No edit summary |
No edit summary |
||
Line 313: | Line 313: | ||
2-Gina masallaci a makabartar waliyan Allah yana da asali a cikin Alkurani, saboda haka yin wani gini a kabarin waliyyai yana da kyau kuma idan masallaci ne. | 2-Gina masallaci a makabartar waliyan Allah yana da asali a cikin Alkurani, saboda haka yin wani gini a kabarin waliyyai yana da kyau kuma idan masallaci ne. | ||
To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na Surar Kahfi. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu. | |||
===Suratul Kahfi, Aya Ta 22-26 (Kashi Na 503)=== | |||
<html> | |||
<iframe width="100%" height="20" scrolling="no" frameborder="no" src="https://w.soundcloud.com/player/?url=https%3A//api.soundcloud.com/tracks/247836124%3Fsecret_token%3Ds-VrY3Q&color=ff5500&inverse=false&auto_play=false&show_user=true"></iframe> | |||
</html> | |||
* http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/audio/18/503.mp3 | |||
* http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/text/18/503.html | |||
Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar Kahfi, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa. | |||
To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 22: | |||
سَيَقُولُونَ ثَلَاثَةٌ رَّابِعُهُمْ كَلْبُهُمْ وَيَقُولُونَ خَمْسَةٌ سَادِسُهُمْ كَلْبُهُمْ رَجْماً بِالْغَيْبِ وَيَقُولُونَ سَبْعَةٌ وَثَامِنُهُمْ كَلْبُهُمْ قُل رَّبِّي أَعْلَمُ بِعِدَّتِهِم مَّا يَعْلَمُهُمْ إِلَّا قَلِيلٌ فَلَا تُمَارِ فِيهِمْ إِلَّا مِرَاء ظَاهِراً وَلَا تَسْتَفْتِ فِيهِم مِّنْهُمْ أَحَداً{22} | |||
"Zã su ce: "Su uku ne, na hudunsu shi ne karensu." Kuma sunã cẽwa, biyar ne na shidansu ne karensu don lalube cikin duhu, (wasu) kuma sunã cẽwa su bakwai ne na takwas dinsu kuma karensu. Ka ce: 'Ubangijĩna shi ya fi sanin yawansu, bã wanda ya san lamarinsu sai yan kadan." To kada ka yi jãyayya game da alamarinsu sai dai a kan abin da yake fili kuma kada ka bai wa wani daga cikinsu fatawa game da su. | |||
Wannan aya tana bayanin cewa, bayan abinda ya faru da mazauna kogo, zamani zai zo da jamaa zasu yi jayayya dangane da su. Maimakon su yi tunani kan manufar wannan lamari sun tsaya suna jayayya kan adadin mutanen da suyka zauna a cikin kogon, kowanne suna cewa adadinsu kaza ne, alhali kuwa ko su uku ne ko biyar ko bakwai ne bas hi da wani babmbamci kuma ma zai yi tasirin komai ba a imaninsu ko ainiknsu ba. Amma yawa yawn mutane suna zato ne kawai kuma ko da akan abinda ba su sani ba ma suna son su fadi raayinsu a kansa. A wannan aya Allah ya na fada wa manzon sa cewa kada ya yi jayayya da muatne kuma kada ya tambayesu komai, Allah ne ya san adadin mazauna kogon. | |||
Darusa: | |||
1-Abinda ba mu sani ba kada mu yi ta zato da kame kame, kuma mu guji yin jayayya a kansa. | |||
2-Wajen binciken alamuran da suka faru a tarihi ya kamata mu yi tunani da daukar darasi ba wai mu tsaya jayayya kan adadi ko mutane ba. | |||
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 23 da ta 24: | |||
وَلَا تَقُولَنَّ لِشَيْءٍ إِنِّي فَاعِلٌ ذَلِكَ غَداً{23} إِلَّا أَن يَشَاءَ اللَّهُ وَاذْكُر رَّبَّكَ إِذَا نَسِيتَ وَقُلْ عَسَى أَن يَهْدِيَنِ رَبِّي لِأَقْرَبَ مِنْ هَذَا رَشَداً{24} | |||
"Kada kuma ka ce ga kowane, "Hakikazai aikatã wannan gõbe." | |||
"Sai dai ka ce 'Idan Allah Ya so'. Kuma ka ambaci Ubangijinka idan ka manta, kuma ka ce: "Ina kaunar Ubangijĩna ya shirye ni zuwa ga mafi kusa da daidai gane da wannan." | |||
Wadannan ayoyi suna bayanin wata doka da ta shafi kowa da kowa koda yake suna Magana ne da Annabi kai tsaye, amma dukan Musulmi dole ne su kiyaye dokar. Ayoyin suna baynin cewa a duk Magana ko aiki da za a yi a nan gaba ya kamata mumini ya ce in sha Allah a duk lokacin da zai ce zai aikata wato y ace idan Allah ya so. Dalilin wannan shi ne saboda mai magana da mai ji duk su san mahinta cewa abionda mai magana yake fadi said a yardar Allah ne zai iya aikata shi, idan kuwa Allah bai so ba babu abinda yake faruwa. Wato masu imani suna dogara da Allah kuma suna cewa in sha Allah, kamar dai yanda Alkurani ya kawo a cikin maganganun wasu annabawa kamar Yakubu, Shuaibu, Haliru da Ismail. Fadar wannan magana ba wai a kan fatar baki ne kawai, hakan yana bayyana imani da mahangar Musulmi ne wanda ya ke ganin cewa babu abinda zai iya faruwa said a izinin Allah. | |||
Ko da yake kowane mutum yana da nufi da zabi amma faruwar kowani aiki baya dogara kan nufin mutane saboda akwai wasu dalilai da hujjoji da ya wadanda suke da tasiri wajen faruwar wannan abu. Lallai ba bu abin da zai tabbata sai idan Allah ya so. | |||
Darusa: | |||
1-Ka da mu dogara kan kokarinmu da dabararmu. Ka da mu dauka muna da yancin ya ba ikon Allah cikinsa saboda haka kada mu manta da Allah wajen daukar ko wane mataki. | |||
2-Idan annabawa suna bukatar shiryarwa daga Allah a alamuransu na rayuwa, ina ga batun mud a ba annabawa ba? Saboda haka har a kullum mu nemi Allah ya nuna mana mafi kyawun hanya. | |||
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 25 da ta 26: | |||
وَلَبِثُوا فِي كَهْفِهِمْ ثَلَاثَ مِئَةٍ سِنِينَ وَازْدَادُوا تِسْعاً{25} قُلِ اللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا لَبِثُوا لَهُ غَيْبُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ أَبْصِرْ بِهِ وَأَسْمِعْ مَا لَهُم مِّن دُونِهِ مِن وَلِيٍّ وَلَا يُشْرِكُ فِي حُكْمِهِ أَحَداً{26} | |||
"Suka kuwa zauna cikin kõgonsu shẽkaru darĩ uku kuma suka kara tara. | |||
"Ka ce: 'Allah ne Mafi sanin tsawon zaman da suka yi.' Asirin da yake cikin sammai da kasa na sa ne. Wa yake da ji da gani irin na sa! Bã su da wani mataimaki in ban da shi; ba ya kuma tãrayya da wani a cikin hukuncinsa." | |||
Wadannan ayoyi suna ci gaba da bayani kan mazauna kogo wato Ashabul Kahfi tana cewa, Da ikon Allah sun zauna cikin kogon nan shekaru 309. Bisa dabi'a su da suka yi wadannan shekaru suna barci da kuma sauran mutane, ba wanda yake da labarin wannan tsawon lokaci, Allah kadai ne ya san da wannan labari kuma shi ya san yanda suka zauna a cikin kogon ya kuma kiyaye su suna barci. Babu shakka rayuwa har shekaru 300 da doriya ba tare da cin abinci da ko shan ruwa ba mujiza ce daga mujizojin Allah. Hakika Allah ya kare rayuwar mutanen kogo a duk wannan zamani domin ya zama darasi ga masu zuwa nan gaba. | |||
Darusa: | |||
1-A duk wurin da adadi ko alkaluma suke da muhimmanci wajen fassara wani abu to ya kamata a ba da alakluman daidai. Adadin shekarun da Ashabul kahfi suka zauna cikin kogo yana nuni da girman ikon Allah a wannna alamari. | |||
2-Ubangiji shi ne mamallakin komai shi ne kuma mai ba da doka, shi ne masanin komai ko bayyane ko boye saboda haka ba mai iya gudu a tsere wa ikonsa a fake a bayan wani, sai dai a gudu daga wani a fake a wurin Allah. | |||
To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na Surar Kahfi. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu. | |||
===Suratul Kahfi, Aya Ta 27-31 (Kashi Na 504)=== | |||
<html> | |||
<iframe width="100%" height="20" scrolling="no" frameborder="no" src="https://w.soundcloud.com/player/?url=https%3A//api.soundcloud.com/tracks/247836122%3Fsecret_token%3Ds-kbUYl&color=ff5500&inverse=false&auto_play=false&show_user=true"></iframe> | |||
</html> | |||
* http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/audio/18/504.mp3 | |||
* http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/text/18/504.html | |||
Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar Kahfi, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa. | |||
To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 27: | |||
وَاتْلُ مَا أُوحِيَ إِلَيْكَ مِن كِتَابِ رَبِّكَ لَا مُبَدِّلَ لِكَلِمَاتِهِ وَلَن تَجِدَ مِن دُونِهِ مُلْتَحَداً{27} | |||
"Ka karanta abin da aka yi wo maka wahayi da shi daag littãfin Ubangijinka. Bãbu mai canja kalmõminSa kuma bã zã kã sãmi wata mafaka ba in ba ta wurinsa ba. | |||
