Overview
- Lesson Title: The Nairobi Declaration on Climate Change-This is a commentary on a conference of African ministers on the environment.
- Language: Hausa
- Topic: Ecology/Geography
- ILR Level: 2+/3
- ACTFL Proficiency: Superior, Advanced-High; This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
- Modality: Reading
- Learning Objective: Maintenance & Improvement
- Subject Area: Language
- Material Type: LLO
- Publication Year: 2009
- ObjectID: T8RHA22
Transcript
Original | Translation |
---|---|
Ministocin harkokin muhalli na kasashen Afirka sun sa hannu kan sanarwar Nairobi A makon da ya gabata, a babban zauren hukumar tsara shiri kan kiyaye muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNEP da ke birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya, ministocin harkokin muhalli na kasashe fiye da 30 na Afirka sun sa hannu kan 'sanarwar Nairobi' domin tinkarar batutuwan da ke shafar sauyawar yanayi tare. Manazarta sun nuna cewa, sa hannu kan 'sanarwar Nairobi' ya almanta cewa, kasashen Afirka sun samu ra'ayi daya kan tinkarar sauyawar yanayi. An sa hannu kan 'sanarwar Nairobi' ne a yayin da aka kammala taron ministocin harkokin muhalli na kasashen Afirka na tsawon kwanaki 9, inda aka mai da hankali kan kalubalen da kasashen Afirka ke fuskanta a fannonin muhalli da sauyawar yanayi, an kuma samar wa kasashen Afirka zarafin yin tattaunawa tare domin fitar da tsarin kula da ayyukan daidaita sauyawar yanayi a karshe. Buyelwa Sonjica, shugabar taron ministocin harkokin muhalli na kasashen Afirka kuma ministar albarkatun ruwa da harkokin muhalli ta kasar Afirka ta Kudu ta nuna babban yabo ga kasashen Afirka da su sami ra'ayi daya a fannin daidaita sauyawar yanayi, a maimakon ci gaba da samun sabani kan kafa hanyar bunkasuwa tare da kiyaye muhalli. Ta kuma kara da cewa, sa hannu kan 'sanarwar Nairobi' ya samar wa kasashen Afirka isassun abubuwan shaidu da su nemi samun goyon baya daga kasashen duniya da murya daya a yayin taron sauyawar yanayi da Majalisar Dinkin Duniya za ta yi a birnin Copenhagen a karshen wannan shekara. Sa'an nan kuma, a ganin Achim Steiner, darektan zartaswa na hukumar UNEP, an jure wahala da yawa da sa hannu kan 'sanarwar Nairobi' a wannan karo. Samun ra'ayi daya da kasashen Afirka suka yi ya nuna babban ci gabansu, kuma a kalla ya shaida cewa, bisa ka'idar hangen nesa a fannin daidaita sauyawar yanayi, kasashen Afirka sun sauke nauyin raya muhalli mai tsabta da maras fitar da abubuwan carbon da yawa. Wannan zai taimakawa kasashen Afirka su tabbatar da samun bunkasuwa mai dorewa, musamman ma zai sa kaimi kan taimakawa matalauta da kuma tabbatar da manufar da Majalisar Dinkin Duniya ta tsara kan samun bunkasuwa a shekarar 2000. Kazalika kuma, Mr. Steiner ya amince da ci gaban kasashen Afirka ta fuskar kiyaye muhalli, kamar kyautata yin amfani da makamashi maras gurbata muhalli da kuma wanda aka yi ta sake yin amfani da shi, da kara zuba kudi kan kafa tsarin muhalli da ke iya karbar carbon dioxide da dai sauransu. Amma duk da haka, kwararrun da abin ya shafa sun nuna cewa, ko da yake kasashen Afirka sun sami ra'ayi daya kan daidaita sauyawar yanayi, amma za su fuskanci cikas da matsaloli wajen gudanar da ayyukan da abin ya shafa. Da farko, sauyawar yanayi ta kawo wa kasashen Afirka babbar illa ta fuskar raya tattalin arziki. Talauci da rashin isasshen karfin gwamnati na kula da ayyuka da dimbin bala'u daga indallahi da hargitsi da dai sauransu dukkansu sun raunana karfin kasashen Afirka na daidaita matsalar muhalli da sauyawar yanayi. Sa'an nan kuma, rashin isasshen kudi ya hana ingantuwar karfin kasashen Afirka na dacewa da muhalli yadda ya kamata. Saboda haka, 'sanarwar Nairobi' ta shawarci kungiyar G8 ta kafa cibiyar kula da yanayi a nahiyar Afirka, da kyautata matsayin daidiata barazana ta fuskar yanayi da gudanar da shirin rage radin bala'u da yawan aukuwar bala'u a shiyya-shiyya, musamman ma su kara mai da hankali kan mata da yara da nakasassun da suka fi samun illa a sakamakon sauyawar yanayi. Ma iya cewa, sa hannu kan 'sanarwar Nairobi' ya almanta cewa, a matsayin abu daya, kasashen Afirka sun samu ra'ayi daya kan tinkarar sauyawar yanayi, amma ba shakka, nan gaba kasashe masu tasowa da suka hada da kasashen Afirka za su ci gaba da fuskantar kalubale da wahalhalu da yawa, shi ya sa akwai doguwar hanya ce a gabansu a fannin daidaita sauyawar yanayi.(Tasallah) |
Africa’s Environment Ministers Adopt the Nairobi Declaration Last week at a special session of the United Nations Environment Programme (UNEP) in the Kenyan capital of Nairobi, environment ministers from more than 30 African countries adopted the “Nairobi Declaration” in order to come together to confront the issue of climate change. Analysts point out that [the ministers’ decision to] adopt the Nairobi Declaration signals a consensus among African countries on confronting climate change. The Nairobi Declaration was adopted at the end of the nine-day African Ministerial Conference on the Environment which focused on the challenge that African countries face concerning the issues of environment and climate change. It provided the opportunity for African countries to consult with each other with the goal of devising a system for managing climate change. Buyelwa Sonjica, president of the African Ministerial Conference on the Environment and also South Africa’s Minister of Water and Environmental Affairs, praised African countries for reaching a consensus with regards to managing climate change instead of continuing to argue about how to