Suratu Yusuf, Aya Ta 1-3 (Kashi Na 368)
Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Bayan kammala surar Hudu yanzu kuma zamu shiga Surar Yusuf, wanda kuma take magana kan tarihin Annabi Yusuf (a.s.). Sabanin wasu surorin Alkurani mai girma wadanda suke kawo bayani kan akida da hukunce hukuncen addinin Musulunci da tarihin annabawa da sauran abubuwa da Alkurani yake koyarwa, wannan sura baki dayanta tana magana kan labarin wannan annabi shi kadai.
A cikin Attaura ma akwai labarin Annabi Yusuf (a.s.) amma akwai bambanci da yanda Alkurani ya fadi wannan labari. Nazari a kan ayoyin da suka yi magana kan wannan labari, yana bayyana kasancewar Alkurani shi ke kan gaskiya da kuma karkatar da ke kwai a cikin yanda aka kawo labarin Annabi Yusuf (a.s.) a cikin wasu littafan da Allah ya saukar amma aka sauya sun a hannun Alhul Kitabi.
To madalla. Da farko bari mu saurari aya 1 da ta 2:
الر تِلْكَ آيَاتُ الْكِتَابِ الْمُبِينِ{1} إِنَّا أَنزَلْنَاهُ قُرْآناً عَرَبِيّاً لَّعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ{2}
"A. L̃. R. Wadancan ãyoyi ne na Littãfi mabayyani." "Hakika Mũ Muka saukar da shi Alkurani da harshen Lãrabci don ku hankalta."
Kamar wasu surori 29 na Alkurani, wannan sura ma ta fara ne da harufa, wadanda bisa hakika wata alama ce da Allah da Maaikinsa suka sani, amma ta wata fuska suna nuna wani nau'i na kasancewar Alkurani mujiza daga Allah, saboda kuwa a akasarin wadannan surori bayan harufan farawa ya ambaci Alkurani da kuma girmansa. Abin nufi a nan shi ne ai Allah madaukakin sarki da wadannan harufan rubutu wadanda mutane suka sani ne ya saukar da Alkuraninsa, wanda kuma shi ne mujizar Annabi mafi girma. Wato tambar Alkurani yana cewa; “idan kuma kuna iyawa to ku kawo littafi kamar Alkurani wanda aka rubuta da irin wadanna harufa.” Wadannan ayoyi suna bayyana batutuwa biyu muhimmai; na daya shi ne, Alkurani littafi ne mai bayyanawa, littafin da yake bayyana hanyar gaskiya yake kuma haskaka hanyar rayuwa don mutane su cimma manufar da suke sa a gaba a karkashinn wannan haske. Na biyu kuma shi ne, wajibi ne kowa ya yi tunani a cikin abinda ayoyin Alkurani suke koyarwa su kuma sami amfanin wadannan ayoyi don bunkasa tunaninsu da hankalinsu. Alkurani bai sauka don a karanta shi domin neman ladar lahira kadai ba, an saukar da shi ne domin dan Adam ya yi amfani da shi don tsara rayuwarsu ta daidaiku da alumma a nan duniya, kuma ya mai da koyarwarsa ta zama ginshikin tafarkin rayuwa.
Wadannan ayoyi suna koya mana cewa:
1-Larabci shi ne yaren Alkurani kuma ya kamata mu koye shi saboda mu iya yin tunani a kan abinda ayoyinsa suke fada.
2-Ba karantawa da neman albarka kadai ne amfanin Alkurani ba, abin yin tunani da amfani da hankali ne da bil Adama.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 3:
نَحْنُ نَقُصُّ عَلَيْكَ أَحْسَنَ الْقَصَصِ بِمَا أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ هَـذَا الْقُرْآنَ وَإِن كُنتَ مِن قَبْلِهِ لَمِنَ الْغَافِلِينَ{3}
"Mũ ne Munã lãbãrta maka mafiya ingancin lãbãrugame da abin da Muke yi maka wahayi da shi na wannan Alkur'ãni, ko da yake kana cikin marasa sanin sa kafin mu yo maka wahayinsa."
A wannan aya Allah yana ce da Annabinsa cewa; “Wannan wahayi da muke yi maka yana yi maka kyakkyawan bayani kan labaran alummomin da suka gabata, kuma shi ma wannan bayani wahayi ne kuma sashe ne na littafin Allah wato Alkurani. Tun farko dai amfanin labari shin ne koya wa mutane tarbiya musamman ma idan labari yana bayyana hakikanin abinda ya faru a zamanin wasu mutane, ba wai tatsuniya ce ba da gwanayen tsara labari suke tsarawa. Sifa mafi muhimmanci na labaran da Alkurani ya bayar shi ne kasancewarsu suna bayyana abubuwa ne da hakika sun faru, abinda a wannan zamani ake kira tarihi wanda kuma ake gudanar da nazari a kansa a cibiyoyin ilimi da bincike.
A cikin wata wasikar da Imam Ali (a.s.) ya rubuta wa dansa Imam Hasan (a.s.) yana cewa, “Da na, sani dai ni na yi nazari cikin tarihin magabata har ka ce a zamaninsu na zo duniya kuma na rayu kamar dukkan tsawon zamaninsu” Muhimmancin da Alkurani ya baiwa tarihi ya kai matsayin da wasu hadisai suna cewa daya daga cikin sunayen Alkurani shi ne “Mafi kyawun Labari”,wato Ahsanul Qasas, kalmar da kuma ta zo a cikin wannan aya, wato kamar yanda ake kiransa Furqan “mai rarrabewa”, da sauran sunaye na Alkurani mai girma. Kuma dadin dadawa, Allah madaukakin sarki ya ce shi ne mai bada labari kuma ya ce shi ne yake bada labarin Annabi Yusuf ga Manzonsa (Ts.), ya kuma sanya wannan labari a matsayin wani bangare na Alkurani da ake karantawa dare da rana.
An kira wannan labari na Annabi Yusuf 'mafi kyawun labari' ne saboda abubuwa da dama; babban wanda labarin yake magana a kansa, wato Annabi Yusuf (a.s.), wani matashi ne wanda tsarki, da rikon amana, da juriya da kuma karfin imani suka mamaye dukkanin samuwarsa. Babban abinda labarin yake koyarwa shi ne Annabi Yusuf ya yaki zuciyarsa ya kuma yi nasara duk da cewa yana cikin tsakiyar kuruciya. Wannan labari ya tara abubuwa kishiyoyin juna kamar-- rabuwa da masoyi da sake hadewa da shi, bakin ciki da farin ciki, fari da yalwar abinci, jafa’i da mutuntawa, bauta da mulki, tsarki da tuhuma.
Gafala da Allah ya ambata a wannan aya yana da maanar rashin masaniya kan wani abu wanda a kashin kansa ba aibi ba ne. Gafala wanda yake abin ki shi ne wanda mutum zai nisanci neman ilimi kamar gafala ga sanin Allah da ayoyin da suke bayyana girmansa. Manzon rahama (Ts.) bai san labarin Annabi Yusuf ba amma ta hanayar wahayi Allah ya sanar da shi.
Darusa:
1-Ya kamata mu bada labaran gaskiya na manyan mutane wadanda suka sami nasara a rayuwarsu domin koyar da matasa da ma sauran alumma yanda ake rayuwa mai kyau.
2-Labaran da Alkurani yake bayarwa na tarihi na gaskiya ne kum aabin dogaro saboda Allah masani mai hikima shi ne ya fade su.
To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na Surar Yusuf. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
Suratu Yusuf, Aya Ta 4-6 (Kashi Na 369)
Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar Yusuf, da fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa.
To madalla. Da farko bari mu saurari aya 4:
إِذْ قَالَ يُوسُفُ لِأَبِيهِ يَا أَبتِ إِنِّي رَأَيْتُ أَحَدَ عَشَرَ كَوْكَباً وَالشَّمْسَ وَالْقَمَرَ رَأَيْتُهُمْ لِي سَاجِدِينَ{4}
"(Ka tuna) lõkacin da Yũsufu ya ce da babansa, "Yã bãbana, hakika na ga taurãri gõma shã daya da rãnã da watã: na gan su sunã yi min sujada."
Labarin Annabi Yusuf ya fara ne da bayanai mafarki wadanda yake nuna alamar cewa a nan gaba zai zama mutum mai girma. Annabin Musulunci Muhammadu (Tsira) yana cewa: “Mafarki iri uku ne: na daya bishara ne daga Allah, na biyu bakin ciki ne daga Shedan na uku kuma mastalolin rayuwar yau da kullum ne da mutum yake gani a cikin barcinsa.”
Mafarkin waliyan Allah da mutane masu tsarki mafarki ne na gaskiya wato mafarkin tamkar wani wahayi ne ko ilmahi daga Allah, kamar yanda Annabi Ibrahim (a.s.) ya gani amafarki yana yanka dansa Ismail (a.s.). Wani abinda mafarkin tsarkakan mutanen yake nufi kuma shi ne bayyana wani abinda zai faru a nan gaba kamar mafarkin Annabi Yusuf din wanda kuma a karshen labarin aka kawo cewa ya sami babban mukami kuma yan uwansa goma sha daya da mahaifinsa da mahaifiyarsa duka sun halarta a gabansa.
Darusa:
1- Mafarki hanya ce wasu mutane suke sanin abubuwa.
2-Idan iyaye suka nuna wa ‘yayansu soyayya ta gaskiya ‘ya'yan zasu bayyana musu abubwuan da suke ciki saboda yarda dasu da suka yi.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 5-----
قَالَ يَا بُنَيَّ لاَ تَقْصُصْ رُؤْيَاكَ عَلَى إِخْوَتِكَ فَيَكِيدُواْ لَكَ كَيْداً إِنَّ الشَّيْطَانَ لِلإِنسَانِ عَدُوٌّ مُّبِينٌ{5}
"Ya ce: "Ya dã na, kada ka labarta mafarkinka ga 'yan'uwanka, sai su shirya maka makirci; hakika Shaidan makiyi ne mai makiyi ne mai mabayyanin kiyayya ga mutum."
Baban Annabi Yusuf wato Yaqub (a.s.) da ya ji mafarkin da dansa ya yi, ya dauke shi wani sako ne daga Allah mai nuna matsasyin da Yusuf zai kai a nan gaba. Saboda haka sai ya ce da Yusuf ya boye wa yan uwansa wannan mafarki da ya yi don ta yi wu su yi masa hasada su kuma cutar da shi. Alamarin hasada, ya kama iyaye da 'ya'ya su maida hankali don kada ta shigo ta haddasa rashin jituwa a gida, saboda haka a lokacin da mutum yake yaba wa wani dansa kan wani abin kirki da ya aikata to lallai ya maida hankali kada yabon ya sa 'yan uwan yaron ko yarinyar su ji zafi. Annabi Yusuf ya fada wa babansa wannan labarin mafarkinsa a kebe, shi kuma Annabi Yaqub ya ce kada ya bayyana shi.
Darusa:
1-Kamar yanda yada labarin wani mafarki yake iya haddasa fitina, haka ma bai kamata mu yi ta fadar abinda muka gani a farke a ko ina kuma wa kowane irin mutum ba, domin da akwai yiwuwar wannan magana ta jawo fitina.
2-Hadarin da hasada ke jawowa a cikin gida da kuma a tsakanin alumma, ba abu ne na wasa ba, don haka idan aka kiyaye shi za a kaucewa matsaloli masu yawa.
Yanzu kuma mu saurari aya ta 6-----
وَكَذَلِكَ يَجْتَبِيكَ رَبُّكَ وَيُعَلِّمُكَ مِن تَأْوِيلِ الأَحَادِيثِ وَيُتِمُّ نِعْمَتَهُ عَلَيْكَ وَعَلَى آلِ يَعْقُوبَ كَمَا أَتَمَّهَا عَلَى أَبَوَيْكَ مِن قَبْلُ إِبْرَاهِيمَ وَإِسْحَاقَ إِنَّ رَبَّكَ عَلِيمٌ حَكِيمٌ{6}
" To haka ne kuma Ubangijinka zai zabe ka ya kuma sanar da kai wani daga fassarar mafarki, ya kuma cika ni'imõminSa a gare ka, da kuma ga gidan Yãkũbu kãmar yadda tun tuni ya cika ta ga iyayenka Ibrãhĩm da Is'hãka. Hakika Ubangijinka Masani ne Mai hikima ne."
Annabi Yaqub (a.s.) ya ci gaba da yi wa dan saYusuf nasiha yana cewa, “Yusufu, a nan gaba Allah zai zabe ka annabi kuma zai cika wa gidan mu niimominsa. Banda haka kuma zai sanar da kai fassar mafarki, ka zama mai fassara mafarkai da bayyana sirrin da suka kunsa.” Annabi Yaqub ya yi wannan magana ne daga ilimin gaibin da Allah ya sanar da shi.
Darusa:
1-Allah yana zabar fiyayyen mutane ya mai da shi annabi ya kuma ba shi ilimin da yake bukata domin ya zama ta hanyarsa ne almumma zata sami shiriya.
2- Adduar da Annabi Ibrahim (a.s.) ya yi na cewa Allah ya sanya annabta ta ci gaba a cikin zuriyarsa, ta zama karbabba. Zuriyarsa sun zama annabawa kuma wannan yana nuna cewa tsarki ya wanzu a cikin wannan gida zababbe.
To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na Surar Yusuf. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
Suratu Yusuf, Aya Ta 7-10 (Kashi Na 370)
Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar Yusuf, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa.
To madalla. Da farko bari mu saurari aya 7 da ta 8:
لَّقَدْ كَانَ فِي يُوسُفَ وَإِخْوَتِهِ آيَاتٌ لِّلسَّائِلِينَ{7} إِذْ قَالُواْ لَيُوسُفُ وَأَخُوهُ أَحَبُّ إِلَى أَبِينَا مِنَّا وَنَحْنُ عُصْبَةٌ إِنَّ أَبَانَا لَفِي ضَلاَلٍ مُّبِينٍ{8}
-"Hakika akwai ayoyi ga mutanen baya dangane da Yũsufu, shi da 'yan'uwansa." -"(Ka tuna) lõkacin da (yan uwan) suka ce: 'Hakika Yũsufu da dan'uwansa babanmu ya fi son su da mu, alhãli kuwa mũ jama'a mai yawa. Hakika babanmu yana cikin kuskure mabayyani."
Kamar yanda muka ji a farkon wannan sura labarin Annabi Yusuf ya fara ne da batun mafarkin da ya yi wanda kuma ya ke bayyana babban matsayin da zai kai a rayuwarsa. Sai dai kai wa ga wannan matsayi mai samu cikin sauki ba domin kuwa ya sha wahalhalu da yawa a rayuwarsa kuma ya kamata masu neman gaskiya su dauki darasi daga hakan, su san cewa ba abinda ake samunsa cikin sauki.
Tun a cikin gida Annabi Yusuf ya fuskanci hasada daga yan ubansa wadanda suka hada mahaifiya daya, shi kuma da Binyaminu mahaifiyarsu guda. Yan uban nasa sun nuna kiyayyarsu da Yusuf da Binyaminu nsuna cewa wai mahaifinsu Annabi yakubu yafi son su biyun a kansu alhali kuwa ba wata soyaya ce ta nuna bambanci ba. Lamarin ya kai ga sun zargi mahaifinsu yana cikin kuskure.
Darusa:
1-Ilmomin da Alkurani yake kunshe da su suna da yawa amma sai wanda yake bincike da tunani a kan ayoyinsa ne yake samun wannan ilimi.
2-Mu yi taka tsantsan wajen alakokinmu da ‘ya’yanmu domin idan wasu daga cikinisu suka ji cewa muna nuna banbanci to hasada zata shigo.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 9-----
اقْتُلُواْ يُوسُفَ أَوِ اطْرَحُوهُ أَرْضاً يَخْلُ لَكُمْ وَجْهُ أَبِيكُمْ وَتَكُونُواْ مِن بَعْدِهِ قَوْماً صَالِحِينَ{9}
"Ku kashe Yũsufu kõ kuwa ku jẽfa shi wata kasa, (yin haka) zai juyo muku fuskar babanku, kuma za ku kasance mutane salihai bãyansa."
Kuskuren fahimtar dalilin da ya sa baban Annabi Yusuf yake nuna masa kauna wacce yan uwansa suka yi wa mahaifin nasu ya sanya wasu daga cikinsu ya bada shawarar cewa a san yanda zaa kawar da Yusuf daga wurin domin yan uwansa su sake su sami karbuwa wajen babansu, kuma dag a bisani Allah zai yi musu gafara kuma zu zama salihan mutane.
Amma ai yin nadama kan aikata sabo shi ne daidai ba wai mutum ya ce tun da yake zai yi nadama ya tuba bari ya aikata sabo ba. Idan mutum ya yace bari in yi sabo a yanzu kana daga baya in tuba, to lallai yana yaudarar kansa ne. Tamkar dai mutum ya ce bari yanzu in ci wannan abinci mai guba sannan daga baya in tafi wajen likita ya bani maganin karya guba in sha.
Shawarar kashe Annabi Yusuf ko kuma nesantar da shi daga waurin babansa aikin Shedan ne mai nuna tsananin hasada da yan uwansa suke yi masa. Wannan babban kashedi ne ga iyaye dangane da yanda hasada take iya cin zuciyar mutum ya aikata mummunan aiki, saboda haka iyaye su kula sosai kan yanda suke mua'mala da yayansu.
Darusa:
1-Munin hasada ya kai ga cewa yana iya kai mutun ga hallaka dan uwansa, kamar yanda muka ji a wanna labari na Annabi Yusuf da kuma a labarin habila da kabila yayan Annabi Adam (a.s.).
2-‘Ya’ya suna kaunar soyayyar iyayensu saboda haka wajibi ne iyaye suyi hattata kada su karancin soyayyar da suke nuna wa yayansu ya sanya ‘yayan aikata mugun aiki.
Yanzu kuma mu saurari aya ta 10-----
قَالَ قَآئِلٌ مَّنْهُمْ لاَ تَقْتُلُواْ يُوسُفَ وَأَلْقُوهُ فِي غَيَابَةِ الْجُبِّ يَلْتَقِطْهُ بَعْضُ السَّيَّارَةِ إِن كُنتُمْ فَاعِلِينَ{10}
"Wani mai magana daga cikinsu ya ce: 'Kada ku kashe Yũsufu; ku jẽfa shi a cikin duhun rĩjiya, wasu ayarin matafiya sa tsince shi, in har vhaka zaku yi."
Da yake hasadar da yan uwan Annabi Yusuf suka yi masa ba daidai take ga dukkansu ba; wani ya fi wani, sai wasu daga cikinsu suka ki a kasha shi, shi nya sa dayansu y ace: ai ba sai kashe shi ba, mu jefa shi ckin rijiya, yin haka ai zai wadatar kuma zamu huta da shi. Idan mun yi haka mun tsira daga laifin kisansa shi kuma matafi zasu zo diban ruwa sais u tadda shi su fiddo shi su tafi da shi. Sauran yan uwan sai suna amiunce da wanna shawara kuma da haka Yusuf ya tsira daga mutuwa.
A nan akwai abin lura, a wani lokaci hani da aikata munkari wanda zai tserar da ran mutum daya zai kawo sakamakon sauyi mai yawa a tarihi kamar dai wannna nna Annabi Yusuf. A lokacinda Yusuf ya zama mai iko a kasar Masar ya kubutar da kasar bakji daya daga matsalar da zata fiskanta sabo da matsanancin fari wanda ya yi mata barazana. A labarin Annabi Musa ma wanda ya rayu shekaru da yawa bayan Annabi Yusfu, matar Firauna ta bai wa mijinta shawarar kada ya kashe Musa kuma a lokacin day a girma shi ne ya yantar da Israilawa daga bautarwar da Firaunonin Masar suka yi musu. Wadannan kyawawan misalai suna bayyana maanar maganar Alkurani mai cewa: “Duk wanda ya raya mutum daya tamkar ya raya mutane ne baki daya.”
Darusa:
1-Idan ba zamu iya hana wani mummunan aiki duka ba mu hana abinda muke iya hanawa don mu rage munin abin da akew sao aikatawa, kamar dai yanda daya daga cikin yan uwan Annabi Yusuf ya kada a kashe shi a jefa shi cikin rijiyta don wasu su tsince shi.
2-Idan ana son aikata laifi kada mu bi mafiya yawan mutane saboda yawansu, a maimakon nhaka mu ma mu fadi raayin mu wanda ya saba da nasu.
To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na Surar Yusuf. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
Suratu Yusuf, Aya Ta 11-15 (Kashi Na 371)
Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar Yusuf, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa.
To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 11 da ta 12:
قَالُواْ يَا أَبَانَا مَا لَكَ لاَ تَأْمَنَّا عَلَى يُوسُفَ وَإِنَّا لَهُ لَنَاصِحُونَ{11} أَرْسِلْهُ مَعَنَا غَداً يَرْتَعْ وَيَلْعَبْ وَإِنَّا لَهُ لَحَافِظُونَ{12}
"Suka ce: "Yã bãbanmu, me ya sa ne ba ka amince mana game da Yũsufu, alhãli kuwa hakika mũ ba shakka masu kula da shi ne?"
"Ka tura shi gõbe tare da mu ya yi kiwo, ya kuma yi wãsa, hakika mu lallai zamu kiyaye shi."
A shirin da ya gabata mun ji yanda yan uwan Annabi Yusuf (a.s.) suka yi shawarar kashe shi amma daga bisani suka janye wannan shawarar suka sauya ta da dauke shi daga gaban mahaifinsu ko da dai yana da rai, su ka kuma jefa shi cikin rijiya don daga baya wasu su tsince shi su tafi da shi wata kasa. Saboda su dauke shi daga gaban mahaifin sai su ka shirya makarkashiya, suka ce da babansu: me ya sa yake ware Yusuf, ya bar shi mana ya bi su wajen aiki a bayan gari don ya motsa jiki da shakata.
Lallai wannan dalili da suka bayar a zahirinsa mai gamsarwa ne wanda kuma zai sa su raba shi da babansu, domin kuwa shakatawa da motsa jiki ababen so ne ga matasa. Saboda haka duk da cewa fitar Yusuf bata kwanta wa zuciyar Annabi yakubu bai hana su tafiya dashi ba.
1-Ba dukkanin abin da aka yi daawarsa ne yake gaskiya ba, saboda haka kada mu yaudaru da duk abinda wani ke fadi, shi kansa Annabi Yakubu ya dai kyale yayansa ne suka tafi da Yusuf ba don ya aminta da su ba.
2-Hasada tana sa mutum ya yi karya hatta wa makusantansa.
3-Matasa suna bukatar shakatawa da wasannin motsa jiki, amma dole ne a kula kada wasu su yi amfani da wannan dama su cutar da matasan.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 13:
قَالَ إِنِّي لَيَحْزُنُنِي أَن تَذْهَبُواْ بِهِ وَأَخَافُ أَن يَأْكُلَهُ الذِّئْبُ وَأَنتُمْ عَنْهُ غَافِلُونَ{13}
"Ya ce: "Hakika lallai tafiyarku da shi za ta bakanta mini rai, ina kuma tsõron kura ta cinye shi ba da saninku ba.."
Annabi Yakubu bai so ya rabu da dansa Yusufu ba amma da yake a lokacin Yusuf yaro ne wanda ya kamata ya fara koyon ayyuka domin da kadan da kadan ya mike kan kafafuwansa saboda a na gaba zai zama babba wanda nauyi zai hau kansa, saboda haka ne babansa ya bada izni ya bi 'yan uwansa su fita tare. Wato a nan akwai yiwuwar wani hadari ya sami dansa Yusuf amma kuma bai kamata hakan ya sa ya boye shi a gida ba, saboda kuwa samun gogewar da zata sa ya iya tsayawa da kafafunsa ya muhimmanci kan kare shi daga hadarin da ake tsammanin yana iya faruwa. Kamata ya yi iyaye su buda wa yayansu kofar samun gogewa duk da kaunar da suke yi musu, alla bashi idan sun hango musu wani abu mai hadari ko illa sai su fadakar da su don su kiyaye.
Darusa:
1-A wajen yi wa yaro tarbiya ya kamata a lura da batutuwa biyu muhimmai; samar da yanayin da zasu sami gogewa har su tsaya da kafafunsu su zama muatanen kansu dangane da alamuran rayuwa, na biyu kuma yi musu gargadi kan haduran da suke iya haduwa da su ke yiwa matashi barazana.
2-Yin gafala da abubuwa masu hadari ya na iya yi wa mutum babbar illa, a wani lokaci ma illar da ba ta da magani.
Yanzu kuma mu saurari aya ta 14-----
قَالُواْ لَئِنْ أَكَلَهُ الذِّئْبُ وَنَحْنُ عُصْبَةٌ إِنَّا إِذاً لَّخَاسِرُونَ{14}
"Suka ce: "Lallai idan kura ta cinye shi ga mu kuwa muna da yawa kuma majiya karfi to ashe hakika mun mun tabe."
A lokacin da 'yan uwan Annabi Yusuf (a.s.) suka kitsa dabarar da suka yi don janje shi daga gaban babansu, sun san cewa babansu Annabi Yakubu zai nuna damuwa amma amsar da kadai suka tanada kan hakan ita ce: suna da karfin jiki da yawa kuma zasu iya kiyaye lafiyar kaninsu Yusuf. To sai dai a sarari yake cewa karfi ba shi ya ke tabbatar da cewa mutum amintacce ne ba. Lallai kam su kasance suna da karfi amma suna kuma da nufin aikata hainci, lamarin da kuma Annabi Yakubu ya gane amma ba bu wata hujja ta bayyane da zata tabbatar da hakan, saboda haka sai ya kyale su suka tafi da shi.
Darusa:
1-Yawa-yawan matasa suna tinkafo ne da karfin jiki da suke da shi kuma basu kula da hadarin da ke tattare da alamarin da suke ciki, amma manya suna taka tsantsan dangane da yiwuwar matsala ko hadari ya kasance cikin kowane abu.
2-Wasu mutane zasu iya aikata komai domin cimma muguwar manufarsu; suna iya yin karya ko yaudara da kuma zubar da mutuncinsu saboda hakan.
Yanzu kuma mu saurari aya ta 15-----
فَلَمَّا ذَهَبُواْ بِهِ وَأَجْمَعُواْ أَن يَجْعَلُوهُ فِي غَيَابَةِ الْجُبِّ وَأَوْحَيْنَا إِلَيْهِ لَتُنَبِّئَنَّهُم بِأَمْرِهِمْ هَـذَا وَهُمْ لاَ يَشْعُرُونَ{15}
"To lõkacin da suka tafi da shi suka kuma hadu kan su saka shi cikin duhun rĩjiya, Muka kuma masa wahayi (da cewa): 'Lalle wata rana za ka ba su labarin wannan al'amari nãsu alhali su ba sa jin haka zai faru."
Yan uwan Annabi dai sun raba shi da mahaifinsu suka tafi da shi bayan gari kuma kamar yanda suka shirya tun farko, sai suka sanya shi cikin rijiya amma ba cikin ruwa; sun sanya shi ne a cikin kogon rijiyar kusa da ruwa domin kada kishi ya halaka shi, kuma a lokaci guda ya tsira daga namun daji a sanyi da zafi na waje. Har wala yau idan ayarin fatake ya zo domin diban ruwa a rijiyar sai su fiddo shi su ceci ransa. A wannan yanayi kuma na duhun rijiya mai ban tsoro musamman ga matashi, Allah ya kwantar da hankalin Yusuf ya kuma yi masa ilhamin cewa kada ya damu domin a na gaba zai bai wa yan uwansan nan labarin wannan mugunn aikin da suka yi, kuma zai sami matsayin da har sai ya yi musu alfarma.
Darusa da zamu koya daga wannan aya su ne:
1-Ilhami da Allah yake yi wa bayinsa bai kebanta da annabawa ba; salihan bayin Allah suma suna samun ilhami, a wancan lokaci shi kansa Yusuf (a.s.) bai zama annabi ba tukuna amma ya sami ilhami daga Allah.
2-Kyakkwarar fata ita ce babbar hanyar da take taimaka wa gudanar da rayuwa, domin debe kyauna shi ne matsakin farko na rashin nasara.
3-A lokacin da mutum ya shiga tsanani, wajibi ne ya koma ga Allah ya yi tsammanin samun rahamarsa, kuma ko da wasa bai kamata mutun ya yanke kauna ba.
To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na Surar Yusuf. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
Suratu Yusuf, Aya Ta 16-18 (Kashi Na 372)
Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar Yusuf, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa.
To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 16------
وَجَاؤُواْ أَبَاهُمْ عِشَاء يَبْكُونَ{16}
"Suka Kuwa dawo wa babansu da dare sunã kũka.
