Toggle menu
24.1K
670
183
158.6K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:amount

Discussion page of amount

Glosbe's example sentences of amount [1]

  1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar amount:
    1. 4 Jesus miraculously provided a large amount of fine wine, enough for a sizable group.
      4 Wannan mu’ujiza da Yesu ya yi ya sa dukan mutanen sun sami isashen ruwan inabi. [2]

    2. Other Scriptural responsibilities may reduce the amount of time that we can set aside for the preaching work.
      Wasu hakki na Nassi suna iya rage yawan lokaci da za mu keɓe don aikin wa’azi. [3]

    3. Patience is required to allow a reasonable amount of time for God’s Word and holy spirit to work on the student’s heart.
      Muna bukatar mu ba shi lokaci don Kalmar Allah ta ratsa zuciyarsa kuma ruhu mai tsarki ya taimaka masa. [4]

    4. And by saying that the mountains were “born” and the earth was brought forth as with “labor pains,” the psalmist is showing great respect for the amount of work involved when Jehovah created these things.
      Cewa an “ɓullo” da duwatsu kuma an sifanta duniya kamar da ‘naƙuda,’ mai Zabura yana daraja yawan aiki da ke ciki ne yayin da Jehovah ya halicce waɗannan abubuwa. [5]

    5. No amount of prayer or research will reveal a complete answer to questions like these.
      Ba za mu iya sanin amsoshin waɗannan tambayoyin ba ko da mun yi addu’a ko kuma tunani a kansu. [6]

    6. Just as he uses sexual immorality and materialism to cause some to stumble, he tries to breach the integrity of others by means of questionable treatments that amount to the use of occult powers and spiritism.
      Kamar yadda yake amfani da lalata da kuma abin duniya don ya sa wasu su yi tuntuɓe, yana ƙoƙarin ya lalata amincin wasu ta wajen yin amfani da hanyoyin magani da suka yi daidai da yin amfani da sihiri. [7]

    7. 3 No amount of satanic opposition will ever prevent Jehovah’s Witnesses from giving Jehovah the exclusive worship that he deserves.
      3 Babu hamayya da Shaiɗan zai kawo da za ta taɓa hana Shaidun Jehobah su bauta masa shi kaɗai don ya cancanci hakan. [8]

    8. It takes a considerable amount of energy and time to adapt to new food, a new climate, a new language, and a new preaching territory and to make new friends.”
      Ba shi da sauƙi mutum ya saba da sabon abinci ko yanayi ko yare ko sabon yankin wa’azi ko kuma abokai.” [9]

    9. The entire camp, including women, children, and the Levites, may amount to over three million people.
      Dukan mutanen, mata, yara, da kuma Lawiyawa ƙila sun fi miliyan uku. [10]

    10. * Thus, seven times —twice the amount of three and a half times— would equal 2,520 days.
      * Da hakan, in ka ninka lokatai uku da rabi sau biyu, za ka sami lokatai bakwai kuma hakan zai yi daidai da kwanaki 2,520. [11]

    11. MIA: “It takes persistence and a tremendous amount of patience to teach Angelo the simplest things.
      MIA: “Ko da abu mai sauƙi ne muke so mu koya masa sai mun dāge kafin Angelo ya fahimta, saboda haka, muna bukatar mu bi da shi cikin haƙuri sosai. [12]

    12. 11. (a) How did Jesus illustrate that not all would be able to do the same amount in spreading the Kingdom message?
      11. (a) Ta yaya ne misalin Yesu ya nuna cewa ba duka ne za su iya sa daidai yawan lokaci ɗaya cikin shelar saƙon Mulkin ba? [13]

    13. His conduct may not amount to gross wrongdoing, but it disturbs you.
      Abin da yake yi ba laifi mai tsanani ba ne, amma yana damunka. [14]

    14. Rather than specifying an amount or a percentage, Paul merely suggested that “on the first day of every week, each one . . . should set aside a sum of money in keeping with his income.”
      Maimakon ambata ko nawa za a bayar ko kuma yawan ushiri, Bulus ya ba da shawara cewa “a kan rana ta fari ga bakwai kowane a cikinku shi ajiye ajiya, gwargwadon samuwa da ya ke yi.” [15]

    15. 13 Consider, too, the amount of time you spend on recreation and entertainment.
      13 Ka yi la’akari kuma da yawan lokacin da nishaɗin zai ci. [16]

    16. Because my life is now centered on spiritual things, I have a measure of happiness and contentment that no amount of money or prestige could give me.”
      Saboda yanzu na sa zuciyata a abubuwa na ruhaniya, ina samu farin ciki da kuma gamsarwa da arziki ko ɗaukaka ba za su iya ba ni ba.” [17]

    17. If we have a limited amount of energy, we may find it appropriate to avoid exhausting activities earlier in the day so that we will have strength to attend a Christian meeting in the evening.
      Idan ba mu da ƙarfi sosai, zai dace mu guji ayyuka da za su gajiyar da mu da sauri don mu samu ƙarfin halartan taron Kirista da yamma. [18]

    18. Soon thereafter, she received a job offer that would pay her 3,000 euros a month —a high amount in comparison with the average wages in her country.
      Ba da daɗewa ba, ta samu aikin da za a biya ta daloli 4,200 a wata, kuɗin yana da yawa sosai idan aka gwada da kuɗin da ake biyan ma’aikata a ƙasarsu. [19]

    19. And we can do further research using the vast amount of material provided by the faithful and discreet slave class.
      Kuma za mu iya ƙara neman bayani ta wajen amfani da abubuwa da yawa da bawan nan mai aminci mai hikima ya yi tanadinsu. [20]

    20. But they do not in themselves amount to real love for God.
      Amma ba daidai yake da ƙauna ta gaske ga Allah ba. [21]

    21. On this occasion, King Ahasuerus made an exception to what appears to have been a Persian custom of urging one another to drink a certain amount at such gatherings.
      A wannan bikin, Sarki Ahasuerus ya yi watsi da al’adar Farisawa na ƙarfafa juna su sha barasa daidai kima a irin wannan taron. [22]

    22. It is just the right distance from the sun to get the proper amount of light and heat.
      An ajiye ta da nisa yadda ya dace domin samun haske da zafi da ake bukata. [23]

    23. (Ephesians 5:15, 16) True, circumstances vary, and not all can spend the same amount of time in this lifesaving work.
      (Afisawa 5:15, 16) Hakika, yanayi sun bambanta, kuma ba duka ne za su iya ɓad da yawan lokaci ɗaya a wannan aikin cetar da rai ba. [24]

    24. I also saw the need to stop smoking and to control the amount of alcohol I drank.
      Na kuma gane cewa ina bukatar daina shan taba da kuma daidaita yawan giyar da nake sha. [25]

    25. Jesus showed the right view when he commented on the treasury box at the temple in Jerusalem and those contributing: It is one’s capacity to give and the spirit of giving that count, not the amount of money.—Luke 21:1-4.
      Yesu ya nuna ra’ayin da ya kamata a kasance da shi lokacin da ya yi maganar asusu a haikali cikin Urushalima da waɗanda suke ba da kyauta: Abin da mutum zai iya ba da ne, ta halin bayarwa ke da muhimmanci, ba abin da aka bayar ba.—Luka 21:1-4. [26]


Retrieved June 24, 2019, 6:35 am via glosbe (pid: 2204)