promote development while simultaneously protecting the environment. She went on to say that [the fact that] the Nairobi Declaration was adopted provided African countries with sufficient evidence of consensus to seek support from the international community at the United Nations Climate Change Conference in Copenhagen at the end of this year. According to UNEP’s Executive Director, Achim Steiner, it was no easy task to get the Nairobi Declaration adopted on this occasion. The consensus reached by African countries represented a major step forward for them and, at the very least, provided evidence that as far as long-term measures for managing climate change are concerned, African countries have accepted responsibility for promoting a cleaner environment with less carbon production. This will help African countries ensure sustainable development, and in particular, will encourage assistance to the poor and achieve the Millennium Development Goals set forth by the United Nations in 2000. Moreover, Mr. Steiner endorsed the progress made by African countries regarding environmental protection, such as improving the use of clean and renewable energy, increasing funding to establish an environmental system that could store carbon dioxide, etc. However, experts in these matters suggest that although African countries have reached a consensus on managing climate change, they will face a host of challenges with regards to overseeing these activities. First of all, climate change has led to major challenges for African countries from the perspective of economic development. Poverty, a lack of sufficient government oversight, numerous natural disasters, social turmoil, etc., all weaken African countries’ ability to address environmental problems and climate change. Moreover, a lack of adequate funding has undermined African countries’ ability to take appropriate action on the environment. Therefore, the Nairobi Declaration advises the G8 to establish a center for climate protection on the African continent to better address the climate threat, to administer a program to alleviate the severity and frequency of natural disasters in the region, and in particular to focus more on women, children, and the disabled, who are the [groups that are] most vulnerable from the effects of climate change. While it is true that adoption of the Nairobi Declaration signals that, as a first step, African countries have reached a consensus on confronting climate change, the developing countries, including those in Africa, will undoubtedly continue to face considerable challenges and difficulties. They have a long road ahead of them on the issue of managing climate change. (by Tasallah) |
Glossary
Hausa term | English meaning |
---|---|
UNEP | abbr. for The United Nations Environment Programme (UNEP) |
'sanarwar Nairobi' | Nairobi Declaration |
tsarin kula da ayyukan daidaita sauyawar yanayi | devising a system for managing climate change |
bisa ka'idar hangen nesa | (lit: following the principle of projection) long-term measures for managing climate change |
kasashen Afirka sun sauke nauyin raya muhalli... | African countries have accepted responsibility for promoting a cleaner environment with less carbon production |
makamashi maras gurbata muhalli da kuma | clean energy |
wanda(makamashi) aka yi ta sake yin amfani da shi | renewable energy |
tsarin muhalli da ke iya karbar carbon dioxide | environmental system that could store carbon dioxide |
bala'u daga indallahi (also annoba daga indallahi) | natural disasters |
akwai doguwar hanya ce a gabansu | they have a long road ahead of them on the issue of managing climate change |
Notes
1. Impact of Climate Change in Africa
There are many obvious consequences of climate change apparent in Africa today, ranging from desertification, shortened rainy seasons, floods and droughts, and food shortages. These also lead to civil disputes and an urbanization of the population, as people leave the rural countryside for the cities.
2. The United Nations Environment Programme (UNEP)
The United Nations Environment Programme (UNEP) is based in Nairobi, Kenya, and oversees all issues and activities related to the environment, in general. UN Under-Secretary General Achim Steiner, has been the Executive Director of UNEP since 2006.
3. The African Ministerial Conference on the Environment (AMCEN)
The African Ministerial Conference on the Environment (AMCEN) holds meetings regularly to discuss environmental issues concerning the African continent. AMCEN provides support in the effort to protect the environment and promote related sectors for sustainable human, social, and economic development of the continent.
4. Buyelwa Sonjica
Buyelwa Sonjica is a member of South Africa's Parliament, the country’s Minister of Water and Environmental Affairs, and President of the African Ministerial Conference on the Environment (AMCEN).
5. More Information
a) For more information about the impact of climate change in Africa, please visit the following links:
http://www.wsws.org/articles/2007/jul2007/clim-j18.shtml
http://www.sciencedaily.com/releases/2006/11/061126115458.htm
b) For more information about UNEP and the “Nairobi Declaration”, please visit links:
http://www.unep.org/Documents.Multilingual/Default.asp?DocumentID=287&ArticleID=1728&l=en
http://www.unep.org/Documents.Multilingual/Default.asp?DocumentID=589&ArticleID=6199&l=en&t=long
c) For more information about the African Ministerial Conference on the Environment, please visit the following links: