Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:aikatau

Discussion page of aikatau

Glosbe's example sentences of aikatau [1]

  1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar aikatau:
    1. Wannan kalmar ta kusa da ta ƙarshen ta fassara aikatau na Helenanci da yake nufin “gogewa, . . . kashe ko kuma halaka.”
      That last phrase translates a Greek verb that can mean “to wipe out, . . . cancel or destroy.” [2]

    2. ‘Mutum ya yi tsayin daka, tsaya da aminci, ko kuma nacewa’ shi ne abin da aikatau na Helenanci da ake yawar fassara shi “jimrewa” yake nufi cikin Littafi Mai Tsarki.
      ‘Standing one’s ground, remaining steadfast, or persevering’ is the thought behind the Greek verb often translated “endure” in the Bible. [3]

    3. (2 Timothawus 2:15) Furcin nan “rarrabe . . . sosai” daga kalmar aikatau ne na Helenanci mai goyo da ainihi take nufin “yanka a miƙe,” ko kuma ‘a yanka babu karkata.’
      (2 Timothy 2:15) The expression “handling . . . aright” is from a compound Greek verb that originally meant “straightly cutting,” or ‘to cut straight.’ [4]

    4. Aikatau na yare na asali da aka yi amfani da shi a nan yana nufin ci gaba da aiki.
      The original-language verb used here denotes continuous action. [5]

    5. Mecece ma’anar aikatau na Ibrananci da aka juya “saurara” da kuma ‘tarar da’ a Kubawar Shari’a 28:2?
      What is the meaning behind the Hebrew verbs rendered “keep listening” and “overtake” at Deuteronomy 28:2? [6]

    6. An yi amfani da wannan aikatau, “sauri” sau huɗu game da wannan matar a labarin.
      Four times in this one account we find the same verb, “to hasten,” used regarding this woman. [7]

    7. Wata ma’anar aikatau na Helenanci da aka fassara ‘kula da’ yana nufin “a ziyarci.”
      One meaning of the Greek verb translated “to look after” is “to visit.” [8]

    8. Abin farin ciki, kalmar aikatau na Helenanci da Bulus ya yi amfani da ita a nan an ɗauko ne daga kalmomin nan “tafin hannu.”
      Interestingly, the Greek verb Paul used here is derived from the word for “knuckles.” [9]

    9. 2 Aikatau na Ibrananci da aka juya “saurara” a Kubawar Shari’a 28:2 na nufin ci gaba da sauraro.
      2 The Hebrew verb rendered “keep listening” at Deuteronomy 28:2 denotes continuous action. [10]

    10. (b) Menene aikatau na Ibrananci da aka fassara ‘[ka] yi tunani’ yake nufi?
      (b) What does the Hebrew verb translated “concern [oneself]” mean? [11]

    11. 10 Kalmar aikatau ta Ibrananci da aka fassara ‘yin tunani’ tana nufin “bin abu a zuciya.”
      10 The Hebrew verb translated “concern [oneself]” also means “meditate, muse,” “go over a matter in one’s mind.” [12]

    12. Wani littafin bincike ya bayyana cewa: “Aikatau na Ibrananci na kalmar nan ji yana kuma nufin matakan da aka ɗauka a sakamakon hakan.”
      One reference work explains: “Hebrew verbs for feelings sometimes refer as well to the actions that result from them.” [13]

    13. (Zabura 97:10) Kalmar nan “lizimci” fassara ce ta aikatau na Helenanci da take nufin “mannewa.”
      (Psalm 97:10) The word “cling” is a translation of a Greek verb that literally means “to glue.” [14]

    14. Alal misali, ka yi la’akari da aikatau na Ibrananci ra·chamʹ, wanda sau da yawa aka fassara shi “yin jinƙai” ko kuma “ji tausayi.”
      Consider, for example, the Hebrew verb ra·chamʹ, which is often rendered “show mercy” or “have pity.” [15]

    15. Aikatau na Helenanci da aka fassara “biɗan aiki” yana nufin mutum ya miƙa hannunsa don ya ɗauki wani abin da hannunsa bai kai ba.
      The Greek verb translated “reaching out” means stretching to grasp something, perhaps something beyond your normal reach. [16]

    16. (2 Timothawus 2:2) In ji wani ƙamus, kalmar aikatau “koya” tana nufin “a ilimantar saboda ya dace, ya ƙware, ya gwaninta.”
      (2 Timothy 2:2) According to a dictionary, the verb “to train” means “to teach so as to make fit, qualified, or proficient.” [17]

    17. Kalmar Helenanci da aka yi amfani da ita a nan ta samo asali ne daga aikatau da take nufin “a kyale, ko a sake.”
      The Greek word used here comes from a verb meaning “to let loose, to release.” [18]

    18. Aikatau na Ibrananci da aka fassara ‘tarar da’ an gano cewa furci ne na farauta wanda sau da yawa yana nufin “a kama” ko “a kai ga.”
      The Hebrew verb translated “overtake” has been identified as a hunting term most often meaning “to catch up with” or “to reach.” [19]

    19. Vine ya kuma kula cewa kalmar suna “gicciya” da kuma ta aikatau “gicciye” suna nufin “gungume ne . . . da ya bambanta da wanda coci suka yarda da shi wanda aka gicciye.”
      Vine further notes that both the noun “cross” and the verb “crucify” refer to “a stake or pale . . . distinguished from the ecclesiastical form of a two beamed cross.” [20]

    20. (Yohanna 16:1-3) Wani ƙamus na Littafi Mai Tsarki ya yi bayani cewa irin kalmar aikatau da aka yi amfani da ita a nan “tuntuɓe” tana nufin “a sa mutum ya kasance da rashin yarda kuma ya yi watsi da wanda ya kamata ya amince da shi kuma ya yi masa biyayya; a sa ya bauɗe.”
      (John 16:1-3) One Bible lexicon explains that a form of the verb here rendered “stumbled” means “to cause a person to begin to distrust and desert one whom he ought to trust and obey; to cause to fall away.” [21]

    21. Amma, a Zabura 103:13, aikatau na Ibrananci ra·chamʹ yana nufin jinƙai, ko kuma juyayi, da uba yake yi wa ’ya’yansa.
      Interestingly, though, at Psalm 103:13, the Hebrew verb ra·chamʹ connotes the mercy, or compassion, that a father shows to his children. [22]

    22. Wani littafin neman bayani ya yi bayani cewa aikatau ra·chamʹ “yana nuna juyayi mai zurfi kuma mai taushi, kamar wanda yake zuwa idan aka fuskanci kasawa ko kuma wahalar waɗanda muke ƙauna ko kuma waɗanda suke bukatar taimakonmu.”
      One reference work explains that the verb ra·chamʹ “expresses a deep and tender feeling of compassion, such as is aroused by the sight of weakness or suffering in those that are dear to us or need our help.” [23]

    23. Aikatau na Helenanci da aka fassara “yi alhini” yana nufin “a janye hankalin zuciya.”
      The Greek verb rendered “be anxious” means “to have the mind distracted.” [24]

    24. Aikatau na Ibrananci da aka fassara “daskare” yana nufin ya yi kauri.
      The Hebrew verb translated “congealed” means to shrink or thicken. [25]

    25. A cikin Nassosi, aikatau na Ibrananci da na Helenanci da suke da ma’ana ta juyowa suna da ma’anar juya baya, sake juyawa.
      In the Scriptures, Hebrew and Greek verbs pertaining to conversion have the sense of turning back, turning around. [26]


Retrieved June 23, 2019, 6:12 pm via glosbe (pid: 21001)