Toggle menu
24.1K
669
183
158.4K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:arguments

Discussion page of arguments

Glosbe's example sentences of arguments [1]

  1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar arguments:
    1. No wonder that it often tops the list as the most common cause of marital arguments.
      Babu shakka, shi ya sa ya zama ainihin abin da ke jawo gardama tsakanin ma’aurata. [2]

    2. Rather than seeking to win arguments, it is best to pose questions that make people think and reach their own conclusions.”
      Maimakon yin jayayya, zai fi kyau mu yi tambayoyin da za su sa mutane su yi tunani kuma su tsai da shawara da kansu.” [3]

    3. Like Paul, we should avoid arguments.
      Kamar Bulus, mu guji musu. [4]

    4. (John 7:16) Jesus’ statements were clear, his exhortations persuasive, and his arguments irrefutable.
      (Yohanna 7:16) Furcin Yesu sun fita sarai, gargadinsa suna motsawa, maganarsa ta fi gaban a musanta. [5]

    5. Debates, arguments, and wrangling are the norm among those who look at life in a fleshly way.
      Musu da jayayya abubuwa ne na kullum tsakanin waɗanda suke ɗaukan rayuwa a hanya ta jiki. [6]

    6. When tired parents clash over how to train a child, small disputes might explode into major arguments.
      Idan iyaye da suka gaji suka yi gardama a kan yadda za su yi wa yaronsu horo, gardamar takan yi tsanani. [7]

    7. What additional Scripture texts or arguments can I think of that would provide further support for the conclusions being presented in this article?’
      Wane ƙarin Nassi ko kuma bayani ne zan iya yin tunaninsa da zai ƙara taimaka mini game da bayanin da aka gabatar a wannan talifin?’ [8]

    8. Careful study of his arguments proves beyond doubt the sureness and power of the resurrection hope.
      Nazarin wannan muhawararsa a hankali ya tabbatar cewa begen tashin matattu tabbatacce ne kuma ba wani abin musu. [9]

    9. The prosecutor replied: “I am not competent to comment on clerical arguments.”
      Sai lauyar gwamnatin ta sake cewa yadda take ji bai shi da muhimmanci tun da ba ta san addini sosai ba. [10]

    10. (2 Timothy 2:7) At times, congregation members may get caught up in disputes about trifles and speculative arguments.
      (2 Timothawus 2:7) A wasu lokutta, waɗanda suke cikin ikklisiya sai su kaure da jayayya game da ƙananan al’amari da kuma yin musu. [11]

    11. The apostle Paul admonished fellow Christians in Philippi: “Keep doing all things free from murmurings and arguments, that you may come to be blameless and innocent, children of God without a blemish in among a crooked and twisted generation, among whom you are shining as illuminators in the world.”
      Manzo Bulus ya gargaɗi ’yan’uwa Kiristoci a Filibbi: “Sai ku aikata abu duka banda gunaguni da gardama; domin ku zama marasa-zargi, marasa-illa, ’ya’yan Allah marasa-aibi a cikin tsakiyar karkataciyar tsara mai-serare, da a ke ganinku daga cikinsu kamar haskoki a cikin duniya.” [12]

    12. But later, as I did some research on the apostates’ arguments against Jehovah’s Witnesses, I became aware of how crafty the false teachers were.
      Amma daga baya, sa’ad da na yi wasu bincike a kan gardama da ’yan ridda suke yi game da Shaidun Jehobah, sai na fahimci cewa waɗannan malaman ƙarya masu makirci ne. [13]

    13. 1:9) Paul further stated: “I am saying this so that no one may delude you with persuasive arguments.
      1: 9, Littafi Mai Tsarki) Bulus ya ƙara cewa: “Wannan nake faɗi, domin kada kowa ya ruɗe ku da magana mai-rinjayarwa. [14]

    14. Our arguments were replaced with lively Bible discussions.
      A maimakon haka, muna jin daɗin tattaunawa game da Littafi Mai Tsarki. [15]

    15. Elihu first listened to the arguments presented by Job and his three companions.
      Elihu ya fara saurarar abubuwan da Ayuba da abokanansa guda uku suka ce. [16]

    16. 5:11) We are not benefited by trying to refute the arguments of apostates or those who are critical of Jehovah’s organization.
      5:11) Ba za mu amfana ba idan muna neman mu bayyana wa ’yan ridda da waɗanda suke kushe ƙungiyar Jehobah cewa ra’ayinsu ba daidai ba ne. [17]

    17. 13 After reading with your child portions from the brochure The Origin of Life —Five Questions Worth Asking, you could ask what arguments he finds most thought provoking.
      13 Bayan ka karanta wasu shafuffuka na littafin nan Ka Kusaci Jehovah da ɗanka, sai ka tambaye shi ko wanne cikin bayanan ne zai fi sa mutane tunani. [18]

    18. He was laying a foundation, a common ground on which to build his arguments.
      Yana nanata abin da dukansu suka yarda da shi, don ya bayyana dalilinsa. [19]

    19. If we are not careful, how can the normal exchange of ideas degenerate into harmful arguments?
      Idan ba mu mai da hankali ba, yaya taɗin ra’ayoyi da yake daidai zai kawo jayayya mai lahani? [20]

    20. * Remember, though, that our goal is to win hearts, not arguments.
      * Amma ka tuna cewa muradinmu shi ne mu jawo mutane zuwa gaskiya, ba yin gardama da su ba. [21]

    21. Logical arguments presented in a simple manner are often most effective.
      Tabbatarwa da ake bi da shi da sauƙi yakan zama mafi ci. [22]

    22. However, it presented sound Scriptural arguments that limited the identity of Christ’s brothers to those who would rule with him in heaven, and it described the sheep as those who hope to live on earth under the rule of Christ’s Kingdom.
      Amma an bayyana a ciki cewa ’yan’uwan Kristi su ne waɗanda za su yi sarauta tare da shi a sama kawai kuma an kwatanta tumakin a matsayin waɗanda suke da begen yin rayuwa a duniya sa’ad da Kristi ya soma sarauta. [23]

    23. “The ease with which criminals get away unpunished,” observes the magazine Arguments and Facts, “seems to inspire ordinary citizens to commit the most brutal of crimes.”
      “Yadda masu laifi suke kuɓuce wa horo da sauƙi” in ji jaridar Arguments and Facts “yakan sa talakawa su aikata laifuffuka da suka fi tsanani.” [24]

    24. The Court unanimously found that none of the nine charges had any merit, in a number of cases even reasoning carefully to refute the arguments presented.
      Kotun ya ga cewa duk hukunci tara da aka kai ba gaskiya ba ce, kuma a shari’o’i da yawa da kotun ya yi sun yi ƙoƙari sosai su bayyana dalilin da ya sa ƙarar da suka kai ba daidai ba ne. [25]

    25. Hughes and eight associate judges listened to the arguments presented by Brother Hayden Covington, a lawyer for Jehovah’s Witnesses.
      Hughes da wasu alƙalai takwas, suka saurari lauyan Shaidun Jehobah, wato Ɗan’uwa Hayden Covington sa’ad da yake gaya musu abubuwan da suka faru. [26]


Retrieved June 24, 2019, 12:59 pm via glosbe (pid: 11192)