Suratu Maryam, Aya Ta 1-5 (Kashi Na 520)
Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki ,tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa. Bayan kawo karshen bayani a cikin ayoyin suratul Kahfi yanzu kuma za mu fara bayani a cikin ayoyin suratul maryam kuma sura ta sha tara da aka sabkar da ita a birnin Makka kuma ta kumshi labarain Annabawa irinsu Zakariya,Isa ,Yahaha ,Ibrahima,Isma'ila da Idrisa (AS). Wani abin mamaki bayan Maryam babu wata sura da aka bata sunan mace a cikin surorin kur'ani, kuma za mu shiga cikin shirin gadan gadan bayan mun saurarin wannan abu da aka yi mana tanadi a kan inji.
To madallah yanzu kuma za mu fara shirin ne da sauraren aya ta 1 zuwa ta 3 a cikin suratu Maryam kamar haka:
كهيعص{1} ذِكْرُ رَحْمَةِ رَبِّكَ عَبْدَهُ زَكَرِيَّا{2} إِذْ نَادَى رَبَّهُ نِدَاء خَفِيّاً{3}
1- K̃. H. Y. I . Ṣ̃. 2- Ambaton rahamar Ubangijinka ne ga BawanSa Zakariyya. 3- A lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, kira bõyayye.
Wannan sura kamar sauran surori ashirin da takwas tana farawa ne da hariffofin da Allah ne ya san abin da yake nufi da su. Annabi Zakariya yana daga cikin ayayan annabi Harun dan uwan annabi musa kuma Zakariya yana daga cikin annabawan bani Isra'ila wanda sau bakwai aka ambaci sunansa a cikin Kur'ani .Allah madaukakin sarki a cikin kur'ani yana kawo labarai wasu daga cikin annabawa da manzonni da kuma wasu daga cikin mutane da al'ummomi domin mu samu sani da ilimi da kuma uwa uba daukan darasi kan ayyukan da suka aikata na alheri ko akasin haka da hakan zai taimaka mana wajan gyara gaba a rayuwarmu. To wadannan ayoyi na bayani ne kan lutifi da falalar Allah ga bawansa Annabi Zakariya (AS) wannan a tsakaninsa da Ubangijinsa yake addu'ar Allah ya ba shi da kuma yana buya yana addu'ar ba tare da mutane sun san halin da yake ciki ba la'alla gudun izgilin wasu daga cikinsu cewa ku kalli wannan tsohon a karshen rayuwarsa ga farin gashi ya cika kansa amma yana neman Allah ya bashi da. Duk da cewa ya zo a cikin ruwaya mafi kyauwon addu'a ita ce wadda za a karata a hankali ba tare da an daga murya ba.
A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu kamar haka:
Na farko: ambaton sunaye da ayyukan waliyan Allah a cikin kur'ani wani salo ne mai amfani na koyarwa da Allah ke amfani a cikin kur'ani.
Na biyu:Kar mu sha'afa da yin addu'a a rayuwa domin wata babbar falala da lutifi da rahamar Allah ce a gare mu.
Yanzu kuma sai a saurari karatun aya 4 da ta 5 a cikin surar ta Maryam:
قَالَ رَبِّ إِنِّي وَهَنَ الْعَظْمُ مِنِّي وَاشْتَعَلَ الرَّأْسُ شَيْباً وَلَمْ أَكُن بِدُعَائِكَ رَبِّ شَقِيّاً{4} وَإِنِّي خِفْتُ الْمَوَالِيَ مِن وَرَائِي وَكَانَتِ امْرَأَتِي عَاقِراً فَهَبْ لِي مِن لَّدُنكَ وَلِيّاً{5}
4- Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, kashi na daga gare ni ya yi rauni, kuma kaina ya kunnu da furfura, kuma ban kasance marashin arziki ba game da kiranKa, yã Ubangiji!" 5- "Kuma lalle nĩ, na ji tsõron dangi a bãyãna, kuma mãtãta ta kasance bakarãriya! Sai ka bã ni wani mataimaki daga wajenKa."
Karkashin ruwayoyi Annabi Zakariya lokacin da tsufa ya kawo masa ga shi kuma ba shi da da sai ya shiga cikin damuwa kar wasu daga cikin mutanansa da ba su tsantsanta ba su bayyana kansu a matsayin wadanda za su gadai shi .Ganin haka sai ya dukufa yin addu'a da rokon Ubangijinsa da ya ba shi da salihi da zai ga dai shi da zai ci gaba da riko da hanyarsa bayansa .Amma irin wannan addu'ar da wuya a samu amsarta saboda shi kansa Zakariya kamar matarsa duk sun tsufa a zahirin dabi'a da wuya su samu da.Amma shi lamarin na Allah ne mai zartar da abin da ya ga dama kuma masani mahalicci mai zartar da dokoki da hikimarsa duk inda ya ga dama kamar yadda ya sa wuta mai zafin kuna ta zama sanyi maras cutarwa ga Annabi Ibrahima (AS). Shi mutum mai imani ya yarda da dokoki na kimiya da fasaha amma kudurar Allah ta zarta zahirin dabi'a kuma bukatarsa da kudurarsa ta zarta dokoki na zahirin dabi'a.Kuma lamari ne da ke a fili samin nasara kan wata bukata da ta zarta zahirin rayuwa ta dabi'a ita ce rungumar addu'a kuma ita addu'a ta alheri na karfafawa kamala da rayuwa ta zamantakewar jama'a sabanin bukatu da ba su dace ba na bukatun son zucciya. Bugu da kari addu'a sai an gama ta da kokari da himma. Kuma dole mu sani duk wani kokari da himmarmu sai Allah ya so ne zai amsa mana karkashin hikima da maslaharmu.
A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa kamar haka:
Na farko:Bayin Allah mumunai suna dogaro da rahamar Allah ne kuma babu wanda bay a fatar ga muwa da rahamar Allah sai tabebbe.
Na biyu:Allah yana da masaniya da bukatunmu amma yana amsa mana ne wasu lokutta ta hanyar addu'a da sanin bayunsa salihai da fadakar da mutum sanin yana bukatuwa da Allah ne ba wani bawansa ba.
Na uku: Da salihu babbar ni'ima ce daga Allah da dawwamar ayyukan alheri na mutum ko da bayan mutuwarsa ne.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
Suratu Maryam, Aya Ta 6-11 (Kashi Na 521)
Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki ,tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.
Za mu fara da sauraren aya ta 6 da ta 7 a cikin wannan sura ta Maryam:
يَرِثُنِي وَيَرِثُ مِنْ آلِ يَعْقُوبَ وَاجْعَلْهُ رَبِّ رَضِيّاً{6} يَا زَكَرِيَّا إِنَّا نُبَشِّرُكَ بِغُلَامٍ اسْمُهُ يَحْيَى لَمْ نَجْعَل لَّهُ مِن قَبْلُ سَمِيّاً{7}
6 - "Ya gãjẽ ni, kuma ya yi gãdo daga gidan Yãkũba. Kuma Ka sanya shi yardajje, yã Ubangiji!" 7 - (Allah Ya karba) "Yã zakariyya! Lalle ne Mũ, Munã yi maka bushãra da wani yãro, sunansa Yahaya. Ba Mu sanya masa wani takwara ba a gabãni."
Kamar yadda muka yi bayani a cikin shirin da ya gabata Annabi Zakariya (AS) ya damu kan bayan rasuwarsa dukiyarsa da sauran abubuwan da ya mallaka ya fada hannun wadanda ba su cancanta ba don haka ya roki Allah da ya ba shi da salihi to suma wadannan ayoyi ya yin nuni da magadan Ali Yakuba domin matar Annabi zakaiya daga zuriyar Annabi Suleiman ne kuma daya daga cikin yayan Yahuda dan Yakuba da ya gaji dukiya mai yawan gaske kan haka Zakairiya ya ke tunanin wanda zai gadai shi da zai tafiyar da wannan dukiya ta hanyar Allah amma idan ta fada hannun fasiki wanda bai cancanta ba zai sanya ta cikin hanyar bata da fasadi da gurbata al'umma. Kan wannan dalili ne a ci gaba da addu'ar da yake yi ya roki Allah da ya ba shi da salihi da zai gadai shi wanda yake son Allah ,Allah ma yana sonshi .Sai dai wani hamzari wasu masu fassarar kur'ani suna ganin magadin da Zakariya yake nufi a cikin wannan aya matsayin annabci ne ba na dukiya ba amma ana iya cewa nufinsa yana iya kumsar dukan ma'anonin biyu ,ma'ana ya son allah ya ba shi da da zai gadai shi ta fuskar dukiya da kuma annabci domin ci gaba da yada addinin Allah. Allah ya amsa addu'ar Zakariya da ba shi albishirin da salihi da zai gadai shi kuma annabi kuma Allah ne da kansa ya zabarwa wannan da nasa suna kuma tun yana karami ya ba shi matsayin annabta ,yahya tun yana karamin yaro yana da hankali da kwalluwa da hazaka ba iyaka kuma ya rayu cikin wani yanayi da sharadi na musamman da yin bulaguro kuma bai taba yin aure ba kamar yadda shi ma Annabi Isa bai taba yin aure ba har karshen rayuwarsu.
A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa kamar haka:
Na farko:Son samin da wani buri da bukatar kowane mutum a dabi'ance kuma bukatar da daga Allah bai yi hannun riga da matsayin annabci ba.
Na biyu:Mu yi dogon tunani da nazari kafin mu sanyawa yayanmu suna domin shi suna alama ce da al'ada da akida da bukatar mutum.
Sai kuma a saurari karatun aya ta 8 da ta 9 a cikin surar Maryam:
قَالَ رَبِّ أَنَّى يَكُونُ لِي غُلَامٌ وَكَانَتِ امْرَأَتِي عَاقِراً وَقَدْ بَلَغْتُ مِنَ الْكِبَرِ عِتِيّاً{8} قَالَ كَذَلِكَ قَالَ رَبُّكَ هُوَ عَلَيَّ هَيِّنٌ وَقَدْ خَلَقْتُكَ مِن قَبْلُ وَلَمْ تَكُ شَيْئاً{9}
8- Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Yãya wani yãro zai kasance a gare ni, alhãli kuwa mãtãta ta kasance bakarãriya, kuma gã shi nã kai ga matuka ta tsũfa?" 9 - Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinka Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauki ne, kuma hakĩka Na halitta ka a gabãnin haka, alhãli ba ka kasance kõme ba."
Duk da cewa Zakariya da kansa ne ya bukaci Allah da ya bashi da amma bai san ta yaya ne wannan buri nasa zai cika shin za a maida shi da matarsa matasa kafin su samu dan ko kuma a wannan hali da yanayi na tsufa da kasawa ne Allah zai ba su wannan da mai suna Yahya.Wadannan tambayoyi da mamaki da Zakariya yake bai sabawa matsayinsa na Annabtaka ba dalili ta kowane hali ilimin Annabawa da manzonni yana da iyaka ba su da masaniya kan gaibi sai abin da Allah ya sanar da su kuma sun yi imani abin da Allah ya so ne yake zartarwa.Kuma kudura da irada da dokoki na dabi'a suna hannu da ikonsa cikin hikima yana zartar da abin da yaga dama.
A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa kamar haka:
Na farko:Mace ko namiji da bas u hiafuwa ko ba su da ba kar su yi kasa a guiwa domin rahamar Allah da lutifinsa na nan kamar yadda ya bawa dayawa daga cikin masu irin wadannan matsaloli yaya.
Na biyu:idan muka yi nazari a cikin abubuwan da Allah ya halitta zai kawa da duk wani shakku kan gudura da iradar Allah.
Sai kuma karatun aya ta 10 da 11 a cikin suratul Maryam:
قَالَ رَبِّ اجْعَل لِّي آيَةً قَالَ آيَتُكَ أَلَّا تُكَلِّمَ النَّاسَ ثَلَاثَ لَيَالٍ سَوِيّاً{10} فَخَرَجَ عَلَى قَوْمِهِ مِنَ الْمِحْرَابِ فَأَوْحَى إِلَيْهِمْ أَن سَبِّحُوا بُكْرَةً وَعَشِيّاً{11}
10 - Ya ce: "Yã Ubangijina! Ka sanya mini alãma." Ya ce: "Alamarka ita ce ka kãsa yi wa mutãne magana a darũruwa uku daidai." 11 - Sai ya fita a kan mutãnensa daga masallãci, sa'an nan ya yi ishãra zuwa gare su da cẽwa, "Ku yi tasbĩhi sãfe da yamma."
Karkashin hujjar da wasu masu sharhi suka bayyana,Zakariya domin ya banbance maganar da ya ji shin wahayi ne daga Allah ko yaudara ce daga shaidan sai ya bukaci Allah da ya nuna masa wata alama sai amsa ta zo masa cewa ya kama bakinsa kar ya yi magana sai zikiri ba ya magana da kowa sai ibadodi da kiransu zuwa ga ambaton Allah da salla dare da rana a tsawon kwanaki uku sai ishara irin ta kuramai.
A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa kamar haka:
Na farko:mu sani gabobinmu da duk wani abin da muke da shi mallakin Allah ne komin lafiyarmu sai ya so ne za mu aikata wani abu da gabobinmu.
Na biyu:Ambato da ibada ga Allah dole su kasance a kullum ba wai wani lokaci mai gushewa ba ko dare ko rana dole mu bautawa Allah da gode msa da kuma ambatonsa.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
Suratu Maryam, Aya Ta 12-17 (Kashi Na 522)
Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.
Za mu fara tare da sauraren karatun aya ta 12 da 13 a cikin wannan sura ta Maryam:
يَا يَحْيَى خُذِ الْكِتَابَ بِقُوَّةٍ وَآتَيْنَاهُ الْحُكْمَ صَبِيّاً{12} وَحَنَاناً مِّن لَّدُنَّا وَزَكَاةً وَكَانَ تَقِيّاً{13}
12- Yã Yahaya! Ka kãma littãfi da karfi. Kuma Muka bã shi hukunci yanã yãro. 13- Kuma (Muka sanya shi) abin girmamãwa daga gunMu, kuma mai albarka, kuma ya kasance mai dã'ã da takawa.
A cikin shirin da ya gabata mun bayyana cewa; Allah ya karbi da amsa bukatar Annabi Zakariya (AS) dab a shi da a daidai lokacin da tsufa da kasawa ya kama shi da matarsa inda ya ba su da salihi mai sunan Yahya to wadannan ayoyi na cewa: ne Allah madaukakin sarki mai hikima ya bawa wannan da na zakariya hankali da hazaka da hikima ga tsarki abin kaunar kowa. Har ila yau Allah ya umarce shi day a yi riko da littafin lokacinsa wato Attaura da aiki da ita wajan bayyana shika-shikan shari'a da ke cikin wannan littafi na Attaura.Sai dai abin lura wannan umarni ba wai kawai ya kebanta da Annabi Yahya (AS) a'a ana nufin kowa a wancan lokaci kamar sau tari Allah ke bukatar mabiya annabawa da manzonni da su yi aiki da riko da gaskiya da littafan day a sabkar da aiki da ilimi da aiki kan tafarki na gari ta hanyar umurtar Annabawa da manzonni kai tsaye alhali dam u duka ake nufi.
A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa kamar haka:
Na farko:Annabawa da mabiyansu an umarce mu baki daya da mu yi aiki da hukumce-hukumce na addini da riko da gaskiya da kare addinin Allah a tsakanin jama'a da al'ummomi.
Na biyu:nuna kauna da saura da tausayawa juna da nuna rahama ga bayun Allah wata falala ce daga Allah kuma wata siffa ce da Allah ke bawa waliyansa fiye da kowa.
Sai kuma a saurari karatun aya ta 14 da 15 a cikin wannan sura ta Maryam
وَبَرّاً بِوَالِدَيْهِ وَلَمْ يَكُن جَبَّاراً عَصِيّاً{14} وَسَلَامٌ عَلَيْهِ يَوْمَ وُلِدَ وَيَوْمَ يَمُوتُ وَيَوْمَ يُبْعَثُ حَيّاً{15}
14 - Kuma mai biyayya ga mahaifansa biyu, kuma bai kasance mai girman kai mai sãbo ba. 15 - Kuma aminci ya tabbata a gare shi a rãnar da aka haife shi da rãnar da yake mutuwa da rãnar da ake tãyar da shi yanã mai rai.
Allah madaukakin sarki a cikin wannan ayoyi ya yi nuni da wasu abubuwa da ya kebantu da annabi Yahya (AS) a tsakaninsa da Mahaliccinsa mai yawan bauta ne,tsakaninsa da uwayansa mai yawan biyayya ne da ladabi, a tsakaninsa da mutane ma'abucin tausayi da kauna da fahimta ba mai girman kai da danniya ba ne.
Ci gaban ayoyin na nuni da abubuwa guda uku na rayuwar kowa ne mutum da cewa: tsaro da kwanciyar hankali da lafiya da ya ba mu a gurare guda uku kamar haka: lokacin haifarmu da shigowa wannan duniya domin yin sabuwar rayuwa. Sai kuma lokacin marin wannan duniya da karbar raanmu ta hanayr mutuwa. Sai kuma tayar da mu a ranar kiyama ranar sakamako da adalcin Allah a ranar da kowa za a tayar da shi domin yin rayuwa ta hakika.
A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa kamar haka:
Na farko: Kyautatawa uwaye wani nauyin ne da ke kan kowa a kowane lokaci da yanayi a rayuwa ta zamantakewa matukar babu sabon Allah a ciki.Kominmatsayi da daukakar mutum dole ya yi biyayya da kyautatawa ma'aifansa.
Na biyu:Rayuwar mai kyau da mutuwa na kwantar da ruhi da nutsuwa kuma wani lamari ne da ya kebanta da mutanan kirkiri kuma ana samunsu ne ta hanyar kyautatawa uwaye da bautawa Allah da kaucewa aikata sabo kuma duk wanda ya yi haka ko wane ne zai samu rayuwa mai inganci a wannan duniya da lahira.
Sai kuma karatun ayayo na 16 da 17 a cikin suratul Maryam:
وَاذْكُرْ فِي الْكِتَابِ مَرْيَمَ إِذِ انتَبَذَتْ مِنْ أَهْلِهَا مَكَاناً شَرْقِيّاً{16} فَاتَّخَذَتْ مِن دُونِهِمْ حِجَاباً فَأَرْسَلْنَا إِلَيْهَا رُوحَنَا فَتَمَثَّلَ لَهَا بَشَراً سَوِيّاً{17}
16 - Kuma ka ambaci Maryamu a cikin Littãfi, a lõkacin da ta tsallake daga mutãnenta a wani wuri, a gẽfen gabas. 17- Sa'an nan ta riki wani shãmaki daga barinsu. Sai Muka aika rũhinMu zuwa gare ta. Sai ya bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaci.
Bayan ayoyin da suka yi bayani kan rayuwar Annabi Yahya (AS) a takaice sai wadannan ayoyi suka fara bayani dangane da rayuwar Annabi Isa (AS) saboda rayuwar wadannan annabawa biyu na kama da juna ta bangarori da dama.Da farko ayar ta fara magana ne da ma'aikin Allah ,annabin rahama da cewa; a cikin wannan littafi kuma a cikin wannan sura mai suna Maryam ka bada labarin Maryam da ruhi mai tsarki da yadda Maryam ta kauracewa gidansu da yin I'itikafi a Masallacin Kudus mai tsarki.ta nisanta kanta da sauran da killace kanta a wani guri na musamman domin samun damar bautawa Allah hankali kwance cikin nutsuwa.Karkashin umarnin Allah, dan aiken Allah mala'ika makusanci da daukaka a gurin Allah yayi shigar mutum da bayyana a gurin Maryam ganisa ya firgita ta da mamakin yadda mutum ya shigo gurin da ta kebance domin bautawa Allah. To a ci gaban ayar za mu fahimci abubuwan da suka faru .
Amma a cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa kamar haka:
Na farko:domin isa ga kamala da matsayi mai girma na ma'anawiya babu banbanci tsakanin mace da namiji kawai annabci wani nauyi ne da Allah ya daukawa mazaje amma babu wani banbanci a matsayi tsakanin mace da namiji matsayi daya suke kowa yana iya kaiwa kololuwa matsayi da daukaka daidai da ayyukansa.
Na biyu:Jibra'ila da sauran mala'iku bayan annabawa da amnzonni na iya bayyana ga kowa da yi masa magana.
Na uku:Mace na iya yin wani aiki na girma da zarki da har mala'ika zai kai mata ziyara ta ban girma.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
Suratu Maryam, Aya Ta 18-23 (Kashi Na 523)
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na hannunka mai sanda shirin wanda yake yin dubi cikin wasu ayoyin alkur'ani don su zama fitila a cikin rayuwarmu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.
- .
To bari mu fara shirimmu na yau tare da sauraron karatun aya ta 18 da kuma ta 19 daga cikin suratu Maryam kamar haka.
قَالَتْ إِنِّي أَعُوذُ بِالرَّحْمَن مِنكَ إِن كُنتَ تَقِيّاً{18} قَالَ إِنَّمَا أَنَا رَسُولُ رَبِّكِ لِأَهَبَ لَكِ غُلَاماً زَكِيّاً{19}
18- Ta ce: "Lalle ni inã nẽman tsarin Mai, rahama daga gare ka, idan ka kasance mai tsoron Allah ne." 19-Ya ce: "Abin sani kawai, ni Manzon Ubangijinki ne dõmin in bãki wani yãro tsarkakke."
َA cikin shirimmu da ya gabata mun bayyana yadda Maryamul Batul (s)mahaifiyar Annabi Isa (a) take itikafi a cikin baitul mukaddasi ta shagaltu da bautar Allah a wata kusuruwa na masallacin a lokacinda wani matashi ya bayyana a gabanta. Ganin wannan matashi ya tada hankalinta so sai.Don haka sai ta nemi tsari daga Allah na ya kiyayeta daga wannan matshin.
Don haka wadannan ayoyin sun ci gaba da bayyana cewa, a lokacinda ta ga matashi sai ta ce ina neman tsarin ubangiji mai rahama daga gareka idan kai mai tsoransa ne.
Sanna shi kuma ya bata amsa da cewa ai ni ba mutum ba ne, ni manzon ubangijinki ne, mala'ika don in baki da mai tsarki.
Wannan ya nuna cewa mata masu kamun kai basa amincewa su kebantu da wadanda ba muharramansu ba, abinda ya yi karanci a cikin matammu na lokacin da muke ciki.
Muna iya daukan darussa a cikin wadannan ayoyi kamar haka.
1. Neman tsarin Allah daga sharrin shaitanu da kuma ayyukan shaidana sunna ce ta alkur'ani da kuma salihan bayin Allah. 2. Mala'ikun Allah ba saukar da wahayi kai dai ne aikinsu ba, suna aiwatar da wasu ayyuka wadanda Ubangiji ya umurcesu kuma suna Magana da wadanda ba mala'iku ba.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 20 da kuma 21 daga cikin saratu Maryam kamar haka.
قَالَتْ أَنَّى يَكُونُ لِي غُلَامٌ وَلَمْ يَمْسَسْنِي بَشَرٌ وَلَمْ أَكُ بَغِيّاً{20} قَالَ كَذَلِكِ قَالَ رَبُّكِ هُوَ عَلَيَّ هَيِّنٌ وَلِنَجْعَلَهُ آيَةً لِلنَّاسِ وَرَحْمَةً مِّنَّا وَكَانَ أَمْراً مَّقْضِيّاً{21}
20-Ta ce: "A inã yãro zai kasance a gare ni alhãli kuwa wani mutum bai kusance ni ba, kuma ban kasance kãruwa ba?" 21-Ya ce: "Kamar haka Ubangijinki Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauki ne. Kuma dõmin Mu sanya shi wata alãma ga mutãne, kuma wata rahama ce daga gare Mu.' Kuma abin yã kasance wani al'amari yankekke."
Da farko Maryam (s) ta tsorata da ganin wannan matashin, amma bayan ya bayyana mata cewa shi manzon Allah zuwa gareta don ya bata da mai tsarki, sai ta yi mamakin yadda macce watta bata taba aure ba zata haihi sannan ita tana rayuwar ce ta kauracewa mutane, ta shagaltu da bautar Ubangijinta.
Amma mala'ikan ya bata amsa da cewa hakan wani al'amari yankekke daga wajen Ubangijinki sai ya faru. Sannan shi wannan yaron rahamar Ubangijinki ne kuma aya ce daga cikin ayoyinsa.
Allah ya rika ya hukunta cewa maryam (s) wacce bata taba yin aure ba zata haifi Annabi Isa (a) don ya zama mujiza kuma aya daga cikin ayoyinsa. Wannan aikin mai saiki ne a wajensa.
1. Manufar Ubangiji ta rinjayi duk wasu dalilai na dabi'a, idan ya yi nufin wani abu sai ya tabbata, ba bu abinda zai iya hana shi faruwa. 2. Samuwar annabawa a cikin al'umma rahama ce daga ubangiji ga mutanen. Kamar yadda annabi Isa (a) ya kasance a cikin mutanennsa, yana shiryatar dasu zuwa ga sanin Allah da kuma biyayya a gareshi.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 22 da kuma ta 23 daga cikin suratu Maryam kamar haka.
فَحَمَلَتْهُ فَانتَبَذَتْ بِهِ مَكَاناً قَصِيّاً{22} فَأَجَاءهَا الْمَخَاضُ إِلَى جِذْعِ النَّخْلَةِ قَالَتْ يَا لَيْتَنِي مِتُّ قَبْلَ هَذَا وَكُنتُ نَسْياً مَّنسِيّاً{23}
22-Sai ta yi cikinsa, sai ta tsallaka da shi ga wani wuri mai nĩsa. 23-Sai nãkuda ta kai ta zuwa ga wani kututturen dabĩniya, ta ce "Kaitona, dã dai na mutu a gabãnin wannan kuma na kasance wani abu wulakantacce wanda aka manta da shi!"
Tare da ikon Allah, mala'ika ya hura iska a kanta sai gas hi tad au cikinsa, alamun ciki wanda ya kai tsawon watanni 9 suka bayyana a wajenta. Wannan ya tilasta mata barin wurin bautar, don ta kaucewa haduwa da mutane, ta shiga dajin Allah.
Sannan a cikin dan karamin lokaci, lokacin haihuwarsa ya karato. Daga karshe nakuda ta tilasta mata tsayuwa kusa da wata kututturen dabino. Amma tana ta tunanin ya ya zata fuskanci mutane bayan haituwarta?. Wace amsa zata basu idan sun tuhumeta da rashin tsarki.? Wannan tunani ya kai tana burin, ina ma da ace Allah ya kasheta, an ma manta da ita a kan abinda zata fuskanta na tuhumar mutane da rashin tsarki bayan haihuwa.
Muna iyadaukan darussa a cikin wadannan ayoyi biyu kamar haka.
1. Duk da cewa daukan ciki da haihuwa suna da wahala ga mata, amma tattare da su akwai albarka da kuma alkhairai masu yawa. 2. A wani bayin Allah salihai, mutuwa ta fiye masu rayuwa cikin rashin tsariki. Rayuwa da mutunci ya fiye masu alkhairi.
Masu saoraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yai sai kuma wani lokaci idan Allah ya kaimu.
Suratu Maryam, Aya Ta 24-28 (Kashi Na 524)
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na hannunka mai sanda shirin wanda yake yin dubi cikin wasu ayoyin alkur'ani don su zama fitila a cikin rayuwarmu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.
- .
To bari mu fara shirimmu nay au tare da sauraron aya ta 24 da kuma ta 25 daga cikin surar Maryam kamar haka.
فَنَادَاهَا مِن تَحْتِهَا أَلَّا تَحْزَنِي قَدْ جَعَلَ رَبُّكِ تَحْتَكِ سَرِيّاً{24} وَهُزِّي إِلَيْكِ بِجِذْعِ النَّخْلَةِ تُسَاقِطْ عَلَيْكِ رُطَباً جَنِيّاً{25}
24-Sai (yãron da ta haifa) ya kira ta daga karkashinta, "Kada ki yi bakin ciki! Hakĩka Ubangijinki Ya sanya wani marmaro a karkashinki. 25-"Kuma ki girgiza kututturen dabĩnon, nunannen dabino zasu zuba a kanki,"
A cikin shirimmu da ya gabata mun bayyana cewa mala'ika Jibril ya bayyana da sifar matashi a gaban maryam (s) kuma tare da ikon Allah ta dauki cikin Annabi Isa (a) nan take, ciki wanda ya kai tsofan watanni 9. Daga nan ya zama mata dole ta bar wurin bautarta maimakon ta shiga gari sai ta kama hanyar daji, har sai da nakuda ta tilasta mata tsayawa kusa da wani kututturen dabino, tana burin mutuwa don tsananin bakin ciki.
Wadan nan ayoyi suna bayyana cewa kafin ta haife shi, annabi Isa (a) tun yana cikin mahaifuyarsa kafin faduwarsa ya fara Magana da mahaifiyar, don ya kwantar fa hankalinta, daga bakin cikin da take ciki. yana ce mata, "mahaifiya ta kada ki yi bakin ciki!
Duk da cewa babu wanda zai taimaka maki, amma Allah ya nan tare da ke zai samarda idaniyar ruwa mai gudu nan karkashin kafafuwarki sannan dabino nunanu daga kanki.
A wani hadisi daga amirul muminina Aliyu ban Abitalib (a) daga manzon Allah (s) yana cewa"abinci mafi amfani ga mace mai ciki shi ne dabino rudabi, hakama abinda zata cid a farko bayan haihuwarta ya kasance dabono rudabi.
Muna iya daukan darussa daga cikin wadannan ayoyi biyu kamar haka.
1. Mata masu ciki suka bukatar kwanciyar hankali da nutsuwa, don haka iyalanta yakamata su yi kokarin kwantar mata da hankali gwargwadon iyawa.
2. Dabino na daga cikin abinci wadanda Allah ya ke horewa bayinsa.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 26 daga cikin surar Maryam kamar haka.
فَكُلِي وَاشْرَبِي وَقَرِّي عَيْناً فَإِمَّا تَرَيِنَّ مِنَ الْبَشَرِ أَحَداً فَقُولِي إِنِّي نَذَرْتُ لِلرَّحْمَنِ صَوْماً فَلَنْ أُكَلِّمَ الْيَوْمَ إِنسِيّاً{26}
26-"Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idãnunki. To, idan kin ga wani aya daga mutãne, sai ki ce, 'Lalle nĩ, na yi alwãshin azumi dõmin Mai rahama sabõda haka bã zan yi wa wani mutum magana ba."
Maganan annabi Isa (a) ga mahaifiyarsa tun kafin ta haife shi ya, kwantar da hankalinta kuma ya dauke mata tunanin wahalar haihuwa sai dai abinda ya saura shi ne yadda zata tunkariu mutane da tuhumar rashin tsarki. Sai aka yi mata ilhamin cewa kada ki yi Magana da kowa, ki fara azumin magana kada ki amsa tambayar kowa har sai Allah ya yi maki mafita.
Muna iya daukan darussa daga cikin wannan ayar kamar haka.
1. Don samun mafita daga cikin wasu matsalolin rayuwa bayin Allah sukan yi nazari ga Allah. 2. Wani lokacin yin shiru kan tuhumar da akewa mutum ya dacewa, har zuwa lokacinda gaskiya zata yi halinta.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 27 da kuma 28 daga cikin suratu Maryam kamar haka.
فَأَتَتْ بِهِ قَوْمَهَا تَحْمِلُهُ قَالُوا يَا مَرْيَمُ لَقَدْ جِئْتِ شَيْئاً فَرِيّاً{27} يَا أُخْتَ هَارُونَ مَا كَانَ أَبُوكِ امْرَأَ سَوْءٍ وَمَا كَانَتْ أُمُّكِ بَغِيّاً{28}
27-Sai ta je wa mutãnenta tanã auke da shi. Suka ce: "Yã Maryamu! Lalle ne, hakĩka kin zo da wani abu mai girma! 28-"Yã 'yar'uwar Hãrũna! Ubanki bai kasance mutumin alfãsha ba, kuma uwarki ba ta kasance kãruwa ba."
Bayan haihuwarta ba zai yu ta ci gaba da zama a daji ba, dole ta kama hanyarta ta koma cikin mutane. Dama ba bu wani abin mamaki idan sun tuhumeta da rashin tsarki. Sai dai tuhuma ce ga mafi tsarkin mata a zamanin, kamar yadda zalihau ta tuhumi mafi tsarkin mazaje na lokacinta da rashin tsarki wato annabi Yusuf (a). Wadan nan abubuwan da suka faru a tarihi darasi ne a garemu wajen gaggawa wajen tuhumar mutane kan abinda bai tabbata a fili ba. Saud a dama jahilai a cikin alumma sukan tuhumi mutane don hasada ko kiyayya kan abinda bai da gaskiya ko kadan.
Muna iya daukan darussa a cikin wadannan ayoyi kamar haka :
1. Sau da dama mutane sukan yi gaggauta wajen tuhumar wasu, ba tare da bincike wanda ya dace ba. Don haka mu yi hankali. 2. Iyaye ko sun yarda ko sun ki yarda, su na da laifi cikin irin halayen da yayansu zasu tashi dasu. Don haka dole ne iyaye su yi matukan kokari don ganin sun tarbiyantar da yayansu bisa abinda zai wanzar da mutuncinsu. 3. Mummunan aiki daga ko ina ya fito bai da kyau, amma ya fi muni idan daga babban gida ne, gidan tsarki da annabta.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya cikin shirimmu.
Suratu Maryam, Aya Ta 29-34 (Kashi Na 525)
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na hannunka mai sanda shirin wanda yake yin dubi cikin wasu ayoyin alkur'ani don su zama fitila a cikin rayuwarmu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.
- .
To bari mu fara shirimmu na yau tare da sauraron karatun aya ta 29 da kuma ta 30 daga cikin surar Maryam kamar haka.
فَأَشَارَتْ إِلَيْهِ قَالُوا كَيْفَ نُكَلِّمُ مَن كَانَ فِي الْمَهْدِ صَبِيّاً{29} قَالَ إِنِّي عَبْدُ اللَّهِ آتَانِيَ الْكِتَابَ وَجَعَلَنِي نَبِيّاً{30}
29-Sai ta yi ishãra zuwa gare shi, suka ce: "Yãya zã mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfiar tsumma yanã jãrĩri?" 30-Ya ce: "Lalle ne, nĩ bãwan Allah ne Allah Yã bã ni Littãfi kuma Ya sanya ni Annabi."
A cikin shirimmu da ya gabata mun bayyana vewa maryam (a) ta koma cikin mutane da jaririnta a cikin tsumman goyo, kuma ta yi azumin magana, ma'ana bata Magana ga kowa kamar yadda aka umurceta.
Don haka alokacinda mutanenta suka tambayeta yadda ta haihu amma ba tare da tana da aure ba, kuma gashi ita yar annabi ce, ta ya ya zata bata tsarkin gidansu da kawo masu rashin tsarki a cikinsu.?.
Amma maryam bata bada amsa ba, sai dai tana ishara zuwa ga jaririn na ta. Ko wa ya san cewa jaririn baya iya yin Magana, ta ya ya zata yi nuni zuwa gareshi? Wannan ma wani Karin laifi ne da tayi masu, don ai itace akewa Magana ba jariri ba, sannan jariri cikin tsumman goya a aladance baya magana.
Amma tare da ikon Allah sai gashi jiririn nata ya buda baki yana Magana dasu yana hannun mahaifiyarsa. Ya ce masu ni bawan Allah wanda Allah ya aiko shi a matsayin manzo ga bani isra'ila, kuma ya bani littafi wand azan shiratarda su das hi. Ya sanya albarka a cikin lamari.
Annabi Isa (a) ya bayyana kansa a matsayin bawan Allah, amma mabiyansa daga baya sun wace gonad a iri suna daukansa a matsayin dan Allah-tsirki ya tabbata a gareshi. Wannan hatsarin na daukar mutum a matsayin Allah yana barazana ga dukkan addinai.
Muna iya daukan darussa a cikin wadannan ayoyi kamar haka.
1. Idan gaskiya ne mun tsarkake kammu daga sabo to, Allah bai zai gagare shi ba ya bayyana tsarkinmu ta hanyoyi da dama ga wadanda basu sani ba, idan akwai buakatar su sanin.
2. Samun matsayin annabci da manzanci,ludufin ubangiji ne ga bayinsa salihai.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ya 31 da kuma 32 daga suratu Maryam kamar haka.
وَجَعَلَنِي مُبَارَكاً أَيْنَ مَا كُنتُ وَأَوْصَانِي بِالصَّلَاةِ وَالزَّكَاةِ مَا دُمْتُ حَيّاً{31} وَبَرّاً بِوَالِدَتِي وَلَمْ يَجْعَلْنِي جَبَّاراً شَقِيّاً{32}
31 -"Kuma Yã sanya ni mai albarka a inda duk na kasance kuma Ya umurce ni da yin salla da zakka matukar inã da rai." 32-"Kuma mai biyayya ga uwãta, kuma bai sanya ni mai kaushin zũciya ba marashin alhẽri."
Annabi Isa (a) yana hannun mahaifiyarsa ya yi Magana, ba kawai ya kare mahaifiyarsa daga tuhumar da ake mata ba, a'a ya ma tabbatarwa bani'isra'ila cewa shi annabi ne manzo. Ya zo da sabon littafi bayan Attaura. Kuma an umurceshi da sallah da bada zakka da kuma biyayya ga dukkan umurnin Allah.
Irin wannan bawan Allah dama zai kasance mai albarka, albarka wanda zai game ko ina a cikin mutanensa a cikin rayuwarsa da kuma bayan rayuwarsa.
Muna iya daukan darussa a cikin wadannan ayoyi kamar haka.
1. Sallah da bada zakka ibadu ne wadanda suka zo cikin sauran addinin sama . Basu kebantu da addinin musulunci ba.
2. Kyautatawa iyaye, musamman ga mahaifiya yana daga cikin halayen annabawa.
Yanzun kuma mu saurari karatun ayoyi na 33 da kuma 34 daga cikin suratu Maryam kamar haka.
وَالسَّلَامُ عَلَيَّ يَوْمَ وُلِدتُّ وَيَوْمَ أَمُوتُ وَيَوْمَ أُبْعَثُ حَيّاً{33} ذَلِكَ عِيسَى ابْنُ مَرْيَمَ قَوْلَ الْحَقِّ الَّذِي فِيهِ يَمْتَرُونَ{34}
33-"Kuma aminci ya tabbata a gare ni a rãnar da aka haife ni da rãnar da nake mutũwa da rãnar da ake tãyar da ni inã mai rai." 34-Wancan shi ne Ĩsã Dan Maryamu, maganar gaskiya wadda suke shakka a cikinta.
Banda wannan, annabi Isa (a) ya yi ishara kan rayuwarsa a nan duniya da mutuwarsa da kuma sake tashinsa a ranar kiyama. Wannan yana nuna cewa shima mutum ne, yana rayuwa kamar yadda ko wane mutum yake rayuwa yana mutuwa kamar yadda ko wace rai sai ta dandani mutuwa. Sannan Allah zai tada shi ranar kiyama kamar yadda zai tada kowa. Abinda yake da muhimmanci a cikin rayuwar bayin Allah shi ne amintar addininsu, kasancewa kan tafarkin Allah wacce babu karkata a cikinta.
Sai dai abin bakin ciki shine mutane da dama suna shakkar tafarkin annabawa , imam don jahilci ko kuma don son zuciya da mummunar manufa.
Wasu mutanen sun dauki annabawansu sun kaisu matsayin allantaka, a yayinda wasu kuma suka dawo da su kamar sauran mutane suna ganinsu wawaye ko kuma makaryata.
Gaskiyan al'amari annabawan Allah mutanene kamar ko wani mutum a halittarsu, amma Allah yana wahayi a garesu yana sanar da su abinda sauran mutane bazasu iya sani ba. Don su nunawa mutane tafarkin rayuwa mafi kyau.
Muna iya daukan darussa a cikin wadannan ayoyi kamar haka.
1. Mutuwa da kuma tashi a ranar kiyama na kowa da kowa ne, hatta annabawa da manzanni suna mutuwa kuma zasu tashi tare da sauran muatne a ranar kiyama.
2. Mutuwa da kuma tashi a ranar kiyama bas u ne abin damuwaba. Abinda damuwa shi ne halin da mutuwa zata riskeka. Shi yasa bayin Allah a ko yaushe suke rokon Allah kyekyawan karshe. Su mutu suna musulmi, suna masu mika wuya ga umurnin ubangijinsu.
3. Bayyan inda mabiya addanan da suka gabaci musulunci na daga cikin sakonnin da alkur'ani mai girma yake dauke da su.
Masu sauraro anan zamu dasa aya sai kuma wani ..
Suratu Maryam, Aya Ta 35-40 (Kashi Na 526)
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na hannunka mai sanda shirin wanda yake yin dubi cikin wasu ayoyin alkur'ani don su zama fitila a cikin rayuwarmu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.
- .
To bari mu fara shirimmu nay au tare da sauraron karatun aya ta 35 daga cikin surar Maryam kamar haka.
مَا كَانَ لِلَّهِ أَن يَتَّخِذَ مِن وَلَدٍ سُبْحَانَهُ إِذَا قَضَى أَمْراً فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُ كُن فَيَكُونُ{35}
35-Bã ya kasancẽwa ga Allah Ya riki wani dã. Tsarki ya tabbata a gare shi! Idan Yã hukunta wani al'amari sai kawai Ya ce masa, "Kasance." Sai ya dinga kasan cẽwa.
A cikin shirimmu da ya gabata mun yi maganar cewa annabi Isa (a) yana cikin zanin goyo ya kare tsarkin mahaifiyarsa kuma ya bayyana kansa a matsayin bawa daga cikin bayin Allah zai rayu kuma zai mutu kamar sauran mutane.
Wannan ayar tana Magana da wadanda suka daukaka annabi Isa (a) suka fidda shi daga matsayinsa na dan adam suka kaishi matsayin da, ga Allah, tsarki ya tabbata a gare shi da ya riki da.
Haihuwar annabi Isa (a) ba tare da yana da mahaifi ba, bas hi ne yake nuna cewa shi da ne ga Allah ba. Ai ubangiji idan yana so yana iya halittar mutum ba tare da yana da iyaye ba gaba daya. Kamar dai yadda ya halicci annabi Adam (a). Amma duk da haka ba wanda ya kirashi dan Allah. Kowa ya dauke shi a matsayin bawan Allah.
Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka.
1. Ubangiji mai iko ne bisa kome, duk sanda ya nufi abu sai abin ya kasance.
2. Dole ne a bayyana inda ahlul kitab suka karkace daga ikidar gaskiya da kuma hanyar da ta dace.
3. Dangantaka tsakanin Allah da sauran halittunsa, dangantaka ce ta mahalicci da halittunsa. Ba ta uba da da ba.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 36 daga cikin surar Maryam kamar haka.
وَإِنَّ اللَّهَ رَبِّي وَرَبُّكُمْ فَاعْبُدُوهُ هَذَا صِرَاطٌ مُّسْتَقِيمٌ{36}
36-"Kuma lalle Allah ne Ubangijina kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan shi ne tafarki madaidaici."
Wannan ayar tana bayyana zancen annabi Isa (a) inda yake cewa ni bawan Allah ne ubangijina ubangijinku, don haka kuma ku bauta masa shi kadai. Kada ku hada bautarsa da waninsa. Idan kunyi haka kuna kan tafarki madai daiciya.
Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka.
1. Akidar kiristoci na "trinity" ko iyayen giji ukku ba dai dai bane, ubangiji guda ne. Kuma shi kadai ne abin bauta.
2. Allah ne kadai ya cancanci bauta, shi ne mahaliccin halittu babu wanda ya cancanci bauta in banda shi. Ko kuwa wanin annabi ne.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 37 da kuma 38 daga cikin surar Maryam kamar haka.
فَاخْتَلَفَ الْأَحْزَابُ مِن بَيْنِهِمْ فَوَيْلٌ لِّلَّذِينَ كَفَرُوا مِن مَّشْهَدِ يَوْمٍ عَظِيمٍ{37} أَسْمِعْ بِهِمْ وَأَبْصِرْ يَوْمَ يَأْتُونَنَا لَكِنِ الظَّالِمُونَ الْيَوْمَ فِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ{38}
37-Sai kungiyõyin suka sãbã wa jũna a tsakãninsu. To, bõne ya tabbata ga wadanda suka kãfirta daga halartar yini mai girma. 38-Mẽne ne ya yi jinsu, kuma mẽne ne ya yi ganinsu a rãnar da suke zo Mana! Amma azzãlumai sunã a cikin bata bayyananna.
Wadannan ayoyi suna Magana kan rarraban kai da aka samu tsakanin kiristoci dangane das hi annabi Isa (a). Sun yi sabani a tsakaninsu ko wani bangare yana fadar wani abu daban da na wani bangaren. Amma ranar kiyama a lokacinda za'a yaye labule gaskiya ta bayyana a fili ga kowa. A rannan idanunsu da kunnuwansu zasu ji kuma su ga gaskiya.
Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka.
1. Daya daga cikin matsalolin da addinin Allah ke fuskanta a tsawon zamani shi ne rarraba da kuma samar da mazhabobi. Wanda hakan wani zalunci ne babba ga ayyukan annabawa Allah.
2. Mu yi kokari a rayuwarmu ta duniya mu yi amfani da ji da ganimmu don zabar tafarkin gaskiya tun ranar kiyama bata zo ba. A lokacinda jammu da ganimmu na gaskiya ba zasu amfane mu ba.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 39 da 40 daga cikin surar maryam kamar haka.
وَأَنذِرْهُمْ يَوْمَ الْحَسْرَةِ إِذْ قُضِيَ الْأَمْرُ وَهُمْ فِي غَفْلَةٍ وَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ{39} إِنَّا نَحْنُ نَرِثُ الْأَرْضَ وَمَنْ عَلَيْهَا وَإِلَيْنَا يُرْجَعُونَ{40}
39-Kuma ka yi musu gargadi da rãnar nadãma a lõkacin da aka hukunta al'amari alhãli kuwa sunã a cikin bãta, kuma sũ bã su yi ĩmãni ba. 40-Lalle ne Mũ, Mũ ne ke gãdon kasa da wanda yake a kanta, kuma zuwa gare Mu ake mayar da su.
