Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

UMD NFLC Hausa Lessons/118 All Nigeria Peoples Party

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

Overview

  1. Lesson Title: All Nigeria Peoples Party
  2. This interview with two members of Nigeria's main opposition party, the All Nigeria Peoples Party, addresses the party's internal conflicts.
  3. Language: Hausa
  4. Topic: Economics/Politics
  5. ILR Level: 2+/3
  6. ACTFL Proficiency: Superior, Advanced-High
  7. This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
  8. Modality: Listening
  9. Learning Objective: Maintenance & Improvement
  10. Subject Area: Language
  11. Material Type: LO
  12. Publication Year: 2007
  13. ObjectID: HAUS_12016

Transcript


Original Translation

All Nigeria Peoples Party


A: Rikicin babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya, ANPP, ya ɗau sabon salo inda wani jigon jama’iyyar, Alhaji Abdurrahaman Ɗan Malam, ɗan madamin Daura, ya yi hira da ‘yan jaridu jiya a garin Kaduna. Yana zargin mambobin kungiyar jaddada takarar zaman shugaban Ƙasar na Janaral Muhammadu Buhari, watau Buhari {Organization [English]} TBO, da babakare da kuma … watau, katange Buhari daga … jama’a masu Ƙaunarsa. Da hakan in ji shi, ke neman Ƙara rincaɓar da jama’iyyar. Daga bisani ne, na tambaye shi Alhaji Abdurrahaman Ɗan Malam ko bai ganin hakkan da … watau, ko bai ganin hakkan nada nasaba da rashin biyayyarsu da jama’iyyar da kuma shi Buhari ɗ in, inda ya ce:

B: Tun farko lokacin da ake yaƘi na baya, lokacin da muka tafi kurkutu, suna ina? Lokacin da ake yaƘi, shadaran madaran duk a midiyoyi … kafoffun watsa labarai na gida da waje wa ake ji, yau yaushe rabon da ka ji ni … eh?

A: To, ina matsayin shi jeneral, watau tsohon shugaban kasa, Janeral Muhammadu Buhari, game da wannan dabarwar?

B: Shin.. jama’a, shi suke buƘata. Amma ‘yan gindinshi, ‘yan gaba-gaba, su suke ɓata mar al’amari. Wanda su kuma, ba … ko a can mazaɓarsu, ba wani tasiri da suke dashi. Amma sun zo sun ninnike mar, sun hana ma masu jama’a su zo su [inaud.]. Wannan gwagwarmaya tuntuni, Allah ya jiƙan wada nas, kullum ta Allah,shi kaɗai ne jarimi , wanda ya tsaya, yake yin abin nan domin Allah.

A: To, me isa ku, ba ku … matsa kusan shi janeral ɗin ba ku gaya mar abin da kuke ganin shi ne gaskiya?

B: Yarfa ake mana! Yarfa ake yi! In kace irin baraƘala da ake yi, a..a.. Alhaji, bugun zuciyar ai mu ya kamata ma a ce mun kauce tuntuni. Amma aƘida da … ah … san talakawa, shi yasa muke tafe. Amma ba Ƙaunar mu ake a tafiya ba. Yanda muke jajir cewa mun tafi kurkutu, mun je da ɓacin rai, ba irin duk wasu kafofin { source [English] } ɗin mu, na shigowa, ba wanda ba’a done ba. Amma mutanen nan sun Ƙi tausaya mana,da me za mu ji: gaba kura, baya tsayaki.

A: To, har yanzu … ah … janaral shi ne gwaninku daga cikin ‘yan takara, ko kuwa dai kuna da wani zaɓin dabam?

B: Ai, in sun bari, ‘yan Buhari { organization [English] } mu ba mu da sama dashi . Amma in sun bari, amma baya yiwuwa kana yaƘi, kuma ana ma saɓulla.

A: Wani jigon jam’iyyar ANPP ke nan, Alhaji Abdurraham Ɗan Malam, ɗ an madamin Daura. To, sai dai shi kuma, sakataren kungiyar ta Buhari {Organization [English]} TBO, Alhaji Ya’u Darazau, ya ce waɗ annan zarge-zargen kame kame ne kawai, na marassa san a yi siyasa ta adalci.

