Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/102 buying votes for 2023

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
  1. ''Hausa article: Zaben 2023: Ana nuna fargaba kan yadda masu zabe ke sayar da 'yancinsu a Najeriya'' <> English_Machine_Translation <small style="font-size:smaller;"> --[[bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023]]</small>
    1. Masu sharhi kan harkoki siyasa a Najeriya sun fara nuna fargabar cewa akwai yiwuwar wasu masu hannu-da-shuni da ke neman wani mukamin a zaben da za a yi a shekarar 2023 -
      Nigerian political analyst are beginning to fear that some potential candidates in the 2023 elections - --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    2. ko da ba su cancanta ba - za su sayi kuri'un mutane domin cimma burinsu.
      even if they are not qualified, they will still buy up votes to achieve their goals. --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    3. An soma fargabar ne bayan wani bidiyo da aka dauka a zaben gwamnan jihar Ekiti da aka kammala a baya-bayan nan wanda ya nuna wasu 'yan siyasa na raba wa masu kada kuri'a kudi.
      The fears were sparked by a video of the recently concluded Ekiti state governorship election which showed some politicians handing out money to voters. --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    4. Kazalika a zabukan fitar da gwani ma da aka kammala a kasar an ga tasirin hakan in da aka ga wani daliget na raba wa 'yan mazabarsa kudin da ya ce wani dan takarar shugaban kasa ne ya ba shi.
      In the run-up to the by-elections, the effect was even greater when a delegate allegedly distributed money to his constituents by a presidential candidate. --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    5. Dakta Kole Shettima, shugaban Cibiyar tabbatar da cigaba da kuma dimokradiyya a Abuja,
      Dr Kole Shettima, chairman of the Center for Development and Democracy in Abuja --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    6. kuma mai sharhi kan harkokin siyasa ya shaida wa BBC cewa, wannan abu da 'yan siyasa ke yi na da matukar illa.
      and a political commentator, told the BBC that the move by politicians was "extremely harmful" --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    7. Ya ce "Idan ana haka to idan ba a yi sa'a ba a zabuka masu zuwa da za a yi sai mai kudi ne zai samu nasara ko da bai cancanta ba."
      "If this is the case then if you are unlucky in the next election you will be rich and you will win even if you do not deserve it," he said. --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    8. Dr Kole Shettima, ya ce bisa la'akari da halin da ake ciki a Najeriya na talauci na tsadar kayayyaki,
      Dr Kole Shettima, said in view of the high cost of living in Nigeria, --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    9. masu neman mukaman siyasa za su iya amfani da yanayin da mutane ke ciki su basu kudi don su zabesu.
      aspirants for political office could take advantage of the situation and give people money to vote for them. --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    10. Ya ce "Shawarata ga masu kada kuri'a shi ne duk wanda ya basu kudi don su zabe shi to su karbi kudin dama kudinsu ne,
      He said: "My advice to voters is that whoever gives them money to vote for them should accept their money," --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    11. to amma idan kuka zo yin zabe sai ku zabi wanda ku kuke gani yafi cancanta."
      but when you come to the polls, you have to choose who you think is more deserving." --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    12. Akasari mata su ne suka fi fitowa a lokutan zabe,
      Most women are the ones who cast their ballots during elections, --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    13. kuma ana zargin 'yan siyasa na ba su sabulu da atamfofi ko kudi don su zabe su wanda haka na da illa sosai ga makomar matan a siyasance.
      and politicians are accused of giving out soap and fabrics or money for their votes, which is detrimental to women's political future. --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    14. Barista Aisha Ali Tijjani, mamba ce a gamayyar kungiyoyin fararen hula a jihar Kano,
      Barrister Aisha Ali Tijjani, a member of Kano State Civil Society, --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    15. ta shaida wa BBC cewa ba karamar illa ba ce yadda ake yaudarar mata a ba su kudi ko kaya lokacin zabe.
      told the BBC that women were being misled into giving money or goods during elections. --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    16. Ta ce "Na farko dai mata ba su san damar da suke da ita da kuma 'yancinsu na zabe ba,
      "First of all, women are not aware of their rights and freedoms, she said. --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    17. sun saryar da 'yancinsu da damarsu na zabar wanda ya cancanta."
      they have been deprived of their right to vote," --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    18. Barista Aisha ta ce ya kamata mata su sani duk wani abu da za a ba su a lokacin zabe,
      Barrister Aisha said women should know that whatever they are given during the elections, --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    19. to zai musu amfani ne na kankanin lokaci,
      it will only benefit them in the short term, --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    20. kuma sun cutar da kansu wajen rashin zabar shugaban da ya dace ba.
      and they have harmed themselves by not choosing the right president. --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    21. A cewarta "Shawarata ga mata ita ce ya kamata mata su waye sannan su bude ido su san cewa ba bukatar yanzu-yanzu ake nema a yaye ba,
      She said: "My advice to women is that women should be educated and open-minded and aware that there is no need for breastfeeding right now." --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    22. ma'anar zabe ita ce kadai makamin da talaka ke da shi na canja alkiblar mulki domin ya zabi wanda yake ganin zai ceto shi daga halin da yake ciki."
      choosing the one he thinks will save him from the situation. --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    23. Baristar ta ce idan har talakawa ba su yi amfani da wannan dama ta zabe wajen canja akalar zaben sun zabo wanda ya cancanta da su ba,
      The barrister said that if the masses did not take advantage of this opportunity to change their minds and vote for the right candidate, --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    24. to a gaskiya ba mata ne suka shiga uku ba kadai har ma da maza.
      then in fact not only women but also men were in top three. --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    25. Sayar da kuri'a dai tamkar sayar da 'yancin dan kasa ne na tsawon shekaru hudu,
      Voting is like selling a citizen's rights for 4 years, --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    26. kuma tsalle daya ake a fada rijiya, amma sai a yi dubu ba a fito ba.
      and jumping one step at a time, but then a thousand turns. --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    27. Sannan bisa la'akari da halin da ake ciki a Najeriya,
      And given the current situation in Nigeria, --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    28. ya ishi 'yan kasar su yi karatun ta natsu tare da sauya tunani a kan yadda suke mika wuya ga 'yan siyasar da ke siyan kuri'a a lokacin zabe don gudun fadawa hannun gurbatattun shugabanni.
      it is enough for the people to study hard and change their minds about surrendering to politicians who buy votes during elections to avoid falling into the trap. corrupt leaders. --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023
    29. HAUSA
      ENGLISH --bbchausa_verticals/102 buying votes for 2023