Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Glosbe's example sentences of aiko [1]

  1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar aiko:
    1. Kafin Ibrahim ya ba da hadayan ɗansa, Allah ya aiko da mala’ika.
      At the critical moment, God intervened by means of an angel. [2]

    2. Yesu ya gaya wa almajiransa: “Uba wanda ya aiko ni, shi ne ya ba ni umurni, abin da zan faɗi, da magana da zan yi kuma.”
      “The Father himself who sent me has given me a commandment as to what to tell and what to speak,” Jesus told his disciples. [3]

    3. Lokacin da yake duniya Yesu ya ce: “Ba wanda ya iya zuwa wurina, sai dai Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi . . .
      While on earth, Jesus stated: “No man can come to me unless the Father, who sent me, draws him . . . [4]

    4. (Yohanna 17:20, 21) Cikin ƙauna, Allah ya aiko Ɗansa ya ba da ransa domin ceton shafaffu da kuma duniyar mutane masu biyayya.
      (John 17:20, 21) Out of love, God sent his Son to give his life for the salvation of the anointed ones and the world of obedient mankind. [5]

    5. • Me ya sa za a iya cewa ƙauna mafi girma da Jehovah ya nuna mana ita ce aiko da Ɗansa ya wahala kuma ya mutu dominmu?
      • Why can it be said that Jehovah’s sending his Son to suffer and die for us is the greatest act of love ever performed? [6]

    6. Allah ya yi haka yayin da ya aiko Ɗansa zuwa duniya.
      God did so when he sent his Son to the earth. [7]

    7. Bugu da ƙari, Musa zai gaya wa ’yan Isra’ila: “ ‘[Jehobah] Allah na kakanninku, wato na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu ya aiko ni gare ku.’
      Further, Moses was to tell the sons of Israel: “Jehovah the God of your forefathers, the God of Abraham, the God of Isaac and the God of Jacob, has sent me to you.” [8]

    8. Sai ya bayyana dalilin da ya sa Ibrahim ya aiko shi.
      So he explains why Abraham has sent him. [9]

    9. “Dole in kai bishara ta mulkin Allah ga sauran birane kuma: gama saboda wannan aka aiko ni.” —Luka 4:43
      “I must also declare the good news of the Kingdom of God to other cities, because for this I was sent.” —Luke 4:43 [10]

    10. A ƙasar Babila ta dā, an jefa Ibraniyawa uku cikin wuta don su mutu, amma Allah “ya aiko mala’ikansa, ya ceci bayinsa.” —Daniyel 3: 19-28.
      In ancient Babylon when three young Hebrews were condemned to die in a fiery furnace, God “sent his angel and rescued his servants.” —Daniel 3:19-28. [11]

    11. Amma Jehobah bai aiko da kowace halittar ruhu ba.
      But Jehovah did not send just any spirit creature. [12]

    12. Ƙaunar Jehovah da ya aiko Ɗansa zuwa duniya da ta buɗe hanyar samun rai madawwami ya motsa su.
      They were deeply moved by Jehovah’s love in sending his Son to the earth, thus opening the way to everlasting life. [13]

    13. Kamar yadda muka koya a Babi na 5, an aiko Yesu duniya domin ya fanshe mu daga zunubi da mutuwa.
      As we learned in Chapter 5, Jesus was sent to the earth to serve as a ransom to redeem us from sin and death. [14]

    14. (Matta 3:16, 17) Bayan ya ji kuma ya ga abin da ya faru, Yohanna ba shi da sauran wata shakka cewa Allah ne ya aiko Yesu.
      (Matthew 3:16, 17) After seeing and hearing what happened, John had no doubt that Jesus was sent by God. [15]

    15. Ya ce: “Ba wanda ya iya zuwa wurina, sai dai Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi.”
      He said: “No man can come to me unless the Father, who sent me, draws him.” [16]

    16. 19 Wata mata a ƙasar Guyana ta gaya wa wani majagaba da ya zo gidanta, “Allah ne ya aiko ka.”
      19 “God must have sent you,” said a woman in Guyana to the pioneer at her door. [17]

    17. (Matta 20:20-23) A wani lokaci kuma Yesu ya ce a fili: “Ni bisa ga kaina ban iya kome ba . . . ba na bin nufin kaina ba, amma nufin wanda ya aiko ni.”—Yohanna 5:30; 14:28; Filibbiyawa 2:5, 6.
      (Matthew 20:20-23) On another occasion, Jesus freely admitted: “I cannot do a single thing of my own initiative . . . I seek, not my own will, but the will of him that sent me.” —John 5:30; 14:28; Philippians 2:5, 6. [18]

    18. Sa’ad da Gideon ya lura cewa mala’ikan ya sa wuta ta fito daga sandar da ke hannunsa kuma ta ƙona abincin, sai ya gane cewa lallai Jehobah ne ya aiko mala’ikan.
      When the food was miraculously consumed by fire at the touch of the angel’s staff, Gideon realized that the angel was indeed Jehovah’s representative. [19]

    19. Hanya ɗaya ita ce ta aiko da ruhunsa mai tsarki.
      One way is by sending forth his holy spirit. [20]

    20. • Yaushe aka aiko da “ruhu na gaskiya” zuwa ga Kiristoci na farko, kuma ta yaya ya kasance “mai-taimako”?
      • When was “the spirit of the truth” sent to the early Christians, and how did it prove to be a “helper”? [21]

    21. A nan mun sami waɗannan kalmomi na Babban Malami: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.”
      Here we find these words of the Great Teacher: “This means everlasting life, their taking in knowledge of you, the only true God, and of the one whom you sent forth, Jesus Christ.” [22]

    22. Allah ya aiko da wani bawansa ya taimake shi, a sakamakon hakan, Ba-habashin “ya kama tafiyarsa yana murna.”—Ayyukan Manzanni 8:26-39.
      God sent one of His servants to help him, with the result that the Ethiopian man “kept going on his way rejoicing.” —Acts 8:26-39. [23]

    23. 7 Allah ya aiko da Ɗansa, halittarsa na farko daga ƙungiyarsa ta halittun ruhu wadda take sama mai kama da matarsa don ya zama “zuriya” da aka yi alkawarinta.
      7 God sent forth his Son, his first creation, from His wifelike organization of spirit creatures in heaven to be the promised “seed.” [24]

    24. 27:11, 12) Shekaru saba’in bayan haka, ƙalilan cikinsu sun shaida cikar wani annabcin da Ishaya ya yi, ya ce: “Allah Mai Tsarki na Isra’ila, Ubangiji wanda ya fanshe ku ya ce, ‘Domin in cece ku zan aiko sojoji gāba da Babila, Zan rushe ƙofofin birni.’”—Isha.
      27:11, 12) There, 70 years later, God’s people witnessed the fulfillment of an amazing prophecy: “This is what Jehovah says, your Repurchaser, the Holy One of Israel: ‘For your sakes I will send to Babylon and bring down all the bars of the gates.’” —Isa. [25]

    25. Sun roƙe mu mu aiko wani don ya ƙara koyar da su.
      They begged us to send someone to teach them more. [26]


Retrieved June 23, 2019, 6:13 pm via glosbe (pid: 21004)