Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:difficult

Discussion page of difficult

Was the change difficult?

Shin yin hakan yana da sauƙi ne?



If this seems too difficult, share your feelings about the matter with him.

Idan wannan yana da wuya sosai, ki faɗa yadda ki ke ji game da batun.



Showing Courtesy in Difficult Circumstances

Nuna Hali Mai Kyau a Yanayi Mai Wuya



(Lamentations 3:22, 23) Throughout history, servants of God in the most difficult circumstances have sought to maintain a positive, even joyful, attitude. —2 Corinthians 7:4; 1 Thessalonians 1:6; James 1:2.

(Makoki 3:22, 23) Duk cikin tarihi, bayin Allah a cikin yanayi mafi muni sun biɗi su kasance da hali mai kyau, har na farin ciki.—2 Korantiyawa 7:4; 1 Tasalonikawa 1:6; Yakubu 1:2.



I began sharing with her what I had learned from the Bible, but her Buddhist background made it difficult for her to appreciate it.

Sai na soma koya mata abin da na koya daga Littafi Mai Tsarki amma da yake ita mabiyar Buddha ce, ba ta ɗauki abin da muhimmanci sosai ba.



Scholar Charles Freeman answers that those who believed that Jesus is God “found it difficult to refute the many sayings of Jesus that suggested he was subordinate to God the Father.”

Masani Charles Freeman ya ce ya yi wa waɗanda suka amince cewa Yesu Allah ne “wuya su ƙi amincewa da koyarwar da Yesu ya yi cewa Allah ya fi shi iko.”



At times, though, we may find it difficult to engage in meaningful personal study because of our busy routine.

A wasu lokatai, yawan ayyukan da muke da shi yakan sa ya yi mana wuya mu yi nazari sosai.



18 At times, we may need to make difficult decisions, and the right course to take may not be readily evident.

18 Wani lokaci, muna bukatar mu tsai da shawarwari masu muhimmanci, kuma ba mu san tafarkin da za mu bi da ya dace ba.



19 In our time, Jehovah’s people also endure with joy when they suffer in behalf of Jesus’ name or when they face difficult trials.

19 A yau, bayin Jehobah ma suna farin ciki yayin da suke jimre tsanantawa don imaninsu.



(2 Kings 4:27) Of course, it is difficult for the bereaved father as well.

(2 Sarakuna 4:27) Babu shakka, uba ma yana baƙin ciki sosai.



Or the physical condition of one mate may at times make normal sexual relations difficult or even impossible.

Ko kuma yanayin jiki na abokiyar aure wani lokaci na iya sa jima’i ya yi wuya ko kuma ba zai yiwu ba ma.



Hearing how Jehovah has helped a spiritual brother or sister overcome some weakness or pass some difficult test makes our God even more real to us. —1 Peter 5:9.

Jin yadda Jehobah ya taimaki ɗan’uwa ko ’yar’uwa ta ruhaniya ta ko ya magance wasu matsaloli ko kuma wasu gwaji yana sa Allahnmu ya kasance gaskiya a gare mu.—1 Bitrus 5:9.



He admits that this had a negative effect on his spirituality: “I tend to be rather hotheaded, so scenes of violence made it difficult for me to exercise self-control.

Ya ce wannan ya shafi ruhaniyarsa: “Na kasance mai zafin rai, saboda tsarin ayyuka na nuna ƙarfi ya sa ya yi mini wuya na kame kai.



11 That event led Jesus to say something unexpected: “It will be a difficult thing for a rich man to get into the kingdom of the heavens. . . .

11 Wannan ya sa Yesu ya faɗi wani abin da ba a yi zato ba: “Yana da wuya ga mawadaci shi shiga cikin mulkin sama. . . .



Nonetheless, it is surprisingly difficult to define.

Abin mamaki, tana da wuyar ma’ana.



How foolish it would be to stop serving Jehovah or to speak in a manner contrary to “the pattern of healthful words” simply because some things are initially difficult to understand! —2 Timothy 1:13.

Lalle wauta ce idan muka daina bauta wa Jehovah ko kuma muka yi magana da ya saɓa wa “sahihiyar magana,” domin kawai wasu abubuwa sun zama da wuyar fahimta da farko!—2 Timoti 1:13.



3 Getting Started: Many of us find it difficult to start conversations with strangers.

3 Somawa: Yana yi wa mutane da yawa a cikinmu wuya mu soma yi wa baƙi wa’azi.



One report says that 20 well-known diseases —including tuberculosis, malaria, and cholera— have become more common in recent decades, and some types of disease are increasingly difficult to cure by means of drugs.

Wani rahoto ya nuna cewa cututtuka 20—da suka haɗa da tarin fuka, zazzabin cizon sauro, kwalara—sun ƙaru a shekarun baya bayan nan, kuma wasu irin cututtuka suna da wuyar magani.



Economic pressures, political unrest, crime, and sickness are among the things that make life very difficult.

Wahalar tattalin arziki, hargitsi na siyasa, mugunta, da ciwo suna cikin abubuwa da ke sa rayuwa take da wuya ainun.



During these difficult years, Lucía often uplifted my spirits with warm hugs and reassuring kisses.

A waɗannan shekaru masu wuya, Lucía ta kan ƙarfafa ni ta wajen rungume ni da kuma yi mini sumba.



For One with unlimited power, such things would not be difficult at all. —Isaiah 40:26.

Ga wanda yake da iko marar iyaka, waɗannan abubuwa ba za su kasance da wuya ko kaɗan ba.—Ishaya 40:26.



This is not too difficult for us because we have the support of our heavenly Father and his Son.

Waɗannan ayyuka ba su da wuya a gare mu domin muna da goyon bayan Ubanmu na samaniya da kuma Ɗansa.



3 Though your work as a parent is at times difficult, even exhausting, you may be assured that Jehovah greatly values your efforts.

3 Ko da yake aikin iyaye yana da wuya wani lokaci, yana gajiyarwa ma, ku tabbata cewa Jehobah yana yaba wa ƙoƙarinku.



She had been promoted to solo dancer and her career was advancing, so she had a difficult decision to make.

Ta sami ƙarin matsayi a rawa kuma tana samun ci gaba sosai, wannan yanayin ya sa tsai da shawarar yin aure bai kasance mata da sauƙi ba.



However, he let Jehovah guide him through difficult times.

Duk da haka, ya bar Jehobah ya yi masa ja-gora a mawuyacin lokaci.