Africa's week in pictures: 17-23 December 2021 Published 24 December 2021 [1] <> Hotunan wasu abubuwan da suka faru a Afirka na mako: Daga 17 zuwa 23 ga watan Disambar 2021 (26 Disamba 2021) [2]
Traditional Burundian drummers come out in force in the capital, Gitega, on Monday for a national contest... Masu kidan kalangun gargajiya na kasar Burundi sun fito da karfinsu a Gitega babban birnin kasar ranar Litinin don shiga gasar kasa…. --bbchausa verticals/pics/Dec17-23
Performers leap in the air as the drummers play. Masu wasan daka tsalle sama a yayin da masu buga kalangu ke wasa. --bbchausa verticals/pics/Dec17-23
Traditions are also being celebrated in South Africa on Saturday as women dress in clothes worn by Zulus for a cultural festival in Durban. Har ila yau an gudanar da wasu bukukuwan al'adun gargajiya a Afirka ta Kudu a ranar Asabar yayin da mata sanye da tufafin 'yan kabilar Zulu don wasun nunin al'adun gargajiya a birnin Durban. --bbchausa verticals/pics/Dec17-23
There are celebrations in the Algerian capital, Algiers, on Sunday as the national football team, victorious in the Arab Cup in Qatar, return home. An gudanar da bukukuwa a Algiers babban birnin kasar Algeria ranar Lahadi bayan da kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar ta samu galaba a gasar wasan cin kofin kasashen Larabawa a kasar Qatar, suka dawo gida. --bbchausa verticals/pics/Dec17-23
On Thursday, a photographer snaps vials of expired Covid vaccines before they are destroyed at a dump site in the capital, Abuja. A ranar Alhamis, wani mai daukar hoto ya dauki hoton wasu kwalaben ruwan allurar rigakafin korona kafin a zubar da zu a cikin bola a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya. --bbchausa verticals/pics/Dec17-23
In the east of the Democratic Republic of Congo on Sunday a Red Cross volunteer holds the charity's flag as his colleagues bury a group of people killed in a recent attack. A Gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ranar Lahadi wani mai aikin sa-kai na kungiyar agaji ta Red Cross dauke da tutar kungiyar yayin da abokan aikinsa ke binne wasu mutane da aka kashe a wani hari da aka kai a baya bayan nan. --bbchausa verticals/pics/Dec17-23
The violence in the region, where villages and camps have been targeted, has forced 70,000 people to take refuge near a UN base in Rhoo, which is seen here on Wednesday. Tashin hankali a yankin inda ake kai hari kan sansanoni da kauyuka, ya tilasta wa mutane 70,000 neman mafaka a kusa da wani sansanin Majalisar Dinkin Duniya a Rhoo, da ake gani a nana a ranar Laraba. --bbchausa verticals/pics/Dec17-23
On Sunday, a demonstrator in Sudan's capital, Khartoum, comes prepared for tear gas as people turn out to mark three years since the start of protests that led to the downfall of President Omar al-Bashir... Game da kasar Sudan, wani mai zanga-zanga Khartoum babban birnin kasar Sudan ya zo da shirin tunkarar hayaki mai saka kwalla a yayin da mutane suka fito don tunawa da zagayiwar shekaru uku tun bayan da aka fara zanga-zangar da ta haddasa kawo karshen mulkin shugaba Omar al-Bashir... --bbchausa verticals/pics/Dec17-23
The protesters help lessen the impact of the tear gas which was fired to break up the hundreds of thousands of demonstrators. Masu zanga-zanga na taimaka wa wajen rage tasirin hayaki mai saka kwalla da aka harba don tarwatsa dubban daruruwan masu zanga-zanga. --bbchausa verticals/pics/Dec17-23
Police in Tunisia's capital, Tunis, move in to stop a planned sit-in organised against President Kais Saied, who suspended parliament in July. Yan sanda a Tunis babban birnin kasar Tunisia sun kutsa don dakatar da yunkurin zaman dirshan daga shirya zanga-zanga kan shugaba Kais Saied, wanda ya dakatar da majalisar dokoki na wucin gadi a cikin wata Yuli. --bbchausa verticals/pics/Dec17-23
A make-up artist applies the finishing touches to a model backstage at a fashion show in a baobab forest in Senegal on Saturday. Wata mai yin sana'ar kwalliya na shafa wa wata mai tallar kayan kawa hoda a yayin bikin nuna kayan kawa a kauyen baobab ba kasar Senegal ranar Asabar. --bbchausa verticals/pics/Dec17-23
Street hawkers in Zimbabwe's capital, Harare, on Monday try to persuade motorists to buy a Santa hat or inflatable Father Christmas. Masu talla a bakin hanya a Harare babban birnin kasar Zimbabwe a ranar Litinin na kokarin jan hankalin masu motoci su sayi rigar Santa ko balan-balan din Fada Kirsimeti. --bbchausa verticals/pics/Dec17-23
On Thursday, at the other end of the continent, residents of Egypt's capital, Cairo, pose for a selfie by an illuminated Christmas tree. A ranar Alhamis, a wani bangare na nahiyar, mazauna birinin Alkahira babban birnin kasar Masar sun yi tsayuwar daukar hoton dauki da kan ka a jikin bishiyar Kirsimeti da aka kawata da fitilu. --bbchausa verticals/pics/Dec17-23