A karshen labarin Ashabul Kahfi wannan aya tana magana da Annabin Musulunci Muhammadu dan Abdullahi (tsira da amincin Allah su ntabbata a gareshi da alaten gidansa) tana cewa, maganganu marasa hujja da surkulle dangane da wadanan suna da yawa, amma ka fada wa mutane bayanin da ya zo maka cikin wahayi ka fita sha’anin abinda wasu suke fada. Masu saba wa Annabi saboda dalilai daban daban suna bukatar ya sauya wasu ayoyi ko ya canya su domin su yarda da abinda suka kunsa, amma wadannan ayoyi suna nuna cewa kada Annabi ya kula su ya kuma ce musu Alkurani zancen Allah ne kuma baya yiwuwa a canja shi kuma duk wanda ya aikata haka ba zai sami kariya daga azabar Allah ba. | |||
Darusa: | |||
1-Alkurani maganar Allah ce ba ta mutum ba, saboda haka babu hanyar sauya shi a da balle kuma a yanzu. | |||
2-Alkurani shi ne littafin Allah na karshe kuma an kare shi daga dukkan nau’o’in canji kuma ba ya bukatar wani littafi saukakke domin gyara abinda hala mutane zasu sauya daga cikinsa, domin ba bu canjin da zai same shi. | |||
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 28: | |||
وَاصْبِرْ نَفْسَكَ مَعَ الَّذِينَ يَدْعُونَ رَبَّهُم بِالْغَدَاةِ وَالْعَشِيِّ يُرِيدُونَ وَجْهَهُ وَلَا تَعْدُ عَيْنَاكَ عَنْهُمْ تُرِيدُ زِينَةَ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَلَا تُطِعْ مَنْ أَغْفَلْنَا قَلْبَهُ عَن ذِكْرِنَا وَاتَّبَعَ هَوَاهُ وَكَانَ أَمْرُهُ فُرُطاً{28} | |||
"Ka kuma hakura wa kanka (da zama) tare da wadanda suke bauta wa Ubangijinsu sãfe da maraice, sunã neman yardarSa. Kuma kada ka kawar da idanunka daga gare su kanã neman adon rãyuwar dũniya. Kuma kada ka bi wanda Muka shagaltar da zũciyarsa daga ambaton Mu, kuma ya bi son ransa, wanda kuma al'amarinsa ya zama ketare haddi ne. | |||
A cikin labaran tarihi an bayyana cewa wasu manyan mutanen kabilar Kuraishawa sun gabatar wa Annabi da sharadin sai ya kori talakawa marasa daraja a idon jamaa da kuma maida hankalinsa ga sauraron manyan gari da mnasu hamnnu da shuni don su yi imani da sakon Manzon Allah. A cikin tsurin ido da rashin ladabi suka ce da Annabi, ‘Ba zamu taba zuwa majilisinka ba kum aba zamu saurtari maganaerkja ba idan dai wadsnmnan mutane makasta\\kantya suna taree da kai.’ A zamanin Annabi Nuhu ma mutaensa masu jin ceewaa su manya nne sun yi irin wanna bukata, shi kuma sai ya mayar musu fda martini cewa ba zai rab u tad a munminai saboda talkaucinsu ba. Wanna aya tana sukar irin wanna tunani , tana cewa kada Annabi ya saurari wannan yaudara tasu ya kuma kori muminai na gari kamar Abu Zar da Salman ya kore su saboda talauci ko karancin abin hannunsu, ko kuma ya yi ta fama yana bin mutanen da duniya ta aure ko kuma suka mance da ambaton Allah wai dominsu yi imani, wadanda kuma uske bi son zuciyarsu kuma basu da niyar barin bauta wa duniya. | |||
Darusa: | |||
1-Zama da tausaya wa talakawa ya na da wahala amma muminai talakawa sun fi kafirai masu dukiya daraja kuma alummar Musulmi su yi cikakkiyar kulawa da talakan Musulumi. | |||
2-Hadarin da neman duniya yake yi wa jagorannin alummar Musulmi ya kai munin da har Allah yana yi wa Annabinsa kashedi a kansa. | |||
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 29: | |||
وَقُلِ الْحَقُّ مِن رَّبِّكُمْ فَمَن شَاء فَلْيُؤْمِن وَمَن شَاء فَلْيَكْفُرْ إِنَّا أَعْتَدْنَا لِلظَّالِمِينَ نَاراً أَحَاطَ بِهِمْ سُرَادِقُهَا وَإِن يَسْتَغِيثُوا يُغَاثُوا بِمَاء كَالْمُهْلِ يَشْوِي الْوُجُوهَ بِئْسَ الشَّرَابُ وَسَاءتْ مُرْتَفَقاً{29} | |||
"Kuma ka ce: "Gaskiya daga Ubangijinku take." To wanda ya so sai ya ba da gaskiya, wanda kuma ya so sai ya kãfirta, hakika kam Mun tanadar wa azzãlumai wuta wadda katangarta ta kẽwaye su, idan kuma suka nẽmi taimako to za a taimake su ne da ruwa irin na narkakkiyar darma wanda yake toye fuskoki; abin sha ko ya yi mũgunta, makoma kuma ta munana. | |||
Domin amsa maid a martabi kan bukatun wadannan gafalallun masu dukiya wannan aya ta bmna cewa, ai ba wanda yake bukjatar imanin da zasu yi balle nma su sanya wannan sharadi. Maganar gaskiya ta sauka dagha kuma duk wanda ya ga dama ya yi imani duk kuma wanda ya ga dam aya kafirce. Imani ai ba abinda zaa roki wani ya yi bane; mumini daya na hakika ya fi kafirai dubu da zasu ce wai sai da wani sharadi zasu imani. Dadin dadawa ma, mutanen da suka nitse cikin fasadi da bautar ciki a nan duniya, zasu gamu da wurin zama da abinci da abin sha mafiya muni a lahira. Ka da ka dubi rayuwarsun ta wannan duniya wacce gajera ce mai wucewa. | |||
Darusa: | |||
1-Kafirci ko imaninn mutane bas u da wani tasirei wajen tabbatar da gaskiyar addini. Alkurani gaskiya ne koda dukkanin mutane zasu kafrice masa. | |||
2-Koda yake mutane suna da yancin zabar imani ko kuma kafirci amma a karshen aikin kowane daya wadannan daga cikinsu zai hadu da sakamakon daban da na dayan kuma a lahira kafirai zasu gamu da azabar wuta. | |||
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 30 da ta 31: | |||
إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ إِنَّا لَا نُضِيعُ أَجْرَ مَنْ أَحْسَنَ عَمَلاً{30} أُوْلَئِكَ لَهُمْ جَنَّاتُ عَدْنٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهِمُ الْأَنْهَارُ يُحَلَّوْنَ فِيهَا مِنْ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٍ وَيَلْبَسُونَ ثِيَاباً خُضْراً مِّن سُندُسٍ وَإِسْتَبْرَقٍ مُّتَّكِئِينَ فِيهَا عَلَى الْأَرَائِكِ نِعْمَ الثَّوَابُ وَحَسُنَتْ مُرْتَفَقاً{31} | |||
"Lalle ne wadanda suka yi ĩmãni kuma suka yi aiki na gari hakika Mu ba Mu tõzarta lãdan wanda ya kyautata aiki." | |||
"Wadannan sunã da gidãjen Aljanna na dawwama wadanda kõramu ke gudãna daga karkashinsu, anã sanya musu kawa, a cikinsu, daga mundãye na zinariya, kuma sunã tufantar wadansu tũfãfi kõre, na alharĩni rakĩki da alharini mai kauri sunã kishingide a cikinsu,a kan, karagu. Mãdalla da sakamakonsu. Kuma Aljanna ta kyautatu da zama wurin hutãwa." | |||
Wadannnan ayoyi suna bayanin matsayin muminai sana cewa, su wadannan talakawan da ku ke gani a nan duniya , idan masu biyayya ne ga Annabi da rikon da tafarkin Allah kamar yanda ya dace, a ranar alkiyama zaa saka musu da mafi kyaun wurin zama, wurin da masu dukiya a nan duniya zasu yi dokin su zauna a cikinsa koda na dan lokaci ne. Idan a yau masu mukami suna sanya tufafi na alfarma da kayan ado masu tsada, suna daukar kansu masu girma, to ai su kuma matalauta a ranar lahira zasu sami tufafi da kayan ado wadanda ba za a iya kwatantasu da kayan adon wannan duniya ba. Amma fa marasa galihun zasu sami wannan jin dadi a lahairan ne idan sun yi imanin kwarai da ayyuka na gari, wanda kuma su ma masu dukiya idan sun yi biyayya ga Allah suka nisanci girman kai da sauda yawa dukiya take sa mutum, zasu sami sakamako mai kyau da jin dadi a lahira. | |||
Darusa: | |||
1-Abin da muminai suka rasa a nan duniya saboda bioyayya ga dokokin Ubangiji, a ranar alkiyama Allah zai mayar musu da gurbinsa da abin da fi shi dadi da kuma kyau. | |||
2-Mu yi aiki domin Allah, aikin da ba zai rage mana ladanmu ba kuma ladansa ba irin ladan nan ne mai karewa nan take ba. | |||
To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na Surar Kahfi. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu. | To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na Surar Kahfi. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu. |
Revision as of 17:55, 2 July 2016
IRIB Hausa Tafsir ɗin Suratul Kahf
Links
- Quran/18
- http://www.masjidtucson.org/hausa/Surah_018.pdf
- Quran_translation_in_hausa_language#Chapter_18_.28Sura_18.29
Suratul Kahfi, Aya Ta 1-6 (Kashi Na 498)
- http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/audio/18/498.mp3
- http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/text/18/498.html
Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin da muke kawo muku fassarar ayoyin kur'ani mai girma. Da fatan za a kasance a tare da mu a cikin shirin domin aji ci gabansa daga inda mu ka tsaya a baya.
