Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Last Sermon

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

The Last Sermon Video in English and Hausa

Started on the day of Arafat, Thursday, July 30th, 2020. But then weren't able to get this powerful last sermon of the beloved (may peace and blessings be upon him and his family) out sooner. Unfortunately, the Hausa audio missed a few parts but worked with what we got. Below is the complete side-by-side alignment (with some help from Google Sheets) of the English and Hausa texts, for the video, visit https://youtu.be/LNOJ-GIuCso or https://www.instagram.com/p/CDWRPjUAlaD/

The Last Sermon Parallel Text

The last sermon (Khutabul Wada) of Prophet Muhammad in English (source) Huɗubar ƙarshe ta Annabi Muhammad SAW da Hausa (source)
1. O People Lend me an attentive ear, Ya ku mutane Ku ba ni hankulanku,
2. for I know not whether after this year, I shall ever be amongst you again. domin mai yiwuwa ba zan sake kasancewa da ku bayan wannan shekarar ba,
3. Therefore listen to what I am saying to you very carefully Saboda haka ku saurari abinda nake gaya maku da kyau
4. and take these words to those who could not be present here today. and take these words to those who could not be present here today.
5. O People, Just as you regard this month, Ya ku mutane, kamar yadda ku ka riki wannan wata, (na Hajji)
6. and this day (of Arafat) da wannan rana (ta Arfa)
7. this city as sacred, da kuma wannan gari (na Makka) da girma kuma abin tsarewa,
8. so regard the life to, haka kuma ku riki ran Musulmi
9. and property of every Muslim as a sacred trust. da kuma dukiyoyinsu da girma abin kuma karewa.
10. Return the goods entrusted to you to their rightful owners. Ku maida wa mutane kayan da suka ba ku amana.
11. Hurt no one so that no one may hurt you. Kar ku cuci kowa, saboda kar wasu su cuce ku.
12. Remember that you will indeed meet your Lord, and that He will indeed reckon your deeds. Ku tuna fa, hakika Allah zai yi sakayya akan ayukakanku.
13. Allah has forbidden you to take usury (interest); Allah (SWT) ya hana cin riba,(wato kudin ruwa)
14. therefore all interest obligation shall henceforth be waived. saboda haka, duk abin da aka kulla ta kudin ruwa sai an warware shi.
15. Your capital, however, is yours to keep. You will neither inflict nor suffer any inequity. Allah has Judged that there shall be no interest and that all interest due to Abbas Ibn ‘Abd al Muttalib (the Prophet's uncle) shall henceforth be waived. _HAUSA TRANSLATION UNAVAILABLE_
16. Beware of Satan for the safety of your religion. Ku yi hattara da shaidan, domin kiyaye addininku.
17. He has lost all hope that he will ever be able to lead you astray in big things, Yanzu kan ya fidda ran batar da ku akan manyan abubuwa (na sabo)
18. so beware of following him in small things. saboda haka ku guji binshi akan kanana.
19. O People Ya ku jama'a
20. It is true that you have certain rights in regard to your women, hakika kuna da hakki bisa matayenku,
21. but they also have rights over you. amma su ma suna da hakki bisa kanku,
22. Remember that you have taken them as your wives, only under Allah's trust and with His permission. If they abide by your right _HAUSA TRANSLATION UNAVAILABLE_
23. then to them belongs the right to be fed and clothed in kindness. to hakkin su ne akan ku da kuciyar da su, Kuma ku tufatar da su akan jin kai.
24. Do treat your women well and be kind to them, for they are your partners and committed helpers. ku bi da su kyakkyawan biyarwa. Ku kuma tausasa musu domin su majibintan al'amurran ku ne, kuma mataimakan ku,
25. And it is your right that they do not make friends with anyone of whom you do not approve, as well as never to be unchaste. Hakki ne akan su da kar su yi abota da duk wanda ba ku so, kuma su nisanci zina.
26. O People Ya ku jama'a
27. Listen to me in earnest, _HAUSA TRANSLATION UNAVAILABLE_
28. worship Allah, ku yi kyakkyawar bauta ga Allah(SWT)
29. say your five daily prayers (Salah), ku tsaida salloli biyar (5) na farilla,
30. fast during the month of Ramadan, Ku azumci watan Ramadan,
31. and give your wealth in Zakat. kuma ku bada zakka.
32. Perform Hajj if you can afford to. Ku aikata aikin Hajji idan har kun samu damar yi.
33. All mankind is from Adam and Eve, an Arab has no superiority over a non-Arab nor a non-Arab has any superiority over an Arab; also a white has no superiority over a black, nor a black has any superiority over a white- except by piety and good action. _UNAVAILABLE_
34. Learn that every Muslim is a brother to every Muslim Ku sani fa, kowane musulmi dan'uwan musulmi ne.
35. and that the Muslims constitute one brotherhood. Dukkan ku daidai ku ke.
36. Nothing shall be legitimate to a Muslim, which belongs to a fellow Muslim unless it was given freely and willingly. Do not therefor, do injustice to yourselves. Ba wanda yake da fifiko saman wani sai wajen tsoron Allah da aikata kyawawan ayyukka.
37. Remember one day you will appear before Allah Ku tuna fa (ya ku jama'a) wata rana za ku tsaya gaban Ubangijinku,
38. and answer for your deeds. domin sakamakon ayyukanku,
39. So beware, do not stray from the path of righteousness after I am gone. Saboda haka ku yi hattara kada ku yi sake da hanya madaidaiciya bayan na kau.
40. O People, no prophet or apostle will come after me Ya ku jama'a ba wani annabi ko manzo da zai zo bayana
41. and no new faith will be born. kuma babu wani addini da zai zo (bayan addinin musulunci),
42. Reason well therefore, O people, saboda haka ku yi tunani sosai akan wannan magana da na gaya maku,
43. and understand words which I convey to you. kuma ku fahimce ta (sosai).
44. I leave behind me two things, Zan bar maku abubuwa guda biyu (2);
45. the Quran and the Sunnah (Hadith), (Alkur ani) ga kuma (Sunnah).
46. and if you follow these you will never go astray. Idan kun bi wannan ba za ku taba bata ba.
47. All those who listen to me shall pass on my words to others and those to others again; Duk wanda ya ji wannan sako to ya jiyar da wadansu, su ma su jiyar da wasunsu,
48. and may the last ones understand my words better than those who listened to me directly. kuma sau da yawa wadanda za su ji magana daga karshe su fi masu ji na yanzu fahimtar abinda nake fada.
49. Be my witness, O Allah, that I have conveyed your message to your people." Ya Allah ka zamo shaida a gare ni, cewa na isar da aikenka zuwa ga bayinka.”
  1. https://www.instagram.com/tv/C09yUlZCHg-/?igshid=MzRlODBiNWFlZA==