A shirin da ya gabata mun ji cewa yan uwann Annabi Yusuf sun aiwatar da makarkashiyar da suka kulla kuma sun sanya Yususf a cikkin rijiya sannan suka koma gida. Kamar yanda aka sani gameda alakar uban da dansa, dole ne daga shigarsu gida Annabi Yakubu ya duba don ya ga dansa ya dawo, saboda sanin haka sai suka shigo gida da kuka suna zubar da hawayen karya don su nuna cewa sun ji zafin abinda ya faru da Yusuf tun ma kafin su fadi abinda ya faru, kuma don su nuna cewa ba wata makarkashiya da suka yi ba.
Darusa:
1-Don mutum ya na kuka yana zub da hawaye, ba lallai ne a dogara da abinda yake fadi ba, ai sau da yawa mahainta suna nuna damuwa da alhini suna zubar da hawaye amma na munafunci.
2-Masu munafunci sukan aikata abubuwan da zasu sosa zuciya kamar kuka don su yaudari mutane.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 17-----
قَالُواْ يَا أَبَانَا إِنَّا ذَهَبْنَا نَسْتَبِقُ وَتَرَكْنَا يُوسُفَ عِندَ مَتَاعِنَا فَأَكَلَهُ الذِّئْبُ وَمَا أَنتَ بِمُؤْمِنٍ لِّنَا وَلَوْ كُنَّا صَادِقِينَ{17}
"Suka ce: "Yã bãbanmu, mun tafi munã wasan tsẽre muka kuma bar Yusufu wurin kãyanmu, sai kura ta cinye shi. Ba kuwa za ka gaskanta mu ba ko da muna da gaskiya"
Baicin kukan karya, yan uwan Annabi Yusuf sun kaga karya mai girma inda suka ce kura at cinye Yusuf a lokacin da suka bar shi wajen kayansu yana kula musu da shi, sunn mance da cewa tun farko sun fada wa babansu cewa zasu tafi tare da Yusuf ne don ya yi wasa ya shakata ba don su sanya shi mai kula da kayansu su kuma su yi wasa da tsere ba. Banda ma sun yi karya, sun kuma zargi babansu da rashin yarda da su ko da ma gaskiya suka fada.
Darusa:
1-A wanionlokaci fadar karya daya tana jawo sai mutum ya yi wasukarairayi don ya boye karyar farko. Yan uwan Annabi Yusuf sun yi karairai daya na bin daya ba tareda sun san cewa maganganunsu suna warware juna ba.
2-Dabi'ar makaryaci shi ne zai dage sai mutane su yarda da maganarsa domin yana tsoron bayyanar gaskiya.
Yanzu kuma mu saurari aya ta 18:
وَجَآؤُوا عَلَى قَمِيصِهِ بِدَمٍ كَذِبٍ قَالَ بَلْ سَوَّلَتْ لَكُمْ أَنفُسُكُمْ أَمْراً فَصَبْرٌ جَمِيلٌ وَاللّهُ الْمُسْتَعَانُ عَلَى مَا تَصِفُونَ{18}
"Suka kuma zo da jinin karya rigarsa, babansu ya ce: "Ba haka ba ne, zuciyarku dai ta shirya muku wani abu. Saboda haka (ba ni da wani abin yi ) sai hakuri na gari, Allah kuma Shi ne Mai taimako game da abin da kuke sifantãwa."
Kurakuran yan uwan Annabi Yusuf da suka faro su da kukan karya sun kai ga sun nuna wa babansu rigar kanensu wacce suka jika da jinin wata dabba, don su tabbatar masa da cewa lallai kura ce ta cinye shi. Yaudarar su bata ci Annabi Yakubu (a.s.) ba, don kuwa yana sane da makirci ne suka yi amma kawai sai ya e da su, ai idan kuna so ne ku cutar da Yusuf ku raba ni da shi, ni ma kun cuitar da ni kuma wannan bakin cikin nda kuka cusa mini, ba bu kuma abinda zai kawo mini sauki sai mai da lamari ga Allah da dogara gare shi. Hala abinda ya sa Annabi Yakubu bai wa 'ya'ansa wani hukunci ba, bai kuma yi komai domin neman Yusuf ba shi ne abinda ya faru ya yi daidai da mafarkin da Yusuf ya ba shi labari. Annabi yakubu ya san dansa Yusuf yana raye kuma Allah zai kare shi daga halaka, kuma zai kai ga babban matsayi. Saboda haka abinda kawai ya yi shi ne ya roki Allah ya ba shi hakurin jure wa rabuwa da Yusuf har lokacin da zasu sake haduwa.
Darusa:
1-Gurbatacciyar zuciya tana zayyana wa mutum aikin sabo ya gan shi tamkar aikin kwarai, saboda haka sai ta shirya masa hujjojin da zai kare laifinsa da su.
2-Kowane abin da yake faruwa, ta wata fuska jarrabawa ce daga Allah don haka dole ne mu shirya mata ta juriya da hakuri.
3-Kyakkyawan hakuri shi ne, ko da zuciyar mutum tana kuna akan abin da ya same shi yana kuma zubar da hawaye amma ba zai yi butulci niiomin da Allah ya masa ba ba zai kuma ba zai yi fushi da Allah ba, sai dai ya nemi taimakon Ubangiji kan balain da ya same shi.
To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar Yusuf. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
Suratu Yusuf, Aya Ta 19-22 (Kashi Na 373)
Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar Yusuf, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa.
To madalla. Da farko bari mu saurari aya 19 da ta 20:
وَجَاءتْ سَيَّارَةٌ فَأَرْسَلُواْ وَارِدَهُمْ فَأَدْلَى دَلْوَهُ قَالَ يَا بُشْرَى هَـذَا غُلاَمٌ وَأَسَرُّوهُ بِضَاعَةً وَاللّهُ عَلِيمٌ بِمَا يَعْمَلُونَ{19} وَشَرَوْهُ بِثَمَنٍ بَخْسٍ دَرَاهِمَ مَعْدُودَةٍ وَكَانُواْ فِيهِ مِنَ الزَّاهِدِينَ{20}
"Kuma wani ãyari ya je, sai suka aika mai nẽman musu rũwa, sai ya zura gugansa, ya ce: "Yã bushãrata! Wannan yãro ne." Kuma suka bõye shi yanã abin sayarwa. Kuma Allah ne Masani ga abin da suke aikatãwa." "Kuma suka sayar da shi da 'yan kudi kadan, dirhamõmi kidãyayyu, Kuma sun kasance, a wurinsa, daga mãsu isuwa da abu kadan."
A shirin da ya gabata mun ji cewa yan uwan Annabi Yusuf su sanya shi cikin rijiya sun kuma dawo gida da dare dauke da rigarsa da suka jika da jinin wata dabba suka ce wai kura ce ta cinye shi, kuma sun yi ta kuka domin a zatonsu mahaifinsu zai yarda cewa abinda suka fadi gaskiya ne. A wannan aya kuma zamu ambaci abin da ya sami Annabi Yusuf. Bai dade a cikin rijiyar ba sai wani ayari suka zo don diban ruwa. Mai jawo musu ruwa sai ya zura gugarsa cikin rijiyar amma sai Annabi Yusuf ya kama igiyar aka zago da shi aka fitar da shi waje. Ayarin nan sai suka dauki Yusuf a matsayin bawa wanda zasu sayar a kasuwar bayi in suna so, kuma haka aka yi, suka boye shi cikin kayansu har suka kai kasuwar bayi suka sai da shi kudi kalilan, saboda sun tsince shi ne kuma ba wata wahala da suka yi suka same shi. Haka dan Adam ya ke a wani lokaci ba ya ganin kimar abinda ya samu cikin sauki ba tare da wahala ba.
Darusa:
1-Wani lokaci makusantan mutum zasu jefa shi cikin ramin masifu da wahala amma sai wani bare ya zo ya tsamo mutum daga wannan wahala.
2-Wasu mutane suna yi wa dan Adam kallo irin wanda ake yi wa haja, suna mancewa da bangaren zuciya da abinda ta kunsa.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 21:
وَقَالَ الَّذِي اشْتَرَاهُ مِن مِّصْرَ لاِمْرَأَتِهِ أَكْرِمِي مَثْوَاهُ عَسَى أَن يَنفَعَنَا أَوْ نَتَّخِذَهُ وَلَداً وَكَذَلِكَ مَكَّنِّا لِيُوسُفَ فِي الأَرْضِ وَلِنُعَلِّمَهُ مِن تَأْوِيلِ الأَحَادِيثِ وَاللّهُ غَالِبٌ عَلَى أَمْرِهِ وَلَـكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لاَ يَعْلَمُونَ{21}
"Kuma wanda ya saye shi daga Masar ya ce wa mãtarsa, "Ki girmama mazauninsa, akwai tsammãnin ya amfãne mu, kõ kuwa mu rike shi dã."Kuma kamar wancan ne Muka tabbatar ga Yũsufu,a cikin kasa kuma dõmin Mu sanar da shi daia fassarar lũbũru, kuma Allah ne Marinjãyi a kan al'amarinSa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."
Lokacin da ayarin nan suka kai Yusuf (a.s.) kasuwa sai wani dan aiken fadar sarki ya sayi wannan kyakkaywan saurayi ya kai wa sarkin Masar. Sai sarki ya kai shi cikin gida don ya yi aikin hidima, matar sarki kuwa ta yi farin ciki samun wannan yaro a gabanta, domin ba su haifu ba kuma basu tsammanin samun haifuwa. Shigar da Yusuf cikin gidan sarki ya buda masa hanyar tabbatar da abinda ya gani a mafarki da na samun babban matsayi.
Darusa:
1-Zukata suna hannun Allah kuma shi yake juya su. Sarkin Masar ya kauna ci Yusuf har ya ya mai da shi kamar dan da ya haifa, duk da cewa a zahiri bawa ne.
2-Sau da yawa wahalhalu suna kawo karshe mai kyau kuma wannan kaida da Allah yake gudanar da ikonsa, wanda ake kira Sunnar Allah. Allah cikin ikonsa ya fitar da Yususf daga cikin rijiya ya kuma dora shi kan kololuwar daukaka.
Yanzu kuma mu saurari aya ta 22-----
وَلَمَّا بَلَغَ أَشُدَّهُ آتَيْنَاهُ حُكْماً وَعِلْماً وَكَذَلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ{22}
"Kuma a lõkacin da ya isa mafi karfinsa, Muka bã shi hukunci da ilmi. Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu kyautatãwa."
A cikin labarin Annabi Yusuf Allah ya bayyana matsayinsa na imani. Yusuf ya rayu a cikin fadan sarkin Masar amma da yake shi salihi ne, lokacin da ya kai munzilin da ya dace a ba shi ludufi na musamman daga Allah wato annabci da sanin gaibi sai Allah ya zabe shi ya bashi annabta. Wannan ya yi daidai da tsarin Sunnar Allah yanda daga nan duniya ma Allah ya ke ba shi lada mai girma.
Lallai Allah ya na zabar wasu mutane daga cikin bayinsa a cikin alumma ya mai da su annabawa, kuma yana jarraba su da wahalhalu iri iri domin zukatansu su kai girma da yalwar da zasu iya daukar manyan nauye-nauyen da Allah zai dora musu, kuma cancantarsu da wannan matsayi ta bayyana ga jama'a.
Darusa:
1-Wasu ilmomin da annabawa suke da su daga wajen Allah suke samunsu ba tare da koyo ba.
2-Karbar sakon Ubangiji yana bukatar mutum ya kasance ya mallaki wasu sifofi da cancanta kuma Allah kadai ya san da samuwar wadannan sifofi a tare da wani mutum.
3-Karfin ilimi da na jiki ba su isa don a sami ludufin Allah kamar annabta ko makamancin haka, dole ne mutum ya kasance mai kyakkyawar zuciya da aikata alheri.
To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar Yusuf. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
Suratu Yusuf, Aya Ta 23-24 (Kashi Na 374)
Masu sauraro barkanmu da saduwa da ku acikin wannan shirin na Hannunka mai sanda. Shiri ne dai wanda mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur’ani mai girma, wanda yanzu mun shiga cikin suratu Yusuf. Da fatan za a kasance a tare da mu domin a saurari ci gaban shirin.
Yanzu sai a saurari aya ta 23 a cikin suratu Yusuf.
وَرَاوَدَتْهُ الَّتِي هُوَ فِي بَيْتِهَا عَن نَّفْسِهِ وَغَلَّقَتِ الأَبْوَابَ وَقَالَتْ هَيْتَ لَكَ قَالَ مَعَاذَ اللّهِ إِنَّهُ رَبِّي أَحْسَنَ مَثْوَايَ إِنَّهُ لاَ يُفْلِحُ الظَّالِمُونَ{23}
“Sai wacce ya ke a cikin dakinta ta neme shi bisa tilasarsa akan ya sadu da ita, ta kulle kofofi ta ce da shi, “taho” sai ya ce: “Allah ya kiyashe ni” hakika ubangijina ya girmama makomata, hakika azzalumai ba za su rabauta ba.”
A cikin shirin da ya gabata mun yi magana akan cewa ma’ajin masar shi ne wanda ya aiki da wani mutum zuwa kasuwar bayi da ya siyo masa Yusuf domin ya zama mai yi masa hidima a gidansa. Sai dai lokacin da ya ga kyawun halitta da kuma cikar hankalin da Yusuf ya ke da shi, sai ya fadawa matarsa cewa: Ki girmama shi. Saboda haka sai Yusuf ya zama mutumin da ya ke da matsayi acikin wannan gidan. Ya zamana an banbanta shi da sauran masu hidima.
Yusuf wanda ‘yan’uwansa na jini su ka wulakanta shi, sannan kuma su ka jefa shi cikin rijiya shi ne yanzu ya wayi gari ya zama acikin gidan ma’ajin masar, yana fuskantar jarrabawa mai tsanani. Jarabawa ce wacce za ta iya faruwa da kowane saurayi da ya ke da shekaru irin na yusuf saboda haka ya waja wajibi a kasance cikin shiri domin yin galaba akan biyewa son zuciya.
Matar ma’ajin masar ta kamu da son shi, ta yadda ta bukace shi da ya sadu da ita duk da cewa shi bawa ne kuma ma’aikaci a gidanta. Wannan kuwa wani lamari ne wanda ya sabawa tsarin zamantakewa na wancan lokacin.
Matar ma’ajin masar ta yi amfani da hanyoyi daban-daban domin jan hankalin Yusuf zuwa gare ta, amma lokacin da ta ga cewa Yusuf bai mika kai ga son ciyarta ba sai ta fito fili gaba gadi ta neme shi a cikin dakin da ta kadaita da shi. Ta kulle kofofi sannan ta bayyana bukatrta.
Annabi Yusuf ya bata yankakken jawabi da cewa: Tare da cewa ni bawanki ne, amma a matakin farko ni bawan Allah ne kuma ina neman tsari a wurinsa ya hane ni aikata sabo. Ba kuwa zan fiifta bukatarki ba akan biyayya ga ubangijina. Ubangijina ne wanda ya tseratar da ni daga cikin rijiya sannan ya kawo ni wannan matsayin. Ba zan sabe shi ba. Idan na yi haka kuwa na zalunci kaina kuma na ci amanar mai gidanki-ma’ajin masar wanda ya amince da ni ya shigar da ni cikin gidansa. Ba zan taba zama maci amana ba.
Darussan da su ke cikin wannan aya.
1-Sha’awa tana da karfin gaske ta yadda idan ba a danneta ba, matar ma’abocin sarauta za ta iya neman bawa.
2-A wasu lokutan cakuduwa tsakanin mata da maza da ba muharramai ba, yana iya share fagen afkuwar barna. Saboda haka rikafi shi ne hana wannan irin cakuduwa tun kafin barna ta afku.
3-Biyayya ga mahalicci ita ce sama da gamsar da mutane, ko mai matsayin mutanen koda kuwa uwa da uba ne ko shugaba ko wani mai mukami.
4-Idan dukkanin kofofi sun rufe to kofar rahamar Allah ba za ta rufe ba, za a iya neman mafaka a wurin Ubangiji domin samun tsira daga aikata sabo.
Yanzu kuma sai aya ta 24 a cikin wannan sura ta Yusuf.
وَلَقَدْ هَمَّتْ بِهِ وَهَمَّ بِهَا لَوْلا أَن رَّأَى بُرْهَانَ رَبِّهِ كَذَلِكَ لِنَصْرِفَ عَنْهُ السُّوءَ وَالْفَحْشَاء إِنَّهُ مِنْ عِبَادِنَا الْمُخْلَصِينَ{24}
“Hakika ta yi nufin saduwa da shi, ba domin ya ga hujjar ubangijinsa ba da ya nufe ta. Da haka ne mu ka nesanta mummunan aiki da alfasha daga gare shi. Shi yana daga cikin bayinmu zababbu.”
Ayar baya tana magana ne akan yadda annabi Yusuf ya nemi tsari a wurin Allah daga mawuyacin halin da samu kansa a ciki. To wannan ayar kuwa tana cewa ba domin Yusuf ya nemi tsari daga Allah ba to da ya biye wannan mata ya aikata sabo. Sai dai hasken imani wanda ya ke cikin zuciyar yusuf ya zama hujja mai karfi da ya yi maga kandagarko daga aikata sabo.
Imani, ya fi hankali karfi wajen hana mutum biye wa sha’awar zuciyarsa. Saud a dama hankali kan ci kasa a gaban sha’awa amma imani yana yin galaba. Imani da Allah yana da karfi fiye da sha’awa kowace iri ce.
Darussan da zamu koya daga wannan aya.
1-Matukar mu yi imani mai zurfi da Allah to shakka babu taimakonsa zai riske mu, ba tare da taimakon Allah ba babu wani mahaluki da ba zai iya cin kasa ba.
2-Tsarkake niyya acikin bautar Ubangiji da mika kai a gare shi, yana da tasiri acikin wannan duniyar. Daga cikin wannan irin tasirin da akwai samun taimakon Allah acikin lokuta mafi wuya da tsanani na rayuwa.
3-Annabawan Allah mutane ne daidai kowa a dabi’a ta halitta da ta hada da sha’awa. Sai dai karfin imani da Allah da su ke da shi yana hana su aikata sabo, kuma Allah yana kiyaye su daga fadawa cikinsa.
Wannan shi ne karshen shirinmu na wannan lokacin sai a kasance a tare da mu domin a ji ci gaban shirin.
Suratu Yusuf, Aya Ta 25-27 (Kashi Na 375)
Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin da mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur’ani mai girma. Har yanzu dai muna cikin suratu Yusuf.
Da fatan za a kasance a tare da mu domin jin ci gaban shirin.
Yanzu kuma sai a saurari aya ta 25 a cikin wannan sura ta Yusuf.
وَاسُتَبَقَا الْبَابَ وَقَدَّتْ قَمِيصَهُ مِن دُبُرٍ وَأَلْفَيَا سَيِّدَهَا لَدَى الْبَابِ قَالَتْ مَا جَزَاء مَنْ أَرَادَ بِأَهْلِكَ سُوَءاً إِلاَّ أَن يُسْجَنَ أَوْ عَذَابٌ أَلِيمٌ{25}
“ Sai su biyu (Yusufa da matar ma’ajin masar) su ka yi rigegeniya zuwa bakin kofa, ta keta rigarsa daga baya, sai su ka ci karo da mai gidanta a bakin kofa. Sai ta ce: menene sakamakon wanda ya nufi iyalinka da mummunan aiki idan ba a daure shi ba ko azaba mai radadi.?”
A baya mun yi magana akan yadda matar ma’ajin masar ta kamu da son yusuf har ta kai ga ta shirya makirci domin saudwa da shi a cikin dakin da rufe kofofinsa. Sai dai yusuf bai biye wa son zuciyarta ba saboda haka ya ruga a guje zuwa bakin kofa domin ya sami hanayr tsere mata.
Sai dai duk da haka zulaika ta bishi a baya a guje ta kama rigarsa ta baya tana ja domin ta tsaida shi. Ya ci gaba da gudu abinda ya sa rigarsa ta kece daga baya. A daidai lokacin da su ka isa bakin kofa ne, su ka ci karo da ma’ajin Masar wato mijin Zulaika. Kafin Yusuf ya kai ga bada jawabi gare shi akan abinda ya ke faruwa Zulaika ta rigaye shi yin magana tana mai tuhumarsa da cin amana da kuma kira da a dauki mataki mai tsanani akansa.
Darussan da za mu koya daga wannan aya.
1-Neman tsari a wurin Ubangiji baya takaita acikin fada da fatar baki kadai. Wajibi ne a gujewa aikata sabo a aikace,koda kuwa dukkanin kofofi sun kasance a rufe kuma mutum yana cikin matsanancin hali.
2-A wani loakci ayyuka biyu suna yin kama da juna a zahiri amma a hakikaninsu suna da banbanci. A zahiri Zulaika da Yusuf suna gudu amma daya saboda ya gujewa aikata sabo ne daya kuwa saboda ya aikata sabo.
3-Dole ne a rika yin taka tsantsan wajen yanku hukunci domin a wani lokacin mai laifi ne ya ke yin kuka.
Yanzu kuwa sai a saurari aya ta 26 da 27 a cikin wannan sura ta Yusuf.
قَالَ هِيَ رَاوَدَتْنِي عَن نَّفْسِي وَشَهِدَ شَاهِدٌ مِّنْ أَهْلِهَا إِن كَانَ قَمِيصُهُ قُدَّ مِن قُبُلٍ فَصَدَقَتْ وَهُوَ مِنَ الكَاذِبِينَ{26} وَإِنْ كَانَ قَمِيصُهُ قُدَّ مِن دُبُرٍ فَكَذَبَتْ وَهُوَ مِن الصَّادِقِينَ{27}
“Sai-Yusuf- ya ce ita ce ta neme ni. Sai mai shaida daga cikin iyalanta ya bada shaida cewa idan har taguwarsa ta kece ne daga gaba to ta yi gaskiya shi kuma yana cikin makaryata. Idan kuwa taguwarsa ta kece daga baya to ta yi karya shi kuwa yana cikin masu gaskiya.”
Wannan ayar tana bayyana yadda annabi Yusuf ya ke kare kansa ne daga kazafin da Zulaika ta yi masa. Yana kuma bayyana gaskiyar lamari cewa ita ce ta ke da mummunan nufi akanshi.
Ma’ajin masar wanda ya ji bayanan dukkanin bangarorin biyu ya kasa gaskata cewa matarsa tana neman bawa. Haka nan kuma ba zai iya gaskata cewa bawa zai iya samun karfin guiwar guiwar da zai nemi matar mai gidansa ba.
A cikin wannan irin halin ne wani daga cikin mashawartansa wanda ya ganewa idanunsa dukkanin abinda ya faru ya yi amfani da dabara wajen bada shaida. Ya fadi cewa: Idan har Yusuf yana da mummunan nufi akan Zulaika shakka babu zai su yi jayaya da juna. A hali irin wannan kuwa zai zamana rigarsa ta kece ne daga gaba. Amma saboda rigarsa ta kece ne daga baya, yana nufin cewa yana kokarin guduwa ne. Saboda haka Zulaika makaryaciya ce. Wani abu mai jan hankali anan shi ne cewa wanda ya bada shaidar nan daga cikin iyalan Zulaika ne.
Labarin abinda ya faru tsakanin annabi Yusuf da Zulaika yana sa mutum ya tuno da labarin maryam ‘yar Imrana da cikinta. Gwargwadon yadda mutum ya ke da tsarki ne ya ke fuskantar tuhuma da zargi mar tushe da kazafi. Maryam ta kasance mace mafi tsarki a zamaninta, amma mutanen wancan lokacin su ka zarge ta da alfahasha har ta kai tana yin fatan mutuwa. Shi ma yusufa a zamaninsa shi ne mafi tsarkin mutane amma aka zarge shi da abinda bai dace ba. Shakka babu ubangiji ya kare su ta hanyar tabbatar da tsarkinsu da kuma gaskiyarsu.
Sau uku a cikin labarin annabi Yusuf taguwa ta taka rawa. Na farko shine a lokacin da aka jefa shi cikin rijiya, ‘yan uwansa su ka dauki taguwar tashi da su ka zubawa jinin karya zuwa ga mahaifinsu domin su tabbatar da cewa kyarkeci ya cinye shi. To amma saboda babu inda taguwar ta yage karyarsu ta fito fili cewa kyarkeci bai cinye shi ba. Anan kuwa da taguwarsa ta kece daga baya ya zama dalilin da ke tabbatar da gaskiyarsa. A akrshe kuwa shi ne lokacin da aka kaiwa mahaifinsa annabi Yakubu taguwarsa da kuma jefa masa ita a fuska, idanunsa da su ka kamance sun sake dawowa da gani.
Darussan da za mu koya daga wannan aya.
1-Wajibi ne mutum ya kare kansa idan an yi masa kazafi ya kuma bayyana mai laifi na hakika, koda kuwa ba shi da fatan samun adalci.
2-Allah yana yin nufi dangin mai laifi su bada shaida akansa.
3-Wajibi ne a yi aiki da dalilai domin gano mai laifi saboda a yanke hukunci. Baya ga magana ta fatar baki a matsayin shaida a kuma yi aiki da wasu alamu da mai laifi ya bari wadanda kuma su ke nuni da yadda ya aikata laifin.
Nan ne karshen wannan shirin sai kuma mun sake haduwa a shiri na gaba.
Suratu Yusuf, Aya Ta 28-30 (Kashi Na 376)
Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Hannunka Mai Sanda wanda mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur’ani mai girma. Idan kuma ana bibiyar shirin namu za a iya tuna cewa har yanzu muna cikin suratu Yusuf ne.
Da fatan za a kasance a tare da mu domin jin ci gaban shirin daga inda mu ka tsaya.
Yanzu sai a saurari aya ta 28 a cikin wannan sura ta Yusuf.
فَلَمَّا رَأَى قَمِيصَهُ قُدَّ مِن دُبُرٍ قَالَ إِنَّهُ مِن كَيْدِكُنَّ إِنَّ كَيْدَكُنَّ عَظِيمٌ{28}
“Yayinda ya ga taguwarsa ta kece daga baya sai ya ce, wannan yana daga cikin makircinku-mata, tabbas kaidinku yana da girma.”
A shirin da ya gabata mun yi mgana ne akan yadda Yusuf ya gujewa Zulaika da kuma yadda taguwarsa ta kece daga baya saboda jan da ta yi mata. Haka nan kuma mun ji yadda wani daga cikin iyalan ita Zulaika din ya bada shaida akan cewa idan har daga gaba ne taguwar ta kece to ita ce mai gaskiya, amma idan daga baya ne ta kece to shi ne mai gaskiya ita kuma makaryaciya ce.
To wannan ayar tana ci gaba da yin bayani ne akan yadda mai gidan ita Zulaika ya tabbatar da gaskiyar Yusuf. Saboda haka ne ya ke magana da matarsa yana fada mata cewa: Abinda ki ka fada kina son ki yaudare ni ne da yi mani gadar zare saboda in hau in dauka cewa Yusuf ne mai laifi ke kuma wacce aka zalunta. Makircinku mata yana da girman gaske.
Darussan da za mu koya daga wannan aya.
1-Gaskiya ba ta buya, kuma ko mai dadewa asirin mai laifi zai tonu.
2-Mu karbi zancen gaskiya komai dadin da ya ke da shi a gare mu, kamar yadda ma'ajin masar ya karbi gaskiyar cewa matarsa ce mai laifi.
Yanzu kuma sai a saurari aya ta 29 a cikin wannan sura ta "Yusuf.
يُوسُفُ أَعْرِضْ عَنْ هَـذَا وَاسْتَغْفِرِي لِذَنبِكِ إِنَّكِ كُنتِ مِنَ الْخَاطِئِينَ{29}
“Yusuf ka kauda kanka daga barin wannan lamarin. -Ke kuma -ki nemi gafara ga zunubanki, hakika ke kin kasance daga masu kuskure.”
Wannan ayar tana nuni ne da cewa ma'ajin masar mutum ne mai adalci kuma mai karbar gaskiya. Domin kuwa lokacin da ya fahimci cewa Yusuf ba shi da laifi sai ya bukace shi da rufe maganar domin kare mutuncin matarsa, bai kuma fadi hakan ba cikin baraza ko fada. Ya bukaci haka ne daga Yusuf cikin taushin murya.
A lokaci guda kuma ya dorawa matarsa laifi, sannan ya bukace ta da ta nemi gafara akan kuskuren da ta aikata. Hakan kuwa yana nufin cewa shi mutum ne da ya yi imani da sakamako akan kowane aiki.
Abubuwan da za mu koya daga wannan aya.