Yanzu sai a saurari aya ta 1 zuwa ta 3 a cikin suratul Kahfi.
الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي أَنزَلَ عَلَى عَبْدِهِ الْكِتَابَ وَلَمْ يَجْعَل لَّهُ عِوَجَا{1} قَيِّماً لِّيُنذِرَ بَأْساً شَدِيداً مِن لَّدُنْهُ وَيُبَشِّرَ الْمُؤْمِنِينَ الَّذِينَ يَعْمَلُونَ الصَّالِحَاتِ أَنَّ لَهُمْ أَجْراً حَسَناً{2} مَاكِثِينَ فِيهِ أَبَداً{3}
- Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya saukar da littafin da babu karkata a cikinsa ga bawansa.
- (Littafin ne) mikakke saboda ya yi gargadi mai tsauri daga azabarsa- ubangiji- kuma ya yi bushara ga muminai da su ke yin ayyukan kwarai da cewa suna da kykkyawan lada.
- Za kuma su dawwama a cikinsa har abada.
Wannan surar ta fara ne da yi wa Allah godiya saboda saukar da wahayin da ya yi ga manzonsa. Tana kuma koya mana cewa ba saboda ni'imomin abin duniya ne kadai ake yi wa Allah godiya ba, ana yi masa godiya saboda shiriyar da ya yi mana wacce ita ce ni'ima mafi girma. Ni'ima ce wacce ta zo acikin littafin Allah da ya ke na shiriya wanda babu karkata acikinsa. Littafi ne wanda ya ke a mike da ya ke kunshe da bayani akan addini na gaskiya. Sau da yawa a cikin kur'ani ubangiji yana bayyana addini da cewa: Shi ne addini mikakke, yana kuma kiran mutane ne da su bi mikakkiyar hanya ta gaskiya. Hanya ce wacce sako-sako ko wuce gona da iri a cikinta. Kuma ma'aiki yana yi wa mutane gargadi da kuma bushara saboda su kasance cikin fadaka a koda yaushe.
Darussan da su ke a cikin wadannan ayoyi.
- Ni'imar kur'ani tana da girman gaske da muhimmanci ta yadda ubangiji ya ke yi wa kansa godiya.
- Bushara da gargadi da annabi ya ke yi akan koyarwar da ta zo a cikin kur'ani ne, ba daga gare shi ba ne domin kur'ani shi ne addini mikakke.
Yanzu kuma sai a saurari aya ta 4 da ta 5 acikin wannan sura ta Kahfi.
وَيُنذِرَ الَّذِينَ قَالُوا اتَّخَذَ اللَّهُ وَلَداً{4} مَّا لَهُم بِهِ مِنْ عِلْمٍ وَلَا لِآبَائِهِمْ كَبُرَتْ كَلِمَةً تَخْرُجُ مِنْ أَفْوَاهِهِمْ إِن يَقُولُونَ إِلَّا كَذِباً{5}
- Kuma ya yi gargadi ga wadanda su ke cewa Allah ya riki ɗa.
- Ba su da masaniya da shi, kuma ba su da masaniya da iyayensu. Kalmar da ta ke fitowa daga bakunansu tana da girma. Abinda su ke fada ba wani abu ba ne face karya.
Ayoyin da su ka gabata suna magana ne akan gargadi da wa'azi. Amma wadannan ayoyin kuwa suna yin magana ne akan zance mara tushe da ke cewa ubangiji yana da Da. Kirictoci da yahudawa da kuma mushrikai duk sun yi tarayya akan wannan. Mushrikai suna cewa mala'iku 'ya'yan Allah ne, su kuma kiristoci suna cewa Isa ne dan Allah, yayin da yahduawa su ke cewa Uzairu ne dan Allah. Hakikanin gaskiya shi ne cewa wannan irin tunani yana cin karo da akidar tauhidi wanda ya zo a cikin saukakkun littatafai. Darussan da su ke cikin wadannan ayoyin. 1-Fada da gurbatattun akidu wadanda su ke karkatattu shine aiki mai muhimmanci da annabawa su ke yi. 2-Wajibi ne akida ta ginu bisa ginshikin ilimi idan kuwa ba haka ba to za ta kai mutum ga karkacewa. 3-Jahilci da rashin sani ne su ke ingiza mutum ya rika jinginawa ubangiji abubuwan da ba su dace ba. Yanzu kuma sai a saurari aya ta 6 acikin suratu kahfi. فَلَعَلَّكَ بَاخِعٌ نَّفْسَكَ عَلَى آثَارِهِمْ إِن لَّمْ يُؤْمِنُوا بِهَذَا الْحَدِيثِ أَسَفاً{6} "Tamkar kana son ka halaka kanka saboda bakin ciki idan ba su yi imani da wannan zancen ba." Wannan ayar tana kwantarwa da ma'aiki hankali ne dangane da halin mutane. Ya kasance yana yin bakin ciki saboda ganin yadda mushrikai ba su yi imani da zancen gaskiya ba. Yadda ma'aiki ya ke bakin cikin ganin cewa kafirai sun ki yin imani da gaskiyar da ya zo musu da ita, yana yin tsananin da zai iya sanadiyyar mutuwarsa. Yana yin haka ne saboda jin tausayinsa ga mutane da son ganin sun shirya. To wannan ayar ta sauka ne saboda na bashi nutsuwa akan hakan. Darussan da su ke cikin wannan aya. 1-Damuwa akan cewa mutane ba su karfi gaskiya ba wani abu ne mai kima wanda annabawa su ke da shi. 2-Jagororin addini da masu wa'azi wajibi ne a gare su su rika yin kwazon shiryar da mutane da gyara halayensu da akidunsu, koda kuwa ba su sami sakamako na zahiri ba. Karshen wannan shirin kenan sai kuma mun sake haduwa da ku a cikin wani shirin anan gaba.
Suratul Kahfi, Aya Ta 7-10 (Kashi Na 499)
- http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/audio/18/499.mp3
- http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/text/18/499.html
Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin da mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur'ani mai girma.
Idan kuma ba a mance ba muna cikin suratu kahfi ne da mu ka tsaya a aya ta shida. Da fatan za a kasance a tare da mu domin aji ci gaban shirin daga inda mu ka tsaya a baya.
Yanzu sai a saurari aya ta 7 da kuma 8 acikin suratu kahfi.
إِنَّا جَعَلْنَا مَا عَلَى الْأَرْضِ زِينَةً لَّهَا لِنَبْلُوَهُمْ أَيُّهُمْ أَحْسَنُ عَمَلاً{7} وَإِنَّا لَجَاعِلُونَ مَا عَلَيْهَا صَعِيداً جُرُزاً{8}
"Mune mu ka sanya abinda ya ke kan doron kasa a matsayin ado gare ta, saboda mu jarabce su ko wanene ya fi iya kyautata aiki. Mu ne kuma za mu maida abinda yak e kanta- kasar- ya zama fako busasshe."
A baya mun ga yadda ma'aiki ya ke nuna matukar damuwa akan rashin imanin mushrikai. Damuwa ce ta mai jin tausayi a gare su saboda sun ki karbar gaskiya. Har ubangiji yana yin magana da shi akan cewa damuwar da ka ke ciki saboda ba su yi imani ta yi tsananin da ka kashe kanka.
To wannan ayar tana cewa: Ubangiji ya halicci duniya ne a matsayin fage na jarabawa domin kyawun da ta duniyar ta ke da shi yana fisgar wasu su damfaru da ita har su mance da Allah. A cikin wannan halin ne na fisguwa da duniya rayuwa za ta zo karshe ta yadda dukkani abubuwan da su ke masu sheki za su dushe. A hakikanin gaskiya wadannan ni'imomin masu jan hankali suna a matsayin jarabawa ce domin sani ko wanene daga cikin mutanen zai kyautata aikin kwarai. Kuma su wanene su ka nutse wajen aikata barna da fasadi.