A karshen wannan bangare na surar maryam wanda yake Magana dangane da annabi Isa (a), wadannan ayoyi suna suna Magana da manzon Allah (s) ya ya yi gargadi ga ahlul kitab da su ji tsoron ranar nadama da asara ranar. Ranar da babu komawa baya.
Ka kirasu ga yin imani kafin lokaci ya kure, don duniya da wanda ke cikinta duk zasu zama gadon Allah ne. Kowa zai koma gaban Allah a ranar kiyama.
Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka.
1. Gafalarmu a duniya shi ne zai zama asararmu a ranar kiyama. Don haka ayi hattara.
2. Duniya da dukiya da iko duk zasu tafi zasu kare. Don haka kada su shagaltamu daga gaskiya.
Masu sauraro anan zamu dasa aya. Da fatan an amfana da abinda muka gabatar a huta lafiya wassalamu a laikum warahmatullahi wa barakatuhu.
Suratu Maryam, Aya Ta 41-45 (Kashi Na 527)
Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Maryam, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.
Sai a saurari karatun ayoyi na (41) da (42) a cikin surat Maryam
وَاذْكُرْ فِي الْكِتَابِ إِبْرَاهِيمَ إِنَّهُ كَانَ صِدِّيقاً نَّبِيّاً{41} إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ يَا أَبَتِ لِمَ تَعْبُدُ مَا لَا يَسْمَعُ وَلَا يُبْصِرُ وَلَا يُغْنِي عَنكَ شَيْئاً{42}
41 - Kuma ka ambaci Ibrãhĩm a cikin Littafi. Lalle shi ya kasance mai yawan gaskatãwa, Annabi.
42 - A lõkacin da ya ce wa babansa, "Yã bãba! Don me kake bauta wa abin da bã ya ji, kuma bã ya ga ni, kuma ba ya wadãtar da kõme daga barinka?"
Bayan an ambaci wani abu daga rayuwar annabi Zakariyya (AS) da kuma Maryam (AS) da annabi Isa (AS) a cikin ayoyin da suka gabata, wadannan ayoyin kuma suna yin bayani ne dangane da annabi Ibrahim (AS) inda aka fara bayyana siffarsa siddiq da kuma annabci, ma’anar siddiq a nan na nufin mutum mai tsananin gaskiya da gasgatawa, wato zuciyarsa da harshensa da aikinsa duk abu guda ne, abin da ke cikin zuciyarsa shi ne yake fada a harshensa kuma shi ne a cikin aikinsa, Allah madaukakin sarki da kansa ya yi wa annabi Ibrahim (AS) shaida da wannan siffa.
A lokacin da mahaifin annabi Ibrahim ya rasu, amminsa Azar ya rike shi, ta yadda annabi Ibrahim (AS) ya dauke tamkar mahaifinsa, shi ya sanya ma yake kiransa da babana, alhali Azar ba mahaifin annabi Ibrahim ba ne, mahaifinsa mumini da ya rasu kan akidar tauhidi, amma Azar dan uwansa wanda ya riki annabi Ibrahim, shi ya karkata ga ayyukan shirka, saboda haka ne ma kur’ani kan ambace shi da baban annabi Ibrahim, domin kuwa ya rike tamkar babansa.
Annabi Ibrahim (AS) yana girmama Azar yana yi masa ladabi tamkar mahaifinsa, saboda haka ne ma yake yi masa nasiha da harshe mai taushi kan ya daina bautar gumaka wadanda aka sassaka daga itace, wadanda ba su ji ba su gani, kuma ba su iya amfanar da kansu da komai balantana mai bautarsu. Darussan da za a iya dauka a nan su ne :
1 – A lokacin da mutum yake kokarin shiryar da jama’a, to ya fara da na kusa da shi kafin na nesa.
2 – A cikin sha’anin horu da kyakyawa da kuma hani daga mummuna babu iyaka ta shekaru, domin kuwa annabi Ibrahim ya yi ma amminsa nasiha ta hankali a cikin harshe mai taushi.
3 – A lokacin nasiha a kan munanan lamurra, ana farawa ne da lamurra da suka shafi akida, domin kuwa akida ita ce farko kafin komai.
Sai a saurari karatun aya ta (43) a cikin surat Maryam
يَا أَبَتِ إِنِّي قَدْ جَاءنِي مِنَ الْعِلْمِ مَا لَمْ يَأْتِكَ فَاتَّبِعْنِي أَهْدِكَ صِرَاطاً سَوِيّاً{43}
"Yã bãba! Lalle ni abin da bai je maka ba na ilmi ya zo mini, sabõda haka ka bĩ ni in shiryar da kai wani tafarki madaidaici."
Bayan da annabi Ibrahim (AS) ya fahimci cewa amminsa bai dauki maganarsa da muhimmanci ba, sai fito karara ya sanar da shi cewa shi annabin Allah ne, Allah madaukakin sarki yana yi masa wahayi daga gare shi da ilimi wanda bai zo ma amminsa ba, saboda haka ya ce masa ya bi abin da yake fada masa zai shiryar da shi zuwa ga tafarki madaidaici. Bin tafarkin bautar gumaka mummuna aiki ne na shirka, saboda haka a cikin yanayin na tausayi da neman tserartar da amminsa daga fushin ubangiji, annabi Ibrahim (AS) ya ce masa ya daure ya zo ya bi shi kan tafarkin tauhidi da kadaita Allah, idan ya yi haka zai samu rahamar ubangiji, kuma zai samu kubuta daga azbarsa a ranar kiyama.
Darussan da za a dauka a nan su ne :
1 – Babban tushen shirka jahilci ne kan hakikanin gaskiya, saboda haka ne ma annbawan Allah suke yin iyakacin kokarin domin fadakar da mutane ta hanyoyi daban-daban na ilimi da hikima.
2 – Mutane dole ne su bi mai ilimi da tsoron Allah daga cikinsu komai girmansa ko karancin shekarunsa. 3 – hanyar annabawan Allah hanya ce matsaiciya, babu tauye hannu ko wuce gona da iri a cikinta.
Sai a saurari karatun ayoyi na (44) da (45) a cikin surat Maryam
يَا أَبَتِ لَا تَعْبُدِ الشَّيْطَانَ إِنَّ الشَّيْطَانَ كَانَ لِلرَّحْمَنِ عَصِيّاً{44} يَا أَبَتِ إِنِّي أَخَافُ أَن يَمَسَّكَ عَذَابٌ مِّنَ الرَّحْمَن فَتَكُونَ لِلشَّيْطَانِ وَلِيّاً{45}
44 - "Yã bãba! Kada ka bauta wa Shaidan. Lalle Shaidan ya kasance mai sabãwa ga Mai rahama."
45 - "Yã bãba! Lalle ne ni inã tsõron wata azãba daga Mai rahama ta shãfe ka, har ka zama masõyi ga Shaidan."
Bayan kore duk wani matsayi da daukaka daga gumaka, annabi Ibrahim ya ja hankalin Amminsa dangane da hadarin shidan da sharrinsa, da tsananin gabarsa da hassadarsa ga dan adam, wanda hakan ya samo asali saboda sabon ubangiji da ya yi na kin umurnin da aka ba shi, na ya yi sujada ga Adam (AS) saboda kin bin gaskiya da bautar gumaka bautar shidan ne kai tsaye.
Annabi Ibrahim ya fito karara ya sheda amminsa tsoron da yake da shi a kansa idan dai har bai daina bautar gumaka ba tare da yin imani da Allah, wannan tsoron kuwa shi ne azabar Allah za ta shafe shi matukar dai ya mutu a kan tafarki na shirka, kuma idan har bai yi imani da sakon Allah ba, to ya zama mai jibinta lamarinsa ga shaidan.
Darussan da za a dauka a nan su ne :
1 – A lokacin yin nasiha mutum ya yi amfani da salo na hikima da tausasawa, kada ya yi amfani da kakkausan harshe sai nasiharsa ta rasa tasiri.
2 – Wasu lokuta mutum kan aikata wani da zai fusata Allah, ta yadda idan fushin Allah ya safka a kansa zai yi nisa daga bin gaskiya, duk kiran da za a yi masa ba zai taba dawowa ba.
Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
Suratu Maryam, Aya Ta 46-50 (Kashi Na 528)
Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Maryam, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.
Sai a saurari karatun ayoyi na (46) da (47) a cikin surat Maryam
قَالَ أَرَاغِبٌ أَنتَ عَنْ آلِهَتِي يَا إِبْراهِيمُ لَئِن لَّمْ تَنتَهِ لَأَرْجُمَنَّكَ وَاهْجُرْنِي مَلِيّاً{46} قَالَ سَلَامٌ عَلَيْكَ سَأَسْتَغْفِرُ لَكَ رَبِّي إِنَّهُ كَانَ بِي حَفِيّاً{47}
46 - Ya ce: "Ashe, mai gudu ne kai daga gumãkãna? Yã Ibrãĩm! Lalle ne, idan ba ka hanu ba, hakĩ ka, zan jẽfe ka. Kuma ka kaurace mini tun kanã mai mutunci."
47 - Ya ce: "Aminci ya tabbata a gare ka! zan nẽmi Ubangijina Ya gãfarta maka. Lalle Shi Ya kasance Mai girmamãwa gare ni."
A cikin shirin da ya gabata an bayani kan cewa annabi Ibrahim (AS) ya tashi ne a hannun Amminsa Azar da ya rike shi bayan rasuwar mahaifinsa, wanda shi ya kasance mumini, amma Azar dan uwan mahaifinsa ya kasance kan tafarkin shirka wato bautar gumaka, annabi Ibrahim (AS) ya yi masa hannunka mai sanda kan hadarin da ke tattare da yin shirka da Allah, amma nasihar annabi Ibrahim (AS) ba ta yi tasiri a gare shi ba, maimakon sauraren abin da annabi Ibrahim ya gaya masa ma, sai ya shiga yi masa fada yana daukaka murya sama, yana ce masa ; yanzu Ibrahim kai ne ka wayi gari kana kiyayya da gumakana, idan har ba ka bar wannan abin da ake yi ba, to zan jejjefe ka, ka tafi ka ba ni wuri.
Duk da haka annabi Ibrahim (AS) a cikin tawalu’u da muryarsa a kasa sai ya ce masa ; aminci ya tabbata gare ka, Allah ya huci ziciyarka, ni ba ina nufin wulakanta abin da kuke bauta mawa ba ne, kawai dai na kiraka ne zuwa ga bautar ubangijin kowa da komai ne maimakon bautar abin da ba ya iya amfanar da kansa balanta ya amfanar da kai ko waninka, kuma ba zan tilasta ka bin abin da nake yi ba, kuma da sannu zan roka maka gafara a wajen ubangijina.
1 – A ko da yaushe annabawan Allah suna yin magana ne ta hankali da lissafi da kuma hujja, ba su yin magana maras kan gado. 2 – Haka nan kuma su masu matukar hakuri ne a kan duk abin da za a gaya musu na cutarwa.
3 – A koda yaushe mutum mai hankali yana kashe fushin wasu ne da hakurinsa da salon maganarsa ta hankali da natsuwa.
Sai a saurari karatun aya ta (48) a cikin surat Maryam
وَأَعْتَزِلُكُمْ وَمَا تَدْعُونَ مِن دُونِ اللَّهِ وَأَدْعُو رَبِّي عَسَى أَلَّا أَكُونَ بِدُعَاء رَبِّي شَقِيّاً{48}
"Kuma inã nĩsantar ku da abin da kuke kira baicin Allah; kuma inã kiran Ubangijina, tsammãnin kada in zama mai rashin arziki game da kiran Ubangijina."
Ammin annabi Ibrahim ya ba shi zabi guda biyu, ko dai ya tafi ba su wuri, ko kuma makomarsa ta zama kisa, jin haka sai annabi Ibrahim (AS) ya ce tun da ni ba zan iya tilasta ku barin abin da kuke yi na shirka da Allah ba, to na zabi in tafi in barku domin in bauta ma Allah ta hanyar da ya amince a bauta masa, in bar ku da abin da kuke bauta ma wa koma bayan Allah, ni kuma in ci gaba da butar ubangijina da bauta masa, ina mai fatan ba zan tabe ba daga yin addu ‘a da bautar ubangijina.
Wannan ayar tana yin hannunka mai sanda ga matasa musamman da suka samu kansu cikin dangi da ba su da addini, sai su rike addininsu kuma su yi hakuri da cutarwa ko izgili da abin da ya yi kama da suke fuskanta saboda kiyaye addini.
Darussan da za a dauka a nan su ne :
1 – Yanke dangantaka ita ce mataki na karshe a cikin umurni da kyakyawa da hani da mummuna, idan mutum ba zai iya canja al’ummar da take tafiya kan tafarki na sabo ba, kuma ba za su bar shi ya bauta ma ubangijinsa ba, to ya koma inda zai iya bauta ma Allah.
2 – Hatta annabawa suna tunanin abin da zai kai ya komo a rayuwarsu, saboda haka suke fatan samun taimako daga Allah a cikin lamurransu.
Sai a saurari karatun aya ta (49) da (50) a cikin surat Maryam
فَلَمَّا اعْتَزَلَهُمْ وَمَا يَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللَّهِ وَهَبْنَا لَهُ إِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ وَكُلّاً جَعَلْنَا نَبِيّاً{49} وَوَهَبْنَا لَهُم مِّن رَّحْمَتِنَا وَجَعَلْنَا لَهُمْ لِسَانَ صِدْقٍ عَلِيّاً{50}
49 –To a lokacin da ya nĩsance su da abin da suke bautãwa baicin Allah, Muka bã shi Is'hãka da Ya'akuba alhãli kuwa kõwanensu Mun mayar da shi Annabi.
50 - Kuma Muka yi musu kyauta daga Rahamarmu, kuma Muka sanya musu harshen gaskiya madaukaki.
A lokacin da annabi Ibrahim (AS) ya kaurace ma mutanensa masu shirka da Allah, sai ubangiji ya ba shi baiwa ta musamman daga rahmarsa, ya azurta shi da zuriyya dayyiba, ya ba shi Ishaq ta hanyarsa kuma Yakub, dukkaninsu kuma Allah ya kai su matsayi na annabta.
Duk kuwa da cewa annabi Ibrahim a lokacinsa ya kasance shi kadai ne yake kalubalantar kafirci da shirka ta duniya baki daya, amma duk da haka bai ji tsoron barazanar kisa ko jefgewa ba, ya ki mika kai, kuma ya ci gaba da bin tafarkin da ubangiji ya umurce shi, wannan babban misali ne abin koyi ga dukkanin masu bin addinan da aka safkar daga sama.
Darussan da za a dauka a nan su ne :
1 – Tasirin ayyuka na alkhairi da mahaifa suka aikata ya kan yi tasiri a kan ‘ya’ya, samun da na gari babbar ni’ima ce daga Allah.
2 – Idan mutum ya yi riko da Allah kuma ya dogara da shi a cikin dukkanin lamarinsa, to kuwa a koda yaushe zai yi ta ganin taimakon Allah a cikin lamurransa.
3 – Tsaraka daga cikin mutane ne suke kaiwa ga matsayi na musamman a wajen Allah, ta yadda dukknain rayuwarsu albarka ce.
Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
Suratu Maryam, Aya Ta 51-55 (Kashi Na 529)
Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat Maryam, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.
Sai a saurari karatun aya ta (51) a cikin surat Maryam
وَاذْكُرْ فِي الْكِتَابِ مُوسَى إِنَّهُ كَانَ مُخْلَصاً وَكَانَ رَسُولاً نَّبِيّاً{51}
Kuma ka ambaci Mũsã a cikin Littãfi. Lalle ne shi, yã kasance zãbabbe, kuma yã kasance Manzo, Annabi.
A cikin ayoyin da suka gabata a cikin wannan sura, an ambaci annabawan Allah da waliyyansa, wannan ayar kuma tana kiran ma’aiki da ya tuna da annbi Musa (AS) wanda daya ne daga cikin bayin Allah masu tsarkaka, kuma manzo annabi, wannan abubuwa ne biyu da Allah ya hada ma annbi Musa, wato manzanci da nnabci, domin kuwa ko shakka babu matsayi na manzanci yana gabada matsayin annabci, domin kuwa shi manzo baya ga samun wahayi, an umurce shi da ya isar da abin da aka gaya masa ga sauran mutane, ya zama shi ne mai sanar da su kuma malami mai koyar da su abin da sakon yake dauke da shi.
Annabawa da manzanni dukkaninsu tsarkaka ne, shaidan ba ya da hanyar da zai iya kutsawa cikin lamarinsu balantana ya karkatar da su daga barin tafarki na imani ko canja sakon ubangiji.
Darussan da za adauka a nan su ne:
1 – Tunawa da bayin Allah da girmama su saboda matsayin da suke da shi a wurin Allah umurni ne na ubangiji a kan masu imani.
2 – Tsarkin niyya a cikin lamari yana kai mutum zuwa matsayi na kololuwa a wajen ubangiji.
Sai a saurari karatun aya ta (52) a cikin surat Maryam
وَنَادَيْنَاهُ مِن جَانِبِ الطُّورِ الْأَيْمَنِ وَقَرَّبْنَاهُ نَجِيّاً{52}
Kuma Muka kira shi daga gẽfen dama na dũtse Tur kuma Muka kusanta shi yanã abõkin gãnãwa.
Wannan aya mai albarka tana yin ishara ne da yadda annabi Musa ya isa ga matsayi na manzanci daga Allah madaukakin sarki, an kira annabi Musa daga sama zuwa ga munajati kuma Allah ya kusantar shi zuwa gare shi. A cikin wasu ayoyin na kur’ani an yi ishara da cewa annabi Musa ya yi magana da Allah mdaukakin sarki kai tsaye, duk kuwa da cewa wannan wani lamari da Allah madaukakin sarki ne kawai ya san yadda yake, domin kuwa Allah ba mutum ne balantana ya yi magana irin ta mutane da baki kamar yadda aka saba, annabi Musa yana jin maganar ne ta wani irin yanayi da Allah ne kawai ya san yadda yake jiyar da annabi Musa maganar.
Wannan na nuni ne da irin madaukakin matsayi da annabi Musa (AS) yake da shi ne a wurin Allah.
Darussan da za a iya dauka a nan su ne:
1 – Munajatin ubangiji yana kai mutum zuwa ga samun kusanci da Allah, domin kuwa annabawa ma sun bi ta wannan hanya kafin kaiwa ga matsayi na annabta.
2 – Akwai wurare masu tsarki da Allah madaukakin sarki ya albarkace su, wajibi ne kan mutane su kiyaye tsarkin wadannan wurare, kamar dutsen tur da sauran wurare makamantansa da aka ambata.
Sai a saurari karatun aya ta (53) a cikin surat Maryam
وَوَهَبْنَا لَهُ مِن رَّحْمَتِنَا أَخَاهُ هَارُونَ نَبِيّاً{53}
Kuma Muka yi masa kyauta daga Rahamar,u da dan'uwansa Hãrũna, ya zama Annabi.
Kamar yadda ya zo a cikin wasu kur’ani mai tsarki cewa, annabi Musa (AS) ya roki Allah da ya hada shi da dan uwansa Harun domin ya taimaka masa wajen isar da sakon ubangiji a lokacin da aka tura shi zuwa ga Fir’auna, kuma Allah madaukakin sarki ya karbi rokon annabi Musa, inda aka tura tare da dan uwansa Harun, wanda hakan ke nuni da cewa aikin annabawa ya ginu ne kan manufa guda daya, ita ce isar da abin da Allah ya yi umurni kamar yadda ya yi umurnin, annabi Musa da annabi Harun aikinsu shi ne isar da sakon ubangiji zuwa ga Fir’auna da sauran mutane da suke da suke daukarsa a matsayin ubangiji, su gaya masa cewa ba shi ne ubangiji ba, kuma suna kiransa zuwa ga imani da ubangiji na gaskiya, tare da kiransa da ya daina azabtar da Bani Isra’ila, kuma wannan shi ne abin da annabi Musa da annabi Harun suka yi.
Darussan da za a dauka a nan su ne:
1 – Yin aikin mutane biyu ‘yan uwa juna tare, ni’ima ce ta ubangiji gare su, amma bisa sharadin su kasance masu tunani da akida da kuma manufa iri daya.
2 – A wasu lokuta mutane biyu za su iya kaiwa ga matsayi na cancanta ga jagorancin al’umma, amma daya ya zama yana bin daya, domin kuwa al’umma tana bukatar jagora ne guda wanda lamarin shiryarwa yake hannunsa, kuma kowa yana saurara masa.
Sai a saurari karatun ayoyi na (54) da kuma (55) a cikin surat Maryam
وَاذْكُرْ فِي الْكِتَابِ إِسْمَاعِيلَ إِنَّهُ كَانَ صَادِقَ الْوَعْدِ وَكَانَ رَسُولاً نَّبِيّاً{54} وَكَانَ يَأْمُرُ أَهْلَهُ بِالصَّلَاةِ وَالزَّكَاةِ وَكَانَ عِندَ رَبِّهِ مَرْضِيّاً{55}
54 - Kuma ka ambaci Ismã'ila a cikin Littãfi. Lalle shi, yã kasance mai gaskiyar alkawari, kuma yã kasance Manzo, Annabi.
55 - Kuma yã kasance yanã umurnin mutãnensq da salla da zakka. Kuma yã kasance yardajje a wurin Ubangijinsa.
Bayan ambaton matsayin annabi Ibrahim da annabi Musa dan uwansa annabi Harun, wadannan ayoyin biyu suna yin bayani ne kan matsayin annabi Isma’il (AS) wanda Allah ya bayyana shi da mai gaskiya a cikin alkawalinsa, kuma annabi Manzo.
Annabi Isma’ila an siffanta da shi mai gaskiya a cikin alkawali da ma zance, wanda kuma wannan daya ce daga cikin siffofi na Allah madaukakin sarki, da bayinsa na musamman ne suke siffantuwa da wannan siffa, a nan Allah ya siffanta annabi Isma’il da wannan siffa.
Annabi Isma’il ya kasance mai tsayar da salla tare da umrta iyalansa da yin hakan da ma duk wadanda suke karkashinsa, mai bayar da zakka tare da yin umurni da hakan, mai kiyae dukkanin dokokin Allah tare da yin umurni da hakan, ya kasance yardajje a wurin ubangiji.
Darussan da za a iya dauka a nan su ne:
1 – Ma’auni na girma da daukaka a wurin Allah yana zuwa ne sakmakon tsarkin ruhi da kyautata dangantaka da Allah.
2 – Baya ga nauyi na shiryar da al’umma da ke kan wuyan annabawa, a lokaci guda kuma nauyin shiryarda iyalansu da yi musu hannunka mai sanda a cikin dukkanin lamurra yana kansu, da hakan ya hada da tsayar da salla da kiyaye bayar da zakka da sauransu.
Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
Suratu Maryam, Aya Ta 56-60 (Kashi Na 530)
Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar Maryam, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa.
To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 56 da 57:
وَاذْكُرْ فِي الْكِتَابِ إِدْرِيسَ إِنَّهُ كَانَ صِدِّيقاً نَّبِيّاً{56} وَرَفَعْنَاهُ مَكَاناً عَلِيّاً{57}
"Kuma ka ambaci (labarin) Idrĩsu a cikin Littãfi. Hakika shi ya kasance mai yawan gaskatãwa, kuma Annabi. "Muka kuma daukaka shi a kan daraja madaukakiya.
A shirin da ya gabata an ambaci Annabi Ibrahim da Annabi Musa da Annabi Ismail tare da girmnamawan da Allah ya yi musu, wadannan ayoyi kuma sun ambaci Annabi Idris wanda shi ma ya na cikin manyan annabawa kuma ya rayu ne kafin Annabi Nuhu. A cikin Ataura an kira Idris da sunan Akhnukh. Hadisai sun bayyana cewa shi ne ya fara koya wa mutane dinka tufafi. Annabi Idris ya lakanci ilimin taurari da lissafi da yanayi kuma ya yi rubutu da alkalami Darusa: 1-Fatar gaskiya da aikata gaskiya suna cikin manyan sifofin annabawa kuma dole ne mabiyansu su yi koyi ta su 2-Fadar gaskiya da aika aiki mai kyau suna kawo wa mutum soyuwa a idon jama’a da kuma a wajen Allah kuma zai kara wa mutum daraja ya kai shi matsayin da fi wanda ya ke da shi.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 58:
أُوْلَئِكَ الَّذِينَ أَنْعَمَ اللَّهُ عَلَيْهِم مِّنَ النَّبِيِّينَ مِن ذُرِّيَّةِ آدَمَ وَمِمَّنْ حَمَلْنَا مَعَ نُوحٍ وَمِن ذُرِّيَّةِ إِبْرَاهِيمَ وَإِسْرَائِيلَ وَمِمَّنْ هَدَيْنَا وَاجْتَبَيْنَا إِذَا تُتْلَى عَلَيْهِمْ آيَاتُ الرَّحْمَن خَرُّوا سُجَّداً وَبُكِيّاً{58}
"Wadancan sũ ne annabawa wadanda Allah Ya yi ni'ima a garesu, daga zuriyar Ãdamu, da kuma wadanda muka dauko (a jirgin ruwa) tãre da Nũhu, da kuma zuriyar Ibrãhĩmu da Isrã'ila, da kuma wadanda Muka shiryar da su Muka kuma zãbe su. Idan anã karãnta musu ãyõyin Ubangiji Mai rahama sai su fãdi su yi sujada suna kũka."
A kowace rana a cikinn sallolinmu muna karanta ayar “Ihdinas siradal mustaqim siradallazina an’amta alaihim” wato “Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya, hanyar wadanda ka yi musu ni’ima” wanda ake karantawa a cikin surar Fatiha. Abin nufi a wannan aya, mutanen da Allah ya ya basu babbar ni’ima su ne annabawa kuma hanyarsu ita ce hanaya madaidaiciya. A cikin ayoyin da suka gabata a wannan sura an ambaci sunayen annabawan Allah goma. Annabi Idris jikan Annabi Adam na kusa kusa ne, Ibrahim jikan Nuhu ne, Ishaq da Isamail da Yakub zuriyar Annabi Ibrahim ne, Musa da Haruna da Zakariya daga ziriyar Israila ne wato Yakubu.
Babbar sifar wadannan annabawa ita ce ibada wa Allah, suyna sujada wa Allah madaukakin sarki makadaici.
Darusa:
1-Tsarkin zuriya niima ce daga Allah kuma ya Ubangiji ya zabi tsarkakan mutane don su zama annbawansa.
2-Kasancewar mutum daga asalin tsarkakan mutane ba shi kenan, dole ne mutum ya kasance salihin bawa mai biyayya da kaskantar da kai ga Allah da yi masa ibada kafin ya cancanci samun ni’imomi na musamman.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 59 da 60----
فَخَلَفَ مِن بَعْدِهِمْ خَلْفٌ أَضَاعُوا الصَّلَاةَ وَاتَّبَعُوا الشَّهَوَاتِ فَسَوْفَ يَلْقَوْنَ غَيّاً{59} إِلَّا مَن تَابَ وَآمَنَ وَعَمِلَ صَالِحاً فَأُوْلَئِكَ يَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ وَلَا يُظْلَمُونَ شَيْئاً{60}
"Sai wasu suka maye gurbinsu bayan wadanda suka watsar da salla suka kuma bi sha'awace-sha'awacen (duniya na sabo); to ba da dadewa ba za su hadu da gayyu (wato wani kwari na azaba a Jahannama). "Sai dai wanda ya tũba ya yi ĩmãni ya kuma yi aiki na gari, to wadannan za su shiga Aljanna, kuma bã za a tauye musu kõmai ba.
A ayar da ta gabata mun ji cewa bauta wa Allah shi ne sifar da annabawa da salihai suka ta ita, a wadanna ayiyi kuma Alkurani yana cewa duk da wahalhalun da annabawan suka sha domin tabbatar da addinin Allah mutane da suka zo a bayansu sunn tauye salla wacce it ace babbar alamar bauta ga Allah, sun wulakanta salla sun karkata ga bukatun son zuciyarsu. Wadancan sun bace daga hanya kuma mummunan karshe ne yake jiransu in banda wadanda suka dawo suka gyara ayyukansu. Abin takaici, daya daga cikin masifun da suka addabi bil Adama shi ne akasarin mutane basu kaskantar da kai ga Allah, hatta wasu masu salla ma basu kiyaye ladubban ta kuma suna tauye ta. Sakamakon wannan muguwar hanya da alummomin dan Adam suka dauka shi ne soyace-soyacen zuciya da sha’awowi sun mallake mutane kuma suna haddasa wa bil Adama matsaloli masu yawa a zaman iyali da zamantakewar alumma.
Darusa:
1-Sau da yawa ana samun ‘ya’ya da zuriyar da suke zuwa a baya suna wulakanta kokarin da magabatansu su ka yi.
2- Sallah ita ce fuskar addini kum awulakanta ta tamkar wulakantar da addinin Musulunci ne baki daya.
3-Salla garkuwa ce ga mutum ta take kare shi daga shaawowi kuma idan aka kawar da wanna garkuwa cikin sauki ne mutum zai zama bawan sha’awowi.
4-Tuba ta gaskiya ita ce sauyawa ta ciki ba bayyana sauyi a zahiri ba. Tuba ta hakika tana dawo da mutum daga bata zuwa hanyar alheri da sa’ada, tana canja mutum mai aikata aikin da zai kai shi Jahannama ta mai da shi mutumin aljanna.
- To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na Surar Maryam. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
Suratu Maryam, Aya Ta 61-65 (Kashi Na 531)
Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar Maryam, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa.
To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 61da 62 da 63:
جَنَّاتِ عَدْنٍ الَّتِي وَعَدَ الرَّحْمَنُ عِبَادَهُ بِالْغَيْبِ إِنَّهُ كَانَ وَعْدُهُ مَأْتِيّاً{61} لَا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْواً إِلَّا سَلَاماً وَلَهُمْ رِزْقُهُمْ فِيهَا بُكْرَةً وَعَشِيّاً{62} تِلْكَ الْجَنَّةُ الَّتِي نُورِثُ مِنْ عِبَادِنَا مَن كَانَ تَقِيّاً{63}
"Aljannoni na dawwama wadanda Allah Mai rahama ya yi wa bayinsa alkawari da su alhali ba su gansu ba. Hakika alkawarinsa a tabbata mai zuwa ne. "Bã zasu ji wani zancen banza ba a cikinta ba sai gaisuwa, kuma suna samun abincinsu a cikinta sãfe da maraice. "Wancan ita ce Aljannar da Muke gãdar da ita ga bayinmu wadanda suka zamanto masu tsoron Allah.
