Your IP address will be publicly visible if you make any edits.
bbchausa verticals/101 Kungiyar Ansaru
From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
More actions
''Hausa article'' <> English translation <small style="font-size:smaller;"> --[[bbchausa_verticals/101 Kungiyar Ansaru]]</small>
Kungiyar Ansaru ta ce ba ita ta kai hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ba Ansaru denies involvement with the Abuja-Kaduna train attack. --bbchausa_verticals/101 Kungiyar Ansaru
Ƙu ngiyar Ansaru mai alaƙa da Al-Qaeda da ke ayyukanta a arewa maso yammacin Najeriya ta yi watsi da batun cewa tana da hannu a harin da aka kai kan jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga watan Maris din 2022. Al-Qaeda-linked group, Ansaru, which operates in northwestern Nigeria, has denied involvement in the March 28, 2022 Abuja to Kaduna train attack. --bbchausa_verticals/101 Kungiyar Ansaru
Ansaru ta ƙaryata zargin ne a wani saƙo na bidiyo da ta saki ranar 12 ga watan Yuni a shafukanta na Telegram da RocketChat. Ansaru denied the allegations in a video message released on June 12 on its Telegram and RocketChat pages. --bbchausa_verticals/101 Kungiyar Ansaru
Mai magana a cikin bidiyon ya yi jawabin ne da Larabci sannan ya yi da Hausa. The speaker in the video spoke in Arabic and then Hausa. --bbchausa_verticals/101 Kungiyar Ansaru
An ga a ƙalla mutum bakwai a bidiyon dukkansu sanye da takunkumin rufe fuska kuma suna ɗauke da bindigogi. At least 7 people were seen in the video, all wearing masks and carrying guns. --bbchausa_verticals/101 Kungiyar Ansaru
Mutumin da ke bayanin wanda ba a iya gane shi, ya tsaya a tsakiya ne yana magana kan abin da ya kira An unidentified man, standing in the middle, spoke of what he called a... --bbchausa_verticals/101 Kungiyar Ansaru
"labarin ƙarya da yake yaɗuwa cewa ƙungiyar Ansarul al-Muslimin fi bilad al-Sudan (cikakken sunan ƙungiyar) ta ɗauki alhakin kai harin jirgin ƙasan." "widespread rumor that the Ansarul al-Muslimin fi bilad al-Sudan (the group's full name) claimed responsibility for the train attack." --bbchausa_verticals/101 Kungiyar Ansaru
Ya ƙara da cewa "wannan ƙarya ce tsagwaronta wacce ba ta da tushe." He added that "this is false and has no basis." --bbchausa_verticals/101 Kungiyar Ansaru
Ya ce Ansaru ba ta da hannu ko kaɗan a harin jirgin ko sace fasinjojinsa. He said Ansaru was not involved at all in the train attack and kidnapping of passengers. --bbchausa_verticals/101 Kungiyar Ansaru
da kuma ƙungiyar Boko Haram, wacce take da ƙarfi a arewa maso gabas, and Boko Haram group, which has a strong presence in the northeast, --bbchausa_verticals/101 Kungiyar Ansaru
da hannu a kai wa jirgin ƙasan hari, ko dai kai tsaye ko kuma ta hanyar hada kai da ƴan bindigar da suke ayyukansu a yankin. of being involved in a train attack either directly or indirectly by militants who are active in the area. --bbchausa_verticals/101 Kungiyar Ansaru
inda ya jaddada cewa tana ƙoƙarin kaucewa cin zarafin ƴan yankin kuma tana taɓa waɗanda suke adawa ko fito na fito da ita ne kawai. English --bbchausa_verticals/101 Kungiyar Ansaru
Ansaru ta matsa wajen nesanta kanta da amfani da tsauraran hanyoyin masu ikirarin jihadi kamar su Boko Haram da IS da kuma ayyukan ƴan binciga. English --bbchausa_verticals/101 Kungiyar Ansaru
A wani saƙonta na baya-baya, Ansaru ta nanata cewa tana neman hadin kan mutane ne ta hanyar da'awa maimakon yaƙarsu. English --bbchausa_verticals/101 Kungiyar Ansaru
Mai maganar ya ce Ansaru ta yi amannar cewa harin jirgin ƙasan ba shi da alaƙa da jihadi kuma yin hakan ma jawo fitina ne kuma ya saɓa wa Musulunci da aƙidar masu jihadi. English --bbchausa_verticals/101 Kungiyar Ansaru