Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:enable

Discussion page of enable

(Ephesians 5:15) Studying the Bible and meditating on what we learn enable us to “go on walking in the truth.”

(Afisawa 5:15) Nazarin Littafi Mai Tsarki da bimbini a kan abin da muka koya na taimakonmu mu ci gaba da “bin gaskiya.”



(Ephesians 6:10) After giving that counsel, the apostle describes the spiritual provisions and the Christian qualities that enable us to come off victorious. —Ephesians 6:11-17.

(Afisawa 6:10) Bayan ya gama ba da wannan shawarar, manzon ya kwatanta taimako na ruhaniya, da halaye na Kirista da za su taimaka mana mu ci nasara.—Afisawa 6:11-17.



God acted as one who lifts off or pushes back a yoke far enough to enable an animal to eat comfortably.

Allah ya aikata kamar wanda ya ɗaga ko kuma ture karkiyar da nisa domin dabba ya ci abinci cikin walwala.



Teaching skills also need to be developed, for they enable us to explain matters in a clear, uncomplicated way.

Muna bukatar mu koyi yadda ake koyarwa sosai, domin hakan zai taimaka mana mu bayyana batutuwa a hanya mai sauƙi.



How does the use of the term “wrestling” at Ephesians 6:12 enable us to perceive Satan’s strategy?

Ta yaya ne wannan yaƙi da aka ambata a yaren asali da aka yi amfani da shi a Afisawa 6:12 ya sa muka fahimci dabarar Shaiɗan?



(Daniel 7:13, 14) It is by means of this heavenly Kingdom in the hands of Christ Jesus that God will enable lovers of righteousness to enjoy the countless good things that he purposed when he put our first human parents in Paradise.

(Daniel 7:13, 14) Ta wurin wannan Mulki na sama ne cikin hannun Kristi Yesu, Allah zai ba da dama ga masu ƙaunar adalci su more abubuwa masu kyau da ya nufa lokacin da ya saka iyayenmu na farko cikin Aljanna.



(Job 1:1; 23:15) Godly fear can enable us to persevere in a divinely favored course regardless of what we must endure.

(Ayuba 1:1; 23:15) Tsoronmu na ibada zai iya taimaka mana mu nace wa tafarkin da Allah ke so duk da matsalar da za mu fuskanta.



• How have you been affected by what Jehovah did to enable mankind to be at peace with him?

• Yaya abin da Jehobah ya yi don ’yan Adam su kasance da salama da shi ya shafe ka?



15, 16. (a) What did nourishment from Jehovah enable Elijah to do?

15, 16. (a) Ta yaya abincin da Jehobah ya ba Iliya ya taimaka masa?



The Bible does not specifically name all the unclean and disgusting habits and practices that are prevalent today, but it does contain principles that enable us to perceive how Jehovah must feel about such things.

Littafi Mai Tsarki bai ambaci dukan halaye da ayyuka da ake yi a yau ba, amma yana ɗauke da mizanai da za su taimaka mana mu fahimci yadda Jehobah yake ji game da irin waɗannan abubuwa.



Jehovah chose to allow events to take their course in order to enable all to see whether the accusations leveled against him were true or false.

Jehobah ya ga cewa hakan zai bukaci lokaci, don kowa ya sami damar sanin ko tuhumar da ake masa gaskiya ce ko kuma ƙarya.



(Matthew 24:45-47) Such spiritual provisions enable us to see what we must do to please Jehovah when we find ourselves in trying circumstances.

(Matiyu 24:45-47) Irin waɗannan tanadi na ruhaniya suna taimaka mana mu ga abin da dole mu yi domin mu faranta wa Jehovah rai lokacin da muka samu kanmu cikin yanayi na gwaji.



Having brief meetings for field service will enable all to spend more time in the ministry.

Yin gajeren taron fita wa’azi zai taimaki kowa ya yi wa’azi na sa’o’i da yawa.



These inspired writings tell us the truth about God and enable us to get to know him.

Waɗannan hurarrun kalaman sun gaya mana gaskiya game da Allah kuma sun taimaka mana mu san shi.



What will enable us to understand “the fear of Jehovah”?

Menene zai sa mu fahimci “tsoron Ubangiji”?



This will enable us to determine to what extent we are equipped for our spiritual warfare.

Wannan zai sa mu ƙudura niyyar sanin yadda muke a shirye domin yaƙinmu na ruhaniya.



A strong relationship with Jehovah will enable us to meet trials successfully.

Idan muna da dangantaka ta kud da kud da Jehobah, za mu iya jure matsaloli ba tare da mun yi saɓo ba.



May you look to God for hope that can enable you to soar like an eagle.

Zai dace mu dogara ga begen da Jehobah yake ba mu don mu riƙa tashi kamar gaggafa.



Even if he does not accept the book, he has received the tract, which may enable the truth to take root in his heart. —Matt.

Ko ma bai karɓi littafin ba, amma ya karɓi warƙar kuma hakan zai sa gaskiya ta yi jijiya a cikin zuciyarsa.—Mat.



God’s reminders and his spirit will enable us to do what?

Menene ƙa’idodin Allah da kuma ruhunsa za su taimake mu mu yi?



Spiritual conversations enable us to share our faith with others and to build up our brotherhood.

Taɗi na ruhaniya yana taimakon mu mu gaya wa mutane imaninmu kuma mu ƙarfafa ’yan’uwanmu.



So we would like to get your opinion on this question: Do you think that science and medicine will enable us to live forever one day?

Amma duk da haka, ana fama da yaƙe-yaƙe. Shin a ganinka, me ya sa aka kasa samun zaman lafiya a duniya?”



Sometimes acknowledging the householder’s feelings or circumstances will enable you to continue giving a witness.

A wasu lokuta, idan muka nuna cewa mun fahimci yanayin maigidan, hakan zai ba mu damar yi masa wa’azi.



(Proverbs 2:4, 5) Good study habits enable us to come to a better knowledge of Jehovah and to enjoy a closer relationship with him.

(Karin Magana 2:4, 5) Tsarin nazari mai kyau yana taimakonmu mu sami sanin Jehovah da kyau kuma mu more dangantaka ta kurkusa da shi.



What qualities will enable us to serve Jehovah acceptably, even though we are imperfect?

Waɗanne halaye ne za su taimaka mana mu bauta wa Jehobah da kyau duk da cewa mu ajizai ne?