Wadannan ayoyi suna sifanta yanda aljanna ta ke suna bayyana wasu abubuwan da ta kebanta da su. Wasu daga cikin wadannan sifofi su ne, aljanna dawwamamma ce ta har abada kuma duk wanda ya shige tab a zai fita ba. Wannan aljanna it ace dai alkawarin da ke boye ko kuma na gaibi da Allah ya yi wa muminai kuma suka yi imam ni shi kuma suke riskar gaskiyarsa da idon basira na imani da gaskatawa. Daya dagha cikin abu bwuan da suke yi wa muminai zafi a ann diuniya shi ne zantuttuka marasa kan ngado da wasu mutane suke yi musamman ma kafirai da masu adawa da muminai. Amma a cikin aljanna babu zancen da za mu ji face gaisuwa da kalmomin soyayya da sallama, ga kuma nauo’in abinci wadanda ba zasu kare ba. Aya ta uku daga cikin wadannan ayoyi da muka saurar ta yiu ishara ne da batutuwa biyu: Na farko shi ne mabudin aljanna shine takawa wato tsoronn Allah da kiyaye dokokinsa. Na biyu kuma ayyukan alherin da mutum yake aikatawa a nan duniya basu ne zasu shigar das hi wannan aljanna mai niimomoin dab a iyaka ba saboda duk aikin da mutum ya yi takaitacce ne. Idan aka sa lura za a ga cewa abinda Allah zai baiw a tsarkakan mutane salihai a lahira ya yi kama da abinda ‘ya’ya suke gadonsa daga iyayensu domin babu wahalar da suke yi domin samun wannan dukiya da iyayensu su ka gadar musu, to haka ma aljanna, ko da yake muiminai sun yi aikin alheri sun ma sha wahala a dun iya saboda kiyaye dokokinn Allah Madaukaki, amma idan aka kwatatnta sakamakon da Ubangijinsu zai basu a lahira sai a ga tamkar ma ba wahalar da suka yi domin hakan.
Darusa:
1-Hakikanin yadda aljanna take ya boyu gare mu kuma ita tana cikin abubuwan gaibi ko mu ce na boye. Aljanna alkawari ne wanda mu ka yi imani da shi kumna muna fatar zamu same ta a ranar alkiyama saboda kautar Allah.
2-Idan muna son jiga aljanna to mu nisanci wuraren da ake zantuttukan sabo da hululu.
3-Aljanna gado ne na masu takawa koda kuwa basu sami gado da dukiya irin na duniya ba.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 64:
وَمَا نَتَنَزَّلُ إِلَّا بِأَمْرِ رَبِّكَ لَهُ مَا بَيْنَ أَيْدِينَا وَمَا خَلْفَنَا وَمَا بَيْنَ ذَلِكَ وَمَا كَانَ رَبُّكَ نَسِيّاً{64}
"(Malai'ika ya ce): "Ba ma sauka sai da umuruin Ubangijinka; abin da yake gabanmu da abin da ya ke bayanmu da abin da yake tsakanin wadannan duka nasa ne." Ubangijinka kuma bai zam mai mantãwa da kai ba.
Malaman tafsiri sun nakalto wasu hadisai masu cewa wahayi ya yanke na wani gajeren lokaci bai sauko wa Annabi ba kuma wannan ya sa shi damuwa, makiya kuma suka maid a shi abin suka gare shi, sai wannan aya ta sauka ta ce da Manzon Rahama cewa Allah bai manta das hi ba. Allah ba ya matuiwa kuma saukowar malaikan wahayi wato Jibrilu (a.s.) da sauran maalaiku ai yana faruwa cikin ilimin Allah da hikimarsa da kuma tsarinsa, Allah wanda jiya da yau da kuma gobe duk suke karkashin ikonsa.
Darusa:
1-Ayoyin Alkurani sun sauka ne sannu a hankali a wurare da lokuta da Allah ya zaba kuma Annabi da malaiku basu da ta cewa a wannan.
2-malakiu suna cikakkiyar biyayya da umurnin Allah kuma bas u da wani zabi nasu.
3-Babu batun mantuwa a lamarin Allah kuma shudewar lokaci ko wasu dalilai na daban bas u sa Allah ya yi mantuwa.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 65:
رَبُّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا فَاعْبُدْهُ وَاصْطَبِرْ لِعِبَادَتِهِ هَلْ تَعْلَمُ لَهُ سَمِيّاً{65}
"Shi ne Ubangijin sammai da kasa da abin da yake a tsakãninsu, sai ka bauta Masa, kuma ka yi hakuri ga bautarsa. Shin kã san wani mai suna irin nasa?
Wannan aya tana bayanin tauhidi wato kadaitakar Allah a wajen gudanar da halitta, tana cewa dukkan halittu daga sammai har zuwa kasa suna karkashin gudanarwar Allah, kuma dukansu Mahalicci daya ne ya haliccesu kuma mai gudanarwa daya ne yake gufanar da su. To idan ba wani mahalicci mai kula mda rayuwar komai da gudanar komai a cikin talikai to ku bauta masa shi kadai ku kuma nisanci bauta wa wani bas hi ba. Ba shakka da akwai abubuwan da yawa da zasu sa mutane su baude daga wannan hanya ta tauhidi saboda haka lallai ne mu jure wa wadannan mu kum atsaya kan tafarkin Allah domin kuwa babu wanda zai iya nuna wani abokin tarayya ko kini da Allah madaukakin sarki.
Ba salla da zikiri ne kadai ake nufi da bauta ba a wannan aya saboda ai mirin wannan ibada bata da wahalar aikatawa. Abinda aked nufi da bauta shi ne mika wuya ga Allah cikakkiyar mikwa a dukka alamura na daidaiku da kuma na jamaa saboda aid an Adam a koda yaushe yana fuskantar abubuwa kishiuyoyin juna ta yadda sai ya tsaya ya yi zabi, (alal misali Allah ya hana a yi wani abu amma zuciya tana son wannan abu a nan sai mutum ya zabi daya daga wadannan abubuwa biyu). Wannan ya sa dole ne mu tsaya kyam a kan tafarkin gasikya.
Darusa:
1-Tauhidi ko kadaita Allah a alamuran gudanar da halittu shi ne yake kai mutum ga kadaita shi a alamuran ibada, domin haka Allah ya halata a yi wa ibada.
2-Ibada ko bauta wa Allah yaki ne da soyace-soyacen zuciya da matsin lamba daga waje ne, saboda haka ibada tana bukatar hakurti da juriya.
- To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na Surar Maryam. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
Suratu Maryam, Aya Ta 66-70 (Kashi Na 532)
Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar Maryam, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa.
To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 66 da 67:
وَيَقُولُ الْإِنسَانُ أَئِذَا مَا مِتُّ لَسَوْفَ أُخْرَجُ حَيّاً{66} أَوَلَا يَذْكُرُ الْإِنسَانُ أَنَّا خَلَقْنَاهُ مِن قَبْلُ وَلَمْ يَكُ شَيْئاً{67}
"Kuma mutum (wato kafiri) yana cẽwa, "Yanzu idan na mutu anya kuwa zã a fitar da ni da rai?" "Yanzu shi mutum bai tuna ba cewa Mu muka halicce shi tun farko, alhãli kuwa bai kasance kõme ba?
A shirin da ya gabata mun ambaci wasu sifofin aljanna da kuma masu shiganta, wadannan ayoyin kuma suna magana kan ranar alkiyama da kuma shakku da tababa da wasu mutane suke yi dangance da hakan. Da yawa daga cikin masu inkarin ranar kiyama, ba tare da sun kawo wata hujja kan wannan musantawa da suke yi, suna ganin cewa alkiyama abu ne wanda ba zai yiwu ba a ganinsu. Suna cewa ta yaya mutummin da ya mutu ya zama kasa zai sake dawowa a sake raya shi ya mike ya tsaya da kafafunsa? Amsar da Allah ya basu shi ne ta yaya kuka mance da halinda kuke a farko? Allah ya halicce ku daga babu, ta yaya zaku ce ba zai iya sake halitarku ba, bayan kuma ya aikata irin wannan a baya? A fili yake irin wadannan tambayoyi suna nuni da rashin imanin wawdannan mutane da ikon Allah da karfin sa marasa iyaka, suna kwastanta saninsa da sanin mutane mai iyaka kuma takaitacce, saboda haka kuma suke ganin cewa sake sawo das u a ranar alkiya abu ne dab a zai yiwu ba.
Darusa:
1-Sake halikkar mutane ya fi sauki bisa ga halitta su da farko, ko da yake masu musanta tashin alkiyama suna karya hakan
2-A ranar alkiyama za a tayar da mutane da jikunansu kuma wanna shi ya sa yawancin shakkun da masu musanta alkiyama su ke yi shi ne sake tayar da jikin mutum. Idan da ruhin mutum ne kadai za a dawo das hi a ranar alkiyama da shakkun alkiyama da wasu suke yi zasu ragu.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 68:
فَوَرَبِّكَ لَنَحْشُرَنَّهُمْ وَالشَّيَاطِينَ ثُمَّ لَنُحْضِرَنَّهُمْ حَوْلَ جَهَنَّمَ جِثِيّاً{68}
"To na rantsuwa da Ubangijinka lallai za Mu tãshe su tare da Shaidanu, sannan za Mu kawo su a gaban Jahannama suna a durkushe.
Inkarin tashinnn alkiyama inkarin Allah ne domin ba za a iya raba wadanna biyu ba, wato mutumm ya yarda da samuwar Allah amma bai yadda da ranar alkiyama ba. Saboda haka masu musanta tashin alkiyama mutane marasa addini wadan da suka baude wa madaidaiciyar hanya ta Allah suka kuma faga bata da halaka. Wadannna mutane za a bincike su a ranar lahira kuma idan inkarinsu na taurin kai wa gaskiya ne za a sa su aJahannama amma idan rashin sani ne ya jawo musu karyata lahira sai Allah ya yi musu afuwa. Wannan aya tana kuma cewa za a tayar da kafirai tare da shaidanu na mutane da aljanni, kum awanna tarayya da zasu yi da shaidanun a lahira saboda suna da tarayya a tunani da aiki ne a duniya.
Darusa:
1-Gargadin da Allah yake yi dangane da alkiyama din nan mu dauki shi da gaske kuma mu shirya wa gurfana a gaban kotun Allah a wanna rana.
2-Masu yin izgili wa koyarwar addini a duniya saboda girman kai da jiji da kai, da sun ga wuta jahannama a ranar alkiyama ba zasu iya mike wa kan kafafunsu ba, zasu gurfana ne cikin mafi tsananin kaskanci.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 69 da ta 70:
ثُمَّ لَنَنزِعَنَّ مِن كُلِّ شِيعَةٍ أَيُّهُمْ أَشَدُّ عَلَى الرَّحْمَنِ عِتِيّاً{69} ثُمَّ لَنَحْنُ أَعْلَمُ بِالَّذِينَ هُمْ أَوْلَى بِهَا صِلِيّاً{70}
"Sannan daga kowace jama'a lallai za Mu ware wadanda suka fi tsananin yi wa Allah Mai rahama tsaurin kai. "Sannan ba shakka Mũ Muka fi sanin wadanda suke fi cancanta da kõnuwa da ita (watau wuta).
A ci gaba da bayani kan halartar kafirai a gaban kotun Allah a ranar alkiyama wadannan ayoyi suna cewa, yan wuta ba a wuri daya suke ba a cikin wuta, adalcin Allah ai zai sa kowanne a yi masa horo daidai da laifinsa saboda haka ken an akwai bambamci a azabar da za a yi way an wuta, wadanda suka aikata zalunci mafiya muni a duniya zasu fuskanci azaba mafi muni. Ana iya cewa, masu nlaifi kaso uku ne, wasu suna aikata laifi, wasu suna aikata laifi suna kuma kiran wasu da su aikata shi sun akuma buda musu hanyar sa, kaso mna uku kuma sun amince da sabo da laifuklan da wasu suke yi ne. A sarari yake cewa horon da za a yi wa ko wane daga cikin wadanna uku zai saba da na dayan.
Darusa:
1-Allah shi ne mabubbugar rahama da soyayya amma maimakon dan Adam ya nemi wannan rahama, saboda girman kai da sabo yanan jefa kansa cikin fushin Allah.
2-Jahannama tana da mataki mataki kuma kowani matsayi na sabo da laifi yana da wurin da za a sanya masu aikata shi. Sanin Allah marsa iyaka shi ne ya ayyana ko wanene za a sanya a kowane mataki na jahannama.
- To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na Surar Maryam. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
Suratu Maryam, Aya Ta 71-74 (Kashi Na 533)
Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar Maryam, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa.
To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 71 da 72:
وَإِن مِّنكُمْ إِلَّا وَارِدُهَا كَانَ عَلَى رَبِّكَ حَتْماً مَّقْضِيّاً{71} ثُمَّ نُنَجِّي الَّذِينَ اتَّقَوا وَّنَذَرُ الظَّالِمِينَ فِيهَا جِثِيّاً{72}
"Ba kuma dai daga cikinku wanda ba zai gangara ta wajenta ba, (Wannan) ya kasance tabbataccen abu ne abin hukuntawa a wurin Ubangijinka. "Sannan kuma za Mu tserar da wadanda suka ji tsoron Allah Mu kuma bar azzãlumai a duddurkushe a cikinta.
A shrin da ya gabata mun ji wasu sifofin ranal alkiyama da lada da kuma azabar wanna rana, wadannan ayoyi kuma suna bayani kan yanda yan aljanna zasu wuce ta kan jahannama, suna cewa; dukan mutane na kirki da masu sabo zasu shiga cikin wuta amma kamar yanda hadisan Annabi suka bayyana wuta zata zama mai sanyi ga muminai kamar yanda hakann ya faru da Annabi Ibrahim (a.s), domin wuta bata dace da muminai masu tsarki. Saboda haka nan da nan zasu wuce cikin jahannama su shiga aljanna. Amma mutane masu mugun aiki wadanda suka aiko da watur daga duniya (wato munanan ayyukansu wadan kuma sune wutar) zasu kone a cikin wannan wuta kuma ba zasu sami matsera ba. Hadisai sun bayhan acewa akwai gada ake kira siradi da take kan jahannama kuma kowa zai bi ta kan wannan gada: yan aljanna zasau wuce ta cikin sauri kuma wutar ba zata ta yi musu komai, amma yan wuta ba zasu iya wucewa ba sai su fada cikin jahannama.
Darusa:
1-Banda kotun ranar alkiyama wanda zai bayyana abinda za a yi wa kowa, jahannama da kanta zata bayyana a fili wadanner muatne ne suka cancanci aljanna su wane ne kuma suka cancanci wuta.
2-Hanyar tsira daga jahanna shi ne takawa da tsoron Allah kuma duk wani rashin tsoron Allah naui ne na zalunci, ko zaluntar kai, zaluntar alumma ko zaluntar addini da kansa.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 73:
وَإِذَا تُتْلَى عَلَيْهِمْ آيَاتُنَا بَيِّنَاتٍ قَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لِلَّذِينَ آمَنُوا أَيُّ الْفَرِيقَيْنِ خَيْرٌ مَّقَاماً وَأَحْسَنُ نَدِيّاً{73}
"Kuma idan anã karatun musu ãyõyinMu mabayyana sai wadanda suka kãfirta su ce wa wadanda suka yi ĩmãni, "Wane ne dagq cikin kungiyõyin nan biyu (wato muminai da kafirai) ya ke mafificin matsayi da kuma mafi kyan majalisa?"
