- Hanan Buhari wedding: Aisha Buhari react to viral cartoon of her daughter ceremony pictures
- Nigerian First Lady Mrs Aisha Buhari tok say
- di cartoon wey popular northern Nigeria cartoonist Mustapha Bulama
- do wey show her dey show Nigerians pictures of her pikin Hanan Buhari wedding
- while dem dey drown inside river due to hardship dey 'very unfair'.
- Mrs Buhari tok-tok pesin Aliyu Abdullahi wey speak to BBC add say
- children of any leader get right to get married wen di time come
- whether citizens dey enjoy dia leadership or not.
- "Di cartoon of Mustapha Bulama wey dey go round dey very unfair
- because di wedding
- no in any way dey insensitive to wetin Nigerians dey go through
- infact na because of dat a month to di wedding,
- madam hold meeting with her staff and tell us say
- she wan make di wedding be low key with no massive celebrations."
- "Di foto wey madam (Mrs Buhari) post of di couple for social media
- na after di wedding to thank well wishers and not to rub it in Nigerians faces.
- I fit tell u say di wedding of Hanan Buhari
- na one of di most low key of any Nigerian pikin wedding wey don happun before."
- Di tok-tok pesin also yan say di video wey dey go round
- wey show pipo dey spray money to di couple
- as dem dey dance no happun for dia side as by den di bride don join her inlaws.
- "Dat video wey show some pipo dey spray naira notes no happun for Abuja na wen di bride reach her husband family side for Kaduna e happun." Dis na wetin First Lady tok tok pesin yan.
- Aliyu also say di first lady dey very mindful of Covid 19 and di guidelines wey doctors and scientists give and she make sure say for all di events wey hold for her side pipo maintain those guidelines.
- Hanan Buhari wedding wey happun on 4th September 2020 come at a time when many Nigerians dey complain of hardship due to high increase in food prices, fuel and electricity tariff.
Sani Musa na social commentator wey dey stay Kano for northern Nigeria and e tell BBC say wetin di Nigerian first family suppose do na to shift di wedding to another time when mood of di kontri dey alright.
"To me personally I feel say dis wedding no suppose happun now because di kontri dey in sober mood now due to plenti hardship wey pipo dey face.
For Nigerians wey no fit feed wella and pay dia bills to see president pikin dey marry and pfoto and videos dey go round go surely make many pipo vex." E tok.
|
- Auren Hanan Buhari: Aisha ta ce mai zanen barkwanci Bulama bai yi wa bikin ƴarta adalci ba
- Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta ce
- zanen barkwancin da Mustapha Bulama ya yi
- da ke nuna yadda take nuna wa ƴan Najeriya hotunan bikin yarta Hanan Buhari
- su kuma yan ƙasa na nutsewa a cikin kogi saboda wahala '"babu adalci a ciki".
- Mai magana da yawun Aisha, Aliyu Abdullahi ya shaida wa BBC cewa
- ƴaƴan kowanne shugaba na da damar aure idan lokaci ya zo
- ko da ƴan kasa na jin daɗin mulkinsu ko akasin haka.
- "Zanen barkwancin Mustapha Bulama da ke yawo babu adalci a ciki
- saboda bikin
- ba shi da wata alaƙa da yanayin da yan kasa suka tsinci kansu,
- kuma saboda irin haka ne ya sa wata guda kafin bikin,
- shugabar tawa ta tattauna da ma'aikatanta cewa
- ba ta son a yayata bikin saboda za a taƙaita hidima."
- "Hoton da shugaba ta (Aisha Buhari) ta wallafa na ma'auratan a soshiyal midiya
- na bayan biki ne domin ta gode wa wadanda suka aike da fatan alheri da kuma sanar da ƴan kasa.
- Ina iya tabbatar muku cewa bikin Hanan Buhari
- shi ne wanda kwata-kwata babu armashi kuma aka taƙaita idan aka kwatanta da bukukuwan baya da aka yi a kasar nan."
- Kakakin nata ya kuma ce bidiyon da aka rinka yaɗawa
- da ke nuna yadda mutane ke yi wa ma'auratan liƙi
- ɓangaren dangin ango ne bayan an kai musu amarya.
- "Wannan bidiyon da ke nuna mutane na liƙi da kudin naira ba a Abuja ba ne a gidan surukan Amarya ne bayan ta isa gidan dangin mijin a Kaduna," a cewar kakakin uwargidan Buhari.
- Aliyu ya kuma ce uwargidan shugaban kasa ta damu da annobar cutar korona da dokokin da likitoci suka gindaya da masana kimiyya, kuma ta tabbatar da hidimar da ta shirya mutane sun bi waɗannan dokoki.
- A ranar 4 ga watan Satumban 2020 aka ɗaura auren Hanan Buhari a lokacin da ƴan Najeriya da dama ke ƙorafin mawuyancin halin da suke ciki saboda hauhawar firashin kayan abinci da man fetur da wutar lantarki.
Wani Sani Musa da ke yawan tsokaci a shafukan sada zumunta mazaunin Kano a arewacin Najeriya ya shaida wa BBC cewa abin da ya kamata iyalan shugaban kasa su yi shi ne ɗage bikin zuwa lokacin da lamura za su daidata a ƙasar.
"A ganina, ina ganin bai kamata a yi wannan bikin ba a yanzu, saboda ƙasar na cikin yanayi na korafi saboda wahalhalun da ake ciki.
Ga ɗan Najeriya da ke neman abin kai wa baki sannan babu kuɗin biyan wuta ko ruwa, sannan ya yi kiciɓus da hotunan auren ɗiyar shugaban kasa da bidiyo na yawo dole ya fusata," a cewarsa.
|