Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Ranar Hausa

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

About Hausa Day [1]

Ranar Hausa, 26 ga watan Agusta, rana ce ta musamman da aka ware dan ɗaukakin ilahirin Hausawan dake kafafen sada zumunta na yanar gizo musamman Twitter, su nuna ma duniya daraja, ƙarfi da ƙimar yaren su ta hanyar turo da duk tweet ɗinsu tare da tambarin abin batu na #RanarHausa.

An samu nasara sosai domin ko Hausawa da dama sun nuna kishi da alfahari da yaren nasu ta inda suka (suke a halin yanzu haka) tattauna muhimman abubuwa da dama kama daga karin magana, marubuta da littattafan Hausa, mawaƙa da masu wasan kwaikwayo na da da na yanzu, masarautun Hausa, al-adu da dai sauransu. A taƙaice dai #RanarHausa ya shiga jerin manya-manyan abubuwan da aka fi tattaunawa a Najeria wanda shi ne babban burin mu dan ta haka ne abin zai bazu ta ko ina. --#RanarHausa ta Samu Karɓuwa Augusta 26 2015 by hausatrends, Daga Suleiman Garba Sule (@emlanis_)


https://ha.wikipedia.org/wiki/Ranar_Hausa

Liberty TV on Ranar Hausa 2019

Ranar Hausa (Ko kuma #RanarHausa) da turanci Hausa Day or #HausaDay, rana ce da aka keɓance domin nuna muhimmancin harshen Hausa, tattauna hanyoyin bunƙasa shi da kuma jawo hankali akan irin ƙalubalen da harshen yake fuskanta. an fara bikin farko a shafukan sada zumunta musamman ta shafin twitter da niyyar hada L1 da L2 na masu magana da harshen Hausa. An zaɓi ranar 26 ga watan Augusta domin tuna ranar da aka ƙirƙiro haruffan "ƙ" da "ɗ" da "ɓ" wanda babu su a haruffan Turanci. A Yayin bikin shekara 5, mutane fiye da 400,000 suka gudanar da bikin ta yanar gizo da wasu kasashen da Hausawa suke zaune a sassa daban daban na duniya irinsu Faransa, Amurka, Kamaru, Ghana, Nijar, da Najeriya.

Links (sorted by the latest)

#RanarHausa on Facebook | #RanarHausa on Instagram | #RanarHausa OR #HausaDay on Twitter [2]

  1. August 27, 2020 World Hausa Day: Why Hausa Must Be Adopted As Official Dialect In Nigeria’s North – Historian Malam Rabiu Isa by Daily Trust's ADO ABUBAKAR MUSA, JOS
  2. August 26, 2020 Ranar Hausa ta Duniya Karo na Shida [3]
  3. August 26, 2020 Gatan da ya kamata Hausawa su yiwa Harshensu - By Abubakar SD
  4. August 26, 2020 Miliyoyin Hausawa na gudanar da bikin ranar Hausa ta Duniya - RFI Hausa
  5. August 26, 2020 Tattaunawa kan Ranar Hausa ta duniya ta shekarar 2020. - Mazhun, Muhsin, da Jamila 'yan BANN a DW Hausa
  6. August 26, 2020 A cikin shirin Hantsi na Rahma TV, ana tattaunawa akan #RanarHausa ta Duniya da alfanun ta, tare da Faisal Abdullahi Ismail da Mahzun Idris.[4]
  7. August 25, 2020 Shirin Arewa Radio kan #RanarHausa2020 tare da Faisal Abdullahi (@BANNigeria) da Mazhun (@HausaTranslator) na Bloggers Association of Northern Nigeria. [5]
  8. August 23, 2020 #RanarHausa 2020 - Shirin Daga Taskar Hausa Daga Guarantee Radio 94.7 Kano Here's the 1st 10 minutes on YouTube - Wannan hira ce da aka yi da farfesa Bunza da Dr. Muhammad Sulaiman da Dr. Abdulƙadir Koguna kan muhimmancin ranar Hausa ta duniya.
  9. August 22, 2020 POLL/ZAƁE: Mece ce #ranarhausa a wurinka/ki?
  10. August 21, 2020 What would you like to discuss on #RanarHausa? --BANN
  11. October 2019 Hausa Da Hausawa A Duniyar Кarni Na Ashirin Da Ɗaya (Amsa Kiran Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) Ga Ranar Hausa Ta Duniya – Litinin 26 Ogusta, 2019) [6]
  12. August 31, 2019 Why Hausa is a Fascinating Language By Farooq A. Kperogi, Ph.D. Twitter: @farooqkperogi
  13. August 31, 2019 How Hausa Day Was Born – Gidan Dabino
  14. August 29, 2019 World Hausa Day: Open Letter To Malam Dan-Hausa
  15. August 29, 2019 Ranar Hausa ta Duniya: Kalubalen da harshen Hausa ke fuskanta - Aminiya
  16. August 29, 2019 Karanta Abubuwan Mamakin da Suka Faru a Ranar Hausa Ta Duniya
  17. August 28, 2019 #RanarHausa: The story behind International Hausa Language Day
  18. August 28, 2019 An gudanar da bikin raya ranar Hausa ta duniya - DW Hausa
  19. August 28, 2019 Ranar Hausa: An baje kolin al'adun Hausa a Sudan
  20. August 26, 2019 Video Labarai - Ambaliyar Ruwa na kashe mutane a Najeriya - Ranar Hausa ta Duniya - Mujallar Matashiya
  21. Agusta 26, 2019 Kungiyar Daliban Hausa Ta Gudanar Da Taron Ranar Harshen Hausa - DandalinVOA / VOA Hausa (Audio included)
  22. August 26, 2019 Video: Duniya Ta Dauka, Yau Ake Bikin Zagayowar Ranar Hausa Ta Duniya (Anan Zamu Gane Hausawan Kwarai)
  23. August 26, 2019 Video: Yau ce Ranar Hausa ta Duniya. Albarkacin wannan Rana muke kawo muku tattaunawa kai-tsaye a kan harshe da ala’adun Hausa tare da Hajiya Rahama Abdulmajid da Dokta Garba Dahiru Gandu. #RanarHausa - BBC Hausa
  24. August 26, 2019 Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Kan Ranar Hausa Ta Duniya By Sawaba FM
  25. August 26, 2019 Kacici-kacicin Ranar Hausa ta duniya
  26. September 1, 2018 Video: Shirin BBC Hausa na Ra'ayi Riga akan Ranar Hausa 2018 Ga kuma sautin zalla: https://www.bbc.com/hausa/45377659
  27. September 21, 2017 Ranar Hausa a Manhajar Twitter - Aron Kalma (Word Borrowing) - Aliyu M. Ahmad
  28. August 27, 2018 Hausawa sun baje-kolin basirar rubutun Hausa a ranar Hausa ta duniya - TRT Hausa
  29. August 2018 Ko kun san yau ne ake bikin ranar Hausa ta duniya?, daga Ibrahim M Bawa
  30. August 26, 2018 Ana bikin #RanarHausa a shafukan zumunta - BBC Hausa
  31. August 26, 2016 Video: Bikin ranar Hausa a Internet - BBC Hausa
  32. August 26, 2016 Ana bikin ranar Hausa a Intanet - BBC Hausa