Overview
- Lesson Title: Farming and Young People in Nigeria-This is an interview with the participants of a meeting about African youth.
- Language: Hausa
- Topic: Culture/Society
- ILR Level: 2+/3
- ACTFL Proficiency: Superior, Advanced-High; This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
- Modality: Listening
- Learning Objective: Maintenance & Improvement
- Subject Area: Language
- Material Type: LLO
- Publication Year: 2009
- ObjectID: T8LHA05
Transcript
Original | Translation |
---|---|
Bankin Duniya da Kwamiti mai kula da harakokin matasa na Majalisar Waƙilai, da ECOWAS suka shirya wa Ƙungiyoyin Matasa na Afrika wani taron ƙara wa juna sani A: Sakamakon yadda kididdiga ta nuna cewa akalla kashi sittin cikin dari na adadin matasa kusan milyan tamanin a Nijeriya, ba su da aikin yi, ya sa Babban Bankin Duniya da hadin gwiwar kwamitin dake kula da harkokin matasa na majalisar wakilai ta kasa tare da {ECOWAS [English]} suka shirya wa kungiyoyin matasa na Afrika baki daya wani taron karawa juna sani. Daga Abuja, wakilinmu Garba Ubale Danbatta na da karin bayani. B: Da yake gabatar da jawabinsa, shugaban kwamitin dake kula da harkokin noman na majalisar wakilai ta kasa, wato Honorable Gbenga Peter Makonjola, yace sakamakon yadda wata kididdiga a taronsu na batun kan harkar noma da kungiyar dake ba da tallafi don bunkasa harkokin noma ta duniya ta shirya a makon da ya wuce, ya nuna cewar akwai akalla mutane kusan bilyan daya dake fama da masifar yunwa, ya sa kwamitinsu na majalisar wakilai ta kasa ya tabbatar da cewa harkokin noma a Nijeriya ya samu irin kason da ya dace, wanda ya kai kusan kimanin kashi goma sha biyu daga cikin adadin irin kasafin kudin na shekara ta dubu biyu da tara tare kuma da kokarin kirkiro da wasu dokoki da za su kai ga kafa wasu sabbin hukumomi na tallafawa harkokin nomad a kuma kare muhalli. To amma don jin ko menene makomar matasan a cikin irin tsare-tsaren farfado da tattalin arziki da gwamnatin Umar Musa ‘Yar-aduwa yanzu haka ta ce ta sa a gaba, ko kuma {seven point agenda} [English]} na zanta da Barrister Dauda Kebo wanda shi ne ya wakilci ministan da ke kula da harkokin matasa a Nijeriyar. C: Kamar yadda ka ce ne, abinda wannan gwamnati take nufi shi ne, su matasa dole a samo masu wani madogara inda za su ba da nasu gudumawa ga cin gaban kasa. Alal misali, a kwanakin nan, aa namu, ma’aikatan ta zo da wani tsari wadda mu ka hada kai, aa da {international organizations [English]}, domin a san wane irin mataki ne za a dauka na maganan rayadda matasa. Watau maganar aikin matasa, ba lalai ba ne wai gwamnati ce za ta ba su aiki, a’a, za ta kokari ta ga cewa su din nan za su iya dogaro da kansu. To ka ga kamar yanzu, muna kokarin mu ga yadda za a yi da mu da ma’aikatan gonad a ma’aikatan kimiyya mun hada kai an kawo wasu dabaru na noman zamani domin su matasa su san cewa noma ba aiki ne na talaka ba. Noma aiki ne na kwarai . B: Shi kuwa {Honorable [English]} Nasiru Sule Garo, shi ne mataimakin shugaban kwamitin da ke kula da harkokin matasa na majalisar wakilan ta kasa, kuma daya daga cikin matasa a cikin zauren majalisar wakilan. Ya kuma sheida mun cewar yanzu fa kusan dole ne rawa ta canja dangane da yadda ake yi wa harkokin matasa rikon sakainar kashi. D: Mu za mu yi dukkan iyakacin aikin da ya kamata mu yi na sa ido, domin mu tabbatar da cewar kudaden da aka ware ma bangaren noma an yi amfani da su ta hanyar da za ta taimaki mutane domin su je suyi amfani da su don yin wannan noman. B: Matasa ta yaya za su shigo kenan ciki? D: Matasa za su shigo ciki tun da su na cikin al’umma, kuma kamar yanda ka sani, mu kwamitinmu yana kula da {ministry [English]} ta matasa. Dan haka, duk abinda mu ke ganin ya kamata a tabbatar matasa sun samu, za mu sa ido mu ga cewar an kai domin matasa su amfana da shi, domin kamar irin wadannan abubuwa da ka ga ana yi yau, na yanda za a fitowa da matasa, aa hanyoyi da za su rika yin noma do, domin ba don kawai su samu abinci ba, a’a domin su samu su sayar da wannan abubuwa da suka yi, kuma su samu wani abu a hannunsu domin su rike kansu. Insha Allah dama Nijeriya an san ta da harkar noma a can baya, a’a harkar man fetur ce ta zo ta lalata wannan harka ta noma. To, yanzu da yake man fetur ya fara ja da baya, muna so lallai, lallai a koma wancan kusan lokaci na baya, ko ma mu fi shi, yanda noma zai zama kamar shi ne abinda yake kan gaba wajen kawowa kasa ci gaba. B: Hausawa dai wai kan ce noma tushen arziki, na duke, kowa ya zo duniya kai ya tarar. A saboda haka, dukkan wani kokari da za a yi na samo hanyoyin cusa wa matasa a nahiyar ta Afrika sha’awar shiga harkar noma, kusan ita ce hanya daya da za ta kai ga magance karancin abinci da kuma kuncin talauci dake addabar dimbin al’ummar Nahiyar ta Afrika a yanzu. |
