke yi mata tawaye. West African officials will be going to Ivory Coast in order the mediate between the government and the soldiers who have mounted a rebellion against the government.
A bayan sun gana yau litinin da shugaba Laurent Gbagbo, ministocin harkokin waje da na tsaro da ke cikin tawagar suna fatan shirya ganawa da sojoji masu tawaye da ke riƙe da birnen Bouake da wasu garuruwa na arewacin Ivory Coast. After meeting with President Laurent Gbagbo today, Monday, a delegation of foreign and security ministers are hoping to arrange a meeting with the rebel soldiers who are holding the city of Bouake and several other towns in the northern region of Ivory Coast.
An kafa wannan tawaga jiya lahadi, a lokacin wani taron gaggawar da aka yi na Ƙungiyar Kasuwar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS, a Accra, babban birnin Ghana. This delegation was created yesterday, Sunday, during an emergency meeting of the Economic Community of West African States (ECOWAS) that was held in Accra, the capital of Ghana.
Shugabannin ECOWAS sun yarda cewa ƙasashen Nijeriya da Nijar da Ghana da Guinea-Bissau da kuma Togo su ne za su jagoranci wannan ƙoƙari na sasantawa. ECOWAS leaders agreed that the countries of Nigeria, Niger, Ghana, Guinea-Bissau, and Togo would lead this reconciliation effort.
Shugabanni a wurin taron na ECOWAS sun bayyana goyon baya ga shugaba Gbagbo, sun kuma ce za su tura runduna ta ƙasa da ƙasa ta sojoji dubu huɗu idan har ƙoƙarin sasanta tsakanin sassan ya ci tura. At the ECOWAS meeting, leaders expressed their support for President Gbagbo, and they also said that they will send an international force of 4,000 soldiers if the effort at reconciliation between the two groups fails.
Wannan ƙoƙarin sasantawa ya biyo bayan kwashe ɗaruruwan 'yan ƙasashen wajen da sojojin Amurka da na Faransa suka yi jiya lahadi daga garin Korhogo na arewacin ƙasar, wanda ke hannun 'yan tawaye. This reconciliation effort follows the evacuation yesterday, Sunday, by American and French soldiers of hundreds of foreign nationals from the town of Korhogo in the northern part of the country, which is controlled by the rebels.
A hedkwatar MƊD, jakadan kasar Ivory Coast, Djessan Philippe Djangone-Bi, ya ce ƙasarsa tana son yakar 'yan tawayen da kanta. Ya ce rundunar sojan ƙasar tana sabunta makamanta, tana kuma bukatar karin makamai daga wasu ƙasashe domin murkushe wannan tawaye. Ya ce tuni har sojojin Faransa sun taimaka da kayan faɗa. At the UN headquarters, Ivorian Ambassador Djessan Phillipe Djangone-Bi said that his country wants to fight the rebels on its own. He said that the military of the country is updating its weaponry and that it needs additional weapons from other countries in order to put down the rebellion. He said that France has already given assistance in the form of weaponry.
Har ila yau, Mr. Djangone-Bi ya yi zargin cewa 'yan tawayen suna samun agajin makamai daga wasu ƙasashe, amma bai faɗi ko su wane ne ba. Sai dai kuma ya ce 'yan tawayen sun samo asali ne daga Burkina Faso da Saliyo da kuma Liberiya. Babu wata kafar da ta gaskata wannan ikirari nasa. Furthermore, Mr. Djangone-Bi made the accusation that the rebels were receiving aid in the form of weapons from other countries, but he did not say which countries these were. He also said that the rebels came from Burkina Faso, Sierra Leone, and Liberia. There is no evidence to support this claim.
A yau litinin, gwamnatin Ivory Coast ta ce ta ƙara tsawon wa'adin aiki da dokar hana yawon daren da ta kafa a faɗin ƙasar tun lokacin da aka fara wannan tawaye. Today, Monday, the Ivorian government extended the duration of the nighttime curfew that has been in effect throughout the country since the beginning of the rebellion.