Toggle menu
24.1K
669
183
158.4K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:demonstrating

Discussion page of demonstrating

(Luke 7:1-10) That was in addition to demonstrating by his actions his love for God’s people.

(Luka 7:1-10) Waɗannan domin ya daɗa nuna ta wurin ayyukansa ne yadda yake ƙaunar mutanen Allah.



Start by demonstrating how the magazines may be offered, using the two sample presentations provided.

Da farko, ka sa a yi gwaji a kan yadda za a iya ba da mujallun ta wajen yin amfani da gabatarwar da aka bayar.



2 As time went by, Jehovah shed increasing light on that prophecy, thus demonstrating the certainty of its eventual fulfillment.

2 Bayan wani ɗan lokaci, Jehobah ya ƙara ba da haske a kan wannan annabcin, wanda hakan ya tabbatar da cewa annabcin zai cika.



Conclude by demonstrating how to start a study on the initial call.

Ka kammala ta wajen gwada yadda za a soma nazarin Littafi Mai Tsarki a ziyara na farko.



Start by demonstrating how the magazines may be offered, using the two sample presentations on this page.

Da farko, ka sa a nuna yadda za a iya ba da mujallu ta wajen yin amfani da gabatarwa biyu da ke wannan shafin.



9 Both Moses and Jesus performed miracles, thus demonstrating that they had Jehovah’s backing.

9 Musa da Yesu sun yi mu’ujizai, kuma hakan ya nuna cewa suna da goyon bayan Jehobah.



By demonstrating respect for his feelings, we may open the door for another publisher to give a witness in the future. —1 Pet.

Idan muka daraja ra’ayinsa, hakan zai iya sa ya saurari wani mai shela a nan gaba.—1 Bit.



After a sobering experience demonstrating his own weakness, he was forced to confess the greatness of Jehovah and His almighty power.

Bayan ya fuskanci yanayi na ladabtarwa da ya nuna ajizancinsa, aka tilasta masa ya furta ɗaukakar Jehovah da kuma girman ikonsa.



We might think of an instructor standing before his students, demonstrating what he wants them to learn.

Muna iya tunanin malami yana tsaye a gaban ɗalibai, yana kwatanta musu abin da yake so su yi.



Demonstrating Thankfulness With Our “Valuable Things”

Nuna Godiya da ‘Wadatarmu’



Demonstrating Our Submission

Nuna Biyayyarmu



11 Moses and Korah stand in sharp contrast when it comes to demonstrating respect for Jehovah’s arrangement and his decisions.

11 Za mu yi magana game da mazaje biyu da rayuwarsu ba iri ɗaya ba ce, wato, Musa da Kora.



(Genesis 12:11-13; 20:13) In this, Abram set a fine example for husbands to exercise loving headship, and Sarai, by demonstrating her subjection, is an example for wives today. —Ephesians 5:23-28; Colossians 4:6.

(Farawa 12:11-13; 20:13) Ta haka, Abram ya bar misali mai kyau ga maza su nuna shugabanci mai kyau, kuma Saraya, ta wurin miƙa kanta, misali ce ga mata a yau.—Afisawa 5:23-28; Kolossiyawa 4:6.



20 Yes, by demonstrating humility, displaying diligence, and upholding the high standards of God’s Word, we will continue to enjoy a full and meaningful share in the great spiritual harvest now under way.

20 Hakika, ta wurin nuna tawali’u, ƙwazo, da kuma ɗaukaka mizanai masu girma na Kalmar Allah, za mu ci gaba da moran cikakken aikin girbi mai girma da ake yi a yanzu da kuma yin rayuwa mai ma’ana.



They need an approved standing with God, which they can gain by exercising faith in the sin-atoning value of Jesus’ sacrifice and by demonstrating that faith by obedience.

Suna bukatar su sami amincewa wajen Allah, wadda za su iya samu ta wurin bayyana bangaskiya cikin darajar hadayar kafarar zunubi na Yesu kuma ta wurin nuna bangaskiyar nan wajen yin biyayya.



Ten Plagues were brought on the land, demonstrating Jehovah’s power in amazing ways.

An aika annoba goma bisa ƙasar, yana nuna ikon Jehovah a hanyoyi na ban mamaki.



(b) In what way is demonstrating love for others related to Christian maturity?

(b) Ta yaya Kiristocin da suka manyanta suke sha’ani da mutane?



Start by demonstrating how the magazines may be offered, using the two sample presentations on this page.

Ka sa a yi amfani da gabatarwa biyu da ke wannan shafin don nuna yadda za mu iya ba da mujallun.



In what way is Jesus demonstrating his love of righteousness and justice now, and what should we ask ourselves?

A wace hanya ce Yesu yake nuna ƙaunarsa ga adalci da shari’a yanzu, kuma me ya kamata mu tambayi kanmu?



A world full of injustice gave Jehovah the opportunity of demonstrating himself to be the pinnacle of justice.

Duniya da take cike da rashin adalci ta ba Jehobah zarafin nuna cewa shi ne mafi adalci.



20 min: “Improving Our Skills in the Ministry —Demonstrating a Bible Study by Using the Bible Teach Book.”

Minti 20: “Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi—Nuna Yadda Ake Nazari da Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?”



Let us never allow this cold, loveless world to prevent us from demonstrating our love for others.

Bari kada mu yarda rashin ƙauna na wannan duniya ta hana mu nuna ƙauna ga mutane.



14 Exerting themselves in the ministry, millions of God’s people around the world are demonstrating their appreciation for the training they receive.

14 Mutanen Allah da yawa a dukan duniya suna nuna godiyarsu don koyarwa da suke samu ta wajen yin ƙwazo sosai a hidima.



• What are some experiences demonstrating Christian love?

• Waɗanne labarai ne suka nuna ƙauna ta Kirista?



Start by demonstrating how the magazines may be offered using the sample presentations on this page.

Ka sa a yi gwajin da zai nuna yadda za a iya ba da mujallu ta wajen yin amfani da gabatarwa da ke wannan shafin.