Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:aikin makaranta

Discussion page of aikin makaranta

Glosbe's example sentences of aikin makaranta [1]

  1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar aikin makaranta:
    1. Ka yi aikin makaranta.
      Fulfill your assignments. [2]

    2. 12 Ƙari ga mahalli marar kyau, akwai kuma matsi na aikin makaranta da jarabawa.
      12 In addition to the bad environment, there is the pressure of schoolwork and examinations. [3]

    3. Ka yi aikin makaranta.
      Fulfill assignments. [4]

    4. Domin taronmu abu ne mai tsarki, kada mu bari aiki, ko aikin makaranta, ko makarantar yamma, su hana mu taruwa da ’yan’uwanmu masu bi.
      Out of respect for the sacred nature of our meetings, we do not allow secular work, school homework, or evening schooling to cause us to miss out on meeting regularly with our fellow believers. [5]

    5. A wasu lokatai kuma aikin makaranta na ba da zarafin yabo ga Jehovah.
      At times, school projects have also opened up opportunity to bring praise to Jehovah. [6]

    6. Sa’ad da yaro ya soma makaranta, iyaye suna bukatan su sa ɗansu ko ’yarsu ta ɗauki aikin makaranta a matsayin hakki mai muhimmanci da shi ko ita ya kamata ta kula da shi.
      When a child begins school, parents should expect the child to view his or her schoolwork as an important responsibility that the child must care for. [7]

    7. Da yawa suna shiri don wannan tun da wuri ta koyon aikin hannu a makaranta ko kuma daga iyayensu.
      Many plan ahead for this responsibility by learning a trade in school or from their parents. [8]

    8. Za mu iya gani kamar yin aikace-aikacen gida da makaranta da aikin karɓan albashi da yin cefane da kuma sauransu ba za su iya shafan dangantakarmu da Allah ba.
      Housework, schoolwork, secular work, shopping, and the like might on the surface seem to have little to do with spiritual concerns. [9]

    9. Matasa za su tsai da shawara game da irin makaranta ko aikin da za su yi, da kuma wasu batutuwa.
      Adolescents have to make decisions about education, employment, and other matters. [10]

    10. “Bayan wasu ’yan shekaru da gama makaranta, na sami aikin babban magatakarda na wani sanannen lauya a Landan,” in ji Jean.
      “Within a few years after leaving school, I got a job as an executive secretary for a prominent London solicitor,” says Jean. [11]

    11. Wane ja-gora ne iyaye za su iya ba ’ya’yansu game da darussan da za su zaɓa a makaranta da kuma aikin da za su yi?
      What guidance can parents provide young ones in their choice of school subjects and vocation goals? [12]

    12. Hakika, iyaye suna son ’ya’yansu su sami nasara a makaranta kuma su koyi aikin da za su kula da kansu da shi a nan gaba.
      Of course, they want their children to do well in school and learn the necessary skills for maintaining themselves in the days ahead. [13]

    13. Idan malamin ba zai iya zuwa ba, Elizabeth za ta tsaya bayan an tashi a makaranta ta gabatar da aikin ga malamin.
      If a teacher could not attend, Elizabeth stayed after school and presented the talk to the teacher. [14]

    14. Ka ƙarfafa kowa ya yi aikin da aka ba shi a makaranta, ya yi kalami sa’ad da ake tattauna sashen karatun Littafi Mai Tsarki, kuma ya yi amfani da shawarar da ake ba da mako-mako a littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education.
      Encourage all to be diligent in fulfilling their assignments, in participating in Bible highlights, and in applying the suggestions given weekly from the Ministry School book. [15]

    15. A nan take sai uban ya yi fushi, ya tuna dukan lokatai da yaron bai yi aikin da aka ba shi daga makaranta ba.
      The father immediately gets angry, thinking back to the many times the boy put off doing his homework. [16]

    16. Ka ƙarfafa kowa ya yi aikin da aka ba shi a makaranta, ya yi kalami a taƙaitawa na Littafi Mai Tsarki, kuma ya yi amfani da shawarwarin da ake ba da mako-mako a littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education.
      Encourage all to be diligent in fulfilling their assignments, in participating in Bible highlights, and in applying the suggestions given weekly from the Ministry School book. [17]

    17. “Maimakon in yi amfani da duka kuzari na a wajen aikin likita, zane, ko koyarwa a makaranta, na yanke shawarar yin amfani da rayuwata cikin jituwa da keɓe kaina da na yi ga Allah,” in ji shi.
      “Instead of devoting all my energies to medicine, art, or secular teaching, I resolved to use my life in line with my dedication to God,” he explains. [18]

    18. Emily: “Matsalar ta soma ne sa’ad da ’yata Jenny, ’yar shekara sha uku, ba ta fahimci aikin da malamarta ta ba ta a makaranta ba.
      Emily: “The trouble began when my 13-year-old daughter, Jenny, had difficulty understanding her teacher’s requirements for a school assignment. [19]

    19. Sa’ad da Ɗaliban makarantar Gilead na aji na 124 suke makaranta, sun yi awoyi 3,000 a aikin wa’azi.
      As part of their Gilead training, the 124th class spent a combined total of some 3,000 hours in the preaching work. [20]

    20. Shin ka kusan gama makaranta kuma kana tunanin irin aikin da za ka yi?
      Are you finishing your secular schooling and wondering what to do with your life? [21]

    21. Wani firist kuma yana lalata da yaran makaranta sa’ad da yake duba aikin da ya ba su.
      Another priest sexually abused pupils while reviewing their homework with them. [22]

    22. Wannan ba makaranta ba ce, amma ana koya wa waɗanda suke wannan aikin yadda ake ayyuka dabam-dabam na gini don su taimaka wajen gine-gine.
      This is not a school, but under this arrangement volunteers are taught various skills so that they can assist with building projects. [23]

    23. Ya shaƙu ainun a ayyukan makaranta kuma ya daina halartan taro da saka hannu a aikin wa’azi.
      He became very involved in school activities and stopped attending meetings and participating in the preaching work. [24]

    24. A wasu lokatai, dattiɓan ikilisiya, masu aiki a rassa, waɗanda suke aikin wa’azi na cikakken lokaci (majagaba) suna samun koyarwa ta musamman a makaranta da aka kafa musu.
      From time to time, special courses have been established for training congregation elders, voluntary workers at branches, and those engaged full time (as pioneers) in the witnessing work. [25]


Retrieved June 23, 2019, 6:13 pm via glosbe (pid: 18229)