1-Idan mun ga munanan ayyuka da wasu su ka aikata to bai kamata mu watsa shi ba da kai shi gaba.
2-A tsawon tarihi kuma acikin kowace al'umma alakar da bata dace ba a tsakanin mace da namiji abin kyama ce.
Yanzu kuma sai a saurari aya ta 30 a cikin wannan sura ta "Yusuf."
وَقَالَ نِسْوَةٌ فِي الْمَدِينَةِ امْرَأَةُ الْعَزِيزِ تُرَاوِدُ فَتَاهَا عَن نَّفْسِهِ قَدْ شَغَفَهَا حُبّاً إِنَّا لَنَرَاهَا فِي ضَلاَلٍ مُّبِينٍ{30}
“Sai mata acikin birni su ka ce: matar ma’ajin masar tana neman baranta, hakikai soyayya ta lullubeta. Hakika mu muna ganinta acikin bata bayyananne."
Tare da cewa ma'ajin Masar ya bukaci Yusuf da ya sakaya maganar kada ta fita waje daga cikin fada, sai dai abu ne da ya ke a fili cewa a cikin fadar sarakuna da akwai mutane masu yawan gaske, kuma da akwai tsegumi da gutsuri tsoma. Saboda haka wani ya fito da maganar waje ya yada ta a cikin gari. A karshe kuwa magana ta isa kunnuwan matan gari wadanda su kuma su ka nuna rashin yardarsu akan cewa matar ma'ajin masar ta nemi bawanta. Saboda haka su ka cece-kuce akan lamarin.
A gefe daya wajibi ne a fahimci cewa wannan bawan da matar ma'ajin masar ta nema, ya banbanta da sauran bayi, shakka babu yana da wasu siffofi na halitta da kuma halyayya da su ka ja hankalin Zulaika akansa har ta kamu da sonsa. Wannan shi ne ya sa su kansu matan da su ke tsegumi akan lamarin su ka bukaci ganin wannan bawan da idanunsu. Hassada ma ta taka rawa acikin wannan tsegumin nasu.
Wani abu mai jan hankali akan annabi Yusuf (a.s) shi ne cewa da akwai gungun mutane biyu da su ka wuce gona da iri akansa. Na farko su ne 'yan'uwansa na jini da su ka nuna masa hassada akan kaunar da mahifinsa ya ke yi masa su ka fada cewa: " Tabbas mu muna ganinka akan bata bayyananne."
Sai kuma matan masar da su ka zargi Zulaika da bata bayyananne a fadinsu cewa: "Hakika muna ganinta akan bata bayyananne."
Kaunar da mahaifin ya ke yi wa dansa mai tsarki ce, amma son da Zulaika ta nunawa Yusuf gurbatacce ne. Sai dai wani darasi da za dauka anan shi ne cewa wanda duk bai fada cikin kogin soyayya ba to ba zai fahimce ta ba kuma zai rika ganin mai yinta a matsayin batacce.
Masu bautar abin duniya su na ganin waliyyan Allah da su ka nutse a cikin kaunar ubangiji a matsayin batattu ko kuma mahaukata.
Darussan da za mukoya daga wannan aya.
1-Rufe kofofi domin aikata zunubi a asirce baya hana a tozarta kuma aikata saboda yana cin dunun mutum ya kai shi kasa.
2-Maigida shi ne wanda nauyin kula da iyalai ke kansa kuma mutane idan daya daga cikin iyalan ya aikata laifi to mutane za su dora masa laifi.
Karshen shirinmu na wannan lokacin kenan sai a kasance a tare da mu domin a saurari shirin na gaba daga inda mu ka tsaya.
Suratu Yusuf, Aya Ta 31-33 (Kashi Na 377)
Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin na Hannunka mai sanda wanda mu ke kawo muku fassarar ayoyin kur'ani mai girma. Idan kuma ba a mance ba muna cikin suratu Yusuf ne kuma mun tsaya ne a kan aya ta 30.
Da fatan za a kasance a tare da mu domin jin ci gaban shirin daga inda ya tsaya.
Yanzu sai a saurari aya ta 31 a cikin suratu Yusuf.
فَلَمَّا سَمِعَتْ بِمَكْرِهِنَّ أَرْسَلَتْ إِلَيْهِنَّ وَأَعْتَدَتْ لَهُنَّ مُتَّكَأً وَآتَتْ كُلَّ وَاحِدَةٍ مِّنْهُنَّ سِكِّيناً وَقَالَتِ اخْرُجْ عَلَيْهِنَّ فَلَمَّا رَأَيْنَهُ أَكْبَرْنَهُ وَقَطَّعْنَ أَيْدِيَهُنَّ وَقُلْنَ حَاشَ لِلّهِ مَا هَـذَا بَشَراً إِنْ هَـذَا إِلاَّ مَلَكٌ كَرِيمٌ{31}
" Yayinda da-Zulaika- ta ji labarin makircinsu sai ta yi musu aike, ta shirya musu- taro- da ta yi musu tanadin matashi kuma ta ajewa kowace daya daga cikinsu wuka sannan ta ce da shi-yusuf- ka fita zuwa wurinsu. Yayinda su ka ganshi sai su ka girmama shi su ka yanke hannuwansu su ka kuma fadi cewa tsarki ya tabbata ga Allah wannan ba mutum ba ne. Hakika shi mala'ika ne mai matsayi."
A shirin bayan mun bayyana cewa yayinda matan masar su ka ji labarin cewa matar ma'ajin masar ta kamu da son bawanta sai su ka rika yin tsegumi da gulma da ita. Sai dai a lokaci guda sun bukaci su ga wannan bawan da idanunsu domin su yanke hukunci ko ya cancanci matar ma'aji ta so shi so kuma mai tsanani.
A lokaci daya kuma ita Zulaika tana son ta kare abinda ta yi ta baiwa kanta gaskiya akan nunawa Yusuf so da ta yi ta hanyar nuna shi a gaban matan domin su ganewa idanunsu kyawun halittarsa. Saboda haka ta tara matan fada da na cikin gari sannan ta shirya walima gagaruma da kayan alatu. A yayinda Yusuf ya fito bisa umarnin Zulaika, kyawun halittarsa ya fisge su da jefa su cikin magagin da ya yi kama da maye. Sun tsarkake Ubangiji cikin mamaki yadda ya yi halitta mai kyawu har haka har suna kore cewa shi mutum ne, su ka danganta shi da mala'ika mai girma.
Zulaika ta maida bugun da matan Masar su ka yi mata na zargi ta yadda idan ita ta kamu da son Yusuf ne to su kuwa sun yanke hannuwansu saboda ganinsa da su ka yi sau guda a rayuwarsu, alhali ita ta rayu tare da shi na lokaci mai tsawo.
Abubuwan da za mu koya daga wannan aya.
1-A wasu lokutan ba son gyara ne ya ke jawo suka ba, yana samo asali ne daga hassada.
2-A wani lokacin mutane suna sukar wasu amma idan da ace za su samu kansu a cikin halin da wadanda su ka suka su ka kassance to ba za su ci jarrabawa ba. Matan masar sun rika zargin Zulaika akan Yusuf, amma lokacin da su ka gan shi na kankanen lokaci sun kasa daurewa.
Yanzu kuma sai a saurari aya ta 32 a cikin wannan sura ta Yusuf.
قَالَتْ فَذَلِكُنَّ الَّذِي لُمْتُنَّنِي فِيهِ وَلَقَدْ رَاوَدتُّهُ عَن نَّفْسِهِ فَاسَتَعْصَمَ وَلَئِن لَّمْ يَفْعَلْ مَا آمُرُهُ لَيُسْجَنَنَّ وَلَيَكُوناً مِّنَ الصَّاغِرِينَ{32}
"Sai ta ce to wannan shi ne wanda ku ke zargina akansa. Hakika na neme shi amma ya kame kansa. Matukar kuwa bai aikata abinda na umarce shi ba shakka babu zai shiga kurkuku ko kuma ya kaskanta."
Tare da cewa a gaban mijinta Sulaika ta zargi Yusuf da aikata laifi sannan kuma ta wane kanta, amma anan a gaban matan Masar ta yi furuci da laifinta. Ta kuma fada musu cewa ku dube shi ku gani ba a banza na kamu da son shi balle ku riga zargina. Amma kuma duk da haka ya ki amincewa da abinda na bukace shi saboda haka zan sa a daure shi a kurkuku saboda ya fahimci cewa bai kamata ya ki bin umarnin masu gidansa ba. Abin mamaki anan shi ne cewa hatta Zulaika ta yi furuci da tsarkin ruhin Yusuf.
Abubuwan da za mu koya daga wannan aya.
1-Tsarkin ruhi yana da kimar da hatta marasa wannan tsarkin suna yin furuci da shi da yabonsa da kuma daukarsa wani abin girmamawa. 2-Idan har iko da mulki su ka shiga hannun mutanen da ba su da tsarkin ruhi za su jefa masu tsarkin ruhi acikin gidan kurkuku saboda idan suna waje za su kawo musu cikas wajen cimma manufofinsu.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 33 a cikin wannan sura ta Yusuf.
قَالَ رَبِّ السِّجْنُ أَحَبُّ إِلَيَّ مِمَّا يَدْعُونَنِي إِلَيْهِ وَإِلاَّ تَصْرِفْ عَنِّي كَيْدَهُنَّ أَصْبُ إِلَيْهِنَّ وَأَكُن مِّنَ الْجَاهِلِينَ{33}
"Sai ya ce ya ubangiji, kurkuku shi ne mafi soyuwa a gare ni akan in aikata abinda su ke kirana zuwa gare shi. Idan ba ka kawar da makircinsu daga gare ni ba zan karkata zuwa gare su, sai ya zamana na shiga cikin jahilai."
Tare da cewa ma'ajin masar ya yi furuci da tsarkin Yusuf da kuma kubutarsa daga aikata laifi, kuma Zulaika ta yi furuci a gaban matan Masar cewa ita ce na nemi Yusf amma ya ki mika mata kai, sai dai duk da haka an jefa Yusuf a cikin kurkuku bisa bukatar Zulaika. Wannan yana nuni da cewa mazauna fada suna biyewa son zuciyar matansu, kuma su ne masu ayyana makomar mutane.
A daya gefen kuma mutane masu tsarkin ruhi suna fifita shiga kurkuku da ace sun mika kai ga son zuciyar wani mahaluki. Su mutane ne da su ke fifita yardar Allah akan kowane abu a rayuwa. Kuma koda bukatar iyayengijinsu mutane ne.
Abubuwan da za mu koya daga wannan ayar.
1-Tsarkin ruhi abu ne mai matukar kyau da muhimmanci. Mutane da dama a tsawon tarihi sun shiga gidan kurkuku saboda tsarkin ruhinsu.
A gefe daya idan har zama cikin 'yanci a sake zai kai mutum ga take abubuwa masu kida da yawa, to wannan 'yancin ba shi da wata kima.
2-Nesantar wurin da ake aikata sabo yana da kima da matsayi, duk da wahalhalun da su ke tattare a cikin hakan.
3-Jahilci bai takaita acikin rashin iya rubutu da karatu ba. Biyewa son zuciya da sha'awa shi ne tsagwaron jahilci.
Masu sauraro karshen shirinmu na wannan lokacin kenan. Da fatan za a kasance a tare da mu domin jin ci gaban shirin.
Suratu Yusuf, Aya Ta 34-36 (Kashi Na 378)
Muna bude shirin namu na Hannunka Mai Sanda a wannan rana da yin salati ga ma'aikin Allah, annabi Muhammad (s.a.w) da iyalan gidansa tsarkaka. Kuma har yanzu muna cikin suratu Yusuf ne da mu ke kawo muku tarihin annabi Yusuf (a.s)
Da fatan za a kasance a tare da mu domin jin ci gaban shirin daga inda mu ka a baya wato aya ta 33.
Yanzu sai a saurari aya ta 34 a cikin wannan sura ta Yusuf.
فَاسْتَجَابَ لَهُ رَبُّهُ فَصَرَفَ عَنْهُ كَيْدَهُنَّ إِنَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ{34}
" Sai ubangijinsa ya amsa masa ya kawar da makircinsu-mata-daga gare shi. Shi-Ubangiji- mai ji ne kuma masani."
A shirin baya mun yi mgana akan barazanar da Zulaika ta yi wa Yusuf aka cea za ta sa adaure shi a kurkuku saboda ya ki mika wuya ga son zuciyarta. Shi kuwa Yusuf ya roki Allah da ya kai shi kurkuku saboda ya zama hanyar da zai gujewa biyewa son zuciyar Zulaika.
To wannan ayar tana magana ne akan cewa Ubangiji ya karba addu'ar da annabi Yusuf ya yi, ya tseratar da shi daga rayuwar makirci da makarkashiya da kutunguila irin ta mata. Wani abu mai jan hankali anan shi ne cewa Yusfu ya shiga kurkuku bisa umarnin Zulaika, amma kuma a cikin wannan ayar Ubangiji yana fadin cewa addu'arsa ce aka karba. Ma'anar wannan ita ce cewa idan ba ace Ubangiji bai so ba to Zulaika ba ta isa ta kai shi kurkuku ba. Wannan darasi ne mai girma ga muminai akan cewa duk yadda makiya za su kitsa makirci da kutunguila matukar Allah bai nufa ba to babu wani abu da za su iya yi. Saboda haka wajibi ne adogara da Allah a cikin kowane abu.
Abubuwan da za mu koya daga wannan aya.
1-Idan har muna son mu zama masu tsarkin ruhi, to shakka babu Ubangiji zai share mana fagen kaiwa ga hakan.
2-Zulaika tana son jefa Yusuf cikin kurkuku domin ta tsorata shi, amma a wurin yusuf kurkuku yana a matsayin hanyar tsira ce daga sabawa ubangiji.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 35 a cikin wannan sura ta Yusuf.
ثُمَّ بَدَا لَهُم مِّن بَعْدِ مَا رَأَوُاْ الآيَاتِ لَيَسْجُنُنَّهُ حَتَّى حِينٍ{35}
"Bayan da su ka ga alamu ( na tsarkin annabi Yusuf) sai su ka ji cewa a tsare shi a kurkuku na wani lokaci."
Daya daga cikin siffofin tsarin dagutanci shi ne cewa masu mulki su ne ginshikin da kowane abu ya ke yi wa dawafi. Abinda su ka halarta shi ne halaliya abinda su ka haramta kuma shi ne haramun. Sun baiwa kawunansu hakkin daukar mataki da sunan duk wanda su ka ga dama bisa daidai ko rashin daidai.
Babu wanda bai fahimci cewa Zulaika ce mai laifi ba a masar domin kuwa ita da bakinta ta fadawa matan masar da ta shiryawa walima hakan. Ta kuma yi furuci da tsarkin da annabi Yusuf ya ke da shi. Sai dai kuma a karshe mutanen Fada sun yanke hukuncin kai Yusuf gidan kurkuku domin su kare matsayin Zulaika har zuwa lokacin da za a mance da abinda ya faru tsakaninsa da ita.
Abubuwan da za mu koya daga wannan aya.
1-Tsarkake ruhi ba abu ne mai sauki ba, domin kuwa a karkashin tsarin dagutu gwargwadon yadda mutum ya ke da tsarki neya ke fuskantar matsala da takura.
2-Acikin gurbatacciyar al'umma mabartana suna cikin walwala da 'yanci, masu tsarkin kuwa su ne ke zama saniyar ware kuma wadanda ake daurewa.
Yanzu kuma sai a saurari aya ta 36 acikin wannan sura ta Yusuf.
وَدَخَلَ مَعَهُ السِّجْنَ فَتَيَانَ قَالَ أَحَدُهُمَا إِنِّي أَرَانِي أَعْصِرُ خَمْراً وَقَالَ الآخَرُ إِنِّي أَرَانِي أَحْمِلُ فَوْقَ رَأْسِي خُبْزاً تَأْكُلُ الطَّيْرُ مِنْهُ نَبِّئْنَا بِتَأْوِيلِهِ إِنَّا نَرَاكَ مِنَ الْمُحْسِنِينَ{36}
" Sai ya shiga kurkuku a tare da wasu matasa biyu. Sai daya daga cikinsu ya ce: Ni na yi mafarki na ganni ina matsar giya. Sai dayan kuwa ya fadi cewa ni na ganni ina dauke da biredi akaina kuma tsuntsu yana gutsurarsa. Ka bamu labarin fassararsa domin muna ganinka acikin mutanen kwarai."
A karshe dai Yusuf ya shiga kurkuku bisa umarnin fada. A tare da shi kuwa da akwai wasu matasa biyu ma'aikatan fada da su ka yi laifi. Kowane daga cikinsu ya yi mafarki sannan kuma sun fadawa Yusuf mafarkin da su ka yi. Kasantuwarsu ma'aikatan fada suna da labarin abinda ya faru tsakanin Yusuf da Zulaika, abinda ya sa su ka kira shi mutumin kirki.
Mutanen kwarai, koda sun shiga kurkuku suna zama abin dogaron mutane. Ya zamana mutane suna sanar da su sirrinsu da neman shawara daga gare su.
Kwane daya daga cikin wadannan matasan ya yi mafarkin da ya sha banban da na dan'uwansa kuma mafarki ne mai ban mamaki. Domin kuwa ya damfaru ne da makomar kowane daya daga cikinsu. Guda daga cikinsu ya ga ganshi a cikin mafarki yana yin giya. Dayan kuwa ya ga kanshi a cikin mafarki yana raba biredi ga tsuntsaye, kuma daya daga cikin tsuntsayen yana gutsurar biredin.
Wani abu mai muhimmanci shi ne yadda Yusuf ya sami matsayi na musamman a tsakanin fursunoni. Kamar yadda ya zo a cikin riwayoyi yana yi wa marasa lafiya magani, yana kuma taimakawa mabukata. Abubuwan da za mu koya daga wannan aya.
1-Mutanen kwarai ababan girmamawa ne a ko'ina hatta acikin kurkuku.
2-Kyautatawa fursunoni da yi musu hidima shi ne matakin farko da annabi Yusuf ya yi amfani da shi domin isar da sakon Ubangiji na tauhidi gare su.
Karshen shirin namu kenan na wannan lokacin sai a lokaci na gaba inda za a ji mu da ci gaba.
Suratu Yusuf, Aya Ta 37-40 (Kashi Na 379)
Muna bude shirinmu na Hannunka mai Sanda a wannan rana da yin salati ga ma'aikin Allah da iyalan gidansa tsarkaka. Da fatan za ku kasance a tare da mu domin jin ci gaban shirin daga inda mu ka tsaya a baya.
To yanzu sai a saurari aya ta 37 a cikin wannan sura ta Yusuf.
قَالَ لاَ يَأْتِيكُمَا طَعَامٌ تُرْزَقَانِهِ إِلاَّ نَبَّأْتُكُمَا بِتَأْوِيلِهِ قَبْلَ أَن يَأْتِيكُمَا ذَلِكُمَا مِمَّا عَلَّمَنِي رَبِّي إِنِّي تَرَكْتُ مِلَّةَ قَوْمٍ لاَّ يُؤْمِنُونَ بِاللّهِ وَهُم بِالآخِرَةِ هُمْ كَافِرُونَ{37}
"Sai- Yusuf- ya ce: Kafin abincin da za ku ci ya iso gare ku zan fada mu ku fassarar shi-mafarkin. Wannan kuwa yana daga abinda Ubangijina ya sanar da shi. Ni na yi watsi da al'ummar da ba ta yi imani da Allah kuma su ke kafricewa ranar lahira."
A shirin bayan mun bada labarin cewa da akwai wasu samari biyu ma'aikatan fada da su ka shiga kurkuku a tare da yusuf saboda sun aikata laifi. Sun yi mafarkin da su ka fadawa annabi Yusuf saboda suna son ya yi musu fassara.
To wannan ayar tana ci gaba da bada labarin cewa yusuf ya fara da yi musu alkawalin cewa zai fassara musu mafarkinsu saboda su saurari abinda zai fada musu. Daga nan sai ya shiga yin wa'azi akan illar shrika da tara wani da Allah da kafrici. Ya fadi cewa: Idan ubangiji ya yi mani wannan baiwar ta fassara mafarki, to saboda na yi watsi da mutanen da su ke hada wani da Allah ne. Wannan baiwar ba tawa ba ce Allah ne ya bani ita bisa jin kansa da tausayinsa.
Annabi Yusuf yana sane da cewa wadannan samarin guda biyu mushrikai ne ba muminai ba, amma duk da haka baya yin magana da su a matsayinsu na kafirai, yana danganta shirka ne kafirci ga wasu.
Darasin da za mu koya daga wannan aya.
1-Wanda duk ya nesanci duhun shirka da kafirci to Allah zai yi masa baiwa da haske da ilimi da kuma hikima ya fahimci hakikanin lamurra da waninsa ba su gani.
2-Wajibi ne a yi amfani da damar da ta samu bisa hanya mafi dacewa. Annabi Yusuf (a.s) da ya sami kansa a cikin kurkuku ya yi wa'azi da wayar da kan fursunoni.
Yanzu kuma sai a aurari aya ta 38 acikin suratu Yusuf.
وَاتَّبَعْتُ مِلَّةَ آبَآئِـي إِبْرَاهِيمَ وَإِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ مَا كَانَ لَنَا أَن نُّشْرِكَ بِاللّهِ مِن شَيْءٍ ذَلِكَ مِن فَضْلِ اللّهِ عَلَيْنَا وَعَلَى النَّاسِ وَلَـكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لاَ يَشْكُرُونَ{38}
"Ni ina bin tafarkin mahaifana Ibrahim da Ishaka da Yakub. Bai dace da mu ba mu tara Allah da wani abu, Wannan kuwa yana daga falalar da Allah ya yi mana da kuma mutane, Sai dai mafi yawancin mutane ba su yin godiya."
A ci gaba da wa'azin da annabi Yusufu ya ke yi wa wadannan samarin biyu akan illar shirka da kafirci yana cewa: Ni ina tafiya ne akan tafarkin manyana annbawan Allah ne irinsu annabi Ibrahim , bai kuma dace da ni ba in karkace daga kan tafarkinsu. Samuwar wadannan annabawan wata ni'ima ce daga Allah a gare mu da kuma mutane, amma abin takaici ne cewa mafi yawancin mutane ba su san matsayin wadannan annabawan Allah din ba, balle su saurari sakon da su ke dauke da shi zuwa gare su.
Darussan da za mu koya daga wannan aya.
1-Yin alfahari da mahaifa zai zama karbabbe idan tafarkin da su ke bi na gaskiya ne.
2-Samuwar annabawa wata ni'ima ce mai girma daga Allah kuma yin biyayya a gare su yana nufin yi wa Allah godiya. Rashin bin tafarkinsu kuwa rashin yin godiya ne ga Allah.
Yanzu kuma sai a saurari aya ta 39 da 40 acikin wannan sura ta Yusuf.
يَا صَاحِبَيِ السِّجْنِ أَأَرْبَابٌ مُّتَفَرِّقُونَ خَيْرٌ أَمِ اللّهُ الْوَاحِدُ الْقَهَّارُ{39} مَا تَعْبُدُونَ مِن دُونِهِ إِلاَّ أَسْمَاء سَمَّيْتُمُوهَا أَنتُمْ وَآبَآؤُكُم مَّا أَنزَلَ اللّهُ بِهَا مِن سُلْطَانٍ إِنِ الْحُكْمُ إِلاَّ لِلّهِ أَمَرَ أَلاَّ تَعْبُدُواْ إِلاَّ إِيَّاهُ ذَلِكَ الدِّينُ الْقَيِّمُ وَلَـكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لاَ يَعْلَمُونَ{40}
" Ya ku abokan zamana na kurkuku shin iyayengiji barkatai su ne mafi alheri ko kuma Allah guda daya gagara buwayi? Abinda ku ke bautawa waninsa ba su da wani matsayi da ya wuce sunayen da ku ka kirkiraku da iyayenku wacce kuma Allah bai saukar da wata hujja akanta ba. Hukuncin Allah shi kadai ne hukunci. Ya bada umarni da cewa kada ku bautawa wani face shi. Wannan shi ne addini mikakke, sai dai mafi yawancin mutane ba su sani ba."
A ci gaba da wa'azin da annabi Yusuf ya ke yi wa samarin da su ke tare da su a kurkuku dangane da tauhidi da watsi da shirka, annabi Yusuf (a.s) yana fada a cikin wannan aya, yana cewa: Ku gwada tsakanin shirka da tauhidi ku gani. Mushrikai suna bautwa iyayengiji mabanbanta kuma kowanensu yana son ya sami yardarsa. Amma muminai su na bautar ubangiji ne guda daya tilo wanda shi ne mamallakin komai da komai. Shi ne mai iko akan kowane abu kuma yana da masaniya akan komai. Shin wannene ya fi tsakanin wadancan iyayengijin barkatai da kuma Ubangiji guda daya tilo? Ku yanke hukunci ku gani.
Mushrikai suna kirkirawa kowane abu ubangiji. Suna cewa ruwa yana da ubangiji. Iska tana da nata Ubangijin. Dukkanin wadannan iyayengijin a cikin kwakwalensu kadai su ke basu da samuwa ta hakika.
Ubangiji guda daya ne tilo wanda babu wani sai shi, kuma ya yi umarni da kada a bautawa wani sai shi.
Darussan da za mu koya daga wannan aya.
1-Daga cikin salon yin wa'azi akan akida da akwai yin tambayoyi da kuma katanci- wato kiyasi.
2-Wajibi ne akidodjin da mutum ya yi imani da su su ginu bisa kwararan dalilai ba kwaikwayo da riko da al'adu ba.
Karshenshirnmu na wannan lokacin kenan. Sai mun sake haduwa da ku acikin wani shirin domin ci gaba.
Suratu Yusuf, Aya Ta 41-43 (Kashi Na 380)
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na hannunka mai sanda shiri wanda yake yin dubi cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwar mu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin wannan shirin.
To bari mu fara shirimmu nay au da sauraron karatun aya ta 41 daga cikin suratu Yusuf kamar haka.
يَا صَاحِبَيِ السِّجْنِ أَمَّا أَحَدُكُمَا فَيَسْقِي رَبَّهُ خَمْراً وَأَمَّا الآخَرُ فَيُصْلَبُ فَتَأْكُلُ الطَّيْرُ مِن رَّأْسِهِ قُضِيَ الأَمْرُ الَّذِي فِيهِ تَسْتَفْتِيَانِ{41}
41-"Yã abõkaina biyu, na kurkuku! Amma dayanku, to, zai shãyar da uban gidansa giya, kuma gudan, to, zã a tsĩrẽ shi, sa'an nan tsuntsãye su ci daga kansa. An hukunta al'amarin, wanda a cikinsa kuke neman bayani ."
Annabi yusuf (a) ya fadawa abokansa na kurkuku cewa daga daga cikinsu za'a sake shi, kuma zai koma aikinsa na da, wato shayar da maigidansa giya kamar yadda ya saba. Amma dayan kuma za'a tsire shi a kashe shi sannan za'a bar gawarsa a waje har tsuntsaye su zo suna cin kansa. Kuma ya tabbatar masu cewa fassarar mafarkin nasu a yanke take babu komawa baya.
Amma annabi Yusuf (a) ya yi amfani da wannan damar inda ya kirasu zuwa ga kadaita Allah.
Wannan yana tabbatar mana cewa hatta waanda ba muminai ba suna iya yin mafarki wadanda suke tabbata gaskiya.
Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka.
1. Wasu daga cikin mafarkan da mutane suke yi, muminai ko kafirai suna zama gaskiya, duk da cewa fassarar wasu bai da dadi a wasu kuma mai kyau ne. Sannan Allah yakan sanar da wasu bayinsa fasarar mafarki. Har'ila yau mafarkan annabawa gaskiya ne kuma yana iya zama wani nau'I ne na wahayi. Kamar yadda ya faru da annabi Ibrahim.
2. Waliyyan Allah annabawa ba shashi fidi suke yi ba, a fassararsu ta mafarki, duk abinda suka fada gaskiya ne daga wajen Allah.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 42 daga cikin surar Yusuf kamar haka.
وَقَالَ لِلَّذِي ظَنَّ أَنَّهُ نَاجٍ مِّنْهُمَا اذْكُرْنِي عِندَ رَبِّكَ فَأَنسَاهُ الشَّيْطَانُ ذِكْرَ رَبِّهِ فَلَبِثَ فِي السِّجْنِ بِضْعَ سِنِينَ{42}
42-Kuma ya ce da wanda ya tabbatar da cẽwa shi mai kubuta ne daga gare su, "Ka ambacẽ ni a wurin uban gidanka." Sai Shaidan ya mantar da shi tunãtar da Ubangijinsa, sabõda haka ya zauna a cikin kurkuku 'yan shekaru.