Shakka babu rayuwar ba ta tafiya falle daya, idan wata rana an sha zuma to wata rana za a sha madaci. Idan wani lokacin an sha wahala wani lokacin a sha dadi.
Saboda haka jarabawa ce da ta ke banbanta daga wani zuwa wani a cikin yanayi irin wannan. Kuma da haka ne ita kanta rayuwar ta ke zama mai ma'ana.
Darussan da su ke cikin wannan aya.
1-Kyale-kyalen duniya mai gushewa ne ba shi dawwama. Za a iya amfani da kyale-kyalen duniya domin kyautata ayyuka, amma ba a maida su su zama manufa ta karshe ba.
2-Duk wata ni'ima da abin duniya suna a matsayin jarabawa ne ga mutum. Domin kuwa duk wani abu da Allah zai baiwa mutum yana tare da nau'i a tare da shi, kuma dole ne ya bada jawabi akansa.
3-Yadda aka kyautata aiki shi ne mai muhimmanci ya yawansa ba. Ubangiji yana son mu yi aiki mafi kyawu ne, ba aiki mai yawa ba.
Yanzu kuma sai a saurari aya ta 9 da kuma ta 10 acikin suratu kahfi.
أَمْ حَسِبْتَ أَنَّ أَصْحَابَ الْكَهْفِ وَالرَّقِيمِ كَانُوا مِنْ آيَاتِنَا عَجَباً{9} إِذْ أَوَى الْفِتْيَةُ إِلَى الْكَهْفِ فَقَالُوا رَبَّنَا آتِنَا مِن لَّدُنكَ رَحْمَةً وَهَيِّئْ لَنَا مِنْ أَمْرِنَا رَشَداً{10}
"Shin ka san cewa mutanen kogo da Raqimu suna daga cikin ayoyinmu masu ban mamaki? "
"Yayin da samarin su ka nemi mafaka acikin kogo su ka ce ya ubangijinmu ka bamu rahamarka ka kuma shiryar da mu acikin ayyukanmu."
Shugabannin kuraishawa sun aike da mutane guda biyu zuwa ga yahudawa domin su yi musu nazari da bincike dangane da annabin musulunci. Su kuwa su ka fada musu cewa ku yi masa tambayoyi guda uku idan ya har ya ba ku jawabi ingantacce to ku tabbata annabi ne. Idan kuwa bai baku jawabi ingantacce ba to makaryaci ne.
Tambaya ta farko ita ce dangane da wasu samari da su ka kauracewa mutanensu, sai ku ji ko ya makomarsu ta kasance?
Manzon Allah ya fada musu cewa: Gobe zan ba ku jawabi sai dai bai hada da fadin cewa: Insha Allahu ba. Sai da aka dauki kwanaki goma sha biyar sannan jibrilu ya sauka ga manzon Allah.
Mutanen kogo, wato ashabul-kahafi, wasu samari ne masu imani da su ke rayuwa cikin ni'ima da jin dadi na abin duniya. Sai dai domin kare akidarsu ta tauhidi sun juyawa duniya baya su ka fake acikin kogo. Cikakken bayani akan abinda ya faru da wadannan samarin bayan shigarsu cikin kogo zai zo a ayoyi masu zuwa.
A kusa da wannan suna na ma'abota kogo sunan Raqimu ya zo. Suna ne na wuri da kuma kogon da ma'abota kogon su ka fake acikinsa. Saboda haka ana kuma kiransu da sunan ma'abota Raqimu.
An kuma rubuta sunayensu ajikin allon da aka kafe a bakin kogon da su ka fake acikinsa. Domin kuwa kalmar raqim tana nufin rubutu.
Kamar yadda ya zo acikin littatafan tarihi mutanen kogo sun rayu ne bayan annabi Isa a garin da ya ke a karkashin ikon daukar Roma. Kuma dagutun da ya ke mulki a wancan lokacin shi ne Daqayanusu.
Alkur'ani mai girma a cikin wadannan ayoyin ya bayyana cewa mutanen kogo sun yi hijira ne zuwa kogo domin su kare addininsu da imaninsu. Ya kuma bayyana su a matsayin samari wanda ya ke nufin masu jarunta ba nuni ne da shekarunsu ba.
Imam ja'afar sadiq ya bayyana cewa: Wasu daga cikinsu suna da shekaru masu yawa, amma saboda imanin da su ke da shi ne aka ambace su da samari.
Labarinsu a cikin kur'ani ya fara ne daga kan hijirarsu zuwa cikin kogo. Bai yi magana akan rayuwarsu ta baya ba. Sai dai addu'ar da su ka rika yi tana nuni da cewa suna son ka iwa ga kamala ne da samun shiriya. Ba saboda neman abin duniya ko mukami na siyasa ba ko wani dalili da ya ke sa mutum ya kauracewa mutanensa. Suna neman hanyar tsira a wurin Allah da son kare akidarsu.
Darussan da su ke cikin wannan aya.
1-Kare addini, shi ne mafi muhimmanci daga kare gida da iyali. Idan har ya zama wajibi sai an yi hijira to dole a yi ta duk da matsalolin da su ke cikinta.
2-Addu'a tana da ma'ana idan an hada ta da aiki. Mutanen kogo sun yi hijira sannan su ka yi addu'a, ba zama su ka yi su ka mika hannu ba suna addu'a kadai ba tare da aiki ba.
3-A cikin koyarwa ta addini samartaka tana nufin sadaukar da kai domin kare addini da yin hijira daga cikin gurbatacciyar al'umma domin kiyaye addini.
Karshen shirin namu kena sai kuma wani lokacin idan mun sake haduwa.
Suratul Kahfi, Aya Ta 11-14 (Kashi Na 500)
- http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/audio/18/500.mp3
- http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/text/18/500.html
Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin na Hannunka Mai Sanda, wanda mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur'ani mai girma. Idan kuma ba a mance ba har yanzu muna cikin suratu kahfi ne. Da fatan za a kasance a tare da mu domin jin ci gaban shirin daga inda mu ka tsaya a baya.
Yanzu sai a saurari aya ta 11 da 12 a cikin wannan sura ta Kahfi.
فَضَرَبْنَا عَلَى آذَانِهِمْ فِي الْكَهْفِ سِنِينَ عَدَداً{11} ثُمَّ بَعَثْنَاهُمْ لِنَعْلَمَ أَيُّ الْحِزْبَيْنِ أَحْصَى لِمَا لَبِثُوا أَمَداً{12}
" Sai mu ka rufe kunnuwansu shekaru masu yawa acikin kogo." "Sannan mu ka farkar da su domin mu san wanene daga cikin kungiyoyin biyu ya fi kididdige tsawon lokacin zamansu.?"
A shirin baya mun fadi cewa wani gungu na masu imani sun fice daga cikin al'umma zuwa kogo domin su tsira da imaninsu. Sun roki Allah da ya ba su hanyar tsira.
To abinda wannan ayar ta ke cewa shi ne: Allah ya sa su yin bacci mai nauyi ta yadda ba idanuwansu ne kadai su ka lumshe ba, haka nan ma kunnuwansu sun yi nauyi ta yadda ba su jin wata kwaramniya ko motsi. Wani abu mai jan hankali anan shi ne cewa ayar ta ambaci cewa ubangiji ya rufe kunnuwansu.Watakila saboda a bisa dabi'a mutum zai zama yana barci amma motsin wani abu ya sa shi farkawa. Saboda haka ne Ubangiji bisa hikimarsa ya rufe kunnuwansu a tsawon lokacin da su ke bacci saboda kada wata kwaramniya ta dame su ko ta farkar da su.
Ayar kuma ta ci gaba da cewa: Yayin da su ka farka sai su ka sami sabani akan tsawon lokacin da su ka dauka suna bacci kamar yadda zai zo a cikin aya ta gaba.
Darussan da su ke cikin wannan aya.
1-Idan har wani aikin da mutum ya ke yi saboda Allah ne kuma akan tafarkin addini, to taimakon ubangiji zai riske shi a farke ya ke ko cikin bacci.
2- Ubangiji yana da cikakkiyar masaniya akan komai, alhali mutane ba su da masaniya akan komai.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 13 da ta 14 acikin wannan sura ta Kahfi.
نَحْنُ نَقُصُّ عَلَيْكَ نَبَأَهُم بِالْحَقِّ إِنَّهُمْ فِتْيَةٌ آمَنُوا بِرَبِّهِمْ وَزِدْنَاهُمْ هُدًى{13} وَرَبَطْنَا عَلَى قُلُوبِهِمْ إِذْ قَامُوا فَقَالُوا رَبُّنَا رَبُّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ لَن نَّدْعُوَ مِن دُونِهِ إِلَهاً لَقَدْ قُلْنَا إِذاً شَطَطاً{14}
"Mu ne za mu ba ka labarinsu da gaskiya. Su samari ne da su ka yi imani da ubangijinsu sai kuma mu ka kara musu shiriya. Mu ka kuma karfafa zukatansu yayin da su ka jajurce su ka ce ubangijinmu shi ne ubangijin sammai da kasa ba kuma za mu kirayi waninsa a matsayin Allah ba.( Idan mu ka yi haka) to mun fadi karya."
Bayan ambaton labarin ma'abota kogo a jumlace, wannan ayar tana magana hijirar da su ka yi dalla-dalla. Da fari tana yin magana ne da ma'aiki tana cewa: Watakila da akwai riwayoyi daban-daban akan labarinsu da mutane su ke watsawa, amma wanda ubangiji madaukaki zai fada shi ne na gaskiya.
Babu muhimmanci a cikin ambaton adadinsu ko kuma a wane lokaci ne su ka rayu kuma shekaru nawa su ka yi. Abinda ya ke mai muhimmanci shi ne cewa sun yi imani da Allah sannan kuma su ka yi tsayin daka akansa. Saboda haka ne Allah ya kara shiryar da su, ya kuma karfafa zukatansu saboda su iya daurewa matsalolin da za su shiga gabansu.
Mutane sun kasu gida uku wajen fuskantar barna da fasadi acikin al'umma. Kaso na farko su ne wadanda su ke bin shanun sarki a yi da su. Ba su da karfin zuciya ko 'yanci da tunani na kansu balle kuma iya yin wani abu.
Kaso na biyu su ne wadanda su ke iya kare kansu su gina katanga tsakaninsu da barnar da ta ke faurwa acikin al'umma ba za su bari ta iso gare su ba.
Kaso na uku su ne wadanda su ke kokarin kawo sauyi da sauya barnar da ta ke cikin al'umma da kawar da ida. Wannan aiki ne na annabawa da imamai.
Ma'abota kogo suna daga cikin nau'i na biyu na wannan kason na mutane. Ba su bari barnar da ta ke cikin al'umma ba ta isa gare su balle ta gurbata su. Saboda su tsira da imaninsu sun kauracewa al'ummarsu.
Al'kur'ani mai girma yana gabatar da labarin mutanen da su shude ne a matsayin wata hanya ta wa'azi da fadakarwa. Saboda haka da akwai kaso mai yawa na ayoyin kur'ani da su ke magana agaba al'ummun da su ka gabata.
Labaran da su ke zuwa a cikin kur'ani na al'ummun da su ka gabata, ba su yi kama da almara ko kissoshin nishadi ba irin wanda mawaka da marubuta su ke yi, ana kawo su ne domin a dauki darasi.
Darussan da su ke cikin wadannan ayoyin.
1-Ubangiji madaukakin sarki ne ya ke bada labarin al'ummun da su ka gabata acikin kur'ani domin su zama hanyar yin tarbiyya. Labaru ne na hakika na abubuwa da su ka faru. 2-Yunkurin da mutum ya ke yi akan tafarkin imani zai sa shi samun shiriya daga Allah ya kuma kai shi ga samun kamala ta imani.
Karshen shirin namu na wannan lokacin kenan sai a saurare mu a lokaci na gaba domin jin ci gabansa.
Suratul Kahfi, Aya Ta 15-17 (Kashi Na 501)
- http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/audio/18/501.mp3
- http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/text/18/501.html
Masu sauraro barkanmu da saduwa da ku a cikin wannan shirin na Hannunka Mai Sanda. Shirin da mu ke kawo muku fassarar ayoyin kur'ani mai tsarki. Kuma har yanzu muna cikin suratu Kahfi ne a akan aya ta 14.
Da fatan za a kasance a tare da mo domin a ji ci gaban shirin.
To yanzu sai a saurari aya ta 15 a cikin wannan sura ta Kahfi.
هَؤُلَاء قَوْمُنَا اتَّخَذُوا مِن دُونِهِ آلِهَةً لَّوْلَا يَأْتُونَ عَلَيْهِم بِسُلْطَانٍ بَيِّنٍ فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَى عَلَى اللَّهِ كَذِباً{15}
"Wadannan mutanemu ne wadanda su ka riki iyayengiji sabaninsa-ubangiji. Me ya sa ba su zo musu da kwararan dalilai ba.? Babu wanda ya fi yin zalunci daga wanda ya kirkiri karya ga Allah."
A cikin ayar baya mun yi Magana ne akan cewa ma'abota kogo sun fice daga cikin al'ummarsu domin su tsira da imaninsu. To wannan ayar ta nkalato maganar da su ke yi ne a tsakaninsu. Sun cimma matsaya akan cewa tare da cewa a cikin wannan al'ummar aka haife su, kuma anan ne su ke rayuwa, sai dai ba za su iya karbar abinda wannan al'ummar ta ke da shi ba na imani da akida da sabanin Allah. Domin kuwa su wadannan mutanen suna bautar wasu iyayengiji ne na daban ba Allah ba. Ba kuma tare da wani dalili da za su iya gabatar da shi ba. Ga shi kuwa ubangiji guda daya ne tilo ba shi da abokan tarayya. A hakikanin gaskiya wadannan mutanen sun yi wa Allah karya, saboda sun yi masa abokan tarayya. Wannan kuwa ba abu ne da ma'abota kogo su ke jin za su iya karba ba.
Darussan da su ke cikin wannan aya.
1-Damfaruwa da kabila ko kasantuwa a cikinta ba dalili ne ba da zai sa mutum ya amince da abinda wannan kabilar tashi ta ke da shin a gurbatattun akidu ko kuma kura-kuran da ta ke tafiya akansu.
2-Karya tana a matsayin zalunci ne mai girma, idan kuwa mutum ya yi wa Allah karya to shi ne babban makaryaci.
Yanzu kuma sai a saurari aya ta 16 acikin wannan sura ta Kahfi.
وَإِذِ اعْتَزَلْتُمُوهُمْ وَمَا يَعْبُدُونَ إِلَّا اللَّهَ فَأْوُوا إِلَى الْكَهْفِ يَنشُرْ لَكُمْ رَبُّكُم مِّن رَّحمته ويُهَيِّئْ لَكُم مِّنْ أَمْرِكُم مِّرْفَقاً{16}
"To tunda kun kaurace musu, kuma kun kauracewa abinda su ke bautawa sabanin ubangiji, sai ku nemi mafaka acikin kogo domin ubangijinku ya bude mu ku rahamarsa ya kuma samar muku da sauki a cikin lamarinku."
Bayan da ma'abota kogo su ka yi tattauanawa a tsakaninsu da kuma 'yan'uwansu da danginsu, sun cimma matsaya akan cewa ba su da karfin da za su iya samar da suyi acikin wannan al'ummar. Kuma ba za su iya zama a cikinta ba saboda kada su karkatar da su, saboda haka ne su ka yanke shawarar cewa za su fice daga cikin wanann al'ummar. Anan ne jagoransu ya fada musu cewa: To tunda kun yanke shawarar kauracewa wannan al'ummar taku masu bautar gumaka da kuma su kansu gumakan, sai ku nufi kogo saboda ubangiji ya ji kanku ya kuma sauko muku da rahamarsa.
Darussan da su ke cikin wadannan aya.
1- Wajibi ne a yi hijira daga cikin al'umma mai gurbatacciyar akida kuma mabarnaciya domin kare akida, koda kuwa za a yi hannun riga da jin dadi na abin duniya. Zaman kogo da za a bautawa Ubangiji cikin tauhidi, shi ne mafi alheri da zama cikin fada mai cike da ni'imomi tare da barna da shirka.
2-Yunkuri da kuma kokari akan tafarkin Allah, yana share fagen saukar rahamar Ubangiji.
Yanzu kuma sai a saurari aya ta 17 a cikin wannan sura ta Kahfi.
وَتَرَى الشَّمْسَ إِذَا طَلَعَت تَّزَاوَرُ عَن كَهْفِهِمْ ذَاتَ الْيَمِينِ وَإِذَا غَرَبَت تَّقْرِضُهُمْ ذَاتَ الشِّمَالِ وَهُمْ فِي فَجْوَةٍ مِّنْهُ ذَلِكَ مِنْ آيَاتِ اللَّهِ مَن يَهْدِ اللَّهُ فَهُوَ الْمُهْتَدِ وَمَن يُضْلِلْ فَلَن تَجِدَ لَهُ وَلِيّاً مُّرْشِداً{17}
"Kana ganin rana idan ta fito tana karkacewa ta daman kogon, da kuma ta hagu idan za ta fadi, su suna cikin wuri mai yalwa a cikin kogon. Wannan yana daga cikin ayoyin Allah, wanda Allah ya shiryar da shi, shi ne shiryayye. Wanda kuma ya batar to ba za ka sami mai jibintar lamarinsa ba mai shiryarwa."
Wannan ayar ta kebanta da bayanin taswirar kogon da wadannan muminan su ka shiga ciki, kuma yana daga cikin ayoyin ubangiji. Kogon yana a wani wuri ne.