Wadannan aya tan a ishara da zuciyar jiji da kai na manayan garin Makka, tana cewa lokacon da suka ga marasa galihu kamar Ammar da Bilal da Khabbab sun yi imani da Annabi sai suka ce ta yaya za a ce bayi da attajirai na cikin alumma a ce daidai suke? Wadannan sune karshen kaskanci da talauci wadannan kuma sune kololuwar iko da daraja? A zamanin jahiliyya sanda ma’aunin kimar mutum shi ne iko da karfi, masu duniuya suna ganin kansu madauykaka talakawa kuma makaskanta ne wadanda basu da wani matsayi a cikinn alumma, alhali kuwa dukiya da karfi ba sune maaunin gaskiya da bata ba, maauninsu shi ne sahihan akida da tunani.
Darusa:
1-Maaunin gane gaskiya da bata shinne hankali da tsararren tunani, ba dukioya da iko ba. Ko da rayuwar wasu kafirai ta fi kyau a nan duniya hakan ba hujja ce ba cewa suna kan gasikya ko kuma Allah ya yi musu rahama ba.
2-Alfahari da jiji da kai suna yin shimfida wa kafirci da karyata addini.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 74:
وَكَمْ أَهْلَكْنَا قَبْلَهُم مِّن قَرْنٍ هُمْ أَحْسَنُ أَثَاثاً وَرِئْياً{74}
"Da yawa alummu wadanda Muka hallaka a gabãninsu wadanda suke da mafi kyan abin duniya da kyawun gani.
Wannan aya tana magana da wadannan masu girman da alfahari kai tana kafa musu hujja mai karfi cewa, ‘Shin kun mance da tarihi ne ku ke yi wa muminai kallon wulakanci ku ke ce musu su makaskanta ne? Idan dukiya da karfi da iko suna nuna cewa masu su suna da matsayi a wajen Allah me ya sa Allah ya hallaka irin wadannna mutane a zaman da suka yi mummunan karshe? Dukiya da abin hannu baya nuna cewa mai su yana cikin rayuwar kwanciyar hankali da saada, ba ya kuma hana azabar Allah, sai ma akasin haka, a cikin akasarin lokuta duniya da matsayi suna jawo wa mutum girman kai da gafala yamna kuma kai mutum ga aikata zalunci da taurin kai wa Allah wannan kuma daga karshe suke kai wag a halaka.
Darusa:
1-Mu koyi darasi daga tarihi, faduwa da halakar masu girman kai da azalumai hanya ce da zata sanar da mu gaskiya da bata da kuma yin izina da daukar darasi.
2-Abin da masu dukiya suke tinkafo da shi tarkacen duniya ne da ba shi da tabbas, ba a duniya yake kawo tsira ba ba kuma a lahira ba. Zahirin wannan duniya da matsayi da suke tatare da zalunci yana da kyaun gani amma badininsa kazanta ne da gurbata.
- To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na Surar Maryam. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
Suratu Maryam, Aya Ta 75-80 (Kashi Na 534)
Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin na Hannunka Mai Sanda. Shiri ne da mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur'ani mai girma. Da fatan za a kasance a tare da mu domin aji ci gaban shirin daga inda ya tsaya a baya.
Yanzu sai a saurari aya ta 75 a cikin suratu maryam.
قُلْ مَن كَانَ فِي الضَّلَالَةِ فَلْيَمْدُدْ لَهُ الرَّحْمَنُ مَدّاً حَتَّى إِذَا رَأَوْا مَا يُوعَدُونَ إِمَّا الْعَذَابَ وَإِمَّا السَّاعَةَ فَسَيَعْلَمُونَ مَنْ هُوَ شَرٌّ مَّكَاناً وَأَضْعَفُ جُنداً{75}
" Ka ce, wanda ya ke acikin bata, to Allah mai rahama zai tsawaita ransa har sai idan sun ga abinda aka yi musu alkawali kodai azabar duniya ko kuma ta lahira, da sannu za su san wanene makomarsa za ta munanta kuma rundunarsa ta ke da rauni."
A cikin shirin baya an bayyana cewa masu more jin dadin rayuwa da kuma masu hannu da shuni na makka suna yin magana cikin kaskanci da cewa: Shin mu ne masu matsayi ko kuwa wadannan muminan matalauta? To wannan ayar ta zo ne a matsayin maida martani a gare su da cewa: Sunna ce ta rayuwar duniya wacce Allah ya tsaida ita akan cewa zai baiwa kowa dama, mumini da kafiri da su gina kawunansu su kuma ci gaba. Babu kuma banbanci a tsakanin mutanen kirki da ashararai.
Sai dai kada wannan sakin talalar da ubangiji ya yi mu ku ya yaudare ku ku za ci cewa ni'imomin da ku ke cikinsu za su dawwama. Su kuma sa ku ci gaba da wanzuwa a cikin kafirci da kuma zaluncinku. Za ku fuskanci sakamakon ayyukanku anan duniya ko a lahira. A wannan lokacin ne za ku fuskanci wanene mai matsayi ku ne ko kuma wadannan muminan talakawa.?
A fili ya ke cewa ubangiji madaukaki yana bada dama ga dukkanin batattu saboda su tuba su koma kan tafarkin gaskiya. Sai dai kuma batattun mutane suna sake nutsewa acikin batansu ba su cin moriyar wannan damar da ubangiji ya ba su.
Darussan da su ke cikin wannan aya.
1-Sunnar ubangiji ce bada dama daidai wa daida ga kowa da koma, saboda ya zamana kowane mutum bisa zabin kansa ne zai bi hanyar da ya ga dama.
2-Sakamakon ayyukan mutum da ubangiji ya ke saukarwa ba sai a lahira kadai ba, wasu ayyukan suna cancantar sakamako tun anan duniya.
Yanzu kuma sai a saurari aya ta 76 a cikin wannan sura ta maryam.
وَيَزِيدُ اللَّهُ الَّذِينَ اهْتَدَوْا هُدًى وَالْبَاقِيَاتُ الصَّالِحَاتُ خَيْرٌ عِندَ رَبِّكَ ثَوَاباً وَخَيْرٌ مَّرَدّاً{76}
"Ubangiji yana kara shiriya ga wadanda su ka shiriya, ayyukan kwarai da su ke dawwama a wurin ubangijinka shi ne mafifci ta fuskar lada da kuma karshen makoma."
A cikin ayoyin da su ka gabata mun ji cewa batattu suna sake nutsuewa acikin munanan ayyukansu wanda hakan ya ke kaisu fadawa cikin azabar ubangiji.
To wannan ayar tana fadin cewa: Wadanda su ke tafiya akan hanyar shiriya ubangiji yana kara musu shiriya. Aikata ayyukan kwarai suna daga mutum sama, kuma gwargwadon yadda mutum ya ke nutsewa wajen aikin kwarai ayyukan nasa za su zama tabbatattu. Ayyukan kwarai sun fi dukiya da kuma kudi kima, kuma babu yadda za a ayi a kwatanta su. Dukiya da kudi suna karewa amma ayyukan kwarai kuwa dawwamammu ne.
Darussan da za mu koya daga wannan aya.
1-Shiriyar Allah tana da matakai da darajoji wanda gudanar da ayyukan kwarai ne su ke share fagen samunsu.
2-Kyakkyawan karshe yana tare da ayyukan kwarai ba tara dukiya da abin duniya ba.
Yanzu kuma sai a saurari aya ta 77 zuwa ta 80 a cikin wannan sura ta maryam.
أَفَرَأَيْتَ الَّذِي كَفَرَ بِآيَاتِنَا وَقَالَ لَأُوتَيَنَّ مَالاً وَوَلَداً{77} أَاطَّلَعَ الْغَيْبَ أَمِ اتَّخَذَ عِندَ الرَّحْمَنِ عَهْداً{78} كَلَّا سَنَكْتُبُ مَا يَقُولُ وَنَمُدُّ لَهُ مِنَ الْعَذَابِ مَدّاً{79} وَنَرِثُهُ مَا يَقُولُ وَيَأْتِينَا فَرْداً{80}
- "Shin ka ga wanda ya kafircewa ayoyinmu ya ce zan sami dukiya da 'yaya?
- Shin ya leko gaibu ne ko kuwa ya sami tabbaci daga ubangiji ma'abocin jin kai?
- Ko kadan! Za mu rubuta abinda ya ke fada sannan mu kara masa azaba mai yawa.
- Za kuma mu gadar masa da abinda ya ke fada- na duniya- sannan ya zo mana shi kadai."
Wannan ayar tana yin magana ne akan tunani wanda ya yi kama da mafarkin tsaye irin na kafirai da masu bautar duniya da abinda ya ke cikinta. Tana cewa suna yin magana kai kace su ne su ka mallaki duniya da abinda ya ke cikinta, kuma suna da ikon su yi abinda su ka ga dama. Suna tsammanin tara duniya da kuma 'ya'ya kai kace Allah ne ya yi musu alkawali.
Abin mamaki shi ne yadda su ke yi wa muminai alfahari da hakan.
Al'kur'ani mai girma yana ba su jawabi da cewa: Maganar da su ke yi na cewa rayuwa za ta yi musu kyawu a gaba, ya yi kama da zance na sanin gaibu. Abin tambaya shi ne ya aka yi su ka san gaibu? Ko kuma sun kulla alkawali da Allah ya tabbatar musu da cewa rayuwar gaba za ta yi musu kyau?
Gaskiyar lamari shi ne cewa abinda ya ke jiransu agaba ita ce azaba mai tsanani wacce za a rubanya musu. Dukiyar da su ke magana akanta kuwa za su barwa magada ne aduniya su isa ga ubangiji hannu rabbana.
Darussan da su ke cikin wannan aya.
1-A mahangar kafirai, kafirci ne ya ke kawo ci gaba, imani kuma yana hana ci gaba. Hakikanin lamari kuwa shi ne akasin haka, kuma sunnar Allah ba ta ayyana cewa kafirci ya zama dalili na ci gaba ba.
2-Dukkanin magangnun da mu ke yi da kuma ayyukanmu ana rubuta su kuma za mu bada jawabinsu.
Karshen wannan shirin kenan sai kuma wani lokaci da za a ji mu da ci gaban shirin.
Suratu Maryam, Aya Ta 81-86 (Kashi Na 535)
Masu sauraro barkanmu da saduwa da ku a cikin wannan shirin na Hannunka mai sanda wanda mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur'ani mai girma.
Da fatan za ku kasance a tare da mu acikin shirin domin jin ci gaba daga inda mu ka tsaya.
Yanzu sai a saurari aya ta 81 da 82 a cikin wannan sura ta Maryam.
وَاتَّخَذُوا مِن دُونِ اللَّهِ آلِهَةً لِّيَكُونُوا لَهُمْ عِزّاً{81} كَلَّا سَيَكْفُرُونَ بِعِبَادَتِهِمْ وَيَكُونُونَ عَلَيْهِمْ ضِدّاً{82}
"Sai su ka riki iyayengiji sabanin Allah saboda su zamar musu- dalilin- daukaka. Ko kadan ( ba za su sami hakan ba) da sannu za su kafircewa bautar da su ke yi musu su kuma zama makiyansu."
A shirin baya mun fadi cewa wasu mutanen sun damfara sukatansu da duniya da daukar cewa dukiya da 'ya'ya su ne za su basu daukaka da karfi. To wannan ayar tana fadin cewa: Kafirai suna neman daukaka ne a wurin wanda ba ubangiji ba. Kuma a ranar kayama wadannan abubuwan da su ke bauta za su kubuta daga gare su, sannan kuma maimakon su cece su za su zama abokan gabarsu ne.
Wasu ayoyin na kur'ani mai girma suna fadin cewa hatta duwatsu da gumakan da mushrikai su ke bautawa za su yi magana da izinin ubangiji a ranar lahira. Za kuma su bayyana kubutarsu ne daga bautar da mushrikan su ka yi musu.
Imam Sadiq (a.s.) yana fadin cewa: Abinda ake nufi da iyayengiji shi ne mutanen masu matsayi wadanda wasu mutane su ke jin cewa kusantarsu yana ba su daukaka. Domin kuwa ibadar da ake magana akanta a cikin wannan aya ba ruku'u da sujjada ba ne, yana nufin daukar umarni da biyayya, kuma duk wanda wajen yin biyayya ga wani mahaluki ya aikata sabon Allah to ya bauta masa."
Darussan da su ke cikin wannan aya.
1-Sun daukaka da matsayi yana a cikin dabi'a wacce Allah ya halicci mutum da ita. Sai dai mutane su na yin kuskure wajen sanin inda ya kamata su nemi wannan daukakar. Maimakon su neme ta a wurin Allah sai su nemeta a wurin mutum.
2-Mutanen da ake damfaruwa da su da daukarsu kamar iyayengiji za su kafircewa mutanen da su ka yi musu biyayya a ranar kiyama.
Yanzu kuma sai a saurari aya ta 83 da 84 acikin wannan sura ta Maryam.
أَلَمْ تَرَ أَنَّا أَرْسَلْنَا الشَّيَاطِينَ عَلَى الْكَافِرِينَ تَؤُزُّهُمْ أَزّاً{83} فَلَا تَعْجَلْ عَلَيْهِمْ إِنَّمَا نَعُدُّ لَهُمْ عَدّاً{84}
"Ashe ba ka ga cewa muna aikewa da shaidanu zuwa ga kafirai ba suna ingiza su ingizawa mai yawa." "Saboda haka kada ka yi gaggawa akan ( halakar) su, muna kididdige kwanakinsu, kididdiga cikakkiya."
Kamar yadda mu ka ambata a baya, babu wani alfanu da kafirai su ke samu daga bautar gumaka da kuma biyayya ga mutane masu dagawa. Kuma su da abubuwan da su ke yi wa bauta za su tsaya a gaban ubangiji a ranar kiyama. Saboda haka me ya sa mu ke yin gaggawa da son ganin sun halaka da sauri? Dukkanin ayyukan da su ke yi an kididdiga su, hatta lumfashin da su ke shaka a kididdige ya ke.
Kididdiga rayuwar mutum yana nufin kididdga ayyukan da ya ke yi aduniya. Kamar kuma yadda zaman jariri a cikin mahaifiyarsa ya ke kai shi ga kamala ta gangar jiki haka nan zamansa a duniya ya ke kai shi ga kamala da cika har zuwa lokacin da ubangiji ya ayyana masa zai rayu.
Saboda haka babu bukatar mutum ya yi fatan mutuwar wani ya kuma so a ce ya mutu da gaggawa. Fajirin kafiri ne ko mumini salihi? Gwargwadon rayuwar kafir mai fajirci a duniya shi ne gwargwadon munanan ayyukan da ya aikata da ake kididdigawa. Haka nan shi ma mumini. Dukkaninsu za su tsaya a gaban ubangiji su bada jawabi.
Darussan da su ke cikin wannan aya.
1-Wadanda su ke zabarwa kawunansu sakamakonsu shi ne shaidan ya shimfida iko akansu ya rika sarrafa su yadda ya ga dama.
2-Shidan yana motsa mutane ne amma ba ya yi musu tilas, duk da cewa motsawar da ya ke yi wa mutane tana da karfi.