C: To, abun da yake faruwa, shi ne: Akwai wadansu mutane da suka dauki siyasa sana’a, kuma sun gina kansu, ko kuma an gina su akan … za’a yi wani mutumin yana zaune shi ne … dodonsu, wanda sai abun da ya ce za’a yi. To, da Janaral Buhari ya shiga siyasa, sai suka dauka hakan ya kamata a yi, shi kuma Janaral Buhari ya ce bai shiga siyasa don haka ba. Kowane ɗ an taliki, yana da ‘yanci, ya yi magana kuma a saurare shi. Saboda haka, in nan in har… in ko za ka saurare mutum, to sai a zauna ayi jarjejeniya, a bi ka’ida. To, in an bi Ƙa’idan nan, to kowa ya yadda da ita. To, Janaral Buhari ba ya tashi akan ta. Shi ya sa kaga Janaral Buhari duk da yana neman takarar shugaban kasa. Amma za’a yi taro a Katsina, na Ƙaramar Hukumar Daura zai shiga za‘a yi a {ward [English] din sa, zai shiga, za’a yi na jihar Katsina zai shiga, balantana na Ƙasa a baki ɗ aya.

A: To, amma masu wannan Ƙorafin cewa suke yi ku kuke kasancewa shinge tsakanin Buhari da su jama’a masu son ganin Buhari ɗ in su gaya mar ainahin abin da ya ke tafiya?

C: Ah! to, ai, in dai da wanda yake lura ne da yadda Janaral Buhari yake gudanar da ayyukansa zai san cewa ba wani mutumin da zai iya … tattale masa jama’a. Domin masu ganinsa, shi dama na talakawa ne. Shi jama’arsa talakawa ne, ba wai ‘yan gutsiri tsoma,’yan sana’ar siyasa ba. Yawwa, ba su bane mutanensa . Mutanensa talakawa ne, kuma talakawa na kauyen {ward-ward [English] } ma, zaka ga sun zo wajen Janaral Buhari. ‘Yan acaba, zaka gansu sun zo wajen Janaral Buhari. Direbobin tifa, zaka gan su sun zo wajen Janaral Buhari. ‘Yan kasuwa, ‘yan tazi, kowane ne ‘yan yankan farce, da masu yo wanke kwanika da {shoe-shine [English]}, za kaga sun zo wajen Janaral Buhari.

A: Alhaji Ya’u Darazau ke nan, sakataren kungiyar Buhari {Organization [English]} TBO. Ibrahim Ka’almasi Garba, Muryar Amurka, daga Kaduna a Nijeriya.

All Nigeria Peoples Party

A: The dispute of the main opposition party in Nigeria, the ANPP [All Nigeria Peoples Party], took on a new twist when a party official, Alhaji Abdurrahaman ‘Dan Madami, the title-holder of ‘Dan Madami of Daura, had a conversation with journalists yesterday in Kaduna. He accused members of the organization devoted to presidential candidacy of General Muhammadu Buhari, known as the Buhari Organization or TBO, of obstruction and also … well, alienating Buhari from the public and his admirers. He said their action is throwing the party into disarray.

For my part, I asked Alhaji Abdurrahaman ‘Dan Madami if he didn’t surely think that … well, if he didn’t surely think about winding up lacking, and lacking loyalty to the party and also to Buhari himself, when he said:

B: Since the first time we were fighting before, when we went to prison, where were they? When we were fighting … talking to the mass media at home and outside, when was the last time you heard me talking … eh?

A: OK, what’s the position of the General, that is, the former president, General Muhammadu Buhari, regarding this problem?

B: It is … the public, they need him. But his underlings, progressives, they have spoiled the matter for him. And they … even out among their constituency, they are irrelevant. But they came and overwhelmed him, and prevented the public from coming and [inaudible]. This struggling long ago, God have mercy on Wada Nas, forever by God, it’s he alone who was the brave one, who stood up and did this thing on God’s account.

A: Why is it that you didn’t … take the General aside and tell him what you thought was true?

B: They wouldn’t hear of it! They wouldn’t hear of it! If you knew the kind of battle that was going on, they’d … they’d … Alhaji, we would have had a heart attack, so we had to sidestep it first. But the belief that … we know the common people, this is why we went away. But we didn’t want to go. As we were objecting to going to prison, we went despondently, without any sources of income among us, and on entering, there was no one who wasn’t choked up. But the people there refused to pity us, and the reason we would, we hear: we were trapped in a difficult situation [a hyena in front, another behind].

A: So, until now … ah … has the General been your top man among the candidates, or do you have a different choice?

B: Well, if they leave the Buhari Organization, we have no one higher than him. But if they leave, but it won’t be possible for you to fight, and one is stripping away.

A: That was a leader of the ANPP, Alhaji Abdurrahaman ‘Dan Madami, title-holder of ‘Dan Madami of Daura.

But the secretary of the Buhari Organization, TBO, Alhaji Ya’u Darazau, said these accusations are just random arguments, made without an understanding of politics.