The World Bank, ECOWAS, and the Committee in Charge of Youth in the Nigerian House of Representatives Organized an African Youth Workshop A: In response to statistics showing that at least 60% of nearly 80 million young people in Nigeria are unemployed, the World Bank has joined up with the House of Representatives Committee on Youth Affairs and the Economic Community of West African States (ECOWAS) to organize a seminar in order for youth organizations from all over Africa to get to know each other better. From Abuja, our correspondent, Garba Ubale Danbatta, has the details. B. During his speech, the chair of the House of Representatives Agricultural Committee, the Honorable Gbenga Peter Makanjuola noted that the statistics released last week at their agricultural conference organized by the Wold Food Organization indicated that there are close to a billion people who are suffering from extreme hunger. He also stated that this had led their House of Representatives committee to ensure that agriculture in Nigeria receives an appropriate share of the budget—close to 12% for the year 2009—and to try to create certain laws that would make progress in establishing new agencies to assist agriculture and protect the environment. In order to get a better understanding of what the future holds for young people with respect to the economic recovery arrangements that the government of Umar Musa Yar ‘Aduwa recently said it would put forth—that is, the seven-point agenda—I spoke with Barrister Dauda Kebo, who represents Nigeria’s Ministry of Youth. C: As you said, the goal of this administration is to find a calling for young people, so they can make their own contribution to the country’s advancement. For example . . . um . . . our staff recently proposed a plan whereby we would cooperate . . . um . . . with international organizations to determine what kind of steps to take on the issue of youth development—that is, on the issue of youth employment. The government is not going to provide them with work; no, instead it will try to ensure that they can be self-sufficient. So, you see, we are currently trying to see how to go about this. We have cooperated with farmers and scientists, and some modern agricultural plans have been proposed, so that young people realize that farming is not just low-level work. Farming is real work. B: The Honorable Nasiru Sule Garo is the vice-chair of the Committee on Youth Affairs in the House of Representatives, and also one of the youngest members of the House. He informed us that we must change the way youth affairs are handled because they are handled so poorly. D: We will do everything necessary to handle this [issue] so that we can guarantee that the funding set aside for the farming sector is being used in a way that will help people go out and use it to farm. B: How will young people become involved? D: Young people will become involved because they are part of the community, and, as you know, our committee oversees the Ministry of Youth. So, we will consider everything that we believe necessary to ensure that our young people receive. And we’ll see to it that it is distributed for young people to use, so that what you see being done today will be made available to our youth . . . um . . . the methods they will use to farm, not just for them to get food, but for them to have things to sell that they have made, and to have something in their hands to keep for themselves. God knows, Nigeria was known for its agriculture way back when, but then the oil came and ruined our agriculture. So, now that oil has begun to recede, we really want to return to what it was like before, or make it even better, so that farming will become a means of advancement, for moving the country forward. B: The Hausa people say that farming is the foundation of wealth; with determination, everyone who engages in it can prosper. Therefore, every effort will be made to find ways to get the young people of Africa interested in agriculture, and this may be one way to address the food shortages and debilitating poverty that now afflict so many communities on the African continent. |
Glossary
Hausa | English Meaning |
---|---|
rawa ta canja | change the way youth affairs are handled |
rikon sakainar kashi | (lit: holding the potty) they are handled so poorly
The expression rikon sakainar kashi implies neglect or mistreatment. |
noma tushen arziki, na duke, kowa ya zo duniya kai ya tarar | farming is the foundation of wealth; with determination, everyone who engages in it can prosper |
kuncin talauci | debilitating poverty |
Notes
1. African Youth
Africa’s youth are an essential component of the continent’s sustainable development. However, many factors create barriers to their full involvement in social, economic, and political matters concerning the continent. Discrimination, lack of adequate education (often caused by school drop outs), and infectious diseases hinder young Africans from fulfilling their potential. Recently, declarations were made by regional organizations and the African Union in an effort to engage Africa’s youth in the continent’s development.
The African Regional Youth Initiative (ARYI) was registered in 2004. It aims to organize people and groups in joint projects, share resources between members, provide grants, develop long-term relationships, and assist in general development.
2. African Agriculture
Agriculture is the foundation of Africa’s economy. It provides food to a fast growing population and generates revenue through domestic and international trade. Farming is considered a profession for the older and illiterate generation of the rural areas. It is mainly done in traditional ways, despite the degradation of the soil caused by these practices. Deforestation, urbanization, and climate change have diminished farmland; therefore African leaders have resorted to their youth and modern farming techniques to ensure food security. They have started implementing programs that attract young people to agricultural activities.
3. More Information
For more information about programs and organizations focused on the development of African youth, please visit the following links:
http://knowledge.cta.int/index.php/en/layout/set/print/content/view/full/3235
http://allafrica.com/stories/200902161464.html
http://www.africa-union.org/root/UA/Conferences/Mai/HRST/Charter%20english.pdf