3-Sunnar Allah ce ya yi wa mutane daurin talala; Ba ya kuma gaggawa wajen daukar rayukan kafirai.
Yanzu kuma sai a saurari ayoyi na 85 da 86 acikin wannan sura ta Maryam.
يَوْمَ نَحْشُرُ الْمُتَّقِينَ إِلَى الرَّحْمَنِ وَفْداً{85} وَنَسُوقُ الْمُجْرِمِينَ إِلَى جَهَنَّمَ وِرْداً{86}
" Ranar da za mu tayar da masu tsoron Allah zuwa ga ubangiji mai rahama a matsayin manyan baki." "mu kuma kora masu laifi zuwa jahannama a gurguje."
Wannan ayar ta kasa mutane zuwa gida biyu a ranar kiyama. Masu tsoron Allah da kuma masu laifi. Kuma ta yi bayanin halin da kowanensu zai kasance a takaice.
Masu tsoron Allah suna a matsayin bakin ubangiji za a kai su aljanna. Su kuwa masu laifi halinsu ya sha banban. A cikin jin kishiruwa za a kora su zuwa jahannawa kamar yadda ake kora awaki.
An yi amfani da cewa masu tsoron Allah za a tshe su: Zuwa ga Allah, masu laifi kuma zuwa jahannama. Abin fahimta anan shi ne cewa muminai din za su nufi aljanna ne, duk da cewa an bayyana cewa za a tashe su zuwa ga ma'abocin rahama, wanda shi ne kusantar ubangiji.
Wannan ayar ta yi amfani da cewa masu laifi za su nufi jahannama domin a fahimci cewa dalilin shigarsu jahannama shi ne laifin da su ka aikata. Kamar yadda shiga aljanna ya kebanta ne da masu tsoron Allah.
Darussan da su ke cikin wadannan ayoyin.
1-Kiyama rana ce ta bayyanar banbanci da ke tsakanin masu tsoron Allah da kuma masu laifi. Masu tsoron Allah bakin Allah ne, su kuwa masu laifi suna cikin kaskanci.
2-Abinda ya fi shiga aljanna muhimmanci shi ne samun rahamar ubangiji wanda zai shafi 'yan aljanna.
3-Makullin aljanna shi ne tsoron Allah wanda ya kamata ya jagoranci dukkanin rayuwar mutum.
Karshen wannan shirin kenan sai mun sake saduwa da ku a cikin wani shirin domin ci gabansa.
Suratu Maryam, Aya Ta 87-92 (Kashi Na 536)
Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin na Hannunka mai sanda. shiri ne dai wanda mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur'ani mai girma.
Kuma idan ba a mance ba dai har yanzu muna cikin suratu maryam ne.Da fatan za a kasance a tare da mu domin jin ci gaban shirin daga inda mu ka tsaya a baya.
Yanzu sai a saurari aya ta 87 a cikin suratu maryam.
لَا يَمْلِكُونَ الشَّفَاعَةَ إِلَّا مَنِ اتَّخَذَ عِندَ الرَّحْمَنِ عَهْداً{87}
"Babu mai ikon yin ceto sai wanda ya riki alkawali a wurin ubangiji mai rahama."
A cikin shirin da ya gabata mun fadi cewa mushrikai suna damfaruwa da dukiyarsu da kuma 'ya'yansu, adaya gefen kuma suna tsammanin cewa iyayengijin da su ke bauta za su yi musu amfani.
To wannan ayar tana cewa: "Wadannan abubuwan da ku ka rike su a matsayin iyayengiji ba za su iya cetonku ba balle su tseratar da ku daga wuta. Annabawa da imamai da waliyan Allah za su yi ceto idan ubangiji ya basu izini.
Abisa tushe ceto a ranar kiyama yana da sharudda. Ba kowane mutum ba ne zai sami ceto kuma ba kowane mutum ba ne zai yi ceton. Wadanda za a ceta su ne muminai masu ingantacciyar akida wadanda su ka aikata sabo. Idan sun kama kafar waliyan Allah abu ne mai yiyu wa ubangiji ya bada izini su sami ceto.
Samun afuwarsu yana damfare ne da yadda ubangiji ya bada izini ga masu ceton su cece su.
Saboda haka bai kamata mutum ya rika aikata laifi ba a duniya bisa tsammanin cewa zai sami ceto a lahira.
omin kuwa babu tabbacin ko wadanne mutane ne za a ceta.
Darussan da su ke cikin wannan aya.
1-Ceto a hannun Allah ya ke shi ne zai yi izini ga wanda ya ga ya dace.
2-Waliyyan Allah za su sami izinin Ubangiji domin su ceci wasu mutane. Wanann kuma yana daga cikin rahamar ubangiji ga mutane.
Yanzu kuma sai a saurari ayoyi na 88 da 89 a cikin wannan sura ta Maryam.
وَقَالُوا اتَّخَذَ الرَّحْمَنُ وَلَداً{88} لَقَدْ جِئْتُمْ شَيْئاً إِدّاً{89}
"Mushrikai- su ka ce: Ubangiji ma'abocin raham ya riki 'Da." "Hakika kun zo da magana mummuna."
Daya daga cikin akidojin mushrikai shi ne dangantawa ubangiji 'Da. Kuma sun yi imani da cewa mala'iku 'ya'yan Allah ne mata. Abin mamaki shi ne cewa kafin musulunci wannan akidar ta yadu a cikin mushrikai. Haka nan kuma ayoyin kur'ani sun bayyan yadda yahudawa su ka dangantawa Allah Da da shi ne Uzairu. Su kuma kiristoci su ka ce annabi Isa dan Allah ne.
Wannan yana nuni ne da yadda gurbacewa ta shiga cikin addinan da su ka agbata.
Kur'ani mai girma yana maida martani da kakkausar murya akan wannan karkataccen tunani da fadin cewa: Wannan maganar da su ke yi tana da muni."
Darussan da su ke cikin wannan aya.
1-Dangantawa Allah Da, zance ne mummuna. Komai matsayin mutum koda annabi ne kuma waliyi to bai wuce bawa ga ubangiji ba.
2-Yin imani da cewa Allah yana da 'Da shirka ne da kafirci kuma kaucewa tafarkin tauhidi ne.
Yanzu kuma sai a saurari aya ta 90 zuwa ta 92 a cikin suratu maryam.
تَكَادُ السَّمَاوَاتُ يَتَفَطَّرْنَ مِنْهُ وَتَنشَقُّ الْأَرْضُ وَتَخِرُّ الْجِبَالُ هَدّاً{90} أَن دَعَوْا لِلرَّحْمَنِ وَلَداً{91} وَمَا يَنبَغِي لِلرَّحْمَنِ أَن يَتَّخِذَ وَلَداً{92}
"Sammai suna neman tarwatsewa kassai kuma tsagewa daga wannan ( mummunan zance) duwatsu kuma su yi rugu-rugu." "Saboda sun dangantawa ma'abocin rahama "Da. "Ba abu ne da ya dace ga ma'aboci rahama ya riki 'Da ba."
Saboda tsarin halitta baki dayansa ya ginu ne bisa tauhidi ya ke girgiza idan aka dangantawa ubangiji 'Da. Wannan ayar tana fadin cewa: Sama da kasa da duwatsu sun kusa tarwatsewa aduk lokacin da wadannan mushrikan su ka dangantawa Allah 'Da.
Sammai da kassai ba su iya daurewa jin an dangatawa Allah "Da. Allah ba shi da bukatuwa da 'Da saboda haka bai dace ba ya rike shi, domin ba alamar kamala ba ce gare shi kaskantar da matsayinsa ne.
Darussan wadannan ayoyin.
1-Aikata sabo zai iya haddasa rushewar tsarin duniya.
2-Shirka shi ne fasadi mafi muni da hatsari a duniya wanda ya sa hatta dabi'a ta ke girgiza.
3-'Da, ba ya samuwa sai da mata, ubangiji kuwa ba shi da tamka balle ya riki mace ya zamana yana da 'da.
Karshen wannan shirin kenan.
Suratu Maryam, Aya Ta 93-98 (Kashi Na 537)
Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin da mu ke kawo mu ku fasarar ayoyin kur'ani mai girma. Idan kuma ba'a manta ba har yanzu muna cikin suratu maryam ne.
Da fatan za a kasance a tare da mu domin a ji ci gaban shirin daga inda ya tsaya a baya.
Yanzu sai a saurari aya ta 93 a cikin suratu Maryam.
إِن كُلُّ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ إِلَّا آتِي الرَّحْمَنِ عَبْداً{93}
" Babu wani abu wanda ya ke cikin sammai da kasa sai ya zo wa ubangiji ma'abocin rahama yana a matsayin bawa ."
A cikin shirin baya mun yi magana akan cewa mushrikai suna daukar mala'iku da kuma wasu abubuwan da su ke bauta a matsayin iyayengiji, kur'ani kuma ya maida musu martani ta hanyar rusa waccan akidar tasu.
To wannan ayar tana cewa: Ba ku mutane kadai ba, hatta mala'iku da kowa da komai suna a matsayin bayi ne ga Allah kuma aranar lahira hakan za ta fito fili. Alaka a tsakanin Allah da halittu tana a matsayin ta ubangiji ce da bayi, ba alaka ce ta Uba da 'Da ba, ko kuwa wani nau'in alaka na daban.
Kuma tare cewa dukkanin wadannan halittun na ubangiji da su ke a cikin sammai da kassai suna a matsayin bayi ne a wurinsa, ubangijin ba shi da bukatuwa da ibadarku. Hakikanin lamari shi ne cewa ku ne ku ke bukatuwa ku yi masa bauta.
Darussan da su ke cikin wannan aya.
1-Kowa da komai da su ka hada mala'iku da mutane suna a matsayin bayi ne ga ubangiji, kuma babu wani mahaluki da ya ke da ya mallaki rayuwarsa ko mutuwarsa.
2-Dukkanin halitta baki dayanta, tana a karkashin ikon ubangiji ne kuma za su koma ne zuwa gare shi.
Yanzu kuma sai a saurari aya ta 94 da kuma 95 a cikin wannan sura ta Maryam.
لَقَدْ أَحْصَاهُمْ وَعَدَّهُمْ عَدّاً{94} وَكُلُّهُمْ آتِيهِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فَرْداً{95}
"Hakika shi ya kididdige su, ya kuma lissafasu daya bayan daya." "Kuma dukkaninsu za su zo masa a ranar kiyama kwara-kwara."
Wannan ayar tana yin magana ne da harshen da mutane za su fahimta akan cikakkiyar masaniyar da Allah ya ke da ita akan halittunsa. Domin kuwa sanin Allah da halittun da ya yi baya bukatuwa da lissafi da kididdiga irin wanda mutane su ke yi. Kuma masaniyarsa da halittun ta ciki da waje ce domin kuwa shi ne makirkirinsu.
Kuma a ranar kiyama kowane daga cikin wadannan halittun zai zo ga ubangiji shi kadai ya bada jawabi, saboda kada wani ma ya yi zaton cewa cincirindon taron mutane a ranar kiyama zai sa ya boye ko ya labe a bayan wasu. Sannan kuma babu dangi ko 'ya'ya da za su yi masa rakiya a lokacin tsayuwa a gaban ubangiji, mutum ne daga shi sai aikinsa.
Darussan da su ke cikin wannan aya.
1-Ubangiji yana da cikakkiyar masaniya akan kowa da koma kuma farin sani, ciki da waje.
2-A ranar kiyama, kowane mutum shi kadai ne kuma kowa zai shagalta ne da aikinsa, hankalinsa ma ba zai kai ga waninsa ba saboda yana ta kanshi.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 96 a cikin wannan sura ta Maryam.
إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ سَيَجْعَلُ لَهُمُ الرَّحْمَنُ وُدّاً{96}
"Tabbas wadanda su ka yi imani su ka kuma yi aiki na-gari, ubaniji zai san a kaunace su."
A cikin wasu shirye-shirye da su ka gabata mun ambaci cewa, a ranar kiyama iyayengijin da mushrikai su ke bauta za su kubuta daga gare su, sannan kuma su zame musu abokan gaba.
To wannan ayar tana cewa muminai wadanda su ke yin ayyukan da ubangij ya yi umarni, ba kaunar ubangiji kadai za su samu ba, kuma Ubangijin zai cusa kaunarsu a cikin zukatan mutane. Hatta makiya acikin birnin zukatansu suna kaunar mutanen kwarai, duk da cewa a zahiri suna yin fada da su saboda kare manufofinsu na abin duniya. Da akwai misalai da dama akan hakan a tsawon tarihi.
A bisa raiwayoyi da dama, Imam Ali (a.s) yana daga cikin mutanen da wannan ayar ta sauka ne akansu. Kuma tarihi shi ne shaida akan cewa makiyansa ma suna bada shaida akan tsarkinsa kuma suna yabonsa.
Darussan da za mu koya daga cikin wadannan ayoyin.
1-Imani da aiki kwarai suna da jan hankali mutane, domin kuwa mutane bisa dabi'arsu suna son tsarki da gaskiya da jarunta da sadaukar da kai. Hatta mutane marasa tsarki suna son wadannan siffofin.
2-Ubangiji ne ya ke cuwa kaunar mutane a zukata, domin kuwa dukkanin zukata suna hannunsa ne.
Yanzu kuma sai a saurari ayoyi na 97 da 98 a cikin wannan ta Maryam.
فَإِنَّمَا يَسَّرْنَاهُ بِلِسَانِكَ لِتُبَشِّرَ بِهِ الْمُتَّقِينَ وَتُنذِرَ بِهِ قَوْماً لُّدّاً{97} وَكَمْ أَهْلَكْنَا قَبْلَهُم مِّن قَرْنٍ هَلْ تُحِسُّ مِنْهُم مِّنْ أَحَدٍ أَوْ تَسْمَعُ لَهُمْ رِكْزاً{98}
" Mun saukake maka shi- kur'ani- akan harshenka, saboda ka yi wa masu takawa bushara da shi, ka kuma gargadi mutane masu karkata." "Mun halakar da mutane da dama a gabaninsu, ko kana jin duriyar wani daga cikinsu, ko kuwa kana jin muryarsu? "
Wadannan ayoyin da su ke a matsayin karshen ayoyin suratu Maryam suna yin magana ne akan matsayin kur'ani mai girma na shiryar da mutane da kuma samar musu sa'ada. Tana cewa mun saukar maka da wadannan ma'anonin na koli da kuma ilimin da ke ciki tare da saukake shi akan harshenka domin mutane su amfana da shi. Masu tsarki za su karfafa marasa tsarki kuma su fahimci cewa kamun Allah da azabrsa hakika ce samammiya, su kuma dauki darasi daga rayuwar mutanen da su ka gabata.
Kada kafirai su tsammaci cewa za su iya kaucewa kamun ubangiji ko kuma su ji cewa za su iya rusa gaskiya. Idan za su yi dubi akan tarihin al'ummun da su ka gabata za su ga cewa babu su babu labarinsu.
Darussan da su ke cikin wadannan ayoyin.
1-Hanyar shiryar da mutane ita ce, yin bayanin koyarwar addini da ta zo a cikin kur'ani da harshe mai sauki da kowa da kowa zai fahimta.
2-Wajibi ne a yi wa kowadanne mutane da harshen da za su fahimta, a karfafa muminai da yi musu bushara, su kuma makiya a yi musu gargadi.
Karshen shirin namu kenan, da fatan an amfana da abinda mu ka saurara daga farkon shirin har zuwa yanzu. Wassalamu Alaikum Wa rahmatullahi Wa Barakatuhu.