Hadrat Ibn ‘Abbas reported that a desert Arab came to the Holy Prophet and said, “I have seen the new moon i.e. the new moon of Ramadhan.” He asked, “do you testify that there is no god but Allah?” he said: yes. He then asked: do you testify that Muhammad is the Messenger of Allah?” He said, “Yes.” So, the Messenger of Allah said, “O Bilal, announce to the people that they must fast tomorrow.” [Sunan Abi Dawud, Vol 1, Page 320 and Tirmidhi, Vol 1, Page 148]
Wani baƙauyen balarabe ya zo wajen annabi SAW, sai ya ce masa: Lalle ni na ga jaririn wata, ma'ana jaririn watan Ramadan. Sai annabi ya ce da shi: "Ka shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah?" Sai balaraben ya ce "E na shaida" Sai annabi ya sake cewa da shi: "Ka shaida ni kuma annabi Muhammadu manzon Allah ne?" Sai mutumin ya ce E na shaida haka. Sai annabi ya ce, "Ya kai Bilal! Ka je ka sanar da mutane cewa kowa ya tashi da azumi gobe." ([1] = 11th min)