Toggle menu
24.1K
669
183
158.4K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/7/IRIB Hausa Tafsir

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

Suratul A'araf, Aya Ta 1-5 (Kashi Na 225)

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.

A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 1 zuwa 2 da suke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

المص{1} كِتَابٌ أُنزِلَ إِلَيْكَ فَلاَ يَكُن فِي صَدْرِكَ حَرَجٌ مِّنْهُ لِتُنذِرَ بِهِ وَذِكْرَى لِلْمُؤْمِنِينَ{2}

"A. L̃. M̃. Ṣ̃" {Wannan} Littãfi ne da aka saukar zuwa gare ka, saboda haka kada wani kunci ya kasance a cikin kirjinka dangane da shi, dõmin ka yi gargadi da shi. Kuma tunãtarwa ne ga mũminai".

A'arafi suna ne na wani yanki a lahira kamar yadda ake da aljanna da wuta, inda wannan yankin zai kasance mazauni wasu daga cikin mutane, aya ta 46 da 48 da suke cikin wannan surah sun ambaci gungun mutanen da suke wannan yankin na A'araf kuma daga nan ne aka samo sunan, don haka ake kiran wannan surah da suratul-A'araf. Daga cikin surori dari da goma sha hudu da suke cikin alkur'ani mai girma, ashirin da tara daga cikinsu sun fara ne da kuramen haruffa kuma suratul-A'arafi tana daga cikinsu. Kamar yadda muka bayyana a suratul-Baqara kuramen haruffan wani sirri ne tsakanin Allah da Manzonsa wanda hakikanin ma'anarsu zasu bayyana a lokacin bayyanar Imam Al-Mahdi {a.s}, amma kamar yadda ya zo cikin tafsiri ana fassara sune da cewa; Allah yana son bayyana cewa ne; na saukar da wannan kur'ani ne da wallafa shi daga wadannan haruffa, ba da wani sabon yare ko kalmomi na wallafa ba, daga wannan haruffa da kalmomin larabci da aka saba amfani da shi na wallafa littafin, wanda kuka kasa zuwa da makamancinsa.

Aya ta biyu kuma tana nuni ne da cewa: Ya kai Annabi wannan littafi tabbas daga wajen Allah ne aka saukar gare ka, kuma dukkanin abin da ke cikinsa gaskiya ne, saboda haka kada rashin amincewar mushrikai da kafirai da littafin ya sanya ka kokwanto kansa ko shiga cikin kangin damuwa da zai kuntata maka, iyaka dai aikinka shi ne isar da sakon Allah da gargadi ga mutane, su kuma mutane suna da 'yancin amincewa da zancenka ko rashin amincewa.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:

{1} Isar da sakon addini da kiran mutane zuwa ga hanyar Allah yana bukatar budeddiyar zuciya da karfin juriya.

{2} Aikin Annabawa shi ne gudanar da wa'azi da gargadi, ba tilasta mutane da wajabta musu yin imani ba.

Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 3 da ke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

اتَّبِعُواْ مَا أُنزِلَ إِلَيْكُم مِّن رَّبِّكُمْ وَلاَ تَتَّبِعُواْ مِن دُونِهِ أَوْلِيَاء قَلِيلاً مَّا تَذَكَّرُونَ{3}

"Ku bi abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, kuma kada ku dinga bin wasu majibinta baicinSa. Kadan ne kwarai masu wa'azantuwa".

Ayar da ta gabata ta yi bayanin cewa; aikin Annabi shi ne gudanar da wa'azi da gargadi ga mutane, amma wannan ayar tana bayani ne kan hakkin da ya hau kan mutane na amsa kira da yin biyayya ga kur'ani. Duk da cewa kur'ani ya sauka ne ga Manzon Allah, amma a hakika kur'anin ya sauka ne ga mutane wanda Manzon Allah yake matsayin wakilin wahayi, kuma mai fassararsa a tsakaninsu. Sannan abu mafi muhimmanci a cikin wannan ayar shi ne; baya ga wasici da yin riko da koyarwar alkur'ani, ayar kuma ta yi hani ga mutum kan bin wasu hanyoyi da suka yi hannun riga da koyarwar alkur'ani mai girma, wato ayar tana bayyana cewa; hanyar gaskiya da zata tsiratar da mutum ita ce kawai bin littafin Allah.

A cikin wannan ayar zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Matsayin Allah na Ubangiji kuma majibancin dukkanin al'amura, to shi ke da hakkin saukar da dokoki da umurni da zasu shiryar da mutane tare da kai su ga rayuwar jin dadi.

{2} Duk wanda bai dauki Allah Makadaici a matsayin Ubangiji kuma mai jibantar al'amura ba, to zai afka cikin rudun daukan wasu abubuwa a matsayin masu jibantar al'amuransa, kuma maimakon ya amince da Allah Makadaici, to zai amince da wasu abubuwa masu yawa a matsayin majibantarsa.

Yanzu kuma zamu saurari aya ta 4 zuwa 5 da suke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

وَكَم مِّن قَرْيَةٍ أَهْلَكْنَاهَا فَجَاءهَا بَأْسُنَا بَيَاتاً أَوْ هُمْ قَآئِلُونَ{4} فَمَا كَانَ دَعْوَاهُمْ إِذْ جَاءهُمْ بَأْسُنَا إِلاَّ أَن قَالُواْ إِنَّا كُنَّا ظَالِمِينَ{5}

"Kuma akwai da yawa daga alkaryu da Muka halaka, sai azãbarMu ta je musu da dare kõ kuma sunã mãsu kailũla". "Sannan bãbu abin da suke riyawa lõkacin da azãbarMu ta jẽ musu, fãce suka ce: "Lalle ne mũ mun kasance mãsu zãlunci,"

Ayar da ta gabata tana bayani ne kan wajabcin yin riko da alkur'ani mai girma, yayin da wannan ayar ke bayanin cewa; duk da tsananin kokari da gwagwarmayar da Annabawa ke yi wajen ganin sun shiryar da mutane, kuma babu wani kasa a gwiwa da suke yi kan hakan, amma duk da haka kadan ne daga cikin mutane suke amsa kiransu da yin riko da hanyar shiriya, don haka ayyukan laifuka na fasikanci da tsageranci suke wanzuwa a tsakanin mutane sai azabar Allah ta sauka a kansu, duk da cewa a ranar kiyama ce ake tarar asalin sakamakon ayyuka na lada da azaba, amma wasu laifuka misalin gudanar da zalunci kan wasu, Allah yana dauka fansansu kan azzalumai tun daga nan duniya a lokacin da ba zato ba tsammani, sai azzalumai su wayi gari cikin hasara suna masu furuci kan zaluncin da suka gudanar, tare da ikrarin cewa sun cancanci azabar da aka saukar kansu.

Hakika irin wannan furuci ba ya da wani amfani ko kima, kuma furuci ne da ba zai tseratar da azzalumai daga azabar Allah ba, amma irin wannan lamari zai iya kasance mana wa'azi da fadakarwa, misali idan muka yi takaitaccen nazari kan tarihin gwamnatoci da azzaluman shugabanni-irin manyan daulolin Farisa da Roma- saboda zaluncin da suka gudanar kan mutane hakan ya yi sanadiyyar tarwatsewarsu, kuma aka maye gurbinsu da wasu gwamnatocin.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Azabar Allah bata takaita da ranar kiyama ba kawai, don haka kada mu taba tsammanin samun aminci da kwanciyar hankali a lokacin da al'umma ta dulmiya cikin ayyukan laifuka, dole ne mu jira saukar nau'o'in azaba.

{2} Kafin azaba ta sauko mana tare da yin furuci da laifukan da muka aikata a gaban fadar Allah, muna da damar da zamu tuba ga Allah da hakan zai hana saukar azaba a kanmu tare da samun rahamar Allah Madaukaki.

To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul A'araf, Aya Ta 6-10 (Kashi Na 226)

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.

A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 6 zuwa 7 da suke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

فَلَنَسْأَلَنَّ الَّذِينَ أُرْسِلَ إِلَيْهِمْ وَلَنَسْأَلَنَّ الْمُرْسَلِينَ{6} فَلَنَقُصَّنَّ عَلَيْهِم بِعِلْمٍ وَمَا كُنَّا غَآئِبِينَ{7}

"Saboda haka lalle ne zamu tambayi wadanda aka aika musu da {manzanni}, kuma lalle ne zamu tambayi Manzannin". "Sannan kuma hakĩka zamu ba su lãbãri kan sani na hakika, kuma ba Mu kasance mãsu fakowa ba".

A shirinmu da ya gabata mun tabo batun azabar da ake saukarwa ga azzalumai ne da masu wuce gona da iri tun a nan rayuwar duniya, yayin da wadannan ayoyi suke bayyana cewa: Asalin sakamakon ayyukan halittu na lada da azaba ana tarar da su ne a ranar kiyama, inda dukkanin mutane ciki har da Annabawa da Manzonni zasu fuskanci tambayoyi da hisabi kan kyawawan ayyukansu da munana da suka gudanar, duk kuwa da cewa; Allah yana sane da dukkanin ayyukan da bayinsa suka aikata a rayuwar duniya, amma Allah zai tsayar da bayinsa a ranar kiyama ce domin cika hujja a kansu ta hanyar tabbatar musu da abin da suka aikata.

Ya zo cikin ruwaya cewa: Allah zai yi hisabi wa mutane a kan duk wata ni'ima da ya ba su, ciki har da gabobin da suke jikin dan Adama da rayuwarsu tun daga yaranta har zuwa tsufa, haka nan shugabanci, wato dole ne dukkanin mutane su amsa tambayoyi kan ayyukansu da dabi'unsu, sai dai kowa za a masa hisabi ne gwargwadon irin ni'imar da aka bashi.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Dukkanin mutane zasu fuskanci hisabi a ranar kiyama ciki har da Annabawa da shugabannin al'umma, inda za a tambayi Annabawa; shin sun gudanar da ayyukan da aka daura musu na shiryar da mutane tare da fadakar da su? Kuma a tambayi mutane; shin sun amsa kira tare da yin biyayyya ga Annabawan?

{2} Tambayar ranar kiyama domin masu laifi su yi ikrari da ayyukansu na laifi ne, tare da aibanta su kan abin da suka aikata na laifuka, da jinjinawa bayin Allah da suka gudanar da kyawawan ayyuka a rayuwarsu.

Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 8 da ke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

وَالْوَزْنُ يَوْمَئِذٍ الْحَقُّ فَمَن ثَقُلَتْ مَوَازِينُهُ فَأُوْلَـئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ{8}

"Kuma awo a wannan rãnar na gaskiya ne. Saboda da haka duk wanda ma'aunansa suka yi nauyi, to wadannan sũ ne mãrabauta"

Hakika Allah ne alkali a kotun ranar kiyama, inda zai tara dukkanin halittu a wannan ranar ya gudanar musu da hisabi, kuma hisabinsa zai kasance ne a kan tubalin gaskiya da adalci a tsakanin bayinsa, ba hisabi ba ne da zai gudanar a kan rashin tsari da kafa hujja kamar yadda wasu al'ummar musulmi ke cewa: Tun da Allah shi ne mai iko a kan komai yana da hakkin gudanar da hukunci yadda ya ga dama koda kuwa zalunci ne, amma a hakika Allah Madaukaki a cikin wannan ayar yana bayyana cewa: A kan tubalin gaskiya da adalci zan yi hukunci kan ayyukan.

Mafi daukakan mizani na auna ayyukan mutane a ranar kiyama shi ne kwatanta ayyuka mutane da na cikakkun halittu misalin Annabawa da Salihan Bayinsa.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Lalle ranar kiyama gaskiya ce, hisabi gaskiya ne, kuma a kan tubalin adalci za a yi hukunci a tsakanin halittu.

{2} Tsammanin tsira da rabauta a ranar kiyama- ba tare da gudanar da kyawawan ayyuka masu nauyi ba- tsammani ne maras amfani da kima.

Yanzu kuma zamu saurari aya ta 9 da ke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

وَمَنْ خَفَّتْ مَوَازِينُهُ فَأُوْلَـئِكَ الَّذِينَ خَسِرُواْ أَنفُسَهُم بِمَا كَانُواْ بِآيَاتِنَا يِظْلِمُونَ{9}

"Kuma wanda ma'aunansa suka yi sauki, to, wadannan su ne wadanda suka yi hasarar rayuwarsu, sabõda kasancewarsu masu jayayya da ãyõyinMu".

A cikin wannan aya da wadda ta gabace ta sun jaddada batun yawan ayyuka da ingancinsu, sannan suna bayyana cewa: Wanda ma'aunin ayyukansa ya yi sako-sako a ranar kiyama ya yi hasarar rayuwa, kuma babu hasarar da tafi wannan, saboda ba a samu wata riba a rayuwa ba. Rayuwar mutum kamar kankara ce matukar ba a yi amfani da ita ba, to zata narke ya zame an yi hasarar jarinta.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Karancin kyawawan ayyuka yana janyo hasara a ranar kiyama, ina kuma babu ayyukan kwata-kwata.

{2} Duniya kamar kasuwa ce, jarinta shi ne rayuwa, ribarta kuma shi ne aiki na gari, don haka rashin gudanar da kyakkyawan aiki ba karamar hasara ba ce.

Yanzu kuma zamu saurari aya ta 10 da ke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

وَلَقَدْ مَكَّنَّاكُمْ فِي الأَرْضِ وَجَعَلْنَا لَكُمْ فِيهَا مَعَايِشَ قَلِيلاً مَّا تَشْكُرُونَ{10}

"Kuma hakĩka Mun sarautar da ku a kan kasa, kuma muka sanya muku hanyoyin samun abinci a cikinta; kadan ne kwarai masu gõdẽwa {daga cikinku}".

A ci gaba da bayani kan gabatar da sakamakon ayyuka mai kyau ko maras kyau a ranar kiyama, a cikin wannan aya Allah yana bayyana cewa: Hakika mun azurta ku da duk nau'o'in ni'ima da jin dadi tare dab a ku damar amfani da su a kan ku kasance mutane na kwarai, amma abin bakin ciki kadan ne daga cikinku suke godiya.

A fili yake cewa; godiya ta fatar baki ba ita ce kawai godiyar ni'imar Allah ba, saboda mafi daukakan godiyan Allah yin amfani da ni'imominsa ta hanyar da ta dace da babu sabonsa ciki. Misali 'ya'yan marmari irin Inabi yana daga cikin ni'imar Allah ga mutane, don haka amfani da Inabin ta hanyar da Allah ya amince yana daga cikin godiyansa, amma sarrafa Inabin wajen samar da giya yana daga cikin nau'in sabawa Allah mahalicci kuma kafircewa ni'imarsa ne. Haka nan dantse da ke jikin mutum ni'ima ne da Allah ya yi masa domin biyan bukatunsa da gudanar da hidima ga sauran sauran halittu, amma Allah ya halitta wa mutum dantsen ba ne domin cutar da mutane da musguna musu.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Amfani da ni'imomi da arzikin da suke karkashin kasa, hakki ne na dukkanin mutane babu bambanci a tsakaninsu, kuma babu wani da yake da fifiko a kan dan uwansa.

{2} Dole ne ni'imomi su kasance dalilin godiyan Allah, ba wai su zame dalilin gafalar mutane da mance Allah ba, ko dalilin yaudaruwa da duniya da yin nitso cikin sharholiya ba.

To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul A'araf, Aya Ta 11-15 (Kashi Na 227)

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.

A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 11 zuwa 12 da suke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

وَلَقَدْ خَلَقْنَاكُمْ ثُمَّ صَوَّرْنَاكُمْ ثُمَّ قُلْنَا لِلْمَلآئِكَةِ اسْجُدُواْ لآدَمَ فَسَجَدُواْ إِلاَّ إِبْلِيسَ لَمْ يَكُن مِّنَ السَّاجِدِينَ{11} قَالَ مَا مَنَعَكَ أَلاَّ تَسْجُدَ إِذْ أَمَرْتُكَ قَالَ أَنَاْ خَيْرٌ مِّنْهُ خَلَقْتَنِي مِن نَّارٍ وَخَلَقْتَهُ مِن طِينٍ{12}

"Kuma hakĩka Mun halicce ku, sannan kuma Muka sũrantã ku, sannan kuma Muka ce da malã'iku: "Ku yi sujada ga Ãdam." Sai suka yi sujadar fãce Iblĩs, bai kasance daga mãsuyin sujadar ba". "Ya ce: "Mẽne ne ya hana ka yi sujada a lõkacin da Na umurce ka?" Sai ya ce: "Ai ni ne mafĩfĩci a kansa, Ka halicce ni ne daga wuta, alhãli kuwa Kã halicce shi ne daga yunbu".

A shirin da ya gabata an yi nuni ne kan ni'imomin da Allah ya yi wa mutane domin amfanin rayuwarsu, amma wadannan ayoyi suna nuni ne kan matsayin mutum a farkon halittansa, inda suke bayyana cewa: Ba kawai ni'imomin da suke kasa ba har ma ma'abuta sama da Mala'iku sun rusuna wa mutum da kankantar da kai gare shi, kuma matsayin mutum da daukakansa ya kai ga Allah ya umurci Mala'ikunsa da su yi sujjada ga Adam, a wannan lokacin Iblis ne kawai baya daga cikin jinsin Mala'iku da aka musu umurnin yin sujjada ga Adam, duk da cewa yana cikin sahun Mala'iku, amma ya yi tawaye ga umurnin Allah.

Kamar yadda ya zo cikin sauran ayoyin kur'ani, Iblis yana daga cikin jinsin aljanu ne, amma saboda tsananin ibadunsa ya kasance a cikin sahun Mala'iku, don haka umurnin Allah ya hada da shi.

Ba kawai Iblis yaki nemi uzuri kan rashin bin umurnin Allah ko nuna bakin cikinsa kan abin da ya aikata ba ne, har ma yana kokarin kare matsayin tawayen da ya yi ne da cewa: Allah ka halicce ni ne daga wuta, shi kuma Adam ka halicce shi ne daga yunbu, kuma wuta ta fi daukaka a kan yunbu. Wannan da'awa ta Iblis bata da tushe domin umurnin Allah na yin sujjada ga Adam ba yana magana ba ne kan asalin sinadarin da aka halicci Adam ballantana Iblis ya bijiro da wannan zance, iyaka dai saboda matsayi da daukaka da Adam ya samu ne na daga wajen Allah da kuma ruhin da Allah ya hura masa, don haka dangane da umurnin Allah na yin sujjada ga Adam babu maganar bijiro da wani uzuri ko dabara ko kuma hujja ta kiyasi, a nan kamar Iblis yana son cewa ne; ni na fi Allah fahimta kuma umurnin da Allah ya yi masa na yin sujjada ga Adam kuskure ne! Abin bakin cikin wasu mutane ma suna kokarin yin kiyasi da hankalinsu a kan hukunce-hukunce da umurnin Allah, alhali mafi yawan hukunce-hukuncen shari'a sun shige matsayin hankulanmu, domin zurfin hankalinmu yana da iyaka, kuma a matsayinmu na bayin Allah, babu abin da yake kanmu sai mika wuya da yin biyayya ga hukunce-hukuncensa, ba tare da yin shisshigi ba.

A cikin wadannan ayoyi zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Mutane suna da dama da cancantar kai wa ga matsayin da Mala'iku za su yi musu sujjada.

{2} Idan dai dukkanin Mala'iku zasu bi umurnin Allah su yi sujjada ga mutum, to lalle abin bakin ciki ne a samu mutane ba su yin sujjada ga Allah da yin biyayya ga umurninsa.

{3} Kasancewar mutum namiji ko mace ko dan kabila kaza, hakan baya zama dalilin daukakansa, kamar yadda yawan shekaru da kwarewa ba su zama dalilin daukaka, iyaka dai mika kai da biyayya ga umurnin Allah shi ne dalilin daukaka.

{4} Mene ne dalilin da zai sanya mutum ya zama mai yin biyayya ga shaidan, alhali shaidan ba a shirye yake ya yi sujjada ga mutum ba ko girmama shi?.

Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 13 da ke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

قَالَ فَاهْبِطْ مِنْهَا فَمَا يَكُونُ لَكَ أَن تَتَكَبَّرَ فِيهَا فَاخْرُجْ إِنَّكَ مِنَ الصَّاغِرِينَ{13}

"{Allah} Ya ce: "To, ka sauka daga gare ta {wato aljanna} dõmin bãi kamata ka yi girman kai a cikinta ba. Saboda haka ka fita. Hakika kai kanã daga cikin kaskantattu".

Wannan aya tana ci gaba da bayanin tawaye da girman kai da shaidan ya yi ne ga umurnin Allah, inda take nuni da cewa: Sakamakon rashin bin umurnin Allah sau guda da shaidan ya yi, ya rasa matsayin da yake da shi tsawon shekaru na cikekken bawan Allah a fadar Ubangijinsa, kuma Allah ya kore shi daga cikin sahun Mala'iku yana ce masa: Sakamakon wannan girman kai da jin fifiko ka fice kana kaskantacce.

Kamar haka ne Manzon Allah {s.a.w} ke bayyana cewa: Duk wanda ya kankantar da kai da tawali'u Allah zai daukaka shi, kuma duk wanda ya yi girman kai da nuna ji-ji da kai, Allah zai kaskantar da shi tare da mai da shi abin takewa a taron ranar kiyama.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Ilimi da ibada kadai ba zasu tseratar da mutum ba, sai da cikekken biyayya ga Allah - Saboda shaidan masani ne kuma mai gudanar da ibada ga Allah, amma ba a shirye yake ya kasance mai cikekken biyayya ga Allah ba- .

{2} Girman kai yana sanadiyyar rusa kyawawan ayyukan mutum, kuma yana kai shi ga kan iyakar rushewa.

Yanzu kuma zamu saurari aya ta 14 zuwa 15 da suke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

قَالَ أَنظِرْنِي إِلَى يَوْمِ يُبْعَثُونَ{14} قَالَ إِنَّكَ مِنَ المُنظَرِينَ{15}

"{Iblis} Ya ce: "Ka yi mini jinkiri har zuwa rãnar da za a tãyar da su". "{Allah} Ya ce: "Hakika kanã daga wadanda aka yi wa jinkiri".

Bayan fitar da shaidan daga fadar Allah, shaidan ya bukaci Allah da ya jinkirta masa ya barshi a raye har zuwa ranar kiyama, sai Allah ya karbi rokonsa, don haka zake ci gaba da rayuwa har zuwa lokacin da za a tashi kiyama. A nan za a iya gabatar da tambayar cewa; Mene ne dalilin da zai sanya Allah ya jinkirta wa shaidan har zuwa tashin kiyama? Dangane da amsar wannan tambaya, sai a ce: A ranar kiyama ce ake tarar da asalin sakamakon ayyukan da aka aikata na lada ko azaba, don haka Allah yake jinkiri ga masu laifi zuwa wannan ranar, saboda haka ba wai da zarar mutum ya aikata babban laifi, sai kawai Allah ya hanzarta saukar masa da azaba ko ya halaka shi.

Baya ga haka a karkashin sunnan Allah na jaraba mutum, dole ne ya sanya shi a tsakanin alheri da sharri saboda 'yancin da ya bashi na zaben mai kyau ko maras kyau ya kasance mai ma'ana, don haka shaidan yana daga cikin hanyoyi jarraba mutane. Har ila yau dole ne a san cewa; shaidan bayan tilasta mutane a kan gudanar da aikin laifi, aikinsa shi ne sanya waswasi a cikin zukatansu, amma mutum yana da cikekken 'yancinsa na zaben hanyar da ya ga dama.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

Allah yana jinkiri ga masu aikata laifuka, watakila mai laifin ya yi amfani da wannan jinkirin wajen tuba daga laifin da yake aikatawa.

Shaidan yana da masaniya kan ranar kiyama, amma baya dauke da cikekken imani da Allah da ranar ta alkiyama, don haka baya tunanin tuba da yin nadama kan laifin da ya aikata.

To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul A'araf, Aya Ta 16-19 (Kashi Na 228)

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.

A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 16 zuwa 17 da suke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

قَالَ فَبِمَا أَغْوَيْتَنِي لأَقْعُدَنَّ لَهُمْ صِرَاطَكَ الْمُسْتَقِيمَ{16} ثُمَّ لآتِيَنَّهُم مِّن بَيْنِ أَيْدِيهِمْ وَمِنْ خَلْفِهِمْ وَعَنْ أَيْمَانِهِمْ وَعَن شَمَآئِلِهِمْ وَلاَ تَجِدُ أَكْثَرَهُمْ شَاكِرِينَ{17}

"{Iblis} Ya ce: "Saboda halakarwar da Ka yi mini, To lalle wallahi zan zauna {in bambanke} musu hanyarka madaidaici". "Sannan kuma hakĩka zan je musu ta gabansu da ta bãyansu da ta damansu da kuma ta hagunsu; saboda haka bã zã ka sãmi mafi yawansu mãsu gõdiya ba."

A cikin shirin da ya gabata mun bayyana cewa: An kori shaidan daga fadar Allah saboda rashin bin umurnin Allah na yin sujjada ga Adam, lamarin da ya wurga shi cikin fushin Allah, amma kasancewar a karkashin sunnan Allah asalin hisabi da tarar da sakamakon ayyuka na lada ko azaba zasu kasance ne a ranar kiyama, don haka Allah yana jinkirtawa masu laifi a duniya domin su yi amfani da wannan damar su tuba ko kuma har dubunsu ya cika, to haka nan shi ma shaidan aka masa jinkiri zuwa ranar kiyama.

A cikin wadannan ayoyi zamu ga cewa; shaidan ya yi alkawarin daukan fansa kan mutum saboda a sanadiyyarsa ne ya halaka kuma aka kore shi daga cikin fadar Allah, inda yake cewa zai farma mutum ta hanyoyi hudu, kuma ta kowace hanya zai kai ga burinsa na batar da mutum.

Ya zo cikin ruwaya Manzon Allah yana cewa: Bayan shaidan ya yi alkawarin daukan fansa kan mutum ta hanyoyi hudu, sai Mala'iku suka ce: Ya Allah; ta yaya mutum zai tseratar da kansa? Sai Allah ya amsa musu da cewa: Akwai hanyoyi biyu da suke bude a sama da kasa, a duk lokacin da mutum ya daga hannuwa sama ya yi addu'a ko ya sanya goshi a kasa ya yi sujjada, to zai tsira daga sharrin shaidan. A cikin wannan ayoyi zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Aikin shaidan ne mutum ya jingina aikin laifinsa da bijirewa umurnin Allah ga Allah ta hanyar cewa haka Allah ya so ko kuma shi ya kaddara hakan.

{2} Shaidan makiyi ya yi rantsuwar halakar da mutum, to maimakon mu biye masa, mu kara matsa kaimi mu kasance masu biyayya ga Allah mai jin kai.

{3} Wasiwasin shaidan ya tabaibaye mutum ta kowane bangare kuma mutum yana cikin tarkonsa, don haka wajibi ne mu kasance cikin kare kanmu a kullum.

Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 18 da ke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

قَالَ اخْرُجْ مِنْهَا مَذْؤُوماً مَّدْحُوراً لَّمَن تَبِعَكَ مِنْهُمْ لأَمْلأنَّ جَهَنَّمَ مِنكُمْ أَجْمَعِينَ{18}

"{Allah} Ya ce: "Ka fita daga gare ta kanã abin zargi kõrarre. Lalle ne duk wanda ya bĩ ka daga cikinsu, ba shakka zãn cika jahannama da ku gabã daya."

A cikin wannan ayar Allah ya sake mai da martani ne kan rantsuwar da shaidan ya yi na cewar zai batar da mutane, inda ke bayyana cewa: Kai da duk wanda ya bi hanyarka zaku fuskanci kaskanci da kunya, sannan zaku shiga cikin wutan jahannama tare da fuskantar azaba matsananciya, kuma Allah ya cewa shaidan; ka fice daga wannan waje, saboda waje ne na tsarkaka da salihai da kuma masu biyayya.

Lalle laifin da shaidan ya aikata na girman kai, ji-ji da kai, yaudaran kai da alfahari shi ne ya yi sanadiyyar ficewarsa daga fadar Allah, kuma duk mutumin da ya yi girman kai ga umurnin Allah, to ya kama hanyar shaidan, kuma zai fuskanci kaskanci da wulakanta kamar shaidan.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Shaidan yana cusa waswasi ne a zukata, amma baya tilasta kowa kan aikata laifi, don haka mutum ne da kansa ke daukan matakin bin hanyar shaidan.

{2} Hakika bin shaidan a duniya zai kai ga zama tare da shi a makoma daya a ranar kiyama.

Yanzu kuma zamu saurari aya ta 19 da ke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

وَيَا آدَمُ اسْكُنْ أَنتَ وَزَوْجُكَ الْجَنَّةَ فَكُلاَ مِنْ حَيْثُ شِئْتُمَا وَلاَ تَقْرَبَا هَـذِهِ الشَّجَرَةَ فَتَكُونَا مِنَ الظَّالِمِينَ{19}

"Kuma; Ya Ãdam! Ka zauna kai da matarka a Aljanna, kuma ku ci daga inda kuka so; amma kuma kada ku kusanci wannan itãciya sai ku kasance daga azzãlumai."

Bayan shaidan ya yi tawaye ga umurnin Allah ta hanyar kin yin sujjada ga Adam lamarin da ya yi sanadiyyar ficewarsa daga fadar Allah; a wannan ayar da ayoyin da suke biye mata suna nuni ne kan abin da ya faru dangane da zaman Adam da matarsa a cikin aljanna, kuma ayar tana tuni da cewa shi ma Adam da matarsa sun fice daga wannan aljannar ce saboda sabawa umurnin Allah, tare da fuskantar matsaloli a rayuwarsu, ayar tana cewa: Hakika mun tanada wa Adam da matarsa wani lambun aljanna da yake dauke da nau'o'in 'ya'yan itatuwa da bishiyoyin ni'ima, kuma muka zaunar da su a cikin aljannar tare da ba su damar amfani da duk 'ya'yan itatuwan da suke cikin aljannar, sai kawai wata bishiya guda daya da muka hana su cin wani abu daga gare ta, amma sai suka zalunci kansu suka ci daga wannan 'ya'yan itaciyar da muka hane su, wanda hakan shi ne farkon sabawa umurnin Allah da mutum ya aikata, lamarin da ya yi sanadiyyar bullar matsaloli gare shi tun daga wannan lokacin.

Dangane da aljannar da Adam da Hauwa'u suka zauna a ciki, akwai sabanin malamai a kai; shin aljannar da Allah ya yi alkawari ga bayinsa ne a ranar kiyama ko kuma wata aljanna ce ta duniya? Amma a fili yake cewa aljannar da aka yi alkawari ga bayin Allah a ranar kiyama a cikinta babu wata bishiya da aka hana amfani da 'ya'yan itaciyarta ko yin umurni da hani a cikinta, don haka wasu malaman tafsiri suke ganin aljannar da Adam da Hauwa'u suka zauna a cikinta, wani lambun aljanna ne da ke cikin wannan duniya a kan doron kasa, kuma aka fitar da su daga cikinta saboda saba umurni.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Allah Madaukaki ya so wa mutum jin dadi da saukin rayuwa don haka ya zaunar da shi a cikin aljanna, amma saboda sabawa umurni mutum ya janyo wa kansa matsala da wahalar rayuwa.

{2} Mu kiyaye cikinmu daga ciye-ciyen rashin tsari saboda farkon saba umurni da Adam ya yi ya samo asali ne daga biyan bukatar ciki.

{3} Kafin bayanin al'amuran da aka hana kusantarsu da wadanda suke haramun, da farko mu bayyana hanyoyin halal da al'amuran da aka bada damar amfani da su domin su kasance shimfidar biyan bukatun rayuwar mutane na yau da kullum.

{4} Ba aikata laifi ne kawai aka hana ba, har ma kusantar hanyar laifin an hana domin kusantar hanyar laifin zai iya gurbata mutum.

To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul A'araf, Aya Ta 20-23 (Kashi Na 229)

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.

A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 20 zuwa 21 da suke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

فَوَسْوَسَ لَهُمَا الشَّيْطَانُ لِيُبْدِيَ لَهُمَا مَا وُورِيَ عَنْهُمَا مِن سَوْءَاتِهِمَا وَقَالَ مَا نَهَاكُمَا رَبُّكُمَا عَنْ هَـذِهِ الشَّجَرَةِ إِلاَّ أَن تَكُونَا مَلَكَيْنِ أَوْ تَكُونَا مِنَ الْخَالِدِينَ{20} وَقَاسَمَهُمَا إِنِّي لَكُمَا لَمِنَ النَّاصِحِينَ{21}

"Sai Shaidan ya sanya musu waswãsi dõmin ya bayyana musu abin da aka boye musu na tsiraicinsu, kuma ya ce: "Ubangijinku bai hanã ku {cin} wannan itãciya ba fãce dõmin kada ku kasance malã'iku ko kuma ku kasance masu dawwama {a cikinta}". "Kuma ya yi musu rantsuwa; Lalle ne hakĩka ni mai yi muku nasĩha ne".

Kamar yadda muka bayyana a shirinmu da ya gabata, bayan korar shaidan daga fadar Allah, shaidan ya yi rantsuwar daukar fansar wannan al'amari a kan Adam. Wannan ayar ta fara da ishara ce kan wasiwasin da shaidan ke cusawa, inda ayar ke cewa: Duk da kasancewa Allah ya hana Adam da Hauwa'u cin 'ya'yan wata bishiya, amma sai shaidan ya je musu a wata siffa, ya ce musu; duk da cewa Allah ya hana ku cin 'ya'yan itaciyar wannan bishiya, amma matukar kuka ci wannan 'ya'yan itaciya, to zaku kasance kamar Mala'iku, kuma zaku kasance cikin rayuwa dawwamammiya.

Hakika Adam da Hauwa'u ba su taba jin karya daga wani ba, kuma ba su tsammanin aukuwar irin wannan makirci daga wani, don haka suka afka cikin tarkon shaidan, tare da mance umurnin da Allah ya yi musu. Duk da cewa manufar shaidan ta asali ita ce kokarin ganin ya kawar da kunya da suturar da Adam da Hauwa'u suke dauke da su, inda tsiraicinsu zai bayyana ya zame ba su da wata tufa, wanda hakan zai zame masa shimfidar haifar da watsuwar ayyukan laifi a tsakanin jinsin bil-Adama a nan gaba.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Shaidan baya tilasta wani, aikinsa shi ne cusa waswasi a zukata, zabin makoma kuma ya rage gare mu.

{2} Yana daga cikin manufar shaidan kokarin ganin ya wurga Adam da Hauwa'u cikin halin tsiraici, don haka mu kiyaye kada mu tsiraita kanmu.

{3} Shaidan yana yaudarar mutane ta hanyar dogon burinsu misalin burinsu na neman jin dadin rayuwa da kwanciyar hankali na har abada.

{4} Ba kowace rantsuwa ba ce zamu amince da ita, domin shaidanu suna amfani da rantsuwa da nufin cimma manufarsu.

Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 22 da ke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

فَدَلاَّهُمَا بِغُرُورٍ فَلَمَّا ذَاقَا الشَّجَرَةَ بَدَتْ لَهُمَا سَوْءَاتُهُمَا وَطَفِقَا يَخْصِفَانِ عَلَيْهِمَا مِن وَرَقِ الْجَنَّةِ وَنَادَاهُمَا رَبُّهُمَا أَلَمْ أَنْهَكُمَا عَن تِلْكُمَا الشَّجَرَةِ وَأَقُل لَّكُمَا إِنَّ الشَّيْطَآنَ لَكُمَا عَدُوٌّ مُّبِينٌ{22}

"Sai ya yaudare su da rũdi. Saboda haka a lõkacin da suka dandani itãciyar sai tsiraicinsu ya bayyana gare su, sai suka fara lĩka ganyen aljanna. Kuma sai Ubangjinsu ya kira su {ya ce} : "Shin ban hanã ku {cin} wannan itãciya ba, kuma ban ce da ku lalle Shaidan makiyi ne mabayyani a gare ku ba?".

Shaidan ya samu nasarar cimma burinsa, bayan da Adam da Hauwa'u suka dandani 'ya'yan itaciyar da aka hane su, sai al'aurarsu ta bayyana, ya zame musu dole su suturce al'aurar nasu daga barin kallon junansu, saboda haka suka dinga tsinkar ganyen bishiya suna likawa a jikinsu, sai suka ji kira Allah yana ce musu: Mene ne ya sanya kuka mance umurnin Ubangijinku, kuka afka cikin yaudarar shaidan? shin ba ku da masaniyar cewa; a dalilinku ne shaidan ya wulakanta, kuma yana neman hanyar daukan fansa a kanku? Shin ba ku da masaniyar cewa shaidan makiyinku ne kuma yana bayyana kiyayyarsa a fili?.

A cikin wannan ayar zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Mace da na miji ba su da bambanci dukkaninsu suna iya afkawa cikin tarkon waswasin shaidan, don haka kowane jinsi yana iya aikata laifi.

{2} Zama cikin tsiraici wani nau'i ne na azabar Allah -ba alama ce ta wayewa da cika ba- don haka rashin bin umurnin Allah da cin wasu nau'in abincin da suke haramun ne suna share fagen kawar da kunya da rungumar dabi'ar bayyana tsiraici a tsakanin al'umma.

{3} Sanya sutura dabi'a ce da aka halicci mutum da ita wato fidira ce ta dan Adam, don haka yaro tun yana karami yake fara neman tufar suturce al'aura koda kuwa da wace irin tufa ce.

{4} Dole ne mu nemi sanin wane ne makiyinmu na hakika, kuma kada mu kuskura mu gafala da shi, saboda dole ne shirin fuskantar makiyi.

Yanzu kuma zamu saurari aya ta 23 da ke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

قَالاَ رَبَّنَا ظَلَمْنَا أَنفُسَنَا وَإِن لَّمْ تَغْفِرْ لَنَا وَتَرْحَمْنَا لَنَكُونَنَّ مِنَ الْخَاسِرِينَ{23}

"Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Hakika Mun zãlunci kanmu. Kuma idan ba Ka yi mana gafara ba, kuma ba Ka ji kanmu ba, to hakĩka zamu kasancẽ daga mãsu hasãra."

Babu kokwanto Adam da Hauwa'u sun afka cikin yaudarar shaidan amma cikin gaggawa suka fahimci kuskurensu, don haka cikin bakin ciki kan abin da suka aikata suka koma ga Allah suna neman ahuwansa, suna cewa ya Ubangijinmu hakika mun zalunci kanmu don haka muna neman gafararka da jin kanka. Na'am shaidan da Adam dukkaninsu biyu sun sabawa umurnin Allah, amma shaidan maimakon ya nemi gafara da ahuwa kan laifinsa, sai yana neman kare laifin da ya aikata, har ta kai ga yana inkarin adalci da hikimar Allah. Amma Adam da Hauwa'u sun yi furuci da laifinsu, kuma suka nemi gafara da ahuwa kan laifin, don haka Allah ya kori shaidan daga fadarsa, kuma ya la'ance shi la'ana ta har abada, amma Adam da Hauwa'u ya yi musu gafara tare da lullube su da rahamarsa. A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Rashin bin umurnin Allah zalunci ne da ke komawa kan mutum ba Allah ba, kuma duk wani laifin da muka aikata baya cutar da Allah, kanmu muke rusawa.

{2} Adam da Hauwa'u sun yi tarayya a aikata laifi, don haka tare suka nemi gafara, kuma babu bambanci tsakanin mace da namiji wajen aikata laifi ko neman gafara, asali ma dai babu bambanci tsakanin mace da namiji a fagen kai wa ga cikan kamala da kyawawan dabi'u, haka nan a fagen tsageranci da tawaye ga umurnin Allah.

{3} A fadar Allah ne kawai muke da hakkin yin furuci da laifukanmu, kuma hakan yana matsayin shimfida ce ta samun gafara da jin kai a wajen Allah.

{4} Aikata laifi shi ne tushen hasarar mutum, kuma ta hanyar neman gafara ne kawai zamu kai ga shawo kan hasarar da muke yi.

To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul A'araf, Aya Ta 24-27 (Kashi Na 230)

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.

A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 24 zuwa 25 da suke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

قَالَ اهْبِطُواْ بَعْضُكُمْ لِبَعْضٍ عَدُوٌّ وَلَكُمْ فِي الأَرْضِ مُسْتَقَرٌّ وَمَتَاعٌ إِلَى حِينٍ{24} قَالَ فِيهَا تَحْيَوْنَ وَفِيهَا تَمُوتُونَ وَمِنْهَا تُخْرَجُونَ{25}

"{Allah} Ya ce: "Ku sauka {daga cikinta} sãshinku suna masu gaba da sãshi, kuma kunã da wajen zama a kasa da kuma abin jin dãdi har zuwa ga wani lõkabi". "{Allah} Ya ce: "A cikinta ne zaku rãyu, kuma a cikinta za ku mutu, kuma daga gare ta ne za a fitar da ku."

Kamar yadda ya zo cikin wasu ayoyin alkur'ani, Allah ya karbi tuban Adam da Hauwa'u kan laifin da suka yi na rashin bin umurni, amma duk da haka cin wannan 'ya'yan itaciyar da aka hane su ya haifar musu da mummunan tasiri, inda ya yi sanadiyyar ficewarsu daga cikin aljanna zuwa kan doron kasa, don haka wadannan ayoyi suke bayyana cewa: Allah ya umurci Adam da Hauwa'u kan su fice daga cikin lambun aljannar da suke ciki, domin su rayu a kan doron kasa, saboda wannan wajen ne ya fi dacewa da su har zuwa lokacin da Allah ya ga damar raba su da duniya ta hanyar mutuwa domin fuskantar hisabi a ranar kiyama.

Har ila yau wadannan ayoyi suna nuni kan yadda kiyayya zata watsu tsakanin mutane da kuma kiyayya tsakanin mutane da shaidan, inda suke bayyana cewa: rayuwa a kan doron kasa tana tattare da kiyayya da gaba, sabanin rayuwar a gidan aljanna, inda a wajen ake rayuwa cikin kwanciyar hankali da kaunar juna.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Wasu ayyukan da mahaifa ke aikatawa suna janyo koma baya ga zuriyarsu da zasu zo a bayansu, saboda laifin Adam da Hauwa'u suka aikata ya yi sanadiyyar wurga zuriyarsu cikin kangi da matsalolin da suke kan doron kasa.

{2} Duniya waje ne na rikici da sabani, saboda matukar aka samu sabani a manufofi da bukatu, to hakan yana haifar da sa-in sa a tsakani tare da kiyayya.

Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 26 da ke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

يَا بَنِي آدَمَ قَدْ أَنزَلْنَا عَلَيْكُمْ لِبَاساً يُوَارِي سَوْءَاتِكُمْ وَرِيشاً وَلِبَاسُ التَّقْوَىَ ذَلِكَ خَيْرٌ ذَلِكَ مِنْ آيَاتِ اللّهِ لَعَلَّهُمْ يَذَّكَّرُونَ{26}

"Yã ku 'yan Ãdam! Hakika Mun saukar da tufa a gare ku wadda zata suturce muku al'aurarku da kuma kayan ado. Da Kuma tufa na tsoron Allah, wannan tufar ita ce mafi alhẽri. Wannan yana daga ãyõyin Allah ko watakila su wa'azantu".

Kamar yadda muka bayyana a cikin ayoyin da suka gabata bayan shaidan ya yaudari Adam da Hauwa'u sun ci 'ya'yan itaciyar da aka hane su, farkon tasirin da laifin ya yi kansu shi ne bayyanar al'auransu, don haka ya zame dole a kansu su yi amfani da ganyen bishiya wajen suturce jikinsu.

Wannan ayar kuma tana bayyana cewa ne: Bayan saukar da Adam da Hauwa'u zuwa kasa domin zama a ciki, sai Allah ya samar musu da hanyar suturce jikinsu da gashin dabbobi, inda gashin dabbobin ya kasance musu sutura kuma ado, hakika tun bayan dubban shekaru har zuwa wannan lokaci dan Adam yana ci gaba da amfani da gashin dabbobi a matsayin tufa, kuma tufar da aka sarrafa daga gashin dabbobin ne mafi kyau da ado a cikin tufofin da mutane ke amfani da su a rayuwarsu wanda hakan yana daga cikin ni'imar Allah a kan bayinsa.

