BBC Hausa Shirin Safe (Tue Feb 12th 2019 - 6:30am NG) [1]
- Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi
- USA: 'Yan jam'iyyun Democrat da Republican, sun cimmawa matsayar kaucewa sake dakatar da ayyukan gwamnati a Amurka.
- Nigeria: Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyar PDP, ya ce rashin kayan aiki ne ke dawo da hannun agogo baya a yaƙi da ta'addanci a ƙasar.
- "I beleive our military are not getting the best of equipment... <> Na yi imani sojojin mu basa samun ingantattun kayan yaƙi. Wasu lokuta ma, za ka ga makaman da 'yan ta'adda ke amfani da su, sun fi na sojoji inganci da zamunanci."
- Election special: Sashen Hausa na BBC sun yi tanadi na musamman a lokacin zaɓen.
- "Saboda idan ka fara shiri, ba za ka tsaya ba, tun ƙarfe shida na safe (6 AM), har zuwa ƙarfe goma sha ɗaya na dare. Ɗanɗanon shirin da sauran shirin zai sauya, kamar yadda muka sauya shi a lokacin da muka yi bakukuwan cika shekaru sittin da kafuwa."