Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

gora

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

Noun

Tilo
gora

Jam'i
gorori

f

  1. wata irin sanda mai kai kwagiri-kwagiri da gajajjeru ko dogayen gaɓoɓi da ake yin makami da ita ko kuwa a yi sangwami da ita.
  2. ja gora ko jagora: wato nuna wa wani hanya. <> leading the way, showing someone the path or directions.
  3. ƙawa.
    Da Kande da Zainabu suna gora.
  4. gogar guga: wata irin 'yar lanƙwasa ko kaifi a jikin gogaggen wando ko riga.
  5. buga gora: roƙo ko maula a fakaice. <> quietly or secretly begging.
  6. gorar kitso: doka. <> law.

Noun 2

Tilo
gora

Jam'i
gorina or goruna

m

  1. fafaffen ƙaton duma da ake amfani da shi wajen fito a kogi ko zuba nono ko kifi.
  2. buta ko jallo ko gyanɗama.
  3. goran ruwa: wani ƙarfe fari marasa nauyi. <> a lightweight white steel.
  4. nonon shayarwa na mace. <> a female's feeding breast.
  5. kumburin ƙurji da ya ɗuri ruwa.
  6. bayyanar girman rana da kewayenta dab da fitowarta ko faɗuwarta.
  7. duban gora: harara-garke.