Kur'ani ya ci gaba da bayyana cewa: Dukkanin wadannan tufa da aka ambata tufa ce ta adon duniya, amma tufa da tafi ita ce tufar tsoron Allah, saboda tsoron Allah sutura ne na tsarkin zuciya, kamun kai da kunya, kuma garkuwa ne daga afkawa cikin munanan ayyuka da suke bayyana ga mutane.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:- {1} Shaidan yana kokari ne na ganin ya tsiraita mutum, yayin da Allah yake samar da hanyoyin suturce mutane.

{2} Ado da sanya tufa ta kwalliya abu ne mai kyau, kuma Allah yana son hakan, don haka ba a hana yin ado da kwalliya ba matukar ba zai kai ga sabawa umurnin Allah ba.

{3} Duk tufar da mutane ke amfani da su misalin tufar auduga, gashin dabbobi, leda da sauransu, dukkaninsu suna daga cikin halittun Allah ne, wanda matukar mutane suka zurfafa tunani kan samuwarsu zasu kai ga fadaka da nisantar duk wata gafala a rayuwa.

Yanzu kuma zamu saurari aya ta 27 da ke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

يَا بَنِي آدَمَ لاَ يَفْتِنَنَّكُمُ الشَّيْطَانُ كَمَا أَخْرَجَ أَبَوَيْكُم مِّنَ الْجَنَّةِ يَنزِعُ عَنْهُمَا لِبَاسَهُمَا لِيُرِيَهُمَا سَوْءَاتِهِمَا إِنَّهُ يَرَاكُمْ هُوَ وَقَبِيلُهُ مِنْ حَيْثُ لاَ تَرَوْنَهُمْ إِنَّا جَعَلْنَا الشَّيَاطِينَ أَوْلِيَاء لِلَّذِينَ لاَ يُؤْمِنُونَ{27}

"Yã ku 'yan Ãdam! Kada Shaidan ya yaudare ku, kamar yadda ya fitar da iyãyenku daga Aljanna, yanã mai yaye musu tufafinsu dõn ya nũna musu tsiraicinsu. Hakika shĩ da rundunarsa suna ganinku, ta inda bã ku ganin su. Hakika Mun sanya Shaidanu majibinta ga wadanda bã su yin ĩmãni".

Kiyayyar shaidan ba ta takaita kan Adam da Hauwa'u ba, kiyayya ce da ta game kan dukkanin zuriyarsu, don haka Allah Madaukaki a cikin wannan ayar yake wasiya ga 'ya'yan Adam da cewa; ku kiyaye kada shaidan ya yaudare ku kamar yadda ya yaudari mahaifanku Adam da Hauwa'u. Hakika ta hanyar waswasi shaidan ya samu damar fitar da Adam da Hauwa'u daga cikin aljanna, kuma ya yi sanadiyyar bayyanar al'auransu domin shimfidar watsuwar munanan ayyyuka. Lalle shaidan da rundunarsa suna ganinku amma ku ba ku iya ganinsu, sai dai duk da haka ba su da iko a kanku saboda ba zasu iya tilasta muku aikata wani laifi ba, iyaka dai su yaudare ku ta hanyar waswasi, inda mutumin da ba shi da imani da Allah da ranar kiyama zai bi wannan waswasin tare da aikata laifi.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Kada mutum ya raina tarkon da shaidan yake tana masa na hatsari komai kashinsa domin baya da amincin kare kansa daga afkawa cikin bata, musamman ganin Adam da Mala'iku suka masa sujjada amma ya afka cikin yaudarar shaidan, kuma ya yi sanadiyyar fitar da shi daga aljanna.

{2} Bayyanar tsiraicin Adam da Hauwa'u shi ne ya sanya aka fitar da su daga cikin aljanna, don haka duk wani shiri da ake nuna tsiraici a ciki, to shaidanci ne.

{3} Shaidan yana da runduna mai yawa a tsakanin mutane da aljanu, don haka ba shi kadai yake ba.

{4} Imani na gaskiya da Allah yana hana shaidan ya yi galaba a kan mutum.

To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul A'araf, Aya Ta 28-30 (Kashi Na 231)

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na hannunka mai sanda, shirin da a cikinsa muke dubi a ayoyin alkur'ani mai girma domin su kasance mana jagora a rayuwa, sai a biyo mu don jin abin da shirinmu na yau ya kunsa.

A shirinmu na yau zamu fara ne da ambaton aya ta 28 da ke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

وَإِذَا فَعَلُواْ فَاحِشَةً قَالُواْ وَجَدْنَا عَلَيْهَا آبَاءنَا وَاللّهُ أَمَرَنَا بِهَا قُلْ إِنَّ اللّهَ لاَ يَأْمُرُ بِالْفَحْشَاء أَتَقُولُونَ عَلَى اللّهِ مَا لاَ تَعْلَمُونَ{28}

"Kuma idan suka aikata mummunan {aiki sai} su ce: "Haka Muka sãmi iyayenmu a kai, kuma Allah ne ya umurce mu da shi."Ka ce {da su}: "Hakika Allah bãya umurni da mummunan {aiki}. Shin kunã fadar abin da bã ku da saninsa ga Allah?".

A shirinmu da ya gabata mun bayyana cewa: Shaidan ya yaudari mutum har ya yi sanadiyyar bayyanar tsiraicin Adam da Hauwa'u, don haka Allah ya yi wasici ga 'ya'yan Adam da Hauwa'u da su kiyaye kada su afka cikin tarkon yaudarar shaidan da zata kai su ga bayyana tsiraicinsu da bayyanar munanan ayyuka daga gare su.

Wannan ayar tana nuni ne kan daya daga cikin misalin yaye sutura da bayyana tsiraici a tsakanin mutane a lokacin jahiliyya wato kafin bayyanar addinin Musulunci; kamar yadda ya zo cikin tafsiri cewa: Mushrikan Makkah a kan sunnar Annabi Ibrahim a kowace shekara suna gudanar da aikin hajji, kuma suna da imanin cewa dole ne dawafin aikin hajjin ya kasance cikin tsarkakekkiyar tufa kuma ta halal, don haka a duk lokacin da suka zo aikin hajji sai su dinga kokwanto kan tsarkin tufarsu da halaccinta saboda haka a lokacin gudanar da dawafi sai su tube tsirara suna zagaya dakin Allah na Ka'abah, kuma suna daukan hakan a matsayin ibada. Sakamakon haka wannan ayar ta sauka tana bayyana abin da suke aikatawa a matsayin mummunan aiki kuma kazanta, inda take cewa: Mushrikai suna kokarin kare wannan mummunan aikinsu da cewa; haka suka tarad da mahaifansu suna aikatawa, saboda haka sunna ce ta magabatansu, kuma kasancewar suna aikata hakan ne a lokacin ibadan Allah, to Allah ne ma ya umurce su da yin hakan. A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Mafi yawan ayyuka marassa tushe da suke tsakanin al'umma sun samo asali ne daga koyin da kanana suke yi da magabatansu, duk kuwa da cewa kiyaye al'adun magabata baya nufin mutum ya yi watsi da tunaninsa tare da mai da kansa a matsayin dabba.

{2} Dole ne bautan Allah ta kasance ana aiwatar da ita ce kamar yadda Allah ya yi umurni, idan kuma har aka kauce umurnin, to babu makawa za a afka cikin bidi'a da kirkire-kirkire marassa tushe.

Shirinmu zai ci gaba ne ta hanyar ambaton aya ta 29 da ke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

قُلْ أَمَرَ رَبِّي بِالْقِسْطِ وَأَقِيمُواْ وُجُوهَكُمْ عِندَ كُلِّ مَسْجِدٍ وَادْعُوهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ كَمَا بَدَأَكُمْ تَعُودُونَ{29}

"Ka ce {da su}: "Ubangjina yã yi umurni ne da ãdalci; kuma ku tsayar da fuskõkinku {ga Allah} a wajen kõwane masallãci, kuma ku rõkẽ Shi kunã mãsu tsarkake addini gare Shi. Kamar yadda Ya halicce ku za ku kõmã gare shi".

A matsayin mai da martani kan furucin da mushrikai suka yi na jingina mummunan aikinsu ga Allah domin su zame a matsayin marassa laifi; wannan ayar tana bayyana cewa: Hakika Allah yana umurni ne da adalci da gaskiya da abu mafi kyau da tsarki, don haka yana bukatarku a lokacin da kuke masallatai musamman masallacin haramin Makkah wato Ka'abah a yayin gudanar da salla da dawafi, ku tsayar da fuskokinku kawai zuwa gare shi, tare da gudanar da tsabtataccen aiki da babu kirkire-kirkiren wani abu maras tushe a cikinsa, haka nan ku tsarkake akidarku daga duk wani nau'in shirka, kuma ku sani lalle kamar yadda ya samar da ku tun da fari, tabbas yana da ikon sake komar da ku zuwa gare shi.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Hakika umurnin Allah ya ginu ne a kan tushen adalci, kuma neman gudanar da adalci shi ne muhimmin umurninsa. {2} Zama bayin Allah na gaske shi ne shimfidar watsuwar adalci da daidaito, tare da tabbacin gudanarsa da wanzuwarsa.

Yanzu kuma zamu saurari aya ta 30 da ke cikin suratul-A'arafi kamar haka:-

فَرِيقاً هَدَى وَفَرِيقاً حَقَّ عَلَيْهِمُ الضَّلاَلَةُ إِنَّهُمُ اتَّخَذُوا الشَّيَاطِينَ أَوْلِيَاء مِن دُونِ اللّهِ وَيَحْسَبُونَ أَنَّهُم مُّهْتَدُونَ{30}

"Wata kungiya Yã shiryar da ita, kuma wata kungiyar bata tã tabbata a kansu; hakika sun riki shaidanu majibinta ba Allah ba, kuma sunã zaton cewa sũ shiryayyu ne".

Bayan ayar da ta gabata ta yi bayani kan yadda za a gudanar da rayuwa da ibadu a kan tubali na adalci; wannan ayar kuma tana bayani ne kan cewa: kungiyar da ta yi riko da umurnin Allah, to lalle zata samu shiriyarsa, amma kungiyar da ta bijire wa umurnin Allah da bin tafarkin shaidan, to lalle tana tafiya ce a kan hanyar bata, idan kuma tana tsammanin ta kama hanyar shiriya ce kuma zata tsira daga duk wani hatsari da ke barazana ga mutum, to tabbas tana cikin rudu da tunani maras tushe, kamar karin magana ne da ke cewa; ci gaba mai tonon rijiya; wato mutum yana kara nutso cikin rami yana murnar samun ci gaba, lalle wannan daya ne daga cikin yaudarar shaidan, inda yake surantawa mutane batar da suke kai cewa ita ce hanyar gaskiya da zata tsirar da su, kuma yana kiransu kan su ci gaba da yin riko da ita. Alkur'ani a cikin wasu ayoyinsa yana bayyana irin wadannan mutane da cewa; sune mafi hasarar mutane; domin sune wadanda suke ganin munanan ayyukansu a matsayin kyawawa, alhalin ayyukansu tun a nan duniya sun riga sun rushe, kuma zasu fice daga cikin duniyar ba tare da wani abu ba.

A cikin wannan aya zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Lalle shiriya daga wajen Allah take, amma bata da kauce hanya daga gare mu take saboda zabe maras kyau da muka yi.

{2} Bijirewa Allah yana sanadiyyar afkawa cikin tarkon shaidan da karbar jagorancinsa, don haka maimakon mutane su kasance masoya Allah, sai su zame majibintan shaidan.

{3} Mu kiyaye kada mu kasance cikin mutanen da suke tsammanin suna kan tafarkin gaskiya alhalin ayyukansu batattu ne.

To a nan ne shirin na mu ya zo karshe, sai kuma a gamo na gaba. Wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul A'araf, Aya Ta 31-33 (Kashi Na 232)

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin da mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur'ani mai girma. Da fatan za a kasance a tare da mu domin a ji ci gaban shirin daga inda mu ka tsaya a baya.

Yanzu sai a saurari aya ta 31 acikin suratu A'araf.

يَا بَنِي آدَمَ خُذُواْ زِينَتَكُمْ عِندَ كُلِّ مَسْجِدٍ وكُلُواْ وَاشْرَبُواْ وَلاَ تُسْرِفُواْ إِنَّهُ لاَ يُحِبُّ الْمُسْرِفِينَ{31}

" Ya ku 'yan adam, ku yi kawa a kowane masallaci kuma ku ci, ku sha, kada ku yi israfi. Allah ba ya son masu yin israfi."

Ashirin da ya gabata mun yi magana akan abubuwan da Ubangiji ya kirayi 'yan adam da su rika aikatawa. To a cikin wannan ayar ma ci gaba ne da nasihohin da Ubangijin ya ke yi ga 'yan adam da yin kira a gare su da su rika yin kawa da kwalliya a yayin dawafi a dakin Allah. Haka nan kuma a cikin kowane masallaci da su ke zuwa domin yin ibada. Domin kuwa a zamanin jahiliyya larabawa suna yin dawafi a ka'aba ne tsirara ba tare da sun suturta jikinsu ba. A cikin riwayoyi na addini ana kiran musulmi da su rika sanya kyawawan tufafi da kuma turare a lokacin zuwa masallaci.

Ci gaban ayar kuwa magana ce akan cin abinci da kuma abin sha. Tana kiran 'yan adam da su ci kuma su sha daga ni'imomin da Allah ya yi musu amma kada su yi israfi.

Kamar yadda ya zo a cikin labari cewa annabi Adamu da matarsa Hauwa'u an kore su ne daga gidan aljanna saboda sun ci wani dan iccen da aka hana su. Saboda haka kuma 'ya'yansu ku yi hattara kada ku fuskanci samakamo irin nasu saboda abinci.

Abubuwan da za mu koya daga wannan aya.

1-Masallaci dakin Allah ne da bayin Allah su ke taruwa acikinsa, saboda haka wajibi ne a yi adon da ya dace idan za a shige shi.

2-Abincin ruhi shi ne a gaba da abincin da gangar jiki ya ke bukata. Salla ita ce farko sannan abinci da za a kai bakin salati.

3-Ya halarta ga mutum da ya yi amfani da albarkatun da su ke a cikin dabi'a iya gwargwado ba tare da ya wuce gona da iri ba.

Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 32 acikin wannan sura ta A'araf.

قُلْ مَنْ حَرَّمَ زِينَةَ اللّهِ الَّتِيَ أَخْرَجَ لِعِبَادِهِ وَالْطَّيِّبَاتِ مِنَ الرِّزْقِ قُلْ هِي لِلَّذِينَ آمَنُواْ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا خَالِصَةً يَوْمَ الْقِيَامَةِ كَذَلِكَ نُفَصِّلُ الآيَاتِ لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ{32}

" Ka ce wanene ya haramta kyawawan (ababen) ado da Allah ya samarwa bayinsa da kuma arziki mai tsarki karbabbe ga zuciya? " " Ka ce wadannan ni'imomi ne na rayuwar duniya ga muminai, a lahira kuma zai kasance na muminai ne su kadai. Da haka ne mu ke bayyana ayoyi ga mutanen da su ke da sani."

A cikin ayar baya Ubangiji ya yi kira ga 'yan adam da su rika amfanuwa da ni'imominsa. To wannan ayar tana jan kunne ne da gargadi akan cewa wanenen ya haramta cin moriyar wadannan ni'imomin da Allah ya halatta domin bayinsa?

Ubangiji ya halicci wadannan ni'imomin ne domin bayinsa salihai masu imani su amfana da su, kuma a lokaci guda bai hana kafirai amfanuwa da su ba. Sai dai a ranar lahira kafirai ba za su ci moriyar ni'imomin Allah ba, muminai ne kadai za su amfana da su.

Idan wasu mutane suna wuce gona da iri a yin israfi wajen cin moriyar ni'imomin da Allah ya yi musu, wasu kuma suna takura kawunansu ne da rike hannu wajen amfanuwa da ni'imoimin na Allah. To kur'ani mai girma yana fada da dukkanin wadannan halayen guda biyu. Yana kiran bangare na farko da cewa me ya sa ku ke yin israfi? Yana kuma tambayar bangare na biyu da cewa meya sa ku ke haramta abinda Allah ya halarta?

Abubuwan da za mu koya daga wadannan ayoyin.

1-Kamar yadda halarta abubuwan da su ke haramun bai dace ba, haka nan haramta abubuwan da su ke halaliya bai dace ba.

2-Ubangiji yana karfafa muminai da su ci moriyar ni'imomi da yin kawa da ya halarta musu a karkashin dokokin addini.

3-Muminai da kafirai daidai wa daidai su ke wajen cin moriyar ni'imomin rayuwar duniya da Allah ya samar, amma a lahira muminai ne kadai za su amfana da wadannan ni'imomin.

Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 33 acikin wannan sura ta A'araf.

قُلْ إِنَّمَا حَرَّمَ رَبِّيَ الْفَوَاحِشَ مَا ظَهَرَ مِنْهَا وَمَا بَطَنَ وَالإِثْمَ وَالْبَغْيَ بِغَيْرِ الْحَقِّ وَأَن تُشْرِكُواْ بِاللّهِ مَا لَمْ يُنَزِّلْ بِهِ سُلْطَاناً وَأَن تَقُولُواْ عَلَى اللّهِ مَا لاَ تَعْلَمُونَ{33}

" Ka ce abubuwan da su kadai ne Ubangiji ya haramta, su ne munanan ayyuka na sararinsu da na boye da sabo da zalunci ba da hakki ba da kuma shirka da Allah wanda bai saukar da wata hujja akansa ba, da kuma fadin abinda za ku fada dangane da Allah wanda ba ku sani ba."

Wani sashe na muminai suna tsammanin cewa hanyar kusantar Ubangiji ita ce kauracewa rayuwar duniya da kauracewa al'umma. Suna tsammanin cewa tsoron Allah yana cikin sakin duniya da dukkanin abinda ya ke cikinta kuma kokarin samun abin duniya ba shi da kyau. To wannan ayar tana yin maganan ne da muminai irin wadannan tana fada musu cewa: Abubuwan da Allah ya haramta kididdigaggu ne su ne kuma wadanda ayar ta lissafa su, duk wani abu wanda ba hakan ba halaliya ne. Ubangiji ya haramta cutar da mutane da yin sa saboda da keta doka da munanan ayyuka na shirka da cin kudin ruwa da bidi'a da camfe-camfe. Ku nesanci wadannan abubuwan idan ya so ku ci moriyar ni'imomin da su ke cikin duniya da Allah ya halarta mu ku.

Abubuwan da za mu koya daga wadannan ayoyin.

1-Abubuwan da su ke halaliya sun fi wadanda su ke haramun yawa. Ubangiji ya baiwa mutum hakkin cin moriyar abubuwa da dama acikin abubuwa kadan ne ya yi masa kaidi.

2-Abubuwan da Allah ya haramta su ne munana masu gurbata gangar jiki da kuma ruhin mutum. Abubuwan da mutum bisa fidirarsa bai amince da su ba.

3-Munanan ayyuka jinsin sabo ne, mutum ya fahimci hakan ko bai fahimta ba. Ba mutum ne zai ayyakan abindaya ke haramun ba ko abinda ya ke mummuna.

A karshen wannan shirin muna yin ban kwana da ku sai kuma mun sake hadewa acikin wani shirin.

Suratul A'araf, Aya Ta 34-38 (Kashi Na 233)

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin na Hannunka Mai Sanda. Da fatanz a kasance a tare da mu domin a ji ci gabansa daga inda mu ka tsaya a baya.

Yanzu sai a saurari aya ta 34 acikin wannan sura ta "A'araf.

وَلِكُلِّ أُمَّةٍ أَجَلٌ فَإِذَا جَاء أَجَلُهُمْ لاَ يَسْتَأْخِرُونَ سَاعَةً وَلاَ يَسْتَقْدِمُونَ{34}

"Kuma kowace al'umma tana da kayyadajjen lokacin da aka deba mata. Saboda haka da lokacin ya zo, ba za a jinkirta mata ba daidai da sa'a daya, kuma ba za a gaggauta mata ba."

Wani abu da mafi yawancin mutane su ke mantawa da shi shi ne mutuwa a karshen rayuwa, ba kuma ta daidaikun mutane ba ta al'umma kaco-kau, da kuma durkushewar ci gaban da wannan al'ummar ta gina. Kamar yadda ya zo a cikin wannan ayar al'umma da ci gaban da ta gina suna zuwa karshe su kuma mutu kamar yadda daidaikun mutane su ke yi. A tsawon tarihin bil'adama a doron kasa an yi al'ummu wadanda su ka kafa ci gaba amma daga karshe wannan ci gaban ya rushe saboda zalunci da kuma rauni ta fuskar kyawawan halaye da nutsewa cikin jin dadin duniya.

Mafi yawancin ma'abota dukiya a masu more jin dadin rayuwar duniya suna tsammanin cewa za su dawwama acikin wannan halin ba tare da ya gushe ba. Sai dai wannan ayar tana bayyana cewa idan Allah ya yi nufi komai zai kau ya kuma gushe.

Abubuwan da za mu koya daga wannan aya.

1-Dama da kuma hajoji da ake samu a rayuwar duniya masu gushewa ne da karewa, saboda haka a yi amfani da su ta hanya mafi dacewa.

2-Kada azzalumai su tsammaci cewa Allah ya kyale su ne suna yin abinda su ka ga dama, karshensu yana zuwa kuma dole ne su bada jawabin abinda su ka aikata.

Yanzu kuma sai a saurari ayoyi na 35 da 36 a cikin wannan sura ta "A'araf."

يَا بَنِي آدَمَ إِمَّا يَأْتِيَنَّكُمْ رُسُلٌ مِّنكُمْ يَقُصُّونَ عَلَيْكُمْ آيَاتِي فَمَنِ اتَّقَى وَأَصْلَحَ فَلاَ خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلاَ هُمْ يَحْزَنُونَ{35} وَالَّذِينَ كَذَّبُواْ بِآيَاتِنَا وَاسْتَكْبَرُواْ عَنْهَا أُوْلَـَئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ{36}

" Ya ku 'yan adam, idan manzanni su ka zo mu ku daga cikinku suna karanta mu ku ayoyina, to wanda ya ji tsoron Allah ya kuma kyautata-aikinsa- to babu tsoro a gare su kuma babu bakin ciki." "Wadanda su ka karyata ayoyinmu kuwa su ka yi girman kai a gare ta, to wadannan su ne 'yan wuta, suna madawwama acikinta."

Idan a cikin ayoyin aya Ubangiji ya yi wa 'yanadam ne nasihohi da abubuwan da ya kamata su rika aikatawa to a cikin wadannan ayoyin ana yin bayani ne akan banbancen da ke tsakanin mutane dangane da karba ko rashin karbar shiriya. Ayar tana fadin cewa:Allah ya rika aiko da manzanni acikinku ya ku 'yan adam wadanda aikinsu shi ne yin kira ga ayyukan kwarai. Sai dai mutane sun kasuwa gida biyu wajen fusakntar kiran na annabawa. Bangaren farko su ne masu tsoron Allah da son kawo gyara, su ne kuma wadanda za su sani sa'ada a duniya da lahira. Saboda sun kyautatta alakarsu da Allah to ba za su kasance acikin tsoro da bakin ciki ba. Wanda duk ya ke jin tsoron Allah babu wani ma'abocin karfi da ya ke bashi tsoro a duniya kuma a lahira ba zai kasance cikin bakin ciki ba.

Bangare na biyu kuwa su ne mutanen da su ka yi wa gaskiya girman kai, su ka ki karbarta da kuma karyata ta. Mutane irin wadannan sun fifita jin dadin duniya akan samun sa'ada, su ne kuwa wadanda a lahira za su kasance a cikin azaba.

Abubuwan da za mu koya daga wadannan ayoyi.

1-Takawa tana tafiya ne kafada da kafada da yin aiki domin kawo gyara acikin al'umma, ba killace kai da komawa gefe ba domin yin ibada.

2-Kwanciyar hankali da nutsua na asali suna samuwa ne a karkashin gudanar da ayyukan kwarai wadanda su ne abubuwan da su ke nesanta bakin ciki da tsoro.

Yanzu kuma sai a saurari aya ta 37 a cikin wannan Sura ta "A'araf."

فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَى عَلَى اللّهِ كَذِباً أَوْ كَذَّبَ بِآيَاتِهِ أُوْلَـئِكَ يَنَالُهُمْ نَصِيبُهُم مِّنَ الْكِتَابِ حَتَّى إِذَا جَاءتْهُمْ رُسُلُنَا يَتَوَفَّوْنَهُمْ قَالُواْ أَيْنَ مَا كُنتُمْ تَدْعُونَ مِن دُونِ اللّهِ قَالُواْ ضَلُّواْ عَنَّا وَشَهِدُواْ عَلَى أَنفُسِهِمْ أَنَّهُمْ كَانُواْ كَافِرِينَ{37}

"Kuma wa ya fi zama azalumi fiye da wanada ya yi wa Allah karya ko kuma ya karyata ayoyinsa? Wadannan rabonsu da aka rubuta musu zai same su har sai lokacin da 'yan aikenmu su ka zo musu domin su karbi rayukansu, sai su ce, ina wadanda ku ke kira sabanin Allah su ka shuga ne? Sai su ce: Ai sun bace mana, su ka kuma shaidi kansu da cewa sun kasance kafirai."

Wannan ayar tana bada labarin halin da kafirai za su shiga ne a ranar kiyama. Alokacin mutuwa ne za su fahimci cewa su makaryata ne ba annabawan da su ka rika fada musu gaskiya ba a duniya ba. Shakka babu mutane irin wadannan Allah bai haramta musu cin moriyar ni'imoninsa a duniya ba, amma alokacin mutuwa za su gane kuransu na karkacewa da su ka yi daga barin gaskiya.

Abubuwan da za mu koya daga wadannan ayoyi.

1-Kafirci da kuma inkarin gaskiya su ne nau'oin zalunci mafi girma. Dominzalunci mafi muni shi ne wanda mutum zai yi wa kansa.

2-Kowane mutum yana da rabon da Allah ya tsaga masa a duniya.

3-Lamirin mutum shi ne alkalin farko da zai bada shaida a kansa.

Yanzu kuma sai aya ta 38 a cikin wanann sura ta "A'araf."

قَالَ ادْخُلُواْ فِي أُمَمٍ قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِكُم مِّن الْجِنِّ وَالإِنسِ فِي النَّارِ كُلَّمَا دَخَلَتْ أُمَّةٌ لَّعَنَتْ أُخْتَهَا حَتَّى إِذَا ادَّارَكُواْ فِيهَا جَمِيعاً قَالَتْ أُخْرَاهُمْ لأُولاَهُمْ رَبَّنَا هَـؤُلاء أَضَلُّونَا فَآتِهِمْ عَذَاباً ضِعْفاً مِّنَ النَّارِ قَالَ لِكُلٍّ ضِعْفٌ وَلَـكِن لاَّ تَعْلَمُونَ{38}

"Sai-Allah- ya ce: "Ku shiga cikin al'ummun da su ka gabace ku na daga aljanu da mutane acikin wuta. A duk lokacin da wata al'umma ta shiga-wuta- sai ta la'anci 'yar uwarta wadda ta tarar. Idan su ka hadu a cikinta gaba daya sai na karshen su ce da na farko, ya ubangijinmu wadannan ne su ka batar da mu ka rubanya musu azaba. Sai Ubangiji ya ce kowannensu za a rubanya masa, sai dai ba ku sani ba."

Wannan ayar tana yin bayani ne akan tattaunawar da za yi a tsakanin 'yan wuta, musamman ma dai jagororin bata. Idan an gama hisabi 'yan wuta sun shiga cikin jahannama gungu-gungu, kowane gungu zai rika tsinewa wanda ya gabace shi. Gungun mutane da aljanu da su ka shiga su riski wadanda su ka batar da su za su fada musu cewa: "Ku ne wadanda ku ka batar da mu saboda haka dole ne a yi mu ku azaba linkin balinkin.

Darussan da su ke cikin wannan aya.

1-Aljanna wuri ne na nutsuwa da zaman lafiya, jahannama kuwa wuri ne na kwaramniya da tsinuwa da zarge-zage tsakanin 'yan wuta. "Yan aljanna suna kaunar juna da kuma mutunta juna da girmamawa, amma 'yan wuta suna tsinewa junansu.

2-Aljanu kamar mutane su ke wajen daukar nauyi na ayyukan da su ke yi, na kwarai da sabo. Kamar yadda wasu mutane za su shiga wuta, haka nan kuma wasu aljanun za su shiga.

3-A ranar lahira masu laifi suna kokarin dora alhakin laifin da su ka yi awuyan wasu, ko kuma su sami abokan da su ka aikata laifi a tare da su.

Wannan shi ne karshen shirinmu na wannan lokacin sai kuma lokaci na gaba.

Suratul A'araf, Aya Ta 39-43 (Kashi Na 234)

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku acikin wannan shirin na Hannunka Mai Sanda wanda mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur'ani mai girma. Kuma har yanzu dai muna cikin suratu, A'araf ne inda mu ka tsaya akan aya ta talatin da takwas. Da fatan za a kasance a tare da mu domin jin ci gaba daga inda mu ka tsaya.

Yanzu sai a saurari aya ta 39 da ta 40 a cikin wannan sura ta A'araf.

وَقَالَتْ أُولاَهُمْ لأُخْرَاهُمْ فَمَا كَانَ لَكُمْ عَلَيْنَا مِن فَضْلٍ فَذُوقُواْ الْعَذَابَ بِمَا كُنتُمْ تَكْسِبُونَ{39} إِنَّ الَّذِينَ كَذَّبُواْ بِآيَاتِنَا وَاسْتَكْبَرُواْ عَنْهَا لاَ تُفَتَّحُ لَهُمْ أَبْوَابُ السَّمَاء وَلاَ يَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ حَتَّى يَلِجَ الْجَمَلُ فِي سَمِّ الْخِيَاطِ وَكَذَلِكَ نَجْزِي الْمُجْرِمِينَ{40}

"Sai ta farkonsu ta fadawa ta karshensu cewa ba ku da wani fifiko akanmu, ku dandani azaba saboda abinda ku ka kasance kuna aikatawa".

Wadanda su ka karyata ayoyinmu su ka yi musu girman kai ba za a bude musu kofofin sama ba, kuma ba za su shiga aljanna ba har sai idan rakumi zai shiga ta kafar allura. Da haka ne mu ke sakawa masu laifi."

A shirin baya mun yi magana akan tattaunawar da 'yan wuta su ke yi a tsakaninsu. To a cikin wannan ayar kur'ani yana fadin cewa, duk da cewa masu laifi da su ka shiga wuta suna dora laifi akan jagororinsu, to su jagororin nasu da su ka riga su shiga cikin wutar suna maida musu jawabi da cewa: Ba ku da wani fifiko akanmu balle ku sami sassauci ko wani sauki na azaba, ku ma masu laifi ne daidai da mu. Ubangiji yana fadin cewa babu daya daga cikin bangarorin biyu da zai sami wani sauki daga azaba. Domin kuwa sun kasance masu jayayya da girman kai ga gaskiya a rayuwarsu ta duniya. Anan Allah yana buga misali da cewa idan har rakumi zai iya kutsawa ya fita ta kafar allura to su ma wadannan masu laifin za su iya fita daga cikin azabar wuta. Darussan da za mu koya daga wannan aya. 1-Makomar mutum a duniya da lahira tana damfare ne da ayyukansa. manyan laifukan da mutum ya yi ba za su sa a mance da kananan laifukansa ba. 2-Sabo, yana rufewa mutum kofofin rahamar ubangiji ya kuma haramta masa samun jin kan ubangiji. 3-Tushen kafrici da karyata ayoyin Allah shi ne girman kai da neman daukaka da matsayi.

Yanzu kuma sai a saurari aya ta 41 a cikin wannan sura ta A'araf.

لَهُم مِّن جَهَنَّمَ مِهَادٌ وَمِن فَوْقِهِمْ غَوَاشٍ وَكَذَلِكَ نَجْزِي الظَّالِمِينَ{41}

"Suna da shimfida daga wutar jahannama kuma rubushin wuta ya yi musu rumfa. Da haka ne mu ke sakawa azzalumai."

Wannan ayar tana bayyana cewa wuta da azaba su ne shimfidar 'yan wuta kuma su ne rumfar da za ta yi musu inuwa. Azaba ce ta ke zagaye da su daga kowace kusurwa babu wata kafa komai karancinta da za su samu sararawa. A cikin wannan ayar ubangiji yana kiran kafirai da sunan masu laifi da kuma azzalumai, domin kuwa kafirci yana a matsayin mai share fagen aikata laifi ne da kuma zalunci. Darussan da za mu koya daga wannan aya. 1-Wadanda ba su da wata manufa a duniya sai gwagwarmayar samun hutu da jin dadi da morewa, to a lahira mazauninsu wuta. 2-Wuta za ta zagaye kafirai da azzalumai ta kowace kusurwa.

Yanzu kuma sai a saurari aya ta 42 a cikin suratu "A'arafi.

وَالَّذِينَ آمَنُواْ وَعَمِلُواْ الصَّالِحَاتِ لاَ نُكَلِّفُ نَفْساً إِلاَّ وُسْعَهَا أُوْلَـئِكَ أَصْحَابُ الْجَنَّةِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ{42}

" Wadanda su ka yi imani sannan kuma su ka yi ayyukan kwarai, ba mu kallafawa rayi sai abinda za ta iya. Wadannan su ne 'yan aljanna za su dawwama a cikinta."

Salon kur'ani mai girma ne aduk lokacin da ya yi bayani akan sakamakon da masu aikata laifi za su fuskanta a lahira to sai kuma ya yi bayani akan sakamakon masu ayyukan kwarai. A cikin wannan ayar Ubangiji yana bayyana cewa: Muminai masu aikin kwarai za su shiga aljanna kuma za su dawwama a cikinta, domin kuwa a rayuwarsu ta duniya sun yi aiki iya gwgrgwadon iyawarsu. Darussan da za mu koya daga wannan aya. 1-Hada imani da aiki yana da sakamako a ranar lahira wanda shi ne dawwama a cikin aljanna da zama tare da salihan bayin Allah. 2-A musulunci babu wani aiki da ake dorawa mutum sai wanda zai iya, ba wanda ya fi karfinsa ba, kowane mutum iya gwargwadon karfinsa da ikonsa.

Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 43 a cikin wannan sura ta A'araf.

وَنَزَعْنَا مَا فِي صُدُورِهِم مِّنْ غِلٍّ تَجْرِي مِن تَحْتِهِمُ الأَنْهَارُ وَقَالُواْ الْحَمْدُ لِلّهِ الَّذِي هَدَانَا لِهَـذَا وَمَا كُنَّا لِنَهْتَدِيَ لَوْلا أَنْ هَدَانَا اللّهُ لَقَدْ جَاءتْ رُسُلُ رَبِّنَا بِالْحَقِّ وَنُودُواْ أَن تِلْكُمُ الْجَنَّةُ أُورِثْتُمُوهَا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ{43}

" Sai mu cire duk wata kwafa da ta ke cikin kirajensu, koramu suna gudana a karkashinsu. Sai su ce mun yi wa Allah godiya wanda ya shiryar da mu zuwa ga wannan. Ba domin Allah ya shiryar da mu ba da ba mu shiryu ba. Hakika manzannin Ubangijinmu sun zo mana da gaskiya. A ka yi shela cewa an gadar mu ku da wadannan aljannatai saboda abinda ku ka kasance kuna aikatawa."

Daga cikin ni'imomin da Allah zai yi wa 'yan aljanna da akwai cire rike juna da kwafa da hassada daga cikin zukata. Babu abinda zai saura acikin kirajen 'yan aljanna sai kaunar juna. Kuma a kodayaushe mazauna aljanna suna tuna ubangijinsu da yi musu godiya akan shiryar da su da ya yi ta hanyar aiko da manzanni a duniya. Darussan da za mu koya daga wannan aya. 1-Rayuwar da babu hassada da rike juna a zuci acikinta, ita ce rayuwar aljanna. 2-"yan aljanna ba su ganin cewa ayyukansu ne su ka shigar da su cikinta, suna daukar cewa shiryar Allah ce da rahamrsa ta shigar da su cikin aljanna.

Masu saurare karshen shirinmu kenan a wannan lokacin. Da fatan za a kasance a tare da mu anan gaba domin jin ci gabansa.

Suratul A'araf, Aya Ta 44-48 (Kashi Na 235)

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin da mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur’ani mai girma. Da fatan za a kasance a tare da mu domin a saurare shi daga inda mu ka tsaya a baya.

Yanzu sai a saurari aya ta 44 a cikin wannan sura ta “A’araf.’

وَنَادَى أَصْحَابُ الْجَنَّةِ أَصْحَابَ النَّارِ أَن قَدْ وَجَدْنَا مَا وَعَدَنَا رَبُّنَا حَقّاً فَهَلْ وَجَدتُّم مَّا وَعَدَ رَبُّكُمْ حَقّاً قَالُواْ نَعَمْ فَأَذَّنَ مُؤَذِّنٌ بَيْنَهُمْ أَن لَّعْنَةُ اللّهِ عَلَى الظَّالِمِينَ{44}

“Sai ‘yan aljanna su ka kirayi ‘yan wuta suna cewa: mu mun sami abinda ubangijinmu ya yi alkawali da gaske, shin kun sami abinda ubangijinku ya yi mu ku alkawali da gaske? Sai su ce: “Na’am mun samu. Sai mai shela ya yi shela a tsakaninsu da cewa: La’anar Allah ta tabbata ga azzalumai.”

Ayoyin baya sun yi magana ne akan tattaunawa da ‘yan wuta su ke yi a tsakanin. To a cikin wannan ayar bayani ne akan tattaunawa a tsakanin ‘yan aljanna da ‘yan wuta, wanda ya ke a matsayin darasi ne mai girma a gare mu tun anan duniya. Ya zamana mun fahimci cewa alkawalin da Allah ya ke yi na sakamako da gaskiya ne zai tabbata. Wadanda su ke yin munanan ayyuka za su ga sakamakon ayyukansu a lahira haka nan kuma masu ayyukan kwarai. Darussan da za mu koya daga cikin wannan aya. 1-Yanayin aljanna da wuta zai bada dama ga mazaunansu su rika yin magana da juna. 2-Zaluntar kai da zaluntar iyali da zaluntar al’umma su ne tushen shiga wuta.

Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 45 acikin wannan sura ta A’araf.

الَّذِينَ يَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ اللّهِ وَيَبْغُونَهَا عِوَجاً وَهُم بِالآخِرَةِ كَافِرُونَ{45}

“Wadanda su ke yin togiya ga bin tafarkin Allah, su ke kuma son karkatar da ita, su ne kafirai a ranar lahira.”

Abinda wannan ayar ta ke yin bayani akansa shi ne cewa, ba wadanda su ka ki bada gaskiya ba ne kadai azzalumai, su ma wadanda su ke kokarin hana mutane bin tafarkin Allah azzalumai ne, kuma su ke kokarin gurbata addini da bata masa suna domin hana mutane binsa da riko da shi.

Kirkiro bidi’a da camfe-camfen da ake damfara su da addini suna daga cikin ayyukan masu jayayya da addini wadanda su ke shiga a karkashin zalunci.

Darussan da za mu koya daga cikin wannan aya.

1-Makiyan addini za su ya ki masu addini da makamai idan sun sami dama, idan kuma ba su samu ba za su yake su da gurbata sunan addini. 2-Zalunci na tunani da kuma gurbata al’adun al’umma suna daga cikin nauo’in zalunci mafi girma da samakonsu ya ke da tsanani.

Yanzu kuma sai a saurari aya ta 46 acikin wannan sura ta “A’araf.’

وَبَيْنَهُمَا حِجَابٌ وَعَلَى الأَعْرَافِ رِجَالٌ يَعْرِفُونَ كُلاًّ بِسِيمَاهُمْ وَنَادَوْاْ أَصْحَابَ الْجَنَّةِ أَن سَلاَمٌ عَلَيْكُمْ لَمْ يَدْخُلُوهَا وَهُمْ يَطْمَعُونَ{46}

“ A tsakaninsu-‘yan wuta da ‘yan aljanna- da akwai shamaki. Akan katangar la’arafi da akwai mazaje da sun san kowane-dan wuta da dan aljanna- daga alamunsu. “Yan aljanna su ka ce gaisuwa ta tabbata a gare ku. Ba su kai ga shiga aljanna ba alhali su suna kwadayi.”

Wannan ayar tana yin magana ne akan wani wuri na musamman mai suna A’araf wanda kuma ya ke a tsakanin aljanna da wuta. Da akwai wasu mazaje akan wannan wurin wadanda suna ganin ‘yan aljanna da kuma ‘yan wuta. A bisa wasu riwayoyi da su ka zo a cikin tafsirai, mazajen da su ke a tozon la’arafi, waliyan Allah ne na musamman da su ke sa ido akan yadda ‘yan ajanna su ke shiga aljanna da kuma yadda ‘yan wuta su ke shiga wuta. Sai dai da akwai wasu malaman tafsirin da su ka bayyana cewa masu raunin imani ne za su kasance a tozon la’arafi. Suna fatan shiga ajanna amma ayyukansu ba su cika ba. Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-Ayyukan mutum suna da tasirin da ya ke fitowa a kamanninsa na zahiri da yin ishara da badininsa. 2-A’araf wani matsayi ne na koli na ‘yan’adamtaka, mu yi aikin da za mu sami zama a cikinsa.

Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 47 da 48 a cikin wannan sura ta “A’araf.

وَإِذَا صُرِفَتْ أَبْصَارُهُمْ تِلْقَاء أَصْحَابِ النَّارِ قَالُواْ رَبَّنَا لاَ تَجْعَلْنَا مَعَ الْقَوْمِ الظَّالِمِينَ{47} وَنَادَى أَصْحَابُ الأَعْرَافِ رِجَالاً يَعْرِفُونَهُمْ بِسِيمَاهُمْ قَالُواْ مَا أَغْنَى عَنكُمْ جَمْعُكُمْ وَمَا كُنتُمْ تَسْتَكْبِرُونَ{48}

“Idan an juyar da maganansu zuwa kan ‘yan wuta sai su ce: Ya ubangijinmu kada ka sanya mu a cikin wuta tare da azzalumai.” “Yan la’arafu su ka kirayi wasu mutane da su ke gane su saboda alamunsu suna cewa: Abinda ku ka tara( na dukiya da mukami) bai wadatar da ku da kome bad a girman kanku da barin gaskiya.”

A kodayaushe mazauna tozon la’arafi suna kallon aljanna ne, amma idan maganansu su ka dubi ‘yan wuta suna rokon Allah da ya nesanta su daga zama tare da ‘yan da su ke azzalumai. Darussan da su ke cikin wadannan ayoyin. 1-Tun kafi mu kai ga fuskantar gargadin masu aikin kwarai mu kaucewa girman kai da son daukaka anan duniya, domin kuwa karshensa kaskanci. 2-Dukiya da mukami suna amfani ne aduniya, mu yi tunanin abubuwan da za su amfane mu a lahira. 3-Siffofin mutane a lahira suna nuni ne da cewa su ‘yan aljanna ne ko wuta.

Karshen shirinmu na wannan lokacin kesai sa a kasance a tare da mu domin jin ci gaban shirin.

Suratul A'araf, Aya Ta 49-52 (Kashi Na 236)

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin Hannunka mai sanda wanda mu ke kawo muku fassarar ayoyin alkur'ani mai girma. Da fatan za ku kasance a tare da mu domin jin ci gaban shirin daga inda mu ka tsaya.

Yanzu sai a saurari aya ta 49 a cikin wannan sura ta A'araf.

أَهَـؤُلاء الَّذِينَ أَقْسَمْتُمْ لاَ يَنَالُهُمُ اللّهُ بِرَحْمَةٍ ادْخُلُواْ الْجَنَّةَ لاَ خَوْفٌ عَلَيْكُمْ وَلاَ أَنتُمْ تَحْزَنُونَ{49}

"Shin wadannan ne ku ka yi rantsuwa akan cewa Allah ba zai yi musu rahama ba? Ku shiga aljanna ba ku cikin tsoro kuma ba ku bakin ciki."

A shirin bayan ana magana ne akan tattaunawa a tsakanin mazauna tozon la'arafi da kuma 'yan wuya da 'yan aljanna. A karshen managar da su ka yi wa 'yan wuta mazauna tozon la'arafin sun fada musu cewa: "Yanzu kun gani da idanunku cewa dukiya da kuma matsayin da ku ke da su a duniya ba su yi muku wani amfani ba anan lahira. Ga shi nan kuna konewa acikin wuta. A cikin wannan aya ci gaba da yin magana da 'yan wuta da fada musu cewa: "Wadannan 'yan aljannar su ne mutanen da ku ke wulakantawa a duniya kuna fadin cewa mu ne wadanda Allah ya ke kauna saboda haka ne ya bamu dukiya da matsayi. To yanzu ku duba ku gani wadancan mutanen da ku ke yi wa kallon wulakanci ne su ka shiga aljanna ku kuwa da ku ke rayuwa cikin hutu ga ku nan kun kare da shiga wuta. Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-Imani da kuma aiki su ne abubuwan da su ke jawo wa mutum samun rahamar Allah, ba dukiya da matsayi na duniya ba. Kuma talauci da kuncin rayuwa a duniya ba ya nufin cewa mai su ba zai shiga aljanna ba. 2-Kada mu yi gaggawa wajen yanke hukunci a ranar lahira ne kowa zai gane matsayinsa. "yan wuta za su shuga wuta, yan aljanna za su shiga aljanna.

Yanzu kuma sai a ya ta 50 a cikin wannan sura ta "A'araf.

وَنَادَى أَصْحَابُ النَّارِ أَصْحَابَ الْجَنَّةِ أَنْ أَفِيضُواْ عَلَيْنَا مِنَ الْمَاء أَوْ مِمَّا رَزَقَكُمُ اللّهُ قَالُواْ إِنَّ اللّهَ حَرَّمَهُمَا عَلَى الْكَافِرِينَ{50}

"Sai 'yan wuta su kirayi 'yan aljanna-suna cewa- ku 'yammana ruwa kadan ko kuma wani abu daga cikin abinda Allah ya huwace muku. Sai su ce ai Allah ya haramta su ga kafirai."

Baya ga tattaunawar da ta gudana a tsakanin mazauna tozon la'arafi da 'yan aljanna da kuma 'yan wuta, wannan ayar tana magana akan halin da 'yan wuta da 'yan aljanna su ke ciki bayan da kowanensu ya shiga makomarsa. Tana fadin cewa: Zafin da ke cikin jahannama yana da kunar gaske ta yadda abu na farko da mazaunta su ke da bukatuwa da shi, shi ne ruwan sha. Da fari za su tambayi masu tsaron aljanna amma su yanke kauna da cewa za su samu, daga nan sai su koma kan mazauna aljanna. Sai dai 'yan aljanna basu da hakkin da za su baiwa 'yan wuta ruwa domin kuwa Allah ya hamata shi ga 'yan wuta haka nan kuma sauran ni'imomin da su ke cikin aljannar. Darussan da za mu koya daga wannan aya. 1-Wadanda tunaninsu shi ne tara abin duniya kadai, to su ne talakawa a lahira da za su kasance mabukata. 2-Wadanda a duniya ba su tsaya akan iyakokin Allah ba su ke tsallake haram to za su rasa nimi'momin Allah a lahira.

Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 51 a cikin suratu A'araf.

الَّذِينَ اتَّخَذُواْ دِينَهُمْ لَهْواً وَلَعِباً وَغَرَّتْهُمُ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا فَالْيَوْمَ نَنسَاهُمْ كَمَا نَسُواْ لِقَاء يَوْمِهِمْ هَـذَا وَمَا كَانُواْ بِآيَاتِنَا يَجْحَدُونَ{51}

"Wadannan da su ka dauki addininsu abin wasa da nishadi kuma rayuwar duniya da rude su, to a yau za mu mance da su kamar yadda su ka mance da haduwa da wannan rana tasu da kuma jayayyar da su ke yi da ayoyinmu."

Ayar bata tana magana akan koken da 'yan wuta su ke yi suna neman agaji daga 'yan aljanna akan ruwan da za su sha. To a cikin wannan ayar ubangiji yana cewa ne ba mu zalunce su ba, abinda su ka samu na azaba sakamakon ayyukansu ne a duniya. A lokacin da annabawa su ke kiransu zuwa ga gaskiya sun rufe kunnuwansu ba su jin abinda ake kiransu zuwa gare shi. Maimakon haka ma sai su ka rika yin isgili da addini suna kuma bugun kirji da alfahari da dukiya da mukamin da su ke da shi. Suna tsammanin cewa tsayuwar kiyama da kuma hisabi wasa ne ba da gaske ba. Wannan shi ne abinda su ka aikata a duniya saboda haka su ka fuskanci sakamakon da ya dace a lahira. Darussan da za mu koya daga wannan aya. 1-Kafirai, suna wasa da addini da daukarshi abin nishadi. 2-Duniya mayaudariya ce saboda haka damfaruwa da ita shi ne abinda zai ke haddasa gafala da lahira.

Yanzu kuma sai aya ta 52 a cikin wannan shirin na "A'araf.

وَلَقَدْ جِئْنَاهُم بِكِتَابٍ فَصَّلْنَاهُ عَلَى عِلْمٍ هُدًى وَرَحْمَةً لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ{52}

" Hakika mun zo mu su-mutane- da littafi wanda mu ka fayyace shi bisa ilimim saboda ya zama mai shiriya da rahama ga wadanda su ka bada gaskiya."

Addini kamar yadda ayar ta ke bayyanawa hanya ce ta shiriya wanda Allah ya sauko da shi ga mutane a cikin littafi a matsayin dokoki. Littafi ne wanda dokokinsa su ke tafiya da fitirar bil'adama da kuma hankalinsa. Sai dai kafirai ba a shirye su ke su karbe shi ba, maimakon haka ma sun dauke shi a matsayin abin wasa. Darussan da za mu koya daga wannan aya. 1-Ubangiji yana yankewa mutane hujja ne ta hanyar littafin da ya saukar a gare su saboda kuma yanke uzuri a gare su. 2-Wahayin Ubangiji yana sauka ne bisa ilimi kuma yana zuwa ne gwargwadon bukatar mutane zuwa ga kamala da samun sa'ada.

A nan ne karshen wannan shirin sai kuma mun sake haduwa da ku acikin shiri na gaba domin ci gaba daga inda mu ka tsaya.

Suratul A'araf, Aya Ta 53-56 (Kashi Na 237)

Masu sauraro barkanmu da sake da haduwa da ku acikin wannan shirin da mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur’ani mai girma. Sai a kasance a tare da mu saboda a ji ci gaban shirin daga inda mu ka tsaya.

Yanzu sai a saurari aya ta 53 a cikin suratu “A’araf.”

هَلْ يَنظُرُونَ إِلاَّ تَأْوِيلَهُ يَوْمَ يَأْتِي تَأْوِيلُهُ يَقُولُ الَّذِينَ نَسُوهُ مِن قَبْلُ قَدْ جَاءتْ رُسُلُ رَبِّنَا بِالْحَقِّ فَهَل لَّنَا مِن شُفَعَاء فَيَشْفَعُواْ لَنَا أَوْ نُرَدُّ فَنَعْمَلَ غَيْرَ الَّذِي كُنَّا نَعْمَلُ قَدْ خَسِرُواْ أَنفُسَهُمْ وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُواْ يَفْتَرُونَ{53}

“Shin su-kafirai- suna tsumayen wani abu na daban ya faru ne sabaninsa- alkawalin Allah? Ranar da tawilinsa zai sauka- wato ranar kiyama- wadanda su ka mance ita-ranar- a baya, za su fadi cewa: Hakika manzannin Ubangijinmu sun zo da gaskiya, shin da akawai masu ceto da za su cece mu, ko kuwa za a koma da mu- gidan duniya, saboda mu yi wasu ayyukan sabanin wadanda mu ka kasance muna aikatawa. Sun riga sun yi asarar rayukansu, kuma abubuwan da su ke dauka bisa karya- na gumaka a matayin masu cetonsu- sun bace musu.”

Idan masu sauraro ba su mance ba a cikin ayoyin baya an yi bayani ne akan tattaunawa a tsakanin ‘yan aljanna da kuma ‘yan wuta. To wannan ayar tana magana ne akan furucin da masu laifi su ke yi a ranar kiyama. Suna fadin cewa: Ubangiji ya aiko mana a manzanni a duniya domin shirya amma mun ki karbar sakonsu, mu ka kau da kai daga gare su. Shin ko wannan furucin da mu ka yi da laifukanmu za su mu sami masu ceto, ko kuma a maida mu duniya saboda mu yi aikin kwarai? Shakka babu jawabi a gare su shi ne cewa, yin furuci a lokacin da azaba ta zo ba shi da wata kima. Abubuwan da za mu koya daga wannan aya. 1-Mu bada muhimmanci ga gargadin da kur’ani mai girma ya ke yi tun anan duniya domin kuwa a ranar lahira koke ba shi da wani amfani. 2-Samun ceto a ranar lahira yana da sharadi, kada mu zama masu tsammanin samun sabo alhali muna ci gaba da aikata sabo.

Yanzu kuma sai a saurari a ya ta 54 a cikin wannan sura ta “A’araf.’

إِنَّ رَبَّكُمُ اللّهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَى عَلَى الْعَرْشِ يُغْشِي اللَّيْلَ النَّهَارَ يَطْلُبُهُ حَثِيثاً وَالشَّمْسَ وَالْقَمَرَ وَالنُّجُومَ مُسَخَّرَاتٍ بِأَمْرِهِ أَلاَ لَهُ الْخَلْقُ وَالأَمْرُ تَبَارَكَ اللّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ{54}

“Hakika ubangijinku shi ne wanda ya halicci sammai da kassai a cikin kwanaki shida, daga nan sai ya daidaita akan al’arshin iko da tafiyar da duniya, yana rufe rana da dare,kuma kwallon rana da kwallon wata da taurari suna biyayya ne ga umarninsa. Ku sani cewa halitta da tafiyar da ita nashi ne. Tubarkallah da Allah, ubangijin talikai.”

Wannan ayar tana rusa karkatattun akidu ne na mushrikai dangane da Ubangiji. Tana cewa ubangiji na hakika wanda shi ne ya halicci sammai da kassai da rana da wata da taurari da dukkanin halittu shi ne ya halicce ku, kuma ya ke tafiyar da duniya bakidaya. Duk wani abu da ya ke cikin halitta yana tafiya ne a karkashin iko da umarnin Ubangiji. Tare da cewa yana da ikon da zai halicci duniya acikin kasa da kyaftawar idanu, amma hikimarsa ta sa ya yi halitta bisa mataki-mataki. Abubuwan da za mu koya daga cikin wannan aya. 1-Halitta duniya ta kasance ne bisa wani tsari na musamman na Ubangiji, kuma yana tafiyar da ita ne cikin hikima. 2-Hanzari yana daga cikin ayyukan shaidan, yin aiki bisa mataki-mataki daga Allah ya ke. 3-Halitta baki daya tana tafiya ne cikin aikin tare da dukkanin bangarorinta, kuma tafiyarta da ci gabanta ya jingina ne da falalar ubangiji.

Yanzu kuma sai a saurari aya ta 55 da 56 a cikin wannan sura ta A’araf.

ادْعُواْ رَبَّكُمْ تَضَرُّعاً وَخُفْيَةً إِنَّهُ لاَ يُحِبُّ الْمُعْتَدِينَ{55} وَلاَ تُفْسِدُواْ فِي الأَرْضِ بَعْدَ إِصْلاَحِهَا وَادْعُوهُ خَوْفاً وَطَمَعاً إِنَّ رَحْمَتَ اللّهِ قَرِيبٌ مِّنَ الْمُحْسِنِينَ{56}

“ Ku kirayi ubangijinku kuna masu kaskantar da kai kuma a asirce. Ubangiji ba ya son masu shisshigi. “Kada ku yi barna a doron kasa bayan an gyara ta. Ko roke shi kuna masu tsoro da kuma kwadayi. Hakika rahamar Allah tana kusa da masu kyautatawa.”

Wadannan ayoyin tana yin magana ne akan dalilan kulla alakar mutum da Ubangiji. Tana cewa: Ku kiraye shi ta hanyar yin addu’a, ba ku je wurin gumaka ba. Ku kiraye shi cikin karantar da muryarku ba daga murya da karfi ba. Bugu da kari ayar tana magana akan kyautata ayyuka wadanda su ke kusantar da mutum ga Allah. Abubuwan da za mu koya daga wannan ayar. 1-Addu’a tana nufin nuna bukatuwa ga Allah, wanda baya rokon Allah yana nufin shi mai girman kai ne. 2-Sanin Allah kadai ba isa ba, dole ne kuma a bauta masa, kuma bauta ba tare da addu’a ba, ba ta cika ba. 3-Al’ummar kwarai tana fuskantar hatsari, saboda haka jagororin kwarai na al’umma suna da bukatar yin addu’a da rokon Allah. Wannan shi ne karshen shirinmu na wannan lokacin, sai mun sake haduwa da ku acikin shiri na gaba.

Suratul A'araf, Aya Ta 57-62 (Kashi Na 238)

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin na Hannunka Mai Sanda. Da fatan za ku kasance da mu domin jin ci gaban shirin.

Yanzu sai a saurari aya ta 57 acikin wannan sura ta "A'araf.

وَهُوَ الَّذِي يُرْسِلُ الرِّيَاحَ بُشْراً بَيْنَ يَدَيْ رَحْمَتِهِ حَتَّى إِذَا أَقَلَّتْ سَحَاباً ثِقَالاً سُقْنَاهُ لِبَلَدٍ مَّيِّتٍ فَأَنزَلْنَا بِهِ الْمَاء فَأَخْرَجْنَا بِهِ مِن كُلِّ الثَّمَرَاتِ كَذَلِكَ نُخْرِجُ الْموْتَى لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ{57}

"Shi ne wanda ya ke aiko da iska gabanin saukar ruwa da ya ke rahama, saboda idan ta dauki gajimarai masu nauyi mu kora su garin da ya ke matacce, sai mu saukar da ruwa daga gare shi, mu kuma fitar da dukkanin 'ya'yan marmari. To kwatankwacin haka ne mu ke fito da matattu."

A baya mun yi magana akan iko da kudurar Allah a cikin halittar sama da kasa. Wannan ayar kuwa tana yin magana ne akan rahamar Ubangiji ta saukar da ruwa wanda shi ne ya ke rayar da kasa. Tana cewa iska tana kadawa ne bisa umarnin ubangiji saboda haka kada ku dauka cewa dabi'a wani busasshen abu ne, ko kuma haka kawai halitta ta samu ta hanyar arashi. Baya ga kasantuwar sanadarorin dabi'a a matsayin dalilan da su ke nuni da samuwar Ubangiji, suna kuma nuni da cewa da akwai tashi bayan mutuwa. Darussan da su ke cikin wannan aya. 1-Sanin sirrin da ke cikin dabi'a da kuma yadda ta ke aiki, bai kamata ya zama dalilin rafkanar mutum daga tushen halitta ba. 2-Mutuwa ba ta nufin karewa, tana nufin fita ne daga wani hali zuwa wani halin, kamar yadda bushewar kasa ba ta nufin mutuwarta.

Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 58 a cikin wannan sura ta "A'araf.

وَالْبَلَدُ الطَّيِّبُ يَخْرُجُ نَبَاتُهُ بِإِذْنِ رَبِّهِ وَالَّذِي خَبُثَ لاَ يَخْرُجُ إِلاَّ نَكِداً كَذَلِكَ نُصَرِّفُ الآيَاتِ لِقَوْمٍ يَشْكُرُونَ{58}

"Badadayin gari, yana fitar da tsirransa da izinin ubangijinsa, wanda kuwa ya ke baragurbi baya fitar da-tsiro-sai dan kadan gurbatacce. Da haka ne mu ke sarrafa ayoyinmu ga mutanen da su ke godiya."

Idan ayar baya ta yi magana akan cewa ruwan sama yana taimakawa wajen raya kasa, kamar yadda ayar da ta gabata ta nuna, to wannan ayar tana yin magana ne akan cewa kyawun kasa ma yana taimakawa wajen fitar da tsire-tsire. Darussan da za mu koya daga cikin wannan ayar. 1-Saukar rahama kadai ba ta wadatar ba wajen shiriyar da mutum, da akwai bukatar mutum ya zama mai cikin shirin karbar wanann rahamar. 2-Tsarki yana a matsayin fagen samun sa'ada kuma yana a matsayin garkuwa daga bacewa.

Yanzu kuma sai a saurari aya ta 59 da kuma 60 acikin wannan sura ta "Aaraf."

لَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحاً إِلَى قَوْمِهِ فَقَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُواْ اللَّهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَـهٍ غَيْرُهُ إِنِّيَ أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ{59} قَالَ الْمَلأُ مِن قَوْمِهِ إِنَّا لَنَرَاكَ فِي ضَلاَلٍ مُّبِينٍ{60}

"Mun aiko da Nuhu zuwa ga mutanensa sai ya ce: Ya ku mutane ku bautawa Allah ba ku da wani Allah sai shi. Ina ji mu ku tsoron azabar rana mai girma.

"Sai wani gungu na mutanesa su ka ce, mu muna ganinka a cikin bayyanannen bata."

Wannan ayar tana yin magana ne akan annabi Nuhu (a.s.) dangane da da'awarsa ta tauhidi zuwa ga mutanensa. Tsawon shekaru masu tsawon gaske ya yi yana gargadinsu akan azabar wuta. Sai dai mutanen nashi sun bijirewa gaskiya. Darussan da za mu koya daga wannan aya. 1-Dukkanin annabawan Allah a tsawon tarihi suna yin kira ne ga tauhidi da kadaita Allah. 2-A tsawon tarihin bil'adama a doron kasa, masu nuna adawa ga annabawa su ne masu jan wuya acikin kowace al'umma.

Yanzu kuma sai a ya ta 61 da kuma 62 a cikin wannan sura ta "A'araf."

قَالَ يَا قَوْمِ لَيْسَ بِي ضَلاَلَةٌ وَلَكِنِّي رَسُولٌ مِّن رَّبِّ الْعَالَمِينَ{61} أُبَلِّغُكُمْ رِسَالاَتِ رَبِّي وَأَنصَحُ لَكُمْ وَأَعْلَمُ مِنَ اللّهِ مَا لاَ تَعْلَمُونَ{62}

"Ya ce: Ya ku mutanena babu bata a tare da ni, sai dai ni manzo ne daga ubangijin talikai. Ina isar mu ku da sakwanni daga ubangijina ina kuma yi mu ku nasiha. Na kuma san abinda ba ku sani ba daga Allah."

Wannan ayar tana bayyana martanin da annabi Nuhu (a.s) ya mayarwa da masu jan wuyan mutanesa da su ka zarge shi da bata. Ya yi magana da su cikin girmamawa ba tare da amfani da kalmomi irin wadanda su ka yi a kansa ba. Ya fada musu cewa shi ma'aikin ne da ya zo musu da sakwanni. Darussan da su ke cikin wannan aya. 1-Mu zama masu hakuri wajen fuskantar wulakancin jahilai da isgilinsu. Bai kamata mu biye musu ba mu rika yin maganganu irin wadanda su ke yi. 2-Mai yin tarbiyya da mai isar da sako ya zamana mai son alheri ga mutane da kuma tausaya musu. Ya kuma zama ma'abocin ilimi domin ya wayar da kan mutane akan abinda ya ke bata. 3-Annabawa suna da ilimin da sauran mutane ba su sani ba.

Karshen shirin namu na wannan lokacin kenan sai mun sake hadewa a cikin shiri na gaba domin ci gaba daga inda mu ka tsaya.

Suratul A'araf, Aya Ta 63-66 (Kashi Na 239)

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku acikin wannan shirin na Hannunka mai sanda. Shiri ne dai wanda mu ke kawo muku fassarar ayoyin kur'ani mai girma. Da fatan za a kasance a tare da mu domin a ji ci gaban shirin.

Yanzu sai a saurari aya ta 63 a cikin suratu A'araf.

أَوَعَجِبْتُمْ أَن جَاءكُمْ ذِكْرٌ مِّن رَّبِّكُمْ عَلَى رَجُلٍ مِّنكُمْ لِيُنذِرَكُمْ وَلِتَتَّقُواْ وَلَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ{63}

" Shin kuna mamaki ne saboda wani mutum daga cikinku ya zo mu ku da gargadi daga ubangijinku domin ya ja kunnenku kuma saboda ku ji tsoron Allah ko ayi mu ku rahama?"

Ayoyin aya sun yi magana ne akan annabi Nuhu da yadda mutanensa su ka maida martani akan wa'azin da ya rika yi musu. A cikin wannan ayar annabi Nuhu yana maida musu jawabi akan cewa me ya sa su ke yin mamaki saboda Ubangiji ya saukar da wahayi akan mutane ? Annabi Nuhun ya kuma ci gaba da cewa aikinsa shi ne isar da sakon Allah a gare su, babu wani abu da na ke bukauwa da shi daga gare ku. ko kuwa ba ku son ku sami rahama daga Allah? Idan kuna son rahama to ku zama masu tsoron Allah kuma ku nesanci nutsewa cikin duniya.

Abubuwan da za mu koya daga wannan aya.

1-Manufar saukar da wahayi shi ne yi wa mutum tarbiyya ta hanyar fadakar da shi. 2-Annabawan Allah mutane kuma suna fitowa ne daga cikinsu, wannan shi ne abinda masu more jin dadin rayuwa da girman kai ba su amince da shi ba.

Yanzu kuma sai aya ta 64 a cikin suratu "A'araf.

فَكَذَّبُوهُ فَأَنجَيْنَاهُ وَالَّذِينَ مَعَهُ فِي الْفُلْكِ وَأَغْرَقْنَا الَّذِينَ كَذَّبُواْ بِآيَاتِنَا إِنَّهُمْ كَانُواْ قَوْماً عَمِينَ{64}

"Sai su ka karyata shi, sai mu ka tseratar da shi da wadanda su ke a tare da shi a cikin jirgin ruwa, mu ka kuma nitsar da wadanda su ka karyata ayoyinmu. Sun kasance mutane makantar zuciya."

Tare da cewa tushen azabar da Ubangiji zai yi wa mutane bisa laifukansu a lahira ne, sai dai duk da haka a wasu nau'oin na laifuka ana ganin sakamakonsu tun anan duniya. Wannan ayar tana yin magana ne akan cewa Allah ya umarci annabi Nuhu da ya kera jirgin ruwa domin ya shiga shi da mutanensa saboda zai halakar da kafiran da su ka ki karbar gaskiya su ke kuma yi mata isgili. A karshen ayar kamar yadda ya ke zuwa a duk lokacin da ambaton azaba ya zo, ya kafa hujja akan dalilin yi musu azaba. Yana fadin cewa kurumcewar zukatansu ce ta jawo musu azaba. Domin kuwa Allah ba azzalumin kowa ba ne yana sakawa mutum ne bisa aikinsa.

Darussan da za mu koya daga wannan aya.

1-Imani shi ne musabbabin samun tsira, karyata gaskiya kuma shi ne dalilin halaka. 2-Bala'oin dabi'a suna zuwa ne daga Allah kuma suna a matsayin nuna karfi ne na Ubangiji.

Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 65 acikin wannan sura ta "A'araf.

وَإِلَى عَادٍ أَخَاهُمْ هُوداً قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُواْ اللّهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَـهٍ غَيْرُهُ أَفَلاَ تَتَّقُونَ{65}

"Mun aikewa Adawa dan'uwansu Hudu. Ya fadi cewa ya ku mutanena ku bautawa Allah saboda ba ku da wani abin bauta waninsa. Shin ba za ku zama masu takawa ba? "

Bayan labarin abinda ya faru tsakanin annabi Nuhu da mutanensa wannan ayar kuwa tana yin magana ne akan labarin annabi Hudu da mutanensa. Su dai Adawa mutane ne da su ka rayu a wajen kasar Yamen da ke kudancin Saudiyya a yanzu. Sun kasance mutane masu karfin gaske, amma a lokaci guda sun nutse cikin barna ta halayya da kuma bautar gumaka. Saboda haka ne Ubangiji ya tashi annabi Hudu a cikinsu domin ya shiryar da su. Ya raba su da bautar gumaka da kuma dora su kan tafarkin kamala. Saboda haka sakon da isar a gare su ya zama na kira ga bautar ubangiji da nesantar bautar waninsa. Da kuma kiransu da su nesanci munanan ayyuka da rungumar ayyukan kwarai.

Darussan da za mu koya daga wannan aya.

1-Annabawa suna mu'amala da mutane cikin 'yan'uwantaka da kuma nuna jin kansu da tausaya musu. 1-Yin kira zuwa ga kadaita Allah da nesantar shirka shi ne ginshikin kiran dukkanin annabawa.

Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 66 a cikin wannan sura ta "A'araf.

قَالَ الْمَلأُ الَّذِينَ كَفَرُواْ مِن قَوْمِهِ إِنَّا لَنَرَاكَ فِي سَفَاهَةٍ وِإِنَّا لَنَظُنُّكَ مِنَ الْكَاذِبِينَ{66}

"Sai jagorori daga cikin mutanensa su ka fadi cewa, mu ba ku ganinka sai a matsayin mai wauta, muna kuma tsammanin cewa kana cikin makaryata."

Kamar yadda mutanen annabi Nuhu ba su nutsu sun fahimci abinda ya ke fada musa ba su ka yi masa isgili, haka nan kuma mutanen annabi Hudu su ka kira shi wawa wanda maganganun da ya ke yi ba su da ma'ana. Sun kore cewa yana magana ne daga Allah saboda haka makaryaci ne. A kodayaushe haka kafirai da mushrikai su k magana ta yin zargi mara ma'ana kuma ba su da ladabi na yin tattaunawa. Suna zargin annabawa da Allah ya aiko musu da hauka ko mafarkin tsaye. Darussan da su ke cikin wannan aya.

1-Annabawa suna fuskantar tuhuma mai tsanani da zargi mara tushe daga masu adawa da sakon da su ka zo da shi. Sai dai duk da haka suna ci gaba da yin tsayin daka akan tafarkinsu na isar da sako. 2- Wawayen mutane suna daukar ma'abota hankali a matsayin wadanda su ka fi wauta, sannan kuma suna karyata su.

Karshen shirinmu na wannan lokacin kenan sai mun sake haduwa acikin wani shirin na gaba.

Suratul A'araf, Aya Ta 67-71 (Kashi Na 240)

Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar A’raf, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa. A yau sharhin namu zai fara ne daga aya ta 67 zuwa 71.

To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 67:

قَالَ يَا قَوْمِ لَيْسَ بِي سَفَاهَةٌ وَلَكِنِّي رَسُولٌ مِّن رَّبِّ الْعَالَمِينَ{67}

"Sai ya ce: 'Yã ku mutãnena, ni bã wauta tare da ni, sai dai ni manzo ne daga Ubangijin talikai'"

A shirin da ya gabata mun ce jagorori masu fada a ji na mutanen Adawa basu amsa kiran Annabi Hudu ba kuma maimakon su bada hujjar da hankali nzai karba kan rashin amincewarsu da kiransa sai suka dora fada masa kalmomin wulakanci da zarginsa da wauta da rashin hankali. Wannan aya kuma tana bayyana amsar da Annabi Hudu ya fada musu, inda ya ce da su shi ba shi da wata wauta ko rashin hankali, ya kuma mayar musu da martani da karfi amma ba tare da furta kalmar wulakanci a garesu ba. A wannan aya muna koyon darusa kamar haka: 1-Annabawan Allah sun fuskanci farfaganda da kage da cutarwa daga mutanensu da basu yi imani ba amma basu taba barin aikin da Allah ya dora musu ba. 2-Mutum yana da hakkin ya karyata tuhumar karya da ake masa amma ba shi da hakkin ya tuhumaci wadanda suke zarginsa. 3-Yalwar zuciya da afuwa sharadi ne na samun nasara wajen nkiran mutane zuwa ga gaskiya.

Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 68:

أُبَلِّغُكُمْ رِسَالاتِ رَبِّي وَأَنَاْ لَكُمْ نَاصِحٌ أَمِينٌ{68}

"Inã isar muku da sãkwannin Ubangijina ne, kuma nĩ mai nasiha ne a gare ku amintacce."

A shirin da ya gabata mun yi magana kan kalmomi marasa kan gado da kuma wulakanci da Adawa suka yi wa Annabi Hudu, a wannan aya kuma tabna cewa Annabiu Hudu bai mayar musu da martani na cin mutunci ba, dadin dadawa ma ya yi musu Magana ne mai nuna cewa shi yana so musu alheri ne kuma shi amini wajen isar da sakonnin Allah a garesu kuma shi manzo ne kuma ba zai kara komai daga fadar Allah ba, kuma bay a bukatar komai daga mutanensa. Duk da cewa alummomin da aka aiko annabawa a cikinsu sun san cewa su mutane masu tsarki har ma kafin lokacin da Allah ya aiko su, amma a yayin da suka zo da sakon Allah wanda yake kiran jamaa ga karbar gaskiya wacce kuma take sabawa wasu abubuwan da suke so, mutanen nasu sais u ki amsa kiran annabawan har ma su maid a shi abin izgili da wulakanci da karyatawa. Darusa: 1-Annabawan sun yi dukkan kokarin da suke iyawa domin isar da sakon Allah da addininsa ga mutane. 2-kaunar jamaa da rikon amana sifofi ne masu muhimmanci wajen isar da sakon Allah kuma idan ba a kiyaye sub a mutane ba zasu amsa kiran kamar yanda ya kamata.

Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 69:

أَوَعَجِبْتُمْ أَن جَاءكُمْ ذِكْرٌ مِّن رَّبِّكُمْ عَلَى رَجُلٍ مِّنكُمْ لِيُنذِرَكُمْ وَاذكُرُواْ إِذْ جَعَلَكُمْ خُلَفَاء مِن بَعْدِ قَوْمِ نُوحٍ وَزَادَكُمْ فِي الْخَلْقِ بَسْطَةً فَاذْكُرُواْ آلاء اللّهِ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ{69}

"Ko kuwa kuna mãmãki ne don waazi ya zo muku daga Ubangijinku ta hanyar wani mutum daga gare ku dõn ya gargade ku? Kuma ku tunã lõkacin da Ya shugabantar da ku bãyan mutãnen Nũhu ya kuma kãra muku kira a halitta, sabõda haka ku tuna ni'imõmin Allah don ku rabauta."

Kamar yanda bayani ya zo cikin wasu ayoyin Alkurani, Adawa mutane masu girman jiki da karfi ta yanda, kamar yanda Alkurani ya fadi a lokacin da azaba ta sauko musu sai suka fadi kasa matatu kamar itatuwan dabino. Wannan aya tan ace musu ai Annabi Hudu daya daga cikinku ne ba bare ba ne, to me yasa zaku yi masa irin wannan taurin kai? Ai a cikinku yake kuma yana nema muku alheri ne saboda haka yake yi muku kashadi, kuma wahayin da ake yi masa tunatarwa ce da farkarwa a gareku, kuma Allah yana saukar masa da sako ne wanda zai nisanta ku daga gafala don kada ku mace da niimomin Allah. Ai alherin ku a duniya da lahira zai samu ne idan kun maida hankali kuma ku ka yi imani da Allah da ranar alkiyama. Ku yi imani da Allah day a halicce ku da irin wannan karfi da ku ked a shi, ya kuma mallakar muku da kasa bayan mutanen Annabi Nuhuwadanda suka halaka saboda sabon da suka yi kuma idan kuma kuka karyata wannan makoma ce take jiranku. Darusa: 1-Annabawa daga cikin mutane suke kuma saboda mutane suke isar da sakonninsu, kuma basu daukar kansu masu fifiko kan mutanensu. 2-Karfin jiki niima c eta Allah kuma dole ne a yi aiki das u ta hanya mai kyau idan kuwa ba zai zama dalilin hasara da halaka.

Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 70:

قَالُواْ أَجِئْتَنَا لِنَعْبُدَ اللّهَ وَحْدَهُ وَنَذَرَ مَا كَانَ يَعْبُدُ آبَاؤُنَا فَأْتِنَا بِمَا تَعِدُنَا إِن كُنتَ مِنَ الصَّادِقِينَ{70}

"Suka ce: 'Yanzu ka zo mana ne don mu bauta wa Allah Shi kadai, mu kuma bar abin da iyayenmu suka kasance sunã bauta wa? To ka zõ mana da abin da kake tsorata mu da shi din idan kã kasance daga mãsu gaskiya."

Wannan aya tana bayyana cewa tsananin rashin kan gado da taabbubanci da makauniyar jayayya da ke cikin zancen kafirai yana nuna cewa ba tare da suna da wata hujja ba, kuma kawai saboda iyayensu basu kasance suna bauta wa Allah madaukakin sarki ba, suna karyata samuware Allah, har ma suna izgili da alkawarin da annabawa suka bayyana musu na saukar musu da azaba. Darusa; 1-Makauniyar biyayya ga aladu da abubuwan da wata alumma ta yi imani da su ba tare da hujja ba, abu ne da bashio da kyau. Kaida wajen imani da biyayya ita ce hukuncin hankali ba aladu da alakokin dangantaka ko kabila da sauransu ba. 2-Makauniyar biyayya da riko da akidar dangi ko mutane da mutum yake cikinsu haka nan ba tare da hujja ba yana makantar da mutum yana kuma kai mutum ga taurin kai. 3-A wajen aikinsu na kawar da surkulle da karkacewar tunani, annabawa sun karya wasu aladu na alummominsu.

Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 71:

قَالَ قَدْ وَقَعَ عَلَيْكُم مِّن رَّبِّكُمْ رِجْسٌ وَغَضَبٌ أَتُجَادِلُونَنِي فِي أَسْمَاء سَمَّيْتُمُوهَا أَنتُمْ وَآبَآؤكُم مَّا نَزَّلَ اللّهُ بِهَا مِن سُلْطَانٍ فَانتَظِرُواْ إِنِّي مَعَكُم مِّنَ الْمُنتَظِرِينَ{71}

"Sai ya ce: 'Hakĩka azãba da fushi daga Ubangijinku sun fada a kanku, yanzu kwa rika jãyayya da ni a cikin wasu sunãye da ku ka kago kũ da iyayenku, Allah kuwa bai saukar da wata hujja ba game da su? To ku saurara ku gani, ni ma hakika ina daga masu sauraro tãre da ku."

Duk da hakuri da juriyar da Annabi Hudu ya nuna wajen kiran Adawa zuwa tafarkin Allah, kuma duk da kaunar day a nuna musu, basu yi imani ba kuma sai ma suka ce das hi idan dai akwai tashin alkiyama kuma azabar Allah gaskiya ne to ya saukar musu da wani yanki na azabar daga nan duniya. A wannan aya Annabui Hudu yana cewa azabar Allah zata sauo musu kuwa kamar yanda suka nema, azabar kuwa da ni da ku duk muke saukarta a kan ku, saboda bautan sassake-sassaken duwatsu da katakon da kuke kira alloli wacce ta hana ku yin imani da Allah mahalici, su ba komai bane face raye-rayen da kuke yi cikin zukatanku amma wadannan gumaka basu da wata hakika; basu mallaki komai ba daga sifofin girma da Ubangiji yake dasu, ba su da iko, basu da rahama ba su da hikima. Darusa: 1-Mu nisanci fadawa yaudarar kalmomi da sunayen da ake amfani dasu a wanannan zamani wadanda a zahirinsu akidu ne masu kyau amma holoko ne da basu da wata maana, a madadin wadannan su zam amasu neman gasikya da hakika. 2-Dole ne akidojin da mutum zai yi imani das u su zamanto akidu ne na hankali da hujja ban a gado ko makauniyar biyayya ba.

      • To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar A’raf. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu

Suratul A'araf, Aya Ta 72-76 (Kashi Na 241)

Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar A’raf, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa.

To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 72:

فَأَنجَيْنَاهُ وَالَّذِينَ مَعَهُ بِرَحْمَةٍ مِّنَّا وَقَطَعْنَا دَابِرَ الَّذِينَ كَذَّبُواْ بِآيَاتِنَا وَمَا كَانُواْ مُؤْمِنِينَ{72}

"Sai Muka tserar da shi da kuma wadanda suke tãre da shi da rahamarmu, Muka kuma Muka tumbuke tushen wadanda suka karyata ãyõyinMu kuma ba su kasance mũminai ba."

A shirin da ya gabata mun ce mutanen Adawa sun yi tauyrin kai matu\ka wajen yin watsi da kiran da Annabi Hudu (a.s.) ya yi musu har ma suka yi masa izgili da kuma kalubalen cewa idan gaskiya yake fadi ya kawo wani yanki na azabar lahira don su gani. Wannan aya tane cewa Allah ya kama mutanen na kafirai da azaba mai tsanani aanan duiniya inda ya aiko musu da guguwa mai tsanani na tsawon kwananki bakwai, wacce kuma a bayan wucewarta sai gasu matattatu a guggurafane a kasa kamar itatuwan dabino, amma Annabi Huda (a.s.) da wadanda suka yi imani das hi sun tsira daga wannan azaba na guguwa, Allah ya yiu musu rahama daga gare shi. Darusa: 1-Allah adali ne saboda haka baya murkushe masu aikata alheri tare da masu aikata mugun aiki. A lokacin saukar da azaba; yana tsirar da muminai na gaskiya. 2-Mu dauki darasi gada tarihi, kada mu sabawa Allah da jagororin da ya zaba don kada mu fada cikin azaba.

Sai mu saurari aya ta 73:

وَإِلَى ثَمُودَ أَخَاهُمْ صَالِحاً قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُواْ اللّهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَـهٍ غَيْرُهُ قَدْ جَاءتْكُم بَيِّنَةٌ مِّن رَّبِّكُمْ هَـذِهِ نَاقَةُ اللّهِ لَكُمْ آيَةً فَذَرُوهَا تَأْكُلْ فِي أَرْضِ اللّهِ وَلاَ تَمَسُّوهَا بِسُوَءٍ فَيَأْخُذَكُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ{73}

"Zuwa ga Samũdãwa kuwa (mun aiko) dan'uwansu Sãlihu. Ya ce: 'Yã ku mutãnena, ku bauta wa Allah, bã ku da wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi, hakĩka aya tã zo muku daga Ubangijinku; wannan tãgumar Allah aya ce a gare ku, sai ku bar ta ta ci a cikin kasar Allah, kuma kada ku taba ta da wani mugun abu sai azãba mai radadi ta sãme ku."

Bayan bayani kan labarin Adawa mutanen Annabi Hudu (a.s.), wannna aya kuma zata yio Magana kan Samudawa mutanen Annabiu Salihu wanda akla aike musu. Shi ma kamar sauran annabaw aya kitra mutanennsa zuwa bauta wa Allah makadaici. Mutanensa su ma sun bukani ya kawio musu mujiza. Allah sai ya fitar da taguwa daga cikin dutse, taguwar kuwa ta zo tana da ciki sai ta haifi ‘yar taguwa. Abin mamaki sai wannan taguwa ta zama ita ke bai wa mutane nono, ita suke tatsa kuma ya wadatar das u. Amnmnabi Salihu ya umurce su da kada su yi wani abin da zai cutar da taguwar domin hakan zai jawo azabar Allah. Darusa: 1-Alakar annabawa da alumominsu alaka ce ta yan uwantaka ba alakar uban gida da yaron gida ba. Suna kiran mutane ne zuwa ga Ubangiji. 2-Duk abin da aka ce na Allah ko da kuwa taguwa ce yana da tsarki da kuma alfarma, saboda haka wajibi ne mu mutunta abubuwan da addini y ace suna da tsarki da alfarma

Sai mu saurari aya ta 74:

وَاذْكُرُواْ إِذْ جَعَلَكُمْ خُلَفَاء مِن بَعْدِ عَادٍ وَبَوَّأَكُمْ فِي الأَرْضِ تَتَّخِذُونَ مِن سُهُولِهَا قُصُوراً وَتَنْحِتُونَ الْجِبَالَ بُيُوتاً فَاذْكُرُواْ آلاء اللّهِ وَلاَ تَعْثَوْا فِي الأَرْضِ مُفْسِدِينَ{74}

"Kuma ku tuna lõkacin da Ya shugabantar da ku a bãyan Ãdãwa Ya kuma zaunar da ku a bayan kasa kunã yin benaye a wurarenta masu taushi, kuma kunã sassaka gidaje a duwãtsu. Sabõda haka ku tuna ni'imõmin Allah, kada ku yi barna a bayan kasa."

Annabi Salihu ya tuntar da Samudawa cewa su dauki darasi daga abin da ya faru da Adawa wadanda suka gabace su wadanda kuma taurin kai da jayayya da gaskiya suka halaka kuma Samudawan suka zo a bayansu. Annabi salkihun ya hana su bin hanyar Adawa, kuma yah ore su da tuna niimomin Allah da kuma kiyaye aikata zalunci da fasadi. Ya ce musu su san cewa Allah ne ya basu karfin gina garuruwansu suna sassakar gidaje a cikin duwatsu suna gina wasu a sauran wurare. Darusa: 1-Tarihin magabata fitila ce mai haskaka wa na baya hanya don haka dole ne a kullum mu yi nazarin tarihi mu kuma tuna da shi. 2-Mutyyanen da suke rayuw acinin jin dadi suna morar abubuwan rayuwa da yawa sun fi bukatar tunawa da Allah don kada su fada ayyukan fasadi da barna.

Sai mu saurari aya ta 75 da ta 76:

قَالَ الْمَلأُ الَّذِينَ اسْتَكْبَرُواْ مِن قَوْمِهِ لِلَّذِينَ اسْتُضْعِفُواْ لِمَنْ آمَنَ مِنْهُمْ أَتَعْلَمُونَ أَنَّ صَالِحاً مُّرْسَلٌ مِّن رَّبِّهِ قَالُواْ إِنَّا بِمَا أُرْسِلَ بِهِ مُؤْمِنُونَ{75} قَالَ الَّذِينَ اسْتَكْبَرُواْ إِنَّا بِالَّذِيَ آمَنتُمْ بِهِ كَافِرُونَ{76}

"Sai manya (masu fada a ji) wadanda suka yi girman kai daga mutanensa suka ce ga wadanda suke raunana wadanda suka yi ĩmãni daga cikin su: 'Yanzu kun san cẽwa Sãlihu manzo ne daga Ubangijinsa?' Suka ce: 'Hakika mu dai mun ba da gaskiya da abin da aka aiko shi da shi.'" "Sai wadanda suka yi girman kai suka ce: 'Hakika mu kuma mun kafirce da abin da kuka yi imani da shi."

Duk da tunatarwa da waazin Annabi salihu manya na cikin alummar Samudawa wadanda suke ganin koyarwar addini ta saba da soyace soaycen zuciyarsu basu gaskata kiransa ba, har ma sun yi kokarin jefa shakku a imanin wadanda suka yi imani da shi, suka ce: ta yaya kuka san cewa Salihu manzon Allah ne kuma maganarsa ya ke fada muku? Sai dai wannan farfaganda bai yi wa muminai tasiri ba, kuma sai suka fada musu karara cewa su kam sun yi imani da sakon Abbani Salihu, kum ababu wata shakka ko tababa a kan haka, musamma ma da suka ga babbar mujizar da ya kawo musu. Amma wadanda suka kafirta masu giman kai wadanda ba a shirye suke su karbi gaskiya su yi kaskantar da kai gab gareta sai suka sanar da kafircinsu a fili, suka ce: Mu kam mun kafirce wa abin nan da kuka yi imani das hi. Darusa: 1-A tsawon tarihi akasari masu garajan cikin alumma da masu dukiya da iko sune suke musanta annabawa da hanyarsu. 2-Taluci da rashin galihu ba su ke da kima ba, ba kuma iko da dukiya ke da kima ba, abin da yake da muhimmanci dai shi ne imani da tsoron Allah, don haka ba dukkan talakawa da marasa galihu ne abin yabo ba, ba kuma dukkan masu arziki da iko ba. 3-Tushen kafirci shi ne girman kai da jiji da kai da neman girma.

