Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:kafaɗa

Discussion page of kafaɗa

Martha ta sa mata hannu a kafaɗa ta gayyace ta ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita.

Martha put her arms around Camille and invited her to study the Bible with her.



Wataƙila ya saka fata ko zani a gefen da ake ajiyewa a kafaɗa don ta zama da sauƙi.

Perhaps he lined the contact points with leather or cloth to make the yoke as comfortable as possible.



Ko da yake lokacin bimbini kamar na yin addu’a yana iya sauƙaƙa wahala, haka yake ma idan mutum ya ji amon wani abu ko kuma an dafa masa hannu a kafaɗa.

While it may be true that a quiet moment of prayerlike reflection may relieve stress, much the same could be said about certain sounds of nature or even a back rub.



Ketly ta rasa hannunta na dama har zuwa kafaɗa.

Ketly lost her right arm all the way up to the shoulder joint.



Kuma ɗan’uwan da ya ƙera wannan akwati mai taya ya ce: “Yanzu, na daina ɗaukan littattafai masu nauyi a kafaɗa ta.”

No longer obliged to carry heavy cartons full of books, the inventor himself remarked: “I am not breaking my shoulders.”



Ben ya saka hannunsa a kafaɗa ta, ya yi murmushi, ya ce: “Babu shakka, Jehobah yana ƙaunarka.”

Ben put his arm around me, smiled, and said: “For sure, Jehovah loves you.”



A al’adu da yawa, hanyar nuna cewa ka damu da mai makoki shi ne rungumar shi ko kuma riƙe shi a kafaɗa.

In many cultures, giving the person a hug or a gentle squeeze of the arm is an effective way to show you care.



Sojojin Roma suna riƙe ‘garkuwar’ da take rufe su daga kafaɗa har zuwa gwiwa.

“The large shield” carried by a Roman legionnaire was rectangular and covered him from his shoulders to his knees.



Karkiyar tana iya zama da sauƙi a kan kafaɗa ko kuma ta goge kafaɗar dangane da yadda aka yi ta.

Depending on how a yoke was fashioned, it could be easy on the neck and shoulders or it could chafe.



29:18—Ta yaya ne ‘kowane kan mutum ya yi saiƙo kuma kowace kafaɗa ta goge’?

29:18 —How was ‘every head made bald and every shoulder rubbed bare’?



A sakamakon kula da shi, wuya na, kafaɗa na, da hannaye na suna mini ciwo, kuma ni ma ina zuwa asibitin ƙashi kullum.

As a result of caring for him, my neck, shoulders, and arms ache, and I am an outpatient at an orthopedic hospital.