C: Well, this is what’s happening: there are some people who make an occupation of politics, and they build themselves up, or are built up on … and they’ll have somebody in office who is … their puppet, who only does what he’s told to do. When General Buhari got into politics, they accepted that it must be done this way, and General Buhari said he didn’t enter politics for that.

Every little creature has freedom to speak and be heard. Because of this, now when you … you would listen to someone, then he settles down and starts a family, and follows the rules. If the rules are followed, then everyone agrees with them. But General Buhari didn’t rise to power based on them. This is why you see General Buhari even though he is seeking to run for president. But when they call a meeting in Katsina, and the Daura local authority, he will join in, even in his own ward, and they’ll have another meeting in Katsina State and he will join in, how much more the entire country?

A: But those who are fretting that they’re doing this, say that you are becoming an impediment between Buhari and those people who want to see Buhari to tell him what is really going on?

C: Ah! Well, if you pay attention to how General Buhari is running his activities, you will realize that there’s no one who could block him from the general public. Because those who are coming to see him are mostly the common people. His public is the common people, not the ones who harp on things or those who see politics as an occupation. These are not his people at all. His people are the common folk, and you’ll see those from the rural wards that have come to General Buhari. You’ll see commercial motorcyclists who have come to General Buhari. You’ll see truck drivers who have come to General Buhari. Shopkeepers, taxi drivers, all of the manicurists and shoe-shiners’ operators, you will see that they come to General Buhari.

A: That was Alhaji Ya’u Darazau secretary of the Buhari Organization, TBO. Ibrahim Ka’almasi Garba, Voice of America, from Kaduna, Nigeria.

Glossary

Hausa Hausa Meaning English Meaning
Ɗaukar sabon salo. Kamar sa ke hanyar yin wani abu, ko kuma Kai ga wani hali. To use different tactics in regards to something
Rinciɓar da jama'iyyar. Dagular da jama'iyyar. Mess up the party
Bugun zuciya Ɓacin rai, fargaba da faɗuwar gaba. Unhappiness, to dishearten
Yan gindinshi Mutane na kusa da shi ko mabiyanshi. High ranking members of the party who control access to the leader. They are usually given names that are rather negative like "dogs".
Yan gaba-gaba Masu babba matsayi. High ranking members.
Yarfa Rainawa - nuna rashin ƙauna, ko rashin daraja ga wasu mutane, har dai marassa galihu. To show disdain towards other people, usually people of lower social status.
Gaba kura, baya tsayaki. Wannan karin magana ne cikin Hausa, manufarshi kuma ita ce akwai matsala daga kowane gefe. This is a saying in Hausa that means there is a problem on both sides.
Kana yaƙi, ana ma saɓulla. Wannan karin magana ce. wadda ke nufin, mutun yana ƙoƙari ko tattalin ci gaba amma ana aikata abubuwa da suke kawo cikas ga ƙoƙarin. This is a Hausa saying meaning to impede someone's efforts.
'yan gutsiri tsoma Wannan karin magana ne. Cikin wannan hirar, yana nufin mutane da suke shiga wurin da bai yi daidai da su ba domin su kawo rikici. This is a saying in Hausa which, in this context, means opportunists.
'yan acaɓa. Wannan suna ne musamman a Nijeriya, da ake kiran masu sana'ar jigila da babura. This is a name particular to Nigeria given to riders of taxi motorbikes.

Note

Hausa Note English Note

Shugaba da kuma ɗan takara na babbar jama'iyyar adawa a Nijeriya, All Nigeria Peoples Party, Muhammadu Buhari, ya zo ga iko ta juyin mulki da ya yi a shekarar 1984, kuma ya yi ikon wata ashirin. Ya yi ƙoƙarin komawa ga iko ga zaɓe da aka yi cikin shekara ta 2003, amma Obasanjo ya kada shi. Wannan bai tsayar da shi ba kuma aniyarshi ta kawo shi ga shugabanci jam'iyyar adawar ta ANPP amma wannan ma ba da sauƙi ba saboda ba dukan mambobin jam'iyyar ke goyon bayanshi ba.

The leader and candidate for Nigeria's main opposition party, the All Nigeria Peoples Party, Muhammadu Buhari, seized power in a coup in 1984 and ruled for twenty months. He tried again to return to power, but lost to Obasanjo in the 2003 elections. His determination to regain power and, ultimately, the presidency, brought him to the leadership of the party, but not without problems because he was not widely supported by its members.

For more information, please refer to:http://news.bbc.co.uk/2hiafrica/6205876.stm