To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar A’raf. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu

Suratul A'araf, Aya Ta 77-82 (Kashi Na 242)

Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar A’raf, da fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa. A yau sharhin namu zai fara ne daga aya ta 77 zuwa ta 82

To madalla. Da farko bari mu saurari aya 77 da ta 78:

فَعَقَرُواْ النَّاقَةَ وَعَتَوْاْ عَنْ أَمْرِ رَبِّهِمْ وَقَالُواْ يَا صَالِحُ ائْتِنَا بِمَا تَعِدُنَا إِن كُنتَ مِنَ الْمُرْسَلِينَ{77} فَأَخَذَتْهُمُ الرَّجْفَةُ فَأَصْبَحُواْ فِي دَارِهِمْ جَاثِمِينَ{78}

"Sai suka sõke tãgumar suka kuma yi tsaurin kai game da umurnin Ubangijinsu, kuma suka ce: 'Yã Sãlihu, ka zõ mana da abin da kake tsorata mu da shi idan kã kasance daga manzanni !" "Sai girgiza mai tsanani ta afko musu, sai suka wãyi gari a duddurkushe matattu a cikin gidansu"

A shirin ga ya gabata mun fadi cewa mujizar da Annabi Salihu (a.s.) ya kawo wa Samudawa taguwa ce da ta fito daga cikin dutse kuma ruwan da ta ke sha da kuma nonon da ake tatsa daga gareta, suna da yawan gaske. Umarnin da Allah yi musu shi ne kada su cutar da ita, amma manyan Samudawa masu fada a ji, da suke ganin cewa idan mutane suka yi imani da Annabi Salihu matsayin da suke da shi a cikin alumma zai zama shiga hadari, sai suka umarci wasu mutane don su je su kashe taguwar saboda su kawar da mujizar ma baki daya don kada Annabi Salihu ya sami wani abin da zai nuna wa mutane, sai kuma suka kashe taguwar. Masu jiji da kai sai suka ce da annabin Allah Salihu ya sauko musu da azabar da ya yi musu barazana da ita. Ko da yake mutane ba su da hannu wajen kashe taguwar, kuma wasu tsirari ne kadai su ka kasha ta, amma shirun da jamaa suka yi ana aikata wannan mugun aiki ya sa azaba ta sauka kan diukkan mutane ya kuma janyo halakarsu ba ki daya. Darusa: 1-Jiji da kai da girman kai suna kawo rashin biyayya da tawaye wa dokokin Allah. 2-Yin shiru da amince wa aikin sabo yana daidai da sa hannu wajen aikata shi kuma yana jawo azaba. 3-sau da yawa girgizan kasa da balaoin da suke faruwa, bias hakika ukuba ce kan sabon da mutane suke, don ya kamata a maid a hankali.

Sai mu saurari aya ta 79:

فَتَوَلَّى عَنْهُمْ وَقَالَ يَا قَوْمِ لَقَدْ أَبْلَغْتُكُمْ رِسَالَةَ رَبِّي وَنَصَحْتُ لَكُمْ وَلَكِن لاَّ تُحِبُّونَ النَّاصِحِينَ{79}

"Sai ya rabu da su ya ce: 'Ya ku mutãnena, hakika na isar muku da sakon Ubangijina, na kuma yi muku nasĩha, sai dai kuma ku ba ku son mãsu nasĩha".

Wannan magana ta Annabi salihu kafin saukar azaba tana iya kasancewa kafa wa mutanennsa hujja ko kuma ban kwana da su saboda azaba ta riga ta sauka, yana cewa: Ni na aikata aikin da aka dora mini kuma na yi muku dukkan nasiha da nuna muku dukkanin kauna, amma mummunan aikinku ya nuna cewa ba kwa karbar waazi kuma baku son sauraron maganar masu neman muku alheri. Darausa: 1-Hanyar kira da Annnabawa suka bi shi ne isar da sako tare da nuna kauna ga jamaa da son alheri a garesu, sabanin bayanan da hukumoimi suke fitarwa na ayyukan ofis da gudanarwa. 2-Mu zama masu karbar nasiha, mu dauki masu yin nasiha a cikin alumma a matsayin masoya domin yin watsi da maganar Annabawa da jagorori yana jawo azabar Allah.

Sai mu saurari aya ta 80 da 81:

وَلُوطاً إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ أَتَأْتُونَ الْفَاحِشَةَ مَا سَبَقَكُم بِهَا مِنْ أَحَدٍ مِّن الْعَالَمِينَ{80} إِنَّكُمْ لَتَأْتُونَ الرِّجَالَ شَهْوَةً مِّن دُونِ النِّسَاء بَلْ أَنتُمْ قَوْمٌ مُّسْرِفُونَ{81}

"Kuma lokacin da Ludu ya ce da mutãnensa: 'Yanzu kwa rika yin mummunan aiki wanda ba wani mahaluki da ya taba yin sa gabaninku?'" "Hakika ku kunã zaike wa maza don sha'awa maimakon mata. Ku dai mutãne ne mabarnata."

Bayan mun ji labarin Annabi Salihu da mutanen Samudawa, wannan aya kuma tana bayani ne kan labarin Annabi Ludu da mutanensa wadanda nitsewarsu cikin alfasha ta kai ga cewa maza suna neman maza da shaawa maimakon su auri mata. Wannan alfasha ta game mutanensu har sun dauke ta tamkar alada. Annabi Ludu ya rayu ne a zamanin Annabi Ibrahim, kuma Allah ya dora masa nauyin shiryar da mutanen nan fandararru wadanda suka dauki luwadi aiki ne mai kyau kuma saboda haka ne Alkurani ya ke cewa babu alummar da ta rigaye su a wannan mugun aiki wato luwadi. Sai dai a wannan zamani ma da aka sami ci gaba da wayewa, wannan mummunan aiki ya zama halastaccen abu wanda bai saba doka ba a wasu kasashen Yamma. Annabin Musulunci Muhammad dan Abdullahi (s.w.a.) yana cewa mutanen da suke yin luwadi Allah ya laance su kuma hukuncinsa kisa ne, da wanda ya yi da wanda aka yi masa. Darusa: 1-Luwadi da madigo wadanda bisa hakika fandare wa hanyar dabi’a ta biyan bukatar shaawa ne, wani naui ne na keta haddin maza da mata baki daya a cikin alumma kuma kauce wa madaidaiciyar hanya ne. 2-Babban hadari a nan shi ne yaduwar mugun aiki a cikin alumma zai sa ta zama jiki har ta zama karbabben abu, kuma idan haka ta faru balaoi daban daban zasu sauka kan alumma.

Sai mu saurari aya ta 82:

وَمَا كَانَ جَوَابَ قَوْمِهِ إِلاَّ أَن قَالُواْ أَخْرِجُوهُم مِّن قَرْيَتِكُمْ إِنَّهُمْ أُنَاسٌ يَتَطَهَّرُونَ{82}

"Ba kuwa abin da ya fito daga bakin mutãnensa sai kawai suka ce: 'Ku fitar da su daga garinku, hakika sũ, mutãne ne da su ke nuna su masu tsarki ne'"

Duk da cewa Annabi Ludu ya yui wa mutanensa magana ta hankali da kwarai da gaske amma su suna tunanin fitar da shi da mutanen da suka myi imani das hi daga garinsu. Maimakon su ba da amsa da ta dace kan kiran da ya yi musu na su bar aikata luwadi, sai suka ba shi amsa ta rasar kunya, suka ce: ‘Ku da kuke son tsarkaka ku fita daga garin mana, mu kam dai muna nan ba inda zamu je!’ Darusa:- 1- Ba bu hujjar hankali da za a bayar domin kare aikin sabo da fasadi saboda haka masu sabo basu da abin fada sai dai barazanar korar masu tsarki daga garinsu. 2-Idan mun kyale fasadi ya yadu cikin alumma za a kai matsayin da sai dai mu mu fice daga cikin alumma su kuma masu fasadi masu kazanta su mamaye dukkan alamuran kasa.

        • To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar A’raf. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.

Suratul A'araf, Aya Ta 83-86 (Kashi Na 243)

Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar A’raf, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa.

To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 83 da ta 84:

فَأَنجَيْنَاهُ وَأَهْلَهُ إِلاَّ امْرَأَتَهُ كَانَتْ مِنَ الْغَابِرِينَ{83} وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِم مَّطَراً فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُجْرِمِينَ{84}

"Sai Muka tserar da shi da kuma iyãlinsa, sai matarsa kawai ita ta kasance daga wadanda suka saura." "Kuma Muka yi ruwan azaba a kansu, saboda haka dũbi yadda karshen mãsu laifi ya zama"

A shirin da ya gabata mun bayyana cewa mutanen Annabi Ludu, maimakon su karbi kiransa da nisantar sabo, saisuka daura aniyar korarsa daga garin da shi da mabiyansa, kuma laifin da suka yi kawai shi ne su masu tsarki ne masu rayuwa cikin tsarki. Wannan aya kuma tana cewa: Da yake akasasrin mutane haka suke kuma hakan suke so, azabar Allah ta sauko kan wadannan mutane kuma Annabi Ludu da mabiyansa ne kadaui suka tsira. Abin mamaki a nan shi ne matar Annabi Ludu ita ma azaba ya shafe duk da cewa bata aikata abin da mazan suka yi ba amma saboda ta saba wa mijinta ta kuma goyi bayan ayyukan ashsha da mutane suka aikata. Azabar da aka yi wa myutanmen Ludu (a.s.) ta yi kama da wacce aka yi wa mutanen Abraha wanda ya kai wa dakin Kaaba yaki da giwaye. Dangane da mutanen Annabi Ludu, Allah madaukkin sarki ya cfadi a aya ta 82 ta surar Hudu, "Sai muka yi musu ruwan kananan duwatsu", dangane da maabota giwaye mutanenn Abraha kuwa Allah ya fadi a surar Fil, "Suna jifansu da wasu kananan duwatsu" Darusa: 1-A wajen bada lada ko azaba da Allah yake yi wa mutane, ba bu tasirin da alakokin dangantaka zasu yi, ga matar wani Annabi ta halaka cikin azaba amma mabiyansa sun sami tsira. 2-Mace tana da yanci kamar na miji kuma tana zabar akidar da take so, wannan shi ya sa matar Annabi Ludu ta zabi hanyar kafirai, ita kuma matar Firauna ta riki Annabi Musa ta rene shi. 3-Azabar Allah ba a lahira kadai take ba, a wanio lokaci a nan duniya ma azaba tana sauka.

Sai mu saurari aya ta 85:

وَإِلَى مَدْيَنَ أَخَاهُمْ شُعَيْباً قَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُواْ اللّهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَـهٍ غَيْرُهُ قَدْ جَاءتْكُم بَيِّنَةٌ مِّن رَّبِّكُمْ فَأَوْفُواْ الْكَيْلَ وَالْمِيزَانَ وَلاَ تَبْخَسُواْ النَّاسَ أَشْيَاءهُمْ وَلاَ تُفْسِدُواْ فِي الأَرْضِ بَعْدَ إِصْلاَحِهَا ذَلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ{85}

"Kuma (ka tuna) lokacin da muka aiko wa mutanen Madayana da dan'uwansu Shu'aibu. Ya ce: "Ya ku mutãnena, ku bauta wa Allah; bã ku da wani abin bauta da gaskiya sai Shi. Hakika hujja bayyananniya ta zo muku daga Ubangijinku, saboda haka ku cika mũdu da maauni kada ku toge wa mutãne kãyansu, kuma kada ku yi barna a cikin kasa, bãyan gyaruwarta. Wannan shi ya fi alhẽri a gare ku idan kun kasance mũminai."

Wannan aya kuma tana Magana ne kan kan labarin Annabi Shuaibu da mutanmensa, tana cewa, a garin Madyan wuri mai ne mai yawn ruwa da yanayin noma mai kyau a kasar Sham, Allah ya aiko da annabiun mai suna Shuaibu. Mutane Madyana suna tauye maauni wajen ciniki wanna shi ya sa wannan annabin Allah ya ke ta gargadin su kan su nisanci wannanmugun aiki ya na umurtansu das u kula da daidata mudu da sauran abubuwan da ake auna kayan haja a kasuwa. Annabi SHuaibu ya bayyana musu cewa tauye mudu da sikeli da sauran maaunai na ciniki wani naui ne fasadida barna a bayan kasa kuma bai dace da masu imani ba. Darusa: 1-Mutumin da ba shi da imani a kullum yana iya fadawa karkatacciyar hanya da barna, ko barna ta fuskar munanan dabi’un a wani lokaci kuma a harkar dukiya da tattalin arziki. 2-Addinan Ubangiji da annabawan Allah ba aikin ayyukan ibada kadai suke koyarwa ba, ayyukansu sun hada da bangaren zamantakewa da tatalin arziki kuma suna kokarin gyara ko wace irin karklata a wadannan fannoni ma. 3-Idan dai mutum yana da imani to lallai zai kiyaye hanyar neman arzikinsa tare da kulawa da adalci a harkokinsa.

Sai mu saurari aya ta 86:

وَلاَ تَقْعُدُواْ بِكُلِّ صِرَاطٍ تُوعِدُونَ وَتَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ اللّهِ مَنْ آمَنَ بِهِ وَتَبْغُونَهَا عِوَجاً وَاذْكُرُواْ إِذْ كُنتُمْ قَلِيلاً فَكَثَّرَكُمْ وَانظُرُواْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُفْسِدِينَ{86}

"Kuma kada ku zauna ga kõwace hanya kunã tsoratar da mutane, kunã kuma toshe hanyar Allah ga wadanda suka yi ĩmãni da shi, kuma kunã nufin ita hanyar ta zama karkatacciya. Ku tuna kuma lõkacin da kuka zamanto yan kadan sannan Ya yawaita ku, kuma ku dũbi yadda karshen mabarnata ya zama"

Mutanenm Annabi Shuaibu sun yi wa muminai barazana ta hanyoyi daban daban, suna cutar dasu. Shuaibu (a.s.) ya kasance yana shiryar da alummar Madyana cewa su kula da dabi’un kwarai wajen rayuwar zaman tare kuma kada su yi bi mugayen hanyoyin kamar makirci da karkata gaskiya da kisan kai da tare hanyoyi don dais u yi fada da imanin da mutane suka yi, kamata ya yi su ji tsoron Allah su tuna da niimominsa. Karkatar da muminai daga madaidaciyar hanyar Ubangiji yana cikin baudewar da mutanen Madyana suke yui a wancan lokacin, kumna Annabi Shuaibu hana hana su aikata wadannan ayyuka yana cewa: Ku tuna da niimomin Allah ku nisanci sabo ku tuna cewa kafin wannan lokaci kun kasance kuna cikin barazanar halaka, amma Allah ya ba ku wadata da yawa da karfi, saboda haka ku yi wa Allah godiya ku kuma bar saba masa. Ku dauki darasi daga karshen rayuwar mutane farko ya kasance, ku gane cewa masu barna a bayan kasa suna da mummunan karshe a rayuwarsu. Darusa: 1-Masu gaba da hanyar Allah a kmullum suna kokarin yiwa muminai kofar rago kuma suna yin amfani da kowace hanya don batar da muminai. 2-Daya daga cikin hanyoyin shiryar alumma da yin shimfada domin su karbi gaskiya shi ne tunatar da su niimomin Allah da kuma makomar wadanda suka gabacesu.

      • To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar A’raf. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu

Suratul A'araf, Aya Ta 87-89 (Kashi Na 244)

Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar A’raf, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa. A yau sharhin namu zai fara ne daga aya ta 87 zuwa ta 89 a Surar Aaraf

To madalla. Da farko bari mu saurari aya 87:

وَإِن كَانَ طَآئِفَةٌ مِّنكُمْ آمَنُواْ بِالَّذِي أُرْسِلْتُ بِهِ وَطَآئِفَةٌ لَّمْ يْؤْمِنُواْ فَاصْبِرُواْ حَتَّى يَحْكُمَ اللّهُ بَيْنَنَا وَهُوَ خَيْرُ الْحَاكِمِينَ{87}

"Kuma idan wata kungiya daga cikin ku ta kasance ta ba da gaskiya da abin da aka aiko ni da shi, wata kuma ba ta ba da gaskiya ba, to sai ku saurara har sai Allah Ya yi hukunci a tsakãninmu. Shi ne kuwa fiyayyen mãsu hukunci."

A shirin da ya gabata mun yi bayani kan wasu daga waazozi da shiryarwar da Annabi Shuaibu ya yi wa mutanensa, mun kuma ce mutanen Madyana wato garinda Allah ya aiki Annabi Shuaibu suna tauye mudu da sauran maauai na ciniki kuma cin dukiyoyin juna ta hanyoyin haramun ya zame musu alada kuma fasadi ko barna a harkar dukiya ta watsu a tsakaninsu. Saboda haka ne Annabi Shuaibu (a.s.) ya ya yi ta kiramnsu zuwa ga Allah da kuma kiyaye hakkokin jamaa amma wadanda suka kafirce daga cikin muatnesa sun ki bada gaskiya das hi kuma har ma sun yi ta kokarin karkjatar da wadan da suka yi imani tare da wulakanta su. Su kan ce: ‘Idan abin da kake fadi gaskiya ne ka kawo mana azabar Allah mana.’ Da wannan zance nasu, suna son sanya shakku cikin zukatan wadanda suka yi imani suka bi Annabi Shuaibu (a.s.) har ma a ka kai ga cewa muminan suna cewa: ‘Ya Shuaibu idan mu muna kan gaskiya to me ya sa Allah ba zai yi musu horo da azaba ba?’ Wannan aya tana bada amsa ga muminan da ma wadanda suka suka kafirtan, tana cewa: ‘Ai Allah baya gaggawar saukar da azaba. Yana ba dama ne wa masu sabo su tuba sun dawo hanya, ba wai da zaran an aikata laifi sai aAllah ya saukar da azaba ba. Darusa: 1-Rahamar Ubangiji tana hana gaggauta saukar azaba saboda haka bai kamata jinkirta azaba ya sa kafirai gururi ko ruduwa da cewa ba zata sauka ba, muminai kuma kada su yanke kauna. 2-Hukunci tsakanin mumionai da kafirai a hgannun Allah yake, saboda haka mu nisanci yanke hukunci kan wani mutum domin kuwa Allah da yake da cikakken sani kan tunani da ayyukan mutum shi ne kawai ya ked a hakkin yi masa hukunci.

Sai mu saurari aya ta 88:

قَالَ الْمَلأُ الَّذِينَ اسْتَكْبَرُواْ مِن قَوْمِهِ لَنُخْرِجَنَّكَ يَا شُعَيْبُ وَالَّذِينَ آمَنُواْ مَعَكَ مِن قَرْيَتِنَا أَوْ لَتَعُودُنَّ فِي مِلَّتِنَا قَالَ أَوَلَوْ كُنَّا كَارِهِينَ{88}

"Sai manya (masu fada a ji) wadanda suka yi girman kai daga mutãnensa suka ce: 'Lalle za mu fitar da kai yã Shu'aibu, kai da wadanda suka ba da gaskiya tãre da kai daga garinmu, ko kuwa lallai ku kõmo cikin addininmu.' Sai ya ce: 'Yanzu (za ku yi haka) kõ dã muna kin hakan?'"

Barazanar kora daya ne daga hanyoyin da Firaunoni da masu girmsan kai suek amfani da su wajen tinkarar annabawa da mabiyansu munima. Mun ji a labarin Annabi Ludu inda masu sabon luwadi suka ce da annabin da mabiyansa, 'Ku da kuke tsarkaak ne ku fita ku bar m,ana garin mu.' A labarin Annabi Shuaibu ba jagororin kafirci na garin Madyana sun kasa jimre wa maganar Shuaibu (a.s.) saboda haka suka daura aniyar korar sad a shi da wadanda suka yi imani daga garin, kuma a fili sai suka ce: 'Ko dai ku karbi addinin mu ko kuma mu kore ku gada wannan gari.' Annabi Shuaibu sai ya ce da su, 'Mu ba mu yarda addininku ba, ko kuna so ne ku tilasta mu ne sai mun bi?' Darusa: 1- A tsawon tarihi dan Adam, manya da jagororin alummomin sun kasance suna gaba da annabawa da koyarwarsu amma ba annabin da goyi bayan wani azzalumin shugaba ko sarki. 2-Tafarkin annabawa shi ne jan hankalin mutane da kuima waazi, tafarkinsu masu adawa da su kuma shi ne barazana da kuma karya. 3-Tilastawa mutane sai sun karbi wata akida hanya ce ta kafirai, amma su muminai ba su tilasta wa kowa ya karbi akidarsu.

Sai mu saurari aya ta 89:

قَدِ افْتَرَيْنَا عَلَى اللّهِ كَذِباً إِنْ عُدْنَا فِي مِلَّتِكُم بَعْدَ إِذْ نَجَّانَا اللّهُ مِنْهَا وَمَا يَكُونُ لَنَا أَن نَّعُودَ فِيهَا إِلاَّ أَن يَشَاءَ اللّهُ رَبُّنَا وَسِعَ رَبُّنَا كُلَّ شَيْءٍ عِلْماً عَلَى اللّهِ تَوَكَّلْنَا رَبَّنَا افْتَحْ بَيْنَنَا وَبَيْنَ قَوْمِنَا بِالْحَقِّ وَأَنتَ خَيْرُ الْفَاتِحِينَ{89}

"Hakika mun kago karya wa Allah idan muka kõma cikin addininku bãyan kuwa Allah ya tserar da mu daga gare shi. Kuma ba zai yi wu ba mu kõma cikinsa sai idan Al1ah Ubangijinmu ya so haka. Ubangijinmu kuwa saninsa ya yalwaci daukacin kõmai. Ga Allah ne kawai muka dõgara. Yã Ubangijinmu, Ka yi hukunci a tsakãninmu da mutãnenmu da adalci, domin kuma Kai ne fiyayyen mãsu hukunci."

Amsar da Annabi Shuaibu (a.s.) ya bayar kan maganganun barazana da wulakanci da kafiran mutanensa suke yi masa wacce, amsa ce ta saukin kai da mutuntawa amma kuma amsa mai karfi da kuma hikima a lokaci guda. Yana ce musu: 'Ku kuna so mu koma cikin addininku alhali kuma Allah madaukakin sarki ya yantar da mu daga surkulle da karkatattun aladu ya kuma shiryar da mu madaidaiciyar hanya. Ai idan muka yi haka ai mun karyata maganar Allah ke nan, ai mu ba mu da hakkin barin hanyar Ubangiji mu koma ta ku, sai idan shi ne ya ba mu umarnin aikata hakan, kuma shi Allah baya yi izini a bi hanyar bata. Annabi Shuaibu ya kara da cewa, 'ba yadda za a yi mu ce mun yi imani da Allah amma a aikace kuma mu daidaita da ku domin kuwa shi Allah ya na sane da komai babba ne ko karami kuma ba a boye masa komai. Saboda haka ne mu kam za mu dogara ga Allah kan barazanar da ku ke yi mana kuma muna nema ya yi shari'a tsakanin mu da ku kuma ya bamu mafita. Darusa: 1-Barin hanyar gaskiya da kiyaye koyarwar addini wani nau'i ne na karya alkawari da mutum ya dauka wa Allah, kuma ko da wasa mumini ba zai yi sassauci kan akidarsa ba. 2-Duk da matsin lamba daga masu adawa, wajibi ne mu yi aiki da nauyin da Allah ya dora mana kuma sai mu yi dogaro ga iko da sanin na Allah wadanda basu da iyaka.

      • To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar A’raf. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.

Suratul A'araf, Aya Ta 90-93 (Kashi Na 245)

Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar A’raf, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa. A yau sharhin namu zai fara ne daga aya ta 90 zuwa ta 93 a Surar Aaraf

To madalla. Da farko bari mu saurari aya 90 da ta 91:

وَقَالَ الْمَلأُ الَّذِينَ كَفَرُواْ مِن قَوْمِهِ لَئِنِ اتَّبَعْتُمْ شُعَيْباً إِنَّكُمْ إِذاً لَّخَاسِرُونَ{90} فَأَخَذَتْهُمُ الرَّجْفَةُ فَأَصْبَحُواْ فِي دَارِهِمْ جَاثِمِينَ{91}

"Sai kuma manya (masu fada a ji) wadanda suka kãfirta daga mutãnensa suka ce: 'Ba shakka idan ku ka bi Shu'aibu to a sannan kun zama tababbu.'" "Sai girgiza ta same su, saboda haka suka wãyi gari matattu duddurkushe a cikin gidansu."

A shirye shiryen da suka gabata mun ce mutanen garin Madyana sun bi manyansu suka yi taurin kai suka ki amsa kiran da Annabi Shuaibu ya yi musu na kadaita Allah da bauta masa shi kadai, dadin dadawa ma sai suka nemi fitar da shi da mabiyansa daga garin. Wadannan ayoyi kuma suna bayyana cewa: Manyan garin Madyana wadanda suka zabi hanyar kafirci har a kullum suna yi wa mutane gargadin cewa kada su kuskura su saurari maganar Annabi Shuaibu (a.s.) kuma sukam ce bin tafarkinsa zai jawo hasara. Ba shakka manufar wadannan mutane dai shi hasarar dukiya da abin duniuya saboda haka ne ma babban sakon Annabi Shuaaibu ga mutanennsa shi ne nisantar tauye mudu da sauran maaunai da kuma niosantar tauye wa mutanen kayayyakinsu. A mahanga irinta ta duniyanci tsantsa za a ga kamar tauye wa mutane dukiyoyinsu abu ne mai mriba amma a lokacin da annabin Allah ya tabbatar da hujja a kan haramcin wannan aiki ai babu sauran filin jayayya. Amma mutanen Annabi Shuaibu da suka ga annabin Allah suka kum akarta shi suka kuma yi taurin kai wa dokokin Allah, to suka kuma cutar da annabi da mabiyansa, azabar Allah ta sauko musu kuma basu sami hanyar tsere mata ba. Sun so su gudu su tsere amma sun fadi kan guiwowinsu kuma gidajen su sun rushe a kansu. Darusa: 1-Masu sabawa annabawa akasarinsu masu matsayi da dukiya ne wadanda kuma basu sanda da wahala ba a cikin alumma. 2-Azabar Allah ta fi sauka cikin dare, haka kuma a cikin dare ne ludufi da rahamar Allah na musamman suke sauka kan salihan bayinsa.

Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 92:

الَّذِينَ كَذَّبُواْ شُعَيْباً كَأَن لَّمْ يَغْنَوْاْ فِيهَا الَّذِينَ كَذَّبُواْ شُعَيْباً كَانُواْ هُمُ الْخَاسِرِينَ{92}

"Wadanda suka karyata Shu'aibu, sai ka ce ba su taba zama ba a cikinsu (gidajensu). Wadanda suka karyata Shu'aibu sun kasance sũ ne tababbu. "

Wannan aya ta bayyana cewa tsananin azabar da ta saukan kan mutanen Madyana ya kai ga cewa an bunne su cikin kangayensu ne ta yanda idan da mutum zai ga garin lokaci kankane bayan saukar azabar sai ya zaci cewa shekaru da yawa ba wanda ya zauna a wurin. Alkurani mai girma ya ci gaba da cewa: kafirai suna zaton cewa barin tauye mudu da maaunai na ciniki yana jawo hasara, amma bisa hakika kafircewa ayoyin Ubangiji da rashin biyayya ga dokokinsa ya na janyo babbar hasara, hasarar rayuka da dukiyoyi a nan duniya da kuma hasarar lahira da shiga wutar jahannama. Darusa: 1-Mu dauki darasi daga mummuman karshen da kafirai suka yi saboda haka mu kiyayi cin karo da gaskiya. 2-Mu yi tawakkali ga Allah mu kuma san cewa makircin mutane bata tamkar zane ne a ruwa, kafirai sun so su fitar da Annabi Shuaibu daga garinsu amma sune suka halaka a cikin gidajensu.

Yanzu kuma mu saurari aya ta 93:

فَتَوَلَّى عَنْهُمْ وَقَالَ يَا قَوْمِ لَقَدْ أَبْلَغْتُكُمْ رِسَالاَتِ رَبِّي وَنَصَحْتُ لَكُمْ فَكَيْفَ آسَى عَلَى قَوْمٍ كَافِرِينَ{93}

"Sai ya rabu da su ya kuma ce: "Yã ku mutãnena, ba shakka na isar muku da sãkonnin Ubangijina kuma nã yi muku nasĩha, to yaya zan ji takaici a kan mutãne kãfirai?"

A karshen labarin Annabi Shuaibu (a.s.) da mutanen Madyana wadanmda suka karkare da halaka.

      • To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar A’raf. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.

Suratul A'araf, Aya Ta 94-96 (Kashi Na 246)

Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar A’raf, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa.

To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 94 da ta 95:

وَمَا أَرْسَلْنَا فِي قَرْيَةٍ مِّن نَّبِيٍّ إِلاَّ أَخَذْنَا أَهْلَهَا بِالْبَأْسَاء وَالضَّرَّاء لَعَلَّهُمْ يَضَّرَّعُونَ{94} ثُمَّ بَدَّلْنَا مَكَانَ السَّيِّئَةِ الْحَسَنَةَ حَتَّى عَفَواْ وَّقَالُواْ قَدْ مَسَّ آبَاءنَا الضَّرَّاء وَالسَّرَّاء فَأَخَذْنَاهُم بَغْتَةً وَهُمْ لاَ يَشْعُرُونَ{95}

"Kuma ba Mu (taba) aiko wani Annabi a cikin wata alkarya ba (da mutanenta suka karyata shi) sai Mun kãma mutãnen nata da tsanance-tsanance da cũtuttuka don ko sa kaskantar da (kansu ga Allah)." "Sannan Muka canja jin dadi maimakon wahala, har dai su ka yadu, suka kuma ce: 'Hakika a da can cututtuka da kuma wadata sun sami iyayenmu.' Saboda haka Muka kãmã su ba zato ba tsammani alhali kuwa su ba sa jin haka zai faru."

Bayan bayani kan labarin Annabi Hudu da Annabi Salihu da kuma Annabi Shuaibu a shiryr shiryen baya filla filla, wadannan ayoyi kuma suna magana ne kan wata kaida ta rayuwa da halitta wanda ake irin wadannan kaidoji "Sunnar Allah". Alkurani yana cewa, tare da aiko da annabawa da Allah ya yi domin shiryar da mutane, Allah ya na kawo yanayin da zai taimaka wa mutane su karbi gaskiya ta hanyar kawar da abubuwan da suke sa mutane gafala. Allah yana kawo matsaloli kamar wahalhalu domin jamaa su tun ada mutuwa da ranar tashin alkiyama, domin wannna tunani da tsokaci su yi sa mutane su bar muguwar hanyar rayuwa da suka bi a baya su kuma yi biyayya ga hanyar gaskiya. A wani lokaci Allah yana jarraba mutane da cututtuka ko mutuwa, a wani lokaci kuma hasarar dukiya da fari da sauran wahalhalu domin zukatan mutane su sami saukin nisantar kaunar abin duniya da bauta mata. Amma lokacin da wannan jarrabawa mara dadi zata dauka ba shi da yawa, jin dadi da walwala zasu komo musu. Sai dai abin takaici yawa yawan mutane da zaran sun sami dukiya nan da nan sai su sake fada wa cikin gafala kuma sai su dora musabbabin faruwar abubuwa marasa dadi a kan dalilai na zahiri, kuma sai su fitar da batun Ubangiji a matsayin mai hannu a dora musu jarrabawa tun farko. A wannan yanayi ne kuma Allah yake saukar musu da azabarsa kuma sau da yawa basu ma fahimtar cewa azabar sakamako ne na wannan akida tasu da gafala da suka yi. Darusa: 1-Wahalhalu da matsaloli abubuwa ne da suke gina dan Adam da ci gabansa da kuma maida hankalinsa ga Ubangiji, kuma ba kowace wahala ce azaba ba, don wani tsananin rahama ne mai tunkude balaoin da zasu zo a gaba. 2-Ga mutanen masu karancin tunani, jin dadi yana jawo musu mancewa da niimomi da kuma yin dagawa, saboda haka da duk jin dadi ne rahama ba.

Yanzu kuma bari mu saurari aya ta 96:

وَلَوْ أَنَّ أَهْلَ الْقُرَى آمَنُواْ وَاتَّقَواْ لَفَتَحْنَا عَلَيْهِم بَرَكَاتٍ مِّنَ السَّمَاءِ وَالأَرْضِ وَلَـكِن كَذَّبُواْ فَأَخَذْنَاهُم بِمَا كَانُواْ يَكْسِبُونَ{96}

"Da dai mutãnen alkaryu sun yi ĩmãni sun kuma ji tsoron Allah, to ba shakka da Mun bũde musu albarkõki daga sama da kuma kasa, amma kuma sun karyata, saboda haka Muka kãma su domin abin da suka kasance sunã aikatawa."

A ayoyin da suka gabata mun ji baytani kan gafalar dan Adam da kuma matsalolin da suke tafo masa domin kawar da wannan gafala. Wannann aya kuma tana cewa, ba wai Allah yana son jefa vku cikin wahala da masifu ba ne; idan mutane suka kasance masu imani da tsaoron Allah kuma suka yi aiki da hukunce hukuncen addini a matsayin daidaiku da kuma alumma to lallai Allah madaukakin sarki zai bude musu kofofin niimarsa ta sama da ta kasa wa mutane. Amma ana iya tambaya cewa; me ya sa duk da samuwar wadannan niimomi wasu mutane suke karyata Allah kuma da hakan suke share fagen saukar azaba a kansu? A nan hala mai saurare ya ce me yasa kafirai a wannan zamani suke rayuwa cikin walwala amma Musulmi kuma suke shan wahala, alhali kuwa wannan aya tana cewa imani da tsoron Allah suna kawo saukar da niimomi? Amma idan mutum ya sa lura kadan zai ga cewa a halin da ake ciki a yanzu aksasarin kasashen Musulmi, a matakin kasa sunansu ne kai na Musulunci amma dokokin addini basu aiki a cikinsu. Na biyu kuma kasashen wadanda ba Musulmi ba, ko da yuake sun sami ci gaba a ilimin kimiya da masanaantu amma su na fama da matsaloli masu girman gaske ta fuskar aladu da zamantakewa, kuma mafi girm adaga wadannan matsaloli shi ne damuwa da rashin kwanciyar hankali wanda suka fi yawa a irin wadannan kasashe. A wasu ayoyin kuma Alkurani yana bayani kan wasu irin niimomi marasa albarka. Alal misali aya ta 44 a surar An'am tana cewa "da yake wadancan sun mance da ambaton Allah, Allah ya mantar da su kuma ya rufe dukkan kokofin alheri a kansu." Abin lura a nan shi ne ga muminai albarkoki suna sauka, ga me da klakfirai kuma ba lallai bane albarka ta sauka tae da niimomin da suka rayuwa cikinsu, ta yadda zasu tabbata a kuma kare su daga balaoii. Kasar yanda Allah yake sanya albarkar rayuwa kamar arziki da ilimi da makamantansu, haka ma yake sanya wasu albarkoki musamman domin muminai. Akwai hadisan da suka ce a karshen zamani a lokacin da Imam Mahdi (a.s.) zai bayyana albarkoki daga sama da kasa zasu sauko wa mutane, domin za a toshe dukkan hanyoyin zalunci su kuma kawo karshen su a zamaninsa, kuma za a tabbatar da adalci a dukkan doron kasa. Darusa: 1-Ka da a dauka kowace niima zata zama dalilin samun albarka da rahamar Allah ga muminai, amma ga kafirai kuma bata yin albarka kuma tana iya zama alamar azaba ma. 2-Imani da tsoron Allah da daidaikun mutane zasu yi ba zai wadatar ba wajen samun albarkoki da alumma, dole ne alumma ta tafiu bisa turbar imani da takawa a alummance. 3-Yin aiki domin kyautata imani da aladun kwarai a cikin alumma yana da riba hatta a fagen tattalin arziki domin zai habaka arziki kuma zai kare alumma daga barnar dukiya.

        • To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar A’raf. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu

Suratul A'araf, Aya Ta 97-102 (Kashi Na 247)

Bismillahir rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. A yau sharhin namu zai fara ne daga ta 97 zuwa ta 102 a Surar Aaraf

To madalla. Da farko bari mu saurari ayoyi uku; ta 97 da 98 da 99:

أَفَأَمِنَ أَهْلُ الْقُرَى أَن يَأْتِيَهُمْ بَأْسُنَا بَيَاتاً وَهُمْ نَآئِمُونَ{97} أَوَ أَمِنَ أَهْلُ الْقُرَى أَن يَأْتِيَهُمْ بَأْسُنَا ضُحًى وَهُمْ يَلْعَبُونَ{98} أَفَأَمِنُواْ مَكْرَ اللّهِ فَلاَ يَأْمَنُ مَكْرَ اللّهِ إِلاَّ الْقَوْمُ الْخَاسِرُونَ{99}

"Yanzu mutãnen alkaryu sun amince da azãbarmu ta zo musu cikin dare a hãlin sunã barci?" "Kõ kuwa mutãnen alkaryun sun amince da azãbarMu ta zo musu da hantsi a hãlin sunã wãsanni?" "Yanzu sun amince da azabar Allah? To bãbu mai amince wa da azabar Allah sai tababbun mutãne"

A shirin da ya gabata shirin namu ya yi bayani cewa a wasu lokuta Allah ya na horon da kafiraio da azzalumai tun a nan duniya yana kuma saukar musu da azabtarsa. Wanna aya kuma tana cewa bai kamata kowa ya aminta daga saukar azabar Allah ba, kuma kada duk wani mai aikata sabo ya sakankance saboda azabar Allah bata sallama, tana zuwa ne ba zata ko dare ko rana, ko cikin barci ko a farke. A wadannan ayoyi an ambaci azabar Allah da sunan makirci amma bisa hakika ai makirci ba ne domin kuwa maanar makr a asalin yaren larabci shi ne dabara da shiri domin hana makiyi kaiwa ga nasara a manufarsa, saboda haka a nan makircin ya yi nufin dabara domin hana kafirai kaiwa ga bukatunsu. A sarari yake dai cewa gafala da mancewa da Allah yana sa mutum ya sakankance da duniya ya aikata sabo, wanda kuma hakan yake sa azabar da Allah yake y iwa kafirai ta hada da Musulmin da ya aikata hakan, kuma wannan shi ne hasara mafi girma ga rayuwar mutum. Darusa: 1-A yayin sabo da rashin aikata wajiban da suka hau kanmu, kada mu taba dauka muna da kariya daaga azabar Allah irin wadda ta sami alummomin fda suka gabace mu, domin kuwa tana iya sauka a kowane zamani. 2-Bai kamata mutane su gafala ba saboda karfin soji da mallakar masanaantu da sauran abubuwan da suke da su, domin kuwa karfi da iko da dabara na Allah sun wuce na dukkanin halittu.

Yanzu kum asai aya ta 100:

أَوَلَمْ يَهْدِ لِلَّذِينَ يَرِثُونَ الأَرْضَ مِن بَعْدِ أَهْلِهَا أَن لَّوْ نَشَاء أَصَبْنَاهُم بِذُنُوبِهِمْ وَنَطْبَعُ عَلَى قُلُوبِهِمْ فَهُمْ لاَ يَسْمَعُونَ{100}

"Ko kuwa bai bayyana ba ga wadanda suke gãje kasa bãyan mutãnenta (na farko) cẽwa da Munã so dã sai Mu yi musu azaba saboda zunubansu, Mu kuma rufe zukãtansu saboda haka bã su ji?"

A wanna aya Allah madaukakin sarki ya yi kashedi wa mazauna doron kasa a yalin yanzu cewa, mene ne ya sa ba su daukar darasi daga makomar alummominda suka gabace su wadanda kuma basu yi kwakkyawan karshe ba, ko dai basu sa cewa Allah ya kamasu ne saboda sabon da suka aikata, kuma laifi da sabo sun mmaye zukatan wadancan mutane baki daya ta yadda har suka kas aganin gaskiya. Wasu hadisai suna cewa zuciyar dan Adam fara ta ke fat, amma duk lokacin da ya aikata sabo sai wani bakin digo ya bayyana a kanta. Idan ya tuba sai digon ya bace idan kuma ya ci gaba da sabo wannan digo zai yi ta fadi har ya mnamaye dukkan zuciya, kuma a wannan lokaci kam ba zai sake fahimtar gaskiya ba kuma ba zai kama hanyar sa'ada ba. Darusa: 1-A ko da yaushe mutum yana bukatar waazi da tunatarwa da ma kashedi domin kada gafala ta kama shi. 2-Zunubi ko sabo yana mummunan tasiri a zuciyar dan Adam kuma da kadan kadan yana sauya ta har ta kai ga matsayin da ba zata ga gaskiya ba balle ta karbeta.

Yanzu kuma sai aya ta 101:

تِلْكَ الْقُرَى نَقُصُّ عَلَيْكَ مِنْ أَنبَآئِهَا وَلَقَدْ جَاءتْهُمْ رُسُلُهُم بِالْبَيِّنَاتِ فَمَا كَانُواْ لِيُؤْمِنُواْ بِمَا كَذَّبُواْ مِن قَبْلُ كَذَلِكَ يَطْبَعُ اللّهُ عَلَىَ قُلُوبِ الْكَافِرِينَ{101}

"Wadancan alkaryun Munã ba ka lãbãrinsu ne, hakika kuma manzanninMu sun zo musu da hujjõji bayyanannu, to amma ba su kasance sunã ba da gaskiya da abin da suka karyata tun tuni ba. Kamar haka ne Allah Yake rufẽ zukãtan kãfirai."

Wannan aya tan magana da Annabin rahama Muhammadu (tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayensa) tana cewa, bayanan da Allah ya yi suna ishara ne ga annabawan da suka shude kuma sun kawo wa mutanensu hujjoji mabayyana tare da kiransu zuwa ga Ubangiji amma mafiya yawansu basu karbi gaskiya ba, basu yi iani da Allah ba, saboda sabo ya gama mamaye zukatansu har suka kasa fahimtar abin da annabawan suke fada musu. Darusa: 1-Bai kamata raayoyin jamaa su kashe guiwar masu kira zuwa ga adddinin ba domin a duk tsawon tarihi haka abin yake. 2-A kullum annabawa suna magana ne bisa hankali da hujja bayyananna amma wadanda suka kafirai ba su iya karbar kiran da suke yi domin sun riga sun rufe zukatansu.

Sai mu saurari aya ta 102:

وَمَا وَجَدْنَا لأَكْثَرِهِم مِّنْ عَهْدٍ وَإِن وَجَدْنَا أَكْثَرَهُمْ لَفَاسِقِينَ{102}

"Kuma ba Mu sãmi rike alkawari ba daga yawancinsu. Hakika kuma Mun sãmi yawancinsu fãsikai ne."

Dangane da tushen karyatawa da kafirai suke yi wa kiran annabawa da kuma sakonsu na gaskiya, wannan aya tana bayyana cewa kafirai basu kiyaye akasarin kaidojin dan Adamtaka da fidira da Allah ya sanya a cikin halittar mutum, abinda suka sa gaba kawai shi ne fasikanci da fajirci da sabo. Kuma a fili yake cewa masu irin wannan dabi'a ba zasu bada gaskiya da addinan Allah ba domin zasu hana su aikata sabo da sharholiya. Darusa: 1- Mu yi adalci wajen yanke hukaunci dangane dawasu ko da kuwa masu gaba ko adawa da mu ne. 2- Kiyaye kaidojin dan Adamtaka wajen kare hakkokin yan uwansa mutane kamar cika alkawari, suma suna kare mutum daga aikata wasu sabo.

