m
- wani irin itace dogo wanda ake yin shinge ko danga da shi; yana da ganyaye masu faɗi, kuma yakan yi furanni da rani, ruwa-ruwan da akan samu a cikin furannin yana da zaƙi, don haka yara ke ɓantano shi suna tsotso; an fi samun wannan itace a yankunan Zariya da kudancinta; akan yi tsumangiya da siraran tohonsa, shi ya sa akan yi masa kirari da: aduruku maganin mai ƙwarin kai.