Kogon yana a wani wuri ne ta yadda babu hasken rana ya ratsa acikinsa saboda ya cutar da wadannan muminan. Hakan kuwa ya faru ne saboda kare lafiyar gangar jikinsu har na tsawon shekaru dari uku.
Da akwai maganganu masu yawa akan ko ina ne wannan kogon ya ke a duniya, sai dai mafi shahararren zance shi ne cewa yana a kusa da birnin Damascuss na kasar Syria. Wani zancen kuma yana cewa yana a kusa da birnin Amman ne na kasar Jordan kuma an gina masallaci a kusa da shi. Sai dai sanin ko ina ne inda wannan kogon ya ke ba shi ne mafi muhimmanci ba. Abinda ya ke da muhimmanci shi ne cewa, wadannan muminan sun kauracewa al'ummarsu su ka yi hijira saboda kare imaninsu kuma Allah ya kara musu shiriya. Ma'abota kogo sun so shiriya kuma su ka zabi tafiya akan tafarkinta sai Allah ya kara shiriyar da su. Su kuwa masu bautar gumaka da su ka zabi bata, sai su ka haramtawa kawukansu samun shiriya daga ubangiji.
Darussan da su ke cikin wadannan ayoyi.
1-Taimkon Allah ne ya sa ma'abota kogo su ka sami mafaka ya kuma kiyaye su daga sharrin magauta.
2-Aduk inda bayin Allah su ka kasance to wannan wurin yana zama aya daga cikin ayoyin ubangiji, kuma abin daukar darasi ga mutane.
Karshen wannan shirin namu kenan, sai kuma lokaci na gaba idan Allah ya sake hada mu. Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakatuhu.
Suratul Kahfi, Aya Ta 18-21 (Kashi Na 502)
- http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/audio/18/502.mp3
- http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/text/18/502.html
Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar Kahfi, da fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa.
To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 18:
وَتَحْسَبُهُمْ أَيْقَاظاً وَهُمْ رُقُودٌ وَنُقَلِّبُهُمْ ذَاتَ الْيَمِينِ وَذَاتَ الشِّمَالِ وَكَلْبُهُم بَاسِطٌ ذِرَاعَيْهِ بِالْوَصِيدِ لَوِ اطَّلَعْتَ عَلَيْهِمْ لَوَلَّيْتَ مِنْهُمْ فِرَاراً وَلَمُلِئْتَ مِنْهُمْ رُعْباً{18}
"Kuma za ka zaci a farke su ke alhãli kuwa sũ na barci ne. Munã kuma jũya su ta barin dãma da ta barin hagu, karensu kuma ya shimfida kafãfunsa na gaba a dandamalin kõgon. Dã abin ka lẽka su ne da lalle ne ka fita a guje, lalle kuma da ka cika da tsoronsu.
A shirin da ya gabata mun bayyana cewa Allah madaukakinn sarki tanadar wa wasu mutane yanayin da zasu kare addininsu da akidarsu suka shiga kogo, Allah ya sa sun yi barci kuma kunnuwansu ba su jin komai don ka da su farka. Wannan aya kuma tana cewa, wadannan mutane suna cikin barci amma idanunsu suna bude kuma duk wanda ya gan su zai tsammanci suna farke ne amma basu ji, saboda haka duk wanda ya gansu zai ji tsoro kuma hala ma ya arce. Akwai alamar cewa an yi hakan ne saboda a karesu daga cutuwa kuma a kare rayukansu su daga hadari.
Ayar ta kara da cewa, domin kare lafiyar jikinsu ana juya su daga gefe daya zuwa daya gefen don kada jikunansu su yi ciwo. An yi dukkan shirye shirye dai domin kare lafiyar mutanen Ashabul Kahfi da rayukansu kuma saboda ya zama darasi ga masu zuwa a nan gaba.
Darusa:
1-Idan Allah ya so, sai ya sa kare ya kare muminai da suka fake a kogo a wani lokaci kuma sai ya sanya gizo ya yi saka a bakin kogon ya kare annabinsa daga sharrin abokan gaba.
2-Wata niimar Allah it ace sanya mutane su yi barci mai tsawo.
Yanzu kuma mu saurari karatun aya ta 19 da 20:
وَكَذَلِكَ بَعَثْنَاهُمْ لِيَتَسَاءلُوا بَيْنَهُمْ قَالَ قَائِلٌ مِّنْهُمْ كَمْ لَبِثْتُمْ قَالُوا لَبِثْنَا يَوْماً أَوْ بَعْضَ يَوْمٍ قَالُوا رَبُّكُمْ أَعْلَمُ بِمَا لَبِثْتُمْ فَابْعَثُوا أَحَدَكُم بِوَرِقِكُمْ هَذِهِ إِلَى الْمَدِينَةِ فَلْيَنظُرْ أَيُّهَا أَزْكَى طَعَاماً فَلْيَأْتِكُم بِرِزْقٍ مِّنْهُ وَلْيَتَلَطَّفْ وَلَا يُشْعِرَنَّ بِكُمْ أَحَداً{19} إِنَّهُمْ إِن يَظْهَرُوا عَلَيْكُمْ يَرْجُمُوكُمْ أَوْ يُعِيدُوكُمْ فِي مِلَّتِهِمْ وَلَن تُفْلِحُوا إِذاً أَبَداً{20}
19- "Kamar haka Muka tashe su don su rika tambayar jũnansu. Wani mai tambaya daga cikinsu ya ce: "Mẽne ne tsawon zamanku?" Suka ce: "Mun yi zaman kwana daya ko sashen kwana." Sannan kuma suka ce: "Ubangijinku ne ya fi sanin tsawon zaman da ku ka yi. Sai ku aiki dayanku da wannan azurfa ta ku cikin gari, sai ya ga wanne irin abinci ne ya fi tsarki, to sai ya zo muku da abin da zaku ci da wannan kudi zasu saya. Kuma ya yi taka-tsantsan kada wani ya shaida ku." 20- "Hakika idan suka san da zaman ku to zasu jefe ku, ko kuma su mai dã ku cikin addininsu kuma da ba za ku rabauta ba har abada."
Wadannan ayoyi kuma suna bayani kan maganganun da mutanen Ashabul Kahfi bayan sun farka daga wannan dogon barci. Allah y ace kamar yanda ya sanya su cikin barci ta wata hanya ta musamman mai kama da mutuwa, haka ma ya farkar da su. A tsawon lokacin da suka zauna a cikin kogon sun yi sabanin raayi kan wani abu amma sai daga karshe suka ce sanin abin ya nag a Allah. Bayan da suka farka sun tashi da yunwa kum aba bu abinci a kogon saboda haka sai suka aiki wani daga cikinsu ya je gari ya sayo musu abionci ya dawo. Amma lokacin day a sayi abinci ya mika kudi sai mutanen dfa suka sayar mas ada abincin suka ga cewa kudin day a biyar irin da zamanin da ne sai suka yi shakkunsa suka sanar da jamaa da kuma sarkin garin.
Darusa:
1-Labarin Ashabul Kahfi wato mazauna kogo misali ne mai bayyana ikon Allah.
2-Mumini dole ne ya zama mai basira da kula gwargwadon iko saboda ya kiyaye addini ko da yake akwai yiwuwar abokan gaba su fito ta wata kofar.
Yanzu kuma mu saurari karatun aya ta 21:
وَكَذَلِكَ أَعْثَرْنَا عَلَيْهِمْ لِيَعْلَمُوا أَنَّ وَعْدَ اللَّهِ حَقٌّ وَأَنَّ السَّاعَةَ لَا رَيْبَ فِيهَا إِذْ يَتَنَازَعُونَ بَيْنَهُمْ أَمْرَهُمْ فَقَالُوا ابْنُوا عَلَيْهِم بُنْيَاناً رَّبُّهُمْ أَعْلَمُ بِهِمْ قَالَ الَّذِينَ غَلَبُوا عَلَى أَمْرِهِمْ لَنَتَّخِذَنَّ عَلَيْهِم مَّسْجِداً{21}
"Kamar haka kuwa Muka nũna wa (mutanen nasu) don su san cewa hakika alkawarin Allah gaskiya ne, kuma ita alkiyama ba bu kokwanto a gare ta, kuma ka tuna lõkacin da suke ta jãyayya tsakaninsu gane da al'amarinsu; sannan (wasu daga cikinsu) su ka ce: "Ku gina wani gini a kansu.' Ubangijinsu shi ne ya fi sanin lamarinsu. Wadanda suka yi rinjãye kan al'amarinsu suka ce: "Lalle za mu yi masãllãci a kansu (wato a kan kabarinsu)."
Kamar yanda muka fadi mutumin da mazauna kogo suka aika ya sayo musu abinci ya bad a kudi na shekaru 300 da suka wuce sai jamaa suka yi gayya suka nufi kogon. Shi kuma dan aikensu sai ya koma kogon da sauri da bayyana musu abin da ya faru. Da suka ji labarin da ya basu kan abinda ya gudana a gari sai suka yi addua suka roki Allah ya dauki rayukansu sai kuma ya amsa musu addua. Lokacin da jamaar gari wadanda suka nufi kogon suka isa can sai suka samu mazauna kogo sun mutu amma jikunansu lafiya lau suke duk da cewa sun zauna a kogon nan shekaru 300.Wannan ya na nuna ikon Allah kuma saboda haka wasu mutane sun bada shawarar a gina wani abu ko masallaci. Muminai na gaskiya da yake suna ganin wannan alama ta hakika ce mai tabbatar da gaskiyar addini saboda haka suka ce zasu gina masallaci don ya zama alama mai tunatar das u da Allah a koda yaushe.
Darusa:
1-Ya kamata a kula da alamun ikon Allah a tarihin mutanen da don su zama abin darasi da alumma.
2-Gina masallaci a makabartar waliyan Allah yana da asali a cikin Alkurani, saboda haka yin wani gini a kabarin waliyyai yana da kyau kuma idan masallaci ne.
To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na Surar Kahfi. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
Suratul Kahfi, Aya Ta 22-26 (Kashi Na 503)
- http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/audio/18/503.mp3
- http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/text/18/503.html
Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar Kahfi, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa.
To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 22:
سَيَقُولُونَ ثَلَاثَةٌ رَّابِعُهُمْ كَلْبُهُمْ وَيَقُولُونَ خَمْسَةٌ سَادِسُهُمْ كَلْبُهُمْ رَجْماً بِالْغَيْبِ وَيَقُولُونَ سَبْعَةٌ وَثَامِنُهُمْ كَلْبُهُمْ قُل رَّبِّي أَعْلَمُ بِعِدَّتِهِم مَّا يَعْلَمُهُمْ إِلَّا قَلِيلٌ فَلَا تُمَارِ فِيهِمْ إِلَّا مِرَاء ظَاهِراً وَلَا تَسْتَفْتِ فِيهِم مِّنْهُمْ أَحَداً{22}
"Zã su ce: "Su uku ne, na hudunsu shi ne karensu." Kuma sunã cẽwa, biyar ne na shidansu ne karensu don lalube cikin duhu, (wasu) kuma sunã cẽwa su bakwai ne na takwas dinsu kuma karensu. Ka ce: 'Ubangijĩna shi ya fi sanin yawansu, bã wanda ya san lamarinsu sai yan kadan." To kada ka yi jãyayya game da alamarinsu sai dai a kan abin da yake fili kuma kada ka bai wa wani daga cikinsu fatawa game da su.
Wannan aya tana bayanin cewa, bayan abinda ya faru da mazauna kogo, zamani zai zo da jamaa zasu yi jayayya dangane da su. Maimakon su yi tunani kan manufar wannan lamari sun tsaya suna jayayya kan adadin mutanen da suyka zauna a cikin kogon, kowanne suna cewa adadinsu kaza ne, alhali kuwa ko su uku ne ko biyar ko bakwai ne bas hi da wani babmbamci kuma ma zai yi tasirin komai ba a imaninsu ko ainiknsu ba. Amma yawa yawn mutane suna zato ne kawai kuma ko da akan abinda ba su sani ba ma suna son su fadi raayinsu a kansa. A wannan aya Allah ya na fada wa manzon sa cewa kada ya yi jayayya da muatne kuma kada ya tambayesu komai, Allah ne ya san adadin mazauna kogon.
Darusa:
1-Abinda ba mu sani ba kada mu yi ta zato da kame kame, kuma mu guji yin jayayya a kansa.
2-Wajen binciken alamuran da suka faru a tarihi ya kamata mu yi tunani da daukar darasi ba wai mu tsaya jayayya kan adadi ko mutane ba. Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 23 da ta 24:
وَلَا تَقُولَنَّ لِشَيْءٍ إِنِّي فَاعِلٌ ذَلِكَ غَداً{23} إِلَّا أَن يَشَاءَ اللَّهُ وَاذْكُر رَّبَّكَ إِذَا نَسِيتَ وَقُلْ عَسَى أَن يَهْدِيَنِ رَبِّي لِأَقْرَبَ مِنْ هَذَا رَشَداً{24}
"Kada kuma ka ce ga kowane, "Hakikazai aikatã wannan gõbe."
"Sai dai ka ce 'Idan Allah Ya so'. Kuma ka ambaci Ubangijinka idan ka manta, kuma ka ce: "Ina kaunar Ubangijĩna ya shirye ni zuwa ga mafi kusa da daidai gane da wannan."
Wadannan ayoyi suna bayanin wata doka da ta shafi kowa da kowa koda yake suna Magana ne da Annabi kai tsaye, amma dukan Musulmi dole ne su kiyaye dokar. Ayoyin suna baynin cewa a duk Magana ko aiki da za a yi a nan gaba ya kamata mumini ya ce in sha Allah a duk lokacin da zai ce zai aikata wato y ace idan Allah ya so. Dalilin wannan shi ne saboda mai magana da mai ji duk su san mahinta cewa abionda mai magana yake fadi said a yardar Allah ne zai iya aikata shi, idan kuwa Allah bai so ba babu abinda yake faruwa. Wato masu imani suna dogara da Allah kuma suna cewa in sha Allah, kamar dai yanda Alkurani ya kawo a cikin maganganun wasu annabawa kamar Yakubu, Shuaibu, Haliru da Ismail. Fadar wannan magana ba wai a kan fatar baki ne kawai, hakan yana bayyana imani da mahangar Musulmi ne wanda ya ke ganin cewa babu abinda zai iya faruwa said a izinin Allah.
Ko da yake kowane mutum yana da nufi da zabi amma faruwar kowani aiki baya dogara kan nufin mutane saboda akwai wasu dalilai da hujjoji da ya wadanda suke da tasiri wajen faruwar wannan abu. Lallai ba bu abin da zai tabbata sai idan Allah ya so.
Darusa:
1-Ka da mu dogara kan kokarinmu da dabararmu. Ka da mu dauka muna da yancin ya ba ikon Allah cikinsa saboda haka kada mu manta da Allah wajen daukar ko wane mataki.
2-Idan annabawa suna bukatar shiryarwa daga Allah a alamuransu na rayuwa, ina ga batun mud a ba annabawa ba? Saboda haka har a kullum mu nemi Allah ya nuna mana mafi kyawun hanya. Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 25 da ta 26:
وَلَبِثُوا فِي كَهْفِهِمْ ثَلَاثَ مِئَةٍ سِنِينَ وَازْدَادُوا تِسْعاً{25} قُلِ اللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا لَبِثُوا لَهُ غَيْبُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ أَبْصِرْ بِهِ وَأَسْمِعْ مَا لَهُم مِّن دُونِهِ مِن وَلِيٍّ وَلَا يُشْرِكُ فِي حُكْمِهِ أَحَداً{26}
"Suka kuwa zauna cikin kõgonsu shẽkaru darĩ uku kuma suka kara tara. "Ka ce: 'Allah ne Mafi sanin tsawon zaman da suka yi.' Asirin da yake cikin sammai da kasa na sa ne. Wa yake da ji da gani irin na sa! Bã su da wani mataimaki in ban da shi; ba ya kuma tãrayya da wani a cikin hukuncinsa."
Wadannan ayoyi suna ci gaba da bayani kan mazauna kogo wato Ashabul Kahfi tana cewa, Da ikon Allah sun zauna cikin kogon nan shekaru 309. Bisa dabi'a su da suka yi wadannan shekaru suna barci da kuma sauran mutane, ba wanda yake da labarin wannan tsawon lokaci, Allah kadai ne ya san da wannan labari kuma shi ya san yanda suka zauna a cikin kogon ya kuma kiyaye su suna barci. Babu shakka rayuwa har shekaru 300 da doriya ba tare da cin abinci da ko shan ruwa ba mujiza ce daga mujizojin Allah. Hakika Allah ya kare rayuwar mutanen kogo a duk wannan zamani domin ya zama darasi ga masu zuwa nan gaba.
Darusa:
1-A duk wurin da adadi ko alkaluma suke da muhimmanci wajen fassara wani abu to ya kamata a ba da alakluman daidai. Adadin shekarun da Ashabul kahfi suka zauna cikin kogo yana nuni da girman ikon Allah a wannna alamari.
2-Ubangiji shi ne mamallakin komai shi ne kuma mai ba da doka, shi ne masanin komai ko bayyane ko boye saboda haka ba mai iya gudu a tsere wa ikonsa a fake a bayan wani, sai dai a gudu daga wani a fake a wurin Allah.
To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na Surar Kahfi. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
Suratul Kahfi, Aya Ta 27-31 (Kashi Na 504)
- http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/audio/18/504.mp3
- http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/text/18/504.html
Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar Kahfi, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa.
To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 27: وَاتْلُ مَا أُوحِيَ إِلَيْكَ مِن كِتَابِ رَبِّكَ لَا مُبَدِّلَ لِكَلِمَاتِهِ وَلَن تَجِدَ مِن دُونِهِ مُلْتَحَداً{27}
"Ka karanta abin da aka yi wo maka wahayi da shi daag littãfin Ubangijinka. Bãbu mai canja kalmõminSa kuma bã zã kã sãmi wata mafaka ba in ba ta wurinsa ba.
A karshen labarin Ashabul Kahfi wannan aya tana magana da Annabin Musulunci Muhammadu dan Abdullahi (tsira da amincin Allah su ntabbata a gareshi da alaten gidansa) tana cewa, maganganu marasa hujja da surkulle dangane da wadanan suna da yawa, amma ka fada wa mutane bayanin da ya zo maka cikin wahayi ka fita sha’anin abinda wasu suke fada. Masu saba wa Annabi saboda dalilai daban daban suna bukatar ya sauya wasu ayoyi ko ya canya su domin su yarda da abinda suka kunsa, amma wadannan ayoyi suna nuna cewa kada Annabi ya kula su ya kuma ce musu Alkurani zancen Allah ne kuma baya yiwuwa a canja shi kuma duk wanda ya aikata haka ba zai sami kariya daga azabar Allah ba.
Darusa:
1-Alkurani maganar Allah ce ba ta mutum ba, saboda haka babu hanyar sauya shi a da balle kuma a yanzu.
2-Alkurani shi ne littafin Allah na karshe kuma an kare shi daga dukkan nau’o’in canji kuma ba ya bukatar wani littafi saukakke domin gyara abinda hala mutane zasu sauya daga cikinsa, domin ba bu canjin da zai same shi.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 28: وَاصْبِرْ نَفْسَكَ مَعَ الَّذِينَ يَدْعُونَ رَبَّهُم بِالْغَدَاةِ وَالْعَشِيِّ يُرِيدُونَ وَجْهَهُ وَلَا تَعْدُ عَيْنَاكَ عَنْهُمْ تُرِيدُ زِينَةَ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَلَا تُطِعْ مَنْ أَغْفَلْنَا قَلْبَهُ عَن ذِكْرِنَا وَاتَّبَعَ هَوَاهُ وَكَانَ أَمْرُهُ فُرُطاً{28}
"Ka kuma hakura wa kanka (da zama) tare da wadanda suke bauta wa Ubangijinsu sãfe da maraice, sunã neman yardarSa. Kuma kada ka kawar da idanunka daga gare su kanã neman adon rãyuwar dũniya. Kuma kada ka bi wanda Muka shagaltar da zũciyarsa daga ambaton Mu, kuma ya bi son ransa, wanda kuma al'amarinsa ya zama ketare haddi ne.
A cikin labaran tarihi an bayyana cewa wasu manyan mutanen kabilar Kuraishawa sun gabatar wa Annabi da sharadin sai ya kori talakawa marasa daraja a idon jamaa da kuma maida hankalinsa ga sauraron manyan gari da mnasu hamnnu da shuni don su yi imani da sakon Manzon Allah. A cikin tsurin ido da rashin ladabi suka ce da Annabi, ‘Ba zamu taba zuwa majilisinka ba kum aba zamu saurtari maganaerkja ba idan dai wadsnmnan mutane makasta\\kantya suna taree da kai.’ A zamanin Annabi Nuhu ma mutaensa masu jin ceewaa su manya nne sun yi irin wanna bukata, shi kuma sai ya mayar musu fda martini cewa ba zai rab u tad a munminai saboda talkaucinsu ba. Wanna aya tana sukar irin wanna tunani , tana cewa kada Annabi ya saurari wannan yaudara tasu ya kuma kori muminai na gari kamar Abu Zar da Salman ya kore su saboda talauci ko karancin abin hannunsu, ko kuma ya yi ta fama yana bin mutanen da duniya ta aure ko kuma suka mance da ambaton Allah wai dominsu yi imani, wadanda kuma uske bi son zuciyarsu kuma basu da niyar barin bauta wa duniya.
Darusa:
1-Zama da tausaya wa talakawa ya na da wahala amma muminai talakawa sun fi kafirai masu dukiya daraja kuma alummar Musulmi su yi cikakkiyar kulawa da talakan Musulumi.
2-Hadarin da neman duniya yake yi wa jagorannin alummar Musulmi ya kai munin da har Allah yana yi wa Annabinsa kashedi a kansa.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 29: وَقُلِ الْحَقُّ مِن رَّبِّكُمْ فَمَن شَاء فَلْيُؤْمِن وَمَن شَاء فَلْيَكْفُرْ إِنَّا أَعْتَدْنَا لِلظَّالِمِينَ نَاراً أَحَاطَ بِهِمْ سُرَادِقُهَا وَإِن يَسْتَغِيثُوا يُغَاثُوا بِمَاء كَالْمُهْلِ يَشْوِي الْوُجُوهَ بِئْسَ الشَّرَابُ وَسَاءتْ مُرْتَفَقاً{29}
"Kuma ka ce: "Gaskiya daga Ubangijinku take." To wanda ya so sai ya ba da gaskiya, wanda kuma ya so sai ya kãfirta, hakika kam Mun tanadar wa azzãlumai wuta wadda katangarta ta kẽwaye su, idan kuma suka nẽmi taimako to za a taimake su ne da ruwa irin na narkakkiyar darma wanda yake toye fuskoki; abin sha ko ya yi mũgunta, makoma kuma ta munana.
Domin amsa maid a martabi kan bukatun wadannan gafalallun masu dukiya wannan aya ta bmna cewa, ai ba wanda yake bukjatar imanin da zasu yi balle nma su sanya wannan sharadi. Maganar gaskiya ta sauka dagha kuma duk wanda ya ga dama ya yi imani duk kuma wanda ya ga dam aya kafirce. Imani ai ba abinda zaa roki wani ya yi bane; mumini daya na hakika ya fi kafirai dubu da zasu ce wai sai da wani sharadi zasu imani. Dadin dadawa ma, mutanen da suka nitse cikin fasadi da bautar ciki a nan duniya, zasu gamu da wurin zama da abinci da abin sha mafiya muni a lahira. Ka da ka dubi rayuwarsun ta wannan duniya wacce gajera ce mai wucewa.
Darusa:
1-Kafirci ko imaninn mutane bas u da wani tasirei wajen tabbatar da gaskiyar addini. Alkurani gaskiya ne koda dukkanin mutane zasu kafrice masa.
2-Koda yake mutane suna da yancin zabar imani ko kuma kafirci amma a karshen aikin kowane daya wadannan daga cikinsu zai hadu da sakamakon daban da na dayan kuma a lahira kafirai zasu gamu da azabar wuta.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 30 da ta 31: إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ إِنَّا لَا نُضِيعُ أَجْرَ مَنْ أَحْسَنَ عَمَلاً{30} أُوْلَئِكَ لَهُمْ جَنَّاتُ عَدْنٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهِمُ الْأَنْهَارُ يُحَلَّوْنَ فِيهَا مِنْ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٍ وَيَلْبَسُونَ ثِيَاباً خُضْراً مِّن سُندُسٍ وَإِسْتَبْرَقٍ مُّتَّكِئِينَ فِيهَا عَلَى الْأَرَائِكِ نِعْمَ الثَّوَابُ وَحَسُنَتْ مُرْتَفَقاً{31}
"Lalle ne wadanda suka yi ĩmãni kuma suka yi aiki na gari hakika Mu ba Mu tõzarta lãdan wanda ya kyautata aiki."
"Wadannan sunã da gidãjen Aljanna na dawwama wadanda kõramu ke gudãna daga karkashinsu, anã sanya musu kawa, a cikinsu, daga mundãye na zinariya, kuma sunã tufantar wadansu tũfãfi kõre, na alharĩni rakĩki da alharini mai kauri sunã kishingide a cikinsu,a kan, karagu. Mãdalla da sakamakonsu. Kuma Aljanna ta kyautatu da zama wurin hutãwa."
Wadannnan ayoyi suna bayanin matsayin muminai sana cewa, su wadannan talakawan da ku ke gani a nan duniya , idan masu biyayya ne ga Annabi da rikon da tafarkin Allah kamar yanda ya dace, a ranar alkiyama zaa saka musu da mafi kyaun wurin zama, wurin da masu dukiya a nan duniya zasu yi dokin su zauna a cikinsa koda na dan lokaci ne. Idan a yau masu mukami suna sanya tufafi na alfarma da kayan ado masu tsada, suna daukar kansu masu girma, to ai su kuma matalauta a ranar lahira zasu sami tufafi da kayan ado wadanda ba za a iya kwatantasu da kayan adon wannan duniya ba. Amma fa marasa galihun zasu sami wannan jin dadi a lahairan ne idan sun yi imanin kwarai da ayyuka na gari, wanda kuma su ma masu dukiya idan sun yi biyayya ga Allah suka nisanci girman kai da sauda yawa dukiya take sa mutum, zasu sami sakamako mai kyau da jin dadi a lahira.
Darusa:
1-Abin da muminai suka rasa a nan duniya saboda bioyayya ga dokokin Ubangiji, a ranar alkiyama Allah zai mayar musu da gurbinsa da abin da fi shi dadi da kuma kyau.
2-Mu yi aiki domin Allah, aikin da ba zai rage mana ladanmu ba kuma ladansa ba irin ladan nan ne mai karewa nan take ba.
To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na Surar Kahfi. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.