      • To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na surar A’raf. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu

Suratul A'araf, Aya Ta 103-108 (Kashi Na 248)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake dasuwada cikin shirimmu na hannunka mai sanda shiri wanda yake dubi cikin wasu a yoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwarmu. Da fatan masu saurare zasu kasance tare da mu.

      • .

To bara mu fara shirimmmu na yau tare da sauraron karatun aya ta 103 na surar Araaf kamar haka.

ثُمَّ بَعَثْنَا مِن بَعْدِهِم مُّوسَى بِآيَاتِنَا إِلَى فِرْعَوْنَ وَمَلَئِهِ فَظَلَمُواْ بِهَا فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُفْسِدِينَ{103}

103- Sa'an nan kuma Mun aika Musa, daga bãyansu, da ãyõyinMu zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka yi zãlunci game da su. To, dũbi yadda ãkibar mabarnata take.

Tun farkon wannan sura, zuwa wannan ayar an ambaci labaran annabawa da dama wadanda suka hada da Hudu, Salihu, Ludu da shu'aibu (a). Wannan ayar tana ba da labarin annabi Musa (a) ne, wanda Allah ta'ala ya aiko shi da farko zuwa wajen fir'auna da jama'arsa don ya shiryatar da su, ya kirasu zuwa gaskiya. Sannan daga baya ya aike shi zuwa ga shuwagabannin mutanensa Bani Isra'ila. Duk da cewa annabi musa (a) ya zo masu da mu'jizoji daban daban don tabbatar da gaskiyarsa na cewa Allah ne ya aiko shi. Amma Fir'auna da mutanensa, ba wai kawai sun karyata shi ba, sai dai sun tunkare shi da wawta da shi da ayoyin da ya zo masu da shi. Labaran dauke da sunan annabi musa (a) sun zo a cikin alkur'ani mai girma har sau 136, sannan ayoyin alkur'ani sun yi bayani daga haihuwarsa, yarantarsa, gudunsa daga Masar zuwa Madyana, sannan sun yi maganar bashi manzanci, da kuma aiken sa zuwa ga Fir'auna da fafatawarsa da ya yi da fir'auna zuwa tseratar da shi da mutanensa daga hannun fir'auna da halakar shi fir'auna. Har'ila yau ayoyin alkur'ani sun kawo dangane da rayuwarsa cikin mutanensa bani Isra'ila. Dukkan wadannan labarai sun zo a cikin ayoyin alkur'ani da dama a cikin surori daban daban. Daga cikin wannan ayar muna iya dauna darussa kamar haka. 1. Fafatawa da azzaluman shuwagabanni shi ne aikin annabawa na farko. Don kawo kyara dole ne ya zama daga tushe. 2. Kada mu yi mamakin ikon da shuwagabanni azzalumai suke nunawa a lokacinda suke da iko, don da sauri ikon zai wuce, karshe mutum shi ke da muhimmanci.

Yanzun kuma bari mu saurari aya ta 104 zuwa 105 cikin surar ta Araaf kamar haka.

وَقَالَ مُوسَى يَا فِرْعَوْنُ إِنِّي رَسُولٌ مِّن رَّبِّ الْعَالَمِينَ{104} حَقِيقٌ عَلَى أَن لاَّ أَقُولَ عَلَى اللّهِ إِلاَّ الْحَقَّ قَدْ جِئْتُكُم بِبَيِّنَةٍ مِّن رَّبِّكُمْ فَأَرْسِلْ مَعِيَ بَنِي إِسْرَائِيلَ{105}

7:104 -Kuma Musa ya ce: "Ya Fir'auna! Lalle ne nĩ, manzo ne daga Ubangijin halittu."

7:105- "Tabbatacce ne a kan kada in fadi kõme ga Allah fãce gaskiya. Lalle ne, nã zo muku da hujja bayyananniya daga Ubangijinku; Sai ka 'yentar da Banĩ Isrã'ila tãreda ni."

Fir'auna yana daga cikin sarakunan da suke riya cewa su iyayengigi ne, abin bauta. Banda haka ma yana cewa shi ne Ubangiji babba. Shi yasa a lokacinda annabi musa (a) ya zo ya fada masa cewa ni na z o ne daga bangaren ubangijin talikai gaba daya mahaliccin sammai da kassai shi ne ya aiko ni da sako zuwa gareku. Ya aiko ni tare da wadannan mujizoji don tabbatar da gaskkiya ta. Don haka ina kiranka, ya kai Fir'auna ka bar zalunci ka kyale mutane na Bani'isra'ila su zo tare da ni. Daga cikin wannan ayar muna iya fahintar abubuwa kamar haka. 1. Annabawa basa da kome in banda magana ta gaskiya, sannan basa jin tsoron kowa kan wannan tafarkin. 2. Annabawa sune ke jagorantar kubutar da mutane daga zaluncin tagutai.

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 106 da kuma ta 107 daga cikin surar araaf kamar haka.

قَالَ إِن كُنتَ جِئْتَ بِآيَةٍ فَأْتِ بِهَا إِن كُنتَ مِنَ الصَّادِقِينَ{106} فَأَلْقَى عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ ثُعْبَانٌ مُّبِينٌ{107}

7:106 -Ya ce: "Idan kã kasance kã zo da wata ãyã, to, ka kãwõ ta, idan kã kasance daga mãsu gaskiya."

7:107 -Sai ya jẽfa sandarsa, sai gã ta kumurci bayyananne!

Da farko mutanen Fir'auna sun bukaci a jarrabi annabi musa (a) don tabbatar da gaskiyarsa, ta hanyar bukatar ya kawo wata mujiza wacce zata tabbatar da gaskiyansa. Sannan idan ya kawo wata mujiza sai, su tuhume shi da sihiri.

Don haka ne suka fadawa annabi Musa (a) cewa idan gaskiya kake fada ka kawo dalili wanda zai tabbatar mana cewa Ubangaji ne ya aiko ka. Anan ne Allah ya umrci annabi Musa (a) ya jefa sandarsa, sai gata ta zama jibgegen mumurci. A sannan ne suka kira masu sihirinsu wadanda Macijin annabi musa (a) ya hadiyasu ya sake komawa ya zama sandarsa kamar yadda yake.

Bayan haka ma da wannan sandar ne annabi musa (a), a lokacinda Fir'auna ya bi su ya daki rowan kogin Nilu da ita ruwa ya dare da ikon Allah ya yi masu hanya ya sandare suka tsallaka kogi, hakama a lokacin da suka fuskanci karancin ruwa ya daki dutse da ita, idanun ruwa guda 12 suka bayyan. Muna iya daukan darussa daga cikin wannan ayar kamar haka. 1. Mujiza hujja ce ta tabbatar da gaskiyar annabawa, kuma dole ne ko wane annabi ya kasance yana da mujiza. Duk da cewa sun san mutane irin su Fir'auna ba za su karbi gaskiya ba. 2. Ko wani annabi yana da mujiza da ta dace da zamaninsa, da ta da ce da abinda mutanen lokacinsa suka fi girmamawa da amicewa da shi.

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 108 daga cikin surar Araaf kamar haka.

وَنَزَعَ يَدَهُ فَإِذَا هِيَ بَيْضَاء لِلنَّاظِرِينَ{108}

7:108 -Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu dũbi!

Wata mujiza ta annan musa(a) ita ce, kamar yadda wannan ayar ta bayyana, ya fisge hannunsa, ko kuma yakan sanya hannunsa a cikin rigarsa sai ta fito tana haske kamar rana tana haskaka ko ina a wurin. Sannan idan ya maida ita sai ta koma kamar yadda take ba tare da wata cutarwa ba.

Wannan mujiza ta haske dai tana nuna rahama da alkhairi ne, mai makon tsoro wanda ke shiga zukatan mutane idan sun ga macizai ko makamatansu. Muna iya daukan darussa daga cikin wannan ayar kamar haka. 1. Annabawa masu isar da sakon Allah ne, kuma banda fadar gaskiya da suke yi, suna da mujizoji wadanda, suke nuna ikon Allah da kuma buwayarsa, wasu kuma suna nuna rahama da jinkansa. Masu sauraro da wannan kuma muka kawo karshen shirimmu na yau sai kuma wani shirin idan Allah ya kaimu a huta lafiya wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul A'araf, Aya Ta 109-116 (Kashi Na 249)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake dasuwada cikin shirimmu na hannunka mai sanda shiri wanda yake dubi cikin wasu a yoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwarmu. Da fatan masu saurare zasu kasance tare da mu.

      • .

To bara mu fara shirimmmu nay au tare da sauraron karatun aya ta 109 da kuma aya ta 110 daga surar Araaf kamar haka.

قَالَ الْمَلأُ مِن قَوْمِ فِرْعَوْنَ إِنَّ هَـذَا لَسَاحِرٌ عَلِيمٌ{109} يُرِيدُ أَن يُخْرِجَكُم مِّنْ أَرْضِكُمْ فَمَاذَا تَأْمُرُونَ{110}

109 - Mashãwarta daga mutãnen Fir'auna suka ce: "Lalle ne, wannan,kwarerren, matsafi ne mai ilmi."

110 -" Yanã son ya fitar da ku daga kasarku: To, mẽne ne kuke shawartawa?"

A cikin shirin da ya gabata mun ji yadda Allah ta'ala ya aike annabi musa (a) zuwa ga Fir'auni, inda ya bukace shi da ya daina bautar da Bani Isra'ila. Sannan ya nuna masu mujizoji wadanda suke tabbatar da gaskiyan zancensa. Amma fadawan fir'auna sun tuhumi annabi musa(a) da cewa shi korerren mai sihiri ne, kuma yana nufin ya kwace iko da sarautar kasar masar don ya zama mai iko da bani Isra'ila. Duk da cewa sun san sihiri, dabarbaru ne wadanda ba hakika ba. Amma mutanen lokacin sun san wanda ya kore a cikin aikin mai ilmi ne. Daga cikin wannan ayar muna iya daukan darussa kamar haka. 1. Wadanda suke sabawa annabawa ako yau ce sukan karyatasu. Su karyata abinda suka ji ko suka gani daga wajen annabawan nasu. 2. Sarakuna wadanda suke son ci gaba da iko kan mutane, a ko yau ce sukan tuhumi masu gaskiya don neman ci gaba iko a kansu.

Yanzun kuma musaurari karatun aya ta 111 da kuma ta 112 daga cikin surar Araaf kamar haka.

قَالُواْ أَرْجِهْ وَأَخَاهُ وَأَرْسِلْ فِي الْمَدَآئِنِ حَاشِرِينَ{111} يَأْتُوكَ بِكُلِّ سَاحِرٍ عَلِيمٍ{112}

111- Suka ce: "Ka jinkirtar da shĩ, shĩ da dan'uwansa, kuma ka aika da mãsu gayyar mutãne a cikin garũruwa. 112 - "Su zõ maka da dukkan matsafi, mai ilmi."

Fadawan fir'auna sun shawarta a tsakaninsu, suka tsaida shawara kan cewa, a halin yanzu kada a nemi ran annabi musa(a). Sai dai akwai bukatar a nemi taimakon masu sihiri wadanda za su zo su kunyata shi da sihirin da ya fi nasa. Don haka fir'auna ya bada umurnin a kira duk wani mai sihiri korerre kuma a kira mutane su zo su ganewa idanunsu yadda za'a kunyata annabi musa (a). Muna iya daukan darussa daga cikin wannan ayar kamar haka. 1. Dawagitai a ko yauce sukan gudanar da tarurruka don ganin yadda zasu bullowa gaskiya su rusa shi. 2. Sau da dama ana amfani da wasu nau'in ilmi don fada da gaskiya.

Yanzun kuma mu saurari karatun ayoyi na 113 da kuma 114 daga cikin surar Araaf kamar haka.

وَجَاء السَّحَرَةُ فِرْعَوْنَ قَالْواْ إِنَّ لَنَا لأَجْراً إِن كُنَّا نَحْنُ الْغَالِبِينَ{113} قَالَ نَعَمْ وَإَنَّكُمْ لَمِنَ الْمُقَرَّبِينَ{114}

113 - Kuma matsafa suka jẽ wa fir'aunã suka ce: "Lalle ne, shin, Munã da lada, idan mun kasance mũ ne masu rinjaye?" 114 - Ya ce: "Na, am kuma lalle ne kunã a cikin makusanta."

Bayan an kira dukkan manya manyan masu sihiri a duk fadin kasar Masar suka iso fadar fir'auna kuma aka bayyana na masu aikin da ake son su yi, sai suka ga girman aikin, suka bukaci lada mai yawa a wajen Fir'auna, wanda ya yi masu alkawarin lada mai yawa, sannan banda wannan zasu kasance masu daraja a cikin fadarsa. Amma fa duk wannan da sharadin su sami galaba a kan annabi musa. Muna iya daukan darussa a cikin wadannan ayoyi kamar haka. 1. Masu sihiri ma suna neman lada akan ayyukan sihiri da suke yi, amma su annabawa basa neman ladan kome a wajen mutane. Ayyukansu gaba daya don Allah ne. 2. Dagutai sukan kashe kudade da dukiyoyi masu yawa don kaiwa ga manufofinsu, sannan sukan yi alkawula ga masanan da suke masu aiki don kaiwa ga wannan manufar. Har'ila suna barzana ga wadanda suka kaucewa umurninsu.

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 115 da kuma ta 115 daga cikin surar Araaf kamar haka.

قَالُواْ يَا مُوسَى إِمَّا أَن تُلْقِيَ وَإِمَّا أَن نَّكُونَ نَحْنُ الْمُلْقِينَ{115} قَالَ أَلْقُوْاْ فَلَمَّا أَلْقَوْاْ سَحَرُواْ أَعْيُنَ النَّاسِ وَاسْتَرْهَبُوهُمْ وَجَاءوا بِسِحْرٍ عَظِيمٍ{116}

115 - Suka ce: "Ya Mũsã! Kõ dai ka jẽfa, kõ kuwa mumu kasance, mũ ne, mãsu jẽfãwa?" 116 - Ya ce: "Ku jẽfa." To a 1õkacin da suka jẽfa, suka sihirce, idãnun mutãne kuma suka tsõratar da su; Kuma suka jẽ da tsafi mai girma."

Bayan da masu sihiri suka kammala shirinsu, su kuma an kira mutanen gari su zo su ganewa idanunsu abinda zai faru. Sai masu sihirin suka tambayi annabi musa da cewa, mu a shirye muke ko ka fara ko mu fara, duk daya ne a wajemmu don mun tabbatar mune masu rinjaya. Amma sai annabi Musa (a) y ace masu tare da umurnin Ubangiji "ku fara. Daga nan suka fara jefa sihirce sihircensu wadanda suka bawa mutane mamaki kuma suka tsoratar da su. Sun rufe idanun mutane da shiri mai girma. Daga cikin wadannan ayoyin muna iya daukan darussa kamar haka. 1. Gabban dan adam suna iya yin kurakurai da dama. Kamar yadda idanun mutanen firaune suke kallon abubuwan da masu sihiri suke jefawa a matsayin macizai alhali kuma rufa ido ne. Ba gaskiya ba ne. 2. Alamarin sihiri yana tasiri a jikin dan,adam, don haka ne ma addinin musulunci ya haramta shi da kuma makamantansa. Don abinda yake yi na bayyana gaskiya kari kariya kuma gaskiya ga wasu wadanda ya sami iko a kansu. To masu saurao anan zamu dasa aya sai kuma wani shirin idan Allah ya kaimu wassalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu.

Suratul A'araf, Aya Ta 117-123 (Kashi Na 250)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake dasuwada cikin shirimmu na hannunka mai sanda shiri wanda yake dubi cikin wasu a yoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwarmu. Da fatan masu saurare zasu kasance tare da mu.

      • .

To bara mu fara shirimmmu nay au tare da sauraron karatun aya ta 117 da kuma aya ta 118 daga surar Araaf kamar haka.

وَأَوْحَيْنَا إِلَى مُوسَى أَنْ أَلْقِ عَصَاكَ فَإِذَا هِيَ تَلْقَفُ مَا يَأْفِكُونَ{117} فَوَقَعَ الْحَقُّ وَبَطَلَ مَا كَانُواْ يَعْمَلُونَ{118}

117 - Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa: "Ka jẽfa sandarka." Sai gã ta tanã lãkumar abin da suke karya da shi! 118 - Gaskiya ta auku, kuma abin da suke aikatãwa ya bãci.

A cikin shirin da ya gabata mun ji yadda fir'auna ya kira mutanen gari, sannan ya yi alkawarin lada mai girma ga masu sihiri idan sun sami nasara a kan annabi Musa (a). Sannan masu sihiri ne suka fara jefa abubuwansu wadanda suka tsotarar da mutane, don sun zama macizai manya da kanana. A wadannan ayoyi guda biyu, Allah ya yi wahayi ga annabi musa (a) ya jefa sandarsa wacce ta zama mesa na gaskiya kuma ya hadiya dukkan abinda abinda masu sihiri suka jefa na kariya sannan ya sake komawa sandarsa kamar yadda yake. Da haka kuma gaskiya ta tabbata ta bayyana ayyukan masu sihiri suka lalace. A cikin wadannan ayoyi muna iya daukan darussa kamar haka. 1. Gaskiya guda ce idan ta zo takan lalata kariya dubu a lokaci guda. 2. Sannan ko ba dade ko bajima gaskiya ce zata rinjaya kariya kuma ta lalace a ko wani zamani.

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 119 da kuma ta 120 daga cikin surar araaf kamar haka.

فَغُلِبُواْ هُنَالِكَ وَانقَلَبُواْ صَاغِرِينَ{119} وَأُلْقِيَ السَّحَرَةُ سَاجِدِينَ{120}

119 - Sai aka rinjãye su a can, kuma suka jũya sunã kaskantattu. 120 -Kuma matsafa suka fadi, sunã mãsu sujada.

Bayan nasarar da annabi musa (a) ya samu kan masu sihiri, lamarin Fir'auna ya lalace, don dama ya dogara da masu sihiri ne wajen kalubalantar annabi Musa (a), don ya shi raba shi da mutanen. Sai ga shi masu sihirin da ya dogara da su, su ma sun yi imani da shi har ma suka mika kai suna sujada ga ubangijin musa don nasarar da ya samu a kansu. Daga cikin wadannan ayoyi biyu muna iya fahintar cewa, 1. Mutane masu taushin zuciya, da zaran sun ga gaskiya suna karbanta ba tare da bata lokaci ba. 2. Yin sujada shi ne mika kai mafi girma da mutum zai yiwa Allah.

Yanzun kuma mu saurari karatun ayoyi na 121, 122 da kuma na 123 daga cikin sura Araaf kamar haka.

قَالُواْ آمَنَّا بِرِبِّ الْعَالَمِينَ{121} رَبِّ مُوسَى وَهَارُونَ{122} قَالَ فِرْعَوْنُ آمَنتُم بِهِ قَبْلَ أَن آذَنَ لَكُمْ إِنَّ هَـذَا لَمَكْرٌ مَّكَرْتُمُوهُ فِي الْمَدِينَةِ لِتُخْرِجُواْ مِنْهَا أَهْلَهَا فَسَوْفَ تَعْلَمُونَ{123}

121- Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halittu." 122 - "Ubangijin Mũsã da Harũna." 123 - Fir'auna ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni da shi a gabãnin inyi izni a gare ku?

Ayayin da muka karanta kafin wadannan sun bayyana yadda masu sihiri suka fadi suna sujjada don nuna mika kai ga annabi musa. Sun tabbatar cewa shi ba mai sihiri irinsu bane, mujizan day a bayyana gaskiya ce. Don haka bayan tashinsu daga sujada sai suka bayyana imaninsu da ubangijin annabi musa, wanda shi ne ubangijin sammai da kassai. Wannan lamarin ya kara rikita fir'auni don bai tsamman haka zai faru ba. Anan ne sai ya ce masu, ta yaya za ku yi imani da shi kafin ku sami izini na, a matsayi na na ubangijinku ? daga nan sai ya tuhume masu sihirin da cewa dama sun hada kai da annabi musa (a) tun farko don su kwace mulkinsa su fitar da shi daga kasarsa. Don haka yanzun mai makon ya basu ja'iza zai azabtar da su ne, don ya zama darasi ga sauran mutane. Muna iya daukan darussa daga cikin wadan nan ayoyi kamar haka. 1. Mutum mai cikekken 'yenci da kansa, wani ba zai iya talista masa ikidar da bai amince da ita ba. Don haka masu sihirin wadanda suka kasance karkashin ikon fir'auna tun da dadewa basu yi wata wata ba wajen bayyana imaninsu ga annabi musa ba. Hakama matar fir'aun tayi, bayan ta ga ayoyin Allah. 2. Dawagitai basa amincewa mutane su zabi addinin da suke so ba, suna daukansu a matsyin mallakarsu ne sai abinda suke so zasu yi. 3. Tuhuma da kariya ga masu neman gaskiya shi ne hanyar da dagutai suke bi don fada da masu gaskiya. Don basu da bakin Magana a gaban gaskiya. 4. Azabtarwa da kisa da tsoratarwa su ne hanyoyin da azzaluman shuwagabanni suke bi a ko yaushe don tilastawa mutane bin su. Masu sauraro da wannan kuma muka kawo karshen shirimmu nay au sai kuma shiri na gaba idan Allah ya kai mu wassalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu.

Suratul A'araf, Aya Ta 124-127 (Kashi Na 251)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake dasuwada cikin shirimmu na hannunka mai sanda shiri wanda yake dubi cikin wasu a yoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwarmu. Da fatan masu saurare zasu kasance tare da mu.

      • .

To bara mu fara shirimmmu nay au tare da sauraron karatun aya ta 124 da kuma aya ta 125 daga surar Araaf kamar haka.

لأُقَطِّعَنَّ أَيْدِيَكُمْ وَأَرْجُلَكُم مِّنْ خِلاَفٍ ثُمَّ لأُصَلِّبَنَّكُمْ أَجْمَعِينَ{124} قَالُواْ إِنَّا إِلَى رَبِّنَا مُنقَلِبُونَ{125}

124 - "Lalle ne, inã yayyanke hannãyenku da kafãfunku daga sãbãni, sa'an nan kuma, hakĩka, inã tsĩre, ku gabã daya." 125 - Suka ce: "Lalle ne mu, zuwa ga Ubangijinmu, mãsu jũyãwa ne."

A cikin shirimmu da ya gabata kun ji yadda ma'abota sihiru suka gane gaskiya kuma suka yi sujada suna bayyana imaninsu da ubangijin annabi Musa (a) suna bayyana imaninsu da manzancinsa. Amma Fir'auna wanda dama ba zai iya hakuri da irin wannan yanayi ba, sai ya tuhumesu da hada kai da annabi Musa (a) don kwace masa ikon kasar masar. Wannan ayar tana cewa kari kan tuhuman da yake masu, ya sha alwashin azabtar da su azabu mafi tsanani, zai yanke hannaye da kafafuwansu amma daya ta dama daya da hagu. Wannan yin haka a wajensa zai zama darasi ga sauran mutane wadanda suke tunanin zasu yi imani da Ubangijin Musa (a). Amma masu sihiri ba su tsorata da barazanarsa ba, sun fahinci gaskiya sun karbeta, kuma ko da ya kashesu shahada suka yi zasu koma ga Allah wanda ya haliccesu, kuma ubangijin sammai da kaissai. Muna iya daukan darussa a cikin wadan nan ayoyi kamar haka. 1. Tunanin sarakuna da shuwagabanni azzalumai shi ne, kashewa ko azzabtar da wanda ya saba masu. Amma su muminai abin alfahari ne a garesu su zama shaheedai. 2. Mutum mumini, idan ya yi hakuri ya daure ya na iya nasara kan azzaluman shuwagabanni ko menene karfinsu. 3. Kada mu rudu da imanimmu, kada kuma mu debe kauna daga musuluntar kafirai. Tunda ga shi masu sihiri a lokaci guda sun juya sun zama muminai.

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 126 daga cikin surar Araaf kamar haka.

وَمَا تَنقِمُ مِنَّا إِلاَّ أَنْ آمَنَّا بِآيَاتِ رَبِّنَا لَمَّا جَاءتْنَا رَبَّنَا أَفْرِغْ عَلَيْنَا صَبْراً وَتَوَفَّنَا مُسْلِمِينَ{126}

126 - "Kuma bã ka zargin kõme daga gare mu fãce dõmin mun yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinmu a lõkacin da suka zõ mana! Ya Ubangijinmu! Ka zuba hakuri a kanmu, kuma Ka cika mana munã Musulmai! "

A cikin ayoyin da suka gabata mun bayyana yadda Fir'auna ya tuhumi masu sihiri da hada kai da annabi Musa (a) don kwace iko da kasar Masar. Sai dai fir'aun da kansa ya san cewa bah aka bane, ya fadi haka ne kawai don nemawwa kansa mafita daga shank aye day a sha a hannun annabi Musa (a). Shi masu siribi bayan barazanar da Fir'auna ya yi masu, sun na cewa, kana son kasha mu ne kawai don mun yi imani da Ubangijim musa (a). Don haka suna rokon Allah suna cewa ubangijimmu ka bamu hakuri kan azabtarwa da kisan da fir'auna zai yi mana har sai mun koma a gareka muna muminai. Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka. 1. Yin imani kadai bai wadatar ba, dole ne sai mumini ya yi hakuri ya daure a kan tafarkin Ubangiji. 2. Muminai a ko yauce suna kokari a kan tafarkin Allah kuma suna tawali'u da kuma rokon Allah ya taimake su. Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 127 daga cikin surar Araaf kamar haka.

وَقَالَ الْمَلأُ مِن قَوْمِ فِرْعَونَ أَتَذَرُ مُوسَى وَقَوْمَهُ لِيُفْسِدُواْ فِي الأَرْضِ وَيَذَرَكَ وَآلِهَتَكَ قَالَ سَنُقَتِّلُ أَبْنَاءهُمْ وَنَسْتَحْيِـي نِسَاءهُمْ وَإِنَّا فَوْقَهُمْ قَاهِرُونَ{127}

127 - Kuma mashawarta daga mutãnen Fir'auna suka ce: "Shin, zã ka bar Mũsã da mutãnensa dõmin su yi barna a cikin kasa, kuma ya bar ka, kai da gumãkanka?" Ya ce: "Zã mu yayyanka diyansu maza kuma mu rãya mãtansu; kuma lalle ne mũ, a bisa gare su, marinjãya ne."

A cikin fada da ya aka yi tsakanin Fir'auna a gefe guda da kuma Annabi Musa (a) da masu sihirin da suka yi imani da shi a dayan bangaren. Fir'auna ya yanke hukuncin kisa kan masu sihirin da suka yi imani da ubangijin annabi Musa (a). Sai dai danga ne da annabi Musa (a) bai bayyana takamemmem abinda za'a yi da shi ba. Daga karshe shi da mashawartansa sun tsaida cewa zasu ci gaba da bautar da mutanen Annabi Musa (a) wato Bani Isra'ila sannan kari a kan haka zai yayyanka yayansu masa ya raya matansu, don ya san yana da cikekken iko a kansu. Daga cikin wannan ayar zamu dauki darussa kamar haka. 1. Dagutai wadanda su ne masu barna a bayan kasa, amma suna ganin annabawa da mabiyansu ne masu barna a bayan kasa. 2. Lalata matasa na daga cikin hanyoyin da azzaluman shuwagabanni suke amfani da shi wajen kare mulkinsu. Sannan mata kuma su zama masu khidamar bukatunsu. Ana amfani da wannan tsarin a kasashen yamma a halin yanzu, inda ake maida matasa masu shan kwaya mata kuma sun zama wasilar kasuwanci. Masu sauraro a nan kuma zamu dasa aya sai kuma wani shirin idan Allah ya akimu a huta lafiya wassalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu.

Suratul A'araf, Aya Ta 128-131 (Kashi Na 252)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake dasuwada cikin shirimmu na hannunka mai sanda shiri wanda yake dubi cikin wasu a yoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwarmu. Da fatan masu saurare zasu kasance tare da mu.

      • .

To bara mu fara shirimmmu na yau tare da sauraron karatun aya ta 128 daga surar Araaf kamar haka.

قَالَ مُوسَى لِقَوْمِهِ اسْتَعِينُوا بِاللّهِ وَاصْبِرُواْ إِنَّ الأَرْضَ لِلّهِ يُورِثُهَا مَن يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ وَالْعَاقِبَةُ لِلْمُتَّقِينَ{128}

128 - Mũsã ya ce wa mutãnensa: "Ku nẽmi taimako da Allah, kuma ku yi hakuri; Lalle ne kasa ta Allah ce, Yãna gãdar da ita ga wanda Yake so daga bãyinSa, kuma ãkiba ta mãsu takawa ce."

A cikin shirimmu da ya gabata, mun ji yadda Annabi Musa (a) ya sami nasara a kan masu sihiri wanda ya zama sanadiyyar imanninsu da shi. Sannan Fir'aun ya yi alkawarin azabtar da su, ko kuma ya kasha su da sauran wadanda suka yi imani da annabi musa(a). Wannan ayar tana bayyana yadda annabi musa (a) ya ke bawa mutanensa hakuri akan azabar da suke ciki, ya bukace su da su daure su yi hakuri don kasa ta Allah ce yana gadar da ita ga wanda ya ga dama ikon kome da kome na hannunsa. Yana fada masu cewa idan sun yi hakuri a kan tafarkin Allah nasara tana a garesu. Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamat haka. 1. Hanyoyin samun nasara a kan azzaluman shuwagabannin shi ni dauriya da hakuri a kan tafarkin Allah da kuma tawakkali da shi. 2. Masu tsoron Allah sune da nasara a duniya da Lahira.

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 129 daga cikin surar Araaf kamar haka.

قَالُواْ أُوذِينَا مِن قَبْلِ أَن تَأْتِينَا وَمِن بَعْدِ مَا جِئْتَنَا قَالَ عَسَى رَبُّكُمْ أَن يُهْلِكَ عَدُوَّكُمْ وَيَسْتَخْلِفَكُمْ فِي الأَرْضِ فَيَنظُرَ كَيْفَ تَعْمَلُونَ{129}

129 -Suka ce: "An cũtar da mu kafin zo mana, kuma an ci gaba da cutar da mu bãyan kã zõ mana." Ya ce: "Akwai tsammãnin Ubangijinku, Ya halaka makiyanku, kuma Ya sanya ku, ku maye su a cikin kasa, sa'an nan Ya dũba yadda kuke aikatãwa."

Mutanen bani Isra'ila suna zaton cewa, tunda annabi Musa (a) ya sami nasara a kan fir'auna, zasu samu sauki a cikin wahalan da suke sha, amma sai abin ya zama ba haka ba. Wahala sai ma ya dada karuwa. Fir'auni ya kara takura masu. Amma annabi Musa (a) sai ya fada masu cewa, ai samun nasara a kan azzaluman shwagabanni ba zai zo da sauki haka ba, dole ne sai kun daure kun yi hukuri. Mai yuwa Allah ya halaka makiyanku a maye gurbinsu da su. Ku zama kun e shuwagabanni. Amma ko kuma, Allah zai ga irin ayyukan da zaku yi idan kun zama shuwgabannin shin zaku zama kamar fir'auna ne ko kuma zasu kyautatawa mutane. Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka. 1. Neman saukin rayuwa da hutu daga mabiya addinin Allah suna daga cikin abubuwan da suke maida addin baya. Wadanda suke son hutu basa iya jurewa hukunce hukuncen Allah. 2. Samun iko wata jarrabawa ce ta Ubangiji ga wanda yake ba shi iko. Fir'auna ne ko waninsa. Don haka bayan halaka fir'auna Allah ya jarrabi shuwagabannin da suka zo bayansa ma.

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 130 daga cikin surar Araaf kamar haka.

وَلَقَدْ أَخَذْنَا آلَ فِرْعَونَ بِالسِّنِينَ وَنَقْصٍ مِّن الثَّمَرَاتِ لَعَلَّهُمْ يَذَّكَّرُونَ{130} فَإِذَا جَاءتْهُمُ الْحَسَنَةُ قَالُواْ لَنَا هَـذِهِ وَإِن تُصِبْهُمْ سَيِّئَةٌ يَطَّيَّرُواْ بِمُوسَى وَمَن مَّعَهُ أَلا إِنَّمَا طَائِرُهُمْ عِندَ اللّهُ وَلَـكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لاَ يَعْلَمُونَ{131}

130- Kuma lalle ne, hakĩka, Mun kãma mutãnen Fir'auna da tsananin shẽkaru (fari) da nakasa daga 'ya'yan itãce; Tsammãninsu sunã tunãwa.

7:131 - Sa'an nan idan wani alhẽri ya jẽ musu, sai su ce: wannan hakkimmu ne, Idan kuma "Masĩfa ta sãme su, sai su yi shu'umci da Mũsã da wanda yake tãre da shi, To, shu'umcinsu a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawansu bã su sani ba!"

Wannan ayar tana bayyana cewa, ba wai Bani isra'ila ne kadai suke shan wahala ba. Mutanen Fir'auna ma suna gamuwa da matsaloli kamar fari da karancin abinci. Allah yakan jefa wadnnan matsaloli ne a tsakaninsu don ya zama gargadi a garesu, amma basa fahinta, a duk lokacinda wata musiba ta samesu sun danganta shi da bani Isra'ila. Sai su manta da cewa Ubangiji ne yake jarrabasu da shi ba. Mutanen Fir'auna suna ganin cewa duk abu na alkhairi daga garesu ne, shari kuma sanadiyyar Bani Isra'ila ne, Zamu dauki darussa a cikin wannan ayar kamar haka. 1. Allah ne yake jujjuya lamura a duniya, don haka kada mu ce dabi'a ce haka take. Fari sa karancin ruwa duk daga wajen Allah ne shi yake rike ruwa shi yake sakinsu. 2. Kasa mu yi kuskure wajen bayanin jujjuyawan alkhairi da sharri a cikimmu. Wasu lokutam mune sababin musibon da suke samummu. Masu sauraro da wannan kuma muka kawo karshen wannan shirin sai kuma wani lokaci idan Allah ya kaimu. Mu huta lafiya wassalamu alaikum warahmatullah.

Suratul A'araf, Aya Ta 132-135 (Kashi Na 253)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake dasuwada cikin shirimmu na hannunka mai sanda shiri wanda yake dubi cikin wasu a yoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwarmu. Da fatan masu saurare zasu kasance tare da mu.

      • .

To bara mu fara shirimmmu nay au tare da sauraron karatun aya ta 132 daga surar Araaf kamar haka.

وَقَالُواْ مَهْمَا تَأْتِنَا بِهِ مِن آيَةٍ لِّتَسْحَرَنَا بِهَا فَمَا نَحْنُ لَكَ بِمُؤْمِنِينَ{132}

132 -Kuma suka ce: "Kõ me ka zõ mana da shi na daga ãyã, dõmin ka sihirce mu da ita, to, baza mu zama, mãsu ĩmãni sabõda kai, ba."

Wannan ayar da kuma wasu ayoyi da dama a cikin Alkur'ani mai girma suna bayyana cewa, mafi yawan kafirai basu kafirce don rashin sanin gaskiya ba. Sai dai taurin kai ne da girman kai. Wannan ayar tana bayyana yadda kafirai mutanen fir'auna suke fadawa Annabi musa (a) cewa duk wata aya da zaka zo mana da ita ka kwana cikin sanin cewa baza mu yi imani da kai ba. Amma wadanda suke neman gaskiya, duk lokacinda gaskiya ta zo masu a shirye suka su karbi gaskiya. Kamar yadda masu sihiri suka karbi gaskiya da zaran suka tabbatar da cewa ita ce. 1. Tuhumar Annabawa da sihiri wani abu ne da ya zama ruwan dare a tsawon tarihi. Amma wannan baya hana su aikata abinda yakamata su yi na kira da kuma shiryatar da mutanensu. 2. Cututtuka na zuciya kamar girman kai da taurin kai zasu duk suna hana mutane karban gaskiya a lokacinda ta zo masu.

Yanzun kuma mu saurari aya ta 133 cikin surar Araaf kamar haka.

فَأَرْسَلْنَا عَلَيْهِمُ الطُّوفَانَ وَالْجَرَادَ وَالْقُمَّلَ وَالضَّفَادِعَ وَالدَّمَ آيَاتٍ مُّفَصَّلاَتٍ فَاسْتَكْبَرُواْ وَكَانُواْ قَوْماً مُّجْرِمِينَ{133}

133 - Sai Muka aika a kansu da cikõwa, da fãra, da kwarkwata da kwãdi, da jini; ãyõyi abũbuwan rarrabẽwa; Sai suka kangare, kuma suka kasance mutãne mãsu laifi.

Don irin taurin kai da kafirai suke nunawa Allah ta'ala ya jarrabesu da wasu musibu daya na bin daya. Da farko akwai mabaliyar ruwa wanda yake zuwa ya lalata amfanin gona, sannan Allah ya aiko masu da fari wadanda suke cinye amfanin gona, sannan kwarkwata shi kuma yana hana mutane sakad. Hakama ya sakammasu kwadi da jini duk don su zama aya a garesu. Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka. 1. Dabbobi ma bayin Allah a wani lokaci rahama ne ga mutane kamar yadda tanrabara da kuma gizo gizo suka zama rahama ga manzon Allah (s) a lokacin da suka zama kariya gare shi daga kafirai. Sannan wani lokacin kuma su azaba ne kamar yadda fari suke lalata gonaki. 2. Yawan zunubi da kuma girman kai su ne katangar da ke hana mutane karban gaskiya.

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 134 da kuma ta 135 daga cikin surar Araaf kamar haka.

وَلَمَّا وَقَعَ عَلَيْهِمُ الرِّجْزُ قَالُواْ يَا مُوسَى ادْعُ لَنَا رَبَّكَ بِمَا عَهِدَ عِندَكَ لَئِن كَشَفْتَ عَنَّا الرِّجْزَ لَنُؤْمِنَنَّ لَكَ وَلَنُرْسِلَنَّ مَعَكَ بَنِي إِسْرَائِيلَ{134} فَلَمَّا كَشَفْنَا عَنْهُمُ الرِّجْزَ إِلَى أَجَلٍ هُم بَالِغُوهُ إِذَا هُمْ يَنكُثُونَ{135}

134 -Kuma a lõkacin da masĩfa ta auku a kansu, sukan ce: "Yã Mũsã! Ka rõka mmana Ubangijinka, sabõda abin da Ya yi alkwari a wurinka, lalle ne idan ka kau da azãbar daga barinmu, hakĩka Munã ĩmãni sabõda kai, kuma munã sakin Banĩ Isrã'ila tĩre da kai."

135 -To, a lõkacin da Muka kuranye azãba daga barinsu zuwa a wani ajali wanda suke mãsu iske shi ne, sai gã su sunã warwarẽwa!

Saukar masibu daban daban daya bayan daya ya sa mutanen Fir'auna suka fahinci cewa wadan nan musibu ba ta da'bi'a b ace. Don hak suka garazaya zuwa wajen annabi Musa (a) suka bukace shi da rokammasu Ubangijinsa ya yaye masu musibar da suke ciki, idan ya yi haka zasu yi imani da shi. Amma bayan addu'ar annabi Musa (a) da kuma yayewar musiba sai su koma kan ayyukansu na da. Na azzabtar da Bani Isra'ila da kuma kin imani da annabi Musa kamar yadda suka yi alkawari ba. 1. Tawassuli da bayin Allah don yayewar azaba abu ne tabbatacce. Hatta kafirai sun san da haka. 2. Jin dadi da musibu a rayuwan dan'adam ba haka kawai suke zuwa ba, Allah yana sane da kowanne daga cikinsu. To masu sauraro da wanna kuma muka kawo karshen shirimmu na yau sai kuma wani shirin idan Allah ya kaimu. Wassalami alaikum warahmatullahi wa barakatuhu.

Suratul A'araf, Aya Ta 136-140 (Kashi Na 254)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na hannunka mai sanda shiri wanda yake dubi cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwarmu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare dam u.

      • .

Yanzu bari mu fara shirimmu da sauraron karatun aya ta 136 cikin surar Araaf kamar haka.

فَانتَقَمْنَا مِنْهُمْ فَأَغْرَقْنَاهُمْ فِي الْيَمِّ بِأَنَّهُمْ كَذَّبُواْ بِآيَاتِنَا وَكَانُواْ عَنْهَا غَافِلِينَ{136}

136 -Sai Muka yi azãbar rãmuwa, daga gare su, sabõda haka Muka nutsar da su a cikin tẽku, dõmin lalle ne sũ, sun karyata game da ãyõyinMu, kuma sun kasance daga barinsu, gãfilai.

A cikin shirimmu da ya gabata mun ji yadda fir'auna da mabiyansa suka kafir cewa ayoyin Allah wanda annabi Musa (a) ya zo masu da shi. A wannan ayar alqur'ani mai girma ya bayyana yadda Ubangiji ya halaka fir'auna da mabiyansa a cikin ruwan kogin nilu sannan ya tseratar da Annabi Musa (a) da kuma mutanensa wato bani Isra'ila. Ayar ta ci gaba da bayanin cewa wannan sakamakon kafircinsu da kuma yi ko in kula da ayoyin Allah wadanda Annabi Musa (a) ya zo masu da shi. Daga cikin wannan ayar zamu dauki darussa kamar haka. 1. Allah ta'ala mai yawan tausayi ne kuma mai tsananin azaba ne. 2. Makomar wadanda suka kafircewa Allah shi ne halaka da kuma asara.

Yanzun kuma bari mu saurari aya ta 137 daga cikin surar Araaf kamar haka.

وَأَوْرَثْنَا الْقَوْمَ الَّذِينَ كَانُواْ يُسْتَضْعَفُونَ مَشَارِقَ الأَرْضِ وَمَغَارِبَهَا الَّتِي بَارَكْنَا فِيهَا وَتَمَّتْ كَلِمَتُ رَبِّكَ الْحُسْنَى عَلَى بَنِي إِسْرَائِيلَ بِمَا صَبَرُواْ وَدَمَّرْنَا مَا كَانَ يَصْنَعُ فِرْعَوْنُ وَقَوْمُهُ وَمَا كَانُواْ يَعْرِشُونَ{137}

137 -Kuma Muka gãdar da mutãnen, wadanda sun kasance anã raunana su, a gabacin kasa da yammacinta, wadda Muka sanya albarka a cikinta, kuma kalmar Ubangijinka mai kyau ta cika a kan Banĩ Isrã'ĩla, sabõda abin dasuka yi na hakuri. Kuma Muka murkushe abin da Fir'auna da mutãnensa suka kasance sunã sanã'antawa, da abin da suka kasance sunã shimfidãwa.

Bayan alqur'ani ya bayyana makomar Fir'auna da matanensa, sai ya kawo sakamakon da ya Allah ya yiwa Bani Isra'ila saboda hakuri da dauriya da suka yi a kan tafarkin Allah. Sannan ayar ta kara bayyana cewa banda halaka Fir'auna da mutanensa Allah ya gadarwa bani Isra'ila kasa ya maidasu masu iko da fada a ji a kasashen Palasdinu da sham wadanda suka kasance dama suna karkashin ikon fir'auna ne. Ya gadar masu da dukkan arziki da dukiyoyi da suke cikin wadannan yankuna. Bayan kasancewarsu makaskanta suna rayuwa mai wahalarwa a karkashin ikon Fir'auna. Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka. 1. Hukumar Annabawa ta raunana ce bat a masu karfi da dukiya ba. 2. Yana daga cikin alkawarin Allah ga raunanan mutane, wadanda suka yi hukuri suka daure a kan a tafarkinsa, to wata rana zai daukakasu ya basu iko da kasa.

Yanzun kuma mu saurari aya ta 138, 139 da kuma ta 140 daga cikin surar Araaf kamar haka.

وَجَاوَزْنَا بِبَنِي إِسْرَائِيلَ الْبَحْرَ فَأَتَوْاْ عَلَى قَوْمٍ يَعْكُفُونَ عَلَى أَصْنَامٍ لَّهُمْ قَالُواْ يَا مُوسَى اجْعَل لَّنَا إِلَـهاً كَمَا لَهُمْ آلِهَةٌ قَالَ إِنَّكُمْ قَوْمٌ تَجْهَلُونَ{138} إِنَّ هَـؤُلاء مُتَبَّرٌ مَّا هُمْ فِيهِ وَبَاطِلٌ مَّا كَانُواْ يَعْمَلُونَ{139} قَالَ أَغَيْرَ اللّهِ أَبْغِيكُمْ إِلَـهاً وَهُوَ فَضَّلَكُمْ عَلَى الْعَالَمِينَ{140}

7:138 -Kuma Muka kẽtarar da Banĩ Isra'ila ga tẽku, sai suka jẽ a kan wasu mutãne wadanda sunã lizimta da ibãda a kan wasu gumãka, nãsu suka ce: "Yã Mũsã! Ka sanya mana wani abin bautawa kamar yadda suke da abũbuwan bautãwa " Ya ce: "Lalle ne kũ, mutãne ne kunã jahilta."

7:139 -"Lalle ne wadannan, abin da suke a cikinsa halakakke ne, kuma abin da suka kasance sunã aikãtawa karya ne."

7:140 -Ya ce: "Shin, wanin Allah nike nẽma muku ya zama abin bautãwa, alhãli kuwa Shĩ (Allah) Ya fĩfĩta ku a kan halittu?"

A cikin ayayin da suka gabata mun bayyana yadda Allah ta'ala ya kubutar da bani'isra'ila daga azabtarwan Fir'auna da mutanensa. Sannan ya sanya su masu iko a kasashen sham. Amma kasancewa sun dade a cikin mutanen Fir'auna masu bautar gumaka, sai ya kasance wawaye jahilai daga cikinsu, kamar yadda ayar ta kirasu, sun bukaci Annabi musa ya gina masu gunki abin bauta kamar yadda suka saba, ko kuma kamar yadda suka mga wasu mutane suke yi. Amma wannan bukatar ta bawa annabi musa (a) mamaki, yana fada masu "shin wace irin bukace wannan, bayan da ubangiji ya kubutar da ku daga hannun Fir'auna cikin yan kwanakinnan, amma kuka manta da shi?. Kun manta da cewa gumaka baa bin bauta ban e? shin yanzu har kun manta da ni'amar da Allah ya yi maku. Kuna bayi ya maida ku sarakuna. ?. Me yasa ku bakwa fahinta ne?. Daga cikin wadannan ayoyi muna iya daukan darussa kamar haka. 1. Zama cikin lalataccen al-umma, masu aikata barna, zai kasance mai tasiri a cikin rayuwan mutum ko day a zama mumini daga baya. 2. Wani lokaci jahilan musulmi sukan cutar da shuwagabanninsu fiye da yadda makiya suke iya cutar da su. Masu sauraro a nan zamu daka da wannan shirin sai kuma shiri na gaba idan Allah ya kaimu. A huta lafiya wassalamu alaikum warahmatullahi.

Suratul A'araf, Aya Ta 141-142 (Kashi Na 255)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na hannunka mai sanda shiri wanda yake dubi cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwarmu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

      • .

To bari mu fara shirimmu n ayau tare da karatun aya ta 141 daga cikin surar Araaf kamar haka.

وَإِذْ أَنجَيْنَاكُم مِّنْ آلِ فِرْعَونَ يَسُومُونَكُمْ سُوَءَ الْعَذَابِ يُقَتِّلُونَ أَبْنَاءكُمْ وَيَسْتَحْيُونَ نِسَاءكُمْ وَفِي ذَلِكُم بَلاء مِّن رَّبِّكُمْ عَظِيمٌ{141}

141 -Kuma a lõkacin da Muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, sunã tayã muku mugunyar azãba. sunã karkashe diyanku maza, kuma sunã rãyar da matanku. Kuma a cikin wancan akwai jarrabãwa daga Ubangijinku, Mai girma.

A cikin shirimmu da ya gabata ayoyin da muka karanta sun bayyana yadda Bani'isra'ila, bayan da Allah ya kubutar da su daga Azabtarwan Fir'auna da mutanensa, sannan ya sanya su shuwagabanni a kasashen sham, wasu jahilai daga cikinsu sun bukaci annabi musa(a) ya sanya masu abin bauta gumaka kamar yadda suka ga wasu mushriaki su ke yi. Wannan ayar tana tunatar da su irin ni'imomin da Allah ya yi masu, tana cewa, shin kun manta da cewa, ba da jimawa din nan ba, Allah ya kubutar da ku daga fir'auna da mutanensa? Shin kun manta da yadda Allah ya sanya ku shuwagabanni bayan kun kasance kaskantattu? Shin kunmnata ne yadda Fir'auna yake kashe yayanku maza ya raya matanku su zama masu khimada gareshi da mutanenshi?. Shin ba Ubangijin Musa ne ya yi maku dukkan wadannan ni'imomi ba? Shin way a cancanta ku bauta masa inda shi?. Muna iya daukan darussa dag cikin wannan ayar kamar haka. 1. Gafala daga ni'imomin Allah yana sanya mutane komawa ga kafirci da kuma sharki. Sannan shuwagabanni sukan tunatar da mutane irin ni'imomin da Allah ya yi masu don su gujewa kafirci da kuma karkata daga dafarkin gaskiya. 2. Musibi da wahalhalu yana daga cikin jarrabawan Allah ga mutanen. Kamar yadda ni'imomi da jin dadi ma na daga cikin jarabawarsa.

Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 142 daga cikin surar Araaf kamar haka.

وَوَاعَدْنَا مُوسَى ثَلاَثِينَ لَيْلَةً وَأَتْمَمْنَاهَا بِعَشْرٍ فَتَمَّ مِيقَاتُ رَبِّهِ أَرْبَعِينَ لَيْلَةً وَقَالَ مُوسَى لأَخِيهِ هَارُونَ اخْلُفْنِي فِي قَوْمِي وَأَصْلِحْ وَلاَ تَتَّبِعْ سَبِيلَ الْمُفْسِدِينَ{142}

142 -Kuma Muka yi wa'adi ga Mũsã da dare talãtin kuma Muka cikã su da gõma, sai mikatin Ubangijinsa ya cika dare arba'in. Kuma Mũsã ya ce wa dan'uwansa, Hãrũna: "Ka maye mini a cikin mutãnena, kuma ka gyãra, kuma kada ka bi hanyar mãsu fasãdi."

Aiki na farko wanda Allah ya bawa annabi Musa (a) shi ne kubutar da bani Isra'ila daga hannun Fir'aun wanda duk tare da wahalhalu day a sha ya samu ya kammala aikin. Kuma ya zama shugaba a cikin mutanensa bani Isra'ila. Amma zamantakewa tsakanin mutane yana bukatar dokoki da tsari. Don haka ne Ubangiji ya bukaci annabi Musa (a) ya kebe kansa a kusa da dutsen Tur ya kusance ubangijinsa ta hanyar bauta masa da kuma tsarkake kansa, wanda ya zai ba shi damar daukar sakon Allah wato Attaura zuwa ga mutanensa. A lokacinda Annabi musa (a) zai bar mutanesa ya tafi ganawa da Ubangijinsa na kwanaki 40 ya bar dan uwansa Annabi Harun (a) a matsayin Khalfansa. Ya zo a cikin littafan tarihi cewa manzaon Allah (s) yana nisantar iyalansa ya koma ciki kogo yana bautawa Allah kafin wahayi ya fara sauko masa. Sannan wani abin lura a nan shi ne cewa anna musa (a) zai tafi ganawa da ubangijinsa na kwanaki 40 ne kacal amma said a ya khalifantar da dan uwansa annabi Haruna kan al-ummarsa. Hakama manzon Allah (s) ko da yaki ne zai je sai ya samara da khalifansa a madina kafin ay fita. A yakin tabuka ya khalifantar da Imam Aliyu bin Abitalib (a) a madani kafin ya fita. To ta yaya ba zai khalifantar da wani cikin alummarsa ba bayan ya san zai bar wannan duniya? A wani hadisi yana cewa "Ya Aliyu matsayinka da ni kamar matsayin Haruna da Musa ne sai dai kai ba annabi bane. "

A lokacinda annabi Musa (a) zai tafi ya yi wasiyya gad an uwansa haruna da kula da mutanensa sannan shima ya tabbata kan tafarkin day a barsu a kai. Amma duk da haka sai mafi yawan mutanen suka yi watsi da Haruna (a) suka bi wani daga cikinsu mai suna Samiri ya batar da su. Ya gina masu gunkin saniya suka fara bauta mata.

Muna iya daukan darussa daga cikin wannan ayar kamar haka. 1. Shuwagabanni suna da nauyi mai yawa a kansu don haka suna bukatan kusanci da Allah don samun taimakonsa. Shi ya sa suke samun kebanta daga mutane na wani lokaci don samun wannan kusancin. 2. Dole ne ya kasance al-umma tana da shugaba wacce take wa biyayya ko da kuwa na lokaci kadan ne.

Masu sauraro a nan kuma zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wani shirin idan Allah ya kaimu. Mu huta lafiya wassalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu.

Suratul A'araf, Aya Ta 143-146 (Kashi Na 256)

Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat A'araf, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (143) surat A’araf:

وَلَمَّا جَاء مُوسَى لِمِيقَاتِنَا وَكَلَّمَهُ رَبُّهُ قَالَ رَبِّ أَرِنِي أَنظُرْ إِلَيْكَ قَالَ لَن تَرَانِي وَلَـكِنِ انظُرْ إِلَى الْجَبَلِ فَإِنِ اسْتَقَرَّ مَكَانَهُ فَسَوْفَ تَرَانِي فَلَمَّا تَجَلَّى رَبُّهُ لِلْجَبَلِ جَعَلَهُ دَكّاً وَخَرَّ موسَى صَعِقاً فَلَمَّا أَفَاقَ قَالَ سُبْحَانَكَ تُبْتُ إِلَيْكَ وَأَنَاْ أَوَّلُ الْمُؤْمِنِينَ{143}

Lokacin da Musa ya zo wajen alkawarinmu ubangajinsa kuma ya yi magana da shi,sai ya ce: " ya ubangijina nuna mini kanka in ganka, sai ya ce : Ba ba za ka ganni ba, amma duba zuwa wanna dutsen idan ya tabbata a gurinsa to da sannu za ka ganni, to a lokacin da ubangijinsa ya tajalli ga dutsen sai ya mayar da shi rugu-rugu, Musa kuma ya fadi a some, sa'annan a lokacin da ya farko sai ya ce: tsarki ya tabbata a gare ka, na tuba ya zuwa gare ka kuma nine farkon muminai.

A cikin shirin da ya gabata an ambaci cewa annabi Musa (AS) ya tafi mikati na kwanaki arba’in a cikin dutsen Tur domin karbo littafin Attaura, a lokacin ya yi magana da Allah madaukakin sarki. Daga cikin abubuwan da Bani Isra’ila suka bukaci annabi Musa ya yi musu har da neman su ga Allah kuru-kuru da idanunsu, saboda haka annabi Musa ya gabatar da bukatarsa a wajen kan yana son ya gan shi da idanunsa, domin idan ya koma ga Bani Isra’ila ya gayama su cewa baya ga magana da Allah ya ma ganshi da idanunsa, sai Allah ya gaya ma Annabi Musa (AS) cewa: “ba za ka taba ganina ba.” Domin kuwa Allah madaukakin sarki ba a iya ganinsa da idaniya, saboda haka Allah ya ce annabi Musa yana iya ganin kudira ta Allah idan ya yi duba zuwa dutsen Tur, a lokacin da wani haske daga kudirar Allah ya bayyana a kan dutsen sai ya narke, a nan take annabi Musa ya some, bayan da ya farfado daga bisani sai ya ce; ya ubangijina tsarki ya tabbata gareka, ina mai neman gafara daga gareka kan wannan tambaya da na yi, ni ne farkon wanda ya sheda da karfin ikonka da kudirarka, kuma ina mai imani da kadaitakarka.

A lokacin da Imam Ali (AS) yake amsa tamyar wani mutum da yake ce masa; ya kake bauta ma ubangijin da baka gani da idanunka? Sai Imam (AS) ya ce masa: Ni kam bana bauta ma ubangijin da bana gani, ina bautama ubangijin da nake gani da zuciya ta imani, amma ba da idanu ba.

A cikin wani bayanin kuma Imam (AS) yana cewa; Babu wani abun halitta da zan gani face sai na ga Allah tare da shi, ma’ana duk wani abin halitta da za a gani, to yana nuni ne da cewa akwai mahliccinsa, wanda kuma shi ne Allah madaukakin sarki.

Wadabnnan bayanai na Imam Ali (AS) suna tabbatar mana da cewa ana ganin Allah ne kawai ta hanyar ayoyinsa, amma ba da idanu ba. Aya ta 103 a cikin surat An’am ta bayyana hakan karara da cewa; Allah madaukakin sarki gannai na idanu ba su ruskarsa, shi ne yake riskar dukkanin gannai na idanu. Hakan na tabbatar da cewa babu wani mahaluki da zai iya ganin Allah da idanu har abadan abada, domin kuwa Allah ya ce ma Annabi Musa ba za ka taba ganina ba, ma’ana babu wani lokaci da annabi Musa zai iya ganin Allah.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Ana sanin Allah ne da kudirarsa da karfin ikonsa ta hanyar ganin ayoyinsa.

2 – A duk lokacin da aka aikata wani abu da ake ganin bai yi daidai da yardar Allah ba, to a gaggauta yin tuba zuwa gare shi madaukakin sarki.

Aya ta (144) da (145) a cikin surat A’araf:

قَالَ يَا مُوسَى إِنِّي اصْطَفَيْتُكَ عَلَى النَّاسِ بِرِسَالاَتِي وَبِكَلاَمِي فَخُذْ مَا آتَيْتُكَ وَكُن مِّنَ الشَّاكِرِينَ{144} وَكَتَبْنَا لَهُ فِي الأَلْوَاحِ مِن كُلِّ شَيْءٍ مَّوْعِظَةً وَتَفْصِيلاً لِّكُلِّ شَيْءٍ فَخُذْهَا بِقُوَّةٍ وَأْمُرْ قَوْمَكَ يَأْخُذُواْ بِأَحْسَنِهَا سَأُرِيكُمْ دَارَ الْفَاسِقِينَ{145}

Ya ce: "Ya Mũsã! Lalle ne Nĩ, Nã zãbe ka bisa ga mutãne da manzancina, kuma da maganãta. Sabõda haka ka riki abin da Nã bã ka, kuma ka kasance daga mãsu gõdiya."

Kuma Muka rubũta masa a cikin alluna daga kõwane abu, wa'azi da rarrabẽwa ga dukan kõwane "Sai ka rike su da karfi, kuma ka umurci mutãnenka, su yi riko ga abin da yake mafi kyawunsu; zã ni nũna muku gidan fãsikai."

Allah madaukakin sarki da hikimarsa ya zabi annabi Musa a lokacin rayuwarsa ya zama shi ne mai isar da sakonsa ga mutane, ya zama shi ne shiryarwa zuwa ga tafarkin Allah, shi ne wanda Allah ya kebance da zancensa, saboda haka Allah ya umurci annabi Musa da ya yi riko da abin da aka ba shi kuma ya yi godiya. A cikin kwanaki arba’in da annabi Musa (AS) ya yi a mikatinsa da Allah madaukakin sarki, an ba shi littafin attaura, domin yin wa’azi da iya da kuma fayyace hukunce-hukunce da dokokin Allah, saboda haka aka umurci annabi Musa (AS) da ya yi riko da ita kuma ya umurci mutanensa da su yi riko da abin da ke cikinta.

Darussan da za a dauka a nan su ne:

1 – Bayan kawar da hukumar da ta ginu a kan tsari na zalunci da dagutanci ta Fir’auna da taimakon Allah, to babu abin da ya rage ma Bani Isra’ila illa su bi tsarin adalci da gaskiya da kare hakkokin dan adam karkashin jagorancin annabi Musa.

2 – Safkar da littafi daga Allah madaukakin sarki ga wata al’umma babbar ni’ima ce gare su, kuma yin godiya ga ni’imar Allah, umurni ne daga gare shi, domin kuwa idan mutane sun gode wa ni’imar Allah to zai kara musu wasu ni’imomin da suka sani da ma wadanda ba su sani ba, kuma za su lada mai tarin yawa sakamakon godiyarsu ga ni’imarsa.

Aya ta (146) surat A’araf:

سَأَصْرِفُ عَنْ آيَاتِيَ الَّذِينَ يَتَكَبَّرُونَ فِي الأَرْضِ بِغَيْرِ الْحَقِّ وَإِن يَرَوْاْ كُلَّ آيَةٍ لاَّ يُؤْمِنُواْ بِهَا وَإِن يَرَوْاْ سَبِيلَ الرُّشْدِ لاَ يَتَّخِذُوهُ سَبِيلاً وَإِن يَرَوْاْ سَبِيلَ الْغَيِّ يَتَّخِذُوهُ سَبِيلاً ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ كَذَّبُواْ بِآيَاتِنَا وَكَانُواْ عَنْهَا غَافِلِينَ{146}

Zã ni karkatar da wadanda suke yin girman kai a cikin kasa, bã da wani hakki ba, daga ãyõyina. Kuma idan sun ga dukan ãyã, bã zã su yi ĩmãni da ita ba, kuma idan sun ga hanyar shiriya, bã zã su rike ta hanya ba, kuma idan sun ga hanyar bata, sai su rike ta hanya. Wancan ne, dõmin lalle ne su, sun karyata ãyõyinmu, kuma sun kasance rafkanannu daga barinsu.

Wannan aya tana karfafa ayar da ta gabace ta ne, dangane da wajabcin yin riko da hukunce-hukuncen Allah da dokokinsa da ya safkar a cikin littafan da ya baiwa annabawansa, ayar tana jan hankalin mutanen da suke yin girman kai da juya baya daga bin umurnin Allah, da su shiga taitayinsu, irin wadannan mutanen ba a shirye suke su karbi gaskiya ba a lokacin da ta zo musu kuma ko ta hanyar wane ne, saboda girman kansu ba su bin tafarkin gaskiya a matsayin hanyar rayuwa, amma idan suka ga wata hanya ta bata sai su rike ta hanyar rayuwarsu, ba wani abu ya jawo musu hakan ba illa karyata ayoyin Allah da suka, sun gafala da sanin manufar rayuwarsu, balnatan su yi tanadi domin makomarsu.

Darussan da za a iya dauka a nan su ne:

1 – Girman kai na daga cikin munan halaye da suke mutum zuwa ga karyata ayoyin Allah.

2 – Allah yana yin falala ga mutane baki daya da masu yi masa biyayya da kuma masu yi masa girman kai da saba ma, domin kuwa rahamarsa ta kewaye komai.

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.

Suratul A'araf, Aya Ta 147-149 (Kashi Na 257)

Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat A'araf, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (147) surat A’araf:

وَالَّذِينَ كَذَّبُواْ بِآيَاتِنَا وَلِقَاء الآخِرَةِ حَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ هَلْ يُجْزَوْنَ إِلاَّ مَا كَانُواْ يَعْمَلُونَ{147}

Kuma wadanda suka karyata game da ãyõyinmu da gamuwa da Lãhira, ayyukansu sun bãci. Shin, ana saka musu, fãce da abin da suka kasance suna aikatãwa?

A mahangar addinin Musulunci, kimar aiki tana damfare ne da niyyar gudanar da aikin, koda kuwa aiki ne na alkhairi aka aikata idan niyar aikin bat a alkhairi ba ce, to wannan aikin ba ya da kima a wajen Allah madaukakin sarki. A wasu lokuta ba aikin ba ya da kima ba ne kawai, a'a har ma zai kai mutum ga samun sakamako na azaba a wajen Allah. Misali a nan shi ne, mutumin da ya yi wani na ibada domin riya, to a lokacin aikinsa bai karbu ba, saboda haka yana da zunubi biyu, zunubi na riya, da kuma zunubi na rashin wannan aikin idan ya kasance aiki ne farilla, amma idan aiki ne wanda ban a farilla ba, to ba shi da ladar aikin, kuma yana da zunubi na riya.

Karyata ayoyin Allah bai takaitu da musu da kafirai suke yi da ayoyin ubangiji ba, a'a hatta ma mutumin da yake ikirarin imani amma aikinsa ba na imani ba ne, to ba za a karba daga gare shi, domin kuwa aikinsa yana misilta karyata ayoyin Allah ne a aikace, ko da kuwa yana ikirarin imani da lafazi na fatar baki.

Wannan ayar tana nuni da cewa, wadanda suka karyata ayoyin ubangiji to a ranar kiyama za su zo hannu rabbana, domin kuwa imani da aiki na gari da aka yi domin Allah su ne za su amfani mutum a ranar kiyama, su ne babban guzurinsa, duk kuwa da cewa aikin mutum ba shi ne zai kai shi ga samun aljannar Allah da tsira daga wuta ba, hakan ba zai samu ba sai rahamar ubangiji, amma kuma yin aiki na gari bin umurnin Allah ne, wanda da shi ne mutum zai sa ran samun rahamar Allah a ranar kimayama.

Darussan da za mu dauka a nan su ne:

1 – Yin musu kan ayoyin Allah da manyan lamurra kamar tashin kiyama, da lafazin da aka kudirce ko kuma a aikace, yana da bababn tasiri wajen ruguza ayyukan mutum.

2 – Sakamako mai kyau ko akasin haka a ranar kiyama yana da dangantaka ne kai tsaye da abin da mutane suka kasance suna aikatawa a rayuwarsu ta duniya.

Aya ta (148) surat A'araf

وَاتَّخَذَ قَوْمُ مُوسَى مِن بَعْدِهِ مِنْ حُلِيِّهِمْ عِجْلاً جَسَداً لَّهُ خُوَارٌ أَلَمْ يَرَوْاْ أَنَّهُ لاَ يُكَلِّمُهُمْ وَلاَ يَهْدِيهِمْ سَبِيلاً اتَّخَذُوهُ وَكَانُواْ ظَالِمِينَ{148}

Kuma mutãnen Mũsã bayan tafiyarsa suka riki maraki daga kãyan kawarsu, jikin mutãne yanã rũri. Shin, ba su ganĩ ba, cẽwa shi bã ya yi musu magana, kuma bã ya shiryar da su ga hanya, sun rike shi, kuma sun kasance mãsu zãlunci.

A cikin ayoyin da suka gabata a cikin wannan sura, an ambaci cewa annabi Musa (AS) ya tafi mikati da ubangiji na kwanaki 30 a cikin dutsen Tur domin karbar littafin Attaura, amma kuma an kara masa kwanaki goma na mikatin, inda kwanakin mikatin suka cika kwanaki arba'in daidai.

Bani Isra'ila sun jima suna ganin gumaka da ake yin su da surar shanu a Masar, saboda haka a lokacin da suke wucewa ta koramar Nilu tare da annabi Musa (AS) sai suka ga wasu mutane masu bautar gumakan shanu suna bauta ma wani gunkin maraki, tare da annabi Musa (AS) sai suka bukaci annabi Musa (AS) da ya sanya musu wani gunki kamar domin su rika bauta masa kamar wadannan mutane suke da gunkin da suke bauta mawa, sai annabi Musa ya ce musu lallai wannan tunani nasu na jahilci ne.

A lokacin da Annabi Musa (AS) ya tafi mikati na wata guda a dutsen Turn a tsaon kwanaki 30 domin karbo littafin Attaura, wasu daga cikin Bani Isra'ila sun yada jita-jitar cewa annabi Musa (AS) ya rasu a cikin dutsen, nbayan da suka ga kwanaki 30 sun shude amma bai dawo ba, alhali kuwa an kara masa kwanaki 10 da su ba su da labarin hakan.

Wani daga cikinsu da ake kira Samirri da aka ce mai hazaka ne amma daga bisani ya bijire, ya hada wani gunkin dan maraki, wanda ya yi wasu dabarbaru a cikinsa, ta yadda zai rika huro iska mai sauti kamar na shanu, sai ya ce musu su zo su bauta ma wannan marakin, domin kuwa shi ne ubangijin Bani isra'ila har ma da shi kansa Musa, sai Bani Isra'ila suka bi shi suna bautar gunkin dan maraki.

Kur'ani mai tsarki ya siffanta wannan aiki na Bani Isra'ila da aiki na rashin basira, kuma aiki na zalunci a wani bangaren, domin kuwa mutanen da suke ikirarin imani da ubangijin annabi Musa, bisa da cewa shi ne ubangijin sammai da kassai da dukkanin talikai, amma kuma sun dawo suna bautar gunin maraki da ba ya iya amfanar da kansa balantana waninsa, suna bauta masa ne kawai saboda yana fitar da sauti na kokan shanu, da wannan kuma babu wani abu tare da shi, kur'ani ya bayyana wannan aiki na jahilci da cewa babban zalunci ne, domin Bani Isra'ila sun yi hakan ne bayan da shiriya ta zo musu daga Allah suna sane.

Darussan da a dauka a nan su ne:

1 – A duk lokacin da aka rasa shugaba mai shirya da mutane tare da fadakar da su hukunce-hukuncen Allah, to al'umma tana cikin hadarin komawa zuwa ga bata da bin tafarkin shaidan.

2 – Masu son durmiyar da mutane cikin bata, suna yin amfani da hanyoyi na saddabaru domin jawo yardar mutane, ta yadda za su gasgata a cikin dukkanin ayyukansu.

Aya ta (149) surat A'araf

وَلَمَّا سُقِطَ فَي أَيْدِيهِمْ وَرَأَوْاْ أَنَّهُمْ قَدْ ضَلُّواْ قَالُواْ لَئِن لَّمْ يَرْحَمْنَا رَبُّنَا وَيَغْفِرْ لَنَا لَنَكُونَنَّ مِنَ الْخَاسِرِينَ{149}

Kuma a lõkacin da suka yi nadãma, kuma suka ga cẽwa lalle ne sũ hakĩka sun bace, suka ce: "Hakĩka, idan Ubangijinmu bai yi mana rahama ba, kuma Ya gãfarta mana, to munã kasancẽwa daga mãsu hasãra."

A lokacin da annabi Musa (AS) ya dawo daga mikati, ya nuna ma Bani isra'ila cewa lallai sun kama haryar bata, domin kuwa sun bar ubangiji mahaliccin kowa da komai sun koma bautar gunkin maraki, annabi Musa ya kawar da wannan gunki, ya kuma kure Samirri a gaban mutane, inda ya tabbatar da cewa lallai makida ce kawai ya shirya domin batar da Bani Isra'ila daga kan hanyar shiriya ta annabi Musa, to a lokacin sai Bani Isra'ila suka tuba suka roki Allah gafara kan wannan ta'annuti da suka yi.

Annabi Musa (AS) ya kille gunkin a gaban mutanen da suke bauta masa, yak one shi kuma ya watsa dokarsa a cikin kogi, domin kada wani abu daga gare shi ya yi saura.

Darussan da za a dauka a nan su ne:

1 – Tunatarwa da wa’azi suna da matsayi na musamman wajen shiryar da al’umma, amma kuma dole ne a kawar da abubuwan da suke jaza kaucewar mutane daga sahihin tafarki, kamar yadda annabi Musa bayan ya gargadi Bani Isra’ila sun fahimci kurensu, sai kuma ya kone gunkin dan maraki ya watsa tokarsa a cikin kogi.

2 – Yin nisa daga rahama da gafarar Allah ita ce babbar tabewa da hasara.

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.

Suratul A'araf, Aya Ta 150-153 (Kashi Na 258)

Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat A'araf, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (150) surat A’araf

وَلَمَّا رَجَعَ مُوسَى إِلَى قَوْمِهِ غَضْبَانَ أَسِفاً قَالَ بِئْسَمَا خَلَفْتُمُونِي مِن بَعْدِيَ أَعَجِلْتُمْ أَمْرَ رَبِّكُمْ وَأَلْقَى الألْوَاحَ وَأَخَذَ بِرَأْسِ أَخِيهِ يَجُرُّهُ إِلَيْهِ قَالَ ابْنَ أُمَّ إِنَّ الْقَوْمَ اسْتَضْعَفُونِي وَكَادُواْ يَقْتُلُونَنِي فَلاَ تُشْمِتْ بِيَ الأعْدَاء وَلاَ تَجْعَلْنِي مَعَ الْقَوْمِ الظَّالِمِينَ{150}

Kuma a lõkacin da Mũsã ya kõma zuwa ga mutãnensa, yanã mai fushi, mai bakin ciki, ya ce: "Tir da abin da kuka yi mini a bãyanã! Shin, kun nẽmi gaggawar umurnin Ubangijinku ne?" Kuma ya jefar da Allunan, kuma ya yi riko ga kan dan'uwansa yana jan sa zuwa gare shi. Ya ce: "Yã dan'uwata! Lalle ne mutãnen, sun dauke ni mai rauni, kuma sun yi kusa su kashe ni, sabõda haka kada ka sa makiya su yi mani dariya, kuma kada ka sanya ni tãre da mutãne azzãlumai."

A cikin shirin da ya gabata an bayyana cewa; a lokacin da annabi Musa (AS) ya tafi mikati na kwanaki talatin domin karbo Attaura a dutsen Tur, Allah ya kara masa kwanaki goma, sai mikatinsa ya cika kwanaki arba’in daidai, a lokacin da Bani Isra’ila suka ga kwanaki talatin sun shude annabi Musa bai dawo ba, sai suka fara yada jita-jitar cewa ai ya mutu a cikin dutsen Tur, sai Samiri ya hada musu wani gunkin dan maraki suka koma bautarsa.

Bayan da annabi Musa ya dawo daga mikati ya iske Bani Isra’ila suna bautar gunkin dan maraki maimakon Allah, sai ya yi fushi saboda hakan, inda ya ya jawo kan dan uwansa Annnabi Haruna (AS) yana tambayarsa ya aka yi ya bar Bani Isra’ila suka koma bautar gumaka, alhali ya bar shi a matsayin mai yi musu jagora a bayan tafiyarsa mikati, alhali kuwa annabi Haruna ya yi musu gargadi da wa’azi kan halakar da suka jefa kansu, amma ba su saurare shi ba, bilhasali ma sun yi yi masa izgili da cutar da shi, har ma wasu daga cikinsu sun nemi su kashe shi saboda wa’azin da yake yi musu na su daina bautar gunkin dan maraki.

Darussan da za a dauka a nan su ne:

1 – Mumunai na hakika suna nuna fushinsu ne da takaicinsu a lokacin da aka kauce ma tafarkin Allah, a lokacin da suka ga ana saba ma Allah.

2 – Aikin jagorin al’umma shi ne yin tsayin daka wajen ganin cewa mutane ba su kauce ma sahihin tafarki ba, tare da daukar dukkanin matakai da suka dace domin kafar wando daya da masu kautar da mutane daga hanya.

Aya ta (151) surat A’araf

قَالَ رَبِّ اغْفِرْ لِي وَلأَخِي وَأَدْخِلْنَا فِي رَحْمَتِكَ وَأَنتَ أَرْحَمُ الرَّاحِمِينَ{151}

Ya ce: "Yã Ubangijina! Ka gãfarta mini, nĩ da dan'uwana, kuma Ka shigar da mu a cikin rahamarka, alhãli kuwa Kai ne Mafi rahamar mãsu rahama!"

A lokacin da fushin annabi Musa ya safka, ya roki Allah gafara da rahama ga kansa da kuma dan uwansa Haruna, domin kuwa sun yi dukkanin abin da za su iya wajen safke nauyin da Allah ya dora musu na nuna ma Bani Isra’ila hanya, amma ba su gushe ba suna bin son ransu, duk kuwa da irin baiwar da Allah ya yi musu, da tseratar da su da ya yi daga zaluncin Fir’auna, wanda ya gasa musu azaba tsawon shekaru.

Aya ta (152) surat A’araf

إِنَّ الَّذِينَ اتَّخَذُواْ الْعِجْلَ سَيَنَالُهُمْ غَضَبٌ مِّن رَّبِّهِمْ وَذِلَّةٌ فِي الْحَياةِ الدُّنْيَا وَكَذَلِكَ نَجْزِي الْمُفْتَرِينَ{152}

Lalle ne wadanda suka riki marakin, wani fushi daga Ubangijinsu da wani walãkanci a cikin rãyuwar dũniya zã su sãme su: Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu kirkira karya.

Duk da cewa annabi Musa (AS) ya dawo daga mikati, ya kuma ja gaegadi Bani Isra’ila kan babban laifin da suka yi na daukar gunkin dan maraki a matsayin abin bautarsu koma bayan Allah, ya kuma turke Samiri a gabansu, amma duk da haka wasu daga cikin yahudawan bani Isra’ila ba su daddara ba, sun ci gaba da bauta ma marakin, tare da kudicewa a cikin ransu cewa shi ne abin bautarsu ba ubangijin annabi Musa ba.

Wannan ayar mai albarka tana yin magana kan wadanda suka ci gaba da bautar dan marakin da cewa, hakika fushin ubangiji zai riske su a gidan duniya, haka nan kuma za su hadu da kaskanci na duniya tun kafin su je lahira.

Darussan da za mu koya a nan su ne:

1 – A duk lokacin da waliyan Allah ma’asumai suka yi fushi kan wani lamari, to hakika hakan manuniya ce da fushin kan wannan lamari, domin kuwa annbi Musa (AS) ya yi fushi da Bani Isra’ila da suka riki dan maraki abin bauta maimakon Allah madaukakin sarki, kuma sai gashi fushin ubangiji ya safka kan wadanda suka ci gaba da bautar dan marakin bayan annabi Musa (AS) ya yi musu gargadi, wanda hakan gasgatawar ubangiji ce ga annabi Musa tare da dan uwansa annabi Haruna (AS)

2 – Yin watsi da jagoranci na Allah tare da kama wani jagoranci da asasinsa shifta ce ta shedan, alama ce ta tabewa da hasara tun a gidan duniya, kafin kuma a koma lahira a hadu da Allah madaukakin sarki.

Aya ta (153) surat A’araf

وَالَّذِينَ عَمِلُواْ السَّيِّئَاتِ ثُمَّ تَابُواْ مِن بَعْدِهَا وَآمَنُواْ إِنَّ رَبَّكَ مِن بَعْدِهَا لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ{153}

Kuma wadanda suka aikata miyãgun ayyuka, sa'an nan suka tũba daga bãyansu kuma suka yi ĩmãni, lalle ne Ubangijinka daga bãyansu, Mai gãfara ne, Mai jin kai.

Wannan ayar tana yin ishara ne da wadanda suka wa’aztu da gaegadin da annabi Musa (AS) ya yi musu ne bayan dawowarsa daga mikati, bayan sun fahimci kurensu sai suka tuba suka koma ga Allah, kuma suka yi watsi da shirkar da suka yi ta bautar gunkin dan maraki, to wadannan Allah ya karbi tubarsu kan wannan laifi da suka aikata kuma suka yi nadama ta gakiya a kansa, domin kuwa Allah madaukakin sarki mai matukar tausayi ne ga bayinsa, haka nan kuma kofofin rahamarsa da gafararsa a kowane lokaci bude suke ga bayinsa.

Darussan da za mu dauka a nan su ne:

1 – Idan mutum ya aikata wani laifi ga Allah madaukakin sarki kada ya taba fitar da rai daga tsammanin samun gafara da rahmar ubangiji idan ya tuba ya daina aikata irin wannan laifi, kuma tubarsa ta kasance saboda Allah ba domin wani dalili na daban ba, to a lokacin zai samu gafarar ubangiji.

2 – Allah yana jinkirta masa masu aikata laifuka na sabo daga cikin mutane saboda rahamarsa da tausayinsa gare su, domin wata kila a can gaba sun farga su dawo kan sahihiyar hanya, su tuba daga aikata sabon, domin kuwa yana son su shiga cikin rahamarsa ne a ranar kiyama ba azabarsa ba.

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.

Suratul A'araf, Aya Ta 154-156 (Kashi Na 259)

Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat A'araf, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (154) surat A’araf

وَلَمَّا سَكَتَ عَن مُّوسَى الْغَضَبُ أَخَذَ الأَلْوَاحَ وَفِي نُسْخَتِهَا هُدًى وَرَحْمَةٌ لِّلَّذِينَ هُمْ لِرَبِّهِمْ يَرْهَبُونَ{154}

Kuma a lokacin da fushin Musa ya kwanta, sai ya riki Allunan, kuma a cikinsu akwai shiriya da rahama ga wadanda su ga Ubangijinsu, masu jin tsoro ne.

A cikin bayanin ayar da ta gabata an bayyana cewa, bayan da annabi Musa (AS) ya dawo daga mikatinsa da ubanjiki day a kwashe tsawon kwanaki arba'in, a lokacin day a zo ya samu Bani Isra'ila suna bautar gunkin dan maraki a matsayin ubangiji a wurinsu, ganin haka sai ya yi fushi matuka ta yadda bacin ransa ya kasa boyuwa saboda ya ga mutanensa sun koma mushrikai bayan ya bar su a matsayin masu imani, saboda tsananin fushi har attaura ta fadi daga hannunsa ba tare da ya Ankara ba, amma daga bisani bayan da fushinsa ya safka bayan Bani Isra'ila sun gane kurensu, sai ya dauki attaura domin yi masu bayanin hukunce-hukuncen ubangiji da suke ciki, domin kuwa a cikinta ne shiriya da rahmar ubangiji take ga wadanda suka yi imani da ubangiji daga cikin mutanen lokacinsa.

Darasin da za a dauka a nan shi ne:

Tsoron ubangiji shi ne babban abin da ke bude wa mutum kofofin rahamarsa, domin kuwa babu wani mahaluki da ya cancanci a ji tsoronsa tare da rusuna masa face Allah ubangijin dukkanin talikai.

Aya ta (155) surat A'araf

وَاخْتَارَ مُوسَى قَوْمَهُ سَبْعِينَ رَجُلاً لِّمِيقَاتِنَا فَلَمَّا أَخَذَتْهُمُ الرَّجْفَةُ قَالَ رَبِّ لَوْ شِئْتَ أَهْلَكْتَهُم مِّن قَبْلُ وَإِيَّايَ أَتُهْلِكُنَا بِمَا فَعَلَ السُّفَهَاء مِنَّا إِنْ هِيَ إِلاَّ فِتْنَتُكَ تُضِلُّ بِهَا مَن تَشَاء وَتَهْدِي مَن تَشَاء أَنتَ وَلِيُّنَا فَاغْفِرْ لَنَا وَارْحَمْنَا وَأَنتَ خَيْرُ الْغَافِرِينَ{155}

Kuma Musa ya zabi mutanensa maza saba'in domin mikatinmu. To, a lokacin da tsawa ta kama su, ya ce: "Yã Ubangijina! Dã Kã so, dã Kã halakar da su daga gabãni, sũ da ni. Shin zã Kahalaka mu, sabõda abin da wãwãyen daga gare mu suka aikata? Ba ta zama ba fãce fitinarka Kanã batarwa, da ita wanda ka so, kuma kanã shiryarwa da ita wanda ka so; Kai ne Majibincinmu. Ka gãfarta mana; kuma Ka yi mana rahama, domin kuwa Kai ne Mafi alhẽrin mãsu gãfara."

Duk da irin mujizozin da annabi Musa (AS) ya nuna ma bani Isra'ila, amma mafi yawansu suna nuna shakkunsu matuka dangane da gaskiyar annabi Musa, inda suka bukaci day a nuna musu Allah ko kuma ya yi Magana da su kamar yadda yake yi da annabi Musa, domin su tabbatar da cewa lallai shi Allah ne ya aiko annabi Musa da kasansa, saboda haka sai annabi Musa (AS) ya zabi fitattun mutane 70 daga cikinsu, wadada suka wakilci dukkanin Bani Isra'ila ya tafi da su zuwa dutsen Tur domin yin wani mikati.

A lokacin da suka je wurin mutanen sun bukaci annabi Musa da ya roki Allah ya bayyana musu kansa su gan shi da idanunsu, in kuma hakan ba za ta samu ba, to suna son su ji maganarsa kamar yadda annabi Musa ya gaya musu cewa yana yin zance da Allah. Allah madaukakin sarki ya yi zance da su kuma ya tabbatar musu da gaskiyar sakon annabci a kan annabi Musa (AS) mutanen suka ce sun ji, amma duk da haka suna dai son su ga Allah da idanunsu domin su tabbatar da cewa ba wani saddabaru ne aka yi musu ba, a nan take dutsen Tur ya fara girgiza da karfi, dukkansu suka mutu saboda tsananin tsoro da firgici.

Ganin haka sai annabi Musa ya kaskantar da kansa ga Allah yan amai rokonsa ya sake rayar da su, domin kuwa dukaknin mutanen saba'in zababbu ne daga cikin Bani Isra'ila, idan ya koma ba tare da su ba, to lallai zai fuskanci gagarumar matasala da mutanensa, sai allah ya karbi addu'ar annabi Musa ya sake rayar da su.

Darussan koyo a nan su ne:

1 – Annabawan Allah sukan yi aiki da zahirin abin da mutane suka fi sani domin tabbatar da hujja a kansu.

2 – Bala'oi suna zuwa ne a matsayin jarabawa daga Allah, domin tantance masu imani na gaskiya da kuma bara gurbi.

Aya ta (156) surat A'araf

وَاكْتُبْ لَنَا فِي هَـذِهِ الدُّنْيَا حَسَنَةً وَفِي الآخِرَةِ إِنَّا هُدْنَـا إِلَيْكَ قَالَ عَذَابِي أُصِيبُ بِهِ مَنْ أَشَاء وَرَحْمَتِي وَسِعَتْ كُلَّ شَيْءٍ فَسَأَكْتُبُهَا لِلَّذِينَ يَتَّقُونَ وَيُؤْتُونَ الزَّكَـاةَ وَالَّذِينَ هُم بِآيَاتِنَا يُؤْمِنُونَ{156}

"Kuma Ka rubũta mana alhẽri a cikin wannan dũniya, kuma a cikin Lãhira. Lalle ne mũ,mun tũba zuwa gare Ka." Ya ce: "Azãbata Inã sãmu da ita wanda na so, kuma rahamata, ta yalwaci dukan kõme. Sa'an nan zã ni rubũta ta ga wadanda suke yin takawa kuma sunã bãyar da zakka, da wadanda suke muminai ne da ãyõyinmu."

Wannan aya ci gaban addu'ar annabi Musa ne, yana rokon Allah da ya da shi da shi masu imani daga cikin al'ummarsa da kyakyawan lamari a duniya, da kuma kyakyawan sakamako a lahira. Allah madaukakin sarki ya amsa ma annabi Musa addu'arsa da cewa, azabarsa tana samun wanda ya ga dama, ma'ana wanda yaki shirya kuma tun asali ba ashirye yake da ya karbi shiriya ta ubangiji ba, domin kuwa rahamar Allah ta yalwaci komai sai dai wanda ya fitar da kansa daga cikinta, wato wadanda suka yi wa Allah girman kai da juya baya daga bin umurninsa. Allah ya yi alkawalin yin rahama da gafara a ranar kiyama bayinsa da suka yi taqawa, suka bayar da ahakkin Allah daga dukiyoyinsu sun amasu yin imani da dukkanin ayoyin Allah.

Ya zo a cikin ruwaya cewa, a lokacin da wannan ayar ta safka, shaidan da kansa ya rika kwadayin samun rahamar ubangiji, inda yake cewa tun da rahamar ubangiji ta yalwaci komai, to kenan shi ma zai iya samu rahamar Allah, duk kuwa da cewa sharadin samun rahama da gafara daga ubangiji shi ne taqawa, wanda kuma shaidan mabiyansa sun yi nisa da taqawa wato tsoron Allah.

Darussan da za a dauka a nan su ne:

1 – Daga annabawan Allah ne ake koyon yadda ake yin addu'a, suna rokon Allah alkharin duniya da na lahira.

2 – Rahamar Allah ta rinjayi fushinsa, saboda haka ne ma idan masu aikata laifuka na sabo suka tuba suka koma zuwa ga Allah tuba ta gaskiya, Allah yana karbarsu kuma ya gafarta musu.

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.

Suratul A'araf, Aya Ta 157-159 (Kashi Na 260)

Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat A'araf, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (157) surat A’araf

الَّذِينَ يَتَّبِعُونَ الرَّسُولَ النَّبِيَّ الأُمِّيَّ الَّذِي يَجِدُونَهُ مَكْتُوباً عِندَهُمْ فِي التَّوْرَاةِ وَالإِنْجِيلِ يَأْمُرُهُم بِالْمَعْرُوفِ وَيَنْهَاهُمْ عَنِ الْمُنكَرِ وَيُحِلُّ لَهُمُ الطَّيِّبَاتِ وَيُحَرِّمُ عَلَيْهِمُ الْخَبَآئِثَ وَيَضَعُ عَنْهُمْ إِصْرَهُمْ وَالأَغْلاَلَ الَّتِي كَانَتْ عَلَيْهِمْ فَالَّذِينَ آمَنُواْ بِهِ وَعَزَّرُوهُ وَنَصَرُوهُ وَاتَّبَعُواْ النُّورَ الَّذِيَ أُنزِلَ مَعَهُ أُوْلَـئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ{157}

"Wadanda suke suna bin Manzo Annabi Ummiyyi, wanda suke samun sa rubuce a wurinsu, a cikin Attaura da Linjĩla, yana umurtar su da aikin alheri yana kuma hana su ga yin mugun aiki, yana kuma halatta musu (abubuwa) tsarkaka yana kuma haramta musu najasa, yana kuma sauke musu nauye-nauyensu da hukumce-hukumcen da suka kasance a kansu. Saboda haka wadanda suka ba da gaskiya da shim suka kuma girmama shi, suka kuma taimake shi, suka kuma bi hasken da aka saukar a tare da shi, to wadannan su ne marabauta.

A cikin shirin da ya gabata, an ambaci ayoyin da suka yi bayani kan wasu daga cikin mutanen annabi Musa (AS) da suka yi shishigi a lokacin da suka tafi mikati tare da shi, kuma fushin Allah ya safka kansu sakamakon abin da suka aikata, amma annabi Musa ya yi addu'a tare da neman rahama da gafarar Allah, kuma Allah ya karbi addu’arsa, kuma ya yi alkawari na rahama ga wadanda suka yi imani suka yi aiki na gari daga cikin Bani Isra’ila.

Wannan ayar mai albarka tana yin ishara da cewa, wannan rahamar ta ubanji za ta hada da ahlul kitabi daga yahudawa da kiritoci da suke rayuwa a lokacin manzon Allah (SAW) wadanda suka yi imani da manzonsa Muhammad (SAW) kuma suka bi shi a kan tafarkinsa, kamar yadda suka samu sunansa a cikin littafan da aka safkar musu na attaura da Injila, shi ne manzon da yake halasta musu ababe masu kyau, yake haramta musu munana, yake kiransu zuwa akidar kadaita Allah da barin surkulle da munanan dabi’u, wadanda sukabi shi to za su samu ramahama da gafarar ubangiji, da kuma kyakyawan sakamako na aljanna a lahira.

Darussan da za a koya a nan su ne:

1 – Annabawan da suka gabata sun yi bushara da zuwa manzon Allah Muhammad (SAW) tare da ambaton sunansa da kuma alamu na bayyanarsa, kamar yadda ya zo a cikin littafan attauara da injila.

2 – Annabawan Allah sun ne domin su ‘yantar da mutane daga bautar duk wani abun da ba Allah ba, zuwa ga bautar Allah wanda ya cancanci bautar dukkanin talikai.

3 – Yin imani da annabawan Allah shi kadai ba zai wadatar ba, dole ne a girmama su da girmma sakonsu da kuma kare su da kare sakonsu.

Aya ta (158) surat A’araf

قُلْ يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنِّي رَسُولُ اللّهِ إِلَيْكُمْ جَمِيعاً الَّذِي لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ لا إِلَـهَ إِلاَّ هُوَ يُحْيِـي وَيُمِيتُ فَآمِنُواْ بِاللّهِ وَرَسُولِهِ النَّبِيِّ الأُمِّيِّ الَّذِي يُؤْمِنُ بِاللّهِ وَكَلِمَاتِهِ وَاتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ{158}

Ka ce: "Yã kũ mutãne! Lalle ne nĩ manzon Allah ne zuwa gare ku gabã daya. (Allah) Wanda Yake Shĩ ne da mulkin sammai da kasa; Bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Yanã rãyarwa kuma Yanã matarwa, sai ku yi ĩmãni daAllah da Manzonsa, Annabi Ummiyyi, wanda yake yin ĩmãni da Allah da kalmominsa; ku bĩ shi, tsammãninku kunã shiryuwa."

Wannan aya tana yin ishara da cewa manzon Allah manzo ne zuwa ga dukkanin mutane duniya baki daya, ba annabi ne da aiko zuwa ga kabilar larabawa ko mutanen hijaz ba, shi mai shiryarwa ne zuwa ga hasken shiriya, shi mai kira ne zuwa ga kadaita Allah wanda ya halicci sammai da kassai kuma yake da mulkinsu.

Allah madaukakin sarki ne da kansa ya bayar da umurni ga dukkanin mutane duniya da cewa, su yi imni da Allah da manzonsa Muhammad, kuma su bi wannan mannan manzo mai tsarki, idan sun yi haka to lallai sun samu garanti na shiriya.

Darussan koyo daga wannan aya:

1 – Bayan bayyanar addinin musulunci, abin da ya rataya kan mabiya addinai na annabawan Allah kafin zuwan musulunci shi ne su yi imani da manzon karshe kamar yadda ak umurce su da hakan a cikin littafansu, su yi biyayya gare shi shi ne bin annabawansu, domin kuwa ko da annabawansu suna raye a lokacin da manzon Allah Muhammad ya bayyana, to su ma za su yi imani da shi kuma su zam mabiya a gare shi.

Biyayya ga koyarwar kur’ani na tafiya ne da koyarwar sunnar manzon Allah da iyalan gidansa, yin watsi da daya daga cikinsu tamkar yin watsi da sauran ne, domin kuwa manzon Allah shi ne mai yin bayani kan kan kur’ani, haka nan kuma ya umurce mu da mu yi koyi dakur’ani da kuma sunnarsa ta hanyar yin koyi da iyalan gidansa bayan fakuwarsa, idan muka yi haka to mun yi riko da addinin da ya zo da shi.

Aya ta (159) surat A’araf

وَمِن قَوْمِ مُوسَى أُمَّةٌ يَهْدُونَ بِالْحَقِّ وَبِهِ يَعْدِلُونَ{159}

Kuma daga mutãnen Mũsã akwai al'umma sunã shiryarwa da gaskiya, kuma da ita suke yin ãdalci.

Kur’ani mai tsarki yana yabon wasu daga cikin mutanen annabi Musa (AS) wato Bani Isra’ila, wadanda suka kasance sun yi imani na gaskiya a lokacinsa sabanin mafi yawan yahudawan Bani Isra’ila, wadanda aka sansu da girman kai da zalunci da kin gaskiya, da kuma raina sauran al’ummomi.

Wadannan ‘yan kadan daga cikin cikinsu da kur’ani yake yin magana a kansu, suna kasance ma’abota gaskiya da adalci,kuma suna yin kira zuwa ga bin tafarkin kadaita Allah madaukakin sarki, kamar dai yadda Allah ya umurce su a cikin littafin attaura wanda aka baiwa annabi Musa (AS)

Irin wadannan yahudawa da Allah ya yabe su an samu irinsu a lokacin bayyanar manzon Allah (SAW) kuma sun yi imani da shi tare da mika wuya ga umurninsa, to wadannan nan suna da kyakyawan sakamako a wajen Allah.

Darussan da za adauka a nan su ne:

1 – A lokacin da muke magana kan wadanda muke da sabanin addini da su to mu yi adalci ka da mu yi kudin goro a kan kowannensu, domin kuwa haka kur’ani ya koyar da mu a cikin ayar da ta gabata, duk da irin barnar da yahudawan Bani Isra’ila suka yi a bayan kasa da kur’ani ya ba mu labarin wani abu kadan daga hakan, amma kuma a lokaci guda kur’ani ya gaya mana cewa akwai wasu na gari daga cikinsu wadanda suka yi imani na gaskiya.

2 – A lokacin da muke kiran wasu zuwa ga gaskiya da adalci, to wajibi ne mu fara zama mutane masu gaskiya da adalci.

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.

Suratul A'araf, Aya Ta 160-162 (Kashi Na 261)

Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat A'araf, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (160) surat A’araf

وَقَطَّعْنَاهُمُ اثْنَتَيْ عَشْرَةَ أَسْبَاطاً أُمَماً وَأَوْحَيْنَا إِلَى مُوسَى إِذِ اسْتَسْقَاهُ قَوْمُهُ أَنِ اضْرِب بِّعَصَاكَ الْحَجَرَ فَانبَجَسَتْ مِنْهُ اثْنَتَا عَشْرَةَ عَيْناً قَدْ عَلِمَ كُلُّ أُنَاسٍ مَّشْرَبَهُمْ وَظَلَّلْنَا عَلَيْهِمُ الْغَمَامَ وَأَنزَلْنَا عَلَيْهِمُ الْمَنَّ وَالسَّلْوَى كُلُواْ مِن طَيِّبَاتِ مَا رَزَقْنَاكُمْ وَمَا ظَلَمُونَا وَلَـكِن كَانُواْ أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ{160}

Kuma Muka rarraba su sibdi gõma shã biyu al'ummai. Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã a lõkacin da mutãnensa suka nẽme shi ga shãyarwa, cẽwa: "Ka dauki dũtsen da sandarka."Sai marmaro gõma shã biyu suka bubbuga daga gare shi: Lalle ne kõwadanne mutãne sun san mashãyarsu. Kuma Muka saukar da darba da tantabaru a kansu."Ku ci daga mãsu dãdin abin da Muka azurta ku."Kuma ba su zãluncẽ mu ba; amma kansu suke zãlunta.

Kalmar Bani Isra’ila a cikin harshen Hibru na nufin bawan Allah, wanda kuma ake nufi da hakan shi ne annabi Yakub (AS) idan aka ce Bani Isra’ila ana nufin ‘ya’yan annabi Yakub su 12, wanda kowanne daga cikinsu jigo na al’ummar Bani Isra’ila, ta yadda wannan suna ya bi har jikokinsu.

Wannan aya mai albarka tana bayyana mana cewa, Sanda na daga cikin fitattun mu’ujizozin annabi Musa (AS) wadda da ita ce ya yi abubuwa da dama, wadanda suke tabbatar da annabcinsa, domin kuwa a cikin wasu ayoyin kur’ani ya zo cewa annabi Musa (AS) ya fara tabbatar da mu’ujizarsa ne gaban Fir’auna da wannan sanda, kuma ta hanyar ganin wannan mu’ujizar masu yi ma fir’ana tsafe-tsafe suka gane gaskiya suka koma bangaren annabi Musa.

Haka nan kuma da wannan sandar annabi Musa ya fasa kogin Nilu a lokacin da Fir’ana da mutanen suka biyo annabi Musa suna nufin halaka shi tare da wadanda suka yi imani da shi, kuma tsallake kogin cikin taimakon Allah, daga bisdani kuma bayan fir’auna da mutanensa sun kuma cikin kogin Allah madaukakin sarki ya dawo da ruwan kogin kamar yadda yake, fir’auna da mutanensa suka halaka.

Annabi Musa (AS) ya sanya sandarsa ya fasa dutsen Tur inda idanun ruwa goma sha biyu suka bayyana ga Bani Isra’ila alokacin da suke bukatar ruwa, Allah madaukakin sarki ya yi Bani Isra’ila ni’imomi masu tarin yawa, da suka hada da safkar da giza-gizai domin kare su daga zafin rana, safkar musu da abinci da soyayyaun ‘yan shila, amma duk da haka da dama daga cikinsu ba su yi imani na gakiya da annabi Musa ba, inda suka ci gaba da saba umurninsa da muzguna masa, bisa zaton cewa abin da suke yi suna cutar da annabi Musa ne, alhali kuwa ba su sani ba kansu suka cutar da hakan.

Darussan da za a koya a nan su ne :

1 – Yin tawassuli da bayin Allah domin samun biyan bukata ba shi ne ke tabbatar da imanin mutum ba, domin kuwa Bani Isra’ila sun yi tawassuli da annabi Musa (AS) kan abubuwan da suke bukata kuma Allah ya biya musu bukatunsu albarkacin annabi Musa, alhali kuma da yawansu ba masu imani ba ne.

2 – Allah madaukakin sarki shi ne yake da hakkin halasta wa ko haramta ma bayinsa, kuma halasdin Allah shi ne halas a wurin annabawansa da bayinsa salihai, haka kuma haram dinsa yake a wurinsu, a lokacuin da wani yake karbar halasci ko harmci daga wani ba Allah ba, to a lokacin ya shiga dirkaniya.

Ayoyi na (161) da (162) surat A’araf

وَإِذْ قِيلَ لَهُمُ اسْكُنُواْ هَـذِهِ الْقَرْيَةَ وَكُلُواْ مِنْهَا حَيْثُ شِئْتُمْ وَقُولُواْ حِطَّةٌ وَادْخُلُواْ الْبَابَ سُجَّداً نَّغْفِرْ لَكُمْ خَطِيئَاتِكُمْ سَنَزِيدُ الْمُحْسِنِينَ{161} فَبَدَّلَ الَّذِينَ ظَلَمُواْ مِنْهُمْ قَوْلاً غَيْرَ الَّذِي قِيلَ لَهُمْ فَأَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ رِجْزاً مِّنَ السَّمَاءِ بِمَا كَانُواْ يَظْلِمُونَ{162}

Kuma a lõkacin da aka ce masu: "Ku zauna ga wannan alkarya, kuma ku ci daga gare ta inda kuke so, kuma ku ce: 'Saryarwa,' kuma ku shiga kõfa kuna mãsu sujada; Mu gãfarta muku laifuffukanku, kuma zã Mu kãra wa mãsu kyautatãwa."

Sai wadanda suka yi zãlunci daga gare su, suka musanya magana ba wadda aka ce musu ba, sai Muka aika azãba a kansu daga sama, sabõda abin da suka kasance sunã yi na zãlunci.

Bayan da Bani Isra’ila suka dandana azaba da wahalhalu da dimuwa sakamakon saba ma umurnin annabi Musa (AS) daga bisani Allah ya umurce da su shiga birnin Qods suna masu tawalu’u, suna masu sadda kawunansu kasa, tare da yin Istigfari da neman gafar ubangiji kan laifin da suka aikata na kin bin umurninsa daga annabi Musa (AS) idan suka yi haka to Allah zai gafarta musu wannan babban laifi da suka yi, amma Bani Isra’ila saboda tsananin tsaurin kai, sai suka shiga yin izgili da wannan umurnin na Allah, domin kuwa an ce su shiga birnin Qods suna masu suhada wato safklar da kawunansu kasa suna istigfari, sai suka shiga birnin suna masu yin tantado da kafafunsu, wato suka mike kafafunsu da daga kawunansu sama, maimakon fadin kalmar Hatta, wato neman gafarar Allah, sai suka rika fadin Hinta, wato alkama, saboda tsananin taurin kai da izgili ga ayoyin Allah.

Saboda wannan mummunan aiki na su sai Allah ya safka r musu musu da azba daga sama, kuma Allah bai zalunce su ba, domin kuwa ya yi musu dukkanin falala da ni’ima da ba su tazara, amma maimaikon yin amafani da damar da Allah ya basu wajen yin istigfari da samun rahamarsa da gafararsa, sai suka mayar da abin wani abu na izgili, saboda haka Allah bai zalunce su su ne suka zalunci kansu.

Darussan koyo a nan su ne :

1 – Yin istigfari yana baiwa mutum damar samun hanya ta komawa ga Allah, tare da samun afuwarsa.

2 – Allah madaukakin sarki yana baiwa bayinsa ni’imomi, amma aikata laifuka na saboda kan gusar da ni’imomin Allah a bayan kasa, tare da jawo fushinsa da azabarsa.

3 – Shiga wurare masu tsarki, da suka hada masallatai da wurare na ibada da ake ambaton Allah a acikinsu, na da ladubba na musamman, da suka hada da kaskantar da kai ga Allah da mika wuya gare shi, da tsarkakake bauta gare shi shi kadai.

4 – Ba alokacin annabi Musa (AS) ne ne kawai Bani Isra’ila suke yin Izgili da ayoyin Allah ba, har bayan wafatin annabi Musa sun ci gaba da yin haka, kuma har yanzu wasu daga cikin jikokinsu da suka wanzu suna ci gaba da yin girman kai irin na kakaninsu, tare da karyata ayoyin ubangiji da yin izgili a kansu.

5 – Dukkanin abin da mutum ya samu a lahira khairan ko sharan, sakmako ne abin da ya shuka a gidan duniya.

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.

Suratul A'araf, Aya Ta 163-166 (Kashi Na 262)

Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat A'araf, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (163) surat A’araf

واَسْأَلْهُمْ عَنِ الْقَرْيَةِ الَّتِي كَانَتْ حَاضِرَةَ الْبَحْرِ إِذْ يَعْدُونَ فِي السَّبْتِ إِذْ تَأْتِيهِمْ حِيتَانُهُمْ يَوْمَ سَبْتِهِمْ شُرَّعاً وَيَوْمَ لاَ يَسْبِتُونَ لاَ تَأْتِيهِمْ كَذَلِكَ نَبْلُوهُم بِمَا كَانُوا يَفْسُقُونَ{163}

Kuma ka tambaye su daga alkarya wadda ta kasance kusa ga tẽku, a lõkacin da suke kẽtare haddi a cikin Asabar, a lõkacin da kĩfãyensu suke je musu a rãnar Asabar jere. Kuma a rãnar da ba Asabar ba, bã su zuwa gare su; Kamar wancan ne Muke jarraba su da abin da suka kasance sunã yi na fãsikanci.

Daya daga cikin hukunce-hukuncen ubangiji da suke cikin addinin yahudawa shi ne hutu a ranar Asabar, wato a ranar ba za su yi wani aiki ba na kasuwanci da neman kudi sai dai ibada kawai. Wannan ne ya sanya har yanzu haka yahudawa suke daukar ranar Asabar a matsayin ranar hutu a wajensu.

Wannan ayar tana bayani ne kan wasu yahudawa da suke zaune a wata alkarya da ke gefen wani kogi, wanda kuma sana’arsu ita ce kamun kifi daga wannan kogi da ke gefen alkaryar, Allah madaukakin sarki ya jarrabi yahudawan da suke zaune a wannan wuri domin ganin yadda za su kiyaye dokokinsa.

A ranar Asabar ranar da ba su da hakkin da za su yi kamun kifi, sai kifaye su zo gefen kogi kowa na kallonsu amma babu damar kama su, domin rana ce da Allah ya haramta kamun kifi ga Bani Isra’ila, amma a sauran nakun mako wato ranakun da ba Asabar ba, sai kifayen su koma tsakiyar kogi, ta yadda sai an yi aikin wahala da yin iyo da koma a cikin kogin kafin a iya kama kifi. Wannan sai ya sanya su yin wata dubara da nufin kiyaye dokar hana kamun mifi a ranar Asabar, amma kuma a lokaci guda ba za su yi asarar kifin da ke taruwa gefen kogi a ranar Asabar ba.

Sun tona kananan tabkuna a gefen kogin, tare da jan wutsiyar ruwan kogin zuwa cikin tabkunan, a ranar Asabar kifayen na bin wutsiyar ruwa zuwa cikin tabkunan, sai su datse wutsiyar ruwan bayan kifayen sun shiga, a ranar lahadi wadda rana ce da aka halasta musu yin kamun kifi sai su su tattara kifayen da suke datse a cikin tabkunansu a ranar Asabar, bisa zaton cewa ba su kamun kifi a ranar Asabar ba amma kuma ba su asarar kifayen ranar Asabar ba.

To amma kur’ani mai tsarki ya bayyana wannan dubara ta su da cewa ba dubara ba ce, domin kuwa Allah ya san abin da suke aikatawa, kuma yin haka shishigi ne da karya dokarsa, domin kuwa zuwan kifayen a ranar Asabar a gefen kogi, da kuma rashin zuwansu a sauran ranaku duk yana hannun Allah ne, kuma ya yi hakan ne domin ya jarraba su ya ga shin za su iya yin hakuri su bi dokar Allah komai tsanani da wahala, amma suka fadi wannan jarabawa.

Darussan da za a dauka a nan su ne :

1 – Dubara ba ta kawai da aibun laifi a shar’ance, maimakon haka ma tana karama laifin muni ne, domin kuwa wanda yake aikata laifi na sabo kuma yake yin wata dubara domin baiwa kansa uzuri kan sabon da yake aiakatawa yafi muni a kan wanda yake jin cewa lallai sabo ne yake aiakatawa, domin kuwa shi zai iya tuba, alhali kuwa mai yin dubara domin samama kansa uzuri domin ya ci gaba da aikata sabon yana ganin ba za a kama shi da wannan laifin ba, saboda haka da wuya hankalinsa ya tafi zuwa ga tuba kan abin da yake aikatawa.

2 – Halasta abubuwa da kuma haramta su a cikin shari’a duk wani nau’i na jarabawar ubangiji, domin kuwa kamun kifi halas ne a wurin Bani Isra’ila, amma kuma an haramta musu shi a ranar Asabar, duk da cewa shi aikin na halas amma idan suka yi a ranar Asabar ya haramta.

Aya ta (164) surat A’araf

وَإِذَ قَالَتْ أُمَّةٌ مِّنْهُمْ لِمَ تَعِظُونَ قَوْماً اللّهُ مُهْلِكُهُمْ أَوْ مُعَذِّبُهُمْ عَذَاباً شَدِيداً قَالُواْ مَعْذِرَةً إِلَى رَبِّكُمْ وَلَعَلَّهُمْ يَتَّقُونَ{164}

Kuma a lõkacin da wata al'umma daga gare su ta ce: "Don me kuke yin wa'azi ga mutãne wadanda Allah Yake Mai halaka su kõ kuwa Mai yi musu azãba, azãba mai tsanani?" Suka ce: "Dõmin nẽman hanzari zuwa ga Ubangijinku, kuma tsammãninsu, sunã yin takawa."

Kur'ani mai tsarki ya kasa Bani Isra'ila zuwa kashi uku, kashi na farko su ne masu imani da suke yin nasiha ga masu bijire ma ayoyin Allah daga cikinsu. Kashi na biyu su ne wadanda suka yi imani amma ba su da mu da su yi nasiha ga marassa imani daga cikinsu ba, kashi na uku kuma su ne wadanda ba su yi imani ba, suna y iwa dokokin Allah hawan kawara yadda suka dama, da yi annabawan Allah izgili.

Wadanda suka yi imani amma ba su yin nasiha masu barna daga cikinsu, suna tambayar masu su yin nasiha da cewa; me ya sanya kuke bata lokacinku kuke yin nasiha ga mutanen da Allah zai halakar da su ko kuma zai azabtar da su azaba mai tsanani, sai suka ce musu abin da muke yi ba bata lokaci ba ne, domin kuwa wata kila nasihar ta sanya su shiryu, ko kuma su rage aikata barna, idan kuma duk ba su yi hakan ba, to mu daim un samu uzuri a wajen ubangiji cewa ba mu tare da abin da suke yi, kuma mun kira su zuwa ga tafarkin shiriya ba su saurare mu ba.

Darussan da za a dauka a nan su ne:

1 – Wasu daga cikin mutane ba su yin nasiha ga masu aikata barna, kuma suna nuna halin ko in kula dangane da yin nasiha a cikin jama'a kan aikata ayyuka na barna.

2 – Yin umurnin da kyakyawa da kuma yin hani daga aikata mummuna wajibi ne a kan muminai, domin rashin yin hakan shi ne babbar barna a cikin kowace al'umma.

Aya ta (165) da (166) a cikin surat A'araf

فَلَمَّا نَسُواْ مَا ذُكِّرُواْ بِهِ أَنجَيْنَا الَّذِينَ يَنْهَوْنَ عَنِ السُّوءِ وَأَخَذْنَا الَّذِينَ ظَلَمُواْ بِعَذَابٍ بَئِيسٍ بِمَا كَانُواْ يَفْسُقُونَ{165} فَلَمَّا عَتَوْاْ عَن مَّا نُهُواْ عَنْهُ قُلْنَا لَهُمْ كُونُواْ قِرَدَةً خَاسِئِينَ{166}

To, a lõkacin da suka manta da abin da aka tunãtar da su da shi, Mun tsĩrar da wadanda suke hani daga cũta, kuma Muka kãma wadanda suka yi zãlunci, da azãba mai tsanani dõmin abin da suka kasance sunã yi, na fasikanci.

Sa'an nan a lõkacin da suka yi girman kai daga barin abin da aka hana su daga gare shi, Muka ce musu: "Ku kasance birai kaskantattu."

A cikin bayanin aya da ta gabata an kasa Bani Isra'ila zuwa kashi uku, masu yin nasiha da wadanda ba su yin nasiha da kuma masuaikata barna. A lokacin da masu aikata barna suka yi watsi da nasiha da tunatarwa da aka yi musu, sai Allah y aya kama su sakamakon taurin kai da suka nuna wajen yin watsi da tafarkin gaskiya, haka nan kuma wadanda ba su yin nasiha kuma suke yin kira da a daina yin nasiha ga masu barna su ma azabar ta shafe su, sai masu tunatawar ne daga cikinsu kadai suka tsira.

Daga cikin irin azabar da Allah ya safkar kansu har da canja halittun wasu daga cikinsu, aka mayar da su kamar birai, kuma bayan wani dan lokaci suka mutu.

Darussan da za a iya dauka a nan su ne:

1 – Umurnin da kyakyawa da kuma hani daga mummuna, idan bai zama sanadiyar shiyar wasu ba, to aka zai zama sanadiyar kubutar mai yin hakan daga fushin ubangiji, tare da samun uzuri.

2 – Idan mutane suka daina yin tunatarwa da yin nasiha, to sun bude kofofin fushin ubangiji a kansu.

3 – A lokacin da mutum ya yi shiru kan zaluncin azzalumi ko barnar mai abarna, to shi ma abin da zai samu azzalumai da mabarnata zai iya shafarsa.

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.

Suratul A'araf, Aya Ta 167-169 (Kashi Na 263)

Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat A'araf, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.

Aya ta (167) surat A’araf

وَإِذْ تَأَذَّنَ رَبُّكَ لَيَبْعَثَنَّ عَلَيْهِمْ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ مَن يَسُومُهُمْ سُوءَ الْعَذَابِ إِنَّ رَبَّكَ لَسَرِيعُ الْعِقَابِ وَإِنَّهُ لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ{167}

Kuma a lõkacin da Ubangijinku ya sanar, lalle ne zã ya aika a kansu zuwa rãnar kiyãma, wanda zai dandana musu mummunar azãba, lalle ne Ubangijinka mai gaggawar ukũba ne, kuma shĩ hakĩka, Mai gãfara ne, Mai jin kai.

A cikin shirin da ya gabata an bayanin cewa daya daga cikin hukunce-hukuncen ubangiji da suke cikin addinin yahudawa shi ne hutu a ranar Asabar, wato a ranar ba za su yi wani aiki ba na kasuwanci da neman kudi sai dai ibada kawai, daga ciki kuwa har da masu kamun kifi daga cikinsu da aka haramta musu wannan aiki a ranar Asabar, amma wasu daga cikinsu sun gaban kansu wajen karya wannan doka ta Allah, inda suke kamun kifinsu a ranar Asabar amma ta hanyar dubura, domin kuwa suna haka ramuka gefen kogi a daren Asabar ta yadda ranar Asabar kifaye za su shiga cikin tarkonsu, a ranar lahadi sai su cire dukkanin kifayen da suka shiga tarkon.

Saboda wannan aiki na sabon Allah da yin hawan kawara kan dokokinsa, aka safkar musu da azaba, har ma wasu daga cikinsu aka mayar da su birai. Wannan ayar tana yin karin haske ne dangane da makomar wadanda suka yi watsi da dokokin Allah daga cikin Bani Isra’ila, suka yi izgili da dokokinsa da ke cikin Attaura, cewa Allah madaukakin sarki zai dora akansu wadanda za su ta gana musu azaba har zuwa tashin kiyama, matukar dai ba su tuba suka koma ga bin dokokin Allah ba.

Wannan ayar tana magana ne kan Bani Isra’ila, amma kuma irin wannan sunna ta Allah tana aiki a kan dukaknin al’ummomin da suka yi girman kai da bijire ma umurninsa. Darussan da za a iya dauka a nan su ne :

1 – Azzalumai daga Bani Isra’ila suna cikin kunci da tashin hankali da kuma rashin natsuwar zuci har zuwa tashin kiyama, matukar dai ba su yi imani na gaskiya ba.

2 – Jin tsoron azabar Allah da kuma kaunar rahmarsa, abubuwa ne guda biyu da suke cikin zuciyar mumini, wadanda suke karfafa imaninsa da Allah a kowane lokaci.

Aya ta (168) surat A’araf

وَقَطَّعْنَاهُمْ فِي الأَرْضِ أُمَماً مِّنْهُمُ الصَّالِحُونَ وَمِنْهُمْ دُونَ ذَلِكَ وَبَلَوْنَاهُمْ بِالْحَسَنَاتِ وَالسَّيِّئَاتِ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ{168}

Kuma muka yayyanka su a cikin kasa al'ummõmi, daga gare su akwai sãlihai, kuma daga gare su akwai wanda bã haka ba. Muka jarrabe su da abũbuwan alhẽri da na musĩfa; Tsammãninsu, sunã kõmõwa.

Ayar da ta gabaci wannan ta yi mana bayani ne kan wani nauyi na ladabtarwa da Allah yake yi Bani Isra’ila da suka ki bada gaskiya suna izgili da ayoyinsa, inda za su kasance cikin yanyi na damuwa da kunci har zuwa ranar kiyama.

Ita kuma wannan ayar mai albaraka tana bayyana bayahudawa da cewa al’umma ce da ke warwatse, ba su taba zama a matsayin al’umma guda daya ba. Duk kuwa da cewa akwai salihai kadan daga cikinsu, akwai kuma wadanda ba salohai ba, wadanda su ne suka fi yawa a cikin Bani Isra’ila, wannnan ne ya sanya idan ana magana a kansu sai rika yin amfani da lamirin masu rinjaye daga cikinsu wato batragurbinsu, amma kuma Allah yana sane da salihai daga cikinsu da kuma kyawawan ayyukansu.

Allah madaukakin sarki ya jarrabe su da abubuwa dadada da kuma marassa dadi domin ya ga yadda za su yi, shin hakan zai sanya marassa imani na gaskiya daga cikinsu su dawo kan hanya ko kuwa za su kara yin nisa da gaskiya ne. Darussan koyo a nan su ne :

1 – A lokacin da ake yin magana a kan wasu mutane da ake da sabani da su, to a yi adalci a kansu, kada a kauda kai daga kyawawan abubuwan da ke tattare da su, ko kuma mutanen kirki daga cikinsu.

2 – Daya daga cikin alamun cin jarabawar ubangiji shi ne tuba da komawa zuwa gare shi, tare da yin aiki da umurninsa da kuma nisantar sabonsa.

Aya ta (169) surat A’araf

فَخَلَفَ مِن بَعْدِهِمْ خَلْفٌ وَرِثُواْ الْكِتَابَ يَأْخُذُونَ عَرَضَ هَـذَا الأدْنَى وَيَقُولُونَ سَيُغْفَرُ لَنَا وَإِن يَأْتِهِمْ عَرَضٌ مِّثْلُهُ يَأْخُذُوهُ أَلَمْ يُؤْخَذْ عَلَيْهِم مِّيثَاقُ الْكِتَابِ أَن لاَّ يِقُولُواْ عَلَى اللّهِ إِلاَّ الْحَقَّ وَدَرَسُواْ مَا فِيهِ وَالدَّارُ الآخِرَةُ خَيْرٌ لِّلَّذِينَ يَتَّقُونَ أَفَلاَ تَعْقِلُونَ{169}

Sai wasu' yan bãya suka maye daga bãyansu, sun gaji Littãfin, sunã karbar sifar wannan mafi kaskanci sunã cẽwa: "Zã a gãfarta mana. "Iadan kuma wata sifa irinta ta zo, za su karbe ta. Shin, ba a karbi alkawarin Littãfi ba a kansu cẽwa kada su fada ga Allah fãce gaskiya, alhãli kuwa sun karanta abin da yake a cikinsa, kuma gidan lãhira ne mafi alhẽri ga wanda ya yi takawa? Shin, bã zã ku hankalta ba?

Alkur’ani mai tsarki yana bayar da bayani kan yadda Bani Isra’ila a lokacin Musa suke yin girman kai daga bin littafin Allah, wanda annabi Musa (AS) ya zo da shi, haka nan kuma da ma wasu annabawan wadanda Allah ya aiko musu, saboda rashin bin annabawan Allah ne suka fada cikin dirkaniya.

ya’yansu da jikokinsu da suka zo bayansu, sun samu labari kan abubuwan da suka faru da iyayensu da kakanninsu saboda kin bin annabawan Allah dama cutar da su da suka rikayi har ma da kashe su a wasu lokuta, amma kuma hakan bai sanya ‘ya’yansu da jikokinsu yin imani da tafarkin gaskiya ba, su ma sun ci gaba da bin tafarkin iyayensu da kakanninsu ne.

Suna bayani kan dokokin Allah da ke cikin littafan annabawansu, sun san mene ne halas da haram, sun san mene ne za su aikata su samu yardar Allah, da kuma abin da za su aikata ya yi sanadiyar jefa su cikin fushinsa, suna da labarin lahira a cikin littafansu, amma dai duk da hakan sun zabi su bi son ransu, sun zabi duniya a kan lahira, sun zabi girman kai da izgili da ayoyin Allah maimakon yin imani da tawalu’u da kaskantar da kai a gaban ubangiji, kuma a lokaci guda suna ganin cewa su ne zababbu a wajen Allah fiye da sauran dukaknin mutane da al’ummomin duniya.

Wannan ne ma ya sanya suke ganin cewa koda ba su bi allah ba kuma ba su dokokinsa ba, to za a gafarta musu, alhali suna labarin wadanda suka gabace su da kuma abin da ya same su saboda kin bin umurnin Allah, an riki alkawali daga gare su kan cewa ba su danganta wani da Allah ba face abin da yake gaskiya, kuma Allah ya gaya musu cewa wadanda suka ji tsoransa a gidan duniya ne kawai suke da rabo a lahira.

Darussan koyo a nan su ne :

1 – Shagaltuwa da lamarin duniya kawai da yin saku-saku da lamarin addini ko kuma watsi da shi, hakan na kai mutum ga rafka da sha’anin lahira.

2 – A lokacin da mutum yake fatar samun rahama da gafar ubangiji to ya hada da aiki na gari, domin kuwa abubuwa biyu ne da suke tafiya tare da juna.

Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.

Suratul A'araf, Aya Ta 170-174 (Kashi Na 264)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.

To sai a saurari karatun aya ta 170 a cikin suratun A'araf kamar haka:

وَالَّذِينَ يُمَسَّكُونَ بِالْكِتَابِ وَأَقَامُواْ الصَّلاَةَ إِنَّا لاَ نُضِيعُ أَجْرَ الْمُصْلِحِينَ{170}

170- Kuma wadanda suke rikẽwa da laittãfi kuma suka tsayar da salla, lalle ne Mũ, bã Mu tõzarta lãdar mãsu gyãrãwa.

Idan kuna tuni a shirin da ya gabata mun kawo bayanin yadda kur'ani ya soki lamirin ma'abuta littafi da Allah ya sabko amma sabo da kwadayin abin duniya suka yi watsa da dokokin Allah da kin aiki da su,to ida wannan aya sabanin waccen ce domin kuwa ta jinjinawa ne ga wadanda suka yi riko da littafin Allah da aiki da dokokin Allah da tsaida salla a matsayinta na gimshikin addini kamar yadda ya zo a cikin hadisin ma'aikin Allah kuma suna fitar da zakka kuma suna da matsayi mai girma da daukaka kamar yadda Kur'ani ya ambato su da girmama su girmamawa.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Harda da karatun kur'ani kadai bai wadatar ba ana bukatar aiki da shi da dokokin da ke cikinsa domin samin tsira da sa'ada.

2-Gyara na gaskiya a daidaiku ku a tsakanin jama'a shi ne aiki da dokokin addini ba wai raya gyara al'umma ba tare da aiki da dokokin Allah ba wannan ba za a kai ga nasara ba.

To sai a saurari karatun aya ta 171 a cikin suratun A'araf kamar haka:

وَإِذ نَتَقْنَا الْجَبَلَ فَوْقَهُمْ كَأَنَّهُ ظُلَّةٌ وَظَنُّواْ أَنَّهُ وَاقِعٌ بِهِمْ خُذُواْ مَا آتَيْنَاكُم بِقُوَّةٍ وَاذْكُرُواْ مَا فِيهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ{171}

171- Kuma a lõkacin da muka daukaka dũtse sama da su, kumar dai shi girgije ne, kuma suka hakkake, lalle ne shĩ, mai fãduwa ne a gare su, (aka ce): "Ku karbi abin da Muka kãwo muku da karfi, kuma ku tuna abin da yake a cikinsa, tsammãninku kunã yin takawa."

Wannan ita ce aya ta karshe da ke bayani kan Bani Isra'ila a cikin suratul A'araf kuma tana nuni ne da mu'ujiza daga Allah ga Annabi Musa (AS) da kuma Maryam da cewa; lokacin da Annabi Musa (AS) ya komo daga tutsen dur dauke da dokokin Allah zuwa ga mutanansa.sai bani Isra'ila sun nuna masa adawa karara da bijirewa dokokin Allah.Domin azabtar da su sai Allah ya dauke wannan dutse da daura shi saman kansu tamkar zai fada masu sai tsora ya kama su suka fadi masu sujjada da fadar yin da'a amma wasu daga cikinsu sun koma ga kafircinsu.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa uku akalla:

1-Wani lokaci Allah yana nuna karfi da kudurarsa kan mutane domin fadakar da su .

2-Ya kamata mu yi riko da littafin Allah riko n agaskiya ta hanyar aiki da shi.

3-Sanin dokokin Allah bai wadatar ba dole sai an hada da aiki da tunatarwa don kar a sha'afa.

To sai a saurari karatun aya ta 172 zuwa 174 a cikin suratun A'araf kamar haka:

وَإِذْ أَخَذَ رَبُّكَ مِن بَنِي آدَمَ مِن ظُهُورِهِمْ ذُرِّيَّتَهُمْ وَأَشْهَدَهُمْ عَلَى أَنفُسِهِمْ أَلَسْتُ بِرَبِّكُمْ قَالُواْ بَلَى شَهِدْنَا أَن تَقُولُواْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ إِنَّا كُنَّا عَنْ هَذَا غَافِلِينَ{172} أَوْ تَقُولُواْ إِنَّمَا أَشْرَكَ آبَاؤُنَا مِن قَبْلُ وَكُنَّا ذُرِّيَّةً مِّن بَعْدِهِمْ أَفَتُهْلِكُنَا بِمَا فَعَلَ الْمُبْطِلُونَ{173} وَكَذَلِكَ نُفَصِّلُ الآيَاتِ وَلَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ{174}

172 - Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya karbi (alkawari) daga diyan Ãdam, daga bãyayyakinsu, a zuriyarsu, kuma Ya shaidar da su a kan rãyukansu, (Ya ce): "Shin, bã Nĩ ne Ubangijinku ba?" Suka ce: "Na'am! Mun yi shaida!" (ya ce): "Kada ku ce a Rãnar Kiyãma: Lalle ne mũ, daga wannan, gafalallu ne." 173- Kõ kuwa ku ce: "Abin sani kawai, ubanninmu suka yi shirki daga farko, kuma mũ, mun kasance zũriya daga bãyansu. Shin fa,Kanã halaka mu, sabõda abin da mãsu bãtãwa suka aikata?" 174- Kuma kamar haka Muke rarrabe ãyõyi, daki-daki; tsammãninsu, sunã kõmõwa.

Wadannan ayoyi na nuni da bukatuwar mutum da Ubangijinsa wani abu ne da babu makawa da kuma nuna matsayin Allah da yadda wajibcin bauta masa kuma kowa yana mika wuya ga Mahaliccinsa da firtawa da bakinsa a ranar tashin kiyama inda allah sai yi wa kowa tambaya kan alkawalin da ya dauka kafin zuwansa wannan duniya na tauhidi da kadaita Allah da bauta kuma kuwa ana haifarsa ne kan wannan tafarki amma da zarar ya shigo duniya sai ya manta da sha'afa ko uwayansa da al'ummar da yake rayuwa cikinta sun taimaka masa wajan sabawa wannan alkawali da ya dauka. Nan fa zai yi tsuru-tsuru ya kasa amsa wannan tambaya.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Abu ne da ya dace Mahalicci ya tambayi bayunsa kan wani abu domin kafa masu hujja.

2- Girmama magabata da uwaye da shugabanni kar ya sa mu sabawa bin tafarki na gaskiya da bin akida ta bata da tunani mai tsarki.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul A'araf, Aya Ta 175-178 (Kashi Na 265)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.

To sai a saurari karatun aya ta 175 a cikin suratun A'araf kamar haka:

وَاتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ الَّذِيَ آتَيْنَاهُ آيَاتِنَا فَانسَلَخَ مِنْهَا فَأَتْبَعَهُ الشَّيْطَانُ فَكَانَ مِنَ الْغَاوِينَ{175}

175- Ka karanta a kansu lãbãrin wanda Muka kãwo masa ãyõyinMu, sai ya sãbule daga gare su, sai shaidan ya bi shi, sai ya kasance a cikin halakakku.

Wannan aya tana nuni ne kan wani masani daga bani Isra'ila da ake kira Balam Ba'ura Ko dan ba'ura da hausa wanda da farko yana na sahun gaba-gaba daga cikin sahabban Annabi Musa (AS) amma ta hanayr waswasin shaidan ya yi rida da bin hanyar fir'auna inda dukiya da neman duniya da mukamin gidan sarautar Fir'auna ya rinjaye shi inda daga karshe ya bijirewa Annabi Musa da hakan ya kai karshensa ya munana kamar yadda bayaninsa ya zo a cikin Attaura babi na ashirin da biyu.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa uku akalla:

1-Hadarin kwadayin duniya hatta masana addini yana yi masu barazana kamar yadda abin da ya faru da dan ba'ura da hakan ya zama darasi ga dukan masana da malamai.

2-kar mu kasance masu girman kai da jiji da kai ko nuna wata tsiya muke mu kara jin tsauran Allah a kullum.

3-Duk lokacin da aka bar hanyar Allah za a fada kan ta Shaidan ne da zama bawansa ko da kuwa masani ne zai iya fadawa wannan tarko.

To sai a saurari karatun aya ta 176 a cikin suratun A'araf kamar haka:

وَلَوْ شِئْنَا لَرَفَعْنَاهُ بِهَا وَلَـكِنَّهُ أَخْلَدَ إِلَى الأَرْضِ وَاتَّبَعَ هَوَاهُ فَمَثَلُهُ كَمَثَلِ الْكَلْبِ إِن تَحْمِلْ عَلَيْهِ يَلْهَثْ أَوْ تَتْرُكْهُ يَلْهَث ذَّلِكَ مَثَلُ الْقَوْمِ الَّذِينَ كَذَّبُواْ بِآيَاتِنَا فَاقْصُصِ الْقَصَصَ لَعَلَّهُمْ يَتَفَكَّرُونَ{176}

176- Kuma dã Mun so, da Mun daukakã shi da su, kuma amma shĩ, ya nẽmi dawwama a cikin kasa, kuma ya bi son zũciyarsa. To, misãlinsa kamar misãlin kare ne, idan ka yi dauki a kansa ya yi lallage, kõ kuwa ka bar shi sai ya yi lallage, wannan ne misãlin mutãne wadanda suka karyata game da ãyõyinMu: Ka jẽranta karãtun lãbãrun; tsammãninsu sunã tunãni.