A lokacin da annabi Yusuf (a) ya ga cewa wadannan mutanen biyu zasu fita daga kurkuku, sai ya fadawa wanda zai tsira daga cikinsu, cewa idan ka je wajen mai gidanka ka ambace ne, don an daure nib a tare da wani laifi ba, ina fata da haka zan kubuta daga gidan kaso. Sai dai shaitan ya mantar da wannan mutum wanda ya tsira ya fadawa mai gidansa Fir'auna dangane da labarin Annabi Yusuf (a) har sai bayan shekaru 7. Anan zamu ga cewa, Alqur'ani ya danganta mantuwa ga aikin shaitai, duk da cewa wani abu net a dab'a wanda ke iya faruwa da kowa, sai dai su waliyyan Allah basa mantuwa. Don shaidan baya iya kusantarsu.
Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka.
1. Mutum ya bukaci a bashi hakkinsa abu ne na dabi'a, kowa yana iya yin haka. Amma ga annabawa da waliyyan Allah da farko dole ne su yi tawakkali ga Allah cikin lamarinsu.
2. Shaitan ne yake tsarawa azzaluman shuwagabanni tsare masu gaskiya.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 43:
وَقَالَ الْمَلِكُ إِنِّي أَرَى سَبْعَ بَقَرَاتٍ سِمَانٍ يَأْكُلُهُنَّ سَبْعٌ عِجَافٌ وَسَبْعَ سُنبُلاَتٍ خُضْرٍ وَأُخَرَ يَابِسَاتٍ يَا أَيُّهَا الْمَلأُ أَفْتُونِي فِي رُؤْيَايَ إِن كُنتُمْ لِلرُّؤْيَا تَعْبُرُونَ{43}
43 - Kuma sarki ya ce: "Lalle ne, nã yi mafarki; nã ga shãnu bakwai mãsu kiba, wadansu bakwai rãmammu, sunã cin su, da zangarku bakwai kõre-kõre da wadansu kekasassu. Yã kũ jama'a! Ku yi mini fatawa a cikin mafarkĩna, idan kun kasance ga mafarki kunã fassarawa."
A cikin wannan surar da muce ciki, wato surar Yusuf, ya zuwa yanzu mun yi maganar mafarki guda ukku. Na farko shi ne shi annabi Yusuf (a) tun yana karami. Sai kuma mun karanta batun mafarkin da abkokan zaman gidan yari guda biyu na Yusuf (a). Sannan a wannan ayar da muka saurara a halin yanzu tana maganar mafarki na 4 wanda sarki ko kuma fir'auna na kasar Masar ya yi. Inda ya ga shanu 7 masu kiba, da kuma zangarnun alkama guda 7 korro. Sannan ya ga shanu 7 ramammu suna cinye masu kiba.
Sarki ya san cewa wannan mafarkin nasa masu muhimmanci ne, amma bai san fasararsu ba don haka ne ya damu da sannan fassararsu don kada kasarsa ta fada cikin hatsari.
1. A cikin famarki abubuwa da kuma dabbobi suna da fassaran da suka dace da su. Shanu ramammu a mafarki suna nune ga fari ne. A yayinda shanu masu kiba da kuma zangarnu suna ishara ga wadatar abinci.
2. Ba kowa ne yake iya fassarar mafarki ba. Don haka ilmin sanin fassarar mafarki baiwa ce daga Allah wanda yake yi ga bayinsa.
Masu sauraro mun zo karshen shirimmu na yau a nan zamu dasa aya sai kuam shi na gaba idan Allah ya kaimu. Wass.....
Suratu Yusuf, Aya Ta 44-49 (Kashi Na 381)
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na hannunka mai sanda shiri wanda yake yin dubi cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwar mu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin wannan shirin.
- .
To bari mu fara shirimmu nay au da sauraron karatun aya ta 44 da 45 daga cikin suratu Yusuf kamar haka.
قَالُواْ أَضْغَاثُ أَحْلاَمٍ وَمَا نَحْنُ بِتَأْوِيلِ الأَحْلاَمِ بِعَالِمِينَ{44} وَقَالَ الَّذِي نَجَا مِنْهُمَا وَادَّكَرَ بَعْدَ أُمَّةٍ أَنَاْ أُنَبِّئُكُم بِتَأْوِيلِهِ فَأَرْسِلُونِ{45}
44-Suka ce: "Yãye-yãyen mafarki ne, kuma ba mu zamo masana ga fassarar yãye-yãyen mafarki ba."
45- Kuma wannan da ya kubuta daga cikinsu ya ce: bãyan yã yi tunãni a lõkaci mai tsawo, "Nĩ, inã bã ku lãbãri game da fassararsa. Sai ku aike ni."
A cikin shirimmu da ya gabata mun yi maganar cewa, sarkin Masar ya yi mafarkin shanu 7 masu kiba wasu 7 ramammu suna cinyesu, wanda ya damu da sanin fassarar mafarkin.
Wadan nan ayoyi biyu suna bayyana cewa fadawa da kuma malaman da suka san fassarar mafarki sun kasa fassar su. Suna ganin mafarkin sarkin wani iri ne wanda bai da fassara, kuma bai da wani muhimmanci.
A lokacin ne wanda ya tsira daga cikin abokan annabi Yusuf(a) a kurkuku ya tuna da bukatar da annabi Yusuf (a) ya yi masa na ya ambace shi a wajen sarki.
Sannan ya tabbatar cewa annabi Yusuf(a) kamar yaddda ya fassara mafarkin fitarsu daga kurkuku da kuma makomar ko wannensu ta kuwa tabbas ya san fassar mafarkin sarki. Anan ne ya bukaci sarkin ya bashi damar ganawa da Yusuf (a) a cikin kurkuku don samun fassarar mafarkinsa.
A halin yanzu muna iya daukan darussa daga cikin wannan ayar kamar haka.
1. Ba bayin Allah ne kadai suke yin mafarki na gaskiya ba. Wasu mushrikai ko sarakuna ma suna iya yin mafarki kuma ya tabbata gaskiya ne.
2. Yana da kyau mu fahintar da mutane dangane da malamai masana don su amfana da su.
Yanzun kuma mu saurari karatun ayoyi na 46 da kuma 47 daga cikin surar Yusuf kamar haka.
يُوسُفُ أَيُّهَا الصِّدِّيقُ أَفْتِنَا فِي سَبْعِ بَقَرَاتٍ سِمَانٍ يَأْكُلُهُنَّ سَبْعٌ عِجَافٌ وَسَبْعِ سُنبُلاَتٍ خُضْرٍ وَأُخَرَ يَابِسَاتٍ لَّعَلِّي أَرْجِعُ إِلَى النَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَعْلَمُونَ{46} قَالَ تَزْرَعُونَ سَبْعَ سِنِينَ دَأَباً فَمَا حَصَدتُّمْ فَذَرُوهُ فِي سُنبُلِهِ إِلاَّ قَلِيلاً مِّمَّا تَأْكُلُونَ{47}
46-"Yã Yũsufu! Yã kai mai yawan gaskiya! Ka yi mana fatawa a cikin shãnu bakwai mãsu kiba, wadansu bakwai rãmammu sunã cin su, da zangarku bakwai kõrãye da wadansu kẽkasassu, tsammãnĩna in kõma ga mutãne, tsammãninsu zã su sani."
47-Ya ce: "Kunã shũka, shẽkara bakwai tutur, sa'an nan abin da kuka girbe, sai ku bar shi, a cikin zanganniyarsa, sai kadan daga abin da kuke ci."
A lokacin da wanda ya tsira daga gidan yari ya je gaban Yusuf (a) ya fada masa mafarkin sarki da kuma yadda masana da fadawa suka kasa fassara shi, annbi Yusuf (a) bai aibata shi da cewa me yasa baka tuna da ni ba bayan fitarka daga kukuku na tsawon shekaru 7 sai bayan bukatar fassarar mafarki ta tashi sannan ko zo mani. Ko kuma bai ce, idan na fassara mafarkin sarki, zai sallame ni daga gidan yari ne?. Bai yi duk wannan. Amma sai ya fassara masu mafarkin kuma ya fada masu mafita daga matsalar da take tattare da abinda mafarkin yake nufi, don ya zama mutane basu fada cikin wahalaba.
Daga cikin wadan nan ayoyi muna iya daukan darussa kamar haka.
Sannan a cikin aya an ambashi Yusuf (a) da cewa shi "Siddiki ne" wato mai gaskiya wanda maganganunsa suke tafiya dai dai tare da ayyukansa. Banda shi a cikin alkur'ani mai girma an ambashi annabi Ibrahim da kuma annabi Idrus a matsayin Siddikai.
Har ila yau a cikin ruwayoyi masu inganci manzun Allah (s) ya kira Aliyu Bin Abi Talib (a) a matsayin "siddiku"
Muna iya daukan darrussa a cikin wadannan ayoyi kamar haka.
1. Dole ne hukumomi su yi amfani da masana da kuma masu baiwa a cikin mutane don kaudamatsalolin al-umma.
2. Tanaji da kuma kula da harkokin tattalin arzikin mutane na daga cikin muhimman ayyukan ko wace hukuma ga al-ummarta.
3. Bayin Allah suna tunanin warware matsalolin al-ummarsu kafin su yi tunanin warware tasu matsalolin.
4. Tanaji da kuma tsara lamuran rayuwa bai sabawa iamni da kuma tawakkali ga Abangiji ba. Abinda ya dace shi ne mu tunkari kaddarar Ubangiji da dubaru ko kuma tanaje tanajemmu.
Yanzun kuma mu saurari karatun ayoyi na 48 da kuma 49 daga cikin surar Yusuf (a) kamar haka.
ثُمَّ يَأْتِي مِن بَعْدِ ذَلِكَ سَبْعٌ شِدَادٌ يَأْكُلْنَ مَا قَدَّمْتُمْ لَهُنَّ إِلاَّ قَلِيلاً مِّمَّا تُحْصِنُونَ{48} ثُمَّ يَأْتِي مِن بَعْدِ ذَلِكَ عَامٌ فِيهِ يُغَاثُ النَّاسُ وَفِيهِ يَعْصِرُونَ{49}
48-"Sa'an nan kuma wadansu bakwai mãsu tsanani su zo daga hãyan wancan, su cinye abin da kuka gabãtar dõminsu, fãce kadan daga abin da kuke ãdanãwa."
49- "Sa'an nan kuma wata shẽkara ta zo daga bãyan wancan, a cikinta ake yi wa mutãne ruwa mai albarka, kuma a cikinta suke mãtsar abin sha."
Annabi Yusuf (a) ya fassara mafarkin sarki kamar yadda yake.
Ya fassara mafarkin da cewa, za'a yi ruwan sama a kasar masar na tsawon shekaru 7 a jere, sannan ayi wasu shekaru 7 na fari suma a jere. Don haka ya bayya hanyar kubuta daga rashin abinci a cikin shekaru 7 na fari shi ne a yi amfani da daminar shekaru 7 na ruwan sama a yi noma abinda da za'a ci a cikin shekaru 7 na karancinsa. Bayan wadannan shekaru 7 na fari ruwan sama zai dawo kamar yadda aka saba. Mutane su safe komawa cikin ni'ama na samun yayan itace da albarkatun noma iri iri. Anan yana nufin a shekaru 7 wanda za'a yi ruwan sama, zasu kara yawan noma da suke yi su sami na wancan shekarun sannan su ijiye rara don shekarun tsanani 7 masu zuwa.
Daga cikin wadannan ayoyi muna iya daukan darussa kamar haka.
1. Ba bu lafi wajen ajiye abice bisa hasashen za'a fi bukatarsu nan gaba. Kuma ba za'a kira yin hakan "ihtikari " ne ba, wato boye abinci don takurawa mutanen sannan a sayar masu shi da tsada daga baya.
2. Hasashen yanayi na ruwan sama da iska, abu ne mai amfani, wanda ya zama lazimi a yi amfani da ilmin don kare mutanen daga fadawa cikin hatsari.
Masu sauraro da wannan kuma muka kawo karshen shirinmu na yau sai kuma wani shrin idan Allah ya kaimu a huta lafiya wassa....
Suratu Yusuf, Aya Ta 50-52 (Kashi Na 382)
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na hannunka mai sanda shiri wanda yake yin dubi cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwar mu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin wannan shirin.
To bari mu fara shirimmu na yau da sauraron karatun aya ta 50 daga cikin suratu Yusuf kamar haka.
وَقَالَ الْمَلِكُ ائْتُونِي بِهِ فَلَمَّا جَاءهُ الرَّسُولُ قَالَ ارْجِعْ إِلَى رَبِّكَ فَاسْأَلْهُ مَا بَالُ النِّسْوَةِ اللاَّتِي قَطَّعْنَ أَيْدِيَهُنَّ إِنَّ رَبِّي بِكَيْدِهِنَّ عَلِيمٌ{50}
50 - Kuma sarkin ya ce: "Ku zo mini da shi." To, a lõkacin da manzo ya je masa , ya ce: "Ka kõma zuwa ga uban gidanka, sa' an nan ka tambaye shi; Mẽnene hãlin mãtãyen nan wadanda suka yanyanke hannãyensu? Lalle ne Ubangijĩna ne Masani game da kaidinsu."
Kamar yadda muka bayyana a cikin shirimmu da ya gabata cewa, a lokacinda ma'aikin sarki ya zowa annabi Yususf (a) da sakon neman fassarar mafarki, ba tare da wata wata ba, sai ya fassara mafarkin sannan ya kara masu da bayanin yadda za'a fita daga matsalar fari wanda mafarkin yake nunawa.
Amma a wannan wannan ayar, a lokacinda dan sakon sarkon sarkin ya zo masa da neman ya fita daga gidan kukuku ya je gaban sarki, sai ya kafa sharuddi na fitarsa, don yana son ya tabbara da cewa an zalunce shi a lokacinda aka jefa shi cikin kurkuku.
Shi ne ya bukaci dan sakon da ya tambayi batun matan nan wadanda suka yayyanke hannunsu a lokacinda ya bayyana a gabansu. Sannan yana son ya tabbatar da tsarkinsa.
Don kuma ya tabbatarwa shi sarki cewa kasancewarsa a cikin kurkuku ba wai ya yi laifi bane. Don tsarkinsa ne ma ya shiga kurkukun. Wannan zai bashi matsayin da mutane zasu amince da shi su yarda da jagorancinsa. Kamar yadda ya zo a cikin wani hadisi inda manzon Allah (s) ya ke bayyan tsananin hakurin annabi Yusuf (a) ta yadda a lokacin da ake ce ya fassara mafarki bai nemi lada ba, amma a lokacinda aka ce ya fita daga kurkuku sai ya kafa sharadin fitarsa, wato sai an tabbatar da tsarkinsa kafin ya fita.
Daga cikin wannan ayar muna iya daukar darussa kamar haka.
1. Mahukunta dole ne su dauki shawarar masana da mutanen kirki, Ko da kuwa yan fursina ne.
2. Samun 'yenci ko ta kaka bai da amfani. Mutunci da kuma tabbatar da gaskiyarka ya fi muhimmanci a rayuwa.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 51 daga cikin surar Yusuf kamar haka.
قَالَ مَا خَطْبُكُنَّ إِذْ رَاوَدتُّنَّ يُوسُفَ عَن نَّفْسِهِ قُلْنَ حَاشَ لِلّهِ مَا عَلِمْنَا عَلَيْهِ مِن سُوءٍ قَالَتِ امْرَأَةُ الْعَزِيزِ الآنَ حَصْحَصَ الْحَقُّ أَنَاْ رَاوَدتُّهُ عَن نَّفْسِهِ وَإِنَّهُ لَمِنَ الصَّادِقِينَ{51}
51-Ya ce: "Mẽne ne babban al'amarinku, a lõkacin da kaka nẽmi Yũsufu daga kansa?" Suka ce: "Tsarki ga Allah yake! Ba mu san wani mummũnan aiki a kansaba." Mãtar Azĩz ta ce: "Yanzu fagaskiya ta bayyana. Nĩ ce nã nẽme shi daga kansa. Kuma lalle ne shĩ, hakĩka, yanã daga mãsu gaskiya.
Yana daga cikin sunnar Allah a cikin Alqur'anin mai girma, yana budewa mutane masu tsoronsa kofofin alkhairi da daukaka. Matar waziri na kasar Masar wacce ta tuhumi annbi yusuf(a) da kha'inci ya sannan ta yi hanyar daure shi a gidan yari ba tare da ya aikata wani lafi ba.
Sai ga shi a yau tana tabbatar da gaskiya da kuma tsarkin da annabi Yusuf (a) yake da shi daga dukkan abinda ta tuhumce shi da shi.
Wannan ya share fagen fitarsa daga gidan yari da daukaka da kuma tsarkinsa. Wannan shiri ne wanda Allah ta'ala ya yi wa annabi Yusuf (a), dole ne masu laifi su tabbatar da laifinsu kowa ya ganesu, masu tsarki kuma a sansu. Duk da cewa kaiwa ga wannan matsayin yana bukatar dauriya da hakuri mai yawa, amma shi yafi alkhairi.
1. Gaskiya ba zai ci gaba da muyuwa har abada ba, kamar yadda kariya kuma fure take bata yaya. Wata rana sai an gane ta.
2. Tsoron Allah da kuma kame kai daga fadawa cikin zunubin hulda da matan banza, wani hali ne mai kyau wanda har wadanda basa iya kamun kansu daga barin hakan suke alfahiri da shi.
Yanzu kuma mu saurari karatun aya ta 52 daga cikin surar Yusuf kamar haka.
ذَلِكَ لِيَعْلَمَ أَنِّي لَمْ أَخُنْهُ بِالْغَيْبِ وَأَنَّ اللّهَ لاَ يَهْدِي كَيْدَ الْخَائِنِينَ{52}
52 -"Wancan ne, dõmin ya san cẽwa lalle ne ni ban yaudareshi ba a bõye, kuma lalle Allah bã Ya shiryar da kaidin mayaudara."
Malaman tafsiri suna da ra'ayi daban daban dangan da wannan ayar. Wasu daga cikinsu suna ganin, wannan ayar zancen Zaliha'u ce matar wazirin masar, inda take nuni da cewa, ta bukaci aikata sabo, wanda kha'inci ne ga mijinta, amma hakan bai auku ba don matakan da annabi Yusuf (a) ya dauka don hana aukuwan hakan. Amma mafi yawan malaman tafsiri suna ganin cewa, annan yusuf (a) ne ya ke bayyana cewa, duk da cewa na shimfida sharadin fita ta daga gidan yari, tare da bayyana gaskiyan abinda ya faru tsakani na da Zaliha'u matar Wazirin Masar da kuma sauran kawayenta matan manya manyan mutane. Amma manufata ita ce, na wanke kaina daga aikata wani zunubi. Manufata ba daukan fansa kan Zulaikha matar waziri ba. A'a ina son na maita mutunci na ne a wajen wadanda suke da wata mummunan tunani a kai na.
Wani abin lura anan shi ne, yadda annabi Yusuf (a) ya danganta wannan bukatar ga kaddarar Allah don nunawa sarki cewa Allah ne yake dabbara kome yana sane da abinda yake boye da kuma a bayyane.
Muna iya daukan darussa daga cikin wannan ayar kamar haka.
1. Kha'inci ga wasu mummunan abu ne, ko da kuwa wadanda aka kha'intar ba musulmi bane.
2. Alamun imani na gaskiya shi ne nisantar sabon Allah a bayyana ne da boye.
3. Duk da cewa Allah ya san masu tsarki cikin mutane, amma baya amincewa masu sabo su zubar da mutuncin bayinsa salihai. Don haka ne sai ya yi masu hanyar da tsarkinsu zai bayyana.
Masu sauraro anan zamu dasa aya sai kuma wani shirin idan Allah ya kaimu a huta lafiya wassalamu alaikum warahamatullah. Wa barkatuhu.
Suratu Yusuf, Aya Ta 53-55 (Kashi Na 383)
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na hannunka mai sanda shiri wanda yake yin dubi a cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a garemu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirin.
To bari mu fara shirimmu na yau tare da sauraron karatun aya ta 53 daga cikin surar Yusuf kasar haka.
وَمَا أُبَرِّئُ نَفْسِي إِنَّ النَّفْسَ لأَمَّارَةٌ بِالسُّوءِ إِلاَّ مَا رَحِمَ رَبِّيَ إِنَّ رَبِّي غَفُورٌ رَّحِيمٌ{53}
53-"Kuma bã ni kubutar da kaina. Lalle ne rai, hakĩka, mai yawan umurni ne da mummũnan aiki ne, fãce abin da Ubangjina Ya yi na; rahama. Lalle Ubangjina Mai gãfara ne, Mai jin kai."
A cikin shirimmu da ya gabata mun yi magana dangane da yadda Annabi yusuf (a) ya sanya sharidin fitarsa daga kurkuku shi ne wanke shi daga zunudin da ake tuhumarsa da shi. Sannan munji yadda ita Zaliha'I matar Wazirin Masar ta tabbatar da tsarkin annabi Yusuf (a) a gaban sarki.
A cikin wannan ayar ya yi nuni ga wani abu mai muhimmanci dangane da son zuciyar mutum. Zuciyar dan adam a mafi yawan lokuta yana jansa zuwa ga sabo Allah ne, ko kuma zuwa ga aikata abinda ya sabawa hankali ko kuma fitira na halittar mutum ko kuma dai abinda ya sabawa tsarin zamantewan mutane.
Abinda yake iya kare mutum daga biyewa son zuciyarsa kawai shi ne rahamar Allah da ludufinsa. Wanda Allah ya yi masa rahama zai bashi Imani da kuma tsoronsa. Wadanda zasu taimake shi wajen kare kansa daga bin son zuciyarsa.
A cikin alqur'anin an kasa naf ko kuma zuciyar mutum kashi ukku, akwai wacce take da halaye irin na dabbobi wato na abinda ake kira sha'awar abinci mata da kuma bacci, babu hankali a cikin lamuranta kamar dai dabba to ita ce "naf al-ammara" mai yawan umurni da sabo.
Sai kuma –naf al-lawwama- wato mai rai mai zirgin kanta kan laifuffukan da yake aikatawa. Iran Wannan rai din tana share fage ne ga tuba da kuma komawa ga tafarkin Allah ga masu sabo, sai kuma idan mun kara sama akwai rai wacce ake kira –mutma'inna- wacce ta ke nutsatsiya. Wannan ita ce rai ko kuma ziciya irin ta annabawa da waliyyan Allah wadanda a shirye suke a ko yaushe kuma a cikin ko wani hali su fuskanci duk wata matsalar da zata bijiro masu a kan tafarkinsu na biyayya ga umurnin Allah. Ba sa tababa ko kadan a cikin dogaronsu da kuma amincewarsu ga hukuncin da alkawari da kuma wa'adin ubangijinsu.
A cikin wannan ayar duk da cewa annabi Yusuf (a) annabin Allah ne ma'asumi , amma don ya tawali'u yana cewa, ni ma ina rai irin na sauran mutane wacce take jansa zuwa ga sabon Allah amma Allah da rahamarsa da ludufinsa ya kiyayeni fadawa cikin sabonsa. Ya tsamar da ni daga fadawa cikin tarkon son zuciya.
Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka.
1. Kada ko da wasa mutum musulmi ya tsarkaken kansa, don matukar kana da rai to kuwa kana tattare da hatsarin fadawa cikin sabon Allah.
2. Duk da barazana da kuma hatsari da mutum yake ciki na yiyuwan ya fada cikin sabon Allah to kada ya dabe kauna daga samun rahamar Allah da jinkansa na gamawa da duniya lafiya.
Yanzun kuma bari mu saurari karatun aya ta 54 daga cikin surar Yusuf (a) kamar haka.
وَقَالَ الْمَلِكُ ائْتُونِي بِهِ أَسْتَخْلِصْهُ لِنَفْسِي فَلَمَّا كَلَّمَهُ قَالَ إِنَّكَ الْيَوْمَ لَدَيْنَا مِكِينٌ أَمِينٌ{54}
54-Kuma sarkin ya ce: "Ku zo mini da shi in kẽbe shi ga kaina." To, a lõkacin da Yũsufu ya yi masa magana sai ya ce: "Lalle ne kai a yau, a gunmu, mai daraja ne, amintacce."
Bayan da sarki ya ji abinda Zali'khau matar waziri ta fada na tabbatar da tsarkin annabi Yusuf (a) da kuma tabbatar da hakan da manya manayn makarrabansa suka yi sai ya aikewa Yusuf (a) da ya zo wajensa ya zama amininsa a cikin harkokin kasa.
Daga baya sarkin ya gano cewa Yusuf (a) mutum ne mai tsananin kwakwalwa da fahinta don haka ya kusantar da shi ya bashi lamuran shugabanci da kuma musamman babbam mai kula da ayyukan noma da kuma dukiyar kasa
Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka.
1. Ana bukatar mutane wadanda suke da tajruba a cikin aiki don su rike mukamai masu muhimmanci. Amma banda wannan rikon amana da gaskiya su ne yafi ko wannan muhimmanci.
2. Mutane masu gaskiya da rikon amana abin girmamawa ne a ko ina suke. Abin girmamawa ne, a bin mutuntawa ne a gaban sarakuna ko talakwa, a wajen muminai ko kafirai.
Yanzun kuma masu sauraro mu saurari karatun aya ta 55 daga cikin surra Yusuf (a) kamar haka.
قَالَ اجْعَلْنِي عَلَى خَزَآئِنِ الأَرْضِ إِنِّي حَفِيظٌ عَلِيمٌ{55}
55-Ya ce: "Ka sanya ni a kan taskõkin kasa. Lalle ne nĩ, mai tsarẽwa ne, kuma masani."
Bayan da sarki ya kusantar da annabi yusuf(a) a gareshi kuma ya sanya shi mai bashi shawara na musamman. Annabi yusuf (a) ya san ce wa dole ne a cikin shekaru 7 masu zuwa ayi noma a kuma ajiye rarar abinci bisa tsari da kuma yanayin da ya dace, sannan a cikin shekaru 7 masu tsananin da zasu zo daga baya dole ne a rarraba abincin da aka ajiye a cikin tsari don kada mutane su shiga cikin wahala. Don aiwatar da wannan aiki mai muhimanci sai ya cewa sarki ka sanyani mai kula da dukiyar kasa wato ma'aji. Manufarsa shi ne don ya aiwatar da wannan shirin a cikin tsarin da ya dace. Da sarki ya amince, sai ya aiwatar da shirin nan na ajiye rarar abincin da suka noma na ko wace shekara har zuwa shekaru 7, sannan aka shiga shekaru 7 masu tsanani wadanda a cikinsu ya jagoranci rabon abinci wanda suke ajiye don lokacin a cikin tsari.
Kamar yadda ya zo cikin wasu hadisai, bayan da kamas masar ta tsallaka lokaci mai tsanani na tsawon shekaru 7, annbi yusuf (a) ya cewa sarki duk abinda yake a hannuna na dukiyar jama'a na maida su gareka, don na karbi iko ne don ganin na iawatar da shirin nan na tsamar da mutane daga fari da kuma rashin abinci. Muna iya daukan darussa daga cikin wannan ayar kamar haka.
1. Wanda yake da iyawa da kuma korewa a wani aiki dole ne ya bayyana kansa don yin khidima ga al-umma.
2. A cikin zaben ma'aikata bai kamata shugaba ya kawo batun kabilanci ko launin fata ko yankasanci ba. Annabi Yusuf(s) ba dan kasar Masar ba ne, bilhasalima ya shiga kasar a matsayin bawa, amma sarkin masar ya bashi matsayi mafi muhimanci a kasar don cancantarsa.
Masu sauraro anan kuma zamu dasa a ya sai kuma shiri na gaba idan Allah ya kaimu a huta lafiya wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.
Suratu Yusuf, Aya Ta 56-60 (Kashi Na 384)
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na hannunka mai sanda shiri wanda yake yin dubi a cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a garemu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirin.
To bari mu fara shirimmu na yau tare da sauraron karatun aya ta 56 da kuma 57 daga cikin surar Yusuf kamar haka.
وَكَذَلِكَ مَكَّنِّا لِيُوسُفَ فِي الأَرْضِ يَتَبَوَّأُ مِنْهَا حَيْثُ يَشَاءُ نُصِيبُ بِرَحْمَتِنَا مَن نَّشَاء وَلاَ نُضِيعُ أَجْرَ الْمُحْسِنِينَ{56} وَلَأَجْرُ الآخِرَةِ خَيْرٌ لِّلَّذِينَ آمَنُواْ وَكَانُواْ يَتَّقُونَ{57}
56-Kuma kamar wancan ne Muka bãyar da ĩko ga Yũsufu a cikin kasa yanã sauka a inda duk yake so. Munã bawa rahamarMu ga wanda Muke, kuma bã Mu tõzartar da lãdar mãsu kyautatawa. 57-Kuma lalle lãdar Lãhira ce mafi alheri ga wadanda suka yi ĩmãni, kuma suka kasance mãsu takawa.
A cikin shirim da ya gabata ayoyin sun bayyana yadda sarki ya kusantar da annbi Yusuf (a) ya bashi matsayi mai girma a kasar Masar. Wadannan ayoyi suna bayyana cewa Allah ne yake nufin annabi Yusuf (a) da rahamarsa. Ya bashi iko da daukana yana zagayawa inda ya so ko ga dama. Ammafa tana tunatarwa wannan rahama ta duniya ce, ta lahiri ta fi alkhairi nesa ba kusa ba.
Sunnan Allah ce yakan sakawa masu ayyuka na gari tun a rayuwarsu ta duniya, sannan ladarsu ta lahira kuma tana nan an kiyaye masu ita kuma tafi na duniya nesa ba kusa ba. Amma fad a shiradin imani da tsoron Allah. Ayyuka na alkhairi basa da lada a lahira in babu imani.
Muna iya daukan darasi kamar haka daga cikin wadan nan ayoyi.
1. Sunnar Allah ce yana daukaka mutane masu tsarkin zuciya da tsoronsa, ko da kuwa azzaluman shuwagabannin basa so.
2. A cikin tsarin Allah duk wani aiki na alkhairi yana da sakamako. Don haka masu ayyukan alkhairi kasu su damu. Mai yuwa Allah ya fara basu ladansu tun a duniya.
3. Ladar Allah a lahiri ta fit a duniya nesa ba kusa ba. Don shi bai na nakasa ko tawaya ko kuma karewa. Ladar ta fi karfin mutum ya sawwara shi.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 58 daga cikin surar Yusuf (a) kamar haka.
وَجَاء إِخْوَةُ يُوسُفَ فَدَخَلُواْ عَلَيْهِ فَعَرَفَهُمْ وَهُمْ لَهُ مُنكِرُونَ{58}
58-Kuma 'yan'uwan Yũsufu suka jẽ, sa'an nan suka shiga a gare shi, sai ya gãne su, alhãli kuwa su, sunã mãsu musunsa.
A bisa has ashen da annabi Yusus (a) ya yi – wanda Allah ne ya sanar da shi-za'a yi rowan sama na shekaru 7 sannan shekaru 7 na biyu kuma za'a yi fari. Don haka wannan has ashen ya tabbata. A lokacinda aka fara shekarun fari, rashin rowan sama ya mamaye kasar masar da Palasdinu da kuma kan'ana. Don haka annabi Ya'kub (a) ya aiki yayansa zuwa kasar masar don yin awon abinci. Yayansa sun isa kasar Masar kamar dukkan mutanen yankin suka je gaban ma'ajin dukiyar kasar –wanda ba kowa ba in banda dan uwansu annabi yusuf (a). Shi ya gane su amma su basu gane shi ba. Sannan baya cikin tunaninsu cewa dan uwansu Yusuf (a) yana raye ma, ballantana a ce shi ne mai babbam mukami na ma'ajin dukiyar kasar masar. Don haka annabi Yusuf (a) bai nuna masu cewa ya ganesu ba, ya yi mu'amala da su kamar sauran mutane. Ya bada umurnin a yi masu awo kamar yadda tsarina won yake ga kowa.
Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka.
1. Mutum mai imani yakan tallafawa mabuka musamman a lokacin mai tsanani irin na fari, ko da kuwa ba dan kasarsu ko kabilarsu ba.
2. A cikin lokuta masu tsanani dole ne a daidaita mutane cikin arziki ko tallafin da ake da shi a hannu ba tare da nuna wani bambanci ba.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 59 da kuma ta 60 daga cikin surar Yusuf (a) kamar haka.
وَلَمَّا جَهَّزَهُم بِجَهَازِهِمْ قَالَ ائْتُونِي بِأَخٍ لَّكُم مِّنْ أَبِيكُمْ أَلاَ تَرَوْنَ أَنِّي أُوفِي الْكَيْلَ وَأَنَاْ خَيْرُ الْمُنزِلِينَ{59} فَإِن لَّمْ تَأْتُونِي بِهِ فَلاَ كَيْلَ لَكُمْ عِندِي وَلاَ تَقْرَبُونِ{60}
59-Kuma a lõkacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, ya ce: "Ku zo mini da wani dan'uwa nãku daga ubanku. Ba ku gani ba cẽwa lalle ne nĩ, inã cika ma'auni, kuma nĩ ne mafi alhẽrin mãsu saukarwa?"
60-"Sa'an nan idan ba ku zo mini da shĩ ba, to, bãbu awoa gare ku a wurĩna, kuma kada ku,kasance ni."
Kamar yada ya zo cikin wasu hadisai da kuma littafan tarihi, a dai dai lokacinda yan uwan annabi yusuf (a) suke karban rabonsu na abinci (alkama) sai suka fadawa annabi Yusuf (a) –wanda dama yake sa ido a kan rabon abincin da kansa- cewa suna da wani dan uwa wanda suke hada uba, amma basu zo das hi ba don yana kula da mahaifinsu wanda ya kasance tsoho ne. Anan sai Yusuf(a) ya ce masu, to a wannan karon zan baku rabonsa da kuma rabon mahaifinku na abinci, amma idan kun sake tahowa dole ku zo da shi kafin ya sami rabonsa. Idan baku zo das hi ba, to fa hatta ku da kanku bazaku sami rabon ku ba.
Wannan ayar tana nuna mana cewa Annabi Yusuf (a) da kansa yake kula da rabon abinci don ganin ko me ya tafi dai dai. Ba umurni ne yak e bayarwa kawai a aiwatarba.
Daga cikin wadannan ayoyi muna iya daukan darussa kamar haka.
1. A lokacinda ake fuskatar matsaloli a cikin kasa, bai dace mai iko ya yi amfani da ikonsa don daukar fansa a kan cutarwa da aka yi masa a baya ba. Kamar dai yadda annabi Yusuf (a) ya yi a lokacinda yan uwansa wadanda suka cutar das hi suka zo masa kaskantattu suna neman abinci a hannunsa. Wannan kuma shi ne halayen annabawan Allah, da bayinsa salihai.
2. A lokacin rabon wani abo a cikin dangi ko makusanta bai kamata a nuna fifiko a cikinsu ba.
3. Dokokin da ka tsara na gudanar da al'amuran kasa dole ne a kiyayesu kamar yadda suka. Tausayi da so kada su hana aiwatar das u kamar yadda suke.
Musu sauraro anan yakamata mu dasa aya sai kuma wani lokaci idan Allah ya kaimu a huta lafiya wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Suratu Yusuf, Aya Ta 61-65 (Kashi Na 385)
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na hannunka mai sanda shiri wanda yake yin dubi a cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a garemu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirin.
To bari mu fara shirimmu na yau tare da sauraron karatun aya ta 61 daga cikin surar Yusuf kasar haka.
قَالُواْ سَنُرَاوِدُ عَنْهُ أَبَاهُ وَإِنَّا لَفَاعِلُونَ{61}
61-Suka ce: "Zã mu neme shi daga ubansa. Kuma lalle ne mũ, hakĩka, mãsu aikatãwa ne."
Kamar yadda kuka ji a cikin shirimmu da ya gabata, yan uwan annabi Yusuf(a) sun fada masa cewa suna da wani danuwa karami wanda suke hada uba das hi amma sun barshi a gida yana kula da mahifinsu tsoho. Sun roki annabi Yusuf (a) da ya sayar masu da rabunsu na abincin. Annabi Yusuf(a) ya amince, amma y ace da su idan zasu sake zuwa to su zo das hi, idan bah aka ba, to ba za su sami rabon shi ba hakama su ma bazasu sami rabnsuba.
A cikin wannan ayar sun yi alkwalin zasu zo das hi duk da cewa mahaifinsu baya son rabuwa das hi, zasu yi matukar kokarin ganin sun zo da shi.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 62 daga cikin surar Yusuf (a) kamar haka.
وَقَالَ لِفِتْيَانِهِ اجْعَلُواْ بِضَاعَتَهُمْ فِي رِحَالِهِمْ لَعَلَّهُمْ يَعْرِفُونَهَا إِذَا انقَلَبُواْ إِلَى أَهْلِهِمْ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ{62}
62-Kuma ya ce wa yaransa, "Ku sanya hajjarsu a cikin kãyansu, tsammãninsu sunã gãne ta idan sun jũya zuwa ga mutãnensu, tsammã ninsu, zã su kõmo."
Don ya tabbatar da cewa yan uwansa sun sake dawowa kasar masar, annabi yusuf(a) ya bada umurnin a mayar masu da kudaden da suka bayar na sayan alkama a cikin kayansu ba tare das u san sani ba. Ya yi haka ne don kada rashin kudi da wahalhalun rayuwa su hanasu dawowa. Sannan zamu dauki cewa annabi Yusuf (a) ya mayarwa yan uwansa dukiyarsu ne da aljihubsa, don sanin cewa bai kamata a yi amfani da dukiyar kasa ko dukiyar jama'a don kebance wasu da kyauta ba.
Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka .
1. Sada zumunci shi ne mutum ya kyautatwa yan uwansa na jinni wadansu suke munana masa, musamman a lokacinda suke bukatar taimakonsa. Kada ya kullasu a zuciyarsa. Kada kuma ya nemi daukan fansa a kansu. 2. Dole ne mu dauki darasi a cikin dattakun da annabi yusuf (a) ya nunawa yan uwansa wadansa suka cutar das hi matuka. Inda ba wai kawai bai hanasu sayan alkama a lokacinda suke matukan bukatansa sa ba, a'a sai ma ya mayar masu da kudaden da suka bayar na sayan alkamar daga cikin aljihunsa.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ya 63 da kuma ta 64 daga cikin surar Yusuf (a) kamar haka.
فَلَمَّا رَجِعُوا إِلَى أَبِيهِمْ قَالُواْ يَا أَبَانَا مُنِعَ مِنَّا الْكَيْلُ فَأَرْسِلْ مَعَنَا أَخَانَا نَكْتَلْ وَإِنَّا لَهُ لَحَافِظُونَ{63} قَالَ هَلْ آمَنُكُمْ عَلَيْهِ إِلاَّ كَمَا أَمِنتُكُمْ عَلَى أَخِيهِ مِن قَبْلُ فَاللّهُ خَيْرٌ حَافِظاً وَهُوَ أَرْحَمُ الرَّاحِمِينَ{64}
63-To, a lõkacin da suka kõma zuwa ga ubansu, suka ce: "Yã bãbanmu! An hana mu awo sai ka aika dan'uwanmu tãre da mu. Zã mu yi awo. Kuma lalle ne, hakĩka mũ, mãsu lũra da Shi ne."
64-Ya ce: "Ashe, zã ni amince muku a kansa? Fãce dai kamar yadda na amince muku a kan dan'uwansa daga gabãni, sai dai Allah ne Mafĩfĩcin mãsu tsari, kuma Shĩ ne Mafi rahamar mãsu rahama."
Bayan koma Kan'ana warin mahaifinsu annabi Yakub (a), sun nema shi da ya barsu su tafi da bilyaminu kadan annabi (a) zuwa kasar masar idan zasu sake yi wata tafiyar don ga abinda azizu misra – wato annabi yusuf (a) ya fada masu-. Amma mahaifinsu wanda ko da kadanne bai taba manta da Yusuf(a) ba, yana sane da yadda suka raba bashi da shi, amma kuma bai da zabi don suna bukatar abinci. Don haka sai ya yi tawakkali ga Allah ya amince ya hada su da bilyaminu don su sake komawa kasar Masar su dauko masu abinci.
Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka.
1. A cikin hali da yanayi mai tsanani kamar fari, babu mafita in banda tawakkali ga Allah ta'ala a cikin lamura.
2. Bayan cutarwa mai tsanani da aka yi maka, ba zai yu mutum ya kebe kansa ya manta da sauran bangarorin rayuwa ba. Dole ne ka koma cikin rayuwa kamar sauran mutane.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 65 da ga cikin sura ta yusuf (a) kamar haka.
وَلَمَّا فَتَحُواْ مَتَاعَهُمْ وَجَدُواْ بِضَاعَتَهُمْ رُدَّتْ إِلَيْهِمْ قَالُواْ يَا أَبَانَا مَا نَبْغِي هَـذِهِ بِضَاعَتُنَا رُدَّتْ إِلَيْنَا وَنَمِيرُ أَهْلَنَا وَنَحْفَظُ أَخَانَا وَنَزْدَادُ كَيْلَ بَعِيرٍ ذَلِكَ كَيْلٌ يَسِيرٌ{65}
65-Kuma a lõkacin da suka bũde kãyansu, suka sãmi hajjarsu an mayar musu da ita, suka ce: "Yã bãbanmu! Ba mu zãlunci! Wannan hajjarmu ce an mayar mana da ita, kuma mu nẽmo wa iyalinmu abinci, kuma mu kiyãye dan'uwanmu, kuma mu kãra awon kãyan rãkumi guda, wancan awo ne mai sauki."
Bayan sun bude kayakinsu sai sun gano cewa an maido masu da kudadensu gaba daya, sai suka cewa mahaifin nasu shin kuma me ya rage? Ga shi an maido mana kudademmu, don haka zamu kula da kanimmu mu je mu karo abinci a yanzun kam ma har da Karin rakumi guda wanda shi bilyaminu zai hau.
Annabi yusuf (a) ya karbi kudin da suka bayar na sayan hatsi wanda ba wani abu ne a wajensa ba, amma da ya ki karban kudin tun lokacin, na farko zasu yi shakkansa da biyu kuma kamar kaskanci ne a garesu ganin cewa su matalauta ne mutanen kauye. Amma sai ya mayar masu ba tare da sun sani ba, kuma ba tare da sun sami dammar gode masa ba. Dama ayyukan na alkhairi ga wani ya fi dacewa a boye ba tare da gori ba.
Sanna su yan uwana annabi Yusuf (a) basu su san wa ya mayar masu da kudadensu ba, don haka ne suka ce an mayar mana da kudademmu.
Muna iya daukan darussa daga cikin wannan ayar kamar haka.
1. Wajibi kan mutum ya dauki nauyin iyalansa da kuma iyayensa wadan da suka tsufa.
2. Rabon abinci dai dai tsakanin mutsne a lokacin tsanani yana da cikin adalci, wanda annabwa suka tafi a kai musamman shi annabi yusuf (a).
Masu sauraro anan kuma zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wani shirin idan Allah ya kaimu a huta lafiya wassalamu alaikum warahmatulli wa barakatuhu.
Suratu Yusuf, Aya Ta 66-68 (Kashi Na 386)
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.
A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 66 da ke cikin suratu-Yusuf kamar haka:-
قَالَ لَنْ أُرْسِلَهُ مَعَكُمْ حَتَّى تُؤْتُونِ مَوْثِقاً مِّنَ اللّهِ لَتَأْتُنَّنِي بِهِ إِلاَّ أَن يُحَاطَ بِكُمْ فَلَمَّا آتَوْهُ مَوْثِقَهُمْ قَالَ اللّهُ عَلَى مَا نَقُولُ وَكِيلٌ{66}
"{Annabi Yakubu} Ya ce: "Bã zan tura ku tare da shi ba, har sai kun yi mini alkawari tsakaninku da Allah lalle za ku dawo mini da shi, sai dai idan abin ya fi karfinku." To a lõkacin da suka yi mãsa alkawari, sai ya ce: Allah ne shaida a kan abin da muke fada."
A shirinmu da ya gabata mun bayyana cewa: 'ya'yayen Annabi Yakubu sun zauna suna jiran karamin dan uwansu ne Benyamin kan su tafi tare da shi zuwa kasar Masar domin sayo alkama karo na biyu, amma kasancewar Benyamin kamar dan uwansa Yusuf ne 'yan uwansa suna masa hasada, hakan ya sanya mahaifinsu Annabi Yakubu baya son hada su da Benyami, to sai dai babu makawa sai ya bar Benyamin ya tafi tare da su domin amsar na shi rabon na alkama, don haka Annabi Yakubu ya bukaci sauran 'ya'yayensa da su yi rantsuwa tare da daukan alkawarin zasu kare Benyamin kuma su tabbata sun dawo masa da shi cikin koshin lafiya, sai dai abin da yafi karfinsu. Bayan 'ya'yayen Annabi Yakubu sun yi rantsuwar kare dan uwansu, sai mahaifinsu ke bayyana musu cewa; kada ku taba tsammanin rantsuwar da kuka yi ta fatar baki ne kawai, lalle Allah zai kama ku matukar kuka saba alkawari, saboda Allah mai kiyaye duk abin da bayinsa ke aikatawa ne.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Lalle kulla yarjejeniya da daukan alkwari domin samun tabbaci kan al'amari yana da asali a cikin kur'ani, kuma yana da kyau musulmi su dinga kulla yarjejeniya koda a tsakanin makusantansu ne kan al'amuransu na yau da kullum da na zamantakewa, kuma mafi karancin yarjejeniyar da zasu kulla shi ne daukan alkawari.
{2} Mutane su kula wajen kare dokoki da hakkoki, kuma kada su kuskura su gafala da dogaro da Allah kan al'amuransu.
Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 67 da ke cikin suratu-Yusuf kamar haka:-
وَقَالَ يَا بَنِيَّ لاَ تَدْخُلُواْ مِن بَابٍ وَاحِدٍ وَادْخُلُواْ مِنْ أَبْوَابٍ مُّتَفَرِّقَةٍ وَمَا أُغْنِي عَنكُم مِّنَ اللّهِ مِن شَيْءٍ إِنِ الْحُكْمُ إِلاَّ لِلّهِ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَعَلَيْهِ فَلْيَتَوَكَّلِ الْمُتَوَكِّلُونَ{67}
"Kuma ya ce: "Yã ku 'ya'yayena, kada ku shiga {Masar} ta ƙõfa guda, ku shiga ta ƙõfõfi daban-daban, kuma bã zan kare muku kõmai daga Allah ba. Bãbu hukunci sai na Allah, a gare Shi na dõgara, kuma a gare Shi sai mãsu dõgaro su dõgara."
A lokacin da 'ya'yan Annabi Yakubu suka shirya tafiya kasar Masar; Annabi Yakubu ya musu umurni da wasu al'amura, daga ciki akwai batun cewa idan suka isa Masar kada su shiga cikin kasar gaba da yansu cikin tawaga guda, saboda hakan zai janyo hankulan mutane tare da munanta zato kansu. Annabi Yakubu yana ce musu; ku shiga cikin Masar a rarrabe saboda da kaucewa matsalar jan hankalin mutane, sannan Annabi Yakubu ya tunasar da su cewa: Umurnin da ya yi musu baya nufin umurni ne na Allah da ya hukunta a kansu da zai canja wani al'amari.
Wannan ayar tana nuni da cewa: Nufin Allah da hukuncinsa shi ne sama da komai a wannan duniya, kuma babu wani abu da zai iya canza shi, amma Allah ya ba mu damar tsara al'amuranmu gwargwadon fahimtarmu da saninmu, sai dai kuma duk abin da zamu gudanar mu kasance mun dogara da Allah domin shi ne mai hukunta komai.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Dole ne zurfafa tunani da tsara al'amura, amma hakan baya nufi lalle abin da muka tsara tabbas shi ne kawai zai wakana, iyaka dai sai abin da Allah ya so kawai zai kasance. {2} Da Allah kawai zamu dogaro saboda shi ne kadai mamallakin dukkan komai kuma mai azurtawa, don haka shi ne mafi alherin abin dogaro.
Yanzu kuma zamu saurari aya ta 68 da ke cikin suratu-Yusuf kamar haka:-
وَلَمَّا دَخَلُواْ مِنْ حَيْثُ أَمَرَهُمْ أَبُوهُم مَّا كَانَ يُغْنِي عَنْهُم مِّنَ اللّهِ مِن شَيْءٍ إِلاَّ حَاجَةً فِي نَفْسِ يَعْقُوبَ قَضَاهَا وَإِنَّهُ لَذُو عِلْمٍ لِّمَا عَلَّمْنَاهُ وَلَـكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لاَ يَعْلَمُونَ{68}
"Kuma a lõkacin da suka shiga daga inda mahaifinsu ya umurce su, {wannan} bai magance musu komai ba daga Allah, fãce dai wata bukata ce a zuciyar Yãkũbu da ya samu biyanta. Kuma hakĩka mai ilimi ne da muka sanar da shi, sai dai mafi yawan mutãne ba su sani ba".
Wannan aya tana kara jaddada cewa ne umurnin Annabi Yakubu da tsarin da 'ya'yayensa suka gudanar ba zasu iya canza nufin Allah ba, iyaka dai sun aiwatar da bukatar da mahaifinsu yake so, kuma hakan zai kwantar masa da hankali saboda sun yi aiki da umurninsa.
Ayar ta ci gaba da bayyana cewa: Wannan umurni na Annabi yakubu, haka nan sauran umurnin Annabawa sun samo asali ne daga wajen Allah, saboda shi ne ke sanar da su, ba wai ra'ayi ne da suke kirkirowa bisa radin kansu ba. Hakika Annabawa suna tarbiyantar da mutane ne domin Allah ne ke sanar da su duk abin da suke fada da aikatawa, sakamakon haka suna da bambanci da sauran mutane a wannan bangaren.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Addu'a da bukatun bayin Allah karbabbu ne a wajen Ubangiji, saboda ba su neman wani abu da ya sabawa 'yardan Allah.
{2} Mafi yawan mutane suna kallon dalilan faruwan al'amura na zahiri ne, amma sun gafala daga dalilai na badini da nufin Ubangiji.
To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.
Suratu Yusuf, Aya Ta 69-73 (Kashi Na 387)
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.
A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 69 da ke cikin suratu-Yusuf kamar haka:-
وَلَمَّا دَخَلُواْ عَلَى يُوسُفَ آوَى إِلَيْهِ أَخَاهُ قَالَ إِنِّي أَنَاْ أَخُوكَ فَلاَ تَبْتَئِسْ بِمَا كَانُواْ يَعْمَلُونَ{69}
"Kuma a lõkacin da suka shiga wajen Yũsufu sai ya janyo dan'uwansa zuwa gare shi, ya ce: "Lalle nĩ ne dan'uwanka, sabõda haka kada ka yi bakin ciki da abin da suka kasance sunã aikatãwa."
A shirin da ya gabata mun bayyana cewa; A karshen lamari dai Annabi yakubu ya amince Benyamin ya bi sauran 'yan uwansa zuwa kasar Masar domin karbo na shi rabon daga alkamar da ake sayarwa.
Wannan ayar kuma tana bayyana cewa ne: A lokacin da 'ya'yayen Annabi Yakubu suka shiga wajen Annabi Yusuf, Annabi Yusuf ya yi kokari ya yi magana da Benyamin a kebance, inda ya sanar da Benyamin ko shi wane ne, lamarin da ya yi sanadiyyar gushewar bakin ciki da damuwa daga zuciyar Benyamin, lalle dole ne Benyamin ya kasance cikin fargaba dangane da dabi'un 'yan uwansa tare da tsoron kada su aikata masa abin da suka yi ga dan uwansa Yusuf na raba shi da mahaifinsa. Yusuf ya samu ya shawo kan dan uwansa Benyamin kan ya zauna tare da shi, kuma Benyamin ya amince da wannan bukata ta Annabi Yusuf.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Yin karya bai halatta ba, amma kuma ba dole ba ne sai an fayyace hakikanin gaskiyar lamari a kowane lokaci, saboda Annabi Yusuf baya ganin lokaci ya yi da zai bayyana kansa ga sauran 'yan uwansa, don haka ya kebance daya daga cikinsu ya sanar da shi hakikaninsa. {2} A duk lokacin da muka shiga cikin farin ciki da ni'ima, to kamata ya yi mu mance da duk wani bakin ciki da damuwa, saboda haka a lokacin da Yusuf da Benyamin suka ga junansu, sai suka mance duk wani bakin cikin da suka sshiga a baya.
Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta70 da ke cikin suratu-Yusuf kamar haka:-
فَلَمَّا جَهَّزَهُم بِجَهَازِهِمْ جَعَلَ السِّقَايَةَ فِي رَحْلِ أَخِيهِ ثُمَّ أَذَّنَ مُؤَذِّنٌ أَيَّتُهَا الْعِيرُ إِنَّكُمْ لَسَارِقُونَ{70}
"Sannan a lõkacin da ya hada musu kayayyakinsu sai ya sanya ma'auni a cikin kãyan dan'uwansa, sannan kuma mai shela ya yi yẽkuwa da cewa;" Yã kũ wadannan ãyari lalle hakĩka kũ barãyi ne."
Annabi Yusuf ya so Benyamin ya zauna a wajensa saboda hakan ya zame sanadiyyar da 'yan uwansa zasu kwaso sauran iyalansu da mahaifinsu zuwa kasar Masar a tafiyarsu ta gaba, don haka ya gabatar da shawara ga Benyamin kan shirin da ya yi na ganin ya zauna tare da shi. A baya Annabi Yusuf ya mayarwa 'yan uwansa kudin da suka sayi alkama da shi ta hanyar sanya kudin a cikin kayansu, lamarin da ya yi sanadiyyar sake dawowansu kasar Masar.
A wannan karon kuma sai Annabi Yusuf ya shirya sanya mudu mai kima da yake amfani da shi wajen gudanar da awu a cikin kayan Benyamin, kuma Annabi Yusuf bai sanar da ma'aikatansa wannan shiri na shi ba, don haka a bisa dabi'a sai suka zargi ayarin mutanen da suka zo awu Masar da cewa sun saci mudu, kuma suka dauki matakin gudanar da bincike a kayayyakin da rakumansu suke dauke da su.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Shirya dabarar kai wa ga masalaha madaukakiya ta halatta, amma da sharadin hakan ba zai kai ga zaluntar wani ba, kuma mutumin da za a shirya ma'amalar da shi ya kasance yana da masaniya. {2} Dole ne sanya ido da kula kan abokan tafiya da wadanda ake zama tare da su, saboda samun mutum guda a tsakani da ke da mummunar dabi'a zai sanya a zargi sauran da wannan dabi'ar.
Yanzu kuma zamu saurari aya ta 71 zuwa 72 da suke cikin suratu-Yusuf kamar haka:-
قَالُواْ وَأَقْبَلُواْ عَلَيْهِم مَّاذَا تَفْقِدُونَ{71} قَالُواْ نَفْقِدُ صُوَاعَ الْمَلِكِ وَلِمَن جَاء بِهِ حِمْلُ بَعِيرٍ وَأَنَاْ بِهِ زَعِيمٌ{72}
"Suka ce: {yayin da } suka fuskance su: "Mẽne ne ya bace muku kuke nẽma?" Suka ce: "Munã nẽman ma'aunin sarki ne. Kuma duk wanda ya zo da shi yanã da ladan kãyan rãkumi guda, kuma ni ne lãmuni game da shi."
Bayan jami'an gwamnati sun fahimci cewa mudun da suke gudanar da awun alkama da shi ya bace, sai suka fara gudanar da bincike kayayyakin ayarin mutane, kuma suka fara da ayarin 'yan uwan Annabi Yusuf. Sannan Annabi Yusuf ya kara karfafa musu gwiwa da cewa duk wanda ya samo wannan mudun zai ba shi kyautar alkamar da rakumi zai iya dauka.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Sanya kyauta domin kwadaitar da jama'a kan wani aiki mai muhimmanci al'amari ne mai kyau da Allah ya yarda da shi, kuma sunna ce ta Annabawa.
{2} Kyautar da za a gabatar ta kasance irin wanda ake bukata ce a zamanin da za a gabatar da wannan kyautar, ba wai a gabatar da kyauta da ba ta da amfani ba. A lokacin fari mafi kyaun kyauta shi ne kayan alkama.
Yanzu kuma zamu saurari aya ta 73 da ke cikin suratu-Yusuf kamar haka:-
قَالُواْ تَاللّهِ لَقَدْ عَلِمْتُم مَّا جِئْنَا لِنُفْسِدَ فِي الأَرْضِ وَمَا كُنَّا سَارِقِينَ{73}
"Suka ce: "Wallahi hakĩka kun sani ba mu zo don mu yi barna a bayan kasa ba, kuma ba mu kasance barãyi ba."
A lokacin da 'yan uwan Annabi Yusuf suka fahimci su ake zargi da sace mudun, sai suka dauki matakin kare kansu da cewa: Kuna da masaniyar kafin wannan lokaci mun zo kasarku, kuma ba mu aikata wani abu da ya saba doka ba ballantana mu saci wani abu, to don mene ne a wannan lokaci zaku mana wannan zargi? Hakika kuna da masaniyar ba zamu taba aikata wannan laifi ba.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Sanin mutum da kyakkyawar dabi'a yana sanyawa a masa kyakkyawan zato, matukar babu wani kwakkwaran dalili da zai sanya a masa mummunan zato.
{2} Sata daya ce daga cikin ayyukan barna a kasa, kuma dabi'a ce da ke zubar da mutuncin mutum.
To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.
Suratu Yusuf, Aya Ta 74-77 (Kashi Na 388)
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.
A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 74 zuwa 75 da suke cikin suratu-Yusuf kamar haka:-
قَالُواْ فَمَا جَزَآؤُهُ إِن كُنتُمْ كَاذِبِينَ{74} قَالُواْ جَزَآؤُهُ مَن وُجِدَ فِي رَحْلِهِ فَهُوَ جَزَاؤُهُ كَذَلِكَ نَجْزِي الظَّالِمِينَ{75}
"{Jami'an Sarki} Suka ce: "To mẽne ne sakamakonsa idan kun kasance makaryata?" {Yan uwan Yusuf} Suka ce: "Sakamakonsa wanda aka same shi a cikin kãyansa, to shi ne sakamakonsa {wato a rike shi a madadin abin da aka sata} kamar haka ne muke sãkawa azzãlumai."
A shirinmu da ya gabata mun bayyana cewa: Annabi Yusuf yana son ya zaunar da dan uwansa Benyamin a wajensa don hakan ya zame sharen fagen hijiran mahaifinsa zuwa Masar, kuma tuni ya sanar da Benyamin dabarar da ya shirya na kai wa ga wannan manufar tasa, inda Annabi Yusuf ya sanya mudun sarki mai kima a cikin kayan Benyamin, kuma jami'an gwamnatinsa ba su da labarin abin da ya shirya, don haka aka kama Benyami a matsayin barawo. Sai dai kafin a kai ga kame Benyamin, 'yan uwansa sun kare kansu daga zargin da ake musu na sace mudun sarki, inda suke bayyana cewa; idan mudunku ya bace, to ku sani mu ba mu da hannu a satan. A nan sai jami'an gwamnatin Masar suka ce musu, to mene ne sakamakon wanda aka samu mudun a kayansa? Sai 'yan uwan Yusuf suka ce a yankinmu muna da al'adar duk wanda aka same shi da laifin sata, to mai dukiyar da aka masa satan yana da hakkin rike shi a matsayin bawansa har zuwa lokacin da zai fanshe hasarar da ya janyo masa.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} A matsayin hukunta mai laifi za a iya neman shi kansa mai laifin ya bayyana irin hukuncin da ya dace da shi, domin ya yi saurin mika kai ga abin da ake zarginsa tare da amincewa da hukuncin da ya hau kansa.
{2} Wajen gudanar da dokoki kada a kuskura a nuna bambanci tsakanin mutane, duk wanda aka same shi da laifin sata, to wajibi ne a kame shi kuma komai matsayinsa.
Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 76 da ke cikin suratu-Yusuf kamar haka:-
فَبَدَأَ بِأَوْعِيَتِهِمْ قَبْلَ وِعَاء أَخِيهِ ثُمَّ اسْتَخْرَجَهَا مِن وِعَاء أَخِيهِ كَذَلِكَ كِدْنَا لِيُوسُفَ مَا كَانَ لِيَأْخُذَ أَخَاهُ فِي دِينِ الْمَلِكِ إِلاَّ أَن يَشَاءَ اللّهُ نَرْفَعُ دَرَجَاتٍ مِّن نَّشَاء وَفَوْقَ كُلِّ ذِي عِلْمٍ عَلِيمٌ{76}.
"Sai ya fãra da {binciken} jakunkunansu kafin jakar dan'uwansa. Sannan ya fitar da {Mudun} daga jakar dan'uwansa. Kamar haka muka shirya wa Yũsufu. Ba zai yiyu ya rike dan'uwansa ba a cikin shari'ar sarki {wato a dõkõkin Masar} Sai dai idan Allah Ya so. Munã daukaka darajõjin wadanda Muka so ne, kuma a saman kõwane ma'abũcin ilmi akwai wani masani".
A karkashin shirin da Annabi Yusuf ya tsara babu wata kafar da zata sanya 'yan uwansa su yi zargin dabara ce aka kulla tsakaninsa da Benyamin, kuma shirin ya gudana aka tsari, inda aka fara bincika kayayyakin sauran 'yan uwan Yusuf sannan daga karshe a kai ga kayan Benyamin kuma aka fito da mudun daga cikin kayan nasa, don haka bayyana shi a matsayin barawo, kuma a bisa ikrarin 'yan uwansa dole ne a tsare shi a Masar baya da hakkin komawa garinsu.
Alkur'ani yana bayyana cewa: Duk wannan shiri na Annabi Yusuf ya gudana ne karkashin tsarin Allah da koyarwansa, saboda a karkashin tsarin dokokin Masar Annabi Yusuf ba shi da wani hakkin zaunar da Benyamin a wajensa. Haka nan Annabi Yusuf baya da damar zaunar da Benyamin a wajensa koda a bisa dalilin an same shi laifin sata ne, ba don 'yan uwansa sun bayyana hukuncin da ake gudanarwa a kan barawo a dabi'ar yankinsu ba.
Ayar ta ci gaba da bayyana cewa: Da nufin Allah ne Annabi Yusuf ya kai ga duk wata daukaka da ya samu a Masar, saboda ilimin Allah shi ne mafi daukaka a kan duk wani ilimi, kuma shi ke sanar da Yusuf duk wani mataki da yake dauka domin cimma manufarsa.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Wajibi ne a kan al'ummar duk wata kasa su kiyaye dokokin kasarsu koda kuwa gwamnatin ba ta Musulunci ba ce, sai dai idan dokokin kasar sun yi hannun riga da hukunce hukuncen addini, to a nan dole ne yin hijira domin ba zai yiyu mutum ya take dokokin Allah ba.
{2} Ilimi shi ne ginshikin daukaka da ci gaba, kuma tushen kai wa ga duk wani matsayi madaukaki.
Yanzu kuma zamu saurari aya ta 77 da ke cikin suratu-Yusuf kamar haka:-
قَالُواْ إِن يَسْرِقْ فَقَدْ سَرَقَ أَخٌ لَّهُ مِن قَبْلُ فَأَسَرَّهَا يُوسُفُ فِي نَفْسِهِ وَلَمْ يُبْدِهَا لَهُمْ قَالَ أَنتُمْ شَرٌّ مَّكَاناً وَاللّهُ أَعْلَمْ بِمَا تَصِفُونَ{77}.
"Suka ce: "Idan har ya yi sãta, to hakika dan'uwansa ma yã taba yin sãta a gabãninsa." Sai Yũsufu ya bõye wannan {Maganar} a cikin ransa kuma bai bayyana ta ba a gare su, ya ce: "Kũ ne mafi sharri matsayi. Kuma Allah ne Mafi sanin abin da kuke siffantãwa."
Duk da cewa tabbas 'yan uwan Annabi Yusuf ba su yi sata ba, haka nan suna da masaniyar dan uwansu Benyamin baya da hannu a sace mudun sarki, saboda haka maimakon su tsaya domin su kare karamin dan uwansu, tare da neman kore zargin sata a kansa, amma sai ya zame a zukatansu ba su ki a ce an tsare Benyamin kan zargin laifin sata a Masar ba, domin su koma gida ba tare da shi ba, saboda mahaifinsu yana da kyakkyawar alaka da Benyamin tare da karkata zuwa gare shi, don haka idan babu Benyamin sai ya zame dole soyayyar mahaifinsu ta karkato zuwa kansu. Lalle 'yan uwan Annabi Yusuf ba kawai sun ki kare dan uwansu ba ne har ma dan uwansu Yusuf da ba shi da wata alaka da halin da suka shiga a Masar amma sai da suka jingina laifin sata a kansa lamarin da ya kara karfafa jami'an Masar kan kame Benyamin da laifin sata tare da tsare shi.
Ayar ta ci gaba da bayyana cewa: Duk da cewa Annabi Yusuf shi ke rike da madafun iko a Masar, kuma yana da damar hana 'yan uwansa alkama da suka zo nema tare da bada umurnin tsare su kan zargin sata, amma sai ya hadiye fushin cutar da shi da suka yi na zarginsa da laifin sata, kuma ya yi musu ahuwa kan haka, inda yake cewa: Allah mafi sanin hakika abin da kuke cewa, kuma a halin yanzu yana yin da kuke ciki yafi muni a kan halin zargin da kuke jinginawa ga 'yan uwanku. Sannan lalle an samu ma'aunin sarki a cikin kayanku kuma laifin hakan ba karami ba ne.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Dole ne mu kasance masu budaddiyar zuciya da hadiye munanan maganganun da suke fitowa daga bakuna saboda mu kai ga manufar da muke son cimmawa.
{2} Babu mutunci ko kima tonon asiri a kowane waje, don haka rufe asirin mutane a mafi yawan lokuta wajibi ne, musamman ga mahukunta da suke jagorantar al'amuran mutane, dole ne su duba masalahar jama'a kada su dinga tona sirrin mutane.
To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.
Suratu Yusuf, Aya Ta 78-82 (Kashi Na 389)
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.
A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 78 zuwa 79 da suke cikin suratu-Yusuf kamar haka:-
قَالُواْ يَا أَيُّهَا الْعَزِيزُ إِنَّ لَهُ أَباً شَيْخاً كَبِيراً فَخُذْ أَحَدَنَا مَكَانَهُ إِنَّا نَرَاكَ مِنَ الْمُحْسِنِينَ{78} قَالَ مَعَاذَ اللّهِ أَن نَّأْخُذَ إِلاَّ مَن وَجَدْنَا مَتَاعَنَا عِندَهُ إِنَّـا إِذاً لَّظَالِمُونَ{79}
"Suka ce: "Yã kai wannan shugaba hakika yanã da mahaifi wanda ya tsufa tukuf mai daraja, sabõda haka ka kãma dayanmu a madadinsa Lalle ne muna ganin ka daga mãsu kyautatãwa." Ya ce: "Allah Ya tsare mu da kãma wani ba wanda muka sãmi kãyanmu a wurinsa ba. {Idan kuwa muka yi haka} to hakĩka mun zame azzãlumai ."
A shirinmu da ya gabata mun ambaci shirin Annabi Yusuf na zaunar da dan uwansa Benyamin a wajensa, inda ya sanya mudun sarki a cikin kayansa, sannan aka kame Benyamin da laifin sata.
Wannan ayar tana bayyana cewa: Bayan da 'yan uwan Annabi Yusuf suka mummunan halin da Benyamin ya shiga, kuma suna da tabbacin za su koma gida ba tare da shi ba, sai suka shiga cikin tashin hankali, musamman dangane da alkawari da rantsuwar da suka yi a gaban mahaifinsu, don haka sai suka gabatar da shawarin cewa; a rike daya daga cikinsu ya zauna a Masar a maimakon Benyamin, saboda Benyamin ya koma wajen mahaifinsa, amma kafin nan Annabi Yusuf da Benyamin sun cimma matsaya kan cewa; ba zasu amince da duk wata shawarar da 'yan uwansu zasu gabatar na raba su ba, kuma shawarar ma ta sabawa dokokin Masar.
Baya ga haka, koda Annabi Yusuf ya amince da shawarar da 'yan uwansa suka gabatar na sakin Benyamin a maimakon rike daya daga cikinsu, to tabbas bayan komawarsu gida zasu bayyana wa mahaifinsu cewa; Benyamin ya yi sata, wanda hakan babu makawa zai wurga mahaifinsu cikin damuwa da bacin rai. A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Wadanda a baya ke neman kaskanta Yusuf, a halin yanzu ala-tilas suna girmama shi tare da kiransa madaukaki, hakika wannan doka ce na Allah da yake kaskanta azzalumi ya kuma daukaka wanda aka zalunta.
{2} Dole ne kowa ya girmama doka tare da yin aiki da ita, kuma sabawa doka baya halatta koda a tsakanin manyan jami'an gwamnati ne.
Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 80 da ke cikin suratu-Yusuf kamar haka:-
فَلَمَّا اسْتَيْأَسُواْ مِنْهُ خَلَصُواْ نَجِيّاً قَالَ كَبِيرُهُمْ أَلَمْ تَعْلَمُواْ أَنَّ أَبَاكُمْ قَدْ أَخَذَ عَلَيْكُم مَّوْثِقاً مِّنَ اللّهِ وَمِن قَبْلُ مَا فَرَّطتُمْ فِي يُوسُفَ فَلَنْ أَبْرَحَ الأَرْضَ حَتَّىَ يَأْذَنَ لِي أَبِي أَوْ يَحْكُمَ اللّهُ لِي وَهُوَ خَيْرُ الْحَاكِمِينَ{80}
" A lõkacin da suka yanke tsammãni daga gare shi, sai suka fita sunã mãsu gãnãwa. Babbansu ya ce: "Shin ba ku san cẽwa mahaifinku ya dauki alkawari daga gare ku tsakaninku da Allah ba, kuma daga gabanin haka akwai abin da kuka yi na sakaci game da Yũsufu? Sabõda haka bã zan bar kasar {Masar} ba har sai mahaifina yã yi mini izini kõ kuwa Allah Ya yi hukunci a gare ni, kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mahukunta."
Bayan da 'yan uwan Yusuf suka fitar da rai daga samun amincewarsa kan sakin dan uwansu Benyamin, sai suka daura aniyar komawa garinsu, amma sai babbansu ya bayyana cewa; lalle ba zai iya yin ido biyu da mahaifinsu ba dauke da wannan mummunan labari, musamman saboda munin halin da ya san su da shi a baya dangane da abin da suka aikata kan Yusuf, don haka ba zai koma gida ba har sai mahaifinsa ya yi masa izinin dawowa, ko Allah ya yi hukunci a kansa ko kuma ya samar masa da wata mafita.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Kada kamun kafa da magiya ta hana mutum gudanar da hukunci ko doka, koda kuwa 'yan uwa da makusantansa ne suke kamun kafar, don haka wajibi ne a dauki matakin aiwatar da hukunci kamar yadda doka ta tanada. {2} Daukan alkawari da yin rantsuwa suna sanya mutane su gudanar da ayyukansu a kan doka da tsari.
Yanzu kuma zamu saurari aya ta 81 zuwa 82 da suke cikin suratu-Yusuf kamar haka:-
ارْجِعُواْ إِلَى أَبِيكُمْ فَقُولُواْ يَا أَبَانَا إِنَّ ابْنَكَ سَرَقَ وَمَا شَهِدْنَا إِلاَّ بِمَا عَلِمْنَا وَمَا كُنَّا لِلْغَيْبِ حَافِظِينَ{81} وَاسْأَلِ الْقَرْيَةَ الَّتِي كُنَّا فِيهَا وَالْعِيْرَ الَّتِي أَقْبَلْنَا فِيهَا وَإِنَّا لَصَادِقُونَ{82}
"Ku kõma zuwa ga mahaifinku ku ce da shi: Yã mahaifinmu hakika danka yã yi sãta, kuma ba mu yi shaida ba sai abin da muka sani, kuma ba mu kasance mun san gaibu ba." "Kuma ka tambayi {mutanen} alkarya wadda muka kasance a cikinta da ãyarin da muka zo cikinsa, kuma hakĩka mũ mãsu gaskiya ne."
A tattaunawar da ta gudana a tsakanin 'yan uwan Yusuf; babbansu ya bayyana cewa: lalle zai ci gaba da zama a cikin Masar watakila sarki ya jikansa ya saki Benyamin, sannan ya yi wasici ga sauran 'yan uwansa da cewa; a lokacin da suka koma ga mahaifinsu su dauki matakin sanar da shi da fayyace masa hakikanin abin da ya faru na cewa; tabbas an kame Benyamin a matsayin barawo, kuma shi a matsayinsa na babba yana can Masar zai ci gaba da zama har sai zuwa lokacin da za a saki Benyami, kuma su kafa shaida da sauran mutanen da suke tare da su a ayarin da suka tafi zuwa kasar Masar sanyan alkama.
Hakika duk abin da wannan babba daga cikin 'yan uwan Annabi Yusuf ya fada gaskiya ce, amma saboda mummunan halin da suke dauke da shi a baya, hakan ba zai sanya mahaifinsu ya yi saurin gaskata su ba, kuma zai yi tsammanin wani sabon makirci suka tsara na raba shi da Benyamin kamar yadda suka aikata ga Yusuf, don haka babbansu ya bukaci da su hujja da sauran mutanen da suke tare da su a ayari a matsayin shaida ko mahaifinsu zai amince da labarin da zasu gaya masa kan Benyamin.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Kada mu yi saurin yin hukunci kan mutanen da ake zargi da aikata wani abu na laifi matukar ba mu da wata hujja ko dalili kan aikata zargin. Don haka babba daga cikin 'yan uwan Yusuf ya furta cewa: An kame Benyamin kan zargin sata, amma ba mu da masaniya kan hakikanin yadda wannan lamari ya faru.
{2} Sanin mutum da wata mummunar dabi'a da karya yana sanyawa mutane su yi kokwanto kan maganarsa koda kuwa gaskiya ce, don haka mu kiyaye kada mu janyo wa kanmu mummunar shaida.
To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.
Suratu Yusuf, Aya Ta 83-86 (Kashi Na 390)
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.
A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 83 zuwa 84 da suke cikin suratu-Yusuf kamar haka:-
قَالَ بَلْ سَوَّلَتْ لَكُمْ أَنفُسُكُمْ أَمْراً فَصَبْرٌ جَمِيلٌ عَسَى اللّهُ أَن يَأْتِيَنِي بِهِمْ جَمِيعاً إِنَّهُ هُوَ الْعَلِيمُ الْحَكِيمُ{83} وَتَوَلَّى عَنْهُمْ وَقَالَ يَا أَسَفَى عَلَى يُوسُفَ وَابْيَضَّتْ عَيْنَاهُ مِنَ الْحُزْنِ فَهُوَ كَظِيمٌ{84}
"{Mahaifinsu} Ya ce: "Ã'a, zukatanku dai sun kawãta muku wani abu. Hakuri kawai shi ya fi, kuma akwai tsammãnin Allah Ya zo mini da su gabã daya { Wato Yũsufu da 'yan'uwansa}. Lalle ne Shĩ ne Masani, Mai hikima." Kuma sai ya kau da kai daga gare su, kuma ya ce: "Wayyo kan wannan bakin ciki na kan Yũsufu!" Kuma idãnunsa suka yi fari sabõda bakin ciki yana mai hadiye fushi".
A shirinmu da ya gabata mun bayyana cewa: 'Yan uwan Yusuf sun koma gida wajen mahaifinsu, alhalin Benyamin yana wajen dan uwansa Annabi Yusuf a Masar. 'Yan uwan Yusuf sun bayyana wa mahaifinsu duk abin da faru da tsare Benyamin da aka yi a matsayin barawo.
Wadannan ayoyi suna bayyana cewa: Annabi Yakubu ya mai da martani ga 'ya'yayensa da cewa; lalle zukatanku sun kawata muku mummunan ayyukanku, don haka kuka kyale Benyamin a Masar saboda zuciya ta ci gaba da kuna kamar yadda kuka nisanta Yusuf gare ni. Hakika zan ci gaba da hakuri har Allah ya dawo mini da su dukkaninsu biyu.
Hakika hakurin Annabi Yakubu ya kasance ne tare ne da bakin ciki da nuna damuwa, inda har ya kai ga saboda tsananin kuka idanuwansa sun yi fari ba su gani, kuma bakin cikin da yake ciki yana kona masa zuciya amma baya furtawa a baki. Duk da cewa a wannan karo 'yan uwan Yusuf ba su aikata laifi ba, kuma ba su da wani shirin cutar da Benyamin, amma matsalar irin mummunan matakin da suka dauka kan dan uwansu Yusuf da kuma ci gaba da tafiya kan wannan kuskuren saboda rashin bayyana gaskiyar al'amari ga mahaifinsu, hakan ya sanya Annabi Yakubu yana zarginsu kan lamarin Benyamin, amma duk da haka ya dauki matakin yin hakuri da juriya.
A cikin wadannan ayoyi zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Hakika mumini yana hakuri kan duk wata matsala da ta faru gare shi, kuma yana da masaniyar cewa akwai hikima a duk abin da ya afku a kansa na matsala da tsanani, kuma Allah yana sane da duk abin da ke faruwa kan bawansa.
{2} Lalle yin kuka dangane da rabuwa da masoyi lamari ne dabi'a ce ta dan Adam, kuma wannnan dabi'ar tana gudana a tsakanin bayin Allah.
{3} Irin matsayi da kimar da Annabi Yusuf yake da shi a wajen mahaifinsa ya kai ga saboda bakin cikin rabuwa da shi ya makance, kuma har a lokacin da ya samu labarin kame Benyamin a Masar sai da ya ambaci sunan Yusuf, kuma ya nuna damuwa kan raba su da aka yi.
Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 85 da ke cikin suratu-Yusuf kamar haka:-
قَالُواْ تَالله تَفْتَأُ تَذْكُرُ يُوسُفَ حَتَّى تَكُونَ حَرَضاً أَوْ تَكُونَ مِنَ الْهَالِكِينَ{85}
"Suka ce: "Wallahi bã zã ka bar tuna Yusuf ba, har sai ka kasance Mai rauni kwarai kõ kuma ka kasance daga mãsu halaka."
A fili yake kame Benyamin a Masar zai kara zaburan da Annabi Yakubu kan tuna dansa Yusuf da ambaton sunansa, amma 'ya'yansa da ba su son ganin Yusuf kusa da mahaifinsu, kuma ba su son jin yana yawan ambaton sunansa, sai suke gargadinsa da cewa; matukar ba ka kawo karshen wannan yawan ambaton Yusuf da kake yi ba, kuma ba ka cire bakin cikin rabuwa da shi daga cikin zuciyarka ba, to lalle hakan zai yi sanadiyyar cutar da kai, tare da kai ka ga halin halaka, saboda mu da idonmu mun ga kura tana cinsa, kuma don mene ne ba zaka mance batun Yusuf ba har wannan tsawon lokacin?. Hakika a fili yake cewa; duk wanda zuciyarsa ke kuna saboda son Yusuf, tabbas yana da masaniya kan cikan matsayinsa da kimarsa, amma 'yan uwansa da cutar hasada ta addabe su, sun kasa gane sirrin da ya sanya mahaifinsu ya kaunace shi.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Hakika Annabi Yakubu yana son Yusuf saboda yana da masaniyar matsayinsa, kuma don haka ne yake tuna shi tare da yawan ambaton sunansa. Sakamakon haka idan har muna son Allah, sai mu duba shin sau nawa muke tuna shi tare da ambatinsa?.
{2} Tabbas rabuwa da masoyi tana raunana mutum, don haka mu yi kokarin ganin mun zame masu dauke da soyayya na gaskiya da hakika.
Yanzu kuma zamu saurari aya ta 86 da ke cikin suratu-Yusuf kamar haka:-
قَالَ إِنَّمَا أَشْكُو بَثِّي وَحُزْنِي إِلَى اللّهِ وَأَعْلَمُ مِنَ اللّهِ مَا لاَ تَعْلَمُونَ{86}
"Ya ce: Iyaka dai inã bayyana takaicina ne da bakin cikĩna zuwa ga Allah, kuma ina sane da abin da ba ku sani ba game da Allah."
Wasu daga cikin ayoyin alkur'ani suna bayyana cewa: Bayin Allah suna mika kukansu da matsalolinsu ne ga Allah, kuma suna da tabbacin shi ne zai yaye musu. Kamar haka ne a lokacin da aka jarabi Annabi Musa da talauci da rashi, sai ya mika kukansa ga Allah, haka nan Annabi Ayuba da aka jarabe shi da ciwo da matsaloli. Don haka wannan ayar ma take bayyana cewa; Annabi Yakubu ya mika kukarsa na halin da ya shiga na kuncin rabuwa da dansa ne ga Allah, saboda bayin Allah suna da tabbacin duk wani abin da suka samu na ni'ima, to lalle jin kai ne na Ubangiji, kuma duk wata matsala da wahala da suka shiga, lalle akwai hikima ciki, don haka a dukkanin halayen biyu suke mika al'amarunsu gare shi tare da neman 'yardansa. Baya ga haka Annabi Yakubu yana da tabbacin dansa Yusuf yana raye, kuma mafarkin da Yusuf ya yi tun yana karami lamari ne da ke kara da masa yakinin rayuwar dansa, amma da yana da tabbacin Yusuf baya raye da tuni ya cire shi a ransa domin zuciyarsa ta huta.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Mika kukan matsaloli ga mutane abin zargi ne, amma gabatar da kuka ga Allah sunna ce ta bayin Allah tsarkaka.
{2} Kada mu taba yanke kauna daga samun rahamar Allah da jin kansa, saboda tsammanin kyakkyawar rayuwa bayan wahala da tsanani daya ne daga cikin dabi'un bayin Allah na musamman.
To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.
Suratu Yusuf, Aya Ta 87-89 (Kashi Na 391)
Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.
A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 87 da ke cikin suratu-Yusuf kamar haka:-
يَا بَنِيَّ اذْهَبُواْ فَتَحَسَّسُواْ مِن يُوسُفَ وَأَخِيهِ وَلاَ تَيْأَسُواْ مِن رَّوْحِ اللّهِ إِنَّهُ لاَ يَيْأَسُ مِن رَّوْحِ اللّهِ إِلاَّ الْقَوْمُ الْكَافِرُونَ{87}
"Yã ku 'ya'yayena ku tafi ku nẽmo lãbãrin Yũsufu da dan'uwansa. Kada ku yanke kauna daga rahamar Allah. Lalle ne bãbu Mai yanke kauna daga rahamar Allah sai mutãne kãfirai."
A cikin shirinmu da ya gabata mun bayyana cewa: A lokacin da 'ya'yayen Annabi Yakubu suka ba shi labarin tsare dansa Benyamin da aka yi a Masar, hakan ya kara tunasar da shi abin da ya faru ga Yusuf, don haka ya mika kukansa ga Allah yana neman da ya yaye maa halin kuncin da ya shiga.
Hakika Annabi Yakubu yana da tabbacin dansa yana raye, kuma mafarkin da Yusuf ya yi a lokacin da yake karami ya kara masa yakini kan haka, saboda fassara mafarkin tana nuni ne kan girman matsayi da daukakan da Yusuf zai samu ne a rayuwa. Don haka Annabi Yakubu ya ce wa 'ya'yayensa; ku sake shiryawa ku koma kasar Masar don binciko inda Yusuf yake, kuma ku yi duk kokarin da zaku iya na ganin an sako dan uwanku Benyamin, sai ku zo mini dukkaninku.
A matakin da Annabi Yakubu ya dauka na kadaitar da 'ya'yayensa kan neman inda Yusuf yake, ya yi musu wasici da cewa: Lalle ku sani mutanen da suka yi imani da Allah ba su taba fitar da rai daga rahama da jin kai na Allah, kuma fitar da rai daga rahamar Allah alama ce ta kafirai.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Kafin mu kai ga samun rahama da jin kai na Allah dole ne sai mun yunkura, ba wai mutum ya zauna a gida ba yana jiran saukar rahamar Allah. {Annabi Yakubu yana cewa 'ya'yayensa; kafin gano inda Yusuf yake sai kun yunkura, kuma kada ku kuskura ku fitar da rai daga rahamar Allah}.
{2} Bayin Allah a kullum suna kadaitar da mutane ne zuwa ga rahamar Allah, amma duk mai kokarin ganin a kullum mutane sun yanke kauna, to lalle ya yi nisa da wannan addini na Allah.
Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 88 da ke cikin suratu-Yusuf kamar haka:-
فَلَمَّا دَخَلُواْ عَلَيْهِ قَالُواْ يَا أَيُّهَا الْعَزِيزُ مَسَّنَا وَأَهْلَنَا الضُّرُّ وَجِئْنَا بِبِضَاعَةٍ مُّزْجَاةٍ فَأَوْفِ لَنَا الْكَيْلَ وَتَصَدَّقْ عَلَيْنَا إِنَّ اللّهَ يَجْزِي الْمُتَصَدِّقِينَ{88}.
"Sannan a lõkacin da suka shiga gare shi {wato Yusuf} sai suka ce: "Yã kai wannan shugaba ! Cũtar {yunwa} ta shãfe mu, mũ da iyãlinmu, kuma mun zo da wata hãja maras daraja, to ka cika mana mudu, kuma ka kyautata mana hakika Allah Yanã sãka wa mãsu kyautatawa".
'Ya'yayen Annabi Yakubu sun sake komawa wajen dan uwansu Annabi Yusuf a karo na uku, inda suke magana da shi cikin salo irin na masu bukata da rauni suna cewa: A wannan lokaci mun zo sanyan alkama ce amma kudinmu kadan ne, sai dai muna son ka taimaka ka gabatar mana da cikakken rabo da ake bai wa kowane mutum. A karo na farko da suka zo neman alkama a kasar Masar Annabi Yusuf ya sanya a mayar musu da kudin da suka biya na alkama, amma a wannan karo suna son Annabi Yusuf ya yafe musu sauran cikon kudin alkamar ne saboda rashi da suke fama da shi.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Talauci da fatara suna karya lagon ji-ji da kai da takama da mutum yake dauke da shi. 'Yan uwan Annabi Yusuf da a cikin ji-ji da kai suke cewa; su tawaga ce masu karfi da zasu iya gudanar da komai, don haka mahaifinsu yana kan kuskure, sai ga shi a halin yanzu suna sunkuyar da kai wajen neman alkama!.
{2} Kyakkyawan sakamakon da Allah yake bai wa mutanen da suke taimako da gudanar da hidima ga al'umma yana kara karfin gwiwar gudanar da karamci a tsakanin mutane.
Yanzu kuma zamu saurari aya ta 89 da ke cikin suratu-Yusuf kamar haka:-
قَالَ هَلْ عَلِمْتُم مَّا فَعَلْتُم بِيُوسُفَ وَأَخِيهِ إِذْ أَنتُمْ جَاهِلُونَ{89}
"Ya ce: "Shin, kun san abin da kuka aikata ga Yũsufu da dan'uwansa a lõkacin da kuke jãhilai?"
Irin halin rauni da bukata da 'yan uwan Annabi Yusuf suka nuna wajen neman alkama ya yi tsananin tasiri a cikin zuciyar Annabi Yusuf, inda har ya kai ga matsayin da ba zai iya ci gaba da boye kansa gare su ba, don haka ya dauki matakin gabatar musu da tambaya da zata fadakar da su domin fahimtar hakikanin wanda suke magana da shi. A nan maimakon Annabi Yusuf ya ce musa: Ni ne Yusuf, sannan ku kuma kune 'yan uwana da kuka aikata kuskure kai na, amma sai ya ce musu: Shin zaku tuna a lokacin samarta abin da kuka aikata ga Yusuf da dan uwansa Benyamin saboda rashin sani? Yana gabatar musu da wannan tambaya, sai suka fahimci lalle shi ne dan uwansu Yusuf, kuma yana da masaniya kan duk abin da suka aikata gare shi da dan uwansa Benyamin, kuma lalle idan har yana son daukan fansa, to yana iya gudanar da duk wani hukunci kansu, don haka babu abin da ya rage gare su illa su tuba daga mumunanan ayyukansu.
Batu mafi muhimmanci a cikin wannan fadakarwa ta Annabi Yusuf shi ne, inda Annabi Yusuf yake cewa 'yan uwansa abin da kuka aikata kun aikata ne a kan rashin sani ba wai bisa ganganci ba, kuma Annabi Yusuf ya dauki matakin kwantar musu da hankali ta hanyar gwada musu abin da suka aikata ba abu ne mai girma ba a wajensa, iyaka dai shaidan ne ya yaudare su har ya wurga su cikin wannan mummunan aiki, amma lalle ku 'yan uwana ne ba ku nufin cutar da ni, kawai dai shaidan ne ya nemi shiga tsakaninmu har ya haifar da wannan matsala.
A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-
{1} Aikata zalunci a kan mutane musamman makusanta, yana wuya a mance da shi, don haka komai dadewa wata rana sai an bude shafin tuna wannan zaluncin.
{2} Idan mutum ya munanta mana, sannan daga baya ya shiga cikin matsalar da ya zo wajenmu yana neman mu taimaka masa, to mu kasance masu zurfin tunani da karamci gare shi, kada mu nemi daukan fansa a kansa.
To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.
Suratu Yusuf, Aya Ta 90-92 (Kashi Na 392)
Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Yusuf, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.
Aya ta (90) surat Yusuf
قَالُواْ أَإِنَّكَ لَأَنتَ يُوسُفُ قَالَ أَنَاْ يُوسُفُ وَهَـذَا أَخِي قَدْ مَنَّ اللّهُ عَلَيْنَا إِنَّهُ مَن يَتَّقِ وَيِصْبِرْ فَإِنَّ اللّهَ لاَ يُضِيعُ أَجْرَ الْمُحْسِنِينَ{90}
Saka ce: "Shin kõ kai ne Yũsufu?" Ya ce: "Nĩ ne Yũsufu, kuma wannan shĩ ne dan'uwãna. Hakĩka Allah yã yi falala a gare mu. Lalle ne shi wanda ya bi Allah da takawa, kuma ya yi hakuri, to, Lalle ne Allah bã ya tõzarta lãdar mãsu kyautatãwa."
A cikin shirin da ya gabata an ji cewa a lokacin da ‘yan uwan annabi Yusuf (AS) suka dawo wurinsa suna masu nuna kaskanci da damuwa da kunci, annabi Yusuf (AS) ya yi kokarin ya kawar musu da wannan damuwar da suke ciki, ta hanyar yi musu tambayar da za su iya gane cewa shi ne dan uwansu Yusuf, wanda suka jefa a cikin rijiya, a lokacin sai suka dawo cikin hankalinsu suna tunanin cewa ya aka yi wannan mutum ya san labarin Yusuf har ma da fadin sunansa, kuma tambayarsa na nuni da cewa yana da cikakkiyar masaniya kan abin da suka aikata ga Yusuf, kuma lallai a lokacin babu wani wanda ya san abin da ya faru daga su sai Yusuf kawai, saboda haka sai suka ce masa to kai ne Yusuf ? Sai ya ce musu lallai shi ne Yusuf, wannan kuma dan uawansa wanda suke uwa daya da shi wato Binyaminu, domin ya kara kwantar musu da haknali saboda ya san damuwar da za su shiga bayan jin hakan, sai ya nuna musu cewa dukkan lamarin daga Allah ne, jarabawa ce ta ubangiji a gare shi da kuma a gare su, kuma ga shi yau Allah ya hada su baki daya a wuri guda.
Duk da cewa sun yi zalunci mai girma ga annabi Yusuf (AS) kuma ga shi Allah ya ba shi mukami mai girma tun a gidan duniya, amma ya nuna musu tausayi da soyayya da ‘yan uwantaka da sakin fuska, tamkar ba su ne suka aikata abin da suka aiakata kansa ba, wannan kyakkyawar dabi’a ta annabi Yusuf (AS) kadai ta isa ta sanya ‘yan uwansa jin kunyarsa, amma duk da haka sun san san cewa shi mutum ne na Allah, mutum ne wanda ba zai rike su a cikin zuciyarsa ba, saboda haka farincikinsu ya rinjayi damursu da kunyarsu, domin kuwa son san cewa abin da ya faru tabbas ya wuce a wurin Yusuf.
Darussan da za a iya dauka a nan su ne :
1 – Abubuwa da dama da suka da ba san hakininsu ba, bayan shudewar zamuna gaskiya lamari ke bayyana.
2 – Wanda ya jagoranci al'umma shi ne mutum mai hakuri da yafewa, mai juriya a kan musibu da bala'oi, kamar yadda muka gani a cikin siffofin annabi Yusuf (AS)
Ayoyi na (91) da (92) surat Yusuf
قَالُواْ تَاللّهِ لَقَدْ آثَرَكَ اللّهُ عَلَيْنَا وَإِن كُنَّا لَخَاطِئِينَ{91} قَالَ لاَ تَثْرَيبَ عَلَيْكُمُ الْيَوْمَ يَغْفِرُ اللّهُ لَكُمْ وَهُوَ أَرْحَمُ الرَّاحِمِينَ{92}
91 - Suka ce: "Wallahi! Lalle ne Allah Yã zãbe ka akannmu, kuma lalle ne mun kasance, hakĩka, mãsu kuskure."
92 - Ya ce: "Bãbu zargi akanku a yau, Allah Yanã gãfartã muku, kuma Shĩ ne Mafi rahamar mãsu rahama."
'Yan uwan annabi Yusuf sun ji kunya matuka bisa ga karamcin da suka gani daga gare shi, hakan ya sanya sun nadama har ma suna ikirari da bakinsu cewa duk da abin da suka yi masa da nufin kashe shi, amma kuma ga shi Allah ya raya shi kuma ya daukaka shi a kansu, sun amsa cewa lallai sun tafka bababn kure:
Annabi Yusuf (AS) ya ce babu bukatar wani neman hanzari, su kwantar da hankakinsu, yana mai rokon Allah da ya gafarta musu kuren da suka yi:
Ya zo a cikin ruwayar tarihi cewa, a lokacin da manzon Allah (SAW) ya ci ya yi Fatahu Makka, wato ranar da aka ci birnin Makka, wasu daga cikin sahabbansa sun fara maganar daukar fansa kan mushrikan Makka saboda cutar da su da suka yi kafin hijira zuwa Madina, sai manzon allah (ASW) ya ce yau rana ce ta rahama da afuwa, ba mu zo Makka domin daukar fansa kan mushrikai ba, kuma ya yi afuwa ga wadanda suka cutar da musulmi a birnin Makka. Manzon Allah (SAW) ya ce a yau ya yi abin da dan uwansa Yusuf (AS) ya yi, a lokacin da ya hadu da 'yan uwansa da suka cutar da shi, maimakon daukar fansa a kansu sai ya yi musu afuwa.
A cikin koyarwar addinin Musulunci mutum yana yin afuwa a lokacin da yake da ikon yin ramuwar gayya, domin kuwa wannan wata siffa ce dake daukaka matsayin mutum a wurin Allah madaukakin sarki, domin kuwa siffa ce ta Allah madaukakin sarki, wanda yake yin afuwa ga bayinsa, alhali yana da ikon ya azabtar da su ko ya halakar da su sakamakon barna da laifin da suke aikatawa a bayan kasa.
Annabi Yusuf (AS) ya yi afuwa ga danginsa da suka cutar da shi cutarwa, amma ya yi musu afuwa, kuma bai tsaya a nan ba, sai shiga gaba wajen nema musu afuwar Allah madaukakin sarki kan wannan laifi da suka aikata, inda ya mayar da damuwarsu damuwarsa, tare da kwantar musu da hankali da ba su natsuwa. Wannan ita ce siffa ta hakikanin bayin Allah masoyansa.
Darussan da za a dauka a nan su ne:
1 – Idan wani ya boye matsayin wani da damalarsa saboda hassada, to wata rana za ta zo wadda Allah zai bayyana matsayin wanda ake ma hassada.
2 – Idan mutane suka amsa cewa sun yi laifi kuma suka gyara kurensu, to Allah madaukakin sarki kofofin gafararsa bude suke a gare su.
3 – A wurin bayin Allah na gari, yin afuwa da yafewa shi ne girma da daukaka.
Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
Suratu Yusuf, Aya Ta 93-95 (Kashi Na 393)
Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Yusuf, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.
Aya ta (93) surat Yusuf
اذْهَبُواْ بِقَمِيصِي هَـذَا فَأَلْقُوهُ عَلَى وَجْهِ أَبِي يَأْتِ بَصِيراً وَأْتُونِي بِأَهْلِكُمْ أَجْمَعِينَ{93}
"Ku tafi da rĩgãta wannan, sa'an nan ku jẽfa ta a kan fuskar mahaifina, zai kõma mai gani. Kuma ku zo mini da iyãlinku bãki daya."
A cikin shirin da ya gabata an ji bayani kan ayar da take magana kan yadda annabi Yusuf (AS) ya fadakar da 'yauwansa cewa shi ne dan uwansu Yusuf da suka yi tsammanin cewa ba da ya samuwa, bayan sun jefa shi a cikin rijiya tun yana karamin yaro. Bayan da 'yan uawansa suka gane shi sun ji kunya matuka, kuma sun nemi afuwarsa, inda ya yi musu afuwa kuma ya roki Allah da ya gafarta musu wannan laifi da suka yi.
Bayan da annabi Yusuf (AS) ya ga cewa 'yan uwansa sun dawo cikin hankalinsu, sai ya ba su labarin dukaknin abin da ya faru da shi tun daga lokacin da suka jefa shi cikin rijiya har zuwa lokacin da yake ba su labari, sai suka sheda ma annabi Yusuf (AS) cewa hakika babansu bai amince da zancensu ba a lokacin da suka ce masa kerkeci ya cinye Yusuf, ya kuma gane cewa lallai makirci ne suka shirya domin su batar da Yusuf saboda hassadar da suke yi masa, ya sheda musu cewa dansa Yusuf a raye yake, kuma Allah zai dawo masa da shi, saboda bakin cikin rabuwa da shi da kuma tunanin halin da yake ciki ne ya sanya idanunsa suka makance saboda zubar da hawaye.
Da jin haka sai annabi Yusuf (AS) ya ce to su tashi su tafi gida, kuma su tafi da rigarsa, da sun isa su jefa rigar a kan fuskar mahaifinsa annabi Yakub (AS) ganinsa zai dawo, kuma ya umurce su da tattaro iyalansu da danginsu baki daya su dawo a wurinsa.
Wani abun lura da shi a cikin kissar annabi Yusuf (AS) shi ne, yadda rigarsa ta zama abun ambato a wurare da dama. A lokacin da 'yan uawansa suka jefa shi a cikin rijiya sun kawo ma mahaifinsu rigar Yusuf ne suka ce; kerkeci ya cinye shi a lokacin da suka bar shi a wurin kayansu, su kuma sun shagalta da wasa, inda suka yanka akuya daya daga cikin awakin da suke kiwo, kuma suka cakuda jininta da rigar annabi domin tabbatar da cewa lallai ya mutu ga shedar jini a rigar da ke jikinsa a lokacin da suka tafi kiwon.
Haka nan kuma a lokacin da Zaliha ta nemi annabi Yusuf (AS) Allah ya tseratar da shi daga sharrinta, ta mayar da zargin a kansa, amma wani mai sheda daga cikin iyalanta ya ce a duba rigarsa, idan ta yage daga gaba to lallai shi neme ta ita ce mai gaskiya, amma idan rigarsa ta yage daga baya ta yi karya shi ne mai gaskiya, a lokacin sai aka duba rigarsa , kuma aka samu ta yage daga baya.
Sai kuma batun makantar mahaifinsa, inda wannan ayar ta yi ishara da cewa; annabi Yusuf (AS) ya bayar da rigarsa ga 'yan uwansa, kuma sheda musu cewa su tafi da rigar, idan sun je gida su jefa ta a kan fuskar mahaifinsu makanta za ta kau daga idanunsa, tare da ba su tabbaci kan hakan, lamarin da ke nuni da cewa wannan wani sirri ne tsakanin Allah da annabinsa Yusuf (AS) da ba kowa ne ya san da shi ba.
Annabi Yakub (AS) daya daga cikin annabawan Allah, wanda idan ya daga hannu ya roki Allah da ya kawar da makanta daga idanunsa Allah Ta'ala zai karbi addu'arsa, amma bai yi hakan ba, sai ya sanya sanadiyar warakarsa daga makanta ta hanyar rigar annabi Yusuf (AS) wannan wata manuniya ce kan cewa annabawan Allah da waliyyansa salihan bayi, albarkarsu ba takaitu da su kansu ba, a a har ma abubuwan da suke dangantaka da su albarkarsu ta kan shafe su, domin kuwa rigar annabi Yusuf a matsayinta na riga kawai da aka dunka ta daga kyalle ba ta da wani matsayi, amma kuma ta zama mai albarka kasantuwarta ta annabi Yusuf, har ma Allah ya warwakar da annabinsa Yakub daga makanta daga albarkar annabi (AS) ta hanyar wannan riga.
Darussan da za a dauka a nan su ne:
1 – Taburruki daga abubuwan da suke da dangantaka da annabawan Allah da waliyyansa halastaccen lamari ne, matukar dai hakan bai maye gurbin Allah a cikin akidar mutum ba, ko mayar da hakan wani abu na surkulle.
2 – Samun canjin yanayi ga mutane da suka sha wahala a rayuwa yana tasiri a cikin rayuwarsu, amma annabawan Allah da waliyyansa dukkan yanayi da suka samu kansu na jarabawar ubangiji suna amincewa da shi, ba tare da hakan ya bar mummunan tasiri a cikin zuciyarsu ko rayuwarsu ba.
Aya ta (94) da (95) surat Yusuf
وَلَمَّا فَصَلَتِ الْعِيرُ قَالَ أَبُوهُمْ إِنِّي لَأَجِدُ رِيحَ يُوسُفَ لَوْلاَ أَن تُفَنِّدُونِ{94} قَالُواْ تَاللّهِ إِنَّكَ لَفِي ضَلاَلِكَ الْقَدِيمِ{95}
94 - Kuma, a lõkacin da ãyari ya kamo hanya mahaifinsa ya ce: "Lalle ne nĩ inã shãkar kamshin Yũsufu, bã dõmin kadã ku karyata ni ba."
95 - Suka ce: "Wallahi lalle ne, kai kanã a cikin batarka dadadda."
A lokacin da tawagar 'yan uwan annabi Yusuf ta kamo hanya daga Masar za su koma gida a can Sham wato kasar Syria ta yanzu, duk da irin nisan da ke akwai tsakanin yankunan biyu, amma annabi Yakub (AS) ya fahimci cewa akwai wani abu dangane da dansa Yusuf, wanda yana da yakini kan cewa yana raye, sai ya ce iyalansa da ba don kada ku ce na tabu ba, da na gaya muku cewa ina jin kamshin dana Yusuf.
Da jin hakan sai suka ce masa tun kafin wannan lokacin daman kana cewa Yusuf yana raye, alhali kuma Yusuf ya mutu tun shekaru masu yawa da suka gabata, wannan irin wancan tunanin ne naka da kuma rudu irin na tsofa.
Annabi Yakub (AS) ya shaki kamshin dansa Yusuf daga bagire mai nisa, wannan zai iya zama lamari ne na gaibi, kasantuwarsa daya daga cikin annabawan, haka nan kuma sai iya dangataka ce da shakuwa da ke tsakanin da da mahaifi.
Wani zai iya yin tambaya cewa idan annabi Yakub (AS) ya san cewa dansa Yusuf yana raye duk tsawon shekarun nan me ya sanya bai nemi shi a inda yake ba? me ya sanya ba ya fadin komai dangane da halin da annabi Yusuf yake ciki, sai ya rika fadin cewa da sannu Allah zai dawo masa da shi? kuma tun farko idan har ya san cewa 'ya 'yansa za su jefa dansa Yusuf cikin rijiya saboda hassada me yanya zai tura su kiwo tare da shi?
To a nan za a iya cewa ba dukaknin sirrin da ake tsakanin Allah da annabawansa ne sauran mutane suke iya sani ba, domin kuwa Allah zai iya sanar da annabinsa ko wani daga cikin bayinsa salihai wani abu da mutane ba su sani ba, kuma ko da ya gaya musu ba za su iya fahimtarsa ba, saboda haka sai ya bar su kan abin da yake a zahirikuma wanda kuma ahankalce mutane sun fi amincewa da shi, har zuwa lokacin da Allah zai bayyana lamarinsa.
Ba'ada bayan haka kuma irin jarrabawar da Allah yake yi wa annabawansa da waliyyansa tafi girma da wahala idan aka kwatanta da yadda yake jarraba sauran mutane, domin kuwa annabawan Allah da waliyyansa sa salihan bayi suna da yanayin da za su iya yin hakuri da jurewa dukkanin musibu da bala'oi saboda Allah.
Saboda haka annabi Yakub yana ilhami kan dukaknin abubuwan da suka faru da annabi Yusuf tsakaninsa da 'ya'yansa da bayan hakan, amma hakan sirri ne tsakaninsa da Allah wanda ya bar ma zuciyarsa, kuma hakan babbar jarabawar ubangiji ce a gare, kuma ya ci wannan jarabawa da tsabar hakurinsa.
Darussan da za a iya dauka a nan su ne:
1 – ba dukkanin sirrin da ake tsakanin Allah da annabawansa ne mutane suke iya sani ko riska ba.
2 – Abin da mutum bai sani ba kada ya yi musunsa, domin kuwa abin da wani bai riska ba wani zai iya riskarsa saboda dalilai da dama.
Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
Suratu Yusuf, Aya Ta 96-99 (Kashi Na 394)
Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Yusuf, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.
Aya ta (96) surat Yusuf
فَلَمَّا أَن جَاء الْبَشِيرُ أَلْقَاهُ عَلَى وَجْهِهِ فَارْتَدَّ بَصِيراً قَالَ أَلَمْ أَقُل لَّكُمْ إِنِّي أَعْلَمُ مِنَ اللّهِ مَا لاَ تَعْلَمُونَ{96}
Sa'an nan a lõkacin da mai bãyar da bushãra ya je, sai ya jẽfa ta a kan fuskarsa, sai ya kõma mai gani. Ya ce: "Shin, ban gaya muku ba, lalle ne ni inã sanin abin da ba ku sani ba, daga Allah?"
A cikin shirin da ya gabata mun ambaci cewa, annabi Yusuf (AS) ya bayar da rigarsa ga 'yan uwansa, inda ya ce su tafi da rigar gida, kuma da zaran insa su jefa ta kan fuskar mahaifinsu annabi Yakub (AS) idan kuka yi haka mahaifinmu zai waraka daga makanta, a lokacin da suka iso sai suka jefa rigar a fuskar mahaifinsu, a nan take ganinsa ya dawo tangaram, a lokacin sai annabi Yakub (AS) ya ce ma ‘ya’yansa, a cikin tsawon shekarun nan a duk lokacin da na ambaci Yusuf sai ku ce na cika tunain Yusuf ne shi yasa nake ganin kamar yana raye, alhali kikeci ya cinye shi, saboda haka kuna zaton cewa rudun tsufa ne tare da ni, domin kuwa kun sakankance kan cewa Yusuf ba zai dawo ba. Amma ba ku san cewa ni na san wani abu daga Allah wanda ku ba ku sani ba, bugu da kari kan hakan ni na kasance a ko da yaushe ina mai dogaro da Allah da mayar da dukkanin lamurrana a gare shi.
‘Yan uwan annabi Yusuf wadanda suka kawo rigarsa a lokacin yana karami suka ce ma mahaifinsa kirkeci ya cinye shi, a wannan karon ma su ne kuma suka kawo rigarsa suna masu bushara ga mahaifinsu da Yusuf da cewa yana raye, ba ma kawai yana raye ba a’a yana ma rike da matsayi mai girma a cikin daular Masar.
A nan za a iya daukar darussa :
1 – ‘Ya’yan da ba na gari ba, suna sabbaba ma mahaifinsu matsaloli na jiki da kuma na ruhi, yayin da salihan ‘ya’ya suke damuwa da halin da mahafansu suke ciki tare da dada musu rai.
2 – Daya daga cikin dabi’un annabawan shi ne yarda da alkawalin ubangiji, da sakakancewa da ikonsa a kan komai, tare da dogaro gare shi da neman taimakonsa shi kadai a cikin dukaknin lamurransu.
Aya ta (97) da (98) a cikin surat Yusuf
قَالُواْ يَا أَبَانَا اسْتَغْفِرْ لَنَا ذُنُوبَنَا إِنَّا كُنَّا خَاطِئِينَ{97} قَالَ سَوْفَ أَسْتَغْفِرُ لَكُمْ رَبِّيَ إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ{98}
97- Suka ce: "Yã mahaifinmu! ka nẽma mana gãfarar zunubanmu, lalle ne mũ, mun kasance mãsu kure."
98- Ya ce: "Da sannu zãn nẽma muku gãfara daga Ubangijina. Shi ne Mai gãfara, Mai jin kai."
‘Ya’yan annabi Yakub (AS) da suka cutar da shi sun yi nadama kan abin da suka aikata, saboda haka suka roke da ya nema musu gafara wajen ubangiji, kasantuwarsa daya daga cikin annabawan Allah madaukakin sarki, shi kuma ya daukar musu alkawali kan cewa ya roka msu gafara a wajen ubangiji a wani lokaci na musamman.
Ya zo a cikin wasu ruwayoyi cewa, abin da annabi Yakub (AS) yake nufi da cewa zai roka musu gafara a lokaci na musamman shi ne daren juma’a, domin kuwa shi lokaci na addu’a da neman gafarar ubangiji, kuma Allah yana karba addu’oi na alkhairi a daren juma’a.
Darussan da za a dauka a nan su ne :
1 – Tawassuli da bayin Allah domin gafara a wajen ubangiji lamari ne karbabbe, domin kuwa ‘ya’yan annabi Yakub duk da sun tuba sun yi nadama kan abin da suka aikata, amma sun nemi mahaifinsu kasantuwarsa annabin Allah da ya nema musu gafara a wajen Allah, kuma ya amsa musu da cewa zai nema musu gafara a wajen Allah.
2 – A lokacin da wani ya aikata ba daidai ba, kuma ya dawo ya yi nadama kan abin da ya aikata, to a karbi hanzarinsa a yi masa afuwa, kuma a nemi sauran wadanda ya bakanta mawa da su yi masa afuwa.
3 – A lokacin da wani yake aikata wani laifi na sabo kada a sare masa gwiwa ko sanya shi ya yanke kauna daga samun gafarar ubangiji, maimakon haka a karfafa gwiwarsa da cewa idan ya daina abin da yake yi na sabo kuma ya tuba, to Allah zai gafarta masa laifukansa.
Aya ta (99) a cikin surat Yusuf
فَلَمَّا دَخَلُواْ عَلَى يُوسُفَ آوَى إِلَيْهِ أَبَوَيْهِ وَقَالَ ادْخُلُواْ مِصْرَ إِن شَاء اللّهُ آمِنِينَ{99}
Sa'an nan a lõkacin da suka shiga gun Yũsufu, yã tattara mahaifansa biyu a gare shi, kuma ya ce: "Ku shiga Masar in Allah Ya so, kuna amintattu."
Annabi Yusuf (AS) tare da sauran jama’a sun tsaya a wajen gari suna jiran isowar mahaifinsa tare da iyalansa baki daya, domin ya tarbe su a cikin mutunci da daukaka da girmamawa. Hakika haduwar annabi Yusuf (AS) da mahaifinsa annabi Yakub (AS) babban lamari ne da ke tabbatar da kudirar ubangiji da kuma hikimarsa.
Darussan da za a dauka a nan su ne :
1 – Dukkanin mukamin da mutum ya kai gare shi wajibi ne ya kaskantar da kansa ga mahaifansa tare da ba su girman da Allah ya ba su, da kuma yi musu biyayya, domin kuwa Allah madaukakin sarki shi ne ya wajabta yin hakan, matukar dai ba sun yi umurni da sabon Allah ba ne.
2 – A lokacin da aka samu shugabanni na gari masu imani da tausayi da sanin hakkin dan adam, to a lokacin ne za a samu adalci da kaunar juna da tausayi a tsakanin al’umma, kamar dai yadda aka gani a lokacin da annabi Yusuf (AS) yana mulki.
3 – Duk matsayin da mutum ya kai gare shi kada ya manta da Allah, kada duniya ta rude shi, ta yadda har zai daukin kansa ya fi sauran mutane, hakan ne zai ba shaidan damar halakar da shi cikin sauki. Annabi Yusuf (AS) ya kai ga mukami na mulki, amma kuma a lokaci guda babban burinsa shi ne ya ga ya kyuatata dukkanin mutanen da suke karkashinsa, ta yadda hakkin wani ba salwanta ba.
Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
Suratu Yusuf, Aya Ta 100-101 (Kashi Na 395)
Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Yusuf, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.
Aya ta (100) surat Yusuf
وَرَفَعَ أَبَوَيْهِ عَلَى الْعَرْشِ وَخَرُّواْ لَهُ سُجَّداً وَقَالَ يَا أَبَتِ هَـذَا تَأْوِيلُ رُؤْيَايَ مِن قَبْلُ قَدْ جَعَلَهَا رَبِّي حَقّاً وَقَدْ أَحْسَنَ بَي إِذْ أَخْرَجَنِي مِنَ السِّجْنِ وَجَاء بِكُم مِّنَ الْبَدْوِ مِن بَعْدِ أَن نَّزغَ الشَّيْطَانُ بَيْنِي وَبَيْنَ إِخْوَتِي إِنَّ رَبِّي لَطِيفٌ لِّمَا يَشَاءُ إِنَّهُ هُوَ الْعَلِيمُ الْحَكِيمُ{100}
Kuma ya daukaka iyãyensa biyu a kan karaga, sa'an nan suka fãdi a gare shi, suna mãsu sujada. Kuma ya ce: "Ya bãbãna! Wannan ita ce fassarar mafarkin nan nãwa. Lalle ne Ubangijina ya tabbatar da shi, kuma lalle ne ya kyautata game da ni a lõkacin da ya fitar da ni daga kurkuku. Kuma ya zo da ku daga kauye, a bãyan Shaidan yã yi fisgar barna a tsakãnĩna da tsakãnin 'yan'uwana, Lalle ne Ubangijina Mai tausasawa ne ga abin da yake so. Lalle shĩ ne Masani, Mai hikima."
A cikin shirin da ya gabata an bayyana cewa annabi Yusuf (AS) tare da jama'a sun fita wajen gari domin tarbar mahaifansa, da kuma 'yan uwansa, a lokacin da suka iso ya yi musu tarba ta musamman tare da girmama su girmamawa, amma wannan ayar tana magana ne kan yadda annibi Yusuf (AS) ya yi mahaifansa tarba ta ban girma a cikin fada, inda ya dora su kan kujerar mulkinsa, kur'ani mai tsarki ya ce mahaifan annabi Yusuf da sauran danginsa sun yi sujada a kasa suna masu gode ma Allah kan dukkanin ni'imominsa, daga ciki har da ni'imar sake hada su da Yusuf yana raye, bayan rabuwa ta tsawon lokaci. Bugu da kari kan haka kuma Allah ya daukaka annabi Yusuf (AS) ya kai shi ga matsayi mai girma a cikin al'umma.
Annabi Yusuf (AS) yana tsaye a tsakaninsu a lokacin da suka yi sujada, bayan da suka mike sai ya ce mahaifinsa wannan shi ne fassarar mafarkin da na yi a lokacin da ina matashi, inda na ga taurari goma sha daya da rana da wata suna ma masu yi mani sujada. A cikin ma’anar mafarkin za a fahimci cewa mahaifinsa da mahaifiyarsa su ne rana da wata da ya gani a cikin mafarkin, taurari goma sha daya kuma ‘yan uwansa ne su goma sha daya, wadanda dukkaninsu suka yi sujada ga Allah saboda annabi Yusuf (AS) ma’ana saboda farin cikin haduwa da shi da kuma daukakar da Allah ya yi masa.
Daga nan sai annabi Yusuf (AS) ya ba mahaifansa labari dukkanin abin da ya faru da shi bayan fitowarsa daga gidan kurkun Masar, da kuma yadda ya wayi gari kan matsayin da Allah ya dora shi, kuma ya mayar da komai ga Allah madaukakin sarki, yana mai godiya gare shi a kan dukkanin baiwar da ya yi masa.
Wani abu maimatukar muhimmanci a nan shi ne, yadda annabi Yusuf (AS) bai ambaci abin da ‘yan uwansa suka yi masa ba alokacin da suka tafi da shi kiwo, wato shawawar da suka yi tsakaninsu, inda wasu ke cewa a kashe shi, wasu kuma suka ce kada a kashe a dai jefa shi rijiya, duk kuwa da cewa yana sane da duk abin da suka yi, amma domin kada ‘yan uwansa su kunyata a gaban jama’a da kuma mahaifansa, sai ya ambaci cewa abin da ya faru har ya rabu da ‘ya uwansa aikin shaidan ne kawai, bayan da ya yi waswasi a cikin zukatan ‘yan uwansa.
Darussan da za a iya dauka a nan su ne :
1 – A cikin kowane irin yanayi mutum ya samu kansa wajibi ne ya girmama iyayensa, ya kyautata musu ya faranta musu rai.
2 – Duk da cewa mutum yana da zabi a cikin abubuwan da yake yi, amma kuma alokaci guda Allah madaukakin sarki shi ne keda hada mutum da dukkanin alhairai, haka nan kuma mutum kan iya fadawa cikin tarkon shaidan wanda hakan kan yi sanadiyar jawo masa sharrori a cikin rayuwarsa.
3 – Yin afuwa da yafewa na daya daga cikin dabi’u na annabawan Allah da waliyyansa da sauran salihan bayi.
Aya ta (101) surat Yusuf
رَبِّ قَدْ آتَيْتَنِي مِنَ الْمُلْكِ وَعَلَّمْتَنِي مِن تَأْوِيلِ الأَحَادِيثِ فَاطِرَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ أَنتَ وَلِيِّي فِي الدُّنُيَا وَالآخِرَةِ تَوَفَّنِي مُسْلِماً وَأَلْحِقْنِي بِالصَّالِحِينَ{101}
"Yã ubangijina lalle ne kã bã ni daga mulki, kuma kã sanar da ni daga fassarar lãbaru. Ya mahaliccin sammai da kasa! Kai ne Majibincĩna a dũniya da lãhira ka karbi raina inã musulmi, kuma ka riskar da ni ga sãlihai."
A cikin kura’ni mai tsarki an ambaci hukumomi biyu ne da aka yi, wato hukumar Fir’auna, wanda ya yi mulki na zalunci da girman kai tare da bautar da mutane, wanda yake kallon mutane da duk abin da suka mallaka a matsayin mallakinsa. Sai kuma hukumar annabi Yusuf (AS) wanda yake kallon cewa babu wani iko ko mulki sai na Allah, kuma mulkin da ya samu daga Allah ya samu a matsayin wata jarabawa gare shi, kuma ilimi da yake da shi da fassarar mafarki da yake yi duk ya san cewa Allah ne ya ba shi wannan ba dubararsa ba.
Annabi Yusuf (AS) wanda mulkin Masar yake hannunsa a lokacin yana mai kaskantr da kansa ga Allah yana mai rokonsa da ya karbi ransa yana mai mika wuya ga umurnin Allah, yana rokon Allah da sanya shi a cikin salihan bayansa bayan ya karbi ransa.
Irin wannan addu’a ta annabi Yusuf (AS) ta nuni ne da zurfin imaninsa da Allah madaukain sarki da kuma masaniyar da yake da ita kan mahaliccinsa, wannan ne ya sanya shi duk da mulkin da yake da shi, amma bai taba mantawa da Allah koda daidai da kyaftawar ido ba, bai taba mantawa da mutuwa da tashin kiyama ba saboda mulki, a kowane lokaci yana mai dogaro da Allah yana mayar da komai nasa ga Allah, yana mai neman taimako daga Allah, yana mai rokon Allah da ya karbi rayuwarsa a matsayin bawansa mumini, yana mai fatan Allah ya hada shi da bayinsa salihai masu tsarkin ruhi.
A nan za iya daukar darussa kamar haka :
1 – Dole ne mutum mumini ya rika tunanin karshen rayuwarsa wanda shi ne mafi muhimmanci a kan dukkanin abin da mutum ya yi a cikin rayuwarsa, haka nan kuma domin kiyaye imani da addini dole ne a hada da neman taimakon Allah.
2 – Karfin iko da mulki kan nisantar da mutum daga imani da tsoron Allah, sai wanda Allah ya kiyaye da kiyayewarsa.
3 – Wadanda suke mulki a kan mutane wajibi ne su sani cewa, mulkin da suke yi jarabawa ce ta Allah, domin kuwa Allah yana birbishin duk wani mai mulki a gidan duniya, a lahira kuma babu wani abu mai suna mulki sai mulkinsa shi kadai ne.
Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
Suratu Yusuf, Aya Ta 102-106 (Kashi Na 396)
Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Yusuf, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.
Aya ta (102) surat Yusuf
ذَلِكَ مِنْ أَنبَاء الْغَيْبِ نُوحِيهِ إِلَيْكَ وَمَا كُنتَ لَدَيْهِمْ إِذْ أَجْمَعُواْ أَمْرَهُمْ وَهُمْ يَمْكُرُونَ{102}
Wannan daga lãbarun gaibi ne, munã yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lõkacin da suke niyyar zartar da al'amarinsu, alhãli sunã yin mãkirci.
A cikin shirin da ya gabata an ji yadda kissar annabi Yusuf (AS) ta kawo karshe bayan zuwan mahaifansa da ‘yan uwansa a fadarsa da ke Masar, dukkanin wahalhalu da matsaloli da hassadar ‘yan uwansa da kuma bakin cikin mahaifinsa sun kawo karshe, domin kuwa Annabi Yusuf (AS) ya sake haduwa da mahaifansa bayan rabuwa mai tsawo, kuma ya hadu da su a lokacin da yake a kan wani babban matsayi da Allah ya kai shi, wanda kuma dukkan abin da ya faru a cikin abin da aka ji na kissar annabi Yusuf (AS) wani lamari ne na ubangiji da ya yi niyar jaraba bayinsa Yakub da Yusuf (AS) kuma sun ci wannan jarabawa ta ubangiji.
Wannan ayar mai aklbarka tana magana ne da manzon Allah (SAW) dangane da yadda ‘yan uwan Yusuf suka taro suna tattaunawa kan yadda za su ga bayansa, a lokacin babu wani wanda ya san hakan in ba Allah sai kuma su da suka kulla makircin, wannan na daga cikin labarai na gaibi wanda babu surkulle ko kage a cikinsu, Allah madaukakin sarki masanin gaibi ne baki daya.
Darussan koyo a nan su ne :
1 – Annabawan Allah suna sani abubuwa na gaibi ta hanyar wahayin da ubangiji ke yi musu, ba ta hanyar lissafe-lissafe na kokwanto ba, ko neman labarai daga bokaye ko matsafa. 2 – Duk abin da za a yi a boye a wajen Allah bayyane yake, a duk lokacin da Allah ya ga dama zai iya bayyana shi ko ya sani ya sani.
Ayoyi na (103) da (104) surat Yusuf
وَمَا أَكْثَرُ النَّاسِ وَلَوْ حَرَصْتَ بِمُؤْمِنِينَ{103} وَمَا تَسْأَلُهُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ إِنْ هُوَ إِلاَّ ذِكْرٌ لِّلْعَالَمِينَ{104}
103- Kuma mafi yawan mutãne ba su zama mãsu ĩmãni ba, kõ da kã yi kwadayin haka.
104- Kuma bã ka tambayar su wata lãdã a kansa. Shĩ bai zama ba fãce ambato dõmin halittu.
A nan kur’ani mai tsarki yana bijiro da wasu lamurra ne da suke da dangantaka da manzon Allah da kuma mutanen da yake kira zuwa ga shiriya, duk kuwa da cewa manzon Allah ya zo da mu’ujizoji da suke tabbatar da manzancinsa, amma da dama daga cikin mutane ba a shirye suke su karbi gaskiya ba.
A kan haka ne Allah yake sheda ma manzonsa cewa duk da irin fatar da kake da ita da kuma kwadayin da kake da shi na son ganin mutane sun imani da Allah da sakonsa wanda ka zo musu da shi, amma mafi yawansu ba shirye suke su yarda da kai ba. Ayar tana yi wa manzon Allah ishara da cewa kada ya yi zaton cewa mutane sun ki karbar sakonsa ne saboda ba su gane gaskiya ba ne, a a da dama dga cikinsu sun gane gaskiya ne, kuma ba a bukatar wata lada daga gare su idan sun yi imani, amma dai duk da haka sun zabi bata kan shiriya.
Darussan da za a dauka a nan su ne :
1 – Annabawan Allah sun fi kowa son ganin mutane sun shirya sun bi tafarkin Allah, wannan ne ya sanya suka fi kowa damuwa da kuncin zuciya idan suka ga mutane sun yi watsi da sakon Allah.
2 – Rashin yin imani daga akasarin mutane ba gazawar manzanni ba ce, a a hakan yana komawa ne ga zabin mutane su a kan kansu.
Aya ta (105) surat Yusuf
وَكَأَيِّن مِّن آيَةٍ فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ يَمُرُّونَ عَلَيْهَا وَهُمْ عَنْهَا مُعْرِضُونَ{105}
Kuma da yawa, wata ãyã a cikin sammai da kasa sunã shũdẽwa a kanta kuma sũ sunã bijirẽwa daga gare ta.
Wannan ayar ci gaban ayar da ta gabata ne, da ke yin ishara da mutanen suke juya baya daga barin sakon Allah da bijire wa annabawansa, inda take bayyana ma manzo cewa irin wadannan mutane suna ganin ayoyin Allah a cikin sammai da kasa, da suke tabbatar da samuwarsa, amma duk da hakan ba su yin imani, saboda haka kada manzon Allah ya sanya kansa cikin damuwa idan sun karyata shi.
Mutum yana haduwa da ayoyin Allah a koda yaushe a cikin rayuwarsa, wasu lokuta ayoyi ne a cikin sararin samaniyya, ta hanyar dubi a cikin halittun da Allah ya yi a sama wadanda dan zai iya riska, kamar taurari rana da wata da sauransu. Haka nan kuma a bayan kasa da mutum ke rayuwa a koina ayoyin ubangiji nwe da suke tabbatar da samuwarsa da karfin ikonsa da kuma kadaitakarsa.
Alkur’ani mai tsarki yana yi wa mutane hannunka mai sanda a kowane lokaci domin sanin ubangiji madaukakin sarki sani na hakika, ta yadda mutane za su bauta masa a matsayinsa na wansa ya cancanci bautarsu shi kadai ba tare da abokin tarayya ba.
Darussan da za a dauka a nan sune :
1 – Dukkanin abubuwan da Allah ya halitta da suke cikin duniya alamu ne da suke nuni da cewa akwai mahalicci da ya samar da su, daga cikin wadannan alamu kuwa har da dan adam kansa, wanda shi ne Allah ya fifita daga cikin dukaknin abubuwan da ya halitta a bayan kasa.
2 – Wanda ya rafkana mai yiwuwa wata rana ta zo da zai fadaka ya koma ga bin tafarkin gaskiya, amma wanda ya kauda kai da gangan, ba a shirye yake da yabi tafarkin gaskiya a rayuwarsa ba.
Aya ta (106) surat Yusuf
وَمَا يُؤْمِنُ أَكْثَرُهُمْ بِاللّهِ إِلاَّ وَهُم مُّشْرِكُونَ{106}
Kuma mafi yawansu ba su yin ĩmãni da Allah fãce kuma sunã mãsu shirka.
Ita ma wannan ayar ci gaban ayar da ta gabata ce, domin kuwa tana yin bayani ne dangane da yadda mutane suke juya baya da bijire wa sakon Allah, inda take yin ishjara da cewa ba ma kawai akasarin mutane ba su yin imani da Allah ba ne, a a hatta a cikin wadanda suka yi imanin, akwai wadanda suke hada Allah da wani abu daban a cikin lamurransu, inda sukan dogara da wasu abubuwa na daban maimakon dogara ga Allah, suna masu kudirce tsarki ga wadannan abubuwa na surkulle koma bayan Allah.
Ya zo a cikin ruwaya cewa, a cikin tafsirin wannan ayar mai albarka, Imam Rida yana cewa ; abin da ake nufi da shirka a cikin wannan ayar ba bautar gumaka ba ne, abin da ake nufi shi ne mayar da hankali ga wani abu wanda ba Allah ba tare da dogaro da shi maimakon Allah.
Imam Sadiq (AS) yana cewa ; shirka a cikin mutum tafi boyuwa a kan boyuwar motsin bakar tururuwa a kan bakin dutse a cikin duhun dare.
Darussan da za a iya dauka a nan su ne :
1 – Imani mataki-mataki ne, imanin da babu nakasu a cikinsa ko wani suerkulle kadan ne.
2 – Shirka ma mataki-mataki ce, bautar gumaka ita ce tafi zama bayyananniyar shirka, amma akwai boyayyar shirka wadda wata kila ma mutum ba ya ankara da ita, amma kuma shirka yake yi bai sani ba, kamar riya a cikin ayyukan ibada, a wasu wuraren an bayyanata da boyayyar shirka.
Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
Suratu Yusuf, Aya Ta 107-109 (Kashi Na 397)
Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Yusuf, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.
Aya ta (107) surat Yusuf
أَفَأَمِنُواْ أَن تَأْتِيَهُمْ غَاشِيَةٌ مِّنْ عَذَابِ اللّهِ أَوْ تَأْتِيَهُمُ السَّاعَةُ بَغْتَةً وَهُمْ لاَ يَشْعُرُونَ{107}
Shin sun amince cẽwa wata masĩfa daga azãbar Allah ta zo musu ko kuwa tãshin kiyãma ya zo musu kwatsam, alhãli sũ ba su sani ba?
A cikin shirin da ya gabata an ambaci cewa, Allah madaukakin sarki yana kwantarwa manzonsa rai da cewa, kada ya damu kansa idan mutanen da yake kira ba su yi imani da shi ba, domin kuwa ba su ma yi imani da Allah balantana manzonsa, bugu da kari hakanma ayar da ta gabata ta yi ishara da cewa hattama a cikin wadanda suka yi imani, akwai wadanda suke hada A ;lah da wasu abubuwa na shirme da surkulle, wanda kuma hakan yana cikin babin shirka da Allah.
A cikin wannan ayar ana umurtar manzon Allah (SAW) da ya gargadi kafirai da mushrikai cewa, idan ba su yi imani da Allah da manzonsa da ranar lahira ba, to ba su da tabbacin cewa azabar Allah ba za ta iya riskarsu a kowane lokaci ba, haka nan kuma kiyama za ta zo musu babu shiri, a lokacin kuma ba su da wani hanzari da za su gabatar wa Allah madaukakin sarki.
Darussan da za a iya dauka a nan su ne :
1 – Wadanda bai yi imani da Allah da manzonsa ba, ba ya da aminci a wajen Allah, ko da kuwa yana rayuwa ne cikin matakan tsaro mafi tsauri a duniya, idan Allah ya tashi kama shi matakan tsaro ba su amfanar da shi da komai ba.
2 – Tuna ranar tashin kiyama da azabar ubangiji, na sa mutum ya dawo cikin fadaka da nisantar sabo.
Aya ta (108) surat Yusuf
قُلْ هَـذِهِ سَبِيلِي أَدْعُو إِلَى اللّهِ عَلَى بَصِيرَةٍ أَنَاْ وَمَنِ اتَّبَعَنِي وَسُبْحَانَ اللّهِ وَمَا أَنَاْ مِنَ الْمُشْرِكِينَ{108}
Ka ce: "Wannan ce hanyãta; inã kira zuwa ga Allah a kan basĩra nĩ da wadanda suka bĩ ni, kuma tsarki ya tabbata ga Allah! Nĩ kuma, ban zama daga mãsu shirka ba."
A cikin wannan aya mai albarka, Allah madaukakin sarki yana umurtar manzonsa da ya bayyana ma mushrikai hakikanin tafarkinsa na tauhidi, wanda ya yi hannun riga da abin da su suke bi kuma suke kudircewa na daga shirka, tafarkin manzon Allah shi ne kadaita Allah a cikin bauta, bin umurninsa a cikin dukaknin lamurra na rayuwa, yin watsi da tafarkin surkulle da shirka, a kan wannan nemanzo yake yin kira shi da wadanda suka yi imani da shi, kuma ba manzon Allah da sauran muminai suna bin wannan tafarkin e tare da yin kira zuwa gare shi a kan basira da masaniya, kuma manzon Allah bai taba kasancewa a cikin mushrikai ba, kuma ba zai taba kasancewa a cikinsu ba.
Darussan koyo a nan su ne :
1 – Wadanda suke fadakar da mutane kan addini ne, wajibi ne su zama suna da masaniya kan abin da suke kira zuwa gare shi kafin kiran mutane.
2 – Fadakarwa da yin kira zuwa ga Allah aiki ne na mutane da babu tasirin shirka a cikinsu, ko kuma ba su taba cakuduwa da daudarta ba.
Aya ta (109) surat Yusuf
وَمَا أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ إِلاَّ رِجَالاً نُّوحِي إِلَيْهِم مِّنْ أَهْلِ الْقُرَى أَفَلَمْ يَسِيرُواْ فِي الأَرْضِ فَيَنظُرُواْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ وَلَدَارُ الآخِرَةِ خَيْرٌ لِّلَّذِينَ اتَّقَواْ أَفَلاَ تَعْقِلُونَ{109}
Kuma ba mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã wahayi zuwa gare su daga mutãnen alkaryu. Shin ba su yi tafiya a cikin kasa ba, dõmin su ga yadda karshen wadanda suka gabace su ya kasance? Kuma lalle ne gidan lãhira shĩ ne mafi alhẽri ga wadanda suka yi takawa? Shin bã ku hankalta?
Daya daga cikin abubuwan da masu musu da sakon Allag suke yin korafi a kansu shi ne, mene ne ya sanya Allah ba zai aiko wani mala’ika daga cikin mala’iku ya zo da sakonsa, maimakon haka sai ya turo mutum daga cikinsu wanda suke ganinsa daidai da su.
Wannan aya mai albarka tana ba su amsa da cewa, Dukkanin annabawan da suka gabaci manzon Allah (SAW) mutane ne da Allah ya yi musu wahayi daga cikin mutanen alkaryoyi, su duba tarihi kuma su yi yawo a bayan kasa domin sanin labarin wadanda suka gabace da kuma makomarsu, dukkanin annabawan da Allah ya aiko mutane ba mala’iku ba.
Wannan korafi yana zuwa ne domin gudu daga karbar gaskiya, koda mala’ika ya zo musu da gaskiya daga Allah ba za su bi shi, sai sun kawo wani abun na daban suna masu korafi a kansa. Muhimmi dai shi ne, imani da Allah da karbar gaskiya da kuma binta sau da kafa amfanin hakan na komowane ga masu imani, wadanda suka ji tsoron Allah suka kiyaye dokokinsa a rayuwarsu ta duniya, to a ranar lahira wadannan su ne ma su babban rabo a wajen Allah.
Darussan da za a dauka a nan su ne :
1 – Dukkanin annabawan Allah mutane ne da suka rayu a tsakanin mutane, amma kuma a lokaci guda su sun kasance mutane ne na gari masu kyawawan dabi’u a dukkanin rayuwarsu, domin su zama abin koyi ga sauran mutane baki daya.
2 – Tafiya zuwa wuraren tarihi domin sanin bayani kan makomar al’ummomin da suka gabata, yana da nasa tasiri wajen kara ma mutum masaniya da kuma tabbatar da abin da Allah ya fada a kansu.
3 – Yin amfani da hankali domin sanin tafarkin Allah da kuma gasgata annabawansa, na daga cikin manufar sakon annabawan.
Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
Suratu Yusuf, Aya Ta 110-111 (Kashi Na 398)
Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Yusuf, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.
Aya ta (110) surat Yusuf
حَتَّى إِذَا اسْتَيْأَسَ الرُّسُلُ وَظَنُّواْ أَنَّهُمْ قَدْ كُذِبُواْ جَاءهُمْ نَصْرُنَا فَنُجِّيَ مَن نَّشَاء وَلاَ يُرَدُّ بَأْسُنَا عَنِ الْقَوْمِ الْمُجْرِمِينَ{110}
Har a lõkacin da Manzanni suka yanke tsammãni, kuma suka yi zaton cẽwa an jingina su ga karya, sai taimakonmu ya je masu, Sa'an nan mu tsẽrar da wanda muke so, kuma bã a mayar da azãbarmu daga mutãne mãsu laifi.
Ayoyin da suka gabaci wannan sun yi ishara da cewa, Allah madaukakin sarki yana yin wahayi ga wasu daga cikin tsarkakan bayinsa zababbu a matsayin manzanninsa masu shiryar da sauran bayinsa, kuma suna yin wannan kira ne bisa basira da hikima kamar yadda Allah ya umurce su, amma mutane da dama suna yin musun sakonnin da annabawa suke zuwa da su daga Allah, suna karyata annabawa, suna cutar da su cutarwa.
Wannan ayar mai albarka tana cewa su annabawan Allah mutane masu tsayuwa daram kan tafarkin ubangiji, wani bala’i na duniya ko musiba ko cutarwa ba za ta iya sanya annabawa su bar tafarkin ubangiji ba, domin kuwa su suna imani ne yakini da ubangiji, kuma zukatansu sun damfaru da Allah, ta yadda shi ne ke da girma a cikin zukatansu ba wani abun halitta ba.
Saboda haka suna ci gaba da yin kira duk kuwa da cewa mutane suna karyata su suna cutar da su, amma suna nan daram kan bin umurnin Allah na kiran mutane zuwa ga tafarkin shiriya, ta yadda har sai sun fitar da tsammani daga shiriyar mutanensu, masu musu kan sakon Allah, da sukan ce suna jiran su ga abin da annabawa suke fadi na daga azabar Allah kan wadanda suka bijire ma sakonsa, sai taimakon Allah madaukakin sarki ya zio musu, a lokacin Allah ya kan tseratar da annabawansa tare da wadanda suka yi imani da su, wadanda su ne marassa rinjaye a mafi yawan lokuta, saura kuma fushin Allah da azabarsa su safka a kansu.
Misali a nan shi ne, annabi Nuhu (AS) yan ada cikin annabawan da suka kwashe tsawon shekaru suna kira zuwa g tafarkin ubangiji, inda ya yi shekaru dubu babu hamsin yana kira, amma ‘yan kadan ne suka karba kiran nansa, daga karshe kumaAllah ya tseratar da shi da muminai da suke tare da shi, ya kuma halakar wadanda suka kafirce masa baki daya.
Darussan da za a iya dauka anan su ne :
1 – Bayar da rata da jinkirtawa ga kafirai na daga cikin sunnonin Allah madaukakin sarki.
2 – A wasu lokuta azabar ubangiji kan safka a kan wadanda suka kafirce ubangiji tun a gidan duniya, kafin su je lahira.
3 – Mumini ba ya yanke kauna daga rahmar ubangiji, a kowane lokaci mumini yana tsakanin lamurra ne guda guda biyu, tsoron azabar ubangiji da kuma fatar samun rahamarsa.
Aya ta ( 111) surat Yusuf
لَقَدْ كَانَ فِي قَصَصِهِمْ عِبْرَةٌ لِّأُوْلِي الأَلْبَابِ مَا كَانَ حَدِيثاً يُفْتَرَى وَلَـكِن تَصْدِيقَ الَّذِي بَيْنَ يَدَيْهِ وَتَفْصِيلَ كُلَّ شَيْءٍ وَهُدًى وَرَحْمَةً لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ{111}
Lalle ne hakĩka abin kula yã kasance a cikin kissoshinsu ga masu hankali. Bai kasance wani kirkiran lãbãri ba, amma shi gaskatãwa ne ga abin da yake a gabaninsa, da rarrabẽwar dukan abũbuwa, da shiriya da rahama ga mutãne wadanda suka yi ĩmãni.
Wannan aya ta karshe a cikin surat Yusuf tana yin isharawa da cewa kissoshin da ke cikin kur’ani da suka hada har da kissar annabi Yusuf (AS) da ‘yan uwansa akwai ababen lura a cikinsu, duk da cewa shi kur’ani mai tsarki ba littafi ne na kissoshi ba kawai, amma ya kan kawo kissa domin koyar da darasi ga masu hankali daga cikin mutane, domin kuwa ba dukkanin mutane suke daukar darasi daga abin da suka ji na ilimi ko gargadi hannunka mai sanda kan wasu lamurra ba, wasu daga cikin mutane za su iya jin kissa amma ba su dauki darasi daga cikinta, sun dai ji lamari kawai kamar sauran labarai da suke ji kan abubuwan da suka wakana a tarihi.
Ayar ta ci gaba da yin nuni da cewa, ma’abota hankali da tunani su ne wadanda suke jin ayoyi daga littafin ubangiji kuma su fahimci cewa wannan ba maganar mutum ba ce, zance ne daga mahaliccin kowa da komai, su ne suke gane cewa kissoshin da aka ambata a cikin kur’ani mai tsarki ba kirkire ba ne, wahayi daga Allah madaukakin sarki zuwa ga manzonsa (SAW) domin kuwa kur’ani mai tsarki bai takaitu ba kawai da fadin labarai na al’ummomin da suka gabata ba, a cikinsa akwai ilmomi tattalin arziki, zamantakewa, siyasa, fasaha da sauran lamurra na rayuwar mutum.
Darussan da za mu dauka a nan su ne :
1 – Kissoshin da ke cikin kur’ani mai tsarki bayani ne kan abubuwa da suka faru tare da bayar da darasi ga sauran mutane ‘yan baya, ba tatsuniya ba ce ko shiftar wani mutum ce aka rubuta ba.
2 – Idan ma’abota hankali suka karanta kur’ani a nan tke suke gane cewa zancen Allah, kuma suna daukar darasi daga abin da suka ji daga al’ummomin da suka gabata kamar yadda kur’ani ya ambata.
3 – Duk da irin makircin da aka yi wa annabi Yusuf a cikin rayuwarsa, amma daga karshe Allah madaukakin sarki ya kare shi, kuma ya kai ga matsayi madaukaki a cikin al’umma.
Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.