Africa's week in pictures: 1-7 October 2021 Published 8 October 2021 [1] <> Hotunan Afirka na mako 1-7 Oktoba 2021: Tsalle cikin nishadi da masu tafiya a Sahara (10 Oktoba 2021) [2]
On Friday Nigerians celebrate as the country marks its 61st year of independence from British rule... Ranar Juma'a ƴan Najeriya sun yi murnar cikar shekara 61 da ƙasarsu ta samu ƴanci daga mulkin Burtaniya... --bbchausa verticals/pics/2021-10-01
This woman is part of an acrobatic display band performing in the capital, Abuja... Wannan matar na cikin wasu ƴan rawa da suka yi wasa a Abuja babban birnin Najeriya... --bbchausa verticals/pics/2021-10-01
Many Nigerians take to Twitter under the hashtag #NigeriaAt61... Ƴan Najeriya da dama sun shiga shafin Twitter don aika saƙonni da maudu'in #NigeriaAt61... --bbchausa verticals/pics/2021-10-01
While some are celebrating, others are protesting, and demanding the resignation of President Muhammadu Buhari. Yayin da wasu ke murna, wasu na zanga-zanga tare da buƙatar Shugaba Muhammadu Buhari ya ajiye aiki. --bbchausa verticals/pics/2021-10-01
The following day Sudanese performers dance to welcome a conference delegation in Khartoum. Washe gari a Sudan wata tawagar ƴan rawa ta tarbi wasu baƙi a Khartoum. --bbchausa verticals/pics/2021-10-01
On the same day in Morocco a woman strokes a camel on the eve of the Marathon des Sables - which sees competitors run 250km (150 miles) through the Sahara desert in seven days... A rana guda a Morocco wata mata na shafa wani raƙumi a jajiberin fara tseren Marathon des Sables - wanda masu shiga tseren ke yin gudun kilomita 250 a hamadar Sahara cikin kwana bakwai... --bbchausa verticals/pics/2021-10-01
On Sunday the race kicks off and runners hit the sand dunes. Ranar Lahadi an fara tseren a tarin yashin hamada. --bbchausa verticals/pics/2021-10-01
On Monday, crowds gather in Ethiopia's capital Addis Ababa to celebrate the swearing-in of Prime Minister Abiy Ahmed... Ranar Litinin, an taru a Addis Ababa babban birnin Habasha don shgalin rantsar da Firaminista Abiy Ahmed... --bbchausa verticals/pics/2021-10-01
Mr Abiy, right, has introduced numerous reforms, and become embroiled in a civil war, since coming to power in 2018... Mista Abiy, a dama, ya gabatar da sauye-sauye da dama kuma mulkinsa ya gamu da yaƙin basasa tun bayan hawansa mulki a 2018... --bbchausa verticals/pics/2021-10-01
But there is a jubilant atmosphere amongst those present. Sai dai masu halartar bikin sun yi murna da farin ciki. --bbchausa verticals/pics/2021-10-01
Back to Sudan on Tuesday, and a group of women walk in protest against a peace agreement signed between the government and rebel forces in 2020. Idan aka koma Sudan, ranar Talata, wasu mata na tattaki don nuna ƙin jinin wata yarjejeniyar zaman lafiya da aka sa wa hannu tsakanin gwamnati da ƴan tawaye a 2020. --bbchausa verticals/pics/2021-10-01
Meanwhile in the South African city of Johannesburg, a woman poses for a picture at an LGBTQ event - the Feather Awards nominee announcements. A birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu kuwa, wata mata ta yi tsayuwar ɗaukar hoto a wani taron masu goyon bayan auren jinsi ɗaya. --bbchausa verticals/pics/2021-10-01
Over in London on Wednesday, actor Idris Elba and his Somali-Canadian model wife Sabrina Dhowre Elba attend The Harder They Fall film world premier. A birnin London kuwa ranar Laraba, ɗan wasan fim Idris Elba da matarsa ƴar asalin Somaliya amma haifaffiyar Canada Sabrina Dhowre Elba mai tallar kayan ƙawa sun halarci bikin haska fim ɗin The Harder They Fall. --bbchausa verticals/pics/2021-10-01
Back in Morocco this man is still running the Marathon des Sables - he's on day four of the race. A Morocco, wannan mutumin na gudu a wasan tseren Marathon des Sables - a rana ta huɗu ta tseren. --bbchausa verticals/pics/2021-10-01
On the same day a fruit seller walks past a street art mural in Johannesburg... A rana guda wani mai sayar da kayan marmari na wucewa ta gaban wani zane da aka yi a kan titi a birnin Johannesburg... --bbchausa verticals/pics/2021-10-01
In the same city on Thursday protestors take to the streets over South Africa's economic policies. A birni guda ranar Alhamis masu zanga-zanga sun hau tituna kan manufofin Afrika ta Kudu na tattalin arziƙi. --bbchausa verticals/pics/2021-10-01
Meanwhile Tanzania-born author Abdulrazak Gurnah's books are on display in Stockholm, after winning the 2021 Nobel Prize for Literature. A wani ɓangaren kuwa an jera littafan marubuci Abdulrazak Gurnah ɗan Tanzania a birnin Stockholm bayan da ya lashe lambar yabo ta Nobel ta 2021 a fannin adabi. --bbchausa verticals/pics/2021-10-01