Allah madaukakin sarki ya so ya daukaka wannan bawon nasa da ba shi matsayi mai girma amma sai ya kaskantar da kansa da bin son zucciyarsa da ransa domin Allah ya samar masa da yanayi na cikar kamala da daukaka duniya da lahira ga ilimi da sani da ya ba shi amma sai ya kasa isa ga ainahin inda ya kamata ya isa saboda kwadayin duniya da jiji da kai sai ya fada hanyar shaidan ta bata da ya kwadaitar da shi mummunar hanya.Daga cikin mutane akwai mutane hudu da suke gafala arayuwa kamar yadda kur'ani ya yi nuni kansu.Na farkonsu masani mai kwadayin duniya wanda ba ya aiki da iliminsa wanda zai zama tamkar kurma a lokacin fadin gaskiya da aiki da sanin da yake da shi ,sai kuma mai kwadayin makami da daukaka wanda ba ya koshi ya kuma hadu da girman kai. Ma'aikin Allah na cewa: duk wanda yake da ilimi mai yawa amma shiriyarsa ba ta karuwa to wannan ilimi nasa zai yi sanadiyar nisantarsa da Allah.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa uku akalla:

1-ilimin da sanin Ayoyin Allah na daukaka mutum da matsayinsa da sharadin baya da kwadayin duniya.

2-Malaman addini idan sunada kwadayi da son duniya suna iya karyata ayoyin Allah da shiga sahun kafirai.

3-Tarihin rayuwar wadanda suka gabace mu ta zame mana darasi.

To sai a saurari karatun aya ta 177 da 178 a cikin suratun A'araf kamar haka:

سَاء مَثَلاً الْقَوْمُ الَّذِينَ كَذَّبُواْ بِآيَاتِنَا وَأَنفُسَهُمْ كَانُواْ يَظْلِمُونَ{177} مَن يَهْدِ اللّهُ فَهُوَ الْمُهْتَدِي وَمَن يُضْلِلْ فَأُوْلَـئِكَ هُمُ الْخَاسِرُونَ{178}

177- Tir da zama misãli, mutãnen da suka karyata game da ãyõyinMu, kuma kansu suka kasance sunã zãlunta. 178- Wanda Allah Ya shiryar, to, shĩ ne Mai shiryuwa, kuma wanda Ya batar, to, wadannan sũ ne mãsu hasãra.

Kur'ani bayan bayanin abin da ya faru da Bal'am Ba'ura .Sai ya bada misali da hannunka mai sanda ga kowa cewa; duk wanda ya karyata ayoyin Allah to ya saurari mummunar makoma da sakamako kuma kar mu yi zaton mun cuci Allah da addininsa a'a suna cutar da kansu ne da nisantar rahama da lutifin Allah. Dalili duk wanda ya karyata gaskiya zai rasa shiriya daga Allah kuma wannan shi ne rashi da tabewa babba ga dan adam. Duk da cewa shiriya da tabewa suna karkashin iko da kudurar Allah amma yana tafiyar da su karkashin dalili da tsari da kuma rahamarsa da hikimarsa da zai bawa mutum damar ga kamala ko akasin haka kuma Allah ba ya amfani da karffi ko lutinsa wajan tilasta mutum bin da zabin abin da ya sabawa zuciya da tunaninsa.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa uku akalla:

1- Babban kafirci shi ne kafircewa zucciya da kin karbar gaskiya saboda son rai.

2-Imani ko kafircinmu ba ya tasiri ga Allah domin ba ya bukatuwa da komi sai dai mune masu bukatuwa a gare shi.

3-Ilimi shi daya ba ya kai mutum ga shiriya da samin tsira sai mutum ya gama da aiki da hakan zai kai shi da hanyar shiriya daga Allah da lutifinsa.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul A'araf, Aya Ta 179-183 (Kashi Na 266)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.

To sai a saurari karatun aya ta 179 a cikin suratun A'araf kamar haka:

وَلَقَدْ ذَرَأْنَا لِجَهَنَّمَ كَثِيراً مِّنَ الْجِنِّ وَالإِنسِ لَهُمْ قُلُوبٌ لاَّ يَفْقَهُونَ بِهَا وَلَهُمْ أَعْيُنٌ لاَّ يُبْصِرُونَ بِهَا وَلَهُمْ آذَانٌ لاَّ يَسْمَعُونَ بِهَا أُوْلَـئِكَ كَالأَنْعَامِ بَلْ هُمْ أَضَلُّ أُوْلَـئِكَ هُمُ الْغَافِلُونَ{179}

179- Kuma lalle ne, hakĩka, Mun halitta sabõda Jahannama, mãsu yawa daga aljannu da mutãne, sunã da zukãta, ba su fahimta da su, kuma sunã da idãnu, bã su gani da su, kuma sunã da kunnuwa, ba su ji da su; wadancan kamar bisãshe suke. Ã'a, sũ ne mafi bacẽwa; Wadancan sũ ne gafalallu.

Babban dalilin da burin halittar dan adam shi ne isa ga kamala kuma wannan ya sa Allah ya mallaka masa duk wata dama da zabi .Ya sanya masa ido da kunne da hankali domin ganewa nsaurara da bin gaskiya amma akwai wasu da Allah ya basu duka wannan ni'ima amma kash ba su amfani da su ko suna amfani da sune ta hanyoyin dab a su dace bad a sabawa hanyar Allah da hakan ke sanadiyar ganuwa da mummunan sakamako da karshe .Hatta dabbobi dab a a bas u wannan ni'ima ta hankali ba suna bin sha'afarsu da nuna karfi ba hankali saboda haka aka halicce su amma shi mutum ya kebanta da dabba amma idan mutum ba yi aiki da hankali da ni'imar da Allah ya ba shi ba zai kaskantar da kansa hatta dabba ta fi shi. Saboda sha'afar da ya yi ya kasa aiki da hakalinsa da tunaninsa wajan karba da bin gaskiya kamar yadda wannan aya ke cewa;gaskiya kamar mutum nada wasu alamomi na gane ta ,mutum ya rataya a kansa ya yi aiki da wadannan alamomi domin gane gaskiya da binta amma idan ya kaucewa hanyar gaskiya zai fada da shiga cikin wutar jahannama.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Kar mu yi zabon dukan mutane za su yi imani da samin shiriya saboda kuwa wannan zabi da Allah ya bawa mutum ya sa yawancin mutane na zabar hanyar bata ne a maimakon shiriya.

2-Banbancin mutum da dabba fahimta da aiki da hankali ne.

To sai a saurari karatun aya ta 180 a cikin suratun A'araf kamar haka:

وَلِلّهِ الأَسْمَاء الْحُسْنَى فَادْعُوهُ بِهَا وَذَرُواْ الَّذِينَ يُلْحِدُونَ فِي أَسْمَآئِهِ سَيُجْزَوْنَ مَا كَانُواْ يَعْمَلُونَ{180}

180- Kuma Allah Yanã da sũnãye mãsu kyau. Sai ku rõke shi da su, kuma ku bar wadanda suke yin ilhãdi a cikin sũnãyenSa:zã a sãka musu abin da suka kasance sunã aikatãwa.

Dukan siffofi masu kyau sun samo asali daga Ubangiji ne domin shi ne tushen duk wata kamala da kyau saboda haka duk wata kalma mai kyau da suna mai kyau ya kebanta da shi da girmama suna da siffofinsa kamar yadda daya daga cikin ayoyin kur'ani keumurtarmu da tsarkake sunayen Allah kuma bawai kawai kar mu hada Allah da wani a cikin bauta hatta kar mu hada sunasa da waninsa.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Dukan wani abu mai kyau da amfani na Allah ne idan muna son isa ga su sai mun bi ta hanyar Allah.

2-Addini yana la'akari da suna mai kyau hatat wajan sanyawa yayanmu suna yake umurtarmu da zabar suna mai kyau da ya dace mai ma'ana.

To sai a saurari karatun aya ta 181 zuwa 183 a cikin suratun A'araf kamar haka:

وَمِمَّنْ خَلَقْنَا أُمَّةٌ يَهْدُونَ بِالْحَقِّ وَبِهِ يَعْدِلُونَ{181} وَالَّذِينَ كَذَّبُواْ بِآيَاتِنَا سَنَسْتَدْرِجُهُم مِّنْ حَيْثُ لاَ يَعْلَمُونَ{182} وَأُمْلِي لَهُمْ إِنَّ كَيْدِي مَتِينٌ{183}

181- Kuma daga wadanda Muka halitta akwai wata al'umma, sunã shiryarwa da gaskiya, kuma,da ita suke yin ãdalci. 182- Kuma wadanda suka karyata game da ãyõyinMu, zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba. 183- Kuma Inã yi musu jinkiri, lalle ne kaidĩNa, mai karfi ne.

Wadannan ayoyi sun kasa mutane gida biyu.Bangare na farko bayan ya samu shiriya yana kuma kokarin ganin ya shiryar da waninsa karkashin tafarkin gaskiya da adalci da kuma aiki da zama abin koyi ga sauransa. Amma dayan bangare na mutane sai ya rungumi kin karbar gaskiya da aiki da ita bayan haka yake karyatawa a maimakon ya bautawa Allah sai yake bautawa son zucciya da son ransa.To Allah yana shaidawa wannan gungu cewa yayi masu sausauci da jinkirta masu azaba a wannan duniya da zabar abin da suke so amma kar su yi zaton wannan jinkirtawa don amfaninsu ne .Saboda a maimakon sun yi amfani da wannan dama wajan gyara munanan ayyukansu sai suka zabi ci gaba da nucewa cikin duhun bata da ayyukan sabo da karyatawa. To tun a wannan duniya sannu a hankali za su gamu da azaba kafin ta lahira ta riske su.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa uku akalla:

1- Shiriya ta fatar baki ba ta wadatarwa ana bukatar aiki kuma aikinmu na alheri ya zama abin ko yi ga saura da hakan zai kai ga shiriyarsu.

2- Idan muka aikata sabo kuma ba mu ga azaba ba kar mu yi farin ciki,domin mun yi kwance da kaya ne ,abu mafi kyau yin tuba da gyara kuskuranmu.

3- Damar yin tuba Allah ya bawa kowa amma babu wanda yake amfani da wannan dama da cin ribarta kamar mumuni.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul A'araf, Aya Ta 184-187 (Kashi Na 267)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.

To sai a saurari karatun aya ta 184 a cikin suratun A'araf kamar haka:

أَوَلَمْ يَتَفَكَّرُواْ مَا بِصَاحِبِهِم مِّن جِنَّةٍ إِنْ هُوَ إِلاَّ نَذِيرٌ مُّبِينٌ{184}

184- Shin, ba su yi tunĩni ba, cẽwa bãbu wata hauka ga ma'abucinsu? shĩ bai zama ba fãce mai gargadi mai bayyanãwa.

A cikin shirin da ya gabata mun bayanna cewa mutane sun kasu gida biyu dangane da kiran annabawa bangare na farko yana amsa kiran annabwa da yin imani da gaskanta kiran manzonnin Allah amma dayan bangare na karyatawa da yin jayayya to wannan aya na cewa: domin kafa hujja da fakewa kan jayayyar da suke yi da boye kafircinsu sai suke danganta ma'aikin Allah da wanda aljanni da taba da wani nau'I na hauka kuma tun farkon halitta haka kafirai suke fakewa .Shin meyasa a tsawon shekaru arba'in da manzo ya rayu da su ba su zarge shi da hakan ba ko aikata wani abu da ya sabawa hankali ,shin sun manta ya yi rayuwa tare da su a tsawon wadannan shekaru arba'in.Kuma me yasa a tsawon shekarun nan babu wani da ya fi shi mutunci da gaskiya da adalci a tsakaninsu kuma yanzu ma yana galgadinsu ne da kokarin dora su ga hanya ta gaskiya kamar yadda yayi a baya to me yasa suke danganta shi da mai tabuwar hankali.wannan zargi ne mai girma da ban al'ajabi da kafirai suke yiwa annabwa da manzonni a tsawon tarihi kuma wannan zargi nasu da kuntatawa Annabwa da manzonni bai kebanta da Manzon Rahama ba.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-salon da kafirai ke bi ya sabawa hankali da dali kawai zargi da ya yi hannnun riga da gaskiya da addini da hankali.

2-dole a dace damtse wajan fadakar da masu sabo da aikata ba gaskiya ba.

To sai a saurari karatun aya ta 185 a cikin suratun A'araf kamar haka:

أَوَلَمْ يَنظُرُواْ فِي مَلَكُوتِ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَمَا خَلَقَ اللّهُ مِن شَيْءٍ وَأَنْ عَسَى أَن يَكُونَ قَدِ اقْتَرَبَ أَجَلُهُمْ فَبِأَيِّ حَدِيثٍ بَعْدَهُ يُؤْمِنُونَ{185}

185- Shin, ba su yi dũbi ba a cikin mulkin sammai da kasa, da kuma abin da Allah Ya halitta daga kõme, kuma akwai tsammãni kasancewar ajalinsu, hakĩka, ya kusanta? To,da wane lãbãri a bãyansa suke yin ĩmãni?

Bayan kiran da Allah ya yiwa kafirai da masu adawa da kiran Annabwa da mnzonni kuma bayan suna zarginsu da wasu abubuwa da ba su dace ba sai wannan aya ta ke kiransu zuwa da yin tunani da yin nazari cikin halittun Allah wanda ya halicci sammai da kassai da abin da ke cikinsu da cewa; iko da kudurar Allah ce ke tafiyar da lamuransu :Kuma shin bayan Allah daya mahalicci mai hikima Akwai wani ne? Hatta ku da kuka rungumi jin dadin wannan duniya da bin son ranku ba ku tunani da hasshen mutuwa da karshen rayuwarku da barin wannan duniya. To idan kuna tunanin haka to me yasa har yanzu kuna karyata gaskiya,Kuna gaskata maganganun batattu amma kun kasa yin imani da maganganun Annabawa da Manzonni?.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-tunani da nazari a cikin halittun Allah dole ne ya kasance karkashin hankali da gaskiya da zai kai mu ga fahimta da cimma nasara .

2- Sha'afa daga mutuwa yana daga cikin dalilan aikata sabo da dama kamar yadda tunawa da mutuwa ke taimakawa mutum da ruhinsa .

To sai a saurari karatun aya ta 186 a cikin suratun A'araf kamar haka:

مَن يُضْلِلِ اللّهُ فَلاَ هَادِيَ لَهُ وَيَذَرُهُمْ فِي طُغْيَانِهِمْ يَعْمَهُونَ{186}

186- Wanda Allah Ya batar to bãbu mai shiryarwa a gare shi: kuma Yanã barin su, a cikin batarsu sunã dimuwa.

Wannan aya tana bayani ne kan karshe da makomar masu kafirtawa da jayayya da cewa; jayayya da ta'assubanci da ke hana ji da ganin gaskiya na sawa Allah ya bar mutum cikin duhun bata da tabewa da haramta masa samin shiriya daga Allah.Kuma lamari da yake a fili nisantar hanyar Allah madaidaiciya yana kai wa mutum cunduma cikin bata da riko da hanyar tabewa.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-jayaya da juya kiran Annabawa da littafan Allah da ke zama a matsayin hanyar shiriya na jawo fushin Allah a wannan duniya kamar barin mutum cikin kunci da duhun bata.

2-Mutum a wannan duniya tamkar yana bakin rijiya ne dole Allah ya kama hannunsa don kar ya fada ma'ana wadanda suka zabi bata za su fada da hallaka a cikin wannan rijiya.

To sai a saurari karatun aya ta 187 a cikin suratun A'araf kamar haka:

يَسْأَلُونَكَ عَنِ السَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَاهَا قُلْ إِنَّمَا عِلْمُهَا عِندَ رَبِّي لاَ يُجَلِّيهَا لِوَقْتِهَا إِلاَّ هُوَ ثَقُلَتْ فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ لاَ تَأْتِيكُمْ إِلاَّ بَغْتَةً يَسْأَلُونَكَ كَأَنَّكَ حَفِيٌّ عَنْهَا قُلْ إِنَّمَا عِلْمُهَا عِندَ اللّهِ وَلَـكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لاَ يَعْلَمُونَ{187}

187- Sunã tambayar ka daga Sa'a, a yaushe tabbatarta take? Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Ubangijina yake. Bãbu mai bayyana ta ga lõkacinta fãce shĩ Tã yi nauyi a cikin sammai da kasa. Bã zã ta zo muku ba fãce kwatsam." sunã tambayar ka, kamar kai masani ne gare ta. Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawan mutãne bã su sani."

Daya daga cikin tambayoyin da kafirai ke yiwa ma'aikin Allah domin su kure shi da kasa amsawa ,suna tambayarsa lokacin tashin kiyama alhali abubuwa masu muhimmanci dangane da tashin kiyama ma'aikin Allah (SWA) ya ba su lamarinsu kuma tushe shi ne abkuwarta babu makawa,lokacin abkuwarta ba shi da muhimmanci.Misali mutum a maimakon ya tambayi wanda ya halicci halittu sai ya tambayi shekaru nawa ne aka halicci wannan duniya ya manta da asalin wanda ya yi halitta.Kuma ko da zai amsa masu da cewa shekaru dubu goma masu zuwa babu wanda zai karyata domin ba su da masaniya kan lokacin tashin kiya amma don izgili sai suke tambayar wani abu maras muhimmanci.A cikin wannan aya kur'ani yayi nuni da jaddada kan abubuwa biyu na farko kiyama zata zoma ne kwacam ba zata kuma mutum ba shi da ikon yin hassashe kan lokacin abkuwarta.Abu na biyu ilimin farkon halitta da karshen halittar wannan duniya da abin da ke cikinta ya kebanta da Allah hatta Annabawa da manzonni ba su da ilimin sanin hakan.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1- Mu shirya da sanin cewa babu makawa sai alkiyama ta abku da tara mu a gaban kutun da alakalinta Shi ne Allah.

2- Kan abin da ba mu sani ba kar mu ji kumyar fadin cewa ba mu sani ba domin ma'aikin Allah da kansa abin da bai sani ba cikin sauki yana cewa bai sani ba balantana mu da ba kowa ba.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul A'araf, Aya Ta 188-192 (Kashi Na 268)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.

To sai a saurari karatun aya ta 188 a cikin suratun A'araf kamar haka:

قُل لاَّ أَمْلِكُ لِنَفْسِي نَفْعاً وَلاَ ضَرّاً إِلاَّ مَا شَاء اللّهُ وَلَوْ كُنتُ أَعْلَمُ الْغَيْبَ لاَسْتَكْثَرْتُ مِنَ الْخَيْرِ وَمَا مَسَّنِيَ السُّوءُ إِنْ أَنَاْ إِلاَّ نَذِيرٌ وَبَشِيرٌ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ{188}

188- Ka ce: "Bã ni mallaka wa raina wani amfãni, kuma haka ban tunkude wata cũta, fãceabin da Allah Ya so. Kuma dã na kasance inã sanin gaibi, dã lalle ne, nã yawaita daga alhẽri kuma cũta bã zã ta shãfe ni ba, nĩ ban zama ba fĩce mai gargadi, kumamai bãyar da bishãra ga mutãne wadanda suke yin ĩmãni."

Wasu daga cikin mutanan da suka rayu da ma'aikin Allah suna jira da bukatar ma'aikin Allah ya ba su tabarin abubuwa da suka shafe su da wandan za su fuskanta a nan gaba domin amfanuwa ko kaucewa da yin riga kafi kansu kana haka a cikin wannan aya ma'aikin Allah ke ce masu:Ni an aiko ni ne domin fadakarwa dashiryar da ku ,ba wai ba ku labarin abin da ke boye ba kuma da ina da masaniya kan gaibi da na yawaita dukiya da ambubuwan masu amfani a gare ni kuma da na kare kai na daga abukuwar abubuwa maras kyau. To amma alheti ko lala bani da masaniya kansa kuma iliminsa yana hannun Allah.Kuma ni kai na ba na iya yiwa kaina komi kan haka kuma tushe da masaniyar abubuwan da ke boye yana hannun Allah ne kuma shi ne ke sanar da wasu daga cikin bayunsa wani abu daga cikin abubuwan boye domin shiryar da bayunsa da basu labarin wani abu daga cikin abubuwan da suka wakana a baya da wadanda za su wakana ba tare da ikon yin wani abu na canja abin da zai wakana.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Kar mu nuna girman kai da fankama kan abin da muke da shi na dukiya ko iko domin komi na Allah ne .

2-Ilimin Gaibu na Allah ne sanin gaibu babu wani abu da yake canjawa a rayuwar Annabawa da manzonni.

To sai a saurari karatun aya ta 189 da 190 a cikin suratun A'araf kamar haka:

هُوَ الَّذِي خَلَقَكُم مِّن نَّفْسٍ وَاحِدَةٍ وَجَعَلَ مِنْهَا زَوْجَهَا لِيَسْكُنَ إِلَيْهَا فَلَمَّا تَغَشَّاهَا حَمَلَتْ حَمْلاً خَفِيفاً فَمَرَّتْ بِهِ فَلَمَّا أَثْقَلَت دَّعَوَا اللّهَ رَبَّهُمَا لَئِنْ آتَيْتَنَا صَالِحاً لَّنَكُونَنَّ مِنَ الشَّاكِرِينَ{189} فَلَمَّا آتَاهُمَا صَالِحاً جَعَلاَ لَهُ شُرَكَاء فِيمَا آتَاهُمَا فَتَعَالَى اللّهُ عَمَّا يُشْرِكُونَ{190}

189- Shĩ ne wanda Ya halitta ku daga rai guda, kumaYa sanya, daga gare ta, ma'auranta, dõmin ya natsu zuwa gare ta. Sa'an nan a lõkacin da ya rufe ta, ta yi ciki, ciki sassauka, sai ta shũde dashi. Sa'an nan a lõkacin da ya yi nauyi, sai suka rõki Allah, Ubangijinsu: "Lalle ne idan Ka bã mu abin kwarai, hakĩka, zã mu kasance dagamãsu gõdiya." 190- To, a lõkacin da Ya bã su abin kwarai, suka sanya Masa abõkan tarayya a cikin abin da Ya ba su. To, Allah Yã tsarkaka daga abin da suke yi na shirki.

Wadannan ayoyi na magana ne kan ma'aurata da cewa; Allah ne ya sanya mu ma'auranta juna da rayuwa tare cikin kwanciyar hankali da sanya mu masu aifuwa amma lokacin da cikin mace ya kurato da haifar abin da ke cikinsa da kuma lokacin nakuda tana daga hannunta sama don yin addu'a da bukatar Allah da ya bata da salihi mai albarka da mai yin biyayya ga uwayensa da girma ma mutane to idan ya amsa addu'arku sai ku gode masa wannan ni'ima amma bayan haifar wannan da sai ku manta da wannan falala da wanda ya yi maku wannan falala ma'ana a maimakon ku sanya dan ku cikin hanyar Allah hanayr shiriya sai ku sanya shi cikin hanayar bata da tabewa.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda hudu:

1-Zaman aure na kawo kwanciyar ruhi da ta jiki ga ma'aurata domin kaucewa matsalolin da matasa ke fuskanta sai su rungumi hanyar yin aure.

2-Dan adam na bukatar nutsuwa da kwanciyar hankali don haka Allah ya sanya a yawancin rayuwar ma'aurata.

3-Daya daga cikin burin yin aure samar da zuriya ta gari saliha.

4-Domin shiryar da yayanmu da zama masu tsarki ya kamata mu yi tanadi tun kafin haihuwarsu da neman taimako daga Allah.

To sai a saurari karatun aya ta 191 da 192 a cikin suratun A'araf kamar haka:

أَيُشْرِكُونَ مَا لاَ يَخْلُقُ شَيْئاً وَهُمْ يُخْلَقُونَ{191} وَلاَ يَسْتَطِيعُونَ لَهُمْ نَصْراً وَلاَ أَنفُسَهُمْ يَنصُرُونَ{192}

191- Shin, sunã shirki da abin da bã ya halittar kõme, kuma sũne ake halittãwa? 192 - Kuma ba su iya bãyar da taimako gare su, kuma kansu ma, bã su iya taimaka!

A cikin ayoyin da suka gabata mun bayyana cewa; wasu daga cikin uwaye suna karkata akalar yayansu a maimakon su sanya su kan hanyar Allah da shiryar da su kan tafarki madaidaici ya sanya su kan hanyar bata alhali babu wani mai kuduri da iko bayan Allah don haka wannan ayar ke cewa; wani ba Allah ba me yake da shi ?shin yanada kudurar yin halitta alhali ba ya iya kare kansa balantana waninsa. Rayuwa da mutuwa ta hannun Allah ne to mene ne ya sa ba mu mika wuya da bin tafarkin Allah ,kuma mene ne Allah ba yada da shi ne har muke komawa ga waninsa? Me ya sa muke tarbiyartar da yayanmu kan tafarkin son duniya da dukiya da sha'afa da lahira.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Tarbiyartar da yayanmu yana hannun uwayensu maza da mata ne.

2-Duk wani abu ba Allah ba ba yada komi kuma shi ba komi ne ba.Allah shi ne mamallaki da ikon komi.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul A'araf, Aya Ta 193-196 (Kashi Na 269)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.

To sai a saurari karatun aya ta 193 a cikin suratun A'araf kamar haka:

وَإِن تَدْعُوهُمْ إِلَى الْهُدَى لاَ يَتَّبِعُوكُمْ سَوَاء عَلَيْكُمْ أَدَعَوْتُمُوهُمْ أَمْ أَنتُمْ صَامِتُونَ{193}

193 - Kuma idan kun kirãye su zuwa ga shiriya, bã zã su bĩ ku ba, daidai ne a gare ku, shin, kun kirãye su, kõ kuwa kũ mãsu kawaici ne!

A cikin shirin da ya gabata mun bayyana cewa; wasu daga cikin uwaye a maimakon su ilmantar da tarbiyartar da yayansu tafarkin Allah da sanin Mahaliccinsu da yi masa da'a sai su sanya su kan hanyar bata da tabewa ta wanin Allah don shirka to wannan aya tana cewa ne idan kuna son shiriya to kun makaro domin har abada wadannan ba za su iya biya maku bukata ba. Saboda ba su da kudurar yin hakan.Wanda ba ya iya yi wa kansa magani da wuya ya yi wa waninsa magani.Allah ne kawai abin dogaro a wannan duniya.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Bai dace ba wani bawon Allah ya yi wa wani bawan Allah bauta balantana wani abu marar rai kamar gumaka.

2-Babbar bukatar bawa ga Mahalicci shiriya zuwa ga sa'ada da samin tsira duniya da lahira.

Yanzu kuma za mu saurari aya ta 194 a cikin suratul A'araf kamar Haka:

إِنَّ الَّذِينَ تَدْعُونَ مِن دُونِ اللّهِ عِبَادٌ أَمْثَالُكُمْ فَادْعُوهُمْ فَلْيَسْتَجِيبُواْ لَكُمْ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ{194}

194 - Lalle ne wadannan da kuke kira, baicin Allah, bãyĩ ne misãlanku: to, ku kirãye su, sa'an nan su karba muku, idan kun kasance mãsu gaskiya!

Kamar ayar da ta gabata ce ta itama wannan ayar tana cewa: dukan mutane bayun Allah ne kuma kowa ne daya daga cikinsu mabukaci ne yana bukatuwa da lutifi da taimakon Allah babu wani mutum da yafi wani da baya bukatuwa da Allah ko yafi shi ta wannan bangaren to idan haka ne me yasa muke neman taimakon wanin Allah ba Allah ?. ko shin muna zaton sunada kudura da irada ne / Idan haka ne sai mu rungume su a gani za su iya mangance mana matsaloli ko su magance wa kansu. Wannan aya tana magana ne kan masu bautawa wani ba Allah ba.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Dole wanda ake bautawa yafi wanda yake yi masa bauta fifiko da biya masa bukatunsa.

2-Dole wanda ake yiwa bauta ya biya bukatun bayunsa babu wani da zai iya face Allah madaukakin sarki.

To sai a saurari karatun aya ta 195 a cikin suratun A'araf kamar haka:

أَلَهُمْ أَرْجُلٌ يَمْشُونَ بِهَا أَمْ لَهُمْ أَيْدٍ يَبْطِشُونَ بِهَا أَمْ لَهُمْ أَعْيُنٌ يُبْصِرُونَ بِهَا أَمْ لَهُمْ آذَانٌ يَسْمَعُونَ بِهَا قُلِ ادْعُواْ شُرَكَاءكُمْ ثُمَّ كِيدُونِ فَلاَ تُنظِرُونِ{195}

195- Shin sunã da kafãfu da suke yin tafia da su? Kõ sunã da hannãye da suke damka da su? Kõ sunã da idãnu da suke gani da su? Ko sunã da kunnuwa da suke saurãre da su? Ka ce: "Ku kirãwo abũbuwan shirkinku sa'an nan kuma ku yi mini kaidi, sa'an nan kada ku saurãra mini."

Ayar da ta gabata tana mamakin wadanda suke bautawa mutane yan uwansu mabukata da ganin wawancinsu to ita ma wannan aya tana mamakin wadanda suka fi su hanka da rashin aikin yi domin suna buatawa wadanda suka fi su kaskanci ma'ana suna bautawa dutse da gunkin da suka sassaka da hannunsu da dutse ko icce wadanda ba su iya tafiya ko magana ko gani .To ai wannan rashin hankali ya wuce misali da tunani.Saboda haka wannan ayar ta bukaci ma'aikin Allah da ya tayar da irin wadannan mutane mushrikai daga barci da duhun bata ta hanyar bukatarsu da su bukaci gumaka da su cutar da musulmi kowa ya gani idan sun kasa kowa ya fahimci ba su iya yin komi.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Jagororin shiriya sun yi imani da Allah da kudurarsa ta haka suke fuskantar makiyansu domin nunwa sauran mutane kasawar wadannan mutane.

2-Mushrikai suna ganin ma'aikin Allah mutum ne kamar su amma suna kaskantar da kansu suna bautawa gumaka da suka sassaka da hannunsu.

To sai a saurari karatun aya ta 196 a cikin suratun A'araf kamar haka:

إِنَّ وَلِيِّـيَ اللّهُ الَّذِي نَزَّلَ الْكِتَابَ وَهُوَ يَتَوَلَّى الصَّالِحِينَ{196}

196- "Lalle ne, Majibincĩna Allah ne Wanda Ya saukar da Littãfi kuma Shĩ ne Yake jibintar sãlihai,"

Ita wannan aya tana nuni ne da bayun Allah nagari salihan bayu masu riko da littafin Allah da kuma riko da tafarkinsa da bin umarnin da ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya zo masu da shi sabanin masu bautawa gumaka da mutane yan uwansu mabukata.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa uku akalla:

1-Salihan bayu sunada matsayi mai girma a gurin Allah kamar yadda a cikin kur'ani annabawa da manzonnci aka ba su matsayin salihai.

2-Duk wanda ya yi riko da tafarkin Allah ba yada fargaba domin Allah ya yi alkawalin kare shi.

3-Allah yana umurtar mutum aikata wani abu don amfaninsa kuma ya taimaka masa wajan aiwatarwa.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul A'araf, Aya Ta 197-202 (Kashi Na 270)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki ,tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.

To sai a saurari karatun aya ta 197 da ta 198 a cikin suratun A'araf kamar haka:

وَالَّذِينَ تَدْعُونَ مِن دُونِهِ لاَ يَسْتَطِيعُونَ نَصْرَكُمْ وَلا أَنفُسَهُمْ يَنْصُرُونَ{197} وَإِن تَدْعُوهُمْ إِلَى الْهُدَى لاَ يَسْمَعُواْ وَتَرَاهُمْ يَنظُرُونَ إِلَيْكَ وَهُمْ لاَ يُبْصِرُونَ{198}

197- "Kuma wadanda kuke kira, baicinSa, bã su iya taimakõn ku, kuma kansu ma, bã su iya taimaka." 198- Kuma idan ka kirãye su zuwa ga shiriya, bã zã su ji ba, kuma kanã ganin su, sunã dũbi zuwa gare ka, alhãli kuwa sũ, bã su gani.

Wadannan ayoyi ci gaba ayoyin shirin da ya gabata ne da ke magana kan mushrikai da abubuwan da suke bautawa da cewa; duk wani abu da za ku bautawa ba Allah ba to ku yi riko da shi ko gumki ne ko mutum dan uwanku ba zai amfane ku da komi ba da kare ku daga wani hadari kuna gani wani hadari zai same ku ba tare da sun tabuka maku komi ba wajan kare ku ,saboda kun manta Allah shi ma ya manta ku. Ci gaban wannan aya tana Magana da ma'aikin allah da cewa: idan ka ci gaba da galgadi da nasihantar da su ka ci gaba amma kar ka yi zaton baki dayan su suna sauraren wannan kira naka kuma yawancinsu bas u da banbanci da gumakan da suke bautawa bas u jib a su gani da fahimtar gaskiya.Kuma suna da ido da kunne daba su gani da sauraren gaskiya.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Abin da ake bautawa ya kamata ya zamanto abin dogaro ,wannnan kuwa ya kebantu da Allah ne.

2-Ido da kunne ba shi ne ba sau tari makaho da kurnma na fahimtar gaskiya fiye da mai ido da kunnan saurara.

To sai a saurari karatun aya ta 199 a cikin suratun A'araf kamar haka:

خُذِ الْعَفْوَ وَأْمُرْ بِالْعُرْفِ وَأَعْرِضْ عَنِ الْجَاهِلِينَ{199}

199 - Ka riki abin da ya saukaka; Kuma ka yi umurni da alhẽri, Kuma ka kau da kai daga jãhilai.

Wannan ayar tana magana ne ga ma'aikin Allah da wadanda suka yi imani da umurtarsu da abubuwan Akhalaki da yadda za su zauna da mutane masoya da makiya da cewa: duk wanda ya aaika leifi a gare ku ku yafe masa shi yafi a gurin Allah ,ba hanayr yin ramuwa da maida martani ku kirayo su zuwa ga aikata alheri da girmamawa sabanin ayyukan jahiliya.wannan ya shafi leifin da aka yi wa mutum a matsayinsa na shi kadai ba shi da dangantaka da hakkin al'umma da zamantakewarsu.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Aikata alheri yanada kyau musamman idan ya ginu a tsakaninn jama'a.

2-Jahili ba shi ne ba wanda bai yi karatu ba .aikata ba daidai ba shi ne jahilci.

To sai a saurari karatun aya ta 200 a cikin suratun A'araf kamar haka:

وَإِمَّا يَنزَغَنَّكَ مِنَ الشَّيْطَانِ نَزْغٌ فَاسْتَعِذْ بِاللّهِ إِنَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ{200}

200- Kuma imma wata fizga daga Shaidan ta fizge ka, sai ka nẽmi tsari ga Allah. Lalle ne shi, Mai jĩ ne, Masani.

Wannan ayar tana nuni da cewa hatta ma'aikin Allah bai tsira ba daga kokarin yaudarar shaidan duk da cewa Allah ya yi alkawalin kare su daga fadawa tarkon shaidan.wannan ayar na nuni da cewa shaidan ne ke haddasa kiyayya a tsakanin mutane da hana su yafewa junansu domin ta haka za su samu rahama da falala ta yan uwantaka amma shi ba ya son haka yafi son ya hadda gaba da kiyayya da fushi a tsakani .saboda haka wannan ayar ke cewa: a duk lokacin da muka fahimci fizgar shaidan sai mu nemi tsari daga Allah da neman mafaka a gurinsa da yin tawakkali a gare shi ,domin Shi ne abin dogaro.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Wasiwasin shaidan wani abu da a kullum yake tare da mu babu makawa ,don haka a kullum mu nemi tsarin Allah daga shaidan.

2- Nisantar hanayr shaidan ,kusanci ne da hanyar Allah da ambatonsa da neman taimakonsa.

To sai a saurari karatun aya ta 201 da ta 202 a cikin suratun A'araf kamar haka:

إِنَّ الَّذِينَ اتَّقَواْ إِذَا مَسَّهُمْ طَائِفٌ مِّنَ الشَّيْطَانِ تَذَكَّرُواْ فَإِذَا هُم مُّبْصِرُونَ{201} وَإِخْوَانُهُمْ يَمُدُّونَهُمْ فِي الْغَيِّ ثُمَّ لاَ يُقْصِرُونَ{202}

201- Lalle ne wadanda suka yi takawa idan wani tãshin hankali daga Shaidan ya shãfe su, sai su tuna (Allah) sai gã su, sun zama masu basĩra. 202- Kuma 'yan'uwan su (shaidanu) sunã taimakon su a cikin bata, sa'an nan kuma bã su takaitãwa.

Ayoyin da suka gabata suna magana ne da ma'aikin Allah yayin da ita kuwa wannan aya tana magana ne kan mumunai da cewa: wasiwasin shaidan yana shafarsu ta dukan bangaroru da neman kawo baraka a tsakaninsu amma masu basira da takawa daga cikinsu a duk lokacin da wani abu ya shafe su daga shaidan suna tunawa da ambaton Allah da neman taimakonsa kuma Allah yana sauraransu da ganin halin da suke ciki sai ya gubutar da su da bar wannan aiki na bata da sabo.Sabanin mutane da ba su da takawa da tsoran Allah na ci gaba da yin riko da hanyar shaidan da zama abukan tafiyar shaidan.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa uku akalla:

1-shaidanun mutane da aljannu suna taimakawa juna wajan batar da mutane sai mu yi hankali da takatsantsan.

2-ambaton Allah da baki da kuma a zucci yana kare mutum daga wasiwasin shaidan.

3-Idan mutum ba shi da tsoran Allah yana zama abokin shaidan a hanyar bata.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.

Suratul A'araf, Aya Ta 203-206 (Kashi Na 271)

Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.

To sai a saurari karatun aya ta 203 a cikin suratun A'araf kamar haka:

وَإِذَا لَمْ تَأْتِهِم بِآيَةٍ قَالُواْ لَوْلاَ اجْتَبَيْتَهَا قُلْ إِنَّمَا أَتَّبِعُ مَا يِوحَى إِلَيَّ مِن رَّبِّي هَـذَا بَصَآئِرُ مِن رَّبِّكُمْ وَهُدًى وَرَحْمَةٌ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ{203}

203- Kuma idan ba ka je musu da wata ãyã ba, su ce: "Don me ba ka kãga ta ba?" Ka ce: "Abin sani kawai, inã biyar abin da aka yõ wahayi zuwa gare ni ne, daga Ubangjina. Wannan abũbuwan kula ne daga Ubangijinku, da shiriya da rahama ga mutãne wadanda suke yin imãni."

Kamar yadda kuka sani kur'ani an sabkar da shi ga ma'aiki sannu a hankali a cikin tsawon shekaru ashirin da uku na manzonci saboda haka sai wani lokaci a yi watanni aya ba ta sabka ba ganin haka masu adawa da ma'aiki sai su fake da izgilin cewa ba su bukatuwa da dogara da ayoyi da mu'ujizar da ake sabkarwa ma'aiki.wani lokaci su ce an dauki lokaci wahayi bai sabka na ko Allah ya yi wa ma'aikinsa fushi ne ? To a cikin wannan ayar Allah ya cewa ma'aikinsa ya cewa kafirai masu fakewa da wannan lamari cewa; ba ni ne na ke sabkar da wahayi ba da duk lokacin da nake so sai in sabko da aya ko kuma duk lokacin da kuka yi bukata .Shi wahayi wani lamari ne daga Allah ga mutane masu imani da shiriyar da rahamar Allah ke shafa .

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-A salon yada addinin musulunci ana iya yin amfani da salo masu yawa mabanbanta wani lokaci yin shiru ma yanada da amfani wani lokaci kuma bayani da jawabi.

2-Kar izgili da tankwalar makiya su rude mu ,a kullum mu yi riko da hanyar da muka yi imani da ita.

To sai a saurari karatun aya ta 204 a cikin suratun A'araf kamar haka:

وَإِذَا قُرِئَ الْقُرْآنُ فَاسْتَمِعُواْ لَهُ وَأَنصِتُواْ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ{204}

204- Kuma idan an karanta Alkur'ãni sai ku saurara gare shi, kuma ku yi shiru; Tsammãninku, anã yi muku rahama.

Bayan da ayar da ta gabata ta yi magana kan matsayin kur'ani da matsayinsa na hanyar shiriya da rahama ga mumunai to wannan ayar tana cewa ne ya ku mumunai ku yi shiru da saurarawa a duk lokacin da ma'aikin Allah yake karanta kur'ani da yin tunani a cikin ayoyin kur'ani da yin ladabi da girma maganar Allah kuma rahamar Allah za ta shafe ku.Kuma hatta domin samun falala a lokacin da limami a sallar jama'a yake karata suratun Hamdu da wata sura bayanta da ake bayyana mamu za su yi shiru da saurara domin samin falala da rahama.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Kur'ani magana ce ta Allah ana bukatar karantawa da aiki da shi a aikace da a zucci da kuma saurarawa.

2-Girmama Kur'ani na sabkar da rahama kamar yadda akasin haka ke haddasa fushin Allah.

To sai a saurari karatun aya ta 205 a cikin suratun A'araf kamar haka:

وَاذْكُر رَّبَّكَ فِي نَفْسِكَ تَضَرُّعاً وَخِيفَةً وَدُونَ الْجَهْرِ مِنَ الْقَوْلِ بِالْغُدُوِّ وَالآصَالِ وَلاَ تَكُن مِّنَ الْغَافِلِينَ{205}

205- Kuma ka ambaci Ubangijinka, a cikin ranka da kankan da kai, da tsõro, kuma kõmabãyan bayyanawa na magana, da sãfe da marece, kuma kada ka kasance daga gafalallu.

Ayar da ta gabata tana magana ne kan salon karanta kur'anni da yadad ya kamata a ambaci Allah da yin du'a'I da neman falalarsa to ita wannan ayar tana cewa: ambaton Allah dole ne ya ratsa zucciya da jinin mutum a tsawon lokaci dare da rana ma'ana ya fara rayuwarsa a kulum da rufe ta da ambaton Allah cikin kaskantar da kai da girmamawa da tsoro a matsayinsa da mahalicci. Duk da cewa wannan aya a zahiri tana magana ne da ma'aiki amma tana magana ne da mumunai da sahabbansa

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa uku akalla:

1-Ambaton Allah ta fatar baki yanada da amfani amma ana son ambato da ya ratsa zucciya da jinin mutum da kuma ganin haka a aikinsa.

2-Ambaton Allah ya kamata ya zarta na fatar baki da daga murya ana bukatar nucuwa da zurfafa tunani kan ma'anarsa.

3-ya kamata bawon Allah ya tashi daga barci da ambaton Allah da kuma barci da ambaton Allah kuma duk wani aiki da zai fara ya farad a ambaton Allah.

To sai a saurari karatun aya ta 206 a cikin suratun A'araf kamar haka:

إِنَّ الَّذِينَ عِندَ رَبِّكَ لاَ يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِهِ وَيُسَبِّحُونَهُ وَلَهُ يَسْجُدُونَ{206}

206- Lalle ne, wadanda ke wurin Ubangijinka bã su yin girman kai ga bauta Masa, kuma sunã tsarake shi da tasbĩhi, kuma a gare shi suke yin sujada.

Ayar da ta gabata tana magana ne da umurtar mu kan dauwama a cikin ambaton Allah yayin da ita kuwa wannan ayar ke cewa: Makusanta a gurin Allah da suka hada da mala'iku da waliyai da salihan bayu ba su nuna girman kai wajan bautawa Allah kuma a kullum suna cikin ambaton Allah a zucci da bakinsu kuma su ma'abuta sujjada ne don girmama Allah.Sabanin ma'abuta girman kai da jiji da kai masu nuna dagwawa da girman kai.

A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:

1-Nuna girman kai ga Mahalicci ba shi da wata ma'ana kuma jahilci ne .Abu mafi kyau yin tawadu'u da neman kusancinsa.

2-Bayun Allah na gari ba su nuna girman kai a cikin bautawa Allah saimma jin dadin bautar da yin sujjda cikin girmama da kaskantar da kai ga Allah.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.

Contents