Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:stated

Discussion page of stated

She stated, “I have never been happier in my life!”

Ta ce: “Na fi yin farin ciki yanzu!”



While on earth, Jesus stated: “No man can come to me unless the Father, who sent me, draws him . . .

Lokacin da yake duniya Yesu ya ce: “Ba wanda ya iya zuwa wurina, sai dai Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi . . .



Through the prophet Isaiah, Jehovah stated: “I, Jehovah, am your God, the One teaching you to benefit yourself, the One causing you to tread in the way in which you should walk.

Ta wurin annabi Ishaya, Jehovah ya ce: “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya ke koya maka zuwa amfaninka, wanda yana bishe ka ta hanyar da za ka bi.



Whether the rule is stated in the positive, the negative, or any other form, what is significant is that people in different times and places and with diverse backgrounds have put much stock in the idea of the Golden Rule.

Ko an faɗi wannan ƙa’idar a hanya mai kyau, ko marar kyau, ko kuma a wasu hanyoyi dabam, abin da ya fi muhimmanci shi ne mutane a lokatai, a wurare da kuma al’adu dabam dabam sun ba da gaskiya ga ra’ayin Ƙa’idar Ja-Gora.



More than 2,500 years ago, the prophet Jeremiah stated: “It does not belong to man who is walking even to direct his step.”

Fiye da shekara 2,500 da suka shige, annabi Irmiya ya ce: “Mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafiyarsa.”



He stated regarding Jesus: “He is a propitiatory sacrifice for our sins, yet not for ours [the small group] only but also for the whole world’s [the large group].” —1 John 2:2.

Ya yi magana game da Yesu: “shi ne kuwa fansar zunubanmu; ba kuwa ta namu kaɗai ba, amma ta duniya duka kuma.”—1 Yohanna 2:2.



German researchers stated that “more and more women are complaining about the addiction [of] their partners.”

Masu bincike a ƙasar Jamus sun faɗa cewa “mataye da yawa suna gunaguni cewa mazajensu sun shaƙu da yin amfani da Intane.”



Simply stated, the good news includes all the truths about which Jesus spoke and his disciples wrote.

A taƙaice, bisharar ta ƙunshi dukan gaskiyar da Yesu ya faɗa waɗanda almajiransa suka rubuta.



(Acts 8:4) They must have felt as the apostle Peter did when he stated earlier: “We must obey God as ruler rather than men.”

(Ayukan Manzanni 8:4) Lallai suna da ra’ayin manzo Bitrus da ya ce tun farko: “Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.”



He stated: “Unless anyone is born again, he cannot see the kingdom of God.”

Ya ce: “In ba a sāke haifar mutum ba, ba zai iya ganin Mulkin Allah ba.”



6 As stated earlier, keep in mind your destination.

6 Ka tuna cewa zaɓin da ka yi zai nuna abin da kake son ka yi da rayuwarka.



The article stated: “It seems to be a safe rule to follow, that prophecy can not be understood by us until it is fulfilled or in the course of fulfillment.”

Talifin ya ce: “Kamar dai wannan ce ƙa’ida mafi kyau da za mu bi. Ba za mu iya fahimtar annabcin ba sai ya cika ko yana kan cika.”



Jesus stated that singleness was a “gift” not possessed by all his followers.

Yesu ya ce ba kowane mabiyansa ne za su iya ƙin yin aure ba.



God’s Law to Israel stated: “You must not commit adultery.”

Dokar Allah ga Isra’ila ta ce: “Ba za ka yi zina ba.”



2 The eighth happiness that Jesus stated is: “Happy are those who have been persecuted for righteousness’ sake, since the kingdom of the heavens belongs to them.”

2 Farin ciki na takwas da Yesu ya ambata shi ne: “Albarka [farin ciki] tā tabbata ga masu shan tsanani saboda aikata adalci, domin Mulkin Sama nasu ne.”



“Warm hearts here will make you welcome,” stated the invitation.

Takardar gayyatar ta ce: “Mutane masu fara’a za su sa ka ji daɗin zuwanka.”



Jesus stated: “All authority has been given me in heaven and on the earth.

Yesu ya ce: “An mallaka mini dukkan iko a sama da ƙasa.



Rabbinic rules stated that no one should come within four cubits (about six feet) (1.8 m) of a leper.

Dokar shugabannan addinan Yahudawan ta ce kada kowa ya yi kusa har na wajen kafa shida daga kuturu.



“Even if a disagreement is not stated, our daughter can pick up on the emotions.”

Idan ma ba mu nuna rashin jituwa ba, yaranmu suna gane cewa akwai saɓani a tsakanin mu.”



* As you do so, you too will come to feel as did the psalmist who stated: “As for me, drawing near to God is good for me.” —Psalm 73:28.

* Yayin da kake hakan, za ka ji kamar wani marubucin zabura da ya ce: “Ya yi mani kyau in kusanci Allah.”—Zabura 73:28.



Jesus’ love for Jehovah can be deduced from all the Gospel accounts of his life, but only John records that Jesus explicitly stated: “I love the Father.”

Ƙaunar Yesu ga Jehovah za a iya gani a cikin dukan Linjila game da rayuwarsa, amma a ta Yohanna ce kawai Yesu ya furta cewa: “Ina ƙaunar Uba.”



But Jesus later stated, according to Luke 12:6, 7, that if a person spent two coins, he got, not four sparrows, but five.

Amma, daga baya Yesu ya ce, in ji Luka 12:6, 7, idan mutum ya ba da kwabo biyu, sai ya sami gwarare ba huɗu ba amma biyar.



(John 20:17) He agreed with Moses, who had earlier stated: “Jehovah is the true God; there is no other besides him.”

(Yohanna 20:17) Ya yarda da Musa, wanda da farko ya ce: “Ubangiji shi ne Allah; babu wani sai shi.”



4 The resurrection is, as stated at Hebrews 6:1, 2, a “primary doctrine.”

4 Tashin matattu, kamar yadda aka faɗa a Ibraniyawa 6:1, 2 (NW ), “koyarwar farko” ce.



The apostle Paul stated: “Keep strict watch that how you walk is not as unwise but as wise persons, making the best use of your time.”

Manzo Bulus ya ce: “Ku duba fa a hankali yadda ku ke yin tafiya, ba kamar marasa-hikima ba, amma kamar masu-hikima; kuna rifta zarafi.”