Toggle menu
24.2K
670
183
158.7K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/18/IRIB Hausa Tafsir: Difference between revisions

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Line 205: Line 205:


Da fatan za a kasance a tare da mo domin a ji ci gaban shirin.
Da fatan za a kasance a tare da mo domin a ji ci gaban shirin.
 
{{-}}
*****
 
To yanzu sai a saurari aya ta 15 a cikin wannan sura ta Kahfi.
To yanzu sai a saurari aya ta 15 a cikin wannan sura ta Kahfi.
 
'''
هَؤُلَاء قَوْمُنَا اتَّخَذُوا مِن دُونِهِ آلِهَةً لَّوْلَا يَأْتُونَ عَلَيْهِم بِسُلْطَانٍ بَيِّنٍ فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَى عَلَى اللَّهِ كَذِباً{15}
هَؤُلَاء قَوْمُنَا اتَّخَذُوا مِن دُونِهِ آلِهَةً لَّوْلَا يَأْتُونَ عَلَيْهِم بِسُلْطَانٍ بَيِّنٍ فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَى عَلَى اللَّهِ كَذِباً{15}


"Wadannan mutanemu ne wadanda su ka riki iyayengiji sabaninsa-ubangiji. Me ya sa ba su zo musu da kwararan dalilai ba.? Babu wanda ya fi yin zalunci daga wanda ya kirkiri karya ga Allah."
"Wadannan mutanemu ne wadanda su ka riki iyayengiji sabaninsa-ubangiji. Me ya sa ba su zo musu da kwararan dalilai ba.? Babu wanda ya fi yin zalunci daga wanda ya kirkiri karya ga Allah."'''


A cikin ayar baya mun yi Magana ne akan cewa ma'abota kogo sun fice daga cikin al'ummarsu domin su tsira da imaninsu. To wannan ayar ta nkalato maganar da su ke yi ne a tsakaninsu. Sun cimma matsaya akan cewa tare da cewa a cikin wannan al'ummar aka haife su, kuma anan ne su ke rayuwa, sai dai ba za su iya karbar abinda wannan al'ummar ta ke da shi ba na imani da akida da sabanin Allah. Domin kuwa su wadannan mutanen suna bautar wasu iyayengiji ne na daban ba Allah ba. Ba kuma tare da wani dalili da za su iya gabatar da shi ba. Ga shi kuwa ubangiji guda daya ne tilo ba shi da abokan tarayya. A hakikanin gaskiya wadannan mutanen sun yi wa Allah karya, saboda sun yi masa abokan tarayya. Wannan kuwa ba abu ne da ma'abota kogo su ke jin za su iya karba ba.
A cikin ayar baya mun yi Magana ne akan cewa ma'abota kogo sun fice daga cikin al'ummarsu domin su tsira da imaninsu. To wannan ayar ta nkalato maganar da su ke yi ne a tsakaninsu. Sun cimma matsaya akan cewa tare da cewa a cikin wannan al'ummar aka haife su, kuma anan ne su ke rayuwa, sai dai ba za su iya karbar abinda wannan al'ummar ta ke da shi ba na imani da akida da sabanin Allah. Domin kuwa su wadannan mutanen suna bautar wasu iyayengiji ne na daban ba Allah ba. Ba kuma tare da wani dalili da za su iya gabatar da shi ba. Ga shi kuwa ubangiji guda daya ne tilo ba shi da abokan tarayya. A hakikanin gaskiya wadannan mutanen sun yi wa Allah karya, saboda sun yi masa abokan tarayya. Wannan kuwa ba abu ne da ma'abota kogo su ke jin za su iya karba ba.

Revision as of 11:04, 15 April 2016

IRIB Hausa Tafsir ɗin Suratul Kahf

Links

Suratul Kahfi, Aya Ta 1-6 (Kashi Na 498)

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin da muke kawo muku fassarar ayoyin kur'ani mai girma. Da fatan za a kasance a tare da mu a cikin shirin domin aji ci gabansa daga inda mu ka tsaya a baya.

Yanzu sai a saurari aya ta 1 zuwa ta 3 a cikin suratul Kahfi.

الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي أَنزَلَ عَلَى عَبْدِهِ الْكِتَابَ وَلَمْ يَجْعَل لَّهُ عِوَجَا{1} قَيِّماً لِّيُنذِرَ بَأْساً شَدِيداً مِن لَّدُنْهُ وَيُبَشِّرَ الْمُؤْمِنِينَ الَّذِينَ يَعْمَلُونَ الصَّالِحَاتِ أَنَّ لَهُمْ أَجْراً حَسَناً{2} مَاكِثِينَ فِيهِ أَبَداً{3}

  1. Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya saukar da littafin da babu karkata a cikinsa ga bawansa.
  2. (Littafin ne) mikakke saboda ya yi gargadi mai tsauri daga azabarsa- ubangiji- kuma ya yi bushara ga muminai da su ke yin ayyukan kwarai da cewa suna da kykkyawan lada.
  3. Za kuma su dawwama a cikinsa har abada.

Wannan surar ta fara ne da yi wa Allah godiya saboda saukar da wahayin da ya yi ga manzonsa. Tana kuma koya mana cewa ba saboda ni'imomin abin duniya ne kadai ake yi wa Allah godiya ba, ana yi masa godiya saboda shiriyar da ya yi mana wacce ita ce ni'ima mafi girma. Ni'ima ce wacce ta zo acikin littafin Allah da ya ke na shiriya wanda babu karkata acikinsa. Littafi ne wanda ya ke a mike da ya ke kunshe da bayani akan addini na gaskiya. Sau da yawa a cikin kur'ani ubangiji yana bayyana addini da cewa: Shi ne addini mikakke, yana kuma kiran mutane ne da su bi mikakkiyar hanya ta gaskiya. Hanya ce wacce sako-sako ko wuce gona da iri a cikinta. Kuma ma'aiki yana yi wa mutane gargadi da kuma bushara saboda su kasance cikin fadaka a koda yaushe.

Darussan da su ke a cikin wadannan ayoyi.

  1. Ni'imar kur'ani tana da girman gaske da muhimmanci ta yadda ubangiji ya ke yi wa kansa godiya.
  2. Bushara da gargadi da annabi ya ke yi akan koyarwar da ta zo a cikin kur'ani ne, ba daga gare shi ba ne domin kur'ani shi ne addini mikakke.

Yanzu kuma sai a saurari aya ta 4 da ta 5 acikin wannan sura ta Kahfi.

وَيُنذِرَ الَّذِينَ قَالُوا اتَّخَذَ اللَّهُ وَلَداً{4} مَّا لَهُم بِهِ مِنْ عِلْمٍ وَلَا لِآبَائِهِمْ كَبُرَتْ كَلِمَةً تَخْرُجُ مِنْ أَفْوَاهِهِمْ إِن يَقُولُونَ إِلَّا كَذِباً{5}

    1. Kuma ya yi gargadi ga wadanda su ke cewa Allah ya riki ɗa.
    2. Ba su da masaniya da shi, kuma ba su da masaniya da iyayensu. Kalmar da ta ke fitowa daga bakunansu tana da girma. Abinda su ke fada ba wani abu ba ne face karya.

    Ayoyin da su ka gabata suna magana ne akan gargadi da wa'azi. Amma wadannan ayoyin kuwa suna yin magana ne akan zance mara tushe da ke cewa ubangiji yana da Da. Kirictoci da yahudawa da kuma mushrikai duk sun yi tarayya akan wannan. Mushrikai suna cewa mala'iku 'ya'yan Allah ne, su kuma kiristoci suna cewa Isa ne dan Allah, yayin da yahduawa su ke cewa Uzairu ne dan Allah. Hakikanin gaskiya shi ne cewa wannan irin tunani yana cin karo da akidar tauhidi wanda ya zo a cikin saukakkun littatafai. Darussan da su ke cikin wadannan ayoyin. 1-Fada da gurbatattun akidu wadanda su ke karkatattu shine aiki mai muhimmanci da annabawa su ke yi. 2-Wajibi ne akida ta ginu bisa ginshikin ilimi idan kuwa ba haka ba to za ta kai mutum ga karkacewa. 3-Jahilci da rashin sani ne su ke ingiza mutum ya rika jinginawa ubangiji abubuwan da ba su dace ba. Yanzu kuma sai a saurari aya ta 6 acikin suratu kahfi. فَلَعَلَّكَ بَاخِعٌ نَّفْسَكَ عَلَى آثَارِهِمْ إِن لَّمْ يُؤْمِنُوا بِهَذَا الْحَدِيثِ أَسَفاً{6} "Tamkar kana son ka halaka kanka saboda bakin ciki idan ba su yi imani da wannan zancen ba." Wannan ayar tana kwantarwa da ma'aiki hankali ne dangane da halin mutane. Ya kasance yana yin bakin ciki saboda ganin yadda mushrikai ba su yi imani da zancen gaskiya ba. Yadda ma'aiki ya ke bakin cikin ganin cewa kafirai sun ki yin imani da gaskiyar da ya zo musu da ita, yana yin tsananin da zai iya sanadiyyar mutuwarsa. Yana yin haka ne saboda jin tausayinsa ga mutane da son ganin sun shirya. To wannan ayar ta sauka ne saboda na bashi nutsuwa akan hakan. Darussan da su ke cikin wannan aya. 1-Damuwa akan cewa mutane ba su karfi gaskiya ba wani abu ne mai kima wanda annabawa su ke da shi. 2-Jagororin addini da masu wa'azi wajibi ne a gare su su rika yin kwazon shiryar da mutane da gyara halayensu da akidunsu, koda kuwa ba su sami sakamako na zahiri ba. Karshen wannan shirin kenan sai kuma mun sake haduwa da ku a cikin wani shirin anan gaba.

    Suratul Kahfi, Aya Ta 7-10 (Kashi Na 499)

    Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin da mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur'ani mai girma.

    Idan kuma ba a mance ba muna cikin suratu kahfi ne da mu ka tsaya a aya ta shida. Da fatan za a kasance a tare da mu domin aji ci gaban shirin daga inda mu ka tsaya a baya.

    Yanzu sai a saurari aya ta 7 da kuma 8 acikin suratu kahfi.

    إِنَّا جَعَلْنَا مَا عَلَى الْأَرْضِ زِينَةً لَّهَا لِنَبْلُوَهُمْ أَيُّهُمْ أَحْسَنُ عَمَلاً{7} وَإِنَّا لَجَاعِلُونَ مَا عَلَيْهَا صَعِيداً جُرُزاً{8}

    "Mune mu ka sanya abinda ya ke kan doron kasa a matsayin ado gare ta, saboda mu jarabce su ko wanene ya fi iya kyautata aiki. Mu ne kuma za mu maida abinda yak e kanta- kasar- ya zama fako busasshe."

    A baya mun ga yadda ma'aiki ya ke nuna matukar damuwa akan rashin imanin mushrikai. Damuwa ce ta mai jin tausayi a gare su saboda sun ki karbar gaskiya. Har ubangiji yana yin magana da shi akan cewa damuwar da ka ke ciki saboda ba su yi imani ta yi tsananin da ka kashe kanka.

    To wannan ayar tana cewa: Ubangiji ya halicci duniya ne a matsayin fage na jarabawa domin kyawun da ta duniyar ta ke da shi yana fisgar wasu su damfaru da ita har su mance da Allah. A cikin wannan halin ne na fisguwa da duniya rayuwa za ta zo karshe ta yadda dukkani abubuwan da su ke masu sheki za su dushe. A hakikanin gaskiya wadannan ni'imomin masu jan hankali suna a matsayin jarabawa ce domin sani ko wanene daga cikin mutanen zai kyautata aikin kwarai. Kuma su wanene su ka nutse wajen aikata barna da fasadi.

    Shakka babu rayuwar ba ta tafiya falle daya, idan wata rana an sha zuma to wata rana za a sha madaci. Idan wani lokacin an sha wahala wani lokacin a sha dadi.

    Saboda haka jarabawa ce da ta ke banbanta daga wani zuwa wani a cikin yanayi irin wannan. Kuma da haka ne ita kanta rayuwar ta ke zama mai ma'ana.

    Darussan da su ke cikin wannan aya.

    1-Kyale-kyalen duniya mai gushewa ne ba shi dawwama. Za a iya amfani da kyale-kyalen duniya domin kyautata ayyuka, amma ba a maida su su zama manufa ta karshe ba.

    2-Duk wata ni'ima da abin duniya suna a matsayin jarabawa ne ga mutum. Domin kuwa duk wani abu da Allah zai baiwa mutum yana tare da nau'i a tare da shi, kuma dole ne ya bada jawabi akansa.

    3-Yadda aka kyautata aiki shi ne mai muhimmanci ya yawansa ba. Ubangiji yana son mu yi aiki mafi kyawu ne, ba aiki mai yawa ba.

    Yanzu kuma sai a saurari aya ta 9 da kuma ta 10 acikin suratu kahfi.

    أَمْ حَسِبْتَ أَنَّ أَصْحَابَ الْكَهْفِ وَالرَّقِيمِ كَانُوا مِنْ آيَاتِنَا عَجَباً{9} إِذْ أَوَى الْفِتْيَةُ إِلَى الْكَهْفِ فَقَالُوا رَبَّنَا آتِنَا مِن لَّدُنكَ رَحْمَةً وَهَيِّئْ لَنَا مِنْ أَمْرِنَا رَشَداً{10}

    "Shin ka san cewa mutanen kogo da Raqimu suna daga cikin ayoyinmu masu ban mamaki? "

    "Yayin da samarin su ka nemi mafaka acikin kogo su ka ce ya ubangijinmu ka bamu rahamarka ka kuma shiryar da mu acikin ayyukanmu."

    Shugabannin kuraishawa sun aike da mutane guda biyu zuwa ga yahudawa domin su yi musu nazari da bincike dangane da annabin musulunci. Su kuwa su ka fada musu cewa ku yi masa tambayoyi guda uku idan ya har ya ba ku jawabi ingantacce to ku tabbata annabi ne. Idan kuwa bai baku jawabi ingantacce ba to makaryaci ne.

    Tambaya ta farko ita ce dangane da wasu samari da su ka kauracewa mutanensu, sai ku ji ko ya makomarsu ta kasance?

    Manzon Allah ya fada musu cewa: Gobe zan ba ku jawabi sai dai bai hada da fadin cewa: Insha Allahu ba. Sai da aka dauki kwanaki goma sha biyar sannan jibrilu ya sauka ga manzon Allah.

    Mutanen kogo, wato ashabul-kahafi, wasu samari ne masu imani da su ke rayuwa cikin ni'ima da jin dadi na abin duniya. Sai dai domin kare akidarsu ta tauhidi sun juyawa duniya baya su ka fake acikin kogo. Cikakken bayani akan abinda ya faru da wadannan samarin bayan shigarsu cikin kogo zai zo a ayoyi masu zuwa.

    A kusa da wannan suna na ma'abota kogo sunan Raqimu ya zo. Suna ne na wuri da kuma kogon da ma'abota kogon su ka fake acikinsa. Saboda haka ana kuma kiransu da sunan ma'abota Raqimu.

    An kuma rubuta sunayensu ajikin allon da aka kafe a bakin kogon da su ka fake acikinsa. Domin kuwa kalmar raqim tana nufin rubutu.

    Kamar yadda ya zo acikin littatafan tarihi mutanen kogo sun rayu ne bayan annabi Isa a garin da ya ke a karkashin ikon daukar Roma. Kuma dagutun da ya ke mulki a wancan lokacin shi ne Daqayanusu.

    Alkur'ani mai girma a cikin wadannan ayoyin ya bayyana cewa mutanen kogo sun yi hijira ne zuwa kogo domin su kare addininsu da imaninsu. Ya kuma bayyana su a matsayin samari wanda ya ke nufin masu jarunta ba nuni ne da shekarunsu ba.

    Imam ja'afar sadiq ya bayyana cewa: Wasu daga cikinsu suna da shekaru masu yawa, amma saboda imanin da su ke da shi ne aka ambace su da samari.

    Labarinsu a cikin kur'ani ya fara ne daga kan hijirarsu zuwa cikin kogo. Bai yi magana akan rayuwarsu ta baya ba. Sai dai addu'ar da su ka rika yi tana nuni da cewa suna son ka iwa ga kamala ne da samun shiriya. Ba saboda neman abin duniya ko mukami na siyasa ba ko wani dalili da ya ke sa mutum ya kauracewa mutanensa. Suna neman hanyar tsira a wurin Allah da son kare akidarsu.

    Darussan da su ke cikin wannan aya.

    1-Kare addini, shi ne mafi muhimmanci daga kare gida da iyali. Idan har ya zama wajibi sai an yi hijira to dole a yi ta duk da matsalolin da su ke cikinta.

    2-Addu'a tana da ma'ana idan an hada ta da aiki. Mutanen kogo sun yi hijira sannan su ka yi addu'a, ba zama su ka yi su ka mika hannu ba suna addu'a kadai ba tare da aiki ba.

    3-A cikin koyarwa ta addini samartaka tana nufin sadaukar da kai domin kare addini da yin hijira daga cikin gurbatacciyar al'umma domin kiyaye addini.

    Karshen shirin namu kena sai kuma wani lokacin idan mun sake haduwa.

    Suratul Kahfi, Aya Ta 11-14 (Kashi Na 500)

    Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin na Hannunka Mai Sanda, wanda mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur'ani mai girma. Idan kuma ba a mance ba har yanzu muna cikin suratu kahfi ne. Da fatan za a kasance a tare da mu domin jin ci gaban shirin daga inda mu ka tsaya a baya.

    Yanzu sai a saurari aya ta 11 da 12 a cikin wannan sura ta Kahfi.

    فَضَرَبْنَا عَلَى آذَانِهِمْ فِي الْكَهْفِ سِنِينَ عَدَداً{11} ثُمَّ بَعَثْنَاهُمْ لِنَعْلَمَ أَيُّ الْحِزْبَيْنِ أَحْصَى لِمَا لَبِثُوا أَمَداً{12}

    " Sai mu ka rufe kunnuwansu shekaru masu yawa acikin kogo." "Sannan mu ka farkar da su domin mu san wanene daga cikin kungiyoyin biyu ya fi kididdige tsawon lokacin zamansu.?"

    A shirin baya mun fadi cewa wani gungu na masu imani sun fice daga cikin al'umma zuwa kogo domin su tsira da imaninsu. Sun roki Allah da ya ba su hanyar tsira.

    To abinda wannan ayar ta ke cewa shi ne: Allah ya sa su yin bacci mai nauyi ta yadda ba idanuwansu ne kadai su ka lumshe ba, haka nan ma kunnuwansu sun yi nauyi ta yadda ba su jin wata kwaramniya ko motsi. Wani abu mai jan hankali anan shi ne cewa ayar ta ambaci cewa ubangiji ya rufe kunnuwansu.Watakila saboda a bisa dabi'a mutum zai zama yana barci amma motsin wani abu ya sa shi farkawa. Saboda haka ne Ubangiji bisa hikimarsa ya rufe kunnuwansu a tsawon lokacin da su ke bacci saboda kada wata kwaramniya ta dame su ko ta farkar da su.

    Ayar kuma ta ci gaba da cewa: Yayin da su ka farka sai su ka sami sabani akan tsawon lokacin da su ka dauka suna bacci kamar yadda zai zo a cikin aya ta gaba.

    Darussan da su ke cikin wannan aya.

    1-Idan har wani aikin da mutum ya ke yi saboda Allah ne kuma akan tafarkin addini, to taimakon ubangiji zai riske shi a farke ya ke ko cikin bacci.

    2- Ubangiji yana da cikakkiyar masaniya akan komai, alhali mutane ba su da masaniya akan komai.

    Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 13 da ta 14 acikin wannan sura ta Kahfi.

    نَحْنُ نَقُصُّ عَلَيْكَ نَبَأَهُم بِالْحَقِّ إِنَّهُمْ فِتْيَةٌ آمَنُوا بِرَبِّهِمْ وَزِدْنَاهُمْ هُدًى{13} وَرَبَطْنَا عَلَى قُلُوبِهِمْ إِذْ قَامُوا فَقَالُوا رَبُّنَا رَبُّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ لَن نَّدْعُوَ مِن دُونِهِ إِلَهاً لَقَدْ قُلْنَا إِذاً شَطَطاً{14}

    "Mu ne za mu ba ka labarinsu da gaskiya. Su samari ne da su ka yi imani da ubangijinsu sai kuma mu ka kara musu shiriya. Mu ka kuma karfafa zukatansu yayin da su ka jajurce su ka ce ubangijinmu shi ne ubangijin sammai da kasa ba kuma za mu kirayi waninsa a matsayin Allah ba.( Idan mu ka yi haka) to mun fadi karya."

    Bayan ambaton labarin ma'abota kogo a jumlace, wannan ayar tana magana hijirar da su ka yi dalla-dalla. Da fari tana yin magana ne da ma'aiki tana cewa: Watakila da akwai riwayoyi daban-daban akan labarinsu da mutane su ke watsawa, amma wanda ubangiji madaukaki zai fada shi ne na gaskiya.

    Babu muhimmanci a cikin ambaton adadinsu ko kuma a wane lokaci ne su ka rayu kuma shekaru nawa su ka yi. Abinda ya ke mai muhimmanci shi ne cewa sun yi imani da Allah sannan kuma su ka yi tsayin daka akansa. Saboda haka ne Allah ya kara shiryar da su, ya kuma karfafa zukatansu saboda su iya daurewa matsalolin da za su shiga gabansu.

    Mutane sun kasu gida uku wajen fuskantar barna da fasadi acikin al'umma. Kaso na farko su ne wadanda su ke bin shanun sarki a yi da su. Ba su da karfin zuciya ko 'yanci da tunani na kansu balle kuma iya yin wani abu.

    Kaso na biyu su ne wadanda su ke iya kare kansu su gina katanga tsakaninsu da barnar da ta ke faurwa acikin al'umma ba za su bari ta iso gare su ba.

    Kaso na uku su ne wadanda su ke kokarin kawo sauyi da sauya barnar da ta ke cikin al'umma da kawar da ida. Wannan aiki ne na annabawa da imamai.

    Ma'abota kogo suna daga cikin nau'i na biyu na wannan kason na mutane. Ba su bari barnar da ta ke cikin al'umma ba ta isa gare su balle ta gurbata su. Saboda su tsira da imaninsu sun kauracewa al'ummarsu.

    Al'kur'ani mai girma yana gabatar da labarin mutanen da su shude ne a matsayin wata hanya ta wa'azi da fadakarwa. Saboda haka da akwai kaso mai yawa na ayoyin kur'ani da su ke magana agaba al'ummun da su ka gabata.

    Labaran da su ke zuwa a cikin kur'ani na al'ummun da su ka gabata, ba su yi kama da almara ko kissoshin nishadi ba irin wanda mawaka da marubuta su ke yi, ana kawo su ne domin a dauki darasi.

    Darussan da su ke cikin wadannan ayoyin.

    1-Ubangiji madaukakin sarki ne ya ke bada labarin al'ummun da su ka gabata acikin kur'ani domin su zama hanyar yin tarbiyya. Labaru ne na hakika na abubuwa da su ka faru. 2-Yunkurin da mutum ya ke yi akan tafarkin imani zai sa shi samun shiriya daga Allah ya kuma kai shi ga samun kamala ta imani.

    Karshen shirin namu na wannan lokacin kenan sai a saurare mu a lokaci na gaba domin jin ci gabansa.


    Suratul Kahfi, Aya Ta 15-17 (Kashi Na 501)

    Masu sauraro barkanmu da saduwa da ku a cikin wannan shirin na Hannunka Mai Sanda. Shirin da mu ke kawo muku fassarar ayoyin kur'ani mai tsarki. Kuma har yanzu muna cikin suratu Kahfi ne a akan aya ta 14.

    Da fatan za a kasance a tare da mo domin a ji ci gaban shirin.
    To yanzu sai a saurari aya ta 15 a cikin wannan sura ta Kahfi. هَؤُلَاء قَوْمُنَا اتَّخَذُوا مِن دُونِهِ آلِهَةً لَّوْلَا يَأْتُونَ عَلَيْهِم بِسُلْطَانٍ بَيِّنٍ فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَى عَلَى اللَّهِ كَذِباً{15}

    "Wadannan mutanemu ne wadanda su ka riki iyayengiji sabaninsa-ubangiji. Me ya sa ba su zo musu da kwararan dalilai ba.? Babu wanda ya fi yin zalunci daga wanda ya kirkiri karya ga Allah."

    A cikin ayar baya mun yi Magana ne akan cewa ma'abota kogo sun fice daga cikin al'ummarsu domin su tsira da imaninsu. To wannan ayar ta nkalato maganar da su ke yi ne a tsakaninsu. Sun cimma matsaya akan cewa tare da cewa a cikin wannan al'ummar aka haife su, kuma anan ne su ke rayuwa, sai dai ba za su iya karbar abinda wannan al'ummar ta ke da shi ba na imani da akida da sabanin Allah. Domin kuwa su wadannan mutanen suna bautar wasu iyayengiji ne na daban ba Allah ba. Ba kuma tare da wani dalili da za su iya gabatar da shi ba. Ga shi kuwa ubangiji guda daya ne tilo ba shi da abokan tarayya. A hakikanin gaskiya wadannan mutanen sun yi wa Allah karya, saboda sun yi masa abokan tarayya. Wannan kuwa ba abu ne da ma'abota kogo su ke jin za su iya karba ba.

    Darussan da su ke cikin wannan aya.

    1-Damfaruwa da kabila ko kasantuwa a cikinta ba dalili ne ba da zai sa mutum ya amince da abinda wannan kabilar tashi ta ke da shin a gurbatattun akidu ko kuma kura-kuran da ta ke tafiya akansu.

    2-Karya tana a matsayin zalunci ne mai girma, idan kuwa mutum ya yi wa Allah karya to shi ne babban makaryaci.

    Yanzu kuma sai a saurari aya ta 16 acikin wannan sura ta Kahfi.

    وَإِذِ اعْتَزَلْتُمُوهُمْ وَمَا يَعْبُدُونَ إِلَّا اللَّهَ فَأْوُوا إِلَى الْكَهْفِ يَنشُرْ لَكُمْ رَبُّكُم مِّن رَّحمته ويُهَيِّئْ لَكُم مِّنْ أَمْرِكُم مِّرْفَقاً{16}

    "To tunda kun kaurace musu, kuma kun kauracewa abinda su ke bautawa sabanin ubangiji, sai ku nemi mafaka acikin kogo domin ubangijinku ya bude mu ku rahamarsa ya kuma samar muku da sauki a cikin lamarinku."

    Bayan da ma'abota kogo su ka yi tattauanawa a tsakaninsu da kuma 'yan'uwansu da danginsu, sun cimma matsaya akan cewa ba su da karfin da za su iya samar da suyi acikin wannan al'ummar. Kuma ba za su iya zama a cikinta ba saboda kada su karkatar da su, saboda haka ne su ka yanke shawarar cewa za su fice daga cikin wanann al'ummar. Anan ne jagoransu ya fada musu cewa: To tunda kun yanke shawarar kauracewa wannan al'ummar taku masu bautar gumaka da kuma su kansu gumakan, sai ku nufi kogo saboda ubangiji ya ji kanku ya kuma sauko muku da rahamarsa.

    Darussan da su ke cikin wadannan aya.

    1- Wajibi ne a yi hijira daga cikin al'umma mai gurbatacciyar akida kuma mabarnaciya domin kare akida, koda kuwa za a yi hannun riga da jin dadi na abin duniya. Zaman kogo da za a bautawa Ubangiji cikin tauhidi, shi ne mafi alheri da zama cikin fada mai cike da ni'imomi tare da barna da shirka.

    2-Yunkuri da kuma kokari akan tafarkin Allah, yana share fagen saukar rahamar Ubangiji.

    Yanzu kuma sai a saurari aya ta 17 a cikin wannan sura ta Kahfi.

    وَتَرَى الشَّمْسَ إِذَا طَلَعَت تَّزَاوَرُ عَن كَهْفِهِمْ ذَاتَ الْيَمِينِ وَإِذَا غَرَبَت تَّقْرِضُهُمْ ذَاتَ الشِّمَالِ وَهُمْ فِي فَجْوَةٍ مِّنْهُ ذَلِكَ مِنْ آيَاتِ اللَّهِ مَن يَهْدِ اللَّهُ فَهُوَ الْمُهْتَدِ وَمَن يُضْلِلْ فَلَن تَجِدَ لَهُ وَلِيّاً مُّرْشِداً{17}

    "Kana ganin rana idan ta fito tana karkacewa ta daman kogon, da kuma ta hagu idan za ta fadi, su suna cikin wuri mai yalwa a cikin kogon. Wannan yana daga cikin ayoyin Allah, wanda Allah ya shiryar da shi, shi ne shiryayye. Wanda kuma ya batar to ba za ka sami mai jibintar lamarinsa ba mai shiryarwa."

    Wannan ayar ta kebanta da bayanin taswirar kogon da wadannan muminan su ka shiga ciki, kuma yana daga cikin ayoyin ubangiji. Kogon yana a wani wuri ne.

    Kogon yana a wani wuri ne ta yadda babu hasken rana ya ratsa acikinsa saboda ya cutar da wadannan muminan. Hakan kuwa ya faru ne saboda kare lafiyar gangar jikinsu har na tsawon shekaru dari uku.

    Da akwai maganganu masu yawa akan ko ina ne wannan kogon ya ke a duniya, sai dai mafi shahararren zance shi ne cewa yana a kusa da birnin Damascuss na kasar Syria. Wani zancen kuma yana cewa yana a kusa da birnin Amman ne na kasar Jordan kuma an gina masallaci a kusa da shi. Sai dai sanin ko ina ne inda wannan kogon ya ke ba shi ne mafi muhimmanci ba. Abinda ya ke da muhimmanci shi ne cewa, wadannan muminan sun kauracewa al'ummarsu su ka yi hijira saboda kare imaninsu kuma Allah ya kara musu shiriya. Ma'abota kogo sun so shiriya kuma su ka zabi tafiya akan tafarkinta sai Allah ya kara shiriyar da su. Su kuwa masu bautar gumaka da su ka zabi bata, sai su ka haramtawa kawukansu samun shiriya daga ubangiji.

    Darussan da su ke cikin wadannan ayoyi.

    1-Taimkon Allah ne ya sa ma'abota kogo su ka sami mafaka ya kuma kiyaye su daga sharrin magauta.

    2-Aduk inda bayin Allah su ka kasance to wannan wurin yana zama aya daga cikin ayoyin ubangiji, kuma abin daukar darasi ga mutane.

    Karshen wannan shirin namu kenan, sai kuma lokaci na gaba idan Allah ya sake hada mu. Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakatuhu.