Toggle menu
24.1K
670
183
158.6K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:attempted

Discussion page of attempted

Glosbe's example sentences of attempted [1]

  1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar attempted:
    1. Hence, like former kings of Israel, he attempted to keep them separate by perpetuating calf worship.
      Saboda haka, kamar sarakunan da suka mulki Isra’ila a dā, ya yi ƙoƙari ya raba su ta wajen gabatar da bautar maraƙi. [2]

    2. In May 2012, he was the victim of an attempted robbery and was shot multiple times.
      A watan Mayu ta 2012, ɓarayi sun je fashi kuma ruwan harsashin da suka yi ya same Pablo. [3]

    3. Many men in modern times have attempted to do just that but have failed.
      Wasu mutane a zamaninmu sun nemi su yi hakan, amma sun kasa. [4]

    4. At times, one of Christendom’s churches has attempted to organize and carry out a door-to-door ministry.
      Wasu lokatai cocin Kiristendam sukan yi ƙoƙari su tsara hidima ta ƙofa ƙofa kuma su yi ta. [5]

    5. O’Connor plus 100 rowdies attempted to disrupt the Dublin meeting once more, but the audience enthusiastically supported the speaker.
      O’Connor da maza 100 sun sake zuwa taron da aka yi a Dublin don su ta da ƙura, amma masu sauraron su goyi bayan mai jawabin. [6]

    6. Think about the faith Abraham showed when he attempted to offer up Isaac.
      Ka yi tunanin bangaskiya da Ibrahim ya nuna sa’ad da ya yi kokarin ya mika Ishaku. [7]

    7. At this meeting, held on January 5, 1918, several prominent men who had been dismissed from Bethel attempted to gain control of the organization.
      A taron da aka yi a ranar 5 ga Janairu, 1918, ’yan’uwa da yawa masu ja-goranci da aka sallame su daga Bethel sun yi kulle-kulle don su ƙwace ƙungiyar Jehobah. [8]

    8. Later, he was falsely accused of attempted rape and was imprisoned.
      Bayan haka, an yi masa zargin ƙarya na son yin fyaɗe kuma aka jefa shi kurkuku. [9]

    9. Yet, some copyists and translators have attempted to alter the Bible’s message.
      Duk da haka, wasu mafassara da masu kofe Littafi Mai Tsarki sun nemi su canja saƙon da ke cikinsa. [10]

    10. Centuries later, Agag’s descendants evidently included “Haman the Agagite,” who attempted to wipe out all of God’s people. —Esther 8:3; see Chapters 15 and 16 of this publication.
      Babu shakka, “Haman Ba-agagi” wanda ya nemi ya halaka dukan bayin Allah dangin Agag ne.—Esther 8:3, ka duba Babi na 15 da 16 na wannan littafin. [11]

    11. After Jesus had fasted for 40 days and 40 nights, Satan attempted to appeal to Jesus’ desire for food.
      Bayan da Yesu ya yi azumi na kwana arba’in dare da rana a cikin jeji, sai Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya yaudare shi da abinci. [12]

    12. Jealous Saul, however, attempted —first impulsively, then cunningly, and finally with an army— to kill David.
      Saboda haka, da farko Saul mai kishi ya yi dabarar yadda zai kashe Dauda, a ƙarshe kuma ya kawo sojoji don su kashe shi. [13]

    13. Those inhabitants will also share in the greatest undertaking ever attempted on earth —that of transforming the whole planet into a paradise to Jehovah’s praise.
      Waɗannan mazauna za su kuma sa hannu a aikin da ba a taɓa yi ba a duniya—na mai da dukan duniya aljanna ga yabon Jehobah. [14]

    14. Regarding Julien, a young man who was rather shy, Ludovic says: “Because Julien at times attempted to assert himself in a somewhat clumsy way, his behavior was not natural.
      Sa’ad da Ludovic yake yin kalami game da wani ɗan’uwa mai jin kunya mai suna Julien, ya ce: “Na lura cewa Julien bai da gaba gaɗi a yin wasu ayyuka a cikin ikilisiya, saboda haka, ba ya kintsuwa kuma yana yin wasu abubuwa babu tsari. [15]

    15. After all, he attempted to break down Jesus, so why should he leave us alone? —Matthew 4:1-11.
      Ballantana ma, ya yi ƙoƙarin ya halaka Yesu, me zai sa ya ƙyale mu?—Matiyu 4:1-11. [16]

    16. In a misguided effort to stop hurting my family, I attempted suicide.
      Wata rana, na yi ƙoƙarin kashe kaina, wai don ina so in daina wulaƙanta iyalina. [17]

    17. Or is it because you feel that the other person deliberately attempted to hurt you?
      Ko kuma kana ganin cewa mutumin da gangan ya ɓata maka rai? [18]

    18. These religious leaders attempted to devise a precept to govern conduct in all issues, even trivialities.
      Waɗannan shugabannin addinai sun yi ƙoƙari su kafa ƙa’ida da za ta ja-goranci dukan batu, har ma da ƙananan abubuwa. [19]

    19. One who has attempted to glue two things together knows that both surfaces must be clean before a proper bond can be forged.
      Ƙazamta tana hana mutum samun haɗin kai da Allah da kuma bayinsa. [20]

    20. 15:10, 14; 18:9, 14) Later, Solomon’s brother Adonijah attempted to seize the kingship.
      15:10, 14; 18:9, 14) Daga baya, ɗan’uwan Sulemanu, Adonijah ya yi ƙoƙarin ya ƙwace mulkin. [21]

    21. After false religion is destroyed, what assault on Jehovah’s people will be attempted?
      Wane farmaki ne za a kai wa mutanen Allah bayan an halaka addinin ƙarya? [22]

    22. He even attempted to burn incense at the temple —a privilege reserved for the Aaronic priests.
      Ya kasance da fahariya har ya so ya ƙona turare a cikin haikali, aikin da firistoci ne kawai suke da gatan yi. [23]

    23. Just as Brother Young made arrangements for Brother Rutherford’s talk, the government imposed martial law because of an attempted coup d’état.
      Sa’ad da Ɗan’uwa Young yake yin shirye-shirye don Ɗan’uwa Rutherford ya zo ya yi jawabi, sai gwamnati ta kafa wata doka da ta hana mutane yin wasu ayyuka domin an so a yi juyin mulki. [24]

    24. HISTORY: ADDICTED TO ALCOHOL, ATTEMPTED SUICIDE
      TARIHI: MASHAYIYA, KUMA TA TAƁA YUNƘURIN KASHE KANTA [25]

    25. 18. (a) What happened when David attempted to bring the Ark to Jerusalem?
      18. (a) Menene ya faru sa’ad da Dauda yake son ya kai Akwatin Urushalima? [26]


Retrieved June 26, 2019, 11:54 am via glosbe (pid: 3711)